Furar Danko Book 2 Page 15

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣5️⃣




......Ko kaɗan Lulu bata nuna damuwa da tafiyar ta Dada ba duk da kuwa a ƙasan zuciyarta cinkushe yake matuƙa, amma plan ɗinsu ita da Ummita ya sakata dakewa abinta ta nuna komai ba komai har Dada ta wuce. Washe gari shima Tajuddeen mahaifin nasa ya janye ra'ayinsa ta hanyar tura sa Nigeria da saƙo. Ko kaɗan Tajuddeen bai kawo komai a ransa ba ganin shima Alh. Sulaiman ɗin yayi shiri wai zai wuce ƙasar Brazil ne yin wani business, sai dai ɗan nasa na wucewa yayo sau da baya. Sabon gurin daya shirya za'a kai masa su Lulu acan wani ƙauye ko yanki za'a kirashi ma ne oho ya wuce. Wajene tsibiri ne, dan a tsakkiyar wani irin makeken ruwa mara iyakar kallo tsibirin yake. Gidajene kawai na masu zuwa hutawa a wajen da yawon buɗe ido, sai jiragen ruwa ne kawai ke iya kaika cikin tsibirin. Wajen kam a kwai daɗin zama musamman ga wanda suka je hutawa, zaka tabbatar da hakanne ne idan kaga yanda mutane ke nishaɗi musamman ma masoya da masu kuɗi......


    Kamar kullum yau ma bata fito ba har sai da Ummita ta kamma kimtsa gidan, yay tsaf abinsa sai tashin ƙamshi da ɗumi mai ratsa ɓargon jiki daya gauraye ko'ina. Wando da riga ne a jikinta marasa nauyi, dan haka matashi cikinta ya samu damar fitowa ɗas da shi. Yau gaba ɗaya kasala takeji, dan da ƙyar ta iya fitowa dan yunwa data addaba mata ya sata fitowa ta samu abinda zata ɗan ci. Kai tsaye kitchen ta nufa inda Ummita keta ɓuruntun dama mata kununta, koda tai sallama kafin ma Ummita ta kai ƙarshen amsawa ita harta isa ga freight, ruwa ta ciro mara sanyi ta sha, tana ajiye bottle ɗin da sauran wanda ya rage ta nufi Ummita. Fuskarta da murmushi take faɗin, “Har yanzu ƙarnin kifin nan da Dada tasa kika dafa mata a gidan nan ya ƙi fita wlhy Ummita”.

         Da mamaki Ummita ta ce, “Kai aunty dan dai baki so ne kawai, amma wlhy ni banjin komai sai ƙamshin fresheners a gidan nan.”

    Cikin ɗan yamutsa fuska da tsaki ta ce, “Wlhy Ummita yanzu ne dai bana so, amma da ai kafin na ci miki nama naci kifi, sai dai yanzu na rasa miya haɗani da shi haka ko ƙamshinsa bana so”. Da dariya Ummita ta ce, “Aikin Unborn ne ai Aunty”. Shiru Lulu tai tana kallonta kamar mai nazari kosan tuna abu, abinda ke ƙoƙarin tuna kam nasa ne a zuciyarta ya zo mata. Tabbas Aliyu bama yancin kifi kwata-kwata idan bata manta ba. A take ta haɗe fuska kamar a ɗan ƙufule ta ce, “Ni shikenan saboda wannan cikin duk abinda baya ci nima na daina ci koda ina sonshi, sannan abinda yake so dole sai na so shi kamar abin asiri?”.

       “Wakenan Aunty?”.

  Cewar Ummita cikin nuna mamakin furucin uwar ɗakin nata. Sai dai maimakon bata amsa sai taga ta juya tama fice a falon tana ɗan dafe kai. Bata kawo komai a ran nata ba game da dafe kan ta cigaba da zuba mata kunun gyaɗar a flaks ɗin da ake zubawa. Ta kammala idonta ya sauka akan sauran ruwan da Lulu tasha ta ajiye, ta san da wahala ta sake shansa. Dan haka ta ɗauka ta shanye ta jefa bottle ɗin a shara sannan ta ɗauki flaks ɗin da ƙaramin kofi tabi bayan Lulu. Ɗan turus tai na mamakin ganinta baje a kujera tana barci kamar ba yanzu ta baro ta a kitchen ba. Sai tai dariya da jin tausayin ta. Ta ajiye flaks ɗin itama da nufin komawa kitchen ta gyara kayan datai amfani da su a aikin itama kanta ya sara, da sauri ta dafeshi tana mai ambatar sunan ALLAH, jin hajijiya na neman yadda ta a ƙasa da bin bango ta fito falon itama, sai dai kafin ma ta kai ga kujera ta zube ƙasa, daga haka bata sake sanin ina hankalinta yake ba itama....

       Duk abinda ke faruwa Alh. Sulaiman na kallo ta camera da ya saka musu kamar yanda Ummita ta zarga dama, wata shegiyar dariyar basanci ya saki sai kuma ya gimtse fuska duk a lokaci guda. Wayarsa ya jawo a gefensa tare da shaƙar cocaine ya wani girgiza kan nasa da wani irin style na ƙwararrun ƴan cocaine sannan ya kai wayar kunnensa. Cike da izza ya furta “Nan da awa ɗaya ku tabbatar su da duk tarkacensu suna a gabana” da ga haka ya yanke kiran batare da jiran an bashi amsa ba da ga can...


      Matuƙa hankalin Lulu da Ummita ya tashi a lokacin da suka farka da ga nannauyan barcin da ya samesu suka ga kansu a inda ba'a nan suka kwanta ba. Cikin matsanancin firgici suke kallon juna kafin su miƙe duk a zabure su fara dube-duben inda suke ɗin. Falo ne madaidaici sai dai akwai komai a cikinsa sai bedrooms guda ɗaya mai ɗauke da gado biyu, sai kitchen. Ko ina a kulle yake ta hanyoyin waje sai dai suna iya hango makeken ruwan daya zagaye ko'ina da ina ta cikin gilashi. Basu iya ganin mutanen da ke kai kawo balle iya jiyo hayaniya saboda gilashin manne da ginin bullet proof ne. Yunwar da Lulu keji dan a yanzu sam bata da jimirinta ya sata fara jin yuuu-yuuu kamar jiri zai yadda ta. Da sauri takai zaune cikin rawar murya tace, “Ummita yunwa”. Hankalin Ummita ya tashi matuƙa dan haka ta miƙe cikin rawar jiki ta fara dube-duben ko zata ga abinci, cikin aminci ALLAH ta ganshi an ajiye a gefe kan ƙaramin dining table mai kujera biyu. Ɗakko mata tayi, jikin Lulu har rawa yake wajen karɓar abincin ta fara turawa, duk da baya mata daɗi haka takeci ko zata samu nutsuwa. Tan kammalawa ta fara sheƙa amai kamar zata fidda har hanjin cikinta. Ta jigatu matuƙa dan Ummita har da kukan ta, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta canja kaya ta hau gado ta kwanta ta dunƙule a waje ɗaya cikin rawar sanyi, kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Kuka sosai Ummita ta zauna ta dingayi, babban tashin hankalinta shine basu san wanene ya kawosu nan ba kuma. Duk da suna zargin Alh. Sulaiman sai dai zukatansu sun kasa zama waje guda. Sosai Lulu bata da lafiya gaba ɗaya a wannan daren, gasu a rufe balle Ummita ta fita ta nemo musu taimako. Sai da barcin wahala ya ɗauke Lulun ne Ummita ta samu damar tashi zuwa kitchen ta shiga bincike, ta ɗan samu nutsuwa ganin kayan abinci harda kayan tea, sai dai babu gyaɗa, ga shi a yanzu komai Lulu baci take ba da daɗin rai sai wannan kunun....


       Kwanakin Lulu kusan uku tana fama da zazzaɓi kafin ALLAH ya bata lafiya ta dawo dai-dai, duk ta rame sai wani uban haske data ƙara. Kamar ance su dawo nan ciki ya fara girma, ga shi bata samun kunun gyaɗar da take so sai ɗan tea da take sha kaɗan-kaɗan, abincin ma Ummita kan zauna taita lallaɓata har sai taci ko yaya ne, duk da data gama take yin amansa. Wani bai taɓa zuwa musu ba, sai a randa suke cika sati guda ne suka wayi gari suka ga an ajiye musu kayayyakin abinci dana buƙata a falo, ciki harda gyaɗa abin mamaki. Kallon-kallo kawai sukeyi, a ransu sunajin tabbacin duk abinda sukeyi kenan ana sane da su. Murmushi Lulu ta saki a karo na farko, dan dama kawo su nan ya tabbatar mata da hasashenta akan kawun nata kenan. Basu da hurumin cewa bazasuci abinda aka kawo musun ba, sai dai Ummita kan zauna ta tofeshi da addu'oi sannan. Wannan abin da take ɗin ne ya sake sakama Lulu nutsuwa da ita. A hankali shaƙuwa ta cigaba da shiga tsakanin Ummita da Lulu, har takai yanzu Ummita na ɗorama Lulu karatun Alkur'ani da na wasu littattafan addini da take da su kamar yanda Lulun ta buƙata. Sannan cikin dare Ummita kan tashi tai nafilfilinta, tun Lulu najin damuwa da takurar hanata barci da Ummita keyi kasancewar bata saba da zama mutum biyu a ɗaki ɗaya ba har itama ta fara tashi tana sallar. Hakan ya saka Ummita a farin ciki sosai, haka itama Lulun wannan yanayin na sata jin farin ciki da jinta kamar wata sabuwar hallita, dan wata sabuwar nutduwa ce ta sake zo mata. Kullum sai Ummita ta mata addu'a ta bata a ruwa ta sha, sannan takan gaya mata wasu akan ta dingayi tana shafe cikinta da shi. A haka suka cika wata ɗaya a wannan juyayyen waje da basu san inane ba, sai dai hakan bai hana Lulu cigaba da tattara bayanai akan kawun nata ba, ranar da suka cika wata guda sai ga baƙonsu na farko daya fara ziyararsu. Wato Nurse Usman, babu wanda ya ganesa a cikin su Lulu, shi kuma bai nuna musu sani ba ya ce kawai yazo duba lafiyarta. Da taƙi sai yay kiran Alh. Sulaiman. Wannan ce ranar ta farko da su Lulu suka fahimci wanda ya kawo su nan ɗin duk da ita dama Lulu ta gama bama zuciyarta shi ɗinne. Al'amarin ya sake dilmiya Lulu a kogin mamaki game da abinda kawun nata ke yi akanta, sai dai batace komai ba ba kuma ta hana Nurse Usman ɗin yin aikinsa ba duk da tana ɗar-ɗar tana son a na duba mata lafiyar jaririnta kuma, shot note da Usman ya ajiye mata ya sakata sakin ajiyar zuciya. Shima sai yay mata ɗan guntun murmushi. Ya dubata tare da bata magunguna bayan ya tabbatar mata da lafiyar cikin nata. Tai masa godiya ya tafi. Sunyi mamakin ganin bayan ya kammala sai da ya kira akazo aka buɗe masa ƙofar sannan ya fita, hakan na nufin akwai wani a waje da ke gadinsu kenan ma kamar acan inda suka baro. Ganin Ummita zata saka damuwa a ranta Lulu tai mata murmushin kwantar da hankali. Note ɗin Usman ta miƙa mata, sai ga Ummita na murmushi da sauke ajiyar zuwa. Lulu ta lumshe idanunta a hankali ta furta “Yanzu kin fahimci wasan namu ne ko? Karma ki tadama kanki hankali yanzu lokacin tattara bayanai ne, dan haka babu buƙatar cigaba da shiga damuwa kuma farin ciki kawai domin kama tsuntsu mai wayo”.

        Ƙaramar dariya Ummita tayi, yayinda a ƙasan zuciyarta tamaji ta fara tsoron Lulu, dan fa ta fahimci atsabibiyar kanta ce ashe.....


     Tun daga wannan ranar Lulu da Ummita suka sake sakin jikinsu tamkar basu da wata damuwa, ga ciki nata haɓaka da bunƙasa cikin ƙoshin lafiya. Ganin yanda suka sake jiki da walwala ya saka Alh. Sulaiman bada umarnin a ɗan dinga buɗe su, sai dai yana son duk inda suka saka ƙafa a tsibirin nan yana sani. Dan ya zagayesu da mutanensa kusan goma batare da sun sani ba. A cewarsa yanzu plan zai fara. Kamar yanda itama Lulu take ji a ranta yanzu wasan zai fara........✍️



       _🤣🤣Hahaha anayi muna cin gyaɗa mai gishiri🥱🥱🚴_




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments