Tabarmar Kashi Book 2 page 68

 "HUGUMA*_TABARMAR KASHI_


Book 02 Page 68


Dai dai lokacin da alert na qarshe ya shigo wayarta,wanda aka cire ragowar millin uku last amount da ya rage a bankinta, kuma qarshen abinda ta mallaka kenan duk duniya,don ta saida komai nata ta hade kudin cass cikin account dinta zata sake sabuwar order na dukkan shagunanta,har a ciki take sanya ran gyara da same bungasa plazas dinta da wuta tayi musu mugun ragargaza. Tsaiwa tayi cak a wajen,sai ta dafe kanta ta daga qafa da mugun gudu tana fitowa harabar gidan a birkice kamar wadda take da tabbacin barayin da sukayi mata aika aikar suna 

tsaye a qofar gidan. Saidar tana gara daga qafarta wata muguwar hajijiya ta debeta ta watsar da ita,sai gata tayi d'ai d'ai warwas a qasa. Amma hakan dai bai hanata miga hannu tana son yin kururuwa ba, kururuwar da babu damar fitarta daga bakinta saboda karkacewar da bakin nata yayi,sai wan! kakkauran yawu data fara zubarwa ta gefen bakin nata.


Caaaa ma'aikatan gidan sukayo a kanta, sai suka rasa yadda zasuyi da ita,saboda sunga fitar masu gidan yanzu. Daga qarshe dai bayan kusan awa daya daya daga cikin masu aikinta tayi gundunbala ta shiga bedroom dinta ta dauko key din motarta. Acanne taci karo da kit na sarqoqin gold dinta rankacakaf data fitar dasu a dazun bayan dawowarsu da zummar zata saidasu saboda taji yadda kudinsu yayi daraja ta aikawa gawarta kudin dake dubai ta siya mata sabon design.

Key din motar kawai ta miga musu ta wuce sashen masu aikin gidan ta hada kayanta zakara ya bata sa'a ta falle, cikin zuciyarta tana fadin"Allah ne yayi da rabona, muguwa kina samu amma ke kadai kike amfana,saidai mu mu qare ayi miki bauta" ( shawara a gareku masu ma'aikatan a gurin

Sana'a ko kasuwanci ki cikin gidajenku de sauransu,sanda mutum yake zaune qarqashinka yake maka hidima,a duk sanda Allah ya buda maka,kaima kayi goqarin buda masa ku taru duka kuyiwa Allah godiya,wannan shine abinda zai dawwamar da soyayyarka a zuciyar ma'aikatan ka,da wata iriyar mana ta gaske da zaiyi wuya a hada baki dasu a cutar da kai, ko suna ji suna gani su bari a cuceka, Allah ya bamu ikon kyautatawa dukkan wanda muke tare dashi ameen summa ameen).


Private hospital aka kaita kamar yadda sukasan duka iyalin gidan suna zuwa,babban asibiti ne da suke cazar kudi bana wasa ba,sanda aka isa asibitin da ita

likitan da ya fara dubata ya tabbatar zaiyi wuya bata

samu matsala ba,saboda jininta ya hau sosai, hakanan

barin jikinta ya daina aiki, daya barin ma ya tabu sosai

amfanin da zaiyi mata kadanne, duk wani abu dake daya

sashenma totally ya daina amfani, kama daga idonta

kunnenta hannu qafa da sauransu

Sun tsaya anyi mata komai da komai ba don

halinta da dabi' arta ba. Bayan komai ya kammala akayi total na kudin asibitin kwanciyar da zatayi da sauran bill na abubuwan da zata ci. Elyas na daya daga cikin wadanda suka tallafa aka kawota,don toufeeg din bai fita da kowa ba,daga shi sai maji din sai Dr suka wuce dashi asibitin.


Bayan ya gama duba bili din wayarsa ya ciro yayi

kiran toufeeq,cikin rusunawa yayi masa bayani


"'Kana jina elyas?"


"Eh sir"


"Sisina daga abinda na mallaka da kuma abinda

mahaifina ya mallaka ban amince ka cire ka biya komai

ba,ku batta da su tana da gwarin qwiwar yiwa kanta


komai,ka jini?"


Kai ya gyada cike da biyayya


"'Yes sir" sauke wayar yayi daga kunnensa yana furzar da huci daga bakinsa,shi kansa baisan wanne kalar hukunci ne va dace da ita ba.


Zuwa magariba Dr jarma din ya koma normal, saidai sunce lallai dole sai ya kwana,saboda sunason jininsa da yahau ya dai daita kafin su sallameshi, basason ya tafi kuma ya dawo.


"Bari na yiwa jibril magana maji ya maidaku gida ke da nadeeya,zan kwana a gurinsa in sha Allah" toufeea ya fada yana danna wayarsa.


Murmushi maji din ta saki tana kallonsa


"Kaji dan nema,waini zaka yiwa kaara? to ban yarda ba, kada kana tsaka da yimin jinya ka gudu ka barmin miji sai asuba ka dawo" nauyin maji ne ya kamashi sal ya fara shafar sumar kansa yana murmushi, ko ta fahimci tun dazun yaketa kiran number sãahar din dama bata daga ba? duka hankalinsa yana kanta tunda suka zo


"Itama tana bugatar kulawarka Muhammad, ku tafi gida kai da nadeeya din,ka kula da matarka ni zan kula da milina" ta fadi tana maida dubanta kan dr jarma da idanunsa ke rufe kamar alamun yana bacci ne.


Dan rusunawa toufeeg yayi cikin ban girma


"Allah ya qara girma, Allah ya bashi lafiya" yayi musu sallama bayan ya tabbatar babu wani abu da zasu bugata har wayewar gari.


Suna fita tana qoqarin dauko wayarta daga jaka taji an rigo hannunta, ta daga kanta a hankali sai taga Dr ) jarma ne yana daga kwancen, idanunsa da suka nuna jigatarsa da kuma gazawarsa tare da tarin nadama


"'Na dauka bacci kakeyi ai ashe ka farka" ta fadi tana yunqurin migewa. Maidata yayi ya zaunar da hannunsa daya ya buda bakinsa da muryarsa ke fita da gyar yace"Ido na biyu shifa inajin kunyar hada nawa idanun ne da naki bansan me zance miki ba,bansan ta vadda zan nemi gafararki ba,bansan da wadanne kalamai zanyi amfani wajen neman afuwarki da yafiyarki ba" kanta tadan sadda gasa tana wasa sa hannun jakarta sannan tace


"Tuntuni na yafe maka Dr tun a wancan shekarun don nasan muddin na gullaceka ko na yi maka mummunar addu'a rayuwar 'ya'yana na lalata, saidai kuma daga yau, kada ka sake sakaci da addu'a a rayuwarka,domin ita din garkuwa ce"


"Bazan sake ba shifa,naga illar hakan iyakar ganina,wai 'yaruwata shifa.....uwa daya uba daya..." Sai ya kasa garasa fada. Da sauri ta matso gabansa


"Ka daina tunawa don Allah abban Muhammad taka kalar qaddarar kenan, kuma ai yanzun komai ya wuce ) ko?" Ta fada cikin kalar tausasawar da bai taba gani

daga idanun mansura ba.


Da kalamai masu dadi ta kwantar masa da hankali har sai data tabbatar ya nutsu sannan ta mige


"'Ina zaki?"


"Zan hada maka wani abune ka saka a cikinka" kai ya girgiza


"Ba yanzu ba, banajin cin komai,ki rufe qofar kawai kizo ki zauna kusa dani naji duminki shifa,inason na fanshe bashin shekara da shekarun da na dauka" 


murmushi ne ya qwace mata,cikin salon tsokana tace


"Da wannan tsufar naka?,ai ka makaro" ido yadan fidda


"Inii wa? idan kika cikamin baki da yawa ma tazarar haihuwarku keda surukarki zata kasnace ba yawa, nadeeya itama ta samu 'yan uwa" baki maji ta rufe da sauri tana dariya


"Rufamin asiri"


"Na rufa miki" ya amsa matan shima yana dariyar.


A nutse yake takawa zuwa cikin gidan, har cikin ransa yana gara jin gidan ya qarasa fita gaba daya daga kansa. A cikin gidan al amura masu yawan gaske sun afku,wadanda sukayi silar rugujewar farincikinsa, komai na matsalolinsa a gidanne,a yanzun vanajin bashi da wani sauran bugatar ci gaba da zama a gidan,ya fita fitt daga ransa.


A hankali ya ratsa falukan nasa ya fada hallway dinsu sannan kai tsave ya isa ga bedroom dinta. Murza handle din yayi ya bude sannan ya tura gofar ya shige.

Sam dakin babu wadatar haske a ciki,amma

kuma hakan bai hanashi gain komai dake dakin ba.


Daga can saman abun sallah ya hangeta, sanye da wani baby pink hijab, fadeela na saman gadon a nannade, da alama tayi nisa a baccinta.

Duka hannayensa ya zuba a aljihun wandonsa, ya jingina bayansa da bangon dakin yana kallonta,wani irin kallo da yakejin tamkar zuciyarsa tana narkewa saboda ita, A HEROIN…ta kawowa rayuwarsa haske me tarinyawa da bai zaci samunsa a nan kusa kaf cikin rayuwarsa ba.


Jin bai garaso ba ya sanyata daga kanta a nutse ta bude bakinta a hankali ta langabar da kanta 


"Me kake kalla?‚ka qaraso" hannayensa ya sauke yana murmushi


"Jarumar matata nake kalla, kinyi missing dina ne? ko na qaraso akwai labari?" Wani narkakken kallo ta watsa masa,tadan juya kanta kadan tana murmushi


"Baka gajiya...


"Shshshsh" ya fada sanda ya iso gabanta,ya tsugunna saman qafafunsa idanunsa cikin fararen qwayoyin idanunta


" will never get enough of you moonbeam,you are the only home i want to stay for ever, kinsan wani abu?" 

Yayi mata tambayar kai tsaye. Fararen idanunta ta daga ta kalleshi,saita girgiza kanta tana jin zuciyarta da ruhinta dukka suna narkewa a kansa, tana jin wata iriyar soyayya me zafi da garfi tana fusgarta a kansa. A hankali ya zame va zauna sosai a gabanta kamar me zaman cin abinci,ya kama vatsantsa na tsakiya yana kallon tsakiyar qwayar idanunta,yanason ya aike mata sagon da gaske yadda kowacce gaba ta jikinta zata karba "Duk sanda nakejin kaina ya cika da tunanika kala daban daban my body is weak and my soul is aching....i find everything in your arms,you are my home....you are my peace SAHR" Idanunta ta lumshe qwarai


"Ya salam! wannan wanne irin so ne haka me barazanar fasa zuciva?" Ta furta a hankali da salon magana cikin rad'a. Ji vayi kamar ya hadiyeta su zama abu guda shi da ita ko zasu fi samun saugi a cikin zukatansu. Sai kawai ya jawota a tausashe ya sanyata cikin jikinsa.


Dan janyeta yayi da sauri yana duban fuskarta


"Fever? me yasa zaki damu da yawa hakan akan lamarin matar data riga ta shude cikin rayuwarmu?, muddin wani ,abu ya faru dake tabbas sai ta d'and'ana kudarta bayan wadda zata dandana din, ta gama cutatar mana da ahalinmu har abada in sha Allah " hannunsa ta riqe sosai tana kallonsa


"Cool down hottie, am safe fa,nayi bacci ne da yawa sai ya sanya jikina yayi dumi sosai, but am fine fa" ta fada a shagwabe,iska ya furzar daga bakinsa


"Alright,ta tsira" ya furta a hankali.Zafafabiyar

No comments