Fin Karfi Book 1 Complete

 




*FIN ƘARFI BOOK 1*


                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


                        Page 1


*Wannan littafin na kuɗi ne ₦600 idan kina buƙata kiyi magana ta wannan number 08140004302 ko wannan 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya don Allah👏🏻*

*Masu son a tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


Ya tsura mata ido yana murmushi. "Ina son ki Pretty har ban san irin son da nake miki ba."


Tayi murmushi "Na sani Dady,nima ina sonka na ƙarshe."


Ya ɓata rai gami da harararta, "ban ce ki daina kirana da sunan Dady ba? Ni ba Dadyn ki ba ne gwarama kice min Yusuf ɗina." Ta yi murmushi sannan ta ce, "to na daina Dady." Ya ce, "Kika kuma? To ban yarda ba, sai kin min...... ke na ma yanke hukunci yanzun duk sanda ki ka ce tara goma zaki biya."


Ta dube shi "Na yarda, amma ban da na yanzun ka yi haƙuri ka ji Da.....Oh sorry." Ta faɗa tana dariya gami da girgiza mishi hannu.


Ya ce, "ok,zama ki ƙara ne." Tana dariya tana faɗin "Sorry ka yi haƙuri kaga ai ban faɗa ba ko?"


Ya ce "to naji, amma sai kin biya rata ɗaya na miki haƙurin sauran." Ta ce "To ni me zan rinƙa ce maka dan bazan iya faɗin sunanka ba?"


"Ki ce Darling." Ta tsura mishi ido, sannan ta girgiza kai "Wannan sunan sai mun yi aure ko?" Ya ce"to in bazaki ce Yusuf ba,to ki kalleni kawai,ko kuma ki ce min Dadyn ki biya tara" ta ce ya kamata fa ka tafi gida don dare yana yi."


Ya tsura mata ido.


"Watan ma kina korata ne ko?" Ta zaro ido, "na isa,bana son wani abu ya same ka ne." Ya ce "ashe kina sona?" Ta yi murmushi "Don Allah ka zo kaje gida, ya ce to faɗa min wata kalma mai sanyi da zan tafi ina tunawa tare da farin ciki."


"To zan faɗa maka, amma me kake so in faɗa?"


Ya yi dariya, sannan ya ce "To har sai na faɗa miki abin da zaki faɗa min wanda zai faranta min raina?"


"To Allah ya tsare min kai masoyina. Allah ya barmu tare." Ta faɗa a yayin da take murmushi, shima murmushin yake yi. Da sauri ta juya ta nufi ƙofar shiga cikin gida, ya bi bayanta da kallo. Shi kam komai nata birgeshi yake yi,yana tsananin sonta kai yana mata mahaukacin so.


Tafe yake yana tunanin ta har gida. Ya shiga falo da sallama,Momy tana ƙoƙarin hawa sama wajen Dady, sai ga Dadyn, ta dube shi tana murmushi.


"Sarki mai Ruƙayya, daga can kake na sani."


Ya isa gurinta da murmushi, "Yes daga gurin Pretty nake,ta ce na gaishe ki."


Momy ta ce "ina amsawa, ina fatan tana nan lafiya?" Ya ce "Lafiya lau, Dad yana sama ne?" Ta ce, "Eh." Suka jera da gudu ya isa kujerar da Dad yake ya zauna.


"Dad na dawo."


Alhaji Mansur ya dubi ɗan nashi, sannan ya ce, "Daddyna ɗa guda tamkar da dubu. Ya ka baro Ruƙayyat ɗin taka?"


Cikin jin daɗi, ya ce "Tana gaishe ku Dad ɗina."


Dad ya ce "muna amsawa, sannan ya ci gaba "Ya kamata nan da ƴan ƙwanaki mu shiga maganar saboda ana buɗe maka kamfaninka ga kuma Ruƙayyanka,ko me ka gani?" Dady ya dubi Dad cikin murna "Zan fi kowa jin daɗi, sai dai nafi son Pretty ta ƙare Secondary ɗinta,don bana son tana shan wahala."


Momy ta dube shi "Kai Dady ba ko irin jin kunyar nan?" Dady ya dubi mahaifinsa "Dad ka ji Momy da wata magana fa, bayan ina sonta." Ya dubi uban "Kasan wani abu Dad? Ya girgiza kai, sai in kafaɗa." Dady ya ce, "kullum fa in naje sai ta ce min naje gida dare yayi don bata son wani abu ya same ni a hanya."


Dad da Momy suka sa dariya, Momy ta ce, "to lover Boy,aje a ƙwanta,sannan a tashi ayi sallar dare yau kada ayi na jiya ace an gaji." Ya dubi Momy"insha Allahu yau zan tashi Mom jiya ma ina mafarkin Ruƙy ne, suka ƙara sa mishi dariya, Momy ta ce, "To Sarki mai Ruƙy sai da safe.


Ya isa gurin mahaifinshi, "To Dad sai da safe." Sannan ya yi mishi addu'ar tashi lafiya, ya dubi uwar, "Momy good night." Ta  ce , to sai da safe Dady.



    ***  ***   ***   ***


Yayi rigingine bisa gadonshi.


Gado ne na alfarma,ɗakin nashi tsararren ɗaki ne tamkar a Turai. A ƙirjinshi filo ne ya rungume tsam, ya lumshe ido. Ƙa'ida ne kullum sai yayi tunanin farkon haɗuwarsu da Ruƙayya, sannan zayayi barci tamkar karatu.


Ya soma tunawa da sanyayyar safiyar mai ɗauke da iska mai daɗi,yana tafiya kan titin Indifenden cikin nishaɗi da annashuwa. Gidan Kakarshi Hajja mahaifiyar Dad can ya nufa,don kusan kullum sai yaje,Kabala gidan Hajja kasancewar yana son cin abincin gargajiya irinsu waina da funkasu ɗan wake ko sunasur,sam bai ankara ba sai dai ya ga wata yarinya sanye da kayan makaranta zata tsallaka titi, ta shiga titin ne ba tare da ta kula da yana zuwa ba, ya ce "Innalillahi." Tare da taka birki, tare da taimakon Ubangiji sai ya ɗan hankaɗe ta ba da yawa ba, saboda motar dake bayanshi ce ta ɗan bugi tashi har fitilun bayan suka fashe.


Da sauri ya fito yazo gurin yarinyar tuni ta miƙe jikinta sai rawa yake saboda tsabar tsurewa da tsoro, mutane sun ɗan taru da yawa sai faɗa suke ma yarinyar kan cewa ta shigo titi ba tare da ta duba mota ba.


"Dady ya ce, "ku barta, ke ba ki ji ciwo ba? Jikinta na ɓari ta ce, "a'a." duk da haka ya ce, "Zo muje na kai ki asibiti." Da farko ta ce a'a, amma ganin mutanen gurin sun mata cah! Da masifa, suna faɗin "Don ma kin samu zai kaiki bayan ke kika jawo faruwar abun, Malam ka tafi ka barta kawai, to sai ya ce ba komai zo muje su ɗan duba ki suyi miki Dressing wannan ƙujewar. Sai ta yarda ta bishi asibitin da Hajja Kakarshi take ganin likita can suka je,sun ɗan wanke mata inda ta ƙujen tare da bata magungunan sha.


Suna tafiya a mota ya ce "ina ne gidanku yake?"


Muryarta na ɗan shaƙewa ta ce, "Kabala." Ya ce "Shikenan, bari muje nima Kabala ɗin zan je." Ya kuma dubanta, haka kawai yake son kallon yarinyar idanunta suna bashi sha'awa masu shep ɗin ƙwai farare tar sai zubar da hawaye suke yi,me yasa kike kuka ko zafin ciwon kike ji ne? Ta ɗan dube shi sannan ta girgiza kai alamar a'a ya ce ya sunanki ne? Ta ce,"Ruƙayya" "To Ruƙayya share hawayenki wa yace miki Pretty tana kuka um? Hijabin ta tasa tana share hawayen ta daidai da sanda suka zo Bus stop ɗin Kabala,zaya wuce ta ce nan zamu shiga, ya ce ok, to ya shiga ya miƙe can ƙasa, daidai wani ɗan shago ta ce nan zaka tsaya gidanmu yana cikin lungun. Ta fito suka jera har cikin lungun nan wani tsohon gida ta nuna masa ga gidan nan, na gode." Ya ce, "to ni ma na gode." Ya miƙa mata ledar magungunan "Ga shi sai nazo duba ki" ta ce to sannan ta ɗaga labulan buhu ta shige cikin gida.


Ya jima tsaye yana duban gidan su, "gaskiya su Ruƙy talakawa ne sosai." Ya ce a ransa, sai dai shi yarinyar ta tafi da wani ɓangare na zuciyarsa.


Cikin rashin kuzari ya shiga gidan Hajja, tana zaune idonta sanye cikin gilashi mai ƙara ƙarfin ido,tana kallon TV,ya shiga da sallama yanda hankalinta ya tafi gurin kallon, sai abin ya bashi dariya. Ya soma dariya yana faɗin Hajja nifa ba zan auri makauniya ba,dubi yanda ki ka ƙwafe kina kallon TV ƙila ma ba ki ganin abin da ake nunawa." Ta ce "ba komai na ji,kar ka auri makauniya ɗin, masu idon ma tsoronsu kake ji." Ya ce "ku kun ƙosa in yi aure,ni ban isa aure ba sai nan da shekara goma." Ya ci gaba da cewa, "tashi ni ki kawo min (Break) ko nayi miki saki shida."


Yana zaune akan kafet ɗin ɗan matsakaicin falon nata. Ta dube shi "Yau kuma a ƙasa za'a zauna?" Ya ce "Eh" tasa baki ta kira saude mai mata aiki,ƴar Dattijuwa ce mai hazaƙa da tsafta, don haka Hajja ke son zama da Saude, domin Hajja bata son ƙazanta haka nan bata son lalaci,tsohuwa ce mai sanin ya kamata da ibada.


Saude ta shiga jera mishi kuloli tana faɗin "yau kuma uban masu gida a ƙasa za'a zauna?" Ya ce, "bari kawai Saude,yau ɗin nan a ruɗe nake." Hajja ta dube shi "Naga alama, shi yasa kake ta surkulle, to me ya faru ka ruɗe ɗin?" Ya ce "Wata yarinya na kaɗe da motata." Hajja da Saude suka ɗauki salati.


Hajja ta ce, "Garin yaya Isuhu?" Dady ya ce "To tunda kika ce min Isuhu ba zan faɗa ba." Ya ce yana mai ɗaure fuska.


"Hajja ta ce, "Ai kai kaga matsalarka, ace mutum da sunanshi amma ya ce ba ya so a ce Isuhu kada ka faɗa ta maida kallonta ga TV, yayi murmushi sannan ya ce Hajja yawa ni na Allah,ai hatsarin ya zo da sauƙi,bata kula shi ba sai Saude ce tace yanzun ina yarinyar?" Ya ce, "na kai ta asibitin Alba inda Hajja take ganin likita.


Da sauri Hajja ta ce, ciwo taji ne sosai?" Ya ce, a'a,na kaita ma gidansu." Suka haɗa baki "Allah ya kiyaye gaba." Ya ce, "Amin." Ya soma buɗe kulolin yana cewa "me aka yi minne yau? Ya buɗe ta farko ganin waina da miyar tantaƙwashi sai ya ce "yauwa" ɗayar kuma yaga dafadukan jalof ɗin taliya da nama manya. Yayi murmushi sai ya samu kanshi da cewa, "Hajja ku ne kuke matsa min da nayi aure ina ƙi, to gashi dai wannan karon zan yi."


Hajja ta soma wangale baki "kai ɗan nan! A ina ka samu matar ne? Kuma yaushe ne bikin har an tsaida rana? Kaga ko jiya Babanka ya zo nan da daddare bai gaya min ba,ko ƴar abokin nasa ce da ya soma min maganar ta ƙwanaki?"


Ido Dady ya zuba ma Hajja,yana ta mamakin yanda suka bi suka matsa ma kansu akan ya yi aure,dubi dai yanda Hajja ta wani ruɗe,sai ya soma dariya yana cewa "yau fa muka haɗu da yarinyar ni ko gaya mata ma banyi ba."


Hajja ta ja dogon tsaki ta miƙe. Saude tana ta dariya ta ce, "Kai amma uban masu gida baka da dama,nima na zaci magana ta yi ƙarfi ne da kace zakayi aure!"


Hajja da ke ƙoƙarin saka takalmi ta ce, "daina kula shi Saude,ai dama duk ɗan fari wawa ne. Abin da ya tsana kenan Hajja ta ce masa, domin in har ta ce masa ɗan fari wawane,in yayi fushi sai ya kai wata bai zo ba.


Ya miƙe fuskar nan a ɗauke,Saude tana cewa,yi haƙuri uban masu gida,ko sauraronta baiyi ba ya fito yasa takalmi. Hajja tana alwalla don yin walha ta dube shi sai wani cika yake yana batsewa. Ta so tayi dariya, amma sai ta share.


Ya dube ta sannan ya ce, "ni na zo gidanki shi yasa kike min wulaƙanci,ba sai kin ƙara ganina ba a gidan naki sannan zaki min." Ta ce "kar kazo,ai dama ba kiran ka nayi ba. Nima na huta da irin tsurfarka."


Ya dube ta, "haka kika ce ko?" Ta ce, "Na faɗa ɗin." Tana dariya, ya wuce abin shi.


Tafe yake har ya iso  gidan su dake G.R.A Malali, Baba maigadi ya buɗe mishi get ya shiga,Baba maigadi ya ce "sannu Dady." Hannu kawai ya ɗaga mishi. Baba ya tsaya yana kallonshi, tabbas yau Dady yana cikin damuwa, domin da sai ya mishi magana. Ya fita daga mota ya shiga cikin falon su, Momy tana zaune gaban computer tana harkar kasuwancinta,sai ta hangi Dady yayi sama. Ta ɗaga murya "Dady! Dady!! Ya juyo sam ma bai kula da Momy ba, ya dawo da baya ya ce "Momy" ta ce, "Na'am Babanmu mene ne na ganka wani iri?" Ya zauna kan kujera, itama ta sauka daga kan computer don ta ji matsalar ɗanta,ko ɗaya bata son ganinshi cikin damuwa kasancewar shi ɗa guda ɗaya da suka mallaka. Ta dafa kafaɗarshi "Daddyna menene damuwarka?" Ya ɗan turo baki sannan ya ce, "Momy ba Hajja ba ce tace min ɗan fari wawa,to ni wawancin me nake yi?" Momy ta soma dariya. "Ƙyale Hajja, kada ka ƙara kai mata cefane.


Ince dai kaci abincin? Ya ce ni ban wani ci ba, yauwa na tuna Momy,yau na kusan kashe miki suruka." Ta dube shi da sauri "wacce suruka kuma? Ya ce mata, "yarinya na buge sai da na kaita asibitin Alba. Kafin na kaita gida sai na fara sonta," Momy ta soma dariya so da gaske koda wasa? Ya ce "kawo hannunki ki ji." Ta kawo hannun ya kara a saitin zuciyarshi, "kin ji yanda take harbawa da ƙarfi?' Momy ta ce,ƙwarai na ji, ya ce duk second ƙara sonta nake yi. Momy sunanta Ruƙayya." Momy ta ce naji daɗi, to ka gaya mata? Ya ce ban sanar da ita ba, abin da in na tuna ya ke mugun faɗar min da gaba kenan, kada ta ce bata sona ya ƙwantar da kanshi a jikinta ya zanyi Momy in ta ce bata sona? Ya zan yi ƙila ma in mutu sonta ya shige min da ƙarfi.


Momy ta tsura mishi ido tausayinshi ya kamata,a ranta ta ce, Allah kada kasa ma ɗan nan so mai wahala, cikin ƙarfin hali tasa hannunta a jikinshi tana ɗan jijjiga shi kada ka karaya Daddyna,kai ɗin mai ƙyau ne da ƙyan hali nasan Ruƙayya zata soka. Mai yawa kar ka damu jikina yana bani cewar ita ce matarka wadda zata haifa mana jikoki masu ƙyau.


Da sauri ya ɗago yana murmushi.


"Na gode Momy, ke uwa ce tagari,da dama in kika hango min abu yana kasancewa. Na gode da kulawarki. Ki taya ni da addu'a." Tayi dariya "zan tayaka, kuma yau da dare ka shirya kaje gurinta dan kasan an ce da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe, ya ce shi kenan zan je bari naje ɗaki na na ɗan ƙwanta, Momy ta ce to amma ban da fa tunani, ya ce to.


Da kallo ta bishi yana hawa step sai da ya shiga falonshi sannan tayi ajiyar zuciya. "Allah ka taimake ni kada ka daka yaron nan cikin wani hali kasa yarinyar nan ta zama alheri gareshi damu gaba ɗaya."


Sun jero tamkar abokai shi da Dad ɗinshi,dukkansu suna sanye da fararen jallabiya da carbi a hannunsu, ya dubi Dad.


"Dad please,ka mu yi sauri kasan fa zan fita ne." Dad yayi kamar bai san inda zashi ba, ya ce "ina kuma zaka ne da daren nan Dady?" Dady ya dubi Dad cikin mamaki sannan ya ce yanzun duk surutun da nake maka kama manta, shi yasa nake ce maka Momy tafi damuwa da al'amurana, ya ce,No Dady nima ban manta ba,ina tsokanarka ne. Nasan gidan su Ruƙayya zaka don nuna mata cewa kana sonta,to ka iya hirar soyayya ko na koya maka?" Ya dubi Dad yana dariya, "Dad ba zai gagara ba tunda ni ɗin ɗan soyayya ne. Momy ta bani labarin irin soyayyar da ku kayi." Dad shima cikin dariya yake cewa, "Ok,my son ina maka fatan sa'a."


Sun shiga falo da sallama Momy tuni ta shirya abinci a dinning table,Dad ya nufi gurinta yayin da Dady ya yi saman shi, cikin Jen's da T.shirt ya fito ya yi ƙyau sosai sai ƙamshi yake yi. Ya nufi gurinsu Momy suna cin abinci suna hira, suka dube shi Dad ya soma magana.


"Kayi ƙyau my son,sai ka dawo ina maka fatan sa'a."


Dady cikin jin daɗi yake cewa "Saura Momy." Momy ta ce, "koma samanka ka canza kaya kaftani zaka sa gami da hula, ba tare da ya ce komai ba, ya nufi sama cikin shadda galila ya fito blue,sai maiƙo take hula ƙube mai bluen zare, ya iso gurinsu, Momy ta soma dariya kayi ƙyau sosai Daddyna sai ka dawo.


Kiss Dad ya mishi a hannu, sannan ya ce, "sai ka dawo." Suka rakashi da ido har ya kai bakin ƙafo, sannan ya juyo ya ɗaga musu hannu suma suka ɗaga mishi a tare.


Yayi fakin a daidai lungun su Ruƙayya,a hankali ya taka har bakin ɗan shagon nan suka gaisa da mutanan da ke gaban shagon a zaune. Sannan ya shiga lungun, wani yaro ya fito daga ɗayan gidan.


"Kai Boy,zo Nan mana." Yaron ya iso da sauri "Gani." Ya ce, "shiga nan gidan kace ana kiran Ruƙayya." Yaron ya ƙara duban shi ya ce, to.


Ya dube ta "Pretty kin san abin da ya kawo ni?" Ta ce a'a" cikin faɗuwar gaba, ya ce,bana son jama kaina aji ina sonki ne Pretty,kuma da aure." Da sauri ta dube shi cikin tsoro don bata taɓa jin kalmar ba. Kai hasali ma bata taɓa saurayi ba,kai a ganin ta ma bata wuce ƴar aiken kiran ƴammata ba. Ganin yanda ta tsura mishi ido, sai fargaba da tsoro ya kama shi.


"Please Ruƙy,kar ki ce min baƙya sona. Momy ta ce zaki soni" tsura mishi ido ta ci gaba da yi tana mamakin shi gashi ƙyakkyawa kuma da alama suna da kuɗi, Ta ce "to ka bari na faɗa a gida,in sun yarda shi kenan."


"No ni dai ki sanar dani in kina sona don Allah."


Ta rufe fuska ta ce, to na yarda, da sauri ya ce kina sona? Ta ɗaga kai alamar "eh" ya ce "Oh Allah na gode Pretty to yanzu sai ki bani labarin ki in baki nawa. Ta dube shi kamar ya ya kenan fa? Ya ce to bari kiji nawa sai ki bani naki.


"Sunana Yusuf Al-Mansur,mahaifina Bakatsine ne,mahaifiyata Fulanin Yola ne,tana da ƙyau sun haɗu da mahaifina ne a jami'ar Bayero dake Kano. Soyayya mai tsanani suka yi kafin suyi aure. Bayan auransu, suka shiga amfani da ƙwayoyin hana haihuwa don suyi karatu. Daga baya mahaifina ya koma makarantar Police,ya taka matsayi kala-kala har zuwa ƙwamishinan ƴan sanda ya samu matsayin Gwamnan jihar Katsina sannan ne aka samu ciki na,koda tazo haihuwa sai dai aka yi aiki aka cironi. Likita ya ce masu Momy ba zata sake haihuwa ba saboda ƙwayoyin hana haihuwa da ta rinƙa sha, ƙwayoyin sun ɓata mata mahaifa. Dalilin haka yasa ta damuwa tare da yin nadamar shan ƙwayoyin hana ɗaukar cikin, don haka sai ta maida kai don rainona gami da min tarbiyya. Shi ko Dad ko a jikinshi,dama shi ɗan boko ne komai nashi cikin nasaranci yake yinshi,don haka bai damu ba sam shi bai ga dalilin tada hankali ba.


Yusuf suka sa min sunan Kakana,mahaifin Dad, don haka sai suke kirana Dady. Ko sanda ina primary Dad ya sauka a cikin muƙaman da ya taka har da IG na Nigeria gaba ɗaya, yanzun ya sauka sai dai yana kasuwanci da kamfanoni da gidajen mai a Abuja, na yi primary da Secondary a spen na yi Digree na ɗaya da na biyu fannin kasuwanci, yanzun na gama ina jiran kamfanina da Dad yake gina min nan ba da jimawa ba,zaki san Momy na da Dad ɗina da yayanshi suna Katsina.


Alhaji Musa Yusuf,sunan wan Dad ɗin ƴaƴanshi uku Maryam tana aure a Abuja sai Ahmad yana aiki a NNPC nan Kaduna, sai Yusra tana karatu a Malesia." Ya dube ta na gama nawa sauran ke.


*FIN ƘARFI BOOK 1*


                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


                        Page 2


*Wannan littafin na kuɗi ne ₦600 idan kina buƙata kiyi magana ta wannan number 08140004302 ko wannan 09068032427 idan baki shirya ba ki bari sai kin shirya don Allah👏🏻*


Ta dube shi, sannan ta ce  "Ni saɓanin kai ne don mu talakawa ne,mahaifina Malam Sani da Ummarmu Maimuna,auran zumunci ne,suma Fulanin Katsina ne,zama ne ya kawo su Kaduna. Affa muke kiranshi sana'ar koli yake yi, ya katse ta "menene kuma koli?" Ta ce "Saida su kanwa,citta allura da dai sauransu. Mu shida ya haifa,dukkanmu mata ne. Yaya Sadiya ita ce babba ta na aure a nan Kabala da yaranta biyar sai Yaya Suwaiba itama tana aure a Tudun Wada,sai Yaya Amina watan ta shida da aure tana nan bayanmu. Yaya Fati tana makarantar ƙwana a Soba S.S3 Yaya Murja W.T.C S.S.1 sai ni Ruƙayya ina J.S.3 kuma nice Auta. Affanmu talaka ne amma yana da wadatar zuci ya ɗau nauyin karatunmu da dukkan ɗawainiyarmu. A Islamiyya ina ajin sauka,kaifa? Ya ce ni na sauka tun muna Abuja. A ƙasar Spen Momy ta samo min Malamin da ya ci gaba da koyar dani.


Shi yasa ina son Momy sosai,tana kula da bani tarbiyya mai ƙyau. Har na bar cikin Turawa ban taɓa aikata wata alfasha ba, duk da irin yanda ƴaƴan Turawa suka dinga maƙale min. Ban taɓa soyayya ba,hasalima tsoron mata nake yi,basa burgeni sam, sai yau Allah ya haɗa ni dake. "Yauwa shekarunki nawa nema na ji J.S ma kike?"


Ta ce, "Sha shida." Ya ce,"tabɗi! Ni kam na nunkaki, ta dube shi 32? Ya ce May ɗin nan da zamu shiga zan yi 30 years," ta ce saura biyu ka nunkani ɗin. Suka yi dariya a ranta tana raya dama tafi son ta auri wanda ya fita sosai don tayi shagwaɓar ta son rai. Yaya Murja ta shigo lungun ta dawo daga gidan su Yaya Sadiya, cikin mamaki take duban Ruƙayya, Ruƙayya ta dube ta "Yaya Murja shi ne fa wanda ya ɗan tureni ɗazun yazo duba ni ne." Murmushi Yaya Murja ta yi, sannan ta dube shi da sauri ya ce "Yaya Murja ina wuni ina gajiya? Cikin dariya yaya Murja ta amsa, sannan ta wuce.


Ya ce, "Pretty me yasa ba kice mata ni mijinki ba ne?" Ta ɗan yi murmushi sannan ta ce ai zata sani wata rana."


Sun ɗan jima suna hira, sannan ya miƙe ya ciro sababbin rafar ƴan naira hamsin.


"Ga wannan, gobe nazo na kai ki makaranta?" Ta ce, "ka bar shi kawai na gode. Sannan kada kazo in Affa yasan haka zai hana ka zuwa gurina musamman ni da ba a barina fita. Sai nayi ma Yaya Murja magana yanda ta ce sai na sanar da kai," ya ce to in zo yaushe? Gaskiya ba zan iya daɗewa ban ganki ba,ta tsura mishi ido "to yanzun yaya za'ayi?" Ya ce "mu shiga gidan in gaya musu da kaina."


Ta ce, "A'a,ba zaka ji kunya ba?" Ya ce "wace kunya,kinsan iyayena tamkar abokaina na maida su,sun jani jikinsu sosai duk matsala ta su nake tunkara su bani shawara tare da yi min addu'a sai kiga komai ya zama daidai." Ta ce,kasan mu fulani kar a ga cewa ka yi rashin kunya, kada ka damu. Ya ce to zaki sha mamakin yadda zamu saba da Affa. Kafin na zo nan ko har kayan da zan sa Momy na ta zaɓa min,mu rayuwar gidan mu mai sauƙi muke yi, ina da abokai amma na fiyin shawara da iyayena. Ya ce ta riƙe kuɗin, ta ce a'a ka barsu ta ce sai da safe ta juya ta nufi gida. Sai da taje zata shiga sai ta juyo tana mishi bye-bye,ta shige.


Ya dubi kuɗin tun da rana ya amsa gurin Dad amma ba zai koma da su ba gaskiya,don haka sai ya isa ƙofar gidan yayi sallama. Yaya Murja dake yin wanke-wanke ta amsa, sannan ta ce wanene? Ya ce nine. Ta leƙo ya miƙa mata cikin leda yasa su ga maganin Ruƙayya, ya juya ya tafi."


Da gudu ya shiga cikin falon suna zaune suna kallon labaran ƙarfe tara ya shiga tsakiyarsu ya zauna, suka dube shi suna murmushi. Dad ya ce "an ci nasara ko?" An ci nasara Dad,ta ce tana sona kuma zata aure ni." Momy ta ce "Alhamdulillahi, sai kaima Allah godiya, kuma ka rage rawar jiki ka ji ko?" Ya ce "To Momy." Ya tashi ya nufi ɗakinshi.


Yaya Murja ta yi sallama ta shiga ɗakin Umma,Ruƙayya tana zaune kan tabarma yayin da Umma take zaune bakin gado. Yaya Murja ta dubi Ruƙayya ta ce "lallai Ruƙayya,waton ma ina miki wanke-wanke maimakon da ki ka dawo daga taɗin kizo kiyi ɗaurayar ƙwanukan, sai ki ka share ni ko?" 


Ruƙayya ta dubi Yaya Murja da sauri "Kai yaya Murja! Ba fa taɗi naje ba, gaishe ni fa yazo, kada ki sa Affa ya ji ya ɗauka da gaske ne ya yi min faɗa." Cikin dariya Yaya Murja ta ce, "To ga maganinki."


"Wanne magani kuma?"


"Oho! Yayi sallama ne ya miƙo min wai ya manta bai baki ba."


Ta amsa ta buɗe,sai ga kuɗi, ta saki ledar kamar taga abin tsoro "Me yasa ki ka amso Yaya Murja?"


Itama Yaya Murja cikin tsoro ta ce, "menene?" Ta ɗaga ta zazzaga sai ga kuɗi sun zubo, Umma ta ce, "Wannan fa?" Kafin Murja da Ruƙayya suyi magana,Affa yayi sallama ya shigo. Ya dube su ya dubi kuɗin sannan ya zauna kan kujerar da ta zama ƙwara ɗaya jal a ɗakin,tuni cikin Ruƙayya ya ɗuri ruwa, jin ɗakin ya yi tsit sai ta saci kallon Affa da Umma duk ita suke yi wa kallon tuhuma. Yaya Murja ta ja hannunta suka zauna, jikinta sai rawa yake yi,don ta tsani faɗa bare duka,Affa ya ce "wannan kuɗin fa?" Ruƙayya ta dubi Affa sannan ta dubi Yaya Murja. Affa ya ce "Ban tambayi Murja ba ke na tambaya,duban me kike mata?" Ruƙayya ta ce "in am dama nace ne.....am wanda ɗin nan ne..... Umma ta katse ta da faɗin "kima mutane magana sak bama son in ina,kin ji ko? Sannan ta ce, "wanda ya zo duba ni ne ya bani na ƙi amsa, shi ne yaba Yaya Murja wai ya ce ta bani." Affa ya ce "To shikenan,an gode amma ke Ummansu ki adana." Sannan ya dubi Ruƙayya ya ce, "amma kin daɗe gurin gaisuwar nan, da yazo miki kodai da wani abin?" Ruƙayya ta yi saurin cewa "Ba komai Affa,labarin makaranta muke yi." Ya ce "shi kenan kuje."


Bayan sun kammala wanke-wanke sai suka shiga ɗakinsu.


      ***    ***  ***


Dare ya yi nisa,gari ya yi tsit, ba motsin komai sai ikon Allah.


Yaya Murja tana ta barcinta har da minshari,yayin da ita kuma Ruƙayya barcin ya ƙaurace ma idanunta. Zuciyarta tana ruwaito mata abin da ya faru tun safiya, har zuwa lokacin da Yusuf Al-Mansur (wato Dady) ya kawo mata ziyara.


Ita kanta sukuku ta yini ta rasa dalili ta kasa mance kamanni gami da daddaɗar muryarshi, hatta da ƙamshin turaren shi gizo ya dinga mata. A wannan yini sai ta ji kamar ga ƙamshin sannan ta na jin hirarsu ta daran ta mata daɗi musamman in ta tuna da yanda ya nuna tsananin sonshi gareta, ta kuma juyawa tare da faɗin "Allah kasa Affa da Umma su so shi, Allah kasa mijina ne." Ƙwana tayi juyi da tunani.


    ***  ***  ***


Misalin ƙarfe baƙwai da rabi, Yaya Murja da Ruƙayya sun jera don tafiya makaranta. Suna tsaye a Bus stop, inda Bus suke zuwa suna ɗaukansu, suna kai su makarantarsu kan kuɗi naira ashirin.


Bus biyu suka iso lokaci ɗaya ƴan S.S suka shiga ɗayar har da Yaya Murja, ta ce "Ruƙayya kije waccen Bus ɗin." Ruƙayya ta ce, "To,ai tama cika ku je kawai wata zata zo,ai muna da yawa."


Tashin motocin nan ba da jimawa ba, su Ruƙayya suna tsaye da wasu ƴan ajinsu, suna ƴar hira. Wata jar mota ƴar mitsitsiya ta tsaya a gabansu, duk suka dubi motar kai har sauran ƴan matan da suke tsaye don jiran mota sai da suka tsurama motar nan ido,don ganin wanda zaya fito. Gaban Ruƙayya ya yi mugun faɗuwa ganin Dady ya fito daga motar.


Cikin murmushi ya nufo su Ruƙayya, sanye yake da Blue jeans da farar riga mai dogon hannu, wanda rigar ta ɗan matseshi shine yasa ƙyawun halittar jikinsa ta ƙara fitowa, fuskarshi fes,siririn gashin da ya tara daga haɓarshi har ya zagaye bakinshi ya zarce zuwa gefe da gefen fuskarshi ne ya ƙara fito da ƙyaunshi, hatta gashin idonshi shar suke tamkar ya taje su ne, idanuwanshi masu tsananin haske, tamkar ba namiji ba. Ya zuba su kan Ruƙayya da ita ma take kallonshi,sam gani yake yi kamar ba kowa sai su biyu,yayin da matan dake gurin suka shiga tunanin wurin wacce yazo. Daf, da ita ya tsaya, sannan ya ce, "Pretty na zaci fa ba zan same ki ba." Ta ce, "ina kai zakaje da sassafen nan?" Ya ce "Nazo ne in kai ki makaranta." Ya juya "Zo muje." Ta ɗan tsaya,tsoron bin shin take yi dan kar ƴan makarantarsu suyi mata wata fassara, ya juya ya ganta a tsaye, ya kai hannu ya amshi jakarta.


"Zo muje,don kada kije a late." Ya nufi motar, ta dubi sauran ƙawayenta "Na'ima kuzo muje." Suka nufi motar wasu na mamakin a ina Ruƙayya ta san wannan? Masu gajen haƙuri ma sai da suka tambayeta wanene wannan? Ba ta ce komai ba, har suka isa gurin motar.


Kujera ya ɗaga ma sauran suka shiga, sannan ita kuma ta shiga gaba, sun soma tafiya sannan kanta a sunkuye ta ce "Ina ƙwana?" Ya ce, "Lafiya Pretty,kin tashi lafiya dai ko?" Ta ce "lafiya." Yayi murmushi sannan yayi ƙasa da murya "ko ƴan uwanki ne waɗannan?" Ta ce, "Eh" ya dube su ta madubi, sannan ya dube ta "Duk kin fi su ƙyau." Ta dube shi tana ƴar dariya,nasan kana tsokana ta ne kawai."


Ya ce, "Ba maganar tsokana Pretty,ni ƙyau kike min ba kamar ki."


Daidai nan suka iso makarantarsu W.T.C. Ya riƙo jakarta sannan ya ɗaga ma sauran kujera suka fita,tana tsaye shima ya fito yana dubanta, sai yaga kayan makarantar sun yi mata ƙyau, duk da cewar sun koɗe amma a goge suke, ya mata murmushi "Zan dawo in ɗauke ki." Ta girgiza kai cikin tsoro "Dady kada ka dawo, Allah in Affa ya ji zaya yi min faɗa, sannan zai hana."


Yayi shiru can an jima sai ya ce, "Yanzun ina Affa yana gida ko ya fita ne?"


"Sanda muka fito yana nan, amma yanzun nasan ya fita."


"Shikenan, yanzu sai da dare kenan?"


Ta dubi idonshi, ta ce "kada ka zo fa," ya ce saboda me? Kasan fa ba'a barina fita shi ne dalili, ya ce ni dai zan zo ki tafi. Ta amshi jakar sannan ta tafi yana tsaye yana dubanta har ta kai bakin gate. Ganin yanda prefect suka tare ta yasan dukanta zasu yi,don haka sai ya isa gurinsu, ya dubi ƴanmatan ya ce "kuyi haƙuri don Allah,ni na tsaida ita." Suka dube shi da niyyar yi mishi rashin kunya, sai suka ga yayi musu ƙwarjini, duk da haka sai da ɗayar ta ce, ta tsaya taɗi ne shi yasa zamu dake ta, ya miƙa hannu to ku dake ni, shiga Pretty,Ruƙayya ta ce bari kawai Dady ni su dake ni, ƴanmatan suka ce wuce ki shiga kaima mun yafe.


Gidan Hajja ya nufa sam yama manta cewa sun yi faɗa. Ya shiga falon, Saude ce a ciki tana shara, ya zauna kan kujera yana faɗin "Saude ina wannan ragwargwajajjiyar tsohuwar ne?" Kafin tayi magana sai ga Hajja ta fito daga ɗakin barcinta, ta dube shi da son ta bashi haushi ta ce, "kai amma wannan da rashin zuciya yake, ina ce jiya mun yi faɗa da kai? Ni da kai mun yi hannun riga." Sannan ne ya tuno jiya fa sun yi faɗa da Hajja, amma sai ya share ya dube ta ya ce, "Allah ni kin gama na manta,matsalarki kenan kishi don kin ji na ce zan ƙara aure shiyasa kika tsokane ni faɗa don na fasa, to ba zan fasa ba,je ki kawo min Break." Ta ce "kai dai kawai ka wayance ne don kada na hana ka abinci na."


Yana cin funkasu suna hira, ta ce "In ce Hausi kuke ce mata ko me? Ƴar wurin abokin Baban naka ita ce ku ka daidaita ko?"


Ya dube ta. "Hafsi kike nufi?" Ta ce, "ita." Ya ce, "Ina,nifa wannan ba wani sonta nake yi ba,dama ita ce take haukan ta, da nace ma Dad bana sonta Momy ta ce su bar ni." Hajja ta ce "Yarinyar kirki ta taɓa zuwa nan ta gaishe ni har da ƴan kuɗi ta bani." Ya dubi Hajja yana dariya, ya ce "Ok,kirkin kenan ta baki kuɗi ko? To ni dai bana sonta."


Hajja ta ce, "kar ka sota ina ruwana, na maka sha'awarta ne." Ya ce "To ki daina, zan kawo miki Ruƙayya sai tafi baki sha'awa." Ta ce, "To Allah yasa ƴar gidan masu mutunci ce." Ya ce, "insha Allahu sai kin yi farin ciki." Ta ce, "To Allah yasa haka" ya ce "Amin." Suka ci gaba da hira yana mata bayanin yanda yake son pretty ɗinsa. Hajja ta dube shi sannan ta ce "Yau kun ji zancan banza da sunanta Ruƙayya yanzu naji kuma kana kiranta da suna irin na Kirista,kiristi ka ce kai ko wa?" Dady ya shiga tuntsura dariya har yana ƙwanciya ta ɗaga carbi ni fice min mai abin haushi,me ake kuma da wata kiristi ." Ya miƙe cikin dariya,yana laluban key ɗin motarshi, ta zuga mishi carbi "Ka fice min nace shi kuma uban naka in yazo sai na gamu dashi,zan ji in shine ya ɗaure maka gindin ka auri Kirista."


Dady ya lalubi key ɗin motarshi ya wuce yana dariya.


A mota ya kai hannu yana shafa gefen wuyanshi inda Hajja ta same shi da carbi, ya ce "kai tsohuwar nan fa ta sameni da ƙyau,ji nan sai zafi yake min."


Har ya kai gida dariya abin yake bashi. Dad da Momy sun jero Dad ya buɗe ƙofar mota zai shiga sai suka hango ɗan nasu,don haka sai suka zuba ma motarshi ido,kusa da su yayi parking da dariya ya fito ya nufo su, Momy ta dubi Dad, Son ɗinka yau fa na ganshi cikin farin ciki." Dad ma cikin dariya ya ce, "Ƙwarai." Daidai lokacin ya iso. Dad ya dube shi, "Son yaya dai?" Cikin dariya ya ce, "Hajja ce ta bani dariya, ya faɗa musu yanda suka yi da Hajja,suma dariya suka yi. Dad ya fita su kuma suka koma cikin gidan.


Dady ya dubi agogon dake manne a cikin ɗakin barcinshi, to 5. Yayi ɗan tsaki, "biyar ɗin ta ƙi tayi." Ya raya a ranshi, don haka sai ya janyo durowar gefen gadonshi rafar kuɗi biyu ya ɗauka ƴan hamsin-hamsin, ya saka a aljihunshi ya isa gaban madubin dake manne a bangon ɗakin ya dubi kanshi,yayi ƙyau cikin fari tas ɗin boyil mai tsadar gaske, ɗinkin 3ƙwata ne ya ɗauki turaren for ever ya fesa, sannan yasa hula saƙar Dubai, ya ɗora.


A kitchen ya samu Momy, sai na dawo, ta dube shi,kai amma kayi ƙyau, sai ina? Cikin murmushi ya ce, Kabala zan je, ta ce sai ka dawo ka gaida Hajja da ƴata Ruƙayya, cikin jin daɗi ya ce, to.


Daidai lungun su Ruƙayya yayi parking bayan ya gaisa da masu shagon nan sannan ya shiga cikin lungun.


Sallama ya yi a ƙofar gidan su Ruƙayya don bai samu yaron da zaya aika ba,dama ya zo ne ya gaida Umma in son samu ne yaga Affa,cikin sa'a Affa ya amsa can bayan ƴan mintuna Affa ya fito, kallon Dady yake yi don shi dai bai san shi ba. Hannu Affa ya miƙa ma Dady amma sai Dady ya noƙe gami da tsugunnawa har ƙasa ya gaishe shi. Hakan ne yasa Affa ya ji yaron ya birge shi.


Cikin sakin fuska Affa ya dube shi "Samari daga ina?" Dady ya kuma sunkuyar da kai, sannan ya ce, "Affa ni dai sunana Yusuf, kuma ni ne wanda na buge Ruƙayya, na zo ne gurinka." Affa ya ce, to shigo ciki Yusufu." Umma tana shara suka shiga har ƙasa Dady ya durƙusa ya gaida Umma, sannan Affa ya ce Bismillah,Yusufu Dady ya shiga ɗakin Affa da sallama, ba komai a ɗakin sai katifa irin ta rimi ɗin nan sai wani ɗan teburi mai ɗauke da litattafai na addini sai ƴan kayan shi dake rataye jikin ƙusa,ƴar tabarma da ke shimfiɗe a gefe nan Affa yayi ma Dady umarni ya zauna, sai dai duk da haka ɗakin ya burge Dady kasancewar shi tsaf ga ƙamshin turaren wuta.


Bayan Dady ya zauna, sannan ya dubi Affa ya ce, "ya kasuwa da sauran hidimomi?" Affa ya ce, "Alhamdulillahi Yusufu." Dady ya sunkuyar da kai,yana son yayi magana amma yana jin kunya, Affa ya kula da haka, shi yasa ya ce kada ka damu Yusufu,sanar da ni abin da yake tafe da kai." Dady ya yi ƙarfin hali sannan ya ce, "Kamar yarda nace maka,ni dai na ture Ruƙayya akan titin Indifendence, to Allah da ikon sa sai kuma ya......" Dady ya kasa ƙarasa maganar,yayi shiru yana ƴan soshe-soshen kai.


Affa yayi murmushi sannan ya ce, "Kada ka damu, ina sauraronka." Dady ya ci gaba da cewa, "Sonta nake Affa, to da na mata bayani sai ta ce ita tana jin tsoron kada ka ji labarin zakayi mata faɗa, sannan aƙwai yayunta guda biyu ba ai musu aure ba shi ne na yanke hukuncin in same ka inji ko zan iya ci gaba da nemanta?"


Affa ya dubi Dady da ido sosai, ya tsura ma Dadyn, tamkar mai wani nazari akan shi, shi ko Dady kai ya sunkuyar cike da fargaba da tsoron kada Affa ya ce ba zai ba shi ita ba.


Gyaran murya Affa yayi sannan ya ce, "yau kawai na soma ganinka amma zuciyata ta soka, ba dan kuɗin ka ba,ba kuma don ƙyau ko iya adonka ba Yusufa,sai don abu uku da na kula ka mallaka wanda zan so ace ɗan dana haifa ne ya mallaka, sai dai ni Allah bai bani ɗa namiji ba, to zanyi murna da samun suruki mai wannan hali. Na farko kana da tarbiyya na biyu kana da ilimi da hankali sannan naga wata alama a goshinka wadda ta nuna min cewa kai ɗin mai yawan ibada ne, ba kowa ke da wannan alamar ba, sai mai yawan sujjada, waɗannan halayen su ne suka ja ni naji ina ma ace kai ɗin ɗana ne. In ba matsala Yusufa zan so in san asalinku daga bakinka,don na yarda kai ba zaka min ƙarya na, domin yanayinka bai nuna kai ɗin maƙaryaci ba ne. Daddy ya ji daɗin yadda Affa ya yabe shi, shima sai ya ji son Affa gami da tausayin shi na rashin ɗa namiji, ya ɗaga ido ya dubi Affa sannan ya ce, Affa mahaifina Bakatsine ne, haifaffen garin kurfi,su biyu ne gurin mahaifiyarsu Hajja, ta na nan Kabala,haihuwarta goma amma sauran duk sun rasu sai su biyu,mahaifina da Yayanshi dake can Katsina. 


A da mahaifina ma'aikacin gwamnati ne, amma yanzun yayi ritaya kasuwanci yake yi,ni kaɗai suka haifa. Bayan na gama karatuna yanzun ina jiran a kammala min gurin sana'ata da mahaifina yake gina mini (ko saboda me Dady bai faɗi cewa Babanshi tsohon ɗan sanda ba ne, kuma yayi gwamna? Oho).


Affa ya dube shi "Yusufa." Dady ya amsa, na'am, Affa ya ce, na taɓa rantsuwa da akan ba zan taɓa bari ɗan masu hannu da shuni ya auri ƴata ba, saboda wasu dalilai nawa, sai gashi Allah ya sa min sonka tamkar ɗana. Zan iya yarje ma auran Ruƙayya in har tana sonka, zan yi azumi uku na rantsuwar da nayi a baya, na amince kaje ka nemi so ga Ruƙayya ni kuma zan cigaba da bincike ga mahaifanka."


Dady ya ji daɗi,don yasan mahaifinshi mutumin kirki ne, jama'a suna yaba halayenshi, musamman jama'arsu ta Katsina,kusan duk wani matashin da ya taso a Kurfi sai mishi sanadin samun aiki, Sojoji ne,Ƴansanda ne da dai sauran masu kaki. Hakan nan sanda yayi gwamna a Katsina ƴan Katsina sun ji daɗin shi, har sanda ya riƙe I.G wato Isfekto Janar na Ƴansanda ya bautawa jama'a tare da taimako, shi dai ba zai baka kuɗi ba, sai dai yayi maka hanyar samun kuɗin,in kuma kuɗin ka ce kana so to zai ce maka yaro da a koya maka kamun kifi da a baka gashasshen kifi wanne kafi so?.


Affa ya dawo da shi daga tunanin da ya shiga, "kar ka damu Yusufa,kaje ka nemi Ruƙayya na baka. Godiya Dady ya shiga yi, sannan ya ce, zan iya zuwa gurin ta ko? Affa ya ce ƙwarai zaka iya zuwa mana, don batun yayunta Fati da Murja duk da masu sonsu, yanzun maganar da muke tuni mun tsaida ranar bikin Fati,a son raina in haɗa da Murja, to natan ne ya ce sai dai yayi shawara, inda zai amince kaima ku sasanta sai in tarkata su gaba ɗaya in huta, tunda itama Ruƙayya ta isa auran,don dai ku ƴaƴan zamani kun fi son su girma, amma ai babu auran da ya fi irin ka auri yarinya mai ƙananan shekaru."

*FIN ƘARFI BOOK 1*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


                        Page 3

*Wannan littafin na kuɗi ne ₦600 idan kina buƙata kiyi magana ta wannan number 08140004302 ko wannan 09068032427 idan baki shirya ba ki bari sai kin shirya don Allah👏🏻*


Dady kanshi a sunkuye sai dariya yake yi, ya ce Affa na gode,ni zan wuce." Ya ajiye mishi rafar nan guda biyu, wato dubu goma, Affa ya ce a'a kada ka yarda mu ɓata ɗauki kuɗin ka,Dady ya juya zai yi ma Affa magiya sai yaga ba wasa a fuskarshi, sai yasa hannu ya ɗauki kuɗin, sannan ya ce, sai anjima, Affa ya ce, kada ka sake zuwa ka ɗauki kuɗi ka bani ba don su na soka da ita ba, Dady ya ce, to na gode Affa sai anjima, Affa ya ce madallah,ka gaida iyayen naka, ya fita.


Dady ya na ƙoƙarin saka takalmi su Ruƙayya da Yaya Murja suka yi sallama suka shigo dukkansu suna sanye da kayan Islamiyya. Cikin tsoro Ruƙayya ta dubi Dady shi kuma yana murmushi, ya dube su, Murja ma tayi mamakin ganin Dady a gidansu,dama yanzun a hanya Ruƙayya take bata labarin Dady,da duk yanda suka yi sai da ta sanar da Yaya Murja. Sun yanke shawarar Yaya Murja zata sanar da Umma, to sai gashi suna shigowa sai suka ga Dady ɗin ma a gidan su.


Murja ta dube shi, "ina yini?" Ya ce, "lafiya,ya makaranta? Ta amsa da lafiya, ya dubi Ruƙayya yana murmushi ya juya yana duban Murja yaga ta nufi gurin Umma dake haɗa ƙwanuka, ya ce "Umma sai anjima

" Ta ce, to ka gaida magabatan naka, ya ce, to ya dubi Ruƙayya ya yafito ta da hannu, ta maƙe kafaɗa ta shige ɗakinsu.


Murja ta shiga ɗakin "Ruƙayya ba ke baƙon nan ke kira ba? Ko ba shi bane Dady ɗin?" Ruƙayya ta ce "To ni Yaya Murja sai in cewa Umma me? Ana kirana? Gaskiya ina jin kunya." Murja ta ce, to kada kije ɗin,bai shafe ni ba." Ta fita ba tare da ta cire kayan makarantar ba, ta fito tuni har Umma ta soma ƙwashe tuwan. Yaya Murja tayi murmushi ta ce magulmaciya,yana tsaye jikin gidan ta dube shi ba ka tafi ba? Ya ce ai nayi niyyar in ta zama har a kira sallar Magriba in Affa ya fito in ce masa na kira ki kin ƙi zuwa, ta ce ka sanar da Affa ɗin ne? Ya ce,kina wasa dani, yanzun ma ya ce ya bani ke ko yau nake son aure za'a ɗaura mana dama albishir ɗin da zan miki kenan, anjima zan dawo ta ce wai don Allah da gaske kake yi ne ko da wasa?" Dady ya ce, "to ki tambaya zaki ji." 


Ya juya, sai anjima.


Wannan shi ne mafarin da soyayya mai tsanani ta ƙara samun gindin zama a zukatan biyu, kullum sai Dady ya je ga Pretty ɗin tashi yayin da ya canza mata kayan makaranta kala-kala, ya so ma ya canza mata makaranta zuwa ta kuɗi amma sai Affa ya hana, kasancewar Affa baya amsar kuɗi duk wata sai Dady ya saya musu kayan abinci tun Affa yana faɗa har ya haƙura. Ƴan layin nasu suna mamakin a ina Ruƙayya ta samo wannan matashin mai kuɗin, kullum cikin motoci na alfarma?.


Shi kam Dady ƙara son Ruƙayya yake yi ganinshi bata mishi ƙarama ba, kamar yanda su Hussain abokanansa suke faɗa,yana tunanin da ƙyer zaya barta ta gama makaranta. In an yi bikinsu ya yarda ta ci gaba da karatun.


Dady dake faman wannan tunanin yayi juyi sannan ya tuna da Sadiƙ abokinshi,har cewa yayi dama Murja ya aura,don tafi Ruƙayya ƙyau, shi ko ganinshi ƙarya ne don haka ya ba Sadiƙ amsa da cewa kai ka aure ta ni Pretty na zaɓa. Da wannan tunanin Dady barci mai ƙarfi ya ɗauke shi.


Sati Uku ya rage Birthday ɗin Dady, na cika 30years, kafin wannan lokacin ita kuma Hafsi Muktar ɗiya ga Alhaji Muktar abokin Dad zuciyarta tana tsananin son Dady .


Alhaji Muktar shi ne mataimakin shugaban ƙasa a wannan lokacin, ta kammala karatunta na Digree a fannin lissafi tana da ƙyau da iya tsara ado, itama tamkar Dady ita kaɗai iyayenta suka haifa, don haka suna tsananin sonta duk abin da take so shi zatayi ba ƙwaɓa bare tsangwama, tayi karatunta a Malesia farkon ganinta da Dady tun suna Abuja kafin ya tafi Spen ta maƙale mishi, da farko ya ɗauka sabo ne ashe ba haka ba ne, ita sonshi take yi tun tana ɓoyewa har ta gaji tayi mishi magana, ya ce shi ba wannan ne a ranshi ba,karatu zaya je.


Bayan ya gama ya dawo ta tuna masa tana nan tana jiranshi ya ce baya sonta, sai ta ruɗe ta shiga tashin hankali, daga baya sai ta sanar da Abbanta shi kuma ya tuntuɓi Dad, Dad yana ma Dady magana Dady ya ce, shi fa baya sonta, Momy tasa baki kan cewa babu wanda za ya matsa ma ɗanta,don ita sam bata yarda da irin tarbiyyar Hafsi ba, tun akan irin tufafin da take sawa.


Shi kam Dad har ga Allah yaso haɗin Hafsi da son ɗinshi,saboda wani dalilinshi da shi kaɗai ya sani, amma Momy tana hanawa sai ya haƙura saboda bai cika son ɓata mata rai ba.


Dady ya shigo falonsu da sallama, Momy ya gani tana ƙoƙarin ƙwashe kayan da Dad ya ci abinci, ya iso gurinta yana faɗin "Momy sannu da gida,kina ta fama da aiki?" Ta ce, to me zanyi in ba aikin ba, ya ce to Momy kin ƙi ƴan aikin kitchen kin fi so ko yaushe kina cikin aiki, ta dube shi, aikin nawa guda nawa yake daga ni sai kai da Dad ɗinka,mafi yawancin lokaci ma kai gidan Hajja kake tafiya. Dad ɗinka ma bai cika zama ba, to sai kuma in damu kaina? Masu aikin shara da su wankin bayi dai suyi, amma game da abinci zan dafa mana don ni nafi son nayi abinci da kaina, ya ce to Momy Allah ya baki lada,nima Allah yasa Pretty ta dinga yi min irin haka. Momy ta ce, "Amin" har ya juya sai Momy ta tuna ta ce, "Au! Muna fa da ƴan hutu." Ya ce, hala su Yusrar Katsina? Momy ta ce a'a Hafsi daga Abuja. Dady ya ɗaure fuska, sannan ya ce,ta dai zo yawonta ba wani hutu bata gama makaranta ba? Ko tana aiki ne? Da zata ce wani hutu? Ta dai zo kawai ta matsa min, kuma ranta ne kawai zai ta ɓaci,don ba zan matsa ma kaina ba. Momy ta tsura mishi ido sai da ya gama ta ce, to ina ruwanka da ita? Ka bari sai in ta matsa ma ɗin sannan kayi faɗan da hujja, ya nufi saman shi.


Sallar Magriba ce ta sauko dashi,Hafsi tana zaune sanye da riga da wando duka na jeans,kannan yasha gashin doki sam ya tsani mace mai ɗabi'ar Arna. Kamar zai share ta sai dai ya tuna an ce baƙonka Annabinka, don haka sai ya dube ta da ɗan yaƙe,Hafsi manya,saukar yaushe? Ta taso da fara'a tana fari,ɗazun nan na iso baka nan lokacin ta matso tamkar zata taɓa jikinshi,zo mu zauna mana nayi missing ɗinka da yawa, ya ɗan ja da baya ya ce, zan je masallaci ne sai na dawo, to ina jiranka.


Sai da yayi isha'i kamar kullum sannan ya dawo. Suna cin abinci da Momy ya shigo gurinsu ya nufa, Momy ta sa mishi farar shinkafa da miyar kayan lambu, ya ce Momy ina Dad ne? Ta ce tun ɗazun ya fita a zatona ma kuna tare a masallaci? Dady ya ce ba ma tare, ya dubi Hafsi sai faman cin abinci take yi, ya ce Momy ina mutumina ne banga ƙwalin ba, ta ce Hafsi bude firij din can ki dauko mishi yogurt din nashi na fama,ta tashi tana cewa dama yogurt din ne mutumin ka,wane iri? Momy tace Hollandia zaki dauko masa.


Dady ya dan tsakuri abinci kadan ya tashi,Hafsi sai kallonshi take yi,ta dubi Momy "yanzu Momy har Dady ya koshi?"


Momy ta ce "ai Dady bai cika cin abinci ba"gara ma na gargajiya irin su waina da dangin su fankasu, amma dan wannan sam basu dame shi ba,bar shi dai da shan wannan yogurt din na fama, kullum Hollandia kamar fadin Allah.


Ya fito cikin jeans baki da bakar shirt,ya nufo wajen su ya dubi Momy.


"Momy zan je Kabala"


"To ka gaishe su"


Hafsi ta mike "zan bika Dady" ya ce a'a ba gidan Hajja zanje ba,ta ce eh,zan bika"ya ce a'a ba zanje da ke ba,ta yi yanayin Shagwaba ta dubi Momy.


"Momy don Allah ki ce yaje dani"


Dady ya ce,"Momy in kin yarda to,sai naje da ita,kasancewar Momy in da ya nufa,sai ta ce a'a kinga tafiyar daren nan bana son ta,gun da dan nisa don haka ki bari gobe in zai fita sai yaje dake Ido na ganin ido,kin ji ko?" Momy ta fada cikin sigar lallashi.


Don haka sai Hafsi ta ce "to kaimin tsaraba"ya wuce yana cewa to Allah yasa kar na manta,ta ce in ka manta sai ka koma ya tafi yana fadin sannu Rukayya,bataji ba tace mekake fada? Ba ki ji ba,ya fada dai-dai lokacin da yake ficewa daga falon,ya nufi wajen motarshi.


       ***  ***  ***  ***  ***


Ta idar da sallar isha'i ta nufi gurin wata 'yar kyakykyawar jaka tasa hannu ta ciro ta daga jikin kusa,ka abin sallar ta koma ta zauna.


Kayan shafe-shafe ne a jakar,don haka tuni ta soma mutsika mai maitsananin kamshi, kayan shafan masu tsada ne,Dady ne ya siya mata su.


Ta gama ta mike ta nufi gurin kayan ta, after dress baka ta dauka ta saka aka kayan ta,Yaya Murja da Yaya Fati suna zaune suna dubanta,Yaya Fati mamaki ya cika ta, domin ta ga bakon abu kasancewar yau ta dawo daga makaranta ba ta taba jin labarin Dady ba.


Domin wancan hutun da sukayi a can Giwan ta tsaya, gidan abokin Affa, kasancewar hutun bashida yawa,kuma su ne masu fita.


Fati ta dubi Murja ta ce "Murja kina kallon sabon salo gurin Rukayya?"


Murja ta ce "Yaya Fati ai autarmu Rukayya zai wuya in ba tare zamuyi aure da ita ba,ke in samarin suka tsaya shirme zai yi wuya in bata rigamu ba.


Cikin mamaki Fati ta ce "me yake faruwa ne?"


Rukayya dai tana ta jin su Yaya Murja tana ta ba Yaya Fati labarin Dady,yaro ya yi sallama Umma dake tsakar gida ta amsa,yaron ya ce wai an ce Rukayya tazo a waje inji wani mutumi, Umma ta ce kace tana zuwa,tasa baki ta ce "Rukayya kizo ana kira" Bak'in takalmi ta dauko Fati ta dube ta ta ce,"Gayu mutanen Allah Yar auta" Rukayya ta ja gyalenta tana dariya ta fita.


Fati ta dubi Murja ta ce nayi mamakin yadda Affa har ya yarda Rukayya ta soma fita yanzun tana yar J.S,kin tuna sanda Yasir ya soma zuwa gurin Affa hanawa yayi wai sai na kai S.S, lokacin ma fa in kin tuna nafi Rukayya girma da cika, amma Affa ya hana sai da na shiga S S 2 sannan ya barmu.


Murja ta yi murmushi, sannan ta ce,daga ni har Umma mun sha mamaki wai ace Affa ya bar Rukayya ta na tadi,ba dan mun san halin Affa na rashin son abin duniya ba,da mun ce dan kudi ne,amma sanin halin Affa shi yasa muka ce kauna ce daga Allah.


Murja ta cigaba da cewa,baki sha mamaki bama sai kin ganshi,ga kyau ga kudi zaki sha mamakin yadda yake son Rukayya, sannan in kin ganshi a gaban Affa zaki yi zaton cewa Affa ne ya haifeshi.


Fati sai mamaki take yi,ji tayi tamkar ta tashi ta leka taga Dadyn da taji labarin shi yanzu.


Yana tsaye Rukayya ta fito ta hangoshi gurin da suka saba tsayawa,ta saki murmushi ita kam tayi sa'a sosai ta raya a ranta,tana tsananin son shi,shima murmushi yayi tare da jin farin ciki mai tsanani. So kenan.


Tana isa ya ce "Oh my pretty,kin dade baki fito ba,me yasa?."


Ta dube shi "na dade kenan?"


Eh nafi son da na aika ki fito tare da dan aiken"


Ta yi murmushi ta ce "Dady kenan"ya ce yau dai da rabon sai kin biya tara,ashe nazo a sa'a,nan ta tuna tace yi hakuri ka ji na daina, cikin sigar Shagwaba ta fada,kara birgeshi tayi ya ce to na hakura,kin san inason Shagwaba,dama nima Shagwababbe ne,kin ga sai mu ma juna.


Rukayya ta rufe fuska tana dariya, cikin hirar ne take sanar dashi dawowar Yaya Fati,nan yake ce mata sai ta kira Fati sun gaisa,Fati da Murja suka fito.


Ya dubi Fati ya ce "Yayarmu Fati kin dawo ashe?."


Ta ce "lafiya qalau" ya ce "an gama karatu lafiya?" Ta ce "qalau muka gama".


Sun dan taba hira inda yake basu amanar Rukayya,tare da rokonsu kada su bari ko kuda ya taba ta,suna dariya,suka ce sun dauki komai, amma banda na kuda, domin basu san sanda zaya hau jikinta ba. Nan suka shiga gida suka barsu.


Ya ce Prettyna ke kadai ce,kamarki daban,ta ce haka mutane suke cewa,sai ma ka gansu gaba daya da Yaya Sadiya da Yaya Suwaiba,dukkansu kamarsu daya,su farare ne shiyasa sukeyi min tsiya in mun hadu mu duka,sai suyi ta ce min auta mummuna.


Ya ce "to su basu gane bane,ai ma kinfisu kyau sosai" ta ce haka dai kake cewa,ya ce Allah bada wasa nake ba,kalar fatarki tana da matukar wuyar samu a nan kasarmu ta Nijeriya, fatarki tafi kama da na yan Etopia,kin san suna da fata mai kyau, sannan hancinki ba dogo ba ne kin san an daina yayin dogon hanci,bakinki yana da fadi lips din ki da kuma idanuwank masu sani  in kara sonki tamkar kwan zabo shaf dinsu.


Rukayya sai dariya take yi,ta ce gurinka ne aka daina yayin masu dogon hancin ko gurin wa? Ya ce Eh,gurina ne,ta ce dan nasan hanci yana karawa mace kyau dan dai banda shi ne shiyasa ka ce baka so. Ya ce naji ba komai ni dama yanda kike nan haka nake son matata ta kasance, ke fa? Ta ce.........

🖊️

*FIN ƘARFI BOOK 1*


                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


                        Page 4

*Wannan littafin na kuɗi ne ₦600 idan kina buƙata kiyi magana ta wannan number 08140004302 ko wannan 09068032427 idan baki shirya ba ki bari sai kin shirya don Allah👏🏻*


"Nima haka" ta fada tana rufe fuska gami da dariya.


Ya ce a'a ki sanar dani dama ni din irin mijin da kike so ne? Ta ce Eh, ya ce "gaskiya Pretty kina boye min son da ki ke min, amma bari ki zo gareni,dolen ki ki bayyana."


Sun jima suna hira kafin suka yi sallama,ta shiga gida bada jimawa ba sai ga wani yaro da wata uwar leda wai a ba Rukayya.


Yaya Fati da Yaya Murja ne suka duba kayan zannuwa kala biyar takalma da jaka kala biyu,sai kayan ciye-ciye da Yogurt Hollandia,Umma tace ai abin nan na yaron nan yayi yawa fa,Yaya Fati tace Umma da kanshi yayi ai ba rokonshi akayi ba, Yaya Murja ta ce,Yaya Fati baki gane nufin Umma ba,kin san aure nufin Allah ne,in Allah ya kaddara Rukayya ba matarsa ba ce fa? Yaya Fati ta ce kin san Affa baya yin alkawari ya kasa cikawa, insha Allah auta Rukayya sai Dady,ta fada tana duban Rukayya.


Rukayya kam daki ta fada tana murna,Dadynta ana son shi a danginta.



 ***     ***     ***       ***


Hafsi ta kalli agogon falon,karfe goma saura.


Wanda ya kasance shine falon kasa sai wata kofa da in ka shiga zata kaika wani dan madaidaicin falo mai dauke da kitchen da kuma dakin baki,da dai sauran su, Momy a dakinta ta sauki Hafsi.


Suna shiga sai ta zauna daga bakin gado shi kuma ya tsaya yana cigaba da bata hakuri, cikin rawar murya ta soma magana "Dady don Allah menene laifina don nace ina sonka? Me yasa Dady baka tausayi na don Allah ka taimakeni ka aure ni nayi maka alkawarin zan maka biyayyar duk da mace yakamata tai ma miji,ka ji? Cikin muryar tausayi take magana. Ya tausaya mata sai dai shi ba zaya yaudare ta ba,kuma karya bata daga cikin tarbiyyar da aka mishi,don haka sai ya ce "bazan yaudare ki ba Hafsi gaskiya ina da yarinyar da zuciyata take matukar so,don Allah ki yi hakuri Allah kema zaya yi maki zabi mafi alkhairi.


Ido ta zuba mashi tana tunanin Dady ya kuwa san irin son da take mishi,da har zai dubi tsabar idonta ya ce yana da wata wacce yake so? Tuni hawaye masu zafi da radadi suka soma sunturi a fuskata,don tsabar tashin hankali ta kasa magana sai dai ta kwanta a hankali ta rufe ido.


Dady ya tsorata da ganin irin hawayen dake fita cikin idanuwanta, ya matsa kusa da ita yana cewa Hafsi don Allah ki........"bata bari ya karasa ba, ta daga mishi hannu,sai ya yi shiru da hannu tayi mishi nuni da ya fita. Nan take kuwa ya yi dakinshi.


Yanda Hafsi ta kasa bacci tana tunanin Dady bai mata adalci ba,haka shima ya kasa bacci yana tunanin yadda zai da yi da Hafsi. Ya san cewa Hafsi tana son shi,to amma shi koda wasa bai taba jin sonta ba,tsananin son shi yana ga Rukayya ne, kuma shi kam ba mijin mace biyu ba ne,kuma Rukky din shi ta isheshi.


Da safe Hafsi ta soma hada kayan ta don komawa gida, Momy ta shigo same ta,ta ce Hafsi yanaga kina ta faman hada kaya,ina zaki? Maimakon magana sai kuka mai karfi ya kwace mata, Momy ta rungume ta tana lallashi,daker ta samu Hafsi ta yi shiru,kuma cikin dashewar murya ta soma rattafo mata abinda ya faru jiya tsananin ta da Dady.


Da yake hausawa suna cewa ciwon ya'mace na 'ya mace ne,sai gashi Momy har ga Allah bata ji dadin abinda Dady ya yima Hafsi ba. Ta ce "kiyi hakuri Hafsatu,kin ji zan mishi fada dan yana da wacce yake so ai bai dace mutum ya zo gurinka kai mashi wulakanci ba,don haka ki yi zaman ki in akayi birthday din nashi sai ki tafi,tunda na ce ma Hajiyarku sati uku zakiyi,yau kwananki nawa? Ai kinga bazasu ji dadi ba" haka Momy ta shawo kan Hafsi ta hanata tafiya,har zuciyarta tana raya mata kila ma in Momy tai mishi fada ya amince ya aureta.


Shi kam Dady koda Momy tayi mishi magana, sai ya ce "Momy bazan mata karya cewa ina sonta ba,domin kuwa ni ba ita zuciyata ke so ba" Momy ta ce "Duk da haka idan kana son gamawa lafiya da ita sai ka lallashe ta,gami da nuna mata aure nufin Allah ne. Dady ka san fa ba yadda ubangiji bai iya tsara lamuranshi ba, mai bi ma Hafsi ce matarka.


Da sauri ya mike kamar wanda yaga zaki, cikin daga murya yake ce wa, "haba Momy,haba Momy ya ki ke min fatan rasa pretty,kin san zan iya mutuwa? Cikin mamaki take duban shi.


"Zaka iya mutuwa fa kace Dady?"


Ya ce "tsaf,ni kadai nasan son da nikema yarinyar nan."


Jin hakan yasa Momy ta shiga tunani,lallai akwai matsala domin in har Dady ya rasa yarinyar nan komai zai iya faruwa,haka in baiyi sa'ar yarinya ta gari ba to lallai akwai damuwa in har ta fahimci irin son da yake mata kila ta wahalar da shi.


Momy ta dube shi.


"Dady ina jiye maka tsoron kar ka rasa yarinyar nan ka shiga wani hali muma ka saka mu,gara ka so ta baya-baya,in ka rasa ta sai yazo ma da sauki.


Dady cikin bacin rai ya ce "Momy fatan da kike min kenan?" Ya tashi ya fita fuuu, cikin fushi,sai gidan Hajja tayi matukar mamakin ganin shi cikin fushi irin haka,ta dube shi.


"Me kuma ya faru na ganka cikin fushi da tashin hankali tamkar bujumin Zaki? Kana ta huci" kwanciya ya yi akan kujera. Hajja ta ce "kai da wanene?" Ya soma magana ba Momy ba ce wai tace min bazan auri Rukayya ba" Hajja ta ce "Wacce Rukayya ko itace Kiristin da ka ke fada? Duk da yana cikin fushi sai da yayi murmushi,ta dube shi da kaifa nake, Ya ce Pretty fa nace kina ce mata Kiristi, Hajja itama ta hau fada, ai gara da ta hanaka dama ina son in je in samu iyayan naka nima da kazo ka kawo min kara ba goyon bayanka zan yi ba.


Ya ce to wai ke wayace miki su Kirista ne? Ta ce to baga sunan da kake kiranta dashi nan ba,gara kuma ka canja daga haka ta shige kicin,sai ma ya samu kanshi da son jin muryar Pretty dinshi,yaji haushin Rashin waya da batada shi bari zayasa Dad dinshi ya sayo mata,ina ma ya fara aiki daya siya mata irin tashi da layin MTN na dubu talatin.


Zumbur ya mike ya fita kofar gidansu Rukayya ya tsaya wato bakin lungun su,sai gata da kwanon waina zata wuce,shima yana ƙokarin shiga,taji kunya sosai domin ko wanka batayi ba,shi kam baima kula da hakan ba,ta ce me kazo yi gidanmu da sassafen nan? Ya ce ganinki mana,ina zaki haka? Ta ce zanje ne in siya ma Yaya Fati waina, yace har ina kenan? Ta ce can sama ne,ya ce to zo muje a mota,ta ce a'a kai dai tunda ka ganni ka koma,ya ce to muje in rakaki, zatayi magana ya ce muje bana son musu,haka yabar motarshi suka jera har gurin mai waina,shi ya amshi kwanon ya mika wai yaga maza a gurin,aka ce na nawa? Ya ce a cika kwanon ko nawa ya ci to sai a fada.


Samarin gurin tare da mai waina sai kallonshi sukeyi dan sun san wannan daga ganinshi yafi karfin wannan wainar.


Yaji mamakin da aka ce mishi dari da hamsin,ya duba bashi da dari biyu sai dai dari biyar,don haka sai ya mika mata,ta ce banida canji,yace ki rike kawai,be ma saurari godiyar da take mishi ba suka wuce abinsu suka barsu cikin mamaki,har kofar gidansu ya rakata,ta ce to ka bani kwanon in kai mata,ya ce to in kin kai mata kiyi zamanki dama ganinki nike son yi sai nazo da daddare.


Haka so da kauna ya cigaba da tafiya,tare da tsananin sha'awar juna, gurin Dady da pretty dinsa Rukayya, Hafsi ma yana dan sauraron ta don dai a zauna lafiya kamar yanda Momy ta bashi shawara.



Rukayya tana wanke-wanken kwanuka amma tunanin ta yana can wani gurin,Yaya Murja da take wankin kayan Affa,ta lura da yanayin autar tasu take ciki tazo tayi mata magana, amma sai taga Umma tana shara kusa da su,su kuma ga al'adarsu ba komai bane suke saurin bari Umma taji,sukanyi shawara ne tsananin su,inta gagare su sai su kai ga Yaya Amina haka nan in ta ki sai sukai ga Yaya Suwaiba,haka zasuyi ta yi har kan Yaya Sadiya in ko kikaga matsalar su ta kai ga Umma to lallai tayi kamari.


Bayan sun kammala komai suka shiga daki don karyawa,su tafi hadda kasancewar yau sati babu boko,ga koko da kosai a gabanta, amma ta kasa sha, Yaya Murja ta taba Yaya Fati dake kwance kan katifa tana faman karanta littafi (don ita bata zuwa hadda saboda makarantar kwana ta gama sai dai tana zuwa Islamiyya da yamma tare da su Murja).


Ta nuna mata Rukayya wacce tayi tagumi ta saka koko a gaba,Fati ta ajiye littafi ta ce "ke Rukayya" bata ji ba ta sake cewa "auta" suka ga shiru, Murja ta taba ta gami da cewa "Rukayya" firgigit tayi sannan ta ce "na'am" tsakiya suka taso suka sakata Fati ce ta fara magana,ta ce Rukayya menene matsalar ki da kika kasa sanar damu sai dai ki dinga tunani gaya mana muji auta? Kada ki damu mu din yan uwanki ne masu shirin baki shawara gami da sama miki mafita, Murja ta kara da cewa ki gode ma Allah da ya saki ka kasance cikinmu dominmu masu kashewa mu rufe ne, suka tsura mata ido.


Hawayen da ta jima tana makalewa suka zubo mata,ita dai tana tunanin yanda zata fara gaya musu damuwarta,can kuma sai ta daure ta soma magana.


"Dady ne jiya da yazo sai yace min saura kwana biyar zaiyi birthday kuma zan zo to shine na ce bazan iya zuwa ba,don ban taba zuwa wani party ba, shine maganar ta kaimu da yin dan sa'insa, shine ya yi fushi ya tafi har yana cewa ya hakura da yin celebrating din birthday din nashi,ko fa sallama bai bari munyi ba ya tafi.


Yaya Fati ta ce ke yanzu kukan me kike yi? Ta ce ni ina tunanin kada ya ce nai mishi wulakanci ne kuma ba haka bane ya kasa fahimta ta ne ban taba shiga irin wannan taron ba,bare nasu na masu hali, sannan nasan tunda ya ce min ya fasa celebrating nasan ba zaiyi ba,kuma ba karamin kudi aka kashe ba bari kuga katin gayyatar da ya bani jiyan kafin abin ya faru.


Ta mike ta dauko musu katin,shi kanshi abin ka dora kan T.V ne don kyau, Yaya Fati ta ce dakin ce mishi zakiyi shawara damu tukunna kafin ki aiwatar. Amma duk da haka yaushe zaya dawo? Rukayya tace shine nima ban sani ba,dan ko sallama bamu yi ba.


Murja ta ce "ki kwantar da hankalin ki tunda saura kwana biyar nasan zaya zo insha Allah kafin lokacin,sai ki ce mishi zaki je nasan tunanin ki zaki ce tayaya, to mu munsan yanda zamu yi kije ki dawo ba tare da Affa ko Umma sun sani ba,Fati ta ce tabbas nasan shi din bazai cuceki ba son gaskiya yake miki.


Rukayya ta ji dadi gami da yi musu godiya,ya'ya mata rahama ne,haka ta ce a ranta, sannan ta tashi ta shirya suka nufi hadda.


Ba karamin dagewa Dady ya yi ba yau ya hana kanshi zuwa gurin Pretty dinshi Rukayya,wai don ya nuna mata fushin shi,sai dai haka ya kwana ko runtsawa baiyi ba,koda garin Allah ya waye dakyer ya yarda ya kai dare ya shirya ya nufi gurinta don ya yasamu natsuwa.


Ita ma Rukayya wadda zuwa lokacin ta gama galabaita,da rashin ganin Dadynta tana kwance ko abincin dare ta kasa ci,ta soma tunanin kila ma shikenan ya rabu da ita, hawaye suka soma zubo mata daga idanu,wunin yau sukuku tayi shi gaskiya tana cikin tashin hankali har Umma ta gane koda ta tambaye ta kafin tayi magana Yaya Fati ta rigata.


"Umma tun jiya autarki take fama da ciwon ka." Umma tayi mata sannu sannan ta ce tazo ga magani a dakin Affan su ta dauka ta sha,haka nan yan'uwan suka wuni suna nuna mata cewa kada ta bari Umma ta gane suka bata misali da suma suna samun matsalar da tafi wannan da samarin su sannan su dawo su shirya don haka suka bata shawara akan cewa tayi hakuri kawai zaya  wuce.


Yaron da ya yi sallama ya gaida Umma sannan ya ce ana kiran Rukayya shi ne ya katse mata dogon tunanin da take yi, zumbur ta mike ta zauna Yaya Fati da Yaya Murja suka shigo Fati ta ce gashi nan yazo ki nuna mishi abin bai dameki ba,in ya miki magana sai kice yayi hakuri zaki je, Murja ta cigaba da cewa kuma ki tambaye shi wacce gudummawa zaki bashi,na taya murna a wannan rana,ya zaba Rukayya ta na murmushi tace inya fada ni fa bani da kudi.


Fati ta ce "ina ruwanki ke dai kiyi abinda aka ce"


Suka sata ta canza kaya gami da fesa turare mai sanyin kamshi,yana tsaye ya matukar kagara da jiranta,don ya matsu kwarai ya ganta,sai ko gata ta fito ido ya rattafa mata tamkar yau ya soma ganinta,kyau yaga ta kara mishi.


Da fara'arta ta isa gurinshi,bayan sun gaisa suka fada hirarsu,shima bai yarda ya nuna mata wani abu ba,kuma koda wasa baiyi mata maganar birthday din shi ba,ta kasa hakuri ta ce "wai ya maganar birthday din ka?" Ya ce "ai kin kashe maganar domin na fasa" ta ce "kada ka fasa don Allah"  ya ce to tunda kin ce inyi kin yarda zakije? Ta ce naji zan zo,ya tsaya yana dubanta,waya ce miki ki je kuma? Ta ce ba wanda ya ce min na dai ga ranka ya baci ne,shi ne dalili kayi hakuri ba zan sakeyi maka musu ba.


Wani dadi ya ji ya rufe shi,shi dai kam baima san me zaya ce mata ba,don tsabar murna ya ce "godiya kawai zan miki pretty,kuma zan tanadar miki kayan da zakiyi amfani dasu,ke zan zo muje kasuwa" to kawai ta ce mishi,ya ce to gobe ne zamu je ko yaushe? Ta ce kadan bari sai kazo goben sai na gaya maka lokaci, ya ce to shikenan ta ce "yauwa wai don Allah me zan saya maka a matsayin gift?" Ya ce komai kika bani zan so shi yarda baki tsammani,ta ce shikenan.


Yaya Fati da Yaya Murja sune suka shirya mata yanda zasu hadu a gidan Yaya Amina ganinta na farko kenan da ganin da Dady kuma ta taya Autarsu murna,don miji ne na nunawa tsara.


Katon Boutique suka je riga da siket ya zaba mata kala biyu dogayen riguna ma kala biyu masu kyau da tsada sai takalma da jaka,haka nan ana gobe birthday din yazo ya sameta,sun tashi daga makaranta,ya dauke ta ya kaita aka gyara mata gashi tare da gyara mata kunba da dai sauran su sam bataso zuwa ba,don da batason ya yi fushi ne,kuma Yaya Murja ta ce taje,koda taje gida sai ta ce ma Umma su zasuyi lesson ne sai uku da kwata suka dawo bata bari sun hada ido da Umma ba ta shige dakin su Fati da Murja sun yaba da gyaran da akayi mata, kada ki bari Umma ta gani in yaso in an gama shagalin sai kiyi kitso da sauri kayan kuma a daren ranar su Aunty Fati suka kai gidan Aunty Amina suka ajiye shima can suka ce yaje ya dauketa.


Washe gari Yaya Murja ta samu Umma da Affa take ce masu, Yaya Amina batajin dadi tace Rukayya ta taya ta aiki,haka kuwa sai ta tafi da kayanta na Islamiyya wai in lokaci zata wuce daga can,har Umma tana musu tsiya da cewa,wato don sunga Autarta mai kwazon aiki ce shiyasa kowa sai yazo ya ce bashi da lafiya tazo ta tayashi aiki, Murja ta yi dariya ta ce, Umma ai Auntar takice ba dai ƙokari ba. Affa ya ce to ta gaishe da Aminar Allah ya sauwake mata, suka ce amin.


Karfi biyu yazo ya dauki Pretty din tashi suka nufi gidan su Dady,tasa daya daga cikin riga da siket din daya saya mata,wanda kuma ya ce shi zata sa,sai ya ce ta saka cikin jaka idan sun je gidansu sai yasa Momy ta shirya ta da kyau,ta cika da mamaki tana dubanshi hannunta rike da lebenta, ya ce menene na mamaki? Momy tana da saukin kai kuma nasan zata so ki don kina da saurin shiga rai" murmushi tayi akan riga da siket din sai ta dora after dress,baka da dankwalinta.


Suna tafiya ta dube shi sai tuka mota yake yi,yana bin wakar P square a hankali ta dube shi ta ce,a gidanku za'a yi ne? Ya ce a'a bakiga sunan gurin a jikin katin ba? Ta ce ban gani ba nifa ban ma tsaya duba katin ba,ya ce don me? Tayi wani Takwa-takwa da fuska ta ce, to ba kaine kayi fushi ba,yanda tayi maganar cikin Shagwaba sai ta yi matukar birgeshi,ya rage tafiya ya tsaya akan titi,ya juyo ya dubeta,don Allah Pretty gaya min gaskiya,kin damu da fushin da nayi kuwa,tsakaninki da Allah zaki gaya min" Ta rufe fuska sannan ta ce,na damu mana,kasan banyi bacci ba?" Ya ce "kai naji dadi ashe kina sona."


Ya ce "nima ban runtsa ba sam, Pretty ban san ina tsananin son ki ba sai wannan daren,na azabtu Pretty ina sonki da yawa kada ki dinka batamun rai kin ji?" Ta dube shi yanda yake magana sai duk ya bata tausayi,ya ce kin ji ni? Idonshi yana duban nata ta ce,na ji, ya ce ki dubi cikin idona ki ce kina sona, ta sunkuyar da kai tana yar dariya, ya ce fada min ki ce ina son ka Yusuf, ta dube shi ta ce zan fada maka amma ba yanzun ba,ya ce kin cika wayo Pretty kullum sai kina cewa ba yanzun ba,to sai yaushe? Ta ce kai dai sai lokaci yayi,ya ce in munyi aure? Ta rufe fuska ta ce eh,ya ce in munyi aure Pretty bashin da nike binki yayi yawa,tace duk zan biyaka ya ce kullum sai kin ce min I love you Yusuf sau goma,safe da rana da yamma talatin kenan, dariya sosai take yi,ta ce dozin ma zan dinga fada ma kaga talatin da shida kenan,ya ce nagode sosai don Yaya Fati da Yaya Murja sun ce amana suka bani ke da nayi maki wani abu don dadin maganar ki.


Itama dariya ta saki,ya tada mota suka mike suka shiga wani katafaren layi,tayi mamakin ganin sai da aka daga wani karfe sannan suka shiga layin,ta juya tana kallon yanda yan sandan suka maida karfen suka sauke sannan suka koma mazaunin su.


Kofar wani katafaren gida suka yi horn,ta koma kallon kofar tamkar kofar gari katuwa, take kofar ta rabe biyu kowanne rabi ya yi gefe, sukayi cikin gidan nan kuma ta saki baki tana kallon ikon Allah tun daga bakin geta din tile ne har iya ganinta,ya juyo ya ce sauko ki jirani nan bari na kai motar can. Daga inda take tan hango wani dan lambu gefe ga kayan motsa jiki da wasanni irinsu kwallon kwando,dana tebur sai irin ruwan nan da akeyin wanka don nishadi,ga gurin hutawa da wasu runfuna na gargajiya masu ban sha'awa,ko da ta.....

🖊️🖊️

*FIN ƘARFI BOOK 1*


                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*


                        Page 5

*Wannan littafin na kuɗi ne ₦600 idan kina buƙata kiyi magana ta wannan number 08140004302 ko wannan 09068032427 idan baki shirya ba ki bari sai kin shirya don Allah👏🏻*


Ko da ta hanga gurin da ya nufa da motar sai taga runfunane gasunan kusan guda goma kowacce da mota a ciki,falawowi kuma sun ma gidan ƙawanya.


Shi kanshi gidan sai ka ce an ɗauko shi ne daga wani guri aka sa shi a tsakiyar gurin,suffarshi tamkar jirgin ruwa,tana cikin nazarin gidan sai ta ji Dady yana cewa to zo muje, wani abu ya latsa sai taga ƙofar ta buɗe, shine ya fara shiga tana nan sai ga ƙofar ta ƙara buɗewa ta shiga cikin wani shahararren falo ta gani irin na ƙasashen Turawa wanda suke gani a irin mujallun Turawan nan,ya ce shigo bari in kira Momyna,ɗaki ya nufa yana ƙwalawa Momy kira.


Anan ta dubi falon faɗarshi ma ƙauyenci ne domin ba zata iya ba,ya fito,ga kujera can je ki zauna, bari na gani ko tana sama wajen Dady ɗina,ya nufi ɗaya daga cikin tagwayen benayen dake falon can ya isko Momy suna ƙara magana akan Hafsi da Dad,be bi takan zancen su ba ya soma cewa Momy kizo ga Ruƙayya, Momy ta ce kaje ka hawo da ita ta gaida Dad ɗin ku,da sauri ya sauko,ya ce muje Pretty ki gaida Dad,ita dai duk jikinta yayi nauyi gani take Dad da Momy ɗin shi zasuyi mata wulaƙanci.


Suna shiga Dad da Momy ɗin shi suka bi Ruƙayya da kallo dukkansu sun zata wata cikakkiyar budurwa ce Ruƙayyan, Momy ta kauda mamakin ta ta dinga yiwa Ruƙayya oyoyo, cewa oyoyo yarinyata Ruƙayya zo ki zauna. Ƙasa ta durƙusa tana gaida Momy sannan ta gaishe,da Dad,ya amsa yana mamakin wannan ƴar mitsilar yarinya me ya ruɗi Dady da har yake ma yarinyar tsananin so haka.


Dady ya ce Pretty kinga Momy na da Dad ɗina,ki ɗauke su tamkar Umma da Affa kin ji? Cikin jin kunya ta ce,to,ya juya ga Momy ya ce Momy ga Pretty bari naje na ɗauko Hajja kin san in taji maganar zuwa gidan sha'ani bata barin mutum ya huta yanzu nasan tana can tana jira in ɗauko ta,ta kima wannan gilashin nata kamar fitilar mota, Momy da Dad suka sa dariya,Dad ya ce,wato Hajiyata ka ke ma ba'a ko? Shi ma yana dariya ya ce na tafi Momy, ta ce ka wuce da Ruƙayya sai ta zauna a falon ƙasa,ka bata abin sha kafin na sauko, ya ce to Momy, ina Hafsi da su Yusra ne? (Yarinyar Yayan Dad itama ta zo birthday ɗin) Momy ta ce sun je gyaran gashi, ya ce, to zo muje cikin kunya da ladabi ta miƙe ta bishi, Momy kam ta yaba da tarbiyyar ta sai dai fa yarinya ce.


Suna sauka Nan ya tara mata kayan ciye-ciye a gabanta dana shaye-shaye musamman Hollandia ya ce kisha sosai kuma kiyi ƙoƙari ki saba dashi,dan ni shine best drink ɗina, murmushi kawai tayi da sauri ya fita yana faɗin "bye Pretty sai na dawo kin ji."


Momy ta dubi Dad naga kana ta faman wani ɗaure fuska a gaban yarinyar mutane",Dad ya ce dole ne na ɗaure, dubi yanda fa yaje ya ɗebo wannan kwailar yarinyar,yanzun tsakanin ki da Allah wannan in ya aure ta ai sai ya yi sabon raino tunda me zata iya mishi" Momy ta ce kai dai kabar yaron yanzu da wayau, wannan ɗin da ka raina ta tana iya bashi kulawar da manyan mata ma baza suyi mishi ba.


Dad ya ce,da yake dai kina son ta shiyasa,Ni kam a son raina ya auri Hafsi kuma ga Yusra" Momy ta ce kai dai don Allah ka bar maganar nan kawai domin in ya ji fa ba zamu wanye lafiya ba, ta miƙe bari inje gurin ta.


San da Momy ta ke saukowa daga sama sai ga su Hafsi da Yusra duk sun ɗame da wanduna kan nan yasha mai sai sheƙi yake yi, Momy ta ce kun dawo? Suka ce eh,ta ce to ga baƙuwa nan ku zauna tare.


Yusra ta ce Momy daga ina? Momy ta ce baƙuwar Yayanku ce, sai duk suka dubi Ruƙayya, Momy ta nufi ɗakinta,Hafsi ta harari Ruƙayya ke kamar budurwar sa ce ko? Ruƙayya ta sunkuyar da kai ta kasa magana, Hafsi ta ce in kinje ki ce ma Yayar taki ga rama ta haƙura domin Dady nawa ne nan ni kaɗai,da sauri Ruƙayya ta ɗago kai ta dubi Hafsi, wani masifaffen abu taji ya taso ya tokare mata ƙirji.


"Dama Dady yana da wata budurwa shine ya ɓoye mata?" Ta juyo ta dubi Yusra itama ta balla mata harara ta ce daina kallona kuma munga wanda zai je dake wajen party ɗin dube ki kucaka kawai, Ruƙayya ranta ya yi mugun ɓaci tamkar ta tafi sai kuma ta ga in har ta tafi su Momy zasu ga rashin wayon ta, tunda ta kula ma ganin ta mishi ƙanƙanta suke yi. Haka ta haƙura suka ci gaba da muzantata, kafin Dady ya dawo gida ya cika da abokan Dady maza da mata don haka Ruƙayya duk a takure take ta ƙosa ta koma gida.


Shi ko Dady yana can suna ta ƙwamawa da Hajja ya tasa ta yana mata tsiya,wai baza ta je masa gurin party da atamfa ba sai dai tasa riga da wando koda siket,ita kuma ta ce ai ba ganin Annabi zanje ba,bare ai min ƙa'ida,sai in fasa abinda ba dole ba ne, ya ce zo dai muje dai, ashe Dady da akwai tsiyar da ya shirya ma Hajja. Yasan sarai bata son gudu da mota don haka suna shiga sai ya fizgi motar yayi baya da ƙarfi sannan ya yi gaba da gudu tamkar me tseren mota. Hajja duk ta firgice ta kama Saude ta ƙanƙame tana faɗin, "kaga don Allah tsaya,ka tsaya in sauka ko ka rage wannan gudun" Dady ya ce Hajja yau dai kam sai dai kiyi haƙuri dan sai yanda Allah ya yi damu,in da sauran ƙwananmu musha wuya mu tashi in kuma babu Allah ya jiƙanmu. Da farko dariya Saude take yi amma daga jin bayanin da Dady yayi sai itama ta tsorata ta hau faɗin "don Allah ka taimaka ka sauke mu," gudu Dady ya ƙara tamkar zasu tashi sama,sai faman magiya suke masa amma ko sauraronsu beyi ba suka gaji suka shiga salati,don tsoro Basu san ma an kawo gidan ba sai da suka ji tsayawar motar.


Dady yana fitowa daga motar sai yayi ciki da gudu yana masu dariya,Saude da Hajja suka fito, Hajja ta ce ina yake ɗan buhun uba,ni dai kam na bar ƙara shiga motarka,har gaba da abada mota indai taka ce ko ba kaine matuƙinta ba, to na bar shiga.


Saude ma faɗi take "haddani Hajja ai yau naga mutuwa ƙiri-ƙiri, sun shiga suna ta faɗa Momy ta tambayi su Hajja me yake faruwa suka sanar da ita, Momy ta na dariya ta ce "Ai Dady baya ji kiyi haƙuri Hajja shiyasa ya shigo ya yi saman shi da gudu ashe yasan tsiyar da yayo, Hajja ta ce ai na bar ƙara shiga motarshi ja'irin wofi,nan Momy ta zaunar da su tare da karrama surukar ta ta da abubuwan motsa baki, shiyasa Hajja ke son Momy.


Ta shiga ɗakinta Ruƙayya tana nan inda ta barta zaune kan capet kusa da gado,tun ɗazun ta kira Ruƙayyan dan ta lura irin abubuwan da su Hafsi da Yusra suke mata, musamman ma Hafsi ta ce ma Momy, wannan ƙanwar budurwar Dady ce ko Momy? Momy ta ce"ina na sani ni dai ya bani ajiya" gudun kada su yi mata ƴan tambayoyi game da makaranta duka fannin biyun wato Islamiyya da boko, ta gamsu da amsar da Ruƙayya ta bata na cewa tana J.S 3 going to S.S 1 Islamiyya kuma tana ajin sauka sannan tana hadda.


Momy da kanta ta shirya Ruƙayya cikin riga da siket domin sai ta ji ƴar hirar da suka yi da Ruƙayyar ta shigar mata zuciya sosai, tamkar ƴarta.


Sharaɓarta da damtsenta kurum Momy ta kalla tasan cewa nan gaba kaɗan sai mutane sun yi mamakin yanda Ruƙayya zata zama mace mai cikar halitta,bata saduda ba sai da taga irin baiwar gashin da Allah ya yiwa yarinyar,tsaf ta gyara mata gashin tasa mata wani sarƙa da ɗankunne masu tsada ta kawo mata wani takalmi dogo ya wuce guiwa, rigar ta ɗame ta tsam,siket ɗin me ɗan faɗi, Momy ta yi farin cikin ganin kyawun halitta irin na Ruƙayya, tasa mata turare sannan ta ce ta zauna ta jira zuwan su Dady don yana can yana shiryawa.


Dady ya shigo falo yana tambayar Momy ina ƴar amana? Momy ta ce wa kenan? Ya ce Pretty mana Momy har kin manta, cikin murmushi ta ce tana ɗaki na, ya ce to bari in gani kin shiryata ko yaya, ta ce kaje kasa direbobin gidan nan su soma ɗiban mutane masu mota a hannu sai su bisu don an min waya an gama shirya wurin.


Ya ce Momy sun fa soma tafiya wasu Abokaina ma can kawai suka yi ta sauka,ina zuwa ya nufi ɗakinta da gudu, zaune kan kujerar gaban madubi Ruƙayyar ce.


Yayi matuƙar mamakin ganin yanda Pretty ɗin shi tayi ƙyau,ya ce tashi lobely ɗin na tashi na ganki cikin jin kunya ta miƙe, ya ce kai Pretty ashe kina da gashi haka na ji daɗi ni kam ina son mace mai gashi, ta ɗan harare shi, ta ce to sai in ma ƙulle kaina in fasa zuwa, ya tsugunna a gabanta yana kama kunnuwa.


"Sorry My Pretty." Ya miƙe "bari naje na shirya."


Sun fito Dady yana zaton mota ɗaya zasu shiga da Ruƙayya Momy ta ce a'a,ba zata iya zama kusa da shi ba,ku wuce ku tafi dani je.


A mota Ruƙayya ta dubi Momy ta ce, "yanzu Momy ba ko ɗan gyale zan je kuma gurin ga mutane," Hannu Momy tasa ta rungumo ta kada ki damu Ruƙayya ina da dalilin yin hakan,kin san saurayinki mai jama'a ne so zai so Abokanshi da ƴan mata su ganki bakiyi ƙyau ba,kiyi haƙuri ɗan lokacin ne, Ruƙayya ta ce to amma Momy ina jin kunya, Momy ta ce daina jin kunya in an gama shikenan kin ga kada su Hajja su mashi tsiya dama ɗazun kina jin tana maku ke dashi.


Sun samu guri ya yi guri an cika ga abokan Dad gana Momy, ga kuma na uban gayyar Dady. Ruƙayya tasha mamakin yanda gurin ya tsaru abin sha'awa,kyandira ne aka kunna ga wani cake na gani da faɗa, bata taɓa irin wannan shigar ba shiyasa sai take ganin kamar ita ake kallo Momy ta gane haka shi yasa ko'ina tana riƙe da hannunta sun zagaye cake ɗin bayan an mai waƙa ya hura gyandiran sannan ya yanka cake ɗin Momy ya fara samawa, sannan Dad sai Ruƙayya, Hajja ma tana can a zaune ya bita ya bata Hafsi ta ji haushi sosai,sai hararar Ruƙayya take yi,suma su Momy sun bashi ya ce "Pretty ɗan bani" ta ce a'a kiɗa DJ yasa mutane na tashi suna rawa yazo gurin da suke a tsaye ita da Momy da ƙawayan Momy ya dube ta ya ce, Pretty zo muyi rawa, ta ce ban iya rawa ba, Momy ta ce ka barta je ka kai kayi tayi, ya ce shikenan Momy kin hana ta ko? Ya tafi Ruƙayya tana mamakin yanda Dady yake shagwaɓa kai hatta yanda suke rayuwar su tana mamaki.


Su yaushe Affa zai bar su suyi wani Birthday ba zai yiwu ba to yanzun ma daya san tana nan ai sai ta gane kurenta.


Sai da aka tsaya domin bada gift sannan ta tuna da nata a mota,ta dubi Momy ta ce "Momy nawa gift ɗin fa ya cikin motar da muka zo."


Momy ta ce,bari Isa direba ya zo ya ɗauko miki, wasu mata suna tambayar Momy ina ta samo yarinya ƴar mai ban sha'awa, Momy ta ce Hajiya Baturiya surukarku ce, Momy ta jawo ta ta miƙa musu ki gaida iyayen ki, har ƙasa Ruƙayya ta durƙusa tana gaida su Buturiya, Hajiya Binta ta ce ƴar gidan wanene? Momy ta ce baku san Babanta ba don ba Abokan su Alhaji bane Hajiya Asma'u dake can baya ta ce Abokansu ba ne ai in gwamnati ne ko shahararren ɗan kasuwa za'a san shi, Momy ta ce, to banyi wannan binciken ba dan ba shine damuwa ta ba, damuwa ya samu mai tarbiyya da hankali, Hajiya Baturiya ta ce da kin kashe Ɗanki kin kashe kanki in dai ƴar Malam wane ce ɗanki zai aura,za dai mu zauna da sauran ƙawayanmu.


Nan ya amshi ƙyaututtuka gurin mutane har ya gaji ruƙayya ce ta soma bashi, sannan sauran mutane duk wanda ya bashi Ruƙayya yake ba sai da hannunta ya cika sannan ya soma ba Momy, bayan an gama su Momy suka soma tafiya da Dad, Ruƙayya ta so tabi Momy amma Dady ya ce in tabi Momy ranta zai ɓaci, don za ta yi fushi da ita, sai ta haƙura ta tsaya sai dai jikinta a sanyaye yake tunda taji abin da hamshaƙan ƙawayan Momy suke cewa, sannan ga abin da Hafsi ta ce mata a gidan su Dady.


Ba yanda Dady bai yi da ita ba akan suyi rawa ba, amma taƙi ta ce ita bata iya ba dole ya haƙura ya je suna cashewa ga masu hotuna da na bidiyo har da ƴan jaridu, tana daga zaune ta hango Dady suna rawa da Hafsi,nan take sai ta soma tunanin lallai Hafsi budurwar Dady ce, haushi, takaici suka taru su ka sata gaba idanun ta ya cika da hawaye, ta soma tunanin lallai Dady zai zamo ba rabon ta ba domin tun daga yanda taga gidan su gashi su masu hali ne ta tuno hirar ƙawayan Momy zuwa kan batun Hafsi.


Bayan ma haka ta dubi ƴan matan da suka halarci gurin nan masu ƙyau da ban sha'awa ƴaƴan masu dashi. Ta kai dubanta gurin da suke rawa tana hangen yanda kowacce yarinya burinta ta yi rawa dashi.


Ta miƙe cikin fushi ta nufi ƙofar fita,Saddiƙ babban amininshi shine ya shigo san da zata fita, ya dube ta.


"Ruƙayya ina zaki je?" Bata kula shi ba ta fita tana tafiya a harabar Hotel ɗin amma ranta cunkushe da damuwa tana mai zargin kanta da shishshigi tare da kai kanta inda Allah bai kaita ba.


Bakin titi ta tsaya tana tunanin mashin zata hau ne ko mota? Kuma ina zata dosa da wannan shigar kamar ƴar arna,kota nufi gidan su Yaya Amina? Kai ko unguwar bazata iya dosa a haka ba,in kuma gidan su Dady zata koma to ma ina zata ce?kai idan  ma zata ce ɗin, ina kuɗin sai jaka ba komai a ciki domin ko gift ɗin da ta ba Dady bata san ko menene ba ita dai su Yaya Murja sun ce ta bashi.


Bata ankara ba sai dai taji tsayawar mota Dady da Sadiƙ da Hussain suka fito cikin sauri Dady ya je gaban ta "Pretty ina zaki je ne haka baki kya min magana? Me yake faruwa ne kimin magana,kai ta ɗauke can gefe fuskarta a ɗaure,nan hankali Dady ya yi mugun tashi yama rasa me zai ce mata, to shikenan shiga mota Pretty shiga mu koma ciki,ki sanar da ni me akayi miki, kuma menene ya taɓa min ke,ta ƙi shiga su Sadiƙ da Hussain suma suka sa baki suna bata haƙuri.


Ta ce,ni fa wallahi ba abinda akai min, kuma zan je gida ne, Dady ya ce to shiga in kai ki ta ce,ni fa bazan shiga motar ka ba,Sadiƙ ya ce to kai ne me laifin sai ka bada haƙuri tana share su ta soma tafiya Hussain ya ce ki tsaya bari na ɗauko tawa Saɗik kada ku bar ta ta tafi.


Dady kam kasa magana ya yi don duk hankalinshi a tashe yake,ya rasa to me yayi mata? Motar Hussain suka shiga dukkan su dan Dady bai koma takan motarshi ba,Sadiƙ dake gidan gaba kusa da Hussain shine ya juyo ya dubi Dady da ya tsura ma Pretty ɗin shi ido ita kuma ta kauda kai can gefe.


Ganin yanda ƙarara damuwa ta bayyana a fuskar Dady sai duk dariya ta kama Sadiƙ, ya ce cikin dariya "Dady ina muka dosa ne? Ya ce ku tambayi Rankishidaɗe ɗin, tana jin su ta share.


Sadiƙ ya ce "Allah ya ja da ran Madam ina muka dosa?" Ta ce ku kaini in ɗauki kayana gurin Momy in ya so ma na ƙarasa gida daga can,ku koma gurin ƴan matan naku.


Faɗar haka da Ruƙayya ta yi sai nan take Dady ya gano laifinsa, kafin ya yi magana Hussain ya juyo ya ɗan dubi Dady ka gano kurenka yanzun ko? Dady ya ce, na gane, ya dube ta Pretty na gane kina fushi akan muna rawa,matan nan fa ba ƴan matana ne ba just friends ne kinsan irin yanda nike sonki Pretty ba zan so wake ba.


Harara ta balla mishi idanuwanta masu ban sha'awa da girma suka firgita shi ta ce dole kace haka mana tunda baka son in sani, amma ɗaya daga cikin ƴan matan naka taimani kashedi dan rainin hankali har tana cewa wai tasan ni ƙanwar budurwar kace in naje in cewa Yayata kai nata ne ita kaɗai,watan ma ni ban kai matsayin budurwa ba,to ka koma kuci soyayya na bar mata.


"Oh My God,wane ne yayi min haka? Wace yarinya ce wannan ki gaya min ita." Ta ce kasanta ai.

🖊️🖊️🖊️🖊️

*FIN ƘARFI BOOK 1*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 6



Har suka iso gidan su Dady basu shawo kanta ba, suna shiga cikin gidan Momy ta ce yanzun nake tunanin ƴar mutane to maza ɗauko gyalen ki,kisa su kai ki gida bari na kawo miki tsaraba.


Dady ya bi Momy ɗaki ya shiga ya gaya mata yanda suka yi da Ruƙayya,ɗaki Momy ta kira ta tace ki ƙwantar da hankalinki Dady naki ne kin ji yarinyata,kada ki barshi cikin damuwa ke kaɗai yake so,ba ina bin bayan shi ba ne, a'a ina faɗa miki abinda na sani ne kin ji ko? Kai Ruƙayya ta ɗaga alamar eh,duk kuma sai taji kunya ta kama ta.


Ya dubeta "kinji abinda Momy ta ce ko?" Ta ɓalla mishi harara ya ce "Momy ta ce ko? Ta ƙara balla mishi harara, ya ce "Momy kin ganta ko, tana harara ta bata huce ba, Momy ma harara ta sakar mishi  gami da faɗin fita ka dame mu.


Yana fita Momy ta dube ta tace "ki zama mai biyayya a gare shi zaki sha mamakin yanda zaku zauna," sannan bana son kisa abin da ƙawaye na suka faɗa ɗazun a ranki, domin basu ne masu umarni ko hani akan auren naku ba,ki sa Allah a gaba,ƙara russunawa Ruƙayya ta yi sannan ta ce nagode Momy.


Hussain ya ce Rankishidaɗe to kuma daga nan sai ina? Ta ce ai shi yasan inda ya ɗauko ni,Sadiƙ ya ce Oga ina za'a nufa? Dady ya ce muje.


Sadiƙ ya ce ƴan mata na rubibin Dady tun daga Spain har nan gida Nigeria amma ya ƙuƙe shi dai sai ke, don haka dole ne muce miki Rankishidaɗe, Allah ya bar mana ke, ta ce ba ko zai barni ba tunda ya ɗauki Manzonsa.


Dady ya ce to ku bar wannan labarin domin ita Pretty kamar koda yaushe burinta shi ne ta mutu ta barni bamu kaiga aure ba, dariya suka saka mishi.


Ƙofar gidan Yaya Amina suka tsaya,Sadiƙ ya ce Malam ba sai ka fita ba muma ƴan matan mu suna can bamu je mun kai su gida ba,Basu san ma mun fita ba, Dady ya ce ina ruwana ni nace ku zo? Ai da kun tsaya gurinsu danni sai na taya ta ɗaukar tsarabar ta. Sun yi sallama akan sai yazo.


Idanuwan Ruƙayya sun kaɗa su jajawur hannunta yana dafe da mararta ta dubi Umma cikin yanayin ciwon mararta, Umma ta ce kai nidai wannan ciwon mara naki yanzun zaya ta da mutane tsaye, da har ina murna naga gurin wata uku bakiyi ba, ashe ya ce lafawa na yi ban tafi duka ba, ta ce su kuma waɗannan sun kama sun tafi gidan Amina ballantana su amso mata magani a samu ya lafa.


Daidai wannan Lokacin sai Dady ya farka daga baccin ranar da yake yi,a 3siter dake falon shi, mafarkin Pretty ɗin shi yake wai tana cikin halin rashin lafiya,jikinshi ya bashi cewa lallai bata jin daɗi don haka sai ya nufi toilet sama-sama ya watsa ruwa, sannan ya shirya uku da minti biyar lokacin da gudu gudu ya gangara ƙasa Momy dake falo ta bishi da kallo, yayi shirin fita ta ce Dady ina zaka da sauri haka? Sam be ma ganta ba sai lokacin, gurin ta ya nufa yana faɗin "sorry Momy ban ganki ba saboda hankali na baya tare da ni, Pretty ba lafiya," Momy ma cikin damuwa take tambayar yaushe? Ya ce may be yau ne ko cikin dare don jiya muna tare ni dai cikin mafarki na ganta tana ta birgima a ƙasa.


Tsaki Momy ta yi sannan ta ce "Dady kana ba ni tsoro fa yanzu dama akan mafarki ne ka ke wannan rawar jikin? Dady ina baka shawara ka bi a sannu kada Allah ya jarabce ka da hanaka yarinyar nan ka kasa tawakkali, kuma tashi hankalin shi ya yi ya durƙusa Momy ki dena min wannan fatan mana, Momy bana son bakin ki ya bini fa, Please Momy na.


Tausayin shi ta ji,ta kama shi "to tashi na daina amma ka natsu,gaka mai natsuwa da kamun kai har wasu ƴan matan shakkar tunkarar ka suke yi wasu suna ganin kanada girman kai amma game lamarin Ruƙayya duk sai ka firgice ka fita haiyacin ka Dady.


Ya ce ba zan iya faɗin irin son da zuciyata ke ma Pretty ba,da zaki yarda sai in ce duk wani namiji da yabar tarihin so a duniya,da masu barin gida, masu kashe kansu,ba su kai ƙwataƙwacin son da nake ma Pretty ba,na yi alƙawari tsakanina da Ubangiji duk ranar da na auri Pretty sai nayi azumi na ƙwana uku tare da nafilu don godiya ga Allah.


Momy tsoro ne ya ratsa ta tare da tausayin shi,nan take itama taji bata son Dady tilo ɗan ta ya rasa Ruƙayya zata miƙe da addu'a,ƙwalla ta ji sun ƙwaranyo mata daga ido cikin dabara ta share don bata son ya gani,sai dai bata san ko mene ne dalilin hawayen nata ba,shin tausayin ɗan nata ne? Ko tsoron halin da zai shiga in ya rasa ta? Ta ce to Dady tashi ka tafi insha Allahu ma zaka same ta lafiya ba zaka sameta cikin ciwo ba.


Murja ta dawo daga siyen maganin Ruƙayya, daga chemis tana zuwa dai dai lungun su sai taga motar Dady, tana shiga yana tsaye daf da gidan su,ta ce a'a ƙanina ne? (Haka suke kiranshi ita da fati) ya ce "Ni ne Yayata ina ƴar gidan tawa ne?"ta ce wallahi bata jin daɗi Dady. Shi kanshi yayi mamakin yanda mafarkin shi ya zama gaskiya. Ya ce meke damunta ne? Ta ce ciwon ciki da mara, ya ce ya Allah cikin damuwa da tashin hankali Affa yana nan? Ta ce yana kasuwa,bari in kai mata magani, tamkar ya bi ta ciki,ya je daf da shiga gidan ya tsaya tamkar ya shiga ciki.


Murja bata jima da shiga ba yaji ihun Ruƙayya, "Wayyo Umma ciki na zan mutu." Ai bai san sanda ya afka cikin gidan ba sai dai ganinshi sukayi gaban Ruƙayya ya tsugunna Fati tana riƙe da ita Umma da Murja suna tsugunne a gaban ta,ya ce Umma su kamata mu je asibiti, Umma ta ce aje asibiti, Affan su baya nan a dai jira ga magani,da tasha zaya tsurga mata dama haka ya kan yi mata dan ma ta ɗan ƙwana biyu batayi ba,in fa abin yayi ƙamari har fa amai zakaga tana yi, ya ce ki bari mu je ku shirya su Fati sai ku kamata.


Shiru sukayi suna jiran umurnin daga Umma,salatin da Ruƙayya ta kuma sakawa shi ne sanadin da Dady ya zuba mata ido be ma sani ba, tamkar ya ɗauki jaririya haka yayi mata ba shiri suka biyo shi,tuni ma ya kusan fita daga lungun suka ce kawo ta mu riƙe saboda mutane.



    ***    ***    ***     ***


ALFA HOSPITAL ya kaita Murja ce tayi ma likitan bayanin yanda ciwon yake mata, tun da ita ke gida Fati tana makaranta tasan da ciwon amma bazata iya bayani ba. Tunda suka je duk gwaje-gwajen da akai ma Ruƙayya Dady yana gurin gani yake likitan zaya cire mata ne nan take, Likitoci biyu a kanta sannan suka yi nasarar shawo kan matsalar, sun mata allurar bacci kuma sun samu ya ɗauke ta, likitan ya buƙaci Dady ya biyo shi ofis. Bayan sun zauna ya ce ma Dady menene alaƙarku? Dady ya ce Dakta ita zan aura, likitan ya dube shi cikin mamaki matar da zaka aura? Dady ya ce eh, Dakta ya ɓoye mamakin shi ya ce, kada ka damu matsalar ta me sauƙi ce,kasan kowacce mace ta na da tata irin halittar musamman ma in ta soma al'ada, matsalar tata ba me damuwa ba ce zaya iya yiwuwa inta ƙara girma ta daina tunda kaga yarinya ce in ma bata daina ba da zaran ta yi aure ta sadu da miji shi kenan zata daina, cikin damuwa Dady ya ce, yanzun Dakta duk wata sai ta shiga irin wannan halin? Likita ya ce haka ne sai dai zamu rubuta mata magunguna da zaran lokacin al'adar nata ya zo sai ta rika shan magungunan.


Zufa ce ta keto mishi yanzu duk wata haka Pretty ɗin shi take shan wahala? Ya tambayi kan shi, ya dubi likitan Dakta amma kana ganin ta isa aure yanzu? Ina nufin ba zai kasance da ƙwara gare ta ba? Dakta ya gyara zama sannan ya dubi Dady,ba wata ƙwara bayan haka ma taimako ne gare ta tunda sai ta hakan ne zata samu lafiya, Dady ya ce nagode Dakta yanzun yaushe za'a sallame ta? Likitan ya ce ko zuwa dare ne domin da ya sake ta shikenan, Dady ya ce a'a ta kai gobe dan dare ne abin ji, Dakta ya ce shikenan, suka yi hannu tare da sallama,har lokacin yana mamakin cewa Dady ne zaya auri wannan yarinyar,gata ƙarama kuma daga gani ƴar talakawa ce. Yasan kowanene Dady yasan mahaifin Dady ɗin domin nan asibitin kakar Dadyn take ganin likitan ido.


Shi kam Dady waya ya yi ma Momy ya yi mata bayanin abin da ke faruwa, sannan ya ce Murja ta je ta sanar da su Umma an ba Ruƙayya gado sai gobe.


Kusan magriba sannan Dady ya samu yaje yayi la'asar ana idar da sallar magriba, ya je gidan su tare da Momy suka dawo Asibitin har lokacin Ruƙayya bata farka ba Momy ta tausaya mata ta basu abincin da tazo dashi ta ce gashi.


Daidai lokacin Umma da Affa suka shigo har ƙasa Dady ya tsugunna ya gaishesu, Umma ta ce sannu da ƙoƙari Yusufa Allah ya baka lada, ya ce ba komai Umma ga Momyna ma tazo, kusa da ita Umma ta matsa suka gaisa sannan suka gaisa da Affa Godiya sukai mata, ta haba ai babu komai, ya matsa yana ma Ruƙayya addu'a, Momy ta ce bari na tafi.


Affa Ya ce to Dady kaima sai ka je gida sai gobe ko? Momy ta dubi Dady tana murmushi domin tun a mota ya ce mata shi fa nan zaya ƙwana a asibitin,ta ce a'a, ya ce tayi haƙuri don sonta da Annabi kada ta hanashi don ko gida ya ƙwana bazaya iya bacci ba.


Shiru ta yi mishi don tasan cewa Dad ɗin shi faɗa zai yi, Affa da Umma suka ce Murja da Fati su ƙwana da ita su bari su tafi gida..


Daidai lokacin likita ya shigo ya duba sannan ya bata magunguna,su Fati suka gyara mata ƙwanciya daƙer su Affa suka lallaɓa Dady ya bi Momy.


Affa da Umma tunda sun ga da sauƙi sai suka tafi. Murja da Fati sun ƙara tsinkewa da al'amarin son da Dady yake ma Autar su, Allah kenan.


Momy tana ba Dad labarin ciwon Ruƙayya, Allah ya sauwaƙe kawai ya ce don shi fa ba dan dole ba baya son yaron shi da Wannan Ruƙayyar.


Daga masallaci sallar asuba ko cikin gida be shiga ba,dama da key ya fito don haka sai ya suri mota yayi asibiti. Sanda ya shiga Fati da Murja suna sallah, Pretty ɗin shi tana bacci ido ya tsura mata yana tunanin shi ne kaɗai kenan zaya yi mata maganin wannan ciwon, shi kam zai matsa kafin wani watan ta zama tare dashi. Ko ba'a gama gidan na shi ba, da kamfanin ɗin ba,sun zauna a saman shi,har gari ya waye bata tashi ba, gidan Hajja yaje ya kawo musu abinci, sai kuma ga direban Momy shi ma ta aiko rigi-rigi da abinci,yana zaune gefen gadon ta farka tare da salati gami da miƙa.


Tana ganin Dady kusa da ita sai ta rufe ido da zanin rufarta, ya ce tashi Pretty ko na ji daɗi,don gaskiya kin ruɗa min ciki. Da kanshi ya haɗa mata tea ya so ya bata taƙi, Affa da Umma suma suka shigo da abin karin.


Likitan ya sallame ta don taji sauƙi sosai, Dady ya ɗebe su ya kai su gida, ya gana da Affa inda yayi mishi bayanin yana son ya turo magabatanshi amma Affa ya taimaka mishi kafin ƙarshen wata ayi auransu. Cikin mamaki ya dubi Dady ya ce "Yusufa" Dady ya ce "na'am" Affa ya ce Dady ko menene dalilin ka? Tunda nasan munyi da kai sai ta gama makaranta ko in lokacin bikin su Fati da Murja tunda ka ga Alhamdulillah, sun yarda rana ɗaya,sai kuma gashi kai yanzun ka ce nan da wata ɗaya. Dady ya sunkuyar da kai ƙasa, sannan ya ce dama bayanin likita ne game da ciwon Ruƙayyar, ya ce sai in tayi aure sannan zata samu lafiya, amma likitan zaya faɗi ma zan zo gobe sai muje.


***      ***     ****       ****


Likita ya yi ma Affa bayani sosai kuma ya gamu su, don haka shi ma sai ya yarda akan cewa Dady ya turo magabatanshi. Yana ma Momy bayanin komai itama kuma ta yarda gara ma ayi ta huta.


Shi ko Dad cewa ya yi sam be yarda ba ya za'a yi ma saboda ciwo ne tilo ɗan shi zaya auri yarinya bayan ga lafiyayyun mata masu son shi, shi fa bai yarda ba, Momy ta ce to kada ma ka soma wannan maganar Dady ya ji,kai dai kayi addu'a sannan kayi ma Yaya waya yazo daga Katsina su je wajen magabatan yarinyar. Dad ya ce kiramin Dady ɗin,ta ce ya fita yana gidan Hajja da ƙyar Momy ta shawo kanshi ya yarda.


Saboda Dad baya son auranshi yasa ya ƙirƙiri zuwa Abuja a ranar asabar ɗin da Yayan na Dad zaya zo daga Katsina,dan zuwa neman auran ɗan nasu.


Alhaji Musa Yayan Dad da Alhaji Muktar aminin Dad baban Hafsi da Alhaji Shehu abokinshi a gefen Affa kuma yayi ma ƙaninshi aike gida Katsina sa amininshi da maƙwaftan shi duk sun hallara.


Misalin ƙarfe huɗu Dady ya ja birki a bakin lungun su Ruƙayya Alhaji Muktar ya dubi Dady yaya ka tsaya? Dady ya ce mun zo cikin lungun nan ne. Suka dubi juna kowannen su ya sha mamakin ganin yanda unguwar take kaca-kaca da ƙafa suka shiga har gidan ya nuna musu ga gidan nan.


*AYI MANA AFUWA MUNYI MISSING PAGE 87 BABU SHI INAGA WAJEN BUGA LITTAFIN AKA SAMU MATSALAR👏🏻*


Surikin naka da salo zaya ce wani baya son kuɗi sai da ƴar zayayi kinji ƙarya fa,uban wanene baya son kuɗi,sai faman zage-zagen su suke yi,ran Dady a ɓace suka iso gida.


Shima Affa ranshi ya yi matuƙar ɓaci, sannan baya jin zaya yarda ƴarshi ta shiga cikin wannan zuri'a,zaya tambayi Yusufa ya ji ko akwai mahaifin shi a ciki? Ya yaba da mahaifiyar ta Dady Amina, inda mahaifinshi cikin mutanen nan to ko sai dai Dady ya yi haƙuri. Affa bai cewa Umma komai ba,ya dai nuna musu an sa rana sati huɗu kuma ga kuɗin gaisuwa nan dubu hamsin. Umma ma tayi matuƙar yin mamaki,sai dai batayi magana ba jin bai ce komai ba.


Murja da Fati sun ƙuƙe sai zana yanda bikin Autar tasu zaya kasance suke, suna labarta yanda zasu shiryata su fito da ita,ita kam tana zaune kan sallaya tana jin su,gani take yi ma kamar abin ba zai yiwu ba, sai ta ji jikinta na bata abin ba zai yiwu ba tamkar faɗa ake yi. Tasan tana son Dady amma haka nan taji ta sare da maganar auran nasu, duk da ba wani abu ta ji game da zancan ba.


Fitar yau ta musamman ce Auta in ji Fati don haka zo,ƙwalliya sosai suka yi mata a yammacin na juma'a zasu shiga Kabala ne don gaida Hajja. Yellow ne less ɗin da tasa, takalmi da jaka suka zama farare tas, gyalenta fari mai ƙyau,ɗakin Umma suka shiga Fati ta ce Umma Autar ki ta zo miki sallama, Umma ta dubi Ruƙayya ki zama mai kamun kai a yayin tafiyar ku........

*Wannan littafin na kuɗi ne ₦600 idan kina buƙata kiyi magana ta wannan number 08140004302 ko wannan 09068032427 idan baki shirya ba ki bari sai kin shirya don Allah👏🏻*

🖊️🖊️🖊

️*FIN ƘARFI BOOK 1*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 7



Sannan me zaki kai ma Kakar tashi? Ko haka zaki je hannu rabbana?"


Murja ta ce "au na manta," Ɗakinsu ta koma jim kaɗan ta fito da leda ƴar ƙarama, gashi Yaya Fati ki bata inji Murja, Fati ta amsa ta ba Ruƙayya, turare ne mai ƙamshi da fararen goro masu girma da ƙyau, cikin jaka ta saka ledar, ta ce nagode Yaya Fati da Yaya Murja sai na dawo Umma zan yi yanda ki ka ce, sai na dawo.


Tana fita suka yi arba da juna sai murmushi,ya ce kin yi ƙyau fa Pretty,ta ce nagode, suna tafe a hankali yana jin daɗin yanayin da suke yanzun, cikin murmushi ya ce Pretty saura sati huɗu ki zama tawa har abada ina tunanin ya ya zanyi don farin ciki, Ruƙayya ta ce ni kaina ina murna da wannan.


Sun isa gidan Hajja sun same ta tana alwala, Dady ya ce to kuma sallar me zakiyi yanzun ƙarfe uku? Ta ce ban sani ba,kazo kenan, ya ce kishiyar ki ce ta zo gaishe ki, ta dubi Ruƙayya a'a lallai ga baƙuwa sannu da zuwa,baƙuwa shigo mu je ni bana kishi in dai wannan mijin ne tuzuru na bar miki. Har ƙasa ta durƙusa ta gaida Hajja, Dady ya ce Pretty ki daina durƙusa ma kishiya fa, Hajja ta ce kar kiji zancan sake gaki me ƙyau da ke me yaja miki auran tsoho gaki ƴar yarinya sabon jini, ita ko Ruƙayya ta rufe fuska da gyalenta tana ɗan murmushi. Sun jima sannan suka yi mata sallama, Ruƙayya ta bata tsarabar ta,sai shi mata albarka take yi.


Lokaci yana tafiya shirye-shiryen aure ya kasa ƙarewa. Dubai Momy da ƙawayanta guda biyu suka tafi don haɗo kayan aƙwati, shi kanshi Dady komai ya gani na Pretty ne wannan zaya ma Pretty ƙyau.


Game da Dad kuwa,sam bikin bai sa shi a kai ba, musamman ma da Abokanshi gami da ɗan'uwan shi suka yi mishi bayanin ƙananan mutane ne iyayen yarinyar,wato talakawa.


Kunji shirme sun mata cewa talaka da mai kuɗi duka Allah ya yi su. Sannan sune ma ƙananan mutane,su da basu san mutumci ba, Dad bashi da yanda zai yi ne shi yasa ya haƙura ya zuba musu ido don yana shakkar Momy, ba kuma tana mishi masifa bane,ɓacin ranta da tashin hankalin yaron shi ne ba ya so.


Affa ya samu dama suka zauna da Dady, ya tambaye shi cikin waɗanda suka zo ko akwai mahaifin shi? Dady ya ce a'a sai dai wan mahaifin shi wato waliyinshi. Affa ya ce Yusufa auranku ɗin nan da Ruƙayya sai na ganshi, cikin fargaba Dady ya dubi Affa "me nayi ne Affa, za ka min wannan horon don Allah kada kai min haka." Dady duk ya daburce ya fita haiyacin shi, tausayi ya ba Affa, don haka sai ya ce ka ƙwantar da hankalinka Yusufa za su ci albarkacin ka ne sannan da na mahaifiyar ka don ita kam bata ƙyamace mu ba, koda ta ganmu.


Yusufa ina da tabon da wani mai taƙama da muƙami da kuma kuɗi yayi min, wata rana zan baka labari,bana sha'awar hulɗa da masu hali nafi son daidai ni bani da ƙwaɗayin abin wani ko yaushe nafi son in kai duka da sandar da take hannuna. Allah yasan dan shi zan baka auran ƴata,ba don wani kuɗin ka ko ƙyau ba kamar yanda na taɓa sanar da kai,nasan kana da mutunci sosai kuma zaka riƙe min ƴata. Tashi ka je kada ka damu, haka suka yi sallama duk jikinshi babu ƙarfi tun daga ranar ya ƙosa ayi bikin nashi da Pretty ko hankalinshi zaya ƙwanta.


***     ****     ****     ****


Daren yau sauran kwana sha uku ɗaurin auran Dady da Pretty ɗin sa Ruƙayya, sun zo ne da Abokansa don su gana da ƙawayanta tare da kawo mata katin gayyata saboda rabama ƴan'uwa da ƙawaye. A'isha da Nabila su ne ƴan kusa cikin ƙawayan nata, don haka dasu ta haɗa abokan nashi don su zanta game da shirin bikin.


Ita kuma Dady ya ja ta gefe don jin abin da take buƙata, game da bikin. Ta ce bana buƙatar komai,yayi-yayi da ita amma ta gaddame, don haka sai ya bata wani ebulaf "Ga tawa gudummawar Pretty kuma kada ki ce min bazaki amsa ba, Nagode. Ta dube shi cike da mamaki kai da yin ƙyauta kuma kai ne da godiya? Yana dariya ya ce to dole ne nayi godiya Pretty tun da ba sosai ki ke amsar abin da ya fito daga hannu na ba, ta ce ka daina faɗin haka, nagode, ya ce babu komai.


Sun sha mamakin ganin check na zunzurutun kaɗi naira dubu ɗari, dukkansu sun tsora ta domin basu taɓa ganin irin kuɗin ba bare su mallaka don haka sai suka nuna ma Umma da Affa, amsa Affa yayi sannan ya ce su je su ƙwanta sai da safe ayi maganar.


Cikin nazarin Affa a wannan daren sai yaga baya hango auren nan nasu Ruƙayya,sai dai bai san dalili ba, ya ce kuma zai sa su Fati su fiddo kuɗin daga banki in yaso sai ya saya ma Ruƙayya gara da su shi kenan kuɗin su ya koma musu.


Baki ɗaya ƙawayanta da ƴan'uwa Dady ne yayi musu ankon bikin daga cewa in ga kalolin ankon naku Pretty,ko suna da ƙyau, shi kenan ya hau jidowa, tun abin yana ba su Ruƙayya mamaki har ya daina. Ana sauran ƙwana goma biki suka kawo lefe aƙwati set biyu masu huɗu sai dai suma ƴan kawo lefen sun sha mamakin ganin gidan da Dady ya rikito aure, sun ji dai an ce ƴar talakawa ce, amma su san tilis suke kamar haka ba,nan suka tasa Momy suna mata surutun ta ƙi nema masa mata cikin ƴaƴansu sai gashi dubi irin gidan da ya roro mata, Momy ta ce a'a sufa yaran nan na yanzun sai dai ka barsu da abin da suka gani suna so,ni fa ɗa na ɗaya tilo ne bani da wani sai shi,don haka dole ne nasa hannu biyu na amshi duk abin da ya kawo ya ce yana so,da haka ta kashe maganar.



****      ****      ****     ***


Biki yana matsowa su Yaya Sadiya da Yaya Suwaiba sai faman gyara Autar tasu suke yi da kayan harka yayin da Fati da Murja suka tsaya tsayin daka don ganin bikin ya ƙayatar. Sun kawo sadaki naira dubu saba'in abin har ya shiga ba Affa tsoro.


Abokai sun shirya za'a yi launching da kuma dinner. Sun kasa zaune da tsaye gidan su Dady yasha gyara musamman ma saman Dady inda zasu fara zama kafin a kammala gina gidan su.


Ana sauran ƙwana huɗu biki ƙwance yake kan sabon gadon shi da aka canza mishi su a ɗakin baccinshi,yana rungume da prem ɗin da Pretty ɗin shi ta kawo mishi, lokacin birthday ɗin shi, kullum sai ya rungume shi a yayin barcinsa, sannan yana karanta shi sau uku ko huɗu tamkar mai talawa,ya tsurawa falawoyin da ke jikinshi game da wasu ƴan tsuntsaye masu ban sha'awa,ido bai taɓa ganin ƙyautar da aka bashi tai mishi daɗi kamar wannan ba, ya tsura ma wani ɗan heart ido cikin shi an rubuta Each day is a gift from God.


Zuciyarshi ta nutsa cikin tunanin nan da ƙwana huɗu Pretty ɗin shi ta zama tashi, suna ƙwance wai ko ya zaya ji a wannan ranar? Kai sai Allah ne masani ya mirgina ya janyo filo tsam ya rungume filon zuciyarshi ta na tuna mashi da yanzu ya cire burinshi na barin Pretty in sun yi aure ya ɗan raine ta ta ƙara kumari tunda likitan ya ce hakan shi ne samun lafiyar ta, hango shi ya yi Pretty ƙwance a jikinshi tana ɗauke da ciki shi kuma yasa hannu yana ɗan liliya cikin, kullum tunaninshi kenan har ya yi bacci.


Washegari sauran ƙwana uku ɗaurin aure,su Fati da Murja suka kai Ruƙayya saloon an gyara mata gashi gami da wanke mata ƙafa zuwa gyaran ƙumba. Washegari mai zana fulawar dayis ta zo tana ma Ruƙayya da sauran ƙawayenta. Sun kaita an mata dilka ta yi kyau sosai gwanin ban sha'awa,daren ranar da Dady ya zo a mota suka yi hira.


Haƙiƙa Dady ya ruɗe da ganin yanda Pretty ɗin shi ta fito, waya ya mallaka mata GSM lokacin sai wane da wane ke riƙewa, layin ta na MTN nan ya dage yana koya mata.


Washegari jajibarin biki ranar ne launching,ƙawayen Ruƙayya da ƴan'uwa da abokan arziƙi duk an kammala sai ɗiban mutane ake yi ana kaisu N.D.A gurin da aka tanada don yin launching ɗin, Fati da Murja sun shirya Autar tasu cikin shiga ta alfarma leshin Dubai mai shegen tsada ga gwala-gwalai ko maƙiyin Ruƙayya ya ganta wannan lokacin sai ya so ta don ta hadu ƙarshe.


Sadiƙ shi ne ya jasu don zuwa gurin, a mota Dady ya gama ƙwarƙwacewa bai san sanda ya saki baki yana kallon ta ba, Sadiƙ ya ce kai mutumina kada ka manta da nifa a motar, Dady ya ce kai kuma ga mugun sa ido, ina tare da iyalina amma kana kalle mu.


Sadiƙ ya ce ina jiye maku yanda Kayan ku zasu ya mutse. Gara ma nata kai in wannan kayan naka ya cuƙwuikuye shi kenan, Dady ya yi murmushi ya ce sai dama kenan.


Sun yi launching ɗin su sun tashi lafiya ga gift da aka shiga rabo dangin ango dana amarya. Sun dawo suna motar Dady a bakin lungun su, Dady yana riƙe da hannun Ruƙayya ya ce muyi ma juna alƙawari Pretty ta ce wane kuma alƙawari Dady? Ya ce ke dai in kin yarda bani yatsan ki na alƙawari. Ta miƙa mishi, ya ce duk abin da nace kema ki ce, ta ce to, ya ce ruwa da iska itama ta faɗa, ya ce dare da rana zafi da sanyi, itama ta faɗi, ya ce na ɗauki alƙawarin itama ta ce ta ɗauki alƙawari, ya ce mutum ko aljan ba mai raba mu sai dai mutuwa, itama ta faɗa ya ciro zobe gudu biyu ya bata ɗaya ya ce tasa mishi,ta amsa ta sa mishi, shi kuma da zai sa mata ya ce ciwo ko tsufa bazai sa in barki ba na ɗau alƙawari,ya sa mata sannan ya dube ta cikin farin ciki.


Har kusan goma na dare suna tare da zai tafi ya ce sai mun haɗu gurin dinner in kuma na kasa daurewa zan zo kafin ɗaurin aurenmu ta ce sai na ganka ka gaida min Momy da kowa,sai da yaga ta wuce sannan shi ma ya tafi.


Tana shiga ashe nan jiranta ake za'a fesa mata nono a al'adarsu ta Fulani maimakon lalle. An kamata tana ta kuka suka nufi gidan Aminiyar Umma a can zasuyi zaman lallen. Baba Hajara Aminiyar Umma ce sosai.


Washegari ba zama shagali ya ɓalle har zuwa lokacin ɗaurin aure. Ita dai Ruƙayya ta rasa abin da ke damunta tun safe jikinta babu ƙwari, yanzun ma tana ƙwance akan gadon Baba Hajara ne yara suka shigo suna cewa motoci kala-kala sun cika layin dam,ga ƴan sanda kala-kala,da yake gidan Baba Hajara daf da lungunsu yake sai ta leƙo ta window ta tsorata da ganin yawan jama'ar motoci sai faman jiniya suke yi ƴan sanda kamar ƙasa harda shugaban ƴan sanda na yanzun. Gwamnoni kala-kala ga kuma ƴan jarida mamaki da tsoro ta shiga yi,ta dawo ta ƙwanta.


Shi kam Ango yana can suna shirin zuwa shi da Abokansa ana gama wa zasu wuce gurin walima daga can su nufi partyn da wasu Abokansa suka shirya musu, don haka ma ya soma tunanin yanda zai ga Pretty  don yace mata su shirya,nan ya tuno da wayar da ya kawo mata, don haka sai ya yi farin ciki,kiranta ya yi ashe ma bata tare da wayar, tunda takai gida taba Yaya Fati shi kenan bata kuma shiga shirginta ba,ɗakin ƙwanan su Fati dam da mutane sai suka ji wani kuka kamar na tsuntsu,da gudu suka dinga fitowa. Murja ta shigo don ta ɗaukar musu anko,don su gidan Yaya Amina suke tare da ƙawayan su da suka zo musu bikin Auta,sai taga mutane suna ta faman gudu,ta tambaya ko lafiya? Aka ce kukan tsuntsu ne a ɗakinsu,kai tsaye ta shiga gurin da taji kukan can ta nufa.


Sai taga leda sannan ta tuna da wayar Ruƙayya ta ɗauko ta ce "waya ce fa" kowa kuma sai son yaga wayar yake, bata san yanda zata ɗauki wayar ba don haka duk da kasancewar da mutane sai da Murja ta shiga gidan Baba Hajara saboda ta kaima Ruƙayya wayar, ganin ta ƙwance yasa ta ce,"haba Auta,me yasa bazakiyi wanka ba? Ina ƙawayan ki? Ta ce duk sun je gidajensu wanka.


Murja ta ce gashi wayar ki ce mijinki ya kira,ni kuma ban ma iya ɗauka ba, Ruƙayya ta amsa daidai lokacin da ya sake kira,da shike ya koya mata sai ta ɗauka tana jiyo muryar shi ya ce "Pretty ina ta kiran wayar ki baki ɗauka ba, ta ce yi haƙuri Dady gidan maƙwaftanmu nake,wayar kuma gida na barta, yanzun ma Yaya Murja ce ta kawo min, ya ce ok,dama friends ɗina ne suka shirya mana wani Party a Hamdala ki zama cikin shiri kafin a ɗaura aure,ki fa shirya sosai ana gama ɗaura aure in mun dawo walima zan aiko da motoci, ta ce to, kaima zaka zo ɗaura auran ne? Yayi dariya sannan ya ce in kin ji zuwa ɗaya kenan, shiryawa ma muke yi, ina Yaya Murja ɗin bata.


Ruƙayya ta ce "Yaya Murja gashi inji Dady, ta amsa sallama tayi sannan ya ce "don Allah yaya Murja ku gyara min Ita da ƙyau anjima kaɗan zamu je party zan turo da motoci,ta yi ƙyau fa sosai sannan don Allah kuba ƙawayan ta haƙuri kada su ga kamar an raina musu ne jiya basu zauna da amarya ba kinsan halin abokai kowanne da budurwar shi yake zuwa.


Murja ta ce babu komai bazasu ce komai ba sun ma gode ai da akaje dasu, ya ce to kuma ku zama cikin shiri fa, ta ce to, ya ce bani Pretty ɗin,ga mamakin Murja tana juyowa sai taga Ruƙayya tana hawaye, miƙa mata wayar tayi tana cewa gashi inji Dady.


Ruƙayya ta amsa ta ce "Hello," muryar ta ya ji ta canza, don haka sai ya ce yana ji muryar ki tana rawa? Ta ce bakomai, ya ce to dama zan tuna maki ne in ce kin kuma cin wani bashin fa,ina jin ki kakace Dady,ta ɗan yi murmushi sannan ta ce basu san sunan ka bane, ya ce Ok, haka ma ki ka ce ko? Zakiyi bayani in na ritsa ki,sai anjima I love You so much, ya kashe.


Murja ta zauna kusa da ita ta dafa ta menene ma'anar hawayen idanunki? Ruƙayya ta ce ni kaina ban san dalili ba. Murja ta ce to tashi kiyi wanka sannan ki ƙwantar da hankalinki.


Daidai wannan lokacin Affa da amininshi sun shiga cikin masallaci domin ɗaurin auren Ruƙayya da Yusufa (Dady).


Limamin masallacin juma'a na unguwar shi ne zaya ɗaura ma Ruƙayya aure tare da yardar waliyyinta. Daidai nan Dad ya shigo shi da Yayanshi Alhaji Musa da sauran manyan baƙi. Ɗagowar Affa ke da wuya don ya tarbi jama'ar Yusufa sai suka yi arba da Dad mahaifin Yusufa.


Cikin rawar murya ya ɗago hannu yana nuna Dad da yatsanshi yana rawa.


Al.... Alhaji me kuma ka zo yi nan? Ka kuma biyoni ne nan kaimin fin ƙarfin da kai min a baya?.


Ido Dad ya zuba mishi sannan ya ce "Kar dai ƴarka ce ɗana zai aura?" Cikin rawar murya Affa ya ce "kai ne mahaifin Yusufa?" Dad ya ce "tabbas ɗana ne" Affa ya ce to ko ɗan ka ne autan maza na fasa bashi auran ƴata, bazan haɗa zuri'ata da taka ba, azzalumi macuci......."


Kash mu haɗu a kashi na biyu don ji menene Dad ya yi ma Affa FIN ƘARFI akan shi?


Yaya kuke ganin wannan matsanan ciyar soyayyar zata ƙare?


Taku Halima Abdullahi K/mashi.

*Zaku iya samun ƙarshen labarin wato 2&3 akan farashin ₦600 idan kina buƙata kai tsaye kiyi magana ta waɗannan numbers ɗin👉🏻08140004302 ko wannan 09068032427*


*Idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya*


No comments