Ni da Abokin Babana Complete Hausa Novel




 Compiled by Umar Dalha.



NI DA ABOKIN BABA NA....!!*

              ©JeedderhLawals


                      01


A nutse nayi sallama dakin Daddy na, dakin a shimfide yake da tattausan carpet sakar hannu kirar kasar India, ruwan hanta ne kamar yadda jeren kayan dakin suke.  A hankali na zauna a kusa dashi ina kallon yadda yake sarrafa laptop dake hannunshi cikin kwarewa, ganin bashi da niyar dawo da hankalinshi gare ni, dama dai nasan halin baba in dai yana aiki baya maida hankalinshi ga kowa har ni er gaban goshin shi kuwa har sai ya gama. Remote na dauka na canza channel daga sports zuwa Zee World. Na ma manta ranar suna shirin da nake nacin kallo, Love Look Like What You Made Me Do.  Dan Murmushi nayi nace woah, ni na ma manta da shirin nan. Daddy ya dan yi glancing din wajen da nake zaune ya kafin ya maida hankalinshi ga laptop dinshi. A takaice har aka gama shirin suka fara tallace-tallace Daddy bai gama abinda yake yi ba. Ba a jima ba naji na fara hamma, remote na dauka na mayar mishi da tashar da yake kallo na mike, daidai lokacin daya rufe laptop din nashi ya kalle ni cike da kulawa. "Uwata, ya aka yi ne?" sunan mahaifiyar shi gare ni shi yasa yake kirana da Uwata, su Mommy kam Ummi suke ce min. Baki na turo cikin dan jin haushi nace "ni barci nake ji..... Sai da safe!" er dariya yayi ya kamo hannuna ya rike ya janyo ni na koma kusa dashi na zauna ina kara tura baki na. Kumatu na ya dan ja, "ohhh m soooo sorry princess, na tsaida ki koh? Akwai muhimman bayanai dana tura ne yanzun shi yasa, ayi hakuri. Gobe zamu je mu sha ice cream ni da princess dina, are we good now?" kaina na kawar daga kallonshi, yasa hannu ya juyo da fuskata zuwa gare shi, "hey, m trying to pay for what I did, aren't we good yet?" bansan lokacin dana yi er dariya ba ganin yadda yayi da fuskarshi, Ina son babana fiye da tunaninku saboda yana sona sosai, kaunar da yake min ko mahaifiyar data haife ni bata nuna min kwatankwacinta. Ban sani ba ko don hakan yana da nasaba da cewa ni Kadai ce diyar su??. Kai na girgiza ina dan murmushi, "naji na hakura, but we will also go for shopping, agree??" ya gyada kai, yes. Tashi tsaye nayi nace to sai da safe Daddy. Murmushi yayi, ki tashi lafiya Uwata. 


A main parlour naci karo da Mummy, da alamun turaka zata tafi ganin yadda taci kwalliya, ba wai ta fuska ba, ta jiki sai tashin kamshi take. Murmushi nayi naje na rungumeta, "Mommy sai da safe!" bayana ta dan shafa, "OK, sweet dreams baby" ta sake ni ni na wuce dakina ita kuma ta tsaya tana kashe wutar falon. 


        Ina shiga dakina wuta na kunna na shiga zare kayan jikina daya bayan daya, towel na zara na daura a jikina na fada toilet din dake manne a dakina. Cikin bathtub na shiga na zauna bayan na tara ruwa mai dumi, ban jima a ciki ba na fito. A cikin toilet nayi shafe shafen da zanyi, na fito. Kayan barci na saka marasa nauyi, kayan dana bari a tsakar daki na tsince na watsa cikin kwandon da nake tara kayan datti don nasan idan na bari Mommy ta gani gobe sai raina ya baci. Mommy mace ce mai tsabta da bata jurar kazanta ko ta anini. Kan katoton gadona nayi tsalle na haye kamar wata karamar yarinya, wayana na cire daga jikin socket na kunna data, social media na shiga na fara chat da friends dina. Ban samu barci ya dauke ni ba sai wajen karfe goma sha biyu na dare. Ban jima da fara barci ba naji numfashi ya fara min wahalar shaka, rigar jikina na fara adjusting daga jikina, ji nake kamar ita ta shake min wuya na kasa numfashi. Daga karshe tashi nayi gabadaya na cire rigar na jefar kasan gado na koma na kwanta. Dama don dole nake saka riga idan zan kwanta saboda fadan Mommy, ban cika kwanciya da riga a jikina ba saboda a yawancin lokuta na kan ji kamar rigar na shake ni ne, ban sani ba hakan sabo ne ko kuwa hali ne ko cuta? Ban sani ba, n I don't give a damn akan lallai sai na sani.


                    *☆☆☆☆☆*


Kiran sallar asubahi a cikin kunnena da yake masallacin unguwar mu a jikin gidanmu yake. Na saki gurnani a hankali saboda barcin daya cika min ido, da kyar na samu na iya bude idanuna suna komawa suna rufewa, na dauki kusan mintuna biyar kafin na iya tashi zaune, gashin kaina daya tattare ya barbaje min a fuska na tattara na maida shi baya, a hankali iska ya shiga kada sassan jikina hakan ya ankarar dani yanayin da nake ciki na babu riga, da sauri na dira daga kan gadon na dauki rigata na saka. Daidai lokacin Mommy ta leko, ganina a tsaye yasa ta maida kofar ta rufe ba tare da ta min magana ba. Sighing na danyi softly cike da jindadin bata kama ni ba. Bandaki na fada direct na dauro alwala, nazo nayi sallah na zauna Ina lazumi har sai da gari ya danyi haske, tashi nayi na fita daga dakina. Sai dana je na gaida Daddy sannan na shiga kicin inda na samu Mommy da Mama Sauda wadda take taya ta en aikace-aikace suna ta kokarin hada break fast, a nutse na gaida su sannan nima naje na kama musu. 


Muna gamawa na koma daki nayi wanka na fito, na bata lokacina sosai wajen fente fuskata da nau'in kayan kwalliya Kala-kala kamar wadda zata je biki. Sai dana gamsu da kwalliyar fuskata sannan na tashi na bude wardrobe dina wadda take shake da kaya kamar na mutane biyar ko fi. A hankali nake kare musu kallo har idanuna ya sauka akan wata atamfa cote d'voire ruwan coffee wadda aka mata zane da peach da yellow a jiki, dinkin riga da siket ne. Siket din pencil ne sai rigar doguwa don ta kusa kai kin gwiwa, ita kuma dinkin ya kama ni cif daga kirjina, daga uku ne ya saki sosai yayi baza. Ina gama saka kayan nayi simple daurin dan kwali, na dauko gyale mai dan fadi peach color da er karamar jakar vincci na rataya na fita bayan na dauki wayar hannuna da takalmi coffee color mai dan tudu. Akan dinning na samu Mommy da daddy har sun fara karyawa, duka kallona suka yi ganin yadda naci kwalliya cike da alamun tambaya. Kujera naja na zauna a kusa da daddy ina kallonsu, "School zan shiga in amso IT letter na daddy"  daddy ya gyada kai yaci gaba da cin kosan shi yana korawa da kunun gyada mai gardi, nima kunun gyadar na tsiyaya a cup na bude nadarar peak na kara a ciki na fara sha. A nutse muka gama cin abincin, na tashi na dauki jakata tare da yafa gyalena Ina kallonsu, "Mom, Dad, zan wuce sai na dawo" mom tace Allah ya kiyaye, daddy yace "ko dai in sa driver ya kaiki tunda ba jimawa zaki yi ba?" kai na girgiza, noo daddy, zan bi bus kawai. Ya gyada kai, "kudi pa?" nan ma kai na girgiza, "I've enough money wit me daddy" nan ma kai ya gyada, "OK, take care baby" Murmushi nayi na juya na fita cike da jindadin yadda iyayena suke kulawa dani, ta kowane fanni ni kam sai dai in godewa Allah daya bani iyaye kamar su.


[12/9, 8:26 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!* 

                      ©JeedderhLawalS



                            *02*


       Bus na hau directly har kofar gate din  KadPoly inda anan nake karatun Diploma na akan Science Lab Tech. Kasancewar an tafi hutu makarantar babu mutane sai tsilli-tsillin wadanda basu tafi hutu ba kawai, a hankali nake takawa har cikin ofishin IT coordinator namu na karbi IT letter na na fita. Hostel din mata na wuce daga can dakin kawata Ramla don nasan bata tafi hutu ba, ila kuwa, Ina sallama cikin dakinsu muka ci karo da juna. Cike da doki muka rungumi juna muna juyi a tsakar dakin kafin daga karshe muka dire a Kan gadonta muna dariya. Kallona tayi tun daga sama har kasa har sama, ta gyada kai tana er dariya, "inye diyar daddynta! Wannan fresh haka kamar wadda aka wanke da inji?" duka na kai mata a cinya Ina dariya, "ke ba baki da mutunci Ramla, duk uban kashin wannan dana tara a wuya zaki ce wai nayi fresh?" sai da muka gama shakiyancinmu na abokai sannan na kalleta, "ke ni ba wannan ba, ya zancen inda zamu je muyi IT ne don ban karbi letter na da wuri ba ban sani ba cikin wajajen da suka bamu ko zan samu?" Ta girgiza kai, "duk an cika a wajen pa gaskiya babu, nima tun last week na kai nawa suka ce wae an cika" fuskata ta dan yamutse, "lallai! Ya zanyi kenan?" kafada ta daga, "oho! Bake wae dadi gida ba kinje kin zauna kina hutu ba? Gashi next week zamu fara. Ni a Kano zanyi nawa" na kalleta "Kano? A Ina??" "cikin BUK, kin san Aunty Habi tana aiki da Lab dinsu, shine tace in je can inyi kawai. Har an kai letter sunyi accepting. Abinda ya shigo dani makarantar kenan na kawo accepting letter din" shiru nayi ina jijjiga kai, "Ramla ko dai nima can zanje inyi nawa IT din kawai? Nasan mawuyaci ne in samu waje anan" ta kalleni, "wa kike dashi a Kano?" nace oho! Daddy yana da mutane da dama acan, nasan ba za a rasa ba. Idan can dinne sai in dinga zuwa weekend gida..... Zan tambayi daddy inji dai tukun. Yaushe zaki tafi Kanon?" "ranar assabar kila" ta bani amsa. Na gyada kai kawai. Kayanta na tayata hadawa, tare muka fito da ita na janyo mata trolley ita kuma tana jan karamar jaka. Muna tafe muna hira da ita har bakin gate, anan muka ci karo dashi, My Crush!. Wata irin farinciki da murna suka rufe ni, Ya Allah ji nayi kamar in daka tsalle. Ta gaban mu ya wuce without glancing at us, duk yadda naso in daure kasawa nayi, ban san lokacin dana kira shi ba. "Muneer!!" cikin wata iriyar murya mai kama da whisper, duk da haka sai daya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo ya kalleni, Kai na sadda kasa ina jin wasu irin abubuwa na min yawo a jiki. Cikin siririyar muryar shi da zan iya cewa ita tafi daukar hankalina game dashi yace, "ohh Ummie, ya kike?" Murmushi na saki a hankali kaina a kasa, nace "lafiya qalau, ya karatu?" "Lau..." ya amsa, "....bari in wuce sai anjima..... By the way, I like ur dressing" bin shi nayi da kallo yana tafiya a nutse ina wani irin murmushi kamar kumatuna zasu hade da kunnuwana. Sai dana daina ganin kurar shi sannan na maida Kallona ga Ramlah wadda ta coge a gefe tana jifana da harara, murmushi kawai nayi tare da daga mata kafada naja trolley din nayi gaba. Tsaki taja ta biyo bayana, "wallah Tallahi Babe kina bashi haushi a rayuwa akan Muneer dinnan, kin rabe wa namiji yana yazga ki. Yanzu kaf fadin KadPoly waye bai san cewa kina crushing din wannan player din ba, abun haushi ma da alamun baya yi dake!" fuska na hade sosai. Abinda ke hada ni da ita kenan, kushe Muneer. Bata damu da yadda na hade fuska ba taci gaba, "haba babe, ki daina bayar damu mana. There r so many guys out there ciki da wajen makarantar nan dake karakaina akan ki, don Allah ki kyale wancan yaron. Ba son ki yake yi ba!" a fusace na kalleta, "yeah right! Ai dama ban ce miki yana so na ba koh? Hakan bai dame ni ba, inda rai da rabo, zan ci gaba da bibiyarshi kuma har sai ya so ni Ramlah! Idan hakan yana bata miki rai ki kauda idanun ki daga gare mu, dats all" Kallona ta tsaya tana yi kawai, ba wai yau muka saba irin wannan musun ba in dai akan Muneer ne, Kai ta girgiza a hankali tare da furta Allah ya ganar dake! Cikin gatse na amsa da Ameeen. Muka ci gaba da tafiya har bakin gate ba tare da kowa ya sake cewa komi ba, dama zuciya ce ta kowa a wuya, magana kadan sai ta tunzura mu. Muna fita bakin gate kowa yayi nashi bangaren, ita ta hau motar Abuja ni kuma na dau drop din tricycle har Unguwar Rimi. 


Lokacin dana isa gida karfe sha biyu na rana bata karasa ba, kayan jikina na cire na saka na shan iska marasa nauyi na tafi kicin. Tare da Mommy muka hada abincin rana, ta shiryawa daddy nashi a cikin wani katon Basket mai kyau har da wani kayata shi da roses. Wannan Al'adar tunda na tashi naga Mommy tana yin ta, Indai daddy yana gari to abincin shi daga gida ake kai mishi, ba zan boye ba, abin yana burge ni, ina da niyar yin wannan Al'adar idan nayi aure. Direba ta ba ya kai mishi ofishin kula da harkar shigi da ficin jirage ta jahar Kaduna inda anan ne yake aiki a matsayin President na wajen. Ni kam sallah nayi sannan na fito dinning din, tuwon semovita ne muka yi da miyar danyen kubewa wadda ta sha busasshen kifi da tantakwashi da man shanu sai tashin kamshi take yi, sai zobo mai sanyi Shina anyi decorating dinshi da fruits. Muna hira da Mommy jefi jefi muna cin abincin na gaya mata yadda muka yi da Ramlah game da IT dina, shiru tayi tana Kallona kafin tace "zaki iya kuwa Ummi?" er dariya nayi, "haba Mom! It's not like ban taba zaman Kanon nan bane. I will b fine, after all anan zan dinga yin weekend dina ai" kai ta gyada, "sai ki jira daddyn ki ya dawo".

   

      Koda na fadawa daddy abinda ake ciki ya dan nuna damuwarshi akan gida da zan bari, yace "Uwata tafiya zaki yi ki barmu mu biyu ne a cikin gidan nan kamar mayu?" ni kaina kuma sai a lokacin naji jikina ya fara sanyi, a sanyaye nace to daddy ko dai zan bari ne sai shekara mai zuwa sai inje? dariya suka saki shi da Mommy, daddy yace "oh ma silly princess! M not that wicked da zan hana ki karatun ki, bari in kira Dr. Ibrahim abokina ne, lecturing yake yi a BUK sai muji yadda za ayi" muna zaune ya kira shi suka gama magana suka yi sallama, "wai yace zaki samu sai dai a microbiology lab din su" Murmushi nayi, "daddy kasan fa dama nace maka idan na gama wannan program din zan nemi microbiology a ABU" yace faduwa tazo daidai da zama kenan? Na gyada kaina Ina Murmushi. Yace gobe zan tura mishi letter din sai a kai, Allah sarki princess dina zan yi kewar ki!.


Da dare kuwa kamar yadda daddy ya min alkawari muka fita, chicken republic muka je ya sai min gashin kaji muka tsaya a freeze center ya sai mana ice cream da tarkacen snacks muka koma gida. Tare muka zauna muka ci komi, sauran kayan mommy ta je ta adana su. Mun danyi hira dasu kadan har zuwa karfe tara da rabi, kafin na musu sallama na wuce dakina. Kayan barci nasa na kwanta a rub da ciki idanuna a rufe, daddy gaskiya ya fada. Tun yanzu nake ji kewar su tana dabaibaye ni, anya zan iya kuwa???!

[12/9, 8:30 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*

                      ©JeedderhLawalS



                            *03*


           Tun da muka gama hada breakfast na koma na kwanta barci, ban tashi ba sai wajen karfe goma na safe. Brush nayi na fita falo na karya, daddy ya fita wajen aiki. Dama dai Mommy full house wife ce, babu aikin da take yi. Shi yasa nace muku rayuwar auren iyayena tana matukar burge ni, Mommy tayi karatu har matakin masters akan Pharmacy amma daddy ya hanata aiki, duk wasu bukatu nata kuma ya dauke su ba kamar sauran mazajen yanzu ba da idan matarsu tayi karatu taki yin aiki sai labari yazo ya sha banban saboda ba zasu raba hidimomin gida tare ba. Wanka na shiga nayi, na fito na shirya cikin doguwar riga ta wani material grey mai dan nauyi, dinkin ya kamani tsam ya bi jikina, sai daga kasa ne ya baje sosai. Saboda yanayin kirar jikina dama ba wai kiba gare ni ba, er siririya ce ni amma fa Akwai kira, daga sama har kasa kam sai dai in gode Allah. Kalar fatar jikina baki ne, duk da ba wai can ba, zaku iya cewa chocolate color dai. Gyale na dauka na dora shi akan kafada ta na fita. Dakin mommy nayi knocking na shiga, tana zaune a gefen gado da dan littafin hisnul Muslim a hannunta. Kallona tayi na zauna a gefenta, a dan shagwabe nace "mommy dan Allah inje gidan Anty Uwani?" anty Uwani kanwar mommy ce, yaranta hudu duka maza, mun saba dasu sosai saboda zumuncin iyayenmu. Lokaci zuwa Lokaci na kan je can har in musu weekend. Mommy tace "kinga baki tambayi daddy dinki ba Ummie, babu ruwana pa!" kara shagwabe fuska nayi nayi nace "mommy da wuri pa zan dawo Allah" Kallona tayi na lokaci kafin ta gyada kai, "shikenan,  but kar ki kai yamma fa!" cikin murna na gyada mata kai. Cike da doki na tashi, har na fita na sake komawa, purse dinta na bude na zari dubu biyar na fita da sauri ina dariya, kallo kawai ta bini dashi. A Unguwar Rimi suke zaune, sai dana tsaya na sai dangin fruits a bakin hanya sannan na karasa gidan. A can na wuni sur, sai gab da magrib sannan ta sa direba da danta na biyu AbdulJalal wanda yake kusan sa'ana ne suka rako ni gida. Daddy har ya dawo, Allah ya taimake ni ban sha fada ba saboda Daddy baya son yawo ko kadan. Bayan sallar isha'i ina zaune ina kallon film din Kaabil daga cikin laptop dina Ramla ta kira ni, murmushi nayi da naga sunanta a jikin wayata, wato har ta gama fushin kenan?? Da er dariya ta na daga kiran, "Lauratu ya ne?" haka nake kiranta idan naso tsokana. Ina jin dan siririn tsakin data saki, "ke pa u r a prof a ruining mood din mutum wallahi, meye wani Laure kamar wata Goggo a kauyen kayau?" dariya na sheke da ita cikin tura haushi, hakan ya kara tunzura ta kuwa. Sai da na gama tsokanarta sannan na tsaya ina sauraronta, hakuri ta bani game da abinda ya faru ranar, nima hakurin na bata tunda dukanmu we are at fault. Daga nan hira muka hau yi da ita, mun share fiye da awa daya muna hira har sai dana gaji don ni dama can ba gwanar hira bace musamman ma hirar waya, sallama muka yi kowa ya ajiye wayarsa. 


      Da dare muna falon daddy mu duka muna en hirarraki, aka kira daddy a waya. En maganganu suka yi kafin ya ajiye wayar yana kallona, "Uwata kinji an karbi letter dinki pa!" ban san dalili ba, gabana ya fadi ras! Rasa abin cewa nayi kawai na tsaya ina kallonshi, yaci gaba, "ranar Sunday zaki tafi mun gama magana da Ibrahim din. Sai ki fara shiri koh?" jikina naji yayi sanyi sosai, kafin kace me! Hawaye sun fara min yawo a kumatuna, cike da damuwa daddy yake kallona, "Uwata lafiya?" kai na gyada mishi a hankali, "I just started missing u ne daddy!" Dariya ya saki yayin da mommy tayi murmushi, hannu na ya rike a tausashe, "ohh my loving princess.... We gonna miss u!" group hug muka hada kamar zamu yi kuka. 


Shirye-shiryen zuwa Kano na fara yi, hada tarkace, sallama da dangi da en abubuwa. Komi cikin sanyin jiki nake yin sa, wannan shine karo na farko da zanyi tafiya ta fiye da watanni uku. Daddy dinmu dan asalin garin Malumfashi ne ta Katsina, danginshi duk a Katsina suke zaune don haka mu kan je can idan mun samu hutu in musu kwanaki zuwa sati. Amma Ina jin wannan tafiyar ta banbanta, zuwa zanyi fa in zauna da mutanen da ban sani ba na tsayin watanni hudu zuwa biyar, a garin da ban sani ba duk da cewa mun yi zaman Kano na shekaru biyu, amma that was then, I think tun ina primary 5 ne??? Haka dai naci gaba da Shirye-shiryena har zuwa ranar Sunday. Sai wajen karfe biyar na yamma muka bar Kaduna, daddy ne ke jan motar, mommy na gefen shi ni kuma ina gidan baya. Tafiyar tayi min wani irin sauri, sai naga kamar muna tafiya ne akan iska ba kan kwalta ba. Cikin dan lokaci kankani mun isa Kano, unguwar Tal'udu muka wuce tunda anan gidan yake. Naji daddy yana ba Mommy labari game da abokin nashi, yace lecturing yake yi amma ba a staff quarters yake zaune ba, yace dan asalin garin Kano ne kuma yanzu haka yana neman kujerar dan Majalisa ne. Yaran shi uku da matar shi daya..., ni dai tunda naji yace yana harkokin siyasa na maida hankalina kan wayata, dan siyasa? Allah ya gani basu cika burge ni ba, ban son siyasa. 

Kugi na karshe da motar tayi a cikin garejin gidan ne, tun daga cikin mota nake karewa gidan kallo. Ba wai yanke hukunci kai tsaye ba, yanayin gidan tafiy kafin ace mallakin just a lecturer (sorry lecturers, m not underestimating ur payment or something). Gida ne hawa daya, parking lots din gidan cike yake da manyan motoci ba na wasa ba, ga bikes da kekuna ina ji na yaran shine. Daga nan kana iya hango wani dan karamin garden a can gefen gidan, har wani dan karamin wajen wasanni na gani. 

A hankali muka fito daga cikin motar, already wani da nafi kyautata zaton mai gadi ne ya fara kwasar kayana yana shiga cikin gidan dasu. Shi yayi mana jagora zuwa wani babban falo daya min kama da fadar uwargidan sarkin Kano, ya sha jere na wasu narka narkan leather seats kala biyu, farare da browns, ko wane jeren kaya yana da nashi dinning table, Plasma TV wadda zaka yi zaton zata cinye bangon falon saboda girmanta. Kafafunmu suka nutse cikin wani tattausan rug carpet kamar auduga, nayi iya bakin kokari na wajen ganin cewa ban hangame baki nayi kauyanci ba, maganar gaskiya ban taba shiga tsarraren falo irin wannan ba duk da cewa ba laifi nayi shige-shige a parlours da gidaje na manyan mutane, wannan kam looks extraordinary sosai. Kujera muka samu muka zaun 3 seats, ina tsakiyar su daddy, er aikin gidan ta fito daga kitchen ta gaida su daddy kafin ta shige wata kofa a cewarta zata kira madam. Ina jin lokacin da daddy yake gayawa Mommy ai Ibrahim din baya nan, yaje wani seminar. Ni dai ba baki, I was very nervous a lokacin. Mintuna kamar goma sai gata ta fito, Ya Allahu!! Meye wannan a gabana? Naji zuciyata tana tambaya lokacin da nayi tozali da matar. Don fari fa Akwai fari kamar Baturiya, kyawu ma Akwai shi Masha Allah, wata irin kiba marar fasali ne da ita. Lokacin data zauna akan kujera suna gaisawa dasu daddy sai naga ta shirge a waje guda kamar kayan wanki. Da kyar na iya saisaita kaina na dan zame daga kan kujerar na gaisheta, da er fara'ar ta ta amsa har da ambatar sunana, "Safeenah ko?" na gyada mata kai a hankali. Ta maida kanta gasu daddy suna er hira, idanuna suka ci gaba da wandering a cikin falon bana ma jin me suke fada. Aka kira magrib daddy ya fita sallah, ni da Mommy kuma muka yi a cikin falo don bamu samu albarkacin samun gayyata zuwa dakin matar gidan ba, kuma ba a nuna min inda zan zauna ba, karewa kayana ma suna nan baje a tsakiyar falon. 'yar aikin gidan muka tambaya ta nuna mana bayi dake nan cikin falon muka shiga muka dauro alwala, motar daddy naje na dauko prayer mat muka shimfida anan muka yi sallah abinmu.


Daddy yana dawowa daga sallah yace mommy ta tashi su tafi, nan fa idanuna ya raina fata da naga Mommy ta yiwa er aikin gidan magana akan taje ta gayawa matar gidan zasu tafi, idanuna suka yi raurau kafin kace me na fara hawaye shabe-shabe. Ba a dauki mintuna biyar ba sai gata ta fito tana taku da kyar, ban sani ba na takama ne ko kuwa dalilin kibar ta ne? Sallama suka yi dasu ta koma daki abunta. Hannuna mommy ta kama na musu rakiya har bakin motar su, zuwa lokacin kam kuka nake har da shessheka, suka saka ni a tsakiya suna lallashina har na samu kukan ya lafa. Ina nan tsaye suka shige mota suka ja suka tafi bayan na sha nasihohi daga gare su. Na bi bayan motar nasu da kallo har suka bar gidan aka maida gate aka rufe, na maida kallona ga dankareren gidan da zan rayu a ciki zuciyata cike da tarin damuwa iri-iri, daga can kasan zuciyata ina jin wata irin nadama na dabaibaye ni, Me ya kaini???? A hankali wasu siraran hawaye suka biyo kan Kumatu na.....! 


Just want to say thank u for those following me, commenting and voting on this story. Please keep it up, keep voting, comment, and share it with your friends...... 


                          T

[12/9, 8:32 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*


                      ©JeedderhLawalS


                            *04*


         Sai dana kwashe lokaci mai tsawo a cikin farfajiyar gidan a tsaye kafin na samu kwarin gwiwar jan kafafuna da kyar na koma falon. Ina shiga na ci karo da er aikin gidan wadda saboda tsabar wata irin shiga mara fasali da tayi yasa na kasa gane ko wace irin yare ce, cewa tayi in zo muje ta nuna min dakin da zan kwanta inji madam dinta, babu musu na dauki jakar hannuna na janyo daya daga cikin jakunkunan dana taho dasu nabi bayanta bayan itama ta dauko wasu. Abinda na kula duka dakunan gidan a falon kasa suke, ni tunda nazo ban ga kowa ya hau saman ba. Wani dan madaidaicin daki cikin jerin dakunan dake cikin falon ta bude muka shiga ciki. Dakin yana da fadi ba laifi, Akwai toilet a ciki ga wani medium size gado ruwan golden, mirror da closet sai er karamar sofa da study table. A tsakiyar dakin an malala wani tattausan circle carpet baki, sauran dakin kuwa malale yake da wasu en ubansun marbles fari da gold, well, ba laifi ya burge ni sai dai yadda aka tsara dakin ne sam bai min ba. A raina nace sai na canza shi. Ina ta karewa dakin kallo har ta gama shigo min da kaya na duka, ta tambayeni idan Akwai abinda nake bukata? Kai kawai na girgiza mata tare da mata godiya, ta min sai da safe ta wuce abinta. Jakar hannuna na jefa akan gado na samu gefen gadon na zauna Ina kara karewa dakin kallo, tashi nayi na leka toilet, Shima babu laifi ya hadu, na dawo na bude closet din babu komi a ciki sai er guntuwar kura data yi, tsumma na lalubo na goge ta tas na lalubo turaren kaya a cikin kayana na watsa a gefen closet din kafin na fara shirya kayana a ciki, sai dana cika ta tsil da kaya wasu ma da kyar suka shiga, na makare kan mirror na da tarkacen kayan shafa dana kwalliya da nau'in perfumes kamar a wani dan karamin super store. Sallar isha'i nayi na hada da shafa'i da wutiri, ina gamawa naji wayana tana kara, ringing din dana sakawa daddy ne. Da sauri na tashi na daga kiran, gaisawa muka yi ya fada mun sun isa gida lafiya, mun danyi hira kadan yaba mommy wayar itama muka dan yi hira, sai data kara min da en nasihu akan wadanda ta min sannan muka yi sallama na ajiye wayar. Ruwa na watsa a jikina na nemi kayan barci marasa nauyi na saka na kwanta, amma kwata-kwata barci yace bai san idanuna ba, tunanika iri-iri suka dinga min yawo a kwakwalwa, daga karshe waya ta na dauko na fada duniyar gizo. 


Washegari kamar yadda na saba da asubahi na tashi nayi sallah, shiru Ina kan abin sallah a zaune ina debating akan in fita in taya matar gidan aiki ko kuwa in zauna a daki? Daga karshe dai kawai na tashi na fada wanka, usual ways din harkokin rayuwata na bi, kwalliya data kwashe ni kyawawan mintuna talatin, minti ashirin na fiddo kayan sawa da shiryawa, zuwa lokacin dana tsaya a gaban dogon yaro ina sake duba kaina, karfe bakwai da mintuna ashirin. Cike da tunanin yadda zan karasa cikin makarantar BUK na fito falo, babu kowa  a cikin falon amma na jiyo motsi a can wata kofa dake gefen dakin matar gidan. A hankali na karasa tare da lekawa, hangame baki nayi kamar zai rabe biyu. Wani dankareren kicin dana gani wanda zan iya cewa ya lunka dakina sau biyu, kayan electronics na kicin babu kalan wanda babu. A gaban gas cooker na hangi er aikin gidan tana soya plaintain, karasawa wajenta nayi muka gaisa cikin girmamawa, na tambayeta matar gidan tace min wai bata tashi daga barci ba, Kai na gyada cike da mamaki. Wace matar aure ce ke kai karfe takwas na safe saura tana barci?? Tambayarta nayi yadda zan isa wajen IT dina, tace ai Direban da zai kaini yana waje yana jirana, tun dazu yayi magana. Juyawa nayi na fita, daga kicin din tace min breakfast fa? Nace mata zanyi acan. A farfajiyar gidan na hangi direban, a mutunce na gaida shi ya bude min gidan baya na shiga yaja motar muka wuce. Mintuna talatin mun shiga cikin BUK, har gaban microbiology lab muka je yayi parking, tare dashi muka shiga lab din ya samu lab attendants suka yi maganganun da zasu yi, ya tafi ya barni bayan ya fada mun lokacin da zai dawo ya dauke ni. Ina zama sai ga Ramla sun shigo ita da Antin ta, nan muka rungume juna cike da murna, itama Anty Halima tafiya tayi ta barmu anan. Da yake ranar farkonmu ce a wurin babu wasu ayyuka da muka yi, wajen karfe goma sha daya muka fito ni da ita zuwa Cafeteria din dake cikin department din. Tafiya muke yi a hankali, tsarin makarantar ya burgeni kwarai, er hira muke yi da ita game da wajen har muka shiga cikin cafeteria din, babu students sosai zama kawai muka yi muka yi order din abinda zamu ci.


Muna gama cin abincin lab muka koma, lab attendants din were very friendly don haka cikin dan kankanin lokaci muka saba dasu. Wadanda suke yin aikin project dinsu sun kawo ayyuka, nan ne fa muka tashi muka fara aiki. Sai wajen karfe biyu muka tashi, wani dan karamin garden muka zauna muna ta hirarmu ni da ita ina jiran Direba yazo tunda ita sai ta jira Anti Halima ta gama ayyukanta, sai wajen karfe biyu da rabi sannan Bala Direba ya iso. Ina hango motar na gane ta saboda a cikinta muka zo. Da sauri nawa Ramla sallama na tashi nayi wajen da yayi parking, a mutunce na gaida shi na bude bayan motar na shiga. 




                       *♡Jeedderh♡*

[12/9, 8:35 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*

                      ©JeedderhLawalS


                            *05*


Wata kyakkyawar yarinya cikin kayan makaranta dogon wando navy blue da shirt fara ta dago kyawawan idanunta tana kallona, ban san lokacin dana sakar mata murmushi ba saboda tsananin burge ni din da tayi, a gaban motar kuma maza biyu ne suma cikin shigar kayan makaranta irin na yarinyar, duk suka juyo suna kallona. Zama nayi sosai a gefenta ina ta watsa musu Murmushi yayin da direba yaja motar, yarinyar da nake tunanin shekarunta zasu kai bakwai zuwa takwas tace min ke ce bakuwar da daddy yace zata zo mana gida? Na gyada kai ina kallonta, nice beauty, ya sunanki? Murmushi tayi, sunana Hafsah amma daddy yana ce min pretty Hafsey, su yaya Abdallah kuma suna ce min Hafsatu... Ta karasa tana pouting cike da shagwaba. Er dariya nayi tare da jan kumatunta, "kai amma Yaya Abdallah bai kyauta ba! Hafsatu ai sunan tsofi ne" ta gyada kai tana turo baki tare da kallon wanda yake kama da shine babban yayansu, "ai kullum sai na gaya mishi amma sai yace wae ai nima tsohuwar ce" na kalli yaron Ina Murmushi, "Yaya Abdallah baka kyauta ba gaskiya, tana yarinyarta ka dinga ce mata tsohuwa?" yaron yayi dariya, "sunan maman Daddy gareta pa, don Allah ba tsohuwar kenan ba?" daya yaron na gefenta ya kwashe da dariya, "tsohuwa ce mana, baka ga har ta fara furfura Akanta ba?" Hafsat ta kai mishi duka a kafadar shi, ya kauce yana mata dariya. Tsokanarta suka ci gaba dayi suna dariya har sai data fara kwalla sannan na tsaida su, "here, enough with the teasing, a kyale pretty haka nan ko?" ta gyada kai tana min murmushi, kanta na shafa ina jinta har cikin raina. Yarinyar tana da wani irin kyau duk da suma sauran yaran suna dashi amma ai kun san kyan mace ya banbanta dana namiji, ina mamakin inda ta gado shi a raina nace kila sai dai wajen mahaifinsu don babu mai kama da mahaifiyar su, dama dama dai Qaseem mai bin Abdallah, naga suna dan yanayi da Anti Mubeenah. Kafin kace me mun saba da yaran, dama ni bani da wahalan sabo suma naga hakan a tattare dasu. Muna isowa gida na dauki school bag din Hafsat ita kuma ta rike lunch box dinta, hannunta cikin nawa muka shiga falo ina taya ta miming din wakar twinkle little star. A daya daga cikin kujerun falon, Anti Mubeenah ce zaune ya harde tana duba jarida, yaran suka zube a gabanta suna bata labarin makaranta, sai dana bari suka gama hayaniyar su sannan na duka na gaida ta. Fuskarta dauke da dan murmushi ta amsa tare da ce min Akwai abinci a kicin, godiya na mata tare da cewa sai nayi sallah, dakina na wuce nayi sallah, na janyo wayata na kira mom don nasan daddy yana office ni kuma ban cika son kiranshi a wajen aiki ba, mun jima muna hira da ita kafin muka yi sallama, ana kiran sallar asr nayi na janyo system dina na kunna kallo tunda babu abinda zanyi, da a gida ne kila na shiga kicin ina taya mommy na girkin dare.


Ina zaune anan ina kallo Hafsat ta shigo cikin kayan makarantar islamiya, na daga Kaina na kalleta ina dan murmushi, "pretty Hafsat an dawo ne?" ta zauna a gefena tana turo baki, "malam ya bamu aiki a makaranta kuma ban iya ba, gashi Abbu da yake koya min karatun baya nan" zama nayi sosai akan gadona nace bani littafin in gani, ta bude jakar ta ta miko min na duba, Tawheed ne, tambayoyi akan imani. Murmushi nayi na kalleta nace "yanzu dai je ki kiyi sallahr magriba tunda an kira, bayan isha'i sai ki dawo mu yi" da murnarta ta tashi ta tafi, har ta kai bakin kofa ta dawo da gudu ta rungume ni, "Aunty thank u" dariya nayi na bita da kallo har ta bar dakin, kai na girgiza na tashi na fada bandaki. 


Bayan sallar isha'i ina kan sallaya a zaune Qaseem yayi sallama ya shigo dakin, yace Aunty Nafeesah wae Mami tace kizo mu ci abinci, ba musu na tashi nabi bayanshi don dama yunwa nake ji. A kan dinning na samesu su duka suna cin abinci, gefen Hafsat naja kujera na zauna. Ganin kowa serving din kanshi yake yi yasa na dauki plate na bude flask din abincin, tuwo ne kaman na semovita miyar danyen kubewa, tunda naga miyar tsululu kamar ba danyen kubewa ba nasan cewa tuwon sai a hankali, Illa kuwa ina kai loma daya bakina da kyar na hadiye, tuwon gashi nan latab kamar danyen gari alamun bai gama dahuwa ba, miyar sai dan banzan yaji kamar da taruhu kadai aka yi ta, babu taste ko na anini sai shegen karnin kifi. Da kyar na iya hadiye lomar farko, ban yi kuskuren kai wata bakina ba don na tabbata idan na kuskure ta sake shiga bakina sai na amayar da dan guntun abincin daya rage a cikina. Su kansu na ga tsakura kawai suke yi, kallonsu kawai nake yi cike da mamaki. Ta ya za ayi mutane su rayu da irin wannan abincin a duniya? Koda yake yau ne karo na farko dana ci abincin gidan, ban sani ba kila rana ce ta bacewa mai girkin kawai, da wannan tunanin na gyada kaina na tashi daga kan table din bayan na wa Anty Mubeenah sai da safe. Dakina na koma naje nayi brush na wanke bakin da mouth wash, cikina wani irin hautsinawa yake yi saboda yunwa, jikar dana fita da ita dazu na bude, wata irin ajiyar zuciya na sake ganin Pack din cookies din New Yorkers, na manta dashi ma ni shaf dazu muka saye shi a cikin makaranta. Zama nayi akan gado na bude shi na fara ci, wayata na hannuna ina chatting, Hafsat ta shigo dakin. Tare da ita muka cinye cookies din, daga nan na koya mata aikin da aka basu, kallon film dina da nake kallo muka ci gaba dayi sai wajen karfe goma da rabi ta min sai da safe, na shafa kanta nace ki tashi lafiya pretty., kar ki manta pa kiyi addu'ar kwanciya barci kinji? Ta gyada kai, "thank u Aunty, sai da safe" na dan hade fuskata, "ohh pretty, sau nawa zan gaya miki bana son Aunty dinnan? Call me Yaya Nafee, bai fi dadi ba?" ta girgiza kai cikin tsokana, "babu dadi gaskiya" kofar dakin na nuna mata "oya, bi can sai da safe" ba musu ta tashi ta fita tana er dariya kasa-kasa. Tana fita na janyo wayata ina kallon screen din, a cikin messages nake ina shawara da zuciya ta akan abinda nake shirin aikatawa, daga karshe dai nayi typing, *"you sleep?"* na turawa Muneer, tsawon mintuna sha biyar babu amsa, na sake tura *"seems like you are, good night!"* na kashe wayar na dorata akan bedside table na kashe wuta tare da yin addu'ar kwanciya barci na kwanta. 


                           *♡Jeedderh♡*

[12/9, 8:40 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*

                      ©JeedderhLawalS


                            *06*


           Nayi tunanin idan na tashi zan ga reply daga Muneer ko kuma missed call dinshi, sai dai har na gama shirina tsab babu shi babu alamun shi. Sai zuwa lokacin ne na fahimci imma dai yana sane yaki min reply jiya ko kuma yayi barci wulakanci ne ya hana ya biyo sahuna da safe, kwafa nayi ina jijjiga kai. 


Ranar ma dai abincin safen sai godiyar Allah, plaintain ne aka soya da shayi da soyayyen kwai, tsakani na da Allah nasan ba zan iya cin abincin nan ba, haka nan dai na dan tsakura har zuwa lokacin da Bala yazo muka dunguma gaba daya har su Hafsat muka fita. A mota daya muka tafi dasu, sai da muka biya ta makarantar su muka ajiye su sannan muka wuce. Da rana koda muka dawo bamu samu Anti Mubeenah a gidan ba, har dare bata dawo ba sai bayan isha'i likis sannan. A zaman sati dayan da nayi a gidan zan iya cewa zama ne na takura, if not for Hafsat dasu Abdul I didn't think I would've survived. ita dai matar gidan yadda na kula da ita, bata cika jan mutane a jikinta ba, ni dai tunda nazo gidan ban ga bare ya leko ba, makota ne, abokai ko dangi. Tsakanina da ita gaisawa ne kawai, idan mun hadu a dinning mu danyi hira sama-sama, ga yawo, idan ta saka Kafa ta fita daga gidan tun safe sai dare take dawowa duk da Hindatu mai aikinsu naji tace tana da saloon da take kula dashi. GA er aikinsu kuwa ban ma san me zan ce ba, ni ban ga dalilin da zai sa in dauko er aiki ba kuma ba zata min gamsasshen aiki ba in kyaleta duk da cewa ni har ga Allah I dont have any plan na daukar er aiki Ina nayi aure, ga Hindatu dai kam abin babu bayani, ita ba ga girki ba, ita ba ga gyare-gyare ba. Aikin data iya daya; ta sha kona sanwa idan ta dora ta fara kallo. 


A takaice dai kafin zagayowar ranar juma'a sai da naji Kano ta fita daga raina, ni ban saba irin rayuwar kadaici dinnan ba. Ranar juma'ar kuwa Ina dawowa daga wajen IT dama dan karamin kit dina a Shirye yake tsab, Anty ta fita yawon data saba sai sako na bari a wajen Hindatu nace tace mata na tafi weekend gida, dama Daddy ya turo wanda zai dauke ni, a farfajiyar gidan ma na dawo na tarar dashi yana jirana don haka babu bata lokaci muka wuce Kaduna. Sai wajen karfe biyar da rabi muka isa gida saboda yanayin go slow da muka samu a hanya kafin mu fita daga cikin Kano, da ihu na da komi na shiga gidan, kit dinma sai driver ne ya shigo min dashi. Mommy tana kicin tana girki ita kadai, na rungumota ta baya ina tsallen murna, juyowa tayi tana kallona cikin murmushi, "oh ni wannan yarinya tawa ban san yaushe zata girma ba" na buga kafa cike da shagwaba nace "mommy!!" dariya tayi ta rungumo ni jikinta cikin nuna kewa. Dakina na shiga an share min shi tass sai tashin kamshi yake yi, na cire kayan jikina na fita zuwa kicin na kamawa Mommy girkin, muna yi muna hira, yawancinta tambaya ce akan wajen da nake zaune, babu matsala dai ko? Kina cin abinci? Tambayoyi dai iri-iri. Muna nan Daddy ya dawo, har cikin kicin din ya shigo ya daga ni sama Cak yana juyi dani, dariya na saki na rirrike shi har ya dire ni kasa. Sannu da zuwa na mishi ya amsa yana shafa kaina, na amsa brief case din hannunshi na raka shi har dakin shi kafin na fito na barshi ya shirya. 


Bayan isha'i muna falo zaune akan babbar tabarmar cin abinci, hira nake musu, duk abinda nake yi a Kano babu wanda ban tsallake ba, su kuma suna sauraro cikin nuna rashin gajiyawa na dariya su yi, na mamaki kuma su jinjina kai. Ranar kam sai wajen karfe sha daya muka yi barci muna ta hirar yaushe gamo. Kwana na biyu a gida na koma Kano cike da kewar iyayena, ji nake kamar inyi zama na acan.


Hindatu kadai na samu a gidan, tace yaran dama a gidan kakannin su suke yin weekend, ita kuma Anty Mubeenah tace wajen bikin kanwarta mawuyaci ne ma idan ba kwana zata yi a can ba, na jinjina kai tare da kwaso tsarabar fruits dana musu a hanya na shirya su a cikin fridge. Wajen karfe takwas na dare ina zaune gidan shiru babu motsin kowa, nasan da su Hafsat suna nan da yanzu suna dakin ko dai muna hira ko kallo ko kuma ina koya musu assignment. Horn din mota naji a bakin gate kafin naji karar bude gate, a raina nace Anty Mubeenah ta dawo kenan. Hasken motar ya ratso ta cikin windown dakina zuwa cikin labulaye na da yake window din dakin a kusa da garejin gidan take. Minti kamar biyar na bata na tashi na fita da niyar inje in mata sannu da zuwa. Tsaye a jikin fridge hannunshi dauke da gorar ruwan Sanah yana sha directly daga cikin gorar, hannunshi daya rataye da suit dinshi yana kuma rike da brief case. Dogo ne ba can ba, idan da ba don na sanshi a hoto ba to da zan iya rantsewa da Allah ince bashi bane, saboda ko a cikin hoton ban hangi yarintar dana gani a tattare dashi ba a lokacin, da nace yarinta ba wai ina nufin yaro bane, aah Ina nufin wanda bai kai girman daddy na ba; Abban su Hafsat ne. Wata irin gigicewa naji nayi, haka kawai naji kafafuna sun yi wani irin sanyi wanda ban iya daurewa ba sai dana dangana gwiwoyina da marble din dake malale a tsakiyar falon, ban sani ba tsabar kwarjinin da yayi min ne yasa gabana ya tsananta faduwa ko kuwa wani abu daban?? Cikin rawar murya nace "sannnnnu da..... Zuwa...... Abbbbuh!!".........


                           *♡Jeedderh♡*

[12/9, 8:45 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *07*




_*"There are no rules when it comes to love. I just let love surprise me because you never know who you're going to fall in love with. You never know who's going to come into your life.....*_ ___Taylor Swift. 





            Wasu kyawawan idanu farare tas suka dago suka kalleni, ban sani ba ko tsananin hasken da falon yayi ne ta dalilin hasken chandeliers din falon ko kuwa idanunshi ne a haka? Brown eyelids suna ta wani sparkling da sheki, haka kawai na tsinci kaina da faduwar gaba. Ya sauke robar ruwan daga bakinshi ya jefa ta cikin waste bin tare da cewa,  "lafiya qalau Nafeesah! Kin zo bana gari koh? Hope komi lafiya?" na gyada kaina da kyar, wani irin nauyin mutumin naji ya dabaibaye ni. Ya gyada kai, "OK!" ya wuce dakin Anty Mubeenah abin shi. Kafa na na masifar rawa na tashi na fada daki, hannuna dafe da kirjina kamar wadda take kokarin tsayar da racing din da zuciya na take yi wanda ya wuce misali. Idanu na zare sosai ina kallon reflection dina a jikin mirror, I couldn't believe wai a haka na fita gaban Abbu. Kafar wando na daya a gwiwa, gashin kaina wani yayi baya, wani ya zubo a kafaduna, wani kuma ya tattare a gaban goshina saboda hular dana saka., idan ka ganni dai a lokacin babu bata lokaci zaka danganta ni da psychiatric patient dinnan irin stage one ma, kunya ta rufe ni sosai kamar in nutse a kasa haka naji. Tsalle nayi na dira akan gado na fara birgima, sai da nayi kaca-kaca da gadon sannan na saurara ina maida numfashi... 



       Karfe bakwai da mintuna biyar na safe na fito daga dakina a shirye na tsab, babu kowa a cikin falon. Kan dinning an shirya kuloli manya masu kyau, kila saboda dawowar maigidan ne aka fiddo sabbin kuloli don ban taba ganin irin su a gidan ba. Na bude kulolin, farfesun kan sa ne sai kamshin er daddawa da tafarnuwa yake yi, sai masa fara tas itama tana ta tururi a cikin wata kula, kunun gyada har da kosai. Kujera naja na zauna na zuba farfesun na fara ci kunnena har motsi yake yi, duk yadda aka yi abincin ba daga cikin gidan yake ba, idan ma daga gidan yake to ba Harira er aikin su bace ta dafa. A raina nace kila Anty Mubeenah ce ta dafa, Amma koda wasa ban ji kamshi yana tashi ba jiya ai. Na dai ture tunanin komi na ci gaba da dura abinci abu na, ina nan zaune na kusa gamawa Anti Mubeenah ta fito daga dakinta sanye da wando da riga na barci, ni kaina ina mace sai da shigar ta bani haushi. Gabadaya kirar ta marar fasali ta fita, tumbinta da zai sa kayi tunanin cikin en biyu ne ya fito yayi nashe-nashe a gaban ta, gashin kanta yayi buzu-buzu dan ma wai tana da yalwar gashi babu laifi, fuskarta sai naso take yi bana tunanin tunda ta tashi da safe ta wanke ta. Nayi kokarin kauda takaicin ta daya taso min na gaishe ta, ta amsa a kaikaice tana wani basarwa irin yadda take amsa min ta bude kofar dake fuskantar dakinta ta shiga, ina tunanin nan ne dakin maigidan don ban taba ganin ta shiga ciki ba tunda nazo gidan. Ni dai na gama cin abinci na na wuce abina. A farfajiyar gidan Malam Bala yana jira na, cike da girmamawa na gaida shi na bude bayan motar da kaina na shiga saboda na hana shi ya dinga bude min. Y'all ja motar muka tafi har cikin makaranta, ranar an kai wasu sabbin en IT lab din daga Leather Research Zaria don haka bamu samu cunkushewar ayyuka ba. Cikin dan lokaci muka saba dasu. Ranar tun karfe daya da rabi muka tashi, bayan mun fito daga lab din Zainab da Ikram suka mana sallama suka wuce gida, ni da Ramlah muka zauna a dan karamin garden din da muke zama muna tattaunawa akan saurayinta da yake so ya tura gidansu ita kuma tana ki wai bata so tayi aure yanzu ni kuma ina nuna mata rashin dacewar hakan, muna nan na hangi motar gida tana tunkaro mu duk da ba wadda aka saba kawo ni bace amma nasan duk motocin dake gidan, wannan shine karo na farko ma da aka zo daukar mu da motar, Anty Mubeenah naga tana jan motar. Na tashi muka yi sallama da Ramlah na tunkari motar, sai da nace tazo mu sauke ta tunda gidan su a hanyar mu yake amma tace zata jira Anti Haleemah don haka na kyaleta. Tun daga nesa Hafsatu ta fito daga cikin mota a guje tana min oyoyo, na tare ta da dan guduna muka fara juyi a wajen kamar wata yarinya, sai da muka gaji sannan na ja hannunta muka tunkari motar. Sai dana jira ta shiga sannan nima na shiga, na daga baki da niyar gaida Malam Bala kamar yadda na saba, "Malam Bala barka da war hak.....!" naji maganar ta kakare min sakamakon wanda na gani a gaban motar yana kokarin tada ta, da saurin na sadda kaina kasa tare da cewa "Abbu ina yini?" ya amsa idanunshi na kan titi. Ji nayi kamar wadda aka jefa ni cikin kankara, na kasa maida hirar dasu Qaseem suke min kamar yadda muka saba idan muka taho sai dai in gyada kai ko in bisu da uhm da ehh har muka isa gida. Cikin sauri na bude murfin motar na fita har ina hadawa da tuntube, ban tsaya a ko ina ba sai cikin dakina. Na zauna a gefen gado ina ajiye numfashi da kyar da kyar, ni kam me ke damuna ne haka? Ni dai nasan bani da wahalar sabo da mutane, amma me yasa a gaban mutumin nan nake ji na kamar wata haliita daban? Me yasa na kasa sakewa dashi? Me yasa nake jin kwarjinin mutumin har cikin tsakiyar kaina? Wata zuciyar tace min saboda ban jima da sanin shi bane, after all babban mutum ne kuma idan zan iya tunawa tun daga kan abokan daddy na har zuwa en uwanshi ni dai bude ido nayi na gansu tare, wannan kuwa daga sama kawai na san dashi, hakan da nake ji rashin sanayya ne kawai, idan na saba dashi komi zai daidaita. Da wannan tunanin naji na samu hope, na maida bayana na kwantar akan gadon tare da lumshe idanuna, a hankali barci ya sure ni, nasan biyan bashi ne tunda jiya ban samu nayi barcin kirki ba. 






                    *♡Jeedderh♡*

[12/9, 8:46 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *08*




               *...Then I cross a bridge for over million reasons to hold on.., hide away with me, walk away with me......*

                     *.....Then I cross a bridge for over million troubles to meet....., nothing is easy, nothing is easy......!*          -Savina Drones_Glass Bridge. 




      Sai wajen karfe biyar da rabi na yamma na tashi daga barcin, toilet na shiga nayi wanka na fito na kimtsa jikina cikin wasu simple Pakistan riga da wando marasa nauyi, turare kadai na fesa a jikina da yake bana yin Sallah sai na koma kan gado na fara sana'ar chatting da kallace-kallacen film. Babu wanda ya leko dakina sai bayan isha'i Hafsat ta leko wai inje mu yi dinner, ina jin yunwa amma jin muryar Abbu a falon yasa nace mata a koshe nake, tayi tayi dani naki fita dole ta juya ta tafi tana gunaguni. Can kuma sai gata ta dawo dakin, "wai Abbu yace mai kika ci?" nace ban ci komi ba, Tun lunch ne amma ciki na a cike yake. Ta juya ta tafi, mintuna biyu ta sake dawowa, "Abbu yace ki fito ki ci abinci ko ran ki ya baci!" nayi shagaraaaa da baki ina kallonta cikin rashin abin cewa, ganin bani da niyar tashi yasa ta juya tana fadin "bari inje in gaya mishi kin ce ba zaki zo ba" da sauri na tsayar da ita tare da tashi tsaye na lalubi hijabi dogo har kasa na saka, Hafsatu ta saka ni a gaba kamar wadda zata gudu har gaban dinning table din Inda suke zazzaune bayan ta gama mitar wai gidan wa zan je dana saka hijabi, ban tanka mata ba, fargabar yadda zan zauna a teburi daya da Abbu ta cika min ciki, tsakani na da Allah ina jin kunyar shi. Naja kujera daya na zauna a hankali kamar wadda tayi laifi, daga Qaseem sai Abdul a wajen sai shi Abbu din Anty Mubeenah bata nan ban sani ba ko bata gidan ne? Tun kafin in gaida Abba ya tare ni, "wasa da cin abinci ko Nafeesah??" na sadda kaina a kunyace nace "Abbu na koshi ne" ya girgiza kai, "that's not an excuse, dokar nan gidan ba a skipping meals uku ko da wasa, idan ma mutum bai jin yunwa sai ya tsakura, idan kuma ya ki dura muke mishi koh?" ya kalli su Qaseem kamar yana tambayar su, yaron ya gyada kai yana er dariya wadda ta fito mishi da goyen hakoran shi, ni kaina I couldn't help it sai da nayi er dariya jin abinda yace, yace oya ci abinci. Babu musu na dauki spoon na jefa cikin jollop shinkafa da aka yi an kawata ta da nama, kifi, coleslaw da wainar kwai. Kamar dazu da safe abincin yayi dadi sosai kamar kunnen mutum zai tsinke, ga zobo mai sanyi a gefe ya sha kayan kamshi an yanka kankara, apple, cucumber da wasu nau'i'kan fruits dana kasa tantance ko menene. A nutse muke cin abincin, su Hafsat suna hirarsu da Abbu jefi-jefi su kan Sako ni a ciki ina amsawa da uhm ko a'ah, tun dai ina nodding har na dan sake na fara maida musu amsa sosai, Abbu yake tambayana game da karatu na ina bashi amsa a nutse. Muka gama cin abincin na kwashe kayan duka na kai kicin, sauran abincin da drink din na saka su a freezer su kuma kayan na wanke su tass. Falon na koma na zauna don Hafsat tayi kini-kini ta hana ni tafiya dakina dole na zauna a cikin su, su Abdullahi game suke yi a laptop din Abbu ita kuma Hafsatu na canza channels, bayan dogon lalube muka tsaya a mbc 3 suna hasko Despicable Me part 1. Muna cikin kallon muna kwasar dariya ni da Hafsat, gabadaya mun hade falon da hayaniya. Abbu ya fito daga dakin da yake fuskantar dakin Anti Mubeenah sanye da bakar jallabiya a jikinshi, take nayi tsit kamar bani ce nake ihun dariya ba. Ya zauna a kujera tare da daukar Hafsat ya dora ta akan cinyar shi tare da kallona, "are u a kindergarten kike kallon cartoon da girman ki??" kafin inyi magana Hafsat tayi caraf tace "Abbu tana dasu da yawa a cikin system dinta, har dasu na Disney princesses da fairy tales da......." ta fara jero mishi sunayen films kala kala ni wasu ma ban rike su ba, Abbu sauraren ta kawai yake yi yana gyada kai amma fa idanunshi suna kaina, hakan yasa naji gabadaya kamar wadda aka zare mata duk wani kuzarinta. Sai data gama lissafin sannan ya magantu, "wato dama saboda fina-finai kika sa aka sai miki laptop ba don karatu ba koh?" nayi saurin girgiza kaina, "a'ah Abbu! Ina yin karatu fa. Akwai text books a ciki da yawa da videos dinsu kuma Akwai docs da dama duk a ciki, da gaske ina yin karatu" ya kalli Hafsat, wai?? Ta gyada kai da sauri ehh Abbu, watarana ma tana koya min, kuma har Assignment take koya mana ni dasu Yaya Abdullahi. Ya daga gira daya, "Ohh really? A wani mataki kike a Islamiya?" kaina a kasa nace "nayi saukar Al-Qur'ani mai girma, na gama harda watanni biyar da suka wuce, na sauke littafin Umdatul-Ahkam, Riyadussaaliheen, Tafseerul-Jalalaini da Tafseerul-Ibn-Khatheer, da littafai da dama. Na fara Annissa'u war-rijaalu fil jannah amma ban gama ba har yanzu" yace "Mashaa Allah! I am impressed gaskiya" na sadda kaina kasa ina murmushi zuciyata cike da kaunar iyaye na da suka tsaye min na samu karatu mai inganci, tun ina primary six na sauke Al'Qur'ani mai girma, ban fara harda ba sai dana sake yin wata saukar sannan na fara tare da wasu manyan littafai na addini nasan ko a haka na tsaya Alhamdulillahi bani da matsala amma ban tsaya din ba, har yanzu ina cigaba da karatu na duk da cewa har gida Malamin yake zuwa yana koya min. Ganin ban yi magana ba yasa ya cigaba, "da alamu nima zan kawo nawa littafan ki dinga koya min don cikin wadanda kika ambata Akwai wadanda har yau ban gama su ba, zaki koya min?" mamaki ya matukar Kama ni, duk cikin saukin kan mutumin ne haka ko kuwa wani abu daban? Dana rasa abin cewa sai kawai nayi murmushi na maida kallona ga TV ba wai don ina fahimtar abinda ake yi ba anymore, sai don in janye yawan tambayoyin Abbu wanda nasan da kyar ne in samu amsoshin su. Ina ji yana tambayar Hafsat karatun ta tana gaya mishi abinda suka yi a Islamiya ranar, ta karanto mishi Hadisi da Qur'an ya saurara tare da gyara mata Inda ta kuskure.


Karfe tara da rabi suka gama film din da muke kallo, Abbu ya umarce mu da muje mu kwanta saboda makaranta. Sai da safe muka mishi kowa ya wuce dakin shi, anan muka bar shi yana danne-dannen laptop. Ina shiga daki su Mommy na kira don gabadaya ranar bamu yi waya dasu ba, muka gaisa dasu mun jima muna hirarraki kafin na musu sai da safe muka kashe wayar. Bayi na shiga na kimtsa jikina nazo na kwanta. 


          Washegari abincin mu marar taste da armashi ya dawo, Ashe wanda muka dinga ci daga gidan su Abbu aka kawo shi. Ni dai na tsakuri iya wanda zan iya ci na tashi, suma yaran haka nan dai suka tsattsakura muka tashi muka tafi makaranta.  Ranar juma'a kamar satin daya wuce, ina dawowa naci karo da direba yana jira na, sallama nawa Anty da Hareera na tafi Kaduna wajen Mommy da Daddy na. 




                 ●●●●●●●●●●


    Kimanin wata na daya da zuwa Kano, na riga nayi adopting da garin da yanayin gidan da nake zaune. Abbu bai cika zama a gida ba, it's hardly yayi sati daya cur a gida, yawanci zuwa seminar ko kuma harkokin shi na kasashen turawa, na Ji Malam Bala ne ranar nan yace wai suna shirye-shiryen bude wani kamfanin kirar kayan sawa ne a China shi da abokan shi. Anti Mubeenah ma dai bata cika zama a gidan ba, yawanci ko tana gidan ma bata cika zama a falo ba shi yasa har zuwa lokacin bamu wani shaku da ita ba, tsakani na da ita gaisuwa ne kawai. Abin yana matukar daure min kai, ban taba ganin wani daga cikin dangin Abbu ba a gidan, amma nata da abokanta suna yawan zuwa har yini suna yi, daya daga cikin nasihun da Mommy ta min lokacin da zamu taho Kano shine kada in kuskura in shiga harkar da babu ruwa na, banda shisshigi da sa ido a rayuwar mutane, don haka na kauda kaina daga rayuwar su, koma meye ke faruwa dai rayuwar su ce ba tawa ba. 


          Wannan satin ina gida ban je Kaduna ba saboda su Daddy sun tafi Malumfashi wajen bikin dan gidan Yayan Daddy din, ina zaune a daki ranar assabar da safe Hafsat ta shigo dakin, a shirye take tsaf cikin riga da siket na atamfa da dankwalin atamfar a saman kanta bata daura ba. Na kalleta da mamaki nace Hafsy ina makaranta ne yau baki je ba? Tace "hutu muke yi ai" na kalli kwalliyar da tayi nace "ina zaki je?" ta langwabar da kai, "Yaya Nafee ke da na gaya miki yau sunan Anti Raliya kanwar Daddy?" na dan dafa kaina, "na manta ne wallahi, har zaku wuce kenan?" ta gyada kai, "mu duka fa zamu tafi, idan kina so ki zo muje" cike da jin dadi na kalleta don dama gabadaya na takura da zaman hakanan da nake yi tun safe, nace "really? Can I??" tace why not? Bari in jira ki shirya. Dama ban dade da fitowa daga wanka ba, a gaggauce na shirya, na saka wata doguwar rigar material sky blue dinkin buba ne ta min tsaf a jikina, ban yi wata kwalliya ta azo a gani ba na shafa turare kawai na dauki gyale na yafa. Na kalli Hafsy nace "mu je?" dankwalin hannunta ta miko min tana turo baki yadda ta saba idan tana jin rigima, "dan Allah ki daura min irin yadda kika yi dinnan ranar nan?" ba musu na amsa na nada mata shi kamar gwaggwaro, ta kuwa yi kyau sosai wayata na dauka muka fara hotuna har sai da muka Ji karan horn sannan muka fita da sauri. Su duka suna cikin motar Abbu picnic yana zaune a seat din direba Anti Mubeenah a gefenshi su Abdullahi kuma a baya, ban san ko yaushe Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi ba don tun ranar Laraba baya nan babu mamaki jiya da dare zai dawo. Gabadayan su suka bimu da kallo ni da Hafsy har muka shiga motar, a nutse na gaida Abbu. Thank goodness na daina jin wannan faduwar gaba da rikicewar idan ina kusa dashi, yaja motar a hankali muka bar farfajiyar gidan muka cilla kan titi. Muna baya ina nunawa su Abdullahi hotunan da muka yi ni dai Hafsy su Abbu kuma suna hirarsu shi da Anti Mubeenah kadan kadan Abbu ya kan juyo ya kallemu ko yaja Hafsy da hira har muka isa Gwamna Road inda anan ne ake sunan, ko shiga gidan Abbu bai yi ba yana ajiye mu ya juya tare da cewa bayan Magriba zai zo ya dauke mu. 






                          *♡Jeedderh♡*

[12/9, 8:47 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *09*


      Muna shiga gidan sunan su Hafsat suka yi nasu wurin ko dakin mai jego basu karasa ba. Ni da Anty Mubeenah muka karasa har uwar dakan mai jegon lokacin babu mutane ma sosai, aka dan yi en gaishe-gaishe Anty ta hakimce a gefen gadon ta janyo wayar hannunta ta fara danne-danne da kiraye-kirayen waya. Gabadaya naji na takura don bansan kowa a wajen ba gashi su Hafsat sun bace a cikin gidan kwata-kwata, wata farar mata ta shigo itama kana ganinta Kasan er uwarsu Abbu ce don ga kama nan kamar an tsaga kara, da dan saurinta ta shigo tana mitar ina su Ni'ima suka shiga ne sun barta da aiki ita kadai? Ta kalli sauran matan dake dakin tace ku taso muje mu gama aikin samosa din can don Allah kafin rana tayi mana, duk suka mimmike yayin da Anty Mubeenah ta kara hakimcewa akan gado, ni kam ganin zan takura na tashi na bi bayan wadanda suka tashi. A can BQ suke yin aikin, na shiga na kama musu muka fara aikin suyar Samosa, Anti Amina kamar yadda naji ana kiranta ta Kalle ni tana murmushi tace "kece wadda take IT a gidan Ibrahim ko?" na gyada kaina, tace ai last week na sha labarin ki wajen Hafsat har sai da kunnuwana suka gaji. Nayi er dariya nace Ai Hafsat Akwai surutu, ta gyada kai. Kafin mu gama aikin mun saba da Anti Amina sosai, su Ni'ima suka dawo dauke da plastic robobi wadanda za a zuba soye-soyen da za ayi a ciki, kusan dukan su sa'annina ne Sa'adiya ce ta girme mu sosai don ta bamu kusan shekara uku zuwa hudu, dukansu suna jami'ar Bayero ita Ni'ima a level two tana mass comm yayin da Sa'adiya take shekararta ta biyan karshe a BS.  Kafin kace me mun saba dasu kamar wanda muka yi watanni da sanin juna, muna gama suyar samosa din muka fara shirya abubuwan a cikin robobi muna sawa a cikin Leda, abinci dama odar shi aka yo. Sai gab da la'asar muka koma cikin gidan, Anti Mubeenah bata nan wai ta tafi gidan wata er uwar su dake aure anan cikin unguwar, ina jin kananun maganganu na tashi game da halayen Anti Mubeenah din kun san taron mata ba a raba shi da kananun maganganu balle harka ta hado ku da dangin miji dama sai a hankali, ni dai nayi kunnen uwar shege dasu naki maida hankalina kansu don ba harkar shiga ta bace. Wanka muka sake yi Ni'ima ta bani wasu riga da siket na Swiss lace na saka saboda nawa na lalata su da abun fulawa sun yi fari tas. Bikin suna yaci gaba da gudana lafiya qalau, ina daga cikin masu kai da kawo na entertaining din baki, kawo abinci, dauke kaya, daukar gifts din maijego da wasu abubuwan. Duk Inda na motsa da sannun Anti Ameenah nake motsawa, naga alamu na shiga ran matar sosai. Anti Ameenah itace babbar Yayar su Abbu kuma babbar diya a wajen Alhaji Mad'udu Galadanchi, su shida ne wajen iyayensu kamar yadda Sa'adiya take bani labari, Anti Ameenah ce babba sai Abbu, sai Anti Rahina, Aminu Yayan Sa'adiya yana Bangladesh yana karatu sai Sa'adiya da Ni'ima auta. Family din sun burge ni sosai a gaskiya, na kula da hadin kansu kwarai da gaske abin ya burge ni ba kadan ba, ina son ganin yan uwa wadanda suke kula da zumuncin su sosai. 


Bamu muka samu kanmu ba sai bayan isha'i, mutane duk an tattafi sai baki na nesa da dangin maijegon na kusa, muna wani daki dake kusa dana maijegon inda anan muke bidirin mu, hira muke dasu Ni'ima lokacin da Hafsat ta leko dakin tace in fito Abbu yazo zamu tafi, na dan hade fuska jin an katse min hira mai dadi da muke yi amma haka nan na tashi saboda bani da yadda zanyi na fito su Ni'ima suka biyo bayana, dakin Anti Rahina na shiga da niyar mata sallama. Abbu na zaune a cikin falonta kusa da Anti Ameenah yayinda maijegon take zaune a kujera daya rungume da babynta da alamun hirar en u want aka ce ake yi na durkusa na gaida Abbu tare da yiwa su Anti Ameenah sallama, Abbu ya mike nabi bayanshi. Su duka har maijegon suka fito mana rakiya, su Qaseem na jikin motar Abbu din suna jiran mu, duka muka shiga cikin motar. Su Ni'ima suka leko suna kara min sallama dama mun yi exchange din number waya dasu, Anti Ameenah ta miko min wata Leda mai dan girma tana kara min godiya tare da jaddada min in fa nemi maganin ciwon jiki in sha ina amsa mata da toh, Mai jegon MA ta leko tana min Allah huta gajiya da godiya sosai. Abbu kam baki a sake yake kallon en uwan nashi cike da mamaki, wannan shine karo na farko da suka fito wai da sunan mishi rakiya, sai daga baya ya kula ashe ma ba shi aka yiwa rakiyar ba, kulawar daya kamata ace matar shi ce suke wa sun kare da ba wata can, abinda yakamata ace matar shi ce tayi suke mata wannan yabawar wata can ce ta samu romon. Koda yake bai ga laifin su ba, Mubeenah ita tayi wasa da garinta har yayi ruwa, shi kanshi yaji haushin abinda tayi yau a wajen sunan nan, ance tunda taje ta gaida mai jegon bata kara yiwa kowa magana ba ko Anti Ameenah bata gaida ba, daga baya ma suka ce wai ta ajiye musu dubu goma ta tafi tun kafin ayi Azuhur abinda ya bata ran Anti Ameenah kenan, ya girgiza kai cike da takaicinta, duk iya kokarin shi na ganin Mubeenah ta ra6u da dangin shi don su saba abin yaci tura.  Shi har bai san me zai mata ba kuma.


Sai da muka gama sallamar mu sannan suka koma gefe suka tsaya suna kallonmu tare da daga mana hannu har Abbu yaja mota muka tafi. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, su Hafsy tuni tayi barci akan cinya ta. Muna isa gida na ciccibe ta muka wuce Abdullahi ya dauko min ledar da Anti Ameenah ta bani, dakin Hafsy na fara wucewa na kwantar da ita. Closet dinta na bude na ciro mata kayan barci na dawo na cire mata na jikinta na saka mata wadannan, addu'ar kwanciya barci na tofa mata tare da sauka daga kan gadon a hankali gudun kar in tashe ta daga barci, ina juyawa naci karo da Abbu a bakin kofa a jingine yana kallon mu. Na sadda kaina kasa na je zan wuce ta gefenshi, packet din magani ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, yace maganin ciwon jiki ne Anti Ameenah tace in baki, ki sha kafin ki kwanta. Na gyada mishi kaina, "sai da safe koh?" ya fada yana kaucewa daga bakin kofar dakin, na bi ta gefenshi na wuce ya bini da kallo. Ina shiga dakina kayan barci kawai na saka na afa maganin a baki, sai dana bata mintuna kusan goma yadda maganin zai yi settling a jikina sannan na kwanta, babu dadewa barci ya kwashe ni, ni kaina nasan cewa a matukar gajiye nake saboda ba karamin aiki muka sha a gidan sunan nan ba. 


Sai karfe goma na safe na tashi, nayi mika mai tsawo ina jin ga6o6ina kamar an bubbuge min su, kai tsaye toilet na fada nayi wanka da ruwa mai dumi, nayi brush kafin na fito. Wandon jeans na saka wanda bai kama jikina ba da shirt, na daure kitson kaina a cikin tafkeken hair band na dora hula a kaina. Falo na fito saboda wata mahaukaciyar yunwa da take nanikata, babu kowa a cikin falon haka babu hayaniyar yara nasan suna makaranta. Anti Mubeenah na hakimce a kan kujera a falon da takardu a gabanta tana buga lissafi, na durkusa a gefenta ina gaidata. Hankalinta yana kan takardun ta amsa min, baki na dan tabe na mike, har ga Allah halayen matar basa burge ni, wata na daya a cikin gidanta amma wani idan ya ga yadda take yazga ni sai yayi zaton bakuwar jiya ce a wajenta. Kan dinning table na wuce kaina tsaye sai dai kwalam!  Babu komi, cike da mamaki na tsaya ina kallon wajen a raina ina tambayar ko lafiya? A iya sani na ni dai a gidan nan ko an gama cin abinci ba a dauke kayan sai idan za a sake shirya wani meal din. Daga bayana naji Antin tana cewa "Yau bamu yi girki ba, Harira bata nan taje garinsu wajen biki. Yara ma sai oats na dama musu, kije kicin kema ki dama anjima kadan zan bada a yo take away" na jinjina kaina cike da mamaki, oats? Yaushe rabona da in sha Abinnan? Kicin din na wuce, kulolin da aka yi amfani dasu ba a wanke ba suna cikin sink har sun fara wari, nayi iya dube dube na a kicin din ban samu abu mai sauki da zan saka a bakina ba don bazan iya dama oats Inci ba, kawai ledar da Anti Ameenah ta bani jiya ta fado min a rai da sauri na koma daki na janyo ledar na bude, tarkacen su doughnuts, cake, cincin dasu biscuits ne a ciki har da naman suna, falo na koma na bude fridge na dauko lemun exotic na dawo nayi daidai a tsakiyar daki na fara ci, sai da naji nayi nak sannan na tattare sauran na ajiye a gefen gado. Waya na dauko na bude, missed calls na gani bila adadin nasu Ni'ima dana Daddy sai wata bakuwar number da ban sani ba, su Ni'ima na fara kira suka min ban gajiya sannan na kira bakuwar number nan ashe Anti Ameenah ce, itama dai ban gajiyar ta min har sai data saka ni jin kunya yadda take ta yaba min tana sa min albarka, muna yin sallama da ita na kira Daddy, nan muka kwashe lokaci mai tsaye ina bashi labarin abubuwan da suka faru cikin week din, bayan mun yi sallama kan gado na koma na kwanta ina sake-sake, ban san iya lokacin dana dauka ina tunanika ba sai dai na bude ido naga karfe sha biyu tayi, a raina nace su Hafsat karfe biyu suke dawowa daga makaranta, and I can't stop imagining ya suke manejin oats a cikinsu fiye da awowi biyar. Cimak na tashi na fita falo, Anti ta gama lissafin nata tana zaune ne kawai tana kallon tashar CBN, na zauna a gefenta nace "Anti me za a girka ne na rana naga su Hafsat sun kusa dawowa?" dagowa tayi tana kallona cikin wani kallo dana kasa gane ma'anar shi, ta yamutse baki kafin tace "ke har kin iya girki ne dama?" nace sosai ma, ina taya mommy idan tana yi. A raina kuwa cewa nake "a yadda nake jina akan girki Allah na tuba ai gani nake zan iya karawa ko da wani irin chef ne!" saboda ba yabon kai ba, dishes dai tun daga kan na hausa, na Yoruba da abinda ya danganci na mai jajayen kunne na kware a yin su don mommy na gwana ce in dai akan girki ne. Sai daga kare min kallo kafin tace ki dafa shinkafa da miya to, zaki iya kuwa? Na danyi murmushi kawai, da alamu gani take girki wani katoton aiki ne bata san a wajena kamar shakar ruwa ne, nace "zan iya Anti" tace to shikenan, je ki fara" babu musu na tashi na fada kicin din ina tattare hannun riga ta. 






                            *♡Jeedderh♡*

[12/9, 8:51 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *10*


             *You're the right time at the right moment...., You're the sunlight, keeps my heart going.... Know when I'm with you, can't keep my self from falling...... Right time at the right moment It's You...., You....., It's You....!*

                  A song by; Henry, It's_You dedicated to My Fans. 


        


                 Tsaye nayi a tsakiyar kitchen din ina tunanin ta Inda zan fara, sai dana danyi sighing kafin na tunkari freezer na bude, kayan vegetables da nama ne da dangin kifi a shirye kala-kala a ciki saboda tsabar ajiya duk da cewa a cikin freezer suke amma sun fara sauya kama musamman vegetables din. Kashe freezer din nayi yadda zan samu in ciro kaya ta sauqi, na shiga store nan ma kayan abinci ne dankare kamar a super market babu nau'in da babu daga na gida har na waje. Maimakon shinkafa da miya sai nayi fried rice wadda na wadata ta da dangin veggies, na yanka hanta kanana a ciki. Na dauko fresh sardines na wanke na yanyanka shi na soya wanda zan yi decorating din shinkafar dashi. Ina tsaye ina slicing din albasa wadda zanyi onion sauce da ita, ban ji shigowar mutum kicin din ba sai magana naji a baya na, "what are you doing here?" na juya a firgice na kalli wajen da sautin maganar ya fito. Abbu ne tsaye a kofar kicin din ya rungume hannuwa a kirjin shi yana kallona, naji na diririce da kyar na iya cewa "ammmm.... Girki?!" na fada kamar ina tambayar shi, ya shaki numfashi yana lumshe idanu, yace "woah! What a delicious smell!! meye kike dafawa haka ya cika mana hanci da kamshi?" dan murmushi na saki kadan, "fried rice ne" yace I hope kin kusa saukewa? I can't wait to taste it. Na gyada kai nan ma, nan da en mintuna zan sauke. Ya juya zai bar kicin din, "OK! I'll go and take a shower then sai in dawo" ya karasa fita daga kicin din yana uttering "thank Goodness!" a kasan zuciyar shi, dama dawowa yayi yayi wanka ya fita ya samo musu abincin da zasu ci sai kuma yana shigowa yaji wani mahaukaciyar kamshin abinci yana fitowa daga kicin wanda ya taso mishi da yunwar shi ta kwana da kwanaki da yake dannewa da lemuka, yana shiga kicin din yaci karo da "beautiful sight' a cewar shi, tana yanka albasa a cutting board cikin kwarewa kamar irin chief cook dinnan a 5 stars hotel, da kyar ya iya suppressing din urge din daya taso mishi na aikata wani abu da yasan will never ever be appropriate, wanda yasan mawuyaci ne idan bai zubar mishi da kimar shi ba a idon yarinyar na har Abadan. Sai kawai ya buge da jingina da bango. 


Ina gama yin sauce din na juye shi cikin wani kwanon tangaran, itama fried rice din sauke ta nayi don ta gama, ta min yadda nake so kuwa, wara-wara, yellow shar sai tashin kamshi take yi, na fito da babban food flask na zuba ta a ciki. Oranges na dauko manya da apple da water melon, na bare lemun na saka a juicer ta markada min shi na tace ruwan, na yanka kankanar itama na cire yayan tas, na yanka ta kanana a cikin lemun tare da tuffa, na kawo syrup sugar na zuba a ciki na watsa kankara na fara ciccibar kayan zuwa dinning table. Ina gama shiryawa su Hafsy suka fado falon a guje da alamun gajiya a tare dasu, lokacin dana tare su sai na dinga jina kamar wata Mummy dinnan mai jiran 'ya'yanta su dawo daga makaranta, nayi kokari na kauda weird tunanin daya lullube min zuciya na karbi jakar hannun Hafsy na kai mata daki, ai ko kayan makaranta basu cire ba kowa yayi settling akan kujera na fara serving dinsu kafin na zauna a gefen Hafsy nima na fara ci. Zo kaji santi kuwa, Qaseem har da cewa wai shekarata nawa a makarantar koyon girki? Dariya kawai nake musu acan kasan zuciyana kuwa jin kaina nake a sama, me yafi yabo dadi a duniya?? Abbu ya fito daga dakinshi sanye da wandon jeans da shirt na shan iska, Shima kan dinning din yazo ya zauna. Na mike na fara serving din shi abincin yayin da yake gaisawa da iyalan shi, na zuba mishi komi na ajiye a gaban shi na koma mazaunina na zauna muka ci gaba da cin abincin mu. Wajen cin abincin ya koma shiru, Abbu bai yi magana ba sai kai kawai da yake girgizawa, rashin magana ma yabawa ce. Sai da kowa ya cinye abincin plate din shi duka, suna gamawa kowa ya wuce dakinshi saboda ranar ba zasu koma makaranta ba. Na fara tattare plates din da muka yi amfani dasu na kai kicin, Abbu yana zaune a har a lokacin yana cin dura abinci a cikinshi cikin alamun rashin saurarawa, na fahimci matsananciyar yunwa a tattare dashi. Na kai hannu da niyar dauke jug din juice din da nayi, cikin rashin sa'a shima ya kai nashi hannun don haka nayi saurin janye nawa hannun amma duk da haka sai da hannunshi ya dan gogi hannuna, Ya Allah!! Wani irin current naji ya taba ni kamar na taba budaddiyar wayar wuta. Naja baya da sauri ina shivering, shi kam hannunshi ya kurawa idanu  yana kallo kamar wani bakon abu kafin ya dago idanunshi yana kallona mai cike da ma'anoni wadanda na kasa pathorming abinda suke nufi. A hankali ya maida kanshi ga plate dinshi ya cigaba da cin abincin amma fa cikin rashin kuzari, ganin haka yasa sumi-sumi na wuce dakina kafafuna na shaking. Ina bada baya ya maida kanshi ya jinginar da kujera yana ajiyar numfashi da sauri-sauri, what the hell did he just felt??! Yake tambayar kanshi embarrassingly.



Ina shiga dakina na zube a bakin kofa rawar da jikina yake yi ta karu, Innalillahi!! Kadai naji bakina yana furtawa da karfi, da kyar na iya daidaita natsuwa ta.  Wannan wani irin abu ne haka? It's not as if ban taba gogar hannun namiji bane, God Forgive me amma ni har hugging dinsu nayi amma ban taba jin rabi rabin abinda naji ba yau da Abbu ya taba ni, ban taba jin hakan a tattare da ko wane namiji ba sai shi, ko me yasa hakan?? Ban zurfafa tunani na ba na mike na fara gyara daki na ba wai don yayi wani abu ba sai don bani da aikin yi kawai. Har bayan la'asar ina gyara, dana gama wayata na dauka na shiga dakin Hafsy, tana zaune a kasan carpet tana kokarin warware kitson kanta, na zauna a gefen gado ina kallonta, "ya ne pretty?" as usual sai data yi pouting  kafin ta kalleni da dara-daran idanunta, "na manta ban fadawa daddy a kaini saloon ba har ya fita, kuma idan Anty Kate taga kaina a haka gobe sai ta dake ni!" na shafo kitson kaina nima ina kallonta, yakamata ma in tsefe shi don ya fara tsufa. Nace "to taho in taya ki" ta waro hakora, "yauwa, kin iya kitso ai koh?" na girgiza mata kai, ta 6ata fuska, nace "noo, kar ki damu, zamu san dabarar da zaa yiwa kan yadda Anti Kate ba zata taba min ke ba koh?" ta gyada kai tare da zuwa ta zauna a kusa dani. Haka kuwa aka yi, muna gama tsifar ta dauko kayan kitso dasu ribbons na fara gyara mata kai, kalba na mata manya wadanda na kayata da ribbons din da dutsunan kitso kuma ga mamaki na yayi kyau sosai, ita kanta data kalli kanta a madubi tsalle-tsalle ta hau yi. Ni kam dariya na mata na tashi na fada kicin don yamma tayi sosai, sakwara nayi da miyar ganye, na wadata miyar da nama da busasshen kifi, na hada fruit salad na kai komi kan dinning na ajiye. Da wuri na tattaro kan yaran muka ci abincin mu kowa ya koma daki ya kwanta duk a dabara ta na kaucewa haduwa da Abbu, sai Allah ya taimake ni har na koma daki bai dawo gidan ba. Sai da na gama shirin kwanciya barci sannan na jiyo tashin muryar su shi da Anti a falo da alamun tare suka dawo gidan. 


Washegari tun da safe na fada kicin, potato chips nayi da egg sauce sai ruwan shayi wanda yasha kayan kamshi, na soyawa su Qaseem doya da kwai wanda zasu tafi makaranta dashi na zuba musu a lunch boxes dinsu, yin komi nake yi cike da kuzari da walwalata. Aikin daya jima yana burge ni kenan, kullum naje gidan Aunty Uwani ina ganin tana hadawa yaranta abincin tafiya makaranta irin haka, abin yana burge ni ba kadan ba, at last yau gashi dai nima na hadawa nawa. A gurguje na shirya na fito saboda lokaci daya fara wucewa, yanzu ma mu hudu kadai muka karya don daga Abbu din har ita Aunty din babu wanda ya fito, muka gama karin mu muka wuce makaranta. 



Gabadaya kwanakin girkin gida da kula da gidan ya koma hannuna yayin da ita uwar gida mai gayya mai aiki kullum sai dai tayi rashe-rashe sai dai a dafa ta zauna taci ta tashi ta kara gaba abun ta babu godi bare na gode, dama dama ma Abbu. Yana nuna jin dadin shi kwarai game da hakan, ina kuma shan godiya a wajen shi sosai wanda ina ga hakan ne yasa nake dagewa tun karfi na ina musu dadadan girki wadanda zasu sa zuciyar shi a farin ciki yayi ta mun addu'ar daya saba, halin Aunty kam tun ina damuwa dashi har na daina. Matar is really complicated, gane halinta da Inda ta saka gaba abu ne mai wahala kam, to mai wahala mana. Ban ka kula da cin abincin miji, baka san shan miji ba, Baka san gyara muhallin mijinka ba, ba ido na saka musu ba, amma nasan bata kwanan dakin miji, ko ina suke ko a gaban wa suke she is always making it obvious that bata damu da mijinta, rayuwar Aunty Mubeenah fa tana bukatar gyara sosai da sosai. Allah Allah nake juma'a tazo in wuce Kaduna, va wai don na gaji da hidimar da nake yi dasu ba in fact, kwanaki biyar zuwa shidan da nayi ina yiwa Abbu da iyalan shi girki has been the best and happiest moment na rayuwata, sun kara min kusanci da iyalan, sun kara min so da qaunar su kamar yadda suka kara musu sona da qaunata. Kawai dai nayi kewan su Mommy da Daddy ne don haka ranar juma'a da wuri na dawo na hada kayan da nasan zan bukata, Abbu baya gari yayi tafiya ranar Thursday. Direba yana zuwa na fito tare da kulle gidan don babu kowa, Hajiya Aunty Mubeenah an tafi neman kudi bayan babu abinda ta nema ta rasa a gidan auren ta. 






                         *♡Jeedderh♡*


[12/9, 9:09 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *11*


         *"Paradise is a home of Honor, Dignity, Rest, Satisfaction, Beauty, Joy and Peace., May Allah make it to be your permanent Home Ameeeen, Jumma'at Kareem!!"*

                Abinda na karanta kenan daga wayana bayan na shiga dakina, Kimanin awowi biyu da dawowa na kenan. Na duba kasan message din inda nake zaton zan ga sunan wanda ya turo text din saboda babu suna a jiki sai number kawai. *'_Galadanchi!'* shine sunan dana gani. Crap! Abbu ne!! Zuciyata ta hau fadi ina jin tana wani tsalle-tsalle, wayar na zurawa idanu ina lalubo abinda zan tunana amma komi ya tafi blank, na lalubo su da kyar na shiga jefawa kaina su kamar ni ce Abbu din, "Friday message kuma? Why would he?" zuciya ta tace stupid! Kuma ba zai miki message ba kike nufi ko me? You know this is a normal thing tsakanin mutane yanzu, ke da Daddy da sauran uncles dinki ba kuna exchanging irin wannan messages din a tsakanin ku ba?? Na gyada kai a hankali kamar wawiya, sai a lokacin kuma na gano shirmen da nayi, God! I can be silly sometimes, saboda Allah addu'a ya min mai dadi amma ban amsa mishi ba na hau tuhumar dalilin da yasa ya turo min sakon. Da kwarin gwiwa ta na tura mishi amsa, *'Ameen Abbu, and same to you. How's your presentation? Allah ya dawo daku lafiya Ameen!'*. Shiru har aka dauki lokaci babu reply, na daga kafada ta, watakila I've gone too far ne, meye nawa na wani tambayar yadda harkokin shi suke tafiya kamar wata shakikiyar shi? Na tabe baki na tashi daga kan kujerar dana zauna don wai da zama nayi ina jiran amsar shi kamar wata sakara. Kayan jikina na shiga cirewa ina jifa dasu cikin laundry bin, na daura towel a jikina nazo fada bathroom.


              ☆☆☆☆☆☆☆☆


Idanunshi kur akan wayar yana kallo cikin wani irin yanayi, kalmomi ne da rabon daya jisu daga bakin matar auren shi har ya manta su, anya ma ya taba jin su kuwa? Ta yaya ma aka yi tasan cewa presentation yaje? He can't recall telling her, wani sashe na zuciyar shi yace ba mamaki wajen su Pretty taji don ya kula tana son yarinyar sosai, yana mamakin yadda idan suna hira da Hafsy take maida kanta kamar yarinyar har ka kasa tantance yaro da babba a cikinsu. Ya lumshe idanu a hankali...... Bai san cewa ya zurfafa a tunani ba sai daya ji muryar Chairman dinsu ta microphone, "Dr. Galadanchi?? Anything from you??" yayi firgigit ya dawo daga duniyar imagination daya tafi, "yeah of course Mr. Collins..." ya jefa wayar shi a aljihu ya dauki wasu takardu ya tafi kan step fara bayani a nutse.... 


                        ●●●●●●●●●●


        Wannan weekend din ziyara nayi, naje gidan Anti Uwani na musu yini a can, daga nan ni da AbdulJalal muka shiga gari sai bayan isha'i ya sauke ni a gida bayan mun tsaya a Mcbae mun sayi tarkacen chocolates da ice cream. Washegari lahdi sai wajen karfe biyar na bar gida cike da kewar Mom da Dad, amma fa can kasan zuciyana wani farin ciki da doki ne dankare a cikinta, dokin in koma inci gaba da yiwa Abbu dadadan girki na yana ci yana yaba min har da santi. Sai dai koda na isa sai na tarar Hareera ta dawo daga biki, Abbu kuma baya gari, gwiwa na yayi sanyi sosai, jiki a sanyaye na shige daki na. 

       Washegari a tsaitsaye muka ci abinci muka wuce makaranta, ranar mun sha ayyuka a lab kamar me! A matukar gajiye muka zauna akan dakalin da muka saba zama ni da Ramlah cikin dan garden din da muke hutawa, na kalle ta ina dan murmushi, "ke jiya fa muka hadu da Muneer" bata nuna alamun abun ya dadata da kasa ba kamar yadda nayi zato, tayi fuskar shanu tace a ina? Nace "McBae, mun shiga siyayya ni da AbdulJalal. God! Baki ga yanda gayen nan ya kara kyau ba, yayi fari yayi kiba sosai, I think he misses me so much, kin kuwa ga irin fara'ar daya dinga min? Rabona da in....." tayi saurin katse ni, "ai fa kin kika fara bada labarin Muneer kamar wata radio mai jini ba kya ko son kiyi shiru, to sai ki tashi an zo daukar ki" na kalli inda suka saba tsayawa idan suka zo, gabana ya fadi sosai, Abbu ne yazo daukar mu! Ganin Qaseem ya fito yana tunkarar wajen da nake yasa na mike ina lalubar jakata nawa Ramlah sallama. A hankali kuma a sanyaye na bude bayan motar na shiga, "Abbu ina yini?" na furta cikin siririyar murya ta, ya amsa "lafiya qalau Nafeesah, ya kika baro Kaduna?" na amsa da lafiya lau. Yaja motar muka tafi babu mai furta uffan. Hafsat ce ta ciro drawing book dinta daga cikin school bag dinta tana nuna min Assignment din dana taya ta jiya akan zanen gidaje da motoci, tace "Kuma Uncle Jamilu yace ni na cinye 20 over 20 duk cikin class din" na shafa kanta ina murmushi, "Ohh that's very good princess, am proud of you" tayi dariya tana kwantowa a jikina na rungume ta. Muna isa gida sallah muka yi, na bude fridge na ciro fura da nono dana kawo daga gida, musamman Mommy ta bada aka yi, na zauna na dama ta da dan kaurinta na saka kankara da dan sugar, cups na dauko na zuzzubawa su Abdullahi. Muna zaune a falo muna sha kafin lokacin zuwa Islamiyar su yayi. Abbu ya fito daga daki hannunshi dauke da jakar laptop dinshi, dan karamin coffee table din dake gefen mu ya janyo ya dora laptop din nashi akai, kasa kasa yake kallon mu har ya zauna. Ya kalli kofin dake hannuna yace meye wannan kuke sha haka babu tayi? A kunyace nace fura ce! Idanunshi suka dan ware cikin mamaki, "wow, daga ina muka samu fura?" Hafsat tayi caraf tace "daga gidansu tazo da ita jiya!" ya jima sosai idanunshi suna kaina ban san ko tunanin me yake yi ba, ya kauda kanshi ya maida shi ga laptop dinshi, "tunda ba a mana tayi ba ni zan yiwa kaina, a bani idan da akwai" da sauri na tashi naje na dama mishi na kawo na ajiye mai a gefenshi. Su Hafsy suna wucewa makaranta na koma dakina na zauna ina kallo.

[12/9, 9:48 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *12*


          Ya Allah! Cheerful Abbu din dana sani ya tafi, wannan Abbu din ban taba ganin shi ba, a fusace yake sosai kamar wanda zai tashi daga zaunen da yake ya hau ni da bugu, gabadaya jikina ya dauki rawa hawaye suka ciko idanuna, bana son fada ko kadan a rayuwata. Cikin rawar murya irin ta wanda yake so ya fashe da kuka nace, "Naje saloon ne shine na biya gidan su kawata Ramlah" ya galla min harara, "da ixinin wa??" nace "umh, ai na fadawa su Malam Bala da suka zo dauka na dazu", yayi shiru kawai yana kallona. Malam Bala ya fada mishi tun dazun, that means he have no right to be angry at her, but still, he's just pissed up. Dan siririn tsaki yaja ganin har na fara shesshekar kuka, ya shafa tattausar sumar kanshi da a koda yaushe a gyare take tana sheki, "it's okay....  Bani ruwa a fridge" da sauri naje na dauko na kawo mishi, yasa hannu ya amsa fuskar shi har lokacin a murtuke, ganin nayi tsaye naki in tafi yasa ya juyo yana kallona, "what?" he sounds so pissed up at me, da sauri na hau share kwallar data fara xubo min again nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi ba zan kara ba don Allah" ya lumshe idanunshi a hankali, "it's okay Nafeesah, banji dadin abinda kika yi ba, a gidanku kina kai har Magriba a waje?" nayi saurin girgiza kai, "to me yasa a gida na? Saboda kin raina ni ne ko kuma don kin baro gidanku kina tunanin zaki yi duk abinda kike so anan ba tare da an miki fada ba?" nan ma kai na girgiza a hankali nace "tun dazu muka taho, gidan Akwai dan nisa ne daga yau" yace "bana tolerating abubuwan nan Nafeesah kin gane? Daga yau kada ki sake wuce bayan Magriba a waje...... No! Duk inda zaki fita you must tell me first indai kina cikin garin Kano, understand?" nayi saurin jijjiga kaina, yace "you can go now!" kamar wadda take akan kaya, da sauri na wuce dakina. Sallah na fara yi kafin na kira mommy muka gaisa, labarin abinda ya faru na shiga bata, budar bakinta cewa tayi "ai yayi min daidai wallahi, wato har kin fara yawo barkatai ko?" sai lokacin naga wautata dana fada mata, na batan fuska kamar ina gabanta tare da turo baki, "mommy! Saloon fa naje saboda Allah daga can na wuce gidan su Ramlah, Ramlah ce fa kawata ke kanki kin shaida sau nawa take zuwa gidan mu ta kwana?" tace "but still baby, bai kamata ki tafi ba tare da kin fada mishi ba, kin san dole ranshi ya baci dama" na shiga diddira kafata a kasa ina gunaguni, "ni dana sani dama ban fada miki ba tunda ba zaki goyi bayana ba" ta sassauta muryar ta, "Ohh Nafeesah baki fahimta koh? Ba goyon bayan shi nayi ba, it's just the fact. Ke yanzu amanar muce a hannunsu, kina ganin ya dace ya barki ki dinga fita kina dawowa duk lokacin da kika ga dama a garin da yake bakon ki iye? Ko kina ganin girmamawa ce ki kama hanya ki fita ba tare da kin sanar dashi ba? Wani Malam Bala is not an excuse tunda ba a karkashin kulawar shi kike ba kin gane?" na gyada kaina a hankali she's right. Muryar daddy na jiyo ta cikin wayar, "Habibty ke da waye kuke waya kika kyale ni ni kadai a falo?" da sauri na shiga mata magiya akan Kar ta fada mishi hirar da muke don nasan kadan daga cikin aikin Mommy ne, ta ba daddy din muka gaisa. Hira muka shiga yi yawanci ta wajen aikin shi ce, mun jima sosai kafin muka yi sallama dasu. Kayan barci na na zura na bi lafiyar gado ko abinci ban nema ba.


          Ina kan sallaya ina lazumi bayan nayi sallar asubahi, ban cika komawa barci ba a irin wadannan lokutan, kofar dakin naji ana kwankwasawa, na tashi naje na bude, Harira ce. Muka gaisa da ita a mutunce tace "dan Allah Nafeesah ko zaki taimake ni da girkin yau? Bana jin dadi ne" nayi fuskar tausayi nace "Eyyah sorry pa! Meye za a dafa?" tace "ki dafa duk abinda kika ga ya dace nace "to shikenan" tace nagode ta wuce dakinta. Daki na koma na dauko karamar hijabi data tsaya a kuguna na saka na fita zuwa kicin, yam delight nayi, kafin dahu sai na dauko fresh kifi a cikin fridge na fara shirin yin farfesun kifi. 


       (Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe please, da kyar ma na samu na warci lokaci nayi typing dinshi wollah)


                         *♡Jeedderh♡*

[12/9, 9:50 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *13*


              Hankalina gabadaya ya tafi ga tsame doyar da nake yi daga cikin frying pan naji motsi a bayana, da sauri na juya har mai na fallatsan min a hannu na danyi kara kadan. Abbu ne sanye da wandon Jersey me layi layi irin na sport navy blue da top grey, gaban rigar zuwa tsakiyar kirjinshi ya jike da sweating alamun daga exercise yake. Yadda kayan nan suka mishi kyau suka mayar dashi kamar wani matashi at his Twenteth, you might even mistook him da wani modeler a babban kamfanin nan dake saka kayan sports, ko kuwa..... Ban san cewa na dulmiya cikin tunani ba sai dana ji saukar tattausan hannunshi a dantsen hannuna, tingling feeling din dana ji bashi da maraba da irin wanda naji ranar nan da nayi mistaking taba hannunshi. Na zabura nayi tsalle gefe guda tare da sakin matsamin dake hannuna ya fadi a tsakiyar kicin din, Abbu ya dube ni cike da mamakina, "hey! Are you ok??" cikin zaro idanu da rawar murya nace "ehh?" yace mai ya fallatsan miki a hannu, are you ok? Baki kone ba?" sai lokacin na tuno, sai kuma a lokacin naji zafi a wajen. Na dago hannun na kalli Inda man ya taba, thankfully bai yi komi ba sai dan ja da wajen yayi, nace "lafiya lau babu abinda ya same ni.... Ina kwana Abbu?" na fada ina dan dukawa, ya amsa, tare da dorawa da, "ya aka yi kike girki tun da safe?" na duka na dauki matsamin dana yar a kasa ina cewa., "Harirar ce bata jin dadi, shine tace in kama mata" ya gyada kai. Nace Akwai abinda kake bukata ne? Ya zuba min ido kamar mai tunani, "abinda yake bukata?" me  yake bukata exactly? Shi dai yasan yana cikin yin exercise dinshi yaji kamshin girki mai dadi yana bi ta cikin hancinshi, kamar maganadisu haka yaji ana jan shi har cikin kicin din..., ganin bai amsa ba yasa na juya na fara kwashe doyar dake cikin kaskon na fara tsoma mata. Yayi gyaran murya tare da fitar da dan sautin tari, "ehhhem, ruwa nake so" na bude fridge na dauko mishi mara sanyi na mika mishi da hannuna biyu ya amsa idanunshi na kaina. Na sadda kaina kasa saboda wasu particles da naga suna fita daga cikin idanunshi nashi suna shiga ta nawa kamar mashi, dan murmushi yayi ban san me yake nufi da hakan ba. Sai daya shanye ruwan tas ya miko min goran, na amsa na jefa ta cikin dustbin. "What can I help you with?" na jiyo muryar kamar daga sama, da sauri na dago ina kallonshi cike da mamaki, ta wani bangaren kuma ina tantamar Anya shine ya furta maganar? To amma waye zai furta idan bashi ba? Mu biyu ne kadai a kicin din. Kai na girgiza mishi a kunyace, ya daga kafada, "k! Let me go and take a shower then" ya juya ya bar kicin din, ni kuwa me zanyi ba kallonshi ba? Har ya fita daga kitchen din. Na maida bayana na jinginar da canter, idanuna a lumshe ina kokarin tantance abinda ke faruwa da jijiyoyina, kwalwa da zuciyata. 

        Bakwai saura na gama shirya komi akan dinning table, a gurguje na watsa ruwa na fito. Yau kam ban tsaya yin kwalliya ba balle bata lokaci wajen ciro kaya, simple kwalliya nayi daga hoda sai janbaki, na janyo wata atamfa English maroon color, dinkin rigar fitted ne sai zani 6-pieces, na kashe saurin dankwali kaman inji ne yayi ba hannu ba, na fesa turare tare da daukar jakata na zura flat din takalmi baki naja gyale na fita falon. Gabadaya kowa ya hallara akan dinning, nima sahun su nabi. Naja kujera kusa da Hafsy kamar yanda nake yi na zauna, Anty Mubeenah na gaida wadda yau er kwalliyar safen ma da take yi ba tayi ba da alamun ba zata leka wajen aikinta ba yau kenan. Shima Abbu sai dana sake gaida shi, shi kam a shiryen shi yake cikin Kaftan riga da wando ruwan madara  bai san hula ba amma fa yayi kyau kamar ka sace shi, su Qaseem suka gaida ni kafin muka fara cin abinci a nutse. Abbu ya kaimu makaranta yau, sai da muka ajiye su Hafsy kafin muka wuce. Ina zaune a gaban motar kaina a kasa, a darare nake kamar ace kyat! In zura da gudu, kira'ar Sheik Sudeis ce take tashi a cikin motar cikin suratul-Anfal, munyi nisa sosai babu mai yin magana a cikin mu. Ya kalle ni yayi dan murmushi, "me yasa ba kya sakewa ne idan ina kusa dake Nafeesah?" ya tambaya idanunshi akan titi kamar ma bashi ne yayi maganar ba, na kara sadda kaina kasa, Ya Allah! M I making it too obvious?? "umh?!" ya kara tambaya jin nayi shiru ban amsa ba, "ko kina jin tsoro na ne Nafeesah?" da sauri na girgiza kaina, yace to meye? Da kyar na iya cewa "babu komi Abbu?" ya kalleni sosai da idanuwanshi masu kama da wanda yake jin barci, da sauri na janye idanuna daga cikin nashi, yace "anya kuwa Nafeesah?" na gyada kaina da sauri, "da gaske nake Abbu, ba tsoronka nake ji ba" ya tabe baki yace "koma dai menene Nafeesah kiyi kokari ki rage shi, bana son hakan ko kadan kin gane?" na gyada kaina, yace good! Daga haka muka yi shiru har cikin makaranta, na bude murfin motar zan fita ya miko min kudi yan dubu dubu sabbi kar da ban san adadin su ba, kallonshi nayi cike da alamun tambaya, yace karbi mana! Na dan girgiza kaina, "amma Abbu me zanyi dasu?" yace ki badda mana. Na girgiza kaina da sauri, "no Abbu. Akwai kudi a hannuna wallahi, nagode sosai" ya dan hade fuskar shi, "to dama nace dake babu kudi a hannunki ne? Karbi nan tun kafin raina ya baci mana!!" a kunyace nasa hannu na karba, nace nagode Allah ya saka da alkhairi Abbu. Yayi murmushi kawai, sai dana ga bacewar motar shi daga idona sannan na shiga cikin lab. Ranar kam muka shiga shopping complex a cikin makarantar, sai da muka ga karshen 10k din daya bani tas ni da Ramlah, tarkacen kayan kwalam dana shafawa kamar zamu bude tireda.


   Will update you with the remaining part real soon, I'm kinda busy ne this days wallahi shi yasa amma komi ya kusa zuwa karshe da izinin Mai Sama

[12/9, 11:27 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *14*


                        A


             Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, "Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!....." ya zauna akan kujera yana maida numfashi, "it's just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu" jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. "nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci" jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar "who is she?" mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, "a sister" nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, "Ohh! Ashe sistern ka ce.... Ya kake?" muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya. 


       Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara'ar ta na koma gefe inan kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace "tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar" na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska "kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa" ta Harare shi, "ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?" ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa'an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, "Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?" Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, "Abban  Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda" ya kara kallon wajen, "anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani" ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na'urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, "tsagewar kashi ce!!" ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyaran yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, "da alamun amaryar ce koh?" ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce "ehhh?? Aah!!" ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, "bani ruwa Nafeesah!" da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna.

[12/8, 7:35 PM] ‪+234 813 546 1890‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *15*



         *'In a nation where the Poor face hardships, suffering and fears, only the riches and the one's that has power lives in peace, thrives and prospers....... Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ya Ibaadullaheessaaliheen!!!......'*



              Sai gab da Magriba su Anty Ameenah suka mana sallama zasu tafi, na leka dakin Anty Mubeenah wadda tunda aka kira sallar la'asar ta tashi da niyar zuwa tayi sallah bata dawo ba, na gaya mata zasu tafi ta leko suka yi sallama ta koma dakinta. Ni dasu Hafsy har Abbu mai kafa sai da muka taka musu har gaban motar da Anty Rahina tazo da ita. Anty Ameenah ta kalleni na goya baby Jameel a bayana yana ta shakar barci abin shi, tayi murmushi cike da tsokana tace "to Hajiya Nafee a bamu baby din koh?" na fara kokarin sauke yaron daga bayana, "Allah Anty ji nake kamar ku bar min shi!" su duka suka kwashe da dariya, Anty Raliya tace "kina son yara ne har haka?" nayi dan murmushi, "sosai ma! Amma mommy taki ta haifo mana wasu" na karasa ina pouting kamar inyi kuka dana tuno diramar da muke sha da ita idan ina mata maganar me yasa bata kara haihuwa daga kaina ba? Sai tace ai Allah ne bai kawo ba, ranar nan ma dana takura mata da tambaya zagi ta dankara min tace in cewa daddy na ya karo aure mana sai a Haifa min yaran, na tuna lokacin kuka na fashe dashi saboda zagin data min, shi kuwa daddy dariya ya dinga mana. Daga ranar ban kara mata korafi ba, sai dai in yiwa daddy. Su Anty Ameenah kam dariya suke min, sun fahimci tsantsan yarinta da sokancin da aka san Yaya irinmu nayi a tare dani. Anty Ameenah tace "Kar ki damu, in shaa Allah kema zaki haifi naki, kinga kin huta kenan koh?" na gyada kaina ina murmushi, "daddy ma haka yace ranar nan!" suka kara sakin dariya kafin suka shiga motar, na mikawa Anty Ameenah babyn tare da maida murfin motar na rufe mata tare da daga musu hannu, suka ja motar suka tafi. Na dan saci kallon Abbu kallona yake sosai with astonishment in his eyes, murmushi yake yi kamar kunnen shi zai zage, na samu kaina da tambayar dalilin sudden change dinshi curiously. Na kama hannun Hafsy muka koma cikin gida ya biyomu a baya. Muna gama dinner na musu sai da safe na koma dakina, sosai nake jina a gajiye ga wani barci daya rufe min idanu. 



            Kwana uku muna jinyar Abbu ni da yaran shi, ba laifi ya warke duk da cewa bai fara fita ba, kuma har zuwa lokacin Tafiyar shi bata koma irin ta normal people ba. Cikin wannan lokacin mun ga jama'ah ba kadan ba, ko wace rana sai mun ga bakin fuska cikin masu zuwa duba shi gaskiya Abbu yana da jama'ah sosai. Saurayin Ni'ima zai kawo mata ziyara ranar alhamis, ranar a lab muka wuni tare dasu suna jira mu tashi su wuce gidan su dani, na gaya musu Abbu ya hana ni yawo amma ina! Suka ce they wouldn't take no for an answer, dole suka saka ni kiran shi. Na fita daga cikin lab din bayan na danna mishi kira, bugawa daya biyu ya dauka ana uku, a sanyaye na gaida shi tare da tambayar jikinshi ya amsa da lafiya, nayi shiru ina kamo bakin zaren daga inda zan mishi maganar har sai daya tambaye ni ya? Sannan na gaya mishi kamar wadda take tsoron tayi maganar, shiru ya biyo baya kafin ajiyar numfashi mai nauyi, "amma kada ki wuce karfe bakwai baki dawo ba" da sauri nace "in shaa Allahu Abbu" daga nan muka yi sallama. Ranar tun kafin lokacin tashin mu yayi muka tafi. Unguwar Galadanchi muka nufa, ashe mahaifin su shi yake rike da sarautar Galadanchi ta garin Kano, babban gida ne wanda ginin shi na asalin gidajen sarauta ne, sashen Hajiya Fati muka fara shiga ita ce mace ta biyu a gidan, mace mai karimci ta tarbe mu da faraarta, na kula su Ni'ima kamar babbar Yaya suka dauketa don a sashenta ma suka ce zasu saukar da Bashir din. Cike da girmamawa na gaidata ta amsa da fara'ar ta tare da sawa aka kawo mana ruwa, mun dan jima a sashen nata kafin muka mata sallama muka wuce sashen Hajiya Siyama mahaifiyar su Abbu. Sashen nata in ka shiga baka taba cewa dakin er dattijuwa ka shiga duk da cewa shima sashen Hajiya Fati babu laifi. Babban falo ne wanda yasha saitin royal kujeru ruwan zuma, muka zube a kan wani tattausan carpet muna gaishe ta tana zaune akan sallaya tana lazumi, kana ganin kamilalliyar fuskarta zaka san cewa ka kalli fuskar ma'abociyar addini, babu abinda Abbu ya baro nata sai dogon siririn hancinshi, ita nata yana da dan fadi, sai data gama lazuminta kafin ta amsa mana cike da kulawa. Daga nan su Ni'ima suka jani muka je dakin su muka yi sallah, kayan jikina na canza muka shiga kicin muka fara shirya kayan abinci kala kala. Na bata shawarar mu yi snacks wanda zamu basu a matsayin tsaraba idan zasu tafi gobe, don haka muka yi doughnuts wanda muka yi icing dinshi muka watsa shredded cheese da chocolate akai. Karfe biyar suka karaso shi da abokin shi, mun riga mun kai komi sashen Hajiya Fati, mun shirya koina sai kamshi kawai dake tashi a wajen. Ita uwar gida ta musu rakiya zuwa inda aka tanadar musu mu kuma muka tsaya karasa gyara kicin din, sai da muka gama gyaran jikinmu sannan muka je muka gaisa dasu. Bashir din nata kamar yanda take fada dan kyakkyawa dashi ga barkwanci, abokin nashi ne ma bai mun ba ko kadan, sai wani shisshige min yake yi yana jana da hira duk ya takura min don haka na mike nace musu zan wuce gida, duk suka kalleni da mamaki ni kuwa Na Kauda kaina gefe don ma kar suga fuskar hana ni tafiya. Sa'adiya ta taso ta kama hannuna muka fita, abokin Bashir da naji yana kira da Fahad ya taso ya biyo mu, ganin babu fuska yasa ya juya. Na saki tsaki kasa kasa, Sa'adiya tayi dariya tace da alamun gayen bai miki ba, kai kawai na girgiza mata muka wuce sashen Hajiya Siyama. Tana kan daya daga cikin kujerun falon tana kallon tashar Saudi, ta kalle mu cike da mamaki, "lafiya dai ko?" Sa'adiya tace "wai gida tace zata wuce!" tace Haba ai kin tsaya kici abinci koh?" nace "Hajiya Abbu...." tayi saurin katse ni, "kyale shi kawai, ba zaki tafi ba sai kinci abinci fa" bani da zabi dole na wuce dakin su Ni'ima don bazan iya komawa wajen su nataccen abokin Bashir ba kuma bazan iya zama kusa da Hajiyar ba.


Sai wajen karfe bakwai da rabi sannan muka fito ni da direban da xai maida ni gida, bayan naci tuwon tsakin masara da miyar kalkashi wadda taji yajin daddawa, tantakwashi da man shanu ga kunun aya mai sanyi da Gardi a gefe. Tare dasu Ni'ima muka ci abincin bayan Tafiyar su Bashir, ta bude tarkacen kayan tsarabar daya kawo mata ta ciro min kayan shafa, turare ne da kayan makulashe naki amsa, sai da suka yi kamar zasu yi fushi sannan na saka hannu na dauko turaren 'splendid' tsohon turarena ne tun a secondary school, daga baya ya bata na gaji da nema na komawa kamfanin lily cool, Sa'adiya ta kara min da tarkacen sweets muka fita falo. Kicin na shiga na dauko doughnuts din dana debar wa su Hafsy, Hajiya na falon a zaune na durkusa a kusa da ita na mata sallama, ta min godiya sosai har sai dana ji kamar in nutse a kasa. Ta mikawa Ni'ima wata karamar silver grey din jaka tace ta bani, na mata godiya sosai kafin muka tashi, sai da muka je ta sashen Hajiya Fati na mata sallama kafin muka fita waje inda direba yake jira na, na shiga motar muka kara yin sallama dasu kafin muka tafi. Nayi shiru a bayan mota ina tunanin abinda zan fadawa Abbu, a raina addua nake ina karawa akan kada Allah yasa yayi fushi dani, naki jinin fushin Abbu kamar yadda na tsani bacin ranshi. Har cikin gida direba ya shiga dani, na fito daga motar ina mishi godiya tare da sai da safe, iska ake yi sosai kamar ta dauki mutum tayi yawo dashi, idanuna a rufe saboda kasar da iskar guguwa ta watsa min na shiga falon bakina dauke da addu'ar da ake yi idan guguwa ta tashi, kamar hadin baki ina shiga aka dauke wuta. Na bude idanuna da kyar ina murza su, kafin inyi adjusting da dan guntun hasken falon wanda ya ratso ta cikin shara-sharan labulayen dakin daga farfajiyar gidan wanda lantarkin solar ta samo dashi, naji kafana tayi stepping akan wani abu mai tsananin sul6i, kafin in tantance meye naji ni na fara tafiya sululuuuu.....!! A tsakiyar dakin, na kwala ihu sosai ina salati tare da laluben abinda zan kama in rike tunanin farko daya fado min a cikin raina shine hango ni da nayi na kai da bakina, kyawawan kananun hakora na guda biyu na gaba malale a cikin jinin dake fita daga bakina....... Karo na kaiwa wasu hard muscled chest wadanda ko a cikin duniyar mafarkina ban taba hangoni a kansu ba, sai ga gangar jikina a jikinsu yau kamar a mafarki, dogayen tausasan hannuwa suka zagaye bayana, daya a kuguna daya a gadon bayana, jikina yake dauki rawa kamar wadda ta rungumi kankara cikin hunturun sanyi yayin da naji wasu dogayen zara-zaran yatsu suna suna tapping din gadon bayana a hankali., ban san lokacin dana saki ledojin hannuna, purse dina da wayata akan tiles din dake cikin falon ba.....!!.






                   *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:36 PM] ‪+234 813 546 1890‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *16*


        *-Search across the Oceans for who are been lost for two long......* 

        *'Searching for a secret in coming home we find we have what we need.....!'*

             *-New Empire-* _Across the Ocean_


              Hankalina gabadaya ya dauke daga jikina, babu abinda nake fahimta sai tattausan kamshin dake fita daga jikin Abbu, bugawar da zuciyar shi take yi da dan sauri-sauri, dumin dake fita daga jikinshi....... Ya dago fuskata daga jikinshi yana kallona kamar hadin baki, aka dawo da wuta lokacin. Na samu kaina starring at his brown oily eyes da suke wani irin sheki kamar zaiba, "Nafee, are you ok??" cikin daukewar tunani na daga baki nace "umh???" ba tare dana yi kokarin dauke idanuna daga kanshi ba, ya dan jijjiga kafadata, "hey!" kamar wadda aka daddaba daga barci, nayi firgigit ina kallon cikin falon, Ya Allahu! What the heck just happened?? Da sauri na durkusa na tattara kayana da suka zube nayi hanyar dakina a sukwane, da sauri ya riko tsintsiyar hannuna, nayi cik ina sauraren abinda zai ce ba tare dana juya na kalleshi ba, "lafiyar ki kuwa Nafeesah?" da sauri na gyada kaina, "lafiya lau, kayi hakuri dan Allah" ina jin sautin murmushin daya saki, ya sakar min hannu dama abinda nake jira kenan don haka na bazama dakina a sukwane. Kofar dakin na maida na rufe tare da murza key, nayi wuri-wuri a tsakiyar dakin kamar wadda take neman wajen buya kafin na zube a kasan dakin akan gwiwa na, zuciyana wani irin gudu take yi, na rasa abinda yake min dadi a lokacin. Ban san iya lokacin dana dauka a wajen ina zaune ba, tare da taimakon Innalillahi.... Dana dinga ja na dan samu sukuni a cikin raina, tashi nayi na fara bandaki na watsa ruwa mai sanyi a jikina duk da sanyin da ake yi sakamakon iskan da aka gama yi. Na fito daure da tawul a jikina na tsaya a gaban mirror, lotion na shafa na saka rigar barci wadda ta tsaya min a gwiwa, duk abinnan da nake yi idanun Abbu suna cikin memory na, na rasa abinda zan yi da zai dauke min tunaninshi daga cikin raina, chatting! Zuciyata ta tuna min, da sauri na tafi inda nayi jifa da kayan hannuna tare da wayar na dauko ta, ina daga ta na dan saki kara ganin yadda screen dinta ya tsattsage, na ciza tattausan lebena na kasa ina ji kamar in dora hannu aka in saki ihu saboda yadda nake son wayata dinnan, bana so ko datti ya hau kanta. Ganin chatting din ma bai mun abinda nake so ba yasa na janyo system dina na kunna na fara kallon Baywatch, ajiyar zuciya na dan saki ganin hankalina ya dauke zuwa ga film din. 



         Sai Washegari na ba su Hafsy doughnut din dana kawo musu, tare dasu ma muka cinye shi a cikin mota. Yau Daddy da kanshi yazo daukata, yazo duba jikin Abbu ne. Sai da aka yi sallar la'asar muka wuce Kaduna, bakin daddy bai yi shiru ba a hanya yana ta bani labarin kirki da mutunci irin na Abbu, bai san cewa yanzu bana cikin mood din sauraren labarin Abbu bane, ko sunan Abbu aka ambata sai naji faduwar gaba, shi yasa yau nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin na kaucewa haduwa dashi, nayi, sai dai dole sai da na ganshi lokacin da muke mishi sallama ni da daddy. Kaina na jinginar da jikin seats din da nake kai na lumshe idanuna kamar mai barci, hakan yasa daddy ya kama bakinshi ya bame har muka isa Kaduna. 


Da dare Ni'ima ta kira ni, bayan mun gaisa take fada min wai Fahad dinnan ne abokin Bashir ya dame ta akan ta bashi number na, na tabe baki nace "kada kiyi kuskure bashi Ni'ima" tace me yasa? Nace ban gane ba? Waye a cikin ku bai san cewa Akwai wanda nake dating ba? Taja tsaki, dallah dating ko crushing?? Waye bai san cewa crushing din Muneer kike yi shi baya son ki ba?? Na dan dakata kadan kafin inyi magana, "Ramlah mai bakin Aku!! Ita ta fada muku koh?" daga can tace that doesn't matter ko kadan ai, ni ai zan bashi number! Nace cikin gatse, "ki bashi din toh, zaki gani ne" na katse wayar tare da jifa da ita akan gado. Muneer!! Na maimaita sunan, it's kinda strange. Rana bata taba fita ta koma ga ubangijinta ba ba tare dana tunana bawan Allahn nan a cikin raina ba, amma har ga Allah yau dai, yau gabadaya na manta da existing dinshi a duniya, Anya lafiya ta lau kuwa??! Tashi nayi na koma falo wajen su daddy muka sha hirar mu, sai dana fara hamma sannan na musu sallama na wuce dakina. 


Da safe na ba daddy waya na nace a canza min screen din, Koda ya tambaye ni dalilin tsagewar ta cewa nayi faduwa tayi, to me zan ce mishi? Kafin azuhur sai gashi da sabuwar Samsung edge plus, nayi tsalle, nayi ihu na rungume shi, wayar da nake masifar so kenan sai dai bana so in takurawa iyayena da zancen wayar da nasan kudin abincin wani na shekara daya ne, shi yasa nayi shiru, sai gashi yau Allah ya bani ba tare dana roka ba. Daddy kam yasha addu'a ranar kamar bakina zai tsinke, haka nake ni kam, idan aka min kyauta sai in wuni ina wa mutum godiya. Mommy na cewa ta bada ayi fura don na kula Abbu yana so sosai, duk ranar dana kai fura ranar ita ce abincin shi har ta kare. Washegari na doshi hanyar Kano cike da tsaraba don sai da muka shiga shago na saiwa Hafsy dasu Qaseem sannan muka wuce, cike kuma da wani longing, longing to see someone wanda na ma rasa a wane matsayi zan ajiye shi cikin raina., abokin Babana ko kuwa Abokin Rayuwata??!



Aunty Mubeenah da wata kanwarta Shakirah kadai na taras a gidan, ina ga Abbu ya fita zagaya unguwa kamar yadda yake yi lokaci zuwa lokaci da er sandar taimaka tafiya, na durkusa na gaida su, Anty Shakirah ta mun sannu da zuwa har tana tsokanata da ina tsarabar ta tunda Allah yasa tana nan nazo. Matar tana da kirki, duk tafi sauran en uwan Anty Mubeenah da suke zuwa gidan, wasu idan suka zo ko kallon mutane basa yi balle su amsa gaisuwar su, wasu kuwa kallon mutane suke yi kamar kiyashi shi yasa nima bana kula da kurar data debe su. Dariya na dinga yi tana tsokanata, na ciro chocolate din kit-kat babba na bata nace ta kaiwa yara, na ciro wani hadadden turaren wuta na asalin en maiduguri na ba Anty Mubeenah inji Mommy na, ta amsa babu yabo babu fallasa, babu godiya ba komi kamar wadda ta bani ajiya, naji haushin abun ba kadan ba, na mike daga zaunen da nake na dauki jakar hannuna na wuce dakina. Kayayyakina na ciro na shirya komi a inda ya dace, na ciro fura da nonon da aka wa Abbu na Kai fridge na ajiye, daga kicin ina jiyo hirar dasu Anty Shakirah suke yi saboda a falo na biyu suke wanda yafi kusa da kicin din, Anty Shakirah ce take tambayar Anty Mubeenah mai yasa bata son turaren? Tace to mai zanyi dashi? Idan baki so ki bani ai ban rasa wanda zan ba bane, da sauri naji tace ina so wallahi, turaren ne yana da tsada naga gashi yana da wahalar samu shi yasa! Nayi kwafa ina girgiza kaina, wato kyauta ma tayi da turaren wutar da babu yadda ban yi da mommy akan ta bani in kaiwa Anty Haleemah ba mommyn taki ita ala dole sai ita, to ga abinda ya faru nan ai!. Dakina na koma cike da takaici ban jima da shiga ba naji hayaniyar su Hafsy a falo, da sauri na fita. Suna gani na suka kwashi ihun murna duk suka rugo, kowannen su so yake ya rungume ni, ni kam dariya kawai nake ina ihun su sake ni daga cakumar da suka kin kar su kayar dani amma ina! Sai da suka gaji dan kansu sannan suka sake ni, Abbu yana bayansu ya jingina bayan shi da kujera yana kallonmu cikin murmushi, da sauri na zube a kasa ina gaida shi, can kasan zuciya ta wani irin farin ciki yake mintsini na. Yaran naja muka tafi dakina tun kafin inyi abinda zan zo ina dana sani don wani sashen na zuciyata wai rada min inje in rungume shi yake yi. A daki na baza musu tsarabar dana kai musu, nan muka baje muka ci wasu a gun wasu kuma suka diba suka tafi daki lokacin da aka kira Magriba, ni da Hafsy kuma muka yi tamu a daki.


         Muna gama dinner na mike da niyar inje in kwanta, Abbu ya kalleni yace "Nafeesah Akwai fura ne?" na gyada kaina a hankali, wata irin kasala ta rufar min saboda yadda ya kira sunana, yace dama min pls. Na wuce kicin na dama mishi furar, nasa ayaba lokacin da nake damawa dana gama kuma na watsa kankara a ciki na dauki bowl din dana juye furar a cikin na koma falo, yana sec parlour a kishingide akan kujera da alamu waya yake amsawa, cikin harshen turanci yake wayar. Na ajiye a gabanshi na fara kokarin zubawa a cikin cup ina satar kallonshi, wayar yake amsawa cike da wata irin yanga  yana yi yana wani lumshe ido, accent din turancin shi ko kadan bai yi kama dana bahaushe ba, idan kana ji sai kayi zaton ko rainon kasar Ingila ne, to waya sani? Naji ance a LA ya kammala digiri dinshi na farko. Na danyi murmushi ina girgiza kai, sau tari ina mamakin yadda Abbu yake da yanga kamar wata mace, zaka iya mistaking kace yanga ce kam idan baka zauna dashi ba don a zahirin gaskiya haka yake naturally. Ya ajiye wayar hannunshi akan kujerar yana zama sosai, "what's funny?" da sauri na girgiza kaina "ba komi?" na mika mishi cup din, ya kura min idanu kamar yana so ya karanci abinda ya saka ni murmushin da kanshi, nayi kasa da kaina, ina jin sighing din daya saki kafin ya amshi cup din, da sauri nayi niyar tashi ya tsayar dani ta hanyar tambayana ya Daddy na? Nan fa na zauna na fara zuba mishi labari har na wayar da daddy na ya canza min, ya daga girarshi yana dan murmushi, "inye! Her daddy's girl!!" na sadda kaina kasa ina murmushi in ma zan iya cewa kila har da blushing, ya jefo min tambayar data kada min ciki, "garin yaya har screen din wayarki ya fashe?" na yi wuki-wuki da idanu kamar wadda aka kama tayi karya, ya sake tambayana, kafin in lalubo abinda zan ce wayar shi tayi kara, yana dauka na lallaba na mike da sauri sai dakina. Ina shiga na ajiye numfashi da karfi, Allah ya cece ni yau. Kayan barci na saka, na dauko log book dina na bude na dan dudduba kafin na janyo system dina na cigaba da kallon Pinocchio dana fara yi. Wajen karfe tara da rabi naji wayana tayi kara, na daga ganin bakuwar number yasa na daga da sallamata, daga can wata familiar murya ta amsa sallamar tare da karawa da "gorgeous!" cike da mamaki nace "waye?" sai dana kusa dakin zagi lokacin da naji yace "Fahad ne, abokin Bashir Saurayin Ni'ima" na hade fuska kamar yana gani na, jin nayi shiru yasa yace "gorgeous, baki gane ni bane?" a raina nayi exclamin kalmar 'wai gorgeous!' cike da jin haushi nace na gane ka mana, and please suna na Nafeesah ne ba wani abu wai gorgeous ba ka gane!" ya saki wata dariya data kara kular dani, "Haba gorgeous! To me kin cancanci abinda yafi wannan sunan ma. Kawai ki bani dama in nuna miki how precious you are to me, wallahi tun ranar dana saka ki a idanuna naji cewa na samu macen dana dade ina nema a rayuwata, tun daga ranar na baki wani matsayi mai girma a cikin raina, Gorgeous, wallahi u've become a very special part of my being, you are my happiness, you've got everything I need from my wife you are classy, beautiful, hafiza.....!!" blah-blah-blah ya shiga jero labarai har na gaji da saurare, ganin yaki dasa aya yasa na tsaida shi, "please Malam! Ita wadda ta baka number dina bata yi maka bayanin ina da Mijin aure bane?" ya kara sakin dariya, "ta dai fada min cewa kina da wanda kike so and unfortunately though to my relief baya sonki in return, baby just leave him, bai san ciwonki ba. I promise you zan so ki fiye da yadda yake sonki, na miki alkawarin mantar dake cewa kin so gayen can baby, just give me a chance kinji?" ni kam ina baki? Zuciyata cike da takaicin tonon sililin da Ni'ima ta min. Da kyar na saisaita kaina daga ihun da nake ji a cikin kaina na son in sossoka mishi zagi na dai yi kokari nayi calming din kaina, after all ai ba laifin shi bane, zamu gauraya da mai laifin. Duk da haka ban iya tsaida tsakin daya fito min ba, nace "Malam I don't need your love or whatever trash you are talking about ka gane? Don Allah Kar ka sake kira na!" na kashe wayar da sauri. Ni'ima na kira, cikin sa'a ta dauka a ringing din farko, ko sallama ban bari tayi ba na fara zazzaga mata ruwan masifa, daga farko hakuri ta fara bani, daga kuma sai ta fara tsokanata wai akan ta ma taimake ni? Nace taimakon ki din banza? Nace miki ina so ne? Tace baki fada ba, zuciyar ki ta fada min. Ganin ta maida abun wasa na kashe wayar ina kara maimaita mata ta kira Fahad ne koma uban waye sunan shi ta gaya mishi kada ya sake kiran wayata don duk ranar daya kuma sai naci Mutuncin shi, ita kuma ta jirayi haduwar mu gobe!! Tace "Allah ya kaimu" cike da izgilanci, na kashe wayar ina kwafa. Ajiyar zuciya nake saukewa cike da takaici kamar zan hadiyi zuciyata in mutu. Karan wayata naji, da sauri na wawuri wayar ina tunanin kalar zagin da zan narka, ganin sunan Mommy ne yasa na dan saki fuskata kafin na dauka, gaisawa muka yi ta tambaye ni na sauka lafiya? Na amsa mata da lafiya lau. Mun danyi hira da ita kafin muka yi sallama, na dora wayar akan bedside drawer ni kuma na kwanta bayan nayi dimming din wutar dakin. 





                       *♡Jeedderh♡*


[12/8, 12:46 PM] ‪+234 810 910 7052‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *17*


              *HADITH*

          Abdullah bin `Amr bin Al-`as (May Allah be pleased with them) reported: A man asked the Messenger of Allah (PBUH): "Which act in Islam is the best?'' He (PBUH) replied, "To give food, and to greet everyone, whether you know or you do not.''

[Al-Bukhari and Muslim].


         Washegari kam su Ramlah sun ga tsiya a lab, Tunda muka zo na samu gefe daya na zauna fuskana a cune, ban mata magana ba balle sauran en lab din, su Ni'ima ma Suka zo naki kallon inda suke, ina ji suna tambayar Ramlah meke damuna ne tace itama tunda taxo a haka ta same ni. Har muka tashi a ranar ban kalli inda suke ba, sunyi maganar sunyi tsokanar duk a banza. Muna fita na fara kokarin wuce su, Ramlah tayi saurin tare ni tana harara ta, "wai ke dallah malama meye kike wani yazga mutane tun dazu?" nima na harareta, nace "ban sani ba dallah bani hanya!" Ni'ima ta matso tace "in dai akan zancen Fahad ne don Allah kiyi hakuri, wallahi dana san Abun zai bata miki rai da ban bashi number din ba, kiyi hakuri sis kinji?" na ajiye numfashi tare da kallonta, "ni fa ba bashi number din da kika yi bane ya bani haushi sai zuwa da kika yi kina yada sirrina a wajen stranger. Saboda Allah meye na zuwa kina gaya mishi wai ina crushing din wani?" tayi fuskar tausayi "Nima nasan ban kyauta ba, da gaske ban san lokacin dana gaya mishi ba wallahi, hira ce tayi hira ni kuma na saki baki ina bashi labari, amma don Allah kiyi hakuri" nace shikenan ya wuce, ta rungume ni tana er dariya, thanks sissy. Na harari Ramlah nace "ke kuma ba zaki bani hakurin bane?" ta zaro ido waje, "ni kuma me nayi?" nace waye ya gayawa su Ni'ima cewa ina crushing Muneer idan ba ke ba?" ta ta6e baki, "dadin ta ma ba karya nayi ba" nayi murmushin yake, zan ga ranar da Ramlah zata yi abu like a good girl in dai akan zancen Muneer ne, she's always playing bad, making it obvious that bata son gayen ko kadan, to amma ya zan yi? A gani na Allah ne ya dora min son Muneer bani na dorawa kaina ba. Da haka dai muka shirya muka hau hira har Malam Bala yaxo muka tafi har su Ni'ima din zasu je su ga jikin Abbu. A can muka Tarar dasu Anty Rahina suma sun zo, nan muka wuni dasu muna ta hira har Yamma tayi kafin Suka tafi. Tun daga ranar kuwa ban sake ganin kiran wayar Fahad a waya na ba. 


                Satin Abbu uku yana jinyar kafar shi kafin ya warke ya fara fita harkokin shi. Naje gida weekend muka je Malumfashi, Malam Inuwa kanin baban su Daddy ya rasu, kakanni na na ainihi sun jima da rasuwa ban yi wayo na ganni dasu ba, shi yasa su Hafsy suke burge ni ba kadan ba, suna da kakanni ta kowanne fanni abin su. Wato naji dadin zuwa Malumfashi wannan karon ba kadan ba, cousins dina duk sun dawo daga makaranta wasu hutu suka zo wasu kuwa sun zo wajen gaisuwa ne, nan muka hadu muka yi ta yawace-yawace da ziyara har ban so lahadi tayi ba, haka dai muka yi sallama da dangina muka wuce gida. Muna isowa na wuce Kano Saboda yamma tayi don haka a gajiye likis na isa gida, babu abinda na iya tsinanawa, ina gama sallah na bi lafiyar gado sai da gari ya waye. 


        Mun je lab Ramlah take bani labarin wata er ajinmu a Kasu zata yi aure wannan week din, er Kano ce, ta tambaye ni zan je nace ai dole ne, Sahiba mutuniyar mu ce ta sosai. Tun a ranar na kira daddy na fada mishi ba zan samu zuwa weekend wannan satin ba saboda bikin abokiyar karatun mu yace shi kenan Allah ya kaimu wani satin. Nayi shiru ban kashe wayar ba, tuni ya fahimci abinda nake nufi, "kudin anko koh?" naji ya tambaye ni, na saki murmushi mai sauti, wato Daddy ya karance ni kamar bayan hannunshi, yace "I will wire you the money in the next few minutes" nace "to Daddy nagode, Allah ya bar min kai!" yayi dariya tare da cewa "uwata kenan". A ranar muka shiga kasuwa muka sayo ashoben bikin, muka biya ta wajen telan Ramlah muka ajiye dinkin. Ranar juma'ah muka je saloon aka mana wankin kai da kitso, ni har kunshin hannu aka min, dama gani da son lalle kamar me. Ya kuwa yi min kyau sosai, sai da Ramlah taga na hannuna wai take cewa data sani da an mata itama, na kuwa dinga mata dariya. Daga nan muka yi shatar taxi muka wuce gida, sai da muka ajiye ta kafin muka wuce. Ina shiga falon naci karo da buhunan Irish, plantain ne, kayan marmari dasu doya, tunda na gani nasan cewa Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ibadan taron Doctors na fadin Nigeria, Allah ya taimaki rayuwata na mishi text na gaya mishi zamu biya ta saloon daga lab, yau da na shiga uku na ai. Na taimakawa Harira muka kai kayan kicin muka ajiye su a inda ya dace kafin na wuce dakina nayi sallah. Ina xaune Hafsy ta leko dakin tace in fita mu ci abinci, bana ma jin yunwa amma haka nan dai na fita don nasan bani da wani excuse din badawa. Na dauki gyale mai fadi na dora akan doguwar rigar jikina. Bana yarda in fita daga dakina ba tare da mayafi ba matukar nasan Abbu yana gari sai dai by mistake. Suna kan dinning table a zaune, Abbu na fara hangowa. Sanye yake da shirt din KC brown da bakin Jeans, ya kara wani irin kyau na musamman a kwanaki shida din da nayi ban gan shi ba. Na tafi da dokina na durkusa na gaida shi, shima cike da fara'ah ya amsa min, na gaida Anty Mubeenah kafin naja kujera na zauna muka fara cin abinci. Da muka gama Abbu ya fita, Anty ta wuce daki mu kuwa muka zauna a falo muna kallo har wajen karfe goma da rabi, har lokacin Abbu bai dawo ba. Na kashe kayan kallon kowannen mu ya nufi dakin shi ya kwanta.

[12/8, 12:53 PM] ‪+234 810 910 7052‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *18*


          _'Turn to Allaaah he's never far away......_

           _'Put your trust in him, raise your hands and pray..... Ohhh Ya Allah! Guide my steps don't let me go astray..... You're the only One Who can show me the way..... Show me the way........ Show me the way...........'_

                   *In Shaa Allah by Maheer Zayn*


           Da kyar na samu na sauka daga kan gadona ganin na gaji da juye-juye barci yaki zuwa misalin karfe tara kenan na washegarin ranar Assabar. Na fito daga dakina sanye da wandon Sports da rigar shi cotton ruwan madara, na dora hular beanie akaina wadda na nannade gashin kaina na saka a ciki. Wandering na fara yi a cikin falon hannuwana saye cikin aljihun wandon. Na tsaya a kasan staircase din dake falon, tunda nake a gidan ban taba Hawa saman ba, jifa-jifa dai na kan ga ko dai Abbu ya hau ko kuma yara sun sauko kuma ban taba tambayar me suke yi a wajen ba. Out of curiosity na fara takawa ina hawa saman, Tun kafin in karasa na saki baki galala ina kallo. Gym zan kira shi ko kuwa amusement park?? Kayan wasan yara kala-kala da different types of exercising machines ne birjik a wajen, wasu na san su saboda nima ina zuwa gym duk weekends lokacin da ina gida. Na fara zagaye wajen cike da mamaki, as in Abbu will never cease to amaze beings. Kan Dip station na hau na fara kokarin dagawa amma ko motsi, da alamun yafi karfina ne don haka na sauka. Daga bayana naji ance "hey! What are you doing here??" da sauri na juya, yana tsaye a jikin wata kofa sanye da sportys ya rataya dan karamin tawul a wuyanshi, na sadda kaina kasa cikin rashin abin cewa. Ya fara takowa a nutse har yazo gab dani, ya jingina da station machine din, jin yayi shiru nasan sauraren amsar da zan bashi ne yake yi, nace "umh! Dama kawai ina zagaye ne sai kuma naga na shigo nan" yace "this is your first time here I believe?" na gyada kaina. Yace I see. Are you interested in exercising?? Da sauri na dago ina kallon shi, "sosai ma Abbu! A gida ma ina zuwa gym duk sat...." wani irin kallo yake wata min babu shiri na kama bakina na bame, na sadda kaina kasa ina jin kafafuna suna dan shaking. Kokarin fita ya fara yi yana cewa "sai ki dan motsa jikinki ko? Ni zan sauka kasa..... By the way, I like your lalle!" nayi murmushi ina kara kallon hannuna, ni kaina nasan lallen yayi kyau sosai. Yana fita na fara wasa da karafa, sai wajen karfe goma da rabi na sauko falo, break nayi na koma dakina, sai lokacin naji gajiya da barci sun tarar min na kwanta. Kiran wayar Ramlah ne ya tashe ni daga barcin da nake yi, tace gata nan ta shigo layin mu daga amsar dinki in fito waje, na tashi da sauri na dora hijabi akan kayana na fita. Abbu da maigadi da wani makocin Abbu din suna kofar gida akan dan benci suna hira, na gaidasu. Ina tsayawa sai gata cikin napep, ta fito ta biya mai napep din, ta gaida su Abbu kafin muka shige cikin gida. Muna shiga ta fara jefo mun tambaya a rikice, "ke waccan giant gaye din waye? Anan gidan yake zaune?" cikin alamun tambaya nace wa kenan? Tace "wani farin gaye haka da jallabiya baka a jikin shi??" dariya na kwashe da ita nace "wai dama baki san Abbu ba duk abinnan da ake yi?" tayi turus! Da gaske wancan ne Abbu? Na gyada mata kai, "Ya Allah! He's cool babe, dan dai yana da mata wallahi....!" duka na kai mata ina dariya, "da bashi da mata fa sai kiyi me maras M? Kina da mijin aure a hannu dai shegiya" ta turo baki. A dakina muka zube, ta fiddo kayan sun yi kyau sosai, "sai dai rigar tayi show me da yawa" na fada cikin korafi ina kara juya rigar, ta harare ni, "to sheikha. Ina cewa gyale zaki saka?" na turo baki kafin na daga kafada sama.


                       Wajen karfe hudu muka isa wajen shagalin bikin. Tuni an fara shagalin, yawancin en makarantar mu sun je abin an jima ba a hadu ba nan muka hadu aka yi ta hirar yaushe gamo ana hotuna. Ana gama sallar ishai'i aka fara daukar mu zuwa wajen dinner. Mun sake wata kwalliyar cikin doguwar rigar gown ta ankon zuwa dinner, purple ce sai rose head maroon color da heel shima maroon sai er karamar jaka maroon. Mun sha kyau abinmu kamar ka sace. Mun fito muna kokarin shiga mota zuwa wajen dinner nace karo da Bilyamin abokin Muneer, da mamaki ya min magana na juyo ina kallon shi, nima mamakin ne ya kama ni kafin muka gaisa dashi yake gaya min angon abokin shine. Ya Kalle ni tun daga sama har kasa yace "amma kinyi kyau sosai Nafee" nayi murmushi sosai har da fari, I'm a sucker for compliments. Yace "naga kina yawo ke kadai, Zan iya rokon alfarmar ki zama date dina for today?" nace "y not?" na kira Ramlah tazo muka shige mota abin mu muka wuce. Muna tafe muna ta hira har wajen dinner, wajen ya tsaru sai sautin kida ke tashi muka samu waje muka zauna, amarya da ango ana kan high table. An fara shagali kawayen couple din suka fita fili muka dan taka rawa da liki muka koma wajenmu muka zauna, ana ta shagali har ban san lokaci ya tafi ba sai dana ji karan shigowar message a wayana ta hanyar vibrating, na daga karfe goma da rabi gabana yayi mummunan bugawa, na duba message din daga Abbu ne, *"Where are you now?"* na mike da sauri jikina yana rawa, su duka suka juyo suka kalleni, Ramlah tace meye? Cikin rikicewa nace "Abbu..... Gida. Gida zan tafi yanxu" tace haba! Ki jira a tashi mana dan Allah kinda fa sauran mutane suna nan" nace "noo Ramlah. Abbu just texted me, nasan ma sai na sha fada yau wallahi" ta kalle ni sosai, "to sai me? Ina ce ba Daddy bane? Nasan ko daddy ne ba zai miki fadan kinyi dare a wajen dinar biki ba" na girgiza kai, "baki san Abbu bane Ramlah..... Bilyamin don Allah ko zaka taimaka ka mika ni gida? Babu nisa daga nan" na maida maganar ga Bilyamin don nasan idan nace zan tsaya fahimtar da Ramlah zamu iya kwana a wajen bata fahimta ba, ya mike yana lalubar makulli a cikin aljihun wandon shi, ya ciro key din ya Kalle ni, "muje koh?" na wa Ramlah da wasu daga cikin mates dinmu dake kusa da inda muke muka tafi. A cikin mota Bilyamin yana ta ja na da hira amma sam hankalina baya wajen ko kadan, da kwatance yayi parking a kofar gate. Na bude murfin motor na fita shima ya fita, na zagaya ta gefen shi nace "to Bilyamin ka gaida gida, thanks for the ride" yace "Kar ki damu.... Me za a cewa mutumin ne?" na danyi murmushi nace "kyale mutumin nan naka, kwana biyu shiru amma bai neme ni ba" yayi dariya yace to sai da safe. Sai dana shiga cikin gidan kafin ya tashi motar shi ya tafi. Bakina dauke da addu'ah da komi na shiga falon, babu kowa a ciki, da sauri na shige dakina na rufe, na tuge dankwalin kaina na zauna a gefen gado ina ajiyar xuciya cikin samun relief. Wayata ta dauki kara, ganin Sunan Abbu a jiki sai dana yi kamar Kar in dauka, na dai daure na daga na kara a kunnena tun kafin inyi magana muryar shi ta doki dodon kunnena, a fusace yake maganar, "wato Nafeesah kin raina ni koh? Karfe nawa na kafa miki dokar dawowa gida idan kin fita?" jikina yayi sanyi, naji dama ban je wajen dina din ba da ran Abbu bai baci Saboda ni ba, nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi dinner din ne ba a fara da wuri ba" yace "sai kuma aka ce dole ne sai kin je wajen dinner din koda zaki kai karfe sha biyu ne a waje koh?" na girgiza kai kamar yana gabana, yayi shiru. Har ina murna ya gama fadan shi sai kuma naji yace "waye ya kawo ki yanzun?" nace "Bilyaminu ne, dan makarantar mu ne" yace "dan makarantar ku? Kawai Saboda yana dan makarantar ku zaki kwashi kafa ki shiga motar shi babu tsoron komi a matsayin ki na diya mace?" nayi saurin cewa "ai abokin....." sai kuma nayi shiru, harshe na yayi min nauyi sosai na kasa fadar kalmar. Shiru ya biyo baya, bai yi magana ba ni kuma na kasa karasa abinda nayi niyar fada, "it's okay!" naji yace daga can a hankali kamar ba shine wanda yake daga murya yanxu ba, "goodnight!" ya kashe wayar. Na bi wayar da kallo cikin sanyin jiki, da kyar na iya sauka daga kan gadon na cire kayan jikina nasa na bacci na kwanta. 


                           *♡Jeedderh♡*

[12/8, 12:55 PM] ‪+234 810 910 7052‬: Kamar yadda suka ce, yini sur suka mana a gidan. Da rana Abbu yace kar mu yi abinci, oda aka mana daga Chicken Delicacy peppered chicken da spaghetti lasagna sai yoghurt mai sanyi, muka ci muka yi nak tare dasu Hafsy. Bayan mun gama cin abincin na ja su kicin muka yi baking din cupcakes, babu kayan icing don haka bamu yi icing din shi ba. Da yamma likis Abbu yace su fito ya maida su gida, na rataya gyale a kafada ta muka fita tare dasu zan musu rakiya, cikin motar Abbu picnic su Qaseem ne a ciki sun hakimce Hafsy tana gaba su kuma suna baya Abbun yana jingine da motar yana amsa waya cikin hadadden turancin shi hannunshi daya saye cikin aljihun wandon shi, su Sa'adiya suka shige mota ni kuma na tsaya daga waje muna er hira har ya gama wayar ya shiga motar ya tayar, na ja baya kadan ina daga musu hannu, ya zuro kanshi ta cikin motar yace "yah? Baki zuwa ne ke?" na kalli su Ni'ima kafin na kara kallon shi, "can I?" ya tabe baki, "that is idan kina son zuwa fa" na bude motar nima na shiga ya ja motar. Hira muke dasu Ni'ima amma jifa-jifa idanuna su kan sauka akan Abbu dake tuki hankali kwance, wata dagawa da nayi idanuna suka sauka cikin kyawawan sparkling eyes din shi masu cike da kwarjini ta cikin madubin gaban motar, kamar wadda aka zarewa kuzari haka naji jikina yayi sanyi, gashi na kasa janye idanuna daga nashi sai shine ya janye nashin. Nayi ajiyar zuciya a hankali tare da sauke kaina kasa, ina kallon su Ni'ima suna kus-kus suna en da-re-re-ku a raina nayi fatan Allah yasa ba jirgina suka harbo ba. A gidan muka yi sallar magriba da ishai'i muka ci dambun couscous sannan muka musu sallama muka tafi. Dawowar tamu shiru, su Hafsy kadai su ke shan hirar su ni kam ina kan wayata ina buga game din piano tiles saboda bana son satar kallon Abbu da idanuna suke yi har ga Allah. Muna shiga falo ban tsaya a falo ba nayi hanyar dakina, Abbu ya tsaida ni ta hanyar kiran sunana, na juya a hankali. Cewa yayi "Plss dafa mun shayi mana" nace toh. Kayan hannuna kawai na ajiye a dakin na shiga kicin na dafa shayin da kayan kamshi a ciki, na matsa dan lemun tsami na zuba a cikin butar shayi na dora akan tray tare da kofi na kinkima na kai mishi. Yana zaune ya sa system dinshi a gaba da tulin takardu a gefen shi da alamu aiki zai yi, na ajiye akan coffee table dake gefenshi na durkusa a gaban shi, ya dago a hankali ya kalleni, "lafiya Nafeesah?" na sadda kaina kasa nace "Abbu don Allah kayi hakuri da abunda ya faru jiya, in shaa Allahu ba zan kara ba. Don Allah ka daina fushi dani!" shiru yayi yana kallona kafin ya nisa, "ba fushi nayi ba Nafeesah. Kawai ban ji dadi bane yadda kika biyo namijin da baki sani ba cikin dare, what if God Forbid, something bad happens to you Nafeesah? Bayan wannan kin duba shigar dake jikin ki kuwa? Haba Nafeesah!! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, how could you walk in front of many people with that dressing? And you were smiling and laughing in front of that guy, me yasa??" na sake yin kasa da kaina, ina mamakin ta yadda aka yi har Abbu ya ga irin shigar da nayi da kuma hirar da muka yi da Bilyamin, sai dai yanxu is not the right time to think about that, fata na daya kawai shine Abbu ya daina fushi dani. Last 20 to 23 hours has been like a hell to me, sukuni da walwala sun kaurace min saboda fushin mutumin nan daya; Abbu. Ji nake idan na kai gobe ba tare da na ga murmushin shi a gare ni ba zuciyata zata iya bugawa. Kaina na kara yin kasa dashi nace "kayi hakuri Abbu, ba zan kara ba" yace "dadi na dake Nafeesah kina da saurin admitting mistakes naki ki kuma yi repenting immediately, Allah yasa ki dore a haka" nayi kasa da kaina zuciyata ta fara washewa, da alamun ya huce. Yace "tashi ki je ki kwanta, ki daina damun kanki kuma ba fushi nake yi dake ba kin ji?" na dago a hankali na kalle shi kamar mai son karanta gaskiyar abinda yake fada, ya sakar min murmushin shi reassuringly. Naji wani irin sanyi ya mamaye min zuciyata, nima murmushin na sakar mishi sosai cike da farin ciki nace "Abbu nagode sosai, Goodnight!" na mike cike da kuzari da kwarin jiki na tafi, ya bini da kallo yana murmushi sai dana shiga daki sannan yayi ajiyar numfashi ya dauki shayin dana hada mishi ya fara kurba a hankali yana gyada kai cike da nuna gamsuwa. Ni kam ina shiga daki har sai dana yi dan tsalle cike da murna, na shiga bayi nayi brush na fito ina en wake wakena cike da farin ciki nayi shirin kwanciya barci, tsalle nayi na fada kan gadona, na mirgina daya gefen inda wayata take na bude, sai dana yi chatting na shiga accounts dina na twitter ne, instagram, facebook duk nayi posting ina cikin muudu mai dadi kafin na kashe wayar, na kashe wuta, na balle ma6allan gaban rigata na gaba guda uku naja bargo har wuyana, nayi addu'ar kwanciya barci na shafa na rufe idanuna, ba dadewa barci mai dadi ya yi awon gaba dani. 


                            *♡Jeedderh♡*

[12/8, 1:32 PM] ‪+234 810 910 7052‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *19*


         Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar  Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni'ima ne da Sa'adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace "me kuke yi ne anan yammata?" ni'ima tace ziyara muka kawo, ko it's not allowed? Nace "ni na isa in ce? Amma da safe haka?" idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa'adiya tayi murmushi tace "Abinci fa muka kawo wa babban Yaya." na Kalle su "Abbu?" Ni'ima tace "to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi, tashi kixo ki ci kafin ya huce" na sauka daga kan gadon ina cewa "yanxu kuwa" toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni'ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni'ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni'ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara'ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, "wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?" Sa'adiya tace "bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa" yace "ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?" Ni'ima tace "kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan" yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni'ima a saitin kunnena, "me kike kallo?" nayi firgigit na kalleta, "umh?? Babu komi" ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni'ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa'adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace "you okay?" na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni'ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni'ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu.

[12/8, 2:03 PM] ‪+234 810 910 7052‬: Wajen karfe uku na dare na farka, kishi ya dame ni sosai ji nake kamar numfashina zai dauke dole na farka daga daddadan barcin da nake yi, gidan dama duniyar gabadaya tayi shiru kamar babu mai numfashi babu ko karar fan saboda an dauke wuta. Fitilar wayana na kunna na lalubi goran ruwa dana saba shiga daki da ita a kullum Saboda na sanni da bukatar shan ruwa sometimes sai dai babu, da alamun na manta ban shiga da ita ba ranar. A hankali na bude kofar dakina na fito, na fara tip toeing zuwa kicin kamar wadda zata je yin sata. Daidai kafar dakin Anty Mubeenah na jiyo kamar alamun sautin tashin maganganu, ban san dalilin daya saka ni kara kasa kunne ba, muryar Abbu ce take tashi kamar cikin fushi, "For goodness sake Mubeenah! How long has it been?? Kin san yaushe rabona dake? Kina ma kirga yawan kwanakin kuwa? Me yasa ne?! Me yasa ne ba zaki yi treating dina kamar yadda kowanne namiji yake samun kulawa daga matar auren shi ba? Na tambaye ki time without numbered Mubeenah, idan ma wani laifi na miki don't you think it's high time da zamu manta da komi mu rungumi rayuwar yayanmu hakanan ba?" tsaki naji taja, "kace duk abinda zaka ce Ibrahim! Ba damuwata bace, yaya da kake magana a kansu inaga ai bai kamata ka sako su ba, kai kace I just need to have birth to them, you will take care of them, meye hadina dasu then??" shiru na tsawon mintuna biyu ya wuce yayin dana kara kasa kunne, a sanyaye naji muryar Abbu wannan lokacin, "hakkina fa kuma Mubeenah?" "ni fa kaga ka dame ni ka hana ni barci na haba! Saboda tsabar fitina da jaraba a kyale mutum yayi barci ma cikin kwanciyar hankali ma ba za ayi ba?" amsar Anty kenan. Cikin daga murya yace "am fed up with ur cruel habits Mubeenah, dole ki gyara halinki idan kuma ba haka ba....!" katse shi tayi ta hanyar sakin dariya, ".... Idan ba haka ba zaka kara aure? Go ahead then, ko a da can ma hakan bai dame ni ba Ibrahim balle yanzun ka gane? Allah yasa matan duniyar nan zaka auro, I wouldn't give a damn! Now can u get out please? Ina so inyi barci!!" ina jiyo hucin daya dinga fitarwa a fusace kamar zuciyar shi zata fito waje, cikin wani irin threatening murya yace "zan shayar dake ruwan mamaki kuwa Mubeenah" cikin muryar ko-in-kula, I bet she was shrugging her shoulder up ma lokacin kila tace "m looking forward to it" daga nan naji ana kokarin fitowa daga dakin nata, a sukwane na fada bayan labule tare da saka yatsa na danne saitin wajen dake samar da hasken flashlight a wayata. Yana fitowa ya maida kafar dakin da karfi ya rufe ji kake 6ammmmm!!! Ina jin lokacin daya bude kofar dakinshi ya shiga, sai dana bashi kyawawan mintuna goma kafin na fito daga maboyata na fada daki ruwan da ban sha ba kenan na koma kan gado na kwanta xuciyata fal cike da tausayin ma'auratan. Me ke damun Rayuwar Auren su ne haka?? 


         Am sorry for the late update, jiya through out a kwance na yini ban jin dadin jikina ne sam. Yau din ma ta maza ce nayi shi yasa wallahi. Just kara hakuri dani pa! 


                            *♡Jeedderh♡*


[12/8, 7:26 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *20*



        *Sakon taya murna zuwa ga marubuciya MAIMUNA SANI BELI na lashe gasar HIKAYATA da BBC ta hada na gajerun labarai. Allah ya kara miki kaifin basira*




          "I heard that You are leaving the lab at the end of this week koh?" cewar Mrs Smith Head of Lab dinmu. Na gyada kaina nace "yes ma'am" tace "bayan kin gama Program din me zaki yi? Zaki wuce da HND ne?" nace "I'm not very sure ma, I'm thinking of filling D E form" tace "ina fata a nan BUK ne?" na girgiza kaina da sauri, "no ma'am, ABU Zaria ne" ta kalleni tana murmushi, "why?" na sadda kaina kasa kawai, me zan ce? Nace "maa nafi son Zaria ne sabida mun fi kusa dasu, bana son yin nesa da gida" ....ina so nayi nesa da Abbu da Iyalan sa Saboda ina jin tsoron abinda zan janyowa kaina, naso in kara da gaya mata haka sai dai nayi shiru. Ta gyada kai, tayi signing din takardar dana bata ta miko min nasa hannu biyu na amsa, tace "am wishing you all the best Nafeesah" nace "thanks ma'am" na fita. 

           Mun gama ayyukan mu na ranar muna zaune a cikin lab din muna hira ni da Ramlah, su Khaleesat tuni suka gama nasu IT din sati biyu da suka wuce. Nayi scrolling down ta cikin facebook account dina, anan na ci karo da status din da Muneer yayi mintuna biyar da suka wuce, "Soon.....!" na dan rausayar da kaina cike da alamun tambaya, me yake nufi? Na danna button din like. Ramlah ta kalle ni tana tabe baki, "ni har na rasa abinda zan fada miki game da Muneer wallahi. Ki kyale gayen nan haka nan kin ki kiji, yanxu har ta account din shi kike bi kina stalking din shi?" na yamutsa fuska, "stalking kuma Ramlah sai kace wata mara aikin yi? Kawai ina chatting ne na ci karo da status dinshi nayi liking, shine nayi stalking saboda Allah?" tace "ni dake da marar aikin yi duk daya nake ganin ku wallahi, wani mara aikin yi din ma ya fiki Nafeesah. Kin makalewa namiji daya kamar wata wadda bata da masoya, da girman ki da class din ki da komi. Allah ban taba ganin mutum marar fahimta ba irin ki ban sani ba ko duk sangarta ce ko kuwa? Amma......" "For Heaven's sake Ramlah!!" na katse ta a fusace har ina hadawa da buga hannuna akan bench, "this is my life kin gane? You have no right da zaki zauna kina lecturing dina akan abinda yake feeling dina ne kina ji? Baki son Muneer fine!! Ni da nake son shi sai ki bar ni inyi ta son nashi please!!" cike da mamaki ta kalleni, ta daga baki zata yi magana nayi saurin tashi na bar mata wajen. Yinin ranar haka nan muka karasa shi cikin kuncin rai su kan su en lab dinmu sun fahimci akwai abinda ke faruwa damu don basu saba ganin mu a haka ba, we are always cheerful  koda yaushe muna tare muna hirar mu mai burgewa muna tsokanar juna amma ranar kowa tashi yake yi a cikin lab din, ina kallon Ramlah sosai ranta ya baci don har sai data share hawaye, jikina yayi sanyi sosai, ni kaina nasan Ramlah bata cancanci abinda na fada mata dazu ba, Raina ne ya 6aci sosai, so many annoying thoughts were running through my mind a lokacin, zan iya cewa Ramlah Sara ne tayi akan ga6a na sauke fushi da takaicin wasu a kanta. Karfe biyu tana cika na suri jakar hannuna na musu sallama na fita, a bakin kofar na tsaya, bayan kamar minti goma Ramlah ta fito. Da sauri na tari gabanta, "am sorry babe, I shouldn't have said what I said earlier.... M sorry, really" ta kauce daga gabana, "me zan ce miki Nafeesah? Ban cancanci in miki magana bama balle inyi intruding din personal life dinki ba, m sorry!" nasan cewa magana ce ta gaya min, naji kunya ta kama ni a lokacin, A taron mu da Ramlah I must have hurt her feelings da maganganun dana fada mata, bata cancance su ba ko kadan. Da sauri na kara tarar gabanta tare da riko hannunta, "look Ramlah! Wallahi I really didn't meant what I said da gaske nake, ni kaina abun yana damuna Ramlah. I'm trying, ina kokarin ganin cewa nayi yaki da son Muneer a cikin raina amma na kasa. No matter how hard I try, na kasa shi yasa nake jin haushin kaina nima, ina jin takaicin abun nima Ramlah har na fiki sai dai ya zan yi? Zuciya ta taki aminta da hakan ban san ya zanyi ba Ramlah...." zuciyata ta karye na kasa cigaba da maganar, idanuna suka yi jawur, lebena na ciza ina kokarin tsayar da hawayen dake kokarin xubo min. Ramlah ta dafa hannuna fuskarta cike da damuwa, "m sorry too Nafee. Bana jin dadin abinda yake yi miki ne ko kadan, it's hurting me. I love you babe, duk abinda zai bata ranki ina kin shi har cikin raina, na ga alamun baki son kyale shi bayan nasan cewa yana bata miki rai, I didn't know, ki yafe min" rungumeta nayi ina tapping bayanta, "I love you too Ramlah, m sorry too. I shouted at you" ta rungume ni itama, mun dan jima kafin muka saki juna, ta kalleni fuskarta da wani expression dana kasa ganewa, ta sake cewa "m sorry Nafeesah" nace "what for again? Idan maganar Muneer ce ta wuce don Allah mu daina yin ta haka nan" ta gyada kai. Muka samu waje muka zauna muna er hirar mu har Malam Bala yazo na mata sallama na tafi tana daga min hannu, taren mu da Ramlah kenan!.


         Shirye-shiryen komawa gida nake babu kama hannun yaro, ganin abun nake yi kamar a mafarki. Kamar yau ne fa nake shirin tahowa Kano gashi har watanni shida sun wuce, na fada a cikin raina ina karewa akwatuna na kallo wadanda na gama shirya kayana a ciki. Hafsy ta leko dakin, gani na a tsaye ina karewa dakin kallo ta shigo ciki tare da maida kofar ta rufe, gefen gado ta samu ta zauna ta kalleni a marairaice, "yanxu Yaya Nafee gobe zaki tafi ba zaki kara mana ko kwana daya bane?" na zaro ido ina kallonta, "Lallai ma Pretty ashe baki tausayi na, ko don ke kina gaban Mom and Dad dinki ne shi yasa? Nima ina so in je in gansu saboda nayi kewar su sosai" ta turo baki, "to ba kina zuwa kina ganin su ba duk weekend?" nace "dat's a different magana ai, so nake in koma kusa dasu gabadaya kin gane?" tayi rau-rau da idanu sai ga hawaye shar-shar, da sauri na zauna a gefenta na fara lallashinta har tayi shiru, nace "haba mana da girman ki kike kuka? Kar ki damu zan dinga zuwa kuma ina muku weekend kinji?" da sauri ta dago kanta ta kalleni, "da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi, sai dai daga can kasan zuciyata nasan cewa yaudarar ta kawai nake yi don ta warware, ina fata idan na saka kafa na bar gidan Abbu ya zama fita ce ta har abada, ko a mafarki bana fatan in sake komawa. Da biyu nake gaggawar in koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah, Hafsy ta dauko littafan ta na taya ta muka yi bitar karatu har aka kira Ishai'i muka yi, muka fita wajen cin abinci. Muna gamawa muka koma kan kujeru muna kallo, duk da kallon daga ni sai Hafsy ne su Abdullahi wasan su suke yi abin su. Abbu da Anty Mubeenah suka yi sallama suka shigo falon, muka musu sannu da zuwa duk suka wuce dakinsu da alamun kayan jikinsu zasu canza. Anty ce ta fara fitowa, kamar yadda nayi zato ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga, Kai tsaye kan dinning ta wuce ta zauna. Ba a jima ba Abbu yayi joining dinta shima ya canza kaya zuwa na barci, riga da wando na M$S, muka cigaba da kallonmu har suka gama cin abincin suka dawo inda muke suka zauna. Hirar su suka fara yi su da 'ya'yansu, Anty tace "Nafeesah gobe sai tafiya gida ko?" nayi murmushi tare da gyada kai, tace "eyyah! Zamu yi kewar ki ko don dadadan girke-girken ki" Abbu ya jefa mata wani irin kallo, Qaseem yace "Yaya Nafee amma zaki dinga kawo mana ziyara koh?" nace sosai ma. Hafsy tayi caraf tace "anan ma zata dinga mana weekend koh?" na kalli su Abdullahi da suke kallona cikin zakuwa da son jin amsa ta, murmushi nayi nace "ehh" a hankali. Suka dauki shewa suna ihun murna, kallon su kawai nayi ina murmushi. Karfe goma tana yi na tashi na musu sai da safe, Hafsy ta mike da sauri ta biyo bayana, ina ji Abbu ya tambayeta, "pretty ina zuwa?" ta juya tace "ni dai a wajen Yaya Nafee zan kwana yau" yace "a'ah zo ki wuce dakin ki, zaki takura mata" aikuwa ta bare baki zata fara kuka, nayi saurin janyota jikina, "babu komi Abbu, taho muje kinji?" ta ware hakora tana dariya, naja hannunta muka shiga daki. Brush muka yi muka fito, nace ta zauna bari inje in dauko mata kayan barci, na fita. Falon babu kowa duk sun tafi dakinsu, naje na dauko mata kayan. Na fito kenan daidai Abbu yana fitowa daga dakinshi, ya kalleni, da sauri na sadda kaina kasa nayi niyar wuce shi da sauri, cikin wata irin murya da ban taba jin ta a gun Abbu ba naji yace "Nafeesah!" na tsaya cak duk da ba haka naso in yi ba, so nayi in yi kamar ban ji ya kira ni ba in shige dakina wanda bai fi taku takwas daga inda nake tsaye ba, but damn me and my legs. Ya tako a hankali har inda nake tsaye, zuciyata bugawa take yi da sauri har naji tsoron kar ya jiyo sautin, shiru ya biyo baya na fiye da minti biyu, jikina ya bani cewa kallona yake yi don haka naki daga fuskata balle in kalle shi. Yayi ajiyar numfashi a hankali, yace muryar shi kasa-kasa, "are you sure Pretty ba zata takura miki ba?" na tabbata ko nayi magana ma da kyar muryata ta fita don haka na gyada mishi kai kawai. Yace "umh.... Da gaske zaki dinga zuwar mana weekend?" nan ma kaina kawai na iya gyadawa. Yace "good! I'm happy to hear that. Je ki kwanta sai da safe" da sauri na wuce har kafafuna suna hardewa na fada dakin kamar wadda aka jefa, Hafsy ta daga kai ta kalleni da sauri, murmushi na sakar mata na mika mata kayan barcin ta saka nima na sa nawa, wando ne iya gwiwa don nasan ba fita zan sake yi ba da rigar vest mai budadden gaba zan iya cewa Rabin kirjina a waje yake. Na mana addu'ar kwanciya barci ni da Hafsy muka shafa, na janyo bargo na rufe mu tare da kashe mana wuta. Ban sani ba tsautsayi ne ko kuwa Kaddara ya saka ni janyo wayata na shiga social media?? Well, that's the worst moment I've regretted the most in my life!!!. 






                   *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:29 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *21*





             Ban san lokacin dana saki wayar hannuna akan carpet din dakin ba, na jingina bayana da allon gado ina kallon wayar kamar wadda aka turo mata da ranar mutuwar ta, hoton Muneer ne shi da wata tsaleliyar yarinya ya dora a shafin shi na instagram, a kasan hoton naga yasa *Finally Engaged Alhamdulillah..., getting married in the next 6 months!*. Ban taba sanin cewa numfashin mutum ya kan dauke, zuciyar mutum ta daina bugawa ba alhalin mutum na raye sai a lokacin, lokacin da nayi kokarin warto numfashi na sai gani a tsakiyar carpet din dakin dafe da kirjina, Zufa ta shiga keto min ta ko'ina, jikina rawa yake yi kamar mazari. Allah kadai Yasan iya adadin lokutan dana kwashe cikin wannan hali. Kamar wadda aka zungura nayi zumbur na tashi tare da daukar wayata, ban damu da cewa lokacin karfe sha daya da rabi bane, abinda na sani kawai shine ina so inji daga bakin Muneer, cewa da gaske aure zai yi, wata zai aura ba ni ba. Na kalli Hafsy da take barcinta cikin natsuwa bana so in katse mata barcinta saboda nasan a yadda nake ji na ba zan taba yin kasa da muryata ba, ji nake kamar in bude baki inyi ta kwarara ihu har sai mutanen Duniya sun ji halin da nake ciki. Falo na fita, wutar falon a kashe take duk da haka akwai haske wanda kwayayen waje suka samar. Number Muneer na danna, take ta shiga ta fara kara. Kai kawo nake a tsakiyar falon na kasa zaune na kasa tsaye har tayi karan ta gama bai dauka ba, na sake danna mishi wani kiran, sai dana jera mishi missed calls takwas ina kirgawa ban kuma yi niyar dainawa ba, nayi imani a lokacin idan zai kwana bai daga kiran ba nima haka zan kwana ina kiran shi ba tare da gajiyawa ba. Ana tara ne ya daga cikin muryar barci, "hello Nafeesah lafiya??" sai na ma rasa abinda zan ce mishi, wani irin kuka yake shirin kufce min na datse hakorana ina maida shi ta karfi, Muneer bai kai wannan matsayin ba kuma, kuka akan namiji? Har abada! Ya sake cewa "Nafeesah, are you ok??" cikin gritted teeth nace "Muneer, you evil bastard!!" shiru ya biyo baya da alamun he was in shock, I couldn't suppressed my anger shi yasa, "what?! Excuse me??!" ya fada shockingly, cikin rawar murya mai cike da bacin rai nace "You betrayed me Muneer!! Kayi wasa da zuciyata ka maida ni sakara, abinda ka mun ka kyauta kenan? Kana ganin hakan dacewa ne?" yace "me kike fada ne haka Nafeesah? Me na miki? Ta yaya na yaudare ki??" cikin karaji nace "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what? Aure?? Baka yi tunanin halin da zan shiga ba?" yace "I never Loved you Nafeesah!! Saboda kawai kina so na sai kiyi tunanin zan tauye kaina da rayuwata saboda ke? Why would I?? I mean ban taba cewa ina sonki ba, in fact, ban taba nuna signs na so a gare ki ba ko na taba?" kai na nake girgizawa cikin tsananin bacin rai da bakin ciki, ni Namiji yake gayawa baya so na da Babbar murya!! Muryata ta fara rawa, nace "ka cuce ni Muneer! Kaki ka so ni ka hana ni inso wadanda ke so na, you are one big devilish bastard on earth!" yace "enough Nafeesah! I've heard enough please, bani nace ki so ni ba, ban taba rokon ki akan ki so ni ba don haka you have no right da zaki saka ni a gaba cikin daren nan kina zagina da tuhumata akan laifin da ban sani ba kin gane?" na gyada kaina a hankali kamar wadda take gaban shi, nace "you are right Muneer!! You are right!! Laifina ne, ni naki yarda inji maganar mutane da kashedin da suke min, duk a tunanina kana so na ashe yaudarar kaina kawai nake yi..... Sai da safe kawai, sai dai I'm not sorry about waking u up, ina maka fatan uncomfortable sleep through out the night!!" na kashe wayata gaba daya. Zubewa nayi a kasan falon saboda yadda kafafuna suka yi sanyi, zuciyana kuna take yi kamar wadda ake soyawa. Duk yadda naso akan in daure kukan da yake tuko ni kasawa nayi, gani nayi idan ban yi kukan ba zuciyata zata iya fasa kirjina ta fito. Kuka na fashe dashi sosai kuma da karfi, a wannan lokacin ban damu ba wai Don mutane sun san cewa ina kuka saboda Namiji yayi dumping dina. Sai da nayi kuka na mai isa ta sannan na tashi ina hardewa da layi na shiga dakina, a dakin ma wani sabon kukan na dasa. Bakin cikin dake raina was incomparable da ko wani irin halin bakin ciki dana taba shiga a rayuwata, wallahi ko a cikin mafarki ban taba zaton cewa ni Nafeesah za a samu wani namiji a duniyar nan da zai daga baki yace baya so na ba sai gashi wanda na kwashe shekara curr cikin son shi da mafarkin kasancewar shi uban yaya a gare ni ya daga baki ya fadi kalma mafi munin saurare a gare ni, Lallai Duniya mai cike da abubuwan mamaki. Sai gabannin Asubahi barci ya suraro ya sace ni ina xaune a kasa na jingina kaina da jikina da gado. 







                    *♡Jeedderh♡*


[12/8, 7:27 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *22*




             _'Some nights I can hear you., Screaming on the phone over something that he did....., And I wonder what can I do to make you throw him out so you can let me in.....!'_

          A song by *Shayne Ward* Titled *'Melt the Snow'*. I hope you will enjoy listening to it. 





         Juyi yake yi akan gado, barci yake ji sosai amma ko kadan barcin yaki zuwa. Gadon da yake Kai ya mishi fadi, gado ne wanda a kalla zai iya kwashe mutane biyar ba tare da wani ya takura wani ba amma kullum ta Allah shi kadai yake murzar shi, yana Juyi a kanshi, yana jin shi kamar wani mara galihu. Disappointedly ya sauka daga kan gadon, kan sofa yaje ya kwanta, yafi jin dadin kwanciya anan duk da cewa kafafun shi suna kan hannun kujerar ne saboda tsawon shi. Wani modem daya shigo dashi ya tuna ya baro shi a parlour, wasu muhimman bayanai ne a ciki ba shiri ya tashi ya fita, babu kowa a Cikin falon, wutar falon ya kashe yayi amfani da wayar hannunshi ya dauko Modem din. Kan three seats ya koma ya kwanta a parlour na daya, Family picture dinsu ya kurawa ido yana kallo. Ya gaji haka nan, Ya gaji da jiran canzawar halin Mubeenah, Ya gaji da kasancewa kamar wani marar aure alhalin yana da mata kuma yana da right din karo guda uku kwarara, yana bukatar rayuwar aure irin ta kowane normal mutane, rayuwa mai cike da soyayya da girmamawa ba irin rayuwar auren gidanshi ba, rayuwar auren da ba zaka taba ganin murmushi ko kafar matar auren ka a dakin ka ba sai idan tana bukatar either kudi ko bukatar namiji ta motsa mata, kai kuma naka bukatun ko oho! Yana ganin lokaci yayi da zai maida komi inda yake, maganar gaskiya yana bukatar mace ya kuma gaji da bin kan Mubeenah tana yankwana shi kamar wani mara galihu, Allah ya gani yayi iyaka Kokari da hakurin da zai yi. Yana nan kwance Cikin zazzafan tunani zai iya cewa ma barci ya dauke shi yaji karan bude kofar daki, a hankali ya bude idanunshi yaga Nafeesah ta fito daga dakinta, da mamaki ya bita da kallo a cikin ranshi yana tambayar ko lafiya? Yanayin tsayuwar da tayi tana tapping kafafunta a kasa nervously ga waya a kunnenta ya sashi cikin tunani me ke damun Nafeesah ne haka? A hankali idanunshi suka fara yawo a jikinta, duk da babu wadataccen haske a falon amma hakan bai hana shi hango surar jikinta cikin gajeren wando da vest din data saka, wani irin tension yaji yana building a cikin jikinshi babu shiri ya rufe idanunshi da karfi yana hadiyar yawu yana gayawa kanshi it's not right! A hankali ya sake bude idanun yana kara kare mata kallo yadda jikinta yake swaying halittun jikinta suna motsi suna kara tada mishi hankali, yana so yayi motsi yadda zata san da wanxuwar shi a cikin falon, but hell! He couldn't. God Forgive him but he's enjoying seeing her in that attire, making him go mad, making him want to just drag her and kiss her senseless may be yayi wani abun worst than kiss.....! Maganar da tayi cikin fushi da daga murya ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi, "Muneer you evil bastard!" yaji duniya ta tsaya mishi cak kamar an tsaida kowane wucewar minti da dakika, may be he was mistaken, ba Muneer tace ba, kila ba sunan Namiji ta kira ba, kila Muneerah tace kunnenshi yake gaya mishi Muneer. Ya sake lafewa akan kujerar da yake yana kara kasa kunne, "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what?! Aure??!...." da sauri ya saka hannu ya danne kofofin kunnenshi yana girgiza kai, no! No way!! Karya ne!!! Kwatakwata ya manta a ina yake balle yace ga abinda yake yi, wani irin rugugi yake ji yana mishi ihu a cikin kunnenshi, maganganu mafi muni da daci daya taba ji an furta a gare shi, maganganun da suka girgiza shi suka yi turning rayuwar shi up-side-down, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un ya dinga nanatawa har yaji nutsuwa ta saukar mishi, maganganun Nafeesah sun matukar girgiza shi, the fact that tana son wata halitta, halittar ma jinsin Namiji, abu ne da bai taba zato ba, bai taba zaton cewa tana da wanda take so ba, bai kuma taba zaton cewa abun zai yi affecting dinsa sosai kamar yadda yayi yanzu ba. Yana jin lokacin data tsuguna tana kuka sosai a tsakiyar falon, he wanted to man up yaje ya rarrasheta sai dai a halin da ake ciki shima rarrashin yake bukata, yana ji kamar shima ya fashe da kukan ko ya samu yaji sauki daga azabar zafin da zuciyar shi ta dauka, har ta gama kukan ta tashi ta koma dakinta bai iya tabuka komi ba sai bin ta da kallo helplessly. Lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali kafin yayi karfin hali ya tashi zuwa dakinshi, alwala ya dauro ya kalli Al-Qibla ya fara jera nafilah yana mai rokon Allah akan ya mallaka masa Abinda ya jima yana kwatanta nashi ne.....!.


              ☆☆☆☆☆☆☆☆


        A hankali na bude idanuna da nake ji sun min wani irin nauyi marar misali, na kai hannu na dafe kaina da naji yana sarawa kadan wuyana ya rike shima na kai hannu ina dan taba shi, idanuna suka sauka akan agogo, karfe shida ta wuce, da sauri na tashi tare da daddabar Hafsy ta tashi, muka shiga bandaki muka yi alwala muka fito muka yi sallah, dakinta nace taje tayi wanka ta shirya nima na shiga na watsa ruwa, nayi iyaka Kokari na wajen mantawa da abinda ya faru Jiya da dare, bana son tunawa ko kadan. Na fito daga toilet din daure da tawul a kirjina, na tsaya a gaban mirror ina tsane lemar jikina, idanuna sun tasa sosai sunyi luhu-luhu, ni dama nasan za a rina irin kukan dana sha jiya, kayan kwalliyata na janyo na shiga shafe-shafen abubuwa amma duk kokarin da nayi idanuna basu da alamun dawowa normal dama-dama ma fuskata swollen din da tayi ya rage sosai, tsaki naja na janyo wet tissue na goge kwalliyar da nayi, nayi simple one ko janbaki ban sa ba, riga da zani na saka nayi simple daurin dankwali, na dauki jakata na jefa wayata a ciki ba tare dana damu akan in kunna ta ba. Shades na saka a fuskata wanda ya rufe idanuna da yawancim fuskata, na zura takalmi flat na fita. Yaran ne kadai a falon suna kari iyayen basa nan, naja kujera na zauna a gefen Hafsy yayin da duk suka bini da kallo, dan murmushi nayi kawai, suka gaida ni na amsa Hafsy ta jefe ni da tambayar "Yaya Nafee me ya samu fuskar ki kika sa glass?" sai da nayi gyaran murya saboda dusashewar da tayi kafin nace mata "idanuna suke ciwo, bana so in goga muku ciwon ido ne" ta gyada kai tace Allah ya sauwake Yaya Nafee, Kai kawai na gyada mata. Muka fara cin abincin a nutse, ni kam caccakar abincin kawai nake yi duk yadda naso da inci abincin abun ya gagara, xuciyata a cunkushe take sosai, takaici da bakin ciki ya cika min ciki har babu wajen da abinci zai shiga. Suna gamawa muka fita, hango bakar Matrix da nayi nasan cewa yau Abbu ne zai kaimu kenan, mamaki ya kamani ko me ya hana shi yin break ne?? Muka shiga cikin motar, as usual a baya na zauna. Muka gaida shi ya amsa cikin wata hargitsattsiyar murya wadda tasa na kalli fuskar shi sosai kamar wadda take so ta gaskata Abbu ne ko ba shi bane? Ban taba jin muryar Abbu a hargitse haka ba, wani hargitsattsen kallo daya watso min wanda ya kada min yayan hanji babu shiri na sadda kaina kasa, ina jin Hafsy fadi ba a tambaye ki ba tana gayawa Abbu wai ciwon ido nake yi ina tsoron kar in goga musu shi yasa nasa glass, harara nake jefa mata a kaikaice sai dai wannan shine ainihin abinda bahaushe ya kira da 'harara a duhu' saboda ba gani na take yi ba. Har muka ajiye su a school dinsu ban dago kaina daga sadda shi din da nayi ba, suna fita na tashi na koma gaba kamar yadda muke yi, Abbu ya tashi motar muka wuce su Hafsy suna dago mana hannu. A hankali yake jan motar kamar ba tafiya muke yi ba, ya juyo ya kalle ni a karo na barkatai tunda muka fara tafiyar, gudun da zuciyata yake yi ya cigaba da karuwa a duk wucewar dakika. Kamar daga sama naji ya jefo min tambayar da nake tsoron ya jefo min, "Are you ok Nafeesah???!"






                      *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:30 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *23*



          Kalmar 'Are You Ok' kalma ce da nake matukar tsoro idan ina cikin halin damuwa. I am a very emotional person, shi yasa idan ina cikin halin damuwa bana son mutane a kusa dani saboda gudun su tambaye ni lafiya? Don zan iya fashewa da kuka, ni a gare ni tambayar are you ok kamar fama min gyambo ne. Yanzu ma sai da nayi iyaka kokarin da zanyi na danne kukan da yake kokarin barke min nace "m fine Abbu, kawai bana jin dadin jikina ne" ya kalleni kawai nasan bai yarda da abinda nace ba, ban ga laifin shi ba don yadda nake a hargitsen nan babu wanda zai yarda wai gajiya ce ta maida ni haka. Ya kalleni sosai kamar wanda yake so yayi magana sai kuma kawai ya maida kallonshi ga titi, a raina naji dadin hakan nasan tambaya daya zai kara jefo min zan fashe da kuka, kuka kuma ba abinda nayi niyar in ci gaba dayi bane saboda Muneer. Har yayi parking a parking lot din dept din Microbiology, na yunkura zan bude motar ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana, na Juya a hankali na kalleshi. Idanuwan shi fes a kaina suke, naji wani slight rawar jiki kafin in sadda kaina kasa, muryar shi a sanyaye yace "akwai abinda yake damunki Nafeesah wanda kika ki gaya min and I wouldn't force you to tell me, kawai ina so in gaya miki cewa komi na rayuwa sai da hakuri, koma menene yake damun ki kiyi hakuri ki dauke shi a ba komi. Idan ma wani abu ne kika rasa kike ganin kamar ba zaki iya hakuri da rashin ba kada ki manta Allah yana tare da Ke. Shi ya mana alkawarin canza mana abinda yake sharri ne a gare mu zuwa ga mafi alkhairin shi don haka ki roke shi game da abinda yafi alkhairi a gare ki ba kiyi holding into something wanda yake ba alkhairin ki bane kin gane?" na gyada kaina a hankali maganganun shi sun shige ni. Abinda ya kamata in tuna kenan a lokacin da naga hoton Muneer da amaryar shi jiya, abinda ya kamata inyi kenan ba wai in kira shi ba ina kara fallasa kaina da disappointing kaina, sai yanzu naga cewar hakika abinda nayi jiya ban kyauta ba, naji kunyar kaina ta kama ni har ma data Muneer din, ko da wane ido zan sake kallonshi kuma yanzu??. Nace "na gane Abbu nagode sosai, In shaa Allahu zan yi amfani da shawarar ka" yace "good" shiru ya biyo baya a cikin motar, can naji ya sake magana cikin whisper, kamar kuma wanda yake tsoron yin maganar, "anjima kuma sai gida koh?" na gyada kaina a sanyaye, barin rayuwar Abbu da iyalan shi!! Tunani ne mara dadi dake fadar min da gaba a duk lokacin da ya fado min a cikin raina don haka nake iyaka kokarina wajen ganin na kauda tunanin daga cikin raina. Na sake tsintar muryar shi yana tambayana, "da gaske zaki dinga zuwa kina mana weekend?" nace ehh, a cikin raina nasan fada kawai nake yi ba don zan dinga zuwa ba sai don kawai kada su dameni da tambaya. Kamar yasan abinda nake tunani, yace "da gaske kike ko kuma kina fada ne kawai?" shiru nayi wannan karon, yayi murmushi tare da kallona kawai yace na gane. Dash board ya bude ya ciro wata karamar jaka fara mai hannu ya miko min, na amsa fuskana dauke da alamun tambaya, yace "it's a small thank u gift, thank u for staying with us Nafeesah, we enjoyed having u in our life and we wish you will come back to us forever!" na dan rausayar da kaina cikin alamun rashin gane inda maganar tashi ta saka gaba, me yake nufi ne? Murmushi yayi ganin ya saka kwalwa na cikin rudani. Yayi murmushi yace "oya! Up you go! Naga abokan ki suna jiran ki tun dazu" sai lokacin idanuna suka koma ga inda muke zaune, su Ni'ima na hango tsaye a kofar shiga lab dinmu suna hirarsu da Ramlah, cikin sauri na jefa jakar daya bani cikin handbag dita na mishi godiya tare da bude murfin motar na fita. Gabadaya kallo suke bina dashi cike da alamun tambaya nasan bai wuce na mamakin abinda muka tsaya hirantawa da Abbu bane tun dazu, naja fuska tare da kara gyara zaman gilashi na a fuskana. Tun kafin in karasa wajen su suka iso gare ni, Saadiya da Ni'ima suka kamo hannuna Ramlah kuma ta dafa kafadata, cike da damuwa suke tambayana, "Nafeesah are you ok?" ni duk sai naji sun ma bani haushi, na cire gilashin idona ina kallonsu cike da takaici, "why?? Saboda crush dina zai yi aure sai kuke zaton karewar rayuwata ne yazo ko me?" gabadayan su were relieved da yadda suka ga nayi, Ramlah tace "yeah! I thought about more than that ma, nayi zaton zan ganki kamar sabuwar kamu ne wallahi sai kuma na ganki da hankalinki dai, but are you really ok?" na gyada kaina "yeah, I am Ramlah but that doesn't mean ban ji haushin abinda Muneer ya min ba" Ramlah ta rungume ni da sauri tana tapping bayana, "ohh my poor friend, Am really sorry. Don Allah kiyi hakuri, nasan in shaa Allah wanda yafi Muneer alkhairi a gare ki yana nan zuwa" na danyi murmushi, kwatankwacin abinda Abbu ya gama fada min. Na janye daga jikinta ina kallon su Ni'ima dake tsaye suna kallonmu nace "ba kuna da lectures ba wai me kuke yi anan?" Sa'adiya tace "wallahi Ramlah ce ta kira mu wai muzo mu tayata baki hakuri don tasan yau a hargitse zaki xo sai kuma muka ga akasin haka" ajiyar zuciya nayi nace "na hargitse kam Sady but Alhamdullillah na dawo cikin hayyaci na kuje kawai" suka mana sallama suka tafi mu kuma muka shiga lab. Ranar babu aikin da muka yi, sallama muka yi da staff da lab attendants na dept din don haka wajen karfe sha daya muka bar lab din cike da kewar mutanen da muka zauna dasu. Wajen su Ni'ima muka je na kara musu sallama, daga nan na wuce gida. Ita Ramlah tana Kano tukun.


Ina zuwa gida na kara hada kan kayana na zauna zaman jiran Daddy don yace shi zai zo ya dauke ni. Bayan an fito daga masallaci sai gashi har da Mommy, sai da muka yi Sallar La'asar sannan muka yi sallama da iyalan Ibrahim Galadanchi cike da kewa, kauna da zullumi. Zullumin ko zan sake ganin su a rayuwata ko kuwa? Zullumin ko zan iya da korar wadannan kananun feelings da nake ji game da Abbu? Zullumin ko zan iya yin normal rayuwa kamar da wadda nake yi a gaban Iyaye na? Magana ta gaskiya watanni shida da nayi tare da Iyalan Ibrahim Galadanchi watanni ne masu muhimmanci da tarihi a gare ni, sun koya min abubuwa da dama a rayuwata, sun kuma gaya min ainihin abinda ni, Zuciya, da gangar jikina suke so da Muradi. 


Na daga idanu a hankali na kalli Hafsy dake hannun Babanta tana rusa kuka da iyakar karfinta tana ihun Ita sai ta bini, na kalli su Qaseem suma duk fuskokinsu cike suke da jimami har da kwalla a cikin idanunsu, hakika bahaushe yayi gaskiya da yace 'Sabo turken Wawa' dana kalli fuskar Abbu kuwa sai da naji kamar in balle murfin motar in fito ince na fasa komawa gidan. Damuwar dake fuskar shi was obvious, na karance ta kuru-kuru cikin idanunshi, kallona yake yi da dukka idanunshi, yanayin shi ya min kama da wani wanda yake tsoron rasa wani abu mai matukar muhimmanci a gare shi. Daddy ya bude murfin motar ya shigo ya mata key, Abbu da iyalan shi suka daga mana hannu bakinsu dauke da addu'ar Allah ya kiyaye hanyar yayin da naji kwalla ta cika min idanu, Daddy ya ja motar muka tafi. Nabi gidan da kallo idanuna cike da kwallah, Allah kenan! Kamar a ranar ne nazo gidan, na tuna sanda su Daddy zasu tafi kukan rabuwa dasu nayi, gashi yau kuma ina kukan rabuwa da iyalan Abbu. Tafi tafiya na fara bajewa daga kukan dana fara, su Daddy hirarsu suke tayi game da karamcin iyalan Abbu, ni kam kallon gefen hanya nake yi kawai. Barci ya dauke ni bani na tashi ba sai da muka isa gidanmu shima Mommy ce ta tashe ni, na fito daga motar fuskana a washe ina kallon gidanmu, Finally dai! I am back!. Muka dauki wasu kayan muka shiga dasu yayin da Maigadi ya shigo da sauran, Dakina a shirye na tarar dashi kamar ina gidan don haka ina shiga na ajiye jakar hannuna akan kujera daya dake dakin na zube akan gado ina ajiyar numfashi. 






                     *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:31 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *24*



       _Follow me on wattpad *@Jeeedorhh*_



               Ana kiran sallah Mommy ta leko dakina tace in fito Daddy zai ja mu sallah, sai lokacin na tashi daga kwanciyar da nayi na shiga bayi na dauro alwala na fito, dogon hijabi na dauka na tafi dakin Daddy. Wani dan karamin dakine a cikin dakin shi wanda yake aiwatar da ibadojin shi a ciki, dakin lullube yake da darduma sai tashin kamshi yake yi, shelves shelves na littafan addini a gefe a shirye gwanin ban sha'awa. Daddy ya ja mu sallah, muna gamawa ni da Mommy muka dauko littafin Arrijalu Wan-nisa'u fil Jannah Daddy ya ja mana karatu har aka kira sallar Ishai muka yi. Muka fita zamu yi dinner amma abinci fa yace sam bai ga wajen zama a cikina ba, Mommy ta kalli yadda nake ta juya cokali a cikin Irish Supper data mana wanda yana daya daga cikin favorites dina, na tabbata saboda ni tayi shi amma na kasa ci, tace "Baby lafiyan ki lau kuwa kin kasa cin abinci?" Daddy ya dago yana kallona, cikin sauri na girgiza kai nace "m fine Mom, cikina ne a cike kawai" Daddy ya tsiyayo Pineapple and coconut juice da Mommyn ta hada ya miko min, na amsa tare da kaiwa bakina na kur6a, aikuwa har da lumshe idanuna saboda gardi da sanyin daya ratsa ni, da taimakon lemun na dan samu na kara tura abincin haka nan kafin na musu sai da safe na tafi dakina. Ina shiga na fara kokarin kimtsa kayana cikin wardrobe duk a kokarina na kauda tunanikan dake dankare a cikin raina. Na janyo handbag dita ina kokarin rataye ta a bags rack naji nauyi a ciki, cike da mamaki na zura hannuna ciki na fito da karamar jakar da Abbu ya bani da safe, a hankali na zauna a gefen gado tare da janyo dan karamin purple akwatin dake ciki, cike da mamaki na fiddo shi ina jujjuya shi a hannuna. Ina budewa na zaro idanu sakamakon wata siririyar sarka dana gani a ciki da dankunnenta har da zobe, sarka doesn't look that out of ordinary but daga ganinta kasan ba karamar sarka bace. Hannuna rawa ya shiga yi na rasa abinda zanyi, tashi nayi da dan akwatin a hannuna na fita falo, su Daddy suna zaune suna kallo duk suka bini da kallo, na zauna a gefen Daddy tare da mika mishi akwatin nace Abbu ne ya bani dazu, da mamaki Daddy ya karbi akwatin yana jijjiga shi a hannunshi yace "Shi Ibrahim din ne ya baki wannan sarkar?" na gyada kai a hankali, ni kaina na kasa yarda da hakan gani nake kamar a mafarki, Daddy yace "amma me yasa?" na jijjiga kai "nima ban Sani ba Dad kawai bani yayi" Mommy ta karbi sarkar itama ta dudduba, ta kalli Daddy tace "da alamun sarkar Babba ce fa Habibiy, Anya zamu karba kuwa?" Daddy yace "abinda nake tunani kenan exactly..." yace min "ki je daki ki kwanta, da safe zan tuntube Ibrahim din inji" nace "toh" na musu sai da safe na wuce dakina. Ina kwanciya barci ya kwashe ni, after all it has been one exhausting and stressful day. 

Washegari Daddy ya dawo min da sarkar da Abbu ya bani, ban tambayi abinda ya cewa Abbu ba ni dai yana bani na bude na zura zoben a cikin yatsa na. A ranar sai ga Anty Ameenah ta kira ni, korafi ta min akan na tafi ba tare dana musu sallama ba, hakuri nayi ta bata akan cewa Lokaci ne ban samu ba, bata hakura ba sai dana dauki alkawarin cewa zan je gidanta musamman sannan. Bayan mun gama wayar shiru nayi ina kallon wayar a raina ina tuhumar kaina akan ba mutane false hope na ganina da ziyartar su bayan nasan cewa ba haka bane a cikin raina.


Nayi shiru akan gado duk kadaici ya ishe ni, a raina na raya da ace a gidan Abbu nake da war haka ko dai muna hira dasu Hafsy, ina kicin ina girki ko kuma muna wasa a gym kamar yadda muka saba kwanan nan idan bama aikin komi. Wayata na janyo na latso lambar Abbu, sai kuma na kasa danna mishi kiran, a raina ina mamakin kaina me zan ce mishi ne idan ya dauka? Me zan ce mishi ne dalilin da yasa na kira shi?? Kawai sai na maida akalar wayar zuwa ga Anty Mubeenah, ta shiga tayi ta ringing amma ba a dauka ba, shiru na bata mintuna biyar ko zata kira amma bata kira ba sai na kira wayar Abdullahi, cikin ikon Allah ya dauka, cike da doki muka gaida dashi. Nace ya bani Hafsy mu gaisa yace ai tana gida yau bata je makaranta ba, nace me yasa? Yace ai Tun jiya take kukan Ita lallai sai an kawo ta wajena shine yau ta tashi da zazzabi, a raina naji ba dadi don haka nace idan sun koma gida ya kira ni yace toh. Yana kashe wayar na kira Ni'ima, muna gama gaisawa tace "yanzu kuwa Babban Yaya ya bar nan" nayi jim ina kokarin yin maraba da sunan shi da naji ta ambata, haka kawai naji zuciyata ta dauki bugu da karfi, "umh ya su Mama?" nayi Kokari na kauda hirar Abbu da take kokarin sakowa amma duk da haka ban tsira ba, "next week ne bikin bude kamfanin shi a Beijing, how I wish zan samu zuwa" na hangame baki cikin mamaki nace "Da gaske?" tace wallahi kuwa. Nace "Masha Allah! Lallai zan kira shi in taya shi murna, na dade da jin labarin bude kamfanin wajen Bala Malam, ni nayi zaton ma an jima da budewa ashe har yanzu?" tace "kin san dama bude kamfani a kasar waje is not something easy musamman ga wanda yake ba dan kasar ba, don ma abokin aikin nashi haifaffen Beijing din ne shi yasa" na gyada kai. Tace "Hajiyar mu tayi mamakin tafiyar ki fa dazu da Babban Yaya yana gaya mata, tayi ta korafin baki masu bankwana ba" a raina naji babu dadi, sai lokacin naji ban kyauta ba, haka na baro Kano bayan Iyalan Abbu da Anty Haleemah babu wanda na wa sallama, nace "in shaa Allah duk ranar dana kara shigowa Kano zan zo in gaishe ta" tace better! Muka dan kara hira kafin muka yi sallama. Later in the evening Daddy ya dauke mu muka fita yawon gari, shiga nan fita nan har gidan Anty Uwani muka je acan ma muka yi sallar Magriba kafin muka juyo gida. 


       Sai dana gama shirin kwanciya barci misalin karfe tara na dare sannan na turawa Abbu text message, *"Abbu naji ance zaku bude kamfanin ku next week, Allah ya sanya Albarka da Alkhairi. And thank you for the necklace, it's beautiful, I like it!"*.


Minti biyar tsakani naji Wayata tana vibrating, da sauri na janyo ta, as expected; Abbu ne. Sashe daya na zuciyata cike yake da murnar jin muryar Abbu yayin da a gefe daya nake jin wata er fargaba da tsoro dana rasa ko na menene a cikin raina. Na daga wayar da sallama cikin wata siririyar murya wadda ban san ina da Ita ba. A nashi bangaren sai da yaji wani yarr! Hakan ne ya haddasa mishi sanyin jiki da sanyin murya a lokaci guda, shima cikin sanyin muryar ya amsa min, yace "Why didn't you call early?" ban fahimci abinda yace ba nace "naga dare yayi ne shi yasa na maka text" wanda a hakikanin gaskiya ba haka bane ba, ina jin tsoron abinda jin muryar Abbu zai haddasa min a cikin jikina ne, yace "it's just nine fa, ya kike anyway?" nace "lafiya lau...... Naga sarkar daka bani, nagode sosai" ya dan yi er dariya, "shine Daddyn ki ya kira ni yau tun da safe yana interrogating dina kamar wani wanda yayi kyauta da abinda bai dace ba, sha ya bani dariya sosai ya kuma burge ni" naji na dan saki murmushi, ina so inji ana yabon iyayena, nace "sarkar ce Abbu naji Mommy tace babba ce, why would you give me such a precious thing?" na tambaye shi abinda nake ta tunani tun dazu, me yasa zai bani sarka babba haka ni ba diyar shi ba ni ba matar shi ba,  in fact bamu hada ko wace irin alaka dashi ba sai ta Diyar Aboki da Abokin Uba? Ya katse ni ta hanyar cewa "Because I can ofcoure! So ya kika ga sarkar? Ina fata ta burge ki?" na kalli zoben hannuna naga yadda ta kayata hannun nawa sosai, nace "Sosai ma Abbu, zoben ya zauna a hannuna perfectly kamar don ni aka yi shi" yace "ai dama saboda Ke aka yi shi din" na danyi jim ina so kada in yiwa amsar tashi fahimtar da ba kenan ba, na maida akalar hirar tamu zuwa wata daban ta hanyar tambayar shi ina su Hafsy! Yace "pretty ta sha kuka tun jiya har dan zazzabi tayi saboda tafiyar ki" nace "Allah sarki Hafsy! I really miss her so much!" ba zato naji yace "ni fa?!" tsit nayi ina kifta idanu, maganar tazo min a bazata, ya sake cewa "ni fa? Didn't you miss me?" cikin wata irin seductive murya, Ya Allah! Me Abbu yake nufi da innocent rayuwata ne yake min magana cikin irin wannan muryar? Na tabbata da a kusa dashi nake babu abinda zai hana ni jefa jikina kan shi, cikin rawar murya numfashi na har daukewa yake nace "Abbu... Sai.... Da safe. I gotta go" daga can bangaren shi ya dan hade ran shi, a hankali yace "you are not enjoying having my company?" nayi saurin girgiza kaina, idan da mutumin da nafi jin dadin hira dashi duk duniyar nan wanda nake ganin ko kwana zamu yi akan waya muna hira ba zan gaji dashi ba to Abbu ne sai dai ina tsoron abinda zai je ya dawo, bana fata in sake dandana abinda naji daga Muneer a wajen ko wani namiji kenan ya zama dole in janye jikina daga Abbu tun kafin inyi ending up hurting my self. Nace "m just a bit sleepy ne Abbu" yace "ok, yakamata kiyi barci kam. Sweet dreams to you" "Thanks.... And same to you!" na karasa fada more like a whisper to myself, ban sani ba ko yaji ko bai ji ba? Bana ma so yaji din ni, nayi sauri na kashe wayar. Makale ta nayi a kirjina daidai saitin zuciyata ina ajiyar zuciya idanuna a lumshe, na kwashe Lokaci mai tsawo a haka kafin in silale kan gado in kwanta. Babu abinda ya dinga dawo min a cikin kaina irin fuskar Abbu, yanayin yadda yake gudanar da rayuwar shi very cool and impressive, murmushin shi, yanayin kallon shi, zubin halittar shi.... A takaice dai da tunanin Abbu nayi barci a ranar. Wasu irin mafarkai na dinga yi barkatai kala-kala kuma cikin su babu wanda ban ga Abbu a ciki ba. Muna zaune akan wani lilo ni dashi a wani hadadden lambu mai cike da ni'imah, hira muke yi dashi duk da bana sanin abinda yake fada amma murmushi nake tayi a mafarkin har ina hadawa da dariya, ya dauko strawberry da fork ya miko min, na daga bakina kenan zan karba naji an daka min duka a kafada ba shiri na tashi daga mafarkin da nake, hannuna dafe da kafadata inda yake min xugi na tashi zaune ina kallon wanda ya aikata wannan danyen aiki. Mommy ce tsaye a kaina tana hararata, tunda naga haka nasan abinda nayi. Da sauri na kai duba na zuwa jikina, as I expected; babu riga. Da sauri naja bargo na rufe zuwa wuyana tare da sadda kaina kasa, nasan cewa yau mai kwatana a hannun Mom sai Allah. Cikin hararar da take jifa na dashi tace "Yanzu saboda Allah Ummiey har yanzu baki daina wannan rashin hankalin da kike yi ba? Haka kika je gidan mutane dama kina musu tallar halittar jikin ki?" da sauri na girgiza mata kai, "A'ah wallahi Mom, bana yi a can" tace sai anan koh saboda kin raina ni ko" nayi saurin girgiza kai nan ma "Allah Mommy ba haka bane, ni fa ban ma san lokacin dana cire rigar ba" tace "rufa min baki nan uwar en zagin baki tun yaushe nake miki fada game da haka Ummiey? Amma saboda taurin kai saboda kin maida ni abokiyar wasan ki baki ji koh?" tuni hawaye suka ciko min ido abinda nasan Mommy bata so kenan, cikin shagwaba nace "Allah Mommy da gaske nake. Nima fa ban san lokacin da nake cirewa ba, kawai ji nake yi kamar rigar ta na shake ni sai in kasa numfashi shi yasa nake cire rigar kuma fa na daina Allah da gaske, ban san ya aka yi na cire jiya ba" ta kalleni kafin ta kauda kai ta juya zata bar dakin, "sai ki tashi ai kiyi sallah koh? An kira tun dazu" na bita da kallo har ta bar dakin, sighing nayi a hankali tare da lalubo rigata da nayi jifa da Ita a kasan gado na zura, saukowa nayi daga kan gadon na fada bandaki.






                   *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:32 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *25*



          Yana ajiye wayar ya lumshe idanunshi tare da maida bayan shi ya jinginar da study table din da yake kai a zaune. Nafeesah! Nafeesah!! Sunan dake ta shawagi kenan a tsakiyar kanshi a lokacin, Allah kadai yasan iyaka adadin kewar ta da yayi. Shi kan shi yau sai da yayi Kokari ya iya sauka daga kan gadon shi, gidan da Babu Nafeesah! Teburin cin abincin da babu Nafeesah!! Rayuwar da babu Nafeesah!!! Abinda yayi ta jinjinawa a cikin ranshi kenan yana tunanin ko zai iya surviving a haka?! A hankali ya bude idanunshi tare da gyara zaman shi, hannunshi ya dora akan system din dake gabanshi ya cigaba da typing din da yake yi kafin Nafeesah ta kira shi ya fada cikin shaukin ta. 

     Kofar dakin shi yaji an turo, an shigo, tare da maida kofar aka rufe. Da mamaki ya daga idanunshi da suka gama rinewa da shaukin Nafeesah ya kalli Mubeenah dake tunkaro shi. Shi a karan kanshi ba zai iya tuna Lokaci na karshe daya ganta a tsakiyar dakin shi ba, ya jijjiga cikin wani irin takaici na babu gaira babu dalili daya ziyarce shi she has ruined it! She just ruined dan guntun farincikin daya mamaye zuciyar shi for a while. Kallo ya bita dashi har ta zauna a gefen gadon shi, sanye take da doguwar rigar barci har kasa, jelar kitson kanta da aka mata fiye da watanni biyu da suka wuce (lol) ya fito ta cikin hular data saka a kanta ya zubo har kan kafadunta. Kan shi ya dauke ya maida ga rubutun da yake yi, ya kwashe kyawawan mintuna arba'in kafin ya gama. Ya kashe system din tare da tashi ya fada bayi, brush yayi tare da dauro alwala kamar yadda yake a Al'adar rayuwar shi. Ya fito ya tsaya a gaban mirror, turare mai sanyin kamshi ya fesa a gabban jikinshi ya koma kan gado daga can daya gefen da Mubeenah take a zaune har lokacin, light off yayi ya kwanta. Mubeenah data gama kuluwa da abinda yayi, tace "haba Ibrahim wannan wane irin rashin mutunci ne kana gani na zaka yi wani banza dani ka maida ni kamar wata invisible human being?" ya kalli sashen da take duk da baya ganinta saboda duhun da dakin yayi, yace "au! Ai ban yi zaton cewa kina da abun cewa bane, na sani ko zuwa kika yi kawai kiga yadda dakina yake duba da yadda kika share watanni ba tare da kin leko ba?" ta dan ja siririn tsaki, " amma dai kasan cewa bana zuwa dakin ka haka nan koh?" ya gyada kanshi a hankali, a zuciyar shi yace 'right! Bana ganin ki a dakina sai idan kina bukatar either kudina ko jikina!' yayin da wani irin bakin ciki da takaici ya mamaye zuciyar shi. Tashi zaune yayi tare da kunna wutar dakin ya juya yana kallonta, "What do you want then?" ta dan yamutsa fuska "ina bukatar kudi ne!" ya kalleta sosai, "kudi kuma? Har nawa?" tace "one hundred and fifty k" ya gyara zaman da yayi sosai "n why would I?" ta wani hade fuska, "it's for you Ibrahim! Material ne zan saya da jewelries na zuwa bikin bude kamfanin ka kaga kuwa it's worth it" shi gabadaya ya ma kasa magana, kallonta kawai yake yi har ta dire maganar ta. Yace "duka duka yaushe kika amshi 50k a wajena Mubeenah? Wai saboda meye na bude miki saloon? Ina ce dama saboda idan bukatu irin haka sun taso kiyi amfani dasu ba tare da kin tambaye ni ba ne?" ta wani lankwashe murya Ita ala dole kissa tace "kasan cinikin saloon din ne kwana biyu sai a hankali babu customers shi yasa, yanzu haka bani da ko sisi a account dina" ya girgiza kai kawai, Mubeenah! Bai san wace irin mata ce Ita ba, Kwatakwata bata da damuwar yanayin da mutum yake ciki ko zai shiga, Ita dai kawai a bata abinda take so sai a samu zaman lafiya. Yace "Mubeenah! Baki ganin halin da ake ciki ne yanzu? Dinkin dubu dari a wannan zamanin Mubeenah ki duba mana, ina laifin hamsin?" hararar shi tayi a kaikaice tana mai turo baki, "kaga ni fa ba cewa nayi ka zauna kana bani labarai ba. Kudi, zaka bani ko A'ah?!" Murmushi yayi a sanyaye yace "zan baki mana uwargida sarautar mata..... Amma zo kiji kafin nan..." ya janyo ta zuwa jikinshi, cikin sauri ta zame, ya bita da kallo mai dauke da alamun tambaya. Fir taki amincewa dashi sai da tayi tsayin daka taga a take ya tura mata kudin cikin account dinta sannan ta amince. Shima haka nan ta tsaya abinta shi kadai yake kidan shi da rawar shi tana kwance male-male kamar ruwa. Ba a jima ba ya mirgina daya gefen gadon yayi ruf da ciki idanunshi a lumshe, duk dokin da yake yi sai yaji ya kau daga ranshi saboda yadda tayi kamar bata jindadin kasancewa dashi, he means ta ya za ayi ace mace ana having s*x da Ita amma Ita ko a jikinta, karewa ma Allah-Allah take yi ya sauka daga kanta, does it make sense? (Qalubale a gare ku mata, akwai ire-iren ku kuna nan libge cikin lungu da sako na wannan duniyar, a gyara dan Allah!). Bayan nan Kwatakwata baya jin dadin kasancewa da Ita shima, koda yake abu ne daya riga ya saba dashi. Yana tunanin tun wajen haihuwar Hafsat Mubeenah ta karu kuma bata maida hankali wajen ganin cewa an dinke ta ba, ko don bata damu dashi bane? To shi dai tun daga nan ya daina fahimtar Mubeenah, haka nan yake maleji dai ko don raya Sunnah da kuma kare kai daga dattin Zinah to yanzu abun dai ya fara wuce misali. Yana jin lokacin data tashi ta zura kayan jikinta ta fita daga dakin, bata damu da yadda miji ya juya mata baya suna tsakiyar auratayya ba, bata damu taji dalilin daya saka shi aikata haka ba balle tayi tunanin gyara, Ita dai kawai tunda ta samu abinda take muradi to an wuce wajen. Da kyar ya tashi ya fada toilet yayi wanka da ruwa mai sanyi, babu abinda ta6a Mubeenah ya jayo mishi sai kara hargitsa mishi tunani da kwalwa da yayi. Ya fito ya canza kayan barcin shi kafin ya kwanta, zuciyar shi cike da tunanika barkatai, mafi yawa daga cikin su shine 'He had to make Nafeesah his ASAP, kafin wani ya riga shi ya shiga uku'.



Sati na daya a gida ina hutu, babu inda nake zuwa daga farfajiyar gidanmu shan iska sai kicin, bana aikin komi sai na kallo da chatting, hankalina a kwance yake duk da cewa har zuwa lokacin kewar Abbu da iyalan shi na taba raina babu abinda ya ragu, har yau ina jin abun kamar a ranar na bar gidan. Muna waya dasu Hafsy sosai, zan iya cewa ma kusan kullum sai mun yi waya dasu. Ina kwance a tsakiyar gadona da system a gabana ina duba wasu docs a ciki. Ranar asabar ce daga ni sai Mommy a gidan, Daddy yaje Abuja wajen wani meeting. Mommy ta leko dakina, dagowa nayi na kalleta tace "ki tashi ki shirya muje Airport mu dauko Antynki Shafa" wani irin tsalle nayi na diro daga kan gadon na riko hannunta, cike da doki nace "Mommy da gaske? Yaushe tazo?" tace "she's yet to land, nan da awa daya may b" nayi sauri na fada bandaki ina ihun murna, Mommy kai kawai ta girgiza ta juya. Anty Shafa'atu matar autan su Daddyn mu ce suna zaune a New York, Gynaecologist ce wadda tasan aikinta. Ina matukar son matar saboda nima tana sona, matar ta hadu ne ta kowane fanni, ga kyau ga iya kwalliya ga iya girki, duk lokacin data zo ina makale da Ita ina koyon girki da kwalliya a wajenta. Dan su daya Mukhlis dan kimanin shekaru uku, idan kaga yaron sai ka rantse da Allah dan turawa ne saboda kyan shi. A gurguje nayi wanka na fito, kwalliyar da nayi ba wata ta azo a gani bace amma nayi kyau sosai musamman dawowar nan da nayi nayi wani fresh dani. Doguwar riga fitted gown nasa ta wani yadi navy blue, nayi rolling da gyale shima navy blue na saka takalmi mai dan tsini navy blue, kyakkyawar farar kafata ta fito a fito sosai a cikin takalmin tayi kyau, cikin jikkuna na ciro wata er karama ta vintage ruwan kayan jikina itama na rataya a kafadata, falo na fita. Mommy bata gama shiryawa ba don haka ne nayi amfani da damar nan na tsaya kashewa kaina selfie. Tana fitowa muka wuce, a cikin karamar Motar Mommy din Vibe muka fita, Ita take tukin mota don ni har lokacin ban iya tuka mota ba, Daddy ya fara koya min ban maida hankali na bane shi yasa. Lokacin da muka isa Airport din basu kai ga sauka ba don haka muka tsaya a lounge room muna jiran su. Ba a dauki mintuna ashirin ba jirgin ya sauka, muka tashi muka fita muna jiran su. Ina hango fitowar ta na fara daga mata hannu har ina hadawa da tsalle, suna fitowa na ruga na rungumeta ina tsallen murna a jikinta. Ta dago kaina daga jikinta tana kallona tana dariya, "Haba Ummiey ni me zaki ce min? Shekaru nawa rabon da ki kirani mu gaisa ni nayi ma zaton kin manta dani ai" nayi er dariya nace "Aunty kin san waya daga nan zuwa inda kuke minti daya fa zan iya sayen atamfa da kudin, wannan marra kuma ta economising kudi ce shi yasa, Ke kuma ba kya kira na kema" taja hancina tana dariya, "Ummiey kina nan da dadin bakin nan naki, ba a taba kada ki a xance" Mommy ta karaso wajen mu suka gaisa da Anty Shafa, sai da muka nutsa na kula da ban ga Mukhlis ba, nace "Anty baki zo da Mukhlis bane?" bayanta ta waiwaya tace "nazo dashi mana, yana wajen Harith". Tana rufe baki wani dogon gaye, fari tas dashi kamar Antyn ya tsaya a gabanmu, akan kafadar shi kyakkyawan babe ne yana wasa da abun wasa na yara, da sauri nace "Mukhlis!" yaron ya juyo ya kalleni na en sakwanni kafin ya dauke kan shi, ina mika hannu zan dauke shi yayi sauri ya makale a jikin gayen, baki na kama cike da mamaki, nace lallai Mukhlis har ka manta dani? Last time da zaku koma kuwa da kyar aka banbare ka daga jikina. Anty tace "ai kwanaki sun ja Ummiey, ya kara wayau da shekaru fa" Mommy data gaji da tsayuwa tace mu tafi koh? Sai lokacin wannan gayen yayi magana, cikin wani irin yanga-yanga ko fi'ili zan ce, "Sis, ni zan wuce gida ne fa" tace "ok, ni sai na tsaya a gidan su Yaya sannan. May b da dare in shigo" ya wani tabe baki tare da mika mata Mukhlis, sai lokacin ya kalli Mommy ya gaishe ta, ta amsa da fara'ar ta tare da tambayar Anty "wannan ko kanin ki ne?" tace "ehh, yana karatu ne a can NY din, ya biyo ni wajen biki ne" sai lokacin naji ashe bikin kanwarta Murjanatu tazo. Gayen ya kalleni a fuzge yana wani shan kamshi, wai "sannu koh??" don ba don idon su Anty a wajen ba da wallahi ba zan ko kalleshi ba, a fuzge nima na amsa mishi, "kaima sannunka" Anty tace "can we please? Na gaji da tsayuwar nan" muka nufi motar Mommy muka shiga, ina kallon idanun gayen nan a kaina lokacin da muka ja motar muka tafi, baki na murguda mishi yayin da naga ya saki murmushi yana muttering wasu kalmomi da ban fahimta ba. Already dama an gyarawa Anty daki tun jiya don haka muna zuwa ta fada dakin don watsa ruwa, na shiga dakina na shimfidar da Mukhlis a kan gadona saboda yayi barci. Na fita naje na fara dauko abinci ina kai mata dakinta, kafin ta fito na shirya mata komi don haka zama kawai tayi ta fara cin abinci na zauna a gefenta muna en hirarrakin mu har ta gama cin abincin, sallah tayi ta kwanta nima na koma dakina na kwanta a gefen Mukhlis. 






                    *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:34 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *26*



      Anty Shafa ta fito daga dakin da aka mata masauki tana jan hannun Mukhlis, muna zaune a cikin falo Bayan mun gama cin abinci, ina gefen Mommy a zaune kawai muna hira da ita. Anty tace "Ummiey zo ki raka ni mana?" Na kalli Mommy kafin in maida kallona ga Antyn, Mommy tace "ni fa ba hana ki zan yi ba kike wani kallona, tashi ku tafi mana" murmushi nayi na tashi na shiga dakina, wandon jeans ne a jikina da shirt don haka na saka doguwar hijabi na fita muka wuce gidan su Anty. A Shagari road suke basu da nisa da inda muke don haka tricycle muka yi shata har kofar gidansu, gidan Babban gida ne da parts parts. Mahaifin su matan shi uku saboda haka gidan su gidan iyali ne sosai, Anty Shafa itace autar uwargidan Hajiya Maryam wadda ta rasu shekaru biyu da suka wuce. Muna shiga gidan gida ya dauki sowar murnar zuwanta, da kyar muka samu muka shiga part din Hajiya Talatu uwar gida a halin da ake ciki. Muka shiga har uwar dakanta inda muka sameta akan gado a hakimce, cike da girmamawa muka gaidata ta wani amsa da kyar kamar wadda aka takurawa, dana kalleta sosai sai naga kamanninsu da gayen nan na airport na tabe baki a raina nace ashe gado yayi. Bamu yi minti goma ba muka tashi muka wuce daya part din, Ita dayar da naji suna cewa Hajiya Amarya ba laifi tana da fara'a. Anan sashen nata en sannu da zuwa suka yi ta shigi da fici. Sai wajen karfe goma na dare muka musu sallama, na saba Mukhlis dake ta shakar barci a kafadata. Muna fita waje muka jiyo horn din mota a gefenmu, muka juya. Wata jar mota er karama da Ita mai kyau, Anty tace muje, Harith ne zai mika mu gida. Sai dana turo baki kafin na bi bayanta, haka kawai naji gayen bai kwanta min a rai ba. Na bude gidan baya na zauna a gefen Anty, Harith ya juyo ya kalli Antyn kafin ya kalleni ya sake kallonta, "amma dai ina fata ba Driver zaku maida ni ba ko Sis?" Anty tace min dan Allah tashi ki koma gaba diyata. Ba yanda na iya na fita na koma gaban, ya tashi motar muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikinmu har muka isa kofar gidanmu, yayi parking muka fita, Anty tace mishi "sai da safe koh?" bai amsa ba sai kallona da yayi, "enmata babu godiya ne?" ban san lokacin dana wurga mishi harara ba na juya na wuce abina, na kula he's very arrogant. Anty ta biyo bayana tana ce min wai kar in damu dashi, haka halinshi yake. Ban ma tanka mata ba don a tunanina ai sai ka damu da mutum ne sannan al'amuran shi suke damun ka. Sai da muka shimfidar da Mukhlis sannan na mata sai da safe na wuce dakina, cikin mintuna sha biyar na gama duk shirin da zan yi na kwanta barci. 


 Washegari aka fara bikin gidan su Anty Shafa, tun da safe ta tafi ni kam ko wajen bikin ban leka ba Mommy ce ma taje. Ina gida da yamma Malamin dake koya min karatu yazo ya kara min, lokacin Mommy ta dawo muka shiga kicin muka girka Jollof macaroni da fried chicken, muna girkin nake tambayarta Mama Sauda da yake kwana biyu ta sha rashin lafiya don haka suka maidata kauyen su tace ai taji sauki tuni, Daddy ne yace tayi zamanta a can kawai, na gyada kai.


Ni kadai ce a cikin falon lokacin da Anty Shafa ta dawo, na mata sannu da zuwa tace "tare muke da Harith wai yunwa yake ji, Allah sa akwai abincin?" na kalli dinning nace "akwai, sai dai ban tunanin zai ishe ku ku biyu" tace "nooo, ni nace abinci a gida, shine wai ba zai ci abincin biki ba, he can be picky about foods sometimes" na tabe baki nace shi ya sani ai. Anty tayi murmushi tare da juyawa don mishi iso ni kuma na leka dakin Mommy na fada mata. Ina dawowa falon yana zaune a daya daga cikin kujerun falon, Mukhlis yana cinyar shi, yaron yana ganina ya sauka daga kan cinyar shi ya rugo ya rungume ni, na tare shi ina dariya nace "mun shirya yanzu kenan?" Anty tace dama shi ai kwana daya ake Sabo dashi. Saboda idon Anty ne yasa na kalli sashen da Harith yake, "sannu" kawai nace, ban tsaya jiran amsawar shi ba na wuce dinning nayi serving dinshi abincin a plate na kai gaban shi na ajiye, kan kujera na koma na zauna na ja Mukhlis jikina ina jan shi da hira. Ya kalleni yace 'enmata baki bani ruwa ba" sai dana kalleshi kafin na tashi kicin naje na dauko ruwa mai sanyi a fridge na kawo na ajiye mishi, yace "sorry! Bana shan ruwa mai sanyi" na ciza lebe tare da dauke goran ruwan na je na canzo mishi da mara sanyi na kai mishi ya sake kallona yace "Baku da lemu ne haka kamar fanta ko peach?" zuwa lokacin nasan cewa he's doing it on purpose, ban ko kalleshi ba na koma na zauna abina, ya kalli Anty ya wani lankwashe murya, "Anty lemu nake so" tace Bari in dauko maka to, wanne kake so? Yayi saurin cewa "no no Anty, da girman ki ki dauko mun lemu haba! Bari yarinyar can ta dauko min mana" ban san lokacin da wani irin murmushin takaici ya subucewa fatar bakina ba, lallai ma Harith! Wai yarinya! Anty da bata kula da game din da yake bugawa ba ta tashi tsaye tace "Ummiey don Allah taimake shi da lemu, bari in rage kayan jikina" ta shige dakinta ni kuma naci gaba da wasana ni da Mukhlis, kallona yayi yace "baki ji abinda Sis tace ba? Ki bani lemu!" ban kalli sashen da yake ba nace "the kitchen door is over there...." na nuna mishi da yatsa ta, "zaka iya zuwa ka dauko da kanka, m not someone da u can be ordering around ni kuma in biye maka kamar wata er aikin ka" yayi wani irin smirking tare da dan shafa gefen wuyan shi, "seems like u r one Rude babe, I like it!" a xafafe na jefa mishi harara, "hey watch ur mouth!" ya tsuke baki yana jifana da wani irin kallo, "if not ki raba ni dashi?" tsaki kawai naja na kauda kaina gefe don na kula da neman magana ne kawai yake yi. Anty ta fito daga dakinta ta zauna a gefen Harith, ganin yadda nake jifan shi da harara ta dube shi cike da tuhuma tace "Me ka mata Harith?" ya kalleta kafin ya kalleni cikin dage gira, "Me na miki?" tashi kawai nayi na bar musu falon don na kula idan na zauna Harith zai iya sawa in zage shi a gaban Yayar shi abinda bana so kenan. Dakina na koma na fara chatting, a facebook na ga wani page da wani daga cikin friends dina yayi liking, *Hon. Ibrahim Galadanchi Official Fans Page* cikin mamaki na shiga page din, da gaske Abbu dinne. A Profile pic din da aka dora Abbu ne ya saka wata shadda Skye blue dinkin Abacha, shaddar ta matukar yi mishi kyau, kwarjinin shi da kyawun shi sun fito kamar ka kira shi a hoton ya amsa saboda yadda hoton ya dauku sosai. Na kura mishi ido na dan lokaci kafin na janye kaina, jikina yayi wani irin sanyi wanda ganin hoton Abbu da nayi yanzu ya haddasa min, sai kuma wani tunani daya darsu a raina, kenan Abbu har yanzu yana kan bakan shi akan fitowa siyasa? Ni dana ji shiru kwana biyu ban ji zancen ba nayi zaton ko ya hakura ne ashe bai hakura ba. Kenan idan har na aure shi sai dai in janye kiyayyar siyasa dana sawa raina, kenan zan zama matar dan siyasa? Murmushi nake yi kamar wata doluwa da nayi wannan tunanin, na sake janyo wayata nayi liking din page din. Ranar haka na bata Lokaci na wajen saving din pics din Abbu da suke cikin page din, sai wajen karfe sha biyu na kashe wayar na kwanta. 






                    *♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:35 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *27*




          *When you run too fast to get to Somewhere....., You Miss the fun of getting There.... Life is not a race, so take it slower and enjoy The Music Before The Song Is Over!*



          Sati biyu tsakani muka koma makaranta, ba wani bata lokaci muka shiga lectures ba sauki, Ramlah tuni ta dawo, muka hadu da sauran abokan mu muka fara karatu ka'in da na'in ba sassautawa. Wajen karfe biyar na dawo daga makaranta, mai adaidaita din da nayi shata ya ajiye ni a kofar gidanmu. Na fito ina karewa jar Renault Clio dake fake a kofar gidanmu, dan siririn tsaki naja sanin mamallakin motar; Harith ne. Kwana biyu ya maida gidanmu kamar wani gidan zuwan shi, ya saba dasu Mommy da Daddy sosai cikin dan lokacin sau tari idan bai je gida ba zaka ji Mommy tana ta jajen shi, yayin da a gefe guda har zuwa lokacin mun kasa getting along dashi. Harith yana da yawan tsokana, ni kaina wani lokacin idan yana tsokanata I couldn't resist murmushi duk da is hardly in dara, matsalar Harith daya zuwa biyu, girman kai da son showing up Baban shi mai kudi ne kuma yana karatu a kasar waje, gashi bai iya magana ba, magana duk yadda tazo mishi zai kwabawa mutum ne yayi gaba abinshi duk da dai na fahimci hakan a jinin shi yake but still ni fa sam mutane masu halayen Harith basu cikin en kayana. Kudin mai adaidaitan na ciro na bashi na wuce cikin gida. Sanye nake da wandon jeans pencil da shirt mai tsawo wadda ta sauka har kuguna, na dora bakar rigar kimono a kai tana daya daga cikin tsarabar da Anty Shafa ta kawo min. A hankali nayi ssallama na shiga falon, Harith na zaune akan kujera ya baje shi da Mukhlis suna shan tangerine, Gabadaya sun lalata wajen da bawon lemu, yana ganina ya saki murmushi tare da dago min hannu, "Hii Rudie!" harara na jefa mishi na zauna akan kujera ina kokarin daukar Mukhlis daya xo min oyoyo, na bude jakata na ciro chocolate din Milk Dairy na fasa na mika mishi, Harith bai daddara da hararar dana jefa mishi ba yace "Chocolate aka kawo mana yau? A miko min nawa to" ko kallonshi ban sake yi ba. Mommy ta fito daga kicin hannunta dauke da goran ruwa, ta miko min na amsa tare da dauke Mukhlis daga kan cinyata, tana ganin chocolate din hannunshi ta fara mita, "Ummiey na hana ki ba yaron nan chocolates da sweets amma kin ki, kina so ki lalatawa yaro hakori tun yanzu koh?" nace "Mommy babu abinda zasu mishi yanzu, bayan haka ma ai idan ya girma zai zubda hakoran wasu su fita ne koh?" ta Harare ni "Allah ya shirya min Ke Ummiey, ban san yaushe zaki girma ba" Harith yayi tsulum yace "Mommy kin san wauta irin ta en fari sai a hankali, musamman ma Ita da abun ya hade mata biyu ga faranci ga autanci" kallonshi nayi cike da takaici, nace "wai don Allah meye matsalata da kai ne Harith? Bana shiga harkar ka ka daina shiga tawa pa!" ya wani rausayar da kai innocently, "haba Ummiey, me na miki? Daga fadar gaskiya?" tashi nayi kawai na dauki jakata na shige daki, kayan jikina na cire na duba Lokaci naga da saura kafin a kira Magriba don haka na fita. Tuni Mommy ta gama girki don haka nayi joining dinsu a kallon da suke yi, mommy na tambaya ko ina Anty Shafa? Tace taje gidan su ne yini, Mom ta miko min tangerines masu kyau a bare an shirya su cikin plate tace Harith ne ya kawo musu su ci, na saci kallon inda yake zaune, idanunshi fes suna kaina, muna hada ido ya kanne min ido daya da sauri na janye kaina na dora su akan Mommy. 

 Ina kwance ina sana'ar chatting dina, naga wata sabuwar number ta turo min comment akan hotona dana dora akan status dina na Whatsapp ranar da safe, kayan dana saka ne ranar nayi murmushi hannuna dauke da mug din coffee, cewa aka yi "you look so cute n gorgeous Nafeesah" na danyi frowning tare da tura "who?...." ba a dauki lokaci ba sai ga reply, Hoton Harith ne ya wani kashe ido daya yana smirking da alamun a lokacin ya dauke shi, tsaki naja na tura mishi, "what? Are you a stalker? Or may be a pervert??" bai turo amsa ba, na tabe baki naci gaba da chatting dina. Wayana tayi kara, number ce duk da haka ban fasa dauka ba, ina kara ta a kunne muryar Harith ta doki dodon kunnena, "Ba a taba jifa na da kalma mai muni a rayuwa irin wannan ba, amma naji dadin sunayen, ban sani ba kila na cancance su ne!" nayi rolling idanuna kamar yana gabana, nace "meye na kira na da daren nan?" yace "just...... Manta kawai. Amma you seems to be avoiding me tunda na shigo rayuwar ki Nafeesah, why? Or may be are you afraid to fall for me??" wata mahaukaciyar dariya na saki har ina kwarewa, "stop being ridiculous Harith. You are not my type, rashin zama kusa da kai da bana yi ba avoiding dinka nake yi ba ko tsoron fadawa tarkon son ka ne ko wace shirme kake fada, i found you very annoying and I don't want to get along with annoying people" ya danyi shiru, cikin raina naji babu dadin maganar dana mishi ba sai dai Harith yana shigar min hanci da yawa I really want to get rid of him. Gyaran murya yayi yace cikin murya mai sanyi kamar ba tashi ba, "and I promise to become your type Nafeesahh, I promise you that.... Nooo, challenge you, deal??" bai jira amsa na ba ya kashe wayar ya bar ni da waya a hannu baki a bude cike da mamakin maganganun shi.



         Washegari sai karfe tara da kwata na fito daga dakina cikin shirin makaranta saboda ranar sai karfe goma nake da Lecture, nawa Mommy da Anty Shafa sallama na fita. Shiru-shiru ina tsaye a bakin titi babu alamun wucewar abun hawa, na kara hangar tsawon titin da zai sada ni da Babban titi inda zan samu bus na tabbata idan nace sai na fita bakin titi zan makara ne, na kara duba agogon hannuna karfe tara da rabi ta wuce, na danyi siririn tsaki tare da daga kafa na fara tafiya ina tuhumar kaina dalilin daya hana ni ajiye direba kamar yadda Daddy yaso tun farkon shigata KadPoly ni kuma na kekashe kasa nace A'ah. Motar Harith kawai na gani a gabana kamar wanda aka jefo daga sama, ya tsaya a daidai saitina tare da zuge gilashin motar ya leko da kanshi waje, "will you mind a lift en mata?" ban tsaya neman magana ba na zagaya daya gefen na shiga, yaja motar muka fara tafiya, sai dana mula na mule sannan nace mishi "ka tashi lafiya?" yayi murmushi, "kamar yadda kika tashi ba" daga haka yaja bakin shi yayi shiru har muka isa makaranta, ba karamin jin dadin hakan nayi ba. Yana yin parking na bude murfin motar na fita, dan dukawa nayi ina kallonshi yayin da shima yake kallona, nace "thanks pa!" thumbs up ya min da hannunshi, "Always baby..... Yaushe zaki gama lectures?" nace Four in shaa Allah" yace "idan na samu lokaci zan biyo in dauke ki" nace "noo, you don't have to do that plss" bai amsa ba ya tashi motar ya tafi, a hankali nima na juya na tunkari hall din da zamu yi lecture din. 


Karfe hudu dai dai muka fito daga lecture hall din da muka yi na 1-4, ni da Ramlah muke tafe a hankali a cewarta sai ta raka ni bakin gate, muna gab da fita daga parking lot kawai muka ga tsayuwar mutum a gabanmu kamar daga sama., Muneer ne! Na daga idanu na kalleshi a hankali, tunda abun nan ya faru ban kara waya dashi ba haka tunda muka dawo school bamu taba haduwa dashi ba. He was still the same Muneer kamar yadda na san shi, dogo, wankan tarwada....., Ramlah ta jefa mishi wata irin harara, "Malam Lafiya zaka tare mutane a hanya kamar wani tsoron thug?" bai kula da Ita ba idanuwanshi na kaina, ya kira sunana cikin sanyayyar muryar shi wadda ada nake jinta tamkar busar sarewa amma a yanzu, jinta nayi kamar kukan jaki. Yace "Nafeesah! Dan Allah zaki iya bani minti biyar muyi magana?" Ramlah ta yunkuro zata yi magana nayi saurin dakatar da ita, "it's okay Ramlah I've got this. I'll talk to him" ta kalleni sosai kafin ta dan matsa gaba ta bamu waje, na kalleshi a tsaitsaye, "so me kake son fada Ango-Muneer??" na fada sarcastically. Yace "Nafeesah I am really sorry akan abinda ya faru that night, sai daga baya na fahimci I acted rudely towards you, am sorry. Ba niyya na kenan ba na in tozarta ki, ban...." nayi saurin katse shi, "kaga Muneer! Idan akan wannan maganar ne kada ka damu, I've move on already, ni kaina sai daga baya na fahimci kuskuren da nayi na makalewa wanda baya sona. Kai ni sai daga baya ne ma na fahimci ashe ba sonka ne nake yi ba, burge ni kawai kake yi ni kuma da yake I was stupid then I thought it was love ashe it wasn't...." fuskar shi dauke take da wani irin expression wanda ya kusa saka ni dariya a take, daga ganin yadda yayi bai ji dadin maganar da nayi ba. Ko yana tunanin dana ganshi zan zube a gabanshi ina rokon ya aure ni ne? Ya kalleni da fuskarshi cike da damuwa, "Nafeesah......! Would you please give me a second chance? I promise to be what you want me to be, wallahi sai daga baya na fahimci cewa ina son ki, plss ki bani wata dama" ga mamakina maimakon farin ciki sai naji zuciyata tayi wani irin baki, lallai ma Muneer ni zai rainawa wayau? Fuska na hade nace "Muneer ka riga kayi wasa da damar ka in which I am very grateful for that don haka tun wuri kaje ka rungumi amaryar ka kafin kwado ya maka kafa itama ka rasa ta. All the best!" na zagaya ta gefen shi na wuce, da sauri ya tari gabana, "plsssss Nafeesah! Just a second chance! I know u love me, and I know that u didn't get over ur feelings for me!!" cike da wani irin jin haushin shi da kuma kaina ma gabadaya nace "feelings my a**!! Yaudarar kan ka kake so kayi Muneer, I don't Love you any more!!" na fada cikin daga murya, "now if u can please fuck the hell out of my sight plsssss, you are disgusting!!" amma da alamun ko kadan maganganuna basu shiga kunnen shi ba, kokarin matsowa gare ni ya fara yi da sauri naja da baya, just when he was about to take another step closer na jiyo muryar Harith daga bayan mu, "Nafeesah my Love!!"






~So What did you think about today's Chapter?

~What did you think about Harith sudden appearance in the story? 

~Don't forget, recommendation door is open to me, so feel free to recommend and correct me anytime you spot a mistake in my writings 

~Follow me on Wattpad @Jeeedorhh

 ~♥~Much love Ni Da Abokin Baba Na Fan's.....~♥~





                      *♡Jeedderh♡*


*NI DA ABOKIN BABA NA....!*


             *©°•Jeedderh Lawals•°*


                       *28*


       A hankali na juya na kalleshi, ya sake wanka yasa wani wandon jeans din Vogo da rigar CK mai V-neck, ya matso kusa dani ya tsaya gab dani yana kallon Muneer fuskar shi a cunkushe, sun dauki lokaci suna kallon-kallo shi da Muneer babu wanda yayi magana a cikin su, sai da naga shirun yayi yawa sannan na daga kafa na fara tafiya, na kalleshi nace "muje koh?" babu musu ya biyo bayana muka jera muka tafi, muna fara tafiyar ya tsaya cak tare da juyawa ya kalli Muneer da shima ya juyo yana kallonmu, yatsa ya nuna mishi cikin kashedi yace "and dude, stay out of my Fiancé side, if not....." ya juya ya cigaba da tafiya cikin takama har yana hadawa da wani bouncing, na bi bayan shi ina dan murmushin jin dadin shocked and horror expression din dana gani akan fuskar Muneer. Ramlah dake tsaye a gefe tana kallon dramar da muke bugawa ta kamo hannuna taja gefe tana tambayana wai da gaske na daina son Muneer? In ka kalli fuskarta a lokacin sai ta baka dariya, grinning take ear to ear kamar yaron da aka ba kyauta alewar bounty. Na sabule hannunta daga nawa nace mata "kinga jirana ake yi, anjima zamu yi magana" muka yi sallama na wuce na shiga motar Harith har ya tashe ta don haka ja kawai yayi muka wuce. Harara na jefa mishi, ya juyo ya kalleni "what??" nace "what was that for? That fiancé thing??" yayi rolling idanunshi, "baki gane bane? I was just trying to save you from him so that next time ba zai kara damun ki ba koda bana nan, by the way waye shi?" na danyi sighing softly kafin na kalleshi fuskana a dan hade don ya dauki maganar da zan mishi seriously nace "sanin waye Muneer ko rashin sa babu abinda zai tsinana maka don haka stay out of it, maganar fiancé kuma kada ka kara koda cikin wasa ne kuwa ko trying to help kamar yadda kace" ya kalleni yana murmushi cikin tsokana, "ko dai baki son inji cewa crush dinki ne yayi dumping dinki kuma ya dawo yace yana son ki?" kaina na kawar gefe naki kallonshi, naki jinin a tuna min da tarin yarinta da rashin hankalin da nayi akan Muneer. Amma Harith bai kyaleni ba cewa ya sake yi "tunda baya sonki me zai hana ki zo mu sasanta dake?" a fusace na kalleshi "stop messing with me fa Harith!!" ya tabe baki, "well, m not ai dama" nace "to ni nan da kake gani na I am taken ka gane?" ya juyo ya kura min ido na dan lokaci kafin ya maida hankalin shi ga tukin da yake yi yana chuckling, ban kula shi ba na janyo wayata ina latse-latse har muka isa gida. Yau ko godiya bai samu albarkacin jin ta ba, na fita daga motar har ina banging nayi cikin gida. Kai tsaye dakina na shige, nayi jifa da jakata akan gado kafin nabi bayanta nima na kwanta a rigingine ina tariyo abinda ya faru a makaranta ranar. 


    Vibrating din da wayata ya dauka daga cikin jakata ne ya dawo dani cikin hankalina, na danyi tsaki lokacin da nake laluben wayar, da kyar na iya bude idanuna da suka fara min nauyi saboda gajiya da barci na dora su akan fuskar wayar, sunan dana gani yana bouncing a jikin screen din wayar ne yasa naji zuciyata ta fara daka tsalle cikin wani irin farin ciki. Ya Allah! Yaushe rabona da inji muryar Abbu a rayuwa har na manta, Kun ganni nan kullum ina cikin page dinshi a facebook ina bibiyar rayuwar shi amma na kasa samun kwarin gwiwar kiran shi duk da cewa nayi kewar shi kuwa fiye da tsammanin mai karatu. Ganin kiran yana shirin katsewa yasa nayi saurin dagawa, sallama na mishi a nutse kuma cikin Karya murya, ya amsa cikin wannan muryar tashi cike da kasaita da wani irin huskiness daya kusa saka ni narkewa akan katifata saboda yadda naji wani electricity yana yawo a magudanar jini na. Daga can naji yana magana wadda tayi sanadiyar dawo dani duniyar Earth daga tafiyar da nayi zuwa Mars, cewa yayi "wato Nafeesah idan shekara zamu dauka ba tare da mun gaisa ba hakan bai dame ki ba koh? Ba kya neman mutane idan ba neman ki aka yi ba koh?" da sauri nace "Abbu ba haka bane ba fa!" yayi wata irin sassanyar dariya, "to ya ne Nafeesah?" na dan sosa wuyana tare da dan gyara muryata ina kokarin boye yadda dariyar Abbu ta kassara min gabbai, nace "Abbu muna karatu ne kuma dai bana so in kira ka ko kana aiki ko wani abu in takura ka" 'ina tsoron ka gaji dani, ina tsoron yin sabo da abinda zai zo yayi hurting dina daga baya" yace "that's not an excuse Nafeesah, when you feel like calling me just don't hesitate and call, zan amsa a duk inda nake no matter what m doing" na gyada kai kamar yana ganina nace "toh Abbu" ya sauya akalar hirar zuwa ta harkar karatuna, mun dauki lokaci muna hira kafin yace "Jiya muka dawo daga Beijing, nayo miki lodin tsarabar favorites chocolate crunch dinki, gabadaya na manta baki gidan ashe" nayi shiru kamar ba zanyi magana ba, wani irin dunkulallen abu ne naji ya makale min a kirji da kyar na iya danne shi na bude baki nace "Eyyah!! How I wish ina nan" yace "that's what m saying" nace "a ba Hafsy shi kawai, Allah ya nufa ba rabo na bane shi yasa" yace "um-uhm, abinda yake naki ne dole ki zaki ci shi Nafeesah. Pretty da kowa yaci nashi don haka kema dole naki zaki ce" na saki murmushi cikin jin dadin maganar shi, a hankali kuma cike da wani irin expectation nace "to ya za ayi yanzu?" shima yayi kasa da muryar shi har tafi tawa yin low, "ya za ayi? M thinking of coming to give it to you, Personally!" na karkada kunnena kamar ban ji sosai ba, sai dana dan yi hesitating kafin a hankali na maimaita "you?? Personally???!" sai dai can kasar zuciyata tsoro ne ya cikata, ina tsoron yace ba haka yace ba kila yace ba haka yake nufi ba.... Ya wanke min zargina ta hanyar cewa "yes, I'll come to you in baki tsarabar ki Nafeesah!!". Murnar dana ji ta cika min ciki ta ware a take lokacin da confusion ya dabaibaye ni, nace "amma why would you??" yace "because.... Because...... I.......!!" numfashi na ya dauke yayi sama yaki dawowa, na tabbata zuciyata ta buga sau dari cikin sakwannin da basu fi goma ba ina jiran inji karshen maganar shi, "..... Because I Can Of course Nafeesah!!" sai a lokacin numfashi na ya dawo kasa daga sama din da yayi, na fara yaki da zuciyata wajen ganin gudun da take yi marar adadi da numfashina da yake daidaituwa sun daidaita, a gefe guda wani irin disappointment ne ya lullube min zuciya. I'm such an idiot to think that Abbu zai fada min kalaman so! Yakamata in dawo daga duniyar Fantasy da Tunanin cewa wai Abbu zai so ni, Abbu yana da matar shi har da 'ya'ya abinsu and duk da cewa maimakon Happily, they are peacefully living together rather. Yace "besides Tu Me Manques!!" na dan yamutsa fuska, "Too mey Manqwe? Me kenan??" yayi er dariya, "just..... Sai anjima dai kawai. And please kiyi Kokari ki dinga kira na fa!" daga haka ya kashe wayar ya barni jiki a sanyaye kuma a sankame.

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *29*




         Aunty Shafa tana ta shirye-shiryen komawa nan da kwana biyu don haka bata zama a gida, tana ta faman ziyarce-xiyarce da sallama gidan en uwa da abokan arziki. Ranar juma'ah karfe sha biyu muka gama lectures, muna fitowa ni da Ramlah daga lecture hall din na hango Harith jingine da motar shi hannunshi rike da lemun team yana sha, yana ganin fitowar mu ya dago mana hannu. Ramlah ta kalleshi ta kalleni tace "wai meke tsakanin ki da Harith ne?" na girgiza kai, "to wa ya sani Ramlah? Nima kin ganni nan ban sani ba wlh" ta tabe baki, "to Allah ya kyauta!" nace "ameeeeen". Daga nan muka yi sallama. Tun kafin in karasa ya bude min kofar motar, na shiga na zauna ya maida ya rufe. Yana shiga motar na fara jefa mishi korafi ko bari ya tashi motar ban yi ba, "Wai Harith ba nace na yafe zuwa dauka na da kake yi ba?" sai daya tashi motar muka fara tafiya kafin yace "I was just in the neighborhood ne, nayi dropping Sister gidan Amarya Murja ne, shine nace bari in biyo in dauke ki tunda nasan kin gama lectures dinki" nace "ni ban ga kana shirin komawa ba" ya juyo ya kalleni yana murmushi, "why?? Saboda kin gaji da ganina? To babu inda zan koma, na gama karatuna ai" na juya na kalleshi sosai, "woah! Da gaske?" yayi murmushi more like a grinning, "nayi kankanta koh?" kaina na gyada mishi ina kara kare mishi kallo, dariya ya saka har yana dukan sitiyari. Yayi parking a kofar gidanmu, na dauki handbag dina na rataya a kafada nace thanks fa! Ya gyada kai, "Anytime!". Kallona ya tsaya yana yi, har na saka kafa ta daya waje na juyo ina kallonshi, "meye kake kallona?" murmushi yayi ya kalleni fuskarshi na nuna yana shirin yin serious magana ne, yace "Nafeesah! How about We come together with a plan and help ourselves??" na kalleshi cike da mamaki, "mu taimaki juna? Me kake nufi??" ya daga kafada kamar maganar da zai yi ba mai amfani bace, "you see, there's this girl that I like....." yayi shiru yana kallona, ban ji mamaki ba haka babu shock din da naji saboda maganar shi, to ma akan me zan ji mamaki? Hankalina na mayar kan shi gabadaya ina sauraron shi, ya cigaba "she likes me too, sai dai bata son muyi aure nan kusa. Tana karatu a Turkish ne a Abuja and sai nan da shekara biyu zata gama, ni kuma na kosa... U know....!!" ya daga min gira ni kuma na Harare shi, ya kauda kai. Gyaran murya nayi a hankali bayan na gama digesting maganganun shi, nace "to daka gaya min mai kake tunanin zan yi ne??" ya juyo yana fuskanta ta sosai, "I want us to just play a game ta yadda zamu samu wadanda muke so Cikin sauki." nima na kara gyara zamana, "so??" yace "we will pretend to be lovers infront of them, I mean idan muka yi haka kishin mu zai sa su dawo kan hanya daga kaucewar da suka yi, zamu fara da Muneer ne ko menene? Tunda Ikhram 'Cara Mia' sai nan da two months zata zo gida" na hade fuska sosai, take naji raina ya wani baci, a xafafe na harare shi nace "idan har saboda Muneer kake zaton I'll be your partner in this game then you are wrong Harith, Muneer has become 'a past' ya daina existing a duniyata!" ya sadda kanshi kasa embarrassingly, nace "But we can play it with someone, not Muneer dai" ya dago yana kallona fuskarshi dauke da murmushi, "Really Nafeesah? Oh you're really going to save my life, thank you! But waye wanda zamu bugawa wasan?" nayi rolling idanuna, "just..... By the way meye ma'anar Cara Mia din da kace?" yayi murmushi sosai, "it means My Darling in Russia" na tabe baki nace "wani fi'ili!! Ni kam bari in shiga gida toh!" muka bude motar a tare muka fita yana cewa bari ya shiga ya gaida Mommy.


A hankali rayuwa tana tafiya tana juyawa, cikin Ikon Allah minti yake shudewa ya zama awowi, awowi su koma raneku, raneku su koma satika kamar yanda satika suke juyewa su koma Watanni. Kimanin watanni biyu suka zo suka shude, ni da Harith mun yi developing wani irin shakuwa a tsakaninmu, da yawan mutane suna cewa soyayya ce a tsakaninmu ciki har da su Mommy da Ramlah, mu kadai dai muka san menene Ainihin Akalar mu da juna. 


      A matukar gajiye muka shiga gidan ni da Daddy a safiyar ranar Sunday kenan muna ajiye numfashi daya bayan daya, Gym muka je wanda yake a cikin unguwar mu kamar yadda muke yi a cikin weekends. Muna shiga falon kicin na wuce na dauko mana ruwa mara sanyi na mikawa Daddy daya, nima na fara shan dayan. Sai da muka dan huta kafin muka wuce dakinmu, ruwa na watsa a jikina na saka kaya kawai na fita falo. Su Mommy har sun fara breakfast don haka nayi joining dinsu, a nutse muke cin abincin, ina jin Mommy tana gayawa Daddy bikin diyar wata Kawarta da za a fara cikin satin, tunda suka fara maganar na sha jinin jikina, a gaggauce na fara tura abincin ina so in tashi in bar musu wajen. Kamar daga sama naji Mommy ta jefo min tambayar da nake gudun tayi, "Ummiey Ke kam yaushe zaki gabatar da naki Mijin ne?" sau biyu kenan tana min maganar turo da wanda muke soyayya wanda nasan Harith take nufi, na turo baki tare da kara cusa fried plantain a cikin bakina, Mommy ta kalli Daddy tace "Habibty kana jin mu fa!" Daddy yayi dariya yace "ina jin ku, kina bukatar bakina ne?" Mommy cike da jin haushi tace "Allah Habibty hakan bai dace ba fa! Yarinya kamar Nafeesah saboda Allah ace har yanzu tana gabanmu babu zancen aure, ina mata zancen ta fitar da miji kuma wai ka wani dinga wani tambaya na ko bakin ka nake bukatar ji?? Anya Habibty kana ma so Nafeesah tayi aure ma kuwa?" Daddy ya kalleta a hankali, duk da cewa maganar Mommy ta taba ranshi amma bai nuna hakan ba, he was very calm. Yace "kema kin san ba abunda nake nufi ba kenan Habibty, naga shi auren nan nufin Allah ne. Duk iya kokarinmu da tursasawar mu a gare ta idan Allah bai nufa ba babu yadda zamu yi. Nima ina son in ga auren Uwata saboda nasan Martaba da Mutunci 'Ya Mace suna gidan auren ta ba gidan Iyayen ta ba sai dai kin san bana so in tursasawa Uwata ko kadan. Kema din you are just desperate ne, amma duka-duka nawa Nafeesahr take? She's just Twenty Two Habibty!!" Mommy ta dafe kanta, "Ya Allah meke damun ku ne Kun kasa gane abinda nake nufi?" Daddy ya dafa hannunta cikin sanyin murya yace "mun fahimta Habibty, sai dai muma ki fahimce mu mana. Na fada miki Auren nan...." tayi saurin cewa "naji, naji Habibty ba sai ka maimaita ba!" yayi murmushi, "ki dinga mata addu'ah kawai Habibty, amma tursasawar ki ba shine zai sa ko ya hana ba, only your prayers will" ta gyada kai gami da yin sighing cikin saddakarwa, "To Allah ya zaba mafi Alkhairi!" yace ameeen ko Ke fa Habibty? Na saki ajiyar zuciya a sace, muka ci gaba da cin abincin mu. Can kuma Mommy ta sake dagowa ta kalli sashin da nake, "amma meke tsakaninku ke da Harith ne?" na kalleta, "Mommy, sau dubu nawa kike so in gaya miki babu komi?" Mommy tace "to ku ne na rasa gane inda kuka sa gaba" ni dai na samu na lallaba na bar musu teburin kafin wata maganar ta sake bullowa. Wayata na cire a jikin Caji na shiga cikin whatsapp, dp din Abbu na daga, ya canza shi daga wani hoton shi daya dauka cikin suits bakake ya maida shi zuwa wanda suka dauka shi da 'ya'yan shi kamar a wani restaurant ne ma, na kura musu idanu ina kallo ina murmushi, precious memories dinmu dasu suka dabaibaye ni, take naji wasu irin kewar su ta cika min ciki, har na latso lambar shi zan buga sai kuma na fasa, na sake latsawa na fasa, a tunanina idan Abbu shi yana namiji ya iya kauda kanshi daga gareni why not ni mace? Tun ranar da muka yi waya dashi bamu sake wata wayar ba sai kimanin sati biyu da suka wuce, shima tambayana yayi wai ko ina da muradin zuwa BUK inyi D.E ni kuma nace mishi A'ah, daga ranar bamu sake waya ba sai dai muna exchanging din text messages dashi. A hankali nayi tsaki tare da ajiye wayar. Littafan makarantana na dauko na fara karatu ko na samu in daina tunanin Abbu. Gabadaya lamarin shi ya fara daure min rai, idan ya kira ni a waya ko ya min text, kulawar dake cikinsu sai su sa inyi zaton so ne yasa hakan, amma yanayin yadda mu'amalar mu take ko kadan bata yi mun kama da wani abu mai kama da so ba. Yatsun hannuna na nutsa a cikin gashina ina jan tsaki ganin har lokacin dai tunanin Abbu ne a cikin raina. Tashi nayi tsam na fara canza tsarin dakina gabadaya bayan na cika dakin da sautin music har sai da Mommy ta leko ta min magana sannan na rage. 


     Ranar Laraba a gajiye muka baro makaranta saboda Defense din IT da muka yi, da kyar na iya kai kaina bakin gate saboda gajiya inda nayi shatar tricycle zuwa gida, Harith baya Kaduna kwana biyu kenan, yaje New York wajen hado takardun shi saboda zai fara aiki. Na tura kofar gate din gidan na shiga, yamma tayi likis lokacin. Malam Idi maigadin gidanmu yana zaune a kan dan benci yana sauraron radio, na gaida shi ya amsa da fara'ar shi gami da min sannu da zuwa kafin na wuce falo. Ina shiga sallamar dana fara yi ta kakare a makogorona sakamakon Halittar da nayi ido hudu da ita.......... 






             [truncated by WhatsApp]


*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

       

             *©°•Jeedderh Lawals•°*





                       *30*



       "Hafsy!!" na furta a hankali, surprisingly, shockingly. Yarinyar ta taso da gudunta ta nufo ni, da sauri na kai gwiwoyina kasa na tare ta muka rungume juna cikin farinciki muna dariya. Sai da muka nutsa na dago fuskarta daga jikina na kalleta da mamaki, "ya aka yi haka Hafsy? Waya kawo ki?" tace "Abbu ne!!" na zaro ido sosai, falon na karade da kallo babu kowa sai Mommy dake kallon TV abinta, a hankali kamar mai rada nace "Abbun yana ina?" tace "ya tafi wajen meeting, dama meeting zai zo anan shine nace sai ya kawo ni wajen ki" na gyada kai a hankali ina kokarin boye embarrassment din daya lullube ni, I am still a stupid again to think that musamman Abbu ya kawo Hafsy wajena ko shima yazo gani na ne, ko ni a su wa?? Na tashi na kama hannunta nace "taho muje dakina koh?" ta daga min Kai tana watso min jerarrun fararen hakoranta, na wa Mommy sannu da gida ta amsa tana jefo min wani kallo, ban kula da ita ba dai naja hannun Hafsy sai dakina. A can fa hirar yaushe gamo ta barke, naga ta kara girma Masha Allah kamar ba Ita ba.... Tace hutun makaranta suka samu jiya, su Qaseem suna gidan Anty Amernah ita kuma da Abbu yace zai zo Kaduna ta saka rigima sai daya taho da ita. Naja kumatun ta ina dariya nace Kin kyauta. Sai dana canza kayan jikina, muka fita muka ci abinci muka dawo daki na kunna mana cartoon muna kallo ni da ita, ga popcorn a gefenmu da lemu muna sha abinmu. Da yamma na dauke ta muka fita cikin gari, mun sha yawace yawacen mu har muka gaji, sai da aka kira sallar Magrib sannan muka dawo gida. Bayan mun gama dinner muka koma dakinmu, na bude jakar kayanta na fitar mata da kayan barci tasa muka kwanta. 


Washegari har cikin makarantar mu na shiga da ita, bani da lectures kawai yawo muka shiga. Daga karshe dai muka dire a gidan Anty Uwani. Bayan La'asar muna zaune a falo ni da su AbdulMaleek, The Space Between Us muke kallo a tashar MBC, Sultan Babban dan Anty Uwani ya kalleni cikin tsokana, "wai don Allah meye matsalar ki da wannan film din? Last time da kika zo gidan nan ma fa sai da kika kalleshi" nace "kawai film din ya burge ni ne" ya tabe baki, "a haka kuma idan aka cewa mutum yana acting like a child sai yace ba haka ba, Kun zauna nasara suna raina muku hankali Kun hau kai Kun zauna" filon kujera na dauka na jefa mishi ya cafe yana dariya. Daidai lokacin wayata tayi ringing, da sauri na daga ganin sunan Mom, "Ke kiyi sauri ku dawo Baban Hafsat yazo daukar ta!" wani irin faduwar gaba ta ziyarce ni kafin inji wani irin sanyi ya dabaibaye min jiki, jikina har rawa yake yi lokacin dana tashi ina lalubar gyalena da jakata, duk suka bini da kallo mai dauke da alamun tambaya. Na cewa Hafsy ta tashi mu tafi Abbu ne yazo, yarinyar ta tashi tana gunaguni da turo baki, ban ko bi ta kanta ba. Abinda na damu dashi a lokacin kawai shine in ganni a gaban Abbu, in dora idanuna akan fuskar Abbu. Anty Uwani ta fito daga kitchen, cikin mamaki take kallonmu, "ku kuma sai ina haka? Ba dai tafiya ba koh?" nace "Mommy ce ta kira ni yanzu tace muje Abbun Hafsat yazo tafiya da ita" ta kuma kicin ta dawo dauke da Leda wadda aka saka plastic roba a ciki wadda nasan dambun nama ne a ciki sana'ar ta kenan, bakery gareta wanda ake sarrafa fulawa ta hanyoyi daban-daban, suna kuma yin dambun nama a can. Ta mikawa Hafsy ledar tace "ga wannan sai kici a hanya koh?" Hafsy ta amsa tare da mata godiya, su Sultan suka raka mu har waje. Mun bata mintuna goma kyawawa bamu samu abun hawa ba gashi an aiki direban gidansu, Sultan yace "Kema ku jira direba ya dawo mana, sai ya kaiku. Nasan ba zai jima ba yanzu zai dawo" na girgiza kaina, a yadda nake jina dinnan a kagare, gani nake idan da halin inyi fuffuke da wallahi sai nayi, jiran Direban nan daidai yake da buguwar zuciyata ta tsage, nasan tsakanin doki da kaguwa ma ba zasu bar ni. Naja hannun Hafsy muka fara tattaki, Allah ya taimake mu kafin muyi nisa muka samu mai Adaidaita Sahu muka shiga. Bamu muka isa gida ba kuwa sai karfe Shida saura, a farfajiyar gidan Motar Abbu ce a fake a cikin gareji inda ake ajiye Motocin gidanmu. Zuciyata ta fara wani irin tsallen murna, duk yadda naso in boye farin cikina abun yaci tura. Sai dai muna shiga falo murnata ta koma ciki ganin falon wayam babu kowa, na dan hade fuska. Kamshin abinci na jiyo yana tashi nasan Mommy ce take girki, na shiga kicin din na sameta tana zuba abinci a cikin kuloli tana gani na tace "yauwa, zo ki dauki wannan ki kai sitting room daddynki yana can shi da Baban Hafsat" ban san lokacin dana saki ajiyar zuciya ba a sace, ashe yana sitting room ni ai nayi zaton ya gaji da jiranmu ne ya tafi. Kafin in shiga kicin din babu irin tunanin da ban yi ba a raina, kila ya gaji ya tafi,  kila ma bai zo ba gabadaya, kila motar shi ce ta lalace ya ajiye tashi a gidanmu ya dauki ta Daddy ya tafi, tunanika dai barkatai. Mommy ta kalleni ganin yadda nake grinning ear to ear, tace "lafiya?" da sauri na gyara fuskata nace "babu komi" ta min nuni da Tray din data shirya flasks da jugs na ruwa da lemu akai, na cicciba na fita. Sitting room din yana can a karshen falon, kofar shi ta waje ake shiga ta bayan gidan inda ake hango dan karamin garden din gidanmu, amma akwai karamar kofa a falon gidan wadda muke shiga ta ciki.


Na tsaya a kofar dakin ina kokarin daidaita nutsuwata, a lokacin babu abinda nake da burin yi irin in zubar da kayan hannuna in fada dakin ina tsalle da ihun murna in fada jikin Abbu, if that will not be possible kuma may be I should just shout? So that duniya da mutanen cikinta su san cewa ina cikin farinciki?? Ina jiyo sautin dariyar su dake tashi daga ciki, sautin dariyar shi kadai ma ta saka ni shivering ina ga kallon wadannan sparking brown oily eyes din nashi?? Na cije baki tare da yin knocking a bakin kofar, na tura na shiga a hankali kaina a kasa. Su biyun zaune suke a kan two seats wanda yake Fuskantar kofar shigowa, ina jin kaifafan idanun mutane biyu a kaina, hakan ya dan haddasa min hardewar kafafu. Na dora kayan akan table din dake tsakiyar dakin, na kuma zube anan kusa da teburin, "Abbu ina yini?" na furta a hankali kamar wadda take tsoron yin magana, cikin muryar nan tashi cike da ginshira ya amsa da "lafiya lau Nafeesah er Daddyn ta, kina lafiya?" Daddy ya mishi rada a kunne ban dai san me yace ba na dai ji sun kwashe da dariya a lokaci guda, na kara yin kasa da kaina ba tare dana amsa tambayar Abbun ba. Daddy yace "matso nan Uwata ki zuba mishi abincin, yanzu zai wuce" sai lokacin na dan daga kaina na kalleshi, ina dagowa muka hada ido dashi, nayi sauri na janye nawa idanun. Ban san ya aka yi ba kuma sai sake tsintar idanunshi a kaina nayi ina ga zuciyata taki aminta da hakan ne shi yasa na sake kallonshi ba tare dana shiryawa hakan ba, wannan kallon murmushi yake yi, yace ba tare daya dauke idanunshi daga kaina ba, "Ni fa ba yunwa nake ji ba, zan ci abinci idan muka isa gida" Daddy bai kula shi ba yace "zuba mishi abinci Uwata" na zaro plate na bude flask din na fara zuba Jollof din spaghetti sai da yawu na ya guda saboda yadda kamshinta yake tashi, na tsiyaya kunun aya mai sanyi a cikin cup na dora fork akan plate din na ja teburin zuwa gabanshi, kamshin turaren Hugo boss ya doki hancina lokacin dana matsa gab dashi, na dan lumshe idanu lokacin dana bude hanci na shaki kamshin ina jin wani irin shauki. Ina ajiyewa na kalli Daddy da niyar in tambaye shi ko in zuba mishi ne shima, yace "ni ba yanzu zan ci ba Uwata je ki kawai" na dan yi murmushi na mike na bar musu dakin. Hafsy na zaune akan kujera tana cin nata abincin Mommy kuma tana dakinta, na wuce dakina na shirya kayan Hafsy a cikin Jakarta. Na ciro wasu takalma dana siyo dama nace Hafsy zan ba shi, naje siyan takalmi ne irin shi ya burge ni kuma sosai sai dai babu size dina don haka na siya daidai size din Hafsy duk da ban san ranar da zan bata shi ba. Na kara duba wardrobe dina babu abinda na gani wanda zan bata sai kayan kwalliya kawai na kara mata, na dauki jakar na fita falo. Ina zama Daddy ya shigo falon yace Hafsy ta fita Abbu yana jiranta, tayi raurau da idanunta alamun bata so tafiya ba har ta bani dariya. Na kama hannunta na tasheta tsaye, Mommy ta fito daga dakinta hannunta dauke da leda ta mika mata, Daddy kuma ya ciro kudi daga aljihunshi ya bata. Na dauki jakar ta muka fita, Abbu har ya fiddo motar daga cikin gareji. Na budewa Hafsy passengers seat ta shiga ta zauna, na bude gidan baya na ajiye mata jakarta. Na kalli Abbu da shima yake kallona, cike da damuwa nace "Abbu ba zaku yi hakuri da tafiyar nan ba zuwa gobe kaga fa dare yayi" ya girgiza kai, "kar ki damu, ai In shaa Allah yanzu zamu isa, nan da Kano ai babu nisa" na rausayar da Kai gefe, "shi kenan since you insist, Allah ya kaiku lafiya" yace "Ameen" ya dauko wani kwali anyi wrapping dinshi da gift ribbon ya miko min, babu musu ko tambayar dalili nasa hannu na amsa, "nagode Allah ya saka da alkhairi" na furta a nutse, yayi murmushi "sai gani na biyu koh Nafee??" na kalleshi ina so in tambayeshi gani na biyu kuma as in how? Sai dai irin murmushin dake kan fuskarshi a lokacin ya daskarar dani na kasa daga bakina, ya tashi motar yana kara jifana da murmushi a hankali yaja suka fita, da kyar na samu kuzarin daga musu hannu ina waving dinsu har suka fita daga gate din gidanmu. Na juya a hankali na koma cikin gida, baby kowa a falon nasan suna daki zasu daura alwala saboda naji ana kiran sallar magrib. Nima na shiga dakina na ajiye abinda Ke hannuna akan gado naje na dauro alwala. 


         **********


         Na kwanta rub da ciki akan gadona ina jujjuya wayata a hannu kamar ina jiran wani abu, koda yake jiran kira ko text din Abbu nake yi. Gabadaya raina ba a kwance yake ba da tafiyar nan ta dare da suka yi, gashi tun karfe shida da rabi har karfe tara babu alamun kiran shi bayan nasan duka-duka tafiyar bata fi ta awa biyu ba. Kamar yasan ina jiranshi, text din shi ya shigo wayata, "mun iso Kano lafiya lau, Pretty tana gaida ki" nayi saurin typing "Masha Allah! Sannunku da zuwa" na tura mishi. Sai a lokacin naji kuzari ya shige ni, na tashi zaune na bude kwarin daya bani. Tarkacen chocolates ne da cookies a ciki, daga kasan su na ciro wani frame, hannun mace da namiji ne sarke dana juna a jiki, anyi kananun rubutu da wani irin yare wanda ban fahimce shi ba, daga kasan hannun nasu dai anyi rubutu in bolds kuma in capital letter....... *"TOI ET MOI POUR TOUJOURS! (I Miss You in French)"* Na danyi tsaki kadan, ban san me yasa Abbu yake son rubuta min abu da wani yare na aljanu ba, saboda Allah how in hell would I be able to understand what is written there?? Na kara jan tsaki naje na rataye frame din a jikin bango. 






                         *♡Jeedderh♡*


No comments