Tabarmar Kashi Book 2 page 69

 "HUGUMA*•TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 69


Washegari ta zame jikinta daga nashi ta fita a duvet din ta barshi vana bacci ta shiga kitchen.


Breakfast me kyau ta shirya musu gaba daya,harda wanda za'a kaiwa dr asibiti. Ta gama tsaf tana goge waien taji takunsa a hankali da qamshinsa me sanyin nan,ta waiwaya a nutse tana dubansa. Shima ita yake kalla da tattausan kallo ya garaso a hankali yana duban warmer's din data shirya.


Da idanu ya tambayeta, saita saki murmushi tana dora yatsantsa saman lips dinta alamun yayi shuru. Hannu yasa ya fincikota jikinsa,ya riqe qugunta da kyau suna yiwa juna kallon kallo


"Kin karya doka,kika kwantar dani ina bacci kika taso kina aiki, waye kika tambaya?" A nutse ta miga hannunta zuwa sumar dake kwance baqiqqirin qasan habarsa tana dan wasa da ita idanunta cikin nashi tana sakar masa wani kallo


"A yimin afuwa hottie......but hidimar iyaye ba'a sanya wajen yinta" garamin murmushi ya saka yana jin qaunarta cikin ransa, darajarta da kimarta suna sake qaruwa, sai ya sake matso da ita jikinsa sosai yayi kissing nata a tausashe


"Zanyi wanka sai mu fita dasu jibril na miga masa" langabe masa kai tayi a shagwabe


"'Nifa?, zanje fa" hannu yasa ya lakace mata hanci


"Duk sanda kike min magana kamar haka,sai na dinga ji kamar na tsayar da lokaci ya daina tafiya nayita kallonki kamar haka" hannunta ta sanya ta zagaye shi duk da bata iya ratsashi ba,rungumeshi tayi tana dora kanta saman girjinsa


"Am all yours thank you for loving me you have

Brightened up my life with your beautiful spirit and caring heart" kansa ya kwantar tsakiyar lallausan gashinta dake hargitse yana lumshe idanu, har cikin zuciyarsa yana tasirin saukar kalamanta,a hankali yace


"I only regret one thing in our marriage...

.. Zuciyarta tadan buga kadan,sai ta zame kanta a hankali ta dagashi tana kallonsa da fararen idanunta da suka bayyana fargaba


Wata lallausar dariya ya saki, ya sunkuceta gaba daya ya azata saman kitchen cabinet, hannayensa ya zura ta gasan rigar baccinta,ya soma tafiya dasu a hankali cikin wani salo na tafiyat tsutsa, bai tsaya dasu ko ina ba sai da yakai tsakiyar bayan nata, ya sake matsowa da fuskarsa sosai, hucin numfashinsa yana sauka saman fuskarta tata


"One thing i regret in our marriage... that i haven't met

¿ you sooner" murmushi ne ya qwace mata, sai ta karyar da kanta gefe,tsoro da fargabar da ya dasa mata a lafazinsa na farko ya zagwanye. Binta yayi da kallo yana jin gaba daya tana tayar da tsigar jikinsa,wani mahaukacin kyau murmushi yakeyi mata,inda da hali tabbas da ya hana mata yin murmushi a ko ina


"Kinsan me?" Ya fada a hankali yana matso da bakinsa saitin kunnuwanta,abinda ya sanya tsigat jikinta zubawa sosai, taji yarrrr har tsakiyar kanta, kafin tayi controlling 


kan nata ya fara sauke mata kalaman da suka fara rikitata


"I've tasted your lips in my dreams,and when i woke up, knew for sure what i wanted for breakfast" numfashinta taja da kyau jin kamar zai subuce mata, idanunta a lumshe, tana kunyar budesu yaga abinda ya cikasu


"I need a big, hot steaming cup of you this morning....kin bani d....." Bai qarasa ba ya tsinci bakinsa dumu dumu cikin nata tana aika masa da salon kiss din da yafiso,bai wani tsaya bata lokaci ko daga qafa ba yayi mata kyakkyawar tarba suka soma rikita juna. Basu fahimci me suka aikata ba saida komai ya kammala,suka kalli juna cikin matsananciyar kunya murya qasa qasa tace dashi


"A kitchen?" Girarsa duka biyun ya daga mata yana fidda murmushin da yake tabashi har can qasan zuciyarsa,saboda wani irin farinciki data bashi


"And whe enjoyed it" sai suka saki siririyar dariya a tare.


Hannu ya miga mata ya kuma sauketa a hankali daga saman cabinet din sannan ya rigeta,a nutse suke takawa zuwa bedroom din shi da ita, ya hada musu ruwan wanka bai tsaya shawara da ita ba ya sunkuceta sai bandakin.


Suna gaban madubi yana busar mata da gashinta,wata sassanyar hira suke a madubin ta cikin qwayar idanuwansu ba tare da baki ya furta komai ba.

Dan garamin tsaki yaja gain yadda aketa neman izinin shigowa hallway din nasu ta garamar na'uarar dake magale a bedrooms dinsu. Cumb din hannunsa ya anivya zaro abayarsa ya zura yana fadin


"'Ina zuwa" ya juya a nutse ya fita.


Murmushi ta saki tana satar kallonsa har ya fice din,ta maida idanunta ta kulle tana jin yadda soyayyarsa keyin yadda taga dama a zuciyarta yadda take kassara kowacce gaba ta jikinta. Wani irin sassanyan mutum ne da ya iya cusa zazzafar qaunarsa a zuciyar iyalinsa.


Adadin yadda mu'amalar aure ta hadasu,adadin yadda yake sake ratsa zuciyarta da wata irin zazzafar soyayya,yasan yadda ake tafiyar da mace over and over, batasan yadda bakinta zai iya fasaltawa ba.

Nadeeya ya gani a tsaye sai ya jefa mata harara cikin salon tuhuma da kuma tsare gida


"Am sorry yaaya‚police ne suke nemanka"


"Shine zakizo kiyita disturbing mutane?" Ya fada hankali kwance


"Yi haquri" ta sake fada. Sai a lokacin yaga kamar akwai alamun tashin hankali kan fuskarta


"Are you okay?" Kai ta gyada tana hadiye yawu da ayar,sai ya kewayeta kawai yana ficewa ta bio bayansa


"Kibi ta daya qofan ki koma cikin gida" yace mata ganin akwai maza da vawa a wajen harda ma'aikatan gidan.


Cikin nutsuwa da kamewarsa ya garasa gurin.

Dukkansu sukayi saluting nasa saboda fuskar da basu zata ba suka gani. Babbansun ya matso ya miga masa hannnu sukayi musaba


"'Sir......na shiga tantama da kokwanto, da gaske a nan din meenal ya'agoub aji take?"


"Meenal?" Ya maimaita sunan cikin tantama 


"Oh,right eh nan ne" ya fadi bayan kuma ya tuna wace me sunan. Juyawa yayi kadan ya kalli yaransa sai ya karba wata takarda daga hannunsu ya migawa toufeeq yana cewa


"Am sorru to inform you tayi commiting suicide,ta kashe kanta"


"Subhanallah, subhanallah" toufeeq din ya furta yana maimaitawa tare da karbar takardar yana duba tabbacin gwaji ne na mutuwarta da kuma shaidar kashe kanta tayi din.


"Zamuje tare ku sanya hannu sai mu baku gawarta"


"To babu damuwa, bari na sanarwa da family na"


"Zamuyi gaba sir,sai ka samemu a Murtala Muhammad specialist hospital"


"Ba damuwa" waiwayawa yayi ya kira libril yace ya fiddo mota,ya juya cikin gidan da sassarfa


Sassansu nadeeya ya wuce yana sallama ya samu fadeela zaune tana cin indomie, gefe ga cup data cika da madara, cartoon take kalla a mbc 3. Da mamaki yadan bita da kallo,wasa wasa ta kama abinci sosai tunda akayi aikin fiye da wanda takeci lokacin säahar.

Murmushi ya wadata kan fuskarta,ta ture plate din tana migewa hadi da fadin


"Good morning daddy"


"'Bazan amsa ba, gaisuwarki tazo late" kai ta langabe


"But daddy, banason zuwa na tada ku a bacci fa,nasan anty N a gajiye take sosai,tun kafin ayimin aiki bata bacci, kullum addu'a take kwana tana yimin, inason tayi bacci sosai yanzu don ta haifa min ganne masu garfi da zasu dinga taremin fada" a bisa dole murmushi ya kubce masa,yasan wanna sharrin surutun nadeeya ne, har ya fesa mata kenan, ita kuma bilhaqqi qanne takeso shi yasa take kiyayewa


"Good girl" ya fada yana saluting nata da hannunsa.

Sake gaidashi tayi ya amsa, ya tambayi nadeeya da baaba ramatu tace


"Suna kitchen,abby ka duba abincin da suke bani don

sunga anty N bata kusa" ta fada tana nuna masa abincin da baki. Murmushi ya sake subuce masa,gaba daya yarinyar kamar an sake bude bakinta ne da komai nata


"'Ayyah,zamu kai gara wajen AUNTY N"


"Eh dama na fada,nayi missing abincinta sosai, please

daddy yau tayi mana dinner mana?" Kanta ya shafa


"Nima navi missing abincinta angel, amma sai ta warke sosai zata dafa mana muci ko?"


"Ni ko bata dafa min bama, indai zata kawomin qanne na 1 mu dinga wasa shikenan" dariya ta bashi duk da yanayin zucivarsa babu dadi amma sai da ya sake murmusawa


"'In sha Allah, kiyita mata addu'a yadda tayi miki kema"


"Zanyi daddy,i promise"


"That's good my angel,yanzu jeki kiramin su" da gudu ta cilla tayi kitchen din cike da farinciki, tana wassafa yadda zata kula da nata gannen itama, zata yita bawa 'yan class dinsu labarin qannenta itama yadda kowa yake bata labarin nasa,dama ita kadaice bata da.

Rudewa dukkansu sukayi, nadeeva na hawaye baaba ramatu tana salati


"Relax please, banason SAHR taji yanzu saboda yanayin da take ciki, please take care with her" ya qarashe maganar yana kallon nadeeyan, saboda yasan itace sarkin raki. Kai ta jinjina ya juya yana fita daga sashen.


Batasan me yake faruwa ba,taga dai ya shirya a gaggauce,yayi kissing hannunta yana cewa


"Zanje na dawo,ki kwanta ki sake hutawa kafin anima na sake tara miki wata gajiyar,yanzun bana bugatar kiyi komai saidai ki bani kulawa, idan da hali ma bacci nakeso kiyi" kafada ta maqale a shagwabe


"Kada ki damu,i will handle it with care and softness,it would not be harmful".


Haka ya fita ya barta da tarin tunaninsa a kanta,murmushi kuma fal fuskarta. Ta gaji da zaman,don haka sai ta shirya ta gyara sashen tsaf sannan ta sake gyara jikinta ta fito,don tana sin ganin fadde dinta, tana kewarta.


Hankalin maji yayi masifar tashi da jin labarin mutuwar haseena, ba kuma wai mutuwar ce abun tashin hankalin ba,hanyar da tabi wajen salwantar da rayuwarta.


"Ka shaidawa mamanta ne?" Maji ta tambayi toufeeq


"I think tana asibiti, nidai na gama nawa gawar tana asibiti maji". waiwayawa maji tayi ta dubi Dr jarma da aka gama rubutawa sallama


"Abba,haqqij yi mata sutura yana wuyanku,saidai bansan ta yadda za'a gayawa fauziyya rasuwar ba tunda bata da lafiya itama"


"Dole ta sani ai,ko don ta roqawa 'yarta gafara ko?" Ya fada yana sauka daga saman gadon hadi da duakan wayarsa.


Toufeeq sajjad dr har da maji suka isa asibitin da hajiya qarama ke jinyar.


"Dama muna shirin neman 'van uwanta mu sallameta ne,saboda babu me jinyarta, abinda ya hana mu bata sallama ma ba'a biyamu bill dinmu dake kanta ba" wata nurse ta fada cikin girmamawa sanda taga dr mahmud hadi da toufeeq,wanda kusan ba boyayyu bane kusan kowa yasan fuskarsu.


"Sannan sir,kamar akwai abinda yake shirin taba qwaqwalwarta,akwai magana da yawa da takeson fada ma amma kuma ba'a iya jin abinda take fada sosai,a shawarce a fara ganin likitan qwaqwalwa kafin abin yayi nisa". Shikam toufeeq zame jikinsa yay yabar wajen,don baya jin sisinsa zai iya sanyawa wajen neman lafiyarta.Zafafabiyar

No comments