Qamshi 33-35
*✨QAMSHI 33-35✨*
✍🏿Rashow
tunda na shigo sashin Diddy naga se aikin kaiwa da komowa takeyi fuskarta dauke da murmushi tana ganina ta taso ta kama hannu na ta zaunar dani a daya daga cikin kujerun falon itama ta zauna,da sauri ta mike kamar wacce ta tuna wani abun ta miqar dani tace.
"maza zo kiyi wanka lokaci yana qurewa."
qaramin bakina na turo cikin shagwaba Ina me son kwance hannu na daga hannun Diddy nace.
"ni Diddy nayi wanka a gidan Ammy na, kuma ma lokacin miye yake tafiya ko anguwa zamu Diddy?
nayi tambayar ina kallon Diddy wacce se sauke murmushi takeyi ta mele baki tace.
" kajimin son gantali, mutum bazaiyi wanka ba kenan har Seda inda zaije kenan wannan wata irin magana nane haka qamshi?to kidai dinga neman yafiyar Allah a duk inda kike.
juyawa nayi zan wuce kitchen din dayake falon amma Diddy tayi saurin sanya hannu ta riqo hannuna tace.
"tunda kinyi wanka acan gidan naku to zoki yi wankan matan Sudan tunda kinga yau juma'a kuma naga kinason qamshi shiyasa na miki wannan hadin wankar na musamman."
bin Diddy da ido nayi don gaba daya jikina babu karfi Jina nakeyi kamar wacce zazzabi yakeson kamawa duk jikina yayi sanyi, sosai qamshin turarukan wankan suka Kara saukar min da kasala hakan ya qaramin sanyin jiki, a hankali na Shirya ganin lokacin sallah da saura ne yasani hawa gadona naja bargo na lullube jikina har zuwa kaina lumshe idona nayi take barci me nauyi ya daukeni.Sam bakin Abby yaki rufuwa ji yakeyi kamar wannan ne auren Hatim na farko, duk wanda ya kalli Abby kuma zai dauka auren mashi aka daura don ganin irin farincikin dake bayyane akan fuskar shi,hannu ya bama Baba Alhaji sukayi musabuha tare da rungume juna.
Futowa Abby da Baba Alhaji sukayi haraban babban masallacin juma'ar suka shiga gaggaisawa da jama'ar da suka halacci wannan taron daurin aure wanda ya samu halartan manyan mutane duk da bawai wani Sanarwa akayiba sabida abun yazo akure.
Sosai Hatim yasha mamakin wannan abun da Abby yayi mishi sosai yake nanata kalmar auren da aka daura mishi da wata daban wacce bama ya Santa babe, amma sabida miskili neshi Sam bazaka Kane awani hali yake ciki ba, daga masallacin gurin walima suka wuce wanda aka hadashi na zallan maza wanda ya kayatar sosai.
Se bayan sallar Isha Hatim ya samu kanshi, a gajiye ya shigo cikin falon Ammy bai iske kowaba sabida duk suna sashin Jiddy wacce ta hada ma yaran duka gida biyun qaramar walima duk da ta kwabi duk da ta kwabi duka yaran akan Kar a Sanar min.
hawa sama Hatim yayi ya shige dakinshi ya rage kayan jikin shi ya shiga bathroom don ya sakar ma kanshi shower ko zaiji dadin jikin shi,koda ya fito tsayuwa yayi a gaban mirror ya dauki body lotion na shafawa tare da body spray dinshi mai qamshin dadi, closet dinshi ya shiga ya zabo kananun Kaya ya sanya a jikin shi, hannun rigan jikin shi yake gyarawa yaji Karan shigowar sako wayar shi, Seda ya gama shirin shi tsaf sannan ya dauki wayar ya nufi bakin gadon shi ya zauna tare da jingina bayanshi a jikin kan gadon, a hankali ya bude wayar tare da shiga kan sakon daya shigo wayar, sosai ya bude idon shi don ganin abunda aka rubuto mishi a sakon, sake karanta sakon yayi.
*karka manta nice nake dakai yau nayi maka special tanadi Ina dakina na cikin gidan ku Ina jiran ka*
wani irin yawu Hatim ya hadiye sannan ya runtse idon shi Kamar Wanda zaiyi barci amma ba barcin zaiyi ba.
Nikam tun lokacin da Baba Alhaji ya kirani dakin shi ya damkamin naira dubu dari a matsayin sadaki na wanda aka dauramin aure a yau banjira jin dawa aka daura auren ba na yake jiki na fadi a falon a sume,
Maa saratu ne ta yayyafa min ruwa na farka ta rikoni tana lallashina wanda ni Sam bani gane ma me take fada don gaba daya kunnuwa na sun daina jiyomin komai sai kalmar Baba Alhaji na cewa ga sadakin kinan yau na daura miki aure, wani irin Fashewa da kuka nayi inajin zuciya ta kamar zata Faso kirjina ta fito tsabar bugawan da takeyi sosai nake kuka wanda hakan ne ya haifarmin da zazzabi me zafi,ganin bazan iya nutsuwa na saurari nasihan dayake minba ne yasa Baba Alhaji yace ma Maa Saratu ta kaini gurin Diddy,kamani tayi ta mikar dani muka fita a falon, da sauri na karasa cikin falon mu na fada jikin Diddy na saki wani irin marayan kuka,Diddy bata hanani ba nayi kukana sosai sannan mama saratu ta kamoni tace.
"Khubra ya kamata kiyi shiru da kukan nan haka Kar kanki yayi ciwo.
kallon Diddy nayi da idona da sukayi jazur muryana yana rawa duk da ya dishe sabida kukan dana keyi nace.
"please Diddy ni bani son wannan auren da Baba Alhaji yayi min please ki gaya mishi ni Allah banson."
na karasa maganar da kuka zuciya ta tanamin zafi sosai. ganin bazan yi shiru bane yasa Diddy ta kalli Maa Saratu tace.
" Saratu ni Banga amfanin kawomin ita da kika yi ta sanyani a gaba da kuka ba kamar kanta farau aure to inzaki sake ki sake, Allah ya bama mutanen zamanin da hakuri da aka musu aure irin haka shin ba gamu ba araye babu abunda ya cinye mu, kema haka zakije naki dakin mijin ki zauna zaman bautar aure kedama kikaci sa'a anmiki auren gata zaki zauna a gidan ku, yo Ina nan Ina babban gida da zaki zauna ki tashi hankalin ki, Ammy kune baki sani ba koko su Thariq dinne baki sani ba?
dago kaina nayi idona shabe shabe da haawaye Ina Kallon ta da mamaki, kamar Diddy tasani tace.
"eyy haka nace Hatim da aka aura miki shidin ne baki saniba kokuma Jiddy ne suka zamo wasu baki a gareki daki sanyamu agaba da koke koke?
Wani irin wawan bugawa qirjina yayi najin sunan wanda Diddy ta kira da sunan mijina duk da duk zamana a gidan nan bamu taba haduwaba amma inajin sunan shi a bakin su Thariq.
Sosai mama Saratu ta shiryani cikin milk lace da ratsin gold na wani cotton lace me laushin gaske,duk da bawani kwalliya ne a fuskata ba amma nayi kyau farin mayafi ta yafa min Sannan ta kamo hannu na muka futo falo bamu iske Diddy a falon ba don hakane ma mama saratu ta futa dani muka nufi babban gida,a sashin Ammy muka sauka mun same ta zaune a falo tana kallon africa tv3 sallama mama saratu tayi muka shiga falon ganin mu da Ammy tayi ne yasa ta taso ta rungumeni tana cewa.
"oyoyo daughter."
Jina a jikin Ammy danayi take na saki sirrin kukana hawaye na yana sauka a gaban rigan Ammy, bubbuga bayana Ammy ta shiga yi har Seda kukan ya lafa ta dago da fuskana tace.
"me zan gani haka daughter? “
gurina ne bakison zuwa yau?
da sauri na girgiza mata Kai. kallona Ammy ta kuma yi tace.
" to inba hakaba gayamin wannan kukan na menene?
Sake fashewa da kuka nayi muryana yana rawa nace.
"Baba Alhaji ne Yamin aure kuma yace ma mama Saratu ta kaini gidan mijina....
kasa karasawa nayi sabida yanda nakeji kamar na mutu makwogorona jinshi nakeyi a shaqe.
ido Ammy tayi ma mama saratu akan ta tafi kawai ta bar mata Khubra,hakan akayi kuwa don cikin Sanda mama Saratu ta futa a falon Ammy ta kama hannun Khubra suka haura sama ta shigar da ita falon khubra dake Saman, bata ajiye khubra a falon ba har Seda takai ni bakin gadona ta zaunar dani itama ta zauna tare da riko hannu na tace.
"ya isa kukan haka yanzu ki tashi ki sauya wannan kayan kiyi kwanciyar ki, ki manta da duk wani magana dasu Diddy ta fada miki kiyi kamar kin dawo gurina ne.
*Rashow*

No comments