Furar Danko Book 02 Page 26

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣6️⃣




.......Kamar yanda Daddy ya faɗi zasu tattauna da Smart tun a waya ya cika alkawari, dan washe gari tunda safe ya baro Abba da Uncle Yousuf ya sami Smart a gidan su Usman dan nan ya kawoshi. Sun gaisa cikin mutunta juna kafin su fara tattaunawa. A nutse Daddy ya fara ma Smart bayanin mafarin komai tsakaninsa da Sulaiman har zuwa yau da suke tare. Matuƙar girgiza Smart ya shiga, tare da jinjina ƙarfin halin Daddy da sake ganin kimarsa. Ya jure ɗaci da damuwa saboda kawai karya rama sharri da alkairi, saboda kare mutunci da lafiyar ahalinsa. Cikin zubda hawaye Daddy ya katse Smart da faɗin, “Abu ɗaya ne ke cimun zuciya a yanzu Aliyu shine cutar da matarka da nayi, kwarai da gaske na zalunci rayuwar Mawaddat dan rashin ilimin addini babbar naƙasu a rayuwar ɗan adam. Gara ace mutum bai san komai a limin boko ba dan wannan iya kar alfaharinka da shi shine duniya. Inajin kunyarta ta yanda a duk sanda na tunata nakanji hawaye na zubarmin tunda ba haka naima sauran ƴan uwanta ba. Wlhy alokacin idanuna ne suka rufe da iya tunanin kuɓutar da ita da ga sharrin Sulaiman ne kawai shiyyasa. Iya ƙoƙari Yousuf kuma yayi na ganin ta samu ilimin har malami ya nema mata a can Germany amma tsoron karda a haɗa baki da Malamin a cuta mata yasa na hana hakan. Ashe na manta UBANGIJI shine mai ikon tsarewa da killace bawa da ga sharrin masu makirci da ƙulle-ƙulle ba wai wayo ba. Domin nayi gudun gara na faɗa gidan zago. Dan ALLAH ka tayani bata haƙuri da neman gafararta, ka tayani gina mata sabuwar rayuwa, ka tayani horas da ita sababbin ɗabi'u, ka tayani ɗorata a hanyar tsira Aliyu kafin ɗan sauran lokacin da ya rage min ya ƙure mana ni da ita. Dan nasan da wahala na tsallake da ga tarkon Sulaiman saboda shu'umi ne na gaske. A yanzu haka ya ƙullaci mahaifinka akan maganar kotun nan, amma Alhamdullah babu abinda ya isa masa dan duk inda ya saka ƙafa na saka ƴan sandan farin kaya biye da shi, bama shi ba hatta ƙannenka dake gida dana ma'auri al'amarinsu na ƙarƙashin kulawar hukuma a duk sanda zasu bar gida. Kayi haƙuri kaima Aliyu na sakaka a rigimar da baku san mafarinta ba, shiyyasa raina fansa akan ganin wani abu bai cutar da ku ba a dalilina. Amma dan ALLAH ku yafe min duk laifina ne, da ace nayi nazari kafin na biyema Sulaiman tun farko maybe da duk bamu kai a irin wannan matakin ba.....”

          “Daddy jarabawace kawai, bawa kuma bai isa tsallake ƙaddararsa ba. Ba kamana laifin komai ba sai alkairi a rayuwa. Babu abinda zan iya cemaka sai godiya da cigaba da maka addu'a har ƙarshen numfashina. Ba laifinka bane Mutumin nan hatsabibin ne na gaske. Na fahimci hakan tun a haɗuwata da shi ta farko. Dan haka na zauna na karancesa yanda ya kamata, sai dai rashin sanin abinda ke a tsakaninku yasa ban taɓa wani yunƙuri ba. Amma tabbas na jima da lura da duk inda nake ana biye da ni, hakama ƙannena, na shiga tashin hankali saboda a tunanina Sulaiman ne, sai daga baya na fahimci ƴan sanda ne, sai dai babu irin bibiyar da ban musu ba sunƙi gayamin wanda ya sakasu, sai nai tunanin ma ko Uncle Yousuf ne ko Coach a lokacin, shiyyasa na zaɓi musu shiru a ganina wataran ai zan sani. Kamar yanda na faɗa maka ina son ka bar wannan case ɗin a hannuna yanzu, sannan ina son na bada shawara....”

       Cike da kulawa Daddy ya ce, “Ina jinka Aliyu, ka faɗi komi ke'a ranka kai tsaye tsakaninmu babu wani ɓoye-ɓoye”.

     Kai Smart ya jinjina tare da furzar da iska mai nauyi. “Wato Daddy irin su Sulaiman da hatsabibancinsu yaƙin sunƙuru yake buƙata a farkon fara wasa. Kamar yanda ka ɗauki masa salon shekarun da suka gabata na nuna baka san mi yake ciki ba wannan salon zamu cigaba a yanzu har zuwa wani mataki. Domin idan har akace za'ai masa fito-na-fito a shirye yake da wannan tun ba yanzu ba. Jirace yake da kai kace kule yace cass. Sannan mahaifinsa da kai hallacin shanye komai daminsa zai iya samun bugawar zuciya wlhy in har yaji kasuwancin da yake yi da kuma ketama autarsu mutunci da yayi. Ko kuma shi da kansa ya shirya hanyar halakasu idan yaga zaka cimma burin tona masa asiri. Kaga anyi gudun gara kenan an faɗa gidan zagon dai. Dan haka mu ajiye batun fito-na-fito ɗin nan mu lallaɓa Baba Garko ya sakar masa ɗansa, ka cigaba da nuna masa kana shakkar tasa, sauran yaƙin ka bar mana zamu ƙarasashi ni da Mawaddat da Uncle Yousuf in sha ALLAHU”.

      Idanu kawai Daddy ya zubama Smart, yama rasa abin faɗa akan wannan yaro. Lallai farar haihuwa tayi, dan shikam dole ya kira wannan yaro da farar haihuwa ga iyayensa. Smart ne da yaga kallon da Daddyn ke masa yay ƙasa da kansa yana murmushi kawai....



         __________★


   Yau kam Ammah da kanta ta wanke ɗan jikanta ta gyarashi ɗaras ɗas. Yayinda Mamy ta gyara Mawaddat ita kuma Ummita ta shirya abinci. Lulu da ke jin jikinta wani iri tunda garin ALLAH ya waye cikin damuwa take sanarma Ammah ta mata addu'a gabanta sai faɗuwa yake. Jawo hannunta Ammah tai ta zaunar kusa da ita cikin damuwa da kulawa ta fara mata addu'oi, a hankali Lulu ta dinga samun nutsuwa har ta ɗan sha tea ta kuma shayar da AA abincinsa. Sun kammala kenan Ummita na gyara mata gashinta su Smart suka iso niƙi-niƙi da kayan da ya siyo bisa jagorancin Usman. Da mamaki Lulu ke kallonsu su da kayan, Usman ya nuna Smart cikin ɗaga hannu yana ficewa acewarsa bari yay kiran Dr Lameer.

         Lulu da ke jin faɗuwar gabanta na dawowa tun shigowar Smart ɗin ɗakin cikin dauriya ta ce, “Good morning” a takaice. Bai amsa mata ba sai da ya ɗauki AA tare da kaiwa zaune cikin kujerar dake a gaban gadon ya ɗan ma yaron kiss a goshi da kumatunsa sannan ya dubeta idanu ƙasa-ƙasa. Kamar wanda baya son motsa lips ɗinsa ya furta, “Haka ake gaishe da miji? Kamata yay kizo da gudu ki rungumeni da bani ƙyaƙyƙyawar sumba ki ce good morning rabin raina” yay maganar cikin kwaikwayon muryarta. Harara ta zuba masa da saurin faɗin, “ALLAH ya kiyasheni. Miye wani rabin rai babu ko daɗin ji.....”

        “Ki rantse ni ba rabin ranki bane”.

    “Kana buƙatar ganin likita kam”.

Murmushi ya saki da ɗan lumshe idanunsa yana gyara AA da ƙyau. “To muje a hakan, idan tai wari maji ai. Ina fatan kun tashi lafiya ke da baban Ammah?”.

      Cikin ɗan marairaice fuska ta ce, “Wane lafiya bayan ya hanamu barci, ka masa faɗa gaskiya ni bana son damuwa. ALLAH nima sai da nai kuka duk ya ruɗamu ga Ammah tayi tafiya ta gaji ya sata tanata faman jijjigarsa”.

             Gaba ɗaya neman harmutsa masa lissafi take da salon nata. Ƙaramin gyaran murya yay saboda jin yawu na neman sarƙeshi. Hakan yasa Lulu zuba masa ido, sai yay saurin janye nasa da ke neman canja launi cike da basarwa ya ɗan lakace kumatun AA da faɗin, “My Grandpa miyasa ka hanamin Mata barci? To da ga yau karna sake ji kaji Sadaukina. Kuma ka bama Maah-maah haƙuri” Sai kuma ya ɗago ya dubi Lulu data zuba musu ido, a yanayin ɗan ɗage gira ya ce, “Koda yake ni ya kamata ma na bada haƙurin nan a madadinsa” ya ƙare maganar yana tasowa. Ƙoƙarin sauka tai a gadon tana faɗin, “Ni dai ban gayyaceku ba”.

      Cikin ɗan murmushi ya ce, “Oh oh har ma takai gudunmu akeyi. Haƙuri da kawai zamu baki”.

   “Na haƙura basai kunzo ba”.

“Please mana Baby luv ko ɗuminki ki bari muji mana”.

            Dama ta fahimci wayon nasa kenan, dan haka ta maƙe kafaɗa kamar wata ƴar baby da faɗin, “Naƙi ɗin. Kai koma kunya bakaji a gaban ɗanka sai kayi taɓara. Ka rage halin nan wlhy rashin jin magana zalla”.

       Komawa yay ya zauna yana dariya da faɗin, “Kema ai rashin jin ne ya kaiki ga samo AA Mawashi. Haka kawai kin lalatama Ammah yaro, sai kawai ta ganki da yaro a hannu kuma dai tasan a inda kika samo.....”

           “What!!”

      Ta faɗa da sauri cikin daburcewa kamar Ammah na gabanta. Aiko ya shiga yin dariya a hankali. “Ni dai ai kowa yasan ni babu ruwana salihin ALLAH. Ina zaman zamana kikace sai anyi yaƙin ƙasa da ƙasa. Tsabar zalama baki fito a filin dagar ba sai da ganimar yaƙi wannan yarinya sai a barki kawai amma dai gaskiy....”

        Fillon data ɗauka zata jefa masa ya hanashi ƙarasawa, cikin ɗaga hannaye sama da sauri alamar surrender ya ce, “Yi hakuri nayi shiru, ke kam akwai kawaici nine zalamammen ga shi ma AA ni yabiyo tabbacin haka”.

         Hararsa tai da ajiye filon ta koma ta zauna. Sai kuma cikin damuwa da marairaicewa ta ce, “Da gaske dan ALLAH su Ammah suna ganin bani da kunya ko? Wata goma da kwanaki dayin aure na haifi yaro, wlhy nima abin na damuna, sai nake ganin abin yayi kusa da yawa kamar wata mayyar miji”.

      Daƙyar Smart ya iya danne dariyarsa. Dan ya fahimci tsakaninta da ALLAH take tambayar. Cikin kaɗa kai ya ce, “Kai kai baza'a suce ba Madam. Sai dai ma a kiraki da jaruma mai matuƙar hazaƙar ɗaukar darasi a wajen malaminta. Ammah kam ai zata so nan da wasu watannin goma masu zuwa ki sake santalo mata wata baby girl ma again”.

             Sosai ta waro manyan idanunta kamar zatai kuka. “Hydar wane fatan tsiyane kuma wannan dan ALLAH mutum ko gama dawowa hayyacinsa baiyi ba kamar wata akuya. Kasan miye rainon ciki da haihuwa kuwa?. Wlhy akwai wahala, ni da ga ɗayan nan ma na gama gaskiya”.

        Tsam ya taso da ga inda yake zaune ya dawo kusa da ita. Cikin nuna damuwa ya ce, “Da gaske akwai wahala? Bani labari yaya kika kasance?”.

      Lumshe idanunta tai a hankali tana mai ƙara shaƙar ƙamshinsa mai masifar daɗi, duk da dama dai tun ɗazun take shaƙar, kusancin da suka samu yanzu ne ya ƙara ƙarfinsa sosai a cikin han nacinta. Hannunta ya ruƙo tare da murzashi a cikin nasa a hankali. Idanun ta buɗe tsigar jikinta na tashi. Ta kalli hannayen nasu ta ɗan sake lumshe idanun nata da sake buɗewa. Cikin ƙara ƙasa da muryarta batare da ta farga da canja salon harshen nata ba ta furta, “Ai ya wuce kuma, share kawai”.

        “Please ina son ji nidai”.

      Ya faɗa yana murza mata hannu a ɗan marairaice. Hannun taso janyewa dan yana sata a wani yanayi salon nasa, amma ya hana hakan, sai kawai ta saki ajiyar zuciya a hankali ta furta,........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments