Takun Saka Complete

*_Typing📲_*







             *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_

                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_ZAFAFA BIYAR 2K22_




*_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma. Ka haneni rubuta abinda zai cutar da wanina da ni kaina. ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan bayin ALLAH da suka bar duniya😭🙏🏻_*.


_Masoya abokan tafiya ga ZAFAFANKU BIYAR sun sake dawowa a karo na biyar insha ALLAH☺️🤗_


*_______________________________*


*Chapter one*


............Sosai motocin ƴan sandan guda uku na farin kaya ke zuga uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai jiniya mai tsanani da zata iya tada hankalin duk wani mai tsoro. Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauka suke gefen hanya domin basu fili, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Sai dai kowa mamakinsa da tambayarsa shine (Mike faruwa haka?).

       Basu da mai basu amsa, kamar yanda nima bani da amsar. Sai dai mu cigaba da binsu domin sanin mike faruwar? Baki ɗaya.


★★


      A lokacin da waɗancan motocin ke tsere-tseren gudu mai kama dana kai agaji ko ceton rayuwaka anan headquarters na ƴan sandan jihar a kusan hargitse take a wani yanki na cikinta, hargitsin nata kuma yanada tabbacin alaƙa da waɗan can motocin.

      Kusan gaba ɗayan ma'aikatan department ɗin tsaye suke cirko-cirko a ɗakin na'urorin bincike cikin matuƙar taraddadi da ƙaulanin fargabar abinda ke faruwa. Yayinda kusan ma'aikata bakwai ke zaune sun duƙufa wajen sarrafa Computers ɗin cike da ƙwarewa da nuna matuƙar ƙwazo. Bakajin sautin komai sai na keyboards da ajiyar zuciyoyi.

      “Sir mutumin nan yana da matuƙar wayo, bana tunanin zamu iya dakatar da shi da ga zuƙar kuɗaɗen nan fa a wannan karon ma”.

       Ɗaya daga cikin masu sarrafa computers ɗin ya faɗa yana yarce uwar zufar daketa faman tsatstsafo masa a goshi, duk da ac dake aiki a ɗakin. Dafe kai wanda yake ma maganar yayi cikin matuƙar dagulewar tunani. Sai kuma ya ɗago a fusace yana kallonsa. Cikin tsawa ya daki desk ɗin gabansa yana kallonsu da idanunsa da ke jajur na ɓacin rai.

       “Idan har kuka bari ya cimma burinsa a wannan karon kuma bazan yafe muku ba. Har sai yaushe ne zamu iya daƙile wannan tsageran ɗan ta'addan yaron dake ganin a kullum yafi ƙarfin hukuma?!!”.

     Yanda yay maganar da bugar desk ɗin a tsawace ya saka da yawansu zabura. Wanda yay maganar yay saurin maida hankalinsa ga computer ɗin gabansa jikinsa na ɓari ya cigaba da sarrafata da sauri-sauri. Shima ɗayan dake gefensa tsawar ta rikitashi matuƙa, dan haka ya ƙara ƙaimi wajen sarrafa na'urar gabansa.

        Ogan nasu ya cigaba da masifar data sake hargitsa sauran harma suka rasa nutsuwarsu wajen sarrafa na'urorin. Ɗif komai dake wajen ya tsaya, hakan ya jawo yin tsitt ɗin ɗakin lokaci guda. Gaba ɗayansu suka zubawa Computers ɗin ido a hargitse, dan sun san aikin gama ya gama kawai. kamar yanda ya saba cin nasara a kansu yauma ya sake ci........




                 

        A ɓangaren motoci masu rera gudu bisa titi kuwa sun isa banki ne, inda suka iske mutane da duk ma'aikatan bank ɗin hankalinsu a tashe. Musamman ma shugaban bankin da yafi kowa birkicewa. Dan kuɗin da guy ɗin ya ɗiba ya tatsesune cikin asusun matar gwamna. Duk da dakatar da shi da aka samu nasarar yi ya zuƙi biliyoyin kuɗin da su kansu tsoron bayyanama duniya sukeyi saboda gudun abinda zaije ya dawo kuma.

      Cikin ƙanƙanin lokaci jami'an nan na hukumar farin kaya da ƴan sanda sun gama zagaye bankin dan ana ƙyautata zaton wanda ya aikata laifin ko wani nashi yana cikin bankin har yanzun basuyi nisa ba.

       An garƙame ko'ina da ina, duk wanda ke a ciki baida damar fita sai an bincikesa ciki da bai ɗinsa, musamman ma wayoyin hannu da bags.

      Al'amarin tamkar rufa ido har aka gama bincike mutane aka koma kan ma'aikatan banki babu mai ko alamar aikata laifin. Zuwa yanzu kuma babban ɗa ga gwamna ya iso wajen tare da mahaifiyarsa matar gwamna ɗin da securitys ɗinta. Hakanne yasa wajen ƙarayin tsamari dan ta nuna tsananin ɓacin ranta na ƙarancin tsaro da bankunan ƙasarmu ke fama da shi. Inda kake tunanin ka ajiye kuɗinka ka koma kai barci mai daɗi a gidanka shine kuma ya zama gidauniyar wawaso na salon ɓarayi masu aiki da ilimi, ta tabbatar musu bazata yardaba, kodai kuɗinta su dawo cikin asusunta kokuma ta ɗauki tsatstsauran mataki akan bankin da ma'aikatan cikinsa. Wannan shine ya ƙara ɗaga hankalin duk wani ma'aikaci dake a reshen wannan banki.

      Abu ya ƙara tsamari dan har C.P da kansa ya iso wajen tare da mataimakin gwamna da wasu manya-manyan ƙusoshin gwamnatin dan ɓarnace ta ɗunbin kuɗi wannan ɓarawo ya aikata wadda a ƙiyasi bama ya taɓa aikata kwatankwacin irinta ba a duk hatsabibancin da ya aikata, dan babu hukumar tsaron da babu sunansa a ƙasar matsayin mai-laifi saboda tsagerancinsa.

          Takaici da baƙin cikin halin da ake ciki ne ya saka wani ɗan sanda yima mabaratan dake zaune a ɗan gefen bankin korar kare, dan yanda suka zauna zuru-zuru suna kallon duk wainar da ake toyawa ne yasa takaicinsu kamashi. Ya fatattakesu tare da bada umarnin idan sunƙi barin wajen a saka musu barkonon tsohuwa maisa hawaye.

        Tuni suka fara haɗa kayansu suna barin wajen da sauri-sauri. Wani gurgu dake a tsohon kekensa (Wheelchair) ya murzata da ƙyar yana barin wajen, keken sai wani irin mugun ƙara yake saboda tsabar tsufan da yayi.

       Cikin layi na uku dake akan titin da bankin yake ya shiga, sai da ya iso saitin wani kango makahon dake biye da shi a baya yana raira ƴar waƙarsa da laluben hanya da sanda yace, “Boss mun iso point”.

      Wani irin ƙuuu! Yaja birki da keken, ya waiga bayansa ya kalli makahon da ya buɗe idanunsa ras yanzu, ɗauke kansa yay ya maida idanunsa ga ko'ina na layin babu kowa sai jefi-jefin yara dake wasa. Cak ya miƙe daka saman keke yana jan wani uban tsuki dasa hannu ya yaga daddauɗar rigir malun-malun ɗin shaddar jikinsa data fita hayyacinta saboda tsufa. Ya fincike rawanin daya aza akai da hular suma duk ya jefa saman keken.

        

       Ba ƙaramin ɗunbin al'ajab da mamaki bane suka lulluɓe ni saboda ganin lafiyayyen mutum ƙyaƙyƙyawa tsaye akan ƙafafunsa, a yanayin jiki dai daka gansa kaga matashin mai tashen ƙuruciya da cikakkiyar lafiya, amma abin mamaki fuskarsa ta tsoffi ce, hasalima harda tarin furfura a saman kansa da sajensa zuwa gemu. Sosai raina ke cike da ɗunbin mamakin hakan, dan nidai ban taɓa gani ba tunda nake. Ace matashin saurayi da fuskar tsoffi............✍🏻


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700


Duka gamayyar biyar din(1k)

1,000


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*




*_Typing📲_*



             *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*


                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_ZAFAFA BIYAR 2K22_


*________________________________*


*Chapter two*


.........Idanu sosai na ware domin ƙare masa kallo, sai dai isowar mashinan power bike guda biyar cikin layin ya rabamin hankali biyu, tuni makaho shima ya yaye kayan dattin jikinsa ya fito a lafiyayyensa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin wanda suke a saman mashinan ya faka nasa gabansa, ya sakko tare da sauke jakkar bayansa dake goye ya ciro takalma masu azabar ƙyau da sauran kayan bada kariya daga haɗari na mashin ɗin.

       Cikin sauri wani ma ya sakko a nasa mashin ɗin ya warware kujera ya ajiye masa sai kace wani sarki.

      cikin wani salo na isa da ƙasaita yakai zaune tamkar wanda ya samu kujerar falonsa, yanda yake abu cikin izza da isa ya sani yin zuru ina kallonsu.

       Wanda yake riƙe da takalmin ya kai tsuggunne gabansa ya fara zare masa takalman robar dake ƙafar tasa irin na masu kiwo ɗin nan duk sun fashe saboda wahala. Takalman ya shiga saka masa, shi kuma ya amshi hular kwanon ya ɗaura a kansa tare da sauran kayan. Miƙe yay cike da ƙwarewar ƙasaita ya ɗare bisa mashin ɗin.

       Makaho da wanda ya kawo masa mashin ɗin suma duk suka haye sauran mashinan da ƴan uwansu suke..

       Kasancewar nashi mashin ɗinne a gaba ya sake daidaitashi. Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama, ƙaramin yatsansa ya fara miƙarwa alamar (ɗaya), ya ɗaga na kusa da shi (biyu), yana ɗaga na ƙarshe alamar (uku) suka saki wata irin sautin ƙara data gigita kusan mafi yawan jama'ar layin. Tuni mata suka shiga gudun afkawa cikin ɗakuna, masu ƙarfin hali naɗan leƙowa suga mike faruwa?.

        Kasancewar layin da suke yana gab da bankin tuni saƙonsu ya isa kunnuwan jami'an tsaron dake zagaye da wajen. Har rige-rige jami'an tsaron keyi wajen hawa ababen hawansu, dan sunsan wannan singing ne na tabbatar da shiɗin na kusa da bankin.


        Daga ɓangarensu kuwa a wani irin mugun gudu suka harbo mashinan suka fito daga cikin layin, hakan yayi dai-dai da gabatowar motocin jami'an tsaron kwanar layin suma. Isowar jami'an tsaron ya sakasu danna wani abu a jikin mashinan nasu tuni hayaƙi ya gauraye titin baki ɗaya suka harba mashinansu tamkar walƙiya.


       ALLAH yaso a ƙaramin titi suke, da tabbas babu abinda zai hana haddasuwar gagarumin haɗari saboda yanda gaba ɗaya titin ya lulluɓe da hayaƙi, mai tahowa baya ganin mai tafiya.

      Sai dai duk da wannan hayaƙi hakan bai hana mota ɗaya cikin motocin jami'an tsaron bin bayansu ba a guje suma. Kusan mintuna uku cikakku hayaƙin ya ɗauka kafin ya baje, zuwa lokacin tuni mashinan nan sun ɓace ɓat daga yankin ma baki ɗaya tamkar na aljanu.

       Rai a ɓace sauran jami'an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa. Masu ƙarfin hali ne ke ƙoƙarin tsintar ƙananun takardun dake yashe a ƙasa alamar masu power bike ne suka sakesu tare da hayaƙin. Abinda ke a jiki ya ƙara harzuƙasu, dan kamar yanda ya saba barin sunansa idan ya aikata laifi a wannan karonma hakane. Sunan nasa ne a jikin takardar tare da zanen fuskarsa ta tsoffi raɗam.

      A zabure ɗaya daga cikin jami'an yace, “Kai! Wannan ai yana cikin al'amajiran dake a ƙofar bankin suna bara”.

     “What!!?”

C.P ya faɗa a matuƙar zabure.

       Manager da shima ɗaya daga cikin takardar ke hannunsa muryarsa a hargitse ya ce, “Tabbas wannan al'amajirin sati biyu da suka wuce na fara ganinsa a wajen nan. Amma dai wannan ya cika matsiyaci”.

         Zafi da ƙunar da zukatansu suke musu ya hana kowa ƙara magana. A kuma dai-dai lokacin matar gwamna da yaronta suka iso wajen suma. Dan sun gaji da jiran tsammani a cikin banki. Jin cewar basu kamashiba yasa ɗanta ya fara masifa tamkar zai haɗiye harshensa. Hakama mataimakin gwamna ya tabbatar musu karsu wuce awanni ashirin da huɗu basu kamo hegen ba.

    Daga haka kowa yabar wajen rai ɓace. Jami'an tsaron ma kowa ya koma inda ya fito domin ƙulla mai yuwuwa.




      Jami'an farin kaya harsun kama hanyar barin wajen suma suka dawo, sakamakon kiran wayar oga kwata-kwata na hukumar tasu da ɗaya daga ciki yayi domin sanar masa halin da ake ciki. Shine ya basu umarnin komawa su duba inda wannan gagarumin ɓarawo ya fito bayan barinsa banki.

      Sun shigo layin, inda suka iske mata da yara cike suna kallon kujera da kayayyakin da gurgu da makaho suka cire. Cikin mamaki suma suke duban kayayyakin, tare da ɗanyin tambayoyi ga mutanen wajen kowa na faɗin albarkacin bakinsa.

       Ɗaya daga cikin jami'an yakai duƙe yana ɗaga kayan dake bisa keken guragun. A mamakinsu sai ga facemask exactly da wadda ke jikin fuskar guy ɗin, kuma itace zane a jikin takardar da ya bar musu a titi.

       Komai basuce ba, saboda basusan da mutanen da suke tare a wajenba dan ya zama shu'umi kuma. Suka tattare kayan kaf har sandar makaho suka bar wajen..


      A lokacin da mashinan power bike ɗin can ke reren gudun tserewa wasu daga cikin ɗaliban babbar jami'ar jihar ke tururuwar fitowa domin neman ababen hawa da zasu maidasu gidajansu dan sun ƙare darasin karatu na wannan rana.

       Matasan ƴammata uku dake ƙoƙarin tsalla titi cikin matuƙar gajiya da yunwa suka daka uban tsale domin komawa baya sakamakon gabatowar waɗanan mashina dake gudu tamkar su kaɗai ne a titin.

       Ɗaya a cikinsu takai ƙasa sakamakon tuzguɗewa da takalmin ƙafarta yayi, ƙarar data ƙwalla ne ya maido mafi yawan hankalin mutane da idanunsu ke akan power bikes ɗin kansu. Ɗayar budurwar tai saurin kamo wadda ta faɗin tana ambaton kalmar “Subahanallahi Hafsat!”.

     Ɗayar kuwa a wani irin harzuƙe ta wurga musu wani abu dake hannunta, cikin sa'a kuwa sai gashi ya manne saman jikkar ɗaya daga cikin masu power bike ɗin. Cikin zafin rai da tsiwa tai alamar harba bindiga da yatsunta biyu tana faɗin, “Ku tafi duk iya inda kuke buƙata a tafin hannuna kuke, ko ƴaƴan ubanwaye ku a ƙasar nan zakusha mamaki, dan sai nayi sanadin da hawa power bike zai gagareku insha ALLAH”.

        Karaf wannan furuci na ƙyaƙyƙyawar matashiyar budurwa da shekarunta bazasu gaza sha takwas ba a kunnen ɗaya daga cikin jami'an ƴan sanda nan da suka biyo bayansu, sai dai dandazon ɗaliban daya rufe kusan rabin titin ya rage musu ƙaimin gudun da sukeyi suma domin son cimmasu. Sassauta gudun nasu ya basu damar jin furucin wannan matashiyar budurwa da tuni ta maida hankalinta ga ƴar uwarta data faɗi suna ƙoƙarin ɗagata tsaye dan da alama taji ciwo a ƙafarta ne.

      Cikin sauri jami'in nan da yaji furicin budurwar ya dirgo a motarsu ya nufi wani mai taxi, magana sukai da babu mai jinsu, mai taxi ɗin ya miƙa masa key ɗin motar.

       Sauran ɗalibai na ƙoƙarin tsaidama ƴammatan nan napep da basu shawarar su kai wadda ta faɗin asibiti dan da alama taji ciwo babba jami'in nan yazo gabansu ya faka taxi ɗin nan, batare da yin wani tunani ba suka taimakawa ƴar uwarsu ta shiga suma suka shiga.

         Sai da suka fara tafiya ɗayar budurwar tace, “Kai gaskiya kosu waye akan mashinan nan sun cika tantirai, dole ne a dinga cewa ƴaƴan manyan ƙasarnan sai sun sha kayan haukansu suke hawa power bike sunama mutane hauka da shi a tituna kamar nasune su kaɗai. Yanzu dan ALLAH bayan ALLAH ya taƙaita wahala ai za'a iya rasa rai ta dalilinsu ko?”.

         Wani banzan tsaki budurwar nan data jefa musu abu taja tana cije lip. A tsiwace tace, “Aiko a wannan karon ko duniya suka sha sun sako kansu a tarkon da iyayen nasu da suka saya musu mashinan sai sunyi dana sani insha ALLAHU. Dan wlhy har gidan ubanninsu sai nayi sanadin da za'a bisu ɗai-ɗai a kamo koda iyayensu zasu ɗauki mataki ne sai sunayensu ya ɓacin da bazasu sake gigin hawa power bike a cikin jama'a ba”...........✍🏻


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700


Duka gamayyar biyar din(1k)

1,000


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻._*

      


*_Typing📲_*



             *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*


                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_ZAFAFA BIYAR 2K22_


_________________________


Chapter Three


...........Hafsat tai azamar ɗago kanta tana dubanta, duk da hawayen da ke sharara a kumatunta na azabar da take ji a ƙafarta, cikin ƙarfin halin ta ce, *_“Muhibbat!_*  dan ALLAH karki sakamu a wahala da hatsabibancinki. Kwana huɗu kenan kacal da gama kashe wata wutar da kika kunno, indai dan nice karki damu, dama ALLAH ya ƙaddara sai naji ciwon nan koda bata sanadinsu ba, ina roƙonki kibarsu Ya Abubakar su huta da shegen tsokanarnan taki”.

        Harara Muhibbat ta zubama Hafsat da murguɗa baki tana juya idanu, harta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi shiru saboda isowarsu cikin harabar asibitin.

       Ko kaɗan jami'in nan baiso Muhibbat tayi shiru ba, amma kasancewar yasan aikinsa sai bai nuna hakanba, sai ma ƙoƙarin taimaka musu da yayi domin ganin an shiga da Hafsat taga likita akan lokaci.


      Da taimakon jami'in aka duba ƙafar Hafsat da ta samu tsagewar ƙashi, Zahidah sai godiya take masa saboda ƙoƙarin da yaketa musu, dan sunso su kira gida ya hanasu. Hanawar tasa kuma ta bama Muhibbat haushi, dan a ganinta ya cika shishshigin tsiyane kawai, musamman daya kasance duk wani motsinta sai ta ritsa idanunsa akanta.

      Tun tana hararsa a ƙasan ido da masa ƙunƙuni har takai ta fito fili tana dalla masa harara. Ganin dai ba daina kallon nata zaiyi ba a tsiwace ta ce, “Wai malam kallon fa? Dan ALLAH karka cinyeni a tsaye mana”.

        Sosai yanda tai maganar ya bashi dariya, dan tsaf ya gama fahimtar itaɗin matsiwaciyace ta gaske. Sannan babu tsoro sam a cikin idanunta kona sisin kwabo. Komai baice mata ba, sai ma ɗauke kansa da yayi kawai gefe tamkar bai jita ba. Taja tsoki tana murguɗa baki da miƙewa tabar wajen.

       Can gefe ta koma tana ƙoƙarin sarrafa wayarta cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci kiran da tayi ya shiga, sai da aka ɗaga sannan takai kunne tana faɗin, “Assalamu alaika Yaya”.

    Amsa mata akai da ga can, kafinma ya gama rufe baki cikin shagwaɓa taci gaba da magana. “Yah Uthman muna hospital ne”.

         A tsananin tsorace muryarsa ta bayyana, “Hospital Auta?! Waye bai da lafiya?”.

         “Oh Yaya calm dawn, Hafsat ce taji ciwo a ƙafa amma da sauƙi, dan yanzu haka ma an gama mata gyaran sunce tsagewan ƙashine”.

        “Ya ALLAH! Auta wai sai yaushe ne zakuyi hankali ku kam? Yanzu haka a wajen shegen rawan kan nan naku hakan ta faru?”.

        “Na rantse Yaya bafa da gangan bane, wasu marasa kirki ne suka kusan turemu a power bike”.

       “What?!. Power bike fa? Ku miya kaiku kan titin da masu power bike kebi!!?”.

       Yanda yay maganar a tsawace ne ya sata zabura, duk cikin yayun nata yafi kowa sauƙin hali bayan Yah Abubakar. Sai dai kuma idan ya rikice tafi tsoronsa fiye da kowa a cikinsu..... Cikin katse mata tunani yace, “Zan turo muku Ammar yanzun nan danni naje katsina ne..”

         Yana gama faɗan hakan ya yanke wayar. Kasaƙe Muhibbat tayi tana kallon wayar, yayinda gefen zuciyarta ke ayyana mata neman mafita. A fili tace, “Tab Yah Ammar! Wlhy bazan bari ya samemu a asibitin nan ba wannan ɗan matsalar”. Da sauri tabar wajen zuwa inda jami'in nan mai amsa sunan driver-n taxi yake da Zahidah.

       “Zahidah tunda sunce zasu iya sallamarmu gara mu wuce gida, dan na haɗa gurmi wlhy”.

     Zahidah dake mata kallon mamaki tace, “Gurmi kuma! Nami to?”.

       “Humm daga kiran Yah Uthman fa na faɗa masa shine wai zai turo mana Yah Ammar shi yana katsina. Ni kuma wlhy banason Yah Ammar yazo asibitin nan ya samemu saboda yafi gidan haya matsala kema kin sani”.

       Kafin Zahidah dake dariya tace wani abu jami'in nan yay saurin cewa, “Ai sunma sallemu daman, inaga ku shiga ku fito da ita kawai mana”.

        Harararsa Muhibbat tayi tana ɗaure fuska. “Ikon ALLAH sai kallo, wai ni kam bawan ALLAH ca'akai ka kula damu ne kokuwa? Taxi ɗinka muka hau ka kawomu inda muke buƙata, to sai mi kuma ya rage?”.

        Murmushi yayi idanunsa a kanta, “Sai ku bani kuɗina ya rage ƙanwata”.

       “Ya salam! Dan ALLAH kayi haƙuri bawan ALLAH. Wlhy gaba ɗaya mun shafa'a ne”. Zahidah ta faɗa tana laluben bag ɗinta.

      “Karki damu ƴammata babu damuwa. Nasan kuna a rikicene ai. Amma ƙawar nan taki ya kamata ta rage tsiwa”.

      Zahidah dake miƙa masa ɗari biyar tai dariya, “Kaga fita batunta ga kuɗinka mun gode sosai”.

     “Ai karki damu riƙe kawai sai na kaiku inda zaku yanzu sai na amsa”.

       “Malam gara dai ka amshi kudinka kai gaba, dan bazamu sake shiga motarkaba ɗan sarkin shiga sharo ba shanu”. Muhibbat ta faɗa tana hararsa.

       Saurin toshe bakinta Zahidah tayi itama tana hararta, “Wai nikam Hibbat kodai wadda tai miki wankan jego bata gasa bakin nan bane da baya barin kowa. Ina laifin bawan ALLAHn nan, kigafa ƙoƙarin da yay mana akan Hafsat”.

      Hibbat ta buge hannun Zahidah da haushi, “To dan kuma ya taimakemu sai ya ishemu da shishshigin jaraba. ALLAH ni banason shishshigi da ƙwala kai a faranti irin na wasu mazan”.

    Tana gama faɗa tai shigewarta ɗakin da Hafsat take. Duk binta sukai da kallo, kafin Zahidah ta maido kallonta ga jami'in. “Ayya dan ALLAH kai haƙuri. Ita haka take sam ba'a gane kanta tamkar mai aljanu”.

          Ƙaramar dariya yayi yana sosa tsakkiyar kansa da key ɗin taxi ɗin. Yace, “Kinga karki damu ni salon natama birgeni yakeyi, irin waɗanan sam ba'a cutarsu a duk inda suka shiga. Je kawai ki fito dasu na kaiku kafin a sake kirana ɗan shishshigi”.

       A yanda ya ƙare maganar cikin langaɓe kai kalar tausayi yasa Zahidah ƙyalƙyalewa da dariya tana shiga ɗakin domin su fiddo da Hafsat..


       Da ƙyar Muhibbat ta amince jami'in nan mai taxi ya ɗaukesu zai maida gida. Dan ko sai kumbura take a motar tana ƙananun ƙunƙuni alamar bataso hakan ba. Shi dai yakanyi murmushi lokaci-lokaci idan ya ɗago ya dubeta ta mirror yaga yanda take cika baki da iska tana harare-harare........


           ★.★.★.★.★.★


       Kamar yanda aka saba yau ɗinma tuni media ta ɗauka. Gidajen redio dana televisions harma da yanar gizo mutane sai tofa albarkacin bakinsu suke. Dan lamarin wannan gagarumin ɓarawo ya daina bama mutane tsoro sai al'ajabi da mamaki.  Kullum ji suke jami'an tsaro na farautarsa, mai makon ya tsorata ya ɓuya sai ƙarama gawurta yake a al'amuransa. Gashi babban abinda zai baka mamaki manya-manyan ƙusoshin ƙasar masu lasisin iya ɗaukar mataki yake bi yana yashewa da saka rayuwansu cikin tarkuna. Dan da wahala ya kafa maka ƙahon zuƙa daga ƙarshe baka koma ƙarƙashin binciken hukumar *EFCC🐦* ba, ko ka ƙare rayuwarka da ciwon paralysis saboda barazanarsa idan yay dirar mikiya aka kaddarorinka da kuɗaɗenka. Yanzu dai yanda ya yashe asusun matar gwamna bawai ya barta bane kenan. Duk da neman da ake masa ruwa a jallo cikin kwanaki ƙanƙani zai sake silalowa ya danƙara mata wani harbin mai zafi har sai ya kai rayuwarta ƙasa kwance zai barta.    

       Duk yanda ƴan jarida sukaso jin ta bakin jami'an tsaro da gidan gwamnati akan wannan al'amari abin ya gagara. Sun haƙura dole suna bada labarin iya abinda idanunsu suka gani da ɓarnar da wannan mutumi ya tafka a baya kafin wannan ɗin.

    Yayinda a gefe kuma jama'ar gari suketa tofa nasu. Wasu najin daɗin abinda yakeyi ɗin dan bawai a satar kuɗin manyan ƙasar kawai ya tsaya ba, har ƴan fashi da suka addabi mutane da ƴan ta'adda yakan kama waɗanda har yanzu babu wanda zai iya cewa ga inda yake kaisu ya ɓoye. duk da kuwa shima ɗin mai laifi ne a bayyane, wasu ko na jifansa da ALLAH wadai saboda suna ganin bashi da maraba da ƴan ta'addar da yake kamawa ai. Yayinda ƴan kanzagi ke zaman rubuta shaci faɗi su yaɗa a kafafen yanar gizo game da shi da ayyukansa..............✍


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k)



*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR




*_ALLAH ka gafartama iyayen mu😭🙏🏻_*

   


*_Typing📲_*



             *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*


                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_ZAFAFA BIYAR 2K22_


_________________________


*_Chapter Four_*


...........Suna baro cikin asibitin Muhibbat ta kashe wayarta dan ma kar Yah Ammar ya sameta.

        Tun farkon shigowa anguwar tace a saukesu. Amma sai Zahidah tace sam basu yarda ba a kaisu har ƙofar gida. Zata fara masifa Hafsat ta ce, “Kiyi haƙuri ya kaimu saboda bazan iya taka ƙafarnan ba Hibbah”.

       Shiru tayi bata sake tankawa ba har suka iso ƙofar gidan su Hafsat daya kasance a farko, sai nasu Zahidah, Muhibbat ce ƙarshe. Saboda ciwon dake tare da Hafsat ɗin ya sakasu cewa a tsaya ƙofar gidansu. Zahidah ta bama mai taxi kuɗinsa tana godiya. Amma sai yaƙi amsa. Mamaki ƙarara a fuskar Zahidah da Hafsat. Sun buɗe baki zasu magana yay musu alamar suyi shiru.

       “Basai kunce komai ba, inhar da wannan mai bakin tsiwar tare da ku anta kaiku waje ƙyauta kenan babu ko sisin ku”. Yay maganar idanunsa akan Muhibbat yana wani sassanyan murmushi.

          Hararar da yay tsammani ta watsa masa, cikin takaici tabar wajen batare da tace komai ba. Kira Zahidah da Hafsat suka shiga ƙwala mata suna dariya, amma ko waiwayensu batai ba harta ƙarasa gaban wani gida mai baƙin gate. Sai da ta kama murfin zata shiga ta waigo, ganin har yanzu mai taxi ɗin na tare da su yasata jan tsaki akan laɓɓanta ta ce, “Maye kawai”. Daga haka ta shige ciki.


         Gida ne da zamu iya kiransa babba a girma da ginuwa. Dan a ƙalla akwai ɓangarori biyu zuwa uku a cikinsa. Ɓangarori biyu na farkon shiga gidan sunfi haɗuwa da tsaruwa, zakaga hakan tun daga wajema kafin ka kai ga shiga ciki, sai dai kuma ɗayan dake daga ciki ya fisu girma, amma bai kai su ƙyawu ba.  

      Harara ta zubama sashen guda biyu tana taɓe baki, tana gab da wucesu taja tsaki a zuciyarta wanda batai zaton ya fito har waje ba.

     “K!! Dan ubanki wa kikema tsoki!!”.

Wata buɗaɗɗiyar murya mai cike da hargowa ta faɗa. Cak ta tsaya ƙirjinta na bugawar tsoro, tabbas da ace tasan mugun nan ya dawo gidan da bazata shigo ba sai magriba. Jin takun tafiya a bayanta alamar ya taso ya sakata juyowa. Ƙiris ya rage ya iso gareta, babu shiri ta kwasa da gudu zuwa sashen can ciki tana ƙwala kiran sunan Ummi!.

       “Ya ilahi! Tanee lafiyarki kuwa? Wai sai yaushe ne hankali zai game jikinki kisan girma ya fara zuwa miki!”.

      Ummi dake ƙoƙarin fitowa a kitchen riƙe da ludayin miya a hannu ta faɗa. Dai-dai isowar Hibbah cikin falon itama a guje. Bayan Ummi taje ta maƙale.

      “K da wa kuma?”.

Ummi ta faɗa tana juyowa gareta fuska a ɗaure.

      “Wannan mugunne fa Junaid Ummi. daga na shigo ina tsaki ya hau zagina kamar nasan da zamansa ma a gidan”.

          Baki Ummi ta buge mata, tai saurin ja da baya daga jikinta tana dafewa.

        “Wannan bakin naki da kanwa bata jiƙa a cikinsa shi zaisa kiyita shan wahala a wajen mutanen gidan nan Tanee. Mara kunyar banza matsamin a hanya”.

       Gefe Hibbah ta matsa gudun kar Ummi ta sake kai mata wani dukan hawaye cike da idanunta. Sai da taga ta koma kitchen ɗin sannan ta nufi ɗakinta zuciyarta na ƙara jin tsanar mutanen gidan nasu. Da ace zata samu wata dama a hannunta koda ta yini guda ce sai ta bisu da bulala hansin-hansin, musamman ma Hajiya Mama da Abba da wannan azzalumin Junaid ɗin. Mukulli ta murza a ƙofar tata dan batason sake magana da kowa. 


         Tunda Ummi ta jiyo ƙarar rufe ƙofar Hibbah sai tai murmushi, tasan hakan na nufin tayi fushi, ba kuma zata buɗe ba sai Yah Abubakar yazo ya lallasheta ko jarabar danna Computer ɗin tata ta motsa. Watsar da ita tai ta cigaba da aikinta saboda bataso magriba ta sameta. Cikin ranta tana tunanin yaushe Junaid ɗin ya dawo ƙasar? Dan bataji alamun murna da ga yaran gidan ba sam. Rashin mai amsa mata zancen ya sata watsarwa ta cigaba da aikin gabanta.

      Harta kammala ta shige babu wanda ya shigo a cikin samarin ƴaƴan nata, fatan dawowa lafiya tai musu sannan ta shiga wanka.


       A ɓangaren Hibbah ma wankan tayi, kasancewar tana fashin salla tana kammala kintsawa ta fito, dan ta tabbatar Ummi ta shige. bakuma zata sake leƙo falon ba sai bayan sallar isha'i. Yayunta kuwa bata tsammanin yau zasu kwana a gidan ma. Musamman Yah Abubakar da Yah Usman da yace yana katsina.

          Study table ɗinta ta haye dake can gefen falon a wani ɗan lungun. An shirya mata wajen tsaf da kayan karatu na musamman saboda kasancewarta ƴar gata, sannan haziƙa wajen sanin sirrin sarrafa Computer.  

      Tun ana ɗaukar lamarin nata shashanci har takai yanzu Yayansu Abubakar naci da ga tagomashin ƙwazon nata ta hanyar aikinsa na tsaro. Dan yasha sakata ayyuka masu muhimmancin gaske ana kuma samun nasara tunma bata kai haka shekaru ba. Wannan dalilin ne ya sakashi tsaya mata wajen ganin ta cika burinta akan zurfin nazari game da na'ura mai ƙwaƙwalwa.

         Cike da ƙwarewa ta kunna Computer ɗinta saboda aikin data tarkatarma kanta na bibiyar masu power bike. Dan ta ɗauka alwashin kosu ɗin ƴaƴan uban waye sai ta gano su insha ALLAH.

         Babu wanda ya shigo gidan sai Ummi data fito bayan sallar isha'i tace ta tashi taje taci abinci tunda babu wanda ya dawo a yayun nata har yanzu. Da to ta amsawa Ummin, tana gani ta koma ciki ta cigaba da aikinta cike da zaƙuwa.


      Ummi dake jiyo motsin Hibbah ta shiga ƙwala mata kira ganin dare ya farayi. ta tabbatar kuma inba da gaske tayi mata ba, zata iya kaiwa biyun dare akan Computer ɗin batare da gajiyawa ba.

        *_Tanee! Tanee!!_* wai bazaki tashi a gaban Computer ɗin nan kije ki kwanta ba sai na ci ƙaniyarki ko?!”.

       Hibbah dake zaune a cikin falon daga can gefen study table ta ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka. A kallo ɗaya zaka fahimci tarin ƙuruciyar dake tattare da ita, dan kwata-kwata bazata gaza shekaru goma sha tara a duniya ba. Jin tahowar mutum ta bayanta ta miƙe da sauri a gaban Computer ɗin tana faɗin, “Wayyo Ummi nafa kusan gamawa wlhy”.

      “Ai ba Ummi ɗin bace, mai kunnen ƙashi nine”..   Ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tsananin kama da ita da bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba ya faɗa a bayanta tare da kai mata ranƙwashi bisa kai. Tsalle tai zuwa gefe tana fasa ƙara duk da kuwa bai sameta ba. Ya balla mata harara yana kai hannu kan mouse ɗin Computer ɗin ya kasheta baki ɗaya. Dai-dai lokacin da yake ɗagowa ya nuna mata hanyar ƙofar ɗakinta yana faɗin, “kama gabanki kafin jikinki yay tsami anan”.

        Idanunta dake tara ruwan hawaye ta shiga ƙyaƙyƙyaftawa. Cikin narkewar fuska tace, “Yah Umar dan ALLAH ka barni wlhy zuwa 12 zan shige na kwanta. ALLAH akwai abinda nakeyi mai muhimmanci a ciki”.

            Charger ɗinta dake jikin socket ya fizga da nufin kai mata duka. Da sauri ta dirga wani uban tsalle da ihu tare da kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin nata.

        “Wai wane irin salon iskanci ne haka za'a dinga damun mutane da ihu kamar ƴaƴan rashin ƙwaɓa!”.

    Wata murya mai kauri da amo ta faɗa daga bayansu. Basai an sanar musu wanene ba, dan haka Tanee dake gab da shiga ɗakinta ta ida afkawa da sauri tana rufo ƙofar.  Umar yaɗan rumtse idanunsa yana cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi alamar son saisaita kansa dan jin zafin furucin mutumin da aƙalla zai iya kai shekaru Hamsin da huɗu zuwa da biyar

       “Wai dan iskanci ba magana nakeba akaimin banza saboda rashin tarbiyya!. To dan uban mutum dai duk yanda yake kallona nine uban ubansa ma bama shi ba. Sannan kuma mijin uwarsa ne ni!!”.

     Murmushi mai ɗaci Umar yayi yana haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi saboda kallon da Ummi dake fitowa tai masa. Yaja numfashi a sarƙe da faɗin, “Kayi haƙuri Abba ba wani abu bane ba. Nine da Tanee”.

        “Eh lallai ai basai ka faɗaba na gani kai da taɓararriya ne, to ubanmi kale mata da har takema mutane ihu kamar wadda ake lalub....”

     Cikin ɓacin rai Ummi ta katsesa da faɗin, “Kai Umar wuce ka tafi sai da safe”.

          Zuwa yay ya wuce yana faman taunar lips ɗinsa dan shi kaɗai yasan tuƙuƙin baƙin cikin da yakeji a cikin ransa game da ƙanin mahaifin nasu da a yanzu suke kira da Abba saboda maye gurbin mahaifinsu da yayi dalilin ƙaddarar mutuwa, tabbas badan mahaifiyarsu ba da ko kallon hanyar da sukabi tuni kawun nasu bazai ringayi ba. Amma dasun yun ƙuro itace mai taka musu burki.

         

     Umar na ficewa Abba ya saki wani shegen tsaki da nufar hanyar ɗakin Ummi. Itama bayansa tabi a fusace. Suna shiga cikin ɗakin a zafafe tace, “Halilu ina rabaka da jifarmin ƴaƴa da mugayen furuci amma baka kiyayewa. Ka sani idan ada ni dasu mun ɗauka wulaƙancinka da tozarci wlhy yanzu bazamu ɗauka ba. Dan badan ina takama yaran nan birki ba a kanka bisa dalilin mahaifinsu da tuni sun tabbatar maka da suma sunkai girma. Idan kuma bazaka bariba to lallai zan buɗe musu ƙofar dana rufe domin maka hijjabi akan hakan.....”

        Wata wawuyar dariya ya saki yana faɗawa saman gadonta. Cikin salon iskanci da izgilanci yakai ƙafa ya taɗota sai gata ta faɗo kansa. Yunƙurawa tai zata tashi ya birkiceta zuwa ƙasa ya koma samanta. Dogon gashin da ALLAH ya azurtata da shi duk da tsufa yasa ya fara sirkawa da furfura ya damƙe cikin hannunsa tare da ɗan kwalin kanta ya fisga da ƙarfi, tare da sak ɗayan hannunsa ya danne mata baki............✍


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700


Duka gamayyar biyar din(1k)

1,000


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*



             *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*


                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_ZAFAFA BIYAR 2K22_


🔥🔥🔥🔥🔥

*_LAST BONANZA_*

*KARO NA QARSHE!*


*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*


*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*


*_za'a fara posting in sha Allah 3st January da yardar Allah_*


*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*


*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA


SAIKU TURA SHAIDAR BIYA


08184017082


GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU


09134848107

_________________________


*_Chapter Five_*


............Wani irin rawa jikin Ummi ya fara saboda azaba. Ya ƙyalƙyale da dariya yana wani fici-fici da ƙananun idanunsa jajaye. “Asiya idan kin manta bara na tuna miki. Daga ke har ƴaƴanki da kikeji girmansu ya kai yanzu a tafin hannuna kuke wlhy. Zan kuma iya binku ɗaya bayan ɗaya na salwantar da rayuwarku batare da wani mahaluki ya iya gane hakan ba ko zargina. Kamar yanda na gagareki a baya da kikeji da ƙuruciya a yanzunma hakan take. Dan haka ki cigaba da buɗemin ido da tsagerancin nan naki kiga idan ban kai rayukanku ƙasa ba cikin ƙanƙanin lokaci”.

    Ya ƙare mganar da hankaɗa kanta ta bigi fuskar gadon. Wata siririyar ƙara ta saki ta zaba. Cike da juriyar zaluncin data saba sha daga garesa ta dubesa da idanunta da suka kaɗa zuwa ja tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar dake taruwa a cikinsu. “Insha ALLAHU Haƙilu bazaka taɓa cin nasara akan zuri'ata ba bayan nasarar aure na da kayi a baya, bazan gaji da faɗa makaba ko yanzu kana samun nasarane a kaina saboda wasu dalilai na lizzamin zaren ƙaddara, amma ka jira lokaci, dan kaɗan ya rage azo dai-dai wajen da zakasha mamaki.......”

     Sake buga kanta yay a fusace kafin takai ƙarshen zancenta saboda sukar zuciyarsa da kalamanta sukeyi a duk sanda ta maimaita masa su, ya saka hannunsa ya danne mata baki yana ƙyalƙyalewa da dariya. “Iyakarki kauɗin banza da cika baki Asiya, amma ki sani ni Haƙilu nafi ƙarfinki, dan baki da maraba da wulaƙantacciyar dabba a gareni, amfaninki a wajena kawai samun abinda nai kwaɗayi a gareki tun farko kika hanani, yanda kika wulaƙantani a kansa a baya haka zan cigaba da samunsa a gareki cikin wulaƙantarwa da ƙasƙantar dake a ƙasan takalmana.”

     Da iya ƙarfinta tai yunƙurin turesa amma ta gaza hakan, sai ma ƙara jigata da wahaluwa da takeyi a hannunsa. Yayinda shikuma yake ƙyalƙyala dariyar shaƙiyanci a gareta da izgili, cikin tsantsar zalunci da wulaƙantarwa ya shiga ƙoƙarin yin tarayya da ita kamar wanda ke tare da ƙasƙantacciyar karuwarsa. Yanayi yana kai mata mari saboda ƙoƙarin ƙwatar kanta da takeyi a garesa.

         Kamar kullum sai da ya galabaitar da Ummi son ransa sannan ya barta yana faman tuntsurar dariyar rashin imani. Yaja kayansa ya saka bayan ya goge ƙazantar jikinsa da gashin kanta tare da tofa mata yawu ya fice yana cigaba da ƙyalƙyala dariyar.

         Wani irin siririn kuka Ummi ta saki mai cin rai a wajen. Takai kusan awa ɗaya tanayinsa kafin ta miƙe zuwa toilet da ƙyar saboda azaba. Dukkan dabarun data sabayi domin gyara jikinta a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsu su ta gudanar, koda ta fito doguwar riga ta saka tahau saman abin salla ta fara gayama ALLAH kukanta akan zaluncin Alhaji Haƙilu ƙanin mijinta ada, sannan kuma mijinta a yanzu.

         Bayan tayi nafilfilinta tai zaman karatun AL-QUR'ANI. Sai da taji zuciyarta tayi mata sanyi, nutsuwarta ta dawo jikinta sannan tai addu'a ta ɗan kwanta, cikin lokaci ƙanƙani barci mai daɗi yay gaba da ita tamkar bata da wata damuwa.




        Kamar yanda ta horar da yaranta tun suna ƙanana yau ma tun kiran sallar farko na asuba suka tashi. Sai da duk sukai alwala sanann suka firfito daga ɗakunansu su biyar abin sha'awa, dan a daren duk suka dawo ba kamar yanda ta tsammaci zasu kwana a wajen ba, a tunaninsu tayi barci ita da auta shiyyasa basu shigo ba. Ammar ne ya nufi ƙofar ɗakin Hibbah ya shiga mata knocking da kiran sunanta har sai da yaji ta amsa. “Tashi kiyi salla, saura kuma idan kin idar ki sake kwanciya tunda kinsan dai yau kinada text ɗin safe”.

          Bai jira amsartaba yabar wajen dan yayunsa na jiransa. Basu damu da tada Ummi ba, dan sunsan ita bata makara saboda mace ce mai tsantseni da yawan kula da ibada, bata da wasa sam akan bautar ALLAH. Hakama koda suka fito daga sashen nasu basuyi gigin tada sauran jama'ar gidan ba suka fice abinsu zuwa massallacin anguwar.

        Daƙyar Hibbah ta tashi zuwa toilet saboda barcin dake cikin idonta. Cikin layi da rangaji irin na wadda ta tashi a barci ta shige bayin. Kusan mintuna ashirin sai gata ta fito ɗaure da towel tana tsane gashinta da wani alamun ta samu tsarki. Zani ta ɗaura ta saka hijjab har ƙasa ta tada salla.


*_7:34am_*


           A gurguje take shiri tana yawan kallon agogon ɗakin nata saboda kiran da Ummi keta faman ƙwalamata daga falo.

       Cikin kumbura fuska da ƙunƙuni take faɗin, ‘Kai Ummi wannan kira kamar makauniya, ai ba kowa ne ya jamin wannan makararba sai Yah Ammar, duk da yasan zanje makaranta harda min gargaɗin karna koma barci sai gashi bayan dawowarsu massallaci ya tsareni sai na haɗa masa indomie wai nafi kowa iya dafawa........’

      “Tanee! Tanee!!”.

     Ummi ta sake ƙwalama Hibbah kira again. Ƙoƙari amsawa take cikin zazzaƙar muryata tana tattare tarkacen abinda zata buƙata a cikin bag ɗinta mai zubin school bag. Daga can ta sake faɗin, “Auta kina kallon agogo kuwa?!”.

        Saurin ɗaukar bag ɗin tayi da gyalenta tayo waje da hanzari. Tun kafin ta ƙaraso tsakkiyar falon Yah Umar ya wullomata harara cikin faɗa. “Wai ke kullum sai kin makara kin makarar da mutane hankalinki ke kwanciya a gidan nan ko? Tun kina zuwa secondary halinki kenan, yanzu kin fara jami'ar ma baki canjaba”.

       Fuska ta kumbura tana tura baki, ta ajiye bag ɗinta da gyalen a saman kujera tana ƙarasawa dining ɗin inda duk suke zaune har Ummi, dan haka suke cin abinci a tare duk safiya da dare. Cikin shagwaɓar data saba da tsiwar da bata barin bakinta tace, “Kai Yaya Umar naga dai Yah Ammar ne ya sakani makara, sakanifa yayi na dafa masa noodles”.

        Yah Ammar dake kujerar gefenta yana ƙoƙarin fara cin indomie ɗin data dafa masan ya zubomata uwar harara shima yana faɗin, “Dama can kin saba makararki yarinya zaki wani jingina dani”.

       Baki ta sake buɗewa zatayi magana Yah Usman dake duba wasu takardu dake gabansa a dining ɗin shima ya watso musu harara ita da Ammar ɗin, “Dalla malamai karku cika mana kunne kuma ko”.

     Ummi dake turama Hibbah kofin kunu data zuba mata tace, “Ai inda sabo sun saba, Ammar da Tanee basa taɓa zama waje guda basu isheka ba, sai kace suna ganin hanjin junansu. Nikam babu mai barina da ciwon kai kowa yayi ya gama ya kama gabansa”.

       Baki Hibbah ta kuma cikawa da iska tana duban Yah Muhammad da Yah Abubakar masu kareta. Yaya Abubakar dake hidimar haɗama kansa shayi yayi murmushi, “Auta yada kallona kuma? Nimafa yau gashi kina neman makarar dani bayan nace da wuri zan fita”.

       Cikin shagwaɓar da takema yayun nata saboda so da ƙaunarta da sukeyi ta ce, “Yaya kaima ko?” ta faɗa tana maida dubanta ga Yah Muhammad da ke ta faman latsa wayarsa. Ƙaramar dariya yayi tunkan tace komai, ya ajiye wayar tasa yana amsar kunun da shima Ummi ta zuba masa dan kusan halinsu ɗaya da Muhibba shima bai cika son tea ba. “Kinga autan Ummi manta da kowa ki karya, yau da kaina ma zan kaiki makaranta bazakibi Ammar ba, maza lokaci na sake ja”.

    Jin Yah Muhammad yace da kansa zai kaita makaranta yau ya saka bakinta washewa. Ta kalli Yah Ammar abokin tsamartata tana masa gwalo. Kusan duk sai da sukai murmushi kowa na girgiza kansa cike da mata kallon so da ƙauna.

     Basai an faɗa ba, yanda ƴan uwata da Ummin su kema Hibba a gidan zaisa kowa fahimtar ita ɗin ƴar gata ce kuma shalele. A kullum kowa burinsa yaga farin cikinta. Koda laifi tayi suka zaneta ko mata faɗa daga baya sai su koma mata nasiha da lallashinta har sai sunga ta koma rayuwata ta ƙiriniya da rashin ji suke samun nutsuwa. Sai dai kuma a ɓangaren Abba da sauran matansa sam ba haka bane. Sun tsani Muhibbat tamkar ita kaɗaice ƴa a gidan. Hakama sauran ƴaƴan gidan duk basa sonta. Kafin Hibbah takai haka kullum tambayata mi sukai musu? Amma babu mai bata amsa a tsakanin Ummi da yayunta guda biyar. Sai da tayi hankali ne zuwa yanzu take ɗan fahimtar wasu abubuwan duk da dai ba wani ya taɓa zama ya sanar da ita gaskiyar dalilinba har zuwa yanzun.


     Itace farkon kammalawa, ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllh”.

         Yaya Abubakar ya dubeta da kulawa cikin lallashi yace, “Auta ki dingacin abinci ko zaki ƙara girma fiye da haka dan ALLAH, ke kowa na girma yayi ƙiba banda ke, makarantar nan kamar ƙara tsiyayar dake take ma”.

      Murmushi tayi cike daso da ƙaunar Yayun nata masu sonta. Tace, “Yah Abubakar duk wannan ƙatuwan dana zama, da kaɗan fa Yah Ammar ya fini tsaho”.

    Harara Yah Ammar ya galla mata da faɗin, “Tunda nine marainin wayonki ko? bar ganin Ummi a wajen, na tashi ɓarar dake zanyi ALLAH”.

         Dariya duk suka sanya masa, dan da alama da haushi yake maganar. Hibbah tai masa gwalo da ɗaukar bag da gyalenta ta fice da gudu saboda ganin zai miƙe, tasan kuma kanta zaiyo.

        A ƙofar fita falon taci karo da Abba. Tai saurin komawa baya jikinta naɗan rawar kaɗuwa. Dan duk da rashin tsoro na Muhibbah a rayuwarta tana matuƙar jin tsoron Abba tun tana ƴar ƙarama. Hararar da yake wulla mata ya sata sake sata duƙar da kanta idanunta na tara ƙwalla.

        “Wane kalar shashanci ne kuma haka? Da girmanki amma kullum lalacewa al'amuranki ke ƙarayi saboda ke ƴar ido ce!!”.

        Sam Hibbah bata son tsawa, shiyyasa da zaran Abban ya mata ita take rikicewa, yanzu ɗinma duk sai jikinta ya hau ɓari, muryarta na rawa alamar tahowar kuka tai saurin faɗin, “Kayi haƙuri Abba bansan ka tahoba ALLAH. Ina kwana”.

         Ciki yay batare daya amsa mataba yana jan tsaki. Hibbah ta bisa da kallo wasu hawaye masu zafi na sakko mata bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Ido suka haɗa da Yah Usman. Ya girgiza mata kansa alamar kar tai kuka. Dan tun tsawar da Abban yay mata duk hankalinsu ya dawo kansu.

     Suma koda suka gaishesa bai amsa musu ba. Sai faman mazurai yakeyi. Basu sakebi takansaba duk suka kwashi kayayyakinsu sunama Ummi sai sun dawo. Itako amsa musu take da fara'a tamkar batasan da zaman Abban a wajenba ma.

        Yah Muhammad ne ya kama hannun Hibbah da ko motsi ta kasayi har yanzun. Sai da sukazo har wajen motarsa yasa handkerchief ya share mata hawayenta batare daya ce komaiba. Sauran ƴan uwansa ma kuma bai basu damar cewa komai ɗin ba. Sai umarnin yin addu'ar fita gida kamar yanda suka saba yay musu.

      Suna kammalawa kowa ya hau abin hawansa. Yah Muhammad da Hibbah. Abubakar ya ɗauka Usman da Umar a motarsa dansu basu da mota har yanzu sai mashina. Ammar ma ya hau mashin ɗinsa lifan shi kaɗai tunda yau Hibbah tabi babban yaya...........✍





_BONANZA, BONANZA, BONANZA 20% OFF ZAFAFA PAID BOOKS, OFFER ENDS ON 31st DEC 12AM INSHA ALLAH!_


_ASSALAMU ALAIKUM!!_


_ZUWAGA MASOYA, KUMA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR._


_KORAFI YA KARBU, DAGA YAU LARABA 29 GA WATAN DECEMBER IN SHAA ALLAH, ZUWA 31 GA DECEMBER RANAR JUMU’AH KENAN. BISAGA KORAFI DA NEMAN RAGE KUDIN ZAFAFA NA DUBU DAYA KAN LITTAFAN BIYAR, IN SHAA ALLAHU, KORAFIN KU YA ISA GARE MU. KUMA MUN AMINCE. ZAMU KARBI 800 GA LITTAFAI BIYAR DIN DA KUKE BUKATA, A MAIMAKON DUBU DAYA NA BOOKS BIYAR. YAU LARABA ZUWA JUMU’AH KARSHEN WATAN DECEMBER KENAN. ZAMU RUFE KARBAR 800 KUDIN ZAI KOMA DUBU DAYA KARFE 12 NA DAREN RANAR JUMU’AH INSHA ALLAH._


_GA WATAN JANAIRU (3st JANUARY, ZAMU CIGABA DA KARBAR DUBU DAYA KAN LITTAFAN BIYAR._


_A KUMA 1 JANUARY DINNE IDAN ALLAH YA KAI MU, ZAMU FARA SAKIN PAGES DIN LITTAFAN NA KUDI, WATO PAID PAGES👏🏼👏🏼NA BOOKS DIN._


_LITTATTAFAN SUNE: *DABI’AR ZUCIYA (FALL IN LOVE)* NA SAFIYYAH HUGUMA_


_*HALIN GIRMA (GLAMOROUS LOVE)* NA HAFSAT RANO_


_*DEEN MARSHALL: (INTENSE LOVE)* NA MAMUH GEE_


_*SO DA ZUCIYA (A LOVE SO BEAUTIFUL)* NA: NANA HAFSAT MSS XOXO_


_*TAKUN SAAKA(LOVE IN TIME)* NA: BILLYN ABDULL._


_KAI DAGA JIN SUNAYEN KASAN ZA’A SHA GWAGWARMAYA A KUMA KARU DA DARUSSAN DA ZASU KOYAR, NA FADAKARWA DA NISHADANTAR WA HADI DA TACACCIYAR KAUNA MARAR GAURAYE_


_DOMIN KASANCEWA CIKIN MABIYA LITTAFAN ZAFAFAN SAI A TUNTUBE MU TA.👇🏾_


*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*


*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*


*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*


*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*


*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*


*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*


*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*


*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*


*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*


*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*


*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*


2👉🏾400

3👉🏾500

4👉🏾700

5👉🏾1000


*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*


09134848107


*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽

#team zafafa biyar


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*



__________________


*_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_*


_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_


*_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_*


_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_


*_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_*


https://youtube.com/c/sudaiskura


_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._


_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_


_________________________


*_Chapter Six_*


..............Ƙoƙarin kauda fuskarta taketa faman yi saboda kar Yah Muhammad ya ga hawayen dake guje-gujen sakko mata akan fuska tun bayan barowarsu gida. Sai dai kuma abinda bata sani ba tuni ya fahimci kuka takeyi, yadai mata shiru ne domin bata damar rage nauyin zuciyarta.

       Sai da ya ɗauka titin da zai kaisu har makarantar tasu sannan yay gyaran murya batare da ya kalleta ba. Shiru Hibbah bata motsa ba saboda zurfi da tai a tunani....

      “Auta!”

Ya kira sunanta cike da kulawa. Nanma shiru babu alamar ta jisa. Leɓensa yaɗan ciza na ƙasa yana gangarawa gefen titi. Harya kashe motar gaba ɗaya ya juya yana kallonta batasan mi yakeyi ba. Cikin damuwar data bayyana sosai akan fuskarsa ya ce, “Muhibbat!!”.

       A firgice ta juyo garesa tana sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma tai saurin kai hannunta akan fuskarta ta shiga share hawayenta tana ƙaƙalo murmushi. “Lah Yaya banjikaba ALLAH. Ina can wajen kallon hanya har idanuna na hawaye dan ƙauyanci”.

      Murmushin da bai niyyar yi baneba ya suɓuce masa. A ransa yanajin ƙaunar ƴar ƙanwar tasu da yaba halinta na manya. Duk da rawan kanta da tsiwa ita ɗin yarinyace data san yakamata. Tana da wasu nagartattun halaye da sai ka nutsu gareta kake iya ganosu. Amma a kallo ɗaya zaka iya dangantata da yarinya mai rawar kai da shirme. Ya ɗanja numfashi yana furzarwa a hankali tare da kafeta da idanunsa irin nata.

      “Mi kike tunani Muhibbat!?”.

A yanda yay maganar babu wasa a cikinta ne ya sata ɗago idanunta dake ƙoƙarin tara ƙwalla ta dubesa. Sai kuma tai saurin girgiza kanta tana ƙoƙarin maida kukan dake son ƙwace mata.

     “Ba bu komai Yayah”.

Ta faɗa muryarta na rawa.

        Sosai ya sake kafeta da idanunsa dake canja kala zuwa ɓacin rai. Sai dai kuma cikin tausasa murya ya ce, “Kin dai san banason ƙarya ko?”.

     Kanta ta jinjina masa hawayen da taketa ƙoƙarin makalewa suka gangaro a hankali bisa fuskarta.... “Yaya! Abba ne, miyasa baya sonmu? Musamman ma ni ya tsaneni bayason ganina”.

         Takai ƙarshen maganar tata da fashewa da wani irin kuka mai cin rai ga ma'abocin saurare. Idanunsa ya lumshe a hankali tare da cije leɓensa na ƙasa da ƙarfi. Addu'a ya fara karantowa a zuciyarsa domin samun dai-daito daga fushi da fusatar damuwar ƴar uwar tasa. Ya kamo hannunta cikin nashi ya rumtse da ƙarfi.

         Kamar jira take ta sake fashewa da wani kukan, fuskarta ta kwantar akan hannayen nasu dake cikin na juna, hawayenta suka shiga gangarowa har akan fatar hannunsa data ɗora kanta a kai. Cikin kuka ta cigaba da faɗin “Yaya miyasa Ummi ta yarda ta auresa? Bayan kuma tasan shi ɗin mugu ne. Miyasa bata haƙura ta zauna damu mu kaɗai ba bayan rasuwar Abbanmu?. Wlhy Yaya banason Abba na tsanes.......”

       “Muhibbat!”. Yay saurin katseta da ƴar tsawa.

Ɗago kanta tai tana kalonsa, ganin yanda ya ɗaure fuska ne ya sake sakata fashewa da kukan.

      Yaya miyasa bakwaso nace banason Abba bayan shima baya son mu. Kullum shike gusar da farin ciki a kan fuskokinku. Duk randa yazo sashenmu sai Ummi tayi kuka a ɓoye. Sannan fuskarta tana kumbura kamar wadda aka daka Yayanmu”.

       A matuƙar razane yake kallonta a yanzun. Dan tabbas tun basukai hakaba suke tambayar Ummi mike samunta a fuska a maban-banta lokaci, amma sai takan ce musu wani ciwo ne yake mata haka akan fuska lokaci-lokaci, amma tana shan magani. Sunsha damunta suje asibiti amma sai taƙi yarda. Sai dai kuma yau gashi ƙaramar ƙanwarsu tazo da wani batu mai girma. Shin kodai da gaske ne da ake cewa duk ƙanƙantar ɗiya mace tafi ɗa namiji lura da maida hankali akan abu.......

      “Yayanmu dan ALLAH kasa mubar musu gidansu mu koma can wani gari da zama mu daina ganinsu suma su daina ganinmu.”

      Hibbah ta katse masa tunani ta hanyar girgizasa tana kuka da roƙonsa.

        “Tanee! kinga nutsu muyi magana. Maza share hawayenki na tambayeki”.

     Da sauri ta shiga share hawayenta da handkerchief ɗinsa. Duk da wasu nabin wasu hakan bai hanata faɗin, “Yaya na goge”.

          “Auta kin taɓa ganin wani ya daki Ummi ne?”.

      Kanta ta girgiza masa.

“To miyasa kikace kamar ana dukanta?”.

          “Yaya nidai haka kawai nake ganin kamar shatin yatsu a fuskarta a duk randa fuskan yay kumburi. Sai kuma ranar da Abba ya kwana a sashenmu na taɓa jin kamar tana kuka na fito ɗaukar ruwa dana manta ban ɗauka ba da dare. Tana kuka sosai, ina kumajin muryan Abba yana mata kamar magana cikin faɗansan nan”. 

         Kallonta kawai yake ko ƙyaftawa babu, acan ƙasan ransa kuma yanama kalamanta fashin baƙi dalla-dalla. Ganin yaƙi cewa komai yasata kai hannunta akan masa ta girgiza shi.

     Ajiyar zuciya ya sauke da haɗiye damuwar dake neman kufcewa akan kamilalliyar fuskarsa.

      “Yaya baka yarda ba ko?”.

“A'a Auta, taya zan ƙaryataki bayan nasan ke ɗin baki da ƙarya. Kawai dai ina nazari ne akan maganar taki. Amma inaga yanzu ba shine lokacin yinsa ba. Bara na kaiki makaranta karki makara. Idan mun koma gida zamuyi magana. Amma na roƙeki bayan ni karki faɗama kowa zancen nan har cikin su Usman kinji ko”.

       “Insha ALLAH Yaya bazan faɗa musu ba. Amma dan ALLAH ka tambayi Ummi kaji ko Abba yake dukanta ne?”.

      Ɗan murmushi yayi a ƙasan ransa yana jinjina wautarta. “Karki damu insha ALLAH bazan manta ba.

     Koba komai ta ɗanji sanyi a ranta. Dan haka ta ƙarasa share hawayenta nauyin da zuciyarta yay mata yana sauka a hankali.


       Tunda ya tada motar suka cigaba da tafiya sai shi ya koma cikin yanayin shiru ɗin. Dan gaba ɗaya tunaninsa da hankalinsa sun koma akan zantukan Hibbah.

      Koda suka isa makarantar sai da ya sakata tai addu'a kafin ta fita a motar, ya miƙa mata 1k tare da mata gargaɗin ta dage akan text din da yaji Ammar ya faɗa zatayi. Inba hakaba bazai kaita chaina ɗin da take burin zuwa ƙaro ilimin kimiya da fasaha ba”.

          Cike da son cikar burinta ta tabbatar masa insha ALLAH zata dage wajen cinye text ɗin da maki mai yawa. Daga haka ta shiga ɗaga masa hannu har yay reverse yabar wajen. Ƙoƙarin nufar department ɗinsu tayi ranta fal saƙe-saƙe itama. Ta duba department ɗin su Zahidah a ranta tana tunanin suma sunzo tuni, dan suma sunce mata suna da text yau tun 8am.

             


★★★★


       Koda su Hibbah suka fita a class bata nema su Hafsat ba. Dan tanason samun nutsuwar ƙarasa aikinta na jiya. Kai tsaye ɗakin dake ajiye da na'urori mai ƙwaƙwalwa na department ɗin nasu ta nufa. Dan tana ɗaya daga zaƙaƙuran yara mata matasa dake baje kolin basira da ƙwazon da ALLAH ya basu akan ilimin kimiya da fasa.

          Ta samu ɗalibai irinta masu naci da ƙulafuci ɗai-ɗai a ɗakin. Bataima kowa magana ba ta zauna a table guda ɗaya

dake daga can lungu tana sauke ajiyar zuciya, tsabar yanda take nacema Computer ɗin wajen saboda daɗin da take mata har security ta ƙirƙira ta saka dan tanada ajiye-ajiye da yawa a ciki. Akwai wani yaro da suke ƴar tsama da shi, shima yanada ƙwazo matuƙa akan fannin, ya taɓa mata manaƙisar lalata mata securitys ɗin data saka domin binciken abinda take ɓoyewa a Computer daba tata ita kaɗai ba. Aiko data tashi ita sai da tai masa ɓarnar daya gwammaci da bai aikata mata ba, dan babbar ma'ajiyarsa ta Computer ɗinsa dake gida taima kutse, tare da aikata ɓarna da har iyayensa sai da suka saka police zuwa har gida domin kamata. Sai dai kasancewar tana da Yah Abubakar hakan bata faruba, sukai ƙoƙarin ganin sun rufe case ɗin.

         Flash ta ciro a bag ɗinta tai connecting da Computer ɗin ta shiga abinda ya kawota cike da ƙwarewa da fatan nasara. Kusan mintuna goma sha uku tana abu ɗaya, sai faman sauke ajiyar zuciya take akai-akai. Harma ta fidda rai da nasara sai gashi cikin amincin ALLAH ta kuma dace. Wani lallausan murmushi ta saki da ambaton kalmar “Alhmdllhi” tana rungume Computer ɗin dan farin ciki. Tuno da bata sanarma Yah Abubakar bane ya sata saurin ɗauka wayarta. Batare da tunanin komai ba ta dailing number ɗinsa. Sai dai harta tsinke bai ɗaga ba. Ta tura baki gaba alamar jin haushi tana ƙoƙarin sake kiransa. Nanma ɗin dai babu amsa. Cikin takaici ta ƙara ƙoƙarin sake kira a karo na uku sai ga nashi kiran ya shigo.

     Ɗagawa tai da sauri tare da kwaɗa sallama cikin karaɗinta da shagwaɓa. Daga can Yaya Abubakar ya amsa yana faɗin, “Autar Ummi lafiya dai ko? Ina cikin aiki ne fa”.

        “Lafiya lau Yaya dama fa wani abu zan sanar maka. Jiya baka dawo da wuri bane har nayi barci, ɗazun kuma na manta ne saboda Abba”.

       “Okay to ina jinki”.

“Uhm yauwa Yayana. Kasan wani abu? Jiya muna fitowa a school wasu masu power bike suka kusan turemu, sanadin hakan ma har Hafsat ɗin gidan aunty Kulu ta samu rauni a ƙafarta sai da akai mata gyara a asibiti. To ni kuma tun a jiyan na jefa musu agogon nan nawa, yanzu haka na gano inda suk.......”

      Kafin takai ƙarshen maganar tata ma Yaya Abubakar ya miƙe a zabure da ga can yana faɗin, “Masu power bike?!”.

      “Yes! Yaya. Kasansu ne?”.

“Kinga auta kina ina? Wannan maganar bata waya bace zanzo yanzu na sameki, karfa ki faɗama kowa bayan ni”.

        Kafin ta samu damar cewa wani abu ya yanke wayar.       

     “Oh Yaya kama tsaya na gama maganata mana zaka wani yanke. To nama fasa faɗa maka sai nan da awa uku”. Tai maganar tana haɗa kayanta da fushi ita a dole taji haushi. Tana ƙoƙarin rataya bag ɗinta a baya kira ya shigo wayar tata. Ganin Zahidah ya sata ɗagawa tana kai wayar kunnenta da nufar ƙofar fita daga wajen.

           Tana cikin sauraren Zahidah dake faɗa mata inda take taje ta sameta taga ansha gabanta. Takaici ya sakata janye wayar daga kunnenta ta ɗago domin ganin wane shege ne ya tare mata hanya.

      Turus ta ɗanyi tana kallon zaratan mazajen dake a gabanta riƙe da manyan bindugu tamkar wasu mala'ikun ɗaukar rai. Duk da rashin tsoronta sai da taji wani abu mai kama da firgici ya gitta mata. Ta motsa bakinta a hankali idanunta na wani mar-mar.

      “Bayin ALLAH lafiya kuwa?”.

Ta tambaya tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

        Ɗaya da ga cikinsu ne ya nuna mata i'd card ɗinsa da faɗin, “Mu jami'an tsaro ne da ga hukumar ƴan sanda ta farin kaya. Munzo nan ne kuma dominki Muhibbat Aliyu Hamza”.

        “Wurina kuma? To ni miya haɗani da ku? Wama ya faɗa muku sunana?”.

       “Duk zaki sami amsoshinki idan munje office”.

        A tsiwace tace, “Hu'um ai wlhy bazan biku ba, barama na kira Yayan.....”

         Zare wayar da ɗaya daga cikinsu yayi ne ya saka sauran maganar tata maƙalewa. Ya katse kiran da taima Yaya Abubakar yana kashe wayarma baki ɗaya. 

           Wani yawu Muhibbat ta haɗiye da ƙyar tana binsu da kallo tare da ɗalibai ƴan uwanta da hankalinsu ya fara kaiwa garesu suka ɗan fara taruwa domin kallon mike faruwa. Mota suka nuna mata. Da farko batai niyyar shigaba. Amma tuna tana dasu Yaya Abubakar aduniya ya sata shanye dukkan wata fargabarta ta shiga motar tana ƙunƙunin amshe mata waya da sukayi.

          Dai-dai lokacin da suke shigewa motar suma Zahidah da aka kai mata labarin anga ƴan sanda na neman ƙawarta ta iso wajen. Hankalinta tashe ta shiga ƙwala kiran sunan Hibbah da sam batama jita ba. A firgice ta lalubo wayarta domin san kiran Ummi ta sanar mata ko zata sanarma cikin su Yaya Umar, dan ruɗewar da tayi tasa tama manta da cewar Yaya Ammar shima anan makarantar yake nasa karatun, yana a shekarar ƙarshe ne ta kammalawa..


★♣♠♣♠♣♠♣★♣♠♣♠♣♠♣★


                  Ummi na zaune a can inuwar mangwaro dake backyard ita kaɗai tun barin Abba sashen nata bayan ya gama shuka mata shika-shikan rashin mutuncinsa da ya saba. Lalle take sakama yatsun hannunta dan ita mace ce mai son jan lalle sosai. Har takai ta koyama Hibbah kasancewar tun tana ƴar ƙaramarta take mata itama.

       Kallon wayarta da kira ya shigo tayi duk zatonta ma Hibbah ce. Batai mamakin ganin Zahidah ba, dan tasan Hibbah zata iya amfani da wayar tata wajen kiranta idan tata wayar babu kuɗi. Ɗayan hannunta tasa ta ɗauka wayar fuskarta da Murmushin tuna a yanda Autar tata ta fita cike da tsoron Abba a tare da ita.

         “Autan Umminta yaya dai?”.

Ta faɗa dai-dai lokacin da take ɗora wayar akan kunnenta.

       “Ummi ba ita bace nice Zahidah”.

Jin yanda muryan Zahidah ke rawa kuma a firgice ya saka Ummi ruɗewa ta shiga jera mata tambayoyi..

       “Ummi akwai matsala ne wlhy, yanzu ina capteria muna waya da Hibbah ina faɗa mata ta fito class ina jiranta muci abinci sai wayan ya katse. Ina ƙoƙarin sake kiranta a zatona network ne sai ga wani course mate ɗina yazo yake sanar min ga jami'an tsaro can suna neman sister ɗina. Na tafi domin tabbatarwa kawai na iske harta shiga motarsu sun wuce da ita Ummi. Ni kuma gashi bani da no ɗin su Yaya Abubakar balle na sanar musu shine na kiraki dan ki sanar musu”.

         _(Hasbinallahu wa-ni'imal wakil)_ Ummi ta shiga mai-maitawa da sauri-sauri dan jin wani irin yuuu cikin idanunta da kanta. Cikin ƙoƙarin haɗiye tashin hankalin da take ciki ta ce, “Wani laifin ta aikata ne Zahidah?”.

        “Ni dai Ummi a sanina bata aikata komaiba wlhy.”

       “Shikenan bara na kira Abubakar naji idan yana kusa ko Muhammad”.

       “To Ummi”. Zahidah ta faɗa tana share hawayen da suka gangaro mata akan kumatu. A kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar firgice take. Gashi ita kaɗai ce yau dan Hafsat batazo ba saboda ƙafarta.

     Hango Yaya Ammar da ke nufota da sassarfa ya sakata tunawa da yana a cikin makarantar shima. A zabure itama ta nufosa.

       “Zahidah! Ina Muhibbah?”.

  Ya faɗa cikin furzar da hucin hakkin gudun da yayi dai-dai isowarsa gabanta.

        Bayanin abinda ta sani da wanda taji a bakin mutane tai masa tana share hawaye. Hankalinsa ya ƙara tashi matuƙa shima. Dan duk tsokanarta bata taɓa kaiwa matakin hakaba, a yanda yaji wai ƴan sanda da manyan bindugu ya matuƙar harmutsa tunaninsa.

    Babu shiri ya shiga neman no ɗin Yaya Abubakar, sai dai kuma number busy take nuna masa alamar yana waya da wani kenan ko makamancin hakan. Maida akalar kiransa yayi akan Yaya Muhammad. Bugu biyu ya ɗaga. Ko sallama bai masa ba ya shiga masa bayanin abinda ke faruwa.

      Ko tari kasa yi Yaya Muhammad yay. Sai numfashinsa ne dake tafiya a sarƙe tamkar mai ciwon Asthma. Batare da ya iya furta komai ba ya yanke wayar. Kamar jira sai ga kiran Ummi ya shigo masa.

     Sam baiyi tunanin taji mike faruwa ba itama. Dan haka yay ƙoƙarin saita kansa dan ganin bai tada mata hankali ba. Sai dai a yanda yaji muryarta tun a sallama ya matuƙar tada masa hankalin. A hautsine ya shiga tambayarta lafiya? Dan ko kaɗan basason tashin hankalinta.

          Duk yanda Ummi taso danne damuwar dake a cikin muryarta ta kasa hakan. Cikin gwamewar numfashi ta shiga yimasa bayanin duk yanda sukayi da Zahidah.

         Da sauri ya ce, “Ummi dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zamu nemi idan take bara na nema Abubakar yanzun nan”.

   Bai jira cewarta ba ya yanke wayar dan bayason shima ta fahimci rauninsa kai tsaye..............✍


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

   


*_Typing📲_*




*_Chapter Seven_*


..........Lokaci da aka basu da ga gidan gwamnati na kamo wannan gagarumin ɓarawo da babu wanda yasan ainahin kamanninsa na zahiri yay matuƙar tada hankalin kowacce hukuma ta ƴan sanda dake a jihar. A ɓangaren jami'an ƴan sanda na farin kaya tuni sun duƙufa wajen bincike suma. Musamman da ya kasance jami'ansu ne suka sami nasarar samo wheelchair da sauran kayan da ɓarawon yay amfani da su a waccan ranar.

            Tabbas wannan ɓarawo yana da matuƙar wayo da dabaru kala-kala da ganosa ke bama duk wasu jami'ai wahala kai tsaye. A duk ɓarnar da zai aikata yana aikatata ne da maban-banta fuskoki da salo daban-daban kuma. A kusan shekara biyu kenan da fitowarsa a bayyane babu wanda zai iya cewa ga fuskarsa ta ainahi ko samun wani labari nasa koda ƙanƙani ne.

        Duk da dai wasu a cikin jami'ai da suka ƙware sosai wajen aiki da binciko mai laifi sun taka rawar gani sosai wajen kafa masa tarkuna na musamman amma yana tsallakesu saboda duk tsiyar da zai shuka ba gaba gaɗi yake aikata ta ba sai ya shirya da shiri na gaske.

          Bayan zama na musamman da sukayi jiya game da binciken da sukeyi akansa furucin matashiyar budurwa ya shigo cikin jerin abubuwan da suka zauna domin tattaunawa. Lokaci ne da bai kamata suyi sakaci da duk wata dama da zatazo musu ba komin ƙanƙantarta. Dan haka basu tsaya sanya ba wajen bibiyar matashiyar budurwa mai cikakken suna *_MUHIBBAT ALIYU HAMZA_* da jami'insu ya kawo musu labarin alwashinta akan abin farautarsu. Dan haka suka kasance biye da ita tun a safiyar yau, tun daga ƙofar gidansu har zuwa cikin makaranta, shigarta class da fitowarta zuwa Computers room. Dukkan binciken data gudanar har zuwa kiran da taima Yaya Abubakar duk akan idon wanda ke biye da ita ne batare data sani ba...

       

         Sosai tashin hankali ke tattare da Muhibbah ganin inda aka kawota. Duk da Yayanta jami'in tsaro ne na ƴan sanda mai muƙamin d.p.o bata taɓa zuwa police station ba. Amma a yau sai gata a cikin headquarters na ƴan sandan farin kaya tsumu-tsumu batare da tasan laifin data aikata ba.

         Wani lafiyayyen office aka kaita da yaji kayan more rayuwa tamkar ba'a hukumar ƴan sanda ba. Ta saci kallon dattijon mutumin dake zaune kansa duƙe yana aiki kan takardun dake a gabansa. Cikin girmamawa wanda ya shigo da ita office ɗin ya ƙame yana salute ɗinsa.

        Sai a lokacin ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi ya dubesu ita da shi. Kansa ya jinjinama wanda ya kawota ɗin idanunsa a kanta. Gurin zama ya nuna mata da faɗin, “Ɗiyata bismilla zauna ko?”.

        Ajiyar zuciya ta saki dan har cikin ranta ta ɗanji sanyi. Gaishesa tayi da girmamawa zuciyarta na sake samun nutsuwa da shi. Ko ba'a faɗa mataba a yanayin shigarsa da shekarunsa ya isa tabbatar mata shi ɗin mai faɗa aji ne a hukumar.

           Ɗan kafeta yay da idanusa na kusan sakan ashirin ko ƙyaftawa bayayi. A take tsigar jikinta ta fara tashi tsoro na sake faɗaɗa a zuciyarta. _Hasbinallahu wa-ni'imar wakil_ ta shiga maimaitawa tare da sunayen ALLAH.

          Murmushi ya sakar mata da yin ƙaramar gyaran murya yana ɗauke idanun nasa a kanta. Cikin taushin murya yace, *“Muhibbat Aliyu Hamza ko?”.*

        Hibbah ta jinjina masa kanta cikin dakiya da dauriyar hana bayyanar gazawarta tana faɗin, “Eh yallaɓai”.

       “Ɗalibar koyon kimiya da fasaha a babbar jami'a ta jihar nan?”.

     Nanma kanta ta jinjina masa da faɗin, “Eh yallaɓai”.

        “Uhm masha ALLAH. ALLAH yay riƙo da hannayenki ki zama abar alfahin ƙasarki baki ɗaya. Ina matuƙar son naga ƙananun yara musamman ma mata masu himma da ƙwazo akan abinda yay mana ƙaranci irinki”.

      A karon farko Hibbah ta saki murmushin jin daɗin yabon data samu da ga garesa tana faɗin, “Thanks you Uncle”.

        Murmushi ya sakar mata har haƙoransa na bayyana. “Kinsan miyasa aka kawoki nan?”.

        “A'a Uncle”. Ta faɗa cike da marairaicewarta da taso bashi dariya amma sai ya danne. Cikin ƙwarewar aiki ya ce, “Taimakonki muke nema akan masu power bike ɗin jiya da suka kusan tureku, harma sister ɗinku taji ciwo a ƙafarta”.

        Kallonsa Hibbah tayi cike da tsarguwa. Fahimtar hakan da yayi ya sashi saurin faɗin, “Muna son gano kosu ɗin ƴaƴan waye? a garin nan, mu kuma kamasu mu hukuntasu. Dan bai kamata ba ace dan kawai suna ƴaƴan masu arziƙi ba su dinga shatar tituna suna zabga gudu tamkar nasu su kaɗai. Zasu iya amfani da wannan damar suyita kashe al'umma saboda ƙarfin ikon iyayensu kuma talaka bazai iya kai ƙara a ƙwatar masa haƙƙinsa ba. Yanzu bayan ALLAH ya taƙaita muku wahala jiya da bamusan halin da kuke ciki ba zuwa yanzu ai ko. Kalla nan kiga”.

      Ya ƙare maganar yana ɗaukar remote ɗin da ke gabansa tare da janye idanunsa a kanta ya maidawa ga ƙatuwar tv dake mamake da kusan rabin bangon office ɗin. “Kinsan wannan mutumin?”.

         Fuskar dattijo mai cike da ƙasumba a cikin shigar manyan kaya ta bayyana. Kallon kusan minti ɗaya tai masa kafin ta girgiza kanta. “A'a yallaɓai ban sanshiba. Bamma taɓa ganinsa ba”.

        Wani ya kuma nunowa da faɗin, “Wannan fa?”.

         “Shima haka ban sanshi ba”. Hibbah ta faɗa idonta akan hoton matashin saurayi mai saida rake a Wheelbarrow.

        Cigaba yay da latso mata hotuna kala-kala na mabanbanta mutane tana cewa bata sansu ba. Sai wani guda biyu na kusan ƙarshe data taɓa gani an nuna a labarai kwanaki.

        “Yallaɓai wannan dai na taɓa ganinsa a tv, dan an taɓa nunasa kwanaki a labarai, kuma hoton yata yawo a social media akan cewar shi ɗin babban ɓarawo ne ɗan yahoo da ya yashe manyan kuɗaɗen wani attajiri. Yayana ma yace suma suna nemansa ruwa a jallo. Kuma nemansa kukeyi halan?”.   

        Sosai ma kuwa nemansa muke muma tare da waɗancan na farkon dana nuna miki. Amma rashin mai taimaka mana irinki yasa mun gagara hakan. Amma shiɗin wanene yayan naki?”

      Kanta tsaye batare da tunanin komai ba ta ce, “Uncle shima ɗan sanda ne”.

         “Woow masha ALLAH. Lallai naji daɗin hakan sosai. Kuma zanso ganinsa shima harma nai masa ƙarin girma saboda samun ƙanwa irinki mai ƙwazon da ya kamata ƙasa gaba ɗaya tai alfahari dake”.

     Murmushi tayi cike da jin daɗin jin za'a ƙarama Yaya Abubakar ɗinta girma ta sanadinta. Shima ganin ta hau yanda yake buƙata saboda ƙuruciya sai ya ƙara faɗaɗa murmushinsa da faɗin, “Idan har kikai mana wanann taimakon da zan miki bayani akansa yanzun to lallai yayanki zai ƙara zama babban mutum, kema kuma zaki rama jin ciwon da aka saka ƙawarki tayi jiya. Da ga ƙarshe zaki samu ƙyauta mai tsokar gaske”.

         Batare da tunanin komaiba ta ce, “Insha ALLAH zan taimakeku Uncle, indai Yaya Abubakar zai ƙara samun girma”.

          Cike da jinjina wautarta fara'ar fuskarsa ta sake bayyana. “Yauwa ɗiya ta. Aikin da zaki mana shine gano mana inda masu power bike ɗin jiya suke.”

      “Lah Uncle ai nama g.....”

Sai kuma tai shiru tare da dafe bakinta saboda tunowa da gargaɗin Yaya Abubakar na ɗazun akan karta sake ta sanarma kowa.

      “Miya faru ki kai shiru ɗiyata?”.

        Da sauri ta girgiza masa kanta. “Babu komai Uncle, inason kai musu magana su fara bani wayata nayi magana da Yaya Abubakar”.

        Shiru yayi cike da nazarinta, a zuciyarsa. Yace (Yarinya mai wayo). A fili kam ganin ta kafesa da ido yay saurin sakin murmushi. “Okay okay babu damuwa zan musu magana su baki. Amma kafin hakan zaki cika mana alƙawarin mu. Idan ba hakaba kuma zamu cigaba da riƙeki anan, tare da sakawa a kamo mana Mamanki dasu yaya Abubakar ɗin naki mu faɗama duniya cewar sunada alaƙa da wancan hotunan mutanen da muke nema kin amince?”.

        A take dukkan fara'ar dake kan fuskar Hibbah ta ɓace ɓat. Shima tuni saɓanin murmushi ya maye gurbin tasa fuskar. Ya kuma tsatstsare ta da idanunsa cike da tsoratarwa. “Yanzun nan zan bada umarnin zuwa a ɗakko min Umminki. Tare da Yayanku Muhammad har wajen aikinsa. Sai Umar da Usman. Aliyu (Ammar) kuwa yanzu haka akwai jami'anmu dake zagaye da shi a makarantarku. Kalla nan”.

         Ya ƙare maganar da juya mata lap-top ɗinsa. Wani irin firgici da ruɗani ne suka bayyana a fuskar Muhibbat ganin hotunan Yayunta tare da hotunan ɗazun daya nuna mata na waɗanda ake nema. Kowanne da taƙaitaccen bayanin dangantashi da waɗan can masu laifin. A ƙarshe aka bayyana Ummi matsayin mahaifiyarsu tare da ita mai taimaka musu kasancewarta masaniya akan ilimin sarrafa Computer.

       Saurin ɗora hannunta tayi akan baki saboda kukan dake neman kufce mata. Ta shiga girgiza masa kanta a kiɗime. “Please yallaɓai kar kai haka dan ALLAH. Ni ƴan uwana ba ƴan ta'adda bane. Basu taɓa aikata laifin komai ba sai alkairi. Karka zaluncesu ta dalilina....”

          “Inhar baki so ganinsu a cikin wani hali sai kiyi mana abinda muka sakaki ki zama sanadin alkairinsu. Bawai ina lallaɓaki bane dan bazamu iya sarrafaki kimana dole ba. Inda naso tursasaki da tun a daren jiya zamu ɗakkoki har gida kiyi mana aikin akan dole.” yay maganar a matuƙar kausashe yana bugar desk ɗinsa.

     Ɗan zabura baya Hibbah tai jikinta na rawa. Yayinda shi kuma ya shiga ƙwala kiran sunan jami'in su Nura.

        Da sauri Nura ya shigo yana ƙamewa da faɗin, “Yes sir!”.

          “Maza a shirya jami'an da zasu fita operation yanzun nan.”

     “Okay sir”. Ya sake faɗa da girmamawa yana ficewa.

       Miƙewa yay shima yana nuna Hibbah da faɗin, “Oya miƙe”.

       “Yallaɓ.....”

Hannu yasa yay zipping bakinsa alamar karta sake cewa komai.


            Ɗakin da ke ajiye da na'urori masu ƙwaƙwalwa aka kai Hibbah. Inda suka sami mutane kusan goma sha uku a ciki. Kai tsaye wajen zama aka nuna mata alamar dama ita ake jira. Zama tai tana haɗiyar zuciya. Batason yin aikin saboda gargaɗin Yaya Abubakar. A gefe kuma batason a cutar mata da ahali akan abinda basu ji ba basu gani ba. A wani gefe na zuciyarta kuma nason yi kodan abinda mutanen suka nema yi musu jiya har ga Hafsat da ciwo.

           Waya irin ta jami'an tsaro aka ajiye a gabanta. Tare da kunna ƙaton tv irin na office ɗin data baro da shima ke a jikin bango. Hoton yayunta da rahotannin da aka shirya na karya dan tsoratar da ita suka bayyana.

    Ta sauke idanunta dake cike da ƙwalla a hankali bisa computer ɗin gabanta.

       “Ki nutsu wajen yin aikin da zai ƙuɓutar da ƴan uwanki zama criminals zuwa taurari ta sanadinki, ko kiyi sakacin yin aikin da zai dusashe haskensu da ga taurari zuwa criminals ta sanadinki.”

    Mutumin ɗazu ya faɗa cikin tabbatarwa da murya mai kaushi.

     Kai kawai ta jinjina masa tana maijin wani ɗaci a zuciyarta da taurin zuciya. Sai da tayi addu'a a cikin zuciyarta kafin ta fara aikin cike da ƙwarewa. Kasancewar ɗazun dama ta binciko a inda suke sai yanzu batasha wahala ba duk da wannan Computer ɗin nada matuƙar tsaro fiye da tasu ta makaranta.

           Da wayar gabanta ta dinga amfani wajen yin magana da jami'an da suka fita operation ɗin tana sanar musu hanyoyin da zasu bi har zuwa location ɗin da agogon data jefama masu power bike jiya yake. Hakan shike nufin tabbacin samun su inhar agogon na tare da su basu farga sun yadda ba.......


\★/★\★/★\★/★\★/★\★/★\


                 Anguwar *_jahje street_*, anguwace mai ƙarancin rashin hayaniyar jama'a kasancewar ta ɗauke da manyan gidaje na masu hannu da shuni. Ko da rana ka shigo wannan anguwa zaka sameta tsit tamkar halittun da ke a cikinta basa numfashi. Akan samu ƙarancin gittawar ababen hawa da na mutane masu tafiya a ƙafa sai dai jefi-jefi. Shima hakan tafi kasancewa a ranakun hutun ƙarshen mako ko hutun ranakun ma'aikata da kan gitta.

          Sabo da rashin sakewarsu da juna yasa bazasu iya tantance kansu ba dan rayuwa ake ta babu ruwan wani da wani. Idan kaga magana ta shiga tsakaninsu sai idan ALLAH yasa ka fito maƙwafcinka ma ya fito ai gaisuwar hello hi shikenan kowa ya shige sabgar gabansa.

           A cikin gida mai lamba 110 matasan samari ne da shekarunsu zai iya kaiwa ashirin da biyar zuwa da shida, harma mai da bakwai za'a iya samu. Gaba ɗayansu bakwai zaune suke a ƙayataccen falon gidan mai matuƙar girma da ƙawa ga mai kallo. Su dukansu kowa harkar gabansa ya ke yi. Wasu na kallon ƙwallo, wasu na daga gefe suna sarrafa wayoyin hannunsu.

       Ɗaya da ga cikinsu ya nutsu wajen sarrafa waya. Sai dai a hakan hira kan shiga a tsakaninsu musam akan kallon ƙwallon da mutum huɗu suka fi maida hankali a kansa.

        Wani mahaukacin horn daya nema harmutsa kwaƙwalensu da ga gate ya sakasu miƙewa a rikice gaba ɗayansu suna ambaton *_Master!!_*. Biyu da ga ciki suka shiga tattare ledojin dattin da sukai ciye-ciye tare da gwangwanen maltina da coc.. Ɗaya ya fita a guje domin zuwa ya buɗe masa ƙofar falon da ke rufe da security.

          Buɗe ƙofar yayi dai-dai da isowarsa cikin takun ƙasaita da tabbatar da shiɗin fa ya isa. Sanye yake cikin baƙin wando jeans da baƙar t-shirt. Sai dai ya ɗora jacket baka itama a samanta batare da ya ja zip ɗinta ba. Sam ba'a ganin fuskarsa, sakamakon hular jacket ɗin dake har saman kansa, ga norse mask da baƙin google toshe da idanunsa. Ƙafarsa ma sanye take cikin baƙin takalmi.

     Cikin zafin nama da ALLAH yay masa yasa hannunsa da ke sanye cikin safar hannu ya matsar da wanda ya buɗe masa ƙofar ya shigo cikin falon.

      Hakan ya kara tabbatar musu da babu lafiya, dan kowa bai kalla a cikinsu ba ya nufi wata ƙofa a hargitse.

     Kallon juna sukayi cike da tsoro, cike da ƙarfin hali ɗaya da ga cikinsu yace, “Brothers babu lafiya fa”.

       “Tabbas babu lafiya Khalid. Akwai abinda ya saka Master a wannan yanayi.....”

     Maganar tasa ta kakare a maƙoshi saboda fitowar wanda suke kira Master. Cikin wata irin murya mai amo da nutsuwa ya fara magana da faɗa. “Ina kayan da kuka fita aiki da su jiya?”.

      A tare sukai rige-rigen nufar ɗakunan barcinsu. Babu jimawa sai gasu suna dawowa ɗaya bayan ɗaya da kayan a hannu. Na'urar bincike da ke a hannunsa ya shiga kangawa jikin kayan. Akan jakkar Habib ta tabbatar da zarginsa. Ya fisgi bag ɗin da sauri yana zazzage dukkan abubuwan da ke a ciki, sannan ya ɗaura na'urar akan kayan. Saurin daukewa yay ya sake maidawa akan jakar. ƙaramin fuskar agogo mai kama da flower dake manne a jiki ta fara kawo jar danja tana ɗaukewa. Yay saurin fisge agogon da dudu-du girmansa bai wuce girman ficika ba. Numfashi ya fusga da ƙarfi, hakama sauran yaran nasa duk sai da sukai ajiyar zuciya. Dan abinda sukaga ya cire ɗin ya tabbatar musu wani ya kafa musu tarko ne ba tare da sun farga ba.

           Batare da yace dasu komai ba ya nufi na'urorin dake acan gefen falon an katangesu da glass na ƙawa daya zamewa falon baki ɗaya ado. Cikin wata na'ura ya saka agogon, bayan kamar sakan biyar ya cire ya fito ya nufi waje. Yana fita suka shiga kakkauda duk wani kaya suna maida shi a salon da zai basu kariya dan da alama yau ta ƙwaɓe.

       Baifi mintuna uku da fitarba sai gashi ya dawo. Hanyar ƙofar da ya nufa ya sakasu binsa da sauri suma dan sun kammala kauda dukkan abinda ya kamata su kauda ɗin. A kuma dai-dai lokacin sukejin ƙarar buɗe gate ɗin gidan alamar wanda suka sami nasarar bibiyar tasu sun iso. Sun kumafi ƙyautata zaton ƴan sanda ne abokan *_TAKUN SAAƘAr_* su.............✍

        


         *_Hum, wannan fa shine ana dara ga dare yayi🐒🚶🏻_*


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_MG's SKINCARE_*


*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*💃🏻


*_To maza kuzo ga mg's skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*


*_mg's skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*💃🏻💃🏻


*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne a gareku💃🏻_*


*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi💃🏻_*


*_Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za'a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*


_Duk zaku tabbatar da hakanne ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari💃🏻😍🥰_.


Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call

08064532391

Instagram: glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare

Location:kaduna buh we deliver Nationwide

Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift


_*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_


*___________________________*


*_Chapter Eight_*


...........Wani wawan tsaki ya ja tare da kai hannu kan Wadrobe ɗin dake a jikin bangon ɗakin ya danna wani maɓalli. A take ta zuge kanta, ɓoyayyar ƙofar sirri da ke a jikin bangon ta bayyana.

        Cikin sauri suka shiga shigewa mamaki fal ransu, dan ko su da ke tare da shi tsahon shekaru basu taɓa sanin da ƙofar ba. Bama batun ƙofa kawai ba, ko fuskarsa ta ainahi har yanzun basu sani ba. Yanda yake zuwama duniya da mabanbanta fuskoki suma haka yake zuwa musu, duk da kuwa akwai alaƙa tsakaninsa da wasu a cikinsu ta zuminci.

        Shi mutum ne mai aiki da matuƙar taka tsan-tsan a kowane ɓangare, shiyyasa yay dogon zangon da har yanzu an kasa cimmasa a duk tarkuna da ake ɗana masa, dan kota ina idanunsa a buɗe suke, hakama kunnuwansa. Sai da duk suka gama fita yana kallon jami'an tsaron da ke shigowa cikin gidan da sanɗa ta cikin tab ɗin dake a hannunsa. “Humm” ya faɗa yana rufe tab ɗin, shima yabi bayan yaran nasa tare da maida ƙofar a yanda take kamar babu.

           Koda ya fito bai tankasu ba, sai wasu ƙananun fitilu masu azabar haske daya fiddo a aljihun wandonsa  ya shiga kunnasu yana mika musu, A take ko ina ya gauraye da haske har suna iya ganin gabansu. Sam babu ruwa ko datti a ciki, hanyace ɗoɗar da basusan iyakarta ba, domin dama can ba'a yisa dan ruwa ya wuce ba. Sukam dai ɗunbin tsoro da mamakin Master ɗin nasu tuni ya gama kashesu a tsaye. Tun fitowarsu a ɗakin da suka tsinci kansu a cikin doguwar hanyar ruwa komai ya kuma kwance musu game da shi. Sagade sukai suna kallon ikon ALLAH da sake tsorata da al'amarinsa. Lallai sun sake yarda da gaskiyar zantukan mutane da ke kiransa *Hatsabibi shu'umi*.

          “Zakuje ne ko zaku tsaya kallo na?”.

        Sautin furicinsa ya maido da hankalinsu jikinsu kusan a tare lokaci guda.

       Da sauri suka haɗa baki wajen faɗin, “Sorry Master!”.


★★★


            Jami'an tsaron da suka iso anguwar bisa jagorancin Hibbah da ke basu haske ta hanyar waya kuwa tun kafin su iso gidan suka ajiye motocinsu can farkon layin suka ƙaraso da ƙafa. Mai-gadi da dama yake zaman jiran tsammani kamar yanda Master yay masa bayani ana yin knocking gate ɗin ya tashi ya buɗe bayan ya ƙara ƙarar redio ɗinsa da yake ji.

       Jami'in da ya fara isowa wajen cikin son nuna basaja ya bama mai-gadi hannu yana murmushi. Babu musu shima mai gadin ya bashi hannu sukai musabaha cikin nuna ƙaulanin rashin sani.

        “Sai dai gashi ban waye kaba bawan ALLAH. Kuma su alhaji basu sanarmin wani baƙo zaizo nan ba”. Mai-gadi ya faɗa lokacin da yake sakin hannun jami'i da yazo a suffar basaja.

            Jami'in da furucin mai-gadi ya ɗan tsaya masa a rai ya ce, “Kana nufin masu gidan basa nan kenan?”.

       “Tabbas basa nan mai-gida. Yau kwanansu tara kenan da komawa can ƙasar da suke zaune ai”.

         Wani kallon kama rainamin hankali jami'in yay masa, amma sai ya saki murmushi da maida hannayensa baya yanama ƴan uwansa alamar su taho ba tare da yasan mai-gadin na lure da shi ba.

      Baki mai-gadi ya buɗe zai sake magana sauran jami'an suka iso suma. Bindiga wanda ya fara zuwa ya nuna masa tare da turasa cikin gidan duk suma suka shishshigo. Duk rarrabuwa sukai a kowace kusurwa ta gidan suka fara shiga da sanɗa, wanda ya fara zuwan kuma na tare da mai-gadi da zuciyarsa ke cike da tsoron kar dai ƙaryarsu ta ƙare yau, dan shi duk tunaninsa su Master na'a cikin gidan suma tunda bai sanar masa shirinsa ba bayan aikin da zaiyi kawai. Duk da ya yarda da hatsabibancin uban gidan nasu amma dolene akwai ɓacin rana. Da alama kuma idan har ta ƙwaɓe yau da shi zata fara ruftawa. To amma insha ALLAH zaiyi ƙoƙarin ganin ya bi duk abinda Master ya faɗa masa yanda ya kamata.

            Sai da jami'in nan ya tabbatar abokan aikinsa sun gama zagaye gidan sannan ya tasa ƙeyar mai-gadi shima suka nufi ciki. Ƙofar shiga da suka fahimci a rufe take suka bashi umarnin buɗewa. Amma sai ya nuna musu sam bai san password ɗin ba shi.

         Jikinsa jami'in ya fara laluba, ya ciro waya nokia da tasha ɗaurin ƙyauraye da salataf. Wayar ya jujjuya a hannunsa yana ƙare mata kallo fuska a yatsine, kafin ya maida dubansa garesa yana sake gyara zaman bindigar da ya ɗora masa a saman kai.

       “Nasan dai kanada number ɗin mai-gidan, maza ka kirashi yanzun nan ya faɗa maka password ɗin komu ɓalla ƙofar a yanda muka gadama.”

       Babu wani nuna damuwa ko ɗar mai-gadi ya amsa wayar ya shiga laluben Number. Dailing yayi kansa tsaye, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Ya sake kira a karo  na biyu, sai da taje gab da tsinkewa aka ɗaga cikin muryar isa. Cikin girmamawa mai-gadi yay gaisuwa, sannan ya ɗara da bayanin cewar jami'an tsaro ne sukazo gidan suna buƙatar password na ƙofa wai zasuyi bincike, bai san mi suke nema ba. Carab jami'in ya amshe wayar yasa a kunnensa bayan ya kalla no. Ɗin da mai-gadin ya kira ya tabbatar da ta ƙetare ce.

           “Jami'an tsaro kuma? Rabi'u!. To mu miya haɗa gidanmu da jami'an tsaro?”.

      “Bincikenmu ne ya nuna mana wannan gidan na masu laifine Alhaji. Bazamu tabbatar da ba haka bane ba sai mun shiga mun duba kuma. Dan haka muna jiran mabuɗin sirrin ƙofar da ga gareka kawai, kafin muyi magana ta gaba da kai idan har ya kama”.

      “Okay to babu damuwa yallaɓai”. Daga can aka faɗa tare da zayyano masa password ɗin.

       

      A sakawa ɗaya kuwa ƙofar ta buɗe. kusan rabi a cikinsu suka shiga ciki akabar wasu a waje. Akan idon mai-gadi suka shiga hargitsa gidan tako ina. Sai dai abin mamaki babu wani alamun abun rashin gaskiya da sukayi gamo da shi. Cikin glass ɗin nan da computers ke ciki ɗazun yanzu babu shi, sai wasu ƙayatattun flowers masu ɗaukar hankali da ƙamshinsu ya cika falon.

        “Tabbas yarinyar nan ƙarya take mana. Ko tana ɗaya da ga cikinsu ne yawo da hankalinmu kawai take son yi”. Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa a hasale.

               “Sam banajin hakan a raina, akwai dai wani ɓoyayyen abunda bamu sani ba. Karku manta shiɗin mutum ne mai matuƙar wayo da dabaru kala-kala. Tabbas ya fahimci ana bibiyarsa ne ya bada ƙafa. Kokuma yayi amfani da wanann location ɗin domin sakamu zargi.”

        “Nima zuciyata tafi rayamin hakan yallaɓai”. Wani ma ya sake faɗa cikin jin zafi.

        “Karku samu damuwa. ai rana 99 da tara na ɓarawo, ɗaya tak na mai kaya. Inhar kere na yawo, zabo na yawo watarana dole a gamu. Tunda yace shi hatsabibi ne ya samu dai-dai da shi kuwa. Zamu bar wasu a gidan nan har sai mun tabbatar da gaskiyar babu wani abun zargi a cikinsa”.

      Duk sun amsa da girmamawa. Shi dai mai-gadi kallonsu kawai yake yana kwasar dariya a zuciyarsa. Koda suka fito harabar gidan sun tsara wanɗanda za'a bari, wanda zasu koma kuma suka nufi hanyar barin gidan. Karaf idon ɗaya ya sauka akan bag dake rataye acan ƙarshen gate ɗin gidan ta waje. Saurin zuwa yay ya ɗakko yana nuna musu. Commander ɗin operation ɗin nasu ya amsa yana zazzage jakkar cikin kulawa gudun kar a saka musu bom a ciki.

    Agogon Hibbah ne ya fara faɗowa tare da takarda mai ɗauke da sunansa akoda yaushe da facemark. Sai ɗan gajeren rubutu a bayan takardar.

        *_“Bibiyata na nufin ƙare rayuwarku a wahala. Inhar bani naso kusan niɗin wanene ba, bazaku taɓa ganoni da kanku ba har abada insha ALLAHU rabbi. Dan haka ku daina azabtar da kanku wajen bibiyata komai yana da lokacinsa”_*

         _Master👌🏼_

    Wani wawan tsaki jami'in daya gama karanta takardar yaja. Ya cije leɓensa na ƙasa da ƙarfi, cikin alwashi yace, “Ni kuma na maka alƙawarin da wannan hannun nawa zan kamaka, sannan na maka horo mai tsananin gaske wanda sai ka gwammaci mutuwarka da rayuwarka shaiɗani”.

         Suma sauran zukatansu na matukar ƙuna suka ɗauki nasu alwashin.....


___________★★★__________


          Yaya Abubakar ya shiga tashin hankali matuƙa lokacin da yake isowa cikin makarantar su Hibbah yaji abinda ya faru a bakin Ammar da Zahidah. Tare da samun ƙarin bayani a bakunan wasu ɗaliban.

      Da taimakon wani malamin su Hibbah ya shiga Computers room nasu yay bincike a computer ɗin da ta gudanar da binciken. Sai dai kuma ta saka security, shiga yay gwada passwords kala-kala yayi wanda yasan tana amfani da su a gida ko zata iya amfani da su. Sai dai sam babu wanda ya buɗe. Cike da ɓacin rai ya mike yana bugar desk ɗin cikin ƙunar zuciya. Lalubo wayarsa da ke ring a aljihu yayi. Yaya Muhammad ne, ɗagawa yay sukai yar magana ya yanke. Wani abokinsa ya kira kasancewar shi jami'i ne a hukumar ƴan sandan ta farin kaya. Ya tabbatar shine kawai zai iya bincika masa idan Hibbah na hukumar tasu. Bayan ya ɗaga ko gaisuwar kirki ba suyi ba ya sanar masa bukatarsa. A take jami'in ya tabbatar masa lallai Hibbah na'a headquarters ɗin tasu dan yaji ƙishin-ƙishin ɗin zancen yanzu a bakin wani ogansu cewar akwai yarinya da ke da alƙa da case ɗin na jiya.

     Yanke wayar kawai yayi batare da sun ƙarasa maganar tasu ba, ya kira Yaya Muhammad yana sanar masa a inda zasu haɗu yanzun nan......


__________________________


           Master da yaransa kam bayan ƴar tafiyar da sukayi ta cikin hanyar kwata sai gasu sun ɓilla ta wani ƙaramin gida. Gidane ginanne mai ƙyau na dai-dai mai matsakaicin ƙarfi. Yanda yake bin ko ina cike da nazari haka suma suke kallon gidan. Bayan kamar mintuna biyu ya gyara tsaiwarsa sosai yana fuskantarsu. Binsu ya gamayi da kallo ɗaya bayan ɗaya batare da su suna kallon ko ƙwayar idonsa ba. Tabbas sun jima suna kwaɗayin ganin fuskarsa, amma sam yaƙi basu damar hakan koda da kuskure..

           _Gyaran muryar da yay ne ya katse tunaninsu. Ya sake gyara tsaiwarsa yana tura hannayensa duka cikin aljihun wandonsa. Muryarsa a kausashe da tabbatar musu da fushinsa ya fara magana cike da nutsuwa da ƙasaitar sa,

          “Yau mun tsallake rijiya da baya, amma wataran saboda sakacinku tabbas bazamu tsallake ba. A kullum ina faɗa muku duk sanda zakuyi aiki, ku ringa yinsa da *_ƘWAƘWALWA  DA ZUCIYA_* a haɗe. Dan duk lokacin da ɗan adam yay amfani da ƙwaƙwalwa kawai wajenin aikata muhimman abubuwa to ya tabbatar zai kasance mai yawan shiga ruɗani da tafiya yana dawowa baya saboda wani ya fika kaifin basirar. Idan ko da zuciya kaɗai ka dogara wajen ginin muhimman abubuwa, kasani nasararka ragaggiyace saboda zuciya abinda ke mata daɗi kawai take ayyanawa da buƙatar ya kasance mata. Bai kuma zama lallai ka kasance cikin jin daɗi da farin ciki ba a kowanne daƙiƙa na rayuwarka. Dan wani lokacin hanyar jin daɗi wahala ce, wata hanyar wahalar kuma jin daɗi ce. Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe, idan ba hakaba ni ɗin nan da kaina zan bada ƙafar da za'a kama duk wanda ya cigaba da sakaci a cikinku. Ba kuma zan taɓa kuɓutar da shi ba har sai ya jigata yasan muhimmancin bama kasan kariyar yin aiki cikin tsantseni. Duk wanda ya haremu ya sokemu akan dai-dai kuma na jinjinama ƙwaƙwalwarsa da kaifin tunani. Sai dai na baku awa goma kacal ku ganomin koshi ɗin ɗan gidan uban wanene. Dan sai ya amshi hukunci dai-dai da iyawarsa!”_.

        “Insha ALLAHU zamu kiyaye sir. Muna kuma neman afuwa daga gareka”. Suka faɗa a tare cike da girmamawa a garesa. Yayinda Habib da yasan komai ya farune ta sanadinsa yay ƙasa da kansa bayan ya sake matsowa gabansa. “Ka gafarceni Master, dan wannan tabbas sakaci na ne. Amma wlhy sam bansan ta yaya akai hakan ta kasance ba. Sannan koda muka dawo kuma ban fargaba.”

       Hannu kawai ya ɗaga masa batare da yayi magana ba. Sai kuma ya nufi ƙofar fita da ga gidan baki ɗaya. Da kallo duk suka bisa har ya isa ƙofar ya buɗe sannan ya juyo yana kallonsu shima.

      “Zan sake maimaita muku awa goma kacal, na samu cikakken labarin akan ko shiɗin wanene!......” Daga haka ya ida ficewa baki ɗaya.

         A tare suka sauke ajiyar zuciya. Sun tabbatar a salon da yay maganar babu wasa a cikinta, dama can kuma ba wasan ya ke musu ba ballema su ɗauketa wasa. Suma kuma har cikin ransu suna bukatar sanin wanene wanda yay musu wannan tarkon da suka tsallake rijiya da baya?..........✍


           *_Gadai jami'an tsaro basu sami nasarar aikin Hibbah ba, ga kuma Master ya bada awanni goma domin binciko wanda ya haresu, hibbah dai kuma itace ta kai harin da babu niyyar dalilin da su suke kallo. To yaya zata kasance kenan tsakanin Muhibbat Aliyu Hamza da Jami'an ƴan sanda da Master kenan?🤔. TAKUN SAAƘA wasa farin girki👎🏻_*


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

   




      


      *_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_MG's SKINCARE_*


*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*💃🏻


*_To maza kuzo ga mg's skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*


*_mg's skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*💃🏻💃🏻


*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne a gareku💃🏻_*


*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi💃🏻_*


*_Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za'a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*


_Duk zaku tabbatar da hakanne ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari💃🏻😍🥰_.


Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call

08064532391

Instagram: glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare

Location:kaduna buh we deliver Nationwide

Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift


_*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_


____________________


*_Chapter Nine_*


.............Tunda jami'an suka dawo da labarin rashin nasara zukatan manyansu yay matuƙar ƙunci. Awanni ƙalilan suka rage musu da ga umarnin gidan gwamnati. Cikarsu babu Master a hannunsu kuwa yana nufin sun gaza a idanun al'ummar jiharsu da ƙasa baki ɗaya. Hakama ga gwamna da muƙarrabansa.

        A gefe ga gidajen jaridu da duk wata kafar yaɗa labarai sun baza kunnuwa da idanun domin ganin yanda awanni ashirin da huɗu zasu cika tare da wannan ɓarawo a hannunsu ko saɓanin hakan.

       Waɗan nan tunane-tunanen nasu yasa su shirya zaman meeting na gaggawa.


        Dukkan wani babba mai alhakin faɗa aji ya hallara a ɗakin da meeting ɗin zai gudana. Sai wanda ya jagoranci jami'an da suka dawo yanzun nan da shirin kamo Master da yaransa..

         Kowa ka kalla a ɗakin meeting ɗin kasan yaci ya ƙoshi, dan babu wasu kamannin wahala tare da su. Da'ace ƙasace mai ƙyaƙyƙyawan tsari sun cancanci yin ritaya duk su koma gefe a kawo matasa masu jini a jika da basirarsu ke aiki da kaifin ƙwaƙwalwa a zuba a madadinsu. Su kuma su zama dattijai masu bada shawara wa ƙasa ta bayan fage matsayinsu na iyayen ƙasa. Sai dai sam a wannan ƙasar tamu ba haka bane ba. Anyi sakacin barin matasan da ke da basirar zuwa da salonsu na ƙuruciya wajen kawoma ƙasa cigaba zama ƴan ta'adda, dukkan tarin basirarnan tasu da ƙuruciya ta koma aiki ne ƙarƙashin aikata laifuka. Iyayenmu da gwagwarmayar rayuwa da raunin shekaru sukaima yawa sun zama sune masu riƙe da madafun iko wajen zartarwa da hukuntarwa. A duk lokacin da ƙasa tai sakacin rashin amfani da basirar matasa da ƙuruciyarsu wajen aikata alkairi, to lallai shaiɗanu zasuyi amfani da basira da ƙuruciyar waɗanan matasan wajen kafa tantin ta'addancin da zai ruguza ƙasa.

      A ƙasarmu ta gado iyayenmu sune ƴan siyasarmu, sune masu riƙe da madafun iko na mulkin gargajiya da na siyasa, sune riƙe da hukumomin ladabtar da masu laifi, sune riƙe da manyan kuɗaɗe na kasuwanci, sune riƙe da makarantun da ake bamu ilimi, sune.. Sune... Sune komai.

      Babu wata hanya ko ƙofa da suka barma matasan wajen nuna bajintarsu da ƙwazon da ALLAH ya haliccesu da shi. Kallonmu suke masu yawan wauta, masu shashanci, masu ƙuruciya, masu rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da su. Masu... Masu... Ta ko ina. Amfaninmu kawai mu cigaba da zama a ƙasa har sai lokacinmu yayi. To yaushene lokacin namu zaiyi? Shin sai muma mun kai irin shekarunsu mu danne na ƙasa da mu kenan?. indai har a haka za'a cigaba da tafiya lallai da alamar ƙasar tamu bazata taɓa zama mai sauyawa ba ko samun ci gaba. Domin anyi sakacin ajiye lokaci an ɗauki rauni.

     Shi kuma lokaci a duk sanda aka gaza amfani da shi ta hanyar da ya dace wucewa yakeyi yabar mai shi da cizon yatsa da dana sani. A lokacin kuma daka buƙaci gyarawa sai ya kufce maka dan kayi sakaci wajen sarrafashi a sanda ya dace. To ya kamata manyan ƙasarmu su fahimci MATASANMU sune LOKACINMU. Cigaba da sakacin ƙinyin amfani da baiwarsu akan lokaci na nufin baragurbi amsarsu su su amfana da wannan damar wajen maidasu masu ruguza ƙasar da ku kuke ganin kunata ginawa. Sanda zakuyi ƙoƙarin son tarosu kuma sunyi nisan da bazasuji kiranku ba sam.

    Bawai munason fiddo da gazawarku bane ma duniya ko goyon bayan laifukan matasa. Muna buƙatar ku duba ku kuma fahimci sai da matasa ƙasa ke iya samun ci gaba. Basu dama kuma shike nufin daƙile dama a hannun masu ɗorasu bisa bigiren ta'addanci. Kun cancanci kuma muyi alfahari da ku, dan kun bamu gudunmawa ta musamman bayan kasancewarku iyaye a garemu.


       Bayan ƙarin bayani da suka samu a bakin jami'in da suka fita bibiyar Master zukatansu sun ƙara ɗaci. Ɗakin yayi shiru kowa na nazari da tunani a cikin zuciyarsa. Ɗaya da ga cikinsu da zuciyarsa ke raya masa wani abu ya nema izinin yin magana.

          “Bismillah, an baka dama. Ya kamata kowa ya faɗi abinda ke bakinsa ko hakan zai bamu wani haske da ga kullewar da kawunanmu sukayi.” Ogan nasu ya faɗa cike da taraddadi.

         Kansa ya jinjina da faɗin, “Thanks you sir. Dama wani tunanine yakemin yawo a zuciya game da ita wannan yarinyar datai mana aikin. Shin baƙwa tunanin shine ya tsara duk hakan kasancewarsa shu'umin mutum kuwa?. Al'amarin da matuƙar mamaki ta yanda ta bibiyesa cikin sauƙi. Idan har dama ba shirinsa bane ta yaya akai ta jefa masa abunda ta samu damar bibiyarsa?”.

       Da sauri wanda ke a kusa da shi ya ashe da faɗin, “Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba. Tabbas da alamar akwai lauje cikin naɗi game da wannan al'amarin. Nasan za'a iya samun mai ƙwazo da kaifin basirarta, amma yanda al'amarin ya faru da ƙanƙantar shekarunta sai nake ganin kawai shiri ne na musamman akai. Dan bana hangen tana da wani ƙyaƙyƙyawan tunanin da har zuciyarta zata bata damar aikata hakan. Banda shirme da shiririta mi yaran yanzun suka iya? musamman ma ita da ta kasance MACE”. Ya ƙare maganar cikin jin zafi sosai.

          Wanda ya gana da Hibbah dake ta faman buga pen a kan laɓɓansa yana kallonsu da nazarin maganganunsu yay murmushi. “Wannan tunanin namu na ganin yaranmu bazasu iya komai ba wajen taka rawar gani ke maida ƙasarmu da mu baya a koda yaushe. Da hakan kuma suke samun damar yin amfani da basirar tasu a gurɓatacciyar hanya. Tabbas ita ɗin MACE ce kuma ƙaramar yarinya, amma kallonta da rauni na *ɗiya mace* shine babban kuskuren mu. Banace inada tabbacin bata da alaƙa da shi ba, dan shi shu'umin mutum ne hatsabibi da zai iya aikata duk ma abinda bamuyi tunaninsa ba ko munyi. Sai dai banason mu kasa fahimtar cewar itama duk da kasancewar tata MACE zata iya taka wata rawar gani a harkar tsaro da duk wani sha'ani na rayuwa duk da raunin da ALLAH yay mata. Shawarata anan itace mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya”.

        Sake maida hankalinsu sukai garesa domin sonjin ƙarshen zancen.

      Ya gyara abin maganar gabansa yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. “Ma'anar mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya shine muyi amfani da wannan yarinyar ta hanyar riƙeta a jikinmu ta zame mana ma'aikaciyar sirri. Ta wannan hanyar zamu amfanu da alkairinta da kaifin basirarta. Mu kuma saka mata ido wajen gano shin akwai alaƙar da zuciyarmu take zargin tsakaninta da shi ko babu?”.

          “Yes! Wannan shawarar taka tayi matuƙa *A.G*”. Ogansu ya faɗa yana tafa masa. Hakanne yasa suma sauran tafa masa duk da wasunsu batai musu ba sam. Dansu babu abinda zukatansu ke ayyana musu sai ganin babu abinda Hibbah zata iya matsayinta na ɗiya MACE mai kuma ƙarancin shekaru.

          Sun cigaba da tattaunawa har zuwa wani lokaci, kafin ogan nasu ya bada damar shigo da Hibbah.


           Hibbah da damuwar ahalinta kecin ranta ta shigo fuskarta a cinkushe babu ko ɗigon walwala. Babu abinda zuciyarta tafi bukata a yanzu kamar tozali da Ummi da yayunta dan tabbatar da babu abinda ya faru da su. Zama tai a kujerar da aka nuna mata bayan ta gaishesu ranta fal jin haushinsu, musamman mutumin ɗazun da tun shigowarta da shi ta fara haɗa ido yana mata murmushi.

          Bayan sun gama nazartarta da ƙare mata kallo ogan nasu yay gyaran muryar da ta saka Hibbah ɗago manyan idanun ta kallesa. Ganin yanda ya kafeta da nasane ya sata sake maida kanta ta duƙar tana wasa da yatsun hannunta.

       “Muhibbat Aliyu Hamza!”.

Ya kirayi sunanta murya babu alamar wasa. Hakanne ya saka gabanta faɗuwa, ta sake ɗagowa tana amsa masa da rawar murya. “Na'am yallaɓai”.

        “Miye alaƙarki da Master!?”.

  “Master kuma yallaɓai? Ni ban sanshi ba”.

       “Kin tabbatar?”.

Kanta ta jinjina masa.

     “Taya za'ai mu yarda baki da alaƙa da shi?. Bayan tsahon shekaru biyu kenan kowace hukuma ta jami'an tsaro farautarsa suke, amma sun gaza koda ganin farcen yatsansa. Sai gashi ke a cikin kwana ɗaya rak kin haresa akan dai-dai?”.

        “Ni wlhy yallaɓai bansanshi ba, bakuma ni da wata alaƙa da shi ko sanin wanene shi. Na aikata duk abinda kukaga nayi ne saboda wasa da rayukan mutane da sukeyi ta hanyar power rider amma badan wani dalili ba”.

       “Okay, mu ɗauka hakanne kamar yanda kika faɗa ɗin. Yanzu wane tunani kikeyi game da makomar ahalinki?”.

        Saurin ɗagowa tai tana kallonsa idanunta cike da ƙwalla. Muryarta na rawa tace, “Amma yallaɓai naga na muku aikin da kuka buƙata dan na tabbata kun kamasa. Kuma kun tabbatar min hakan shine fansar ahalina ai”.

        “Eh tabbas haka muka faɗa, sai dai kuma ba'a samu nasara ba kamar yanda mukai tunanin za'a samu. Rashin samun nasarar kuma na nufin shigar ahalinki a haɗari ta fuska biyu. Na farko mu jami'an tsaro ba zamu barsu ba har sai wancan hatsabibin yazo hannunmu. Hakan shine zai wankeki a garemu mu tabbatar baki da alaƙa da shi, ahalinki kuma su kuɓuta. Na biyu dole ne mu baki kariya yanzun dan tabbas zaki zama abin farautarsa kema dan bazai barki ba tunda kin karya masa tarihi. Dolene kowane motsinki dana ahalinki su kasance a tare damu. Idan kin amince ki cike wannan. Kokuma kiyi tafiyarki amma babu ruwanmu da abinda zai samu ahalinki. Zakuma mu fitar da bayanan sune ke aikata laifukan da muka nuna miki ɗazun da mabanbanta fuskoki. Kinga za'a kamasu a kaisu kotu, da ga ƙarshe a yanke musu hukuncin kisa bayan duniya ta sansu matsayin ƴan ta'adda”

           Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Hibbah. Idanunta suka ciko da hawaye ta shiga girgiza musu kai laɓɓanta na rawa. “Dan ALLAH yallaɓai karkuyimin haka. Wlhy bani da alaƙa da mutumin nan sam, iya gaskiyata na sanar muku.”

           “Ta hanyar shigowa kiyi aikin sirri da mu ne kawai zai tabbatar mana da hakan, ahalinki kuma su kuɓuta da ga garesa da mu kammu. Gashi ki cike waɗan nan takardun idan har kin amince”.

         Da ƙarfi Hibbah ta rumtse idanunta. Wani irin zafi da ɗaci na sauka mata cikin zuciya. Karan farko na rayuwarta da taji tsiwa batai mata rana ba. Tanajin tsana mai yawan gaske akan mutumin da batasan wanene shi ba. Yayinda gefe na zuciyar tata ke jin haushin waɗan nan jami'ai da ke son yin amfani da damar da ALLAH ya basu ta hanyar amfani da ita. Wani gefen kuma na haske mata ahalinta cikin bala'i mai muni da idan har ta zama sanadin shigarsu cikinsa har gaban abada bazata taɓa yafema kanta ba. A take wani irin kangarewa da bushewar zuciya suka saukar mata. Batare da yin wani dogon nazari ba wautar ƙuruciya ta fisgeta da zuciya wajen ɗaukar pen ta hau cike takardun da ɓarin jiki, batare data duba mi suka ƙunsa ba..

       Fusatar tata ta basu matuƙar mamaki da al'ajabi. Sai dai zukatansu na ayyana musu tanayin komai ne domin ahalinta. Dan fahimtar sune rauninta ya sakasu yin amfani da su wajen tursasata. Aiko sunci nasara, dan ta cike takardun kamar yanda suka buƙata. Ta kuma saka hannu bisa takardar contract ɗin zatai musu aikin sirri har sai sun kama Master. Su kuma bazasu saki wancan bayanan ƙaryar da suka shirya ba domin mata ɗaurin talala saboda ƙarancin shekarunta.

         Sun mata bayanai sosai da zata iya fahimta. Tare da bata date ɗin da zata fara amsar horo na musamman a ɓoye. Da ga ƙarshe sukai mata dogon gargaɗi akan riƙe dukkan abinda suka tattauna matsayin sirri. Dan inhar ta fitar tamkar ta bayyana ƴan uwanta ma duniya ne matsayin ƴan ta'adda. Daga haka suka sallameta.


        Fitowar Hibbah da aka haɗa da jami'ai biyu zasu mata rakkiya zuwa gida yayi dai-dai da isowar Yaya Abubakar da Yaya Muhammad station ɗin. Tana ƙyalla ido a kansu ta kwasa da gudu garesu. Jikin Yaya Abubakar dake gaba ta faɗa tare da fashewa da kuka.

        Shima rungumeta yay yana mai rintse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Yaya Muhammad ya ƙaraso garesu da sassarfa shima. Dafa kanta da yayine ya sata barin jikin Yaya Abubakar ta rungumeshi shima. Cikin son danne nasa ɓacin ran ya saki murmushi yana ɗagota da shafa kanta. Hannu yasa ya shiga share mata hawaye. “Kukan ya isa haka nan, ba gamu tare da ke ba”. Ya ƙare maganar da sake sakar mata murmushi mai kwantar da hankali.

       Yaya Abubakar da shima ke ƙoƙarin ganin ya shanye tasa da muwar ya ce, “Bara naje zanyi magana da su”.

     Da sauri Hibbah ta riƙo hannunsa tana girgiza kanta. Cikin sanyin da basu santa da shi ba ta ce, “Yaya karka je. Ka barsu kawai babu abinda sukai min”.

            “Karki damu, ba wani abu bane yanzu zan fito”. Yay maganar da zare hannunsa cikin nata yana shafa kanta. Kama hannunta Yaya Muhammad yay shima ya buɗe mota ya sakata, tare da ɗaukar goran ruwa ya miƙa mata. “Sha ruwa ki wanke fuskarki ina zuwa”.

    Hibbah na ƙoƙarin dakatar da shi bai jira cewarta ba ya nufi cikin station ɗin shima. Jitai kamar ta fasa ihu, dan gani take kamar shigar tasu na nufi jami'an zasu riƙesu su sanarma duniyar ƴan ta'adda ɗinne su.

         Ganin an shafe kusan mintuna a shirin tai yunƙurin bin bayansu, sai dai tana buɗe motar suna fitowa kowannensu ransa a ɓace. Ta sauke ajiyar zuciya da yin sagade tai tana kallonsu har suka ƙaraso. Yaya Muhammad ya sake kama hannunta ya sata a motar sannan ya zagaya ya shiga shima. Yayinda Yaya Abubakar ya zauna mazaunin driver.

         

      Suna fara tafiya kiran Ammar ya shigo wayar Yaya Muhammad. Kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga ɗin. Da ga can Ammar ya fara magana cikin ɗacin murya. “Yaya kazo gida dan ALLAH akwai matsala. Hajiya mama da Abba na nan sun taru akan Ummi harda Junaid. Nayi magana kuma ta dakatar dani. Wlhy zanma Haƙilu (Abba) dukan mutuwa sai dai Ummi ta tsinemin. Har wannan shegiyar tsohuwar ba raga mata zanba dan mahaifina ta haifa ba ni ba.”

        “Ammar!!”

Yaya Muhammad ya kirayi sunansa a tsawace jin zai yanke kiran shima jikinsa na matuƙar rawar ɓacin rai.

        Tuni Ammar ya riga ya katse kiran baima jisa ba. Yaya Abubakar da duk yaji komai ya ƙara ƙarfin gudun motar, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu a ƙofar gidan. Tun a waje yay fakin, gaba ɗayansu suka fita da sauri zuwa ciki. Dan tun da ga waje suna jiyo kururuwa da ihun Hajiya Mama da Momy.

         A harmutse suka iske gidan. Ammar da Junaid na kwasar uban dambe. Sai dai duk da kasancewar Junaid yaya ga Ammar hakan bai hana Ammar hayewa saman ruwan cikinsa yana duka ba tamkar ALLAH ya aikosa. Mahaifiyar Ammar ɗin da suke kira Momy taje ceton ɗanta Ammar ya bata mahangurɓa a muƙamuƙi. Tuni ta koma gefe jikinta na matuƙar rawa.

         Abba da hajiya mama kuwa tuni suna a wani lungu maƙale dan su ne Ammar ya fara fafara Junaid ɗin ya maresa. Shine faɗan ya juye a tsakaninsu. Da ga cikin lungun Hajiya Mama keta fama kwaɗa ihu da kururuwar Ammar zai kashe mata jika. Yayinda Abba ke a rikice ga tsoro, yana son zuwa ɗakko waya ya kira ƴan sanda yana tsoron fita Ammar da ya juye musu kamar wani mayunwacin zaki ya gansa ya dawo kansa.

      Ummi ce kawai akan Ammar tana ƙoƙarin janyesa tana kuka amma ta kasa, dan gaba ɗaya ya juye mata tamkar ba Ammar ɗinta ba. Ya koma ainahin sunansa na ALIYU ZAKI.

         

      Kuka Hibba ta fashe da shi ganin yanda Yaya Ammar kema Junaid dukan mutuwa. Sai jini ke fita ta hancinsa da baki amma yaƙi sakinsa. Da ƙyar Yaya Muhammad da Yaya Abubakar suka iya haɗuwa wajen ɗagasa da ga kan Junaid ɗin. A hakanma sai famar turjewa yake yana nuna Junaid cikin gargaɗi.

           “Duk iskanci da kukejin kun iya da rashin mutunci muma mun iyasa. Ba tsoronku bane yasa muke barinku kuna taka mana mahaifiya yanda kuka gadama. Son yin biyayya a gareta da ga taka mana birkin da take na barinku kawai ke dakatar damu. Amma idan har kun isa wani ya sake nuna nata ɗan yatsa a gidan nan ya gani in ban karya shi ba na tauna ƙashin. Wlhy hatta waccan annamimiyar tsohuwar bazan bari ba, sai na ida ƙille ƙafafun nata ta koma gurguwa ta gaske.......”

         Kuka sosai Ummi keyi tana kiran sunan Ammar amma yaƙi yin shiru. Su Yaya Muhammad suka turashi sashen nasu da ƙyar suma rayukansu duk a jagule.

       A dai-dai wannan lokacin ɗaya da ga cikin ƴammatan gidan ta dawo. Horn tayi mai ƙarfi kamar yanda suka saba. Da sauri mai-gadi dake maƙale yana kallon duk abinda ke faruwa da ga windown ɗakinsa shima ya fito  domin buɗe mata gate ɗin. Sai dai shima har cikin ransa yaji matuƙar daɗin dukan nan da Ammar yayma Junaid. Dan duk wani cin zarfi da akema mahaifiyar su Ammar ɗin a gidan akan idonsu ne tun da ƙuruciya.

       A guje Ameera ta danno motarta cikin gidan kamar yanda ta saba. Sai dai hango su Abba akan Junaid da ke kwance kamar ya mutu ya sata saurin taka birki tamkar ba'a cikin gida ta ke ba. Fitowa tai da sauri. Ta zaro idanu sosai cikin ƙaraji na rashin tarbiyya take tambayar miya samu Junaid ɗin?.

           Abba yay saurin ɗago Junaid ɗin da numfashinsa ke fita da ƙyar yana faɗin, “Kinga maza buɗe mana motarki mu kaisa asibiti shine mafi muhimmanci yanzu. Sauran bayani ƙyaji da ga baya dan anzo gabar da yaƙin duniya na uku zai fara tashi a gidan nan.”

       Zata ƙara magana Hajiya mama ta katseta a tsawace. Baki ta murguɗa mata da yin fari da idanu sannan ta nufi motar tata Abba da mai-gadi biye da ita ɗauke da Junaid da gaba ɗaya jini yayma fuskarsa faca-faca...........✍


    *TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

           

    


   

   *_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________

      

       *_Ina miƙa sakon ta'aziyya ga ɗaukacin musulmi musamman hausawa na rashin uba kuma jigo, Haziƙi, gwarzo, abin alfaharinmu Sheikh Dr Ahmad bamba. Ya rabbi ka gafarta masa. Ka yafe masa kurakuransa da iyayenmu baki ɗaya. Munyi rashi irin wanda cike gurbinsa abune mai matuƙar wahala a duniyar musulinci. ALLAH ka yafema wannan jarumin dattijan ƙwarai😭🙏🏻_*


__________________________


*_MG's SKINCARE_*


*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*💃🏻


*_To maza kuzo ga mg's skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*


*_mg's skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar 💯_*💃🏻💃🏻


*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne a gareku💃🏻_*


*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi💃🏻_*


*_Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za'a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*


_Duk zaku tabbatar da hakanne ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari💃🏻😍🥰_.


Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call

08064532391

Instagram: glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare

Location:kaduna buh we deliver Nationwide

Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift


_*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_


________________________


*_Chapter Ten_*


...........Ummi na shigowa falon ta wankama Ammar mari. Lokaci guda falon ya ɗauki tsitt. Hibbah ta zazzaro manyan idanunta waje, jikinta na rawa, dan abinda bai taɓa faruwa ba a tsawon sanin da taima Umminsu. Duk iya ɓacin ran da zata nuna idan sukai mata laifi iyakarta da su faɗa da nasiha tun basu kai haka ba.

        Ba Hibbah kawai ba, hatta Yaya Muhammad da Yaya Abubakar sai da wutar kansu ta ɗauke. Hakama Yaya Umar da Yaya Usman da ke ƙoƙarin shigowa falon saboda kiransu da mai-gadi yayi ya sanar musu abinda ke faruwa tun sanda Ammar ke jibgar Junaid. Sai dai suna shigowa gidan motar Ameera na fita zuwa asibiti kai Junaid. Tare kuma suka tafi gaba ɗaya gidan, har da Hajiya mama dake fama da ƙafarta.

            Ƙananun duka Ummi ta cigaba da kaima Ammar, hawaye masu zafi suna gangaro mata a kumatu. Ammar dake tsaye ƙiƙam tun marinsa da tai kallonta kawai yakeyi shima hawayen na sakko masa na tausayinta. Yayinda wani murmushi mai ɗaci ke bayyana saman fuskarsa. Ummi ta jawosa ta rungume jikinta tana magana cikin rawar murya, “Miyasa zakai haka Aliyu? Miyasa? Ba nace duk abinda zaku gani ba kuyi kamar baku gani ba.”

     Da gudu Hibbah ta zo ta rungume Ummin da Yaya Ammar itama. Gefe Yaya Muhammad ya kauda kansa yana ƙoƙarin ɗauke hawayen da suka ciko idanunsa. Yaya Abubakar ma idanunsa sun kaɗa sunyi jajur. Yaya Umar yafi kowa zuciya a cikinsu, yayinda Yaya Usman duk ya fisu sanyi shi da Yaya Muhammad. A wani irin fusace ya juya zai fita a falon Yaya Usman da yasan halin kayansa yay azamar riƙo hannunsa.

       “Sake ni!”

Ya faɗa cikin kaushin muryar da ya maido hankalin kowa kansu. Girgiza masa kai Usman ya shiga yi alamar bazai barsa ba. Dan yasan dama badan Ummi da ke dakatar da su ba babu shakka da tuni Umar yayma Abba dukan mutuwa a gidan harma da Hajiya mamar kanta... Da ƙarfi Yaya Umar ya fisgi hannunsa da ga cikin na Usman. Hakan yasa Ummi azamar sakin Ammar tasha gabansa.

        Cikin idonsa ta kalla batare da tace masa komai ba. A take yay ƙasa da kansa yana lumshe idanu da cije leɓensa da ƙarfi tamkar zai huda shi. Murmushi tayi tana kamo hannunsa cikin nata. Gaba ɗaya ƴaƴanta tasan lagonsu da hanyar sauke fushinsu. Shiyyasa a kowane lokaci take samun nasarar ladabtar da kowa cikin salon da ya dace. Babu wanda ta sake yima magana a cikinsu, sai kamo hannun Hibbah dake sharar hawaye har yanzu tai tana bin jikinta da kallo tamkar mai neman wani abu.

      Da sauri Hibbah ta ce, “Ummi basuyimin komaiba fa, babu abinda ya faru ki kwantar da hankalinki”.

       “Ai sun sakaki a tarkon da za'ayi miki ne!”.

   Yaya Abubakar ya faɗa a tsawace cikin faɗan da kowa baisan yana da shi ba. Dan shima bai cika hayaniya ba sosai, amma yafi Usman da Muhammad zafi a wasu lokutan.

       Ya riƙe ƙugunsa da hanunsa ɗaya, ɗayan yana murza goshinsa cike da damuwa. Yanda ya ke ɗan kaikawo yasa su fahintar akwai matsala kenan. Ummi da dama yin komai ta ke cike da ƙarfin hali ta kafesa da ido.

        Zaune Yaya Abubakar ya kai saboda jin zai faɗi, dan shi kaɗai yasan a wane irin damuwa ya ke game da halin da Hibbah ta ke ciki. Gaba ɗaya ƙuruciya ta hanata fahimtar ramin da ta jefa kanta a ciki mai haɗari ne.........

       “Abubakar mike faruwa?”

Ummi ta katsesa tana takowa gabansa. Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana kallonta, ya ɗan furzar da zazzafar iska yana girgiza kansa. “Ummi tabbas akwai matsala, rawar kanta ta kaita ga jefamu cikin ramin da sam ita bazata fahimci haɗarinsa ba....”

         Duk da hibbah a tsorace take da yanayin Yaya Abubakar ɗin, tai saurin katsesa ta hanyar faɗin, “Yayanmu wlhy babu abinda ya faru fa. Kawai dai sun sakani na bibiyar musu masu power bike ɗin nan dana sanar maka ne. Amma da ga haka basuyi min koma.........”

       Tsawar da ta sakata kasa ƙarasa zancen ya daka mata. Ta maƙale a jikin bango jikinta na rawa saboda bata taɓa gamo da fushinsa irin haka ba. Shima tsaye ya miƙe yana nunata jikinsa har rawa yake ga idanunsa sunyi jajur. “Idan bakimin shiru ba wlhy sai na ɓallaki a gidan nan yau. Bance miki ki jirani a inda kike nazo na sameki ba? Su masu power rider ɗin da kike tunanin ba komai ba to sune tawagar ɓarawon nan da ake nema ruwa a jallo mai suna *Master!*, shine ya wawashi maƙudan kuɗaɗe jiya a asusun matar gwamna. Kowace hukuma ta jami'an tsaron jiharnan an basu awa ashirin da huɗu ne domin kawosa a mace ko a raye. Ba jihar nan da ƙasarnan kawai ba, hatta duniya baki ɗaya idonsu akan wannan mutumin yake. Amma shine k kika jefa kanki cikin abinda bakisan mafarinsa ba. Su waɗan nan jami'an da suka ɗaukeki zasuyi amfani da ke ne kawai su sami cikar burinsu, sunansu ya sake fiwowa a idon duniya. Kece zakiyi aikin amma sune zasu fito matsayin masu aikin. A tunaninki shi ɗin mahaukaci ne, kosu suna son matsalar tasa ta ƙare ne da wuri? Kuɗaɗen shigar da suke samu su dakata. Kafin yau an sha yimasa tarkuna da sukafi wannan haɗari amma bai kamu ba. Da ga ƙarshe kuma duk wanda yay masa tarkon ana nemansa ne a rasa ma baki ɗaya, ya ɓatar da shi. Wannan yasa a duk lokacin da ya aikata laifin manyan ke makalewa su saka ƙananun ma'aikata yin aikin, da ga ƙarshe suke nuna sunyi aikin ma duniya, wanda yay aikin kuma rayuwarsa ta faɗa a haɗarin da babu wanda zai sakejin yanda akayi, kuma basa wani ɗaukar matakin bashi kariya ko cetosa. Shekarunki goma sha takwas kacal da wasu wattani a duniya Muhibbat! Bama ki gama karatun gina rayuwar taki ba amma kika jefa kanki a wannan haɗarin saboda kunnen ƙashinki. Wannn kunnen babu wanda ya isa ya faɗa masa yaji sa”.

    Ya ƙare maganar da takawa inda take maƙure a bango jikinta na rawa ya damƙi kunnenta da ƙarfi yana murzawa cikin yatsun hannunsa. Rawa jikinta ya farayi tana girgiza masa kanta saboda zafi.

             Sakin kunnen nata yay yana dungure mata kai, yayinda sauran yayun nata da Ummi keta faman ambaton (innalillahi wa-inna ilaihirraji'un) a zukatansu. Yaya Abubakar ya cigaba da faɗin, “Ba wanann kaɗai bace damuwar Ummi, tunda har basu sami nasarar kamashi ba zargi zasu ɗarsa akanta itama. Dan zasu raba hankalinsu ne yanzu akan tunanin ko shine ya shirya komai wajen yin amfani da ita. Dan duk harin da jami'an tsaro ke kai masa ba'a taɓa cin nasara kamar nata ba da ya gudana cikin kanƙanin lokaci. Yanzu da zarar sun fitar da bayanai wa media cewar sun haresa, harin da kuma aka samu ci gaba a cikinsa fiye da na baya, to kowacce hukumar jami'an tsaro sai sun bibiyi yanda hakan ta kasance ta karƙashin ƙasa, walau jami'anmu nan gida kona ƙetare da ke nanuke cikin case ɗin kamar yanda suka saba mana kutse a cikin ayyukan daya shafi ƙasashenmu. Mu kuma bamu isa muyi koda tari akan nasu ba. A ƙarshe kowa ya bincika ita zai gano. Duk kuma zasu kasance wajen bibiyarta da mu kammu ba tsira zamuyi ba. Shima da ta aikata komai dominsa ba barinta zaiyi ba na sani.

       “Ya ALLAH!”.

Ummi da ke neman faɗuwa ta faɗa tana fashewa da kuka. Da sauri sukai kanta gaba ɗaya suna ƙwala mata kira. A wani irin sarƙe numfashinta ya fara fita, ta fara tari.

      Rikicewa suka sakeyi, yayinda kukan Hibbah ke ci musu zukata matuƙa. Cikin bada umarni Yaya Muhammad ya ce su dagata a kaita asibiti. Yanda ya faɗa ɗin haka sukai, sai dai suna fitowa harabar gidan ƴan sanda na shigowa. Basuyi yunkurin bi takansu ba. Sai dai muryar Abba da sukaji yana nuna Ammar da cewar shine ya kashe masa yaro ya saka hankalinsu rabuwa biyu.

     A ɗan firgice Yaya Usman ya furta, “Kisa?”.

         “Eh mara mutunci, ko ƙarya zan masa ne? Tun ɗazun likitoci suke akan Junaid amma babu alamar numfashi tare da shi, dan haka ku kamasa, inhar na rasa ɗana shima sai an kashesa.”

          Tarin Ummi ne ya ƙara ƙarfi, sai ga jini na fitowa ta hancinta. Hankalinsu ne ya sake tashi. Sai a lokacinne Abba ya lura da halin da Ummi take a ciki. Maimakon ya saki batun ƴan sanda ya shiga sahun masu kula da ita, sai hakan ta gagara. A kausashe ya bama ƴan sandan damar kama Ammar yana tabbatar musu pretending Ummi keyi kawai.

        Ganin duk sun shiga mota ƴan sanda kuma sun cukuykuye Ammar dake turjewa dan hankalinsa nakan halin da mahaifiyarsu ke ciki bata tasu yake ba. Yaya Muhammad ya cema Yaya Usman ya fita yabi ƴan sandan dan susan inda za'a kai Ammar ɗin. Su kuma zasu kai Ummin asibitin.

         Badan yaso ba ya fita domin bin umarninsa. Dan duk da an haifesu babu wani yawan tazara a tsakaninsu hakan baya hanasu respecting junansu saboda ƙyaƙyƙyawan training da suka samu da ga mahaifiyarsu.......


★★★★★★★★★★★


               A lokacin da wancan tashin hankali ke baibaye da ahalin Hibbah, anan headquarters ɗin ƴan sanda ƙoƙarin fitar da bayanan harin da Hibbah ta kaima master sukeyi. Sai dai kamar yanda Yaya Abubakar yay hasashe sunansu ne ya fito matsayin waɗanda sukai aikin. Sun kuma tabbatar nan da lokaci ƙanƙani zasu gurfanar da Master a saman gwiwoyinsa gaban duniya.


        Babban abinda ya ɗauki hankalin jama'a da media baki ɗaya shine. Rahoton ƴan sanda na fita da mintuna uku kacal. Sai ga wani babban labari kuma da ga wannan shahararren ɓarawo mai suna *(MASTER)*. Ya fitar da jerin sunayen wasu manyan kaddarori na matar gwamna da mutane basu taɓa kawoma ransu hasashen tana da alaƙa da su ba a wani shafi nasa. Sannan ya rabasu a manyan gidajen redio da television ta hanyar tura musu saƙwanni kai tsaye a shafukansu na sada zumunta masu matuƙar muhimmanci da yawan mabiya.

            Sosai ƙura ta tashi cikin lokaci ƙanƙani, manyan ƴan siyasa abokan takarar wannan jami'iyya suka samu damar baje kolin nasu faɗar albarkacin bakin dan dama tamkar kaɗan ake jira. Yayinda a gefe kuma da yawansu suke goyon bayan shi wanann master da ƙoƙarin wanke laifukansa a idanun mutane.

          Fitar wannan kace nace keda wuya takardar gayyata ta bayyana da ga hukumar *(Yaƙi da ta'annatin kayan gwamnati)* zuwa ga matar gwamna. Acewarsu, suna gayyatarta zuwa ofishinsu da ga nan zuwa awanni ashirin da huɗu domin amsa musu wasu tambayoyi. Idan bataje da kanta ba, zasuje har gida su su ɗakkota.


         Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga ɓangaren gidan gwamnati suma sun yunƙuro wajen maida murtani ta hanyar jifar abokan hamayyar TAKUN SAƘAAr nasu da dangantaka da Master. Suna mai tabbatar ma duniya lallai akwai lauje cikin naɗi. Sannan akwai ayar tambaya dangane da wanzuwar Master. Shin kodai? Kodai......😂🤐.


        Ta kowanne fanni gari ya ɗauka zafi, babu wani babban labari sai na wannan badaƙala ta TAKUN SAƘAA tsakanin Master da ya haɗa gurmin zuwa jami'an tsaro da na gwamnati. tare da ƴan siyasa da masu radin faɗin albarkacin baki. A gefe kuma ga talakawa ƴan bani na iya nata faman sharhi akan komai, kai kace agabansu aka ƙulla al'amarin..........


(😖Wai, sunan wata karya. Sharaton. Bily aɗan dinga sassautawa dai🚶🏻😌😒😏😣😝)


*________________________________*


              Wani ƙayataccen murmushin da ya saka yaransa shagala a kallonsa ya saki lokacin da yake faman duba wasu da ga cikin Comments na mutane da ke wanzuwa a yanar gizo. Cikin salon ƙasaitarsa da izza ya wani juya kujerar da yake zaune cike da ƙwarewa yana lafewa a cikinta hankali kwance. Tare da wani salon da su kaɗai suke gane mi yake nufi idan yayi sa.

        Dariya suka sanya cike da jin daɗin. Dan kobai faɗaba sunsan yana cikin farin ciki matuƙa. A duk sanda ya tada irin wannan ƙurar ya ga taja hankalin ƴan ƙasa da waɗanda yayi dominsu su kansu yakan yafe musu laifuka da sukai masa. Ko ya bisu da ƙyauta mai tsoka da ke sakasu farin ciki. Zai kuma kasance tare da su cike da nishaɗi duk da shiɗin ba mutum bane mai yawan magana akoda yaushe.

         Da wannan damar Habib yay amfani wajen gabatar masa da rahoton binciken da ya gudanar akan aikin da ya basu ɗazun. Dan sun wuce adadin awannin da ya basu sosai. Kuma sunsan bawai ya manta bane, ya sharesu ne kawai bisa wani dalili nasa daban. Zatama iya yuwuwa shi tuni ya gama aikin binciken, suma ɗin ya sakasu yi ne kawai domin hukuntasu bisa laifin sakacinsu.

            Komai baice akan takardun ba. Hasalima baiko buɗesu ba ya cigaba da duba sakwannin. Yayinda murmushi ke cike da ɓoyayyar fuskarsa da har ake ganin bayyanarsa bisa ta bogin da ke a kanta, wadda idan ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa cewa ba fuskarsa bace ba. Su kansu yaransa inda ace da ita kawai yake amfani baya canjawa tabbas zasu ce itace ainahin fuskarsa. Sai dai zuwa da mabanbanta da yakeyi ya sakasu fidda wanann hasashen a cikin ransu.

           Ya kai tsahon lokaci tare da su yana bibiyar kowacce kafar yanar gizo da ta yaɗa labarai. Kafin ya miƙe yana faɗin, *“7:30am* zamu koma *L.E street.* Jahje na buƙatar bada ƙafa”.

        Wani ihun farin ciki suka saka. Dan a gaba ɗaya gidajen da suke zama gidan *_L.E STREET_* yafi kowanne girma da ababen more rayuwa. Suna matukar mamakin yanda yake sama musu manyan gidajen da suke zama, a kuma manyan anguwanni batare da an farga shiɗin baneba. Tsabar hatsabibancinsa kuma a wasu lokutan sukan koma anguwannin talakawa su zauna har na tsahon wani lokaci. Haka suke tamkar fulanin tashi. Da wahala suyi zaman wata uku a gida batare da sun koma wani ba.

        Kansa ya ɗan girgiza da kai kofin coffee ɗinsa saman baki yana barin wajen nasu zuwa jikin windown ƙaramin falon da suke ciki na gidan da ya kawosu ɗazun. Wanda har yanzu basu san taka-maimai a cikin wace anguwa yake ba, dan basu fita ko soro ba har yanzu. Shi kadai ne ya fita bayan awanni takwas ya kuma dawo.

       Wani hatsabibin murmushi ya sake saki idonsa kyam akan ƙwan wutar lantarki da ke a tsakar gidan. Haka ya cigaba da tsaiwa a jikin window ɗin yana cigaba da shan coffee ɗinsa da sauraren iya shegen yaransa akan Comments ɗin mutane da suka koma bibiya suma suna kwasar dariya.

          Kofin da ya sake kaiwa baki yaji babu komai a ciki ya sakashi ɗago kofin ya kalla. Ba komai ciki ya shanye, hakan sai ya bashi dariya. Amma sai ya gintse kayansa baiyiba sai a zuciya. Juyowa yay da baya ya ajiye cup ɗin ya ɗauka file ɗin da Habib ya ajiye. Cikin muryarsa da sautinta ke fita da nutsuwa da amo yace, “Ayi addu'a kafin a kwanta. Goodnight”.

          Kusan a tare suka haɗa baki wajen faɗin, “ALLAH ya tashemu lafiya boss. Sweet dream tare da ƙarin ƙyaƙyƙyawar idea akan ƴan ruda”.

       Daƙƙuwa yay musu batare da ya juyoba. Sai dai ya saki murmushi dai-dai yana shigewa. Duk da basuga murmushin nasa ba kasancewar ya juya musu baya hakan bai hanasu yin kananun dariyar farin ciki ba gaba dayansu.

        Yana shigewa suka farma gasassun kajin da ya kawo musu tun shigowarsa da ci. Dama sun ɗan ɗaga kafa ne ganin yazo a cikin yanayin babu wasa. Yanzu ko sunsan komai normal ne, sai abinda ba'a rasaba saboda rikita-rikitar Master ɗinsu bata taɓa karewa. Daya toshe waccan matsalar zai ɓallo wata da kansa kafinma ƙurar wadda ya tayar ta lafa.


      Shima ko da ya shiga ɗakin zazzafan numfashi ya furzar. Ko'ina fes dan tun bayan barinsu da yayi suka gyara komai. Ya jefa file ɗin hannunsa saman madai-daicin gadon. Kayansa ya shiga zamewa alamar son watsa ruwa. Ya rage da ga shi sai singlet da boxer. A haka ya nufi toilet ɗin.

         Tsahon mintuna ashirin ya ɗauka a ciki kafin ya kammala, tun kafin ya fito da ga bayin ya ziro hannu ya kashe wutar ɗakin baki ɗaya. Batare da damuwa da duhun da ya mamaye ko ina ba ya fito a haka. Ta cikin duhun ya iso bakin gadon, ya kai zaune cikin lalube ya ɗakko wayarsa ƙarama. Fitilarta ya kunna, tare da ɗaukar file ɗin da Habib ya bashi. Sam ba'a ganin fuskarsa. Sai dai shi yana ganin rubutun file ɗin kasancewar shi ya haska kai tsaye. Sai alamun bathrobe ɗin dake a jikinsa wadda iya inda hasken ya haska kawai ake gani.

          “What?!”.

Ya faɗa cikin subucewar baki ganin bayanan na nuna cewar da taimakon mace aka kai musu harin ɗazun. Macen ma ƴar 18 years kacal. Cikin wani irin rawar jiki yay wurgi da file ɗin yana faɗin, “Impossible! Ni! Ni! Ni ne yarinya ƙarama kamar wannan zata hara. Hari irin wanda wani mahaluki bai taɓa samun galabar yimin shi ba. Kuturun ubacan kayyasa😳............✍


       *_HHHH anayi muna ɓallar rake na funtuwa mai zaƙi. Alaji Master yaya take ne😉😝🐒?. In baka saniba ma yanzu ne wasan zai fara😂👎🏻_*


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*





*_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_Chapter Eleven_*


..........Cikin gaggawa aka amshi Ummi a asibiti. Dan da ƙyar take fitar da numfashi, ga jinin da yake fita mata ta hanci da tayo tari da ya harmutsa dukkan zukatan su Yaya Muhammad. Hibbah kam ai tama koma musu tamkar zararriya. Dan koda za'a shige da Ummi sai da Yaya Umar ya riƙota shima hawaye masu ɗaci na cika masa idanu.

      Yaya Muhammad kam da baida wahalar zubda hawaye gefe kawai ya maida kansa yana sharewa. Umminsu itace duniyarsu. Itace farin cikinsu. Itace ta maye musu dukkan gurbi na dangin mahaifinsu da giɓin mahaifin nasu da suka rasa tsahon shekaru goma sha tara. Tayi haƙuri da damuwoyi kala-kala domin taga sunyi farin ciki. A kullum ƙoƙarin ta su zama mutanen kirki. Su zama masu haƙuri, su zama masu juriya. Su zama....  Su zama... Da yawa. To sukam idan akace sun rasata ina zasu saka kansu da rayuwarsu. Idan suna a gabanta sam basa tuna sun girma. Ganin kansu suke tamkar ƴan shekaru goma-goma. Bazasu so Ummi ta tafi ta barsu batare da sun cika mata burinta na ganin sunyi aure ba. Kamar yanda take addu'ar ganin zuri'arsu suma hakan shine fatansu a yanzun. Suna son yawan ganin dariya a saman fuskarta kamar yanda mahaifinsu yay sanda yana raye. Amma hakan duk bazata tabbataba sai tana a kusa da su........

       “Ya ALLAH ka bama Ummi lafiya ka tashi kafaɗunta. ALLAH yasa ni na mutu a madadinta”.

      Furucin Muhibbat da ke kuka ya katsema Yaya Muhammad da su Yaya Abubakar tunaninsu. Gaba ɗayansu suka zuba mata idanu na ɗunbin tausayinta da ƙaunarta. Yarinya ce ita mai yawan walwala, kazarkazar, wauta, tsiwa, rawan kai, surutu duk a dalilin gata da kulawar da take samu da ga garesu. Tana matuƙar son Ummi, suma haka. Batasan mahaifinsu ba, shiyyasa suketa ƙoƙarin ganin sun cike mata gurbinsa.

        A hankali Yaya Abubakar ya taka inda take durƙushe gaban Yaya Umar da rauni ya cika zuciyarsa na tausayin kansu da autar ta su. Hannu biyu yasa ya kamota ya ɗaga tsaye. “Haba Muhibbat, maimakon kima Ummi addu'ar samun lafiya sai ki dinga ma kanki addu'ar mutuwa a madadinta?. Insha ALLAH Umminmu zata tashi da lafiyarta kinji. Ki mata addu'a da fatan alkairi, ALLAH ya na tare da ita kinji”.

        Kanta ta jinjina masa wasu zafafan hawayen na rige-rigen sakko mata. Yasa hannu ya share mata yana murmushin ƙarfin hali.

         “Ƙyaƙyƙyawa mai kama da Umminta a komai, sai dai raguwa ce bata kai Ummi jarumta ba”.

    Yaya Abubakar ya faɗa cikin ƙarfin hali yana ɗan ja mata kumatu. Maimakon tai dariya da tsalle kamar yanda ta saba idan ya faɗa mata hakan, sai ta faɗa jikinsa ta fashe da kuka. Kusan atare duk suka rumtse idanunsu, dan kukanta na matuƙar sake tada musu hankali.


        Kusan mintoci arba'in da biyu likitoci suka ɗauka tare da Ummi. Kafin ALLAH ya basu ikon fitowa. A kusan tare su Yaya Umar suka miƙe a zabure harda Hibbah dake jingine jikin Yaya Umar barcin wahala ya ɗauketa.

         Kusan a tare suka furta “Doctor ya jikin Ummin mu?”.

    Kallonsu yayi cikin furzar da numfashi yana cire norsemask ɗin fuskarsa. “Inason yin magana da ku a office”. Ya faɗa yana ƙoƙarin wucesu. A take suka rufa masa baya har Muhhibat da Yaya Umar ke riƙe da hannunta. Kusan tare suka shiga da doctor cikin office ɗin. Hakan da sukai sai tausayinsu ya sake kamashi. Dan a kallo ɗaya zakai musu ka hango ɗunbin so da ƙaunar da sukema mahaifiyar tasu. Bai wani tsaya ja musu rai ba yay musu bayani akan matsalar da ke tare da Ummi a ƙasan zuciya da hanjinta. Bincikensu ya nuna kuma ta jima da ciwon yana ta cinta a hankali, sai dai yafi nuna kansane a duk lokacin da wani ɓacin rai ko tashin hankali ya sameta. Amma zasu mata aiki insha ALLAH suna mata fatan samun lafiya.

           Duk da maganarsa ta ƙarshe taɗan sakasu jin sanyi hakan bai hana zukatansu shiga cikin matuƙar rauni ba. Ya ɗan ƙara faɗaɗa musu bayanai akan abinda za'a iya buƙata akan aikin da magungunanta. Tare da basu tabbacin inhar sun shirya a yau ɗin nan ma za'a iya mata aikin. A take sukace sun amince, duk da kuwa kuɗaɗen da ya ambata da wuya a iya samunsu kai tsaye da ga garesu. Badan suna da yawa bane sosai, kawai dai suɗin masu tasowa ne ba wasu ɗumbin kuɗaɗe suka tara ba. Amma dai tunda ya ce zasu iya bada rabi idan an kammala aikin su cika zasuyi ƙoƙarin su insha ALLAH.

         Take ya basu takarda Yaya Muhammad ya saka hannu. Daga haka suka fito domin tattaunawa akan zancen kuɗin. Dan doctor yace sai sun tura zaiyi ƙoƙarin haɗa wasu da ga kayan aikin insha ALLAH.

     Su dukansu suna aiki, Ammar ne kawai da Hibbah ƴan makaranta a cikinsu. Sai Yaya Umar da ke ɗan harkar kasuwanci saboda matsalar rashin samun aiki da matasa ke fama da shi a ƙasar nan. Sai ma yazam a yanzu yafi nutsuwa da kasuwancin sama da aikin da yay karatu akansa. Dama kuma su Yaya Muhammad ɗin nata son ganin sun ƙara masa ƙarfin jari tunda ALLAH yayma kasuwar tasa nasibi.

       Sun ɗan tattauna wajen ganin sun haɗa kuɗaɗen, cikin amincin ALLAH ma sai gashi an samu kusan rabin a hannunsu su uku. Idan Yaya Usman yazo shima zasuji mi za'a samu daga garesa. Abba dai basa saka rai game da shi sam.

       Basuyi zaman ɓata lokaci ba wajen fita su tattaro kuɗaɗaɗen har Yaya Usman da ya iso asibitin a yanzu shima, dan ya kasa jure zama acan saboda ya gwada ƙoƙarinsa na ganin an bashi Ammar amma hakan ya gagara saboda mugun ƙulli da Abba yaje yayi a station ɗin. Ya tahone kawai dan yasan insha ALLAH Yaya Abubakar zai fiddosa da zaran hankali ya kwanta. Kafin su dawo kuwa an gama shirya komai na shiga theater ɗin. Cikin amincin ALLAH zuwa ƙarfe takwas na dare aka shiga da Ummi. Sun bita da ƙyaƙyƙyawar addu'a da fatan dacewa a zahiri da baɗini.


      Yaya Muhammad ne ya fara fahimtar akwai yunwa tattare da Hibbah. Dan gaba ɗaya jikinta ya saki tamkar mara laka. Yana lura da ita ko salla a zaune ta dinga yinta. Hannu yasa ya kamo nata cike da kulawa yana faɗin, “Auta yaushe rabonki da abinci”.

        “Tun breakfast ɗin safe Yayanmu, amma kuma banajin yunwa”. Ta faɗa cikin sanyin da basu santa da shi ba.

     Su dukansu sai da suka dubeta cike da tausayi. Yaya Usman yay saurin barin wajen batare da yayi magana ba. Cikin lokaci ƙanƙani sai gashi ya dawo da teakaway.

        Zama yay da kansa zai bata amma sai tace ta ƙoshi. Dukansu babu wanda bai lallasheta ba amma tace ta ƙoshi. Sai da taga duk sun ɓata rai sanann ta amsa ta ci wanda ya saka mata a baki. Amsar cokali tayi ta ɗiba da kanta shima ta bashi. Ta sake ɗebowa ta bama Yaya Umar. Shima Yaya Abubakar haka. Sannan ta bama Yaya Muhammad shima. Dukansu murmushi suke mata a karon farko tun bayan shigowarsu asibitin da duk rayukansu suke a jagule. Amsa Yaya Usman ɗin yay ya cigaba da bata. Kusan lauma uku ta kauda kanta idanunta na cikowa da ƙwalla.

      “Miya faru kuma?”. Yaya Abubakar dake miƙa mata ruwa ya faɗa. Hawayen data matso suka silalo saman kumatunta. Muryarta na rawa tace, “Yayanmu Yaya Ammar fa?”.

         Shiru suka ɗanyi duk suna kallonta. Kafin Yaya Abubakar ya shafa kanta fuskarsa ɗauke da murmushin ƙarfin hali. “Karki damu shima zai dawo, insha ALLAH bazai kwana acan ba. Ƙarasa cin abincinki ina zuwa”. Ya ƙare maganar yana mikewa. Tashi Yaya Usman yay yabi bayansa.


     Police station ɗin da aka kai Ammar suka nufa. Tun shigowar su Yaya Abubakar wasu a cikin ƴan sanda suka shaidashi saboda aiki ya taɓa haɗashi da wasu a cikinsu. Amma duk da haka sai ya nuna musu i'd card ɗinsa. A zabure sauran ma suka shiga gaishesa. Aka kuma masa iso ofishin ogan wajan.

       Tun a shigowarsu ya shaida Yaya Abubakar ɗin. Amma sai ya maze abinsa. Yaya Abubakar ya cije lip ɗinsa dan akwai ƴar tsama a tsakani. Sai dai yana sama da shi. Cikin nuna bai damu da basarwar tasa ba yay masa bayanin kansa. Tare da buƙatar a bashi Ammar.

       Cikin yatsine fuska ɗan sandan yace, “To yallaɓai idan ku matsayinku na manya kuna haka su kuma wanda basu da dangi ƴan sanda kuma fa? Laifi ƙaninka yay aka kawosa nan, sai kuyi haƙuri mu gama tattara bayanai akansa mukai maganar kotu kamar zaifi”.

      Sosai Yaya Abubakar ya kafesa da ido. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana miƙewa dan yasan wannan tsarin da ga Abba yake. “Wanann basirar ba taka bace. Amma ga saƙo ka bama wanda ya tsara maka ya kuma biyaka. Ya kiyayi ranar maida murtani dan zata kasance mai ɗaci da tsauri. Ya kuma bar raina allura dan itama ƙarfe ce. Duk randa zuri'ar Aliyu Hamza gwarzo sukaji a ransu zasu maida murtani TAKUN SAAƘAR bazai masa ƙyau ba. Wannan hanunka mai sanda ne”. Yaya Abubakar ya ƙare maganar cike da gargaɗi.

     Murmushi Yaya Usman yayi. Dan bai taɓa zato da tunanin yaya Abubakar ɗin nasu ya iya zaro zance haka na. Koda suka fito da kansa yasa a kaisa cell ɗin da Ammar yake. Shine ya amshi key tun daga kanta ya buɗesa da kansa.

       Wani irin kallo ya tsaya yanama Ammar da yaci uban duka. Da alama ma ba'a jima da dukan nasa ba, dan duk sabbin raunuka ne a jikinsa dake fidda jini. Komai baiceba a lokacin sai kama hannun Ammar ɗin daya taso da sauri yana tambayarsa “Ina Ummi take?” yayi. Bai amsa masa tambayarsa ba sai da suka iso kantar. Ya duba ƴan sandan wajen da sukai tsuru-tsuru cikin kaushin murya yace, “Su waye sukai wannan aikin?”.

    Kallon kallo aka shigayi. A matuƙar tsawace yace, “Ba magana nake ba ne?!!”.

           Zabura duk sukayi har tsirarun mutane da sukazo belin ƴan uwansu da masu kawo abinci. Cikin rawar murya wani ɗan sanda yace, “Yallabai wlhy ba laifinmu bane sakamu akayi”. Ya ƙare maganar a hankali cike da raɗa saboda fitowar ogansu da ga office dan jin tsawar da Yaya Abubakar yayi.

       Takarda Yaya Abubakar ya fisga ya jefama ɗan sandan da yay maganar. “Ina son duka sunayen members na ƴan sandan dake a station ɗin nan. Wanda sukai wannan dukan kuma sunayensu su kasance a ware”.

     Wani busashshen yawu ya haɗiye da ƙyar yana ɗaukar takardar. Jikinsa sai tsuma yake ya shiga zano sunayensu ɗaya bayan ɗaya. Bayan ya kammala cikin girmamawa ya mikama Yaya Abubakar ɗin. Uffan baice masaba ya amsa tare da jan hannun Ammar da Yaya Usman ya riƙe ta ɗayan gefen suka fice da ga station ɗin.

        Ko a mota ma babu wanda yay magana dan zuciyar Yaya Abubakar takai ƙololuwar ɓaci game da lamarin Abba. Asibitin suka wuce da Ammar shima. Ba ƙaramin tashi hankalin su Yaya Muhammad yay ba ganin dukan da akaima Ammar. Hibbah kuwa kuka ta fashe musu da shi tare da zuwa ta rungume Ammar ɗin.

       “Wash ALLAH auta zafi”.

Ya faɗa cike da shagwaɓa saboda jin ta ƙankame masa hannunsa da yake da tabbacin ƴan sandan sun ji masa ciwo. Saurin sakin hanun nasa tai tana sake fashewa da kuka. Ya kai hannu bisa kanta ya dafa yana murmushin ƙarfin hali. “K karki maidani kamar ba namijiba mana. Bakisan dukan ƙarfi ya ƙara min ba ma”.

         A yanda yay maganar ya saka su Yaya Umar yin murmushi suna girgiza kansu. Hibbah kuwa kukan ne ya sake kufce mata.

       Yaya Umar ne ya kaisa akai treatment ɗinsa da bashi magunguna. Sauran abincin da Hibbah taki ci suka matsa masa yaci da ƙyar shima. Dan sai da Hibbah ta dinga basa a baki yau babu faɗa. Bayan ya kammala yasha magungunan da aka bashi. Duk yanda sukaso yaje gida ya huta yaƙi, yace shima sai yaga fitowar Ummi.

          Sha'awa yanda suke ƙaunar junansu ya bama doctor Bilal. dan haka ya bama Ammar ɗin shawarar yazo office ɗinsa ya kwanta to har komai ya kammala sai a tashe sa. Nanma da ƙyar ya amince bisa umarnin yaya Muhammad. Haka dai ya miƙe yana tura baki Hibbah na masa gwalo.


_____________★★★_____________


   

          Duk yanda yaso yin shirin barci ya kwanta hakan ya gagara. Sai fama kai kawo yake a cikin ɗakin, abubuwa da yawa zuciyarsa ke raya masa game da matakin da ya kamata ya ɗauka a kanta. Inhar zata iya kai masa hari ta samesa a ƙanƙanin lokaci. To wane irin shiri kenan zatai a gaba dominsa? Lallai dole ne yasan ita ɗin wacece? Mi kuma ta taka ne haka?. Shin sakata akai? Kokuwa yin kanta ne?.

      Waɗanan jerin tambayoyi suketa faman masa kai kawo a zuciya da hanashi nutsuwa. Shiri ya canja saɓanin pyjamas da ya kamata ya saka sai yasa wasu kayan daban. 

        Yaransa na falon zaune har yanzu suna sha'aninsu sai ganinsa sukai ya fito. Mamakine ya kamasu dan duk zatonsu ya kwanta.

       “Boss da matsala ne?”.

Salisu ya faɗa cike da girmamawa.

     Kansa ya girgiza masa yana ƙoƙarin ɗaura agogonsa. Sai da yaje gab da fita a falon yace, “Zanje wani waje ne, wani yazo ya rufe gidan”.

         Saurin miƙewa Khalid yayi duk da tambayoyine fal bakunansu amma babu damar yi, dan ya nuna baya buƙatarsu. Su ko saboda trianing da suka samu da ga garesa da kowanne irin yare yay magana ko yay nuni suna fahimtar kayansu.

      Koda ya wuce Khalid ya dawo zaman tattaunawa sukai, amma sai basu gano komaiba, dan haka sukai jigum-jigum......


________________________________


     Alhmdllhi ƙarfe goma aka fiddo Ummi da ga ɗakin theatre cike da nasara. Bayyana muku irin farin cikin da su Yaya Muhammad suke ciki ɓata lokaci ne. Basu sami damar ganinta ba dan an miƙata ɗakin hutu ne. Sai dai bayanin da Dr Sageer yay musu na narar aikin ya saka zukatansu nutsuwa. Har suka amince da shawararsa ta tafiya gida dan ba'a bukatar kowa tare da Ummin sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.

          Basuyi wani zaman ɓata lokaci ba suka tattara suka wuce bayan an tado Ammar da zazzaɓi mai zafi yayma ligif saboda dukan da yaci. Sosai tausayinsa ya bayyana bisa fiskokinsu. Sai dai komai basuce ba bayan Hibbah da ke ta jera masa sannu kamar zatai kuka. Kaɗan-kaɗan ta ɗaura hannunta a goshinsa.

       Suna gab da zuwa gida ya bige hannunta data ɗora masa a karo na babu adadi. “K dalla kin isheni, ga hannunki da sanyi”.

     Baki Hibbah ta tura gaba. Cike da tsiwa ta murguɗa masa baki da faɗin, “Oh dama ka samu na damu da kai zaka min wani iyayi”.

        “To waya aikeki? Uwar iya mai cinikin iya”. Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa jikin kujera.

      Murmushi Yaya Usman da ke kusa da su yayi yana girgiza kansa kawai. Dan inda sabo sun saba gani. Anjima kaɗan kuma kaga sun koma hirar arziƙi. Kafin awa ɗaya ta rufa sunyi faɗa sau biyu.

        Cikin jin haushi Hibbah tace, “Idanma kaga na sake kulaka dan ALLAH ka tsine min Yaya Ammar”.

          Baki Ammar ya taɓe da faɗin “ALLAH na gode maka na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda”.

       “Yaya Usman ka ganshi ko?”. Ta faɗa kamar zatai kuka.

        “Ya isa manta da lamarinsa auta. Ko sannu karki sake masa har ya warke”.

         “Ai baran masa ba ko Yayanmu”. Tai maganar da dungurin wajen ciwon da ke a hannunsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana bige mata hannu dan yaji zafi. Ta ƙyalƙyale da dariyar mugunta. Ranƙwashi mai shegen zafi ya bata wanda ya saka bakinta rufewa ruf, sai kuma ta fashe da kuka.

        Yaya Abubakar da duk yake jinsu da ga gaba ko kallo basu ishesa ba. Sai ma waya da ya ɗauka yay kiran maigadi ya buɗe musu gate. Koda suka shiga cikin gidan tsitt yake alamar jama'ar cikinsa harsun ƙwanta. Kusa da inda Yaya Muhammad yay parking shima yayi gab da sashensu.

    Hibbah da ke kukan ranƙwashin da Ammar yay mata ta fara fita domin kaima Yaya Muhammad ƙara tunda Yaya Abubakar bai bada fuska ba.

      “K zoki wuce ciki ki kwanta”. Yaya Abubakar ya dakatar da ita dan bayasan wani dogon magana a yanzu. Yasan kuma indai Hibbah ce bataƙi su kwana ana shashanci ba. Baki ta tura gaba sim-sim ta nufi sashensu.

     Yaya Muhammad yay ɗan murmushi yana kallon Yaya Abubakar ɗin. “Siddiq yau fa gaba ɗaya ka zama masifaffe. Kasa duk auta ta firgita da kai”.

        “Tana da cika ciki ne wani lokacin”. Yaya Abubakar ya bashi amsa yana kashe motar. Yaya Ammar yace, “Dama hakan kowa ke mata da mun huta da shegen ƙiriniyarta tamkar ƴar mage”.

      Kusan duk sai da sukai ƙaramar dariya. Da ga haka suka shige makwancinsu kowa ya nufi ɗakin barcinsa.

        Hibbah ma da ta shiga tanata zunɓure-zunɓure shirin barcin tai tana kunkunin wai dan anga Ummi bata nan kowa ya tsaneta. Gobe a asibiti zata kwana bazata biyosu su cinye ta ba.

         Da ƙunkunin dai harta kammala shirin barcin ta kwanta bayan tayi addu'a. Sai kuma a lokacin tunanin duk abinda ya faru a wannan yini ya shiga dawo mata. ALLAH dai ya taimaketa barci barawo yaci galaba akanta batare data shirya hakan ba.


*_WASHE GARI_*.


           Yau Yaya Umar ne ya shigo yama Hibbah knocking. Sai da yaji ta tashi sanann ya juya ya fita bayan ya mata gargaɗin karta koma barci ta shiga kitchen idan sun dawo salla zaizo ya tayata haɗa breakfast. Da to kawai ta amsa masa dan harga ALLAH barcin bai isheta ba. Sai dai sanin halin masifarsa yasata bin umarninsa bayan ta idar da sallar tai azkar ta fita kitchen ɗin. Bata jima da fara aikin ba suka dawo. Su dukansu babu wanda bai iya girki ba dan Ummi babu abinda bata sakasu na aikin gida. Shiyyasa bata taɓa damuwa da zama da ƴar aiki ba tun da suka fara tasawa.

     Yaya Umar ne ya tayata sukai breakfast ɗin. Yaya Usman kuma yanata ƙoƙarin gyara gidan shi da Ammar da ya tayasa dan jikin nasa da sauƙi bakamar jiya ba. Magungunan da aka basa sun taimaka masa matuƙa. Cikin kankanin lokaci suka kammala komai tsaf kowa ya tafi dan watsa ruwa. Sabo da fita aiki yasa duk suka hallara akan lokaci bisa dining. Sai uwar latti ce ko motsinta babu sai da Yaya Muhammad ya je da kansa yay mata knocking.

           Koda ta fito masifa Yaya Umar da Usman suka hauta da shi na sakasu yin latti kamar kullum. Cikin son a kareta ta kalla Yaya Abubakar da Muhammad. Duk murmushi sukai mata da nuna mata kujera alamar ta zauna ta rabu da su Umar ɗin. Fuska a kumbure taja kujera ta zauna kuwa. Da ga haka suka fara karyawa.

      Sunyi nisa sosai acin abincin Abba ya shigo fagan-fagan Hajiya Mama biye da shi. A tare duk suka ɗago suka zuba musu ido. Sai wani irin tsoronsu da shakkarsu ya shigi su Abban lokaci guda. Yaya Muhammad ne ya fara ɗaule kansa ya maida ga abincin gabansa. Suma sauran duk sai suka yi kamar yanda yay ko gaishesu basuyi ba.

      Cikin masifa Hajiya mama tace, Kunci ubanku marasa mutunci. mu zaku kalla ku watsar tamkar wasu kashi?”.

     A mamakinsu ko motsi babu wanda yayi, sai ma cigaba da cin abincinsu sukeyi hankali kwance. Hajiya Mama da Abba sukai galala a tsaye kamar gunkuna suna kallon sabon salon iskanci. Suko sunyi tamkarma basusan da zamansu a wajenba.

     Wani irin baƙin cikine ya lulluɓe Abba ya shiga zazzaga tujara musamman akan fiddo Ammar, dan dama tun jiya ɗan sandan ya kirasa ya sanar masa. Ya kuma tabbatar masa da Abubakar yana tare da manyansu sosai, idan ya matsa akan Ammar ɗin tofa wata da tafi wadda suka shirya zata taso. Hakan yasa Abbana ɓam da bakinsa. Ya dai ɗauka alwashin zubarma da Ummi tujara tare da sauke duk fushinsa a kanta. Shiyyasa yana kammala sallar safensa da ya keyi a gida kullum bayan rana ta fito ya nufi sashen hajiya Mama ya sanar mata. Shine fa suka taho yima Ummi taron dangi basu san ma bata gidan ba. A zatonsu kuma su Yaya Abubakar ɗin sun fita.

           Duk iya tujarar da sukeyi babu wanda yay koda motsi balle nuna yasan da zamansu a wajen har suka kammala breakfast ɗinsu Ammar da Hibbah suka kwashe kayan zuwa kitchen. A gurguje suka wanke kwanikan ita da shi su ka fito dauke da basket ɗin abincin da suka shiryama Ummi irin wanda doctor da suka kira ya tabbatar musu zata iya ci tunda ta farfado tun daren jiyan.

     Har yanzu Abba da Hajiya Mama na a sashen suna zubda ruwan tujara. Yayinda kuma babu wanda yay musu koda tari. Hakanne ya sake harzuƙa musu zukata da wanann sabon salon rainin wayon su Yaya Muhammad ɗin. A gabansu kuma suka kulle kowanne ƙofar ɗaki da ke a sashen har kitchen sukai ficewarsu suka barsu a falo. Wannan al'amari yayi matuƙar bakanta ran Abba da Hajiya mama. Kai har ma Momy da ƴaƴanta mata huɗu da duk suka fito saboda hargowar su Abban.

         Motar Yaya Muhammad da Yaya Abubakar duk suka shiga yau ma suka fice batare da kowannensu ya hau mashin ba.


     Bayan fitarsu tujara ta gidan duniya babu irin wadda Abba da hajiya mama basuyiba a gidan. Ummi ta sha gori da tonon sililin asalinta. Sai da sukayi mai isarsu sukaga babu mai taya musu Sannan sukai shiru. Abba ya shirya fagan-fagan yabar gidan zuwa inda zuciyarsa ke raya masa domin yin maganinsu Yaya Muhammad ɗin baki ɗaya.............✍


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_Chapter Twelve_*


..............Oho su bama su san sunai ba. Dan koda suka fice a gidan babu wanda yay koda ambatar sunansu Abba ne balle su nuna sun damu da al'amarinsu. Asibiti suka nufa kansu tsaye. Inda sukai tozali da sanyin idaniyarsu da ke zaman jiran isowarsu.

        Cike da ɗunbin farin ciki duk suka baibayeta kowa na jera mata tambayoyi game da jikinta da yanda takeji kuma. Komai bata iya ce musuba. Sai murmushi da take musu hannun Hibbah da Ammar a cikin nata tana kallon ciwukan jikin Ammar din. Da sauri ya ce,

        “Karki damu Ummi naji sauƙi. Kema ALLAH ya baki lafiya ki cigaba da mana tuwon dawarnan naki da bama son ci”.

      A tare suka kyaƙyale da dariya, Murmushin Ummi ma ya sake faɗaɗa ta kai hannu ta shafa fuskarsa. Hannun Hibbah ta kamo ta maida saman tata fuskar. “Ummi nice auta ni zaki shafama fuska ba wannan garjejen mutumin ba”.

     Ranƙwashi Ammar ya bata akai. Ta dafe kan da sauri tana sakin karamar ƙara. Ammar ya mike da ga inda yake zaune yana mata gwalo.

       “Yaya Umar ka ganshi ko?”.

Harar Ammar Yaya Umar yayi. “Kai wai miyasa baka rabo da zalunci ne. Ko wannan rankwashin da kake mata ma ya hana girma ai taita zama kamar ƴar cilikowa tana addabar mutane da ɗaukar magana”.

       Dariya duk suka tuntsure da shi baki ɗaya. Ransu fes da farin cikin tashin Umminsu. gashi doctor ma ya sanar musu nan da kwana uku zasu sallameta taje gida ta cigaba da shan magunguna. Dan dama irin aikin nata mai sauƙi ne inhar an dace da yinsa bisa nasara.

         Su suka taimakawa Ummin ta tashi suka jingina mata filo. a tare suka haɗu su duka suka ringa bata abinci duk da Hibbah na isarsu da rigima da rinto. Dan a layi aka dinga bi har Ummi tai musu nuni data ƙoshi. Sai da tasha maganinta sannan sukai mata sallama domin tafiya wajen aiki aka bar mata Hibba da Ammar. Dan su sai ƙura ta lafa zasu koma school musamman ma Hibbah.

       Kafin su wuce sun biya office ɗin doctor daya bukaci ganinsu. Bayan sun sake gaisuwa da shi da nuna jin daɗinsu akan nasarar jikin na Ummi ya shiga musu bayani akan wani bawan ALLAH yazo ya biya kuɗin aikin Ummi ɗin duka. Dan haka zai dawo musu da nasu kuɗaɗen insha ALLAH.

      Cikin mamaki suke tambyarsa wanene hakan?. Ya sanar musu shima dai bai sani ba kai tsaye. Dan ansha irin wannan taimakon batare da sunsan ainahin wanene ba. Amma kuma bayan hakan ma wani ma ya sake bada kaso ɗaya bisa uku na kuɗin aikin harma ya shiga ya duba Ummi. shima kuma dama yakanyi hakan a wasu lokutan. Yasan kuma zasu gansa suma kafin a sallami Ummi ɗin dan ya fahimci a yau kawai kamar har sabo ya shiga tsakaninsa da Ummi ɗin.

      Sosai abubuwan suka basu mamaki, amma sai suka watsar da mamakin sukacema doctor a maida musu kuɗin su da kansu insha ALLAH zasu biya kuɗin aikin mahaifiyar tasu basa buƙatar kowa. Cikin nasiha ya nuna musu hakan ba daidai bane. Sam babu ƙyau maida alkairi baya musamman irin wannan. Suma bawai sun biya bane domin sunga sun gaza.

      Dole suka hakura suka amsa tare da yin addu'a ga masu biyan. Da ga haka suka fito domin nufar wajen aikinsu........


_________________________________


            A ɓangaren yaran master kam, tun suna zuba idon zaman jiran dawowarsa har suka fidda rai. Dan sun fahimci dai yayi nisan kiwo. Badan sun so ba dole suka tashi sukai shirin barci duk suka kwanta kowa ransa da addu'ar ALLAH ya dawo musu da shi lafiya.

      Sukan damu idan yay fitar dare. Saboda sunsan shi sam bayasan yawon dare. Ko su duk aikin da zai sakasu inhar magrib tayi ya haƙura kenan. Sai ko idan ya zama dolen dole. Amma da anyi sallar isha'i basa ƙara fita sai ta lalura.

      Koda suka tashi sallar asuba ma basuji motsinsa ba, haka sukai alwala suka fita, dan sunsan duk inda massallacin da ya tadasu yake zasu ganosa a layin insha ALLAH. Sai ga shi fitowar tasu ma ta sakasu fahimtar a ina suke. Ashe bayan layin gidan da suka baro jiya ne. Har cikin ransu suna jinjinama boss ɗinsu, saboda matuƙar wayonsa da basirar iya takun rayuwa. Komai babu wanda ya faɗa suka adana a zukatansu har sukaje salla suka dawo. Sanin yace ƙarfe bakwai da rabi zasu bar gidan yasa basu kwanta ba suka tattare abinda suka ɓata.

         Suna tsaka da kimtsawar ne kusan 6:43 sai gashi ya dawo. Kallon mamakin ta inda ya shigo suka shiga masa. Dan sudai basuji alamar buɗe ƙofar gidan ba. Hasalima sakata suka saka mata ta ciki, dole ne sai yayi musu knocking sunzo sun buɗe masa.

       Sarai ya fahimci ma'anar kallon da suke masa, amma sai ya basar abinsa. Hakan yasa suka shiga gaishesa da masa barka da dawowa bayan Musbahu ya tashi ya amshi bag ɗin hannunsa.

            Hannu kawai ya ɗaga musu, kafin ya fara magana a taƙaice yana nuna bag ɗin da ya shigo da ita, “Gaba ɗayanku zakuyi amfani da kayan cikinta ne, dan a wannan gaɓar magana ake ta kuɗin baƙine ango ya kawo ku kwana anan”.

         Cikin girmamawa suka shiga amsa masa suna murmushi. Yayinda shi kuma yay shigewarsa ciki. Zaidu ne ya fara kwashewa da dariya yana faɗin, “Abokan ango waye angon to a cikinku?”.

        Salis ya nuna kansa yana wani buɗe hannaye irin eh😉😂. Hararsa Habib yay da taɓe baki. “Banza. Kana ɗan yahoo ubanwa zai baka ƴarsa, wataran shima ka yashe masa asusunsa”.

      Sanin boss na gidan ya sakasu fara dariya suna tarewa da hannu. Salis da ke harar Habib ya ce, “Da yake ma talle bataima audi gori duk tafiyar ɗaya ce. Ta wani fanninma gwara ni. Kuma tunda kace haka kwanan nan zakaji na zama ango ɗan baƙin ciki yahoo boy”.

         Duka Habib ya kaima Salis ɗin ya kauce yana masa gwalo. Rabi'u yace, “Kai kai ku tsaya kuji. Ni fa da boss yay maganar ɗaurin auren nan sai naji inama irin shine za'a ɗaurama auren. ALLAH na ƙagu naga mai tsaurin idon da zatai wuff da master”.

        Dungure masa ƙeya Musbahu yayi da saurin cewa, “Wanan saɓon naka banajin zai tabbata a gidan nan. Inko ya tabbata to lallai sai mun yashe asusun tsohonta tas inaga abiya sadaki da kuɗin auren nata”.

     Duk yanda sukaso matse dariyarsu hakan ta gagara, tuni suka shiga ƙyalƙyalewa harda masu faɗowa ƙasa da ga kujera. Khalid ne ya fara farga da Master da tun dariyarsu ta farko ya fito. Tsaye yake a jikin ƙofar ya harɗe ƙafafu da hannayensa a ƙirji kawai ya zuba musu idanu. Da sauri Khalid ya zunguri Rabi'u da ke kusa da shi, babu shiri shima ya gimtse tasa dariya yana zungurin Zaid. Shima Zaid da sauri ya haɗiye tasa yana mintsinin kafar Idris da ke kusa da shi. Musbahu da shima idonsa ya kai yay azamar haɗiye tasa yana rarrafawa zai ɓoye bayan kujera. Habib da Salis da basusan anayi ba kam sai ƙara tuntsurawa suke. Salis yace, “Ni why bana tunanin boss zai wani iya soyayya, dan ita tayi yamma shi yayi gabas. Inagama sai munyi karo-karo wajen badashi sadak......”

     Da sauri Musbahu ya rufe masa baki. Hannu Salis ya shiga bige masa yana ƙoƙarin yin magana idonsa ya sauka akan Master da har yanzun yake tsaye yana jinsu. Dan ya wani lumshe idanu tamkar wani mai yin barci a wajen.

     Babu shiri Salis ya ture Musbahu gefe ya miƙe da gudu ya afka bedroom. Ganin haka suma duk sai suka shiga rufa masa baya. Wani silent numfashi master yaja yana buɗe idanunsa akan ƙofar ɗakin da suka shigan harda rufo ƙofa. Uffan bai ceba ya juya ya koma cikin ɗakinsa.


         Koda suka kammala shirin cikin ɗanyun shaddoji iri ɗaya kalar sararin samaniya suka fito, kasa haɗa ido da shi sukayi. Sai satar kallonsa sukeyi ta ƙasan ido, yayinda dariya ke cin ransu a ƙasan zuciya dan shi tashi shigar ta irin marasa jin direbobin nan ce yayi. Da alama da kansa zai tukasu a mota kenan tsabar iya taku. Gaba yay batare da yayi magana ba duk suka rufa masa baya suna ƙoƙarin gimtse dariyarsu.

         Motar bus da zata iya kwashesu ce a waje a fake master nata faman gogewa kai kace driver ɗinne na gaskiya irin wanda suke zuba iya shege a tafa zuwa agege da maraban jos. Dan facemark ɗin dake fuskarsa bata da maraba da ta direbobin da ke tsaka da cin duniya da allura.

          Da kansa ya buɗe musu motar yana harararsu dan ganin kallon da suke masa a munafunce suna murmushi. Sai da suka gama shiga ya rufe yana zagayawa mazaunin driver bayan ya dagama matasan dake zaune a wajen mai shayi anata fira akan abinda ya faru jiya na mayar gwamna hannu. Sai zabga gaddama suke kowa na kare abin son sa. Wasu Master, wasu jami'an tsaro, wasu matar gwamna ɗin. Yayinda wasu ke faman zuba ashariya kai kace faɗa ne ya tashi.

       Murmushi ya saki yana shigewa a motar saboda jin furicin wani da ke faɗin, “Suma jami'an tsaron lusarai ne da zasu zauna mutum ɗaya ya gagaresu. Kawai dai sunyi niyyar barin shegenne kafin suyi ma rayuwarsa walmakalifatu”

     “To ka sani ko aljanine?”.

Wani ya bashi amsa dai-dai master na reverse da motar. Hannu suka ɗago musu wasu na faɗin ALLAH ya sanya alkairi. Dan sun yarda su ɗaurin auren za'aje😂😝.


            Lallai maganar yaran master gaskiya ne. Wannan gida yaji kayan ƙawa da more rayuwa. Shi kansa yana matuƙar son gidan. Dan a cikinsa ne kawai yafi sakewa sosai. Sanann anan ne kawai yake zama da yaransa. Amma duk sauran gidajen ba kullum yake kwana tare da su ba sai yaso.


*_BAYAN KWANAKI UKU_*


           Alhamdulillahi jikin Ummi yayi ƙyau sosai, dan tattali iya tattali take samu da ga iyalanta sanyin idaniyarta. Yayinda wasu a cikin ƴan uwa ke tururwar zuwa dubata da jiki.

      Hibba ce take kwana tare da ita, su kuma su yaya Muhammad da sun taso aiki anan suke tarewa har sai 11 suke wucewa gida. Har zuwa yanzun Abba bai dawo ba da ga tafiyar da yay randa akaima Ummi ai. Itama hajiya mama taɗan lafa da fitinarta saboda ƙafarta data motsa, duk da dai su su yaya Abubakar ɗin sunsan wani abun suke ƙullawa basu nuna sun damu ba.

         Junaid ma ya dawo gida bayan kwana biyu da yayi a asibiti. Sai dai kuma tunda ya dawo ɗin ko ƙeyarsa basu gani ba, sai sauran ƴammatan gidan marasa kunya. Su kuma ko kallo basu ishesu ba. Dan a cikinsu wai sonsu su Yaya Abubakar ɗin sukeyi.

         Tuni shaƙuwa ta shiga tsakanin Ummi da mutum nan da ya biya kuɗin aikinta kaso ɗaya bisa uku. Dan kamar yanda yaranta ke jurar zuwa kullum safiya dubata haka shima yake zuwa dubata duk safiya. Da rana kuma ya aiko da abinci a kawo mata. Da dare idan ya tashi kasuwa ya shigo da fruits ya sake gaisheta sannan ya wuce. Haka zataita saka masa albarka da masa fatan alkairi akan kasuwancinsa da ya sanar mata yanayi, tare da ma mahaifiyarsa da yace ta rasu addu'a, da mahaifinsa da ke raye.

        Addu'ar da take masa ke sakashi jin daɗi. Da kuma yanda su Yaya Umar suka sake da shi sosai tamkar shima ɗan uwansu ne. Hibbah ce dai da ga gaisuwa bata sake kulashi dan dama ita haka take tana da wahalar sabo duk da rawar kanta. Idan kaga ta sake to tare take da Umminta ko yayunta. Su kaɗaine takema yanda taso.

 

            Yau ma suna tsaka da tattare kaya dan an sallamesu Ummi zataje ta cigaba da shan magani a gida yay sallama. Sai da Ummi ta amsa da bashi izinin shigowa sanann ya shigo. Hibbah da ke haɗa kayan ko ɗagowa batai ba balle ta nuna tasan da zamansa. Shima kallo ɗaya yay mata ya dauke kansa. Dan har cikin ransa kallon miskila yake mata tunda ba yarda take tai magana a gabansa ba. Ko surutu take da ya shigo take gimtse bakinta.

     Cike da girmamawa ya gaida Ummi da tambayar ta yaya jikinta?. Fuskarta faɗaɗe da murmushi tace, “Alhmdllh yaro na. Ykk ya Abban naka shima?”.

       “Lafiya lau ya ke Ummi, yana ma gaisheki da baki haƙurin rashin zuwansa saboda shima yana ɗan fama da ƙafa ne”.

        “ALLAH sarki babu damuwa ai. ALLAH shima ya bashi lafiya yasa kaffara ne. Yaya iyali ko babu kaima kamar ƴan uwan naka?”.

        Murmushi yayi yana duƙar da kansa ƙasa da kai hannu ya shafi wuyansa zuwa ƙeya. “Ku mana addu'a dai Ummi, ALLAH ya bamu nagari”.

        “To amin. Amma ni bansan mi kukema hange-hangen ba sam. Mutum bazai yi aure da ƙuruciyarsa ba kamar yanda iyayenmu sukai mana sai ya gama tsofewa. Ni ban sani ba ko tsoron matan kuke ji ne wai?”.

         Murmushin sa ne ya sake faɗaɗa sosai yana faɗin, “Ummi tsoro kuma? Kawai dai matan ne sai a hankali, sai ka dage wajen zaƙulo mai tarbiyya gudun dana sani”.

         “Da kuma wanan dan wanan. ALLAH ya baku na gari to”.

     “Amin Ummi mun gode”.

Yay maganar yana duban Hibbah. Da sauri tace, “Ina yini”. Yanda tai ɗin ma harya so bashi dariya. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Autar mu ykk ya ƙoƙarin kula mana da Ummi?”.

       A ranta tace, (Kaji ɗan iya). A fili kam sai tace, “Alhmdllhi Yaya Isma'il. Ya Abba?”.

        “Abba yana lafiya, yana ma gaishe ki”.

     Murmushi kawai tai batare da ta sake cewa komai ba. Shima sai ya mike kawai yana faɗin, “Ummi bara naje waje idan kun gama shiryawa sai mu wuce”.

      Zaram Hibbah tace, “Ai ga Yaya Ammar nan zaizo ya maidamu gida a motar Yaya Muhammad. Dama kaje abinka mun gode”.

          Ɗan kallonta yayi na wasu sakanni. “Oh auta, kodai bakison naima Ummi rakkiya na samu lada ne?”.

       Baki ta tura gaba ta dauke kanta batare data amsashi ba.

        Ummi tai murmushi da faɗin, “Kaga manta da ita Isma'il. Tunda kazo ka kaimu kawai shi Ammar ɗin bara na kirasa basai ya amso motarba ma”.

     Godiya yay mata yana ficewa. Hibbah kuma ta hau ƙunkunin ita batason motarsa ya cika shishshigi. Ummi na jinta amma tai mata banza. Sai ma ƙoƙarin kiran Ammar da takeyi a waya akan ya dawo basai ya amso motar ba ga Isma'il yazo.


         Badan Hibbah taso ba Isma'il ya kaisu har gida. Sai dai bai shigaba iyakarsa waje ya juya duk da Ummi tace ya shiga. Haƙuri ya bata akan yana sauri ne zai koma kasuwa.

      Albarka sosai Ummi ta saka masa. Hakama Ammar yayta masa godiya. Hibbah kam dama tuni ta shigewarta cikin gida. Sai Ammar ne ya kama Ummi suka shiga cikin suma. Babu motsin kowa a gidan da alama yaran duk sun fice. Hajiya mama kuma maybe tana barci ko kallon nata na masifa dan bata gajiya da sanya ido a television, shiyyasa jikokin nata har tsiya suke mata akan hakan.


           Ko mintuna ashirin basuyi da shigowa ba maƙwafta suka fara shigowa ƙara yima Ummi sannu. Ciki harda Zahidah da Hafsat tare da iyayensu. Sune suka taimakawa Hibbah wajen gyara gidan tsaf. Suka kuma daura girki. A kitchen ɗinne suka sami damar mata tambayar abinda ya faru ranar game da tafiya da ita da ƴan sanda sukayi.

      Duk da aminanta ne tun ƙuruciya sai bata faɗa musu komai ba yanda ya faru saboda tuno gargaɗi da akai mata akan idan ta fitar da zancen za'a saka mata ƴan uwa a tarko. Ta dai basu labarin iya abinda zata iya. Sosai sukaji takaici har cikin ransu. Nan fa suka shiga labarin rauni da hukumomin tsaron ƙasar nan suke da shi.

       Zahidah tace,  “A kullum ca ake ana aiki amma babu alamar hakan a ƙasa. Shin laifin gwamnati ne ko na jami'an tsaron?.”

       Cikin taɓe baki Hibbah ta amshe da faɗin, “Kema dai ƙya faɗa Zahidah. Ita kullum gwamnati tana faɗar kuɗaɗe da take warewa domin harkar tsaro. Amma su jami'an tsaron kullum ca suke basu da kayan aiki isassu. To wai kuɗinne ba'a warewa? Kokuwa jami'anne basa saye? kasa kuɗin suke a tebir kowa ya dauka kasonsa?”.

       Da tsantsar takaici Hafsat tace, “Duk ma yanda sukeyi ɗin ai akwai ranar tonon asiri. Ranar da babu wani gacci ko mayafi da ya isa lulluɓe tsiyar da aka shuka aka binne. Ranar da za'ai walƙiya muga kowa da ayyukansa”.

     A tare Zahidah da Hibbah sukace, (Insha allahu kuwa).

      Haka dai suka cigaba da tattauna abubuwa da dama har suka kammala girkin suka sake gyara Kitchen ɗin. Koda suka fito ɗakin Hibbah suka wuce dan har yanzu ƴan dubiya nata shigowa. Sai dai bayan maigadi ko karen da ke a cikin gidan har yanzu bai leƙo ba. Dama kuma basuje asibitinba. A cewarsu ai ba'a sanar musu bata da lafiya ba.


            Sai dare samarin na Ummi suka dawo. zuwa lokacin sashen tsit da ga Ummi sai Hibbah kawai. Hibbah ma tayi barci a kujera dan akwai gajiyar asibiti tare da ita. Sai sautin kiɗa dake tashi da ga sashen momynsu Junaid da hayaniyar ƴammatanta. Da alama wani fati sukeyi, duk da dai shan kiɗa a gidan ba sabon abu bane ba dama.

          Sannu Ummi tai musu. Yayinda suka zagayeta kowa nason jin yaya karfin jikinta?. Cike da jin daɗi da fara'a take amsa musu. Kafin tace suje suci abinci kar yayi sanyi. Ammar zai tada Hibbah Ummi ta hanashi.

        “ALLAH ka tada ita sai naci gidanku, ka barmin yarinya ta huta ta gaji wlhy, dan tamace kanta ke ciwo”.

              “ALLAH yasa gaskiya ne Ummi. Ni naga a kwanaki ukun nan wani sabon hankali take ji da shi. Ko ciwonki ne ya sata nutsuwa oho”. Ammar ya faɗa yana dariya.

     Suma su Yaya Muhammad duk murmushi sukayi suna nufar dining.


★★★

     

         Har washe gari babu wanda yazo ya duba Ummi a cikinsu hajiya Mama. Abba dama bai dawoba har yanzun. Ummi ko a fuska bata nuna ta damuba. Haka suma su Yaya Abubakar babu wanda yace uffan akan hakan. Sai ma tarkata Hibbah sukai ta wuce islamiyya tun safe kasancewar yau ɗin weekend ce akwai tahfiz da take zuwa dama har suma kansu.

        Badan taso zuwan ba ta tafi harda ƙwallanta dan taga abokin hamayyarta Ammar yau bazai je ba. Da yake a kafane babu nisa ita kaɗai ta fita. Sai da ta fitane taci karo da Hafsat da Zahidah sun taho biyo mata dama. Gaisawa sukai da tambayar jikin Ummi sannan suka wuce islamiyyar.


       Islamiyya ce babba matuƙa. Dan tun da ga ƴan shekara uku har zuwa saba'in duk zasu iya karatu a cikinta. sai dai su yara da ga shekara uku zuwa ashirin da biyar suna zuwa ne tun safe har yamma. Daga ashin da shidda zuwa har tsoffi suna zuwa bayan sallar azhar har magriba, kuma iya weekend ne kawai. Dan haka su su Yaya Muhammad sai karfe biyu zasuje. Itace dai da Ammar dama ke tafiya tun safe. Ammar kuma yau akwai abinda zaiyi shiyyasa bazai je ba.

        Kamar kowanne sati yau ma sun ɗauki darasi daban-daban har zuwa ƙarfe biyar na yamma da aka tashe su. A ƙafa suka taho Zahidah da Hafsat nata hira banda Hibbah. A yanda suka lura gaba ɗaya ta zama wata shiru-shiru. Kafin faruwar wannan al'amarin a kowane sati sukaje islamiyya sai ta addabi kowa a ajin ko ta takalo faɗa. Su kansu malam sun buga har sun bari, dan mafi yawancin lokaci ƙoƙarin ta ne ke cetonta akan wani tsiyar idan ta tafka.

        Cike da jin haushi Hibbah ta ja tsoki tana tsayawa cak da ga tafiyar da sukeyi. Kallonta Zahidah da Hafsat sukai cikin alamun sonjin lafiya?. Bata tanka musu ba, sai kallonta da ta maida kan motar da ke bin bayansu ta gefen titi tunda suka fito Islamiyyar. Suma su Hafsar ɗin sun lura tun ɗazun, sai dai basu kawo a ransu mai motar su yake bi ba. Musamman da ya kasance ya ɗan basu tazara.

           Domin tabbatar da su ɗin yake bi a bayyane yay fakin dai-dai inda Hibbah da ta cika tai fam da takaicinsa take.

       Cikin takun nutsuwa da cikar haiba ga ma'abocin kallo ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tarin kamala ya sanyo kafarsa ƙasa dai-dai yana buɗe ƙofar motar mai baƙin gilashi (tinted glass). Wani shegen ƙamshin turarensa ne ya daki hancunansu tare da sallamar da ke fita cikin ƙasaitacciyar muryarsa mai tarin nutsuwa da sanyi.................✍


       

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻


*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*


_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawa nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki._


*_Muna da haɗin_*


_Turaren wutane_

_Humrh_

_Kulacham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_


_Gyaran jiki_

_Na amare_

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_


*_Da magungun nan mata_*

_Irin su kaza_

_Tantabara_

_Tsumi_

_Gumba_

_Zuma_


*_Duka akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*


Wushishi road KADUNA


08067807620

09057713999


_________________________


*_Chapter Thirteen_*


............Gaba ɗaya jin su Hibba ya ɗauke ɗaf a cikin kunnuwansu lokaci guda. Dukansu sun zuba masa ido tamkar waɗanda sukai gamo da wata baƙuwar hallita. Namiji ne tsayayye da za'a iya kiransa namijin gaske a kowacce irin nahiya ko ƙabila. Sanye yake cikin shadda oxblood da ta fidda ainahin kalar fatarsa mai sheƙi. Fuskarsa cike take da ƙasunba da wani madaidaicin gemu mai kama da na gayu irin na ustazan wanan ƙarnin (😳Bily🤐).

       A kallo ɗaya zaka fahimci rashin son hayaniya daga garesa. Da alama kuma ba mutum bane mai yawan sakewar fuska a mu'amula ko a yanayi.

         Ganin sun shagala wajen kalon sa ya saki wani shegen murmushi yana ƙarasa takowa gaban Hibbah gab. Haka kawai takaici ya kama Hibbah da kallo guda tai masa ta ɗauke kanta tun ɗazun. Cikin ɓata fuska da yatsineta ta ce, “Malam lafiya? Tun ɗazun ka ke ta binmu sai kace wani mai gadin mu”.

          Murmushi ya kuma saki, jerarrun haƙoransa farare na bayyana. Ƙoƙarin saka ƙwayar idanunsa cikin nata yake, amma sai taƙi. Sai ma harara da ta sake zuba masa ta ɗauke kai. A hankali taja siririn tsakin da yasa Hafsat da Zahidah shurin ƙafarta da galla mata tagwayen mintsini.

          “ALLAH ya isa”. Ta faɗi tana hararsu bayan ta saki ƴar siririyar ƙarar data saka baƙon nasu ƙyalƙyalewa da wata dariyarsa da ke fita a nutse. Harara ta sake zuba masa zata bar wajen yay saurin shan gabanta.

         Haushi ya sake kama Hibba. A tsiwace tace, “Malam kana shigarmin hanci fa”

       “Ba malam ɗin bane ai. *_Muhammad Shuraim Aliyu_* ne. Idan kina son nabar shiga hancinki address da number kawai nake buƙata”.

       “Baka da man kai” ta faɗa tana raɓawa ta gefensa ta wuce batare da ya samu koda harar ba yanzun. Badan Zahidah da Hafsat sun so ba sukace masa (bye) suna bin bayanta. Motarsa yay azamar komawa ya cigaba da binsu duk da uban sauri da Hibbah ke zabgawa tamkar zataci da ka. Jitake a ranta da da akwai lungunan da zatabi ya kaita gidansu da shi zatabi dan taga ƙarshen naci. Sai dai kash, tun daga islamiyyar har zuwa gidansu layine ɗoɗar.

        Itace ta fara shigewa gidansu, dan ata wannan hannun itace farko kafin su Hafsat. Dan haka mai mota Shuraim ya tsayar da su Zahidah. Dole suka tsaya dan baiyi kama da wanda za'a cigaba da yarfatawa ba.

         “Kuyi haƙuri fa na takura muku, naga mahaɗi nane babu damar yin sakaci. Dan ALLAH miye sunan ƙawarku?.”

       Kallon juna Hafsat da Zahidah sukayi. Roƙonsu da ya sake yi ne ya saka Hafsat cewa, “Muhibbat! Aliyu Hamza”.

          “Masha ALLAH, nice name. Nan ne gidansu?”.

     A taƙaice suka bashi amsa da eh. Shima sai bai sake jan zancen ba yay musu godiya ya koma motarsa ya wuce.

           “Gaskiya Hibbah ƴar yawa ce, amma fa guy ɗin nan ya haɗu ALLAH. Yaci sunansa Muhammad Shuraim”. Zahidah ta faɗa tana lumshe ido.

       Hafsat tace, “Shiyyasa ai na faɗa masa sunanta. Waya gaya mata ana sakaci da irin waɗan nan gayun a wanan ƙarnin.”

        “Barta ai zamuyi maganinta. ALLAH dai yasa har a hallaya haka yake, da kuma zancen aure yazo mu raƙwashe. Dan zanso Hibbah ta auri guy ɗin nan kodan ta kere sa'a a cikin shaggun su Amlah ɗin gidansun can. Masu shegen kakkafi da son asani. Su adole suna hawa motoci. ALLAH idan suka ga guy ɗin nan sai sun haukace. Sai dai kuma ya musu nisa da na Hibbarmu ne”.

       “Insha ALLAH”. Cewar Hafsat tana ƙyalƙyala dariyar mugunta. dan harta hango idon ƴan gidan su Hibbah da kullum suke mata iyayi akan su sun waye, sun girmeta. Suna hawa motocin da Abbansu ya saya musu su ƴaƴan so banda Hibbah.


★_____________★____________★


            A ɓangaren Master kam tunda suka koma L.E street shida yaransa sukai luf abinsu tamkar basa ƙasar. Da wannan damar jami'an tsaro suka sami na barazanar cewar ya tsorata da harin da suka kai masa ne, ƙilama sun sami nasarar kashesa dan sun harbesa.

      A lokacin da yaga wannan rahoto ba ƙaramin dariya abin ya bashi ba ƙwarai da gaske, ya saki wani malalacin mmurmushi mai ƙunshe da ma'anoni masu yawan gaske da shi ya barma kansa saninsu. Har cikin ransa yana mamakin sai yaushe ne ƙasarmu ta gado zata canja ne? Ji dai shareriyar ƙarya da wanɗan da suke amsa sunan iyaye manyan ƙasa suka karkace suka gilla dan kawai su burge su kuma kankaro ma kansu girma.

       Yaransa kansu abin ya basu dariya. Har cikin ransu suna tausayin ranar da Master ɗinsu zai maida murtani ga waɗan nan mutanen. Inhar bai kaisu kwance ba tabbas sai ya sakasu kuka da hawayensu ko su ajiye aikin koda lokacin ritaya ɗinsu baiyi ba.

                 Shi ba'a sakashi yin abu dole, dan haka baice uffanba sai ma sake lafewa da yay domin tabbatar da zancen nasu. Yayinda a gefe kuma idanunsa ƙur akan batun matar gwamna da hukumar sa'ido akan ta'annati da kayan gwamnati take bin cika har yanzun. Jira suke suyi wani sakaci ko kaɗanne ya sake bankaɗo wasu surukan nata ma duniya harma da su kansu...


____________★__★__★___________


          

           “K kuma lafiya kika shigo kina cikama mutane baki da iska?”. Ummi ta faɗa tana kallon Hibbah da dawowarta kenan da ga islamiyya.

      “Babu komai Ummi. ALLAH yunwa nake ji ne”.

           “Shi abincin da kika tafi da shi fa?”.

       “Ummi naci fa. Kawai wata yunwar dai nake sake ji”.

          “To ALLAH ya ƙyauta, sai kije ki fara yin wanka kiyi salla sannan kizo kici”.

       “Ummi dan ALLAH ki barni in fara ci ni dai”.

     Komai Ummi bata sake ce mataba. Sai ma miƙewa tai ta shiga takawa a hankali domin zuwa ɗakinta tai salla. Dan har yanzu jikin nata bawai yayi ƙarfi yanda ya kamata bane. Abincin ma Yaya Usman ne ya yisa kafin su wuce tasu Islamiyyar.

     Sai da Hibbah taci tai nak da abinci sannan ta shige ɗakinta. Bata fito ba sai wajen 8:30 da tajiyo hayaniyar yayunta. Cike da ɗokin dawowar tasu ta fito. sai dai ganin harda Isma'il ya sata yin turus.

     Komai babu wanda ya ce mata a akan yanayin nata. Sai ma tsokanarta faɗa da Ammar ya shigayi. Amma sai bata tayashi sunyi ba. Masifa ma taketa faman yi a ranta na yanda yayun nata suka sakema Isma'il ɗin kai kace ɗan gidan ne. Shi kansa yanda yake komai kansa tsaye sai ka rantse gidansu ne.

     Bata wani jimaba tai musu sai da safe ta shige, ta barsu a falon suna kallon ball suna hira da cin abinci. Ummi ma tunda ta leƙo suka gaisa da Isma'il ɗin ta koma ciki abinta. Dan haka Hibbah bata san sanda Isma'il yabar gidan ba.


         Washe gari dai an tafi islamiyya babu fushi. Sai dai kuma damuwar ƴan sandan can da ke damunta har yanzu ya sakata komawa wata silent kwana biyun nan. Ko magana ma bata cika sakin jiki tayi ba. Sannan har yanzu bata sake hawa computer ba. Dama wayarta tunda ta dawo take a kashe taƙi ta kunna.

      Yau ma suna fara tafiya a kan hanyarsu ta zuwa islamiyya ta fahimci ana binsu a baya. Wani takaici ne ya turnuƙe ta dan tsaf ta gane guy ɗin jiya ne da tun a ƙofar gate ta watsar da lamarinsa. Ba kuma ta sake tunawa da shi ba sai yanzu da taga motarsa. Sam Zahidah da Hafsat su basu lura da shi ba. Hakan yasa Hibbah fuskewa batace komai ba har suka shige cikin islamiyya.


        Ƙarfe biyar suka ta shi yau ma tamkar kowane weekend. Da ga nan kuma sai wani satin. Gaba ɗaya ta sake watsar da lamarin wani Shuraim. Amma a mamakinta sai gashi ta sake ganin yana biye da su har gida. Kamar da safe yanzu ma bai yunƙurin fitowa ba. A yanzu kam su Zahidah sun ganshi. Koda sukaima Hibbah magana sai tai musu tsaki ma.

        Ƙyaleta sukai ganin shima bai fito a motar ba.


      ★★


    Duk yanda Hibbah taso watsar da lamarin Shuraim sai hakan bai yuwu ba yau. Dan lokaci-lokaci yakan faɗo mata a rai. Sai dai takan ja tsaki da murguɗa baki tamkar tana a gabansa. Har takai abinda takeyi ɗin ya bama Ummi haushi ta balbaleta da faɗa har su Yaya Muhammad suka shigo.

      Sune suka bama Ummin haƙuri da fara tambayar Hibbah cikin lallashi ko wani abu ke damunta ne?. Sam batasan wani boye-ɓoye ba. Musamman ma awajen yayunta da suke da matukar shaƙuwa da juna. Kanta tsaye ta shiga basu labarin abinda takema tsakin.

        “Woow, ƴar Tanee ɗin Ummi anyi saurayi Congratulations. Yau ɗaya a tarihi dole na rubuta na ajiye na haɗa da shagalin barbaje kolin fati na musamman a gidan nan nayi suriki a matsayina na yaya mai lasisin cin gadon Muhibbat Aliyu Hamza (Tanee)”. Ammar ya faɗa yana tafa hannaye cike da tsokana. Filo Yaya Abubakar ya ɗauka ya jefe sa da shi. Dariya gaba ɗayansu suka kwashe da shi saboda yanda Ammar ya baje a ƙasa da bata fuska alamar yaji zafi..

       Hibbah kam dariya sosai take masa harda faɗowa saman kujera. Ta saka yatsun hannunta a kunne tana masa gwalo kamar yanda yara keyi. Filon da aka jefesa da shi ya ɗauka zai jefo mata ta tashi da gudu tai hanyar ɗakinta.

       “Ummi kanta sai da tai dariya. Cikin dariyar ne ta ce, “ALLAH dai ya shirye ku, kai da Tanee ɗin bansan wanda yafi wani shashanci ba. Ni tashi ka ɗakkomin magunguna na a ɗaki tunda ita ta gudu nasan ba sake dawowa zatai ba kuma”.

       Amsawa Ammar yayi da to yana mikewa ya nufi ɗakin Ummin. A dai-dai kuma wanann lokacin Abba da hajiya mama da wasu tsoffin maza biyu suka shigo falon da sallama.

       Da ga Ummi har yaranta da mamaki suke kallonsu, musamman ma Abba da basusan ya dawo gidan ba. Tsoffin kuma Ummi ce kawai ta sansu. Da ƙyar ta iya buɗe baki cikin ƙarfin hali ta ce, “Kawu sannunku da zuwa”.

    Farin ne kawai yace, “Uhumm”. Ɗaya kam bai tanka ba. Sai dai bin su Yaya Muhammad da yake da kallo tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa.

         Yaya Muhammad da ya lura da kallon ƙurullar da kuma yanayin da Ummi ta shiga tamkar na ruɗani ya saka shi fara gaishesu. Haka yasa suma sauran ƙannensa fara gaisuwar.

     Amsa musu sukai suna cigaba da kallonsu. Yayinda hajiya mama keta faman ƙyaɓe baki. Abba kam sai wani harare-harare yakeyi.

         Ummi tai ƙasa da kai cike da ladabi ta hau gaishesu itama. Basu wani amsa mata da ƙyau ba. Sai ma baƙin tsohon ne a kausashe ya ce, “Uh lallai Asiya an samu guri kam tabbas. Ga manyan sojoji kuma a gefe masu tare miki faɗa. Dama irin wanan ai ake gudu akan auren masu asali irin naki. Saboda shi hali naso yakeyi har jikokin bayan-baya. Gashi ko mun gani yau da idanun mu”.

       Idanu Ummi ta lumshe a hankali kanta a ƙasa. Wasu zafafan hawaye suka silalo saman kumatunta. Sai dai cikin dabara ta kai hannu ta share dan kar ƴaƴanta su gani. Cikin dauriya da juriyar da kowa ya santa da shi ta ɗago murmushi a saman fuskarta. “Kawu ina fatan kunzo lafiya?”. Ta faɗa domin son kauda wancam zancen da ya fara.

      Sai dai sam bataci nasara ba. Dan kuwa hajiya mama ce ta amshe da faɗin, “Ni ko zan faɗa maka hali naso yake Hannafi, dan kuwa gashi nan a zuri'a ta. Wlhy badan jinin ɗan inna (babansu Hibbah) na yawo jikin waɗan man yaran ba da tuni na daɗe da sallama su, babu wanda ya cuceni sai malam da ya ƙarrafa wannan auren da har na mutu bazan taɓa daina kuka da ALLAH wadai a kansa ba. Wai fa kuga waɗan nan sanƙama-sanƙaman yaran ne babu mai ko neman aure. Kuma uwarsu ta zuba musu ido saboda ita ɗin bata hanyar.......”

        “Waɗan nan kuma fa? Da ga ina?”. Cewar Ammar da ya fito da ga ɗakin Ummi yaci karo da abinda bai bari ba. Furucinsa kuma ne ya katse zancen da Hajiya mama ta ɗakko tiryan-tiryan.

      Babu wanda ya bashi amsa. Sai zuba masa ido da tsoffin sukai tare da Abba. Baki ya buɗe zai sake magana Ummi ta girgiza masa kanta. Kansa ya ɗauke kawai tare da durƙusawa gabanta ya na ajiye ɗan basket ɗin da magungunan nata ke a ciki. Ɓalla mata ya shigayi yana miƙa mata tare da saka mata ruwa akan baki.

     Wani uban salllami farin tsohon nan ya shiga jerawa yana tafa hannaye. “Kai mizan gani haka ni Ballo (Bello😂). Wannan wane irin kafurcine kuma haka Hasiya?. Wannan ƙurmisheshen gardin ɗan ke baki ruwa a baki kuma?. A to lallai zancen Hannafi gaskiya ne. Da alama ma ke kinfi uwar taki iya shege”.

      A fusace Yaya Umar ya miƙe zai bar falon. Abba ya katsesa a gadarance da faɗin, “To mara mutunci da baiyi gadon arziki ba sai ka tsaya dan zuwan nakune ai”.

        Ido Yaya Umar ya rimtse da ƙarfi yana dunƙule hannunsa.

     “Kai fitsararre, idan shi ka rainashi ai mu ka ɗaga mana ƙafa kodan rashin saninmu da kai ko.”

     Ƙafa Yaya Umar ya ɗaga zai cigaba da tafiya wasu hawaye masu zafin gaske na gangaroma kumatunsa.

      “Dawo ka zauna”. Umarni da ga Ummi ya hanashi ajiye kafar da ya ɗaga ɗin.

       “Iyeee! A lallai Haƙilu kuna ganin jalalar rayuwa. Wato itace kawai mai sawa da hanawa akan ƴaƴan, bayan wahalar da kaci na kula da su tsahon shekaru. Tabbas Hasiya kinyi asara kekam.

        Da sauri Ammar ya ɗago ya kallesa. Ya miƙe tare da nuna Kawu Bello da ɗan yatsa cikin kaushi da ɗaci yace, “Kai kaine kai asara tsohon banza ɗan tasha”.

        A tare Hajiya mama da Abba da kawu Bello da kawu Hannafi suka zazzaro ido suna zabura. Ummi tai saurin fisgo hannun Ammar tare da daka masa tsawa. “Aliyu!!”.

          Cikin ficewar hayyaci ya fisge hannunta a cikin nasa da faɗin, “Haba Ummi, wai sai yau she ne zaki daina zama anacin kashi akanki a gidannan ne? Babu ruwana da alaƙarsu gareki. Na rantse da ALLAH idan tsoho bai gyara kalaman harshensa ba to kafin ya fita a falon nan zan datse harshen kuwa na jefar ƙasa”.

      Ɗimmm

Ummi ta sauke ma Ammar dundu. “Ammar kanada hankali kuwa? Miyasa kai bana faɗa maka kaji ne wai?. Kasan waɗan nan ɗin su wanene a wajena? To iyayena ne, ƙannen mahaifiyata ne, tamakar yanda Hajiya mama ta ke uwa a gareni itama. Ka shiga hankalinka kona saɓa maka kaji ko”.

      “Amma Umm.....”

Wani kallo da ta masa ya sakashi yin shiru ya haɗiye sauran maganar.

     Wata ƴar dariya Abba yayi da faɗin, “Kun gani ko? Hakafa gidan yake kullum kamar na ƴan tasha. Sun rainani basa ganin mutunci na bale na mama, bayan ma yaƙi nai da zuciyata wajen rufa mata asiri. To uwar tasu ma ba wai raga mata sukeyi ba. Dan haka na ɗakko ku nan dan ayita ta ƙare. Bazan iya cigaba da ciyar da ƙattan banza ba. Dan haka na yanke shawarar aura musu su Amlah, inba hakaba wataran yankan rago za'a samu sunmin a gidan nan. Ita kuma waccan fitsararriyar uwar ƴan janye-janyen jidalin da suke ɗaurama ƙugu a gidan tana zuba taɓara saboda ita ƴar ido ce Junaid zan aurawa. kunga shikenan anyi tuwona maina ko ba komai sun huta da gori ma asalin uwarsu.”

       “Wannan gaskiya ne Haƙilu. Ai kama taimaki rayuwarsu. Dan a zamanin nan kowa yaji tushen zancen ta ina zai basu ƴarsa. Balle ma ita da take ƴa mace. Bayan ma ka riga ka bata Junaidu ɗin ai wlhy da nayima Musa kamu ma”.

          Da sauri Abba ya ce, “Shi Musan sai yay haƙuri tunda na riga naima Junaid ɗin alƙawari dai. ALLAH ya bashi ta shi”.


       Yaya Muhammad da ya ƙule matuƙa da takaicinsu ya buɗe baki zai yi magana. Amma sai Ummi tai saurin girgiza masa kanta cikin gargaɗi. Kawai sai gani tai hawaye suna sakko masa tsabar zuciyarsa ta kai ƙololuwa a ɓaci.

         Ummi itace ke katange dukkan yunƙurinsu, sun rasa miyasa take hakan a gare su game da dangin mahaifin nasu. Abinda ma basu gane ba shine a yau. Shin ta amshi ballagazayen ƴaƴan gidan da ake iƙirarin an basu kenan matsayin matansu ko mi? Koda ace zasuyi haƙuri suyi mata biyayya bazasu taɓa amincewa a aurama Junaid Hibbah ba. Sai dai komi zai faru ya faru wlhy...........✍


*_Tofa masu karatu, yaya kenan? Wanene zai ci nasara tsakanin su Abba da su Yaya Muhammad? Ni kaina inason jin wace ƙaddarace baibaye da Ummi da ta fi bukatar haƙuri da cin kashin waɗan nan mutane haka?. Kumuje zuwa. muna gab da tsunduma cikin wasan gadan-gadan😉👎🏻_*


*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

         

           

    

           

        *_Typing📲_*


*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻


*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*


_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawa nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki._


*_Muna da haɗin_*


_Turaren wutane_

_Humrh_

_Kulacham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_


_Gyaran jiki_

_Na amare_

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_


*_Da magungun nan mata_*

_Irin su kaza_

_Tantabara_

_Tsumi_

_Gumba_

_Zuma_


*_Duka akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*


Wushishi road KADUNA


08067807620

09057713999


_________________________


*_Chapter Fourteen_*


.............A gidan Ummi komai ya canja. Gaba ɗaya ya ranta sun bar walwala. Sun daina fara'a. Sun daina zaman hira, abinci ma kaɗan suke tsakura. Idan tai magana suce sun ƙoshi. Ta ko ina ta gaza gane kansu.

      Da farko tayi biris da su, duk da kuwa ta fahimcesu tsaf. Sai dai ganin abin nasu bana ƙare bane sai itama lamarin ya fara damunta. Dan ita kanta sun jefata a cikin kaɗaici. Hatta da Hibbah ƴar karamarsu itama ta ɗauke mata wuta. Saboda wannan abun daya faru ma ta tattara ta koma makaranta duk da Yaya Abubakar ya hanata zuwa da.

    Duk da ta ɗan fuskanci ƙalubale a wajen mutane a ranar data koma saboda tafiya da itan da ƴan sanda sukazo sukayi ranar haka ta daurema zuciyarta ta cigaba da zuwa. Bakuma ta sanarma kowa ba. Dan a ganinta da zaman gidan su tana cigaba da ganin Abba da baƙinsa gara kallon da ƴan makarantar zasu mata.

        Tunfa Ummi na ɗaukar lamarin nasu wasa sai ƙara girmama ya keyi. Dan kwanakin nan biyu ma basa dawowa gidan sai sun dai-daici tayi barci sannan. Hankalinta sosai ya kuma tashi. Ga damuwar yaranta, ga damuwar auren da aketa ƙulle-ƙullen nana musu na son zuciya. Wanda tsaf ta gama fahimta da gane ina hakan ya dosa. Sarai ta gane manufar Abbah akan son ƙulla auren ƴaƴanta da nashi, manufar kuma duk ɗaya ce tsakaninsa da hajiya mama.

      Gaba ɗaya ta rasa ina zata saka kanta taji sanyi, babu uwa babu uba, babu abokin shawara a cikin ƴan uwa, babu wanda zata kaima ƙara ya duba matsalarta ya share kukanta. Gudun abinda zaije ya dawo kuma ke sakata kwaɓar ƴaƴanta akowane lokaci. Bata son abinda zai rabata da su. Bata son a cutar mata da su. Dan sune hope ɗinta, sune murmushin fuskarta. Sune masu share hawayenta da tun tana ƴar ƙanƙanuwarta suke kwaranya a bisa kumatunta. Tasan nuna ƙarfinsu ya kawo kuma zai iya zama sanadin da komai Abba zai iya aikatawa a garesu domin samun cikar burinsa, kuma kamar yanda yasha faɗa koda ya salwantar da rayukansu babu mai yarda shine ya aikata. Wasu hawaye ne masu zafi suka silalo mata saman fuska.

       Wata banzar dariya Abba da ke shigowa cikin sashen ya shiga tuntsurawa yana tafa hannaye. Cike da izgili ya dubeta sheƙeƙe yana faɗin, “Kuka kuka kuka! Ai kuwa yanzu kika fara kuka Asiya. Yo ina jarumtar taki ne yau? Shin har kin fara zuwa ƙasa ne tunkan ma a ɗaura auran manufarsa kuma ta tabbata?. Tunda har kikace ni ban isaba Asiya, to wlhy kema bazaki taɓa isa ba. Yau ina wanda kike gadar da shi? Ya tafi tamkarma ba'ayisa ba. Abinda kika hanashi yay mana ta hanyar zagon ƙasa ya dawo hannunmu a lokacin da ko ido baki isa ɗagawa akai ba. To suma ƴaƴa mazan da kike ɗagawar kin haifa masa zasu mamaye komai tafin hannunmu zasu cigaba da zama ballagaza kawai. Zaki iya tashi kuma mu shige ciki dan ina bukatar haƙƙina. Inba hakaba kuma zan ƙwata anan cikin falon babu ruwana....”

      Hanyar bedroom ɗinta ya nufa yana gama faɗa alamar ta biyosa. Ummi da ke jin wani ƙullutun abu yazo ya tokare maƙoshinta ta shiga karanto duk addu'ar da tazo mata a saman harshe saboda jin numfashinta na fita a gwagwgwame. A hankali sanyi ya rinƙa shiga cikin ƙashinta, yayin da jikinta ya fara wani irin rawa, har haƙwaranta na haɗuwa waje guda. Hannu takai domin lalubo wayarta da ke saman centre table. Sai dai hakan ya gagara sakamakon gushewar gani da ta risketa a lokaci ƙanƙani. Hannunta ya goce da ga lalube wayar, sai gata ƙasa wanwar da ga saman kujera.....

         A dai-dai wannan lokacin Hibbah ta shigo tana masifar bibiyarta da kullum Shuraim keyi babu fashi balle nuna gajiyawa duk da yarfatashin da take yi a kulum. Data fita da ga gida zuwa makaranta yana biye da ita. Hakama idan ta dawo sai ya rakota har gida ta hanyar bibiyarta. Zuwa yanzun tun lamarin nasa na bata mamaki har ya koma takaici da al-ajab. Har tabbayar kanta take shin baida aikinyi ne ko mi?. Wannan takaicin nasane ya sata yau ana saukesu a napep taje tai masa knocking glass. Yana saukewa ta balbalesa da masifa batare data yarda sun haɗa ido ba dan karma yay mata kwarjini. Sai dai abin ALLAH wadai da takaici, harta gama masifar tata ma bai nuna yaji haushi ba. Sai ma murmushin da ya nema rikita mata lissafi ya sakar mata yana wani narkewa a cikin kujera.

          Wani uban kara ta ƙwalla tana isa inda Ummi ke kwance wanwar tana wani irin tari dake fita da ƙyar. Kiran sunanta ta shigayi tana girgizata hankali tashe. Sai dai ina Ummi ta fita hayyacinta. Dabarar rarumar wayar Ummin ce tazo mata a rai. Batare data nutsu wajen ganin wanda ta kira ba kawai tai dailing numbern farko, dan tasan su ne dai kawai suke yawan kiran no din Ummin tasu a koda yaushe.

       “Yaya dan ALLAH kazo gida, Ummi...Umminmu. Na shiga ukuna. Ummi dan ALLAH ki tashi. Wlhy kika mutu nima mutuwa zanyi. Dan ALLAH Ummi na roƙeki karki mutu. wlhy bazamu sake yin fushi da ke ba. Mun tuba Ummi, mun daina. Mun yarda zamu auresu Ummi.......”

    Sambatu taketa faman yi tama manta da waya a kunnenta. Kukanta ya fiddo Abba da ga ɗakin Ummi ɗin wando a hannu. dan harya cire kaya ya baje a gado yana jiran jakarsa ta shigo ya murza a wulaƙance. Ido huɗu sukai da Hibbah da ke sake ƙwala kuka tana kiran Ummi da girgizata. Ai sai ta sake fasa wata ƙarar ganin a yanda ya fito, saboda bai saka wandon dai-dai ba an samu mishkila wajen bayyanar jikinsa.

       Sakin Ummi tai ta fita a guje da ga sashen baki ɗaya jikinta na rawa. Tana da yayu maza manya. Amma tunda take da su ko zama da singlet da boxers basu taɓa yi a gabanta ba balle a yanayin da Abban ya fito wanda bata taɓa ganin wani mahaluki a yanayin ba.

           Jikinsa ta faɗa dai-dai maigadi ya buɗe masa gate ya shigo, dan Hibbah wayarsa ta kira saboda shine na ƙarahe da ya kira Ummi yaji yaya jikinta? Dan ya kwana biyu baizo gidan ba. Duk yanda yaso ganin ya janyeta a jikin nasa hakan ya gagara, sai sake ruƙunƙumesa takeyi jikinta na rawa, yayinda taketa faman son ɓoye fuskarta a ƙirjinsa duk da tsahon nata gaba ɗaya iya ƙirjin nasa ta tsaya.

           Cikin zafi-zafi ya shiga tureta yana girgizata. “K Muhibbat nutsu, muje inga Ummin gani nazo”.

      Jin muryar da bata yayunta ba ya sata saurin ja da baya tabar jikinsa. Isma'il da ya samu ta rabu da jikin nasa da sassarfa yay gaba abinsa zuwa sashensu har yana haɗawa da ɗan gudu-gudu. kusan cin karo sukai da Abbah da ya koma ya ɗakko kayansa saboda ihun da Hibbah tayi ya farga da halin da yake a ciki. Duk da ya kuma ga Ummi a yashe a ƙasa sai kawai firgici biyu ya kamashi. Na farko kar wani yazo ya gansa a yanda yake sakamakon ihun Hibbah a zata wani abu yaso mata har Ummi ta shiga halin da take ciki a yanzu. Dan haka ya fito dan ya gudu salin alin, idan Hibbah ta sako sunansa a ciki kuwa yasan ta yanda zai kare kansa ai.

         Haka kawai zuciyar Isma'il ta raya masa irin abinda Abban ke gudu. Dan haka yasa ƙafa ya taɗesa sai gashi a ƙasa tim. Takan kafafun Abba yabi da shaggun takalman ƙafarsa, ji kake ƙasss ƙashi na bada sautin karyewa ko tsagewa. Wata iriyar wahalalliyar ƙara Abba ya saki tare da ɗaukewar numfashi na wucin gadi. Ko waiwayensa Isma'il baiyiba ya ida afkawa cikin falon inda ya hango Ummi a ƙasa itama babu alamar rai tattare da ita.

        “Ummi!... Ummi! Ummi!!” ya shiga ƙwala mata kira da kama hannunta yana girgizawa. Sai dai babu alamar motsi tare da ita sam. Mikewa yay da sauri ya ciro wayarsa yay kiran Yaya Umar da yasan shine mafi kusanci da gida. Sai dai bai ɗaga ba. Tunawa ana sallar la'asar yanzu haka ya sakashi cije lip ɗinsa na ƙasa ya cusa wayar a aljihu. Batare da tunanin komai ba ya ciccibi Ummi gaba ɗayanta yay waje. Sai lokacin Hibbah ta nufo falon sabida hango abinda Isma'il ɗin yay ma Abba.

      “Muje asibiti” yace mata kawai yana nufar hanyar gate. Babu musu ta bisa tana kuka da riƙe hannun Ummi ɗin da ya ɗakko. Sai lokacin kuma Hajiya mama ke fitowa da ga sashensu itama. Ta bisu da wani irin kallo mai ma'anoni da yawa saboda ganin baƙon fuska ɗauke da Ummi ɗin. Dan duk zuwan da Isma'il ɗin keyi gidan ba taɓa haɗuwa sukai ba. Wahalallen ihun da Abba ya saki ne ya fargar da ita halin da yake a ciki, babu shiri ta runtuma a guje kansa tana ƙwala kiran sunansa.......


★★★★_____★_____★★★


       Tun kan su ƙarasa asibitin Isma'il yay ƙoƙarin kiran doctor Bilal. Cikin sa'a kuwa ya ɗaga dan mutuminsa ne. Bayani yay masa cewar gasu a hanya tare da mara lafiya su zam cikin shiri. Dr bilal yace babu damuwa sai sunzo.

       Cikin mintuna kalilan kuwa suka iso asibitin saboda uban gudu da yake zugawa a hanya. Kamar yanda yay fata sun sami su Dr Bilal na dakon isowarsu. Babu ɓata lokaci aka shiga da Ummi ciki.

     Kuka sosai Hibbah keyi da son binsu, badan yaso ba ya riƙo hannunta yana ƙoƙarin dakatar da ita. Sai dai taƙi ta nutsu, dole yay mata yanda yasan zata nutsun, ya jawota jikinsa ya rungume. Da ƙarfi ya rumtse idanunsa zuciyarsa na wani irin bahagon gudu.

            Itako Hibbah tuni ta ƙara lafewa tana wani irin kuka mai ban tausayi, dan gaba ɗaya ma ta mance a jikin wa take. Sai da ƴar nutsuwa ta fara zo mata ne sakamakon kiran wayarsa da akayi tai azamar janye jikinta. Komai baiceba shima. Sai ƙoƙarin ciro wayarsa da yay a aljihun wandonsa. Ita kuma ta koma kan kujera ta zauna tana cigaba da kukanta da add'ur ALLAH ya bama Umminsu lafiya.

      Yaya Umar da yaga miss call ɗinsa bayan fitowarsu massallaci ne ya kirasa. Dan haka yay masa bayanin da bazai ruɗar da shi ba. Koda ya yanke kiran sai ya shiga kiran sauran suma.


★★


      Cikin mintuna kalilan yaran Ummi suka gama hallara a asibitin. Gaba ɗaya hankalinsu a tashe yake. Sai dai sunata ƙoƙarin lallashin Hibbah da ke kuka sosai har yanzu. Harda su amai. Ga zazzaɓi mai zafi ya gama lulluɓeta matuƙa.

     Fitowar Dr bilal ya sasu maida hankalinau garesa. Cikin son kawar da damuwarsu yace, “Ku kwantar da hankalinku babu wata matsala mai yawa insha ALLAH. Dan yayi ƙoƙarin kawota asibiti akan lokaci. Sai dai ku kiyaye dan ALLAH kar yazam muna tufƙa ana warwarewa.”

        A take nutsuwa ta saukar musu. suka shiga jerama Isma'il godiya tamkar zasu ɗaukesa su goya. Shi dai ransa a dagule yake da takaicin Abbansu, dan shi baisan ba mahaifinsu bane.


          Sun cigaba da dakon jiran farkawar Ummi da aka sakama ƙarin ruwa a asibitin har wajen sha biyu na dare da aka basu sallama saboda Alhmdllhi komai normal, amma sai Dr Bilal yace su barta anan ta ƙara hutawa har sai gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma. Duk sun gamsu da bayanin nasa. Dan haka sukai masa godiya da fitowa dan su tafi gida Hibbah da zata kwana da ita tare da Nurse tayo musu rakkiya.

         Har sannan Isma'il na tare da su. Karan farko a tarihi da Hibbah ta dubesa cike da girmamawa da idanunta kumburarru. “Yaya Isma'il mun gode sosai. ALLAH ya bada ladan zuminci. Yanda ka jikan Ummin mu, kaima ALLAH ya baka ƴaƴa da zasu jiƙanka. Ya ƙarama Abbanka lafiya da tsahon rai mai amfani, ya jiƙan Umma”.

      Ba karamin ratsa zuciyarsa addu'ar tata tayi ba. Ya kafeta da ido har sai da Yaya Umar ya zunguresa sannan ya sauke ajiyar numfashi da sakin murmushi. “Nagode sosai auta. ALLAH ya karama Ummi lafiya ya albarkaci rayuwarki. ALLAH ya baki miji na gari”.

       Cikin jin daɗi yayunta suka amsa masa da amin. Itama tattausan murmushi da bata taɓa masaba a yanzu ta saki tana juya baya alamar taji kunya da addu'arsa ta ƙarshe. Su Yaya Usman suka ƙyalƙyale da dariya Ammar na tsokanarta. Bata kulashi ba dan yau batajin yin faɗa Ummi bata da lafiya.

      Tun a asibitin suka rabu da Isma'il. Shi yay gida suma suka wuce gida. Inda tunkan su shiga sukaji labari a bakin maigadi cewar Abba ma na asibiti. Ya fadi ne a bakin ƙofa da alama yaji ciwo a kafafunsa. Hakama goshinsa da bakinsa sun fashe yanata zubar da jini ma.

       Kasancewar da ga Hibbah har Isma'il basuyi musu bayani ba sai basu kawo komai a ransu ba suka ɗauka tsautsyine kawai. Addau'ar samun lafiya sukai masa suka shige. Dan ba'ai musu tarbiyyar son ganin lalacewar wani ba koda ace maƙiyinsu ne.


*________________________________*


           A ɓangaren Abba kam da ƙyar aka iya ɗagasa da ga inda Isma'il ya taɗesa. Bakinsa duk ya fashe da goshinsa daya daushi kwalliyar tsitstsigen baranda. Hakama kafafunsa da alamar yayi karaya ko targaɗe. Dan ko takasu baya iyayi ma. Hasalima a sume aka ɗaukesa da ga gidan zuwa asibiti saboda jinin da yayta kwararwa kafin Junaid yazo da mota su fita da shi zuwa asibiti.


      Su hajiya mama babu wanda yasan ainahin abinda ya faru da Abban suma. sai dai kansu ya ɗaure matuƙa ganin da ga shi sai boxer kayan da ya fito da su a hannu sabida ihun Hibbah yashe a gefe. Sunma rasa yaya zasu fasalta al'amarin musamman da likita ya tabbatar musu kafarsa ɗaya ta samu karaya da hannunsa. Ɗayar kuma tsagewar ƙashi ce ga ciwon goshinsa dana bakinsa da yay wanu zundun-dun uwa an saki shantu.

         Hajiya mama ta hana ai masa gyaran karayar wai sunada mai gyaran gargajiya zaizo da ga kauye. Sai a jirasa yana hanyar tahowa. Tun yamma ake jiran mai gyara har dare ya tsala bai iso ba. Haushin abinda Hajiya mama tai musu su kuma likitocin sunce bazasu taɓa ƙafar ba har sai wanda tace ɗin yazo ya gyara masan. Duk roƙon da Momy taita musu sunce bazasuyiba wlhy.


*_WASHE GARI_*


     Da safe acikin su Yaya Abubakar babu wanda yabi takan zancen duba wani Abba. Da dai su Ammar suka kammala yin breakfast suka gyara gida sai suka runguɗa asibiti wajen mahaifiyarsu. Sun isketa zaune Hibbah na shafa mata mai saboda wanka da tayo.

          Ta dubesu cike da tausayi da begen ƙishirwar murmushinsu. Duk wanda ya gaidata sai ta kamo hannunsa ta shafa kansa tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta.

       “Ku daina fushi da Umminku kunji”.

Ta faɗa cikin damuwa da ƙunar da takeji a cikin zuciyarta. Komai basu iya cewa ba sai dai dukansu sunyi ƙasa da kawuna ransu fal tausayinta. Musamman Yaya Muhammad da yasan wani yanki na labarinta batare da itama ta sani ba, shima Abbansu ne ya sanar masa kafin ya rasu. Ya kuma tabbatar masa ya faɗa masane saboda wataran yasan kunnensa zaiji gorin da za'aima mahaifiyarsa kar zuciyarsa ta ɗauki wani abun daban. Shine ya fara jan numfashi da ƙyar da dubanta yana ƙoƙari haɗiye hawayen da suka ciko masa ido.

        “Ummi baki mana laifin komai ba. Amma dan ALLAH a wanan gaɓar munason jin wani abu game da ke. badan bamu yarda dake bane. Sai don son sanin minene dalilin da yasa duk basa ƙaunarki?. Mi kikayi musu haka da zafi? Miyasa kika yarda kika auresa bayan shiɗin kanin Abbanmu ne? Mai fuska biyu ga mutane”.

          Murmushi ta saki mai kuna da kai hannu ta shafo kan Yaya Muhammad. “Muhammadu Aminullahi zan faɗa muku insha ALLAH. Da zaran munje gida yau zakuji komai”.

       A take fuskokinsu suka nuna jin daɗin zancenta. Dan danan suka ɓalle mata hira kamar yanda suka saba a baya. Itako sai murmushi take zuciyarya na kara sanyaya da ɗunbin sonsu da kaunarsu.

       Dr bilal ne ya shigo, bayan sun gaisa yace suje waje zasu ɗan ƙara duba Ummin suga ya ya komai na tafiya normal. Sun masa godiya tare da fitowa su duka. Duk anan ƙofar ɗakin suke zaune Hibbah nacin abincin da sukazo da shi. Kamar ance ta ɗaga kai sai idanunta karaf akan Zahidah da Hafsat, Muhammad Shuraim biye da su.

      Babu shiri ta miƙe zaram tana rarraba idanuwa. Tunkan su ƙaraso tace, “Lallai ma! Miya kawoka nan?”.

       Furucin natane yaja hankalin yayun nata gaba ɗaya. A tare suka sauke idanunsu bisa kan Muhammad Shuraim da ke sanye cikin ado da kamshi na shadda da keta maiƙo, ga hular zanna da ya murza wadda ta kara masa cikar kamala da kwar jini.

      A fusace Hibba ta sake buɗe baki zatai magana Yaya Umar ya harareta. Dole tai shiru tana wani mar-mar da idanu akaikaice tana ballama Shuraim harara.

          Shiko murmushi ya saki yana matuƙar jin mamakin tsaurin ido irin na Hibbah. Ya cigaba da takowa a hankali zuwa gaban su Yaya Muhammad da duk hankalinsu a kansa yake suna kallonsa cike da nazari. Duk da zasu iya yin sa'anni da Yaya Umar cikin girmamawa ya shiga gaishesu su duka. Gashi yaki yarda ya haɗa idanu da su shi a dole yana gaban surukai.

       Hakan ba karamin dariya da burgesu yay ba. Ammar sai wani ƙara buɗe ƙwanji ake su a dole yayu. Yaya Muhammad ya ce, “To sai dai bamu gane baƙon namu ba?”.

       Murmushi Shuraim yay cike da ladabi yana ɗan shafar ƙeya yace, “Yayanmu bazaka sanni ba. Dama ina jiran lokaci ne nazo gareku. Sai dai jin Momy babu lafiya yasa nazo dubata kafin hakan. Sunana Muhammad Shuraim Aliyu. Mai fata da addu'ar samun nutsatstsiyar yarinya mai tarbiyya kamar Muhibbat....”

      Wata malalaciyar harara Hibba ta zuba masa tamkar zata fashe dan takaici da haushinsa. Yayinda Ammar dake guntse dariya a kaikaice yace, “Dama dai a tarbiyyar ka tsaya dana yadda. Amma ba Nutsuw.....”

           Gwiwar hannu Yaya Umar dake gefensa yasa ya bugesa. Yay azamar rumtse ido da ɗaura hannunsa a wajen yana faɗin, “Wayyo Ya Umar zaka kashe ni”.

          Yaya Abubakar kam murmushi ya sakarma Shuraim shi da Yaya Muhammad. Haka kawai su dai Shuraim ɗin ya birgesu matuƙa. Dan haka Yaya Abubakar yace, “Masha ALLAH mun gode matuƙa. Bara doctor ta fito sai mu shiga ka dubata”.

       Sosai daɗi ya kama Shuraim, ya shiga jera musu godiya da addu'ar samun lafiya ga Ummi. Su ma su Zahidah suka shiga gaishesu da tambayar jikin Ummi ɗin. Hibbah kam taƙi kulasu suma wai haushinsu takeji sun faɗama Shuraim sirrinta.

      Suma basu kulata ba dan sun gane manufarta sarai. Haka ta ringa antaya musu harara suna ramawa har Doctor ya fito suka shiga su duka.

      Tunda suka shigo Ummi take kallon Shuraim da ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta da tambayar jikinta. Fahimtar ƙarin bayani take buƙata yasa Ammar fara rattafo zance. Sosai murmushin fuskar Ummi ya sake faɗaɗa. Dan har cikin ranta taji ƙaunar Shuraim da samun nutsuwa da shi. Tana kuma fata da addu'ar ya zame musu mafita akan haɗa Junaid aure da Hibbah da ake ƙoƙarin ƙullawa.

         Basu wani jima sosai ba yace zai wuce, bayan ya ajiyema Ummi ledan dubiya. Godiya suka sake masa Ammar ya tafi rakasa. Yana ƙoƙarin ficewa Isma'il ke ƙoƙarin shigowa. Baya ya koma ya bashi hanya. Batare da tunanin komai ba Ammar ya gabatar da Shuraim ga Isma'il ɗin. Shima Shuraim Ammar ya gabatar masa da Isma'il matsayin ɗan uwansu. Hakan ya basu damar yima juna kallon ido ciikin ido. Da alama kallon da Isma'il yayma Shuraim ɗin na tsantsar kishi ne da shima kansa baisan yayi ba. Haka shima Shuraim kallon alamar tambaya da tsoron sakkiyar da babu ruwa yayma Isma'il ɗin kai tsaye. Cike da basarwa kuma sai suka saki hannun juna kowa na ƙoƙarin haɗiye abinda ke ransa da cikin idanunsa, kafin su kalli Hibbah a tare Shuraim ya ida ficewa, Isma'il ya karasa shigowa............✍


*_Tofa mazaje ya take ne?😂😂💃🏻, kodai Hibbahr mu ta mutunci ta haɗa karo ne😹😹😝. To muje zuwa muga wane mai rabon zai ɗauka a ciki, dan har yanzu itaɗin allura ce a cikin ruwa mai rabo ka ɗauka. zamuga yaya TAKUN SAƘAAR zai kasance a filin dagar dan ga Junaidu ma bin Halilu a gehe yana jiran waman dakala bati siddan. Ga kuma oga master da tabbas sai ya binciko hibban tunda ya ɗau alwashin hakan🐒😉😂._*


_Please kuyi manage da ga nan har Monday na ƙara samun sauƙi😭🙏🏻_






*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

           

    



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*


*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*


_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_


*_Muna da haɗin_*


_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_


_Muna Gyaran jiki_

_Na amare_

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_


_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_


_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_


_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_


_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*


_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_


_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_


••••••••••••••••••••••••••••••••


*_Chapter Fifteen_*


.........Kamar yanda doctor Bilal ya faɗa a ranar suka sallami Ummi tare da sharuɗan da za'a kiyaye game da lafiyarta. Su Yaya Abubakar sun amsa masa tare da tabbatarwa. Wannan ɗin ma akasi aka samu kawai. Da ga haka sukai masa godiya suka tafi da sanyin idaniyarsu gida.

        Koda suka isa gidan babu wanda yayma Ummi zancen Abbah, hasalima su sun manta ma. Hidimarsu suka cigaba da yi hankali kwance har dare. Sai da zasu kwanta ne Ummi taji shirun gidan yayi yawa take tambayar Hibbah data maƙale a ɗakinta zata kwana. Bargo Hibbah taja har saman kanta tana sake bajewa a gadon na Ummi. “Ummi nima ban saniba. Ƙila sunje ƙauye ne”.

     Shiru Ummi tai tana nazari, tasan Momy ko kowa zaije ƙauye ita dai bazataje ba. Hakama ƴammatan ƴaƴanta. Hajiya Mama da Abban ne kawai suke zuwa, suma idan aikin sharrinsu ya tsikaresu, kuma Abba ma ai bai jima da dawowa ba. Ajiyar zuciya ta sauke da kauda zancen a ranta itama ta kwanta tare da kai hannu ta janye bargon da Hibbah tasa har saman kai.

      Duk yanda Ummi taso yin barci gagararta yayi, sai ma dulmiyawa da tai a ƙololuwar duniyar tunani da neman mafita. Taja tsahon lokaci tana ƙullawa da kwancewa kafin ta sami mafitar da take addu'a da fatan ta zame musu alkairi ita da zuri'arta.


          Da asuba bayan sun idar da salla Ummi ta dakatar da Hibbah da ga barcin da take ƙoƙarin komawa gado tayi. Cike da shagwaɓa ta lafe a jikin Ummin tana faɗin, “Wayyo Ummi ALLAH barci nakeji, kinga yau weekend ne babu makaranta sai islamiyya, su Yaya bazasuje aiki ba na san suma barcin zasuyi”.

           Murmushi kawai Ummin tayi, zuciyarta najin tausayin autar ta bisa hukuncin data yanke akan lamarin duk ƴaƴanta a daren jiya. “Muhibbat!”.

    Ta kirayi sunan Hibbah dake lumshe idanu babu wasa. Idanu Hibbah ta buɗe tana kallon Ummin, dan yanda ta kirata da cikakken sunanta babu wasa tasan ƙwarai magana ce mai muhimmanci.

     “Na'am Ummi”.

“Tambayarki zanyi?”.

“To Ummi, ALLAH yasa na sani”.

     Numfashi Ummi taja da kafe Hibbah da ido. “Duka yayunki babu mai neman aure ne dama?”.

    Ɗan jimm Hibbah tai alamar nazari. Kafin tace, “Ummi wai kina nufin sunada ƴammata?”.

      Kai Ummi ta jinjina mata kawai.

Hibbah ta ƙyalƙyale da dariya tana kwantawa ta ɗaura kanta a cinyar Ummi. “Uhm ai Ummi fa dama tun kwanaki nakeson na baki labari Yaya Umar ya gargaɗeni. Wai so suke suyi miki surprise ne. Kinga Yaya Muhammad yana da budurwa, Maimunatu (Kausar) ɗin gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra'uff Maina abokin Daddyn mu, mai islamiyyarmu kuma ɗiyar kawarki.......”

      Wani irin farin ciki da sanyi ne ya lulluɓe zuciyar Ummi lokaci guda. Ta katse Hibba cike da zumuɗi. “Da gaske Tanee?”.

       “Wlhy kuwa Ummi. Kin dai santa babu ruwanta ga hankali, kina zuwa gidansu, suna zuwa nan gidan kinsan tarbiyyarsu. Gata malama a Islamiyyar tamu. Akwai wani dabino da zam-zam da zuma da Yaya Muhammad ya kawo miki kwanaki na rantse itace ta bada a baki. Amma yace idan na faɗa sai ya fasan baki.”

      Yanda Hibbah ta ƙare maganarne ya saka Ummi ƙyalƙyalewa da dariya. “Kai Mamana har yanzu dai ke sakara ce ALLAH, basai ki gayamin a sirri ba. Sam baki biyo mai sunanki ba. To Abubakar fa?”.

          Cikin dariyar zancen Ummi Hibbah tace, “Tab na Zahidah kenan.”

     “Wannan Zahidah ta gidan Auntyn ku Kulu dai dana sani?”.

     “Eh wlhy Ummi. Amma yace karsu faɗama kowa sai ta gama makaranta. Nima basusan na ganeba a ɓoye sukeyi”.

     Nanma dariyar farin ciki ce ta bayyana akan fuskar Ummi. Har ranta zaɓin Yaya Abubakar da na Yaya Muhammad sun mata hundred percent. Hibbah ta cigaba da faɗin, “Shi kuma Yaya Umar Nafisa ce nasan kin sani dama. Yaya Usman kuma Hafsat itama kin sani. Zakin ki kuma babu kasuwa har yanzun”.

     Sosai Ummi taji matuƙar daɗi, dukkan damuwarta sai ta gushe a lokaci guda. Taji ƙwarin gwiwa bisa ga abinda take shiryawa. Dukkan fargabarta ta gushe. A ɓangaren muhalli bata da matsala da yaranta, duk gine-ginensu sai dai ƙarashe. Dan suna fara aiki suka haɗa hannu wajen fara ginin filin da taketa tattali da kaffa-kaffa domin su. Burinta ita da mahaifinsu yanda suka tashi kansu a haɗe su cigaba da rayuwa a waje guda. Shiyyasa koda ya sai filin sai ya damƙashi hannun amininsa kuma malaminsa har sai da suka fara aiki ya basu. Shiyyasa har yanzu Abba da Hajiya Mama basusan da zancen ginin ba........

          “Ummi inje in kwanta?”.

Hibbah ta katse mata tunani. Shafa kanta Ummi tai tana murmushi. “A'a ban gama da ke ba. Dan banji ita autata tana da saurayi ba ko a'a?”.

       Da sauri Hibbah ta ɓoye kanta tana dariya. “Kai Ummi ni banda wani saurayi. Nifa bazanyi aure ba muna tare mutu karaba”.

       “Tab, to auta an taɓa haka kuwa. Muma ai munason zaman gidanmu aka ɗakkomu aka kawo mu naku gidan muka haifeku.” Ummi ta faɗa tana dariya.

       “Ni dai bazanyiba ALLAH Ummi. Banason nesa da ke da su Yaya. Indai zanyi aure sai dai mutafi tare ko mijin yazo ya zauna a gidanmu to”.

       Dariya sosai Ummi keyi, irin wadda ta jima batayi ba a rayuwarta. Tanee ɗinta kayan shirme da wauta kenan. Da ana haka da ƴaƴa da yawa na tare da iyayensu ai.

       Tashi Hibbah tai da gudu ta haye gadon Ummi ta kudundune a bargo ita a dole kunya ta kama ta. Ummi da ke dariya tace, “To shikenan ai ke baki da matsala tunda Junaid ɗan gidan nan ne sai kiyi zamanki tare dam......”

        “ALLAH Ummi bana sonsa. Da na auri mugun nan gara na mutu”. Hibbah tai saurin yaye bargon idanunta na cikowa da hawaye. Yayinda fuskarta ke nuna tsananin tsoro da tsanar Junaid ɗin da Ummi ta ambata.

        “To shikenan naji. Amma ai kina son Isma'il ko?”.

       Idanu Hibbah ta zaro waje a firgice. “Wane Isma'il ɗin Ummi?”.

       “Mai zuwa nan gidan mana”.

   “Ni dai wlhy a'a Ummi. Shi yayana ne dan ALLAH kibar faɗa.”

         “Oh ALLAH, ke kuwa Tanee wa kike so a rayuwarki? To ko wanda yazo dubani a asibiti jiya? Muhammad Shuraim ko?”.

      Baki Hibbah ta turo amma batace komai ba. Ummi ta cigaba da faɗin, “Tanee kinga shima alamunsa sun nuna mutumin kirki ne nutsatstse. Ina ƙyautata masa zaton alkairi insha ALLAH. Amma zansa ai bincike a kansa inhar kina son nasa”.

          Kwanciya Hibbah tai ta juyama Ummi baya. “Ni Ummi ALLAH ya cika iyayi. Gashi baida fara'a. ga shishshigi ”.

        “Duk shi kaɗai?. To lallai tunda kika iya gano waɗan nan kina sonsa kenan, zaki kuma auresa”.

       Da sauri Hibbah taja bargo da cewa, “Nifa Ummi a'a baiminba. Sai naje China na dawo zanyi aure”.

      “Tanee wannan mafarkinki ne. Amma ban fidda miki ran zaki cikashi ba idan kinyi aure mijinki ya kaiki da kansa”.

         Shiru Hibbah tayi dan an taɓo mata inda kuma bata son. Itama Ummi sai bata sake tankawa ba ta cigaba da hidimarta da lissafin ƙullawa da kwancewa.


       Zuwa takwas Ammar ya shigo ya tada Hibbah dansu haɗa breakfast su wuce islamiyya duk da sunyi latti. Hibbah kamar zatai kuka ta bisa. koda sukaje kitchen ɗin suna aikin suna faɗa har sai da Yaya Abubakar ya shigo ya tsawatar musu saboda kuka da Ammar ya saka Hibbah.

     Suna kammalawa sukai shirin islamiyya. karyawar ma a tsaitsaye sukayita suka fice.


      ★★★

   

   A yinin ranar su Yaya Muhammad duk a gida sukayisa. Suna tare da Umminsu suna shan hira. Basu sake mata maganar tarinta ba, itama batai musu ba. Sai bayan sallar zuhur suma suka wuce islamiyya. Ganin dai har zuwa yamma babu motsin Abbah da su Hajiya Mama yasa Ummi fita wajen maigadi ta tambayesa ko sunyi tafiya ne.

        Baiyi mamaki ba. Dan yasan kaf yaranta a fusace suke da Abban. Bayanin faɗuwar Abban ya bata da kaisa asibiti da akai. Kuma har yau babu wanda ya shigo gidan tun jiyan. Duk da abinda suke mata bataji tayi farin ciki da tsautsayin daya afkawa Abban ba. Sai ma komawa tai falonta ta faɗa duniyar tunani........


_________________________________


      A ɓangaren Abba ba ƙaramar jigata yay ba kafin safiya. Ƙafafu sun kumbura suntum. hakama fuskarsa tamkar ƙwaɓun fulawar sabon burodi. Sauƙinsa ma allurar barci da likitocin sukai masa ganin yanda yake rusar kuka ƙafarsa na masa zogi.

       Sai kusan huɗu na maraice mai gyaran yazo, a cewarsa sun sami lalacewar motane a hanya. Sai dai kuma a zahirin gaskiya ƙaryama yake bai taho ba sai da safen. Komai likitocin basu ce ba. Sai ma damar yaje yay aikinsa da suka bashi, dan haka suka basu sallama.

      

      Ummi na tsaka da tunaninta taji shigowar motoci, mikewa tai ta leƙa ta windown falonta sai ta hango ana fita da Abbah da ga motar Junaid tamkar gawa. Wani irin faɗuwa gabanta yay. Babu shiri ta fito zuwa tsakar gidan itama. Kusan tare suka shiga sashen Momy da su Hajiya mama da ke biye da mai-gyara da Junaid da suka ɗakko Abba ranga-ranga.

         A tsakkiyar falon momy aka shimfiɗe Abba. Sai dai ganin yana numfashi yasa Ummi batace komaiba tabi layin ƴan kallo. Mai-gyara ya fito da kayan aikinsa. sanin abinda zaije ya dawo ya sashi faɗama Junaid cewar ya samo wanda zasu tayasa riƙe Abba dan shi kaɗai bazai iyaba. Badan Junaid yaso ba ya mike ya fita. Babu jimawa sai gashi tare da mai-gadinsu da na maƙwafta. Sai wasu yaran makwaftansu su biyu sa'annin Ammar.

         “Yauwa kayi farar dabara da kukazo da yawan”. Cewar mai gyara yana gyara zamansa sosai a gaban kafafun Abba da sukai suntum har ƙyalli sukeyi.

        Junaid da mutanen daya gayyato baki ɗaya suka zagaye Abba mai-gyara ya fara aikinsa. Sai dai abin mamaki duk da barcin da Abba keyi ana taɓa ƙafar yay wata iriyar mahaukaciyar zabura da ballara ihu. “Wayyyyyyyoooooo!!!!!! ALLAH na zasu kasheni na shiga uku ni Halilu!!!”.

      Babu wanda ihun Abba bai gigita ba a falon. amma ahaka mai-gyara ya cigaba da aikinsa ko tausayi babu. Ihu Abbah yake da iya ƙarfin iko. Tun yana zufa har takai ga sakin fitsari. Can fa abin mamaki da kunya sai ga kashi.

      Hanci su Ameerah suka shiga toshewa. Su kansu masu riƙon nashi ji suke kamar su sakesa su gudu dan azabar warin kashin. Suma kuwa yayi ya farfaɗo yafi sau uku. Tun yana ihu da murya mai kauri har ya koma siririya. Daga baya ma akabar jinta gaba ɗaya.

       Duk yanda Ummi taso daurewa sai da taji hawaye sun ciko mata idanu. Tai ƙasa da kanta saboda tausayi.


       A cikin wannan halin su Hibbah suka fara dawowa gidan. Ihun Abba ne ya ringa jan hankalinsu suka dinga nufo sashen duk da sun manta shekarar karshe da suka shiga sashen. Su kansu tsoro ya kamasu ganin yanda Abban ya koma. Badan sun so ba dole suka dinga toshe hancuna suma saboda wari.

     Mai gyara ya ɗora kafa da hannun Abba. Sauran raunikan ma aka gyara. Ya shafa magani ya bada wanda za'a cigaba da masa amfani da shi. Kafin a cake masa ƴan kuɗaɗensa masu nauyi. Aka kuma kaisa masauki dan yace sai da safe zai wuce yamma tayi.

          Sai lokacin Hajiya Mama ta farga da su Ummi da yaranta. Ido ɗaya ta kanne ta shiga zazzaga bala'i wai sunzo ganin ƙwaƙwaf. Cikin subutar baki Hibbah taja wani wawan tsaki da faɗin, “Kaɗan ma ya gani. Ummin mu yaso gani a wanann kwatankwacin bala'in sai shi ALLAH ya tsundumasa. In takamarsa zalunci wataran ƙafar za'a guntule.....”

     Wata muguwar cafka Hajiya mama ta kaima Hibbah ta ko kwasa a guje tabar sashen. Zata bita Junaid ya riƙota cikin masifa. “Barta kakus. Nine nan zanci uban uwarta, wancan bakin nata mai kama da na reza yau sai na ɓaɓɓarkasa wlhy. Shegiyar yarinya mai bakin akku. Idanma an sakata tazo ta faɗa ne to ina dai-dai da kowane shege a gidan nan. Wama ya sani ko kada mana shi akaiyi. Kai bama zan yardaba ALLAH sai munje kotu”.

        Tsaki Ammar yaja tare da kama hannun Ummi suka fice. Su Yaya Muhammad ma kai kawai suka girgiza sukai gaba abinsu da barin su Hajiya mama da takaici. Dan so sukai su tanka su kwashe komai sukai wajen ƴan sanda. Daga nan a wuce kotu har ALLAH yasa sukai gaɓar da suke fata. To sai akai rashin sa'a yaran Ummi masu lurane suka manna musu hauka.

      Koda suka koma sashensu basuga Hibbah ba. Sun san ta boye kanta a daki ne saboda tasan tayo laifi, tunda suma suna hanata rashin kunyar. Alwala ma duk sukayi suka fice masallaci. Ummi ma ta nufi ɗakinta gabatar da tata duk da tana jiyo hayaniyar su hajiya mama daketa zage-zage har yanzun.

       Koda suka dawo bayan sallar isha'i Hibbah bata yarda ta fitoba har suka ci abinci sukai hira kowa ya tafi makwanci. Babu kuma wanda ya nemeta dan a tabbatar mata batai dai-daiba.


      Tun a daren maƙwafta ke shigowa duba Abba dan sunji ihun da yayta zugawa. Duk wanda ya shigo sai su hajiya mama suce yaran Ummi ne suka jima Abban ciwo. Da yawa ba yarda suke ba, saboda sunsan halin matsi da Ummi ke fuskanta a gidan da yaranta tun suna kanana. Dan tunkan ma Hajiya mama ta dawo gidan da zama idan tazo da ga ƙauye haka zataita zubda tujara wa Ummi kala-kala, tunda kuwa mijinta ya rasu ta dawo da zama baki ɗaya sai Ummi ta shiga uku ta lalace itada ƴaƴan ta, gashi nan har yanzu basu huta ba.


  *_______________________________*


               Shiru kakejin Master da yaransa tamkar basa ƙasar. Babu kalar takalar da jami'an tsaro basu masa ba a kafafen ƴaɗa labarai yay kunnen uwar shegu da kowa. Ko randa zancen kai matar gwamna koto ya fito da ga hukumar yaƙi da ta'annatin kayan gwamnati babu wanda yaji ko tarin master. Shi dama ba sanin taka mai-mai accaunt na duka handles nashi akai ba. Dan kullum cikin canja salo yake.

        Sun cigaba da saka idon ganin kozai tanka amma shiru, dan haka suka cigaba da shirya masa tarkuna ta ƙarƙashin ƙasa dan sunsan tabbas zaije kotun.


    ★★


      Yau da yamma Hibbah na makaranta ta fito class cike da gajiya da yunwa. Fatanta kawai ta samu motar komawa gida da wuri dan su Hafsat tuni sun wuce saboda ba department nasu ɗaya ba. Su kuma yau duk lecture ɗin safe sukayi. Ita kaɗaice tayi na yamma.

          Ta samu da yawan ɗalibai dake ta tutsutsun shiga motar da duk tazo wucewa. Dan haka tai gaba saboda kanta dake ciwo. Cikin sa'a kuwa tana matsawa gaban sai ga wata taxi ta faka gabanta. Batare da tunanin komaiba ta afka ciki bayan ta sanarma direban inda zai kaita, shi kuma ya faɗa mata kuɗin. Ko ragi bata nema ba dan buƙatarta kawai taje gidan da wuri. Saboda tana tsoron abinda zaije ya dawo ne musamman akan dangin Abbansu dake cike da gidan nasu dubiyar Abba. Dan zuwa yau da yake cika kwana uku jikin nasa da sauƙi.

      Ƴan can asalin kauyensu ne sukazo mota guda duba shi. Sai dai hakan ya bama Ummi mamaki da su kansu, dan sam da ga Abba har hajiya mama bason mu'amula da ƴan ƙauyen sukeba yanzun. Shiyyasa har ƙasan ranta takejin akwai wata a ƙasa da suke ƙullawa.

        Wasu hawayen tausayin Ummi da su kansu ya cika mata ido. bayan hannu tasa ta share tare da kwantar da kanta jikin sit ɗin ta lumshe idanu ko kanta zai sassauta sara mata.......


         Ummi nacan na dakon jiran dawowar Hibbah itama, dan yau da kanta ta soyama Hibbar wainar filawa da tasan tana matuƙar so. Yayinda can ƙasan ranta ke cike da fargabar taruwar dangin mijin nata da nata a gidan. Dan tasan akwai abinda suke ƙullawar da gaske. Sai dai kuma ta saka a ranta komi zasu ƙulla insha ALLAHU ta gama shirya musu a wannan karon. dan itama tun a jiya data fita ta gama tsara komai akan makomar ƴaƴanta. Nasu kawai take jira yanzu ta ɗora da ga inda ta tsaya. 


        Ilai kuwa hasashen Ummi yayi dai-dai, dan tana tsaka da wannan tunanin akai kiranta sashen Abba ɗin. Hijjab ta saka har ƙasa ta tafi. Tun a falo Maomy ta sakar mata wani habaicin da ya tsaya mata a rai. Sai dai batace komai ba ta ƙarasa falon Abba.

        Su kawu Bello ta samu da wasu a dangin Abban. Sai hajiya mama. Bayan ta gaishesu ta nema waje ta zauna duk da ba dukansu suka amsa ba. 

            A gadarance Kawu Ayuba ya fara bayani. “Hasiya basai mun sake ɓata lokacin tisa magana ba. Nasan kema tunda kika ganmu anan kinsan zancen. Kamar yanda su Yaya Ballo sukazo kwanaki akan maganar auren ƴaƴanki da yaran wajen Alhaji Halilu yanzu batun saka rana ne ya tashi. Saboda tsabar halacci da hangen nesa irin nasa yace kawai tunda munzo dubasa a saka. Shi baya wani bukatar ƴan kunji-kunji tunda batun tuwona maina akeyi. To a yanzu haka dai ga kayan saka rana nan ma duk ya saya dan yace shine uban anguna shine na amare, kuma koma bai faɗa ba dama shine, tunda tun suna kananunsu shiketa wahala akansu. Koda kuwa mahaifinsu na raye shine mai bada auren nasu ai dama. Basai na jaki da nisa ba. Yanzu haka dai an yanke ranar aure wata biyu kacal. Batun kayan aure na akwati da kukeyi anan binni duk yace zaiyi baya buƙatar komai da ga yaran nan. Ita kuma Muhibbatu tunda kun saka yarinya ta nuna bata bukatar wannan haɗin, da azo ta bijire bayan auren kota illata yaro kawai za'a fasa. Za'a bata shi wanda ta kawo ɗin ALLAH ya basu zaman lafiya.....”

      A firgice Ummi ta dago ta dubi Abba. Wani shegen murmushi ya sakar mata tare da kashe mata ido ɗaya. Zatai magana yay saurin katseta cikin marairaicewa. “Hakan ai shine yafi kwanciyar hankali Kawu Ayuba. Kaga da alalata zuminci gara dai abi komai a sannu zaifi. Kuma ita mace ce. Banason a cuta mata akan abinda bataso. Dan yarinyace mai hankali da nutsuwa. Duk da damuwar da Junaid ɗin ya shiga nace ya haƙura kawai tunda tana da zaɓinta. Kuma zaɓin nata ma naga mutumin kirkine sunansa Muhammad Shuraim. Ɗan gidan Alhaji Aliyu ne mutumin kirki. Inajin kunyar ma nace bazan bashi jinina ba”.

        Harga ALLAH Ummi ta shiga ruɗani, ta kuma ji ɗan sanyi ta wani fannin. Dan tana mamakin ta yaya shi Abban yasan da zancen zuwan Iyayen Muhammad Shuraim ɗin? Kodai su masu kawo kuɗinne sukai mistake ɗin zuwa nan kawo kuɗin maimakon gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina? Lallai akwai abinda bata sani ba. Dan akwai manufa da dalilin yin hakan ga Abba, saboda halin makircinsa da ta sani. Hakanan salin alin bazai hana ɗansa ba ya bama wani.........

          “Wannan shaiɗancin dai nasan ita ta kitsashi. Duka yarinyar nawa take da tasan wani bijirema zaɓin iyaye. Ni wlhy dan Halilun yace a barta ne da baza'a bari ba. Sai dai idan an aura mata Junaidun ta mutu”. Sababin Kawu Bello ya katse ma Ummi tunaninta.

      Cikin makirci Abba ya amshe da faɗin, “A'a kawu bello ba'ayi hakaba ai. shima wnanan ɗin mutumin kirki ne wlhy. Dan yamafi Junaid nagarta. Muyi fatan ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”.

     A take duk ƴan falon suka shiga yabon Abbah da jinjinama ƙoƙarin sa, Ummi kam anata zaginta wai bata da godiyar ALLAH akan ƙoƙarin da Abban keyi tun bayan rasuwar mahaifin su Ammar. Tare da yi mata gugar zana na habaicin asalinta.

     Ita dai uffan batace da su ba. Hasalima hankalinta ya rabune gida biyu. Duk sauran bayanan da suka cigaba dayi sai tama koma bata fahimtar komai. Jinsu kawai dai take da kunne da binsu da ido har aka tashi a taron ko nace suka sallameta.


       Koda ta fito a sashen taso zuwa gidan malam sai dai gudun abinda zaije ya dawo da fitar tata yasa ta haƙura. Dan haka tai kiran numbar wayar matarsa da yake ƙawarta ce suna zuminci sosai duka biyun. Sai dai tasan uwargidan Maimunatu yanzu haka tana Oman da autan gidan dake karatu acan.

     Bugu biyu Malama Jiddah ta ɗauka. Bayan sun gaisa da ɗan barkwancin ƙawaye Ummi take tambayarta ko Malam na nan kuwa?.

        Malama Jiddah tace, “Eh yana nan, sai dai yana tare da kamar baƙin da naji kunyi magana ranar zasuzo yau ɗin. Lafiya dai ko?”.

        “Tofa, kaji wani kuma ruɗanin. Umm Muhammad! Lafiya dai ba lafiya ba. Akan baƙin dama na kirasa ban samu ba......” (Komai Ummi ta zayyane mata da ya faru yanzun anan gidansu).

         “Bara muga baƙin su wuce to sai na sanar masa. Duk da dai inaji a raina ko duk shine ya tsara hakan dan mijin nan naki sai da siyasa ake iya kamasa a hannu. Ya riga ya zama mai fuska biyu inba ka saniba babu mai cewa zai iya sheɗancin da yake zubawa shi da uwarsa Umm Abubakar. Amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ALLAH yana tare damu”.

        “Shikenan Umm Muhammad ALLAH yay mana jagora. A gaishe da yaran sai na jiki”.

     Sallama sukai da ga haka zuciyar Ummi fal waswasi da saƙe-saƙe.


*__________________*


             Ido Hibbah ta buɗe a ɗan yanayin razana saboda barcin da ya figeta. Gabanta ya faɗi lokacin da idanunta ke kaiwa waje ta windown motar da aka sauke gilashi baki ɗaya. Mazaunin direban ta kalla tana haɗiyar yawu da ƙarfi saboda bushewar da maƙoshinta yayi lokaci guda. Tai saurin ɓalle murfin motar ta fito domin tabbatar ma kanta inda ya kawotan fa ba anguwarsu bane...............✍



*_Tofa. Ina mai taxi ya kai Hibbah?. Wane ruɗanine ya shiga kan Ummi game da kawo kuɗin auren Hibbah da ga gidan su Shuraim? da alama ta nuna tasan da zancen. Shin malam Aliyu Abdul-Ra'uff Maina ne ya fara aika iyayen Shuraim ga Abba kokuwa yaya abin yake ne? Wane shiri Ummi keyi akan yaranta da takejin ƙarfin gwiwar nasarar kubutar dasu ne haka? Minene shirin Abba shima game da fasa bama Junaid ɗansa auren Hibbah ya yarda ya bama Muhammad Shuraim? Shin kodai dama shine ya turosa batare da ita Ummin ta farga ba?. 🤔tambayoyinfa da yawa. Yayinda ni kaina amsarsu nake nema🚶🏻😩._*


________________________


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*




*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_Chapter Sixteen_*


.........Da sauri ta dafe kanta da ya sara mata da ƙarfi. Cikin ɗacin murya da zafin da takeji a zuciyarta tace, “Wai nikam mina muku ne na laifi? Dan ALLAH kubar rayuwata ta cigaba da tafiya a yanda take karku sakamin ahali a masifa. Wancan karon kunce dan na bibiyi wanine. Wannan karon kuma mina aikata zaku kawoni nan?”.

            “Duk bani da amsoshin tambayoyin nan naki. Aikina kawai shine ɗakkoki na kawoki nan wajen. Gashi kuma na cika. Amma idan muka shiga da ga ciki harma abinda baki tambaya ba za'a baki amsarsa na sani”.

          A fusace Hibbah ta dubesa zatai magana aka katseta......

      “Gaskiya ya faɗa miki, bashi da amsar da zai baki. Dan haka bismilla ɗiya ta”. Dattijon wancan karon da aka kaita office ɗinsa ya faɗa dai-dai yana ƙarasowa inda suke. Dan tun shigowar taxi ɗin cikin station ɗin yake kallonsu ta window. A fahimtar da yay mata na tsiwa da rashin tsoro da kafiya ya sashi yanke shawarar sakkowa da kansa ƙila tafi jin shakkarsa ta shiga.

     Sai dai kuma ina. Shima a fusace ta kallesa wasu hawaye masu zafi suna sakko mata. Ganin tana motsa  laɓɓanta alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. “Nan ba muhallin da ya dace ki cigaba da cewa komai bane ɗiyata. Ina mai tabbatar miki wannan kiran yasha ban-ban dana farko. Dan kai tsaye ke zai taimaka bamuba Muhibbat. Bakomai yasa nace hakaba sai ƴan uwanki dake gab da shiga haɗari”.

       “Ƴan uwa na?!”. 

Hibbah ta faɗa ƙirjinta na wani harbawa. Uffan jami'in dattijo A.G baice ba ya juya zuwa office ɗinsa. Da sauri tabi bayansa har tana haɗawa da ɗan gudu. Dan ba ƙaramin hargitsa tunaninta maganarsa ta ƙarshe tayi ba. Duk da yanajin tana binsa da gudu bai tsaya ba sai da ya isa har office ɗinsa. Kusan a tare suka shiga da Hibbah. Tai saurin zuwa gabansa ta durƙusa.

       “Uncle dan ALLAH karku cutarmin da ƴan uwa. Ku daina tursasani yi muku abu ta hanyar yimin barazana da su. Kunsan kuwa mi kuka nema haddasama rayuwata a wancan karon? Saura kaɗan na rasa Ummi na, gatana ni da yayuna. Farin cikinmu madubin rayuwarmu. Miyasa kuke son saka alkairi da sharri? Miyasa kuke son yin amfani da ni saboda ku haskaka kanku ma duniya? Miyasa ku ke........”

        “Ya isa ɗiyata. Duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba a wannan gaɓar. Yanda kiɗan ya sauya itama rawar zata sauya ne dole. Inason ki nutsu ki bani dukkan hankalinki nan, domin haɗa hannu wajen tabbatar ma mutanenmu abinda suke ganin bazai yuwu ba saboda rauni da ƙarancin shekaru da suke kallo kai tsaye”.

       “Ni bazan nutsu ba, bazan taɓa nutsuwa ba dan ku taurarine masu wutsiya. Dan ALLAH ku daina saka rayuwata data ahalina cikin *_TAKUN SAƘAR KU_* da bawan ALLAHn nan. Bani da alaƙa da komai nasa kamar yanda kuma bani da alaƙa da ku. Indai harkar computer ce na barta har abada duk da kuwa itace burina, itace mafarki na, itace zummata, itace kaifina. Amma saboda cigaba da rayuwar ahalina cikin salama na tattarata na ajiye. Na manta kaina cikin waɗanda suka iya koda kunnata. Please na roƙeku ku barmin rayuwa data ahali su huta. Ku barni naji da damuwar cikin gidanmu ita kaɗai ta isheni”.

      Yanda ta haɗe hannaye tana roƙonsa hawaye na kwarara a kumatunta duk sai tausayinta mai tsanani ya kamashi. Idanunsa suka kaɗa sukai jajur. Kansa ya shiga girgiza mata yana ƙoƙarin kamo hannayenta dake haɗe har yanzu waje guda alamar rokonsa🙏🏻. Sai dai yana kawo hannu ita tai azamar jan nata baya.

        Da sauri yace, “Shike nan naji zan barki ki tafi. Amma ki tabbatar Tabbas kinada alaƙa da Master Muhibbat, saboda wannnan ɗin kasarki ce, kuma a ƙasar taki yake aikata dukkan ɓarnarsa. Sannan rayuwar yayunki da mamanki na cikin haɗari a hannun ƙanin mahaifinku da shi wanda kike ganin baki da alaƙar komi da shi. 1Mu kaɗai ne kawai kuma zamu iya cetosu tare da ke kanki. Zakuma muyi hakanne kawai idan kin amince kin yarda zaki cigaba da mana aiki akan mutumin nan Master. Idan kuma bazakiyi ba zaki iya tafiya kawai”.

       Shiru Hibbah tai tana kallonsa. Kallo mai cike da ma'anoni da yawa da ita kanta ko ca'akai ta fassarasu bazata iya ba. Kansa ya jinjina mata alamar tabbatarwa.

      Sosai zuciyar Hibbah ke ƙara wani irin lugude, babu abinda ke mata kai kawo a zuciya sai batun auren yayunta da ƴaƴan Abba. Dama har cikin ranta tanaji akwai manufa, amma batasan miyasa Ummi ta amince ba bayan kuma ta sanar mata yayun nata nada waɗanda suke so. Wani tunani da yazo mata daban a cikin rai ya sakata kai hannu kawai taja kujera ta zauna tana share hawayenta da suka kasa tsayawa. Shima sai ya sauke ajiyar zuciya da takawa wajen kujerar zamansa ta office ɗin ya zauna yana fiskantarta.

          “Miyasa sai ni kaɗai ce zan muku aikin? Bayan nasan akwai mutane da yawa masana kuma jajirtattu akan wannan harkar, waɗanda idan a gabansu nake ni ɗin bakomai bace, bansan kuma komaiba?”.

           “Tunani mai ƙyau Muhibbat. Tambayarki na da matuƙar muhummanci kuma ta birgeni. Har cikin raina na sake yarda zaki iya domin kina da kaifin ƙwaƙwalwa. Kafin kiyi mana wancan aikin tunanina irin nasune, ina kallon raunin mace matuƙa nima. Ko a cikin hukumar nan aka bama mace aiki raina kan ɓaci naga babu abinda zata iya. Amma sai ke kika ruguza dukan wannan tunanin nawa a waccan ranar, dan kinyi abinda ƙwararru da yawa suka kasa matsayinki na mace mai ƙarancin shekaru kuma ɗaliba da iya ƙasarta kawai ta samu ilimin kimiya da fasaha. Na zauna nayi dogon nazarin da yasa na fahimci irinku ba'a sakaci da al'amarinku, dan da irinku ƙasashen turawa suka cigaba a nasu ƙasashen da suke birgemu a yau. Muhibbat na miki alƙawarin wannan aikin ƙashin kanki zakiyi. wanda dole duniya tasan da zamanki bayan kammaluwar komai insha ALLAHU. Inason barinma bayana alkairi bayan na ajiye aiki, kuma kece wanan alkairin da nake fatan bari insha ALLAH. Da kuma wanan damar zakiyi amfani kema wajen ceto ahalinki da sake darajasu cikinƴan uwanku, ki wanke baƙin fentin da ƙanin mahaifinku da kakarku sukai muku wanka da shi. Da wanan damar zaki canja masu irin tunanina game da ɗiya mace”

               Murmushi Hibbah ta saki wanda ita kaɗai tasan ma'anar kayanta. Ta ɗan muskuta zamanta da faɗin, “Na amince zan muku aiki, sai dai ku sani hakan ba yana nufin idan baku sami nasarar kamashi ba zan cigaba da dawowa nan wajen. Zan muku abinda kuke buƙata ko ba'a sami nasara ba nima zaku kuɓutarmin da ahalina”.

         “Tabbas mun amince, harma da wata gagarumar ƙyauta da zaki samu inhar yazo hannun namu.”

          “Yallaɓai na bar muku ƙyautar basai kun bani ba. abinda kawai nakeso shine ranar auren yayuna ana gab da halartar ɗaurin aure ku kama Abba ku ɓoye min har sai an kammala ɗaura auren yayuna da matan da suke so da kwanaki biyu. Abu na ƙarshe kuma inason amin cikakken bincike akan Muhammad Shuraim da Abba ya iya hana ɗansa ya yarda na auresa duk da zaɓin Ummi na ne shi”.

       “Duk mun amince da sharaɗinki”.

Murmushi Hibbah ta saki a karo na biyu. “Inhar ya kasance Muhammad Shuraim bashi da wani aibu a rayuwarsa zan auresa na rayu da shi matsayin miji kodan son da Ummi na da Yayuna ke masa. Zanbi duk hanyar da zanbi na ganin ya ɗaukeni zuwa ƙasar China yin karatuna akan ilimin kimiya da fasaha. Ni kuma a wannan lokacin zan muku aiki. Ko wanene wanan master ɗin nayi alkawarin insha ALLAH sai na zama sanadin da zaku kamashi a tafin hannunku. Dan haka na baku dama kafin kwanakin aurenmu 60 da aka saka nasan wanene Muhammad Shuraim ciki da bai. A samama ahalina waje na musamman da zasu rayu a lokacin da zan fara farautar MASTER. Dan ko ƙwarzane bana son ya samu koda farcinan hannunsu”.

           Wani irin tattausan murmushi dattijo A.G ya saki, yayma Hibbah jinjina. “Tun a ranar farko da kikazo nan na tabbatar zaki iya a cikin idanunki, tabbas zaki iya. Kuma insha ALLAH dukkanin bukatunki zasu biya Muhibbat, daga ƙarshe ƙyautar dana ambata zata kasance biya miki kuɗaɗen tafiya ƙasar China ko wata ƙasa daban yin karatunki. Abinda kawai zakiyi shine neman yardar mijinki”.

          A take wani irin farin ciki ya baibaye Hibbah. Ta ɗaga hannu tana addu'ar godiya ga UBANGIJI da fatan nasara akan alƙawarinta.

      Shiko dattijo A.G na tayata da amin. Sai da ta sauke hannayenta sannan ya tura mata takarda da pen.

     Ki rubutamin dukkan sunayen ƴan gidanku da duk wanda kike tunanin kawo tangarɗa akan auren yayunki anan”.

         Takardar ta jawo gabanta tana wani irin dariyar ƙeta. Dan babu wanda take hangowa a idanunta sai Hajiya Mama da su Kawu Hannafi. Bayan ta gama zana masa ya bata wata bag dake ɗauke da tarin files da suka shafi Master. Ya ɗora da gargaɗinta akan muhimmancin riƙe musu sirrinsu.

          “Dukkan abinda zaki buƙata da ya shafesa na tanadar miki anan, dole ne sai kin fara shiga kansa, kinyi irin tunaninsa. Ke mace ce, kuma ƙaramar yarinya. Inaji a jikina kafin ya ganoki ko ya farga da ke kin kammala aikin nan insha ALLAH. Kisa a ranki ALLAH na tare da ke, kuma duk inda kika shiga akwai jami'an dana tanada zasu dinga bibiyarki ke da ƴan uwanki domin baku kariya.”

       Kai kawai Hibbah ta jinjina masa. Da ga haka ta fito mai taxi ɗin da ya kawota station ɗin ya sake ɗaukarta domin maidata gida.


★★


           Kamar yanda Hibbah tai fata koda ta shigo gidan nasu bata sami kowa a falo ba, yayunta babu wanda ya shigo, Ummi kuma tana ɗakinta. Ɗaki ta wuce ta adana bag ɗin da tazo da ita sannan ta fito ta sanarma Ummi ta dawo.

       Sosai Ummi ke binta da kallon mamaki ganin tanata washe haƙora kamar ba itace ta fita da ɓacin ran zancen aurensu ba. Komai Ummi batace mata ba akan walwalar tata. Sai ma ce mata da tai idan ta gama taje tai mata list na kayan kwalliya da kayan underwears.

        Cike da zumuɗi Hibbah ta fice dan tasan na kayan lefen yayunta ne da za'a haɗa a gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra'uff Maina. A gurgije tai wanka ta kimtsa kanta. Ko abinci bata nema ba duk da yunwa da ciwon kan da ke damunta har yanzun, tai zaman rubuta list ɗin bayan ta kunna wayarta ta shiga WhatsApp ɗinta tana bugar cikin Hafsat da Zahidah akan kalo da sayis ɗinsu.

      Cikin awa ɗaya ta kammala komai ta fito ɗauke da takardar. Kai tsaye ɗakin Ummi takai ta ajiye sannan ta fito wajen yayunta suka cigaba da hira. Su kansu sunyi mamakin ganin yanda taketa faman walwala tamkar yanda suka santa tun fil'azal. Sai dai komai basuce mata ba suma.


*________________________*


      Kwana uku da faruwar haka Muhammad Shuraim yazo gidan su Hibbah a karon farko. Ya sami ƙyaƙyƙyawar tarba da ga wajen su Yaya Umar, inda aka saukesa ƙaramin falonsu da Dadynsu kan sauke baƙi kafin rasuwarsa.

          Da farko Hibbah catai ita bata gayyatarsa, dan haka bazataje ba. Sai da Ummi tai mata jan ido sanann ta zumbula hijjab ta fita ɗauke da karamin tire da aka ɗora ruwa.

       Tunda ta shigo da sallama ya kafeta da idanunsa manya da ke neman rikitata. Tiren ta ajiye saman Centre table ɗin falon tana harararsa da kumbura fuska.

      “Malam lafiya?”.

Ta faɗa cike da tsiwa.

       Kansa ya ɗan girgiza kawai yana lumshe idanunsa dake a kanta ya sake buɗewa. “Ina tausayin bakin nan naki saboda tsiwansa, amma babu komai lokaci kaɗan ya rage ya daina”.

     Baki ta taɓe da kaiwa zaune cikin kujera tana faɗin, “Karka ɗauka maganin da kaima iyayena suka yarda da kai lokaci guda nima ya cini. Wasu dalilai ne kawai sukasa na yarda da aurenka badan kayi dai-dai da ra'ayin mijin da naima kaina buri ba”.

          “A hakanma na gode. Na kuma sake tabbatar da cewa nazo inda ya dace neman aure. Dan biyayyar da kikai ga iyayenki kawai cikakkiyar amsace akan nagartaciyar tarbiyyar da kika samu da ga garesu mai inganci.”

        “Humm” kawai Hibbah ta faɗa batare da tace komai ba.

      Shuraim ya murmusa batare da ya nuna damuwa da yanayin nata ba. “Kamar yanda na faɗa miki sunana Muhammad Shuraim Aliyu. A garin nan aka haifeni, anan na tashi, anan na girma, anan nai karatun addini dana boko har zuwa secondary. Kafin na ƙetare wajen ƙasar nayo karatun jami'a har zuwa matakin degree na biyu. A yanzu haka ina akan haɗa degree na na uku tare da harkar kasuwanci tamkar yanda na taso na gani anayi a gidan mu. Abinda ban faɗa miki ba bayan wannan kuma na baki damar yin bincike a kaina dan ki sani. Ƙwarai da gaske naji daɗi matuƙa na samunki musamman da ya kasance ban zaci hakan ba. Abinda zance kawai kiyi haƙuri banyi kamar yanda samarin wannan zamanin keyiba na fara shimfiɗa soyayya kafin aure. Ni sam hakan ba ra'ayina bane ba, shiyyasa tun farko ban taɓa zuwa ƙofar gidanku ba kai tsaye sai dai bibiyarki kawai. A randa kuma iyayena sukazo domin neman izinin zuwa zance gunki sai akace anma bani ke, dan ƙa'idarku ku ba'a barinku dama yin zance. Nagode ƙwarai da gaske Muhibbat. Ina fatan zaki amsheni da hannu biyu batare da tunanin nayi miki kutse cikin rayuwarki ba?”.

       Har ga ALLAH kalamansa sun sanyaya ranta. Taji matuƙar kinarsa da girmansa. Sai dai maganarsa ta kusan ƙarshe-ƙarshe akan ba'a barinsu zance ta tsaya mata arai. ta kuma sake tabbatar mata akwai abinda Abba ke ƙullawa game da auren nata da Shuraim, wanda shima da alama baida masaniya akai.

         Numfashi taja tare da duƙar da kanta ƙasa, dan a karon farko taji kunyarsa da nauyinsa ta lulluɓe ta. Cikin sanyin muryar da batasan tana da ita ba tace, “ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”.

      “Amin ya ALLAH”  ya faɗa yana murmushi dan ya fahimci dukkan abin cewar data shigo da shi falon ya gudu.

    Ba wata hira mai tsayi sukai ba, sai ɗan guntun tarihinta itama data bashi sukai sallama ya tafi itama ta shige ciki. Dama ALLAH-ALLAH take ya wuce ta tafi ga aikin da ke gabanta akan files ɗin da dattijon jami'i ya bata (kamar yanda ta raɗa masa suna😂). Dan tun randa ya bata washe gari ta kwashe Computer ɗinta da ga falo ta maida cikin bedroom. Koda Ummi ta tambayeta dalili sai tace babu komai zata ajiyesu ne dan ta daina amfani da su sai nan gaba.

     Ummi ta gamsu da bayaninta ɗari bisa ɗari. Sai dai abinda bata sani ba tuni Hibbah ta haɗa kayan a ɗakinta harma ta fara aiki akan abinda aka sakata. Ta samu bayanai na laifukan da Master ya aikata kashi-kashi, sai flash drive guda uku dake ɗauke da wasu rubuce-rubucensa na yanar gozo, da fuskokin da yake amfani da su. Abinda ta yanke na farko shine zaman yin nazari da kutse na musamman akan facemasks da yake amfani da su. Haka kawai taji a ranta tana son samo ainahin fuskarsa ta ainahi da take kallo a matakin farko na aikinta. Zatayi hakanne ta wasu hanyoyi da take ganin zasu taimaketa duk da ko farcensa baya bari a gani rufesa yake. Sai duka handles ɗinsa na yanar gizo da ya taɓa amfani da su ta hanyar tura saƙo. Da nambobin waya da yay kira dasu masu tsananin tsaro.

     Yanzu gaba ɗaya lokacinta da hankalinta duk sun koma akan binciken Master da ayyukansa. Ta matuƙar maida kanta busy batare da kowa ya sani ba. Sai da safe ne idan Yayunta suka ga idanunta duk a kumbure suyita tambayarta miya hanata barci?. Takance karatune na exam da zasu fara. Tanason ta dage ne saboda shirye-shiryen exam ɗin zai haɗe mata da hidimar biki.

      Duk sun gamsu da bayanin nata, dan haka sukai mata nasiha kawai akan ta ringa sassautawa tana barci dan karta saka kanta a matsala. Insha ALLAH zataci.


★★★★★


          A lokacin da Hibbah keta kaikawo akan ƙoƙarin yin kutse cikin lamarin Master a gidansu shirye-shiryen biki ake tuƙuru ta fanin su Hajiya Mama da Abba da ke faman jiyyar ƙafarsa da hannu. Shiri suke na bikin ƴaƴan gata ta kowanne fanni. Dan hatta da gidajen da su Yaya Muhammad zasu zauna da amare Abba duk ya saka abokinsa ya nema musu haya, ya kuma biya kuɗin hayar da kudinsa acewarsa zai biya na farko daga haka su cigaba da biya.

       Komai dake faruwa Ummi na kallo. Sai dai ta maida kanta makauniyar ƙarfi da yaji bata taɓa nuna alamar tana fahimta ba. Sai ma faman nata shirye-shiryen da takeyi ita da Sheikh Aliyu Maina da iyalansa itama. Dan a yanzu haka ma anata shirin miƙa akwatunan lefen auren su Yaya Muhammad da suka haɗama kansu da kansu zuwa gidan amarensu. Gidansu kuma na gab da kammaluwa sai sam barka da fatan alkairi. 


       *______________________________*


    

          Kwanakin biki sun cigaba da turawa, shirye-shiye na ƙara faɗaɗa a kowanne ɓangare. Sai dai kuma a ɓangaren Hibbah ita hankalinta a tashe yake matuƙa bisa dalilai biyu. Na farko shine har yanzu bata sake ji da ga jami'an tsaro ba, musamman akan binciken da sukace zasu mata game da Muhammad Shuraim da zuwa yanzu shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakaninsu. Dan tun daga waccan ranar duk bayan kwana biyu sai yazo gidansu. Bawata hira sukeba mai yawa, mafi yawanci ma akan karatu ne dan tafi sakin jiki da shi.

        Na biyu ganin yanda su Abba ke shirye-shiryen auren duk da yana kwance har yanzu yana fama da ƙafa sai yake ɗaga mata hankali take ganin tamkar tarkon data ɗana musu domin kuɓutar da yayunta bamai yuwuwa bane a garesu. Cikin ɓacin rai yau ta tattara dukanin kayan da A.G ya bata ta maida a bag ɗin. Dama addu'a taketa faman yi ALLAH yasa Ummi ta fita zuwa gidan malam da taji tana faɗa zata.

      Tana samu yayunta suka fita, Ummi ma ta fita gidan malam ɗin tare da su sai itama ta samu ta siɗaɗa ta fice da addu'ar ALLAH yasa har taje ta dawo Ummi bata dawo gidan ba.

         Tana shirin shiga napep aka dakatar da ita. Tai saurin juyowa a rikice jin an ambaci sunanta. Kallon sama zuwa ƙasa taima matashin saurayin da batasan daga ina ya fito ba. Shima batare da wani damuwar kallon da take masanba ya miƙa mata ƙaramar jakkar hannunsa.

      “Babu buƙatar ki sake komawa can. Zaki sami dukkan bayanan da kike buƙata anan. Akwai waya yace zai kiraki tanan zakuyi magana. Kiyi komai da kula”.

      Batare da ya jira cewarta ba ya juya ya barta tsaye galala da jikka a hannu tana binsa da kallo. Takaici da haushi yasa mai napep jan napep ɗinsa yabar wajen yana masifar an bata masa lokaci.

       Itama Hibbah juyawa tai ta koma gida jiki da sauri..............✍



TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*










*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


Chapter Seventeen_*


............Haushi da takaicine ya turnike Hibbah lokacin da ta iso gida ta buɗe jakar da saurayin ya bata. Babu komai a ciki sai ƙaramar waya da ko number guda ɗaya babu a ciki. Sai wani shegen voice recording guda ɗaya da taji bata buƙatar sanin kona uwar miye. Wadrobe ɗinta ta buɗe ta cilla wayar ciki tana jan tagwayen tsaki.

       Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai fita harkar waɗan nan ƴan sandan. Dan ta fahimci babu abinda zasu mata sai amfani da ita domin samin cikar burinsu tamkar yanda Yaya Abubakar ya faɗa. Inko hakane tayi alƙawarin bazasu sake ganinta ba........

           Sallamar Ummi da tajiyo ne ya sata ajiye komai ta fito tana amsawa. Ummi ta kalleta da mamakin ganin yanayinta. “Tanee kina lafiya kuwa?”.

     “Lafiya lau Ummi, kainane kawai ke ciwo amma nasha magani.”

         “To ALLAH ya ƙara sauƙi. Kije ki kwanta kozai faɗa miki mu gani”.

           Kanta ta jinjinama Ummin dan dama haka take buƙata. Da wannan damar ta koma ɗakinta ta cigaba da nazarin neman mafitar da ya dace ta kuɓutar da ahalinta da ga abinda ƴan uwan mahaifin nasu suke shirin ƙulla musu.

       

       Koda Yayunta suka dawo ma tana jinsu ta kasa fita ayi hira da ita. Tana jiyo duk wanda ya tambayeta sai Ummi tace tayi barci kanta ke ciwo. Duk sun jajanta tare da nuna damuwa tamkar yanda suka saba. Daga nan suka ɗan taɓa hira kowa ya kama gabansa zuwa makwanci.

      Duk yanda Hibbah taso yin barci a wannan daren ya gagara, babu abinda take sai saƙawa da kwancewa har asubahi, tana kuma idar da salla ta yo waje ta hau aiki. Lokacin da yayunta suka dawo salla suka samu tana aikin ba ƙaramin mamaki bane ya kamasu. cikin jan faɗa Ammar ya rike baki da faɗin, “Auta halan yau mafarkin zakici bulala hanun Ummi kikai ko? Inba hakaba kece yau da aiki a wannan sanyin safiyar”.

        Fuska Hibba ta ƙwaɓe kamar zatai kuka. “Yaya Muhammad ka gansa ko! Ni dai ai ban tankashi ba zai kama jana faɗa da safen nan”.

    Ranƙwashi Yaya Muhammad ya kaima Ammar akai, shi kuma ya kauce da sauri yana dariya da yima Hibbah gwalo. Su kansu su Yaya Usman dariyar suke ƙoƙarin dannewa. dan kowa dai yasan ɗan karan lalacin Hibbah akan aikin safe. Tanada kazar-kazar ɗin aiki amma banda na safe saboda shegen son barcinta. Ganin idan suka cigaba da tsiwa zata kufce musu yasa suka bar wajen da sauri. Itama sai ta cigaba da aikinta kawai.

      

     Ranar ita kaɗai tai aikin gidan, ta haɗa musu breakfast mai sauƙi sannan taje tai wanka ta fito. Yanzun kam gaba ɗayansu ido suka zuba mata ganin bata da walwala sam. Sai da taja kujera ta zauna Ummi da ke kallonta tace, “Ciwon kanne har yanzu?”.

      Kanta ta girgizama Ummi a sanyaye. “Ya daina Ummi, kawai dai banajin daɗin raina ne”.

         Shiru duk sukai suna kallonta cike da nazari. Yaya Usman da ke motsa shayi yace, “Auta akwai abinda kike ɓoye mana ƴan kwanakin nan. Sasai walwalarki ta ragu, kin bar zama hirar dare, ko yaushe kina cikin ɗaki. Shin kodai matsalar Shuraim ɗin ce har yanzun baki haƙura ba?”.

        Cikin ɗan rawar murya Hibbah tace, “A'a yaya ba shine ba. Ai nace muku na haƙura zan auresa. Dan nima zuwa yanzu na fahimci mutumin kirkine. Kawai dai ina tunanin ku ta yaya za'a raba ku da auren su Ameerah kamar yanda na samu kubuta daga auren Junaid. Yaya inaji a jikina akwai abinda su Abbah suke ƙullawa game da ku. Ni na rasa miyasa basa son mu? Mi muka tare musu ne a gidan nan? Minene laifinmu a garesu?....” takai ƙarshen maganar da saki kuka mai cin rai da ya saka su ajiye cokulan hannunsu su duka suka zuba mata idanu.

        Ummi ta rumtse kofin dake hannunta da ƙarfi. Wani irin ƙuna da ɗaci na sukar zuciyarta. Batare data farga ba harshenta ya suɓuce wajen faɗin, “Baku musu laifin komai ba Tanee. Sun tsaneku ne kawai saboda ni mahaifiyarku da ƙaddara ta kawoni cikinsu matsayin bara gurbi”.

      Gaba ɗayansu suka maida dubansu ga Ummi. yayinda kalmar bara gurbi data ambata tai matuƙar dakar zukatansu a lokaci guda.

      Cikin rawar harshe Ammar yace, “Ummi bara gurbi?”.

        “Eh Aliyu bara gurbi. Ƙwarai da gaske ni ɗin bara gurbi ce a cikinsu, domin kuwa samuwata ta kasance a jerin abinda mutane da yawa suke ƙyamata duk da muma ba laifinmu bane. Ba mune mukace a haifemu a haka ba. Bada son ranmu aka haifemu a haka ba. Kosu iyayen namu da ke haihuwarmu a hakan da yawansu badan sun so ba ne. Wasu ƙaddara ce ta jefesu da mu kawai.”

          “Kamar yanda kuka sani sunana Asiya. Mahaifina Sulaiman da mahaifiyata Muhibbah duk ƴan gida ɗaya ne. Dan kuwa ƴaƴan wa dana ƙani suke. Tun fil azal mahaifina bayajin magana. Dan mutumne gagararre na gaske da babu mai iya tanƙwarasa balle sakashi da hanawa.  Ba a asalin ƙauyenmu kawai ba, hatta da wasu kauyuka na gefenmu ana shakkarsa matuƙa gaya. Dan saboda hatsabibancinsa hatta da ɓarayi tsoron ratsa ƙauyenmu sukeyi. Tun tasowar mahaifiyata mahaifina ya nuna yana sonta, sai dai babanta yace sam bazai bashi ba, dan bai cika mutum ba. Wanann magana ta ƙona ran mahaifina, har takaisa ga yanke mummunar shawarar keta mutuncin mahaifiyata. A tunaninsa hakan kawai zaiyi a bashi aurenta. Dan ƙwarai da gaske yana son nata da gaken gaske.”

        “Gudun abinda zaije ya dawo ya saka baban mahaifiyata saka mata ranar aure da wani saurayi dake zuwa wajenta. Wannan abu ya ƙona ran mahaifina matuƙa, dan haka hamar yanda ya ƙudira haka ya zartar da wani yammaci, lokacin mahaifiyata ta dawo da ga aiken da akai mata gidan kakanninta, ya tareta a hanya yaransa suka ɗaukar masa ita. Kamar yanda aka sanarmin a wanann daren ya rabata da mutuncinta ta hanyar yi mata fyaɗe, ya kuma gudu ya bar garin washe gari da safe bayan fasuwar zancen da tsintar mahaifiyata da akai a yashe babu alamar rai tare da ita. Hankalin kowa ya tashi a ƙauyenmu, dan wannan shine na farko daya taɓa faruwa. Cikin ƙanƙanin lokaci magana ta yaɗu har ƙauyukan ƙetare, inda anan gida kuma kakaknina keta kai kawo akan ganin mahaifiyata ta farfaɗo. Da ƙyar aka samu ta farfaɗo, sai dai ta zama tamkar wata zautacciya, hakan yasa komai ya cuɗema iyayenta. Ga cece kucen jama'ar gari, gana ciwonta. Gana ALLAH ƙara da dangi suke musu akan tun farko su suka jamata. Inda sunyi haƙuri sun bama mahaifina aurenta da ba'akai ga haka ba. Maybe ma ya zama silar shiryuwarsa. In takaice muku zance sunsha matuƙar wahala kafin su ɗan samu kanta ta fara fahimtar abubuwa, sai dai kuma bayyanar samuwar ciki a jikinta ya sake rikita komai. Komai ya dawo sabo, dan kuwa sabon magana ya ɓalle ta kowacce kusurwar ƙauyenmu, kowa ya manta da ba laifin mahaifiyata bane, bakuma ta aikata da ganganba ƙaddarartace kawai tazo da hakan. Duk yanda kuke tunanin kakannina sunyi iya ƙoƙari na ganin cikin jikin mahaifiyata ya salwanta, sai dai hakan bata faru ba dan ALLAH yayi alƙawarin sai nazo duniya. ALLAH ya riga da ya ƙaddara sai mahaifiyata ta haifeni, dan haka ciki sai da ya kai har watannin haihuwa ta haifeni a wani dare na juma'a. Ina canyara kuka kakana na yanke jiki ya faɗi, faɗuwar da daga ita ko shurawa baiyi ba dan ya mutu. Hakama mahaifiyata tunda ALLAH yasa na fito da ga jikinta ta tada kanta da ƙyar ta kalleni hawaye na kwaranya a idanunta, tai murmushi mai ciwo da faɗin, “ALLAH ya albarkaci rayuwarki, ya ɗaga darajarki, ya kareki da dukkan sharri. ya saka haƙuri da juriyar duk abinda zaki gani a rayuwarki cikin zuciyarki” sai ta shafa kaina ta maida kanta ta kwantar shikenan anyita an gama.”

         “A rana ɗaya aka binne gawar kakana da mahaifiyata kusa da juna, yayinda aka barni hannun kakata da itama ta koma tamkar zautacciya. Bazance ban samu gata ba a hannun kakata, domin kuwa itace ta shayar dani har na tsahon shekara biyu. Sai dai sam bata son ganina, tunda ta yayeni bata sake yarda na raɓu jikinta ba. Kullum cikin tsangwamata take da nuna ƙyamata tamkar yanda jama'ar gari kemun. Babu maison ganina, babu maison na raɓu ɗansa nai wasa. Nasha cin duka wajen iyayen yara da yaran kansu batare da nasan laifin dana aikata garesu ba. Shekarata biyar a duniya mahaifina ya dawo kauyenmu. ko hutawa baiyiba kakata najin labari ta ɗaukeni ni da kayana taje ta damƙa masa batare da tace uffan ba ta juya ta tafi. A kuma wannan daren ta gudu a garin ta bar ƙannen mahaifiyata su Kawu Hannafi. Har yau ɗin nan da nake baku labari babu wanda ya sake jin labarinta.”

         “A yanda mahaifina ya amsheni babu musu ya tabbatarma jama'ar gari ya san ni ɗiyarsa ce, dan kakata na tafiya ya ɗaukeni ya damƙa hanun mahaifiyarsa, ya kuma tabbatar mata dole ta riƙeni dan shima ya dawo gida da zama, dama wani aikine ya sashi tafiya bawai dan yayima mahaifiyata fyaɗe ba. Babu wanda ya iya cewa ƙala saboda tsoron da suke masa. Sai dai dukannin haushinsa da takaicinsa akan saukeshi kainane a gidan. Shima ba sauki nake samu a garesa ba, dan babu irin kalar azabar da bayamin, sai dai kuma wani yana taɓani inhar ya gani sai ya rama mani.”

       “Haka na cigaba da rayuwa cikin azaba da ƙasƙanci, a wajen baban mahaifinku malam Hamza ne kawai nake samun sauƙi. Dan shi mutum ne mai ilimin addini. harma almajirai ke garesa. Sai dai sam bai dace da mace ba (Hajiya mama). Hajiya mama asalinta ba ƴar garin bace, acan indai yay almajiranci aka aura masa ita, hakan yasa ɗanta na fari da suka haifa mai suna Aliyu tun daga yaye da aka kaisa garinsu ba'a dawo da shi ƙauyenmu ba. Sai dai lokaci-lokaci yakanzo ya gaishesu.”

           “Mahaifinku Aliyu shine mutum na biyu da yake nunamin tausayi bayan kakanku kuma kawu na, dan duk sanda yazo kauyenmu nakan shiga cikin farin ciki matuƙa. Shine mutum na farko da ya fara koyamin karatun boko, yayinda kakanku kuma kawu na malam hamza yake koyan na addini duk da matarsa bataso. Saboda tsabar ƙiyayyar da Hajiya mama kemin a duk sanda naje gidan sai ta saka Halilu ƙanin Aliyu yamin dukan tsiya. Dan haka tun fil azal bama shiri da Halilu sam. Shakuwarmu da Aliyu ta cigaba da faɗaɗa a duk sanda yazo hutu ƙauyen. Tun mutane basu fahimta ba har kowa ya fahimta, dan yazamto duk sanda Aliyu yazo bashi da abokin yawo sai ni, akoda yaushe muna tare can bakin fadama. Dare ne kawai ke sakamu rabuwa. A randa labari yazo kunnen Hajiya Mama kowa yaga tsantsar masifa a ƙauyen nan. Dan haukacewa tai matuƙa taita bala'in da har sai da Babana ya kama Halilu yay masa dukan mutuwa saboda dukana da yayi. In takaice muku ranar ɗan ƙaramin yaƙine ya kusa tashi a ƙauyen mu. Karku manta na faɗa muku babana mutum ne da lamarinsa sai addu'a. Duk da kuma yana nunamin halin ko in kula kowa yasan yana sona. Dan soyayyar mahaifiyatace gaba ɗaya ta dawo kaina. Sam yaki aure, hasalima yayi alwashin tunda Mahaifiyata ta bar duniya babu aure a sanadinsa shima har abada bazai auri wata mace ba, zai karasa rayuwarsa a hakan dan itace ta farko da yataɓa so kuma itace ta ƙarshe.”

     “Bayan lafawar komai Hajiya mama ta haramtama Aliyu zuwa ƙauyenmu saboda ni, hakan ya ɗagamin hankali matuƙar gaya. Nayi kuka harda kwanciya ciwo, amma babu abinda ya canja. Haka na haƙura na cigaba da rayuwa a ƙauyenmu cikin halin tsangwama da ƙyara da ƙyama. Kawu Hamza ne kawai nake jin sanyi da sauƙi a garesa. Sai ko babana idan yaso haka. Na kasa samun miji a ƙauyenmu. Dukan sa'annina sunyi aure wasuma sun hayayyafa, kusan dai aure irin nada kuma na mutanen karkara. Duk wanda zaizo da nufin sona sai dai yay yunƙurin lalatamin rayuwa, dan a cewarsu ni ɗin ƴar shege ce. Hakan na matuƙar bani tsoro. yana kuma sakani kukan da babu mai lallashina. Ban kuma shiga tashin hankalin rayuwa da garari ba sai a shekarar da mahaifina ya rasu. Lokacin inada shekaru goma sha tara cif a duniya tamkar yanda Tanee take a yanzun. Duk da ba kulawa yake bani yanda ya kamata ba shi ɗin garkuwa nane. Dan ko a cikin gidanmu shakkarsa nasa a ragamin wani abu. Dama dangin mahaifiyata ba nuna sunada alaƙa dani sukeba. Sun matukar tsanata saboda mahaifiyarsu acewarsu ta gudu ne dan ni, sun kuma rasa ƴar uwarsu dalilin mahaifina. Rayuwa ta ta sake shiga matuƙar garari dan waɗanda suke ɓoye maitarsu akan mutuncina sun fiddosa. Ciki kuwa harda.....”(kuka ya ci ƙarfinta)

      Da ƙyar ta iya haɗiyesa saboda ganin yanda su Hibbah ke kuka. Hatta da Yaya Umar duk jarumtarsa kuka yake rurus. Ummi ta cigaba da faɗin, “Harda Halilu. Dan shine ya kaimin hari na ƙarshe har gida a wani dare. Sai dai ALLAH ya kuɓutar dani saboda ihun da nayi har kakana ya fito shi da kawu Hamza (kakanku). Duk da naga wanda ya shogomin ɗin sai ban faɗa ba, nace kawai ban sanshi ba. Bawai dan ina tsoron faɗar bane, kawai dai ba yaune ranar da Halilun ya fara min irin wannan titsiyen ALLAH na kuɓutar dani ba. Na yau ɗinne dai yaso fin na ko yaushe muni. Washe gari malam da kansa yace na dawo kwana ɗakin kusa da shi, hakan ya baƙanta ran hajiya mama taita masifa a ɓoye, dan tana tsananin tsoron malam. Anyi haka da kwana biyu sai ga Aliyu. Bansan yanda zan musalta muku halin dana shiga ba. Sai dai tabbas naci kukan farin cikin ganinsa matuƙa gaya, shi kansa har ƙwalla yayi, sai dai yayi ƙoƙarin ɓoyemin.”

            “Babu zato babu tsammani  bayan sakkowa massallacin juma'a sai jin an ɗauramin aure da shi kawai nayi. Firgici ya sakani yanke jiki na faɗi a sume sai da aka yayyafamin ruwa. Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya karaɗe gari, yayinda Hajiya mama ta rikice da ihu da kururuwar sam bata yarda ba da wannan haɗin. Babu yanda ta iya dan malam yafi ƙarfinta. Hasalima ana kammala sallar la'asar ya saka Aliyu tattarani da gani sai kayan jikina muka baro ƙauyenmu. Barowar da ban sake komawa ba sai rasuwar malam da kakana data faru kusan lokaci guda. Bazance muku banyi murna da baro ƙauyenmu ba a lokacin, domin kullum hakan shine mafarkina. Nasha aunawa a raina dama na gudu idan har irinsu Halilu sun cigaba da bibiyar mutuncina, sai gashi ALLAH yaymin sutura na barosa tare da igiyar aure da miji ɗan gaske irin mahaifinku.”

         “Nayi matuƙar mamaki lokacin da muka shigo garin nan naga Aliyu ya kawoni wani madaidaicin gida mai ɗakuna biyu da kitchen ƙarami sai toilet da rijiya a tsakar gida. Babu komai a gidan sai katifa a ɗaki ɗaya da ƙaramar Wadrobe ɗin kayansa. Ɗayan ɗakin kuma kafet ne malale kawai sai tv babu kujeru. Sai ƴan kayan girki a kitchen ɗin da alamar shike abinci da kansa. Bai barni na huta ba sai da ya zagaya dani lungu da saƙo na gidan, tare da min bayanin komai na amfani. Da kansa yay mana girkin abu mai sauƙi mukaci a ranar, bayan ya yambayeni girki nace ban iya ba. Dan tunda nake ko zuba manja a wuta babu wanda ya taɓa sakani a ƙauyenmu. Aliyu shine ya koyamin girki, shine ya koyan aikin gida, ya sakani islamiyya. Ya kuma cigaba da koyar dani karatun boko. Kamar yanda bai taɓa zama yamin tambaya akan bayan rabuwarmu ba, nima ban taɓa masa tambaya akan ƙin sake dawowarsa ƙauyenmu ba har ALLAH ya albarkacemu da samun ciki. Ya nuna tsantsar murnarsa da farin ciki akan wannan ciki. wadda har ta ban mamaki sosai, amma sai na shanye mamakina nima ina maijin daɗin zanga jinina bayan mahaifina dana rasa.”

          “Na cigaba da rainon cikin Muhammad a ƙarƙashin kulawar Aliyu har ya cika watan haihuwa, sai a lokacinne kuma wani baƙo ya taɓa zuwa wajenmu da ga ƙauyenmu. Dan kuwa babu zato babu tsammani sai ga Hajiya mama da Halilu. Cikin farin cikina na nuna murnar ganinsu, sai dai tun a tsakar gida Hajiya mama ta katse murnar tawa ta hanyar daka tsalle ta dire tana kallon cikin jikina. Aliyu da abin nata ya bashi mamaki ya tambayeta ko lafiya. Kai tsaye ta nuna masa ciki da tambayar ina aka samosa?. “Mama ƙyautace da ga ALLAH ya bamu mana tunda jinin ɗanki ne”. Aliyu ya bata amsa kai tsaye dan shi ba mutum bane mai ɓoye-ɓoye ko kwana-kwana a magana.”

        “Cikin daka tsawa tace “A gidan ubanwa ya zama jinina? To idanma zaka dawo hankalinka ka dawo. duka-duka ƙaddararren auren naku watansa takwas kenan ace da wannan tulelen cikin mai kama da shekarre. Sai dai idan ɗan shege ne aka zomaka da shi da ga waje kamar yanda aka samota itama za'a nana maka”. Wannan magana ta tashi hankalin Aliyu dani kaina, ya shiga rantsuwa akan sam ba haka bane ba, amma sam hajiya mama taƙi saurarensa. Hasalima washe gari suka juya ƙauye ita da Halilu. Babu shiri shima Aliyu ya bisu batarema dana sani ba. Dan nima tunda hajiya mama ta ɓunta maganar jingina cikina da bana Aliyu ba sai ciwo yaymin rijif. Ba ƙaramar ƙurace ta tashi akan cikin jikina ba. Har takai da malam yace a jira na haihu sai a san mai gaskiya. Cikin amincin ALLAH kwana goma sha ɗaya dayin wannan al'amari sai ga naƙuda. Batare da ALLAH ya ƙaddaramin shan wahala ba na haifo Muhammad Aminullahi. Wanda tunma yana cikin jininsa daka kallesa kaga Aliyu tamkar yayi kaki ya ajiye. Bakin kowa ya mutu tun daga haihuwar Aliyu, har takai dangin hajiya mama sunzo taron suna, kafinma taron wata tsohuwa tazo ta zauna dani dan malam yace koda wasa kar Aliyu ya kaini ƙauyenmu. Babu kowa a dangin mahaifina da mahaifiyata bayan malam da Halilu. Duk da hajiya mama bataso ba Aliyu yayi bajinta dai-dai karfinsa.”

        “Bayan haihuwar Muhammad abubuwa da yawa sun buɗe mana musamman ƙofofin arziƙi. Dan abin tamkar roƙo sai ga alkairai nata shigowa, cikin shekara biyun danai ina shayar da shi harmun canja gida, Aliyu ya sai mota. Wannan arziƙi shine ya sake saka damuwa tsakanina da Hajiya mama. Dan gaba ɗaya ta tashi hankalinta akan bazanci ni kaɗai ba sai Aliyu ya ƙara aure. Shi kuma da yake mutum ne mai taurin tsiya yace bashi da ra'ayin zama da mace fiye da ɗaya yayi kenan dan yanaso na. An buga an buga yaƙi. Ganin fitinar ma tayi yawa sai ya daina zuwa ƙauyen bisa shawarar mahaifinsa. Sai dai kuma an gudu ba'a tsira ba, dan kuwa hajiya mama na ganin an kulleta ta ko ina sai ta canja salo, ta kwantar da kai ta nuna nadama a lokacin da akace mata ina da wani cikin. Da farko malam bai yarda da ita ba, sai da akaja lokaci ina gab da haihuwa bansan yaya akaiba sai ga Halilu da jakar kaya wai yadawo zama da mu zai dinga tsare shago da Aliyu ya buɗe a kasuwa tunda shi aiki baya barinsa zama. Hankalina bai tashi ba, dan ni a tunanina ai yanzu na wuce da duk wani shaiɗancin Halilun na kafin aure na. Dan haka na amshesa hannu bibbiyu na kuma saki jiki da shi. Shima kuma sai ya kwantar da kai yay tamkar babu komai a ransa. A wanann karon ma na haihu lafiya namiji, wanda yaci suna Abubakar, shima dai gaba ɗaya ya kwaso kamanin Aliyu. Tun bayan haihuwar Abubakar Halilu ya fara fiddo min wasu sabbin halaye, sai dai sam baya yarda yayi a gaban Aliyu da Malam ko gaban mutane. Iya ni kaɗai yakemawa sai Muhammad da zaita duka babu gaira babu sabar, hatta da Abubakar na goye bai ƙyale ba. Ko kallon inda yake banayi balle na nuna nasan yanayi ɗin. A haka na sake samun ciki na uku, shima na haifi Umar. A wannan haihuwa kam banjita da daɗi wajen Hajiya mama da danginta ba. Dan ƙiri ƙiri suka dinga kwaɓamin magana na mamaye musu ɗan uwa. Babu mai cin arziƙinsa sai ni da ƴaƴana. Duk alkairan da yake musu da yanzu ya bari komai sai ni. Haka suka dinga tsogumi har sai da abin nan ya sani kuka, sai dai ban yarda na sanarma Aliyu ba dan ba'a gabansa sukai ba. Ina da tsohon cikin Usman ne muka dawo wannan gidan, dan haka lokacin dana haifesa sai yazam ƴan uwa sunzo suna haɗe da tayamu murnar sabon gida. A wannan zuwa ma dai ba daɗin naji ba. Dan maimakon tayani murnar haihuwa sai habaicin ina haihuwa bi da bi ba hutu, wai inayine danna mamaye komai na Aliyu shiyyasa duk sai ƴaƴa maza. A wannan karon kam ɓacin ran dana shiga har sai da takai malam yazo da kansa. Dan gaba ɗaya na sauya harshi Aliyun yama kasa gane kaina. Na tubure masa akan ya ƙara aure kozan sami sassaucin cin kashin nan nasu. Musamman ma Halilu da ya zama mai fuska biyu, a gaban malam ya nuna babu wadda yafi ƙauna da so sama da ni da ƴaƴa na. Dan aurensa ma da aka saka da matar daya samo acan cikin dangin hajiya mama yace nice uwar biki. Nasan a zancen nasa akwai manufa, amma sai na watsar da shi kawai. Malam ya lallasheni da kalamai masu daɗi harna huce komai ya wuce muka koma yanda muke da Aliyu.”

        “Hidimar auren Halilu ce ta sake canja komai. Dan kuwa naci matuƙar wahala a lokacin. Komai aka nema sai suce a zo wajena shi da hajiya mama. Ko ɗan kwali ƙin saya sukai balle ƙwayar abinci. Idan nace ma Aliyu yayi yayta faɗa akan ai ya basu kuɗaɗe masu nauyi na hidimar nabar damunsa. Haka na shiga tsaka mai wuya a tsakanin. Duk ɗan abinda nake samu na haihuwa na ƙwaƙule nai hidimar Halilu dan nasan bazan taɓa fita a garesuba idan ma na nuna Aliyu baiyiba. to ashe yin danayi ma ba mafita bace dan sabon zancene ya tashi akan eh da gaske na mamaye komai ɗin. Bani da abin cewa dan haka nai musu shiru akai biki aka ƙare lafiya amarya ta tare a tsohon gidanmu da muka taso, dan da hajiya mama ta matsa anan zasu zauna tare damu tunda akwai ɗakuna. Aliyu yace sam bai yarda da wannan gwajin gwalar ba. Salon haɗa rikici. indama kowa da part nashine sai ya amince. Amma flat ɗaya ne a gidan iya na iyalinsa sai BQ. ita kuma tace Halilu bazai zauna BQ da matarsa ba ni ina ciki inacin daɗi. Bayan ƙurar data tashi ta lafa dan malam ya tsawatar suka yarda Halilu ya zauna acan. Sai dai kuma duk wani abu da zasuci acan bazai saya ba, sai dai yazo nan gidan direct ya ɗiba koda kuwa gishiri ne. Ban taɓa faɗama Aliyu ba sai da ya gani da idonsa. ranar naga asalin faɗansa. Dan murje ido yay yayma Halilu tas har nima na samu rabona a ciki. Wata sabuwar ƙurar ta sake tashi akan wanann magana, har takai Hajiya Mama ta nema Aliyu ya sallami Halilu da ga kasuwa shima ya rinƙa juya na kansa, kokuma su dinga raba ribar duk abinda aka tara a ƙarshen shekara. Ƙince musu komai yay akan hakan, yaƙi kuma bashi kuɗin ya ƙi sallamarsa. Shine dalilin da yasa Halilu ke ganin nice na hana shi da hajiya mama. Duk da kuwa a shekarar Aliyu ya biya mata hajji ita da malam da shi sukaje. Wannan karon na samu hutu, dan tun Usman babu wani labari. Hakan yamin daɗi, dan na samu sauƙin wasu fituntunin, duk da shi kullum mahaifinku cikin tambayata yake wai yaji shiru, danshi mutum ne mai son yara matuƙa. Shiyyasa kuka kasance ƴan gata a wajensa. Komai na buƙatunku baya sakaci da shi komai ƙanƙantarsa. Wanann yasa ake ganin ya lalace a kanmu. Shekara na zagayowa ya sake biya mana hajji ni da shi mukaje. Muna dawowa ya sayamin mota tare da danƙamin wani ƙaramin gida yace na zuba haya, sai jari na sana'a.”

        “Musalta muku halin da na shiga awanan tsakanin bazai musaltu ba. Dan saida na gwammace da bai baninba. Dama akan tafiyarmu hajji ansha dabi hajiya mama tace bata yardaba sai dai ya biya musu shi da Halilu. Bansan miyazo kan Halilu a lokacinba shi ya nuna goyon bayan naje, harda nunama hajiya mama bayajin daɗin abinda takemin, ai koba komai na haihu da Aliyu ya kamata a ɗagamin ƙafa zuwa yanzun. Hakan da yayi ya saka malam jin daɗi. Tun daga sannan ma suka koma ɗasawa dan shi malam ya yarda da tuban Halilu ɗari bisa dari. A cikin wannan tarnaƙin na samu cikin Ammar. Wanda yazomin da matuƙar wahala da jigatuwa. Bani kaɗaiba hatta mahaifinku yaji a jikinsa kafin ALLAH ya sa na haihu ko nace akaimin cs aka cirosa. Babanku na ɗaukarsa ya gansa ƙato da shi ga kamanninsa sak nashi tako ina sai cewa yay “Lallai kaci suna Aliyu gadanga kodan wahalar daka bama matata”. Hakan ya sani murmushi, dan har cikin raina naji daɗin sunansa da zai maimaitamin cikin ƴaƴana. Ammar yaci suna Aliyu, a wannan sunan kam kowa ƙin zuwamin yayi, ƙiri-ƙiri suka nunamin jin zafina da suke, sai malam da Halilu da canjin nasa keta bani mamaki ne sukaita komai. Dama dangina nidai wani bai taɓa nemana ba, garama da maganar siyamin mota da gida ta fito su kawu Bello sunzo wai tayani murna. Bandamu da a yanda sukazo min ɗinba nai musu alkairi Aliyu yay musu suka koma. Bayan haihuwar Ammar babu jimawa Aliyu ya fara ciwo a tsaitsaye, inata fama da shi yaje asibiti yaƙi, har dai ta kaisa da kwanciya sannan ya yarda mukaje. A gwajin farko aka gano yanada ciwon ƙoda, yama daɗe a jikinsa dan harya harbi hantar sa. Hankalinmu ya tashi amma sai yayta kwantar mana akan shi ya samu sauƙi. Na jigatu a wannan tsakanin, daga zuciya har gangar jiki. Ban samu nutsuwa ba sai da jikin yay sauƙi ya koma kan harkokinsa. Ashe dauriya kawai yakeyi dan ganin hankalina ya kwanta. Haka mukaita lallaɓawa wataran ya kwanta kwana biyu ya mike ya cigaba da hidimarsa harna yaye Ammar. A watan dana yaye Ammar a watan ciwo ya kai Aliyu ƙasa, har takaisa ga kwanciyar jiyya. Dole Hajiya mama da Malam suka dawo gidan nan da zama muna kula da shi tare dan abin yayi tsanani. Da yake kwana ya ƙare kwanakinsa goma sha bakwai kacal a kwance ALLAH ya amshi abinsa. Mun shiga gigita, mun shiga ruɗani irin wanda bama zai musaltu ba. Dan har wata ƙaramar mahaikaciya na koma a tsakanin nan, sai da malam ya dinga min addu'a na dawo hayyacina. Hajiya mama taso a tafi ƙauye dani nayi zaman takaba. malam yace a'a a ɗakina zanyi. Ta dawo cewar yara su dawo hannunta. Nanma yace a'a ni zan cigaba da rike abina. Duk ta inda ta ɓullo sai ya goce, ganin babu mafita ta haƙura na cigaba da takaba. Su kuma suka koma ƙauye. Acikin zaman takabanne na fara laulayin cikin da ni nasan ina maƙale da abina tun cikin satin da Aliyu ya rasu, sai dai yana bayyana ga kowa Hajiya mama tace bana Aliyu bane..............✍


*_Bara mu dakata anan, naga page ɗin nata ƙara tsaho🚶🏻😖_*


   ZAFAFA KARO NA FARKO


SUNAYEN SU:


1_GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDULL


2_KAI MIN HALACCI

NA MISS XOXO


3_BURI DAYA

NA MAMUH GEE


4_DAURIN BOYE

NA SAFIYYAH HUGUMA


5_SAUYIN KADDARA

NA HAFSAT RANO


    DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500


SAI ZAFAFA TAKU NA BIYU


1-DAURIN GORO

NA HAFSAT RANO


2-ALKAWARIN ALLAH NA

SAFIYYAH HUGUMA


3_QAUNAR MU

NA MAMH GEE


4_IGIYAR ZATO

NA MSS XOXO


5_WUTSIYAR RAKUMI

NA BILLYN ABDULL.


DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500.


SAI ZAFAFA TAKU NA 3,


1_MIN QALB

NA MAMUH GEE


2_SARAN BOYE

NA BILLYN ABDULL


3_KIBIYAR AJALI.

NA MISS XOXO


4_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA

NA HAFSAT RANO


5_SIRADIN RAYUWAR BILKISU

NA SAFIYYAH HUGUMA


DUKA DOCUMENTS DIN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)


SAI ZAFAFA TAKU NA HUDU.


1-ALKIBLA

NA SAFIYYAH HUGUMA


2_DALAAL

NA MISS XOXO


3_UBAYD MALEEK

NA MAMUH GEE


4_MABUDIN ZUCIYA

NA HAFSAT RANO


5_MAKAUNIYAR KADDARA

NA BILLYN ABDULL


DUKA LITTAFAN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)


SAI ZAFAFA KARO NA BIYAR DA AKE A HALIN YANZU, (ON GOING PAID NOVS)


1-SO DA ZUCIYA

NA MSS XOXO


2-TAKUN SAAKA

NA BILLYN ABDULL


3_HALIN GIRMA NA HAFSAT RANO


4_DAB'IZAR ZUCIYA

NA SAFIYYAH HUGUMA


5-DEEN MALEEK

NA MAMUH GEE


DUKA BIYAR DIN NERA DUBU DAYA NE( 1K)IDAN AN KAMMALA SU KUMA 1500.


YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:


ACCOUNT NAME: MUSAA ABDULLAHI SAFIYYAH..


BANK NAME: KEYSTONE BANK


SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA: 


08184017082


IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:


09134848107



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*


*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*


_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_


*_Muna da haɗin_*


_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_


_Muna Gyaran jiki_

_Na amare_

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_


_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_


_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_


_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_


_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*


_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_


_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_


••••••••••••••••••••••••••••••••


*_Chapter Eighteen_*


..............Tashin hankalin wannan magana yasa na yanke jiki na faɗi, dan ko sanda akai na Muhammad da sauƙi inada garkuwata Aliyu. Amma wannan ni kaɗai ce naketa ƙoƙarin kare kaina sai malam da Halilu da bansan miye manufarsa na bani kariyar ba. Kamar na Muhammad wannan ma malam yace sai a jira na haihu. Haka kuwa akai, na cigaba da rainon ciki Halilu nata hidima dani da ƴaƴa na. Abin na bani mamaki yana sakani a ruɗani., ya kuma bani tsoro Dan sam na kasa hango manufarsa a kan hakan har takai ALLAH ya saukeni lafiya na haifo ɗiyata mace a karon farko. Itama dai tunda ta diro duniya kowa ya shaida jinin Aliyu ce. Dan kamanni sak ta ɗebo nasa dana ƴan uwanta harma taso ta fisu ɗebo komai nashi, sai dai kawai dan ita mace ce. Bakin kowa ya mutu kam, dan ko tari ba'a sakeba akan batun na cigaba da shayar da ɗiyata da taci sunan mahaifiya Muhibbat. Bakowa bane da wannan aikin sai malam. Ya tabbatarmin da wasiyya ya cika shima. Mahaifina ne ya roƙesa dan ALLAH inhar ALLAH yasa na sami miji nai aure na haifi ɗiya mace duk rintsi yana son a saka mata suna Muhibbat sunan mahaifiyata. Sai ko gashi ALLAH yaja da ran malam ya cika wannan wasiya. Sakama Tanee sunan mahaifiyata shine abu na farko daya jawo mata baƙin jini itama a wajensu. Dan anata ƙananun magana Halilu ne kawai ke karewa. Haka dai sukayi suka gama har ƙura ta lafa. Bayan na yaye Tanee aka raba gadon ku, sai dai malam ya kirani gefe mukai maganar da kunyarsa bazata barni na bijire masa ba. Dan yamin hallaci irin wanda bai kamata ni na saka mishi da butulci ba.”

       “A wancan lokacin bayan na samesa ya fara da faɗin, (Asiya ke ɗin ɗiyace ɗaya tamkar da dubu. Kuma ɗiya kamar sauran ƴaƴa. Dan baki da banbanci da su kamar yanda wasu suke gani. Baki da laifin komai dan bakece kika aikata laifinba. Ita kanta mahaifiyarki ƙaddara ce ta afka mata har aka sameki. Kiyi haƙuri na ɗakko miki wannan zancen ne saboda abinda nake hangowa da zaije ya dawo game da zuri'arki da wannan dukiyar tasu. Nasan baki wuce aure ba. Dan haka manema yanzu zasu fito gareki tako ina. Sai dai bai zama lallai su kasance dan ALLAH zasuzo ba ko dansu riƙe waɗan nan marayun. Banason bayan babu raina ki shiga gararin rayuwa. Dan mahaifinki kafin yabar duniya yayi matuƙar nadama ya duƙufa neman gafarar ALLAH, ya duƙufa neman ilimin addini a wajena batare da kowa ya sani ba. Shiyyasa ya danƙa amanarki a gareni. Kuma insha ALLAHU zan yi iya bakin ƙoƙarina naga na tsare wannan amanar har zuwa sanda nima ta ALLAH zata kasance. Asiya babu wanda yafi cancanta ya adana dukiyar ƴaƴanki sai ke da kanki, amma dole sai da taimakon namiji. Ni kuma gashi ƙarfina ya ƙare, dan bani da isashshiyar lafiyar nima tun bayan rasuwar Zaki (da yake haka yake kiransa). Amma inata nazari har zuciyata ta yanke min wata shawara da nake fatan zata zama mafita agaremu baki ɗaya. Halilu ɗan uwane ga zaki, duk da halayyarsu ta banbanta. Amma shima idan kin lura ya jima da dawowa hankalinsa. Rasuwar ɗan uwansa kuma ta sake lausasar dashi ko mahaifiyarsu baya son yaji ta aibantaki. Shiyyasa nake ganin mizai haka ki amince ki auresa ku haɗu ku riƙe wannan amanar da ALLAH ya bar mana ta yaran nan da dukiyarsu har sanda zasu kai girma. Na tabbatar hakan zai sakaki nutsuwa da kwanciyar hankali Asiya. duk runtsi babu mai rabaki da ƴaƴanki kema kina gidan mijinki tare da su. Ko sake haihuwa kikai dai duk zasu zama da ga tsatson jini ɗaya ba zaki rarraba kan zuri'arki ba. Amma bawai dole bane fa. Na baki dama kije kiyi nazari daga nan har wata guda. Hukuncin da kikaji ya kwanta miki a rai sai kizo min da shi. ALLAH yayi miki albarka, yayama yaranki albarka. ya baku kariya a dukkan motsinku da numfashinku). Cikin kuka na amsa masa da amin”.

         “Tunda malam ya tafi ya barni ban huta ba dare da rana akan tunani da nazarin wannan tayi nasa nake. Na hanga na hango naga zancensa shine kawai mafita a gareni da ku kanku. Sai dai har cikin raina ina matuƙar tsoron abinda zaije ya dawo akan Halilu. Dan gaba ɗaya yanzu ba iya gane inda ya dosa nake ba kai tsaye. Ya riga yayma kansa lulluɓin biri da fatar kura. Ta wani gefe kuma ina kallon kima da darajar malam. ALLAH ne ya zaɓa min Aliyu matsayin miji shine ya zama sila kuma. Bai duba ni ɗin wacece ba, bai ƙyamaceni kamar yanda kowa ke ƙyamata ta ba. Ɗansa ya karɓeni da hannu biyu babu musu, ya nunamin dukkan soyayya da ƙauna. Ya bani farin ciki a ƙarƙashin igiyar aurensa. Koda suɓutar baki bai taɓa gorantamin akan asalina ba. Idan ma na faɗa ƙwaɓata yake ya nunamin ɓacin ransa. To nikan inba butulci ba mizai sa na bijirema zaɓinsa a karo na biyu. Ina ganin koda Halilu mutumin banza ne zanyi fatan dawo da shi hanya. Yanda mahaifinsa da ɗan uwansa basu ƙyamaceni ba shima bazan ƙyamacesa ba. Da waɗan nan kalolin tunanin na gama yankema kaina shawara, a ƙarshen watan da malam yazo ziyararmu tamkar yanda ya saba a kowane wata sai na nuna masa kawai na amince. Ya matuƙar nunamin farin cikinsa da jin daɗi. Yayta sakamin albarka da sakama ƴaƴana. Indai ta ƙaice muku zance da ga ƙarshe an ɗaura aurena da Halilu, auren da ya bama kowa mamaki, musamman da akaga Hajiya mama ko tari batai akansa ba balle asan bata so ko tana so. A farkon auren nan a kunyace nake da lamarin Halilu kota wane fanni, amma ina iya bakin ƙoƙarina na sauke haƙƙokinsa a kaina. Shima kuma yana bani kulawa da respecting ɗina. Hakama ƴaƴana ƙauna yake nuna muku tamkar mahaifinku. Hankalina ya sake kwanciya da shi, na saki jikina sosai tare da ɗaukar duka dukiyarmu na danƙa a hannunsa akan cewar sai kun girma za'a bama kowa nashi. Da farko ya nunamin bazai amsaba. Sai da naita roƙonsa da nuna masa muhimmancin zaman komai a hannunsa saɓanin ni mace. Da ga ƙarshe dai ya amsa da ƙyar. Sati biyu kacal da yin haka ALLAH yayma malam rasuwa. Ƙwarai da gaske na shiga ruɗani fiye da rasuwar mahaifina. Dan malam ya taka matukar rawar gani a rayuwata wadda baki bazai musalta ba. A wannan lokacin naje ƙauye rasuwar malam, duk da a ɗarare nake da kowa ban samu matsi kamar sanda ina rayuwa a ciki ba. Sai ma abin kallo da na zama ni da ƴaƴana saboda da kaina naja mota ta har can. Kwanan malam huɗu da rasuwa kakana ma ya rasu, mahaifin babana kenan. Ban wani ji tasa rasuwar ba. Dan da shi da babu a gareni duk ɗaya dai. Satina guda a kauye muka dawo tare da Halilu, inda tun shigowarmu na fara ganin sabbin al'amura da ga garesa da suka nema rikita mani tunani. Cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja. Hajiya mama ta dawo nan da zama, hakama matar Halilu da ƴaƴansa. Ya cireku da ga makarantar da kukeyi ya maidaku ta gwamnati, nima ya haramtamin tuƙa mota. Al'amarin ya matuƙar gigitani da sani a tashin hankali, amma saina daurema zuciyata saboda halaccin mutane biyu da nake tunawa a koda yaushe. Kawu na da mijina. Komai ya sauya da ga salonsa. duk wata cusgunawa ita Halilu da Hajiya mama kemin harma da matarsa da yaransa. Ku kanku baku da sukuni a gidan koda nayin wasa ne. Abubuwa da yawa kullum cikin gorantamin su yake, tare da neman komai gareni ta ƙarfi (uwa ta gari kenan, maimakon tace yana mata fyaɗe saita sirranta domin mutunta kanta😭). Ɗawainiyarku duk ta dawo hannuna. Komai baya mana ya bari. sai ma filin garden ɗinmu da Aliyu ya kashe kuɗi sosai yayisa saboda mutumne mai tsananin son furanni da ƴayan itatuwa Halilu ya bajesa ya kafa wancan ginin, part ɗinsa da matarsa, sai part ɗin hajiya mama. Bayan an kammala suka koma can da zamam babu ruwansu damu balle yaya mukaci, sai tarin masifa da hantara a garemu. Gidan da Aliyu ya sai min da kuɗin hayarsa na cigaba da ɗaukar nauyin karatunku, sai taimakon Sheikh Aliyu Maina abokinsa. Dan ya matuƙar taka rawar gani akan rayuwarmu shima. kullum nunamin yake nayi haƙuri na cigaba da rayuwa da Halilu har kukai girma dukiyarku ta dawo hannunku sannan na rabu da shi. Wannan yana cikin dalili na na karshe bayan tuna halacci da ƙauna da mahaifinku da Malam suka nunamin a rayuwa, yayinda kowa ya gujeni har ƙannen mahaifiyata. Shiyyasa kukaga ina cigaba da jure komai har kawo iyanzu da insha ALLAHU komai yazo ƙarshe, zamu bar musu gidan duk da kuwa haƙƙinmu ne. Dukiyarku kuma idan ma bai baku ba ku barsa da ALLAH kawai tunda ya rufa mana asiri bamu rasa ci ba balle sha da suturar sakawa. Fatana kar wannan labarin ya sakaku tunanin ɗaukar wani mataki akan hajiya mama da Halilu. Ku barsu ALLAH zai muku maganinsu ta hanyar da bakuyi zato ko tsammani ba. Dan banason ya cutarmin daku. Dan ALLAH na roƙeku ku barsu mu rabu lafiya salin alin”.

           Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, sai faman sharar hawaye kawai sukeyi. Hibbah ta fara miƙewa taje ta rungume Ummi, sai Yaya Ammar ma yaje ya haɗasu su biyun ya rungume. Hakan yasa suma sauran duka suka miƙe sukaje suka rungumesu baki ɗaya. Idan ka gansu dole ne su baka sha'awa, su baka tausayi, su kuma birgeka.

      Sun ɗau tsahon lokaci a haka kafin su koma su zauna suna mai kallon Umminsu cike da tausayinta da tsananin soyayyarta. Yayinda Hibbah duk ta fisu jin kewar mahaifinsu da ko cikinta baisan ya bari ba. Duk da kuwa yayi ƙwaɗayin a haifa masa ɗiya mace matuƙa ALLAH bai ƙaddara zai gani ba.

      “Ummin mu ai kece ZAKIN, SARAUNIYAR DUNIYA TA MATA”. Ammar ya faɗa cike da zolaya yana share hawaye. A tare suka sanya dariyar da basuyi niyya ba. Dan yanda Ammar ɗin ya faɗa yana salute na Ummi dole ne ya baka dariya.

      Duk yanda sukaso ɗakko maganar Ummi ta hanasu, sai ma ta shiga jansu da wata hirar cike da tsokana suna kwasar dariya. Gaba ɗaya sun shagala da batun fita aiki da makaranta, balle kuma breakfast ɗin da sukai zaman yi. Kafin su farga sai kiran sallar zuhur sukaji. Nanfa aka shiga jaje da sallami. Ummi kuwa ta dinga musu dariya wai yau itace gwamnatin da sukaima aiki ai.

         Suma dariyar sukeyi cike da nishaɗin ganinta cikin farin ciki, da ga karshe kowa yabi hanyar data dace wajen neman excuse a wajen aikinsa. Yaya Umar dama kasuwa ce baida matsala. Su Hibbah kuwa makaranta ce. Haka suka ƙarasa wannan yinin a tare, salla kawai ke fiddasu ƙofar gida har dare. Da za'a kwanta ma Hibbah ta maƙale tare da Ummi zata kwana.


*_WASHE GARI_*


     Yau da sassafe duk sukai shirin fita aiki kasancewar jiya basu fita ba. Kamar yanda suka saba kullum yanzu suna ɗan fita da kayansu masu muhimmanci zuwa sabon gida saboda masu gidan yau ma sai da Yaya Muhammad da Yaya Abubakar suka ciccika booth ɗin mota sanan suka fice. Ammar kuna ya dauka Hibbah a mashin shima suka wuce makaranta. Yayinda suka bar Ummi na cigaba da haɗe musu abubuwansu masu muhimmanci da suka rage.


*________________*


     Kwanakin biki sun cigaba da gabatowa gab, dan yau gashi har an kawo lefen Hibbah gidan. Lefe ne na ƴar gata da ya bama kowa mamaki. Dan ƙiri-ƙiri yaran Abba suka shiga nuna hassadarsu da baƙin ciki. Ita kanta Hajiya mama da Momy tunma baƙin na nan suke yadda habaice-habaice dan zubarda mutunci. Ita dai Ummi komai batace ba. Dama ta gayyato ƙawayenta iyayen su Zahidah sai matan Sheikh Aliy su mama Jiddah😜 da suka amshi lefen. Dama hidimar tarbar baƙi duk da ga gidan Sheikh Aliyun aka yota. Komai sai gani su Hajiya mama sukai ana shigo da shi gidan. Ga makwafta sunyi hallaci duk sun shigo ana komai da su.

     Lefe kam yayi sai sam barka. dan Muhammad Shuraim ya kankaroma Hibbarmu  mutunci😂😉. Ita tanama makaranta sai da ta dawone taga akwatina da kayan su sweets biscuits da sauransu. Sosai abin ya bata mamaki har tana ƙorafin kamar hauka. Ita batason fariya. Ai basai ya nuna sunada shi ba.

         “Oh ni Ali, yau naga uwar kutsugu. Danma kin samu ya kankaro miki mutunci zaki mana iyayi a gida”. Ammar ya faɗa yana dalla mata harara. Itama harar ta dalla masa tana murguɗa baki. “To karya kankaro mutuncin mana. Wayace masa shi ake jira ya kankaro”.

       “Ni wlhy ina so da fatan ganin randa wanann bakin naki na akku  zai mutu murus auta.”

      “Ai bazaka gani ɗin ba kuwa Yaya Ammar.”

       “Hhhhh ALLAH dai ya kaimu ranar shiga labour room, kafin sannan ma nanda kwana goma sha bakwai kacal nasan ya gama mutuwa kodan rabuwa da ni da Ummi. Ayye mama ayye mama, mamaye iye, ayye mama labo labo, mamaye iye. Da aure yana raka aure, mamaye iye, dana biki mun tafi tare. Mamye iye, ko tuƙin tuwo ƙya koya, mamaye iya, har damun fura ƙya koya.........”

      Kuka Hibbah ta fashe da shi da faɗin, “Ummi kin gansa ko. Wlhy nama fasa dan babu inda zanje to”.

     Da farko dariya Ummi da su Yaya Muhammad da suka shigo keyi, sai da sukaga abin nata da gaske ne sai kuma duk jikinsu yay sanyi. Dama su kansu dauriya kawai sukeyi. Dan tun shigowarsu sukaci karo da akwatinan sai zukatansu suka raunana. Suna matukar son Hibbah, gashi aure zai rabasu rana tsaka. Ita kanta Ummi wani lokacin har tambayar kanta take wai miyasa ma ta amince aima Hibbah aure yanzun ne. Itakam bataso a rabata da ɗiyarta. Zuciyarta kan gaya mata su waɗanda ƴayanta maza zasu auro fa? Da ta tuna hakan kuma sai tai shiru ta miƙa wuya.

     Ɗaki Ammar ya wuce yana sharar hawaye, dan dama komai da yakeyi dauriya ce kawai. Da gudu Hibbah ta tashi tabi bayansa ta rungumesa. Sai kawai suka fashe da kuka a tare. Duk yanda su Yaya Usman sukaso daurewa hakan ya gagara, suma sai gasu suna share ƙwallan a kaikaice.  Saurin barin falon Ummi tai, batasan yaya suka ƙare ba sai da ta fito bayan sallar isha'i ta samesu suna kallo ball Hibbah da Ammar na gaddama harda jefama juna filos tamkar basune suka gama shan kuka ba ɗazun.


       Washe gari bayan wucewar su Yaya Muhammad aiki aka miƙa kayan nasu auren gidajen matansu batare da sanin su Abba ba. Dan daga gidan Sheikh Aliy aka ɗauka. Hibbah ce kawai taje aka kai da ita ko ina. Dan haka ranar bataje makaranta ba. Sai da yamma liƙis ta shigo gidan a gajiye, ga ciwon kai. Sama-sama ta gaida Ummi ta shige ɗakinta acewarta zata watsa ruwa.

     Tana fitowa wankan ta tsinkayo muryar Ummi na kwala mata kira.

          “Tanee! Tanee!!”  muryar Ummi dake ƙwala mata kira da ga falo ta cigaba da shiga kunnuwanta. Amsawa tai cikin saka kaya sauri-sauri sanann ta fito. Ganin Ummi zaune tare da Isma'il ya sata ƙalaro fara'ar dole ta yafama kanta. “Uhm su Yaya Isma'il ne yau a gidan namu? Yaushe a gari inji maƙi baƙo?”.

        Guntun murmushi ya saki dai-dai yana ɗagowa ya kalleta. “Auta nifa hausar nan taki cikin hausa na dulmiyar dani da yawa.”

         “Tofa, abinma ƴar zolayace kenan Yaya Isma'il. Ykk ya Abba da Dubai?”.

        “Abba yana lafiya. Nima kuma haka. Dubai kam tana can mun baro musu abinsu, mun dawo ƙasar gado”.

       Dariya Ummi da Hibbah sukai a lokaci guda. Yayinda Ummi ta ɗora da faɗin, “Yau kusan sati kenan inata jajen rashin dawowarka. Ga bikin ƴan uwanka nata matsowa ko faɗa maka ba ai ba”.

      “Biki kuma Ummi? Badai su Yaya Muhammad bane zasu angwance?”.

        “Aiko sune Isma'il, komai yazo ne a ƙurarren lokaci. Su duka huɗun ne insha ALLAH sai Tanee kuma”.

      A take alamar shock ta bayyana saman fuskar Isma'il har Ummi da Hibbah suka lura. Da sauri ya ce, “Ummi Muhibbat kike nufi kowa?”.

        “Eh ita kuwa Isma'il. Muma dai haka abin yazo mana tamkar haɓo”.

         Duk yanda yaso ɓoye ɗacin da ke tattare da muryarsa kasawa yay. “Ummi dama akwai maganar aure akan Muhibbat kenan?”.

          Ummi da yanayin Isma'il ɗin ya raba ma hankali biyu tace, “A'a Isma'il. Cikin kwanakin nan dai aka fara. Da yake kuma ALLAH yasa abin a kusa yake sai gashi har an kammala magana. Dan gaba ɗaya bikin yau saura kwana goma sha uku ne”.

           “A...ALLAH sarki, UBANGIJI ALLAH ya sanya alkairi ya basu zaman lafiya Ummi. Dama zan wuce ne nace bara na leƙoku. Inga bara inje zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan dawo. Ga tsarabarki nan ke da Muhibbat”.

           A yanda yake maganar ne ya saka wutar kan Ummi da Hibbah ɗaukewa. Sukai tsit a falon harya fice basu iya furta komai ba. Sai kallon juna da sukai suka kuma sake maida dubansu ga ƙofar tamkar zasuga Isma'il ɗin tsaye bai tafi ba.

         “Ummi kamarfa ransa ya ɓaci?”.

“Nima abinda ya bani mamaki kenan Tanee. Ko maganar aurenku ce ta ɓata ransa?”.

        “To Ummi mizai bata masa rai anan? Maybe dai akwai abinda ke damunsa daban ba wannan ba”. Hibbah ta ƙare maganar tana sakkowa da jawo ledar daya ce tasunce. Turarrukane a ciki da make-up box ƙarami mai ƙyau. Sai takalmi da jakka suma masu ƙyau kala biyu. Na Ummi da nata.

         Tana tsaka da ƙoɗa ƙyawun kayan Yaya Muhammad ya shigo. Ummi ce kawai ta samu damar masa sannu, Hibbah kam sam hankalinta baya wajensa. Sai da ya kai zaune yake faɗin, “Ummi lafiya kuwa? Miya faru da Isma'il?”.

          “Wlhy ban saniba Muhammad, nima man mamakin yanayin nasa ne ya sani zaman jugum nan.” (gaba daya ta kwashe yanda sukai ta bashi labari).

       “Tofa, anya kuwa Ummi Isma'il ba son Hibbah yake ba?”

    Da sauri Hibbah ta juyo ta kalli Yayan nata. “Yaya so kuma? Ni?”

       “Tabbas auta. Dama zuciyata ta jima tana rayamin Isma'il dan ke yake tare da mu. Dan take-takensa gaba ɗaya sun nuna akwai soyayyarki a zuciyarsa. Shiyyasa naso ace yana nan maganar nan ta taso na aurenkin nan. Koba komai ni hankalina ma zaifi kwanciya da Isma'il ɗin fiye da shi Shuraim ɗin nan. Duk da shima dai babu wani aibu tare da shi dan yau ɗin nanma sai da na sake samun bayanan binciken da na saka akaimin a kansa bayan waɗan can na baya”.

      Nannauyan numfashi Ummi taja, gaba ɗaya zuciyarta ta dagule. Dan harga ALLAH tana jin son Isma'il matsayin siriki a gareta. Sai dai kuma ƙaddara ta rigada ta riga fata. Dan babu ta yadda za'a gyara abinda tun farko aka ɓata. Shima harda laifinsa da bai fito ya nuna ba, a yanzu kuma basu da hurumin rusa maganar Shuraim inba so suke su kasance ƙananun mutane ba kuma.

     Ita dai Hibbah ko a jikinta. Tama cigaba da harkar gabanta ne dan kallon yaya take masa har cikin zuciya.


★★★


     Kwanaki uku Isma'il bai sake dawowa gidanba. Hakan duk sai yabi ya dami Ummi harta ɗauka waya ta kirasa akan tana son ganinsa. Baiko musa ba sai gashi yazo da hantsi. Lokacin su Hibbah duk sun fice sai ita kaɗai.

        Ummi tanada dabaru sosai na iya sarrafa mutum bisa ƙyaƙyƙyawar hanya. Shiyyasa ta tarbiyanci ƴaƴanta da tarbiya mai ƙyau da ke bama kowa mamaki da yaba ƙoƙarin ta. Duk da Isma'il yazo mata ransa a cinkushe cikin hikima da dabarun da ALLAH ya bata ta bi da shi da nasiha. Cikin ƙankanin lokaci sai gashi yayi laushi, ya kuma gane cewar laifinsa ne da yabar zancem a ransa bai furtaba.

      “Ummi nagode matuƙa da gaske. Kiyi haƙuri ban tashi da uwa ba shiyyasa abubuwa da yawa bana ganesu kai tsaye sai sun ƙure min. Idan kuma ba'an fahimtar dani bane haka zanta kallonsu a yanda na ɗauka. Bazan boye miki ba ina matuƙar jin daɗin kasancewa da ke. Kuma ina miki kallo ne irin na uwa wlhy. Shiyyasa kikaga ko yaushe ina nane da ke. ALLAH ya sanya albarka a auren Hibbah na haƙura. Amma tabbas ina sonta da ƙaunarta. Wasu kuma nagartattun halayenki ne da nata suka jani ga hakan abinda ban taɓa tsintar kaina a ciki ba. Amma dan ALLAH koda wataran inaso ki cigaba da tuna hakan. Kuma kamar yanda kika fahimtar dani wanann bazai zama ƙarshen zumincinmu ba. Zan cigaba da kasancewa da ku a koda yaushe tamkar da. Zanje na nema yan uwana su Yaya Muhammad mu cigaba da hidimar biki”.

        “Alhmdllh naji daɗin hakan Isma'il, ALLAH yay maka albarka. Kaima ALLAH ya baka wadda tafi Tanee ɗin”.

     Murmushi ya saki mai sanyi laɓɓansa na ɗan motsawa alamar amsawa. da ga haka ya saki jiki da Ummi suka cigaba da tattaunawa akan hidimar bikin. Bata ɓoye masa zancen barinsu gidan ba da planning ɗinsu akan rusa auren ƴaƴan Abba da yaranta. Shima kansa yaji daɗin haka. Ya kuma tabbatar mata zai bada muhimmiyar gudun mawa. Da ga haka yay mata sallama ya tafi.


*___________________________*


         Alhamdulillahi, akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, shirin biki kam da gaske ya ɗau harama. Dan kuwa baƙi harsun fara sauka a gidan musamman na ɓangaren momy matar Abba. Hakama dangin hajiya mama sun fara sauka. A ɓangaren Ummi ne dai babu ko kare da yazo har yanzu. Ko'a jikinta dan dama batasa rai ba. Mutanen arziƙi ma da zata tara anan a cewarta sun wadaceta.

           A ɓangaren amaren su Yaya Umar na ɓoye har sun jajje sunyi jere a sabon gidansu. yayinda suma anan su hajiya mama suna shirin zuwa suyi nasu jeren na ƴaƴansu a gidajen Hayar da Abban ya kama.

          Itama dai Hibbah kayan nata jeren har sun isa gidanta. Dan kuwa yayunta sun haɗa ƙarfi da ƙarfe da taimakon Isma'il sun mata kaya ƴan gaske na ƴar gata. Dan data ga kayan sai kawai ta fashe da kuka dan daɗi. Ita kanta Ummi da ta gani sai da ta koka a ɓoye. Musamman da ƴan jere suka dawo cike da farin cikin tarbar da suka samu da kuma ƙyawun gidan na Hibbah.

      Hibbah Amarya kuwa da su Zahidah amaren su Yaya Usman Ummi da Mama Jiddah ce ke gyaresu da ingantattun magungunan sanyi harda amaryar Yaya Umar. Sai ingantaccen tsumi da duk ta sami iliminsu da ga Sheikh Aliyn ta (karku manta masanin sirrin magunguna ne😹). Dan hatta maganin sanyin ma shine ya haɗama su Hibbah da kansa. Sai Haɗaɗɗun kayan gyaran fata na dilka da ƙamshi da Mama Maimoon uwargidan malam ke gyaresu da su itama. Ta ko ina Ummi dai ta zama ƴar kallo.


       Gaba ɗaya Hibbah ta tattara batun wasu ƴan sanda da wani master can😏 ta watsar, dan kasancewar su waje guda da su Hafsat ya mantar da ita komai. Iyakarsu susha shaftarsu, kowa idan nata angon ya kirata ta koma gefe tasha soyayya. To ita Hibbah ma bazatace soyayyar take sha ba, dan sam Shuraim bai cika damuwa da kiranta a waya ba. Yafi tura mata text massege na sonjin lafiyarta kai tsaye. Ita kuma jan aji yasa itama bata kiran nasa balle nuna damuwarta da hakan garesa. ko sau ɗaya ma bata taɓa ƙorafi ba.


        ★★★


   A yau laraba aka saka dukkan amaren a lalle. Dan kamar yanda aka saka su Ameerah da Hibbah anan gidansu, haka aka saka su Zahidah a nasu gidajen batare da duk wanda ke zagaye da su yasan su waye angunan ba. An dai san ana biki, hatta da Momy da Hajiya mama sunsani tunda anguwa ɗaya ne layi ɗaya. Sai dai basusan anguna ba basu kuma damu da sani ba tunda ba wani mu'amula mai karfi ce a tsakaninsu ba. Hasalima sun tsanesu saboda suna huɗɗa da Ummi. Ko gidan sukazo aka gamu da ƙyar suke amsa gaisuwarsu.


    Yau akai kamu da ya kayatar matuƙa anan harabar gidan. Dan ƙarya sosai momy ta nuna ma ƙawayenta data tara cike da gida da danginta. Sai dai kuma koda anguna sukazo fili bisa gayyatar da akai musu sai suka ƙare da bama autarsu kulawa ta musamman. Dan har liƙeta sukai da kuɗaɗe sanda masu kiɗan ƙwarya ke bugawa. Nanfa ƙananun magana suka fara tashi, zukatan su Ameerah fal baƙin ciki da takaici. ji suke wata muguwar tsanar Hibbah na sake shigarsu matuƙa, amma dai duk sun danne a zukata bisa huɗubar iyayensu akan shirinsu.

     Oho su Yaya Abubakar ma basusan sunai ba. Su dai kawai burinsu autarsu tayi farin ciki, tafi kuma kowa. Burin nasu kuwa ya cika. Dan ta haska haskawa mai tsayawa a rai duk da ango baizo ba danginsa sunzo ansha shagali da su.


     Washe gari kuma alhamis akai walima da hajiya mama ta ɗauki nauyi😝. Aka gayyato matan Sheikh Aliy sukai wa'azi, yayinda aka ci aka sha kowa yay ɗiff. Gab da magrib aka tashi. Su Ameerah kuma suka dasa nasu fatin su da kawayenau maza da mata a hotel. Babu ango ko ɗaya a wajen, dan su su Yaya Muhammad ma zuwa lokacin suna manne da Umminsu dake ta musu nasiha suna sharar hawaye tamkar ba gida ɗaya zasu cigaba da kasancewa ba. Hibbah kuwa kuka take iya iyawarta harda amai. Da ga ƙarshe kuma sai zazzaɓi ma ya rufe ta. Har sai da Isma'il da yazo kawo drinks da za'ai amfani da shi na ɗaurin aure ya kira family doctor ɗinsu yazo ya dubata. Ana mata allura yay tafiyarsa shi da doctor ɗin.


*_RANA BATA ƘARYA........_*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😂.


*LALLAI YAU AKE TAKUN SAƘAA😖🐒*


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082




*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*




*_Chapter Nineteen_*


...........Kamar yanda suka saka ɗaurin aure bayan sakkowa sallar juma'a su Ummi basu canja ba. Gida ya gama cika da dangin Momy da na Hajiya mama anata hidimar girki. Sai wasu tsiraru da ga abokan arziƙin Ummi na nan anguwa dana nesa.

        Anguna kam suna can a gidan da suka samu aro anan anguwar da abokansu. Sai dai tunda safe sun shigo sun gaida Umminsu. Tare da sake lallashin ƴar ƙanwarsu Hibbah da duk tabi ta takura kanta. Zazzaɓin nata yama sauka tunda safe amma duk ta zama wata kalar tausayi. Magana kaɗan sai ta kama hawaye. Ga ƙawayenta na secondary cike da ɗaki amma duk ta ƙi sakewa. Sai faman shaƙiyanci suke mata ta kasa maida murtani dan bakin ya mutu murus.

          Kusan sha ɗaya wata ƙawar Ummi ta shigo ta sata tashi dole tai wanka. Mai kwalliya ta shigo tai mata dai-dai misali dan da farko ma catai bataso sai da Ummi tai magana. Itama taci gayunta ɗas tamkar wata ƴar talatin. Dan sam Ummi bata da ƙiba, ALLAH yayi mata jiki mai ƙyau, shiyyasa da yawan mutane idan akace itace ta haifa su Yaya Muhammad sukan musa, inba ka nutsu wajen kallon fuskarta ba sai ka ɗauka yayarsu ce kawai.

      Amarya Hibbah ta fito ras abinta, tamkar ka saceta ka gudu. Ƙawayenta nata tsokanarta akan gaskiya ya kamata a ɗauka hoto a turama ango. Banza tai musu dan ita sai ma yanzu ta tuna da wani ango. Tun jiya damuwarta kawai rabuwa da ahalinta batashi take ba. Ga shi tanajin kewar su Zahidah da babu dama suzo nan suma suna gidajen iyayensu.


      A ɓangaren amare su Ameera ma kowacce ta ɗau kwalliya ta gani kasheni, da ka gansu kaga amare kam dan anata zuba iyayi da gwalli. Su barin gidan ma ko'a jikinsu suke jinsa. Ga ƙawayensu sun zagayesu sai taɓara da zancen banza suke zubawa suna sheƙa dariya.


         Ƙarfe sha biyu da kusan kwata anguna suka shigo gidan cikin kwalliyar fararen shaddoji tas iri ɗaya. Hatta da Ammar irin kayan ya saka shima. Idan ba'a faɗa ba sai ka ɗauka shima angon ne. Guɗa mata da ke kai kawon girki a tsakar gida suka shiga musu. Kowa na yaba ƙyawun nasu da yima mahaifinsu addu'a da babu rabon ya ga wannan rana.

         Ummi da ƙawayenta na zaune a falo suka shigo. Tai sagade tana kallonsu idanunta na cika da ƙwalla. Tanaji a ranta inama ace Aliyu na raye wannan rana...... Durƙusawar da sukazo gabanta sukai duka ne ya katse tunaninta. Tasa hannu ta share ƙwallar da suka taru mata a ido tare da kai hannu ta dafa kan Yaya Usman da ke kusa da ita. Sai kawai ta fashe da kuka. Har rige-rigen matsawa suke gabanta kowa ya riƙe hannunta idanunsu na cikowa da ƙwallan suma.

        Sosai abin ya birge mutane ya kuma basu tausayi. Ummi ta shiga kwarara musu addu'oi da sanya albarka ana amsawa da amin. Kafin a kira Hibbah itama mai hoto yay musu. Itama kanta sai da tai hawayen jin daɗin ganin ƴan uwanta kamar ka sacesu ka gudu dan ƙyawun da sukayi. Sai dai tanajin ɗacin kasancewar su Amlah matsayin matansu bayan su Zahidah.

      Suna tsaka da hotunan kira ya shigo wayar Hibba. Tayi ƙoƙarin sharewa aka sake kira. Yaya Muhammad dake kusa da ita ya ɗauka wayar ya duba. Ganin Shuraim ke kiran nata ne ya sashi hararta yana miƙa mata. “Auta bana son rashin ji fa. Maza kije da ga waje sai ki ɗaga”.

      Kanta kawai ta ɗaga masa. Tare da tashi tabi ta kitchen ɗinsu ta zagaya baya domin kiran Shuraim ɗin......

      “Yauwa A.G zamu iya magana yanzu na fito”.

    Muryar Abba ta saka Hibbah saurin dakatawa a ƴar barandar kitchen ɗin nasu. Abu biyu ne yaja hankalinta ga Abban. Na farko yanda yake tsaye a laɓe wajen tamkar wani tsohon munafuki, na biyu sunan A.G da taji ya ambata. Wanda inhar hasashenta yayi dai-dai sunan dattijon jami'in nan haka yake shima A.G. Maganar Abba ta sake katse tunaninta.

          “A.G nawa, kasan mutunuyar taka tana nan tana jira kazo ka saceni ni da duk masu hannu a ɗaurama yayunta aure da ƴaƴana.”

        Batajin mi ake faɗa da ga can, sai dai yanda Abba ya tuntsure da dariya ne ya saka zuciyarta tsargawa duk da batasan wane A.G ɗin ba. Abba ya ciga da faɗin, “Inaga zan fito yanzun nan kuwa insha ALLAH, dama munyi shirin wucewa wajen ɗaurin auren ne. To amma su zan barsu su wuce kai kuma mu haɗu a gidan hutuna muyi magana”.

       Gaba ɗaya jikin Hibbah rawa yake, tai saurin leka bayanta. Ganin hankalin yayunta da su Ummi duk yana kan yin hoton ya sata saurin jan ƙofar kitchen ɗin tayo waje. Bayan Abba da ya bar wajen tabi da sauri. Kasancewar da sanda yake tafiya saboda kafarsa da bata gama warkewa ba yasa Hibbah cin masa, sai dai a sace take binsa yanda bazai gane ba. Suna gab da fita ta ɓarauniyar ƙofar da ke bayan ɗakunan su Abba taci karo da hijjab ɗin wata mata dake alwala a fanfo. Dauka tai ta saka, tai saurin bin ta gate ta fice batare da an ganeta ba dan harda nikaf. Cikin sa'a ta cimma Abbah ta baya saboda harda gudu ta haɗa duk da tarin mutane dake shirin tafiya ɗaurin aure a ƙofar gidan nasu. Ganin Abban ya shiga wata baƙar mota dake fake a barauniyar ƙofar tasu itama tai azamar tare mai napep.

        “Malam dan ALLAH motar can nakeso kabi, amma banason ya fahimci shi ɗin muke bi Please”.

        “Babu damuwa hajiya, amma kenan kuɗinki zasu kasance masu nauyi fa?”.

       Batare da tamaji abinda yace ba tace, “Babu damuwa muje”.

      Kasancewar mai napep da alama kwararren matuki ne ya dinga bin Abba abaya ta yanda bazai iya fahimta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso wata anguwa mai ƙarancin hayaniyar mutane. Da alama sabuwar anguwa ce, dan ga uncompleted buildings nan bar-katai. Sai dai kasancewar inda Abba ya faka motar a farko-fatkon anguwar ne sai ya zama wajen yayi ɗan rukunin gidajen da aka kammala. Tun a titin ta sauka. Ta dubi mai napep ɗin cikin raba hankalinta biyu. “Dan ALLAH ka jirani nan bazan jimaba zan fito. na maka alƙawarin ko nawa ka bukata zan baka”.

     Cikin farin ciki da tunanin yayi babban kamu yace, “Babu damuwa hajjaju a fito lafiya”.

      Gaba Hibba tai batare data amsashi ba. Ta bi ta bayan gidan inda take addu'a da fatan samun koda karamar hanya ce da zata shiga gidan. Dan Abba na shigewa aka rufe gate ɗin. Sam babu wani hanya data samu, dan haka tai azamar sake dawowa ta gaban gidan zuciyarta na ayyana mata wata dabara. Gate ɗin ta ƙwanƙwasa kaɗan tana waige-waigen bayanta da addu'ar dacewa. Batare da zaton anjita ba taji an buɗe gate ɗin. Tai saurin kallon wajen tana jan numfashi. “Barka da rana”. Ta faɗa cikin matukar kashe murya.

     Kallon sama da ƙasa mai gadin yay mata, kafin yace wani abu tai azamar faɗin, “Ni baƙuwar Alhaji ce”.

         Maigadi yay ɗan shiru alamar tunani. kafin yace, “Amma hajjaju idan Alhaji zaiyi baƙuwa yakan sanar min, yanzu ko bai faɗa ba ya shige duk da naga kamar cikin sauri yake”.

       Cikin ƙara ƙasa da murya Hibba tace, “Ka bama kanka amsa kenan, saurin nasane yasa bai faɗa maka ba inaga. Amma bara na kira maka shi zai fi.....”

       Da sauri maigadi yace, “A'a hajiya bama sai anyi haka ba. Nasan inba da sanin Alhaji ba babu wani mahaluki kam da zaizo nan. Bismillah”.

     Ya kai karshen maganar yana matsawa ya bata hanya. Wani shegen ajiyar zuciya Hibba taja tana ƙoƙarin haɗiye busashen yawun da ya daskare mata a baki tana ƙoƙarin shigewa.

      “A fito lafiya hajjajuuu”.

Maigadin ya faɗa cike da shaƙiyanci.


★★★★


        A ɓangaren su Yaya Muhammad kam sun cigaba da hotonsu da tunanin Hibbah nacan na waya da Shuraim ne. Sunyi hotuna sosai da jama'ar da ke a sashen na Ummi kafin su fito domin tafiya massallaci karsu rasa salla. Kusan tare suka fito da gayyar su Kawu Hannafi da ƙannen Momy da yayunta.

        Cikin tsari gayyar motocin ɗaurin aure suka bar anguwar batare da kowa ya farga babu Abba a tafiyar ba. Yayinda aka bar mata na cigaba da himar abinci da shagali a cikin gida. Sun isa massallacin juma'a gab da za'a fara khuɗuba. Kamar yanda aka tanadar musu gaba saboda za'a ɗaura aure duk aka basu hanya suka shige. Sai da suka nutsu waje guda Sheikh Aliy ya fara gabatar da khuɗuba mai taɓa zuciya akan kashe-kashen dake faruwa a ƙasar nan na zalunci. Tare da jan hankalin hukuma da gwamnati akan sake jajircewa. Hakama jama'ar gari ba zama zasuyi kallon gwamnati da hukumaba suma. Dolene a miƙe da addu'a kuma kowa ya zama jami'in sirri akan abinda bai gamsu da shi ba. Sosai khuɗuba tai tasiri a zukatan bayin ALLAH. Da ga haka aka fara gabatar da sallar Juma'a.

       Kasancewar mutane sun san da ɗaure-ɗauren aure bayan idar da salla babu wanda yay yunƙurin tafiya. Sai lokacin su kawu Bello suka fahimci babu Abba tare da su. Nan fa aka shiga tambayar juna, sai dai kowa yana cewa bai gansa ba maybe bai ƙaraso ba..

       Miƙewa ƙanin Momy yay ya fita a taron da zummar neman wayar Abba suji ko ina ya tsaya.....


★★★★★


         Addu'a Hibbah ke karantowa tana ƙara kutsa kanta cikin gidan da batasan kansa ba. Sai da ta ga ta bacema idon maigadin sanann ta ɗan dakata ta sauke numfashi. Haggu da damanta ta kalla ko zataga ƙofar shiga. Cikin sa'a idonta ya hango mata window. Da sauri ta nufi windown tana addu'ar ya kasance inda zata iya hango su Abba.

     A rufe windown take, dan haka tai gaba cikin takaici da fatan samun mafita a gaba. Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke saboda cin karo da ƙofar kitchen irin ta bayan nan. Ta kama handle ɗin ta murɗa a hankali cikin sa'a ta buɗe. Wani irin daɗi ne ya baibayeta kamar ta tashi sama. kitchen ne babba, komai na amfani akwai, da alama ma ana amfanin da shi, dan yanzu hakama ga alamun anyi girki a ciki. Gaba tai zuwa ga ainahin ƙofar kitchen ɗin ta cikin falo, tai saurin maida kanta baya saboda ganin Abba zaune tare da wani mutum a dining ɗin abinci jere tamkar masu shirya fati.

      “Ina fatan kukun nan taka ta fita ko?”.

      Mutum da ke tare da Abban ya faɗa. Ƴar dariya Abba yayi, cikin salon narke murya tamkar wanda ke gaban mace yace, “Karka damu nace taje waje ta zauna. Bakuma zata shigo ba sai na bata umarni kaima ka sani”.

      “Hakane baƙon ya faɗa yana sumbatar hannun Abban”.

    Wani irin mugun faɗuwa gaban Hibbah yay. Tai saurin kauda abinda zuciyarta ke bijiro mata ta sake maida hankali akansu.

       “A.G kasan a ƙage nake da son jin abinda ke bakinka, duk da kuwa kwana biyu ina tare da kewar harka saboda jiyya data cikuykuye rayuwata. Amma soon zan dawo, fatana a ɗaura auren nan yau cikamakin bukatuna su sake shiga tafin hannuna sannan na dawo. Kaima kasan banida wani buri da ya wuce dukiyar ƴaƴan Aliyu cigaba da kasancewa a hannuna. Hakan kuma naga bazata taɓa tabbata ba har sai na aura musu ƴaƴana, sannan na bisu ɗaya bayan ɗaya na halaka su. Dan duk wadda ta fara samun ciki a cikin ƴaƴana to mijinta ne zai fara baƙuntar lahira. Ko ƴaƴan nawa da mahaifiyata basu san da shirin nan nawa ba. Sai na gama da su kaf sannan na ɗinke bakin zaren *_TAKUN SAAƘA_* ta da Asiya. Wadda ubanta ne ya fara sarƙata akan mugun bugun da yay mini tun tana ƴar shekara goma sha ɗaya kacal a duniya.”

      Dariya A.G yayi da faɗin, “Baka da dama Gwarzo. Wato kai sam baka manta bashin gaba.”

       “Har abada kuwa A.G. Naso fanshewa akan budurcinta hakan ya gagara, abin takaici da baƙin ciki ta sake hawa kaina, aka aurama Yayana uwa ɗaya uba ɗaya shi ya mora bayan na ƙwallafa rai. Tazo ta katantane komai, duk hanyar dana ɓullo akan wasoson dukiyarsa sai tabi ta toshe ta hanyar fargar da shi. Shiyyasa yanzu daya mutu bayan ya tara musu na shirya hawa kan dukiyar, sai dai nafison nacita a gaɓar da Asiya zatafi jin ciwo da raɗaɗi, kamar yanda na ɗauki tsahon shekaru ina jin ciwo da raɗaɗin abubuwa masu yawa a kanta. Wannan dalilin ya sani yin dakon shekaru goma sha tara ina haƙurin cigaba da juyata tana haɓaka har zuwa yanzu da wasan zai fara. Sai na ɗan-ɗana-ma Asiya azabar ciwon mutuwar ƴaƴanta ɗaya bayan ɗaya a tafin hannunta”.

       “Anya kuwa hakan ta kasance Gwarzo? Dan wannan ƙaramar ƴar tata ta fi sauran yaran tsaurin ido da rashin tsoro. Shiyyasa nake ganin wautarka na canja ɗanka da zai aureta zuwa wani daban, duk da nasan wanda ka canja ɗin yafi ɗanka kwaƙwalwa da wayo da hatsabibanci. Kagafa shekararta sha takwas kacal amma take da dabarar ƙulla agreement da ƴan sanda akan a ƙwamusheka ranar aurensu domin yayunta su kuɓuta daga auren ƴaƴan naka. Ina jimaka tsoron wannan yarinyar fiye da kowa cikin ƴaƴan matarka. Koda yake nasan Master bazai taɓa yarda da mace ba”

        “Humm kai kasan tun randa ka bani labarin nan da mamakin yarinyar nan nake kwana nake tashi a raina. Yanzu haka fa tana can tana jiran ku tattareni kenan fa?. Batasan kai ɗin mutumina bane.”

     Atare suka kwashe da dariya. Yayinda Hibbah dake makale tana saurarensu ta daskare a tsaye, dan zuwa yanzu ta gama fahimtar dattijon jami'in nan ne dai A.G da ya sakata bibiyar Master.......

     Maganar Abba ta katse tunaninta.

  “Karka damu ita na gama da lamarinta kaima ka sani. Shi wanann yaron dana kawo ya canji Junaidu dan ya aureta kamar yanda ka faɗa yafi Junaid hatsabibanci kaima ka sani, sannan a tafin hannunmu yake a kuma gaɓar da muke more ƙuruciyarsa. Ana gama ɗaura auren zanbi shawararka na biya mata kuɗin karatun tafiya China kamar yanda take buri, da wanann damar zanyi amfani na ɓadda rayuwarta. Dan rashin nata ne zai fara karya rayuwarsu saboda tsananin son da suke mata matsiyatan sai kace ƴar gwal. Ku kuma da ya ɓaddata zaku amfani da wannan damar ne ku fito ku nunama duniya shi wannan Master ɗin da kuke nema ruwa a jallone ya sace ta. Kaga shikenan babu mai zargin Halilu Hamza gwarzo kenan ko”.

    Ya kare maganar da shaƙiyancin da ya sakasu sake kecewa da dariya. Jikin Hibbah ne ya kama rawa. Tai saurin kai hannu ta toshe bakinta jin kuka zai kufce mata. Dai dai nan A.G ke faɗin, “Gaskiya mun iya maida mutane wawaye. Kowa ya saki baki kullum muna aikin tukuru na son kamo Master, basu san shi kansa Master ɗin mune muka ƙirƙiresa ba. Yana gama tattare mana kuɗaɗen shima zamu ɓaddashi a doron ƙasar baki ɗaya, mu kuma cigaba da amfani da rigar jami'an tsaro wajen tsula tsiyarmu. Yayinda duk wanda ya fito da niyyar aikin gaskiya mu ɓadda banza, dan mu ba gyaran kasarne gabanmu ba. Wanda suke gaba damu kuma mu cigaba da kwantar musu kai muna nuna mun fisu san ƙasar da cigabanta, da tabbatar musu aiki muke tuƙuru. Kaga mun toshe ko ina kenan”.

      Dariya suka kuma kwashewa da shi, har sai da kira ya shigo wayar Abba sanann suka tsagaita. Ya miƙe yana faɗin, “Alhaji Alu ne ke kira, ina kyautata zaton suna wajen ɗaurin aure tashi muje dan nasan ana gab da ɗaurawa kar ayi babu mu.”

     Da sauri A.G ya riƙo hannun Abba cikin marairaicewa yake faɗin, “Gaskiya ina da bukata, shine ma dalilin da yasa na kiraka nan. Ka barsu kawai su ɗaura tunda ko baka akwai masu amsa da bayarwa, ni kuma ka ragemin zafi anan. Dan kwana biyun nan matasan ma da muke ɗan samu mu taushe wa'azin malaman nan ya fara tasiri a ransu gudunmu sukeyi shegun.” Abba ya buɗe baki zaiyi magana A.G ya sake marairaice masa da rungumosa jikinsa cike da salon shaiɗanci da bushewar zuciya irin ta masu fasadi da rashin tsoron ALLAH a ban ƙasa😭. (Wa'iyazubillah. ALLAH mun tuba ka yafemu🙏🏻😭😭).


(Ya ALLAH ka gafarta mana badan halinmu ba, ka kare mana zuri'armu da mazanmu da ƴan uwanmu da matasan al'ummar musulmi baki ɗaya😭🙏🏻. Abba ɗan homo, A.G ɗan homo, da ire-irensu abokan ƙazantarsu da yawa dake lullube da rigunan mutunci suna cin dunduniyar al'umma da addini. Kuga dai A.G, ya shige cikin jami'an tsaronmu jajirtattu yana tsula tsiyarsa ta hanyar ruguza shirye-shiryensu batare da sun sani ba. Shin kamar yanda ya faɗa Master yaronsa ne? Su Master kema aiki?. Mu cigaba da kasancewa a cin TAKUN SAAƘA domin jin yaya take ne?)

      

        Gaba ɗaya jikin Hibbah rawa yake yi, ta shiga tafiya da baya-baya zuciyarta na tsitstsinkewa tamkar zata faɗo waje. Wani irin duhu-duhu idanunta suka farayi, abinda takeji a labari shine yau a zahirin rayuwa take gani ga ƙanin mahaifinta da idan aka tsaga jininsa za'a ga nata a ciki. Innalillahi wa inna-ilaihirraji'u. (Dole ne kafin a daura auren nan tayi wani abu) wannan tunanin ya sakata zabura ta fito a guje. Kotakan maigadi dake zaune yana sauraren redio bataiba ta buɗe gate ta fice. Saurin miƙewa yay yana tambayarta lafiya?. Ina batama san yanai ba. Yay saurin bin bayanta wajen, sai dai kafinma ya leƙo ta kusa kaiwa titi inda take tsammanin mai napep ɗin nan na jiranta.

       Waige-waige ta shigayi dan babu mai napep babu alamarsa. Cikin hakki da rawar jiki ta ciro wayarta dake maƙale cikin zani ta hau laluben wayar Yaya Muhammad. Harta katse bai ɗaga ba. Ta sake kira nan ma bai ɗaga ba. Ta maida akalar kiran nata kan Yaya Abubakar tana fassewa da kuka. Sai dai shima harta katse bai ɗaga ɗin ba.

        “Yaya ku ɗaga dan ALLAH”. Ta faɗa a kiɗime tana zubewa ƙasa da sakin wani kuka mai ban tausayi. Tunanin kiran Ammar ne yazo mata a zuciya. Cikin sa'a kuwa ya ɗaga a bugu biyu, sai dai batajinsa sosai sai tsananin hayaniyar ƴan ɗaurin aure. Da ga can shima sai faman faɗin, “Hello! hello! Auta bana jinki wlhy, ki yi haƙuri zan kiraki za'a fara ɗaura auren ne”.

    Kafin tace wani abu ya yanke wayar ƙit. Daga wayar tai zata dasa da kasa sai kuma ta fasa. Tai azamar yage niƙaf ɗin fuskarta ta jefar da tunanin fara gudu tabar cikin anguwar kozata sami abun hawa. Inda rabo sai ta isa massalacin kafin a fara ɗaura auren.

        

      ★★


   Matashin saurayin da ke can baya kaɗan da Hibbah cikin wata farar mota ya gyara zaman abinda ke kunnensa, cike da girmamawa yace, “Boss ta fito. da alama abin hawa kuma take nema, tunda na kaɗa mai napep ɗin da ya kawotan”.

      Bansan amsar da aka bashi ba da ga can, ya dai gyaɗa kansa cikin ƙara bama wanda yake maganar da shi girma, tamkar yana gabansa ya sake faɗin. “Yes Master. Insha ALLAH”. Da ga haka yay ma motar key tare da harbata kan titin ya nufi Hibbah da ke tsaka da tattare hijjabi da alama gudun da ta yankema zuciyarta shawara take shiryamawa.

         Sai dai jin tamkar tahowar mota a bayanta ya sata sauri juyowa ga titin tana ƙoƙarin yin alamar tsaidawa. Bai tsaya ba sai da ya ɗan gota ta sannan ya dawo da baya. Yana tsayawa ko tunanin taga waye bataiba ta buɗe murfin ta shiga baya. “Bawan ALLAH dan ALLAH babban masallacin juma'a na Sheikh Aliy Maina zaka kaini, ka taimakeni kayi sauri na roƙeka dan ALLAH.”

        Jin shiru bai amsata ba bai kuma tada motar ba ya sakata cigaba da magana cikin tsumar jiki da ƙaguwa. “Malam dan ALLAH ka taimakeni, wannan ita kaɗaice damar da nake da ita ta ƙuɓutar da ƴan uwana da ni kaina. Tana kufcewa mun faɗa gararin rayuwa”.

        Yanzun ma komai bai ceba. Sai handkerchief ɗin da ke saman cinyarsa ya ɗauka ya jefa mata a kan fuska. Hannu tasa ta kaɗe handkerchief ɗin da faɗin, “Malam wane irin wulaƙanci ne haka? Minene wannan ka.........”

      Ta kasa ƙarasa abinda take shirin faɗa ɗin saboda duhu da ya mamaye ganinta baki ɗaya. Tai ƙoƙarin fisgo numfashin da ke san kufce mata tana kai hannu bisa ƙofar da laluben neman sa'ar buɗewa. Sai dai ina abinda ke jikin handkerchief ɗin ya gama tasiri a cikin jikinta, tai baya jikin kujerar yaraf tamkar wadda aka zarema rai.

         Sassanyan numfashi Habib ya sauke yana mai ƙoƙarin hana kansa yimata kallon ƙurulla ta cikin mirror ɗin gaban motar ko dan kima da darajar wanda ya sakashi ɗakkotan. Ya ɗan murmusa yana ma motar key tare da harbata kan titi............✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azbazb


_________________________


*_Chapter Twenty_*


.............A can wajen ɗaurin aure kuwa babu jimawa ƙanin Momy ya dawo. Ta gefen Sheikh Aliy yaɗan ranƙwafo yana magana a hankali cike da alamar ruɗani. “ALLAH ya gafarta malam akwai matsala fa. Na kira Alhaji Halilu yana faɗa min wai a jirasa kar a ɗaura yana zuwa akwai matsala”.

        Sheikh Aliy da ke saurarensa ya ɗan juyo ya dubesa cike da nazari, dan haka kawai sai yaga tamkar ba'a cikin hayyacinsa yake ba, saɓanin ɗazun da ya fita kiran Abba. Fahimtar hakan da Garba yay ne ya sashi sauri gyaɗa kansa cikin son kauda ma malam shakku. Ya sake buɗe murya da ƙyau yana satar kallon na kusa da shi daya ɗaura masa bindiga a kan gefen cikinsa ta cikin malun-malun . “Inaga fa akwai wani abune da bamu sani ba game da su yaran nan. Dan ƴar uwata ma ta kirani akan a dakata”.

        Cike da wasiwasi Sheikh Aliy yace, “To sai dai mu dakata da su na ɓangarensu ɗin, bara a ɗaura wannan. Idan ya iso kafin a kammala kaga sai muji ba'asi ko?”.

         Garba da ke ta faman sinne kai ƙasa wata irin mahaukaciyar zufa na cigaba da tsatstsafo masa ya gyaɗa kai da sauri. Gaba ɗaya jikinsa rawa yake zuciyarsa tamkar zata tsinke dan firgici. Tabbas da yasan abinda zaiyi gamo da shi kenan idan ya tashi kiran Abba da bai tashinba ya kirasa anan gaban su Sheikh Aliyn.

        Su Sheikh Aliy da basu fahimci halin da Garba ke a ciki ba babu ɓata lokaci suka fara gabatar da ɗaurin aure. An fara ɗaura na Yaya Muhammad da ɗiyar Sheikh Aliyu mai suna Maimunatu, sai Yaya Abubakar da Zahidah. Yaya Umar da tasa amaryar mai suna Farida. Sai yaya Usman da Hafsat. Yayinda Muhibbat Aliyu Hamza Gwarzo da angonta Muhammad Shuraim Aliyu suka kasance a ƙarshe.

        Kowa yasha matuƙar mamakin jin yanda al'amarin ya canja. Musamman abokan Abba da danginsu irinsu Kawu Bello. Cikin yanayin shiga ruɗani Kawu Hannafi yace, “ALLAH gafarta malam yaya akai hakan ta faru?. Abinda mukai tunani ba shine muka gani ba mu anan?”.

      Sheikh Aliy da ya dago ya dubesa cike da kamala da sanin darajar kai yace, “Eh lallai an samu tangarɗa ne a tsarin, amma tun farko a haka yake dama. Gaba ɗaya anguna za'a aura musu mataye bib-biyu ne kamar yanda na sani, idan ka cire Muhammad Shuraim mai auran Muhibbat kawai. To sai kuma na samu bayani da ga ɗan uwanku ga shinan.”

     Ya ƙare maganar da nuna musu Garba da shi kaɗai yasan a halin bala'in da yake ciki. Da ƙyar ya haɗiye bushashshen yawun da ya tokare maƙoshinsa tare da ɗan duban inda Shuraim ya ke zaune. Sai dai abinda zai baka mamaki shi Shuraim ɗin ma bashi yake kallo ba. Hankalinsa ma baki ɗaya yana kan gaisuwa da mutane. Ya ɗan muskuta da duban na kusa da shi a kaikaice kafin ya fara jawabi tamkar zai fashe da kuka a ƙasan zuciyarsa. “Eh na kira Alhaji Halilu ne saboda rashin isowarsa akan lokaci, to to shine yake min bayanin a dakata da ɗaura auren ƴaƴan wajen nasa yana zuwa akwai da... Da damuwa”.

        Damuwa?.

Suka haɗa baki kusan tare wajen tambaya. Kai kawai ya gyaɗa musu yana kai hannu ya shafe zufar da ke tsatstsafo masa a goshi.

        Tsofo mai furfura da ke amsa sunan ƙanin Hajiya mama ya mike a fusace. “Wanann ai zancen wofi ne. Anya kuwa Halilu na cikin hankalinsa. Kunga ku tashi muje gidan sai muji ba'asin wannan lalatar da ga ina ta fito haka ne?”.

        Garba ne farkon mikewa kafin kowa. Cikin rawar jiki ya shiga kutsawa tsakkiyar mutane domin samun damar gujema Idris. Shima ɗin bai bisa ba, sai wani shegen murmushin ƙeta da ya saki a kaikaice yay salute ɗin sauran ƴan uwansa da ke cikin taron a maban-banta waje.

         

      To su dai sauran mutane da basusan mike faruwa ba tuni sun mimmiƙe suna mai mikama angunan da suma suke a daskare da tunanin mike faruwa? hannu da tayasu murna. Cikin yaƙe kawai su Yaya Muhammad ke amsa musu. Dan tabbas sun shiga matsanancin ruɗani da wannan lamari. Tabbas basa tunanin Abba zai janye ɗaurin auren nan babu gaira babu dalili cikin sauƙi haka. A kuma shirin Ummi da Sheikh Aliy babu zancen ruguje auren. Dama sun shirya cewar za'a ɗaura auren, za kuma su zauna da matan bibbiyu. Da ga karshe su ginama Abba gadar zaren amfani da yaran wajen ganin dukiyarsu ta dawo hannayensu. Amma ta yaya Abba zai janye auren a wannan ƙurarren lokacin bayan sun san harda shi aka fito zuwa wajen ɗaurin auren ma.

          Duk yanda sukaso son tsayawa su gaisa da ƴan uwa da abokan arziki da suka taru dan tayasu murna hakan ya gagara. Dole suka kwashi tawagarsu suka nufi gida kamar yanda su Kawu Bellon sukayi.

          Wani mugun murmushi Musbahu ya saki lokacin da tawagar su Kawu Bello ke rige-rigen shiga motoci domin tafiya gida. Hannu ya kai bisa kunnensa ya gyara abinda ke maƙale, kafin ya fara magana cike da girmamawa. Yanda yake magana  hankali ne yasa babu mai jinsa, sai jinjina kansa da yayi tayi da kai  dubansa ga Zaidu da ke facing nashi. Da idanu yay masa alamar ya bi bayansu. Da alama yayi hakanne bisa umarnin wanda yake wayar da shi.

       Cikin masa jinjina Zaidu ya kaɗa kai tare da saurin buɗe motar gefensa ya shige ya rufama su Yaya Muhammad da suka wuce a ƙarshe baya.

        Shima janye jikinsa yay da ga cikin mutane yana yima sauran alama cikin inkiya. Motocin da duk sukazo a cikinsu suka shishshiga. Da sauri shima Rabi'u da ya tuƙo Musbahu da ke amsa sunan Shuraim a fuska ya buɗe masa motar da sukazo. Duk wanda ya ga a yanda suka bar massallacin zai ɗauka suma sunbi bayan su Yaya Muhammad ne. Sai dai sam ba haka bane. Dan suna hawa titi duk suka rarrabu.

       Rabi'u da ke ƙara gudun motar yace, “Musbahu kira Habib mu haɗu a roundabout”.

         Musbahu na ƙoƙarin zare malum-malum ɗin jikinsa ya amsa da faɗin, “Okay ka ƙara gudu mu samesu muma, dan Master yace karmu ɓata lokaci”. Yay maganar yana ƙoƙarin kiran Habib ɗin da ke can tare da Hibbah, wadda har zuwa yanzun a cikin sumar abinda suka shaƙa mata take.

        Musbahu ya ajiye wayar da kallon  Rabi'u ta mirror. “Insha ALLAHU zamu isa a tare dan shima yana hanya”.

       Kai Rabi'u ya jinjina masa yana cigaba da tuƙinsa. Yayinda Musbahu ya kuma shiga ƙokarin kiran waya again. Ana ɗagawa daga can ya fara magana cikin tattaro nutsuwarsa. “Master komai ya kammala gamu nan a hanya. Kamar yanda kace kuma Zaidu ya bisu can”. Ya ɗanyi shiru yana sauraren mi ake faɗi da ga can, kafin ya sake faɗin, “Okay sir” cikin girmamawa tamkar yana  gabansa.

       Yana ajiye wayar Rabi'u ya fara dariya. “Angon bogi sai ka cire facemask ɗin tunda mun baro wajen”. Dariya shima Musbahu ya sanya da kai hannu yana ƙoƙarin zame facemask ɗin. “Ai ka bari kawai ɗan uwa. A kullum al'amarin Master ƙara tsoratani yake. Shi wannan auren kuma ko miye manufarsa? Oho. Kaga dai komai ya tafi tamkar yanda ya tsara. Yarinyarnan ta saka kanta a ramin *Damisa*”.

        “Tsundum ma kuwa. Sai dai ALLAH Musbahu har cikin raina ina addu'ar ALLAH yasa mun sami aunty ke nan har abada. Tunda kaga tunda muke bai taɓa saka mace a cikin lamarinsa ba, koda tai masa laifi ne sai dai ya hukuntata ya barta a inda ya ganta. Amma wannan harda su aure”.

       “Ai ni kaina al'amarin na ɗauremin kai. Sai dai kasan shi mutum ne tamkar hawainiya, baka isa gane launin da yake sara ba. ALLAH dai ya ƙarama Master mu lafiya da nisan kwana”.

      “Amin ya Rabbi” Rabi'u ya faɗa dai-dai suna isowa roundabout. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gane junansu. Gefen titi suka gangara bayan sun shanye roundabout ɗin. Su Idris da ke a sauran motocin suka firfito suka shiga inda su Musbahu suke. Yayinda Habib yake tare da Hibba shi kaɗai. Nan suka bar motocin da su Salis ɗin suke ciki da suka tafi da mota biyu kacal.


★★★★★


        A ɓangaren abokan Abba suma abin dai ya basu mamaki, dan da yawansu sun san wanann aurene na manufa mai muhimmanci ga rayuwar Abban. Musamman ma abokan shiɗancinsu su Alhaji Alu. Gashi tun kiran da Alhaji Alu ɗin yay masa bai daga ba kowama bai sake samun lambar tashi ba. Sai lamba busy ake nuna musu.

      Ran Alhaji Alu ya ɓaci matuƙa, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tunanin kodai ba lafiya ba?. Dan shi kam yasan Abba tamkar yunwar cikinsa. Hasalima shine wanda ya sakashi a harkar Homo tun farkon zuwansa garin. Dan haka yasan sirrinkan abubuwa masu yawan gaske na Abban.

       “Yauwa ga ɗayan layinsa ya shiga”.

     Cewar Alhaji Balele abokin shaidancin su Abban shima.

       Gaba ɗaya su Alhaji Alu suka zuba masa ido dai-dai shi kuma yana saka wayar a kunne kasancewar an ɗaga. Cikin nishin sheɗancin da Abba suke tsaka da aikatawa shi da A.G ya ɗaga wayar da ƙyar yana kaiwa kunnensa.

       Cikin suɓutar baki da takaicin kishi Alhaji Balele ya ce, “Iyee. Wato kai kana can akan wani ana nan ana dama fura akanka. Halan daɗin abinda kakeyi ne ya sakaka janye ɗaurin auren ƴaƴanka bayan ka taramu anan tamkar wasu marasa aikinyi Alhaji Halilu!!”.

       A wani irin firgici da dukan zuciyar Abba da maganar Alhaji Balele tayi ya sakashi hankaɗa A.G gaba yana janye jikinsa a nashi da faɗin, “What?!, Alhaji Balele mi kake faɗa haka ne?”.

      Tsaki Alhaji Balele yaja tare da yanke wayar. Hakan ya saka Abba sake rikicewa ya ingije A.G da ke ƙoƙarin sake ruƙosa. Wandonsa ya fisga a firgice yana ƙoƙarin sakawa.

       “Alhaji Halilu wai miye haka?”.

       “Bazaka gane ba A.G.”

Abba ya faɗa yana fincikar tissue ya goge jikinsa tare da ƙarasa saka wandonsa. Sandunan da ke taimaka masa a tafiya ya ɗauka cikin rawar jiki da tsallen da zuciyarsa keyi a ƙirji ya fice.

      Wani irin wawan tsaki A.G ya ja cike da tsantsar takaici yana raka bayan Abba da ke tafiya da ɗangyashi da harara. Ina Abba baima san yanai ba. Dan gaba ɗaya a birkice yake da jin bayanan Alhaji Alu. babu wanda yake zuwa masa cikin ido sai Hibbah da labarin da A.G ya basa akan Hibbah dama tayi agreement da su akan su kamashi da duk mai hannu a ɗaurin auren. Inhar abinda yaji da ga bakin Alhaji Balele gaskiyane kenan matsiyaciyar yarinyarnan bada Jami'an tsaro kawai ta shirya hakanba? Ko kuwa ta fahimci A.G wasa zaiyi da hankalinta shiyyasa ta canja salo. Su suna mata kallon ƙaramar yarinya shakatafi ashe ba haka bane sam, sune takema kallon shakatafin.

         Tun fitowar Abban maigadi ya fahimci babu lafiya, musamman da ba jimawa yay da gama reren gudun bin matar ɗazun ba. ya mike zaram tare da nufar gate danya buɗe ganin mota ya nufa shima. A wani irin mahaukacin gudu Abba ya fice a gidan..............✍


     

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*za




*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_Chapter Twenty one_*


............A matuƙar hargitse Abba ya samu gidan, da ƙyar ya iya kutsa kai ya isa ga su Hajiya mama da Garba kema bayanin yanda akayi. Saboda labarin yanda ɗaurin auren ya kasance na faruwa Hajiya mama ta nufi sashen Ummi a hargitse zata fara zubar da tujara Garban ya dakatar da su.

        “Sam ba laifin Asiya bane. Dan a wannan gaɓar tafi kowa cancantar aima jaje, a kuma tausaya mata.”

        A fusace Hajiya mama ta juyi garesa kasancewar ɗa ne a gareta. dan kuwa ɗan ƙanwarta ne. “Garba har yaushe kasan makircin Asiya? da shaiɗancinta da zakayi ƙoƙarin kareta akan abinda yake zahiri. Ni dama nasan shurun da tai da yarda da wannan auren bana arziƙi baneba. To wlhy yau ɗin nan......”

      “Inna ku saurareni”. Garba ya katse hajiya mama. A dai-dai lokacin kuma Abba ya iso da ƙyar garesu, dan illahirin ƙafarsa rawa ma take tamkar karayar tasa na neman dawowa sabuwa ne.

        Garba ya cigaba da faɗin, “Sam ba laifin Asiya bane. Dan ba kowa ne ya canja ɗaurin auren nan ba sai shi yaron da ya auri ita Muhhibatu.

        Cikin matuƙar mamaki hajiya mama ta ce,“Shi Shuraim ɗinne ya canja ɗaurin auren? To a dalilin mi zaiyi hakan?”.

        “Wlhy Inna nima ban saniba. Sai dai gaskiya kunyi ganganci haɗa auren yarinyar nan da yaron. Dan hatsabibin mutumne fiye da hasashen mai hankali. Na tabbatar da hakan da idanun. Shine ya hanani kiran Yaya Halilu. Ya tsaramin abinda naje na sanarma Sheikh Aliy. Ya tsoratani da inhar banyi yanda yake so ba zai kasheni. Ya nunamin mutanensa da ke a kowace kusurwa na cikin massallacin, wanda alama kawai zai musu numfashin duk wanda ke cikin massallacin ya dakata da aiki. Na tsorata matuƙa, dan nasan zai iya aikata abinda yafi haka. Mutumin daya iya zuwa muku da fuskar mutanen kirki ya yaudareku sai kasheni zai gagaresa. Hakanne ya sani bin umarninsa naje na faɗama malam yanda yace. Wlhy ban sake kiɗima ba sai da na tsugunna gaban malam ina faɗa masa wani yaro dake gefen malam ɗin ya ɗoramin bindika akan ciki batare da kowa a cikinku ya lura ba. Tayaya kuke tunanin zan iya ƙin bin umarninsa.”

             Yaya Abubakar da zukatansu ke neman faso ƙirazansu su fito a rikice yace, “Uncle Garba kace shine Shuraim?”.

         “Abubakar wlhy shine Shuraim, na tabbatar da shi kuka ɗaurama ita wannan yarinyar Muhibbatu aure”.

           Ai gaba ɗaya wajen ya sake ruɗewa. Ummi tai baya zata faɗi sai da Hajiya Mardiyya ta tarota. Abba kam wata mummunar hajijiyar ruɗani ce ke neman zubar da shi shima. Yayinda wani tsoro-tsoro firgici-firgici ya sashi fara waige-waige tamkar Shuraim ɗin na tare da su a wajen.. Abinda bai ganeba anan, miyasa Shuraim zai dakatar da ɗaurin auren ƴaƴansa da su Usman? Tunda gashi ya cika umarnin aikin auren ita Muhhibat?. Wayarsa ya shiga lalube yana ƙoƙarin fita a wajen.

      A.G ya kira, wanda sai da tana gab da tsinkewa ya ɗaga cikin ɓacin rai. “Malam miye kuma na kiran....?”

     Katseshi Abba yay da faɗin, “Ko kasan Master ne ya rusa ɗaurin auren ƴaƴana bayan shi an ɗaura nasa da yarinyar nan”.

     Cikin taɓe baki A.G yace, “To kai mi kake tunani? Kasan dai shi baya abu da ka, zata iya yuwuwa akwai dalilinsa nayin hakan, dan kawai ya bada ƙafa kamar yanda ya saba”.

      “Ina ba haka banee!!”.

Abbah da ke a birkice ya faɗa cikin matsananciyar tsawa.

     “Ya kake min ihu haka ne? Alhaji Halilu?”.

       “Ya bazan maka Ihu ba bayan kai ne ka tsara komai.....”

      “Muka dai tsara, tunda komai da yardarka akayi, a kuma gabanka bawai a boye ba.”

        Abba ya buɗe baki zaiyi magana A.G ya katsesa da faɗin,

    “Kaga ina zuwa gashi ana kirana da ga office. Zan kiraka”. Bai jira cewar Abba ba ya yanke kiran dan ogansa ne ke kiran nasa, da alama tsiyar da Master ya tafka harta fito kenan. Wani irin ƙarajin baƙin ciki Abba ya saki shi kaɗai a ɗakinsa, ji yake tamkar ya rotsa wayar tasa da ƙasa kawai ya huta. Jikinsa kansa ta ko'ina rawa yake da tsatstsafo da zufa, kansa ya kulle ya kasa fahimtar komai game da abinda Master ya aikata.


        Hargitsewar gidan yasa babu wanda ya farga da rashin Hibbah. Dan ita kanta Ummi ƴaƴanta nacan zagaye da ita kowa nason ganin hankalinta ya dawo jikinta. Yayinda acan tsakar gida Hajiya mama ke doka rantsuwa tana direwa akan sam bata yarda ba wanann shirin Ummi ne da ƴaƴanta. Tabbas sune suka saka Shuraim ɗin yayi haka. Da yawan mutane maganar Hajiya maman tayi tasiri a garesu, musamman da ya kasance alaƙar Hibbah da Shuraim ɗin kawai kowa ke kallo a zahiri da kuma ɗaura auren su Yaya Muhammad da wasu matan daban alhalin su su Hajiya mama basu san da zancen ba sai yanzu da aka ɗaura.

      Gidan ya ruɗe sai cece kuce ke tashi ta ko ina. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa da hasashen zuciyarsa.


        Cikin ƙarfin hali Ummi da tun fara tujarar Hajiya Mama yaranta suka kamata suka shige ciki da ita ganin yanda duk suka tattara kansu gareta ta haɗiye tashin hankalinta da ruɗani tana mai duban su Yaya Usman ɗin da su kansu bawai suna cikin cikakken hankalinsu bane akan al'amarin. Kan Yaya Abubakar da ke kusa da ita ta dafa tana murmushi. “Har yanzu zuciyata ta kasa daina yimasa ƙyaƙyƙyawan zato. Dukkanin cikamakin kamala da mutunci a bayyane suke garesa, shiyyasa nai saurin aminta da aura masa Tanee. Amma ta yaya fari zai koma baƙi a wanan ranar?, bayan har yanzu idanuna da zuciyata sun ƙi kallon komai da baƙin”.

        Cikin taraddadi da jan gwauron numfashi Yaya Abubakar yace, “Dama nasan hatsabibin nan bazai ƙyale Hibbah ba. Dan ta masa tabo irin wanda bazai gogu a cikin tarihinsa ba. Hakan yasani yarda da amincewar aima ta aure ko zata kuɓuta daga garesa. Ashe mun riga mun daɗe da kasancewa cikin lissafinsa, ko tantama banayi akan lallai shu'umin nan Master ne yazo mana da fuskar Shuraim. Sai dai ina mamaki matuƙa ta yanda ya kuɓutar da mu daga auren waɗan nan yaran. Mi hakan ke nufi ne?”.

          Ammar ya ɗago kansa da ga ɗorawar da yay bisa cinyar Ummi a firgice yana faɗin, “Yayamu Master fa kace? Gawurtaccen ɓarawon da kuke nema ruwa a jallo ko wa? Danni ban gane ba”.

         Numfashi yaya Abubakar ya fusga da ƙarfi yana jinjinama Ammar kai alamar tabbatarwa. Tare da bin fuskokin sauran ƴan uwansa da suma ruɗanin ne ƙarara ya bayyana akan fuskokinsu har suka gaza motsawa.

      Cikin ɗan rawar jiki Ummi tace, “Abubakar mi kake faɗane haka? Kana nufin yaron kwanaki da ƴan sanda suka sakata tai aiki akansa?”.

      Yaya Abubakar da shi kaɗai yasan lissafin da zuciyarsa keyi ya ɗan firzar da numfashi yana ciza lip ɗinsa na ƙasa da duban Ummin tasu cike da kulawa. “Ummi ki kwantar da hankalinki. Babu abinda zai samu Muhibbat da izinin ALLAH.....”

      Da sauri Ammar ya amshe zancen da faɗin, “Ummi mugodema ALLAH ma da kafin a kaita gidansa ne komai ya fito. Yanzu kunga ko a kotu ne a raba auren kawai sai a bama Yaya Isma'il dama sunfi dacewa”.

        Sosai maganar Ammar ɗin tai tasiri a garesu har Yaya Muhammad ya shafa kansa yana ɗan murmushi.

        Yaya Abubakar kam ɗago kai yayi ya kallesa tamkar wanda zancen yayma allura. cikin nazarin furucin na ammar, ya ɗan kaɗa kai yana jujjuyawa, dan baya son faɗar abinda a yanzu zuciyarsa ke hasko masa kai tsaye saboda Ummi. Miƙewa yay yana faɗin, “Komai ma da baƙwa tunani zai iya yi. Sai dai inaji a jikina Muhibbat ce tarkonsa a wannan karon”.

        “Yaya Abubakar kana nufin zai cigaba da bibiyar auta?”. Cewar Usman a tsorace yayinda duk suka bisa da kallo har Ummi.      

     Numfashi Yaya Abubakar ya fesar yana gyaɗa kai dai-dai yana ƙoƙarin kaiwa ƙofar fita. “Bazaka gane lissafinba Umar. Ku dai da ga yanzu dukkanin idanunku su kasance akan Muhibbat ne. Dan duk yanda kuke tunanin wanann shu'umin mutumin yafi ga haka. tabbas bazai taɓa bayyana kansaba bayan bai gama tsara yanda komai zai tafi masa ba.”

      Da kallo kawai suka bisa harya fice yana ƙoƙarin kai waya bisa kunnensa. Da alama kira yayi. Kafin Ammar ya miƙe yana faɗin “bara na nemota itama.”

      Kai kawai suka iya jinjina masa, dan jikin kowa ya gama sanyi a cikinsu.


★★★★


       A ɓangaren su Musbahu kam koda suka iso L.E street. Habib ne ya shiga sanarma ogan nasu isowar tasu, duk da kuwa sarai yasan yaji.

         Zaune ya sameshi ƙafa ɗaya kan ɗaya a katafaren falon nasu da yaji kayan more rayuwa yana sarrafa system da ke saman cinyarsa. Duk da yaji shigowar Habib ɗin bai ɗago da ga abinda yake ba, sai dai ya amsa masa sallamar akan laɓɓa.

        Habib da ya ɗan kallesa ya risinar da kansa ƙasa da girmamawa yace, “Barka da hutawa Master”.

      Uffan baice ba, bai kuma ɗago ya kalli Habib ɗin ba har tsahon wasu sakanni, sai dai ya jinjina kansa alamar amsawa.

       Habib da ya fahimci ƴan mulkinne a kusa yau sai kawai ya cigaba da magana. “Aiki ya kammala, itama gata tare da mu”.

       Dakatawa yay da ga sarrafa lap-top ɗin, a hankali ya ɗago idanunsa cike da ƙasaitarsa ya saukesu kan Habib ɗin da ya nutsu waje guda saboda tsabar girmamawar da suke bashi.

       Kallo daya yay masa ya janye idanunsa ya maida akan system ɗin da faɗin, “Su Salis?”. Yay maganar a taƙaice cikin sigar tambaya”.

       “Dukanmu tare muka shigo”. Habib ya bashi amsa.

         Lap-top ɗin ya ajiye ya miƙe, batare da ya sake cema Habib ɗin komai ba ya nufi hanyar fita cikin takun da ke nuna cikakkiyar lafiyarsa da nutsuwar da ALLAH ya azurtashi da ita.

       Shima Habib bayansa yabi da saurai suka fita a kusan tare. Kallo ɗaya yay ma su Salis da ke ƙoƙarin fitowa a mota ya ɗauke kansa da cigaba da tafiya cikin izza da ƙasaitarsa tamkar wani jinin mulki. 

       Dai-dai yana isowa inda suke suka haɗa baki wajen faɗin, “Barka da gida Master”.

     Hannu kawai ya ɗaga musu yana nufar motar da Habib ya fita da ita. Da sauri Habib ya buɗe masa motar ta sashin da Hibbah ta ke yana matsawa gefe tamkar yanda sauran suka nutsu.

     Duk da yasan a sume take hakan bai hanashi sake ɗaure fuska ba kafin ya sauke nutsatstsun idanunsa masu kaifin gani a kanta. Sai kuma ya ɗan kaudasu tare da ƙarasa takawa gaban motar da ƙyau yana yamutse fuska. Dai-dai lokacin da yake ranƙwafawa su Habib suka kalli juna, yana ɗagowa ɗauke da Hibbah suka waro idanu waje da saurin maida kawunansu ƙasa.

       Ko kallo basu ishesa ba, sai ma sake tamke fuskar boginsa da yayi ya shiga taku cike da izzarsa da kasaita zuwa cikin gidan ɗauke da Hibbah da batasan wainar da ake toyawa ba.

        Idris ya haɗe yatsunsa waje guda alamar love yana wani cije baki. Sauranma idanu suka shiga kashewa da yin alamar nice👌🏼 cike da shaƙiyanci.

       Tsaf yaga duk iya shegen nasu ta glasess ɗin windows. Ya ɗan ciji lip ɗinsa na ƙasa da tura ƙofar falon da ƙafa. Hakan ya saka su Khalid saurin mara masa baya gudun yin laifi.

        Koda ya shigo falon up stairs ya nufa, anan ma falo ne babba masha ALLAH, wanda babu abinda baijiba na kayan more rayuwa. Sai tashin ƙamshi yake ga sanyin ac mai saka nutsuwa. Kai tsaye ya nufi ɗaya da ga cikin bedroom ɗin da ke a up stairs ɗin. ya shimfiɗeta saman gadon ɗakin yana wani sake ɗaure fuska da yamutseta irin shifa ya gajin nan. Ya ɗan zubamata harara yana janye jikinsa. Wayarsace ta fara tsuwwa alamar shigowar kira.

      Sharewa yay tamkar bazai amsa ba. Sai da ta na gab da tsinkewa ya zarota a aljihun wandon baƙin jeans ɗin jikinsa yana jan siririn tsaki da jingina jikin mirror ɗin ɗakin yana kaiwa kunnensa batare da ya ce uffan ba, sai dai shirun nasa na nuna alamun sauraren mai magana ya ke da ga can. Tsawon minti biyu da wasu sakanni ya ce, “Uhmm” da ɗan gyaɗa kai.

          Dai-dai nan akai Knocking ƙofar a hankali, kasancewar sun san idan yana a irin wanann yanayin duk wata hayaniya baya buƙatarta.

        Cikin ƙosawa da motse-motsen kuwa ya bada izinin shigowa yana janye wayar a kunnensa...........✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


________________________


*_Chapter Twenty two_*


..........Da sallama Habib ya shigo tare da ƙarasa shigowa cikin ɗakin, leda ɗin da ke a hannunsa ya ajiye saman mirror ɗin da yake jingine.

        “Minene wannan ɗin?”.

Ya faɗa yana zuba lumsassun idanunsa bisa kan Habib ɗin.

       A ladabce Habib ya ce, “Makarin abinda aka shaƙa matane”.

        Kallo ɗaya yayma ledar ya ɗauke kansa. Cikin halin ko in kula ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Ɗakko ledar yay ya miƙa masa, ya ɗan janye hannunsa yana girgiza kansa, Habib da ya fahimci mi yake nufi sai ya buɗe ledar ya ciro handkerchief ɗin da ke ciki ya sake miƙa masa. Amsa yay ya zubama handky ɗin ido tamkar mai nazari, kafin yaja numfashi ya fesar yana ɗago agogon da ke a tsintacciyar hannunsa ya kalla. Ganin lokacin sallar la'asar ya gabato sosai ne ya sashi miƙama Habib Handkerchief ɗin. Batare da yayi magana ba ya nufi hanyar fita ɗakin.

       Sukan fahimci abubuwa masu yawa da ga garesa koda ta kurma yay musu. Hakan yasa yanzun ma Habib ɗin ya fahimta. Handky ɗin shima ya maida a ledar ya ajiye saman mirror ɗin ya bi bayansa.

          Koda ya fito bedroom ɗinsa da ke a saman upstairs ɗin ya nufa, sai dai yana da ga can kusan ƙarshen bangon gabas da falon saman, hakan yasa akwai tazara tsakanin shi da inda ya kai Hibba. Tamkar falukan nan ma komai tsaf, bakajin komai sai tashin ƙamshi da sanyin ac da ya gauraye ko ina. Yanda yake kure sanyin zai tabbatar maka shi ɗin ma'abocin son sanyi ne matuƙa. Dan yanda gaba ɗaya saman upstairs ɗin da ke nuna alamar anan komansa yake ya ɗauki sanyin wani bazai iya jimirin zama cikinsa ba. Shiko ko a jikinsa bai damu ba. Agogon hannunsa ya cire ya ajiye saman mirror ɗin ɗakin, tare da tattare dogon hannun rigar jikinsa sannan ya nufi wani ɗan dogon glass daya ci kusan rabin bangon yana facing ɗin gadon sa. Wani abu ya danna ya zuge kansa, yana shiga kuma ya maida ya rufe.

     Baifi mintuna sha biyar ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga na wandon jeans da t-shirt. Hakama fuskarsa ta canja zuwa wani daban, gaba ɗaya ƙamshinsa ya gauraye ko ina ya danne na fresheners ɗin da ke tashi a sashen.

      Cikin yanayin kamar fushi-fushi da yake cikine ya ƙarama tafiyar tasa bayyana cikin izzarsa da ƙasaita ta musamman. Ya shiga sauka a steps ɗin cikin salon zafin nama da ALLAH ya azurtashi da shi.

         Daga falon ƙasan yake jiyo hayaniyar su Salis da alamu ya nuna suma shirin massallacin duk sukeyi. Batare da ya ko kalli sashen da suke ba ya zauna a kujerar da ke gab da ƙafar benen idonsa akan wayar sa dake hannunsa.. Saman kunne ya kai wayar tare da ɗaura ƙafarsa ɗa ya kan ɗaya. Ana ɗagawa da ga can cikin bada umarni yace, “Ka sameni kai da baba Saude”. Da ga haka ya ajiye wayar a table ɗin kusa da hannun kujerar ya maida idanunsa ya lumshe.

         Mintuna biyu kacal tsakani Khalid ya fito da ga wata ƙofa bakinsa ɗauke da sallama.

     A saman laɓɓa ya amsa masa batare da ya buɗe idanun nasa ba. Sai da baba Saude tai sallama a ƙarshe sannan ya buɗesu a hankali.

       “Babana an shigo ashe? Sannunku da dawowa”. Dattijuwar tsohuwa mai cikar kamala ta faɗa tana ƙoƙarin kaiwa zaune ƙasan tattausan carpet ɗin dake a tsakkiyar kujerun.

        Kujera ya nuna mata yana girgiza kansa cike da bata girma. Kafin ya buɗe baki tamkar bayaso ya fara magana. “Tun ɗazun na shigo ai. Na zata kina barci ne baba”.

        Murmushi tayi dai-dai tana kaiwa zaune. Ta ce, “Eh barci ya ɗan figeni kam sanda suka shigo. Nima motsinsu ne ya tadani”.

        Kansa kawai ya ɗan jinjina mata, tare da duban baƙin agogon fatar da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa. Cikin rashin son hayaniyarsa ya maida kallonsa ga Khalid da ke tsaye har yanzun. “Tsayuwar zaka cigaba da min a kai. Ko kiransu ku wuce masallaci!”.

       “Ayi haƙuri boss”. Khalid ya faɗa yana ɗan shafa ƙeya da komawa ciki domin kiran ƴan uwansa.

       Master ya janye idanunsa da ga kallon Khalid da yayi ya maida kan baba Saude. “Baba Saude zaki dawo nan da zama. Akwai yarinya zata kasance da mu anan na wani ɗan lokaci ne, ALLAH yasa bamu takuraki ba”.

       Baba Saude ta ɗan wawwaiga falon, dan ita bama ta lura da kowa ba. Amma sai ta ce, “Babu damuwa Babana, sai na dawo nan ɗin tunda ba wani abu nake acan ɗin ba, ba kuma wanine tare da ni ba balle nai tunanin barinsa. Kwana ne dama kawai ke kaini ai. Sai ina neman lamunin tahowa da ƴar marainiyar yarinyar nan dake wajena”.

      Kansa ya ɗan jinjina mata, kafin a takaice yace, “Nagode”.

      “Ai nice ya kamata nai godiya da karamcinka gareni babana. ALLAH ya saka maka da alkairi ya jiƙan iyaye da rahama. ALLAH ya bani tsahon rai da lafiyar kaiwa ran aurenka”.

      Wani ɗan ƙasaitaccen murmushi ya saki da kaɗan ya nuna akan fuskarsa. Batare da ya ce komai ba ya maida dubansa ga su Habib da ke fitowa da shirin tafiya masallaci.

           “A gyara mata ɗaki a nan ƙasa”.

     Ya faɗa yana miƙewa.

Cikin rashin fahimta Habib ya ce, “Auntyn ko Baba Saude?”..

       Wani malalacin harara ya zubama Habib ɗin tare da nufar hanyar fita. Batare da ya amsa masa tambayar ba yace, “Kaje da ita ta duba abinda babu zuwa anjima a faɗa min idan kun dawo salla, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nake son ta dawo gaba ɗaya”.

        Cike da jin daɗi su Habib suka juyo suna duban baba Saude fuska a washe. “Finally baba Saude zata dawo kusa da mu gaba ɗaya”.

        Ƴar dariyar jin daɗi tayi itama cike da so da ƙaunar yaran tana miƙewa domin yin salla. Suma suka fice cike da murna wannan zance na dawowar baba Saude kusa da su saɓanin da da zuwa kawai take tai musu girki ta wuce da yamma.

      

    

★★★★★


         A can gidan su Hibbah kuwa zuwa yanzu ƴan uwanta sun fara shiga ruɗani, dan kamar wasa babu ita babu alamarta a cikin gidan. Lungu da saƙo sun zagaye har sashen su Hajiya mama da basama tunanin zataje. Tun sunayi su kaɗai har mutane da suka farga suka fara tayasu. Da ga cikin gida takai har an fito waje amma babu ko mai kama da ita. Babu ma wanda yace ya ganta bayan wanda suke a falon Ummi.

     Yaya Muhammad ne ya tuno kiran da Shuraim yay mata. Wanda a dalilinsa ya sakata fita waje dan ta amsa. Kuma tabbas daga haka bata dawo ba har suka fita massallaci.

       Kansa ya dafe yana ambaton “innalillahi....”

      Gaba ɗaya suka maida dubansa gareshi a ruɗe. Ya cigaba da faɗin, “Tabbas Abubakar kayi gaskiya yaron nan hatsabibine na gaske. indai har hasashena yana kan dai-dai tun kafin a ɗaura auren nan ya ɗauke Hibbah.”

      “What!?”.

Yaya Abubakar ya faɗa a razane, illahirin jikinsa sai tsuma yake.

            Yaya Muhammad da ke jin juwa na kwasar sa cikin raunin murya yace, “Ƙwarai kuwa Abubakar ya ɗauke mana ita. Dan shine ya kirata lokacin da muke ɗaukar hoton nan amma sai taƙi ɗagawa, nine na korata waje akan taje ta ɗaga. Na tabbatar da ga lokacinne ya sace mana ita”.

     Saurin riƙosa Isma'il dake a bayansa yayi ganin yayo baya zai faɗi. Yaya Umar kam ai dole ya kai zaune dan ya tabbatar ya cigaba da tsaiwar faɗuwar zaiyi shima. Yayinda tuni idanun Usman da Ammar sun fara kawo ruwan hawaye. Sauran abokansu kam da ke wajen kowa ya shiga halin taraddadi da tausayin su Yaya Muhammad. Dan kallo ɗaya zakai musu ka fahimci tsananin ƙauna da sukema ƙanwar tasu.

      Komai ya kwance musu, tunani ma sun gazayi na neman mafita. Ammar da ke kuka ya nufi cikin gida da zummar sanarma Ummi dama tunda suka dawo sallar la'asar basu koma ciki ba. Saurin riƙosa Isma'il yayi yana girgiza masa kai. “Ammar ba yanzu ba. Ummi bata cancanci sanin wannan tashin hankalinba yanzu. Inaga muɗan jinkirta har a samu mafita”.

         Kuka sosai Ammar ya fashe da shi, hakan yasa Isma'il ɗin rungumesa cike da lallashi.

      Yaya Abubakar da zancen Isma'il yaja hankalinsa cikin gamsuwa da ƙarfin hali ya ce, “Shawararka tayi Isma'il, dolene mu jinkirta sanarma Ummi wannan batun duk da cewar zuwa yanzu tasan babu Hibbah a gidan. Sai musan mi zamu sanar mata dan hankalinta ya kwanta”.

          Cike da gamsuwar jawabinsa duk suka kaɗa kansu. Suna nan tsaye suna tattauna yanda zasu ɓulloma Ummin suka juyo sabuwar hayaniya ta ɓalle a cikin gidan, har takai wasu na fitowa a guje. Da sauri suka shiga, dan tun daga nan suna jiyo kururuwa da ihun Hajiya mama.

      Da ƙyar suka iya kutsa kai cikin falonsu. Inda ke cike da ƴan biki da ke zagaye da Hajiya mama da Abba da Junaid wai zai daki Ummi. Hajiya mama nata zagin Ummi akan itace ta tsara komai akan auren su Yaya Muhammad. Abba ma yana zazzaga tasa masifar da tattaro duk laifin Shuraim (ko nace master) yana azawa kan Ummi. Duk da kuwa sarai yasan gadar zaren da ya ƙulla ce ta rufta da shi. Yayi iya hasashensa kuma ya gagara kamo bakin zaren da dalilin Master na juya shirin nasu zuwa tsarinsa daban, shiyyasa yazo sauke haushin da takaici akan Ummi marainiyar wayonsa. Harda yo gayyar ƴan tayo..

         Isma'il ya finciki Junaid ta baya yana ƙoƙarin riƙe katakon da ya ɗaga wai zai bugama Ummi da ke zaune ta dafe kanta tana jiran saukar katakon. A take mutane suka dare saboda yanda ya zubar da Junaid ɗin a ƙasa ya take masa wuya. Riƙesa Yaya Muhammad yay ƙoƙarin yi amma sai ya fisge jikinsa, da ƙarfi ya daka katakon da ya kwace a hannun Junaid ɗin a ƙasa saitin kansa, jikinsa sai wani irin tsuma yake tamkar mafaraucin zaki. Duk yanda Junaid ke kakarin mutuwa yaƙi ɗaga ƙafarsa a wuyansa, sai ma sake murzawa yake cikin tsananin taurin zuciya.

       A matuƙar firgice Abba ya ƙai hannu wai zai ture Isma'il. Sai dai ko motsi bai yiba. Sai ma waiwayowa da yay ya duba Abban da wasu irin jajayen idanun da suka bama kowa matuƙar mamaki. Dan gaba ɗaya ya birkuce musu da ga Isma'il ɗin da suka sani zuwa wani daban.

          “Idan jikinka ya ƙara gigin taɓa nawa saina ɓallaka yanda ko uwar data haifeka bazata sake gane kamaninka ba.”

        A wani irin zabure Abba ya waro idanu yana nuna kansa, “Da ni kake?”.

      Ƙafar da yake murza wuyan Junaid da ke kakarin mutuwa ya ɗaga. Yay wani irin tsalle tamkar ɗan ƙwallo zai buga ball ɗin daga kai sai mai tsaron gida ya halbi hakarƙarin Junaid. Wata irin wahalalliyar ƙara Junaid ya saki tare da jan numfashi tamkar zai shiɗe sai ga aman jini.

       “Innalillahi... Isma'il!”.

Yaya Muhammad ya faɗa da sauri yana kawo hannu zai riƙesa. Saurin ɗagama Yaya Muhammad ɗin hannu yayi idanunsa na kan Abba da gaba ɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake. Dan yanda Isma'il ɗin ke tunkarosa sai yake ganin tamkar zai haɗiyesa da idanunsa masu suffar na Zaki ne.

      “Yaya Muhammad barni na kartama wannan shashashan dattijon warning na ƙarshe. Dan inhar ya sake koda kallon Ummi da wata manufa to lallai saina maidashi abin kwatance. Kai bama shi ba. Ko karen gidan nan ya sake mata kallon banza lallai ni Isma'il zan daddatsa shi gunduwa-gunduwa na cinye namansa ɗanye dan uban da ya haifesa”. Ya ƙare maganar idonsa akan Abba. Yatsansa na nuna Hajiya mama da ta koma jikin bango ta maƙure jikinta na rawa kar-kar-kar. Ga fitsarin da ya cika mata mara tuni ya ɓalle ya fara bin kafafunta yana sauka saman tiles.............✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


______________________


*_Chapter Twenty Three_*


.............“Kaga wani salo kamar a film”.

Ammar ya faɗa dariya na kufce masa a bazata. Dan haka kawai wasan yay matuƙar birgesa da ƙayatar da shi.

        Su yaya Abubakar kam da gaba ɗaya mamaki da al'ajab ɗin Isma'il ɗin ya daskarar da su a tsaye da ƙyar suka iya fisgo numfarfashinsu sukai azamar zuwa suka sha gabansa ganin Abba ya ke nufa gadan-gadan. Dan su gaba ɗaya abinda zukatansu ke basu lallai Isma'il yana tare da wani bahagon aljani ne ƙila.

      Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ganin sun tare sa. Cikin wata irin murya mai ƙaraji da saka firgici ga ma'abocin saurare yace, “Minti uku na baku a fitar min da wanann sauran gawar anan. Kar kuma na sake ganin ƙafar waninku anan. Inba hakaba.... Ya ƙyalƙyale da dariyar da ta saka su Yaya Abubakar sake zama turus a gabansa.

       Jiki na rawa Momy ta kama ƙafafun Junaid ta fara ja tana kuka. Yayinda tuni Hajiya mama ta fece da gudu har tana cin tuntuɓe zata faɗi. Su kawu Garba da ke gefe a maƙure suma ne sukai karfin halin matsowa suka taya Momy ɗaukar Junaid da zuwa yanzu ya sume sabida azabar murzar da wuyansa yasha da haƙarƙarinsa.

        Da gudu Ammar ya taho ya rungume Isma'il ta baya yana dariya da hawaye a lokaci ɗaya. Hakan yasa Ummi ma da tai mutuwar zaune tana kallon Isma'il ɗin ta miƙe zuwa garesu. Hannun Isma'il ta riƙo cikin nata hawaye na sakko mata saman kumatu. Jawo hannun nasa tai ta zaunar da shi akan kujera tare da ɗaukar goran ruwa da ke a saman centre table da aka ajiyema baƙi ta ɓalle murfin ta ɗora masa a baki tana shafa kansa.

      Babu musu ya hau sha yana jan ajiyar zuciya. Sai da ya shanye shi tas ta janye goran tana cigaba da shafa kan nasa.

     A hankali ya lumshe idanunsa da komawa baya ya jingina jikinsa da kujerar, numfashinsa tun yana sauka da zafi-zafi har ya koma sauka a hankali alamar zuciyarsa nayin sanyi.

     Ummi ta share hawayen fuskarta tanayin murmushi da duban su Yaya Usman da har yanzu ruɗani da al'ajabin mamakin Isma'il ɗin ya gaza barinsu. Matsowa sukai gareta. Yaya Umar da yaya Usman suka rungume Isma'il ɗin. Yayinda Ammar yazo ya zauna gabansa ya ɗaura kansa a saman cinyarsa fuskarsa washe da dariya tamkar gonar audiga.

    Hannu ya kai a hankali bisa kan Ammar yana shafawa. A karon farko ya saki murmushi da ɗago kansa ya na kallon Ummi da su Yaya Muhammad.

       “Kiyu haƙuri Ummi, lamarin mutanen nan sai da over acting. Na fahimci wannan ce kawai mafita a garemu. Inba haka ba sai wata fitinar ta kaure har akai ga jima wani ciwo”.

     Yanda yay maganar cikin sanyin murya tamkar yanda suka sanshi ne ya saka su Yaya Usman sakin ajiyar zuciyoyi.

        “Amma Isma'il ka bani tsoro matuƙa wlhy, har mun fara tunanin ko baka da lafiya ne”. Cewar Yaya Muhammad yana murmushi.

     Ɗagowa Isma'il yayi zaune sosai yana saki ƴar dariya. “Yayanmu lamarin tsohuwar nan ne sai da haka. Sai dai fa nasan wlhy ba haƙura sukai ba, dan da alama na jima wancan wawan yaron Junaid ciwo a haƙarƙari. Ummi inhar shirinku na barin gidan nan na nan to lallai dole ne ki tafi kema a yau ɗin nan. Kamata yay ma ace yanzu kawai. Kinga sai ki tarbi amare da kanki”.

       Yaya Abubakar da har yanzu shi dai yake kallon Isma'il ɗin cike da nazari da wasiwasi ya gyaɗa kansa cikin gamsuwa. “Wannan mafita ce mai ƙyau. Dan Abba kam ba kanwar da za'a lasa bace aji kaifi kawai. Ummi kamar yanda Isma'il ɗin ya faɗa barin gidan nan yanzu shine mafita kawai”.

       Sosai itama Ummi ta gamsu da zancen. Dan duk abinda zai ɓata mata taron auren yaranta bata fatansa. Sarai kuma ta fahimci abinda su Hajiya mama ke burin yi kenan. Sai dai kuma cikin damuwa da rauni ta ce, “Tanee ɗin fa an ganta?”.

         Da sauri Yaya Umar ya gyaɗa mata kai. “Eh karki damu tana tare da ƙawayenta ashe. Zuwa anjima nasan zatabi masu kai su can kawai”.

        Duk da zuciyarta a raunane take hakan bai hanata gamsuwa ba. Ta mike tana warware mayafinta da dama tana tare da shi tun ɗazun ta sake yafawa. Dama ba wani muaten bane sosai a sashen. Makwafta da suka shishshigo sukai mata ALLAH sanya alkairi duk sun fita saboda yamma tayi sosai. Sai ƙawayenta na kusa sosai irinsu Hajiya Mardiyya. Suko sunsan da shirin barin gidan. Dan dama sune zasuje amsar amare acan. Jin hukuncin da su Yaya Muhammad ɗin suka yanke ne ya sakasu mimmiƙewa suma suka hau kimtsawa.

     Su Ummi basu da matsala da komai na sashen dan sun tsince masu muhimmancin sun killace sauran. Su hajiya mama nacan akan Junaid cike da ruɗani suka samu suka fice dan dama gari ya fara duhun magrib da ake ta faman kira a masallatan anguwar. Mutanen da ke a tsakar gida kuwa gulma da tsugudidin da suka haɗa kai sunayi group-group yasa basu hankaltu da su Ummin ba. A tunaninsu kawai ƴan biki ne zasu wuce gida.

         


★★★★★


        

           A can L.E street kuwa cike da farin ciki da ƙaunar yaran har cikin rai baba Saude ta mike domin gabatar da sallar la'asar ɗin itama. Tana idarwa ta fito ta hau shirya musu abincinsu na rana da basu ci ba.

           Kasancewar yunwar kuwa na ƙwaƙular cikinsu ana idar da sallar la'asar ɗin suka dawo gidan. Sai dai su kaɗai suka shigo falon banda Master da yay zamansa a ƴar runfar bunun da ke a gefen swimming pool ɗin gidan. Dan yasan tunda suka dawo gidan shegen surutinsu ba zai barshi ya huta yanda yake bukata ba.

        Suko da ga can cikin zalamar kayan daɗin da baba Sauden ta baje musu a babban dining ɗin suka baje da fara ɗurama cikinsu. Yayinda kowa ya fara kai lauma sai sabon surutu ya ɓalle, baba Saude na gefe na musu dariya kamar yanda ta saba har suka kammala. Sune suka zaɓar mata ɗakin da zata zauna anan downstairs ɗin. Hundred percent kuwa ta gamsu da ɗakin, dan yana ɗan nesa da ɗakunansu ga shi kuma gab da kitchen.

      Sune suka shiga gyara mata komai duk da bama wani datti bane da ɗakin. Bayan sun kammala Salis yay list ɗin abubuwan da yasan Baba Sauden zata buƙata na amfani musamman a toilet. Da ga haka suka dawo falo kowa ya kama hidimar gabansa. Lokaci-lokaci suka sakko zancen Zaidu da ke can gidan su Hibbah yana gano duk cakwakiyar da ke faruwa batare da kowa ya fahimci shi ɗin wanene ba.


*_8:16pm_* ya shigo gidan. Lokacin su Idris da dawowarsu da ga sallar isha'i babu jimawa na baje a falo suna kallon ƙwallo. Duk sun cika falon da hayaniyar gaddamarsu.

      Khalid da ya fito da ga kitchen riƙe da drik ne ya fara farga da Master da ko sallamarsa basu ji ba. Cikin ɗan daga murya yanda zasu fahimta ya ce, “Barka da dawowa Master”.

      A take falon kuwa yay tsit duk suka juyo ga ƙofa. Cikin ɗan hararsu ya ajiye ledojin da ya shigo musu da shi ya haura sama da ɗaya batare da ya amsa sannu da zuwan da suka haɗa baki wajen masa ba. Suna ganin ya gama hayewa har rige-rige tasowa Zaidu da bai jima da dawowa gidan ba suke shi da Salis wajen zuwa su ɗauka ledojin da ya jiye. Suma sauran tasowa sukai akan ledojin cike da farin ciki da ƙaunar Mastern nasu.

       “Dalla malamai karkuyi mana hayaniya anan kuja a samu barcin dole”. Cewar Adam yana harar su Zaidu da suka ƙanƙame ledojin.

      Cikin ƴar dariyar shaƙiyanci Musbahu yace, “Wanann kaɗan da ga aikin Master. Balle fa yau ango yake a gidan nan kuna ganin harda kazar tarbar amarya”.

        A tare suka wage bakuna zasu ƙyalƙyale da dariya Idris yay musu nuni da sama. Saurin saka hannayensu sukai suka dafe bakunan kowa na ƙoƙarin danne ta shi. Da ga haka suka koma tsakkiyar falon zaune  Salis na ƙoƙarin buɗe ledojin dake ɗauke da kwalayen pizza da shawarma.

       Sosai suka shiga farin ciki kowa yaja shawarma ɗaya dan dama a lissafe suke. Pizza kuwa kwali huɗu ce itama.


       Da ga ɓangaren oga Master kuwa koda ya haura sama a falo ya ajiye ledar ya nufi bedroom ɗinsa. Kusan mintuna goma sha biyar sai gashi ya fito. Ya sake ɗaukar ledar ya nufi ɗakin da ya kai Hibbah ɗazun. A yanda suka barta a haka ya isketa. Ya ajiye ledan a saman mirror fuskarsa na sake tsuƙewa. Ledar da Habib ya ajiye ɗazun ya ɗauka. Ya zaro handkerchief ɗin cikinta yana nufar gadon. Wata ƴar ƙwafa yayi dai-dai yana ranƙwafowa akan Hibbah da batasanma ya nai ba. Kansa tsaye ya ɗora handky ɗin saman hancinta. Tsahon minti ɗaya taja wani irin dogon numfashin da zai iya razanar da mai tsoro. Bai ɗaga handkerchief ɗin ba sai ma sake danna mata shi da yay akan hanci.

       Numfashin ta kuma ja da ƙarfi tare da sakin tari lokaci guda. Ya janye hannunsa da jikinsa yana mikewa da ƙyau. Ganin yanda take jujjuya kanta da cigaba da tarin ya sashi ɗaukar goran ruwan da ya ajiye a bedsite tare da ɗora kafarsa ɗaya akan gadon ya sake ranƙwafowa kanta. Murfin gorar ruwan mai ɗan sanyi ya ɓalle ya shiga tsiyaya mata a saitin wuyanta duk da akwai hijjab a jikinta har yanzu dan basu cire mata ba. Yanda yake kwarara ruwanne ya sashi tsalle har saman fuskarta zuwa ƙirjinta da kan gadon.

       Tai wata irin zabura da jawo numfashinta da ƙarfi ya iso har cikin hancinta. Duk da wani irin nauyi da jikinta yay mata hakan bai hanata ɗago hannunta ba ta shiga ƙoƙarin sharce ruwan da har yanzu yake kwarara matan.

       Ɗayan hannunta ta kai cikin lalube da rashin ƙarfin jikinta da nufin ture ruwan da ke sakko matan. Sai dai hannun nata bai kai ba, sai kafarsa data ɗan shafo kaɗan ta ajiyesa yaraf tana ƙoƙarin son buɗe idanunta da sukai matuƙar nauyi.

        Dakatawa yay da tsiyaya mata ruwan jin ta fara magana a fisge. “Y... y... ya... ya... Mu.... ham.... mad... kar... Kar...ku ɗaura zasu kashe ku”. Ta shiga faɗa a rarrabe cikin ƙoƙarin fisgar numfashi da yunƙurin son tashi. Sai dai kuma luuu ta koma yaraf bisa gadon dan sam babu wani ƙarfi tare da ita. Hasalima abin bai gama sakinta ba baki ɗaya.

        Fahimtar hakan da yayi ne ya sakashi jan tsaki da cillar da goran ruwan yana sauke kafarsa ya miƙe tsaye sosai. Kallonsa ya kai ga agogon hannunsa yana sake tsuƙe fuska.

        Tunanin mi yayi oho masa, sai kawai ya ja bargo aɗan fusace ya lullu ɓa mata, tare da sake ranƙwafowa ya kama hijjab ɗin jikinta yaja da ƙarfi ya farkesa. jansa yay baya ya fita da ga wuyanta. Da ga haka ya ɗauka ledan da ya shigo da ita ya fice ransa fal takaici.

   Bedroom ɗinsa ya wuce, duk da yana jiyo hayaniyar yaran nasa da ke cigaba da kallon ball da ciye-ciyen abinda ya kawo musun suna zabga gardamar da sukafi ƙwarewa akai.


★★★★


        Su Ummi sun isa katafaren sabon gidan da su Yaya Muhammad sukai matukar ƙoƙari wajen ginasa. Dan babu abinda su Hajiya Mardiyya ke ambato sai masha ALLAH. Ƙwarai da gaske matasan samarin na Ummi sun nuna ƙwazon da za'a yaba musu ƙwarai da gaske. Dan komai yayi cif a talauce ba'a sarauce ba. Sashen Ammar ne kawai ba'a karasa ba daga linta aka barsa.

       Kai tsaye sashen Ummi da ke a farko suka shiga. Inda nanma dai su Hajiya Nafisa keta sakama yaran albarka dan komai yayi a asashen tamkar bana dattijuwa Ummi ba. Akwai ɗakin Ammar da na Hibbah a sashen Ummin. Sai bedroom ɗinta dana baƙi guda biyu. Ga babban falukanta biyu da kitchen da dining babba da ke ɗauke da dogon dining table na family baki ɗaya. A kallo ma zaka san sashen Ummin yafi kowanne sashe girma a gidan, sai dai nasu kawai upstairs ne su kuma. Itama kuma catai bataso shiyyasa akai mata nata flat da ya kayatu da zamani.

        Suna shirin fara gabatar da salloli dan mazan sun fice sai ga kuloli ana shigowa da su. Cikin mamaki Ummi ke tambayar da ga ina?. Matasan samari biyu da ke shigo da kulolin suka bata amsa kai tsaye da faɗin. Isma'il ne ya turosu.

      Rasama mi Ummi zatace akan wannan yaro ɗan albarka tayi, sai kawai ta saki murmushi zuciyarta na ƙara jin matukar ƙaunarsa har cikin jini............✍


      


*_Amin afuwa da jina shiru. Ciwo me ya kadani a bazata._*


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_Chapter Twenty Four_*


............Kusan karfe tara na dare amare suka fara isowa. Sheikh Aliyu Abdul-Ra'uff Maina ne ya fara isowa da tawagarsa. A bisa al'adarsa na kai duk ƴaƴansa gidan aurensu kuma. Ba wani gayya bace yayo. Mota uku ce kawai ta ƴan uwansa mata sai ɗaya mazan ƴan uwansa sai ɗaya shi da Amarya Maimunatu da ke jikinsa tana faman kukan rabuwa da gida tamkar kowacce amaryar ƙwarai.

        Ya fara damƙata a hannun Ummi matsayin uwa kafin ya damkama Yaya Muhammad da musu addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, harma da sauran angunan da amarensu. Da ga haka yay musu sallama ya taho ransa fal kewar ɗiyarsa data kasance ta ƙarshe a cikin ƴaƴansa da ya aurar.

       Tamkar jira suna barin ƙofar gidan gayyar abokan su yaya Umar ƴan ɗaukar sauran amaren uku suka iso anguwar suma. Dama su su Yaya Umar ɗin duk suna nan gida basuje ba. Suna can gefe sun kulle kansu suna tattauna batun Hibbah dan sam hankalinsu baya a kwance. Yaya Abubakar ma tun ɗazun baya gidan da alama shima dai duk akan Hibbah ɗinne.

       Sosai gidan ya kacame da hayaniya. Suma sauran amare duk sai da aka kawosu sashen Ummi aka damƙasu gareta kafin a mimmiƙasu sashen su. Waɗanda bazasu kwana ba suka firfito domin a maidasu. Aka bar masu kwanan nan da ƙawayen amare.

      Hayaniyar mutane yasa Ummi bata maida hankali akan rashin ganin Hibbah da akace tana tare da su Zahidah ba. Gaba ɗaya hankalinta ya ɗauke. Har takai gidan ya koma tsit batasan kai kawo da ƙulle-ƙullen da ƴaƴanta keta faman yiba akan autar tasu.


★★★★


        A can gidan ɓangaren su Abba kam dole aka kwashi Junaid zuwa asibiti, yayinda ran Abba ke a ɓace a jagule matuƙa. Babu abinda zuciyarsa ke kitsa masa sai ɗaukar alwashi kala-kala akan Ummi da zuci'arta. Musamman Hibbah da yakeji zai iya dasa wuƙa a maƙoshinta a halin da yake ciki. Dan tabbas kuwa yaga *ɗan hakkin da ka raina shike tsone maka idanu* har yaushe ma aka samu cikin Hibbah aka haifeta da zata iya ruguza masa shirinsa na tsahon shekara da shekaru?. Bama ita ba, hatta da Master ɗin ya ɗauki alwashin bazai bari ba. Dan da'alama Hibbah da su Ummi ɗinne suka sashi wargaza zancen auren.

        Irin waɗan nan tunane-tunanen yaketa faman yi da kaikawo a ɗakinsa tun barin su momy da Junaid zuwa asibiti. Sai hayaniyar ƴan biki da har yau suketa gutsiri tsoma yake faman jiyowa. Wayarsa ya ɗauka ya shiga neman number A.G amma sai taƙi shiga saboda network. Cike da haushi ya wurgata saman gadon yana dafe kai. Tsabar ruɗanin da yake ciki ko salla baiyi ba gaba ɗaya yinin yau. Babu azhar, la'asar, magrib balle isha'i. Bai kumayi tunanin yinsu ba har dare ya raba ya cigaba da ƙullawa da kwancewa batare da ya samo wata mafitaba akan al'amarin.


       Da ga wajen amare kuwa su Amlah kuka sunsha shi har sun godema ALLAH. Su kansu babu irin kalar tsinuwa da zagin da basu rakito sun sauke akan Ummi ba. Ga ƙawayensu na tayasu da tunzurawa. Tashin hankalin dukan da Isma'il yayma Junaid ne ya ɗauke hankalinsu zuwa can suma sukabi su Momy asibiti dan suna tsananin son ɗan uwan nasu ɗaya namiji tilo a cikinsu.

     To har dai gari yay tsit alamar rabawar dare babu wanda ya dawo da ga asibitin. Hakama sauran ƴan biki babu wanda ya farga da rashin su Ummi balle tunanin rashin kawo amare har yanzun.


*_WASHE GARI_*


           Sassanyar iskar sanyin asuba, da sabo da tashi sallar asubar ne ya saka Hibbah farkawa da ga nannauyan barcin da ya dunƙule rayuwarta tun daren jiya bayan master ya maidota hankalinta da ga sumarwa. Da ƙyar ta iya buɗe idanun da sukai mata matuƙar nauyi. Ta kai hannu bisa kanta da ya sara mata tana ambaton, “Wash ALLAH Ummi kaina”.

        Jin shiru babu alamar Ummi a kusa da ita ya sakata ƙoƙarin ganin ta tashi duk da azabar da kan nata ke mata ga jiri-jiri hajijiya-hajijiya na ɗibar idanunta da taketa kokawar ganin ta buɗesu ko kaɗanne.

         Da ƙyar ta iya tashi zaunen cikin lalube ta jingina jikinta da fuskar gadon. Tsahon mintuna kusan goma taja a zaune haka duk da kuwa kunnuwanta na jiyo mata salla a mabanbanta masallatan da takejin tamkar bana anguwarsu ba. Sai da yanayin nata ya ɗan dai-daita ta sake shiga kokawar buɗe idanun tana ambaton sunayen ALLAH.

        Dishi-dishi take ganin ɗakin da ya kasance baƙo a gareta, har ganin nata yaɗan dai-daita. (Tabbas wannan ba ɗakinta bane, ba kuma ɗakin Umminta bane, to inane?) ta ayyana a zuciyarta tana sake bin ɗakin da kallo cikin ƙarfin hali. (Sabon gidan mu) zuciyarta ta sake ayyano mata duk da bataji gamsuwa ba a cikin ranta.

    Kokawar son tunano abinda ya faru jiya ta shigayi da zuciyarta. Cikin amincin ALLAH kuwa komai ya shiga dawo mata dalla-dalla. Ƙirjinta yay wata azabar bugawa ta zabura da niyyar dira a gadon sai dai rashin ƙarfin jiki ya dakatar da ita ga hakan. “Innalillahi wa-inna'ilairraji'un inane nan? Wanene na shiga motarsa?”.

        Ta faɗa a fili jikinta na rawa. Sakkowa tai a gadon cikin dabara, tai ƙoƙarin kunna wutar ɗakin mai haske. A take kuwa ko ina ya gauraye kasancewar akwai wutar. Da bin bango ta nufi ƙofar data gani, sai dai koda ta murza a kulle take. A take wani tsoro ya sake dirar mata a rai. ta zame a hankali tai ƙasa zuciyarta na wani irin tsitstsinkewa. (Idan har hasashenta yayi dai-dai azzalumi Abba ne ya farga naji sirrinsu yasa aka satoni aka kawo nan. Shikenan an ɗaura auren yayunna da ƴaƴansa. Shikenan zai kashe min ƴan uwa) ta shiga ayyano hakan a ranta. Tai saurin dafe kanta da ya sake sara mata.

     “Abba mi mukai maka da zafi haka? Miyasa kai azzalumi ne maci amana. Ya ALLAH ka karemin ahalina daga cutarwar waɗanan azzalumai fasiƙan mutane. Ya ALLAH bamu da wani ƙarfi sai naka, kai ne bangonmu abin jingina ka tallafi maraicinmu dana mahaifiyarmu ka bamu kariya”. Yanda take maganar tana kuka abin tausayi.

    Sai kuma taɗan zabura saboda tunowa da ko sallar Azhar na ranar jiya batayi ba. Dan a dai-dai lokacin da akeyinta tana tare da su Abba. Miƙewa tai a zabure. Duk da jirin da ke kwasarta bata saurara ba sai da ta dangane da ƙofar da take ƙyautata zaton toilet ne da ƙyar. Cikin sa'a kuwa ta samu toilet ɗinne, duk kuma abin amfani akwaishi a ciki. Shawarar zuciyarta tabi cike da dauriya ta haɗa ruwan wanka mai zafi sosai, kayanta ta cire tana faman layi da dafe kai. Bayan ta cire kayanta da ƙyar cikin ruwan ta shige gaba ɗayanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya da numfashi. Yanda ruwan ke ratsa kowacce gaɓa ta jikinta haka jijiyiyin jikinta ke saki a hankali wani ɗan ƙarfi-ƙarfi na mamayeta. Sai da taji hankalinta ya dawo jikinta kafin ta miƙe daga ruwan da har ya huce tai wanka sama-sama. Ganin sabon brush ya sata ɗauka tayi sannan ta ɗaura alwala. Tasan bata da wasu kayan anan. Babu kuma tabbacin samu dan haka ta maida wanda ta cire ta fito. Dan gaba ɗaya hankalinta kuma ya koma ne ga sallolin da ke a kanta.

      Ɗan kwalinta ta shimfiɗa a ƙasa tare da ɗaukar yagaggen hijjab ɗin ta ta ƙulle daidai wuyan ta saka tama mamakin yanda akai ya yage haka ta tada salla. Duk yanda shaiɗan yaso mata kutse cikin sallar da bijiro mata damuwa da tashin hankalin da take a ciki haka ta dinga turesa tai sallarta a tsanake tana faman zirar da hawayen. Tsaf ta kammala rama sallolin har zuwa sallar asubahi. Taja doguwar addu'a akan wannan yanayi da suke ciki tana kuka. Ta jima a wajen zaune har rana ta fito sosai. Agogon ɗakin ta kalla, ganin takwas har tayi yasata miƙewa ta sake nufar gadon saboda yunwar da takeji da rashin ƙarfin jikinta. Karaf idanunta suka sauka akan wayarta dake tsakkiyar gadon, da alama dai a wajen bacci ta fita da ga cikin zaninta. Wani irin daɗi ne ya lulluɓeta. Ta kai hannu ta ɗauka da sauri tana murmushi da share hawayenta. Cikin rawar jiki da matsanancin ɗoki ta danna kiran number yaya Muhammad.

         Sai ɗan yarfa hannuwanta ta ke da cizar lip ɗinta na ƙasa cike da zumuɗin son jin ya ɗauka......

       “Ko zaki shekara kiransu bazasu gani ba, koda kuwa ta shiga ne”.

     Wata ƙasaitacciyar murya ta faɗa a bayanta. A zabure Hibbah ta juyo duk da rashin ƙarfin da jikinta ke da shi. Babu shiri ta sake zabura tai baya, duk da kuwa tayi tunanin shiɗin zata gani anan tunda yaron su Abba ne. “Shuraim?!” ta faɗa a ɗan kausashe tana masa wani irin kallon tsana.

        “A.K.A Master!”. Ya faɗa yana cigaba da takowa cikin izza da kasaitarsa tsakkiyar ɗakin. Sai da yazo gab da ita ya kai hannu saman face nashi ya cire facemask ɗin face ɗin Shuraim.

       “What?!!”. Hibbah ta faɗa tana sakin wayarta ƙasa a ɗan firgice.

      Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki da cigaba da takawa gabanta har yanzu hannayensa duka na zube cikin aljihun wandon jeans ɗin jikinsa. Ganin yanda ya ke tinkarota yasa ta fara ja baya tana jifansa da wani irin kallon tsana da ruɗanin ganin facemask a matsayin fuskar Shuraim, (kenan sace Shuraim yayi ya maye gurbinsa da shi?). Jin ta dangane da jikin bango ya sata rumtse idanunta da ƙarfi zuciyarta na wani irin harbawa dan gaba ɗaya tama rikice, gashi babu ƙarfin yin tsiwar dake cin ranta gareshi.

      Sosai ya matsa jikinta har suna jin fita da saukar numfashin juna. Hibbah ta sake maƙurewa a bango dan tsoro da rashin sabo. Shiko tsumammun idanunsa ya zubama fuskarta tare da zaro hannunsa ɗaya daga aljihun wandon ya ɗaura bisa bangon ya tokareta ganin zata zille.

       Matse jikinta tayi da sake rumtse idanunta dan har cikin ranta bata fatan ya taɓata kodan tuna ƙazantar da suke aikatawa shi da su Abba da tayi. Shiko fuskarsa ya sake kaiwa gab da tata tamkar zai haɗe bakinsu sai kuma ya waske akan kunnenta. Cikin kaushin muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara magana,

        “Babu farauta mafi wahala a duniya sama data *_DAMEESA_*. Da ga yau da ga yanzu ki sani. Master tamkar google yake. A kowane lungu da saƙo yanada ido tamkar google a yanar gizo. Duk wanda ya ce zai hanani barci, shima bazaiyi nasa ba. Ina fatan kin ganee karatun?!!”.

    Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga hanunsa jikin bangon cike da tabbatarwa da kaushin murya yana jan jikinsa baya.

      Nannauyan numfashi Hibbah ta fisga jin ya matsa a jikinta. Ta buɗe idanunta ta watsama bayansa da ya juya harara. Cikin yunƙurowar tsiwar tata da a yanzu ta samu filin fita tace, “Ni kuma Muhibbat Aliyu Hamza gwarzo sai na karya wannan alwashin naka, ina a cikin gidan nan tare da kai zanyi sanadin da za'a faraucekan cikin sauƙi a kuma kama ka. Idan takamarka haɗa hannu da munafukai kuna zaluntar mutane ku sani ko'ina bazakuje ba. Kuma wlhy ko ƙwarzane ya sami ɗaya da ga cikin yayuna sai kayi nadama da ga kai harsu ƙazamai masu ɓoyayyar manufa suna aikata ƙazanta da fasadi aban ƙasa. Shuraim kuma da ka saci fuskarsa kazo ka wargaza aurenmu a ranar ɗaurasa, idan ma ɓoyesa kai ko halakashi kasani sai na ɗiba fansar jininsa akanka”.

          Wani shegen malalacin murmushi ya saki. Tare da fara tafa hannayensa a hankali yana juyowa gareta cikin salo da ƙasaita. “Nice baby girl, ina son irin haka👌🏼.”

        Sai kuma ya tamke fuska yana sauke mata razanannen kallon da har cikin ranta takejin hantar cikinta na kaɗawa. Amma tsaurin ido da tsiwa ya sata ƙoƙarin danne hakan tana hararsa harya ƙara takowa inda take.

       Gira ɗaya ya ɗage da yin mutsu-mutsun fitina da idanunsa. “Da ni Master kike tunanin yin *_TAKUN SAAƘA?._* Lallai zan baki dama, tabbas kuwa zan baki, amma sharaɗin faɗuwa ko nasara zan zartar da sune a lokacin da ɗaya ta kasance.....”

       “Ko ka bani ko karka bani dama damata a hannuna take na tona muku asiri. Satoni da kukayi nan bashine ke nufin nasara ba ko cigaba da rufuwar sirrinku. Ɗaura auren yayyena da ƴaƴansa da kuka ƙulla bashike nufin nasarrku akan ahalina ba. Dan haka ka sani, *_TAKUN SAƘA_* da kai dama a cikinta nake tsundum. Dan koba komai a harin farko na maka TAMBARIN da ya saka gudun ceton rai batare da kayi tsammani ba mai idon google”.

     Ƙafa yasa ya taɗeta ta faɗa saman gadon, cikin zafin naman da ALLAH ya azurtashi da shi ya ɗaura ƙafarsa ɗaya akan gadon tare da ranƙwafowa kanta. Ƴar mitsitsiyar bindigar da ya zaro a aljihun bayan wandonsa ya ɗaura mata a kan kunne yana zuba firgitattun idanunsa cikin tsakkiyar nata. “Zan iya kasheki a cikin wannan gidan. Na binne gawarki batare da wani mahaluki ya taɓa tunanin binciko inda na kafa ramin ba”.............✍


        

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_______________________


*_Chapter Twenty Five_*


...........Hibbah ta haɗiye yawu da ƙyar da ƙoƙarin haɗiye tsoronta ta zuba masa harara. “Dan ka kasheni ai ba abin mamaki bane, mutumin da ya ke gawurtaccen ɗan Homo ne kashe rai zai zama abin damuwa a garesa, wama yasan iya adadin nawa ka kashe ka binne a gidan”.

      A yanda tai maganar cikin tsoro da ƙarfin hali yay matuƙar bashi dariya. Sai dai ya shanye abarsa cikin rai, a zahiri ma sai sake tamke fuska da yay yana yamutseta. Ya janye bindigar a kanta tare da kaita ya ɗan buga a saman laɓɓanta. “Wannan bakin naki shine zai halakaki stupid girl”. 

      Ya faɗa yana sauke ƙafarsa ƙasa da miƙewa da ga ranƙwafowar da yay a kanta yana ƙwafa. Nannauyan numfashi Hibbah ta sauke a ɓoye da lumshe idanunta ganin ya fice a ɗakin ko waiwayenta baiyi ba, tai saurin kai hannu saman ƙirjinta ta dafe saboda yanda yake bugawa da sauri-sauri. Dan harga ALLAH ƙarfin hali kawai tayi da ganin wannan bindigar akanta. Ga shegun idanunsa da ke saka zuciyarta tsargawa tamkar zatai zallo ta fito waje idan ya zuba mata su. A fili tace, “Gashi ɗan iska ɗan homo, amma sai shegen kwarjini.


(Hibbarmu karki sake kiji tsoronsa. Dan karma su o.e ƙannensa suji kansu ya ƙara girma ehe😖😎🚶🏻😏.)


★★★★★★


        

            Dauriya Ummi kawai takeyi na rashin ganin Hibbah bata shigo musu ba har kusan goma na safe. Tanaji a ranta anya su Yaya Muhammad basa ɓoye mata wani abu kuwa? Dan babu yanda za'ai su kwana gida ɗaya da Hibbah ta iya haƙurin kawai yanzu bata nema inda take ba. Musamman anan da take ganin sabon gida tunda ba'a taɓa zuwa da ita ta gani ba sanda ake ginin. Hasalima babu wanda ya taɓa sanar mata ita da Ammar. Sai da ga baya ne Ammar ɗin ya sani, suka kuma gargaɗesa da kar ya faɗama Hibbah.

          Shigowar Isma'il gidan kusan sha ɗaya na safe ne ya ɗan rage mata ƙulafucin son ganin Hibbahn. Bayan sun gaisa cike da girmamawa yay mata bangajiyar biki tare da yima anguna addu'ar zaman lafiya.

       Cike da kulawa a garesa Ummi da ke murmushi ta ce, “Saura kai Isma'il. Ya kamata ka nemo matar aure haka nan, dan shi aure cikar kamalace ta ɗan adam koda ace ya kasance mutumin banza ne. Idan kuma kaima irin nasu Usman ɗin zan maka to”.

       “Ƙayataccen murmushi ya saki da sake duƙar da kansa yana shafa ƙeya. Ummi karki damu kiyimin addu'a kawai”. Ya faɗa murya a tausashe saboda yanda yake jin Ummi matuƙa a rai kodan yana ƙishirwar mahaifiya.

        “Kullum addu'ar nan ita muke muku Isma'il. ALLAH ya cigaba da tsareku a duk inda kuke. Ya baku kariya da ga dukkan abun ƙi. Yay muku albarka ya baku ƴaƴa nagari da zasu kwatanta muku ƙyautatawar da kuke mana da biyayya”.

        Tasowa yay ya durƙusa gaban Ummi hawaye na ciko idanunsa, yay haɗiyesu da ƙyar yana faɗin, “Amin ya rabbi Ummi nagode”.

       Hannunta ta ɗora saman kansa ta shafa dan tsaf ta fahimci abinda yake buƙata kenan. Tausayi yake bata yaron har cikin rai, dan ta jima da nazartar yana matuƙar bege da ƙishirwar mahaifiya ne.

          “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai albarka Ummi”.

      “Amin Isma'il”. Ta faɗa tana murmushi da sake shafa kansa har fararen haƙwaranta na bayyana.

           “Uhmm kaga ɗan gatan Ummi, ashe kana nan?”. Su yaya Abubakar da ke shigowa suka haɗa baki wajen faɗa suna kallon Isma'il ɗin. Ƙaramar dariya yayi da miƙewa da ga gaban Ummin ya koma inda ya taso. “Gara nai sauri na kwashi rabona kafin kuzo ai mana raba dai-dai.

       Usman da ke dariya ya ce, “Gaskiya Yaya Isma'il i'm jealous”.

       Dariya suka sanya gaba ɗayansu harda Ummi. Kafin su ƙaraso cikin ɗaki su mimmiƙa masa hannu har Yaya Muhammad. Da ga haka suka zauna aka dasa sabuwar hirar da ta sake ɗauke hankalin Ummi duk da kuwa zuciyar tata naga son ganin Hibbah ta shigo. Dan a cikin firarma sunayi suna sakko sunanta da rashin jinta suna dariya. Basu taso gaban Ummi ba sai ƙarfe ɗaya suka fita massallaci. Da ga nan Isma'il yay gaba su kuma suka koma cikin gidan da yake ya ƙara cika da dangin amare ƴan buɗar kai dan yau anguna zasu shiga ɗakunansu.


★★★★★


          A ɓangaren Abba kam barazanar rashin barci da ya fuskanta a daren jiya ce ta kaisa ga makara sai kusan takwas ya farka. Farkawar ma ba kaitsaye yayita ba masifar Momy ce da ta dawo asibiti ta gansa yana barci ta farkar da shi.

       “Yanzu wannan wane kalar rashin mutunci ne haka Hadiza? Ina tsaka da barci kizo ki tadani saboda rashin mutunci”.

        “Ni da kai a tantance mara mutuncin Abban Junaid. Yanzu dan ALLAH ko kunya bakaji ba ɗan ka namiji tilo na asibiti rai a hannun ALLAH amma kai kana nan kana barci hankali kwance. Bakaje kaga halin da yake a ciki ba baka ɗauki wani matakiba kuma ga wanda ya aikata masa. To sai ka miƙe dan Asiya da yaranta duk basa gidan nan. Yanda alamu ma suka nuna basu kwana ba a cikinsa”.

       “What?!”

Ya faɗa yana wantsalowa da ga gadon ƙirjinsa na wani irin bugawa. “Hadiza wace maganar banza ce wannan. Ita Asiyan idan ta fita anan gidan ubanwa zataje tunda bata ajiye kowa ba bayanan nan ɗin?”.

       “To waya san ko tana da wajen zuwan abu a duhu. Ga dai Hajiya mama can ta gama bincike ko ina na gidan nan ita da su Garba amma babu komai kama da su. Alamuma sun nuna dama da shirin hakan tare da su dan duk sun tattare kayansu masu muhimmanci da ga sashen”.

      “Kutuman bura'uban nan kayyasa”. Abba ya danna ashariya tamkar ɗan gidan maguzawa. Ita kanta Momy jin ashariyar tasa sai da ta zaro idanu waje. Hannu yasa ya ingijeta tare da fisgar sandarsa ya yo waje. Tun daga sama yake hango su kawu bello tsaye cirko-cirko a falo cike da tararrabi.

       Bai iya tanka musu ba tsabar rikicewar da yay ya fice da sassarfa duk da azabar da yakeji sabuwa ƙafarsa na masa.


      Tabbas babu alamar Ummi da ƴaƴanta a gidan. Wannan al'amari ya matuƙar hautsina kan Abba. Babu shiri ya shiga bige-bigen waya. Kafin ya tattara yabar gidan batare da ya tuna da ƙarin sallar asuba da ke a kansa ba bayan sallolin jiya da bai sauke ba har yanzun.

       Yayinda ya bar ƴan biki nata kace nace akan wannan al'amari. Harda masu yima ƴaƴan Ummi da ita kanta addu'ar tsiya suna mai goranta mata asalinta. Oho bama tasan sunai ba, su aiki ya sama😜👎🏻.


★★★★★


        A ɓangaren Hibbah kam Master na fita babu jimawa taji sallama a ƙofar ɗakin tare da knocking. Sam jikinta babu wani ƙarfi dan yunwa takeji matuƙa ga rashin ƙarfi. Hakan yasa tun bayan fitarsa bata motsa da ga inda take ba. Tunanin shine ya sake dawowa ya sakata harar ƙofar tamkar idanunta zasu faɗo. Ta kuma ƙiyin magana.

    Baba Saude dake tsaye ta sake ɗan buga ƙofar da ɗaga murya sosai wajen sallamar. Ɗan zabura Hibbah tayi jin muryar mace. Ta amsa da ƙoƙarin son tashi, sai dai kafinma ta tashin Baba Saude da taji an amsa mata harta shigo abinta ɗauke da tray.

     Wani irin daɗi ne ya tsarga zuciyar Hibbah ganin mace. Macen ma babba da zata iya kira uwa ko kaka. “Sannu mama” ta faɗa cikin girmamawa. Murmushi baba Saude tai mata tana ajiye trayn.

       “Yauwa ɗiyata sannu kinji. Yaya ƙarfin jikin naki?”.

       Da ɗan mamakin jin abinda tace Hibbah ta dubeta. Har zatai magana sai kuma ta fasa ta amsa da “Alhmdllh mama”.

     Baba Saude ta ce, “Masha ALLAH. ALLAH ya ƙara afuwa kinji. Babana yace ga abinci kici”.

      (Babana) Hibbah ta maimaita sunan a zuciyarta tana gyaɗama baba Saude kai batare data sani ba. Baba Saude da har cikin ranta kallon mara lafiya take ma Hibbah saboda yanayinta ta fice abinta ganin kamar batason hayaniyar.

     Jin ƙarar rufe ƙofar yasa Hibbah ɗan zabura tana ƙoƙarin dakatar da ita. Sai dai harta fice abinta. Kanta ta dafe tana cije lips nata dan takaici. Sai kuma ta duba trayn abincin da ƙamshinsa ya gauraye ɗakin tunkan ma ta buɗe. Cikinta ta shafa dan babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar abincin. Hakan yasata miƙewa ta nufi trayn da tunanin abincin kawai zataci ta samu ƙarfin yin tunani akan halin da take ciki a yanzun.

       Lafiyayyen abincine da ƙamshinsa kawai ya isa saka ma'abocin ganinsa kwaɗayin fara ci. Duk da zuciyarta na gargaɗarta da cewar kartaci na ɗan homo ne sai ta kasan daurewa saboda yunwa. Jikinta har ɓari yake ta haɗa ruwan tea duk da bai wani dameta ba ta fara sha. Dan tasan yanda yunwar nan ta cita shine kawai zata fara sha ta samu nutsuwa. Ai ko cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala wata irin zufa ta fara karyo mata. Yanda yake ratsa jijiyarta yasa dole sai da takai kwance na wasu ƴan mintuna. Sai da ya nutsu a cikin jikinta sannan ta sake miƙewa ta hau cin lafiyayyen breakfast ɗin shima. “Alhamdulillahi” ta faɗa a hankali jin uwar hanjinta ta ɗauka. Hakan ya sata miƙewa zuwa saman gadon ta sake kwanciya ƙananun zufa na cigaba da tsatstsafo mata.

           Idanu ta lumshe dan zuwa yanzun hankalinta ya fara dawowa jikinta. Sai kuma ƙwaƙwalwarta ta shiga kai kawon lissafi da tariyo abinda ya faru jiya akan bin bayan Abba da tayi. (Idan har lissafinta yayi dai-dai tun farko dama A.G da Abba tare suke. Da farko ta shiga rayuwar ƴan sanda a dalilin jefama masu power rider na'urar bibiya. A dalilin bincike da sukayi akanta suka gano ita ɗin wacece kuma ɗiyar wanene?. Ta wanann hanyar A.G yasan tana da alaƙa da Abba abokin shaiɗancinsa. Zata iya yuwuwa ya sanar masa komai da ya faru shine shi kuma yay amfani da wannan damar wajen saka A.G ya cigaba da amfani da ita wajen bata ayyukan Master da sukace yaronsu ne. Su kuma zasu dinga samun sirrin ƴan uwanta da Umminsu ta wanann hanyar suna musu illa da sunan suna bata kariya batare da sun fargaba.) “Tabbas babu tantama wannan lissafin nawa haka yake. Dan alamu ya nuna lokacin danai tracing wanann shu'umin shegen jami'in can ne ya sanar masa shiyyasa ya gudu. Shi kansa sun maidashi wawa suna amfani da shi da ƙuruciyarsa wajen gina kansu da wargazashi batare da ya sani ba. Wannan itace matsalar da *_MATASANMU_* suke fuskanta a wannan lokacin. Kuɗi da rashin aikinyine rauninsu. Azzaluman kuma sunda kuɗi da faɗa aji a hannunsu. Sai suke amfani da wannan faɗa ajin da kuɗin da matasan ke ƙishirwa su jawosu a jiki suna amfani da ƙuruciyarsu wajen sakasu zama ƴan ta'adda. Shima da alama wannan tarkon ya faɗa. Ya ALLAH!”. Ta kare maganar da dafe kanta da ya sara mata. Duk da sunce amfani suke da shi su gama mora su yadda dolene ta tonama guy ɗin nan asiri ma duniya shi da ubannin gidan nasa. Hakan na nufin kuma zata cigaba da zama a wajensa kafin burinta ya cika. Idan kuma ta zauna Yayunta da Umminta da ke a cikin tarkon su Abba fa?. Kuma hakan bazai yuwu ba sai ta kasance da su suma ta sanar musu gaskiyar shirinsa. Amma kuma wannan mutumin bazai bar hakan ta faru ba. Dan bai sato ta nan danta kuɓuta ba, saboda duk yana cikin shirin Abba na wargaza rayuwar ahalinta.

     Hannu ta kai ta share hawayen da suka silalo mata. Sai kuma ta tashi zaune tare da mikewa ta hau safa da marwa a cikin ɗakin. Lissafin Abba shine sai ƴaƴansa sun sami ciki zai fara salwantar da rayuwar yayyunta. Hakan na nufin dole tayi wani abu kafin nan da wata guda kenan. Babban abinda zatai kuma shine nutsuwa ta fahimci nan ɗin da aka kawota. Na biyu tai iya ƙoƙarinta na tattara bayanai akan wannan mutumin acikin wata guda ɗin nan shi da iyayen gidansa. Na uku duk tsanani karta bama kowa wannan binciken idan ta kammala sai Yaya Abubakar. Na huɗu duk yanda za'ai tayi ƙoƙarin yin magana da ko ɗaya da ga cikin ƴan uwanta ne. To amma ta yaya? Tunda shi da kansa ya tabbatar mata kozata shekara nemansu bazata samu ba.

    “Ya rabbi ka agajeni”. Ta faɗa tana dafe kanta. Cikin sauri ta ɗan zabura sai kuma ta saki murmushi saboda tuno wannan dattijuwar data kawo mata abinci. Tabbas inhar tana da waya da ita ya kamata tayi kiran. A kuma sirrance batare da tsohuwar ta sani ba.

       “Kenan zan sato wayar”. Ta faɗa a fili tana ƴar dariyar farin cikin zuwan mafita ta farko a gareta............✍


*_Alhamdulillahi na biya bashin wanann satin duka harma da ɗaya na wancan week ɗin. Asha hutun lahadi lahiya guys. Dangin su Master kuma zamu dawo da hirinmu ne ku kiyayemu😎😖😏🚶🏻_*


  

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_Chapter Twenty Six_*


...........Kai tsaye gidan A.G Abba ya nufa. Dan yasan yau ranar hutu ce baya a Station. Kasancewar basu cika haɗuwa a gidajensu ba yasa da ƙyar maigadin gidan A.G ya yarda yay masa sallama da shi. Dan ya kira wayarsa yafi a ƙirga amma bata shiga.

      Cikin takaici A.G ya fito, dan yayi zaman yin breakfast ne maigadi ya sanar masa zuwan baƙo. Turus yayi na ganin Abba. Sai dai tunda ya gansa babu damar komawa. Dole ya karaso inda yake yana faɗin, “Alhaji Halilu wai dama kai ne?”.

        Kai kawai Abba ya iya kaɗa masa. Kafin ya ce, “A.G akwai babbar matsala fa”.

     Saurin dakatar da shi A.G yay yana ɗan waige-waige. “Alhaji Halilu kayi haƙuri maganar nan bata nan bace. Inaga shigo ciki har motarka”.

    Babu musu Abba ya koma mota. Maigadi ya wangale masa gate bisa umarnin uban gidansa. Koda yay fakin ciki suka shige babban falon baƙi na gidan. A.G na niyyar fita domin kawo masa wani abin taɓawa Abban ya dakatar da shi.

        “A.G ci ko sha duk bashi bane a gabana yanzu, zo muyi magana.”

        “Humm Alhaji Halilu kanada ruɗani kai dai. Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka dan nasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi dai”.

      “A.G bazaka gane ba. Kai dai zauna kaji mike tafe da ni kawai.”

     Babu musu A.G ya koma ya zauna. Abba da ke a firgice ya fara masa bayani muryarsa har rawa take. “Asiya da ƴaƴanta sunbar gidan a daren jiya. Zuwa yanzu kuma bamusan ina suke ba. Hakan ya sake tabbatarmin yaron nan Master ne ya taimaka musu.......”

        Katsesa A.G yay da faɗin, “Master kuma Alhaji Halilu? Wai nikam miyasa duk kake zargin Master ne? Tayaya zai taimakesu miye ribarsa? Bayan kasani na sani akwai jiƙaƙiyar TAKUN SAƘA tsakaninsa da ƴarsu ma. To kai miye ma na damuwa da tafiyar tasu ne? Ba dama ta samu ba na hawa kan dukiyar da kake dako tsahon shekaru kaci karenka babu babbaka”.

         “A tunaninka kenan. Amma da ga abinda ya faru zuwa yau ka auna da hankalinka da ka fahimci inda alkiblar yaron nan ta dosa mana. A wannan karon da alama burgar banza kakeyi baya tare da kai. Dukiyar nan kuma da kake ganin zan cita cikin sauƙi bazata ciyu ba, koka manta duk kaddarorinsa sunayen ƴaƴansa ya sa matsayin next of kings. Wasu kuma sunan Asiyar ne ma”.

      “Hhhh wannan ganganne Halilu. A yanda na raini Master ni da abokan aikina bai isa zillemana ba ya maidamu abokan TAKUN SAƘAr sa. ai kaima kasan ko a gidan giya akwai babba. Maganar dukiya kuwa shi da kansa ma zai mana aikin”.

       “Ni duk ban musa maka kun raini master da wani blaa blaa ɗin zancenka ba. Yanzu so nake ka kirasa ka bigi cikinsa ko zamu san inda su Asiya suke. Sannan duk yanda za'ai inason ka samamin ma'aikacin banki da zaimin aikin sirri kuɗaɗen dake a accaunt ɗin Aliyu su dawo accaunt ɗina baki ɗaya, ka kuma saka shi Master ɗin nemo mana lauyan Aliyu duk inda yake”.

        “Maganar kiran Master ba damuwa bane, hakama zancen canja kuɗi zuwa accaunt ɗinka koshi zai iya mana wannan aikin.  Matsalar ɗaya ce ka yarda Master bazai zama shashasha akan mace ba. Macen ma ƙaramar yarinya kamar ɗiyar ɗan uwanka”.

         “To naji na yarda kirashi”. Abba ya faɗa badan ya yarda ɗin ba har cikin rai. Dan yanaji a jikinsa Hibbah tayi shu'umcin na mata akan Master. Sai dai shi A.G tsananin yardar da ya bama Master ɗinne yasa bai fahimtaba.

        “Kiran Master bazai yuwuba a yanzu. Amma zan tura masa saƙo da kansa zai biyo lokacin da yaga ya dace”.

     “To ashe kuwa yau a gidanka zan kwana”. Abba ya faɗa kansa tsaye.

     “Gidana kuma?”.

“Ƙwarai kuwa. Dan babu inda zanje saina tattauna da Master.

       “Humm Alhaji Halilu kai fa sam baka da haƙuri. Maganar zama anan bazai yuwuba. Kaje zan sameka gidan hutawarka. Kokuma mu haɗu wajen su Alhaji Alu”.

      “Kawai jeka shirya ina jiranka mu tafi tare”.

             Ɗan tsaki A.G yaja dan Abbah ya takura masa. sai dai babu yanda ya iya dole yace ya jirasan to.


       

★★★★★


            A ɓangaren Hibbah kam Shawarar data yankema zuciyarta ne ya sata sauka a gadon ta nufi toilet. Fuskarta ta wanko ta fito. ɗaukar tray ɗin kwanikan da tai breakfast tai ta fita da addu'ar ALLAH yasa yabar gidan. Babu inda ta sani amma tsabar ƙarfin hali yasata yarda zata gane. Taji matuƙar daɗin ganin baya falon, taɗan tsaya yima falon saman kallon tsaf. Sosai tsarinsa ya mata ƙyau. Ga wani ƙamshi mai daɗi da sanya zuciya nutsuwa na tashi duk da mayataccen ƙamshin turarensa na neman dannewa. Tunaninta ya bata baza'a samu kitchen anan ba, dan haka ta nufi downstairs ɗin kai tsaye.

        Tunda ta fara tako staps ɗin su Adam dake zaune a dining suna breakfast suka ɗago kusan a tare. Hibbah da ke sakkowa tayi ɗan turus ganin matasan samari kusan bakwai. (Su kuma waɗan nan fa?) tai tambayar a zuciyarta. Kai tsaye zuciyarta ta sake ayyana mata (Kin manta minene aikin mai gidan, ba dole kiga maza ba tare da shi). Tsaki taja a ƙasan maƙoshi tana ɓata fuska. Akan laɓɓanta tace, “Asararru”. Tana cigaba da sakkowa.

        Suko su Habib tuni sun maida kawunansu ƙasa tun kallo guda da sukai mata. Tana sakkowa step ɗin ƙarshe suka haɗa baki wajen faɗin, “Barka da safiya aunty”.

       “Aunty?!” ta faɗa tana kallonsu cikin ware idanu. Sai kuma ta turo baki, “Kujimin mutane dan ALLAH. Rusa-rusa daku zaku wani kirani aunty wannan ai zagi ne”.

        “Tofa ga mai gayya mai aiki, Kunga wata zuƙeƙiyar halitta.

Cewar Salis a hankali.

    Zungurinsa Zaidu yayi cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Karkai maganar banza matar babban yaya ce, akwai tazarar taku”.

     “A gafarceni wlhy suɓutar baki ce”.

      Baba Saude da ke zaune da ga can falo tana murmushi ta ce, “Kinga manta da waɗan nan shaƙiyyan ɗiyata. Keda baki da lafiya ai da baki fitoba kinma barsu zanzo na ɗauka.

       Sai da Hibbah ta ɗan harari su Musbahu da murguɗa baki duk da bawai jin mi suke faɗa tayi ba sannan ta maida dubanta ga baba Saude tana sakin murmushi. “A'a babu komai mama. Ai naji sauƙi Alhmdllhi. Inane kitchen ɗin?”

       Cikin jin daɗin wayewar kan yarinyar da ko alamar baƙunta babu tattare da ita ta nuna mata hanyar kitchen. Kan Hibbah tsaye ta nufi kitchen ɗin kuwa. Komai ƙal fes tamkar ba girki aka kammala a cikinsa ba. Ganin hakan yasa Hibbah ajiye kwanikan a wajen wanke-wanke ta fara yunƙurin wankewa.

      Motsin wanke-wanken natane ya saka Baba Saude shigowa. “Ya ALLAHU ƴar nan inake ina wanke-wanke kina fama da kanki. Ki barsa su Habibu zasuzo su wanke idan sun gama shiritar cin abin nasu”.

        (Uhm ai da yake ƴan daudu ne) Hibbah ta ayyana a ranta. A fili kuma sai tai ɗan murmushi. Karki damu mama zan wanke kawai. Ina maza ina wanke-wanke banda dai gidan naku a haguggunce yake”.

      Baba saude da ba fahimtar ina Hibban ta dosa tai ba tai ƴar dariya da faɗin, “Taɓ. Ai indai waɗan canne komai yi suke har girki. Babana ya musu horon tarbiya mai ƙyau ai. Sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi”.

        Ɗan kallonta Hibbah tayi danjin abinda ta faɗa. Sai kuma ta saki guntun murmushi. “Mama iyayensu dai, shi da ya samesu da ga sama ai ba'ace tarbiyyarsa ba”.

       “To ƴar nan ai shine iyayen nasu. Dan dukansu da kike gani nan shi yay wahala da su tun daga gidan marayu, yawancinsu ma tun suna jarirai. Tarbiyarsa ce, horansa ne. Shine uwa a garesu shine kuma uba. Shine dangi. Ai samun mutum irin babana a wannan zamanin abune mai matuƙar wahalar gaske. ALLAH dai ya saka masa da alkairi ya cigaba da dafama rayuwarsa.”

        Karon farko da Hibbah tai sagade tana kallon Mama Sauden. Dan ba karamin dukan zuciyarta zancen yayi ba. Sai kuma tunawa da fasikancin da su Abba ke aikatawa da shi da tai yasata juyawa tana taɓe baki. A ranta tace (dan ya taimakesu shine kuma ya ajiyesu yana ɓata musu rayuwa kenan. ALLAH ya saka musu).

        Baba Saude da bata fahimci abinda Hibbah tai ba ta cigaba da bata labarin ƙoƙarin Master da jarumtarsa akan su Khalid na tsayama rayuwarsu har suka sami ingantaccen karatu a fanin islama da boko. Hibbah dai gyaɗa kai kawai take, dan zancen wani na shiga wani na fitane kawai. Ita duk wannan tarin alkairin nasa bawai gani take ba sam. Tsiyar da suke aikatawa da su Abba ta goge mata duk wannan farin nasa baƙi ya maye gurbinsa.

      Sai dai cikin son bugar cikin Baba Sauden sai catai “Uhm lallai yaci sunan nasa Muhammad Shuraim”.

         Baba Saude tai ƴar dariya da faɗin, “Wai ƴar nan kinko iya faɗar sunan. Ni wlhy wahala yake min sunan nan nasa na larabawa. Shiyyasa nafi ganema kiransa da baba na saboda asalin sunan sa”.

      Gaban Hibbah ne ya faɗi. Kenan sunansa ne Muhammad Shuraim ɗin? Da sauri ta juyo tana duban baba Saude. “Oh mama bayan Muhammad Shuraim ɗin yana da wani sunan yanka ashe?”.

        Baki Baba Saude ta buɗe zata bama Hibbah amsa Habib ya shigo kitchen ɗin wuff tamkar an jehoshi. Waya ya mikama Baba Sauden. “Baba Master na magana”.

         Cike da farin ciki Baba Saude ta amsa wayar takai kunnenta da faɗin, “Alo babana”.

     Batare da Hibbah tasan mi ake faɗa da ga can ba taga Baba Saude na gyaɗa kai da faɗin, “To to babu matsala babana sai a dafa maka. ALLAH ya dawo dakai lafiya”. Da ga haka ta mikama Habib wayar. A dai-dai nan kuma su Salis suka shigo ɗauke da kwanikan da sukaci abinci.

    Ganin Hibbah ke wanke-wanke suka zaro idanu waje. “Aunty da kanki? Rufa asirinmu kar boss yay mana walmakalufatu”.

     Cikin bata fuskar haushi biyu Hibbah ta juyo tana dubansu. “Malami kubar wani kirana da Aunty niba auntynku bace.”

         Dariya kawai sukayi batare da sunce mata komai ba. Sai ma Habib da ya sake faɗin, “Aunty kibar wanke-wanken zamuyi Please”.

     Harara ta dallara masa. Yay saurin ɗora hanunsa saman baki yana faɗin, “Na tuba”.

     Dauke kanta tai batare data tanka ba. Idris ya matsa tacan gefe yana tattare hanun rigarsa. Bara to na miki ɗauraya kawai. Banza tai masa ta cigaba da wanke kwanikan a cikin kumfar data ƙara ganin sun ƙaro kwanikan. Wannan taruwar tasu a kitchen ɗin ya hanata jin ɗayan sunan na Master. Hakan kuma ba karamin takaici ya sakata ba shiyyasa ta haɗe fuska har suka kammala wanke-wanken bata sake kulasu ba. Sai sauraren hirarsu da Baba Saude da takeyi. A ranta kuwa sai gulmarsu take wai sun cika surutu.

         Suna kammala wanke-wanken Baba Saude tace taje ta huta zata ɗaura girkin rana. Cike da jin daɗin hakan Hibbah tace zata tayata. Duk yanda Baba Saude ta lallaɓata akan tabari sai ta ƙara jin sauƙi ta dage zatayi. Fahimtar yarinyar babu ruwanta akwai sauƙin kai yasa baba Saude barinta sukai girkin tare. Kusanma Hibbahr ce tayi komai kaɗan baba sauden ta tayata.

      Har sukai girkin suka ƙare tas Habib na nane dasu a kitchen ɗin yaƙi fita. Hakan ya ƙarama Hibbah takaici matuƙa dan bata samu yanda take so ba.

        Sai dai cikin sa'a Baba Sauden ta fita jera abinci dining dai-dai Habib ɗin yana fita a kitchen ɗin saboda lokacin salla yayi zasuje massallaci.

         Harara ta raka bayansa da shi tana sauke numfashi, dan duk surutunta da rawar kai ta kula waɗan nan samarin sun damata sun shanye. Sauran kayan da suka rage ta ɗakko ta fito zuwa dining ɗin itama. Tana tsaka da taya baba Saude shirya kwanikan taji ƙarar waya nokia. Da sauri baba Saude ta nufi falon tana faɗin, “Tofa wake kirana ni Saudatu?”.

        Wani ɗan tsalle Hibbah tayi dadi kamar zai karta. Sai kuma tai saurin kama kanta ganin baba saudan ta dawo dining ɗin tana faɗin, “To nidai Bara'u banajinka sam. Nasan dai so kake kayi magana da Zaituna gashi kuma bana gida ina wajen aiki. Ka kira wayar Habu mai shago sai ya bata dan nasan yanzu ta dawo gida”. Da ga haka ta cire wayar a kunnenta tana mita.

        “Kai samarin zamani dai babu kunya. Kigafa wanann ja'irin ɗan makwafcinane. Akwai ƴar maƙwaftanmu da yake so bata da waya kullum sai ya kira a wayata sunyi wayar dare. Yau kuma bansan wace fitina tasashi kira da ranar ALLAH ba”.

      Hibbah da ke cikin jin daɗi tai ƴar dariya kawai.

        Baba sauden ma sai bata sake cewa komai ba ta ajiye wayar a dining ɗin ta cigaba da aikinta. Aiko wani sanyi ya sake sauka a zuciyar Hibbah. Cikin dabara da wayon da ALLAH ya bata ta shiga gyara zaman kayan dining ɗin harta iso ga wayar. Cikin dabara ta ɗauka tai ƙasa da ita tasa a silent. Kafin ta faki idon Baba Saude ta tura a cikin zani.

       A dai-dai wanann lokacin Master ya turo ƙofar falon ya shigo da sallama ciki-ciki. Cike da mutuntawa a garesa baba Saude ta washe baki tana faɗin, “Babana sannu da dawowa”

        Saurin juyowa Hibbah da sam ba jin sallamarsa tai ba tayi, idonta ya sauka akansa dai-dai yana gyaɗa ma Baba Saude kansa. “Baba ya gidan?". Ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin wuce Hibbah da ya nuna tamkar ma bai ganta a falon ba.

      “Gida Alhmdllh babana. Dan yau na ƙara samun ƴar tayen hira”.

    Sarai ya fahimci Hibbah take nufi, dan haka ya fara hawa steps ɗin kawai batare da ya sake cewa komai ba.

      Harara Hibbah ta raka bayansa da ita. Wani sashe na zuciyarta najin tsananin takaicinsa da kallonsa mutum mai tsananin girman kai da wulaƙanci. Sai da ya ɓacema ganinta ta ɗauke kanta da duban Baba Saude, “Uhm Mama tunda mun gama nima bara naje nai salla”.

     Juyowa baba saude da ke nufar kitchen tai ta dubeta. “Eh ɗiyata kin fini gaskiya kam. jeki kiyi nima bara na haɗa ma Babana abinci da Habibu sun dawo sai ya kai masa saman”.

        “To mama”. Hibbah ta faɗa tana nufar upstairs. Harta hau step na biyu baba Saude ta dakatar da ita. “Kinga yi haƙuri ko zaki dawo ki tafi masa ma da abincin ma kawai, a saman nan ake shirya masa shi. Dan tunda kikaga ya dawo to yunwa yake ji”.

     Hibbah dai da yake neman hanyar kuɓuta take kafin baba Saude ta farga da rashin wayarta da sauri tace, “To baba ki bari kawai su dawo sai sukai masa kamar yanda kuka saba. Kar kuma kaiwar tawa yasa hakan bai masa ba”.

       Gamsuwa da zancen nata da kuma sanin halinsa yasa baba Saude faɗin, “Eh gaskiyarki kuma, dan dama inba Habibu ba babu ma mai yawan hawan saman kai tsaye sai inshi ya bukaci ganin wani a cikinsu. Jeki kawai”.

      

         Hibbah da batai tsammanin samunsa  zaune a falon ba tai ɗan diri-diri. Ƙoƙarin haɗiye abinda ya tsarga matan a maƙoshi tai tana cigaba da takowa ganin baiko nuna alamar yasan da shigowarta ba, kamar barci yake ma a hakan.

     Ta ɗan taɓe baki saboda ganin wani zaman ƙasaita da yay a cikin kujera. Hanyar ɗakin data tsinci kanta a ciki ta nufa zuciyarta na tsitstsinkewa saboda shegen sanyin da falon ya ɗauka. Amma shi ko a jikinsa, da alama ma matsanancin daɗi yake masa.

         “Kin koma satan waya ne?”.

   Ƙasaitacciyar muryarsa mai amo da kamewa ta daki dodon kunnenta. Cak ta tsaya da rumtse idanunta da ƙarfi,  dan duk tsiwarta tana shakkar wanda baizo mata da wasa ba. Ko yau da safe takaicin tuno maganarsu Abbah yasata iya maida masa murtani badan bata ganin girmansa a idanunta ba. Ko bai tanka maka ba kwarjininsa da kame kai yasa ma'abocin mu'amulantarsa jin shakkarsa.

        Juyowa tai a hankali tana ɓata fuska ranta fal mamakinsa. Ta ɗan saci kallonsa amma sai taga yana a yanda ta shigo ta samesa ido lumshe bai motsa ba. Duk yanda taso yin tsiwar ta gagara koda motsa laɓɓanta tsabar yanda ya cika mata idanu har bata ganin wani fili a falon, dan fuskarsa tamau take babu alamar yasan minene fara'a.

       Cikin pretending da shagwaɓar da takema su Yaya Muhammad ta ce, “Ni wlhy ba ɓarauniya bace. Tunda dai ba'a taɓa cewa na ƙwamushe kuɗaɗen bankin mutane b?”. Tai maganar da ɗan murguɗa baki duk da zuciyarta kuwa babu abinda take sai lugude.

          Lumsassun idanunsa da suka kaɗa jajur kamar wanda yake cikin ɓacin rai ya buɗe akanta. Sallama Habib ɗauke da tray babba ya hanashi yin maganar da yay niyya..

     Itama sai ta juya tana amsa masa sallamar da yay ranta fal murnar samun hanyar kuɓuta. Habib ɗin ya ɗan risinar da kansa cike da girmamawa ya ce, “Sannu Aunty”.

    Harara Hibbah ta zuba masa tana sake ɓata fuska. Shi dai yay gaba abinsa yana murmushi. A tunaninta zuwan Habib ɗin zai kuɓutar da ita. Sai taga saɓanin haka dan ko motsi baiyiba, baima amsa gaisuwar Habib ɗin ba, sai mayatattun idanunsa da har yanzu ke a kanta.

       Ƙasa tai da kai, ta kasan ido ta gama auna tafiyar da zata kaita ɗakinta. Ta ɗan dago ta sake dubansa. Ganin har yanzu ita ɗin dai yake kallo sai ta ɗan fara taku kamar zata koma wajensa. Hakan da tai ne shi kuma ya sashi ɗauke idanunsa ya maida kan Habib da ke zuba masa abinci.

       Tana ganin haka ta zambaɗa da gudu. Sai ƙarar takun gudunta kawai suka jiyo.

        Habib yay saurin saka hannu ya danne bakinsa jin dariya zata kufce masa. Shiko gogan wani irin fici-ficin fitina yayi da idanunsa yana sake tsuƙe fuska. Cikin muryar da babu wasa ya dubi Habib.

      “A rufemin network ɗin gidan nan na tsahon awa biyu”.

           Tamkar Habib zai fasa kuka ya dubesa. “Master awa biyu?”.

     Harara ya zuba masa. Habib yay saurin gyaɗa kansa da amsawa da to. Kasancewar ya kammala zuba masa abincin ya nufi hanyar downstairs dan babu damar ƙara yin musu.

     Shi ko lip ɗinsa na ƙasa ya dan ciza da jawo abincin gabansa ya fara ci a nutse. Sai dai kuma tun a laumar farko yaji banbancin girkin dana baba Saude. Idanu ya lumshe ya sake buɗewa akan abincin, dan ɗanɗanon sak na wadda a yanzu yakema kallo irin na uwa mai saka zuciyarsa farin ciki da yin rauni.

       A hankali saman laɓɓansa ya furta “ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka Ummi”............✍


Ni dai na ce “Hummm Master wace Ummi?”🚶🏻😹  




TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*




*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


______________________


💥🔥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥

*HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI 'DAUKA BA, INA MATA MASU BUK'ATAR 'DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK'ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE  AKANSU DAN FARIN CIKIN  MA'AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MAMAKI* 07034251528

🔥💥🔥💥🔥💥🔥🔥💥


kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji💃🏻💃🏻💃🏻🔥


Kad'an daga cikin abubuwan da muke dasu 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had'u pc +234 703 425 1528


Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k'ara suyi  dass abun sha'awar kowane  namiji 🔥💥


Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan💥🔥💃🏻


Ingantacce Kuma sahihin maganin k'iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar  , Rama batayi ba Sam Yar uwa😉😉


Sabulun wanka

Kalolin sabulun tsarki 

Turaren tsugunno

Turaren al'ajab

Hatsabibin turare

Da sauransu 07034251528


Kalolin gumba👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


Gumbar Dabino

Gumbar gero

Gumbar madara

Gumbar matsi

Gumbar ukku bala'i

Gumbar tada zaune tsaye

Gumbar sabon budurci

Gumbar sa buzu kuwa

Gumbar aya da kwakwa

Gumbar ridi

Gumbar mazari

Sarauniyar gumba 3in1


Da sauran kalolin da bansamu fadi ba,


Kalolin gari

Garin mallaka

Garin hutar da malaminki

dakan jaraba

Dakan Amare

Dakan Ni'ima

Dakan kishiya in bakiyi bani waje

Garin sa buzu kuwa

Garin buje.sharkaf

Garin Dan la'asar


Yayan hadiya mai suna dan la'asar

Original Dan goshi

Original Dan goshi (sabon salo)

Original man damo

Original man ayu

Kitsen damo

Sirrin tafin kafa

Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata

Kwallin idonka idona


Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki👍🏼💃🏻💃🏻


Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d'a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had'u pc 💥🔥


Kalolin tsumi👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


Tsumin mallaka

Tsumin jaraba

Tsumin madarar ni'ima

Tsumin tabaje

Tsumin Amare

Tsumin sabon budurci

Tsumin nono  raƙumi

Matan gaske

Ruwan jaraba,

Da sauran kalolin da ban fada ba


Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar HQ💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Matsin Dan mannau

Matsin mallaka

Dan la'asar

Sabon budurci

Mak'alemata

Mashahurin matsi

Ukku bala'i

Matsin uban budurwa

Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi


Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta,


Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake

*Kyallen al'ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al'ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu ,


KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen  nagari maida kudi gida🥰🥰🥰🥰🥰👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼


07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah🤝🏼🤝🏼


Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528


Maman zarah  mabera sokoto state💥🔥💥🔥💃🏻


_________________________


*_Chapter Twenty Seven_*


...........Madam Hibbah na shiga ta danna ma ƙofar ɗakin key. Cike da jin daɗi ta daka uban tsalle ta dire da taka ƴar rawa. Kafin ta harari ƙofar ɗakin da yin gwalo. A fili ta ce, “Ɗan tara dangin su Halilu yau dai call zaku kwana. Dan yanzun nan zan dokama Yaya Abubakar kira”.

        Ta ƙare maganar da ƙyalƙyale wa da dariya ta je gadon ta haye. Jinta take kamar an mata gafara. “Yaya Abubakar kai ya kamata na fara kira. Sai Ummi, sai Yaya Muhammad. Sai Yaya Umar da Yaya Usman. Yaya Ammar mai kan gwanda ne ƙarshe”. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya ita kaɗai kamar zararra. Dan kaf yayunta babu lambobin wanda bata riƙe akai ba tsaf.

     Kamar yanda ta tsara lambar Yaya Abubakar ta fara lodawa. Tanayin dailing Habib na rufe network ɗin gidan. Ɗin! Ɗin! Ɗin!! Wayar ta bada sauti, alamar tambarin mtn ta kona Emergency.

    Zumbur Hibbah ta miƙe da bubbuga wayar. Sai kuma ta ɓalle murfin ta cire batir ɗin. Zaman sim ɗin ta gyara a tunaninta gocewa yay. Sanann ta sake maida batir ɗin ta kunna. Still Emergency. Ta ɓata fuska kamar zata fasa kuka tare da sakkowa saman gadon tana bibbiga wayar da ɗagata sama. Sai dai sam babu alamar network ɗin. Wayarta ta ɗakko danta duba, sai taga nanma hakan take.

      “Inaga network ne ya ɗauke duka”. Ta faɗa cikin gamsar da kai. Sai kuma ta koma ta zauna bakin gadon zaman jiran dawowar network.

     Kamar wasa Hibbah na zaune zaman jiran dawowar network har la'asar. Ta tashi tai salla ta sake komawa ta zauna. Kaɗan-kaɗan saita ɗauka waya ta duba amma wayam. Ahaka ta sake shafe awa guda. Agogon ɗakin ya nuna 5pm. Mamaki ne ya kamata matuƙa, sai kuma tunanin fitowa ta bincika yazo mata a rai. Sai da ta fara leƙo kanta ta ga baya falon sannan ta fito, dan harma kayan abincin da yaci an tattare. Cikin sanɗa  tazo har bakin karfen da aka ƙawata upstairs ɗin ta leƙa ƙasa. Babu kowa a falon sai ɗan motsi a kitchen, da alama baba saude ce.

         Juyawa tai da nufin sauka ƙasan gab tai karo da abu. Cikin sauri da rawar jiki ta ɗago dan jin mayataccen ƙamshin turarensa ya daki hancinta. Baya taja da sauri ta manne da ƙarfen ta fara karanto addu'a.

        Fuska ya sake tsukewa dan tsaf ya fahimci inda ta dosa. Irin dai taga aljanin nan. Sai da ya ɗan kai dubansa a downstairs ɗin ya tabbatar babu kowa sannan ya matsa jikinta sosai, hannayensa duka biyu ya ɗora saman ƙarfen, hakan yasata kasancewa a tsakiya, idan ma kana nesa da su ne sai ka ɗauka rungumarta yayi.

           Ƙara manne jikinta tai da ƙarfen jikinta na ɗan rawa saboda yanda take iya jiyo fitar numfashinsa, “Dan ALLAH ka matsa wannan fa iskanci ne wlhy.”

         Dara-daran idanunsa ya zuba a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta, tare da ɗago hannunsa na dama ya ɗaura saman cikinta. A bazata Hibbah taji wannan al'amari. Babu shiri ta zabura ƙafarta na gocewa tai baya. Cikin zafin nama ya taro ƙugunta ta dawo saman ƙirjinsa, sannan kuma ya tura hannunsa da ke kan cikinta ƙasan rigarta.

        A matuƙar firgice Hibbah da taji saukar lallausan tafin hannunsa saman fatar cikinta daya tura cikin zaninta  ta ce, “Na shiga uku Ummi”.

         Shima da ƙarfi ya cije lip ɗinsa yana zaro wayar baba Saude da ta soke a zani da sakinta ya matsa saboda fitowar baba saude da ga kitchen tana faɗin, “Ƴar nan lafiya? Badai faɗuwa kikai ba?”.

        Ina Hibbah bama taji baba Saude ba. Dan yana sakinta ta zame ƙasa saboda wani irin rawa da jikinta keyi. Shi ko tini ya fara taka steps ɗin tamkar bai aikata komai ba. Dan ko tanka maganar baba Sauden baiyiba harya ƙarasa sakkowa ƙasan.

      “Babana kamarfa ihun yarinyar nan naji”. Baba Saude ta faɗa aɗan rikice.

          Cike da basarwa ya ɗan dubi Baba Sauden ya janye idonsa. “Kunnenki ne kawai baba”. Yay maganar yana nufar hanyar fita abinsa.

      Cikin shakku baba Saude ta bisa da kallo, sai kuma ta kaɗa kai kawai ta juya kitchen tunda taga da ga saman ya ke. Maybe kunnen nata ne kamar yanda ya faɗa.   


        kuka sosai Hibbah ta saki jikinta a ƙanƙame. Dan wannan sabon abune wanda a tsayin rayuwarta bata taɓa fuskanta ba ga wani ɗa namiji. Ga baƙin ciki da takaicin wayar da ya amsa. Sosai takejin kewa da tsoron kar wani abu ya sami ahalinta. Dan babu abinda ta gano a tsakkiyar idanun Master sai ɗunbin hatsabibanci da mugunta. Tabbas zai iya aikata duk abinda zuciyarta take tunani. Anya bazata janye kalamanta ba kodan ceton ahalinta?, Ummi tana da ciwon da bata buƙatar damuwa, rashinta a gida kuma babbar damuwace ga Ummin da yayyenta. A yanzu haka ALLAH kaɗai yasan halin da suke ciki na rashin ganinta.

       Cikin Kuka ta ke faɗin,, “Wlhy Ummi zan iya sadaukar da komai domin ke, na haƙura da *takun saƙar* da shi zan roƙesa ya dawo dani wajenki”. Tana maganar tana miƙewa a wajen, ɗaki ta koma ta faɗa saman gadon da jan bargo ta ƙudindine har saman kanta. Dan harga ALLAH wani irin zazzaɓi-zazzaɓi ma takeji. Ummi tasha gargaɗinta da tsoratar da ita akan illar sakarma namiji jiki harya iya kai hannu wani sashe naka. Sai gashi tsohon najadun nan yau ya tura ƙazamin hanunsa har kan mararta.


★★★★★


             A ɓangaren Abba suna fita daga gidan A.G gidan shakatawar Alhaji Sallau suka nufa. Sun samesu kusan su biyar da alama zaman jiransu suke suma. Da ido R.D yay ma A.G alamar miya kawo Abba cikinsu?, dan gaba dayansu manyan masu faɗa aji ne a ƙasa da mukamai ke hannunsu. Sannan a shekaru duk sun girmi Abban, hasalima sune suka ɓata rayuwar Abban dan lokacin da Alhaji Balele ya sakoshi a harkar wajensu yake kawosa kasancewar su ubannin gida a garesa. kai A.G ya gyaɗa masa da masa alamar cool down.

     Cikin kaɗa kai R.D ya janye idanunsa yana gyara zamansa cike da isa. Kasancewar duk ubannin gida suke a wajen su Abban cikin girmamawa ya gaidasu. Kafin ya kai zaune inda A.G ya nuna masa.

         Alhajin Mande ya dubi Abban da faɗin, “Lallai Halilu idonka kenan?”.

     Ƙasa Abba yayi da kai a girmamame. “Ayi hakuri ranka ya daɗe na samu raunine a ƙafa, amma Alhmdllh zuwa yanzun na fara fita kaɗan-kaɗan”.

       Alhajin Mande ya gyaɗa kansa da faɗin, “Eh A.G ya sanar mana ai randa ya kawo mana invitation ɗin auren yaran wajenka. Sai dai kuma muna baka haƙuri bamu samu zuwa ba bisa wasu dalilai”.

       “Babu komai ranka ya daɗe dan auren ma ba'a ɗaura ba”.

       “Tofa miya faru aka fasa?”.

Cewar Engineer Zailani Ginger.

      “Engineer matsala aka samu, wadda a dalilintane ma muka zo nan ni da A.G”.

       Gaba ɗaya dattijan ala kwankwan ɗin suka maida dubansu ga A.G.

      A.G ya gyara zamansa yana dubansu shima. “Hatsabibin yaron nanne ya ɓata masa aiki”.

     Kai tsaye R.D yace, “Kana nufin Master?”.

       “Shi kuwa”.

Kusan a tare suka haɗa baki wajen faɗin, “Ya akai yasan Master shi?”.

        A.G yay ɗan tiri-tiri da faɗin, “E..e eh ya sanshi ne sakamakon yarinyar nan data hari Master ɗin kwanaki ƴar yayansa ce. To da mukai bincike ta office akan yarinyar ne na fahimci haka. Shine na nemesa danjin wani abu akanta. Daga nanne ya roƙeni muyi masa wani aiki akan yayun yarinyar da uwarta shima zai taimakemu ta yanda zamu amfani da basirar yarinyar. Shine fa na saka Master akan aikin dan nasan zai iya, gashi kuma yarinyar dama ta shiga gonarsa. Hakan yasa muka yanke shawarar ya aureta...........”

         “Aure fa kace?”.

Dr Sufi ya faɗa da mamaki.

      “Eh Doctor, dan aurenne kawai zai iya bashi damar ɗaukar yarinyar cikin sauƙi saboda ƙanwar shegen jami'in nanne Abubakar Aliyu Hamza Gwarzo. Kasan kuma shima hatsabibin kansa ne mai faɗa aji wajen I.G”.

      Lokaci ɗaya ruɗani ya bayyana a kan fuskarsu. Engineer Zailani yay saurin tare numfashin A.G da faɗin, “To yanzu dai yaya akai?”.

       Carab Abba ya karɓe zancen. “Ya auri shegiyar yarinyar, sai dai ni ya wargazamin nawa aikin na hana yayun yarinyar auren nawa ƴaƴan. Yanzu hakama ya ɓoyesu inda ban sani ba”.

         “Alhaji Halilu kabi a hankali, na tabbata master bazai aikata hakanba sai da manufa”. A.G ya faɗa cikin jin haushi. Kafin Abbah ya ce wani Abu Alhajin Mande ya karbe da faɗin, “Master kam banajin zai ɓata lokacinsa akan wanann shiriritar, amma ku jira na san yana gab da zuwa nan”.

        Cike da zalama Abbah yace, “Yauwa Alhmdllhi. Gara yazo naji yaya aka faɗi a ragaya ranka ya daɗe”.

       Komai babu wanda ya sake ce masa. Dan ama kusan dai-dai rufe bakinsa maigadi ya shigo yana sanar dasu isowar Master ɗin.

      Da hanzari R.D ya bada damar shigo da shi, dan sun rasa miyasa baya yarda ya shigo musu kai tsaye a duk sanda suka buƙaci ganinsa. Koda waya ya gama da su sai ya nema iso yake shigowa.

        Cikin izzarsa da ƙasaita ya shigo falon da sallama ciki-ciki. A kusan tare suka amsa suna zuba masa ido tamkar tsoffin mayu. Yana matuƙar birgesu da tafiya da imaninsu. Sai dai sam sun kasa samun kansa domin biyan bukatar zukatansu. Ya dai amince yay musu sauran ayyuka, hatta kisan kai idan sukace sunaso ayima wani yakan amshi aikin, amma sanin yaya yake aikin har yanzu basu da tabbas. Kuma bai basu wata ƙofar masa tambaya ba, dan duk da karancin shekarunsa a cikinsu baya ɗaukar raini koda na kallon bamza ne.

         Zaune ya kai bisa kujera yana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cike da ƙasaita. Kafin ya kai hannu bisa glass ɗin fuskarsa ya gyara masa zama da ƙyau yana kare musu kallo ta ciki. “Barkan ku”.

     Ya fada a taƙaice yana zuƙar iska da fesarwa. Sosai sukejin takaici na salon iskancinsa da izza. Sai dai basu da damar tankawa dan duk sun kasance a tafin hannunsa, saboda sirrikansu da yawan gaske ya gama sani.

        Bakuna suka shiga washewa. Kowanne na ƙoƙarin tambayarsa yaya yake. Nanma a takaice ya amsa musu da cewar,

      “Normal”.

  Ya tsuke bakinsa.

          A.G ya nuna masa Abba. “Ina fatan ka gane wannan ko Master?”.

      Cikin ɗan yamuste fuskar boginsa ya ce, “Kamar..”

      Haushi ya kama Abba. Ya zuba masa harara da faɗin, “Kai saurayi miye kuma Kamar? Ni nasan ka ganeni kodan maƙudan kuɗaɗen dana sauke maka kafin karɓar aiki na”.

      Mai makon ya amsa Abbah sai ya duba A.G da faɗin, “Wanann shine dalilin kiran?”.

        “A'a ina” R.D yay azamar faɗa saboda sanin wulaƙancin Mastern. Kaɗan da ga aikinsa ya karta musu rashin m ya tashi yay tafiyarsa.

       Abba da ya fahimci gadara bazatai ba sai ya kwantar da murya. “Kai ko saurayi dan ALLAH ka saurareni. Wlhy ina cikin matsala fiye da zatonka. Kuma ba kowa bane ya sani wabilahillazi sai kai. Miyasa munyi maganar ka auri yarinya kawai sai ka wargaza auren nawa ƴaƴan kuma? Bayan kuma duk na sanar maka ƙudirina akansu”.

     Nan ma banza yay masa bai tanka ba, sai ma agogon hanunsa da ya kalla. Da sauri A.G da ya fahimci ma'anar kallon agogon ya ce, “Ayi haƙuri a sauraresa Master. Rashin tabbatar wannan aikin zai iya saka masa ciwon zuciya wlhy. Nasanka kuma baka karya alƙawari, ga shi bamu san dalilinka na hana auren yaran nasa ba”.

       Kamar bazai tanka ba kuma sai ya dubi Abban. “Mi kake buƙata yanzun?”.

      Baki Abba ya washe yana gyara zama. “Yauwa ɗan albarka. Su yaran da ka wargaza auren yaran nawa da su nakeson sanin inda suke su da uwarsu. Idan da hali kuma a karminsu ɗaya bayan ɗaya dan ALLAH kamar yanda mukai da kai a farko, ni yanzu ma basai sun auri yaran nawa su wani sami ciki ba. Sanann akwai dukiyarsu da ke a hannuna da kaddarori duk sunayensu ubansu ya saka matsayin masu gadarsa, dole sai sun saka hannu su da lauyan baban koda zan iya amfana da su. To shi kuma lauyan ya ɓata ɓat tsahon shekaru shegen shine nakeson a kwashe kuɗaɗen a maidosu accaunt ɗina. Takardun kaddarorin kuma a maida sunana. Amma inason a fara kashemin ita yarinyar da aka ɗaura aurenku da itan sannan, dan wlhy da baka ɗauketa ba a jiya ni da kaina da zan kasheta”.

        “Zamu sake sabon ciniki. Dan baka sanarmin gaskiya ba a wancan aikin shiyyasa na wargaza auren ƴaƴanka. Ni idan za'a bani aiki bana son ƙarya bana son munafinci. Yanzu ma idan ka ƙara zakaga ba dai-dai ba. Ka tattara dukan bayanai da accaunt no. Ɗin da kuɗin suke da takardun kaddarorin ka bama A.G tare da kuɗin aikina”.

       Yawu Abba ya haɗiye da ƙyar, dan awancan aikin fa 5mil ya bashi. Amma dan tsabar wulaƙanci ace wai sun ciwu batare da an masa aikin ba. Shikam ya fahimci yaron nan zigidir yake son masa. To amma ai yanzu kuɗaɗene masu nauyi zai samu. Dan haka ya sake gyara zama. “Na yarda zan sake biya. Amma nawane to? Dan ALLAH amin ragi”.

         Cike da shan ƙamshi Master ya ɗan dubesa ta cikin glass ɗin idonsa ya ɗauke kai. “Zaka fara bada 10mil yanzun nan, bayan naga takardu da nauyin kuɗaɗen asusun zan faɗi farashi”.

      “Bantan uba kana nufin 10mil ɗin ma ba farashi bane?”.

      “Kuɗin saka data and transport ne”. Master ya faɗa a gadarance.

    Abbah zai kara magana A.G ya zunguresa. Kallonsa yay a marairaice tamkar zaiyi kuka. Amma sai ya girgiza masa kai alamar karya sake cewa komai. Dole Abbah yay ƙasa da kansa. A zuciyarsa kuwa sai jama Master kwando-kwandon tsinuwa yakeyi.

        Da ido Alhajin Mande yay ma A.G alamar ya sallami Abba. Kansa ya gyaɗa yana duban Abban. “Alhaji Halilu kaje ka tattara abinda ya ce idan na fito zan biyo ta gidanka na amsa”.

     Miƙewa Abba yay yana faɗin, “To. To bara naje ɗin, amma dan ALLAH ka ɗan sake nemamin ragi kuɗin yayi yawa wlhy, dan ya zabtare kaso biyu bisa ukun abinda na mallaka idan aka haɗa da biyan farko. Gashi nayi hidimar kamawa shegun yaran can gidajen haya babu gaira babu sabar”.

     “Babu damuwa kaje. Zamuyi magana da shi”. A.G ya faɗa cikin ƙosawa.           

     

      Sai da sukaji fitar motar Abba a gidan suka maida hankalinsu ga Master da ya lafe cikin kujera idanunsa da ke cikin glass a lumshe. Dr Sufi ya fara magana yana ɓalle murfin robar ruwa. “Master taruwarmu anan tana da nasaba da wani babban aiki da ya sake taso mana. Amma kafin mukai maganarsa nakega ya kamata ace kuɗaɗen hannunka daketa taruwa kusan shekara biyu mizai hana a ɗan raba wasu a ciki kar asusun ya cika da yawa har wani yay mana ƙafar angulu. Kaga tunda aka fara aikin nan biyanka kawai muke kuɗin aiki amma kuɗaɗen ko nera bata shiga aljihun ɗaya da ga cikinmu ba, sabanin da da kayi aikin kake bamu abunmu”.

        Miƙewa yay zaune sosai tare da zare glass ɗin idonsa. Ya zubamasa razanannun idanunsa masu kama dana Zaki. “Likita kasan bana magana biyu, shiyyasa tun farko na sanar muku sai na kammala muku wannan aiki zan baku sakamako. Ko kana tunanin da kuɗaɗen nan nake harkar rayuwata ne?”.

        Da sauri Alhajin Mande ya ce, “Haba karma ka kawo hakan a ranka Master. Mu da kake gani anan mun matuƙar yarda da kai shiyyasa muke iya fasa maka sirrin cikinmu, karka manta tun kana ƙaramin ɗan jagaliya kake tare damu. Sam ba haka Dr Sufi ke nufi ba. Amma nima sai nake ganin ko kaso ɗaya bisa uku ne na kuɗin aɗan raba mu farfaɗo koda bayan ka gama wannan aikinne na yanzu da zamuyi magana. Dan shima asusun manyan gwasake ne”

      Komawa yay jikin kujerar ya kwanta yana maida glasess ɗinsa cike da salonsa na izza. “Zaku bani accaunt numbers naku na sirri. Bayan aikin nan ya kammala zakuji billions ɗari-ɗari”.

      Wani irin kallon zazzaro idanun mamakin jin nauyi kuɗaɗen da kawai tsakurowa zaiyi ga abinda ya tara musu sukai. Atake bakunansu duk suka washe. Alhaji Sallau yace, “Kace abin na gaske ne Master mu ƙara ƙaimi”.

     Wani ɗan salo kawai yay masa da yatsunsa🤙🏻 ba tare da ya bashi amsa ba.

         Wani irin shegen daɗi ya baibayesu. R.D ya jawo takardun gefensa yana faɗin, “Waɗan nan sune jadawalin sunayen waɗanda za'a wawashe ma asusu. Uku da ga ciki munason a fallasasu wa duniya bisa handamar da suka shuka akan kuɗaɗe. Na farko I.G na ƴan sanda. Sai ministern man fetur. Da shegen can Barau na ALLAH shaharren ɗan kasuwa a zahiri a baɗini kuwa kuɗin kwangilar gwamnati ne yake handama da ga aminansa da suka ɗaure masa ƙugu a gwamnatin. Sai gwamnan jihar gabas damu.”

         Wani shegen murmushi Master ya saki yana miƙewa. ga accaunt no ɗina nan naji alert. Da ga safiyar jibi idan ALLAH ya kaimu zakuji sakamakon aiki.”

     Dariya suka shiga ƙyalƙyalewa da shi suna tafawa. R.D ya miƙa masa takardun sunayen duk waɗanda suka lissafo da bayanai akansu yana faɗin, “Master muna son rayuwar shegen I.G ɗin can ta salwanta fiye data kowa. Kaima dai kasan yanda yake tsaye kullum akan son damƙoka da gurfanar da kai harma da alwashin da yake ɗauka na tabbatar da hakan. Ko nera kartai saura a asusunsa. Akwai bayanai shiryayyu akansa da fitarsu sai ta saka zuciyarsa bugawa kafin ma hukumar daƙile ta'annati da kayan gwamnati ta fara bincike a kansa. Kaga sai muga da wane taurin kan nasa zai cigaba da bibiyarka balle ya gano sunanmu da ke manne da naka a baɗini”.

      Komai Master bai ce ba. Sai amsar takardun da yay ya nufi hanyar fita yana ɗaga musu hannu alamar bye.


        Yana gama ficewa kusan dukansu sukaja tsaki. Dr Sufi yace, “Shegen yaro mun ɗorasa akan samu amma yana neman fin ƙarfin yanzu ɗan banza hatsabibin aljani”.

       Cikin takaici Engineer ya karɓe, “Nifa wlhy namafi tsanarsa sama da maƙiyan namu a yanzu. Nakanji kamar na kar shege a wuce wajen tun yanzu”.

        “Kulll” Alhajin Mande ya faɗa yana gyara zama. “Kudai mu cigaba da lallaɓashi da haƙuri kuɗaɗen nan da aka tara su dawo hannunmu. Cikin sauƙi zamu sakashi a tarko mu da kammu musa a kamashi, sai mun ƙasƙantar da shi a gaban duniya da kullum burin kowane jami'i ya ga gwiwarsa a ƙasa kafin mu ɗurama shege allurar guba namansa ya zaganye kowa ya huta. Dan ba karamar fitina uwar wannan ta haifama duniya ba”.

        “Mu kuma ta haifa mana abinda ya amfanemu ai”. Cewar A.G.

      Dariya suka sheƙe da ita baki ɗaya suna tafawa.


★★★★★★


        A gidan Ummi kuwa zuwa magrib duk wasu baƙi sun kama gabansu. An kimtsama kowacce amarya sashenta an barta ta jira shigar ango. Sashen Ummi ma dai babu kowa sai ita da samarin ƴaƴanta. Suma ɗin sun fita sallar isha'i basu kai da dawowa ba.

      Da Ummi taji motsi sai ta kalla ƙofa da tunanin ganin Hibbah ta shigo. Sai dai shiru kakeji. Harga ALLAH zuwa yanzun zuciyarta a matuƙar raunane take. ji take kamar numfashin Hibbah baya tare da nasu a cikin gidan. Dan babu yanda za'ai Tanee ɗinta ta kwana ta yini batare data sakata a ido ba. Musamman idan ta tuna miya faru akan aurenta.

      Kai anya kuwa bata yaudarrar kanta ma. Tayama akai ta amince cewar Hibbah na tare da su Zahidah bayan abin daya faru, dan babu kuma yanda za'ai ace Hibbah bata sani ba. Zaram ta miƙe da ga zaune da take a saman sallaya dan idar da sallarta kenan ta isha'i.

      A yanayin kiɗima ta fito falon ƙirjinta da zuciyarta na wani tsitstsinkewa. Gaskiya haƙurinta ya ƙare da kanta zataje sashen su Zahidah ta bincika.

       Yanke wannan hukuncin a rantane ya sakata nufar ƙofar falon. A dai-dai nan suma su Yaya Muhammad suka kawo jiki zasu shigo. Baya Ummin tai tana dubansu cikin rauni.

         A take suma kuma yanayin nata ya saka gabansu faɗuwa. “Ummi lafiya? Kuwa”.

     Yaya Muhammad ya faɗa yana matsowa kusa da ita sosai.

       A raunane ta ce, “Muhammad Tanee. Dan ALLAH ku faɗa min gaskiya ina yarinyata take ne? Zuciyata na tabbatar min kuna ɓoyemin wani abu”.

        Cikin son kauda mata hankali yaya Umar ya kama hannunta yana faɗin, “Ummi zauna kiji, kwantar da hankalinki indai auta ce tana cikin ƙoshin lafiya.”

       “Ban yarda ba Umar, dan zuciyata tana bani numfashin Tanee yana nesa da nawa”.

        Cikin in ina Yaya Abubakar ya buɗe baki zai yi magana akai knocking ƙofar.

       “Tanee!”

Ummi ta ambata da sauri tana duban ƙofar. Gaba ɗayansu suma ƙofar suka duba, sai dai sanin Hibbah bata tare da su yasa su basuyi wannan zaton ba. Mikewa Ammar da illahirin jikinsa ke tsuma yay ya nufi ƙofar. Batare da tunanin tambayar wanene ba ya buɗe ƙofar da janta baya yana kai kansa zai leƙa aka ɗaura masa bindiga.

       “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”. Ya ambata yana jan jikinsa baya.

    Hakkane kuma ya bama wanda ya ɗaura masa bindigar akai damar sakko ƙafarsa cikin falon. A zabure su Ummi duk suka miƙe saboda jin sallallamin Ammar ɗin. Yayinda idanunsu ya sauka akan bindiga da mai shigowar duk suma sai suka ɗauki ambaton ALLAH.

        Mutumin da dukkan illahirin jikinsa ke a rufe ya cigaba da takawa Ammar naja da baya cikin rawar jiki har suka iso tsakkiyar falon. Wani irin kyarma jikin Yaya Abubakar ya shigayi na tsantsar ɓacin rai, ya yunƙura zai nufesu Ummi da jikinta ke karkarwa itama tai saurin damƙe hannunsa tana girgiza kanta.

         Idanunsa ya rumtse da ƙarfi cikin tsumar jiki da riƙon da Ummi tai masa a kausashe ya ce, “Who are you?!”.

       Shiru bai amsa ma yaya Abubakar ɗin ba, sai hannu da ya kai saman fuskarsa ya janye hiramin da ya naɗe fuskarsa da shi.

     Lokaci ɗaya suka zabura a tare, har suna haɗa baki wajen faɗin............✍


    


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*




*_Typing📲_*


💥🔥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥

*HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI 'DAUKA BA, INA MATA MASU BUK'ATAR 'DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK'ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE  AKANSU DAN FARIN CIKIN  MA'AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MAMAKI* 07034251528

🔥💥🔥💥🔥💥🔥🔥💥


kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji💃🏻💃🏻💃🏻🔥


Kad'an daga cikin abubuwan da muke dasu 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had'u pc +234 703 425 1528


Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k'ara suyi  dass abun sha'awar kowane  namiji 🔥💥


Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan💥🔥💃🏻


Ingantacce Kuma sahihin maganin k'iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar  , Rama batayi ba Sam Yar uwa😉😉


Sabulun wanka

Kalolin sabulun tsarki 

Turaren tsugunno

Turaren al'ajab

Hatsabibin turare

Da sauransu 07034251528


Kalolin gumba👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


Gumbar Dabino

Gumbar gero

Gumbar madara

Gumbar matsi

Gumbar ukku bala'i

Gumbar tada zaune tsaye

Gumbar sabon budurci

Gumbar sa buzu kuwa

Gumbar aya da kwakwa

Gumbar ridi

Gumbar mazari

Sarauniyar gumba 3in1


Da sauran kalolin da bansamu fadi ba,


Kalolin gari

Garin mallaka

Garin hutar da malaminki

dakan jaraba

Dakan Amare

Dakan Ni'ima

Dakan kishiya in bakiyi bani waje

Garin sa buzu kuwa

Garin buje.sharkaf

Garin Dan la'asar


Yayan hadiya mai suna dan la'asar

Original Dan goshi

Original Dan goshi (sabon salo)

Original man damo

Original man ayu

Kitsen damo

Sirrin tafin kafa

Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata

Kwallin idonka idona


Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki👍🏼💃🏻💃🏻


Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d'a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had'u pc 💥🔥


Kalolin tsumi👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


Tsumin mallaka

Tsumin jaraba

Tsumin madarar ni'ima

Tsumin tabaje

Tsumin Amare

Tsumin sabon budurci

Tsumin nono  raƙumi

Matan gaske

Ruwan jaraba,

Da sauran kalolin da ban fada ba


Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar HQ💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Matsin Dan mannau

Matsin mallaka

Dan la'asar

Sabon budurci

Mak'alemata

Mashahurin matsi

Ukku bala'i

Matsin uban budurwa

Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi


Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta,


Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake

*Kyallen al'ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al'ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu ,


KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen  nagari maida kudi gida🥰🥰🥰🥰🥰👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼


07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah🤝🏼🤝🏼


Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528


Maman zarah  mabera sokoto state💥🔥💥🔥💃🏻


_____________________


*_Chapter Twenty Eight_*


.............“Shuraim!!”.

      “Sunana ne”.

Ya faɗa cikin izza da garada yana gyara zaman bindigar akan Ammar da yay surrender suna cigaba da takowa tsakkiyar falon har gaban Ummi da gaba ɗaya jikinta tsuma yake da kyarma..

       Cikin raunin murya da tashin hankali ta dubi Ammar tare da maida kallonta ga Shuraim ɗin. “Yaro dan ALLAH karka cutarmin da zuri'ata. Kar kai ƙoƙarin sakanka alkairi da sharri. Ka faɗa mana komi kake buƙata zamu maka, amma karka cutar da mu”. Ummi ta ƙare maganar jiri na neman kwasarta. Yaya Muhammad yay azamar tarota shima nasa jikin na tsumar ɓacin rai.

      A kausashe yaya Abubakar da ke ta faman taunar lips ɗinsa ya ce, “Ummi barsa ya kawo kansa a dai-dai lokacin da ya da ce ai.”

       “Dama sai da na auna lokaci sannan nazo”. Shuraim ɗin ya faɗa yana mai maida dubansa ga Yaya Abubakar. Sai kuma ya janye bindigar da ga kan Ammar. Nannauyan numfashi Ammar da ya gama sadaukar da rayuwarsa ya sauke a hankali.

      Sai dai kuma ganin ya nufi Ummi gadan-gadan ya sakasu zabura kansa lokaci guda. Turus suka ja suka tsaya ganin yay ƙasa a hankali ya durkushe yay kneeling down gaban Ummi yana mai ajiye bindigar hannun nasa a ƙasa, ta re da haɗe hannayen nasa waje guda🙏🏻 yay ƙasa da kansa cike da nuna tsantsar nadama da girmamawa a gareta.

     Ba Ummi kawai ba, hatta su Yaya Muhammad sagade sukai suna dubansa. Ummi da illahirin jikinta yay sanyi dan mace ce mai tsananin tausayi ta tsura masa idanu cikin wani irin kallon wasiwasi da shakku.

        Kansa ya ɗago a hankali shima tare da ɗora hannunsa saman fuskarsa ya zare facemask ɗin fuskarsa ta ainahi ta bayyana.

     Gaba ɗayansu zabura sukai baya a razane. “Yaya Isma'il?”. Ammar ya faɗa jikinsa na karkarwa da kaiwa durƙushe gabansa domin ƙafafunsa sun gaza ɗaukar nauyin jikinsa dan firgici.

         Cikin takaici Yaya Muhammad ya ce, “Isma'il wane kalar shashashan wasa ne haka zaka danganta kanka da wannan fuskar da zukatanmu ke mana zargin mai ita ɗan ta'adda ne?”.

        Ƙasaitaccen murmushi ya saki yana mai ɗago dara-daran idanunsa tamkar na zaki masu cikar gashi ya duba Yaya Muhammad.

       “Yaya Muhammad ba wasa bane, zahirin gaskiya ce a gabanku. *_Isma'il Aliyu Hikima_* ne a gabanku. *_(Muhammad Shuraim Aliyu)_* Sannan kuma *_Master!_*”.

       “What?!”.

Ammar ya faɗa yana ja da baya cikin tsuma. Haka suma su Yaya Usman bayan sukayi idanu waje.

       “K..k...kana nufin kai ne Master? Gawurtaccen ɗan ɓarawon nan da ake nema ruwa a jallo?”.

       Murmushi Master ya saki yana mai maida dubansa ga yaya Muhammad da yay maganar cike da son tabbatarwa da ƙaulani.

         Hannu ya kai saman kansa ya sauke hular jacket ɗin jikinsa da ya kai har saman kai. Kafin ya miƙe da ga kneeling ɗin da yay yana kallon Ummi da ko motsin kirki ta kasa. A take idanunsa sukai rauni har wasu ƴan ƙwalla na taruwa a cikinsu. “Ummi dan ALLAH ki saurareni”.

      Ummi da gaba ɗaya zuciyarta ta gagara gaskata abinda Master ya faɗa ta gyaɗa masa kai cikin sanyi da rauninta. Sai kuma ta duba su Yaya Muhammad da ke ta ƙyalli cikin shaddoji na zuwa ga amarensu. Da idanu tai musu umarni.

        Ita ba abar wasansu bace, dan haka babu wanda ya nuna alamar musawa suka ƙarasa ga kujerun falon duk suka zauna.

      Master ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana jingina bayansa da kujerar da ya zauna tare da lumshe idanunsa. Tsahon minti ɗaya da wasu sakanni ya buɗesu a hankali yana tasowa zaune sosai ya fuskanci Ummi.

      “Da farko zan fara da neman gafararki Ummi, matsayinki na uwa da nake kallo da kima da daraja bayan mahaifiyata. Tabbas kin bama Isma'il gata da kulawa irin wanda a kowane dare yake kukan kishirwar rashin samu tun daga ƙuruciya. Na shigo jikinku a dalilin kutse da Muhibbat taima rayuwata. Kafin isowa ta gareku da nufin yaudararku na hukuntata nazo, sai dai labarin ya canja tun a ranar farko, awannin farko, mintunan farko, sakannin farko. Ummi kece kika canja komai, a lokacin da zuciya batai tunanin sauyawar ba. Dan da ga lokacin da wanann hannun naki mai albarka da daraja ya sauka saman tsakkiyar kaina yayin da kike a gadon asibiti, kika furta kalma mai matuƙar tsada da girma a gareni komai ya canja.”

      (Na gode ɗana. ALLAH yay maka albarka. Ya tsare rayuwarka da imaninka). “Wannan addu'a ce da kika ambata a gareni wadda zuciya ta daɗe tana ƙishirwa da bege”. Yay murmushi mai ciwo tare da kai yatsa ya ɗauke wasu guntun hawaye da suka ciko idanunsa suka taru a gefe.

    Gaba ɗaya jikin su Yaya Muhammad yay sanyi. Duk sun tsaresa da ido.

    Ya cigaba da faɗin, “Naji matuƙar fargaba da tsoro a lokacin da su Yaya Muhammad sukace bazasu amshi kuɗin aikin nan ba, dan ina tare da su batare da sun san ni ɗin wanene ba. Tabbas da basu amsaba Ummi bazan yafema kaina ba. A yau a kuma yanzu zan sanar daku wanene *_Master_*. Na zaɓi wannan lokacinne domin samarwa ƴan uwana kwanciyar hankalin shiga sabuwar rayuwa. Amma kafin sannan zan sake tabbatar muku Muhibbat tana hannuna”.

     Duk da dama shi suke zargi maganar ta dake su matuƙa. Musamman da labarin ya canja salo zuwa Isma'il da Shuraim da Master duk abu guda ne.

       “Kuyi haƙuri, badan na ƙuntataku na ɗauketa ba. Nayi hakane domin kuɓutar da ita”.

     Wata nannauyar ajiyar zukata suka sauke kusan a tare. Ummi ta kai hannu ta share hawayen da suka ziraro mata har cikin ranta tanajin nutsuwa da ƙaguwar son jin wanene shi?.

         “Aliyu Ibrahim Hikima shine sunan mahaifina. Shahararren ɗan kasuwa da sunansa yay shura matuƙa a wasu shekaru da suka shuɗa. Sunan mahaifiyata Maryam. Auren soyayya sukai da mahaifina duk da dangin mahaifiyata basa so sam. Ba komai yasa basa son auren ba sai dan mahaifina bashi da komai a lokacin. Su kuma mutanene masu dukiya. Dagewar da mahaifiyata tayi akan sai shi ne yasa babanta yarda ya bashi aurenta. sai dai ya tabbatar masa babu shi babu ita.”

        Ya saki ɗan murmushi da cigaba da faɗin, “Ko'a jikinta ta amince da sharaɗin, saboda son da takema mahaifina bashi da iyaka. Anyi aurensu babu wani shagali aka mikama mahaifina. Dukansu basu damuba, dan su dai burinsu ya cika kawai. A farkon zama sun fara rayuwa mai cike da ƙuncin talauci da fatara, amma sai soyayyar da sukema juna tai matuƙar tasiri wajen mantar da su hakan. Shekararsu biyu a wannan hali na matsi da kakana ya sakasu batare da sun sani ba. Dan kuwa duk wata hanya da mahaifina zai samu kakana ke tosheta wai duk dan mahaifiyata ta magantu. Amma sai akai rashin sa'a ko'a jikinta. Sai ma shi Abbana ne kan damu musamman idan yay dubi da ga gidan data fito. Dan ƴar gata ce sosai Mamy na a gidansu, sannan ita kaɗai iyayenta suka haifa. Rayuwa ta musu tsanani sosai, gashi babu ciki babu alamar samuwarsa. Fahimtar komai zai iya lalacewa yasa mahaifina ɗauke Mamy na suka bar garin. Wannan tafiya itace sanadin canjawar komai.”

        “A yayin tafiyarsu sukai gamo da wani dattijo wanda alamu suka tabbatar da ba ɗan ƙasar nan bane. Dattijon nan shine ya fahimci akwai damuwa da talauci tare da su, dan ko kuɗin mota ma basu da isashe. Shine ya biya musu kuɗin mota na inda zaije, dan ya fahimci su kansu basu san ina suka dosa ba. Tafiya mai nisan zango ta kaisu wani gari dake akan gaɓar barin ƙasa. A garin suka kwana wajen dattijon nan daya hanasu matsawa ko nan da can, washe gari da safe ya sake basu umarnin su bishi. Mahaifina bashi da wata mafita banda ya bisan, da yake lokacin duniya na bacci azzaluman basuyi yawaitar yanzun ba. Sun sake yada zango a ƙasar Niger. Inda sukai kwanaki biyu anan dattijo ya kammala harkokinsa. Koda ya sake tabbatar musu gaba zasuyi basu damu ba, suka nuna masa amincewarsu. Yaji matuƙar daɗin yanda suka aminta da shi babu bincike ko nuna shakku”.

        “Bara dai karna jaku da nisa. Daga ƙarshe Iyayena sun tsinci kansu ne a ƙasar haihuwa ta wannan dattijon. Tun a tarbar da akai musu suka fahimci dattijon nan da ko sunansa bai sanar musu ba ƙasurgumin mai arziƙi ne. Yayinda suka isa katafariyar daular sa kuwa sai mamaki ya kamasu na dalilin zuwansa ƙasarsu, dan kuwa dai ya fito ne da ga gidan sarauta mai faɗa a ji da tarihi. Dattijo yasa an karrama rayuwarsu da basu muhallin zama mai tsafta. Bayan kwana biyu sun huta ya nema jin labarinsu. Mamana taso a ɓoye. amma sai babana yace su faɗa masa gaskiya kodan karamcin da yay garesu. Wannan dalilinne ya sakasu fayyace masa komai na rayuwarsu har barowarsu gida. Ya nuna tausayawa a garesu da ga ƙarshe ya ɗauka mahaifina ya ɗaura akan dukiyarsa. Amana da jarumtar da Abbana ya nuna wajen tsare dukiyar da nuna gaskiya yasa Dattijo yarda da shi, harya maidashi babban yaronsa makusanci, komai ya koma hannunsa. Wannan abu ya baƙanta ran ƴan masarautarsu ƙwarai da gaske. Harma da sauran yaransa da ke hidima ma dukiyar kafin zuwan su Abbana. Ƙiri-ƙiri suka ɗauka karan tsana suka ɗorama Abbana, kullum cikin masa gorin shi din baƙon haurene suke.”

        Rayuwa ta sauyama iyayena. Dan cikin ƙanƙanin lokaci dukiya ta bunƙasa garesu. Basu da wata matsala sai ta rashin haihuwa da tsangwamar mutane. Haka suka cigaba da haƙuri da juriya na tsahon shekaru har ALLAH ya azurtasu da samun cikina. Sunyi matuƙar farin ciki, irin wanda baki bazai misalta ba. Hakama Dattijo Isma'il yayi farin ciki tamkar shi za'aima haihuwar, dan shima bai taɓa haihuwa ba. Bayan cikina ya cika watanni tara aka haifoni, inda naci sunan dattijon nan wato Isma'il. Sai dai kallon mahaifi da babana ke masa yasa sukemin alkunya da suna Muhammad Shuraim.”

      Na tashi ɗan gata a wajen dattijo Isma'il da mahaifana. Yayinda tsiraru a cikin jama'ar masaruta ke sona. Wasu ko yanda suka tsani mahaifana haka suka tsaneni duk da ƙanƙantar shekaru na. Shekarata uku a duniya Abbana ya maido mamana ƙasarmu ta haihuwa saboda bazai juri tsangwamar da ake musu nima aimin ba. Dangi sunyi murna, sun kuma sha mamakin ganin ya kuɗance lokaci ƙanƙani. Dan yama take kakana ya shanye dukiyar da suke ƙinsa a dalilinta. Koda ya ajiyemu komawa yay ya cigaba da lura da dukiyar dattijo. Daga ni iyayena basu sake samun wani cikin ba har na kai tsahon shekaru takwas, kafin mamana ta wayi gari da ciki. Nanma sunyi murna, hakama ƴan uwa, musamman ma ni. Cikin mamana na watanni uku ciwo ya kai dattijo Isma'il ƙasa, wanda ake zargin sammu akai masa. Mahaifina shine ya koma jinyarsa, dan ƴan uwansa kowa ya noƙe, burinsu kawai ya bar duniya suhau kan dukiyarsa har matansa.”

           “Dattijo Isma'il ya riga yasan da wannan tun ba yanzu ba, dan haka a wani dare ya zaunar da mahaifina cikin dauriya ya sanar masa ɗunbin dukiyarsa daya tattare ya killace batare da sanin masu jiran ya wuce su hau kai ba. Gaba ɗaya ya mallakama mahaifina wanann dukiya, sannan yay masa umarni da ya bar ƙasar bayan ya damƙa masa fuskokin jabu (Facemask) guda uku yace koda ya dawo ƙasar haihuwarsa ya cigaba da amfani dasu shi da mamy na da ni dan yasa ƴan uwansa zasu bibiyesa bazasu barsa ba. Mahaifina yayi kuka sosai a wanann dare, kuka irin wanda ɗa ke yi yayin rasa mahaifa ko yin nesa da su. Shidai dattijo Isma'il nasiha yayta masa da addu'oin fatan alkairi da gamawa da rayuwa lafiya. ALLAH sarki rayuwa ashe nasihar ƙarshe ce, dan kuwa a safiyar wannan ranar aka wayi gari da rashin dattijo Isma'il. Abbana ya shiga ɗimuwa matuƙa harma ya rasa ina zai saka kansa. Yayinda tsoro ya kamashi ganin yanda matan dattijo da danginsa tun kan akai gawarsa harsun fara rigima akan dukiyar da suke tsammanin ya bari. Ana kai gawar dattijo Abbana ya silale ya baro ƙasar da dukiyar daya mallaka masa bisa umarninsa. Inda yabar baya da ƙura. Dan kuwa dattijo kashi uku ya raba dukiya yabar musu kashi guda kawai. Wannan dalilin yasasu farga da rashin Abbana da wuri saboda sunce a nemosa yay musu bayanin ina sauran dukiyar take.”

       “Abbana ya dawo ƙasarsa ta haihuwa cikin zuri'arsa, sai dai kuma anyi rashin sa'a dangin dattijo nacan na bincike a kansa har suka gano inda yake. A nan kuma ɓangaren Abbana koda ya dawo ni kaɗai suke sakama Facemask idan za'a kaini makaranta ko zan fita waje. Su mutane a tunaninsu baƙon yaro mukai, shiyyasa basu taɓa kawo hankalinsu a kaina ba. komai ya sake canjawa. hankalin iyayena ya kwanta, sunan mahaifina ya sake yin shura musamman akan harkar kasuwanci. A ƙanƙanin lokaci ya zama bashi da abokan mu'amula sai manyan mutane, a ƴan uwa kuwa dama zuwa yanzun iyayensu duk sun rasu, babu wasu shaƙiƙai na jini dan shima tamkar Mamyna shi ɗaya aka haifa a gidansu, baima san mamansa ba.”

     “Lokacin da cikin Mamy na ya shiga watan haihuwa a lokacin komai ya sake canjawa, dan kuwa dai dangin dattijo sun ƙaraso ƙasar nan batare da sanin Abbana ba. Hasalima har sun kammala bincike akansa da inda yake.”. Hannu ya kai ya ɗauke ƙwallar da suka cika masa ido, kafin ya cigaba da faɗin, “Ranar da bazan taɓa mantawa ba. Rana mafi ciwo da zafi, ranar da duk nisan tarihi bazai gogeta ba a gareni itace ranar juma'ar dana rasa iyayena duka. Dan kuwa dangin dattijo da taimakon wasu hatsabibai sukaima gidanmu dirar mikiya. Hankalin mahaifina ya tashi, dan ya tabbatar tamu ta ƙare, amma sai cikin jarumta ya faɗama mahaifiyata duk tsanani karta buɗe ƙofa shi zai fita shi kaɗai, idan kuma zamanta da nawa bazai yuwu ba ta tabbatar ta fita zai janye hankalinsu, ta kuma sakamin facemask ɗin wajen dattijo itama ta saka nata. Mahaifiyata na kuka ta shiga roƙonsa kar yaje amma sai ya lallasheta da bata ƙwarin gwiwa. Ya fita garesu, inda suka zagayesa da mahaukatan makamai tare da basa umarnin fiddo musu dukan dukiyarsa. Gane dangin dattijo da yay ya sakashi yarda zai basu, tare da roƙonsu idan ya basu su barsa da ransa cikin iyalansa. Sun nuna sun amince, dan haka Abbana ya tattara kuɗaɗen ya basu harma da dukkan takardun kaddarori suna kammala amsa ɗaya da ga cikin dangin dattijo cikin bada umarni yace (Master kashe shi). Shigar wannan furuci a cikin kunnena ya sani fashewa da kuka a cikin dakin da muke maƙure ni da Mamy. Na mike a razane da nufin fita Mamy ta hanani. Kuka nake ina fisgewa har na samu damar guduwa na leƙa ta jikin window. A dai-dai wanann lokacin wanda aka kira da Master yasa yaransa suka kama Abbana suka danne yay masa yankan rago cikin rashin tausayi da rashin imani duk da kwata-kwata shekarunsa bazasu gaza ashirin ba a duniya”.

     “Kuka na fasa wanda ya jawo hankalinsu ɗakin da muke. Cikin bada umarnin ɗan uwan dattijo ya ce muma a kashe mu. Hankalin Mamy da ya fara gushewane ya dawo jikinta saboda tuna wasiyyar Abba. Cikin rawar jiki ta kama hannuna muka fita ta ƙofar baya su kuma suna ƙoƙarin buɗe ƙofar. Kasancewar a cikin falo komai ke faruwa muka fice a gidan ina kuka mahaifiyata na kuka jini na zuba a jikinta ga tsohon ciki. Tafiya muke ta ceton rai dan kuwa suna buɗe ƙofa sukaga alamar mun fita ta ɓarauniyar hanya sai suka take mana baya. Fahimtar ana binmu yasa Ummi cikin galabaita ta ce naje kawai. Kaina nake girgiza mata ina kukan ni bazanje ko ina na barta ba. Sanin taurin kaina yasata juriyar cigaba da tafiya batare da mun fahimci inda muke jefa ƙafa ba dan gari yayi shiru kasancewar dare ya tsala. Sosai Mamyna ta sake galabaita, saboda alamar haihuwa data zo mata gadan-gadan, ga jini na zuba mata. Yanke jiki tai ta faɗi, na durƙusa a gabanta ina kuka da kiran sunanta ta tashi, amma ina bazata iya ba. Cikin amincin ALLAH mutumin da muke a ƙofar gidansa yaji kukana ya fito. (Sun kashemin Abbana da Ummina baba sun kashesu) na faɗa cikin kukan daya saka Hankalinsa tashi ya kamani ya muƙar tare da ɗaukar Mamy gaba ɗaya ya shige damu cikin gidan. A daidai lokacin su dangin dattijo da ke binmu suka iso ta ƙofar gidan tare da ƴanta'addan hayarsu. Sai dai rashin tabbatar da muna anan ɗinne ya sasu wucewa dan baban nan daya taimakemu ƙarar tahowarsu ta sakashi sa hannu ya toshen baki. Wucewarsu da kamar mintuna biyar naƙudan mamana ya tsananta. Baba ya rasa yanda zaiyi dan bashi da mata. Haka yanaji yana gani ya sama Mamyna ido harta haihu. A galabaice ta damka amanarmu a hannunsa tare da roƙonsa da cewar ya kaimu gidan marayu dan zama anan gidan bazai bamu tsaro ba tunda ta tabbatar dangin dattijo Isma'il sun gama sanin komai a kammu da kamanina na gaskiya tun kan suzo garemu. Tana gama faɗar haka ta bar duniya.”

        “Na ɗanɗana raɗaɗi biyu na zafin rashi a dare ɗaya a kusan lokaci ɗaya. Ga kuma ƙani Ummi ta haifamin. A taƙaice dai a ɓoye dattijo ya samo maƙwafta sukai jana'izar mamyna a washe gari da safe, bayan wata tsohuwa ta suturtata. Bani da wayo sosai dan shekarata tara kacal. Amma na shiga damuwa sosai. Dan ma kallon jaririn Mamy na ɗan ragen jin zafi. Wasiyyar Mamyna tasa baba ɗaukarmu a washe garin da Mamy ta cika kwana uku mu da shi duka muka koma gidan marayu gudun kar makasan su gano inda muke. Ashe shima bai taɓa haihuwa bane shiyyasa matansa duk suka gujesa.”

         “Mun koma gidan marayu da zama inda baba ya tambayeni sunan da zai sama jaririn Mamy na ce Habib. Babu musu baba yay masa huɗuba da suna Habib. Nine na cigaba da rainon Habib a gidan marayu, tare da matar da ke kula da mu da baba wanda a yanzu shine tamkar mahaifina. Karku manta inada facemask ɗin da dattijo Isma'il ya bama Abbana. Kuma ni kaɗai nake sakawa su basa amfani da ita. A kuma lokacin da zamu fito Mamyna ta ɗauka ta sakamin ita. Kuma koda muka zo gidan marayu ban cire ba na cigaba da amfani da kayana batare da kowa yasan ainahin fuskata ba”...............✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*



*Albishirinku mata💃.*


shin Ina ma'abota ado da kwalliya🗣️? Ina team no makeup🗣️? Mata gareku ina mai tabbatar muku dacewa duk wanda takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar marari agurin kowa😍Mata inamai tabbatar muku dacewa kujaraba kayan mg's skincare Koda gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki🧚🏻‍♀️ domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki😘Kuma wani abun jindadin ma shine duka kayansu organic ne  Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b💁‍♀️mekike jira hjy maza garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi kwalliya inzaki fita😃kifita aganki da zallar kyawunki hjy😍kanawa mutanenmu ina godiya Kuna nunama mg's one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg's na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu🥺Yar shawarmannan karta gagareni🤧😂

Henajiku lvs🤭

Meso should chat

08062991549

07046881166

Call 08064532391

Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare


Team glow✅


munayin makeup Yan kaduna gamai bukata ze iyazuwa nd munazuwa gida shima in anaso


08062991549


_________________________


*_Chapter Twenty Nine_*


..............“Ina da son yara matuka, duk da ban son yawan hayaniya da yawan magana. Sannan kuwa nima yaro ne, hakan yasa a koda yaushe zaka ga yara zagaye da ni musamman saboda Habib da wasu jariran biyu da mama mai kula damu take raino tare da Habib. Wannan dalilin yasa suka taso tamkar ƙannena a gidan marayun, idan sukai laifi nike hukuntasu na musu faɗa, sannan nine ke kula da karatunsu dan mun cigaba da zuwa makaranta musamman ma ni dana fara secondary a wajen gidan marayun da baba ke kaini da kansa kullum bayan na ƙarasa shekara ɗaya a primary ɗin gidan marayun. Mama mai kula damu ce ta sakamin suna Master duk da bana so banƙin amsa mata. A hankali sai sunan ya bini a gidan kowa ya koma kirana da Master har su Habib”

          “Ina girma sunan Master daya kashe Abbana na ƙara zama a ƙwaƙwalwa ta fiye da karatu, a gefe kuma da an tashi a makaranta nake tafiya talla batare da sanin baba ba da hukumar gidan marayu. Kai wani lokacin ma bana zuwa makarantar gaba ɗaya. Da kuɗin sana'ar nake sayoma su Habib sweets, biscuits da kayan kwaɗayi na yara. Tun kowa bai farga ba har suka farga dani. Baba ya dinga min faɗa, sai dai da ga ƙarshe kuma da kansa ya bani kuɗaɗe da bawani yawane da su ba na cigaba da sana'ar dan ya fahimci inaso. Saboda tunda aka hanani saina ɗauka ƙunci da fushi na sakama kaina.”

      A lokacin dana kammala secondary su Habib suka shiga na fara tunanin kutsa kaina cikin ƴan jagaliya, dan na gama nazarina kaf ta wannan hanyarne kawai zan iya nemo Master daya kashe mahaifina. Anan ɗin ma batare da sanin Baba ba na faɗa cikin ƴan daba tare da zama da kaina naima facemask ɗina wasu gyare-gyare saboda ni mutum ne mai fasaha matuƙa tun ina da ƙarancin shekaru, sai dai ALLAH ya tsareni bana shan komai na maye, duk sanda kuma zasu aikata tsiyatakunsu nasan ta yanda zan zille musu. Dan na shiga cikinsu ne kawai dan neman ilimi da kuma neman Master. A gefe kuma na takura baba akan mubar gidan marayu, dan na tabbatar zan iya rikemu mu duka da sana'ata da zuwa lokacin tayi ƙwari na daidai talaka mai neman cin yau da gobe. Da ƙyar baba ya yarda muka dawo cikin mutane da zama a gidansa ɗin nan da muka bari shekarun baya. Ni na cigaba da buga-bugar karatu akan su Habib duk da lokacin dai da ɗan saukin wahalhalu akan mai karatun secondary. Yayinda niko a dalilin ƙoƙarin da ALLAH ya bani wani bawan ALLAH ya ɗauki nauyin karatuna na jami'a a ranar taron tshoffin ɗalibai da akai na makarantarmu.”

        “Na cigaba da kutsa kai cikin ƴan daba ina neman Master a sirrance har ALLAH yasa na dace na kasance ɗaya da ga cikin yaransa, dan zuwa yanzu ya matuƙar gawurta. Cikin ƙanƙanin lokaci na zama amintacce a wajensa, dan ina bala'i-bala'in kwantar masa da kai har sauran yaransa najin haushi da takaici na. Ban damu ba, dan tunaninsu da nawa dabanne suke haukarsu. A zahiri ina cigaba da karatun jami'a. Baɗini ina karantar kowanne motsi na rayuwar Master, gefe kuma ina kasuwancina da ALLAH ya sakama albarka mukeci muke sha ni da waɗan da nakema kallon ƙanne kuma ahalina bayan Habib. Bayan kammala jami'ata na shirya takanas na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya. Yaji daɗi, ya kumayi farin ciki a take anan ya bani jari mai kauri da zan iya riƙe kaina harma da ƙannena.”

          “Koda na dawo na nunama baba ya sanyamin albarka, ya kuma bani shawarar maida hankali akan kasuwa basai na jira aiki ba, na amince da shawararsa dan haka na ƙara jari akan kasuwancina, UBANGIJI mai rahama dan-danan harkoki suka buɗe na canja mana gidan zama, na kuma koma makaranta nima. Domin cigaba da karatuna akan computer a wajen ƙasarnan. Tunda na tafi ban dawo ƙasata ba sai da na kammala karatuna. Amma koda yushe ina sanin motsin su Habib. Tun kafin na dawo na gama tsara yanda an tunkari master, dan kuwa na samo horo na musmman akan abubuwa masuyawan gaske.”

             “Yarana sunyi farin ciki da dawowata nima kuma nayi farin ciki da ganin sun zama manya sun kuma sake hankali. Sai dai kuma na iske baba babu lafiya. Hankalina ya tashi matuƙa dan ina sonsa hakama su Habib, duk muna masa kallo ne na uba. Kwanana biyar ALLAH yay ma baba rasuwa. Tabbas munji wannan mutuwa dan su Habib kuka rurus suka dinga yi suna sake ɗaga hankalina. Sai da na dage matuƙa suka dawo hankalinsu. Da ga lokacinne na fara basu horaswa ta musamman da basu san manufarta ba. Na kuma sake komawa cikin su Master da zuwa yanzun dukkan sirrinsa a tafin hannuna yake, dan dukkan abokan mu'amularsa a cikin manya da ƴan ta'adda irinsa na sansu nasan inda suke, nasan makamar harkokinsu. Na iya maganarsa. Na iya salon tafiyarsa na iya abubuwa da dama irin nasa wanda inhar na juye maka shi baka isa cewa bashi ɗin bane, musamman idan na saka mask na fuskarsa. Indai taƙaice muku zance a wani dare batare da sanin kowaba a cikin yaran Master na ɗaukesa, zuwa safiya na maye gurbinsa, yaransa kuma duk nabi hanyoyi daban-daban aka kamasu ɗaya bayan ɗaya ta yanda babu yanda ubannin gidan Master zasu iyama ganosu balle cetonsu.........”

       “Kenan yanzu duk kuɗin da ake sata a banki da sunan Master wancan ne ba kaiba Yaya Isma'il”.

    Ammar ya faɗa cikin katsesa da zaƙuwar son jin yaya take ne.

        Wani ƙasaitaccen murmushi Master ya saki. tare da kai hannu ya shafa kan Ammar. “Da ga shekara biyu zuwa yau duk nine”.

     Kai Ammar ya jinjina cike da gamsuwa. Sai faman murmushi yake dan shikam jin wata sabuwar ƙaunar shi yake har cikin jini da ɓargo duk da har yanzu bai faɗi dalilinsa na wawasar kuɗaɗen ba bayan dalilin kama Master daya kasance mai laifi a garesa.

       Master ya cigaba da faɗin, “Na shigo rayuwarku ne a dalilin Muhibbat, sai dai labarin ya sauya adalilin karamcin Ummi da ku kanku. Sai kuma randa na jima Halilu ciwo saboda ranar na fara ganinsa a gidanku, na kuma sansa a matsayin yaron su Alhajin Mande. Wannan dalilin ne ya sani yin bincike akanku sosai harna gano mummunar manufar da yake da ita a kanku. Cikin sa'a kuma abinda yake shiryawa a kankun sai aikinsa ya faɗo hannuna duk da dai nina saka A.G yay hakan batare da shima ya sani ba. Shiyyasa na koma ta bayan fage nazo ma Muhibbat matsayin Muhammad Shuraim. A lokacin da naita bibiyarta nine da kaina. Sai dai kuma ƙanina Musbahu shine yake zuwa gareku da fuskar Shuraim. Yayinda shima kansa baisan niɗin nine Isma'il ba, na kuma cigaba da ɓoye musu zahirina saboda wani dalili nawa daban. Dan basu taɓa sanin ainahin fuskata ba duk da kuwa tun suna ƙanana suke tare dani. Sannan basu taɓa sanin aikin dana tsundumasu a ciki munayi tare ni miye dalilinsa ba. Tsabar biyayya da soyayyar da sukemin ce kawai tasa basu taɓa min musu ba akan komai da nace suyi. Domin gaba ɗayansu na horar da su akan harkar Computer.”

      “Kune mutane na uku da kuka san ainahin fuskar Isma'il bayan iyayena da baba. Wanda da farko naje asibiti da wata fuska ne daban, a dalilin Ummi naji bazan iya zuwa mata a baɗinina ba shiyyasa na sake komawa na biya kaso ɗaya bisa ukun kuɗin aikinta bayan na biya duka a farko. A yau kuma na zaɓi bayyana muku zahirin gaskiya ne a dalilin Ummi. Banason ta shiga wani hali akan rashin Muhibbat, sannan ya kamata kusan wane ƙudirine a zuciyar Halilu kar yabi ta wata hanyar ya cutar da ku idan yaga ban masa aikinsa yanda yake so ba. Dan na tabbata zai binciko gidan nan yanzu hakama dan a rikice yake kuma shi mutum ne kamar sauna idan ya ƙwallafa rai akan abu.”

         “Na ɗauke Muhibbat ne saboda bin bayan Halilu da tai ranar ɗaurin aure batare da kun sani ba, yayinda ta jiyo sirrikansa masu yawa. A ranar ɗaurin aure yawan mutane yasa bazaku fahimci bana tare da ku ba. Amma kuma nazo, sai dai ganin fitowar Muhibbat da duk da ta saka hijjab da Niƙab na ganeta ya sani fasa bin ƴan ɗaurin aure nabi bayanta. Sai da na tabbatar da inda ta nufa sannan na  koma gida a hanzarce, amma tunkan na ƙarasa na kira Habib ya sameta a wajen, hakama maigadin gidan halilun, saboda duk gidajensu na sirri da suke aikata tsiyatakunsu akwai yarana a ciki, amma ba cikin su Habib ba. wasu masu gadi, wasu masu musu aikin gidan batare da sun sani ba. Aurenku kuwa da yaransa dama can na shirya wargazashi tsaf. Dama na tsara sai an kai Muhibbat gidana zaku san nine master, a gefe kuma na cigaba da kasancewa daku matsayin Isma'il. To sai akai rashin sa'a autar Ummi ta buɗemin aiki saboda rashin jinta”.

       Murmushi Ummi tayi da kai hannu ta share hawayenta. Suma su yaya Muhammad duk murmushin suke da sauke ajiyar zuciyoyi.

      “Kuyi haƙuri da fuskokin yaudara dana zo muku daban-daban. Ni kaina inaji haushin yaudarar Ummi, shiyyasa na zaɓi zuwa na bayyana muku kaina dan ku kanku ku sami nutsuwar shiga sabuwar rayuwa a yau. Hakama Ummi hankalinta ya kwanta kar garin neman gira a rasa ido dan bazan yafema kaina ba idan wani abu ya sameta adalilina. Auta na tare dani tana zubamin tsiwa da tsaurin ido Ummi, sai dai banason ta san niɗin wanene yanzu har sai nan gaba. Aiki akan Halilu kuwa ita daya raina itace zatayi komai da kanta insha ALLAH”.

         Dariya duk sukayi, Yaya Abubakar da gaba ɗaya ya tsunduma tunani da nazartar labarin Isma'il Master yay ɗan murmushi, “Ai ni auta kamar ba'a gasa mata baki wajen wankan jego ba. Dan wannan bakin natane ya jefata a tarkon jami'an tsaro su A.G sukaso yin amfani da ita. To ashe wanda suke bulayin neman shi tuni ya gama neme su”.

        Nanma dariyar suka sanya. Yaya Umar ya karɓe da faɗin, “Ai bakin auta ya mana rana. Tunda gashi ya jawo mana Master har cikin gida batare da mun saniba. Sai dai muna son sanin ƙyaƙyƙyawar manufarsa kodan mu cirema ranmu zarginsa a jerin na ɗan ta'adda ɓarawo da kowa ke kallonsa da shi.”

      “Wannan gaskiya ne yaya Umar. ALLAH ya jikan su Mamy yay musu rahama ya saka musu, amma ya kamata musani kam”.

        Cewar Yaya Usman da hawaye suka ziraro masa na tausayin Master ɗin. Gaba ɗaya suka amsa da amin, sannan suka shiga ƙara jero sabuwar addu'a ga mahaifansa. Ummi kam tama gaza cewa komai. Dan zuciyarta a matuƙar raunane take da tausayinsa. Yayinda a gefe takejin matuƙar nutsuwa da kasancewar sa miji ga ɗiyarta ɗaya mace tilo marainiya duk da yaƙi faɗar dalilin nasa na shiga wannan harkar, sai dai tana masa ƙyaƙyƙyawan zato. Sai ɗunbin al'ajab na son zuciya da shahara a zalunci na Halilu wanda suma su Yaya Muhammad ɗin duk yake cin zukatansu......

     Master ya katse tunanin Ummi da faɗin, “Ƴan uwana kuyi haƙuri wannan sirri ne mai matuƙar daraja a gareni, badan ban yarda daku ba kuma na ɓoyesa. Insha ALLAH zaku san dalilina wataran. Na yarda ku san niɗin wanene saboda kuma kun sanar dani sirrinku a lokacin da baku gama sanin niɗin wanene ba. Kun kuma yarda dani duk banzo muku a yanda kukai tsammanina ba. Dan ALLAH ina roƙonku ku bizne wannan sirrin a wannan falon har sai ranar da ya kamata gaskiya ta bayyana kanta ga kowa”.

         “Tabbas ita amana abuce mai nauyi Isma'il. Kuma ka cancanci muriƙe maka ita dan kaima ka riƙe tamu, yayinda kaketa hidima da gwagwarmaya a kanmu batare da mun sani ba. ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kariya akan ayyukanka. Ya kuma baka ikon sanar mana dalilin naka wataran. Bani da haufi game da sauran ƴan uwana akan riƙe maka wannan sirrin, dan nasan mahaifiyarmu ta mana horo akan hakan tunba yanzuba. Ballema wannan sirin riƙesa a garemu tamkar rike namu sirrine. Fita da shi kuwa tamkar tozarta kammune.”

       Yaya Abubakar ya amshe da faɗin, “Wannan gaskiyane Yaya Muhammad. Insha ALLAHU bazakai baƙin ciki akanmu ba Isma'il. A matsayina na jimi'in tsaro kuma zan cigaba da baka gudunmawa insha ALLAH a duk sanda kake buƙata, sai dai ina roƙonka ka tabbatar duk abinda kake aikatawar nan kanada hujja ta gaskiya aranar kare kai, dan idan naci karo da saɓanin hakan komai zai iya faruwa”.

        Murmushi yayi na ƙasaita yana jinjina kansa, “Nagode matuka yan uwana da Ummin mu. Abubakar karka damu kaima insha ALLAH, dan na jima da saninka da kuma gaskiyarka da ƙwazon aiki.

         “Shiyyasa kazo kaketa min ƙafar angulu akan auta ko?”. Yaya Abubakar ya faɗa cikin barkwanci.

    Dariya suka sanya baki ɗaya. Banda Master da murmushi ne kawai nasa dan dama can yawan fara'a ba ɗabi'arsa bace. Sunema yake sakewa da su matuƙa fiye da zato da hasashe. Duk da dai lokacin baya yana zuwa musu ne da fuskar mutane masu sanyin hali saboda salon acting daya ƙware akai like wani ɗan film. Miƙewa yay yana duban agogo ganin dare yaja. “Kai kai bara na barku kuje ga amare fa Yaya Muhammad kar mu take shari'a. Ummi samin albarka na gudu nima”.

         Kansa Ummi ta dafa tana murmushi dan ita kallon ɗa take masa bawai suruki ba. Tai masa addu'a da sanya albarka saboda har yanzu zuciyarta bata gama dai-daita da sheɗancin da Halilu ke shiri akansu ba. Dan ma bataji yana aikata ƙazantar luwaɗi ba kenan. Sallama yay musu ya fita akan zai dawo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai zama busy a satin nan.

     Har ƙofar gida su Yaya Umar suka rakoshi zukatansu sakayau bakamar yini da kwanan jiya ba da suka kasance a damuwar rasa Hibbah. Yana tafiya suka rufe gidan suka dawo ciki, zukatansu kuma fal tunanin miyasa yake aikata yahoo? Dan suna buƙatar sanin hakan kodan ƙanwarsu da ke a hannunsa matsayin mata. Bazasu so ta kasance a gararin rayuwa ba, ba kuma zasu so ta kasance da mijin da zai ciyar da ita ta hanyar haram ba.

       Sun so zama su tattauna maganar Ummi ta korasu suje ga matansu da safe zatai magana da su.

     


★★★★


     Tunda yabar gidan su Ummi ajiyar zuciya yaketa faman saukewa da dafe kai saboda ciwon da yake masa na rashin sabon dogon surutun daya zuba a yau. Sai dai kuma yanajin zuciyarsa sakayau tamkar ya sauke wasu kaya masu azabar nauyi dake a kansa ne. Sai da ya biya ta gidan A.G ya amshi takardun aikin Abba sannan ya wuce gida.


       Koda ya isa gidan a falo ya samu su Habib sun baje kowa da hidimar da yakeyi, ga kayan ciye-ciye sun baje tamkar wata sabuwar bola. Shigowar tasa ce ta saka falon ɗaukar shiru kowa ya nutsu. Cike da girmamawa a garesa tamkar yanda suka saba suka shiga masa barka da zuwa. Hannu ya ɗan ɗaga musu yana bin falon da kallo fuska a tamke da binsu da harara. Sun san laifinsu dan haka suka shiga sosa ƙeya kowa na kai hannu a sace yana ɗauke ledar gabansa da su gwangwanaye.

    Komai baice musu ba ya nufi upstairs ɗin yana hawa steps ɗin a kasalance da izzar data zamewa gaɓansa jiki. A dai-dai nan Hibbah da yunwa da damuwa ke neman halakawa ta fito daga cikin ɗaki itama cikin ɗan layin barcin data fara tun bayan idar da salar isha'i. Abincin data hanga a shirye a dining ɗin falon saman ya sata nufar can duk da ta fahimci mai faɗa ajin gidan aka shirya mawa. Kujera taja ta zauna a fili take faɗin, “Daga gani shegen ci ne da wannan mutumin, tunda kuwa ya sakani kuka ɗazun na rantse da yunwa zai kwana shima mugu dangin su Halilu mtsoww ”.

       Karaf kuwa wannan zance a kunnen Master da ke hauro step ɗin ƙarshe. Cije lip ɗinsa na ƙasa yayi tare da kai dubansa gareta da lumsassun idanunsa da tsantsar gajiya da ciwon kai ya kanainaye. Ya ɗan sake tsuke fuska da nufar inda take batare da ita kuma tasan da shigowar tasa ba. Hidimar ma zuba lafiyayyen abincinsa da baba saude ta haɗa masa na musamman takeyi cike da mugunta. Ta ɗiba gasashen hantar da yaji kayan haɗin salad zata kai baki ya riƙe hannun..............✍


*_Gashi nan harda na gobe idan ALLAH ya kaimu😌🚶🏻_*


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_Chapter Thirty_*


...........Saurin kallon hannun tayi, ƙamshin mayen turarensa dake daɗewa jikinsa yana rige-rigen shigaa hancinta, hannunta tai ƙoƙarin fisgewa ya ƙara damkewa. Zafin daya ratsata saboda yanda ya matse tafin hannunta da spoon ɗin ne ya tilastata ɗago idanunta dole ta dubesa fuska a kumbure. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tai azamar janye nata dan harga ALLAH ƙwayar idanunsa mai kama data gawurtaccen bajimin zaki tsoto take bata. Ɗan luuu yay da idanun tare da dafa makarin kujerar da take zaune ya ranƙwafo kanta har yanzu hannunsa na riƙe da nata.

       Gaba ɗaya ta dabirce, ta matse jikinta tana sake ƙoƙarin fisge hannunta amma ta kasa.

       “Bayan satan waya ashe har na abinci kin iya kandala?”.

       Ya faɗa a saitin kunneta cikin wani irin slow voice daya saka Hibba ɗan zabura ta matsar da kanta saboda wani irin harbawa da zuciyarta tayi, yayinda gaba ɗaya tsigar jikinta ya miƙe. “Ni wlhy bana sata, kuma ba sunana kandala ba”. Tai maganar da saurin yunƙurawa zata tashi ya sake tsare ko ina har tana jin fita da saukar numfashinsa.

        Wani ɗan lalataccen Murmushin gefen baki ya saki tare da ɗago hannun nata ya kai spoon ɗin bakinsa batare da ya saki hannunba ya sake faɗin, “Tunda na sameki akan abincin da ba naki ba ai sata ne. Sai shegen handama kin cinye naki zaki haɗa da nawa. Da kin sake ko spoon ɗaya ya shiga wannan bakin mai kama dana akku sai kinyi amansa”. Yay maganar yana sake ranƙwafota da ƙyau cikin alamar tabbatar da zancensa. Sai kuma ya saki hannun nata.

        Da sauri ta yarfar da cokalin tamkar wadda ta riƙe maciji. Shima ɗagawa yay da ga ranƙwafawar da yay kanta ya miƙe tsaye sosai akan kafafunsa. Kujerar kusa da ita yaja ya zauna duk da bai ra'ayin cin abincin ba da farko. Plate ɗin data zubama abincin yaja gabansa, tare da sake ɗaukar wani cokalin ya fara ɗiba ya kai bakinsa. Miƙewa tai cikin fushi ta ture kujerar baya tabar gurin hawaye na sakko mata.

         Yi yay kamar baisan da tashin nata ba. Sai da ta kai ƙofar ɗakinta ya ɗan ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi da kai abincin bakinsa. (Burum!!!) ta rufo ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ƙasaitaccen Murmushin ya sake saki yana miƙewa. Ya ja tissue ya goge bakinsa sannan ya janye idonsa daga ƙofar ɗakin nata. Ɗakinsa ya nufa dan babu abinda yake bukata sama da son jin ruwan ɗumi a jikinsa. Tun kafin ya shige ya zame facemask ɗin fuskarsa ya bayyana a Isma'il ɗinsa.


     Hibba na shiga ta faɗa saman gado ta riƙe ciki, dan da gaske yunwar takeji sosai. Babu yanda Baba saude batai da ita ba taci abinci bayan fitarsa gidan amma taƙi. Har tea tace ta haɗo mata tace ta ƙoshi. Hawayen da suka ciko mata ido ta share tana matuƙar jin kewar Umminta da su yaya Muhammad. Ga kayan jikinta sun isheta matuƙar har ƙyanƙyaminsu takeji. Miƙewa tai da tunanin bara ta ɗanyi wanka ko zata rage halin da take ciki ma ta samu damar yin tunanin mafita akan azzalumin nan ɗan homo.

      Kusan mintuna sha biyar sai gata ta fito ɗaure da ɗankwalin kayan nata da dudu iyakarsa cinyarta, cinyar ma ko rabi bai rufeba. Da ace zata duka babu abinda zai hana a ga jikinta. Bakin ɗan kwalin ta ɗan sa tana goge gefen kunnenta zuwa goshinta da ƙananun gashi suka kwanta sosai. Dan masha ALLAH hibbah nada gashi yalwatacce. Ga cika ga tsaho gwargwado.

       A dai-dai lokacin ne kuma Master da har yay shirin barci bayan ya watsa ruwa ya iso bakin ƙofar riƙe da plate daya zuba abincin kaɗan sai tab.. Da kaya kala ɗaya. Hannu ya ɗaura bisa handle ɗin yana sake tsuƙe fuska dan kansa ciwo yake masa matuƙa. A firgice Hibba ta juyo jin an buɗe ƙofar. Ta zazzaro idanunta saboda daburcewa ma ta gagara neman mafita.

        A kanta ya sauke mayatattun idanunsa da barci da gajiya suka maidasu fici-fici. Janyewa yay cike da basarwa yana cigaba da takowa cikin ɗakin tamkar ma bai fahimci dalilin ruɗewar tata ba. Hibba da ta samu nasarar jan hijjab ta saka ta haɗe fuska sosai tana hararsa. “Shi dai musulinci ya bada dokar yanda ya kamata mutum ya shiga waje ai. Amma ba'a dinga faɗoma mutane kamar wata kirsimeti (Christmas) ba”.

      Banza yay mata kamar bai jita ba. Sai ma ajiye tarkacen hannunsa da yay saman mirror ɗin ɗakin. Batare da ya sake dubanta ba ya fara magana a daƙile. “Kiyi shopping na duk abinda kike buƙata ta online, idan kika cimin data bayan haka kuma....humm”. Ya ƙare maganar yana watsa mata hararar data hanata sake magana.

     Harya fara tafiya tunanin da tayi yanzu-yanzu yasata azamar zabura tai saurin zuwa tasha gabansa. Wani irin shegen kallon da ya saka hantar cikinta kaɗawa yay mata, amma itama da yake gwanace ta taurin kai da kafiya sai tai ƙasa da kai kawai bata miƙe ta bashi hanyar data tare masa ba.

       Sake raɓawa ta gefenta yayi zai wuce tamkarma bai gantaba. Sai dai yanda ta durƙusa a gabansa hawaye na zirara a kan fuskarta ya sakashi satar kallonta ta ƙasan ido yana ɗan takawa ya wuceta, sai da ya kama handle ɗin ƙofar sai kuma ya ɗan rumtse idanunsa yana cijar lip nasa tare da dakatawa.      

     Jin ba'a buɗe ƙofar ba yasa Hibba fahintar bai fita ba, bazai tanka mataba ne ya sata fara magana cikin raunin murya na drama ɗin data shirya masa cikin ƙanƙanin lokaci, dan halin da Ummi zata iya tsintar kanta a ciki kawai take hangowa. “Na roƙeka dan ALLAH ka maidani ga ahalina. Mahaifiyar mu tana da rauni na ciwo da kan tashi a dalilin damuwa. Rashina kuma yana ɗaya daga manyan abinda zai iya tada mata shi. Indai nice na janye alwashina, bana buƙatar wani TAKUN SAƘA da kai. Da ga karshe ina roƙonka dan ALLAH ku barmin ahalina. Ku duba maraicinmu da raunin mahaifiyarmu🙏🏻”.

      Ta kare maganar da haɗa hannayenta waje guda alamar roƙo kukan gaskiya na suɓuce mata yanzu kam. Jin bai tanka ba yasa ta ɗago idanunta da hawaye ke cigaba da mata zarya a kumatu ta dubesa. Har yanzu idanunsa a rumtse suke, kuma bai juyoba bai kuma saki ƙofar ba, sai dai sarai yana jinta. Amma tsabar ƙasaita da mulki yamayi tamkar bai san da kasancewarta a wajen ba.

     Wasu irin zafafan hawaye ne suka sake ziraro mata na tsananin tausayin yayunta da begen Ummin ta. Tana buƙatar zuwa garesu kodan ta sanar musu abinda taji ga Abbah, shiyyasa ta ƙudiri ɗaukar duk wani wulaƙancinsa, indai hakan zaisa ta dace da fatanta na komawa gida.

      Tsahon mintuna biyu bai tanka ɗin ba, yana dai sauraren kukanta dake ƙara saka jijiyoyin kansa miƙewa. Ganin haƙanta bai cimma ruwa ba ya sata miƙewa da nufin barin wajen, dan ta gama sallama taurin rai da rashin tausayinsa. Takunta biyu ana uku Ƙasaitacciyar muryarsa ta sakata dakatawa.

        “Ni bana magana biyu”.

    Wani irin ɗaci da jin zafinsa ne ya soki zuciyar Hibbah. Ta cije lips ɗinta da ƙarfi tana matso hawayen da suka sake ciko mata idanu. Cigaba tai da tafiyarta wani duhu-duhu na mamaye idanunta.

       Da ƙyar ta ƙarasa saman gadon kuka na sake kufce mata. Tana tsoron rasa Ummi da yayunta, tana takaicin fasiƙi azzalumi irin Abba ya samu galaba akansu. Sai a yanzunne take jin matuƙar takaicin biye masa tun farko harta maida murtani. Dan zuwa yanzu ta fahimci irin wannan mutumin ba'a cinsu da yaƙi ta ƙuru-ƙuru sai ta siyasa da taku. Hakan na nufin kuma sai ka kwantar da kai wajen fara fahimtar su ɗin su wanene kafin ka samu damar kutse a lamuransu. Inama ɗazu shiru tai masa har yayi ya gama. (Dole ne yanzu ta sake sabon shiri), ta ayyana a ranta tana miƙewa zaune. Mamaki ya kamata ganin bai fita ba. Ya saki ƙofar ya juyo hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya tokare ƙafarsa ɗaya jikin ƙofar daya jingina bayansa. Sai idanunsa da ke matuƙar hanata sukuni da tsiwa da ya zuba mata yana wani kallonta tamkar a ɗage.

     Kanta ta maida ta duƙar tana share hawayen. Lumshe idanun yay ya buɗe yana ɗaukesu da ga kanta ya maida kansa ga ƙofar ya jingina. Ta ƙasan ido ya koma kallonta batare da tasan yana cigaba da kallon nata ba duk da tanajinta a takure har yanzun.

      “Zan iya baki dama bisa sharaɗi”.

Da sauri ta dubesa jin abinda ya faɗa. Tai saurin miƙewa ta nufosa cikin sassarfa. “Dan ALLAH Yaya kana nufin zaka barni in tafi wajen Ummi na?”.

       Ta faɗa tana matsoshi gab batare da tasan tayi hakan ba saboda zumuɗi. Idanunsa ya buɗe da ƙyau a kanta jin yanda ta kusanta kanta da shi. Yanda ya zuba mata idanun ya sata tura baki tai ƙasa da kanta.

       Warware hannayensa yayi yana miƙewa da ƙyau ya tsaya kan ƙafafunsa. Hakan sai ya sake kusancin nasu matuƙa. Baya ta ɗan ja tana sake ɓata fuska. Takowa yay ya sake matsawa suka koma yanda suke, bayan ta shiga jan ƙafafunta. Shi kuma ya cigaba da takawa yana binta har suka dangane da mirror. Hannayenta duka biyu ta dafe mirror ɗin da su tai ɗan baya saboda yanda ya tsaya mata ƙiƙam tamkar soja. Bakinta ne ya shiga motsawa alamar akwai magana amma babu damar faɗa.

       Fahimtar hakan ya sakashi fara magana a daƙile yana bin fuskarta da kallo. “Zakiyi aiki na wata guda tare da mu....”

       Zabura tai babu shiri, hakan ya sata faɗawa jikinsa saboda kusancinsu. Bai riƙeta ba, dan haka ta sake komawa baya jikin mirror ɗin tana faɗin, “Kana nufin nima na fara sata?”.

       “Itama sana'ace ai”.

Yay maganar yana tura duka hannayensa a aljihu da lumshe ido ya buɗe lokaci guda.

      “Tab wlhy ban yarda ba. Ƴar yahoo fa kenan mai datsan accaunt ɗin mutane, zamb.......?”

      Tai saurin rumtse idanun da bakinta batare da ta ƙarasa ba saboda ganin ya ɗora hannayensa saman mirror ɗin yayo kanta. Saurin maida lips ɗinta tai cikin baki ta matse tana ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka, dan yanda ya kusanto da fuskarsa da tata har yana busa mata numfashinsa sai ka ɗauka wani abu zai mata. Janye fuskar tasa yay ya maida saitin kunnenta yana sake tsuke fuska. Cikin wani irin Slowly voice da ke nuna gajiyarsa matuƙa ya fara magana yana shaƙar ƙamshin da gyararren gashinta keyi duk da ya ɗan mimmiƙe ta gaba dan tun gyaran ranar ɗaurin aure. “Ashe zaki dawwama tare da Master har tsufanki babu ganin Ummi”.

      “ALLAH ya kiyaye na zauna da mai homo, wlhy kota katanga sai na haura”.

       Baki ya taɓe da ɗage kafaɗa irin I don't care ɗinnan. Batare da ya sake ko kallonta ba ya nufi ƙofa abinsa cike da takun ƙasaitarsa da izza. Kukan ƙarya Hibbah ta fashe da shi duk da dai har cikin ranta tanajin raɗaɗi da takaicinsa. Baiko nuna yasan tanai ba ya buɗe ƙofar ya fice abinsa.

       “Mugu danginsu Halilu. Na rantse sai kayi dana sanin satoni wannan gidan naka, dan saina addabi kowa. Da wani idanunsa abin tsoro”.

     Oho shi baima san tanai ba. Dan tuni ya kai downstairs. Kamar yanda ya saba a duk dare sai da ya leƙa ɗakunan su Salis ya tabbatar suna lafiya. Waɗanda basu kashe fitila ba ya kashe musu. Wasu ma har barguna ya gyara musu a ransa yana ɗan mamakin kwanciyar tasu da wuri yau, sai da ya ƙara musu addu'ar barci kamar yanda ya saba sannan. Compound ya fito ya dudduba. Sai da ya tabbatar komai normal ma anan sannan ya dawo ciki ya kashe sauran fitulun ya haura sama. Ƙarasa shirin barcinsa yay ya haye gado yana godema UBANGIJI da ya kaisa wanann lokaci da rai da lafiya bayan wasu na asibiti wasu ko na gida cikin jiyya matsanciya. Cikin ƙanƙanin lokaci barci yay awon gaba da shi dan yayi matuƙar gajiya. Gashi dama yasha maganin ciwon kan.


     A ɓangaren Hibbah kam sai da ta gama sharce-sharcen ƙwallarta ta cire hijjab ɗin bayan taje ta murzama ƙofar key. Kayan daya ajiye ta warware. T-shirt ɗinsa ce mai gajeren hannu da three quarter wando sai mayen ƙamshinsa sukeyi. Ta ɓata fuska tana cillar da kayan. “Ni bazansa kayan ƴan homo da yahoo ba”. Tai maganar tamkar zatai kuka.

     Abincin da ya ajiye ta ɗauka da bottle water ɗin da suma ya ajiye ta zauna a bakin gado ta fara ci dan da gaske yunwa takeji. Taci sosai tasha ruwan sannan ta miƙe. Kayan ta sake harara dan harga ALLAH tana buƙatar saka sutura a jikinta. Bazata taɓa iya barci da guntun ɗankwalin dake ɗaure a jikin nata ba. Hakama kayan data cire ƙyanƙyaminsu take bazata iya maidasu jikinta ba. Wando da rigar data gama mita a kansu ta ɗauka ta saka. Sai ga three quarter ita ya zamar mata dogo, dan kaɗan ya rage ya rufe idon sawun ƙafarta. Hakama rigar tai mata burun-burun tamkar kaita mata dariya. Baki ta taɓe da yamutsa fuska tana duban kanta a mirror, dan ba karamin addabarta ƙamshin turaren nasa yayi ba.

   Idonta ne ya sauka akan tab ɗin daya ajiye mata. Ita sam tama manta da ita. Ɗauka tai da saurin tana faɗin, “Stupid me. Wai mima ya kaini masa magana bayan ga maganin kukana anan”. Ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariya. Ta dira tsalle ta ɗane gado ranta fal farin ciki. Babu lock a tab ɗin, hakan ya bata damar sauke idanunta akan hoton su Habib su bakwai sai shi na takwas a tsakkiyarsu, duk sun wani kanannaɗe masa jiki tamkar tata. Shima ya shafo fuskar Adam da Khalid dake gefe da gefensa yana ɗan murmushi. Daga ƙasa Habib da Idris suna zaune sun ɗaura kawunansu bisa ƙafarsa ɗai-ɗai sun kwantar. Sai bayansa Musbahu, Zaidu, Salis suna akan kafaɗarsa suma. A kallo ɗaya zaka fahimci tsantsar ƙaunar da sukema juna. Ta ɗan taɓe baki da faɗin, “A haka dai kamar mutanen kirki, sai dai ALLAH kaɗai yasan tsiyatakun da kuke aikatawa.”

       Kauda hoton tai da nufin shiga inda applications suke taci karenta babu babbaka sai taga saɓanin haka. Dan kai tsaye ga shagon da zatai sayayya ya kaita. Cikin takaici tai ƙoƙarin fitowa amma hakan ya gagara. Tamkar zata fasa kuka dan haushi. Har tayi niyyar ajiye tab ɗin sai kuma ta tuna bata da sutura kota yin salla. Da bai taimaketa ya bata waɗan nan ba ma da batasan yaya zatai ba. Kaya ta fara zaɓa harda underwears tanata faman ƙunƙuni. Yanda taketa zaɓar abubuwa zaka fahimci harda mugunta a ciki. Dan sai faman taune lip take tana murmushi. Sai da ta gama yayar kaya san ranta sannan ta dangwarar da tab ɗin tana hararta ta koma ta kwanta duk da bata tunanin zata iya yin barci saboda kewa da damuwar rashin ahalinta a tare da ita.


*_WASHE GARI_*


         Kamar yanda ya saba shine ya tashesu suka wuce massallaci duk da kuwa bayajin daɗi, dan ciwon kan har yanzu bai sakesa ba duk da yayi barci. Koda suka dawo su kaɗai suka shiga ɗakin motsa jiki shi sama ya dawo. Bai ko kalli ɗakin da Hibbah take ba. baima nuna ya tuna tana gidan ba ya shige abinsa.

       A ɓangaren Hibbah ma ta farka dan ta saba. Sai dai tana idar da salla ko azkar batai ba ta haye gado ta koma barci. Barci sosai ta sha har kusan goma saura. Tana buɗe ido da ledoji taci karo manya-manya guda uku. Fahimtar kallo daga nesa bazai mataba ya sata sakkowa taje garesu. Ɗan bubbuɗewa tai sai taci karo da kayan datai shopping jiya da dare ta online. Babu shiri ta shiga sungumar ledojin duk da akwai nauyi tana kaiwa saman gado ta dinga ɗagasu tana zazzagewa.

      Mamakine ya bayyana a saman fuskarta ƙarara. Dan duk abinda ta zaɓa ɗin an sako mata. Harma da wanda bata zaɓa ba na fanin kayan shafa, sabulai, kayan gyaran gashi, da kayan yan kunne sai takalma. total na kuɗaɗen da aka sakko ta shiga dubawa mamaki na neman halakata. “Anya mutumin nan yana da man kai kuwa? Koda yake ina ɗan yahoo ma yasan zafin kuɗi tunda wasu suka tara ya wawasa. ALLAH ya gani naidai tunda badani ya sato ba ko naci banda zunubi”. Ta faɗa cike da yarda da kai.

       Dama azababben ƙamshin turaren kayansa ya isheta, dan haka ta faɗa wanka. Bata wani jimaba ta fito dan dama bata daɗewa a wanka, da sabbin kayan shafanta tai amfani, dan tana son fara aiwatar da shirinta na yanda zata kuɓuta a gidan nan. Tai kwaliyarta gwargwado ta shirya cikin wata doguwar riga maroon mai laushi da tabi jikinta kasancewar kamar roba take. Sai dai bata fidda mata jiki ba. Dan daga sama an mata wani ado da yay tamkar mayafi ya rufe ƙirjinta duka hakama ya sauka bayanta har kasan mazaunai. Ita kanta tasan tayi kyau gwargwado. Dan haka ta tattare sauran kayan tasa a Wadrobe ɗin ɗakin ta ɗauka gyale karami dake cikin kayan ta yana a kanta. Tab ɗinsa da plate ɗin da taci abinci jiya ta ɗauka ta fito, dan yanzun ma yunwar takeji.

       Babu kowa a falon saman sai ƙamshin air Fresheners da mayataccen ƙamahin turarensa alamar ya gitta falon. Baki ta tabe da nufar ƙasa. Kasancewar hankalinta na kan tab ɗin yasa bata kallon gabanta, so take ta fito a shop ɗin jiya amma har yau yaki, da alama shi yay hakan dan karta samu damar shiga ko ina.

      “Good morning Aunty Queen!!”.

Su Zaidu dake kan dining suna karyawa suka haɗa baki wajen faɗa dai-dai Hibbah na taka step ɗin ƙarshe zata dire ƙafarta ƙasa tamkar wasu ɗaliban makaranta. Fasa saukar da kafar tai ta ɗago aɗan razane ta dubesu. Kawunansu sukai saurin maidawa ƙasa suka duƙar saboda harar da boss ya gallaro musu da ga inda yake zaune can gefen falon saman ɗaya daga cikin kujeru biyun da aka ajiye dan hutawa ta musamman yana ta faman sarrafa lap-top.

       Fuska Hibba ta ƙwaɓe itama tana hararar su, dan sam bata lura da Master ba. “ALLAH idan baku daina cemin auntyn nan ba sai na haɗaku da jarababben uban gidankun nan da wata ɗaurarren face ɗinsa kamar mala'ikan ɗaukar rai.”

       Idanu suka waro waje tare da saka hannu sukai saurin ɗorawa a saman bakunansu, saboda dariya dake neman kufce musu babu shiri.  Yayinda ita kuma ta kaɗa kanta ta cigaba da tafiya fuska a kumbure. Turus taja ta tsaya saboda cin karo da wanda batai tunanin gani ba zaune a falon, duk da yayi tamkar baya jinsu sarai tasan duk abinda tace masa akan kunnensa ne. Ita kanta baba Saude dake daga kitchen dariya ta shigayi, yayinda wani sashe na zuciyarta ke ayyana mata (inama ace....)

          Hibbah ta ɗan saci kallon fuskarsa da ke a tsuke ta ganta babu alamar rahama, wani irin sake tsargawa cikinta yayi, dan ta tabbatar zai iya mata walmakalifatu. Dabara ce tazo mata, dan haka cikin ɗan raunana murya da langaɓe kai gefe ita a dole kalar tausayi tace, “Yaya Master dama tab ɗinka ce na kawo maka ko zaka nema. Kuma na......”

     Wani shegen kallo daya watso matane ya sakata saurin duƙewa ta riƙe ciki da faɗin, “Wayyo Ummi na cikina. Yaya Muhammad!!...”

     Da sauri baba saude ta fito a kitchen, hakama su Khalid duk mikewa sukai duk zatonsu gaske takeyi tunda kansu a duƙe yake basuga harar da yay mata ba. Amma sunji mitace akan tab. Baba saude data ƙaraso ta kamata ta tayar tana jera mata sannu. saman doguwar kujera ta kaita duk ta rikice. Hakama su Habib falon suka nufo a rikice suna tambayarta dama bata da lafiya ne?.

       Murƙususun ƙaryar da takeyine ya hanata basu amsa. Baba Saude dake a rikice ta dubi Master da yay kunnen uwar shegu da su kamarma baisan sunai ba. “Babana ko akwai wani maganine da zata sha a cikin maganinta?”.

        Idanunsa ya ɗago a hankali ya dubi baba Sauden, kafin ya janye ya maida kan Hibbah data haƙiƙance ita ciwo cikinta ke mata da gaske. Lip ɗinsa yaɗan ciza ta gefe yana mikewa da ajiye lap-top ɗin saman table ɗin kujerun. Cikin halin ko in kula ya nufa inda suke cike da ƙasaita. Musbahu ya kalla a ƙasan maƙoshi yace, “Ɗakko min maganin feshin flowers ɗin nan a bata yana maganin ciwon ciki....”

       “Kaji mugunta”.

Hibbah ta faɗa tana mikewa zaune dingangan. Ta dubi baba saude data wangame baki tana kallonta. “Baba wlhy so yake ya kasheni kawai mutumin nan dama ba ƙaunata yake ba”.

       Babu shiri su Habib suka kwashe da dariya. Sai kuma sukai saurin gimtsewa saboda kallon da yay musu. Hibbah ta mike zumbur ganin ya nufota. Bayan baba Saude ta koma ta maƙale.

        “Wayyo baba!, wayyo baba saude!!”............✍


*_fajin he tsaho ike😌🙄😏🚶🏻_*


      


    TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


L09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 


*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


_________________________


*_Chapter Thirty one_*


...........Tab ɗinsa data yasar a ƙasa ya ɗauka ya bar wajen batare da yako kalleta ba. Hakan yasa taɗan sauke ajiyar zuciya tana fitowa da ga bayan Baba Saude data ɓuya. Kallonta baba Saude da ke murmushi tayi. Cikin son tsokanarta tace, “Anya baza'ai ƴar gida ba anan ɗiyata?”.

     Cikin rashin fahimta Hibba tai ƴar dariya tana zama. “Baba Saude ina kwana”. “Lafiya lau”. Ta amsa mata da kulawa. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Ke da baki da isashen lafiya ya kamata kizo ki karya”.

      Kallon su Habib da suke tattare plates ɗin da suka gama tayi. “Baba nifa lafiyata lau ALLAH. Waya ce miki banda lafiya ne?”.

       Da sauri gudun karta ɓaro musu aiki Khalid ya ce, “Baba saude yau dama tuwon rana akai mana miyan ɗanyen kuɓewa”. Hankalinta ta maida garesa da faɗin, “To shikenan Khalid inhar suma duk suna so ai sai ayi.”

     A mamakin Hibbah da ke kallonsu sai gani tai sun hau murna harda rawa. Baki ta ɗan taɓe tana mikewa, a ranta ko tana ayyana taɓararsu.


       Duk yanda Hibba take dojema su Habib a wannan yini sai da ta saki jikinta da su ƙarfi da yaji, saboda yanda suke shiga lamarinta. Da ga ƙarshe sai gashi sun baje a falo suna hira tare cikin nutsuwa. Dan idan taso nutsuwar bazaka taɓa ɗauka ita bace. Ita kanta Baba Saude tayi mamaki. Takuma fahimci cewar gata ne kawai ke ɗawainiya da Hibbar.

      Tare suka shiga kitchen ita da baba Saude sukai girkin rana. Bayan sun kammala ta fito ta koma sama. Salla tayi tai kwanciyarta sai barci. Da ga haka babu wanda ya sake jin ɗuriyarta har bayan la'asar. Dan koda ta tashi tai salla sai tai zaman shan kukan kewar ahalinta. Sai kusan biyar ta fito falon.

     Kowa bata samu ba sai motsin baba saude a kitchen. Ta leƙa ta gaisheta tana tambayarta su Idris. Computers room ɗinsu baba sauden ta nuna mata. “Suna cikin can, suna dawowa da ga sallar la'asar babana ya kaɗasu can kinsan su ƙwararrune na na'ura mai ƙwaƙwalwa anan suke wasu ayyuka nasu da nima bansan kona minene ba”.

       “Na satar kuɗaɗen mutane mana”. Hibbah ta faɗa a hankali batare da baba Saude tajita ba. Ɗakin ta nufa, ganinsa a buɗe yasa ta danna kai da sallama. Shi kaɗai da ke tsaye a kansu ya ɗago ya kalleta. Su Salis kam duk sun duƙufa aikin gabansu. Haɗa idon da sukai yasata janye nata ta maida kansu Adam. Yanda suke sarrafa kwamfitocin sun matuƙar birgeta. Dan sai ka ɗauka bada hannu suke sarrafa keyboards ɗin ba tsabar ƙwarewa da yawan dannawar da suke a koda yaushe.

           “Guys are you ready?”.

Musbahu ya faɗa da ɗan ƙarfi. A tare suka haɗa baki wajen faɗin yes. Sosai Hibbah ta nutsu wajen kallonsu matuƙa, suko sunata aikinsu cikin maida hankali garesa har aka kira sallar magrib. Ganin ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa da faɗin, “Lokacin salla yayi” ya sakata juyawa zata fita.

     “Hii Auntynmu”.

Salis ya faɗa yana ɗaga mata hannu. Juyowa tai tai wani ɗan yaƙe tana ɗaga masa hannu sai kuma ta gimtse fuska da hararsa. Ya haɗe hannayensa alamar tuba fuskarsa ɗauke da murmushi kamar yanda suma sauran sukeyi mata. Sake tsuke fuska tai ta fice batare data sake tankawa ba.


      Tunda Hibbah ta koma ɗakinta taketa faman kai kawo na mamaki. Gashi takadari shu'umi, amma a ɗan kwanan da tai a gidan biyu ta fahimci sam baya wasa da salla baya barin su suma suyi wasa da ita. Anya bazata amshi tayin yimasa aikin na wata guda ba kodan ta yo leƙen asirinsa. Dan bata da wani babban burin da ya wuce ganin ta damƙa su Abba da dukkan mabiyansu ga hukuma kodan kuɓutar da kanta da ahalinta garesu.

     Wannan shawarar da ta yankema zuciyarta ne ya sata fitowa bayan sallar isha'i. Cikin sa'a kuwa ta samesa a falon saman shi kaɗai zaune yana aiki a system. Gefe kuma yana shan baƙin shayin da keta tashin ƙamshi. Sarai ya ganta ta gefen ido, sai dai a ransa yana mamakin ganin yanda ta fito a nutse tamkar ba ita ba. Mamaki bai karasa kasheshi a zaune ba sai da ta zauna a ƙasa tana faɗin, “Yaya Master barka da aiki”.

    Duk yanda yaso shareta sai ya kasa. Batare da ya kalleta ba yace, “Kina buƙatar wani abu ne?”.

      Duk da ta ɗanji haushin yanda yay ɗin sai ta danne. Cikin sanyin murya da kwantar da kai tace, “Dama zance maka ne na amince zanyi maka aikin. Amma dan ALLAH nima ka cikamin alƙawarin barina naje ga ahalina bayan na kammala. Sai dai ina roƙonka abu biyu. Ka haɗani dasu ko waya muyi dan su sami nutsuwa nima na samu. Sannan dan ALLAH karka sakani aikata abinda ba dai-dai ba. Kaga ni ɗin marainiya ce, sannan kuma mace. Ɓacin sunana ko fitar tambarin fuskata da sunana ga al'umma tamkar daƙile wata ƙofar mutunta sunan gidanmu ne. Sannan zaiyi wuya ace na sami mijin aure bayan wannan shine fatan kowacce ɗiya. Abu na ƙarshe bana fatan a tada mahaifina a nuna masa ni matsayin ƴar ta'adda bayan ban nema masa mutunci da addu'a ba. Sai kuma dan ALLAH ka zamemin garkuwa na mutuncina a gidan nan duk da tunda na shigo babu wanda ya nufeni da ko maganar banza a cikin yaran ka da ya shafi iskanci. Kaima ka ɗan rage kusancin da kake son haifarwa a tsakaninmu kodan gujema sharrin shaiɗan”.

        Tunda ta fara magana ya gagara cigaba da danna system ɗin. Karo na farko a rayuwarsa da ya sakata a jerin masu hankali da nutsuwa. Ko sanda yake zuwa gidansu da farko kallon miskila yake mata sangartacciya. Sai daga baya ya fahimci kawai gatane data tashi a ciki ya sata zama kamar wata sakalya ga shegen baki........

      “Dan ALLAH”.

Ta faɗa cikin katse masa tunani. Numfashi yaja ya fesar tare da janye idanunsa a kanta. Kujerar gefensa ya nuna mata alamar tazo ta zauna. Babu musu ta mike ta zauna kanta a ƙasa dan batason kallon idanunsa tsoro suke bata.

     “Muhibbat!”.

Ya kira sunanta a karo na farko tun shigowarta gidan.

      Ta amsa masa da “Na'am” a nutse kai kace ba ita ɗin bace ba.

      “Shekararki nawa ne?”.

“Sha tara”.

Ya gyara zamansa yana fuskantarta sosai. “A shekarun nan naki nasan dai kinsan minene aure tunda har kika ambacesa, sannan kina zuwa islamiyya kinsan minene addininki”.

    Kanta ta jinjina masa, tana wasa da yatsun hannunta.

          “To Alhmdllh. Da farko dai naji duk bayaninki da amincewarki. Na biyu inason ki kauda duk wani tunani akan waɗan nan yaran da kike gani a gidan nan. Duk da nasan zuciya bata da ƙashi bana fatan wata rana da wani a cikinsu zai miki kallo irin wanda kike tsoro. Dan kasantuwar hakan na nufin tabbas zan iya halaka yaro kona nakasashi.” Ɗagowa tai ta ɗan kallesa saboda jin abinda ya ce. Sai dai ganin shima ita yake kallo ne yasata maida kanta ta duƙar.

      Cikin halin ko in kula da yanayin nata ya cigaba da faɗin, “Bazance miki na amince da kowa a cikinsu ɗari bisa ɗari ba, sai dai ina musu ƙyaƙyƙyawan zato kasancewar su ɗin tarbiyyata ne. Nasan su ba muharramanki bane ba, hasalima bai dace na kawoki cikinsu ki zauna ba. Sai dai nayi hakanne bisa ga lalura da kuma sanin nan ɗin shine kawai yafi tsaro a gareki. Abu na ƙarshe inason ki sani ni ɗin mijinki ne”.

       “Miji?”.

Hibbah ta faɗa a kiɗime.

     Kansa ya jinjina mata yana tamke fuska fiye da da saboda sanin halinta. “Kamar yanda naje neman aurenki gidanku ban ɗakkoki nan ba sai da na biya sadaki aka ɗaura da shaidu”. Ya ƙare maganar da ɗakko lap-top ɗinsa dake gefe ya danno mata video. Tabbas taron ɗaurin auren yayinta ne. Dan yana saka play da fuskar Yaya Umar ta fara cin karo, wanda yake sanye cikin kayan da suka saka ranar ɗaurin auren. Yanata waya alamar baima san ana ɗauka ba. Cikin tsumar da jikinta ke mata ta cigaba da kallo har aka gama ɗaura auren duka yayunta dasu Zahidah aka ɗaura nata a ƙarshe ita da ango mai suna Muhammad Shuraim Aliyu. Kuma hakan na nufin shine kenan. Tunda Baba Saude ta tabbatar mata sunansa ne.

     Kanta ta shiga girgizawa hawaye na kwaranyo mata. Ta buɗe baki kamar zatai magana sai kuma ta kasa kuka ya kufce mata. Tashi tai da gudu tabar falon zuwa ɗakinta. Ya bita da kallo harta shige. Baki yaɗan taɓe da ɗauke kansa irin ko'a jikinsa ɗin nan.


★★★★★★★★


          A gidan Ummi kam yau anguna sun gwangwaje daren alkairinsu ga matansu. Inda suka samu ƙyaƙyƙyawan sakamako daga tsare kai ga zina. Basu ɓata rayuwar ƴar kowa ba suma ALLAH ya kare matayensu ya basu cikakku nagartattu.

      Kowanne ka kalla a wannan safiyar zaka fahimci ransa fes yake da shiga sabuwar rayuwa. Ita kanta Ummi farin cikin nasu data gani ya sakata a farin ciki itama. Tasan ko basu faɗaba sunga wani abu na daga sakamakon haƙuri.

        Sun so zama da ita su tattauna akan Isma'il tace karsu damu tana kan nazarine game da shi. Suma ta basu dama kowa yaje yay nazari yazo mata da sakamako. Amma kar suyi gaggawar yanke hukunci akan ƙaddara balle fara TAKUN SAƘA da shi game da sirrin da UBANGIJI ne kawai yaso basu haske shiyyasa ya aiko Isma'il ɗin a cikinsu.

     Badan sun so ba sukai shiru. Dan ita ɗin ba abar rainawa bace a garesu.


★★★★★


       Da ga ɓangaren haji Halilu ma dai sai a hankali. Gaba ɗaya ya maida kansa kiɗimammen ƙarfi da yaji. Ga momy na addabar rayuwarsa akan ciwon Junaid. Ta dage sai an kamo Isma'il an miƙa ga hukuma. Hakama su Ummi.

      Ya yarda da nemo Isma'il dan haka ya bama jami'an tsaro dama. Sai dai damuwar itace babu ko hoton Isma'il bakuma su san ɗan inane ba shi ɗin. Gashi su Ummi da za'a iya samun bayanai da ga garesu an memsu an rasa. Dan haka suka saka aka kama baban hafsat da baban Zahidah da Sheikh Aliy akan sunsan ina su Ummi suke tunda ƴaƴansu aka aurama yaƴan Ummin.

       Su kuma an kaɗa dambu da taliya sunce sam basusan ina Ummi take ba. Batun tarewar yara kuwa wani gida suka nuna akan nan aka kai amaren. Sheikh Aliy dai uffan baima ce musu ba. Kwarjininsa kuma da sanin shi ɗin wanene ya hanasu kausasa harshe garesa. Koda akaje gidajen aka duba sai aka samu gidajen da Abban ya kama musu hayane su zauna da ƴaƴansa.

      A take ƴan sanda suka fahimci wani abu su ummin suka ƙulla shiyyasa sukai ɓaddabami. Sai kawai suka duƙufa neman su ummin suma bayan Isma'il.


★★★★


          Suma su A.G tunda suka mikama Master sunaye da accaunt Numbers nasu suka koma gefe suna jiran sakamakon aikin da suka bashi. Yayinda a zahiri suke tsakkiyar manyan mutane masu kishin ƙasa ana ta tattauna ta ina za'a nemo master da tawagarsa. Ɗari bisa ɗari an yarda da su. Saboda yanda suke nuna kishi da taɓarɓarewan tsaron ƙasar da son ganin an hukunta masu irin halin master. Ta ko ina sun kafa tsun tsare sune dai😏😥.


★★★★★★★★


       Tun daga wannan ranar Hibbah ta shiga wasan ɓuya da kowa na gidan. Idan ka cire baba Saude da kan ɗan ganta lokaci-lokaci. Master ya share kamar ma ya manta da lamarinta. Dan gaba ɗaya hankalinsa ya tattarune yanzu akan aikin da yasa gaba. Su kansu su Habib abinda ya janye hankalinau kenan ko zaman gidan basayi yanzun. Dan lokuta da dama ma da ga ita sai baba Saude suke yini a gidan. Sai weekend ne Hibbah tahaɗu da yarinyar da baba Saude ke riƙo wadda tsintarta tai ta rena tun tana jinjira gashi har tana da shekaru biyar yanzun. Sosai Hibbah taji daɗin ganin yarinyar, dan gata ƙyaƙyƙyawa da ita ga wayo. cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu harta manta da wasu ababen halitta su Master a gidan. Sai dai kuma a duk minti cikin bin kwaƙwƙwafin komai take na gidan batare da ko baba saude ta farga ba.

     A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai ga Hibbah da sati biyu a gidan Master. Yau tsahon kwanaki goma sha biyu kenan bata sakashi a idonta ba. Ba kuma ta haɗu da su Zaidu ba, dan suma basa ma kwana a gidan, daga baya ne kuma ta fahimci shima uban gayyar baya kwana a gidan kusan sati guda kenan.


        Yau ma kusan la'asar bayan ta gama sharɓar kukanta ta tashi ta gyara fuskarta ta fito wajen Baba Saude. Zamanta baifi da mintuna goma ba ya shigo falon da sallama ciki-ciki. Sam Hibbah bata wani jisa ba saboda ta maida hankalinta gaba ɗaya wa tv ne. Sai da taji baba Saude ta ce, “A'a babaa barka da dawowa”.

      Saurin juyowa tai jin abinda baba Saude ta faɗa. Dai-dai ya ɗago idanu yana gaishe da baba Saude. Haɗuwar idanun nasu waje guda ya saka Hibbah saurin janye nata ta maida ƙasa. Dan gaba ɗaya ta koma cikin yanayin rashin walwala a ƴan kwanakin nan, shiyyasa duk wani rawan kan nan nata da tsiwa kamar an mata ruquyya a kansu.

     “Ina yini”.

Ta faɗa acan ƙasan maƙoshi batare da tayi tunanin zaima jita ba. Duk da yaji ɗin bai amsa ba. Yana dai cigaba da kallonta dan a kallo guda ya fahimci bata a cikin walwalarta. Cigaba da takowa yay inda suke. Batare da ya janye idanun nasa ba ya ajiye ledar hannunsa a saman centre table tare da janye idanunsa da ga kan ta ya maida ga baba Saude.

       “Baba kuyi haƙuri mun barku gidan shiru”.

     “A'a babu damuwa wlhy babana. Ai da yake inada abokiyar hira dan ma dai kwanakin nan nakega kamar tana da damuwa ne. Ban dai tambayeta ba dan kar na ƙara ɗaga mata hankali”.

      “Karki damu baba baƙunta ke damunta kawai”.

        “Ai yaci ace baƙuntar nan ta tafi babana. Amma zan ƙara dagewa wajen ganin na gusar da ita.”

       Hibbahr ya sake ɗan kalla da janye idanunsa. Batare da yace komai ba ya nufi sama. Sai da ya hau kusan steps biyar sannan ya tanka. “Ki sameni anan”.

    Ya faɗa batare da ya juyo ba.

Ganin bata motsa ba harya gama hayewa ne yasa Baba Saude kallonta. “Muhhibatu tashi kije babana na kira kinji”. Dan ita duk zaton ta ƴana da alaƙa da Hibbahr ne. Tunda ita shaidace a kansu bata taɓa ganinsu da matan banza ba har ƙannen nasa. Dan haka take kyautata masa zato.

        Mikewa Hibbah tai a hankali ta nufi saman hawaye na ciko mata idanu. Babu wanda take muradi da ƙulafucin gani kamar Ummi da su Yaya Muhammad. Tsaye ta samesa a tsakkiyar falon da alama ita yake jira. Ta samu damar ƙarema bayansa kallo tunkan ta ƙaraso saboda da ya juya mata baya. Kaya na masa ƙyau, musamman ƙananun kaya da take ganinsa da su kawai dan bata taɓa ganin yasa manyan kaya irin na hausawa ba. Kullum cikin shigar kananun kaya yake tamkar dangin masu jajayen kunnuwa.

      Jin idanu a kansa ne ya sashi juyowa. Saurin duƙar da kai Hibbah tayi ƙasa. Cikin dakewarsa yace, “Baki iya gaisuwa bane?”.

      “Ina yini?”.

Ta faɗa da sauri kafinma ya rufe baki. Juyawa yay ya karasa ga kujera batare da ya amsa ba. Sai da ya zauna sannan ya ɗago ya dubeta. “Mike damunki?”.

    Yay maganar cikin nuna kulawa duk da fuskarsa a tsuke take babu walwala.

       “Ba komai”.

Ta bashi amsa hawayen da take maƙalewa suna rige-rigen sakkowa a kumatunta. Idanunsa ya janye a kanta yana ɗan furzar na numfashi. “Ummi ko?”.

     Saurin ɗagowa tai ta dubesa. Sai kuma ta fashe masa da kuka tare da durkushewa a inda take. Lip ɗinsa ya ɗan taune da lumshe idanunsa. Sai kuma ya buɗe yana miƙewa. Fridge dake a falon ya nufa. Ya ɗakko gorar ruwa ya dawo inda take durƙushe tana kuka. Mika mata yayi batare da yayi magana ba. Ganin taƙi karɓa ya sashi yin wani ɗan dirƙuso a gabanta. Yatsunsa biyu yasa a kan haɓarta ya ɗago fuskar tata. Babban yatsansa kuma na goge mata hawayen gefe guda yana cigaba da kallon fuskar tata. Ɗayan hannun kuma ya karasa fincike murfin goran ruwan ya kai bakinta. Abinda ya tokare maƙoshinta ne ya sata fara shan ruwan ko zai wuce. Tasha kusan kaso ɗaya bisa uku kafin ta janye kanta. Komai baice mataba ya janye shima tare da mikewa. Ya kai hannu ya kamo nata hanun. Dole ta miƙe tsaye dan kulawar daya batan kawai yasa zuciyarta ɗan yin sanyi taji kamar daya da ga cikin su Yaya Abubakar ne.

     A doguwar kujera ya kaita ya zaunar. Hannun nata ya saki ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Hibbah ta bisa da kallo zuciyarta na ayyano mata wata kamanceceniya data rasa a ina take son gano ta. Ta yi zurfi a tunani barci ya fara fisgar jijiyoyin idonta. Duk yanda taso hana kanta hakan ya gagara. Cikin kanƙanin lokaci jikinta duk ya saki, dole ta zame ta kwanta a kujerar batare data shiryama hakan ba.

      Duk abinda take yana kallonta ta cikin ƙofa. Yana ganin ta zube kwance ya fito. Wata Wadrobe dake a gefe an shirya littatafai a ciki ya nufa. Key ya ɗauka a kasan wani littafi ya saka jikin kwabar sai ga shi ya buɗe alamar ƙofa. Yasa hannu ya juya katakon ƙofa ta bayyana. Dawowa yay ya leƙa kasa. Ya tabbatar baba saude hankalinta baya a wajen sanann ya ɗauka Hibbah gaba dayanta yabi ta ƙofar da tai ƙasa yabi ta barauniyar hanyar data fiddashi ta backyard ɗin gidan. Da sauri Habib da ke tsaye cikin parking space ya buɗe masa ƙofar motar. A bayan ya sata, shima ya shiga. Habib ya zauna a mazaunin driver suka fice a gidan bayan maigadi ya wangale musu gate.............✍


*_Kuyi haƙuri, yau gaba ɗaya na ɗauka Sunday ce ashe monday muke🥲🙏🏻🙌🏻_*



     TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_Chapter Thirty Two_*


..........A ɗan firgice Hibba ta farka da ga gajeran barcin da Master ya sakata na dole. Waige-waige ta shigayi cikin ruɗanin ganinta a sabon waje. Yayinda wani irin tsoro da tsantsar firgici ke bayyana akan fuskarta. “Na shiga uku wa kuma ya kawoni nan?”.

      Ta faɗa muryarta na rawa alamar son yin kuka........

      “Hi aunty queen!”.

Da sauri ta juyo tana kallon Habib mai maganar da maɗaukakin mamaki, sai kuma ta ɗan sauke ajiyar zuciya koba komai taga wanda ta sani, duk da suma ɗin ba wai abin yarda bane.

       “Barka da yamma aunty queen”. Aka sake faɗa ta ɗayan gefenta. Khalid ne yay maganar dan haka ta ɗan hararesa. Ta buɗe baki zatai magana Master ya fito ta wata ƙofa waya manne a kunnensa. Ga kofin baƙin shayi a hannunsa. Baiko kalli kowa a cikinsu ba ya kai zaune bisa kujerar dake kallonsu yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

      Yayinda yake amsa wayar cikin rashin sakewa da ƙasaita. Hararar gefen ido Hibbah tai masa tana gulmarsa a cikin rai. Ta dubi su Habib da suka nutsu a tsaye. “Ni ku bani abinci yunwa nakeji aka satoni nan”.

      Cikin gumtse dariya Khalid yace, “Mi zaki ci to?”.

       “Komai ma”.

   Barin wajen yayi. Babu jimawa sai gashi ya dawo da damammiyar madara da kwalin cornflakes. Yaja ƙaramin stool gabanta yana faɗin, “Gashi auntynmu”.

       Komai batace ba. Sai dai babu musu ta zuba cornflakes ɗin batare data kalli inda Master yake ba, har zata kai baki kuma sai ta dakata. Ta ɗan saci kallonsa tana faɗin, “Khalid inji dai ba'a saka ka barbaɗa wani abun mutuwa ba ko?”.

       Idanu ya ɗan waro waje. “Abin mutuwa kuma Aunty Queen? Wazai saka miki abin mutuwa?”.

       “To na sani, tunda agabana ranar akace a bani maganin feshin ƙwari nasha”.

         Habib da Khalid suka dubi juna suna satar kallon Master daya gama wayar yana daƙilarta ne kawai alamar akwai abinda yakeyi, duk da yana jinsu yayi kamar baisan dasu a wajen ba. Cikin danne abinda ke taso musu Khalid yace, “A'a babu abinda aka saka miki aunty. D......”

        “Zaku wuce abinda ke gabanku ne? Ko zaku zauna surutu?”.

     Ya faɗa batare da ya ɗago ya dubesu ba. Kafinma ya rufe baki sun bar wajen. Hibbah ta taɓe baki da cigaba da shan cornflakes nata dan yunwar takeji da gaske. Cigaba da abinda yakeyi yayi harta kammala bai dubeta ba. Sai da ta mike tana ɗan dafe kai ne ya bita da kallo.

      “Ina ne kitchen?”.

  Ta tambaya cikin kwantar da murya dan ita tayi alƙawarin daina tsiwa har sai ta gano wanene shi.

       Da yatsa ya nuna mata yana miƙewa. Ficewa yay da ga falon yana sake ɗaura wayar a kunnemsa alamar wani kiran yayi. Gaba Hibbah tai itama inda ya nuna mata. Bata wani jima ba ta fito tana gyara hijjab ɗin jikinta da batasan ta yanda akai ta sakashi ba, balle inda ta samoshi. Sake komawa tai kan doguwar kujerar ta kwanta ranta fal tunanin dalilin da yasa aka kawota nan ɗin kuma?. Harga ALLAH hatsabibancinsa na bata mamaki. Mutum ne da sam baka taɓa gane ina ya dosa balle manufarsa. A ɗan zaman da tai da su sosai ta fahimci wasu halaye na mutanen kirki tattare da shi. Sai hakan ke yawan raba mata hankali daga ɗabi'unsa na zahiri da kowa ya sani. (Zan dai sake nutsuwa na fahimci guy ɗin nan).

     Ta ayyana a zuciyarta cikin yarda da kai. Cigaba tai da tunane-tunanenta har ta fara jiyo hayaniyar su Adam da batasan ta ina suka fita ba. Jin hayaniyar tasu na cigaba da tashi sama-sama ya sata miƙewa dan zaman shirun baya mata daɗi, ga jikinta duk babu ƙarfi kanta kuma na mata ciwo kaɗan-kaɗan. Ta riga ta saba da baba Saude acan da Sharifat. Duk da ba sanin ko'ina tai ba haka ta fito compound inda take jiyosu. Girman gidan ya bata matuƙar mamaki, an wadatashi kuma da abubuwa kai kace ba a cikin gurguwar ƙasarnan tamu bane ba.

       Tsaye tai tana kallon su Habib da ke faman buga basket ball. Haka kawai taji wani nishaɗi har fuskarta na bayyana murmushi. Ta shagala sosai a kallonsu ta hango wata ƙyaƙyƙyawar mage na fitowa da ga ɗakin maigadi. Tana son mage, tsoronta da yaya Usman keyi a gida ya saka Ummi ta hanata ajiyewa. Magen ta nufa tana faɗin, “Woow Cutie”. Tai maganar tana kaiwa duƙe ta ɗauka magen.

       Master da ke kallonta da ga can inda yake ta gaban ruwan da aka ƙawata na swimming pool ya ɗan yamutse fuska ganin ta ɗaga magen ta rungume a jikinta tana murmushi tamkar ta samu ɗa. Sam shi bai wani damu da mage ba amma ba tsoronta yake ba, baya son dai sam ta taɓa masa jiki. Ɗauke kansa yay ya cigaba da  danna wayarsa.

      Hibbah ba lura da Master tayi ba, dan haka ta cigaba da hidimarta da mage cikin nishaɗi. Lokaci-lokaci takan ɗaga kai ta kalli su Salis. Wani ɗan zare ta ɗauka tana ɗagawa sama magen na tsalle zata kamo. Hakan yasaka Hibbah ƙyalƙyalewa da dariya tana tafiya da baya-baya magen na binta da son kama zaren.

     Tana gab da isa inda Master yake Idris ya farga. Zungurin Musbahu da ke kusa da shi yayi. Musbahu ya ɗan waro ido dan ganin abinda ke shirin faruwa. Yay saurin ɗaga hannu zai fargar da Hibbah da ke gab da zuwa inda Master yake Idris ya rufe masa baki.

        “Kai malam waye ya saka. Barta dan ALLAH, wlhy ni so nake babban yaya ya amsheta matsayin matar gaske bawai ta wucin gadi ba. Dan sun matuƙar dacewa.”

     Musbahu da ya gamsu da bayanin Idris ya jinjina kansa yana janye hannunsa. “Ashe bani kaɗai nake da fatan nan ba.”

    “Sosai kuwa”

Cewar Idris cikin bada tabbaci.

            A ɓangaren Hibbah kam gab take da kaiwa ga Master da gaba ɗaya hankalinsa nakan wayar dan abu mai muhimmanci yakeyi a ciki. Khalid da sai yanzu idanunsa ya kai shima ya ɗan zaro ido. Da sauri ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Aunty Queen bayanki”.

       Tsorata Hibbah tayi, dan duk zatonta wani abun cutarwa ne, musamman ganin yanda Khalid ɗin yayi maganar. Tai ƙoƙarin juyawa da sauri sai dai ta rigada tazo gab da shi, ga magen ta ɗane ƙafarta saboda kama zaren da tasamu damar yi. Uban tsalle ta doka da ƴar ƙarar tsoratan data fargar da Master. Cikin zafin nama ya riƙo hannunta ganin tayi baya zata kai ƙasa, sai ko gata gaba ɗaya a kansa.

       Hawar masa ƙafa da magen tayi ne shima ya sakashi saurin ɗaga ƙafarsa, ga Hibbah ɗare-ɗare a cinyarsa. Yanda yayi ɗinne kuma ya sake firgitata ta duƙunƙunesa gaba ɗaya har yana sakin wayarsa a ƙasa babu shiri. Cikin sauri su Idris suka shiga jan hannun juna suna barin wajen ransu fari tas..

     Master ya sake rumtse idanunsa da ƙarfi jin yanda Hibbah keta sake cusa kanta a ƙirjinsa da dabaibayesa. Ga mage da kamar ance ta nane musu sai tsale-tsallenta take. Dole ya miƙe gaba ɗayansa dan bayason magen na taɓa masa jiki. Hibbah ta fasa ƙara da son sake ruƙosa jin zata faɗi ƙasa, sai dai abisa tsautsayi ta riga tayi baya da yawa, idan kuma takai ƙasa tabbas zata cutu. Magen ya yakice a jikinsa yana ƙoƙarin kai ɗayan hannunsa ya riƙo nata ganin gaba ɗayanta zata sulmiya cikin ruwan ne.

     Maimakon ta riƙe hannun sai ta damƙe rigarsa gaba ɗayansu suka antaya a cikin ruwan ji kake tanjamm😬😱. 

 

           Yanda ruwan ya bada ƙara yasa su Habib fitowa kusan duk a guje sukayo wajen pool ɗin har maigadi. Sam Master bai iya ruwa ba. Hasalima bai cika son ganin babban ruwa ba, kona swimming pool ɗin idan ya zauna wajen saboda son sanyi baya yarda yay masa kallon daya haura sakanni yake ɗauke ido. Idanko damina tazo duk wani rashin jinsa nutsuwa yake saboda rashin sakewa, ko yaya ruwa ya dakesa sai yaji a jikinsa dan sai yayi ciwo.

      Hankalin su Habib ya tashi saboda sanin bai iya ruwaba. Gashi basu da damar cewa zasu shiga ruwan saboda Hibbah dake tare da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci Master ya shaƙi ruwa, sai dai kuma ƙoƙarin son ceto Hibbah yake a zatonsa bata iya ruwanba itama. Duk yanda yaso hakan ta kasance ya gagara, dan harya fara galabaita. Hibbah kuwa tanata ƙoƙarin ganin taje gaɓa dan itama dai bawai ta iya swimming ɗin bane ba, amma ta fisa dan ta kuɓutar da kanta batare data fita hayyacinta ba. Ruɗewar data lura su Zaidu sunyi ne ya sata saurin waigawa bayanta tana ƙoƙarin sharce ruwan fuskarta. Idanu ta zaro matuƙa, dan Master harya fara yin ƙasa.

       Da sauri ta koma bayan inda yake. Tasa hannu ta toshe hancinta tai ƙasa wai zata ɗagosa. Ina yafi ƙarfinta, amma tsabar ƙarfin hali tanata kici-kici cikin rawar jiki na tsoro, dan ta fahimci bai iya ruwa ba. Da ƙyar ta samu da taimakon su Habib data miƙoma hannunsa suka kama ta ɗagoshi, sai faman cije baki take dan ya mata nauyi a jiki, tana turawa suna ja har suka ɗagosa gaba ɗaya.

         Ganin kamar bashi da rai yasa Hibbah fashe musu da kuka, dan gaba ɗaya kanta ta bama laifin. Ruɗewar da tai yasata fara danna ƙirjinsa kamar yanda taga Musbahu nayi. Amma babu alamar ruwan daya shaƙa zai fita.

      Adam yay saurin faɗin, “Aunty Queen taimakon gaggawa ta baki Please”.

           Ruɗewa ta sakata ranƙwafawa kansa ta ɗaura bakinta kan nasa, yayinda ta toshe masa hanci da yatsunta biyu, bada wani tunani ba ta shiga bashi taimakon gaggawa. Ganin taja numfashinsa na farko babu wani alama yasata jawowa a karo na biyu da iya ƙarfinta tana matse ido.

          Gaba dayansa ya yunƙuro saboda tahowar numfashinsa mai haɗe da tari da ruwan daya shaƙa. Hannayensa duk biyu sukai sama, tana ƙoƙarin dagowa ya sake rungumota ta dawo kan ƙirjinsa. Tsam ya matseta yana cigaba da tarin ruwan daya shaƙa na fita.

      Nannauyar ajiyar zuciya su Khalid duka shiga saukewa na godiya ga ALLAH. dan da gaske sun shiga tashin hankali. Sai mutsu-mutsu Hibbah take nason ƙwace jikinta amma ta kasa koda motsi. Sai da tarin ya lafa masa ne ya ɗan janye hanun daya dabaibayeta yana buɗe idanu da ƙyar. Cikin sauri ta miƙe a kansa duk kunya da takaici sun dabaibayeta. Ya ɗan kalleta ya maida idanunsa da sukai jaa ya lumshe.

        Ganin ya saki Hibbahr su Salis da duk sukai ƙasa da kai tunda ya kawo numfashi duk sukayo kansa. Sune suka taimaka masa ya tashi zaune. Zasu kamashi ya mike ya girgiza musu kai alamar zai iya. Baya duk sukaja. Shi kuma yabi Hibbah dake jike da ruwa ta nufi hanyar falo da sassarfa da kallo. Mikewa yay da ƙyar yana dafe kansa da ke juya masa. Shima ya nufi falon su Habib suka take masa baya sunata jera masa sannu. Har cikin ransu kuma ganin laifinsu suke dan sun bada gudunmawa a wannan accident ɗin.

       A falon suka iske Hibbah sai rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa. Duk tausayi ta basu, tayi tsumu-tsumu tamkar an tsamo ɓera a ruwa😹👐🏻. Shi kansa ta bashi tausayi, duk da bayajin ƙarfin nasa jikin shima gabanta ya ƙarasa. Babu zato Hibbah da duk kunya ta dabaibaye saboda yanda kayan suka manne mata a jiki sai ji kawai tai anyi sama da ita.

          Da sauri ta harɗo hannayenta a wuyansa saboda wani Masifaffen  kunya daya rufeta tashi a karo na farko tun zuwanta gidansa. Ta tura kanta akan ƙirjinsa da riga ta manne shima yanata ɗigar da ruwa.

        Ƙin ɗagowa tai har sai da taji ya direta ta ɗan buɗe ido. Da sauri ta kalla inda ya kawotan shima ta kallesa. kafin ta ɗaga baki tai magana ya kammala dai-daita ruwan ɗumin ya saki ruwan shower ɗin ya sauka a kansu. Wani irin bahagon ajiyar zuciya Hibbah ta saki jin ruwan akansu. Ta rumtse idanunta da sauri tana juya masa baya ganin zai cire riga abinsa hankali kwance.

          Juyawar tatace ta bashi damar cire duka kayan jikinsa ya bar boxer kawai ruwan na ratsa masa jiki kozai samu nutsuwar abinda yakeji na ƙutsa masa cikin ƙashi. Sai da yaji ya ɗan fara samun nutsuwa ne ya kashe gaba ɗaya, batare da yace komaiba yaja bathrobe ya saka. Tun kafin ya fita a toilet ɗin ya fara sakin atishawa a jajjere.

      Ajiyar zuciya Hibbah ta kuma saki jin ya rufe mata ƙofar hawaye na gangaro mata. Gaba ɗaya kallon komai take tamkar a mafarki yau itace a banɗaki daya da namiji.

       Jin sanyin na neman dawo mata a jikine ya sata zuwa ta sama ƙofar key ta fara zame nata kayan. Dan dole ne idan tana bukatar zaman lafiya tayi yanda ruwan zai ratsata ta kuma rabu da kayan gaba ɗaya. Hatta da gashin kanta ji take kamar ta kwashe ta yar.

         Sai da taji tamkar fatarta zata ɗaye dan saukar ruwan dumin nan sannan ta kashe tana sauke numfashi da atishawa itama. Towel ya rage a toilet ɗin gashi guntu, bata da zaɓin daya wuce ɗauka ta sakama jikinta, ta sake jan karami ta naɗe kanta tana sakin atishawa da kallon facemask ɗin daya cire a fuskarsa. mask ɗin ta ɗauka tana jin takaicin kanta na juyawar da tai da tabbas saita ga face nashi yau. Jin atishawa zata halakata ya sata ajiyewa ta matse kayan data cire da nasa. Gefe kuma tana tunanin yanda za'ai ta fita a toilet ɗin da guntun towel ɗin?.


       A ɓangaren Master kam rawar sanyi sosai yakeyi, da kyar ya iya daukar wani mask ɗin ya saka a face nashi. Gadon ɗakin dake a gyare ya haye yaja bargo ya rufa yana sakin atishawa da rawar ɗari.

         Hibbah da taji kamar babu motsinsa ta ɗan leƙo kanta. Babu kowa a ɗakin dan haka tai tunanin ya fita dan bata farga da gadon ba. Sai da ta fito tsakkiyar ɗakin ya saki wasu tagwayen atishawa. Da sauri ta duba kan gadon saita ga a lulluɓe yake. Ajiyar zuciya ta sauke da saurin nufar Wadrobe ɗin ɗakin duk da bata tunanin samun kaya. Cikin sa'a taci karo da kayansa. Cikin sauri taja jallabiyar data fara gani ta zura  a jikinta duk da ta mata yawa sosai. Tanayi tana juyawa ta dubesa wai ko zai kalleta.


★★


     Da ga can falo su Habib nata kai kawon dafa masa ruwan zafi mai kayan kamshi, dan sun tabbatar a yanzu shine yafi bukata bisa taimakon farko. Su duka bakwai sun haɗu a kitchen ɗin abin tausayi da dariya. A haka dai suka haɗa Habib ya ɗakko ya nufo ɗakin nasa. Sai da yay sallama da knocking Hibbah ta amsa sannan ya shigo. Ganin yanda har yanzu a ruɗe yake ya bama Hibbah mamaki. Ta bisa da kallo lokacin da yake kaiwa durƙushe a gaban gadon saitin kan Master. A marairaice yake kiransa kamar zai saki kuka.

     Master dake jinsa ya buɗe ido da ƙyar tare da kai hannu ya ɗan ja bargon daga saman kansa. Sosai idanunsa sukai wani irin kaɗawa jazur, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu dan ma mask ya tare abin tausayi da tsoro. Sosai gaban Hibbah ya faɗi ganin cikin kanƙanin lokaci ya fita hayyacinsa. Batare da Hibbah ta sani ba tuni ta karaso gabansu itama har rigar na neman harɗeta zata faɗi ta dai dafe gado.

         Shayin Habib ya miƙa masa kamar zaiyi kuka. Da ƙyar Master ya mike ya jingina da fuskar gadon sai atishawa yake akai-akai. Habib ya zuba shayin a muq ya mika masa. Amsa yay babu musu yana matse idanu dan yasan shine kawai abinda zai taimakeshi a halin yanzun. Sai dai maimakon ya kai baki sai ya miƙawa Hibbah yana mata nuni data zaune a gefen gadon.

        A yanayin da yake ne yasata kasa musa masa, dan ita sam bawai ta shiga wani hali bane, shi kansa ta fahimci kamar dai yanada wani ciwone da baya buƙatar shiga ruwa, musamman wannan da yay sanyi sosai, ko kuma halittarsace hakan. Gashi shi kuma ya shagesa da yawa. (Dama akwai mazan da basu iya ruwa ba?). Ta faɗa a zuciyarta tana satar kallonsa ta gefen ido.

      Wani shayin Habib ya sake zubawa ya miƙa masa, amsa yay. Habib dake kallonsa cikin damuwa yace, “Salis yaje gida ya ɗakko maka kaya masu kauri. Akwai abinda kake buƙata bayan shayin?”.

        Ƙasa yay da idanunsa ya ɗan kalli shayin ya ɗago ya duba agogon dake ɗakin. Ganin lokacin sallar magrib ma yayi sai ya girgiza masa kai kawai.

      “Kuje kuyi salla”.

Yay maganar a hankali miryarsa harta canja launi tamkar ba shi ba.

            Sannu Habib ya sake masa yana mikewa. ya dubi Hibbah da yake fatan ita babu komai da ga gareta. “Aunty ke bakijin komai ko?”.

      Batare da Hibbah ta kallesa ba ta girgiza masa kai. “Alhmdllhi” Habib ɗin ya faɗa da nufar ƙofar fita. Shuru ɗakin ya ɗauka kamar babu kowa, ita dai Hibbah kanta a ƙasa zuciyarta na wasuwasi da saƙe-saƙen mike damunsa haka daga shiga ruwan da kwata-kwata basu gaza 30minutes ba a ciki? Dan gaba ɗaya yanda ya birkice ɗin zaka fahimci akwai damuwa da yake fuskanta game da hakan. To amma kuma a koda yaushe ai cikin warware ac yake kamar goyon larabawa shi baya masa illa kamar haka kenan? Kuma yana wanka, Kenan shima duk basa masa illah?.

      Oho shi dai Master baima san tanayi ba. Dan shayin yake sha cike da dauriya, amma lokaci-lokaci yakan ɗan kalleta ya janye idonsa. Duk da alamu ya nuna yanajin sanyi sosai haka ya miƙe dan shan shayin ma ya ɗan bashi nutsuwa. Bayan ya buɗe wadrobe ya ɗauka kaya toilet ya nufa yayo alwala da ruwan zafi sosai ya canjo kaya. Gaba ɗaya yanda yake jinsa bazai iya fita massallaci ba, dan haka yay ma Hibbah nuni alamar taje tayo alwala.

       Haka kawai ta tsinta kanta dajin nauyinsa. Dan haka babu musu ta mike tana faman naɗe rigarsa. Batai tunanin jiranta zaiyi zaman yi ba sai da ta fito ta gansa a zaune ya rufa da bargo idonsa a rumtse. Sai atishawa da yake cigaba da jerawa. Motsinta ya sakashi buɗe idon, ya miƙe batare da yayi magana ba yana tunanin abinda zata rufa tai sallar.....

     Sallamar Salis ce ta sakashi sauke ajiyar zuciya. Hibbah ta amsa ganin shi muryar tasa tayi ƙasa. Itace ta bama Salis ɗin damar shigowa. Sai ko gashi da sabuwar sallama ɗauke da leda babba. Ya ajiye yanama Master daya koma bakin gadon ya zauna sannu. Kai ya jinjina masa kawai tare da miƙa hannu ya amshi ledar da faɗin, “Kaje kai salla”.

     Cikin girmamawa Salis ya amsa. shi kuma ya buɗe ledar sai ga Hijjab da kayan Hibbah a sama. Hijjab ɗin ya miƙa mata yana mikewa. Amsa tayi ta saka. A karan farko ya ja musu sallar magrib, koda suka idar ran Hibbah fal mamakin jin yanda yake karatun sallar cikin nutsuwa da tabbatar da ashi ɗin yanada ilimin addini.

    Bai wani samu nutsuwar addu'a ba ya miƙe dan jikinsa sai rawar sanyi yake. Ledan da Salis ya kawo ya buɗe, ya fiddo safa ya saka a ƙafarsa ya sake hayewa gadon yaja bargo. Sai dai kafin yakai kwance Habib yay sallama ɗauke da ruwan ɗumi. Yanzunma Hibbah ta amsa masa, ya shigo idonsa akan Yayansa da ya tabbatar yana cikin wani hali, sai dai shi mutumne mai juriya shiyyasa ba'a cika ganowa ba,  amma yasan yana da raki idan yana ciwo kuma. Dan in yana ciwo koma musu yake kamar shine karamin sune manyan tsabar rakinsa, kai kace ba Master bane maiba su A.G ciwon kai da jami'an tsaro da manyan ƙasa😂.

       Ita dai Hibbah tana gama shan maganin da Habib ɗin ya bata ta mike tana faɗin, “Habib wane ɗaki zan zauna?”.

      Habib da yasan gidan bawasu ɗakuna bane kuma ga halin da Master ke ciki na bukatar wani a kusa, dama idan yana ciwo shine ke zama tare da shi, tunda kuma gata yana ganin ai an wuce wajen. Mastern da yay kamar baisan sunai ba ya kalla. Ganin yanzun ma bashi da alamar cewa komai yasa Habib cewa, “Anan zaki zauna gidan babu ɗakuna sosai, sannan yana bukatar wani a kusa da shi, kiyi haƙuri ki zauna anan doctor na zuwa dubashi”.

       Ta buɗe baki zatai magana. Yay ma Habib alamar yaje. Babu musu ya juya ya fita. Fuska ta ɓata sai dai babu damar yin magana. Komai baice mata ba shima yaja bargo ya sake rufe har saman kansa. Tamkar Hibbah zata fasa kuka ta cigaba da zama a saman abin sallar har lokacin isha'i, a ranta tana tunanin ita tayaya ma zata iya zama da shi a ɗaki guda. Batai zaton zai tashi sallar ba sai gashi ya miƙe da alama ma ba barcin yakeba daman. Yanzun ma shine ya ja musu sallar isha'i kowa yay shafa'i da wutirinsa. Gadon ya sake komawa ya kwanta, baifi mintuna biyarba Habib yazo da doctor. Wani farin dattijone mai cike da kamala. Gaishesa tai ta cigaba da kallon yanda taga yana tarairayar master ɗin. Sai faɗa yake masa a tausashe akan shiga ruwa da yay bayan yasan minene matsalar jikinsa da ruwan sanyi da kuma rashin iya ruwa.

        Shi dai Master komai baice ba sai wani langabewa yake. Doctor yay masa allura yana faɗin, “Kaga yanzu babu abinda kafi buƙata daga dakatawar wannan rawar sanyi kamar ɗumin jikin mutum. Gashi kaƙi aure Shuraim. Last daka samu irin wannan matsalar Habib ne ya baka ɗumin jikinsa lokacin bai kai haka girma ba. Amma ni yanzu bansan yanda za'ai ba”.

         “Doctor Ibrahim mutumin kirkine kuma ɗan amanarsu. Wanda suke kallo tamkar uba a yanzu, duk da ya musu nisa saboda bai cika zama ba. Shiɗin ɗan uwa ne ga baba wanda ya taimaki mamynsu kuma ya riƙesu. tunda Mastar na yaro shine yake kula da issue ɗin ciwon nasa na rashin son ruwan sanyi da likitoci da yawa suka tabbatar masa yanada alaƙa da jininsa ne. Sam jikinsa baya son ruwan sanyi, shiyyasa ya kasance ko alwala zaiyi sai da ruwan ɗumi, amma kuma yana son sanyin ac duk da shima yakan bashi wahala wasu lokutan.

        “Uncle ai yayi aure fa”.

Habib ya faɗa a hankali yana satar kallon Master. Cike da mamaki Doctor ya kalli Master ɗin dake kallon Habib cikin alamar waya tambayeka”.

      “Shuraim da gaake ne?”.

Doctor yay tambayar yana raba hankalinsa biyu na kallon Master da Hibbah. Kai kawai Master ya ɗaga masa, sai kuma ya motsa baki a hankali yace, “Haka abin yazo babu shirine Uncle”.

      Daɗi ne ya kama doctor Ibrahim. Ya shiga sakama Master albarka da Hibbah, dan shi da da farko harya fara zargin ko master ya fara neman mata ne duk da yaga Hibbah ƙaramar yarinyace. To amma yanda zamani ya sauya komaima zai iya faruwa. Ya nuna farin cikinsa sosai, tare da yi musu addu'ar zaman lafiya da zuri'a mai albarka. Da ga ƙarshe yay ma Hibbah bayanin yanda zata kula da shan maganin master ɗin tare da bashi ɗumin jikinta.

     Ita gaba ɗaya ma tabar fahimtar yaren da yake magana. Saurarensa kawai takeyi da kunne. A ganinta tayaya zata bashi ɗumin jikinta tunda ba jini bane balle a ɗiba?. Harya gama ya miƙe zai wuce bata dawo hayyacinta ba. Sai da Habib ya kirata da ɗan ƙarfi sannan ta ɗago ta kallesa. “Uncle ne ke miki sallama”.

         Cikin sanyin murya taima Uncle Ibrahim ɗin godiya dan itama sanyin ruwan zuwa yanzu ya fara tasiri a jikinta na alamar saukar mura. Shi dai ficewa yay yana murmushi. Master da tuni ya koma cikin bargo ya kwanta dai yana saurarensu sama-sama. Koda suka fice kuma baicema Hibban komai ba har Habib ya dawo.

     Tattare syringe ɗin da akai masa allurar yayi yana faɗin. “Aunty Queen mizaki ci ne?”.

     Kanta ta girgiza masa alamar babu. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Yay mata sai da safe yana ficewa abinsa. Idanu Hibbah ta rumtse da ƙarfi dan itafa babu yanda za'ai ta kwana ɗaki guda da namiji. Dan haka ta cigaba da zama a wajen tana yan tunane-tunanenta. Sai atishawa da Master keta faman yi akai-akai batare da tasan idonsa biyu ba ko barci yakeyi.

      Ta jima a wajen zaune har batasan adadin awannin data ɗauka ba. Sai gyangyaɗi take dan barci takeji ga sanyi itama tanaji dan ma tasha maganin da Habib ya bata na mura itama. Tashi tai cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ta fito, babu shiri tai saurin komawa ciki ganin falon dunɗum da duhu, ga ko'ina tsitt alamar su Adam sun kwanta suma. Ta jingina da ƙofar zuciyarta na wani dif-dif. Ganin tsaiwar bazata mataba yasa ta dawo saman abin salla ta kwanta. Wani mugun sanyi taji yana kaɗata. Ta sake mikewa kamar zata fasa kuka tana harar gadon. Bazata iya kwanciya a saman tiles ɗin nan ba gaskiya, kuma harga ALLAH barci takeson yi dan maganin murar ya fara aiki. Zuwa tai ta kashe fitilar ɗakin, cikin sanɗa tazo ta hau gadon a ɗosane taɗan ɗaga bargon ta shiga zuciyarta na addu'ar ALLAH yasa karya farka har sai ta fara tashi. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barci yay awon gaba da ita.

       Master da barcin ya kasa ɗaukarsa sai rawar ɗari yake duk yana jinta............✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 

*_Chapter Thirty Three_*


...........Can cikin dare Hibbah tai ɗan juyi cikin barci, da sauri ta sake mirginowa baya jin zata faɗa ƙasa. Gaba ɗaya ta manta a inda take ma. Ƙara bajewa tai jinta yanda takeso. Hakan sai ya sake bata damar matsawa jikin Master da har yanzu baiyi barci ba saboda zazzaɓi da jikinsa ya ɗauka mai zafin gaske.

       Jin yanda ta matsosa har tana janye masa bargo ne ya sakashi ɗan buɗe idanunsa, hannu ya kai zai gyara bargon sai yaji ta duƙunƙunesa a jikinta, ya cija lip ɗinsa kamar ya mangareta, dan wannan shine karonsa na farko a rayuwa da yake kwance tare da mace a gado ɗaya. Ya ɗanja bargon da ƙarfi, Hibbah da batasan mi ake ba ta biyo bargon gaba ɗayanta ta shige jikinsa. Zafin zazzaɓinsa ya sata sake matsawa sosai dan ɗumin ya mata daɗi kasancewar itama har yanzu tana ɗan jin sanyi.

     Saurin jan numfashi da rumtse idonsa yayi da ƙarfi. Babu shiri yakai hannu zai janyeta ta sake dabaibayesa har dayin filo da damtsen hannunsa. Ta sakala hanunta ta gefen cikinsa. Wani irin harbawa da ƙirjinsa yayine ya sakashi matseta babu shiri yana datse leɓansa cikin haƙora kai kace zai hudasu ne.

       Ƴar ƙara Hibbah ta saki tana ƙoƙarin janye jikinta cikin lalube. Ina ta rigada tazo hannu, dan wani ƙara matseta yayi da ƙyau. Cikin rawar sanyi dana harshe ya ce, “Please ”. A hankali cikin kunnenta.

       Kanta ta shiga jujjuya masa duk da kuwa a cikin duhu suke. Jikinta sai tsuma yake najin sabon al'amari ga rayuwarta. Bata sake tsurewa ba sai da ya tattaro jallabiyarsa dake jikinta yay sama da ita alamar zai cire dan ta rage masa wasu kaso na ɗumin jikin nata da yafi buƙata a yanzu. Duk da kuwa shima jikin nasa tsumar yake na shiga sabon yanayi akaf tarihin rayuwarsa. Rashin ƙarfin jiki da ciyo ya haddasa masa baisa tafi ƙarfinsa ba. Dan cikin ƙanƙanin lokaci ya zare rigar ya barta yanda Ummi ta sulmiyita duniya. Kuka ta fashe masa da shi tana yunƙurin tashi. Yasa hannu ya kuma matseta, cikin muryar ciwo da rakinsa ya fara magana a cikin kunnenta.

        “Baki da tausayi ko?, kina son kiga na mutu. Please Muhibbat 30minutes kawai...”

      Sake firgicewa Hibbah tayi dan bata taɓa jin makamanciyar muryar daga garesa ba. Gaba ɗaya ya tashi mata da ga Master data sani mai mazurai da tsare gida ya koma mata wani daban. Harga ALLAH tanajin tausayinsa, sai dai ayanda suken akwai tashin hankali da tsoron kar wani abu ya faru, dan sarai tasan minene aure, tunda tanada iliminta dai-dai gwargwado. Ɗan karatun nan na littafi tana taɓawa a waya, ga kawaye a gefe.......

         “Ina jin tsoro Yaya Master, dan ALLAH kar kaimin komai”. Ta faɗa cikin suɓutar baki.

       Duk da halin ciwo da yake ciki maganarta sai da ta saka wani lallausan murmushi subuce masa. Ya tura yatsun hannunsa cikin sumar kanta tare dayo ƙasa da kansa yasa goshinsa akan nata. Hancinsu na gogar na juna. Cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa yace, “Ashe Tanee ɗin Ummi tasan minene aure?”.

         Kanta ta shiga ja baya tana faɗin, “Ni wlhy A'a, dan ALLAH ka bari”. Yanda ta ƙare maganar hawaye na rige-rigen sakko mata a kumatu ya sashi sake yin murmushi da har taji sautin fitarsa a maƙoshinsa. A gefen zuciyarsa kuma yana sake yarda da tarbiyyarta, dan yanda ta ruɗe zai tabbatar maka bata taɓa tsintar kanta a yanayinba. “Relax!, Yaya master ba ɗan iska bane bazaiyi komai ba ga ƙanwar nan tasa mai bakin akku himyim??”.

        Baki ta tura gaba duk da a cikin duhu suke. Ta sake ƙoƙarin ja baya ya sake matseta a jikinsa da har yanzu yake tsumar sanyi. Duk yanda taso ya barta hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda badan taso ba. Sai dai yanda zuciyarta keta faman harbawa da sauri-sauri zai baka tabbacin haƙurin na dole ne kawai, ta riga tazo hannu babu mafita. Itama a ɓangarenta tana jiyo sautin motsin da zuciyarsa keyi a cikin ƙirjinsa. Har abin na bata mamaki da tsoro. Dukansu sunyi shiru kowa na sauraren na ɗan uwansa. A hankali barci ya fara fisgar Hibbah, dan yanda yake ɗan motsa yatsun hannunsa da har yanzu suke a cikin gashinta tanaji kamar yana mata susa ne.

     Cikin ƙanƙanin lokaci Master ya farajin numfashinta na sauka a hankali jikinta na saki alamar barcin yaci ƙarfinta. Bakinsa ya matsar bisa goshinta ya sumbata da sake turata a jikinsa sosai yana maijin nutsuwa da wani yanki na guntun damuwarsa na sauka. Yayinda wata sassanyar ajiyar zuciya ke sauka a hankali. Sai gashi barcin da ya kasa tun ɗazun na fisgarsa yayinda jikinsa ke ƙara ɗaukar zafi.


        Barcin da basu sami yi da wuri ba ya sakasu makara da asuba. Dan sai wajen bakwai saura Master ya farka. Har yanzu jikinsa da zazzaɓi bai gama sauka gaba ɗaya ba. Ga idanunsa sun ƙara girma na alamar mura ta tabbata. A hankali ya buɗe idonsa saboda nauyin da kansa yay masa. Akan Hibbah dake lafe a jikinsa ya saukesu. Barcinta take hankali kwance, gashin kanta daya warware dukya baje akan filon da fuskarta. Bakin da baya barin saita kwana yake kallo, idanunsa ya sake lumshewa da buɗewa a kanta lokaci guda. kafin ya saka yatsunsa yana janye mata gashin daya sakko mata akan fuska. Taɓa rumfar idonta da yatsansa yayi a mistake ya sata farkawa. Idanunta ta buɗe itama a hankali dan tama manta a inda take. Akan fuskar boginsa ta sauke, wadda inba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba tashin bace. Wani zabura tai babu shiri tai azamar juya baya zuciyarta kamar zata wantsalo ta fito. “Innalillahi....” ta faɗa tana rumtse idanunta da ƙanƙame bargo da ƙarfi.

      Uffan baice mata ba, sai ma mikewa yay zaune yana dafe kansa da yay masa nauyi. Kafin ya miƙe gaba ɗayansa ya nufi toilet da alamun har yanzu jikinsa babu ƙarfi. Yana shigewa Hibbah ta miƙe zaune da nufin guduwa tabar ɗakin sai ta ganta salin alin. Bama tasan sanda ta daddage ta fasa ƙara ba da maida bargon ta rufe jikinta.

        Cikin sauri Master ya fito a zatonsa wani abune ya sameta. Yay saurin yaye bargon data ƙudundune a ciki, wata sabuwar ƙarar ta sake fasa masa da saurin faɗawa jikinsa ta duƙunƙunesa ita a dole batason yaga jikinta. Babu shiri wata dariya ta nema kufce masa. Dan ya fahimci abinda takema wannan kwakwazon. Sai dai yay ƙoƙarin danne dariyar ya dafe kansa da hannu ɗaya. Sanin su Habib na a cikin gidan yasashi fara mata magana a Master ɗinsa babu wasa. “ALLAH idan baki rufemin bakin nan ba a safiyarnan zan canjaki”.

        Duk da magana yay ta hikima kuka Hibbah ta fashe masa da shi. “Ni wlhy bazan yarda ba. ni ba ƴar iska bace ka maidani wajen Ummi na. Ummina tace karna sake namiji ya tabamin jiki, amma kai har ganina kayi, nashiga ukuna ni Muhibbat bazan yafe ba.”

      Ɗagota yay gaba ɗayanta ya maida ya zaunar, tai azamar lalubo bargo ta sake duƙunkunewa tana kuka wiwi. Harara ya zuba mata, cikin ɗan faɗa-faɗa yace, “Ohhh! To ni Mamyna tace na bari mace ta taɓamin jikine mai Ummi. Koni na gayyatoki bisa gadona? Idan wannan bakin baimin shiru ba anan na rantse sai na haɗiyesa”.

     Ya ƙare maganar yana matsota da dungure mata kai. Babu shiri tasa bargon ta toshe bakinta hawaye na sakkowa. Sake zuba mata harar yayi da jan siririn tsaki yana miƙewa. “Sai shegen tsiwa ga tsoro”. Ya faɗa yana nufar toilet.

      Sake fashewa da kuka Hibbah tai da komawa ta kwanta tana jan bargon har saman kanta. “Ni wlhy ban yafe ba kwarto kawai”.

       Karaf a kunnen Master dake fitowa a bayi alamar alwalar daya fara ihunta ya fiddosa yaje ya sako. Kobi takanta baiyiba dan kansa ciwo yake ya kabbara salla. Harya idar bata tashi ba. “Zaki tashi kiyi salla ko saina hawo gadon?”.

        Ya faɗa a yanda yasan dole zataji tsoro. aiko zumbur ta miƙe, ta ƙudundune bargon har kanta tana sauka a gadon da gudu tai toilet. Saurin riƙota yay, dan yasan tana shiga da bargon toilet ya gama yawo. “K miyasa sam mai bai wadaci kanki ba?”. Yay maganar fuska a tsuke. Jikinta taso fisgewa ya zuba mata ranƙwashi tare da fisgota ta dawo jikinsa. Zata fashe masa da kuka yace, “Karma ki soma”.

     Dolenta ta haɗiyesa kuwa. Jallabiyar sa daya cire mata jiya da daddare ya ɗakko mata. Yana ajiyewa a kan gadon ya juya ya fice a ɗakin yana danne dariyar dake taso masa. Raka bayansa tai da harara kafin taja jallabiyar ta saka. Koda ta shiga toilet ɗin saita yanke shawarar yin wanka. A gurguje tai wankan tayo alwala ta fito.

        Salla ta fara gabatarwa kafin ta kimtsa cikin kayan da aka kawo mata.   Har lokacin master bai dawo ɗakin ba. Dan haka ta fara gyara ɗakin. Tana gab da kammalawa Habib yazo yay kiranta. Sai da ta saka Hijjab sannan ta fito tana ta faman ɓata fuska. Duk zaune ta samesu a dining har uban gayyar daya canja kaya alamar yay wanka a inda bata sani ba. A kallo ɗaya zaka fahimci baida lafiya. dan idanunsa jajur suke ga wata ƙatuwar rigar sanyi daya ɗora. Gaisuwar da su Musbahu sukai mata ta amsa cikin ƙara ɓata fuska tana hararsu. Su dai murmushi kawai sukai dan babu damar magana boss na a wajen. Habib yaja mata kujerar kusa da Master dake karyawa, koda suka fito baiko ɗago ya kallesu ba abincinsa yake tsakura fuska a ɗaure, dan sam baya masa daɗi saboda mura. Dan ma yasa sun masa mai ɗan yaji da kayan ƙamshi ne.

       “Nifa na ƙoshi”.

Ta faɗa kanta a ƙasa dan gani take kamar duk suna kallon abinda ya faru jiya da daddare a fuskar tata. A karon farko ya ɗago ya kalleta da jajayen idanunsa. Babu shiri takai zaune dan kallo ne na gargaɗi da babu alamar wasa a cikinsa. Kofi ya ɗauka da kansa ya haɗa mata shayi tare da zuba mata soyayyan doyan ya tura gabanta. Kallon juna su Habib sukayi cike da iya shegensu. Adam ya dafe saitin zuciyarsa yana wani lumshe ido irin dai ƙauna takai ƙauna kenan.

      Hibbah kam kamar zatai kuka murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Dan ALLAH a rage yamin yawa”.

      Bai ma nuna yajita ba, balle tasaka ran zai karɓi ƙorafinta. Sai ƙaramin bowl ɗin daya sha farfesun ya ture yana warwarar tissue ya goge bakinsa. Baya ya ɗanyi da kujerar yana ɗaukar wayarsa yabar dining ɗin. Su Idris na ganin haka sukai azamar cigaba da cin abincinsu dan sunsan yau akwai aiki tunda basu sami damar yi a daren jiyan ba saboda abinda ya faru. Ɓata lokaci kuma yana nufin amsar hukunci a wajen babban yaya.

       Khalid ne da yaga Hibbah na tsakurar abincin yace, “Aunty Queen ALLAH ki maza dan yana kallonki”. Hararsa tai tana tusa doya cikin baki. “To shikenan ashe da rabon ai miki ɗura ko”.

     Cokali ta ɗauka zata jefesa yay saurin mikewa yana dariya sauran ma na tayasa. Tashinsu a dining ɗin ya bata damar cigaba da cin abincin, sai dai kunnenta na jiyo mata bayanin da yake musu wanda bata fahimta ba cikin muryarsa da ke tabbatar da mura ta shakesa bana wasa ba. Har ya gama jawabinsa duk suka mike bata kammala ba. Sai da Habib ya fito yana sanar mata tayi maza ta kammala ita yake jira sannan ta mike. Ganin yana tattara kwanikan ta tayasa suka kai kitchen. Fitowarsu yayi dai-dai da fitowar su Salis cikin sabon shiri. Da kallon mamaki ta bisu ganin kowanne ya canja kamanni zuwa na daban. Zatai magana Master ya fito, dole ta haɗiye tata ta dauke kanta dan bata son koda wasa su haɗa ido.

       Cikin dakewarsa da ƙasaita ya fara magana cike da gargaɗi. “Ku kula, komai kanƙantar matsala ku sanar dani. Khalid kai da Salis zaku tafi a napep. Idris da Musbahu ku hau mashina. Idan komai ya dai-daita ku sanar dani muma zamu taho. Musbahu ka tabbatar duk layin da zaka shiga ya zamto mai tsayi ne, kamar na masu amsar ATM ko Customers care ”.

       “Insha ALLAH sir”.

Musbahu ya amsa cike da girmamawa. Kallonsu kawai Hibbah take tamkar ta samu television. Mamaki bai nema halakataba sai da taga sunkai zaune a falo sunyi addu'a nema nasara ga UBANGIJI kafin su Salis duk su fice a barta ita da sauran sai shi. Batare da ya kallesu ba yace. “Ku kuma ku biyo ni”

_______________________________


          ☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠

*_K'AMSHI,K'AMSHI RAHAMA NE MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA SU SUKA SAN MUHIMMANCIN DA K'AMSHI YAKE DASHI MUSAMMAN A WAJAN MAI GIDA ,_*💃🏻💃🏻

*_Zafafan turarruka masu zazzafan k'amshi hade da wasu irin manyan sirrika na mallaka cikin sauki ba boka ba malam hajiya , Zaki jefe tsuntsu biyu da dutse d'aya , domin zamowa star azuciyar mijinki_*🌟🌟🔥


*_nasan dai kunada labarin mashahuriyar Mai Saida kayan k'amshin Nan Wanda akafi sani da *HUMKAM GIDAN K'AMSHI* *_a wannan karon ma ta sake kawo maku da sabbin kayanta masu abun al'ajabi Wanda da kud'i k'alilan zaku more zafafan turarruka Kuma ki shiga jerin Mata masu aji_*


*IDAN SARI KIKE BUKATA INA BADAWA SANNAN INAGYARAN JIKI CIKI DA WAJE SHIN KINA FAMA DA INFECTION INA HADA MAGANIN SA DA IZININ ALLAH KISHA KI WARKE*

*Kadan daga cikin kayan da muke dasu*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻


*BLACK KAJII*

shin kina bukatar turaren da Zaki turara gidanki ya dauke maki warin sanyi ya kwana biyu Yana k'amshi ,?ki saye black kajiji Zaki Gane banbancinsa da sauran wannan ba k'amshi kawai yake ba idan kina turara. Jiki dashi Yana maki maganin kala kala ciki kuwa har da na sanyi , nemi naki Kar ayi Babu ke☀️🟢☀️🟠🌟08132506044 HUMKAMINCENSE


*ANA WA HABIBY* Wannan harkan na oza room ne special turare Dan matan aure kadai yana dauke da abubuwa Wanda bazan fadesu anan ba sannan bashi kadai bane akwai Crazy powder da na ke hadawa dashi zakisha garin sannan kishafa turaren hmm


*SUDANESE HUMRA* Turare dake dauke da sirrika Mai DAUKAR hankali kamshin ya banbanta da sauran turare Hajiya babbar sirrine Wannan hadin manyan Mata  08132506044 HUMKAMINCENSE


*GLOWING OIL*

Wannan yasha bam bam da irin Wanda kuka Saba gani ,Yana kashe kuraje Yana cire tabo Yana maganin kezbi da duk wani matsalan fata ,stretch marks duk Yana ciresu ....


*MOWAR MACE*

turaren mowar mace turare ne da larabawa suke amfani dashi Wanda da yawa mutanenmu Basu San da wannan iccen ba Mai dauke da magani k'amshi da sauran abubuwan masu matukar amfani ga fata ba

Shi wannan iccen yanasa hasken fata yanasa fata tayi laushi da santsi sannan d'an alk'awari ne matuk'ar kina amfani dashi zai tsirga maki cikin fata ta yadda ko Bakiyi amfani dashi ba zakiji k'amshin shi na fita  ta cikin fatar ki ,ke amfanin iccen mowar mace yanada yawa jaraba ko don gyaran fatarki , 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Muna gyaran jiki na amarya da uwargida zakizo har gida ayi maki gyaran jiki irin na Mata masu aji zakiyi kyau kiyi fresh ga kamshin da zai Kama jikinki💃🏻💃🏻💃🏻


Munada 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*JAS OUD* (hatsabibin turare kenan )


*AL'AJAB* ( Mai abun mamaki kenan )AL'AJAB Turaren tsuguno mai abubuwan Al'ajabi  Yana maganin sanyi (infection) Yana matse HQ (Tightening)sosai 08132506044 yasa HQ dumi yasa jikinki da hq kamshi lokacin da kike AMFANI dashi idan Yana shiga gabanki zakiji wani Dadi na ratsaki Yana k'ara Dadi da Yana ciko gaba ya rikita oga🙈


*FIRST LADY*   na Mata masu aji turaren Kaya Dana daki

HAWII

KAJIJI

HALUT

👸🏻 *_PRINCESS_*

_Sabon turare Dana hada na shafawa ajiki da gashi *PRINCESS* Yana da Dadi cool kamshi gare shi babu hayaniya na fad'a muku sabbin turaruka na Nan tafe princess na daya daga ciki kisayi *PRINCESS* kiji sabon Hadi me sanyin kamshi babu kosarwa da ace zan iya zabi tabbas zan zabi princess a matsayin turaren gashina zan dauki princess ya zama shi zan farawa shafawa jikina idan zan kwanta zan dauki *PRINCESS* sbd yara na Dan kamshi bamai hayaniya bane musamman zan rika yi musu amfani dashi *PRINCESS* salon na daban kamshin daban dadin na daban *PRINCESS*  Zabin ku ne Zabin Humkam shine farin cikin ku Masoya *PRINCESS* gidan kowa_


Duk wad'an Nan turarruka ne hatsabibai masu rikita mazaje masu wani irin k'amshi Mai shiga zuciyar masoya 💃🏻💃🏻💃🏻


*SHU'UMAR HUMRA*

ke daga jin sunan kinsan ta dabance mashahuriyar humra ce ta tayi shuhura wajan birkita tunanin Yan maza , humra ce da indai namiji yajita a jikinki to komai muskilancinshi sai ya susuce maki tana tado da sha'awa shauk'i sirrin mallaka, cikin kankanin lokaci ki rikita maigidanki da daddadan k'amshin ki😍😍😍🥰


*HUMKAM GIDAN K'AMSHI INA NAN ZAUNE A KANO GA MASU BUK'ATAR ZAFAFAN KAYANA INA AIKAWA KOWANE GARI DAKE NIGERIA HAR MA DA K'ASASHEN K'ETARE , KARKU MANTA A DADE ANAYI SAI GASKIYA* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


________________________________

    

      Duk mikewa sukai sukabi bayansa. Ganin Hibbah batako motsaba Habib yay mata alamar ta taho. Da ga can table ɗin da aka ajiye computers suka nufa. Kowa ya zauna ɗaya Hibbah dai na tsaye. jerarrun atishawa ya saki a cikin tissue ɗin daya warwara kafin ya dubeta da idanunsa dake jazur. “K zauna nan”.

     Yay maganar yana nuna mata kujerar dake kusa da inda yake tsaye. Idanu taɗan waro waje zatai magana ya tsatstsareta da nashi cikin gargaɗi. Tarasa miyasa take jin yau gaba ɗaya bazata iya masa tsiwa ba. Haka kawai wani irin shegen kwarjini yay mata ga kunyarsa da takeji matuƙa. Zuwa tai ta zauna a kujerar da ya ɗan ja mata baya.

          “Zaidu! Ka tabbatar ka dakatar da number Alhajin Mande daga shigar kira ko fita na tsahon awa guda shi da A.G. Adam! Accaunt na Engineer da Dr Sufi ka karasa aikinka na jiya a kansu, duk sauran kuɗaɗen dake a sauran bankunansu ka maida kuɗin a accaunt ɗinsa da na baka. Zakuyi da sauri. dan su Salis na gab da kaiwa, a yanzu haka suna cikin holdup ne”. Ya ƙare maganar idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hannunsa alamar tanan yake bibiyarsu.

         Gaba ɗaya Hibbah tama rasa kalar tunanin da zatai, dan duk sun wani daburta mata ƙwaƙwalwa. Taja numfashi da sauri jin ya ranƙwafo ta bayansa, tare da ziro duka hannayensa biyu ta gefe da gefenta ya dafe table ɗin. A sarƙe taja numfashi tsigar jikinta na tashi, “Zaki fara aikinki da ga yanzun madam”.

         Yanda yay maganar a hankali saitin kunenta ne ya sata ɗan janye kanta, sai hakan ya bata damar jingina da kafaɗarsa ta gefen haggu, da sauri ta sake gyara zamanta a yanda take tana cigaba da shaƙar mayen turarensa dajin hucin zazzaɓinsa. Master da ke daƙilar keyboard ɗin Computern gabanta ya cigaba da mata bayanin abinda zatayi da nuna mata.

       “Shi aikin akan minene?”.

Ta faɗa cikin rawar murya.

“Babu ruwanki da ko na minene. Ke dai kiyi kawai”. Yay maganar yana ɗaukar hannunta ya ɗaura bisa mouse ɗin. Yatsansa manuniya ya ɗaura akan nata dake dai-dai kan ƴar tayar tsakkiyar mouse ɗin. Tai ƙoƙarin janyewa ya matse hannun. “Ki nutsu bana son shirme fa ok!".

         “Amma ai ya kamata a sanarmin aikin kafin nayi”.

     “Ashe baki son komawa wajen Ummi kuwa”.

     Amsar tasace ta sata sake ƙwaɓe fuska tamkar zata fasa ihu. Ga a yanda suke duk kunya ya dabaibayeta. Badan kujera data shiga tsakanin bayanta da ƙirjinsa ba a yanda suken tamkar ya rungumeta ne. Sai da ya gama nuna mata duk yanda yake bukatar tayi kafin ya janye jikinsa da ga nata. Wani wawuyan ajiyar zuciya ta saki lokacin da yake mikewa. Har sai da su Habib suka ɗan kalleta. Dan tunda ya duƙo kanta basu sake yarda sun kalli sashen da suke ba. Wata ajiyar zuciyar ta sake saki ganin ya nufi hanyar bedroom ɗin da suka kwana. Badan yace idan ta ƙiyi bazai kaita wajen Ummi ba da tabbas bazatayi ɗin ba, amma tana buƙatar ganin ahalinta zata iya komai dominsu. Kusan mintuna goma sha uku da shigarsa sai gashi ya fito. Badan ta tabbatar da bayan shi ɗin babu wanda ya shiga ɗakin ba da babu yanda za'ai ta yarda shine. Ya canja kayansa zuwa manyan kaya irin na tsoffin dattijan Alhazan kauyen nan harda rawani, ga uban farin sajen da ke akan sabuwar fuskar daya canzo sak wani dattijon ƙwarai irin wanda basuko damu da duniya ba. Sai sanda a hannunsa da dogon carbi. Hannunsa kansa sun canja da ga nasa zuwa kalar fuskar zam. Ya zaro ƴar karamar wayar nokia ɗin data sha wani shegen farin salatap da har ya fara komawa brown dan tsufa. Kunnensa ya kai alamar kira ya amsa. Yana sauke wayar a kunne yana duban su Adam da suka mike.

      “Done”.

Suka faɗa a tare shi da Zaidu. Kai ya jinjina musu yana maida dubansa ga Habib. “Ka kula da komai, abinda bata gane ba ka nuna mata, aikinta ne na tsakkiya samun matsala daga gareta yana nufin komai zai ɓaci”.

      Kai Habib ya jinjina masa da faɗin, “Insha ALLAH mune da nasara. ALLAH ya dawo daku lafiya”.

     Amin ya faɗa yana duban ɗakin da su Zaidu suka nufa, sai kuma ya kalli agogon hanunsa irin na sarƙa ɗin nan da yaci duniya ya koɗe matuƙa duk da Silver ne dama. Dai-dai nan su Zaidu suka fito da sauri cikin sabuwar shiga suma. Daka kalli Adam bashi da maraba da driver. Zaidu kam tamkar irin yaran alhazan kauyen nan da bakinsu bai rabo da tsugudidi. Ga jikka ya riƙe wadda ko ba'a faɗaba kasan ta alaramma Muhammad Shuraim Master ce dai.

     “Ga kuɗin an shirya Master”.

Zaidu ya faɗa yana buɗe jakkar hannun nasa mai kama da karamin akwatin maza na tafiya. Shiryayyun kuɗi ne a ciki ƴan ɗari biyar-biyar da ɗari bibbiyu. Kai ya jinjina masa kawai alamar komai yayi.

      Inhar ana mutuwa a zaune to yau dai da alama Hibbah ta mutu. Dan harsu Master suka fice a falon bata gama dawowa hayyacinta ba sai da Habib ya fargar da ita. Cikin alamar ruɗani tace, “Ina zasuje wai?”.

    Murmushi Habib yayi yana ɗan matso da kujerarsa kusa da tata kaɗan. “Aiki zasuje mana.”

      “Aiki?”.

Hibbah ta faɗa cikin sigar tambaya. “Babu lokacin tambaya aunty Queen mu cigaba da namu aikin dan mune tamkar ƴan jagorarsu. “Gaskiya indai satar kudaɗen mutanene bazanyi ba”.

    Tai maganar tana ƙoƙarin mikewa. Kamar daga sama taji muryarsa yana faɗin, “Ashe kuwa ke da Ummi har abada. Na kuma gama aiki nace yayunki sukayisa”.

    Waige-waige ta shigayi cikin falon sai dai babu alamarsa. Sautin muryar tasane kawai data kasa fahimtar da ga ina yake fitowa. Kuka ta fashe dashi tana komawa ta zauna a kujerar. Lallai ta tabbatar yau tana a tsaka mai wuya. Abinda takeji a labari yau shi hannunta zai aikata.

      “Kuka bazaiyi magani ba aunty Queen, duk wani motsinki dake anan tamkar akan idonsa ne garama kiyi kawai".

     Habib yay maganar cike da lallashi. Kamar ta makesa shima takeji, shiyyasa taki tanka masa ta cigaba da abinda takeyi zuciyarta na kawo mata wani shawara acan gefe. Yarda da shawaran yasata share hawayenta ta maida hankalinta ga aiki kamar yanda Habib ke nuna mata shima yanayi.


      A ɓangaren Master kuwa sun isa banki a tsohuwar motar da Adam ya tuƙasu. Adam ne ya taimaka masa ya fito a motar shi a dole ga dattijon da yaci duniya jiki yay laushi. Yana gaba Zaidu na biye da shi yana zuga surutu da kyalƙyala dariya irin dai garorin nan yan bani na iya na gefen alhaji. Shiko Master sai wani gaftarar goro yake yana ƴar dariya da bama Zaidun amsar wasu zantukan nasa.

     Gaba ɗaya kallon garori securitys ɗin bank ɗin sukai musu. Bayan an dubasu babu alamar wani abun ashha tare da su aka basu damar shiga. Yanda Zaidu ke zabga surutu Master na dariya yasa mafi yawan mutanen dake akan layin tura kuɗi da amsa kallonsu, wasu na musu dariya wasu na musu kallon ƙauyawa ne. Master dake lure da motsin kowa ya yafito wani gaye da ya tsuƙe cikin shigar manyan yara yanata bada iska. “Yaro yaka nan ka taimakeni, dan wannan mai bakin kamar bututun mai yanda bansan a ba shima ba bihim ya sani ba. Garama ni nayi yaki da jahilci lokacin da nake zuwa sarin atamfofi na manta wasu abubuwanne kawai.

     Gayen da gaba ɗaya ya gama ƙiyastama ransa tsuntsu da ga sama gasashshe ya karaso yana wani taɓe baki. Wata cimirmiɗaɗɗiyar takarda Master ya fiddo a aljihu ya mikama gayen. “Yarona duba mini nan, ƴan kuɗaɗena na kayan amfanin gona dana noma na sayar zan buɗe akawun na zuba. Nima jikana dake can kudu ya bani shawara amma yace na nema wannan daya rubuta min anan zai taimaka mini aimin komai na buɗe akawun din na zuba kuɗaɗena a ciki naje gida nai barci babu ruwana da takadarai”.

     A karon farko gayen ya dashare baki da faɗin, “Ai babu damuwa baba koni ma na maka. Kaga zomuje can sama acan ake buɗewa.”

    Babu musu Master ya amince. Suka nufi saman bene Zaidu na biye da su. Gaye da gaba ɗaya hankalinsa nakan jakar hannun Zaidu ya sami ma'aikaci guda sukayi magana. Form aka basu da zasu cike suka koma can gefe inda babu yawan mutane.

     A ɓangaren master tun shigowarsu wajen yaga Musbahu, shima kuma ya gansa dan cike da ƙwarewa sukaima juna alama da ido. Kafin Master ya ɗauka ƴar nokia ɗinsa ya fara magana da ƙarfi har hankalin mutane na dawowa kansa. Wasu na dariya wasu na tsaki wasu taɓe baki. Dan kuwa dai garanci zam Master ke zubawa abinsa Zaidu na tayasa cikin kwakwazo shima.

     Da wannan damar gaye yay amfani wajen saƙala hannunsa a hankali ta ƙasan teble ya zuge jakkar hannun Zaidu. Rafar yan dari biyar ya jawo har sau uku ya tura aljihu, yayinda a gefe tuni Zaidu ya sane wayar gaye daya ajiye akan table shi kuma. A dai-dai nan Musbahu yazo a ɗan fusace yana faɗin, “Haba baba dan ALLAH kake magana a hankali mana. Nan fa ba ƙauye bane ko gida cikin banki ne”.

      Cire wayar Master yay a kunne yana zabgama Musbahu dakuwa. “Kaci gidanku dan bantan ubanka. Anki ayi a hankalin idan lahirace nan ɗin jefani a wuta. Mara mutunci takadarin banza.”

     Yanda Master ke masifar yasa mutane fara bashi hakuri da nunama Musbahu kuskurensa na kodan furfurar Master ɗin ya kamata ai ya tauna harshensa yay masa magana ta hankali. Yayinda wasu kejin daɗin abinda Musbahun yayi. Ga Zaidu da tuni ya zurama Musbahu wayar gayen nan a aljihu yana nunashi da dan yatsa alamar bama ogansa kariya. Yanda suke abun baka isa tunanin suna da wata alaƙa ba. Musbahu ya fice a wajen a fusace saboda securitys da sukazo suka tasashi gaba. Yayinda suke bama Master dake matsar kwalla haƙuri.

     Sai da wajen ya samu nutsuwa Gayen nan ya cigaba da cikema Master form yana tambayarsa. Yayinda Master ke amsa masa cikin raba hankalinsa. Dan nokia ɗinsa yake ta dannawa wai yana neman lambar jikansa daya sakashi zuwa ya buɗe akawun..........


    Anan bangaren Hibbah kam aiki take yanda Habib ya nuna mata hankalinta na ga ɗakin da suka kwana. Habib na cewa su ɗan dakata ta miƙe wai zatayo fitsari. Ɗakin ta shiga ta maida key ta kulle ranta fal farin ciki, dan tayi alƙawarin saita buɗema su Master aikin da suka tafi yi. Wadrobe ta nufa ta fiddo wayar da taga ya ajiye a ciki yau da safe, cikin sa'a kuwa ta ganta. Koda ta ɗakko a kashe take, cikin rawar jiki ta kunnata sai ko gata ta kawo. Wani ɗan tsalle ta buga zuciyarta na mata canki in canka akan wayarwa zata fara kira ne. (Ta yan sanda) zuciyarta ta bata tabbaci. lambobi da yaya Abubakar ya taɓa sanar mata cewar na taimakon gaggawane da ga hukumarsu ta loda a wayar, cikin sa'a tanayin dialing kuwa ta shiga😱..............✍


(Hibbah😬😬😬🙆🏻🤦🏻).


        *_Kuyi haƙuri na zama sai a hankali sa kun haɗa da addu"a_*



TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 


*_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


______________________


*_Chapter Thirty Four_*


...........Harta yanke ba'a ɗaga ba, sai dai da ga ƙarshe ake sanar mata ta dakata ana amsa wasu kiraye-kirayen ne. Bakin gado taje ta zauna tana sauraren a ɗaga ɗin, dan an saka taken ƙasa ne domin kar a bar mai jira shiru. Kusan mintuna uku ba'a amsa mata ba taji haushi ta yanke. Tagumi ta rafka ranta zattakaici, taci alwashi duk ma yanda za'ai a yau ɗin nan sai tayi sanadin da za'a kama Master da su Halilu. Bazata yarda ta kira yaya Abubakar ba dan gudun kar'a sake irin na farkon kaita wajen ƴan sanda.

 

       ★★★★


     A ɓangaren su Master kuwa koda Musbahu ya fita sai ya koma can gefe. Da wayar gayen nan da Zaidu ya sano musu yay amfani, sai da ya tabbatar yayi duk wani abunda bazai saka rayuwar gayen a haɗari ba sannan ya ƙaddamar da shirinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci shi da Master dake can ana cike masa form yana danna waya da subaɗi suka shiga wawasar kuɗaɗe. Yayinda acan kuma su Salis suma suke kaddamar da nasu shirin akan sauran asusan. Dan yau aikine ba'akan mutum ɗaya ba. Kusan asusu goma sha zasu yashe a ƙiyasi.

          Master na gab da tatse kuɗaɗen asusai uku daya haɗa gabansa yay wata irin faɗuwa. Addu'a yay saurin karantowa zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Cikin sauri ya dubi Zaidu.

      “Ba'are anya kuwa baƙaƙen shanun gidan ɗan sandamu basu shirin kaima gonata ta yammaci hari? Inaji a jikina maƙwafcina ya samu damar yimin ƙafar angulu kuwa”.

        Kai tsaye Zaidu ya fahimci zaurencen, dan haka ya ɗan kallesa a ɗan firgice. “Alhaji Baba wanne maƙwafcin a ciki? Mati mai igiya ko sambo?”.

       “Bansan waye a cikiba ba'are, sai dai zuciyata na min zargin Mati mai igiya ne dan nayi kuskuren ajiye wayar lantarkin nan da za'aimin wayarin wuta a kogon ɓaure. A lokacin Kuma Mati na cikin gonata zai bani taimakon ruwa saboda zafin ranar da akai jiya. Inhar hasashena yayi dai-dai akan idonsa na ajiye wayar lantarkinnan. Ɗakko tarho ɗinka ka kira min ɗan ƙane ka shaida masa ya leƙa gonata ya bincikamin waya a cikin kogon ɓaure, sannan ya sanar maka Mati mai igiya yana kan tudune koya tashi?”.

       “An gama alhajin ALLAH”.

Zaidu da duk jikinsa ke tsuma ya faɗa yana nufar hanyar fita daga cikin bankin. Waya master ya ɗaga yay kira. Ana dagawa ya fara magana cikin wani zaurancen. “Sallau kun gama tattare harawar nan kuwa?”.

       Gaban Salis dake gab da kammala nasa aikin ya faɗi. Cikin ɗan waige-waige ya bashi amsa da faɗin, “Muna gab dai”.

       “To maza kuwa ku tattare dan Mati mai igiya ina tabbatar da ya turo baƙaƙen shanun ɗan sandamu cikin gonar yamma. Da alama kuma zasuyi ɓarna bawai a gonata kawai ba harda ta maƙota. Kuyi himmar tafiya gonar yamman harda su Kalla ku tasamin ƙeyar mati kafin shanunsa su iso ya koma gabashi. Ni kuma zan kira maigari na tabbatar masa tsiyar da matin ke shirin tafkawa”.


     Lokacin da Master ke wannan ƙoƙarin na fargar da yaransa halin da ake ciki a dai-dai lokacin Hibbah ta sake kiran wayar. Kuma cikin sa'a aka dauka mata. Jikinta har rawa yake jin an amsa. Daga can aka tabbatar mata ta kira wayar taimakon gaggawane daga police station mai lamba talatin da uku a anguwar andu dake jihar. Wane taimako take buƙata.

       “Babu taimakon da nake bukata, ina dai tabbatar muku a yanzu haka gawurtaccen barawon nan da yaransa na kan hanyarsu ta wawasar kuɗaɗen wasu mutane ta banki. Nima satoni yayi yanzu haka sun barni anan gidanne sun wuce”.

      “What!?”.

Aka faɗa daga can ana mikewa. “Ƴammata minene sunan anguwar da kike yanzu haka?”.

       “Nima ban sani ba yallabai. sai dai ku bibiyi wannan kiran nasan zaku dace. Dan a yanzu haka suna gab da dawowa na tabbatar”.

     


★★★


      *_Bank_*


       Cikin jin haushi gaye yace, “Nikam Baba kodai baka shirya buɗe accaunt ɗin nan bane na kama gabana? Inada abunyi fa na zauna taimakonka amma sai wani kiran waya kake akan wata wayar lantarki ɗin banza ne ko harawa ma oho maka”.

         “Kai ja'iri waccan harawar tanada mahimmacin da tafi wannan buɗe akawun ɗin. Kaga nama fasa buɗewar sai wani satin zanzo da jikana muzo tare.”

     Master yay maganar yana mikewa. A take mutane suka shiga bashi haƙuri da wasu ma'aikatan bankin, amma fafir yaƙi dan gab aikinsa yake da kammala shiyyasama ya tsaya yana biye musu. Kuɗin daya wawasa na kammala shiga accaunt ɗinsa wani irin jiniya ya fara a cikin bankin. Yanda abin yazoma mutane a bazatane ya tsoratasu bankin ya hargitse aka fara fita a guje. Tuni master yabi rububi ya fice bayan ya cire babbar rigarsa da mask ɗin fuskarsa ya yarda, da sandarsa da carbi. Securitys da ma'aikatan bank ɗin da sukasan minene ma'anar jiniyar dan an sakatane saboda tsaro dama hankalinsu yay masifar tashi. dan fara ƙaɗawar jiniyar yayi dai-dai da fitar maƙudan kuɗaɗe a cikin wasu asusai biyar na manyan mutane dake bank ɗin. Ƙoƙarin hana mutane ake fita ta ƙarfin tsiya, yayinda daga cikin bank har sun kira jami'an tsaro.

     Master na fitowa ya sake cire dayar mask ɗin face ɗinsa ya yarda, dan zuwa yanzu zuciyarsa ta gama bashi Hibbah ta ɓallo musu ruwan da yafi na bankin tsauri. Sam baiyi tunanin taga sanda ya ajiye wayar nan ba. Babbar damuwar wayace da sam babu wani tsaro tare da ita sai idan tana a kashe. Dan yana amfani da itane wajen yin magana dasu A.G, ya tabbatar inhar ta kunnata ko tai kiran wani cikin sauƙi zasu gano inda take musamman da ya san saƙon da ya aika na wawashe musu kuɗaɗe zuwa yanzu ya isa garesu. Hankulansu yana a tashe ne, tare da tsintar kansu ckin ruɗanin yanda akai reshe ya juye da mujiya.


★★★★


              Kamar yanda Master yay hasashe hakance ta kasance. Dan kuwa aikinsu na cika dukkanin wayoyin su A.G saƙwanin alerts na fitar kuɗi suka fara shiga musu. Duk da a mabanbanta wajeje suke kusan a lokaci ɗaya duk suka miƙe zumbur a cikin matuƙar ruɗani da tashin hankali kowa na tambayar mike faruwa? Yaya haka?. Zukatansu na jera musu waɗan nan tambayoyin suna ƙoƙarin kiran juna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fahimci cewar ɗan zakin da suke tunanin sun raina ya girma. Dama a kwanakin nan babu abinda sukeyi sai zaman meeting akan Master. Dan zukatansu na raya musu lallai akwai abinda yake shiryawa shiyyasa yaƙi basu kuɗaɗen da ake tarawa tsahon shekaru biyu. Sun yankema kansu shawarar yana kammala musu aikin nan da suka bashi zasu ruftashi kawai. Sai gashi shi ya fara rufta rayuwarsu alamar shirinsa daɗaɗɗe ne a kansu.

     A.G ne ya saka bibiyar masa number master ɗin duk da basu da tabbacin samu, ana tsaka da bibiyarne batare da an samu ɗin ba Hibbah ta kunna wayar, cikin hanzari jami'in da ke zaune a computer room ɗin nasu yana aiki akan number ya sanarma A.G. shine ya bashi damar yin azamar saita layin akan duk kiran da za'ai ya shigo wayarsune, sannan ya bibiyi a inda lambar take. Shi kuma ya fita yana bada umarnin a haɗa runduna za'a fita operation na gaggawa. Yana dawowa computers room ɗin ya samu Hibbah na zuba bayani ta waya, kuma komai akan kunnensa shima ta zayyane.

      

         A ɓangaren Abba shi kuwa sai da aka fara lasa masa zumane, dukannin kuɗaɗen dake a asusun mahaifin su Hibbah sai da aka juyesu a asusun sa. Farin ciki ya sakashi kaiwa duƙe yay sujida (irin mufa mun fara tsoron ALLAH ɗin nan). A lokacin duk yaransa na zagaye da shi dan an sallamo Junaid ne yau da ga asibiti duk da bawai ya warke bane ba. Gaba ɗayansu galala sukai suna kallonsa. Ameera tace, “Abbah halan yau wani ya maka kyautane? Dan inba kuɗi ba banga abinda zai sakaka wannan rawar jikin ba harda su salla babu alwala babu kallon gabas?”.

      Farin cikin da yake a cikine ya hanashi tanka mata, sai baki da ya sake washewa yana nufar hanyar bedroom ɗinsa cikin ɗunbin farin ciki. Sai kuma ya dawo da baya domin ɗaukar babbar wayarsa da nufin turama Master kuɗin tukuyci kafin yaji farashin sauran na aiki. Dan ya saka a ransa ko nawane Master ya nema sai ya bashi harma da ƙari. Yana ƙoƙarin ma Master transfer ɗin dubu ɗari biyar na tukuyci wasu sabbin alerts ɗin suka fara rige-rigen shigowa. A zatonsa wasu kuɗinne suka shigo dan haka ya buɗe da zumuɗi.

      “Wayyyyiiiihuuuuuu!!!!! Ni Halilu na mutu!”.

     Ya faɗa a matsanancin firgici har sai da su hajiya mama suka toshe kunnuwa suna miƙewa tsaye a matuƙar firgice ganin Abba ya yanke jiki ya faɗi a wajen wayoyin duk sunyi gefe.


★★★★★


     Abinda ke a kunnensa ya danna lokacin da yake shiga motar da sukazo yabar wajen, dan tuni su Zaidu sun ware. “Habib ka ɗauki yarinyarnan yanzun nan kubar gidan nan, ka tabbatar kafin ku wuce ka kashe wayar hannunta ka cire sim card ɗin ciki kayi flushing ɗinsa. Ga su Zaidu nan isowa. Kubi ta cikin store ɗin kitchen akwai hanyar da zata fiddaku ta wancan layin.”

     Sosai hankalin Habib ya tashi, dan yanzun nan dama ya kama Hibbah da waya. Yana tsaka da tambayarta ne kiran master ya shigo masa. Wayar ya fusge daga hanunta a fusace ya takata bayan ya fashe. murfin ya ɓalle da kyar, ɗan pin ɗin dake jikin blackboard ɗin inda computers ɗin suke ya ɗauka ya cire sim card ɗin ya karya. Yay azamar danna wani abu a jikin teble ɗin yay ƙasa.

    Baki Hibbah ta taɓe dan a ganinta kafin ya gama duk wannan abun da master yace ta tabbatar ƴan sanda sunzo. Ranta fes yau ALLAH yayi dubun masu aikata saɓon ALLAH ya cika.

       Dawowar Habib yayi dai-dai da shigowar su Salis kusan a tare. Gaba ɗaya firgice suke. Jakunkunansu suka shiga ɗakin da suke kwana suka tattaro. Habib ya fisgi hanun Hibbah da duk abinda suke tana tsayene kamar dogariya tana kallonsu. Sai faman taɓe baki take irin ko'a jikinta ɗin nan. Hannun ta fige tana ture Habib, a dai-dai na Master ya shigo falon shima.

      “Ku tafii!!!”.

Ya faɗa da ƙarfi jin jiniyar ƴan sanda na gabato anguwar. Yay maganar yana nuna musu hanyar kitchen, kallo ɗaya zakai masa kai kanka ka firgita dan gaba ɗaya ya rikiɗe tamkar wani bajimin zaki. Kobi takan Hibbah da tsawarsa ta firgita baibi ba. Ya nufi ɗakin da suka kwana cikin zafin nama. Mintun uku tsakani ya dawo falon, wanda yay dai-dai da ƙarasowar ƴan sandan ƙofar gidan. Ga kuma Hibbah data nufi hanyar waje da gudu. Baya ya take mata shima. Sabon tashin hankalin daya yunƙuro masa ne yasashi fisgo Hibbah cikin zafin nama ya yarfa mata wani shegen mari mai azabar zafi da saida jinta da ganinta suka gushe na wucin gadi. Ya kama kunnenta ya murɗe da shegen karfi yana magana cikin matuƙar hasala da hargowar da bata taɓa gani tare da shi ba. “Stupid girl!!, idan ni baki kasheni ba, ke da hannunki da wannan shegen taurin kan naki zaki kashe ahalinki”. Wani irin rawa jikinta ya fara hawaye na mata ambaliya akan fuska. Ya turata ta zube ƙasa dan ji yake kamar yay mata bugun mutuwa kozai huce daga abinda yakeji a halin yanzun. Sake miƙewa tai da gudu, Fitowarsu compound ɗin gidan yayi dai-dai da shigowar ƴan sandan cikin gidan.

        “Ku buɗe musu wuta gaba daya!!!”.

     A.G ya faɗa da ƙarfi.

        A razane wani a ciki ya bashi amsa da cewar, “Oga yarinyarfa data bamu information akai gata tare da shi”.

       “Har ita ku haɗa”.

A.G ya faɗa cikin karaji. Ba ƙaramin firgita Hibbah tayi ba. Ta waiga ta dubi Master take biyota ta kalli ƴan sandan da suka saita bindugu akansu da alamun cika umarnin ogansu zasuyi ta rumtse idanu da ƙarfi wasu zafafan hawayen nadama da dana sani na sakko mata. Ita data bada bayani akansa amma jami'in tsaron daya kamata ya bata kariya wajen kubutar da itane ke cewa a harbeta baida matsala. Wace irin ƙasa muke da ita kenan? Ahaka akeson wanda yaga mai laifi ya tona masa asiri.......

           Master da gaba ɗaya kamaninsa sun canja duk da bindugun da aka saitasu da shi ya nufota a guje da alamar son kubutar da ita saboda harsasai guda uku da jami'an suka harbo gaba ɗaya kanta sukayi gadan-gadan, sai ɗaya ne ya nufosa shiko ya saka bullet proof jacket a jikinsa, yasan duk tsiya harbin bazai samu makasrsa ba sai dai idan kwanansa ne ya ƙare yau. Yana gab da isowa gareta bullet ɗin ya shiga cikin kafarsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana kaiwa duƙe, hanunsa ɗaya na zaro karamar bindigar jikinsa shima ya fara maida murtani. Wani irin zabura Hibbah tai babu shiri ta nufosa, hakan ya bata damar gocema bullets ɗin da suka nufo kanta har guda biyu ɗaya ya sake samun master a hannu.

        Hankalinta ya ƙara matuƙar tashi ganin shi ƙoƙarinsa ya bata kariya, yayinda waɗanda ya kamata su bata kariyar su son kasheta sukeyi. Sam rikicewa ya hanats gane fuskar dattijo A.G. Shiko Master ya gansa ne duk da yana ƙoƙarin ɓoye fuskarsa garesa. Duk da tasan ya mata nauyi haka ta miƙa hannu ta kamo nasa tana kuka. Haɗin kai ya bata ya miƙe shima da ƙyar cikin dakiya da dauriyarsa duk da tuni jini ya ɓalle masa ta ƙafa da hannu. Kasancewar suna gab da ƙofar falon suka sami nasarar afkawa ciki, Master ya danna security jin A.G ya bama yaransa damar bin bayansu duk da dama ba daina harbin sukaiba ALLAH dai ne ya bama su Master kariya bayan biyun da suka sameshi wasu basu sake taɓasu ba. Jakkarsa daya yasar a falon ya ɗauka, da sauri Hibbah ta amsa ta goya a bayanta. Ya fisgi hannunta cikin bama kansa ƙwarin gwiwa suka afka cikin kitchen ɗin suma. Sai dai su a tsakiyar kicin ɗin ya tsaya ya haye saman table ɗin wajen duk da jini dake kwaranya masa. Hannu ya miƙa ta tsakkiyar p.o.p ɗin kicin ɗin ya burma sai ga ƙofa. Ya ɗan daka tsalle ya fisgo wani zare mai kama da tsani. Hannu ya miƙa mata ta ɗora nata sai faman wai-waige take jin ƴan sandan nata ƙoƙarin buɗe kofar falon. Ta tabbatar suka shigo kuwa sun gama yawone. Cak ya ɗagota duk da tanada nauyi.

        Da taimakonsa ta fara hawan zaren tsanin harta shige. Kafin shima ya fara hawa. Yana gab da shigewa suka sami nasarrar ɓalla ƙofar falon. Cikin sa'a ya ida shigewa da jan tsanin ya maido ƙofar ya rufo. Karan farko a tarihin rayuwa Hibbah a cikin zinc bisa gangancin da taso tafkama rayuwarsu. Wani ƙaton bututu kamar na ruwa suka samu cikin zinc ɗin, Master da ya fara ɗan galabaita saboda jinin dake fita a jikinsa dama ba isashen lafiyane da shi ba ya nuna mata cikin bututun da bata fitila ƴar karama mai shegen haske.

      Ɗan kwalin kanta ta cire tana kuka ta yagashi biyu, ƙafarsa ta ɗaure masa dai-dai wajen da bullet ɗin ya shiga. Sauran rabin ta ɗaure masa hannunsa. Cikin taune lips ya turata cikin bututun shima yabi bayanta dan yasan jinin da yake zubarwane zai nunama su A.G inda sukabi.

     Da rarrafe suka dinga kutsa kai cikin bututun batare da Hibbah tasan ƙarshemsa ba, balle inda suka dosa. Sunyi tafiyar da har sai da ta fara galabaita saboda ƙura sannan ta fara hango haske alamar karshensa kenan. Koda suka fito batasan inane nan ɗin ba. Amma dai gidane a wajen shima mai kyawun gaske. Ya fisgi hannunta ya danna cikin motar dake fake a wajen bayan ya yaye tanfol ɗin da aka rufeta da shi. Shima shiga yay yana jan numfashi da ƙyar dan idanunsa sun fara ganin jigari-jigari. A mamakinta sai gani tai ya danna wani abu gate ɗin ya buɗe kansa. Ya fita da motar da gudu daga gidan. Har daga nan tana iya jiyo jiniyar motocin yan sanda da karar harbe-harbe alamar gidan da suka baro kusa yake da wannan. Gudu yake tsulawa na fitar hankali wanda dole motoci da napep ke basa hanya. Masu zagi nayi masu kiransa ɗan giya nayi. Baimasan sunai ba. Dan bai tsaya ba sai a wata anguwa. Motar taga ya faka a wani dan lungu ya fita. Batare da yayi magana ba itama ya zagayo ya fisgota. Key wani mai shushaina dake a lungun zaune shi kaɗai yana gugar takalma ya jeho masa. Ya cafe dajan hannunta suka sake shiga wata motar, yayinda tunkan su fice a lungun ta hango mai shushaina ɗin nan na rufe waccan motar da tamfol.

         Wani irin tsoransa ne ya tsargama Hibbah. Ta kafesa da ido cike da alamar tambayoyi sai dai babu damar yinsu. Yanzu kam ta cikin anguwanni ya dinga bi da su har suka sake zuwa wani layi sukai canjin mota, anan ko motar kawai suka samu sai mai tallan rake a gefe can shi kaɗai. Sai da ya shiga motar ne ya yafito mai tallan raken yana cizar leɓe. da gudu mai rake ya turo Wheelbarrow ɗinsa zuwa inda suke. “Rake na ɗari uku”.

    Master ya faɗa da ƙyar yana lumshe ido.

      Raken mai rake ya ɗebo ya zuba a leda. Ya turo kansa ta Window ɗin motar yana ajiye keys a cinyar master. “Gida mai lamba takwas, anguwar bauranya”.

     Komai masbaiceba yaja motar suka bar wajen. Gaba ɗaya hibbah ta mutu a zaune a karo na biyu, kallonsa kawai take kamar gunkiya har suka iso anguwar da mai raken taji ya faɗa. horn yayi maigadi yay saurin wangale masa gate ya danna hancin motar. Gaba ɗaya su Salis dake tsaye sunata faman kaikawo a compound gidan mai sashe biyu sukayo inda yay fakin. Hakama baba saude dake can zaune goye da Sharifat ta mike da sauri duk da batasan ainahin abinda ke faruwa ba. Kawai dai su Habib sunje sun taho da itane acan L.E street batare da sun mata bayanin komai ba.

     Kusan gaba dayansu suka rufu akansa. Yayinda wasu a cikinsu harsun fara kuka ganin yanda ya samu harbi. Ga jikinsa harya fara saki saboda jinin da ya zubar. Da taimakonsu suka nufi sashen da ke a hannun dama suna shartar hawaye. Yayinda Hibbah wani irin nadama ke sake shiga bargonta, dan itama kukan da taga su Habib nayine ya sake tayar mata da hankali.

     Kanta baba saude tayo ta kamata itama tana tambayarta miya faru?  Jikin baba saude ta faɗa tana girgiza kanta hawaye na kwarara mata. Sai kuma tai saurin barin jikin baba sauden tabi bayan su Adam. Itama Baba sauden bayansu tabi jikinta sai rawa yake ganin jikin Master duk jini.


        A falon suka zaunar da shi bisa wata kujera mara tudu mai laushin tsiya. Cikin sauri Musbahu ya dakko First aid box ɗin daya hango can gefe. Cikin sauri Khalid ya kai tsugunne ya fara warware dan kwalin hibbah data daura masa. Yayinda Idris ke kwance na hannun shi kuma. Cikin rumtse ido Khalid ya zuba masa ruwan magani akan wajen. Wata wahalalliyar ƙara Master ya saki yana sake damƙe hannun Zaidu dake gefensa. Khalid na kuka yasa wani ƙarfe cikin ramin ya fisgo bullet ɗin. Baki kawai Master ya datse da azabar ƙarfi. Tashi Khalid yay ya koma wajen hanun, yayinda Habib ya duka gaban kafar ya cigaba da treating ɗinta. Acan ma Khalid ya cire bullet ɗin hannun, ganin Habib bai gama treating ƙafar ba sai shi ya cigaba dana hannun.

         Tunda aka cire bullets ɗin wani irin zufa ke ketoma Master akowacce hudar gashinsa. Yayinda yaketa faman sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da suka kammala tsaf suka goge jinin da duk ya bata ko'ina sannan ya buɗe idanunsa da sauri saboda abinda yazo masa a rai yanzun nan.

          “Ya ALLAH! Akwai matsala, akwai matsala!!”.

     Ya shiga faɗa yana jujjuya kansa. Hankali tashe su Salis ke tambayarsa wace irin matsala kuma?.   

        Bai iya basu amsa ba, sai wayar da ke a jikinsa ya laluba da sauri yana duban su Adam. Cikin wani yare da ko Baba saude bata taɓa ji Mastern yayi ba yayma su Adam magana. Cikin sauri suka nufi hanyar fita a falon suna amsa masa da girmamawa. Su biyar suka fice aka bar Idris da Khalid kawai.

         Da ido yayma Idris maganar da su kaɗai suke fahimtar yarensa ta hakan. Idris ya jinjina masa kai da duban baba Saude da har yanzu take sharar hawaye.

         “Baba muje na kaiki ki huta ko? Karki damu komai yayi dai-dai insha ALLAHU ”.

     Badan baba Saude taso ba tabisa ɗauke da Sharifat dake barci a bayanta. Dan tunda ta fasa kuka sanda su Habib ke shiga gida suna ce mata tafito saita lallaɓata tai barci lokacin da suka shigo mota, koda suka iso gidan kuma saita goyata da gyalenta.

        Kuka sosai Hibbah keyi wanda ke sake hasala zuciyar Master. Sai dai da yake yanzu hankalinsa nakan wani abu daban yasa ya shareta. Sai da yaji ta cigaba da cika masa kunne ne ya daka matsawar da ba ita kadai ba hatta da Khalid sai da ya zabura.

      Idan baki bar min wannan garshekan kukan ba saina daddage kanki da bullets a gidan nan!!. Kuma ki tashi min anan kafin na hambaraki a ƙasa kanki ya bugi tiles ɗin nan!!”.

        Da gudu ta miƙe tabi bayan su baba saude. Dan yanzu kam ta tabbatar ada ba Master ta sani ba yanzu ne taga ainahin Master ganin idonta ba labari ba. Gaba ɗaya idanunsa sun koma na ainahin tsohon bahagon zaki da babu abinda ya sani sai farauta. Idanunsa kai kace aman wuta zasuyi saboda tsabar jan da suka koma.

             Kansa ya dafe da faɗin, “Ina ji kamar na kashe yarinyar nan a yau na manta da shafin rayuwarta a tarihina.”

        Sosai tausayinsa ya sake ɗarsuwa a zuciyar Khalid. Ya tabbatar yau Hibbah ta ballo ruwa na gaske wanda batasan harda aikin taimakon ahalinta suka fita ba. Mastern su baya kuka sai domin tausayin al'umma. duk haɗarin da zakaga ya jefa kansa a cikin domin taimakon wanine. Kullum wahala yake da mutane batare da sun san manufarsa ba. Kowa kallon ɗan ta'adda takadari yake masa. Hatsabibi shu'umi ɓarawo. Amma hakan bayasa ya sare daga aikinsa duk da waɗanda yake dan su ɗin ko 1% basu fahimcesa ba.............✍


*_Asirin da xoxo taimin yau ya warware🙄😏🚶🏻😖_*


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 *_Typing📲_*



*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*


https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*


https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_Chapter Thirty Five_*


..........Yaran A.G sun gama bincike ko ina babu Master da Hibbah a gidan. Sai da ga ƙarshe A.G ya farga da bin jinin da Master ya dinga zubarwa har cikin kitchen. Yay tsam yana auna inda jinin ya tsaya ya kuma zuba da yawa.

     “John!”.

Ya kira sunan ɗaya da ga cikin yaran nasa cikin da ka tsawa. A guje sukazo. Batare da yayi magana ba ya nuna musu p.o.p yana zaro waya aljihu. Cikin ƙanƙanin lokaci suma suka shige cikin p.o.p ɗin. Koda suka shiga suma ta cikin bututun sukabi suna sanar masa abinda suka fahimta. Sai da suka ɓilla har ta wancan gidan sannan suka sanar masa ta waya.

        Wasu yaran ya bari anan ya fito ta cikin layin, gida uku ne tsakanin gidan da inda su Master suka zauna.

       “Lallai guy ɗin nan ya cika matsiyaci shu'umi. Kaga shege kamar wani kurege ta ko'ina fasa hanyoyi yake.”

      Ɗaya da ga cikin yaran A.G ya faɗa rai a ɓace. Komai A.G bai iya cewa ba. Dan zuciyarsa tabbas tana gab da fashewa a cikin ƙirjinsa. Jin shigowar wasu ɓangarori na jami'an tsaro cikin layin ya sakashi fita. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ma baki ɗaya ta gama hargitsewa. Bakaji da ganin komai sai jami'an tsaro da ƴan jaridu. Kowa burinsa yaji wani abu da ga bakin su A.G da suka fara zuwa wajen. Sai dai ina komai ya kasa fita da ga bakin A.G. da ga ƙarshe ma zare jikinsa yay ya baro anguwar saboda kiran da Alhajin Mande yay masa akan ya maza yazo inda suke tunda zancen guduwar master harta sake bazuwa cikin ƙanƙanin lokaci.


         Gaba ɗayansu sun hallara ne a gidan hutun Dr Sufi, duk da kuwa kiraye-kirayen wayoyi da suketa samu daban-daban akan neman tabbacin kuɗaɗen da akace Master ya wawasar musu. R.D na zaune yana rusar kuka kamar ƙaramin yaro shi da Alhaji Sallau. A.G na shigowa R.D ya miƙe ya nufesa cikin rawar jiki.

      “A.G an kamashi?”.

A.G da shima kusan kan nasa so yake ya juye ya girgiza masa kai.

       Kuka R.D ya sake fashewa da shi saboda tsabar tashin hankalin da yake a ciki. “A.G ya nakasta min rayuwa ya yasheni matsiyacin nan. Naira dubu hamsin kawai ya barmin a accaunt tsinannen......”

         “Kowa ma abinda ya bar masa kenan R.D. yanzu ba lokacin zaman kuka bane ko jajantama juna. Lokacine na himmar cimma rayuwarsa dan baiyi nisa ba. A yanzu haka na baro cikin gidan da yake ne saboda kiran da kukaimin. Amma na bar yarana duk da kuwa ya gudu. Yarinyar nan ta wajen Halilu ne ta tona asiri. Amma abinda ya bani mamaki da ga ƙarshe bayan mun tarfasu a cikin gidan duk da abinda tai masa shine ya ringa bata kariya daga harbin dana saka ai musu, sai shi harbin yayta sama shi a dole jarumi”

       “Dan ALLAH da gaske kun harbeshi!!”. Engineer yay maganar tamkar wani zararre. Dan alamu ma sun fara nuna kamar notin kan nasa ya fara kwancewa shima fiye da nasu R.D ɗin”.

      A.G ya kaɗa masa kai cikin tabbatarwa. “Tabbas mun harbesa. Sai dai harbin duk ya samesa inda bazai mutu ba.......”

      Cikin katse A.G Alhajin Mande yace, “Idan matsiyacin yaron nan ya mutu yanzu to ai muma mun mutu A.G. dolene yaƙinmu ya kasance na dawowar dukiyarmu hannunmu harma da wadda muka sakashi ya tara. Kafin mu walakanta rayuwarsa da duk ma wanda ya shafesa. Tunda har ya bama yarinyar kariyar hakan na nufin yana sonta kenan, dan nidai nasan baida imanin da zai kareta batare da soyayya ba.......”

         “So! Kuma? Kai gaskiya bana tunanin haka”.

   Cewar Dr Sufi cikin kokwanto.

           Tsaki Alhaji Sallau yaja da faɗin. “Dr Sufi kana mamakin wacece mace. Duk wani shaiɗanci da kake ganin matsiyacin yaron nan ya iya bazai saka ya kasa shiga kaidin mace ba. Ai ni tun randa akace ya ruguza auren ƴaƴan halilu nakeji a raina akwai wata a ƙasa. Shiyyasa ban zauna ba sai da na gano inda ƴan uwan yarinyar suka koma yanzu haka. Jiya-jiya aka kawomin bayanan dama a meeting na weekend ɗin nan naso kawo zancen dan mu masa tarko da su koda yaso aikata cutarmu, to ashe shaiɗanin ya gama shirya mana tsaf.

      A zabure A.G yace, “Da gaske ka samo inda suke?”.

     “Tabbas kuwa bar kokwanto A.G”.

Alhaji Sallau ya faɗa yana zaro waya a jikinsa.

     Wata shegiyar dariya A.G ya sanya da faɗin, “Tabbas Master kazo hannu dan uban babanka. Dan da yarinyar zamuyi amfani kazo garemu. Yanda take son ahalinta muna damƙesu kaima bazata barka ka shaƙi numfashi lafiya ba”.

     Fahimtar gaskiyar zancen da manufarsa ya sakasu jin wani ɗan karen sanyi na ratsa zukatansu. A take suka gama aminta da zuciyarsu cewar Master yazo hannu ya gama kawai. Dan Alhaji Sallau na gama basu adireshin su Ummi A.G ya kira ya ransa ya basu Umarnin binsu Yaya Umar har wajen ayyukansu a kamo masa. Hakama su Ummi.


(Tabbas Master kayi gaskiya akwai matsala🙆🏻🤦🏻🚶🏻)


__________________________


            Ummi da surukanta gaba ɗaya na a sashenta suna hira kamar yanda suka saba zuwa mata a kowanne safiya su ɗan zauna bayan fitar mazajensu, matar Yaya Umar ta fara ganin abinda ke faruwa awayar hannunta. Cikin waro idanu waje take faɗin, “Tabɗi jan, shahararren ɓarawon nan yau ma ya sake guma uwar satar datafi ta kowanne lokaci a tarihi”.

      Kusan a tare suka haɗa baki wajen tambayar waye?.

     “Master mana. Gashi bbc ma har sun saki”.

     Ta basu amsa kanta tsaye. Gaban Ummi ne ya faɗi dan a saninta dai na yanzu Isma'il shine Master. Kafin ta samu damar cewa wani abu Zahidah tace, “To bara mu kunna television”. Batare da jiran amsaba ta dauka remote ta kunna. Cikin sa'a kuwa ana tsaka da nuna rahoton ne dan kowanne gidan tv da na redio shine latest labarinsu na yanzu-yanzun nan da gaba ɗaya ya hargitsa ƙasar dama duniya. Dan anyi itifaƙin bai taɓa mahaukacin sata makamancin na wannan karon ba ma. Ya yashe asusu goma sha ɗaya a lokaci guda. Asusai kuma masu matuƙar nauyi na kuma manyan mutane da ake matuƙar ganin mutuncinsu cikin dattijan ƙasa. Harda jami'an tsaron da ke farautar rayuwarsa.

       Hankalin Ummi bai gama tashi ba sai da taji sabon rahoton da ɗan jaridar ke faɗa cewar a yanzu haka labari yazo musu wata matashiyar budurwa da Master yay garkuwa da ita  ta samu nasarar tona masa a siri ta hanyar kiran wayar ƴan sanda ta sanar musu a inda ya ɓoyeta. Sun sami labari kuma a majiya mai ƙarfi a yanzu haka ƴan sanda sun zagaye gidan inda suke da tabbacin Master yana ciki shima.

     Karkarwa jikin Ummi ya farayi, ta ɗauka waya da nufin kiran layin yaya Abubakar taji tabbacin zancen, sai ga ƴan sanda sun faɗo musu su huɗu. A razane duk suka miƙe da ɗaga da yin surrender, dan bindigu duk suka nuna musu.

     “Duk ku fita!!”.

Ɗaya da ga cikin ƴan sandan ya faɗa cikin daka tsawa. ALLAH ya taimakesu dukansu akwai hijjabai a jikinsu har Ummin, dan basu iya zuwa su zauna mata babu hijjab ko mayafi. kamar yanda itama idan suka shigo bata taɓa zama cikinsu babu mayafi ko hijjab tare da ita. Haka suka fita cikin matsanancin tashin hankalin rashin sanin laifinsu. Da ga su sai wayoyin hannunsu. A cikin mota guda aka zuba su Ummi. suma ƴan sandan suka shiga tasu.


★★★★


      A ɓangaren su Yaya Muhammad ma suna wajen ayyukansu cikin tashin hankalin abinda suka gani a labaran daketa yawo a wayoyin hannu. Zukatansu sun gama basu Hibbah ce ta tonama Isma'il asiri. Duk da suma har yanzu basu san ainahin gaskiyar dalilinsa na aikata waɗan nan abubuwanba hakan bai musu daɗi ba. A daren shekaran jiya yake sanar musu akwai aikin da yake kanyi yanzu haka, yana kammalawa zai kawo Hibbahr ta gaida Ummi. Sai gashi koma ya hargitse tunda gashi suma ta shafesu.

      Dan batare da sun san nasu laifin ba suma dai sai ga ƴan sanda sunzo kamasu suma. Hatta da Yaya Abubakar da ke matsayin jami'in tsaro suna tsaka da kai kawo akan abinda ke faruwar kawai akazo akai arresting ɗinsa. Ƴan sandan dake station ɗinsu sun so ɗaga hankalinsu Yaya Abubakar ɗin ya kwantar musu da hankali yabi jami'an farin kayan da sukazo kamasan. Dan shima a ransa yanason zuwa kodan wani bincike.


★★★★★


         Kusan awa ɗaya kenan da barin su Habib gidan amma babu su babu labarinsu. Gaba ɗaya su Idris sun kasa zaune sun kasa tsaye. Sai kaiwa da kawowa suke a falon hankalinsu nakan wayoyinsu suna ganin abinda ke faruwa ta yanar gizo. Basu kunna tv bane saboda fahimtar gaba ɗaya Master baya buƙatar wata hayaniya. Dan tun korar Hibbah da yay a wajen ya maida idanunsa ya lumshe kai kace barci yakeyi. Koda Khalid ma ya tambayesa ko zaisha tea bai tanka ba dan yayi zurfi matuƙa a tunani.


       “What!!?”

Khalid dake rike da waya a hannu ya ambata yana mikewa tsaye a zabure cikin alamun gigita. Idris dake zaune gefensa yay saurin dubansa da faɗin. “Lafiya?”.

      “Inafa lafiya!, wai kaji mi matsiyacin A.G ɗin nan ke faɗama ƴan jarida kuwa akan alaƙar Master da aunty queen?!”.

        Hannunsa ya janye a kansa da ke masa tsananin ciyo, tare da buɗe lumsassun idanun ya sauke akan  Khalid da yay maganar. Kafin Idris dake ƙoƙarin buɗe baki yay magana yayi ɗin ya katsesu.

       Cikin muryarsa da ke a shaƙe na mura da tsananin ɓacin rai ya ce, “Television”.

       Kai Khalid ya jinjina masa da ajiye wayar hannunsa ya ɗauka remote ɗin tv ya kuna. Hakan kuwa yayi dai-dai da hasko A.G da ke bayani ga ƴan jarida, da alama yabar wajen su alhajin Mande ya koma office.

            “Tabbas har yanzu babu wanda yasan fuskarsa. Saboda yana amfani da facemasks iri daban-daban idan zai aikata laifinsa. Misali kamar yau an samu fuska biyu da yaje banki da ita, inda mutane da yawa suka tabbatar da sun gansa a matsayin alhajin ƙauye daya shigo bankin tankar baisan komai ba. Sai a yanzu ne kowa ya fahimci shine yay shigar ɓurtu tamkar yanda ya saba. Tabbas mun bibiyesa adalilin yarinyarsa kuma har mun sami nasarar harbinsa. Sai dai yanzu-yanzun nan muke samun labari a majiya mai ƙarfi dangane da ita yarinyar da tai kiran ta sanar da inda yake. matarsa ce, soyayya sukai kuma kafin aure. Hakan na nufin ahalinta sun san wanene shi suka ɗauketa suka bashi. Dan a yanzu haka zancen da nake muku harda ƙanin mahaifin ita yarinyar dake dauke da ɗawainiyarsu tun suna kanana saboda mahaifinsu ya rasu suka yashema asusu. Kenan hakan na nufin harda ita a cikin tawagar tasa.......”

        “Amma yallaɓai idan harda ita mi zaisa ta tona masa asiri?”.

    Wani yayma A.G tambayar cikin katsalandan na ƴan jarida.

        A.G yaja numfashi, “Muma wannan itace tambayar da muke nemawa amsa. Sai dai a ganina kawai sun shirya mana wasa da hankaline kawai sai suka rufta..”

       “Kenan dama kuna bibiyar al'amuransa a koda yaushe?”.

     “Sosai ma kuwa. Dan bamu da burin daya wuce mu kamashi. Shiyyasa dare da rana muke tsaye tuƙuru akan dukkan motsinsa...”

       “Amma yaya akai duk da jajircewar nan taku harya samu nasarar yashe asusan bankunanku kuma a yau?”.

      A.G ya kafe ɗan jaridan da yay tambayar da ido har saurayin ya tsargu. Ganin sauran ƴan jaridar na juyawa suna kallon saurayin saboda kallon da yake masa ya sashi basarwa yana sakin murmushi. “Tambaya mai ƙyau. Sai dai zan bada amsartane anan gaba bawai yanzu ba...”

       “Tabbas zaka amsata kuwa! Koda su sun manta ni Isma'il Aliyu Hikima zan sakaka ka amsata!!”.

      Master ya faɗa cikin wani irin kaushin murya da ɗaci yana sake maida idanunsa ya rufe. A haka ya cigaba da sauraren A.G daya ke tabbatarma da duniya a yanzu haka sun sami nasarar tattaro ahalin Hibbah, dan sune kaɗai zasu iya faɗama duniya a inda master yake a yanzu.

       Cikin tashin hankali su Khalid ke duban Master daya maida idanunsa ya rufe. Sun san sarai yana jin A.G ɗin shima. “Innalillahi.... Boss akwai matsala kenan”.

     Bai motsaba, bai kuma tanka ba duk da yaji abinda Idris ɗin yace. sai dai faman taunar lip ɗinsa yake na kasa alamar zuciyarsa na masa zafi da ciwo. Dan tsabar yanda yake taunar lip ɗin har ya koma jaa sosai.

         Shigowar baba saude da ke faɗa musu Hibbah fa babu lafiya jikinta sai rawa yake ga kuma zazzaɓi ya sakashi buɗe idanu a hankali. Kallon baba Sauden kawai yakeyi yana cizar lip. Su Idris kam duk sun zabura kan baba saude suna tambayarta miya sameta? ba yanzu ta shigaba lafiya lau.

     “Gaskiya inaga firgici ne. Da alama bata taɓa gamo da makamancin wannan tashin hankalin ba. Tunda ta shiga fa sai surutai takeyi. Maida idanun yay ya lumshe, gaba ɗaya kansa ciwo yake masa tamkar zai buga.

       Jin yaƙi cewa komai yasa sukai tsuru-tsuru suna kallonsa. Musamman ma su Khalid. Ganin haka yada Baba Saude takowa ta ƙaraso inda yake. Cikin taushin murya tace, “Babana ko jikin ne?”.

     Idanunsa ya sake buɗewa, yanda suka sake kaɗawa sukai ja har kamar suna ƙyallin ruwa sai ka ɗauka kuka yake. Yay ɗan murmushi mai ciwo yana girgizama baba sauden kansa.

       “Naji sauƙi baba, kice mata tazo nan”. Yay maganar acan ƙasan maƙoshi cikin rauni da ɗacin dake addabar zuciyarsa da maƙoshinsa.

        Baba saude da gaba ɗaya itama zuciyarta ta ƙara raunana. Ta kaɗa masa kai da juyawa ta koma. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito riƙe da hannun Hibbah da kallo ɗaya zakai mata ta baka matuƙar tausayi. Duk ta susuce ta firgice. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta sun kumburo matuƙa, jijiyoyin kanta duk sun miƙe ruɗu-ruɗu. Duk da haushinta da su Khalid ke ji sai wani irin tausayinta ya kamasu. Suka shiga jera mata sannu cike da damuwa. Bata iya ta amsa musu ba, dan gaba ɗaya a yanda Hibbahn take ta fita hayyacinta ba lallaine ma tana fahimtarsu ba.

      Shi kansa master tunda baba Saude ta zaunar da ita gefensa ya buɗe idanu ya kalleta sai da tsigar jikinsa ya tashi. Yaja numfashi batare da ya ce komai ba ya maida dubansa ga baba Saude. “Baba kije abinki kawai”.

      “To babana, amma babu wani abinda kuke buƙata?”.

     Kansa ya jinjina mata kawai. Sai kuma ya maida dubansa ga su Khalid.  “Tea da bargo”. Ya faɗa a taƙaice dan baya son yawan maganar.

     Cikin sauri Khalid ya nufi inda yake tunanin kitchen ne. Idris kuma ya nufi bedroom. Sai da duk suka shige ya maido dubansa gareta, batare da yace mata komai ba ya ɗaura hannunsa mara ciwon saman goshinta. Zafin da ya ratsa masa hannu ne ya sashi cije lip yana janyewa ya maida kan wuyanta. Ɗan zabura tai dan abin yazo mata a bazata duk da taji sanda ya taɓa goshin. Baice komai ba ya janye hannun. Hakan yayi dai-dai da fitowar Khalid ɗauke da babban bargo mai laushi. Zai warwaresa Master ɗin ya girgiza masa kai. Dai-dai nan shima Idris ya dawo ɗauke da shayin. Saman table ɗin ya ajiye yana jawosa gaban master ɗin duk da ya fahimci na Hibbah ne.

         Zamansa ya ɗan gyara yana riƙo hannunta, a ɗan zabure ta buɗe idanunta, kallon cikin idonsa da tai a mistake ya sakata saurin maida idanun ta rumtse hawaye masu zafi na silalo mata. Ɗan jawo hannunta da yay ne ya sata matsowa jikinsa dan gaba ɗaya a firgice take da shi da komai ma. Fahimtar hakan da yay ne ya sakashi kwantar da kanta a kafaɗarsa. Ta ja wata nannauyar ajiyar zuciya na tabbacin babu abinda tafi buƙata kamar ɗumin jikin uwa. Ganin haka yasa su Khalid barin wajen.

        “Bana son kuka”.

Ya faɗa acan ƙasan maƙoshin da yasa ita kaɗai ta jisa. Haɗiye kuka ta shigayi tana jan tagwayen ajiyar zuciya. Dan tunda ya ɗan jinginata da jikinsa tsinkewar da zuciyarta ke mata ya ɗan fara sassautawa. Hannu ya kai bisa fuskarta ya share mata hawayen yana faɗin, “Kinsan zuciyarki bazata iya ɗaukar duk wannan ba miyasa kika ƙirƙira?.”

      “Dan ALLAH kayi haƙuri”.

Ta faɗa tana fashewa da sabon kuka. Komai baice mata ba, sai kofi tea ɗin da ya ɗakko ya miƙa mata. Babu musu ta amsa ta hau sha, dan yau babu wata ƙofar samun damar masa gardama. Taso mata yake amma haka ta danne taita sha. Tana ajiye kofin tamkar jira sai ga amai. Ƙoƙarin barin jikimsa tai amma ya riƙeta. Tanata jujjuya masa kai alamar ya barta shi kuma bai fahimta ba. Sai kawai ta saki aman ya wanke musu jiki baki ɗaya.

         Da sauri su Khalid suka miƙe zuwa garesu. Hakan kuma yayi dai-dai da fitowar baba saude itama a firgice.

        “Dan ALLAH kayi haƙuri”. Tai maganar wani aman na yunƙuro mata, duk ta sake firgicewa, ta cire hijjab ɗin jikinta ta fara goge masa aman daya ɓatasa. Komai baice mata ba, sai riƙeta da yay ganin kamarma jiri na neman ɗibarta ta faɗi. Sai da ya tabbatar ta gama ya maida kanta kan kafaɗarsa ya kwantar.

     Duban su Idris da ke ta faman jera mata sannu yayi, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Mikewa yay riƙe da ita suka nufi bedroom duk da bayajin daɗi da ƙarfin nasa jikin shima. Har cikin bathroom ya rakata, bayan ya zaunar da ita ya haɗa mata ruwan ɗumi. Batare da yace mata komai ba ya fito ya barta.

      Da kallo tabisa wasu hawaye masu zafi na sake silalo mata. A ranta tana mamaki da tambayar kanta shi ɗin wanene shi?. Rashin mai bata amsa ya sakata fara zame kayan jikinta ta fara wankan batare da tunanin zai iya sake dawowa ba. A kiɗime ta waro idanu da saurin saka hannu ta kare jikinta tare da kaiwa tsugunne ganin ya turo ƙofar ya shigo kansa tsaye, shima da ga shi sai guntun towel.

       Ɗauke idanunsa yay da ga kallon da yay mata shima, kayan da ya cire na jikinsa data ɓata da amai ya ajiye yana ɗan jan numfashi a sarƙe.............✍


*_Kuyi manage da wannan, da hanau gara mannau😬🚶🏻_*


    


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 

 


*_Chapter Thirty Six_*


...........(Kura ga tsoro ga ban tsoro) ya faɗa a ransa ganin yanda jikinta keta uban tsuma tama rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Kansa ya sake ɗaukewa tamkar baiga halin da take a cikin ba ya ƙaraso gareta bayan ya ajiye kayan. Kuka ta fashe masa da shi tana girgiza kai, dan a duniya bata taɓa shiga cikin tsananin kunya da firgici kamar na yau ba. Tayi matuƙar daburcewa, wajen ɓuya kawai take nema amma babu.

         Hannusa mai lafiya yasa ya zame hannayenta duka da take faman rufe jiki, duk ƙoƙarinta na son ganin ta faɗa jikinsa ta ɓuya kuma yaƙi bata daman hakan, sai ma sake mannata da yay da bango ya tokare ta da hannunsa mai ciwo duk da zogin da yake masa har zuwa yanzun. Cikin tsareta da idanu babu ko kunya ya fara magana cikin izza da ƙasaitar fushin da yake ciki har zuwa yanzun, “Nuna tsoro anan gazawace ga wadda ta nunama duniya ta girma, tunda har kika iya ɗaukar wancan da kika ƙulla, wannan ma dole ki ɗauka. Lokaci yayi daya kamata nima naga little Master a duniya, kafin ki ɗanamin tarkon da bazan tsallake ba Hibbaty”.

       Duk da ba komai ta fahimta a maganganunsa ba saboda ruɗanin da take a ciki, kanta ta shiga girgiza masa. Cikin rawar harshe da son ɓoye kanta tace, “Dan......”

        “Shiiii!!.” Ya faɗa yana ɗaura yatsansa bisa leɓenta.

       “Karma ki roƙeni dan zugani kike. Barinki a haka gareni haɗarine, saboda wannan kan naki ba kowane yare yake ganewa a cikin baƙi. Kinfi buƙatar dalla-dalla. Gara na tabbatar da kaina a gareki, kafin lokaci ya ƙuremin na ajiye jini na a jikin ki, maybe ki fara nazari kafin kiyi abu” .

    Baki ta buɗe zata sake yin magana ya rufe bakin da yatsunsa yanda har sai da azaba ta sakata cire hannuwanta da take kare jikinta da shi ta riƙe nasa hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta.

       A karon farko ya saki wani lalataccen murmushi mai bayyana ƙunar zuciya, “K tsoro ce mai ban tsoro Muhibbat. Da yaren tsoro kawai ake fahimtar da ke karatun duniya. Tunda haka kikafi buƙata kuwa, sai ki shirya zaman jira da rainon ƴata ko ɗana har na fito a gidan yari tunda a can kikafi buƙatar ganina”. 

       Yana gama faɗa ya ɗan lakaci hancinta da janye jikinsa a nata, tana son yin magana yay mata alamar gargaɗi, idanunsa tamkar zasuyo aman bala'in da ke a zuciyarsa. Bai sake ce mata uffan ba ya juya mata baya ya sakarma kansa ruwa tare da cire towel ɗin jikinsa kansa tsaye tamkar yama manta da ita a wajen. Da sauri ta zame tai ƙasa jikinta na matuƙar rawa ta ɓoye fuskarta. Jin kamar ya kashe ruwan ya sata sake rumtse ido da ƙarfi kamar zatai kuka. Dan ita duk tunaninta tsayawa yay kallonta, duk da tanajin motsin da yakeyi alamar yin wani abu. Kaɗan ta buɗe idanunta sai taga har yanzu yana a yanda ya juya mata bayan. Ta ja ɓoyayyar ajiyar zuciya da fara ɗauraye jikinta da sauri-sauri. Duk da yanajin yanda take facal-facal da ruwa har yana fallatso masa a jiki bai juyoba, sai da ya kammala abinda yake a wajen sannan.

      Juyowar tasa tayi dai-dai da fisgar towel ɗin daya ajiye ta ɗaura. Duk da bai gama rufe mata jikin ba dai taji ƴar nutsuwa fiye da ɗazun da take a sule. Ya ɗan bita da kallo ganin yanda ta nufi hanyar fita da sauri har tanayi kamar zata faɗi, ga santsin ruwa da tiles ga na rashin ƙarfin jiki.

       Ya ɗan girgiza kansa da sakar ma kansa ruwan shower tausayinta na ratsashi. Tabbas yasan abinda ya faru a yau ɗin rubutaccene da ga alƙalamin ƙaddarar Sa. Ko babu ita sai hakan ta faru, tana da laifi yanada laifi. yasanma yafi yawa fiye da natan, sai dai yanda ya santa inhar ya nuna mata sassauci sake birkice masa zatayi, a yanzu kuma rayuwarta tafi ta kowa haɗari dan ita kowa kema kallon lagonsa. Haka dai ya kammala wankan cikin dabara da tunane-tunane. Bathrobe ya saka maimakon towel ɗin da ya shigo da shi tunda ta ɗauke. dan ya fahimci gaba ɗaya tsurewa take idan ta gansa babu rigan. Koda ya fito kwance ya sameta a kan gado ta kudindine da bargo. Komai baice mataba ya ƙarasa ga mirror yana ɗan duban kansa zuwa real face nasa na Isma'il da ya fito da shi. Jakar kaya daya gani ajiye a gefe ya sashi fahimtar su Habib sun dawo kenan. Koda ya buɗe kayansa ne a ciki da dukkan abin buƙatarsa na yau da kullum irinsu mai, turare da makamantansu. Ya ciri abinda zai buƙata ya ajiye gefe da wanda itama zata buƙata ɗin. Harya gama kintsawa Hibbah na cikuykuye abinta a bargo duk da tana jin motsinsa. Amma tsananin kunya da zazzaɓi sun hanata ƙwaƙwaran motsi.

        Shima duk da yasan idonta biyu komai baice mata ba, sai ma salla da ya tayar ta azhar. Sai da ya idar ya miƙe ya saka sabon mask sannan ya karasa saitin inda take a gadon. Hanunsa dafe da kansa dake sara masa ya kai zaune. Batare da yace komaiba ya yaye bargon da ɗaura hanunsa saman goshinta. Sosai jikin ya ƙara zafi, dan haka ya ɗan tsura mata jajayen idanunsa da ke sake tabbatarma mai kallonsa baida lafiya. “Ki tashi kiyi salla, sai ki sha magani ki kwanta”. Yay maganar har yanzu muryarsa bata fita da ƙyau.

         Sarai Hibbah tajisa. sai dai ta kasa koda motsawa harya tashi. Sai da taji ya fita a ɗakin gaba ɗaya sannan taja numfashi tare da miƙewa zaune tana share hawayen da ke ziraro mata wanda ba komai ya kawosu ba sai tsananin kunya da nadamar abinda ya faru. Ga kewa da ƙulafucin son ganin ƴan uwanta da Umminta da ke cike da zuciyarta.


    ★★

  

      Sosai su Habib sukaji daɗin ganin yay wanka ya sauya kaya. Sai dai tsananin tausayinsa na nan shimfiɗe akan fuskokinsu. Dan a kallo ɗaya da zaka masa zaka iya fahimtar rashin jin daɗin jiki dana zuciya dake tattare da shi. Kawai dai ƙarfin hali ne da juriya irin tasa.

       Sannu da tambayar yaya jikinsa suka shiga jera masa. Batare da ya iya buɗe bakin yayi magana ba ya shiga ɗaga musu kai kawai alamar amsawa. Basu damu ba, dan su kansu idan yana cikin irin wannan yanayin sunajin tsananin shakkarsa. Yanayine da yake a cikin fushi da zafin zuciya. Ƙiris yake jira wani ya shiga gonarsa ya tabbatar da fushin a kansa.

         “Ga magani ko a kawo tea sai ka sha?”.

    Musbahu ya faɗa cikin girmamawa. Master da ke kallonsu na tabbatar da suna a cikin ƙoshin lafiya ya jinjina kansa kawai yana rufe idanu. Sai kuma ya motsa laɓɓansa a hankali ya ce. “Kunyi salla?”.

       “Eh”

  Suka faɗa kusan a tare.

Komai bai sake cewa ba da ga hakan sai da Adam ya gabatar masa da magungunan da suka shigo da shi. Khalid kuma yay saurin nufar kitchen ya ɗakko ruwa tare da tea da ya haɗo masa. Batare da yayi magana ba ya ɗauka tea ɗin yasha kusan rabin cup. Shima maganin yasha.

        Fahimtar ya kammala ya saka Habib fara masa bayani a nutse game da aikin daya turasu. “Alhmdllh Master anyi bani gishiri in baka manda. A yanzu haka dukkanin iyalansu suna a hannumu”.

       Kansa ya jinjina fuskarsa har tana nuna alamun jin daɗin yanda sukai aikin cikin sauƙi da sauri babu wani mishkila. Musbahu ya dire jakkar da suka shigo da ita shima yana faɗin. “Wannan wayoyinsu ne duka anan. Duk da mun yanke network ɗin gidan gaba ɗaya saboda tsaro dai sai muka taho da su. Kayi haƙuri munyi abinda baka saka mu ba. A cikin yaran akwai wani mai taurin kai ya nema mana gardama muka bibbigesa, dan mun nunama mamansa ta tsawatar masa amma taƙi”.

         “Yaron waye?”.

Master ya tambaya yana kafe Musbahu da ido. Adam ne ya bashi amsa da cewar, “Kamar dai yaron Engineer ne”.

        Komai Master bai sake cewa ba, sai hannu da ya miƙama Habib da ke riƙe da lap-top ɗinsa. Cikin sauri Habib ya buɗe lap-top ɗin ya kunna ya miƙa masa. Filo ya sa a cinyarsa sannan ya ɗaura system ɗin. Sai kuma yay ma Adam nuni da jakkar da sukazo da ita na wayoyi. Jakar ya zuge ya zazzage wayoyin a saman table ɗin. Komai Master bai ce ba ya miƙa hannu ya ɗauka ɗaya da ga cikin wayoyin ya jujjuya a hannunsa. Kamar zai kunna sai kuma ya fasa ya ajiyeta. Wayarsa da ke a gefen damarsa ya ɗauka, ya ɗanyi danne-danne tare da kaiwa kunnensa ya lumshe ido da kwantar da bayansa jikin kujera jin ta shiga.

       Duk sake nutsiwa su Habib sukai da tunanin wa yake kira a cikin wannan ruguntsumin kuma?. Rashin samun amsa ya sakasu nutsuwa a saurarensa.

       Wayar na gab da tsinkewa aka daga. Shiru baice komaiba. Takaici ya saka A.G dake can faɗin, “Waye ke magana?”.

        Wani lalataccen murmushin gefen baki ya saki, cike da izzarsa da ƙasaita yace, “Master!!”.

       Duk da sunan ya daki zuciyar A.G sai ya dake, harda saki wata dariyar gatsatsa wadda tafi kuka ciwo. “Hhhh karen farauta! kai har kana da zarrar ɗaga waya ka kira wani a cikinmu a wannan lokacin kenan? Kako san su wanene mu kuwa?”.

       Master ya sake sakin murmushi a karo na biyu da gyara zamansa. “Sai da na sanku ma sannan na fara wasan kaima kasan wannan”.

        A.G da kejin zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito ya rumtse idanu da ƙarfi batare da ya tuna a tsakkiyar jami'an tsaro yake ba, dan meeting sukeyi akan Master ɗin ya ce, “Kai kare! Idan damar da ka samu a baya kake tunanin tana hannunka har yanzu to ka sani rayuwarka ta ƙare a wannan gaɓar.”

          A bazata su Habib sukaga Master ya ƙyalƙyale da dariya, sai kuma ya haɗe fuskar cikin kaushi da barazanarsa ya cigaba da magana.

       “A.G! A.G! Na master. Shin ba kune kukace ɓoyayyen wasa bane ba babban jami'i mai gaskiya?. Ya da tada jijiyar wuya tun a farkon karo haka?.........”

        A fusace A.G ya miƙe yana buga table ɗin batare da ya tuna a inda yake ba. “Kai tsinanne, ka sani duk randa kazo hannu ni ɗin nan da hannuna zanyi gunduwa-gunduwa da namanka na bama karnukan farauta da suka fika giyata su cinye namanka a tsakkiyar kasuwa!!”.

       “Tofa babbar magana, wai da wuri haka har ka fara fusata?. Nifa ta ɓangare ɗaya kawai na fara buga wasan a yanzu, amm har kake tada jijiyar wuya da ɗaukar alwashi kamar haka. To kwantar da hankalinka dan bamma fara komai ba, yanzu ma na kiraka ne danna sanar maka tarkacenku na hannuna, a kuma daren yau wasu a ciki zasu iya tsallakawa barzahu, gawawwakinsu kuma zasu iya zuwa maku ƙarfe biyar ɗin asubahi. Ku shirya dakatar da hakan ta dawo min da ahalin MATATA. Sannan ku tabbatar kun lashe aman da kukai na kalamaku daga nan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu, daga nanne sai ai wasan fili ba TAKUN SAƘA ba. Umarnine ba shawara ko neman alfarma ba..”

      Ya katse kiran da jefar da wayar gefensa yana cija lebensa na ƙasa da haƙori tamkar zai huda shi. Sai kuma ya buɗe jajayen idanunsa dake fusace ya dubi su Salis da sukai tsuru-tsuru.

      “Kuje ku huta, zuwa dare ku tattara min dukan bayanai akan maganganun su A.G da duk wani mai faɗa aji da ya fito yay magana. Salis ka turama Faisal cewar ya kawo saƙon nan, sannan ya faɗama *_WALƘIYA yayi barci a farkon dare, ya farka a farar asubahi. Kar yay baƙin ciki akan rubutacciyar ƙaddara, farautar *MASTER* ba wawaso akan naman shanu bane. Masu tambari a bayan ƙeya sun tabbatar da shiryawarsu tunda suka bayyana wasan a fili. Ya shirya dan yanzune TAKUN SAƘA zai fara”_*.

        A tare suka ƙame jikinsu da salute nasa. Fuskokinsu washe da fara'a suka hada baki wajen faɗin, “Yes master!!”.

      Wani shegen lalataccen shu'umin murmushi ya saki a karon farko da ɗaga lumsassun idanunsa ya dubesu. Tausayin ƙannen nasa kuma ahalinsa a halin yanzu na ratsashi, a hankali ya buɗe hannayensa ya mika musu alamar suzo garesa saboda yanda duk suka koma kalar tausayi a dalilin halin da yake ciki, baya son ganinsu cikin damuwa sam. Cikin ɗoki da zumuɗi suka nufo jikinsa batare da sun yarda sun fama masa ciwukansaba saboda tsabar taka tsantsan ɗinsu garesa. Ya haɗiye hawayen da suka ciko masa idanu cikin muryarsa da ke bayyana kaushinsa da ƙaunarsu ya furta, “I love you so much my sweet Brothers. ALLAH yay muku albarka.”

        Hawayen dake bin fuskokinsu suka shiga sharewa kamar yanda suka saba a duk lokacin da ya furta tsananin kaunar da yake a garesu. Cikin haɗa baki suma suka shiga sanar masa da ɗunbin ƙauna da soyayyar da suke masa har cikin ruhi da ɓargo. Irin wadda gaba ɗayansu suke jinsa a ransu tamkar mahaifi. Dan ya ɗaukesu lokacin da nasu iyayen suka jefar da su. Ya raineso lokacin da iyayensu suka nisancesu. Ya kaunacesu lokacin da iyayensu suka manta da su. Ya basu tarbiyya lokacin da iyayensu suka toshe idanunsu da kunnuwansu. Ya inganta rayuwarsu lokacin da iyayensu suka nuna gazawa da su. Ya yalwata farin cikinsu tamkar yanda kowaɗannen iyayen ƙwarai suke yalwata na ƴaƴayensu da basu gata. Bai taɓa banbantasu da Habib ba balle nuna ya fisu a gareshi.

      “Bana son kuka”.

  Ya faɗa a hankali yana shafa kawunansu da hanunsa mara ciwo tare da ɗan jan kunen Salis dake gefen damarsa cikin salon da yake musu punishment tun suna yara idan sun masa laifi. Dariya suka sanya dukansu suna share hawayen. Kafin su miƙe kowanne ya manna masa kiss a gefen kumatunsa, dan wannan itace fuskar da suke ɗauka real face ɗinsa saboda ita suka taso suka sanshi da ita. Hakan ya sakashi sakin murmushi ƙarfin hali. Tausayinsu na ratsashi da tarin ƙaunarsu. Sune ahalinsa, sune farin cikinsa, sune raunin sa, sune... Sune... Sunee.... Da yawan da babu adadin kididdiga.


         ★★★

  

   Gaba ɗaya A.G ya birkice, jiya yake tamkar ya jawo Master ta cikin wayar. Su kansu sauran jami'an kallon mamakin rikicewar tasa suke duk da sun san cewa mastern yay masa illa. Cikin gaggawa aka fara bibiyar lambar da yay kiran. Sai dai kash babu wata hanyar da za'a iya samun sa.

        A.G da gaba ɗaya jikinsa ke matukar rawa ya fice tare da wasu jami'an domin tabbatar da zancen master ɗin. Cikin lokaci ƙanƙani hukumar ƴan sandan ta sake rikicewa. Suma su Alhajin Mande aka fara kiran wayoyinsu domin ji da ga garesu....


★★


     A ɓangaren Abba kam sai da suka zuba masa ruwa sosai ya farfaɗo. Koda ya buɗe ido ya kallesu tsaitsaye a kansa sai ya fashe da kuka. Cikin mamaki da tsoro suke dubansa. Hajiya mama da zuciyarta ke tsitstsinkewa da tunanin waye kuma ya rasu tace, “Halilu kabar mana wannan kukan ka sanar min wanene ya rasu ne?”.

     Sake fashewa yay da wani sabon kuka saboda jin abinda hajiya mama ta faɗa. Sai kuma ya rarumo wayarsa batare da ya bata amsa ba. Number A.G ya shiga nema amma kuma ya gagara samu. Sai busy take nuna masa. Ya maida akalar kiran kan Alhaji Balele. Sai da tana gab da tsinkewa ya ɗaga. Ɗan gidan Alhaji Balele da ya ɗaga wayar cikin kuka da ga can yake sanarma Abba ai suna asibiti, tunda yaga yasar da Master yay masa shima ya yanke jiki ya faɗi. A yanzu haka ma likita ya sanar musu paralysis ta kama shi.

      Rawa jikin Abba ya kamayi, sai kuma ya fashe da sabon kuka yana jeroma Master tagwayen ALLAH ya isa da tsinuwar alkaba'i kala-kala. Takaici yasa Momy fisgar wayar a hannunsa ta fara dubawa. Dan yaki musu bayanin da zasu fahimta gashi yana rusar kuka tamkar wani ƙaramin yaro.

      Komai bata fahimta ba, dan haka ta dangwarar masa da wayar tana jan tsaki tabar wajen, hakan yasa suma su Ameera bin bayan uwarsu suma cikin takaici suka bar Hajiya mama ita kaɗai tsaye akan Abba.

     Sai daga baya suka fahimci abinda ke faruwa ta hanyar kunna tv. Hankalinsu ya tashi suma matuƙa. Dan a take momy ma tai zaman ƴan bori da ƙwala ihu. “Na shiga Uku dadyn Junaid kai ko miya haɗaka da Master har ka shiga lissafinsa?”.

         “Tsautsayi!. Wlhy Tsautsayi ne ni Halilu na shiga uku. A.G ka gama da rayuwata. Nayi dana sanin sanin matsiyacin yaron nan mai kama da bokan tsauni”.

        

    *_________________________*    


            Har zuwa yammaci abu ɗaya ke maimaita kansa a kowacce kafa ta yanar gizo da kafafen yaɗa labarai. Manyan masu fashin baƙi nata famanyi tare da jami'an tsaro da jama'ar gari ƴan bani na iya. Babu wanda yasan da ga ina hoton Hibbah da ahalinta ya fito sai gashi yana yawo. Master dai babu ma wanda ya sansa balle ya fidda hoton nashi. Sai dai hotunansa na ɓadda kama da keta yawo wanda yake a cikin fuskoki kala-kala da ko yatsansa ba'a gani.

       Ana tsaka da wannan kace nace kuma sai ga sabon zance ya fito da ga su A.G cewa anyi kidnapping ahalinsu har gida. Hatta da ma'aikatan gidansu ba'a bari ba sai masu gadi kawai.. Dan shi A.G ma securitys ɗin da ke a gidansa suna bada tsaro saboda kasancewarsa babban jami'i kansu an kwashe harda su.

         Komai ya sake tashi sabo anata kace nace na hasashen dalilin yin hakan da Master yayi, sai dai abinda ke ba mutane mamaki a wannan gaɓar miyasa Master ɗin zaiyi hakan? Tunda kowa yasan a baya iyakarsa satar kuɗi ba'a taɓa jinsa da yin garkuwa da mutane ba.

      A gefe kuma na manya irinsu A.G da wasu kasashen ƙetare na ƴan bani na iya har wasu na iƙirarin saka sunan Master ɗin a jeren ƴan ta'adda na duniya. Sun kawo hujjoji da dama na cewar hakan da hasashensu ya basu. Musamman da a wannan karon al'amarin nasa ya fito fili da kuma sabon salo. Sai kuma hasashen yana da yara masu masa aiki a wajeje daban-daban.


      Har zuwa dare dai Master bai sake cewa komai ba tun wayarsa da A.G. Duk da kuwa yana ta bibiyar shafukan sada zumunta da ganin dukkan labaran da ke yawo duk da tsananin buƙatar son hutu da yake a ciki. Ga mura da ke nuƙurkusar rayuwarsa har yanzu. Ya jima zaune a falon salla kawai ke tashinsa har isha'i. Sai da su Zaidu suka fito suna masa shagwaɓar yunwa sukeji sannan.

         Da farko bai kulasu ba. Sai da yaga zasu addabi rayuwarsa dan su a ɓangaren ci babu wasa ne, sannan ya ɗauka waya yay musu order ɗin abinci yana hararsu. Tattare kayansa yay ya barsu a falon. Duk da baice musu komai ba sun san za'a kawo abincin.

         Koda ya koma ɗakin kwance ya tadda Hibbah a tsakiyar gadon ta ƙudindine. Sai dai da alama ta tashi tayi dukkan salloli. Daga tsayen da yake ya kai hannunsa mai ciyo ya ɗan janye bargon data lulluɓa har akan fuska. Barci takeyi. sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci bana jin daɗi bane. dan ta wani nannaɗe kanta a waje guda kamar wadda take a firgice. Kusan kallon mintuna huɗu yay mata kafin ya janye idanunsa yana furzar da iska mai ɗaci.

        Toilet ya shiga yay abinda zaiyi ya fito yai shirin barci. Zama yay a gefen gadon kusan mintuna goma yana kallon Hibbah da sauraren hayaniyar su Idris da alamu ya nuna an kawo musu abincin. Sai kuma ya zame a hankali ya kwanta yana matse fuska alamar dai bayajin daɗi sosai. Kwanciya yay a rigingine ya lumshe idanunsa, tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lula duniyar tunani.

          A yanda yake ɗin sai ka ɗauka barci yake, sai dai yanda yake murza babban yatsan kafarsa dana kusa da shi zaisa kasan ido biyu yake ran mazane a wuya kawai. Shi mutum ne mai matuƙar fushi da zafi idan aka ɓata masa rai. Shiyya su Habib kanyi matuƙar taka tsantsan da shi idan yana a cikin irin wannan halin. Ya jima a haka yana ƙullawa da kwancewa akan shirinsa na safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu kafin barci ɓarawo ya sace sa.


*_WASHE GARI_*


            A safiyar yau tamkar yanda ya tsara ya fidda video a karon farko na tarihin rayuwarsa. Video ne da ya ƙunshi abubuwa da yawa da suka danganci jerarrun tambayoyi da ga kalaman su A.G ɗaya bayan ɗaya. Dama duk wani babba da ya fito ya tofa albarkacin bakinsa dan gane da abinda ya faru jiya.

      Da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “Ina da abin cewa da yawa, amma bazan ce ba, saboda lokacin cewar baiyi ba. Sai dai inason kamar yanda nai tambayoyin nan ga duk waɗan da na ambata su amsa min su. Da ga ƙarshe ina mai tuna muku acikin awa ashirin da huɗu saura awanni goma sha ɗaya suka rage muku akan ahalinku, Idan har kuna buƙatarsu ku sakarmin nawa nima na baku naku, dan ko ƙwarzane ya samu ɗaya daga cikinsu babu fashi sai na rama. Dan Master baya yafiya wa abokin gaba koda akan harara ne............🔥


(Tofa turƙashi, bara mu kama kanmu kenan master).


*_Ku sani a addu'a na bar posting dare ɗin nan🤦🏻😥🚶🏻_*


 


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 


*_Chapter Thirty Seven_*


..........Gaba ɗaya komai ya sake ɗaukar zafi a ɓangaren jami'an tsaro. Dan kuwa dai zuwa yanzu an tabbatar da ahalin su A.G suna hannun Master, sai dai kuma su su A.G sun tabbatar ma da duniya su Ummi basa tare da su. Kawai dai sun faɗa zasu kamasu domin master ya bayyana kansa. Kuma koda sukaje sai basu samesu a gidan ba kwata-kwata.

         Wannan magana ta fara canja salon zantikan bakunan mutane harma da wasu a manyan masu fashin baƙi da ke faɗa aji na ƙasar. Da yawa suna faɗin anya kuwa babu wani abu a ƙasa da ke tsakanin su A.G da Master. Dan kuwa dai kalamansu suna kamanceceniya da wanda sukai amai suka lashe abinsu.

      Master dai da duk keji da ganin komai bai sake ko tari ba. Tunda ya baje a falo dai ya duƙufa akan aikin da suma su Habib basu san na miye ba. Dan tundama suka shigo suka gaidashi duk sai suka koma ɗayan sashen inda yake kamar matsayin nasu har baba saude. Nan kuma ya zama nashine shi da iyalinshi su madam Hibbah mai zamani😜.

         Har kusan sha ɗaya na safe baiga Hibbah ta fito ba, shi kuma tunda ya fito a ɗakin bai komaba saboda busy da yayi. Sanin dalilin rashin fitowar tata ya sashi aika Habib kiranta lokacin da ya kawo masu breakfast. Tana zaune bakin gado bayan tayi wanka ta shirya harda gyara ɗakin akai knocking ƙofar. Cikin sanyin murya ta amsa tana miƙewa. Habib da ke tsaye da ga waje ya faɗa mata saƙon Master.

         Tamkar tana gabansa ta kwaɓe fuska zatai kuka. Sai dai sanin babu damar tsallake kiran yasata warware ƙaramin mayafin jallabiyar kanta ta naɗashi.

      “Good morning”.

Habib ya faɗa fuskarsa sam babu walwala. Ɗago kanta tai ta dubesa a karo na farko. Sai dai kafinma tace wani abu shi yayi gaba abinsa. Idanu taɗan rumtse tana haɗiye abinda ya zo maƙoshinta ya tsaya mai ɗaci. Sai kuma jikinta ya sake yin sanyi dan sam bataso taga mutum yana fushi da ita. Ko sadda tana gaban Ummi inhar tai laifi akai mata faɗa takan yi kuka ta manta, amma inhar taga Ummi cikin ɓacin rai da yayyenta saita kasa zaune ta kasa tsaye. Shiyyasa a yanzu ma duk ta firgice da fushin Master duk da tasan itace mai gaskiya.

          Koda ta iso falon tsaye ta iske Habib na tambayarsa a haɗa masa abinci. Batare da ya ɗago akan takardun da yake dubawa a hannunsa ba ya girgiza masa kai da faɗin, “Barshi ta zuba”.

       Kai Habib ya jinjina masa. “Okay, bayan hakan babu abinda kake buƙata kuma?”.

        Yanzun ma bai ɗago ba ya bama Habib ɗin amsa. “Da ga yanzu itace zata ringa komai anan sashin”.

       Daɗi ya ratsa zuciyar Habib. Ya ɗan juyar da kansa gefe yana murmushinsa da ya kasa ɓoyuwa. Ya haɗiye hawayen da ke neman kufce masa tare da duban Hibbah da ke tsaye tana saurarensu, dan kalaman Master ɗin ruɗar da ita sukayi. Ita dake fatan ya barta ta koma ga ahalinta ake kuma ƙirƙirarma aiki. Kallon karki sake cutarmin da ɗan uwa Habib ɗin yay mata, cikin nuna alamar rauninsa da bata dukkan amana. Batare da ya furta komai ba ya juya ya fice a falon tana binsa da kallo harya fice......

         “Amana ya baki, duk da bayada tabbacin zaki riƙe masa. Dan a farko sun baki dukkan yarda babu shakku ko ɗar game da ke, amma sai kika sauya musu tunani....”

       Master yay maganar har zuwa yanzu idanunsa da hankalinsa naga lap-top ɗin da takardun hannunsa. Idanunta dake kallon ƙofar har yanzu ta lumshe a hankali hawaye masu ɗumi suka ziraro mata. Takai tsugunne gabansa, “Nima iyayena sun yarda da kaine suka baka aure na da tabbacin bazakaci amanarsu ba amma sai kaci Yaya Master. Ka tausaya musu dan ALLAH dan Ummi na da ƴan uwana sunada rauni a kaina tamkar yanda ƴan uwankama kai ne rauninsu. Nima sune dukanin hope ɗin rayuwata. Bani da kuɗin dazan baka sama da wanda su Abba suka baka akan musu aiki. Sai dai inada kalaman roƙo da ban haƙuri a gareka kaji tausayin maraicinmu. Dan ALLAH a wannan gaɓar ka barni na koma ga ahalina su auramin wanda zuciyarsu tafi so da nake da tabbacin bazaici amanarsu ba......”

      Tunda ta fara magana bai ɗagoba bai kuma daina uzurin gabansa ba sai yanzu. Idanunsa da har yanzu suke da kalar ja ya ɗago ya zuba mata. Duk son danne ɗacin dake kan harshensa da yayi ya gaza sai da ya bayyana acikin muryarsa. “Wanene shi?”.

        A yanda yay maganar ne ya saka Hibbah ɗagowa ta kallesa cikin mamaki. Amma ganin ita ɗin yake kallo shima sai tai azamar maida kanta ƙasa cikin suɓutar baki da fashewa da kuka tace, *_“Yaya Isma'eel!”_*.

        Numfashi Master ya fesar a hankali da lumshe ido....

    Hibbah da bata san yanayi ba ta cigaba da faɗin, “Yaya Isma'il ya kasance abin alfaharinmu a tun farkon haɗuwa. Sannan shi abin so ne ga ahalina, sun so inama ace shine ya zama zaɓina tun farko, sai dai kash yazo a makare. A makaren da ka rigada kaima rayuwata kutse da yazo bisa alƙalamin ƙaddara ta, sai dai inaji zuwa yanzu a zuciyata tamkar bai makara ba. Gani gabanka gwiwa biyu ina roƙonka domin daraja da rahamar wanda ya haliccemu dan mu bauta masa, ka sawaƙemin aurenka dake kaina ka kuma maidani garesu. Sannan kayi haƙuri akan kuskuren da nai jiya gareka, nima bani da wani zaɓin da ya wuce hakan ne. Ahalina na cikin tarkon masifar ƙanin mahaifinmu, kai kuma ka kawoni nan ka ajiye kana musu aiki bayan suma burinsu ka kammala musu aikinne su ɓadda rayuwarka. Bazan tambayeka miyasa kake biye musu ba, sai dai zan sanar da kai kaima ba komai bane a garesu, lokaci suka ajiye domin ka. A zahiri dai kanada ibada da kiyaye dokokin ALLAH, amma a baɗini kana saɓa masa da babban laifi da ƙazantarsa da muninsa yasa ko'a kan harshe yake da ɗacin faɗa. Miyasa ka zaɓi saɓa masa bayan ni'imar lafiya da yay maka, ya baka ilimin addini, ya baka damar tarbiyantar da marayu, ya baka dukiyar da kake ci kake sha kake tufafi da shimfiɗa abubuwan jin daɗin rayuwa. Yayo ka a musulmi da baya barin lokutan salla biyar su wucesa sai da kuskure. Kaji tsoron ALLAH ka barsu tun kafin kai ALLAH ya barka......”

          Duk yanda yaso cigaba da abinda yakeyi hakan ya gagara, dan kalamanta ba zuciyarsa kawai suka daka ba jinin jikinsa da ɓargonsa suke daddatsawa da tsinkawa a lokaci guda. Batare da ya shirya ba bakinsa ya suɓuce wajen faɗin, “Miyasa kike tunanin Isma'il ya fini nagarta?”.

        Duk da bawai cikin lallashi ko taushi yay maganar ba sai Hibbah ta samu kanta da sakin murmushi tana ɗan dubansa. “Saboda bai taɓa cutar da mu ba. Kullum burinsa ya bama Ummi da mu kariya a wajen azzalumi Halilu. Bai taɓa tunanin rabani da Ummi na da su Yaya Muhammad ba. Kana ganin kuwa akwai sama da wannan nagartar wajen ƙayatar da yarinyar dake neman mijin aure?”.

         Shu'umin murmushi shima ya saki da maida kansa ga aikin gabansa batare da yace mata komai ba. Sai da yaja kusan mintuna uku harma ta fidda ran samun amsa sannan ya bata amsar batare da ya kalletan ba yanzun. “Duk manta da waccan nagartar ta Isma'il ɗin da tunanin mi nake aikatawar ki riƙe Muhammad Shuraim (MASTER) dan a yanzu shine ƙaddararki. Na baki damar farko da zaki iya komawa ga ahalinki amma bakici jarabawar ba saboda gaggawa da ci da zuci irin wanda ke kai rayuwar da yawan mutanenmu ƙasa. Ba ko mai ne akema TAKUN SAƘA ba. Kamar yanda bada kowa ake kafa tubalin ginin TAKUN SAƘA ba. Dakinyi juriyar bina a yanda na ɗoraki da yanzu ba wannan matsayin muke ba. Amma zan miki alfarma a karo na biyu, zakije ga ahalinki, sai dai da sharaɗin tsarabar JINI NA”.

         Hibbah da sam bata fahimci ma'anar furcin ƙarshe ba tai saurin jinjina masa kanta, “Na yarda da sharaɗinka, ko wanene jinin naka ka haɗani da shi muje wlhy baza'a taɓa cutar da shi ba koda da harara”.

        Kallonta yay cike da salon izza yana sakin wani shaiɗanin murmushi da ɗage gira sama. “Kin tabbata?!”.

      “ALLAH shine zai zama ahaidarmu”.

     Hibbah ta faɗa cikin sauri da kaguwa.

        “Da ga yanzu zuwa ko yaushe zaki iya ganin kanki gaban ahalinki da Isma'il ɗinki, amma ni minene makomar igiyoyin aure na dake kanki?”.

         “Zan tayaka addu'ar ALLAH ya baka wadda ta fini”.

       Maimakon amsa sai ya nuna mata kayan breakfast ɗin da Habib ya ajiye. Da sauri tace masa “Banajin yunwa”.

      “Nike ji ai”.

Ya bata amsa kansa tsaye. Hankalinsa nakan aikinsa. Batare da musu ba Hibbah ta haɗa masa komai gabansa tana satar kallon takardun dake barbaje a ƙasan carpet da bata san na minene ba.

        Shi dai duk da yana lure da kallon kurillar da takema takardun bai nuna ya gani ba. Sai ma turesu da yay gefe yaja abincin data haɗa masan ya hau ci hankalinsa kwance, kai kace baida wata damuwa. Sai da yasha kusan rabin cup na tea ɗin sannan ya miƙa mata. Kai ta girgiza masa batare da ta kallesa ba. Shima batare da yace komai ba ya kamo hannunta cikin nasa. Yanda yay ɗin ya tilastata ɗago idanu ta kallesa. Kofin ya ɗaura mata yana ɗan wani cizar lip da ƙanƙance idanunsa.

       Haka kawai kallon da salon nasa ya saka tsigar jikin Hibbah tashi. Babu shiri tai azamar amsar kofin shayin tana maida kanta ƙasa ta duƙar. Shima ɗauke kansa yay ya maida ga aikin da ke gabansa. Lokaci-lokaci yana amsa wayar da ita kanta batasan da su wanene ba dan maganar ma a cuɗe suke yinta.

        “Ciwonka ya daina zafi?”.

Ta faɗa cikin suɓutar baki daboda idonta daya sauka akan ƙafarsa dake harɗe ɗaya kan ɗaya tamkar wani jinin sarauta.

         Duk da ya jita bai tanka ba. Hakan yasata ɗago ido ta ɗan dubesa. Ganin gaba ɗaya hankalinsa nakan system ɗin tai tunanin baiji ba, sai ta sake maimaitawa.

      “Kin damu da ni har haka?”.

Ya faɗa batare da ya kalleta ba. Fuska ta ɓata, tare da kumbura baki ta cigaba da shan shayinta. “Daga tambaya”.

         Kallonta ya ɗanyi ya ɗauke kansa. Yanda tai maganar kamar zatai kuka ne yaso bashi dariya. Amma sai ya gimtse abarsa yamaki cewa komai. Itama bata sake cewar ba harta kammala ta ajiye kofin zata miƙe. “A ina baba Saude take zanje wajenta”.

         “Aiki zakimin nima anan”. Ya fa ɗa yana nuna mata gefensa. A marairaice ta ce, “Zanfa gaisheta ne”.

      Maimakon ya bata amsa sai ya ɗakko lap-top da ke gefensa kalar pitch ya miƙa mata fuskarsa sam babu alamar wasa. Maganarsa ta dazun da yace mata rashin haƙurinta ya hanata zuwa wajen su Ummi ne ya sata zama a inda ya nuna matan. Koda ta kunna sai taci karo da hoton yayunta a screen ɗin harda yaya Isma'il. Babu shiri ta saki tattausan murmushi tana dubansa. “Nagode sosai ALLAH ya shiryeka kabar ƙwamushe kuɗaɗen mutane”.

        Harara ya zabga mata yana sake tsuƙe fuska. A zuciyarsa kuwa kokawa yake da dariyar dake taho masa yana mamakin shegen kauɗinta. Wato tsoron jiya harya barta ta dawo normal. “Idan kikai wasa yau babu accaunt ɗin dazai kwana da ko naira acikin yayunki har Isma'il ɗin naki ma”.

        “Wayyo, dan ALLAH kayi haƙuri wlhy wasa nake maka fa. Ai kaima kaga yanzu ka zama ɗan uwanmu ko”.

         Hararar ta ya sakeyi ya ɗauke kansa. Itama sai bata sake magana ba ta ɗauke kanta tana murmushi. Dan idan yay harara ita dariya yake bata. Sai da ta kammala dai-daita komai sannan ta dubesa. “Mizanyi to?”.

         Batare da yayi magana ba ya jawo takardun gefensa ya miƙa mata, sai kuma ya ɗan matso har jikinsu na haɗuwa. matsawa ta ɗanyi kaɗan, komai baiceba ya fara nuna mata abinda zatayi.

       “Ni dai dan ALLAH karka sakani satar kuɗ...”

      Bata ƙarasa ba yasa yatsa ya ɗalli laɓɓanta. “Idan wannan baki bai daina damuna ba sai na cinyesa ALLAH”.

       Hannu tasa ta dafe bakin hawaye na ciko idanunta dan taji zafi. Shiko ya ɗauke kansa da cigaba da nuna mata ɗin kamar bai ganta ba. Sam ta manta da gargaɗinsa, yana gama faɗa cikin marairaicewa ta sake faɗin, “ALLAH bana son cutar kow.....”

          Tai saurin sake dafe bakin batare data ƙarasaba ganin yanda ya juyo. Kanta ta shiga girgiza masa idanunta na cika da ƙwalla. Lap-top ɗin da ke akan cinyarsa ya ajiye tare da juyowa gaba ɗaya. Babu shiri ta miƙe zumbur tana ajiye tata gefe tare da takardun zata gudu yasa ƙafa ya harɗota. Gaba ɗayanta ta faɗa saman cinyarsa. Ya cije baki saboda ciwonsa. Cikin daburcewa ta shiga son tashi a jikin nasa tana faɗin. “Dan ALLAH kayi haƙuri ALLAH bazan sake ba”.

        Bakin da ke maganar ya zubama lumsassun idanunsa da ke cike da mura. Sai yatsun hannunsa da ya tallafo ƙugunta har zuwa saman cikinta da yake ɗan motsawa. Zata sake yunƙurawa ta tashi ya sake nutsa hannunsa a saman cikinta dole ta koma ta sake zama tamkar zatai kuka. Kunyar duniya ta baibayeta tamkar zata halaka ta. Narkakken kallon da yake mata ya sata kai hannu zata rufe idonta dan rumtsewar ma ji take kamar bazai hanata ganin idanun nasa dake da matuƙar kaifi a gareta ba. Tana gab da kaisa saman fuskar tata ya riƙe. Da ƙarfi ta matse idanun da sake shagwaɓe fuska. “Nace fa kayi haƙuri”.

      Hannunta daya riƙo ya murza cikin nasa da wani salon da yasa jininta tsinkewa a lokaci guda. ya sake kusanto da fuskarsa gab da tata yana sake marairaice idanunsa “Ni idan akai min laifi sai na rama ai”.

       Ya faɗa cikin wata irin murya data saka Hibbah buɗe idanu ta kallesa babu shiri. Ganin fuskarsa gab da tata tai saurin sake maida idanun ta rumtse tana motsa baki alamar maganace a ciki babu damar faɗa. Fuskar tasa ya sake kusantawa da tata yana busa mata numfashinsa. Ji take tamkar ta fasa kuka dan yanayine da bata taɓa fuskanta ba a rayuwarta na kusanci da namiji irin haka. Tana ƙoƙarin buɗe idonta da son roƙonsa taji saukar laɓɓansa saman nata a bazata. Wata irin zaburar data bashi damar sake nutsata cikin ƙirjinsa ya rungume tayi. Tsabar rikicewar datai bama tasan ta saƙalo hanunta a wuyansa ba tana mintsini. Wata zazzafar ajiyar zuciya yaja yana sake narkewa bugun zuciyarsa na ƙara ƙarfi dan shima wannan shine karon farko a rayuwarsa daya tsinci kansa a irin wannan yanayin mai wahalar fassara da mantawa, daga shi har ita jikinsu rawa yakeyi, duk yanda yaso ganin yay control ɗin kansa ya barta ya kasa, sai ma sake ƙaimi yakeyi da canja salon tafiyar tasu zuwa wani abu daban.

     Firgici ya saka Hibbah fara jujjuya kanta hawaye na zirara, duk mintsinin da take masa baisa yajita ba balle ta samu kubutar da take fata da ga garesa, sai ma yazam tamkar ƙara masa ƙaimi take da mintsinin.

         Samun damar ɗaura hannunta da tai saman ciwonsa ta ɗan danna ya sashi janye jikinsa yana jan wani bahagon numfashi. Ba ƙaramin shiga tai cikin matsanancin firgici ba ganin yanda gaba ɗaya kamanninsa suka sauya mata lokaci ƙanƙani. Tai ƙoƙarin fisge jikinta da son tashi ya sake riƙota. “Na roƙeka dan ALLAH ka bari banaso, ka tausaya min karka ci amanata. Inason na cikama mahaifiyata burinta na tun farko akan auren Yaya Isma'i......”

        Ruf ya sake rufe mata bakin batare data ƙarasa ba. A Kokawar son ƙwatar kanta da take cikin rawar jiki da firgici ne ta samu damar ɗayo mask ɗin face nashi, cikin zafin nama ya kai hannu domin hanata da ƙoƙarin jan kansa baya aka samu matsala ta zareta baki ɗaya, real face ɗinsa ta Isma'il ta bayyana kanta gareta............✍


_______________________


Hi team no makeup

Ina kanawa mutanena🗣️

Shin Ina masoyan mg's ina ma'abota ado da kwalliya kusaurara kuji dame nazomuku 💃

Nasan dayawa kunsiya kayanmu Kuma kunshaida yadda suke gyaranjiki cikin lokaci kalilan Koda iyasabulun kikayi anfani dashi sekinyaba balle kankat wato beauty kit dinmu toh inamaitabbatar muku cewa ynx kayanmu ankaramasu kayayyaki Wanda zasu Kara gyara fata fiye da tsammanin Mai tunani within 2weeks zakicanza kiga duk inda kikayi se anbiki d👀 domin ynd fatanki zaikoma Shar kamar madara bawanda zemiki kallo daya yadauke idanunshi😃😍

Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?

Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki

Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘

Soap:3k

Beauty kit:12k

Chat:08062991549

07066210195

Call :07046881166

08064532391

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare

amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra'ayi🥰

Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲

Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝

Nd guest what🤩

Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃

Pamper your skin🧖‍♀️

Shine like a bride👰🏻

Glow🧚🏻‍♀️.


_________________________


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*



*_Chapter Thirty Nine_*


...........Duk da ba sanin mitake tattaunawa da zuciyarta yayi ba yaji a ransa yau ƙila har ALLAH ya isa sai tai masa. Tama nutsu ta tabbatar da shiɗin Isma'ill ɗinne ko wanine daban hakan ya gagara saboda rashin man kanta. Komai bai iya yace ba, yasa bargon kawai ya share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawan. Wayarsa ya sake ɗauka dai-dai shigowar sabon saƙo. Yasan Abdull ne dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba ya buɗe saƙon. Duk da dai sai da Abdull ɗin ya gama masa sheri irin nasa ya rubuto masa dukkan abinda ya buƙata baibi takansa ba. Kwantar da kanta yay bisa filo a ransa yanajin haushin ya akaima baiyi tunanin yin duk hakan ba, duk da dai ba fitowa fili yay wajen gayama Abdull ɗin ba, shegen bin ƙwanƙoninsu ne kawai irin na likitoci zaisa ya fahimta. Toilet ɗin ya sake komawa yay duk yanda ya rubuto masa sannan ya dawo wajen Hibbah.

     Da ƙyar ya samu ta tashi tana faman masa raki. Nokewar farko da tai saboda babu kaya a jikinta ya sashi ɗaukar rigarsa dake gefe ya saka mata. Koda ya mikar da ita azaba ta sata faɗa masa jiki ta fashe da kuka.

       Kansa ya ɗan girgiza da ɗaukarta dukanta kawai dan shi kansa wajen hutawar yake bukata. Ga tausayinta fal ransa dan shi bayason ganin mutum a damuwa dalilin sa. A banɗakin ma ba tsira yayiba. dan harda cizo ya sake sha. Ummi da su Yaya Abubakar kam sunsha kira matuƙa. Da ƙyar ya samu ya taimaka mata tayi yanda Abdull ɗin ya rubuto masa. Koda ya tambayeta batun wanka bata tankaba. Dan dama tunda suka shigo bata yarda tako kalli yatsan hannunsa ba idonta a rufe suke. Sai da yaja mata gargaɗi a kausashe sannan tayi, shi ya sake taimaka mata suka fito. Ya zaunar da ita a gefen gadon yasa karamin towel ya rage mata ruwan kanta. Gudun kar lokacin salla ya cigaba da shigewa ya sashi ɗakko mata wata doguwar rigan a kanyan da batasan a ina ya samoba. Shiya taimaka mata ta saka nan ma. Ya saka mata hijjab ɗin da faɗin, “Tashi kiyi salla”.

      Wani irin bugawa ƙirjinta yayi a karo na biyu, saboda jin da muryar da yay magana sak na yaya Isma'il. Sai dai ta dake matuƙa na hana kanta dubansa ta tada sallan cikin layin rashin ƙwarin jiki har yanzu tana hawayen. Sauƙinta ma ta ɗanji daɗin taimakon ruwan zafin da yay mata duk da sai da ya haɗa da mazurai.

        Sallar ma dai haka tayita harta kammala tana kuka. Yayinda shi kuma yake kimtsa gadon cikin mamakin abinda ya ci karo da shi. Bai daice komai ba ya naɗe zanin gadon ya hau duba wani a ɗakin kozai samu. Sai dai babu. Dole ya fito zuwa ɗayan ɗakin dake a sashen. Zanin gadon dake ajiye na gadon ɗakin ya dauka ya koma. Da kansa ya shinfiɗa cike da karfin hali. Gamawar tasa tayi dai-dai da kammalawar Hibbah sai dai ta kasa tashi a wajen.

        Duk da ya fahimci ta idar baiyi magana ba. sai ma zama da yay a bakin gadon ta gefen ta yana latsa waya. Massege ya turama Habib akan ya kawo masa abinci ya ajiye a falo. Wayar ya ajiye yana maida hankalinsa gareta. “Kin idar?”.

      Kanta kawai ta jinjina masa tana share hawayen da suka ziraro mata. Duk da ya fahimci kukan take baice komai ba ya miƙe ya fita a ɗakin. Yasha mamakin iske abincin da yasa Habib ɗin ya kawo harma da wanda baiceba. Dan harda magunguna a leda. Tambarin jikin ledar maganin ne ya sashi shan jinin jikinsa. A fili ya furta “Abdull”. Aljihun wandonsa ya ɗan laluba domin cirar wayar sai ya tuna ya barta a bedroom. Dan haka ya ɗauka abincin kawai ya koma. A inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ma ta sake haɗe kai da gwiwa.

       Komai baice mata ba har sai da ya haɗa mata abincin, cikin dakewarsa, dan ya fahimci lallaɓawar bazatai masaba, Hibbah bahaguwar mutumce kuma zuma ce sai da wuta. yace, “Tashi kici abinci”.  

         Ɗagowa tai, dan muryarsa kawai razanata takeyi a halin yanzun. batare da ta yarda ta kallesa ba cikin rawar muryar kuka tace, “Na ƙoshi, dan ALLAH ka kaini wajen Ummi na, inason na ganta”.

        Maimakon ya amsa mata sai ya miƙa mata kofin tea kawai. Ganin taƙi amsa, tamaƙi ɗagowa ta dubesa ya kamo hannunta ya ɗaura kan kofin. “Baki gaji ba kenan mu koma a ƙara”.

    Da dauri ta amshi kifin jin abinda yace, yay gajeren murmushi yana ɗauke kansa daga kallonta. Uziri ke garesa na fita, gashi babu dama baima san yanda zaiyi da ita ba. Tsoro da yunwar da takeji ga zazzaɓi yasata shanye tea ɗin akan lokaci ta ajiye kofin, komai baiceba anan ma ya ɗauka ledar maganin ya duba. Ƴar takardar da yaci karo da ita a cikin maganin ya warware ya fara karantawa. Yanda duk za'a sha maganin ne a ciki, sai ƴar tsokanar da yay masa a ƙasa wadda ta sashi sake tabbatar da zarginsa akan Abdull ɗin yana kusa da shi. Ajiyewa yay ya ciri maganin ya bama Hibbah. Babu musu ta amsa ta sha.

          “Wai nikam baza'a kalleni ba?”.

Yay maganar yana ƙoƙarin ɗago haɓarta ganin taƙi yarda koda kuskure ta dubesa. Idanunta ta rumtse hawaye suka ziraro. “Kuka dai, kuka dai babu hutu?. Bakisan yanzu ke kin girma ba ne? Kin tashi da ga autar Ummi, shalelen su yaya Muhammad. Nanda ƙanƙanin lokaci za'a fara kiranki Mamy insha ALLAH ”.

        Sake fashewa tai da kukan tana ture masa hannu da juya kanta gefe, sai hakan ya bashi dariya. Amma yay ƙoƙarin gimtsewa da faɗin. “ALLAH ya baki haƙuri tashi muje ki kwanta”. Yay maganar Yana miƙar da ita. Koda ya kwantar da ita a saman gadon shima sai ya kwanta a gefenta tare da ɗan ranƙwafowa yay mata runfa da jikinsa. Hannu yasa yana share hawayen da take zirarwa har yanzun. “Bana son kukan nan Muhibbat, kinga yana ƙara miki zazzaɓi da ciwon kai, yaya Isma'il yayi laifi. amma a yafe masa shalelen Yaya Ammar....”

        Cikin dasashshiyar muryarta ta katsesa da faɗin, “ALLAH ya kiyaye, kai ba Yaya Isma'il bane. Gara ma ka daina wannan ɓoye-ɓoyen fuskar da yaudarar mutane kana jefa rayuwarsu a haɗari kai kazo ka kwana lafiya”.

         Murmushi kawai yayi batare da ya amsata ba da sumbatar laɓɓanta ya rungumeta a jikinsa dan kansa ciwo yake masa. Tun tana jan ajiyar zuciyar kukan da take har barci ɓarawo ya saceta. Shima dai barcin ke son ɗibarsa saboda maganin da yasha. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka tafi duniyar barcin.


       Barci sukai sosai har magrib ma ta ɗan gota. kiran wayarsa da akai ne ya farkar da shi harda ma Hibbah, sai dai ita tayi luf bata nuna ta tashin ba harya janyeta a jikinsa ya ɗauka wayar. “Barka da yamma sir”.

       Ya faɗa cikin muryar barci lokacin da yake kai wayar saman kunnensa. Jin abinda wanda ya kira sir ɗin ya faɗa da ga can ya sashi miƙewa da sauri yana kallon agogon ɗakin. Kansa ya ɗan dafe ganin yanda lokacin yaja sosai harma anyi magrib. “I'm sorry sir kaina ke ciwo na ɗan kwanta ne bansan lokaci yaja ba haka”.

        Amsar da aka sake bashi da ga can ta ɗan sakashi sakin ɓoyayyen murmushi da faɗin, “No sir insha ALLAH yanzun nan zan iso ɗin ka jirani, dan ina son baka gaba ɗaya bayanan kawai kafin na ida tattara sauran gobe idan ALLAH ya kaimu.”

       Idanu Hibbah da maganganun nasa suka bama mamaki ta ɗan buɗe tana kallonsa. Gabanta ya sake faɗuwa dan still dai Yaya Isma'il take gani har yanzu, kamar yanda a murya ma dai ɗin shine. Duk da ta jima tana wasiwasi akan muryar master idan yayi magana dama batun yanzu ba. Sai dai tsakanin ɗazu zuwa yanzun muryar tasa tafi kamanceceniya data Yaya Isma'il ɗin fiye da ko yaushe. Ganin ya juyo ya dubeta bayan ya katse wayarne ya sata saurin maida idanunta ta lumshe zuciyarta na azabar bugu da sake shiga a ruɗani. Ya fahimci ta tashi. dan haka ya miƙe batare da yay magana ba ya shiga toilet a ɗan hanzarce.

         A gaggauce yay alwalar ya fito yana duban gadon. “Tashi kiyi salla”. Ya faɗa yana shinfiɗa sallaya ya tada salla. Ganin ya fara sallarne ya sata yunƙurawa ta tashi da ƙyar. Alhmdllh taji matuƙar daɗin jikinta, da alama maganin daya bata na kashe raɗaɗi da zogi ne. Sai dai jitake bakinta babu daɗi. hakama jikinta fayau kamar isaka zata ɗauketa. Sai da ta ɗan samu ta sake shiga ruwan zafi ya ratsata fiyema da ɗazun da taita raki dan batajin dai-dai a wajen har yanzun sannan ta sake samun nutsuwa, tana fitowa ta samu ya idar da sallar, motsinta yasa shi juyowa suka haɗa ido.

        Saurin maida kanta tai ƙasa hawaye na sakko mata. “Dan ALLAH ka cire fuskar nan, ni basai ka suffanta kanka da yaya Isma'il ba zanyi haƙuri har ALLAH ya kuɓutar dani da ga gareka”.

       A yanda tai maganar saita bashi tausayi da dariya. komai baice mata ba ya miƙe, har inda take tsaye yazo ya kama hannunta. Ɗayan hannunsa kuma yasa ya ɗago fuskarta tare da ɗan matso tasa gab har sunajin saukar numfashin juna. “Karki tsananta tunani, duk abinda kike buƙatar fahimta zaki tabbatar da shi nan da kwanaki biyu kacal insha ALLAH. Kiyi sallan ki sake kwanciya ki huta zan fita bazan jimaba, kukan nan kuma ya isa haka ok”. Ya ƙare maganar da sumbatar laɓɓanta.

     Komai ita dai batace ba, sai ma sake rikitata da yay. Shiko ganin yanda time ya ja ya sashi daukar wayarsa da jacket ya daura saman t-shirt ɗin jikinsa da sabon mask ya fita a ɗakin da ɗan hanzari. Takardun da ya bari a falon Habib ya tattare masa lokacin da ya kawo abinci ya ɗiba ya fito cikin zafin naman da ALLAH ya azurtashi da shi. Mota ya buɗe ya zuba kayan hannunsa sannan ya zagaya mazaunin driver. Su Habib da keta aikin da ya sakasu a sashensu sai jiyo fitarsa sukai. Basu damu ba. dan tunda safe suka fahimci jikinsa da sauƙi Alhmdllh. Sun kuma san a yanda komai ya rikice bazai zauna ya zuba ido ba. Dan tun ɗazun da yamma labari da ɗumi-ɗuminsa keta yawo a kafafen sada zumunta da gidan redio dana tv akan binciko wasu mafakar master ɗin da sirrikansa da jami'an tsaro sukayi. Harma suna iƙirarin cewar suna gab da kamashi harma da samo iyalan su A.G da ke a hannunsa.

         Sun san wanene Master ɗinsu sarai akan iya taku, duk da kuwa akwai ƙaddarar ɓacin rana da kan iya gittawa tamkar ta jiya da har yakai sun harbesa. amma basa tunanin wannan binciken da suke iƙirarin yi yana akan layin dai-dai. Dan a duk gidan da ya fahimci za'a iya ganesu cikin sauƙi idan sukai aiki sau ɗaya basa sake maimaita ko bin layinsa ma balle shigarsa. So duk inda zasu binciko sai dai ya sake sakasu a ruɗani badai a hanyar kama master ɗinsu ba.


         A ɓangaren Hibbah kam tana idar da sallar ta miƙe. So take tayi wani abu amma tasan duk hanyar da zatayin bazai bari ba sai ya toshe ta kafin ya fita. Tunda ta sha shi sau ɗaya bazaiyi sakaci na biyu ba koda da kuskure. Gadon ta sake hayewa ta kwanta da cigaba da cuɗawa da kwancewa akan wannan sabon salon da ya dauka na zuwa mata da fuskar yaya Isma'il dan yaji ta ambaci nagartarsa ga reta ga ahalinta kuma. Tun tana lissafin dai-dai har idanunta suka fara lumshewa, dan dama barcin ma ba sakinta yay ba.


★★★★


          A ɓangaren Master kuwa tafiyar da bata gaza mintuna goma sha bakwai bace ta kaisa babbar headquarter ta ƴan sandan jihar. Tunda yay horn securitys da ke a wajen suka leƙo suka gansa sai suka wangale masa ƙofar cike da girmamawa da ɗokin ganinsasuna sara masa. Ɗan salute ɗinsu yay shima yana tura hancin motar tasa ciki.

        Cike da ɗoki wasu jami'an samari biyu suma suka iso garesa dai-dai yana buɗe motar ya fito. Wellcome sir!”. Suka haɗa baki wajen faɗa. Murmushi yay musu tare da miƙa masu hannu alamar suyi musabaha. Ɗabi'arsa ce hakan tunkan yay balaguron da babu wanda yasan ina yaje, sudai sun bar ganinsa ne kawai. Hannun suka bashi suma suka gaisa. Kafinyay musu nuni da Kayayyakinsa da ke cikin motar alamar su ɗebo.

          Yayinda shi kuma yake bin ko'ina na station ɗin da kallo cike da kewa, duk da dai yakan shigo dama a sace cikin ɓadda kama.

      Duk da dare ne akwai jami'ai sosai a ciki ta kowanne department, kuma mafi yawancinsu sun duƙufa ne akan batun Master ɗin, dan shine aikin da gaba daya ya birkita kowacce hukuma daga jiya zuwa yau.

      Duk ta inda ya gitta sannu da zuwa ake masa bisa balaguron da yay na kusan shekaru biyu da rabi da girmamasa tamkar yanda shima yake bama kowa girma a rayuwarsa. A gefe kuma abokansa da manyansa na nuna jin daɗin dawowar tasa a dai-dai gaɓar daya dace. Masu kuma jin haushinsa najin takaicinsa dan mutum ne jajirtacce akan duk abinda yasa gaba tun ma yana ƙaramin ɗan sanda.

         Katafaren office ɗin da yafi kowanne girma da alfarma a headquarter ɗin ya nufa kai tsaye su Rayyan biye da shi. Tun kan ma suyi knocking aka buɗe musu ƙofar alamar ansan da zuwansa. I.G da ke zaune shi da wasu manyan ginshiƙai na hukumar ƴan sandan EFCC da General na sojoji suka maida hankalinsu ga ƙofar fuskokinsu cike da fara'ar tarbar gwarzonsu, wanda ya yarda zai sadaukar domin ƙasarsa da yankinsa bisa aikin sirri na haɗin kai da suka shirya a tsakaninsu kawai saboda tashin hankali da rikicin da kowa ya kasa gane bakin zarensa a yankunansu..........✍



_________________________


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 

*_Chapter Forty_*


..........A kallo ɗaya da sukai masa suka fahimci lallai bashi da wadataccen lafiya, dauriya da jarumtace kawai irin tasa ya sashi amsa kiran nasu. I.G da gaba ɗaya dama burinsa yaga halin da Master ɗin ke ciki dan bashi da nutsuwar zuciya akan harbin da akai masa tun jiya ya mike da sauri ya nufesa.

        Dai-dai master na karasowa garesa ya dan kame jikinsa alamar girmamawa. “Shuraim wannan gangancine ai. Shiyyasa nace maka basai kazo ba a wannan halin da kake ciki ka aiko Habib kawai”.

        Murmushi Master yay mai ciwo, cike da girmamawa a garesa ya ce. “Karka damu Uncle ina lafiya. Idan mun biyema ciwon da kawai mukeji a jiki su kuma masu ji a cikin zuciyoyinsu fa?. Tabbas inajin ciwo a jikina, dan shigar bullets a cikin jiki ba wasan yara bane, amma idan ina kwatantashi da ciwon da su waɗanda babu inda zasu kai kukansu sukeji sai naga ban cancanci raki ba”.

         I.G da ke murmushi mai ciwo ya ɗan bubbuga kafaɗar Master. Tabbas shima yanajin irin ciwon da Master ɗin keji a cikin ransa. Dan shine ma ya horesa akan wannan tsarin duk da dama shima yanada irin wannan zuciyar ta damuwa da halin da al'umma ke ciki fiye da kansa. Bin master ɗin dake ƙoƙarin isa gaban Efcc Chairman da General yay da kallo, yana jin ƙaunar yaron matuƙa a cikin ransa tun kafin randa ya gansa a wajen taron bikin gama secondary school. Kwazonsa ya sashi jin kwaɗayin biya masa kuɗin karatu.

        Master da ya juya ga General da efcc chairman duk da kuwa haɗakace ta aiki ta haɗasu dalilin I.G duk yana basu girma suma, kodan shekarunsu da ƙyaƙyƙyawar zuciyarsu. Ƙame jikinsa ya sakeyi da risinar da kansa ya ce. “Good Everning Sirs”.

            Sosai ƙwazonsa da ƙoƙarin mutunta na gaba da shi ke sake saka musu ƙaunar yaron a zuciya. Efcc Chairman ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha. Babu musu Master ya bashi dan shima yafi bukatar hakan. Shima General musabahan sukai.

           Cikin nuna kulawa suka tambayesa jikinsa? Akan harbin da ya sha. Ya tabbatar musu babu wani damuwa yaji sauƙi. Karkuma su damu tsautsayi ne kawai.

     Dukansu murmushi sukai, dan sun san dai Master ɗinsu ya faɗa soyayya da gaske. Dukansu sun san Hibbah, tun harin farko data kai masa batare da wani niyya ba I.G ya bashi shawaran aurenta, a cewarsa ba'a sakaci da irin waɗan nan yaran masu ƙwazo. Ko basu fito duniya ta sansu ba zasu taimakama mazajensu da ƙasa a gidajen aurensu. Da farko Master yaso zillewa. Sai dai kuma shiga cikin ahalinta da yay ya fahimci matsalar da suke ciki a hannun Halilu ya sashi amincewa. I.G ɗin ma da kansa suka nema masa auren nata.

        “Madam dai ta rantse sai da kasha bullets”.

        Efcc Chairman ne mai maganar cikin ƴar tsokana. Dariya sukayi gaba ɗaya, yayinda Master ya ɗan kai hannu ya shafi ƙeyarsa yana murmushi shima. A zuciyarsa kam aiyanawa yake (ai itama yau tasha nata bullets ɗin).

            Sai da suka ɗan gama barkwancinsu Master dai na tayasu da murmushi kafin su fara abinda ya tarasu. Cikin nutsuwarsa da bama aikinsa dukkan hankalinsa ya fara musu bayani akan abinda suka buƙata. Harma da wanda basu san da shi ba.

        Mamakin yanda Master ke tafida aikin da har wanda bai shafesaba ya basu. Shi dai ɗan sanda ne, ɗan sandan ma normal ɗan sanda. Sai dai a dalilin faruwar wani abu da ya shafi I.G yake ɗaurasa akan wasu ayyuka na sirri da yake yi domin hidimtama ƙasa batare da wani mahaluki ya sani ba. General abokinsa ne, hakama Efcc Chairman. Kamanceceniyar halinsu na kirki yasa akoda yaushe suke zaman tattaunawa akan abinda ya shafi yankinsu dama ƙasar baki ɗaya. Wanda suna iya bakin ƙoƙarinsu sai dai sukan rasa a ina matsalar take akoda yaushe suna tufƙawa ana warwarewa?.

      Akoda yaushe sai dai suyi zaman kawai su tashi, dan duk da kasancewarsu manya masu faɗa aji a hukumomin tsaro basu iya yin komai dake dai-dai da burikansu. Aikin da I.G ya fara ɗaura master a sirance yayi nasarane yaja ra'ayinsu gareshi har sukai kwaɗayin dinga sakashi ayyuka na musamman, duk da kuwa shi baida alaƙar aiki da su ta wani fanin. Ba yau kawai bane Master ya fara musu aiki. Yasha zaƙulo musu bara gurbi a cikin jami'ansu da manyan mutanen dake akan karagun mulki, kuma idan sukabi diddiginsu sukan samu abinda suke buƙatar.

    Bai wani jimaba tare da su saboda halin da yake ciki, sun tabbatar ƙarfin haline kawai yakeyi badan lafiya ta ishesa ba. Sallama yay musu akan zai ƙarasa sauran ayyukan da suka rage masa na tattare dukkanin bayanai na kowanne fanni nan da kwanaki biyu insha ALLAH da zasu kasa komai a fai-fai dangane dasu A.G da ire-irensa. Daga haka yay musu sallama ya fito cike da dakewa kamar yanda ya shigo. dan baya buƙatar wani ya fahimci halin da yake ciki musamman akan ciwukan harbin dake tare da shi.


★★★★


        Gudu yayi sosai akan titin, hakan yasashi isowa gidan cikin ƙanƙanin lokaci duk da kuwa ya ɗan tsaya a wani waje. Ledojin dake bayan motarsa na tsarabar su Habib ya ɗiba zuwa sashensu. Koda ya shigo suna baje a falo suna aikin da ya sasu, sai dai hakan bai hanasu shan shaftarsu ta hira ba kamar ko yaushe. Ko sallamarsa basuji ba sai da Sharifat ta nufosa da gudu tana kiran “Uncle oyoyo”.

      Tattausan murmushi ya saki a karon farko yana ajiye ledojin hanun nasa ya kai duƙe dai-dai da tsahonta yana buɗe mata hannayensa. Jikinsa ta haye tana dariya, ya lakaci hancinta shima yana murmushi da faɗin, “Beauty ɗin gidanmu batai barci ba”.

         Sharifat data makale masa kafaɗa tai yar dariyarta da kwantar da kanta kan kafaɗarsa. “Uncle ina game ne a wayan Yaya Idris”.

        “Lallai ƴar gatan Yaya Idris”.

Ya faɗa yana kaiwa zaune batare da ya kula su Habib da sukai tsitt ba tun kiran da Sharifat tai masa. Ledojin daya ajiye ma Adam ne ya miƙe ya kwasosu. Leda ɗaya ya amsa a ciki ya bama Sharifat. “Tom ga wannan maza ki cinyesa duka ki kara ƙatuwa. Kina gamawa kuma ayi brush da alwalan barci ai addu'a. Ki gaidamin baba sai da safe”.

      Cike da ɗoki ta amsa sheƙa da gudu tana faɗin, “Yeee thanks you Uncle ”.

          Hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa yana binta da kallo da murmushi harta shige. Yana son yara matuƙa tun shima yana yaron, shiyyasa a yanzu bashi da babban burin daya wuce yaga jininsa a rayuwa. Numfashi ya ɗan ja da gyara fuskarsa ya gimtse yana maido dubansa gasu Habib. A kusan tare suka haɗa baki wajen gaishesa da tambayarsa jikinsa. Cike da nazartar yanayinsu ya amsa musu dai-dai idonsa na sauka kan Habib da yaƙi yarda ya kallesa.

        Dukansu tarbiyarsa ce, dan haka ko laifi sukai masa a ƙanƙanin lokaci yake gano wanda ya aikata ɗin. Komai baice ba game da abinda ke a bakinsa ya miƙe, kai tsaye ƙofar fita ya nufa, sai da yaje gab fitar batare da ya juyo ba yace, “Habib ka sameni”. Daga haka yay ficewarsa.

         Dama tun kallon da yake binsu da shi suka sha jinin jikinsu akan an masa laifi, kowa fatansa kar yazam shine ya aikata. Jin ya ambaci Habib ya sasu maida kallonsu kansa. “Yaron nan wane ruwa ka ɓallo mana ne?”.

   Cewar Musbahu cikin ɗan tsoro. Harararsa Habib ɗin yayi yana miƙewa yabi bayan Master ɗin dan gudun sake wani laifin. Yana fita Adam yace, “Ni wlhy tun shigi da ficin danaga yanayi jiya akan waya nai tunanin hegen mai jajayen kunne wata tsiyar yake shiryawa. Sai dai banyi tunanin bahagon zaki zai ɓallo ba”.

          Salis yace, “Ni nasan laifin daya aikata, amma ku jira dai ya dawo muji a bakinsa”.

        Kansu duk suka jinjina alamar gamsuwa. Kafin su ajiye aikin gaban nasu a koma buɗe ledojin tsaraba cike da jin daɗi da farin ciki.


     Habib kam koda ya fito can ya hango master ya ɗebo sauran ledan daya bari a motan. Nufarsa yay ya amsa suka sufi sashen nasa tare. Kamar yanda yabar falon a haka ya samesa. Ya kai zaune bisa kujerar 1seater yana ɗan dafe kansa da ke masa ciwo har yanzun. Yasan akwai issue ɗin jini tattare da shi, shiyyasa ciwon kan yaƙi barinsa sam. Bayansa ya kwantar jikin kujerar da zare mask ɗin fuskarsa ya ajiye, yana daura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, razanannun idanunsa ya zuba akan Habib dake tsaye kai a ƙasa.

          “Miyasa ka aikata?”.

  Yay maganar yana dauke idonsa a kansa ya maida ga takardun dake a saman centre table ya ɗebo su yana dubawa.

          Habib da kansa ke ƙasa saboda girman laifin da ya aikata. Sanin halin yayan nasa akan buƙatar yin magana kai tsaye koda ta laifi ce, yace, “Itama taji irin raɗaɗin da kaji”.

       Master da bai ɗago ba ya sake tamke fuska da cizar lip yana cigaba da aykin gabansa

         “Yaushe na fara wasan banzan nan da kai?”.

        Shiru Habib yay yana faman haɗiyar zuciya.

  Master da yaji shiru ya ɗago ido ya dubesa fuska a tamke. “Ince da kai nake magana ko?”.

      Yanda yay maganar aɗan zafafe yasa Habib ɗin girgiza masa kai. “Yaya hakan dazan mata ne kawai zaisa na huce da ga abinda ya faru, itama kuma zata kiyaye sake yin wani yunƙuri makamancin hakan.”

        Idanu kawai Master ya zuba masa saboda mamakin Habib ɗin matuƙa. Shiko yaki yarda ya kallesa dan yasan yayi ba dai-dai ba.

        Kansa ya sake maidawa ga takardun, “Hum aure kake buƙata kenan? Ko ka fara neman mata ne?”.

        Da sauri Habib ɗin ya ɗago ya dubesa yana girgiza masa kai. “Wlhy Yaya ni ko ɗaya babu a raina. Kawai dai.....” sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba

        Takardun hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba ɗaya garesa yana sake tsuke fuska irin yanda bai taɓa gani ba. “Ƙawai dai me?. ƙarya kakeyi, idan har baka neman mata taya kasan ka sakamin pills nasha dan naje ga mace koda babu niyyar haka a gareni.”

       Habib da idanunsa suka kaɗa sukai jajur ya kai tsugunne gabansa. “Wlhy yaya ban taɓa aikata zina ba ka yarda dani, kamar yanda na faɗa maka kawai nayine dan karta sake tunanin kwatanta abinda ta aikata, sannan inason ku rayu har abada”.

      “Kai da wa kukai shawarar aikata hakan a cikinsu?”.

        “Ni kaɗai ne, dukansu babu wanda yasan abinda ya faru sai Yaya Abdull da ya bani”.

      Idanu kawai master ya zubama Habib ɗin batare da ya sake cewa komai ba. Dama ya zargi babu wanda zaiyi wannan aikin garesa sai Abdull ɗin. Tunda aka ɗaura aurensa da Hibbah kullum cikin masa tsegumi yake su baby suke so da wuri. Habib da yaji yay shiru ya ɗago ya dubesa, shi kaɗai ne ya san ainahin fuskarnan a cikinsu, dan haka bai wani damu da ganinta a yanzu ba. “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri. Nasan nayi kuskure tunma kan na aikata hakan. Inason naga kunyi zama irin na kowaɗanne ma'aurata da ita. Bana son ka rabu da ita saboda ƙyawawan halayyarta. Duk da ƙarancin shekarunta tasan kanta matuƙa kuma tanada tarbiyyar da kowanne irin nagartaccen namiji zaiso ta kasance uwar ƴaƴansa. Mu ɗin nan marayune, daga mace tagari kawai muke saran samun zuri'a mai albarka da zamu sake ginawa. Wadda zaka fara ginawa kuma itace ginshiƙin da zata riƙe tamu mu duka bakwai ɗin”.

        Harararsa Master yay, da alamar dai ya huce ya ɗauke kansa. Matsowa Habib yay jikinsa ya ɗaura kansa bisa ƙafafunsa. “Please yaya karka rabu da ita dan ALLAH, inaji a raina idan tasan kai ɗin ko wanene zata sakko ta fahimceka ku rayu tare”.

       Lumshe idanu yay bai tankaba nan ma. Shima kuma Habib bai janye kansa ba. Kusan mintuna biyu yaja ajiyar zuciya da furzar da numfashi, a hankali ya kai hannunsa bisa kan Habib ɗin ya shafa. Habib da wani farin ciki ya mamayesa ya miƙe da sauri ya rungumesa yana dariya. “Thanks you Mastern mu. I love you so much”.

        Karan farko Master ya rankwashi kan Habib ɗin yana murmushi. “Mara kunya tashi mun a jiki tunda ka sadaukar dani ai.”

     Cikin shagwaɓa Habib yace, “A'a Yaya ba duka na bataba fa. Ita rabi mu rabi.”

    Nan ma murmushi kawai yayi baice komai ba. Sai da ya miƙe batare da ya dubesa ba ya nufi hanyar bedroom ɗin da Hibbah ke ciki yana faɗin, “Kaje ka sanar musu kowa ya nemo matar aure nan da wata biyu”.

       Idanu Habib ya zaro, kafin yace wani abu Master ya shige. Wata shaƙiyyar dariya ya saki yana haɗiye sauran maganar a ransa ya juya ya fita da gudu dan kai rahoto.


      Master da ke jiyo dariyar Habib ɗin baima san murmushi ya kufce masa ba shima. Ya ɗan girgiza kai yana ƙarasawa cikin ɗakin da sallama a bakinsa. Shiru babu motsin komai alamar barci Hibbah keyi har yanzun. Ya zare jacket ɗin jikinsa yana ƙarasawa gaban gadon ya zauna ta gefenta. Babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kwanciya. Sam bayajin ƙarfi da daɗin jikinsa dauriyace kawai. Dan bashi da burin daya wuce ya tattare aikin nan ya ɗauki matarsa suje su huta. Bargon da take ciki ya ɗan janye da kai hannunsa saman goshinta. Zazzaɓin ya sauka, a yanda numfashinta ma ke fita kawai ya isa tabbatar da hakan. Yaji daɗi har cikin ransa, fasa tashinta yayi dan karya takaloma kansa wata rigimar, ya ɗauka ledar daya shigo da ita ya sake fita. Babu jimawa ya dawo ɗauke tea. Zama yay yasha tare da maganinsa. Shima yay shirin barci ya haye gadon yana sauke ajiyar zuciya............✍🏻


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 


*_Chapter Forty one_*


.............*_WASHE GARI_*


       Da asuba Hibbah ta rigashi tashi, dan cikin barci ya dinga jiyo motsinta a bayi. Tashi yay da ƙyar yana ambaton sunan ALLAH. Alhmdllhi jikin ya masa daɗi, dan magungunan da yake sha sun matuƙar taimaka masa. Koda ta fito kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shima baice komai ba ya mike zuwa bayin yayo alwala. Koda ya fito shine yaja musu sallar, yana lure da yanda Hibbah taƙi yarda ta kallesa bai nuna ya damu ba. Bayan sun idar tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙota ya zaunar a jikinsa. Kanta ta kauda gefe tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar da suka ciko mata idanu.

       Hijjab ɗin jikinta ya cire, tare da riƙo fuskar tata cikin tafin hannunsa ya juyota garesa. “Nikam wai har yanzu ba'a huceba”. Yay maganar yana ɗaura kansa bisa goshinta”.

       Duk yanda taso ƙwace fuskar tata hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda, gashi tanason yin magana amma babu dama. Ta tabbatar datayita kusancin laɓɓansu zai iya sawa ya haɗu da nasa.

       Fahimtar hakan da yayine ya sashi ɗaura laɓɓan nasa saman nata ya ɗan sumbata. Sai kuma ya janye goshinsa yana kallonta da ƙyau. Duk yanda yaso su haɗa ido ko tayi magana taƙi. Sarai ya fahimci borin kunyane kawai. Dan haka ya saketa yana murmushi.

       Zumbur kuwa ta miƙe tabar wajen, har tana cin tuntuɓe da ƙafarsa.

       “Ni dai kar amin asarar ɗan tayi na”.

      Ya faɗa cike da shaƙiyanci yana binta da kallo. Cikin tunzura baki gaba ta haye gadon taja bargo ta rufe har kanta tana ƙunƙunj. Duk da dariyar dake son kufce masa dai ya danne abinsa baiyi ba. Sai ma ya miƙe shima ya hau gadon dan barci yake son ƙarayi. Hibbah data ƙudundune waje guda tai saurin buɗe idanunta a tsorace. Zata miƙe ya riƙota yana daidaita fuskarsu waje guda. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓanta ya shiga zagayawa dashi a hankali. Tsigar jikintane ya fara tashi amma sai ta danne taƙi nunawa.

      Cikin ƙasa da murya sosai tamkar mai raɗa yace, “Mikike faɗa da banaji?”.

      Hannunsa ta ɗan ture daga bakinta tana kumbura bakin kamar zatai kuka, “Ai dai ALLAH ya sani bance komai ba”.

        Ganin zata juya masa baya tana maganar yay azamar tareta, laɓɓansa ya matsar gab da nata yana wani narke idanu, “Ni nasan kince ai”.

       Kafin ta samu damar cewa wani abu ya rufe bakin nata, cikin shauƙin dake ɗibarsa ya shiga aika mata da sumbata a nutse data saka zuciyarta shiga tsoro harta fara tsuma. Duk da yaji a yanda jikin nata ke ɓari bai saketa ba ya cigaba da abinda yake har sai da ya tabbatar tayi laushi. Hagitsatstsun idanunsa da suka kaɗai sukai jajur ya ɗago yana kallon fuskarta, idanunta dake hawayen tsoron ya sumbata da jan nannauyar ajiyar zuciya.

         “Nasan ni mai laifine a gareki ta kowacce fuska Muhibbat, sai dai inason kisani kece kika faramin laifi.”

     A karon farko Hibbah ta buɗe idanunta ta kallesa, ga hawaye shaɓe-shaɓe. Sai kuma cikin sauri ta sake maidawa ta rufe, dan batason ganin idanun nan nasa da fuskar nan ta yaya Isama'il da ya saka, ga matsananciyar kunyarsa dake matuƙar cizon ranta da ɓargo. Batare da ya damu ba ya tura yatsun hanunsa cikin gashin kanta da sake matsota jikinsa. “Inason ki nutsu a yau kisan kowanene Muhammad Shuraim (Master). Asalin sunan shine Isma'il Aliyu Hikima”.

       Cikin sauri Hibbah ta sake buɗe ido har yawu na sarƙe ta. Ganin ta miƙe zaune shima ya miƙe, ruwan dake a bedside ya ɗakko ya ɗora mata a baki. Babu musu tasha tana kallonsa tamkar idanunta zasu zubo a karon farko wajen kallonsa.

        “Tabbas Isma'il shine sunan, kuma shine a gabanki yanzu haka da fuskar zahiri bata bogi ba Muhibbat.”

      Wani irin bugawa ƙirjin Hibbah ya sakeyi. Cikin rawar jiki da son ƙin gaskatawa takai hannunta saman fuskarsa tana rumtse ido. Sake buɗe idon tai da sauri taja baya jikinta na sake ƙarfin karkarwa. “M....master kana nufin kaine Yaya Isma'il?”.

        Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta.

        “Na shiga uku ni Muhibbat wane irin rikitaccen mafarkine wannan nake a ciki?. Impossible hakan ta kasance”.

     Tai maganar tana ƙoƙarin sauka a gadon. Saurin riƙota yay ta dawo jikinsa. “Shiyyasa nace ki nutsu ki saurareni”. Ya faɗa a cikin kunnenta da wata murya mai taushi tamkar bashi ba. Batare da ya bata damar sake cewa komai ba ya cigaba da maganarsa. “Sunan mahaifina Aliyu..........” tiryan-tiryan ya cigaba da bata labarinsa tamkar yanda ya bama su Ummi. Sai kuma ya ɗora da “A farkon shigata tawagar su Master an taɓa kamamu, lokacin ina farkon shiga aji shida na sakandiri. Tunda aka kawomu police station wani babban jami'i keta kallona har kallon ya gundireni naji haushi. Fahimtar hakan da yay yasashi ɗauke kai yana murmushi. Bansan yaya akai ba bayan kamar awa guda aka fiddani ni kaɗai kuma babu wani bayani. Hakan ya tsayamin a rai, daga baya kuma saina watsar na cigaba da harkar gabana.”

        “Bayan na kammala jami'a na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya, sai naci karo da jami'in nan da yayta kallona a station, abin ya ɗauremin kai, na kuma sha mamaki amma sai na danne. Yaji daɗi ya kumayi farin ciki a take anan kuma yaymin tayin aiki saboda ganin yanda nake da matuƙar ƙwazo da kaifin basira akan harkar kimiya da fasaha. Babu musu na amsa cikin farin ciki da murna dan kuwa aiki ne na jami'an tsaro. Na miƙe cikin farin ciki zan tafi ya dakatar da ni ta hanyar faɗin, (dakata yarona ai bamu gama magana ba). Komawa nai na zauna ina basa dukkan hankalina.”

        “Yarona zaka zama jami'in ɗan sanda amma na sirri, dan haka zakai aiki kafaɗa da kafaɗa ne da mu ƴansanda amma a sirrance batare da kowa yasan wannan ba sai ni. Inada abubuwa masu yawa dake cimin rai da zuciya, sai dai ina matuƙar jin tsoro da shakku akan wanda zan ɗora yaymin. Wannan yasa a randa na fara ganinka a station naji a raina zaka iya. Hakan yasani komawa na biya maka kuɗin karatu dan a cikin idanunka na fahimci da gasken zaka iya. A yau zan sanar da kai wani abu, duk tsahon shekarun nan daka ɗauka kana karatu ina biye da kai, hatta shiga cikin ƴan daba da kakeyi wanda na fahimci kanada wani dalili duk ina sane da kai).”

       “Nayi matuƙar razana dajin zancensa. Dan haka na miƙe ina girgiza masa kai. Saurin riƙoni yayi shima yana girgizamin nasa. cikin taushin murya kuma ya shiga lallashina. (Yarona zaka iya, ni na tabbatar zaka iya insha ALLAH. Wannan Master da kake ƙarƙashinsa ko kasan gawurtaccen ɗan ta'addane da muke fako tsahon shekaru. Sai dai a bincikenmu ya nuna yana tare da manya-manyan masu faɗa ajin da ko kamashi mukai munyi a banza zai fito kamar ko yaushe. Daga ƙarshe ma wanda ya kamasan shine zai rasa aikinsa ko rayuwarsa. Jami'anmu sun halaka da yawan gaske a dalilinsa. Sai dai a yanzu haka akwai yarona a cikin yaransa shine duk ke bani bayani game da kai, dan shima ya shiga jikinsa ne domin mana cid. Inason dan ALLAH ka sanarmin miyasa ka raɓu da shi kai?).”

         “Ina ganin kima da mutuncinsa. Dan ya ƙyautata rayuwata na samu ilimi a gaɓar dana yanke ƙauna da samun hakan. Dan haka babu musu na zauna na zayyane masa koma na rasa iyayena a dalilin Master da dangin Dattijo Isma'il suka saka. Na kuma tabbatar masa da fansa zan ɗauka dan bazan bar Master ba. Har hawaye sai da yayi domin tausayina. Ya kuma tabbatarmin burina zai cika cikin sauƙi amma saina zama jami'in sirrin da yaymin tayi. Na amince a lokacin. tare da bayyana masa ainahin fuskata ta Isma'il Aliyu Hikima. Yasha amamaki kwarai da gaske, musamman da yaji cewar tun ina yaro nake ɓoye fuskata ta zahiri, bayan iyayena shine na biyu daya ganni a hakan. Hakama da yaji nike haɗa dukkan Mask ɗin wa kaina yaji daɗi ya kuma yabama fasaha ta. Domin abune daba kasafai ake samunsa anan yankunanmu ba.”

      A dalilin ganin zan iya ɓoye fuskata yace babu damuwa ma zan iya aiki kafaɗa da kafaɗa da su kamr kowane ɗan sanda a zahiri, a baɗini kuma aikin sirrinmu, sai dai zan cigaba da ɓaddabamin ɓoye ainahin fuskar Isma'il zuwa wani lokaci. Na amince da hakan. Na kuma shiga cikin tawagar horaswa da fuskar Muhammad Shuraim, cikin amincin ALLAH na fito a jerin jami'ai masu matuƙar ƙwazo. Sai dai ana kammalawa na sake ɓacewa ɓat bisa umarnin I.G. Na sake komawa cikin su Master da zuwa yanzun dukkan sirrinsa a tafin hannuna yake, dan dukkan abokan mu'amularsa a cikin manya da ƴan ta'adda irinsa na sansu nasan inda suke, nasan makamar harkokinsu. Na iya maganarsa. Na iya salon tafiyarsa na iya abubuwa da dama irin nasa wanda inhar na juye maka shi baka isa cewa bashi ɗin bane musamman idan na saka mask na fuskarsa. Indai taƙaice miki zance a wani dare batare da sanin kowaba a cikin yaran Master na ɗaukesa, zuwa safiya na maye gurbinsa, yaransa kuma duk nabi hanyoyi daban-daban aka kamasu ɗaya bayan ɗaya ta yanda babu yanda ubannin gidansu zasu iyama ganosu balle cetonsu. A gefe kuma ina aikina a zahiri tuƙuru game da dukkan abinda ya dace”.

         “Duk da kasancewana normal ɗan sanda, nayi ayyukan sirri da yawa bisa umarnin I.G ni da ɗansa Abdull da ya zama aminina tun a jami'a. Efcc Chairman da General abokaine na I.G tun ƙuruciya, hakanne yasasu sanin ayyukana a wajen I.G har suma suka fara jana jikinsu dan halayyarsu ɗaya da I.G akan ganin ƙasarmu ta dawo hayyacinta. Sai dai rashin mabiya na ƙwarai yasa basa iya tufƙa sai an warware musu. Nasha kawo musu information da yawa daya shafi ayyukansu a dalilin bincike na. Hakanne yasa a wasu lokutan nakanyi aiki kafaɗa da kafaɗa dasu tamkar yanda akasan jami'an tsaro da yawa sunkanyi hakan a sirrance a tsakaninsu. Kin shigo rayuwata a dai-dai gaɓar da nake gab da kammala tattara bayanai akan duk wasu masu hannu bisa ta'addancin Master. Naso hukuntaki, dan kin kusa ruguzamin aiki, amma sai labarin ya canja salo a dalilin I.G, shine yasa akai masa bincike akanki da ahalinki harya gano bakida wani dalili na harata tsiwace kawai da rawan kanki. Babu wani kwanakana ya bani shawarar aurenki. Ban iya cemasa komai ba dan yanada mutunci da girma a idanuna. Sai dai na dauka ɗammarar shiga jikinki nima dan tabbatarda ƙwazonki da yaketa yabawa harda kwaɗayin na aureki. Dukkan abinda su A.G sukai miki mun sani, musamman daya kasance ni suke ɗauka Master ɗinsu a halin yanzun. Muhibbat a yau na gama aikina daya shafi wancan Master ɗin, zan kuma damƙashi ga hukuma shi da su A.G, zan kuma bayyana fuskar Isma'il ma duniya, shiyyasa na fara nunata gareki bayan iyayena, baba, Habib, I.G, da kuma su Ummi. Sai dai kafin hakan inason ki sani tun randa na fara ganinki a asibiti kikaima zuciyata shigar sauri. Kece kika ruguza dukan yaƙinina akan ƙin yarda da mace, kece kika ɓata duk wani alwashina akan soyayya. Da gaske nake ina sonki”.

          Hibbah da gaba ɗaya hawaye suka gama wanke fuskarta tun fara bata tarihinsa ta matsa jikinsa da sauri ta rungumesa tare da fashewa da sabon kuka, sai kuma ta ɗago tana kai masa kananun duka a ƙirji kukan na sake kufce mata..........✍

      


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 


*_Chapter Forty Two_*


...........Har cikin ransa sai da yaji shock dan bai zaton hakan ba da ga gareta cikin sauƙi. Sai dai idan yayi dubi da tarbiyanta da yanda ta tashi za'a iya mata koda wayone da yaudara ta amince. Idanunsa ya lumshe tare da riƙe hannuwan nata yana murmushi, ya rungumeta da ƙyau shima yana jerama UBANGIJI godiya, dan jinsa yake tamkar ya sauke wasu kaya masu nauyi dake bisa kansa.

         Muhibbat da gaba ɗaya ta kasa tsaida kukanta ta sake yunƙurin barin jikin nasa.

        “I'm sorry Hibbaty”.

    Ya faɗa cikin kunnenta yana sake matseta da busa mata iskar numfashinsa cikin kunnen dake tada mata tsigar jiki..

      “Ni ka sakeni, wajen Ummina zanje, karka sake shiga sabgata kuma. Karka sake zuwa mana gida.”

         Cikin gimtse dariyarsa ya ɗagota da riƙe fuskarta cikin tafukan hannunsa. “Buɗe idanun mana ki kalli cikin nawa ki faɗa. Kefa kikace da Isma'il zaki zauna, taya kike tunanin kunnen Isma'il yaji wannan zance yay sakacin barinki kiyi nesa da shi kuma?”.

          Sake matse idanun tayi hawaye na zirarowa. Batare data iya buɗesu ba tace, “To na fasa. Yanzu bazan zauna da kai ba”.

        “Shi kuma babyna kimin yaya da shi? Dan bazaije ko ina ba a gidansu zai tashi”.

         Babu shiri ta buɗe idanun sai dai bata kallesa ba. Cikin motsawar sakarcin nata tace, “Ni yaushe naga wani babyn ka balle na rakitama kaina har yaje gidanmu”.

      Hannunsa ya ɗaura a saman cikinta yana ƙasa da shi a hankali, cikin muryar raɗa ya ce, “Gashi anan insha ALLAH, zaki gansane kema soon”.

             Hanunsa ta ture da faɗin, “ALLAH ya kiyaye”.

      “Na yanzu kam ya faru sai dai ya kiyaye na gaba kuma”. Ya bata amsa yana kwantar da ita shima ya kwanta a gefenta. Duk yanda taso tashi kuma ya hana dole ta haƙura. Sai dai ta masa shiru bata sake tankawa ba. Shima gajiya da suruntunne ya sashi rufe idanunsa da fatan samun barci.


     Koda suka tashi wajen sha ɗaya duk yanda Hibbah taso zillewa hanata yayi tare sukai wanka. Ta gama ƴan koke-kokenta na shagwaɓa ta bari. Breakfast ma tare sukayi, tanason taje gaida baba Saude ya hanata. Dole ta haƙura tanata faman sinne kai dan sam bata buƙatar su haɗa ido. Sai dai dukan motsinsa saita bisa da kallo, har yanzu zuciyarta na kaikawo akan kasancewarsa Isma'il kuma Master. Sarai yana lure da ita amma sai ya basar yanata aikinsa tana gefensa. Lokaci-lokaci yakan sakata tai masa wani aikin.

      A yau dai komai yinsa take babu musu ko tsiwa, dan idan ka ganta bazaka taɓa ɗauka Hibbahn Ummi da su Yaya Ammar bace. Haka suka kasance har yamma salla ce kawai ke tashinsu. Abinci ma da aka kawo na rana catai ta ƙoshi. Shima kuma baici ba dan bayajin daɗin bakinsa tamkar ita. Har dare bai fita ko inaba yanata aiki, sai bayan sallar isha'i ne Habib ya shigo musu da ledar kayan kwaɗayin da suka fita yawo suka siyo. Koda ya shigo falon Hibbah na kwance a doguwar kujeran da Master ke aiki kanta a saman cinyarsa. Dan ta kwanta tai filo da hanun kujerar ya taso daga inda yake zaune ya ɗagota yasa kan nata saman cinyarsa. Duk yanda taso tashi kuma bai bata fuska ba dole ta haƙura ta kwanta ƙamshin turarensa na mamaye kwanyarta a hankali. Aikinsa yake ita kuma tana kwance idanu a rufe ta lula duniyar tunani.

      Koda Habib ɗin ya shigo bayan ya amsa masa sallamar da bashi iznin shiga kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa zuciyarsa na masa wani fari fat. Kayan ya ajiye yana masa sannu da aiki.

          Amsawa yay yana ɗago idanu ya kalli ledar, sai kuma ya maida dubansa ga Habib ɗin.

         Da sauri Habib yace, “Na aunty Queen ne, sai da safe”.

       Kafin ma master yace wani abu tuni ya fice. Kansa ya ɗan girgiza da maida dubansa ga Hibbah da duk take jinsu amma tayi luf. Ganin bata motsaba komai baice ba ya cigaba da aikinsa. Sai zuwa can da yaga barci na meman dibarta ne ya ajiye aikin yana buɗe ledan. Gasashshen namane mai romo da ice-cream. Sai Haɗaɗɗun chocolates masu daɗi. Roban ice-cream ɗin ya ɗauka ya buɗe. Dan shima ma'abocin sonshi ne. Batare da yayi magana ba ya ɗiba yakai baki.

       Hibbah dake sauraren taji yace ta tashi ta hadiye yawu da ƙyar. Jin alamar ya ƙara kaiwa baki yasata buɗe idanunta da miƙewa zaune. Hannu tasa ta warce roban tana ɗan hararsa ƙasa-ƙasa da ƙunkuni.

      “Ai nidai banji ance nakaba amma ka hau kai da sha”.

         Gira ɗaya ya ɗauke yana sauke mata wani shu'umin kallo. “Naga kamar baki da ra'ayine shiyyasa nace bara na maida jinina da kika tsotse jiya da wanda kikasa bindiga ta zubarmin”.

        Baki taɗan murguɗa gefe da kai cokalin ice-cream ɗin zata sha ya kai hannu zai riƙe ta tura da sauri.

     “Humm rowa ko?”.

  Kumburarrun idanunta ta ɗan juya masa “Kai da baka da rowar ka taɓa siyamin ne?”.

       Master daya shagala a kallonta har tana saka tsigar jikinsa tashi ya ɗan waro idanu kaɗan. “Aunty Queen kiji tsoron ALLAH ban sayo miki kazan first night ba randa aka kawoki?”.

          “Kadai satoni! Kuma ni babu wata kaza daka sayamin”.

        Dariya ta bashi, amma sai ya gimtse yay murmushi kawai. “Ai ke amaryace ta musamman, shiyyasa kaiki gidan mijinki ma ya zama na musamman.”.

      Yay maganar da ɗan kwantowa jikin kafaɗarta yana wani sassanyan murmushi idanunsa akanta. Matsawa taso yi ya tura hanunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta. Cikin marairaicewa yace, “Ki sammin ko kaɗan mana, inba hakaba kuma a daren nan na ɗiba rabona a can”.

        Sam Hibbah bata fahimci a ina zai ɗiba rabon nasa ba. Dan haka ta sake juya kanta gefe tana kaiwa baki da faɗin, “Gara kaje ka ɗiba rabon naka a can amma ba nan ba”.

       Wata ƴar dariyar ƙeta yay da ɗaura hanunsa saman ƙirjinta, “Ina godiya sarauniyar gidanmu”.

     Da sauri ta ture hannunsa har tana neman sakin robar ice-cream ɗin ya riƙo da sauri. Kafin tayi wani yunkuri ya miƙe zaune sosai da fige ɗan spoon ɗin ya juya mata baya. Shaf ta manta da wanda take tare, ta ɗane bayansa cikin shagwaɓa tace, “Ummi kin gansa ko”.

       Ice-cream ɗin ya dinga ɗiba yana kaiwa baki da kakkauce mata. Itako ta maƙalƙalesa ta baya da daura kanta a saman wuyansa tana son amsa amma ta kasa. Master da ke sha da sauri-sauri ya fara ƴar dariya mara sauti da batai zaton ya iya ba. Ganin yasha kusan rabi yasata barin bayansa ta sakko da sauri a kujerar taje gabansa zata warce ya kauce ta faɗa jikinsa. Zaune tai ɗare-ɗare bisa cinyarsa. “Ni wlhy ka bani abuna, ai dai baice naka bane, nawa yace”.

       Master dake murmushi ya sake kaiwa bakinsa da ajiye robar ta gefen kanta batare data sani ba. Ta buɗe baki zata sake magana ya haɗe bakin nata da nasa ya fara juye mata ice-cream ɗin daya gama narkewa a cikin bakinsa. Bata da wata mafita saita shanyewa. Dan ganin tana son ture masa fuska ya sashin toshe mata hanci dole ta haɗiye. Koda ya saki hancin bai saki bakinba ya zarce da kissing ɗin ta. A salon da yake sumbatar natane ya sata nutsuwar dole tana amsar sakonsa. Sai da taji hannunsa cikin rigarta ne tai ƙoƙarin turesa jikinta na fara rawa.

        Matsar da bakin yay yakai saitin kunnenta yana sake rungumota da ƙyau. “Kemafa yarinyar nan na kula fitinanniya za'ai. Dan sosai jikinki ke amsar kowanne saƙo”.

        Hibbah jitai tamkar ta tsala ihu. Tai azamar wuntsilowa a jikinsa, yana son kamota ta zille da gudu tabar wajen.

         Binta da kallo yayi yana sakin murmushi da lumshe idanu.


★★★


       Hibbah bata sake jin ɗuriyar Master ba har tai shirin barci ta kwanta, zuciyarta cike da tunani da kwaɗayin ganin ahalinta. Wani gefe kuma na imagine yanda su Ummi zasuji cewar Isma'il shine master ashe, dan ita kam har yanzu zuciyarta ta kasa gaskata hakan, neman wanda zasu tattauna maganar kawai take a ranta. Dan tambayoyine fal bakinsa amma kunyarsa da nauyin daya aza mata yasa ta kasa masa ko guda ɗaya.

     Tun tana a tsorace da tunanin zai shigo har barci yay awon gaba da ita bai shigo ɗin ba. Sai kusan ƙarfe ɗaya har tamayi nisa a barci sannan ya shigo a matuƙar gajiye da tsananin bukatar barci. Yaji daɗin ganin tayi barcin, hakan na nufin ta ɗan samu ƴar nutsuwa a zuciya da jikinta daya murza a jiya. Shirin barcin yay shima da dukkan abinda yake na al'adar rayuwarsa sannan ya kwanta a gefenta.


    *_Washe gari_* tamkar jiya tare sukai sallar asuba. Hibbah dake ta faman sinne-sinnen kai ma ta gaishesa da tambayar jiinsa. Amsa mata yay da tambayarta nata jikin itama, tace ita dai lafiyarta ƙalau. Murmushi yayi kawai bai sake cewa komai ba harya kammala azkar ɗin dayay zamanyi sannan ya mike ya bita gadon. Harta fara lumshe idanu taji saukar hannunsa a jikinta. Babu shiri ta buɗe tana kai hannu zata ture nashi. Hanawa yay ta hanyar riƙe hanun nata da busa mata numfashinsa cikin kunne.

         Zatai magana yay saurin tareta da faɗin, “Shiiii bake kikace lafiyanki ƙalau ba”.

         “Da wasafa nake ALLAH akwai ciwo”. Ta faɗa da sauri tana buɗe idanunta sai gasu a cikin nasa. Duk kuma yanda taso janyewa ya sarƙesu ta gagara. Wasu mayatattun halittun fitina take gani suna yawo a cikin idanun nasa. A take nata suka fara tara ƙwallar da shi kuma suka sake ɗaga masa hankali.     

         “A ina ciwon yake?”.

Yay maganar da wata kasalalliyar muryar dake tabbatar da ɗunbin begenta dake cizonsa. Sake rikicewa Hibbah tai zata fara ja da baya yay mata runfa da jikinsa yana jan sassanyan numfashi da busa mata akan fuska. Sosai ta rikice, dan irin abinda tagani cikin idanunsa a shekaran jiya da rana yanzunma shine tattare da shi. A hankali ya ɗaura hanunsa saman nata yana sake matso da fuskarsa gab da tatan. Kai ta shiga jujjuya masa laɓɓanta na motsawa alamar son roƙonsa.

     Yasan bazai iya ɗaga mata ƙafa ba, hakan yasashi lumshe idanun nasa dai-dai yana kai laɓɓansa saman tausasan nata, dan dama dauriya kawai yakeyi harya iya ɗaga mata ƙafa da daddare. Rawar jikinta da kukan da take masa yau har yaso yafi na shekaranjiya dan wahalar data sha kawai take ƙiyastowa. Shiko da idanunsa suka rufe bida ita kawai yake ta salo-salon da baisan yama iyaba sai yanzun.


         Kuka take sosai tana lafe a jikinsa, nata jikin na ɗan rawa dan yauma ɗin dai wahalar tasha, duk da dai ta shekaranjiyan tafi ta yau sai dai ta yau ɗin ma babu sauƙi dan famine. Shiko babu abinda yake iya furtawa sai shafa bayanta zuwa gashin kanta.

     “ALLAH yay miki albarka”.

Ya faɗa a fusge yana sake turata cikin jikinsa har saida ta ɗan saka masa kuka ya sassauta mata. Sai da yaji kukan nata ya ƙi tsayawane ya mike cike da dauriya ya kaita toilet. Yau ɗin ma dai da taimakonsa ta gyara jikinta tana faman masa raki da roƙon ya kaita wajen Ummi ita dai karya kasheta.

       Sosai yaji tausayinta dan shima yasan dai yayi gaggawar koma mata duk da wahalar data sha kwana biyu da suka wuce. “Indai wajen Ummi ne zan kaiki, amma sai kin barmin kuka. Kin yarda?”.

     Da sauri ta jinjina masa kai alamar eh ta yarda. Ya sumbaci kumatunta da faɗin, “Good girl! ko ke fa. Kefa yanzun kin girma harkan yara yawane Hibbaty”.

        Da wannan daɗin bakin ya taimaka mata suka fito, koda suka sake komawa suka kwanta lafe masa tai a jiki tana jan ajiyar zuciya har barcin wahala yay awan gaba da ita cikin ƙanƙanin lokaci. Sumbata ya kaima goshinta, a ransa wani nutsuwa da kaunarta na ratsashi. Dan a yau yafi jin matuƙar nutsuwa fiye da shekaranjiya da komai yayisa ba cikin hayyacinsa ba.


        Barci sosai sukayi batare da wani ya takura musu ba. Dan su Habib ma tun safe suka bar gidan. Baba Saude kuwa da ba sanin mike faruwa tayi ba ita duk ɗaukarta ma Hibbah bata gidanne. Dan tun randa sukazo bata sake ganinta ba master ya kasa ya tsare.

      Kusan a tare suka farka. Sai dai jin motsinsa yasa Hibbah ƙin buɗe nata idon. Idanunsa ya zubama fuskarta yana ƙare mata kallo, yanda yaga idonta naɗan motsawa yasan ta tashi. Baiyi magana ba, sai yatsansa daya ɗora saman rumfar idon yana wasa da shi. Dole ta buɗe idanun da ture hannunsa tana kumbura fuska. Murmushi yayi da saƙalo hanunsa ta bayanta ya matso da fuskokinsu dab da juna yana kai mata sumbata.

       “Nifa kwana biyu naga harma kin nutsu autan Ummi”.

       Yay maganar cikin raɗa tamkar mai tsoron ajisu.

     A ranta tace, (ba dolena ba. kana min wannan muguntar nacika magana kace na maka rashin kunya ka fake da hakan ka maidani machine). A fili kam saita marairaice masa fuska tana mar-mar da idanu. “Dan ALLAH yaushe zaka kaini wajen Ummin?”.

          Yasan dama shine matsalarta. Maimakon ya bata amsa sai ya lumshe idanunsa yay shiru tamkar bai jita ba. Idanunta ta buɗe tana kallon fuskarsa har batasan ta shagala ba. Sosai yaji idanu na yawo masa a jiki, amma ya dake harda sauya saukar numfashinsa tamkar mai barci. Tunaninta barcin gaskiyarne ya ɗaukesan. A hankali takai hannu bisa girar idonsa ta ɗan gyara, sai kuma ta murza goshinsa kaɗan duk dan son ta tabbatar ba facemask ya saka ba. Sake kumawa tai kan laɓɓansa nan ma dai taji, ta cigaba da shafa kumatunsa da siririn gashi na saje ke kwance har zuwa kunnensa ta ɗan murza nan ma zuwa bayan kunnen da ƙeyarsa. Yanda take masa gaba ɗaya tsigar jikinsa miƙewa take, ganinfa da gaske neman firgita masa jiki takeyi sai da ya shammaceta ya buɗe idanunsa da suka fara sauya kala. Aiko karaf suka faɗa cikin nata. Saurin janye hannunta tai a fiskarsa amma ya riƙe ya dannesa da nasa. Gaba ɗaya ta daburce, baya ta juya masa murmushi na kufce mata dan taji kunya harga ALLAH.

           Shima murmushin ya saki da kwantowa bayanta yana son leƙa fuskarta. “Ki kalli mijinki nakine auta, yanda kike auta a gidanku insha ALLAH kece ta fari kece auta a zuciyar Shuraim ɗinki. Karkiji komai, kiyi komai ba komai baby luv”.

       Fuskar ta cusa a cikin filon, duk yanda yaso ya janye taƙi. Dole ya haƙura ya miƙe yana dariya da take mamaki. Tanaji ya shiga toilet ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Jin motsin ruwa ya sata tabbatar da wanka yake dan haka ta miƙe ta fara gyara gadon, fatanta ta fice kafin ya fito. Tana cikin gyaran takardun daya ajiye idanunta ya sauka akan wadda ke sama da tsautsayi yasa file ɗin ya ɗan goce suka zubo. Tsugunnawa tai tana tattarosu sai taga tamkar sunan Abbansu a jiki. Duk yanda taso hana kanta dubawa ta kasa, ɗaya bayan ɗaya ta dinga dubasu sai taga duk takardun kaddarorinsu ne da ta taɓa jin su Yaya Muhammad na maganar suna hannun Halilu. Mamaki ya kamata ta cigaba da dubawa har zuwa na ƙarshe da ke rubuce da dogon bayani. Ƙofar bayin ta ɗan kalla jin har yanzu akwai motsin ruwa yasata zaman dirshan ta fara karantawa a nutse..........✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


 


*_Chapter Forty Three_*


...........Bayanine tiryan-tiryan daya shafi takardun da harƙallarsu, harda kuɗaɗen daya kwashe na Halilun da yanda akai ya amshesu, da masu mallakin dukiyar da alaƙar dake tsakaninsa da su A.G. A yanzu kam Hibbah ta sake tabbatar da Master baya tare da su A.G ɗin, duk da ya mata bayanin komai ta yanda ya shiga jikin nasu da tunanin shaiɗaninsu ne shi. Wasu irin irin hawaye suka gangaro mata saman fuska zuciyarta na tunano mata randa Isma'ill ya karyama Abba ƙafa akan abinda yay ma Ummi.....

       Zare takardar da akai ta bayanta da ɗisowar ruwan wankan jikinsa ne ya sata juyowa da sauri. Master daya tamke fuskarsa matuƙa kamar bashine ya gama tarairayarta yanzun ba, ya ɗan harareta yana ɗaukar sauran takardun ya maida cikin file ɗin. Ya ajiye ya juyo kawai yaji ta faɗa masa jiki a bazata ta rungumesa da sakin wani marayan kuka. Babu shiri ya dafe towel ɗin daya ɗauro a ƙugunsa dake neman faɗuwa. Dama ba wani rigan arziƙi bane a jikin nata, hakan sai ya bashi damar jinta bisa fatarsa dake ta faman raɓar ruwa yanda ya kamata. Ya lumshe idanunsa  yana riƙota da ƙyau shima da sakin nannauyar ajiyar zuciya.

        Baice komai ba sai yatsun ɗayan hanunsa daya tura cikin gashinta, ɗaya kuma yana shafa bayanta a hankali, zuciyarsa sai wani irin zallo take da tsalle-tsalle kamar zata fito waje. Ganin kukan nata bana ƙare bane yajata suka zauna a bakin gadon tana jikinsa. Fuskarta ya ɗago dasa babban yatsansa yana share mata hawayen.

       “Miya faru kuma?”.

  “Ka yafe min”.

Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki yana ɗan ɗage gira sama, idanunsa na yawo akan fuskarta. “Ni baki min laifin komai ba”. Yay maganar yana ɗan sumbatar laɓɓanta.

       Kanta ta girgiza masa hawayen na sake rige-rigen sakkowa. “Nasan na maka laifi, na fahimceka a bai-bai, amma wlhy karkaga laifina nima inada hujjata. Nagode, ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kariya a dukkan motsinka da al'amuranka. Abinda naji wajen su Abba da shegen jami'in nan yasa nake maka kallon bai-bai. Kuma koba niba duk wanda yaji tunda baisan gaskiya ba zaiyi komai kamar nine”.

       “Na sani Muhibbat, shiyyasa naita miki uziri. Duk da kin hasalamin zuciya a ranar, dan kaɗan ya rage ki buɗemin dukanin aikina da zai iya sa harsu Ummi su rasa ransu ma. A hakanma kaɗan ya rage ki jefa rayuwarsu a haɗari, ALLAH ya taƙaita. Ina ƙaunar Ummi Muhhibat, hakama su yaya Muhammad. Bayan yaran nan da kike ganina da su a yanzu ahalinki sune ahali na biyu da nake kallo mafi kusanci dani a duniya. Tun bayan rasa mahaifiyata Ummi ce ta fara dafa kaina taimin addu'a cike da soyayya. Taya kike tunanin bazanyi yaƙi a kan zuri'arta ba. Taya bazanso haɗa jini da ita ba.” ya ɗaura hannunsa saman cikinta “Ina fata da addu'ar ALLAH yasa wannan cikin nayi ajiyar jinina da zai miki rakkiya zuwa wajen Ummina”.

       “Nidai ba yanzu ba”.

Ta faɗa tana tura baki da kwantar da kanta a kafaɗarsa.

       “Haba baby luv kiji tausayina mana, Su uncle Habib mafa shi suke jiran gani”.

        “Waɗan nan na daina kulasu a gidan nan ai, dan suma haushina sukeji”.

      Ƴar dariya yayi mara sauti da kamo hannunta ya ɗaura bisa fuskarsa. “Kefa kikai musu laifi, kika sa aka harbar musu Yayansu. Ba dole suyi fushi da ke ba. Amma nasan da sunga kin ɗan fara amai sun samu ɗa zasu daina ai”.

          Baki ta tura tana ƙara cusa kanta a wuyansa. “Ni dai nace ba yanzu ba”.

         “To ai ya riga ya shiga insha ALLAH, dan ban buga ƙwallona da wasaba tun a farkon fari”.

        Tashi tai zata bar jikinsa da faɗin, “Nidai babu ruwana wlhy inada kunya”.

         “Nima ai inada ita. Bakiga tun shekaran jiya kunyarki nake ji ba”. Yay maganar yana binta da kallo.

        Juyowa tai ta kallesa da ɗan waro idanu tana riƙe haɓa “Kai ɗinne kake wani jin kunyata?”.

       A yanda tai maganar da waro idanun da bage bakin ya bashi dariya, amma sai ya gimtse baiyiba, yay ɗan murmushi kawai da ɗage gira ɗaya. “Baki yarda kin kalleni ba yazaki gani. Idan kina son tabbatarwa zoki gani”.

     Kafinma ya rufe baki ɓurum ta faɗa toilet da sauri. Murmushin fuskarsa ne ya sake faɗaɗa. Ya miƙe domin shiryawa yana godema ALLAH da wannan farin ciki daya bashi a lokacin da bai zata ba. Harya kammala shirinsa tsaf cikin ƙananun kayan nasa na fama Hibbah bata fito ba. Yasan inhar tanajin motsinsa a ɗakin kota gama bazata fito ba. Dan haka ya tattara wayoyinsa da lap-top yayo falo.


          Tun a ƙofar fitowa yaja ya tsaya saboda cin karo da baƙon dake zaune a falon ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallo. Abdull da ya ɗan ɗago ya kallesa ya ɗauke kansa yana wani shaƙiyin murmushi. Hararsa Master yayi da cigaba da takowa cikin falon. Ya zube kayan hannunsa saman centre table ɗin da fisge remote ɗin hanun Abdull ɗin ya rage ƙarar tvn.

      “Banza ɗan nanaye ko ina ake sai an nuna hali”.

      Murmushi Abdull ɗin ya sake saki har da ƴar dariya. “Ni da kai a tantance ɗan nanaye ai ayanzun. Mutumina kafa samu lafiya da alama. Na wani tada hankalina a banza harda baro canada babu shiri”.

        “To ubanwa yace kazo mai kan gwanda kawai.”

      “Zakako cika baki yanzun tunda harbi yayi sauƙi, tsabar zalama ma ga ciwo sai da ka tafi kwaɗayi filin ball”.

            Murmushi master yayi dan Abdull ba ƙaramin tasa rayuwarsa yake gaba ba. Shima mutum ne mara son hayaniya da yawan magana, dan harma yafisa miskilanci. Amma inhar suna tare to bakin Abdull cau-cau akansa.

        “Wai yaushe ka shigo haka dan ALLAH?”.

      “Tun randa aka harbeka. Daddy (I.G) ya sanarmin naji bazan iya kwana a canada banzo naga rabin jiki ba.”

        Dariya Master yay yana gyara zama. “Shine sai yau nake ganinka, kazo kuma kanamin iskanci anan. ”

            “Tun randa kasha harbi ina gidan nan, kai ne dai kai wahalar gani saboda kana daga lungu kana tsinkar fure.”

       “ALLAH ya shiryeka to”.

Master ya faɗa yana murmushi.

       “Amin ya rabbi tunda addu'a kaimin. Ina madam ɗin tazo na ganta, dan na huce zuwa yanzu tunda nasa an rama mana harbinmu”.

         “Mara kirki, ALLAH zai saka mata ai”. Master ya faɗa yana miƙewa. Dariya Abdull yayi yana binsa da kallo, “Eh lallai ka shiga hannu ɗan gimbiya. Da alama dai ƴar shilar nan taka tauraruwa ce cikin taurari”.

        Master da ke haɗo musu coffee yay murmushi kawai batare da ya bashi amsa ba. Sai da ya kammala ya dawo falon ya ajiye a centre table ya zuba musu sannan ya zauna bayan ya mikama Abdull ɗin nasa.

      “Bestie ya yarana da madam?”.

   Abdull ya ɗan ɗage kafaɗa da faɗin, “Lafiya lau suke, sunata gaisheka.”

       “Ina amsawa, nayi kewarsu da yawa gaskiya”.

     “Karka damu suna gab da dawowa kusa da kai insha ALLAH. Ya gwagwarmaya? Daddy nata bani labarin ayyukanka da jajircewarka. ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”.

        Master dake murmushi ya kai kofin coffee ɗin bakinsa ya ɗan kurɓa. “Uncle baya gajiya da yabona, shi baya tsoron kar wataran naci amanarsa”.

    Harararsa Abdull ɗin yayi ya ɗauke kansa. Zaiyi magana Hibbah da batasan da zaman Abdull ɗin ba ta fito cikin shirin son zuwa gaida baba Saude yau. Ganin Abdull ɗin na kallon hanyar bedroom ɗinne yasa Master juyawa ya kalla wajen shima. Numfashi ya ɗan ja a hankali ganin yanda kayan sukai mata ƙyau, baiyi zatonma zasu mata ba a lokacin daya sayesu. Ganin ta ɗan daburce kamar zata juya yay mata alama da idanu tazo. Babu musu ta gyara ƙaramin gyalen data yafo saman wando da rigan parkistan ɗin ta nufosu cike da nutsuwa tamkar ba ita ba. Abdull da tuni ya ɗauke kansa da ga kallonta ya maida ga tv yace, “Amarya baƙya laifi ko kin kashe ɗan masu gida”.

        Murmushi Hibbah tai da kaiwa zaune a kujerar da ke kusa da ita. Cikin girmamawa ta shiga gaida shi. Shima amsa mata yay da kulawa yana kallon Master da ya cigaba da shan coffee ɗinsa yana saurarensu.

      “Amarya yaya kina kulamin da bestie na sosai ko?”.

      Murmushi tayi, dan gaba ɗaya jitai kunya ta dabaibayeta. Sai take ganin kamar kowa zai iya fahimtar halin da take ciki tsakaninta da Master yanzun. Shi dai Abdull ya cigaba da tsokanarta ne. Yayinda ita kuma ta kasa amsawa dan kunya. Sai da ya gaji dan kansa ya barta. Master dai bai tanka musu ba har sai da Abdull ɗin yay shiru sannan ya duba Hibbahn, saboda nutsuwar tata yay masa daɗi.

      “Muhibbah!”.

Ya kira sunanta a hankali. Ɗan ɗagowa tai ta dubesa da amsa masa. Ganin ita yake kallo ya sata sake maida kanta ƙasan.

     Ya ɗan sake kwantar da bayansa jikin kujera yana kallon nata. “Wannan sunansa Abdul-Hakim. Aminina ne kuma ɗan uwana. Likita ne a yanzu haka yana zaune a canada tare da iyalinsa da yaransa biyu”.

       Jin yayi shiru ne yasa Hibbah jinjina masa kanta. Tace, “Masha ALLAH Yaya sannu da zuwa. Ka baro su lafiya?”.

           Abdull da Hibbahr ta birge ba kamar yanda yake tunanin ganintaba yay murmushi, “A lallai na samu ƙanwa kenan. To ina godiya sosai Muhibbat. Suna lafiya, suna kuma gaisheki”.

      “Nagode ina amsawa”.

  “Nima nagode sosai da samun tarba daga gareki”.

        Kanta kawai ta jinjina masa tana miƙewa. Rasa madafar ina zata dosa ya sakata nufar kitchen, a yanda ta samu kitchen ɗin sai kawai ya birgeta taji sha'awar yin abinci a ciki. Ƙofar baya ta fita ta kitchen ɗin, wadda daga nan babu nisa da sashen su Habib. Babu wani tunani ta nufi can. Sai dai bata samu kowa ba sai baba Saude da taji daɗin ganinta. Dan sai tambayoyi take mata akan yaya take? Ina ta shiga? Yaya jikinta?.

     Hibbah da itama tai kewarta harsu Habib ɗin ma da Sharifat ta amsa mata cike da girmamawa. Daga nanne suka ɗan taɓa hira har Hibbah ta sakko zancen sonyin girkin amma ta duba a can sashen babu kayan abinci.

     Karan farko da baba Saude taji aranta kodai akwai alaƙa ta aure tsakanin Master da Hibbah ne? Kamar zata tambaya dai sai tai shiru. Sai ma sanar mata da tai cewar gama breakfast ɗinsu nan tun ɗazun take jiran shigowar su Salis sukai amma babu wanda ya shigo tun fitar safe da sukayi.

       A nutse Hibbah ta amsa mata har baba Saude na mamakin yanda ta canja mata a ƙanƙanin lokaci. Sai dai ta danne a ranta ta bita da kallo harta fice.


     Koda ta dawo sashen nasu a yanda ta fito ta kitchen da babban tray ɗin sai Abdull yay tunanin ita ta haɗo musu abincin, Master dai da kallon mamaki ya bita amma sai baiyi magana ba harta kai trayn ajiye saman centre table. Ɗan ɗagowa tai ta dubesa. “Ko akai muku dining?”.

       Tsabar mamakin daya rufesa da ƙyar ya iya kaɗa mata Kansa. Kafin ya iya motsa laɓɓa da ƙyar yace, “Nan ma yayi sannu da ƙoƙari”.

      Kanta kawai ta kaɗa masa tabar wajen, kitchen ta koma ta haɗo duk abinda zasu iya buƙata ta ɗauraye ta sake kawowa, kafin ta koma ta ɗauka ledan jiya data gani cikin fridge. Chocolates ne a ciki sai naman da ko taɓashi basuyi ba. Sai roban ice-cream guda ɗaya data rage. Chocolates ɗin ta ɗiba guda uku ta ɗauka naman ta koma sashen su Habib.

         Yanzun kam ta iske sun dawo, dan tana shiga suka haɗa baki wajen gaisheta da kiranta aunty Queen kamar yanda suka saba. Harararsu tayi itama kamar yanda ta saba ɗin, kafin takai zaune kusa da baba Saude tana ɓare ledan chocolate ɗaya ta kai baki. Koda suka cigaba da hira sunsha matuƙar mamakin yanda take amsa musu a nutse tamkar ba ita ba, hakan yasasu fahimtar dama tsiwa ce ke damun bakinta kawai badan batasan komaiba ko bata da nutsuwa ne. Habib ma tun yana ɗan basar da ita harya saki jikinsa kuma. Itako tayi mirsisi tamkar ma bataga yana fushin ba.

      

          Har akai sallar azhar Hibbah na nan tare da su Musbahu. Sallar ma a ɗakin baba Saude tayi abinta. Bayan sun idar kuma ta bita suka shiga kitchen tare sukai girki mai sauƙi. Baba Saude ta haɗa na master tamkar yanda ta saba.

      “Ɗiyata ga abincin mijinki ko”.

Tai maganar cike da son bugar cikin Hibbahr. Har ko cikin rai Hibbah taji kunyar kalmar mijin nan. Tai ƙasa da kanta cikin sabon sanyin daya saukar mata ta ce, “To baba”.

      Kafeta da idanu kawai baba Saude tai cike da mamaki fal ranta. Kenan dai hasashenta ya zama gaskiya aure ne tsakanin Master da Hibbahn. Sai taji wani farin ciki ya baibaye zuciyarta harta kasa ɓoyewa sai da ta tanka. “Oh ni ƴar nan, dama babana mijinki ne amma kuketa ɓoye-ɓoye?”.

        Da sauri Hibbah ta ɗauka trayn abincin ta fice tana murmushi. Baba Saude ta ɗaga hannu sama tana ma ALLAH godiya da wannan haɗi, dan ɗari bisa ɗari taga dacewar wannan ma'aurata. Ta kumayi farin ciki matuƙa.


         Hibbah ko data koma sashensu ta iske su Master basu dawo ba da ga salla da suka fita. A dining ta ajiye musu abincin yanzu kam, ta tattare falon da kwanikan da sukai amfani na ɗazun. Kitchen ta kai ta wanke. Tana tsaka da goge inda tai wanke-wanken taji ƙamshin turarensa.

    Jiyowa tai ta duba ƙofan dan bataji takunsa ba. Ido suka haɗa yana tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannaye a ƙirjinsa yana kallonta. Hararar sa tai kaɗan da ɗauke kanta. “Ni dai abar kallona gaskiya”.

        “Ai sadaki na na kalla”.

Ya bata amsa da ɗage gira sama duk da ba kallonsa take ba. Hibbah dake cigaba da aikinta tai murmushi kawai. Cikin son kauda zancen nasa da idanunsa dake binta da mayataccen kallo ta ce, “Ga abinci can a dining kai da baƙo”.

     Hannayensa ya warware daga ƙirjinsa ya ƙarasa takowa cikin kitchen ɗin, ta ɗan gefenta kaɗan ya tsaya tare da jingina da jikin kitchen cabinet ɗin yana kallonta. “Da gaske autar Ummi tayi hankali irin na kowace mata a gidan miji, nagode sosai da kika fiddani kunya Hibbaty”.

        Hibbah dai bata yarda ta kallesa ba, amma taji daɗin ganin yanda ya nuna jin daɗinsa akan abinda tayi badan tayi tunanin tayi dai-dai ba.....

        Katse mata tunani yay da faɗin, “Ki shirya idan mun kammala zamuje anguwa”.

        Ɗagowa tai ta dubesa cikin wani irin shauƙi da zumuɗi. “Dan ALLAH da gaske Yaya?”.

       Kansa ya jinjina mata, “Sosai ma kuwa. Ai na cancanci bada tukuyci bisa ƙyautar dana samu mai ɗunbin daraja baby luv”.

             Kafimma ya rufe baki ta nufi ƙofa da sauri zata fice. Yay azamar riƙota ganin tana neman kaiwa ƙasa dan zumuɗi.

       “oh-ouh nifa a dinga kula saboda ɗan tayina bai gama zama da ƙyau ba”.

     Ba wani fahimtar zancen ɗan tayin nan take ba, dan haka ta amsa masa da “to”, dan so take ya saketa ta tafi tai shiri. Fahimtar hakan da yay ne shima ya sashi sakin nata kawai. Amma yayi gaba ta bisa a baya. Waya suka iske Abdull nayi, dan haka Hibbah tai bedroom harda haɗawa da ɗan gudinta............✍



*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

           

    


        *_Chapter Forty Four_*


............Ba'a ƙaramin harmutse su A.G suke ba. Dan ƙaimin da suke nunawa akan neman master yasa mafi yawan al'umma maida hankali garesu da son ganin yaya za'a kwashe. A gefe kuwa sunyi zaman meeting yafi sau goma shi da su Alhajin Mande. Gaba ɗayansu sun fita hayyacinsu cikin lokaci ƙanƙani. Babu iyalai babu kuɗi. Dan ma mutane manya irinsu da suke huɗɗar arziƙi nata tura musu kuɗaɗe ana musu jaje. Hakanne ya ɗan sanya zukatansu ƙarfin ringa zaman meeting akan Master ɗin da suka kasa samun bakin zare koda guda akansa. Sai dai ga al'umma sai faman cika baki suke akan suna gab.


      Yau ma kamar kullum bayan A.G ya gama da zaman meeting ɗinsu na jami'an tsaro nan yayo gidan hutun Alhaji Mande. Inda gaba ɗayansu sun hallara ne domin tattaunawa tamkar yanda suka saba.

        A kallo guda da zaka musu zaka fahimci ɗunbin damuwar dake tattare da rayuwarsu, da yawansu hawan jini neman bugesu yake, wasu kam dama suna da shi ya motsa yana neman fin ƙarfinsu. R.D da yafi kowa jigata ya duba A.G idanu jajur dan sai da ya kora giyarsa yay mankas ko zaiji ɗan sanyi a ransa.

     “A.G ya ake ciki ne wai? Har yanzu matsiyacin nan ba'a gano inda yake a fake ba?”.

          Kai A.G ya girgiza masa, shi kansa har wata ramar dole yayi a kwana ukun nan. Cikin rauni da ɗacin murya yace, “Lamarinsa ya fara bani tsoro gaskiya. Dukan hanyoyin da muka sani ada da mafakarsa jami'anmu sun shiga amma babu alamarsa. Sannan babban abinda ke ban mamaki ko yaransa su katafila banga alamar zamuga kowa ba, idanma kunyi tunani ya jima baya barin mu haɗu dasu. Anya kuwa yaron nan ba ƙasar nan ya bari ba...”

         “Ƙasa kuma? Haba A.G ya kake wannan maganar tamkar ba jami'in tsaro ba. Tayaya zai iya ƙetare wannan ƙasar bayan bala'in da yake ciki ta ko'ina nemansa akeyi. Kadai sake wani tunanin amma ba wannan ba. Idan ma ance yabar ƙasa su kuma iyalanmu fa?”.

      “Gaskiya ne Engineer. Nima dai nafi yarda da cewar wanine ya bashi mafaka kodai a cikinmu, kokuma wanda ya sammu, danni nama fara zargin acikinmu ɗin nan akwai maiyi mana SARAN ƁOYE wlhy...”

      A harzuƙe Dr Sufi yace, “Haba Alhaji Sallau ya zakai wannan maganar haka babu daɗin ji. Shekararmu nawa tare babu wanda ya taɓa munafuntar wani sai a yanzu da muke a tsaka mai wuya. Naga yaron nan tare ya kwashe mana kuɗaɗe, yay kidnapping iyalanmu. Ta yaya za'a zargi wani kuma banda dai son zuciya!!”.

      A harzuƙe Alhaji Sallau ma yace, “Ya kakemin ihu danna faɗi gaskiya. Dan an sace iyalanmu tare an kwashe mana kuɗi sai ya zama lallai zukatanmu ɗaya. Ai wanda ma zai munafuncemu ɗin zai iya yarda a kwashi kuɗin nasa da iyalan dan ya bada ƙafa. Ya dawo cikinmu kuma yana jin sirrikanmu yanda bazamu taɓa sanin ina matsiyacin nan yake ba. Inba da saka hannun wani acikin namu ba tayaya za'ai wannan ɗan iskan yaron da muka raina da hannunmu yafi ƙarfinmu. Yanda kukasan ya mana magani muka dinga barin masa tarin kuɗi a hannunsa mun gagara cewa uwar komai ma sobada mu manyan lusarai ne.....”

      Alhajin Mande ya katsesu a tsawace da faɗin, “Kai ya isa haka dan ALLAH. Dr Sufi, Alhaji Sallau ya kamata ku barmu muji da damuwarmu. Idan hankali ya ɓata hankali ke nemosa ba wannan haukar naku ba.”

        Engineer da ransa ya ɓaci shima yace, “Faɗa musu dai dan ALLAH. Kai nifa bama irin tunaninku duk nakeyiba a yanzun. Tunanina tun a daren jiya ya karkata ne ga wata katoɓara da mukayi”.

      “Tami?”.

Cewar R.D cikin rawar jiki.

      Engineer yace, “Ta kawo Halilu cikin al'amarinmu na kwanaki. Bana raba ɗayan biyu Halilu yasan ina yaron nan yake. Kuma ko tantama babu ranar da yazo suka haɗu da shi koda ya fita bai tafi ba laɓewa yay yaji sirrinmu. Kugafa ya yashe masa accaunt shima amma bai ɗaukar masa iyalai ba. Sannan matar tasa da ƴaƴan ɗan uwansa mun aika dan a ɗauka mana su an tarar basu a gidan har wajen aikinsu. Ya kamata ku sakama wannan batun alamar tambaya. Yanda Halilu yake mayen kuɗi ace an yashe accaunt ɗinsa harda kuɗin daya ƙwallafama rai amma zuciyarsa batako bugaba. Wannan al'amari da matuƙar mamaki yake”.

       Kusan gaba ɗayansu sun nutsu suna sauraren Engineer ne. A fuskokinsu kuma zaka tabbatar da zancen nasa na shigarsu matuƙa. Alhajin Mande yace, “Wato Engineer kanka naja matuƙa. Kuma wlhy Halilu komai zai iya aikatawa akan kuɗi. Ka tuna abinda sukaima Alhaji Dauda shi da Balele. Karku manta yaranmune fa su, amma yaran nan har wani gasar sayen motoci da gina gidaje sukeyi damu. Bayan mune muka sakasu a harkar nan muka kuma jiƙasu da dukiyar da suke taƙama da ita. Lallai a nemo mana Halilu ya amsa tambayoyi”.

       A take duk suka gamsu da hakan. Babu wani ɓata lokaci A.G ya kira yaransa biyu ya aikasu gidan su Hibbah ɗakko Halilu.


(Kawunmu🤔🙆🏻😱).


★★★


       Tunda abinnan ya faru Abba baida maraba da zararre. Bashi kawai ba hatta hajiya mama da momy basa cikin hayyacinsu. Yaranma kansu hankulansu a tashe yake. Dan suma ba ƙaramin shanawa suke da dukiyarba gashi yanzu komai an yashe. Ga Junaid babu lafiya hakama Abban. Duk wani motsinsa zakaji yanata surutai da lissafin kuɗaɗe. Koda mai gyaran karaya ma ya dawo domin duba ƙafarsa data goce ranar ansha fallasa. Dan surutai yayta zubawa harda yanda ya ƙulla alaƙa da master. Hankalin su Momy ya tashi, indama ALLAH ya taimakesu dagasu sai su sai ko mai gadi daya taimaka musu suka riƙesa. Mai gyara kuwa basa tunanin ma yana fahimtar inda zantukan na Abba suka dosa. Bayan an kammala gyaran suka sallamesa da abinda ya samu. Surutan Abban ne yasa suka banka masa maganin barci. Koda ya farka kuwa sambatun yake yana kuka da faɗa musu yawan kuɗinsa da master ya yashe.

         Hajiya mama da lamarin keta sake birkita mata tunani ta kora su Momy waje ta kulle ɗakin tanama Abba tambayoyi. Bai ɓoye mata komai ba akan kuɗaɗen da yaso handamewa dan mafita yake nema yanzun. Hankalin Hajiya mama a tashe ta yarfa masa mari tana kuka. “Yanzu nan Halilu sokai ka kashemin jikoki kenan? Inda kamin bayani duk yanda zanyi kuɗin su dawo hannunmu ni ai zanyi. Koda kake ganin bana kula su Muhammadu ina sonsu kodan Aliyuna. Uwarsu ce kawai ni bana ƙauna dan bata da tsarki ƴar zina ce. Yanzu ai gashi nan mu bamuci kuɗinba wani matsiyaci ya cinye harda nakan daka tara da guminka. ALLAH wadaranka Halilu lusarin banza. Wlhy ni haihuwarka bata amfaneni da komaiba, dama kai ka mutu aka barmin Aliyuna. Dan ni dai tunda na haifoka duniyarnan banda masifu da tashin hankali babu abinda kake jangwalomin. Ga waɗannan shegun ƴaƴan naka nan riɗa-riɗa a cikin gida suna kallon kansu dai-dai damu babu aure”.

     Takaici yasa Abba saka ƙafarsa mai lafiya ya hankaɗa Hajiya mama dake kusa da shi zaune a bakin gadon ta faɗa. Wata irin wahalliyar ƙara ta saki tana dafe ƙugu dan azaba. Da gudu su Momy suka iso ƙofar sai dai kuma a rufe. Yanda Hajiya mama ke ihu da kururuwar ƙugunta yasa dole aka kira maigadi ya ɓalle ƙofar. Kafin su shigo ta haɗa gumi tayi kashirɓan dan azaba. Duk kanta suka rufu, yayinda Abba ya juya musu baya yana kwasar kukansa shima.

       Yanda take jera kalaman tsinuwa ga Halilu da gaba ɗaya zuci'arsa ne ya bama su momy mamaki suka shiga tambayarta miya faru?. Cikin kuka da azaba tai musu bayanin shine ya turota a gadon. Bakuma zata yafe masa ba. Sudai komai basu iya sunce ba. Dan sun lura Abban da Hajiya maman neman basu sabon ciwon kai suke bayan wanda suke ciki. Ga gida zagaye da jami'an tsaro an hanasu fita ko ƙofa.

     Ganin yanda hajiya maman taƙi nutsuwa ya sakasu banka mata maganin barcin itama dan bazasu iya da kwakwazonta ba. suna ganin ta tafi sukai kama-kama suka kaita ɗakinta suka zubar a gado suka fito. Abban ma maganin barcin suka ɗirka masa dansu sami lafiya.


       Wannan abu daya faru a jiyane ya saka ƙafafun Hajiya mama kumbura suntum kafin safiya, dan kuwa dai da gaske taji ciwo a ƙugunta. Hankalin su momy yaɗan tashi sai dai basu wani damuba. Dan sukam dai dama tsohuwar ta gallabi rayuwarsu da hanasu rawar gaban hantsi komai saita saka baki. Suna tsaka da jajanta yanda zasuyi da hajiya mamar sai ga yaran su A.G wai sunzo kai Abba asibiti. Jin hakane yasa su momy cewar a haɗa da hajiya mama. Da farko sunƙi yarda dan Halilu kawai akace su ɗakko. Sai dai gudun kar jami'an da aka zagaye gidan dasu su zargi wani abu tunda su ba nasu bane su duka yasa su kiran su A.G suka sanar musu. Umarnin ɗakkosu duka suka basu, dan a ganinsu ma kawo hajiya maman zaisa Halilu ya faɗi gaskiya ko bayaso ai......


______________________


      Tunda ta kammala shiryawa dan harda yin sabon wanka taketa faman leƙen falon. Ji take kamar ta kora Abdull a gidan amma babu dama. Sarai master na sane da ita amma ya basar abinsas cigaba da hirarsu shi da Abdull. Dan abincin ma basu cisa ba sai gab da la'asar. Zuwa sannan Hibbah ta cika da takaici harta koma ɗaki ta kwanta harda su kuka. Kiran sallar la'asar ne ya sata miƙewa ta ɗauro alwala. Koda master ya shigo yin alwalar shima batako kulasa ba. Shima baice mata komai ba ya shige toilet yayi abarsa yazo ya fita.

     Bayan sun dawo salla Abdull baima shigo ba shi kaɗai ya dawo ciki. Yanzun ma Hibbah na kwance a inda tai salla tana jinsa tai likimo. Komai baice mata ba ya nufi toilet bayan ya rage kayan jikinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya fito yana raɓar ruwa da alama wanka yayo.

      Fitowar tasa tayi dai-dai da miƙewar Hibbah dake faman kumbura baki na haushi. Da sauri ta juya baya saboda kallon datai masa. Shiko ko'a jikinsa ya nufi gaban mirror. Shiryawa ya farayi a nutse yana kallon duk motsinta ta cikin mirror ɗin. Harya kammala baya tunanin tako kalli sashen da yake. Sai da yazo gabanta yana baza ƙamshi cikin ɗanyar shadda getzner dake ta maiƙo da ɗaukar ido ɗinkin haf jamfa na zamani. Duk da ba wannan bane karon farko da Hibbah ta fara ganinsa cikin manyan kaya a fuskar Isma'il, sai ta samu kanta da saki baki tana kallonsa batare dama ta sani ba, dan gani take tamkar bashi baneba wanine daban.

       Ɗan duƙowa yay ya hure mata idanu. Ta shiga ƙyaƙyƙyaftasu da saurin kauda kanta zata juya masa baya. Ƙugunta ya riƙo da kamo hanunta na dama ya zuba mata link ɗin da zaisa a hannu. “Miye na juyawar bayan lada kike samu idan kina kallona madam”.

       Sake ƙasa Hibbah tai da kanta duk da yana maganar ne da ƙoƙarin ɗago fuskarta dan son su haɗa idanu amma taƙi yarda.

       “Fushi kikeyi ne?”.

Ya sake faɗa yana ɗago haɓar tata sosai duk da taƙi kallonsa. Kanta ta girgiza masa da zare hanunta daya zuba mata link ɗin a ciki. Shima komai bai sake cewa ba ya miƙa mata hannun nasa. Cikin son ɓoye kukan dake son taso mata ta ce, “To ka sakeni sai na saka maka”.

      Babu musu ya saketa, ta sauke ƴar ajiyar zuciya da fara saka masa link ɗin. “Nagode”.

    Ya faɗa a hankali yana binta da kallo. Batace komai ba ita dai. Sai da ya ɗakko ledar da taga ya ajiye a gefen gadon ya saka cikin hannunta ne ya sata ɗagowa ta dubesa. Ido suka haɗa, dan haka ta kauda nata. “Na miye?”.

      “Ki saka su ina jiranki a falo”.

Daga haka ya nufi hanyar fita ya barta da binsa da kallo. Iska ta ɗan shaƙa ta furzar tana buɗe ledar ganin ya fita. Sai kuma ta fiddo kayan cikin ledan. Lass ne mai ƙyau kusan kalar kayan jikinsa, sai mayafi babba da takalma da bag masu ƙyau suma. Mamaki ya kamata da tunanin inda ya samosu yaushe kuma ya kawosu ɗakin? Rashin amsa ga kowa yasata fara cire na jikinta ta canja. Sai ga kaya ɗas a jikinta tamkar an gwada. Ita kanta tasan tayi ƙyau koda ba'a faɗa ba, saita samu kanta da sakin murmushi. Tsaf ta shirya ta sake gyara fuskarta, ɗan kunne da sarƙan ta ɗauka a hannu bayan ta saka takalmin ta cire tarkacen takardun cikin bag ɗin ta ɗan jefa turare da ƙananun abubuwa irinsu handkerchief da ɗan Norse mask saboda tsaro.

      Master dake zaune a falon yana waya a nutse takun takalmanta yasa shi ɗago idanu ya zubama ƙofar. Ya ɗan fusgo numfashinsa da ke neman harɗewa. Duk da ba tun yau yasan kwalliya na ɗaukar jikin Hibbah ba idan tayi, sai yaga yauɗin ta zamar masa ta musamman. Dan ta fito a amryarta ne ƴar gaske abin sha'awa. Ga ƙuruciyarta ta bayyana kanta tamkar amaryar ƴan shila😜.

         Harta ƙaraso garesa baima sani ba. Daga can sai faman hello-hello wanda suke wayar ke faɗa amma bama yajinsa...

        “Yaya dan ALLAH ka samin”.

Maganarta ta katse masa tunani har yaji hello ɗin wanda suke wayar. Yanke kiran yayi yana jan ɓoyayyar ajiyar zuciya tare da miƙa mata hannunsa ta ɗora masa sarƙa da ɗan kunnen. Hannun nata ya kamo ya zaunar da ita akan cinyarsa. Hibbah ji take kamar ta nutse dan kunya. Amma dai ta daure ta dake zuciyarta. Ɗan kunnayen ya fara saka mata. Kafin sarƙar. Yanda numfashinsa keta sauka mata a jiki sai faman matse jiki take. Shi kansa kasancewar tasu a haka ba ƙaramin canja masa salon gudin jini yake ba, ya dai daure ya gyara mata sarƙan bayan ya saka da gashinta daya fito ta ƙasan ɗan kwalin kasancewar irin ɗaurin nan tayi da ake yayi.

      “Nagode”.

Ta faɗa a hankali tana miƙewa daga jikinsa. Idanunsa kawai yaɗan lumshe da jinjina mata kai shima ya miƙe. Gaba yay ta bisa a baya, su dukansu sunajin wani shauƙi a ƙasan zukatansu wanda basusan kona minene ba. Tunda suka fito compound ɗin Abdull keta ƙyalla musu hotuna dan yanda suke tafiya a jere gwanin birgewa. Daka gansu kaga ango da amarya da ke ji da tashen more lokacinsu. Master da ya harari Abdull da yaƙi daina hotunan ya buɗe ma Hibbah baya da mata nuni da ta shiga. Shigar tayi, sai da ta zauna ya ɗan ranƙwafo ya gyara mata mayafinta daya sakko sannan ya rufe. Shima shi da Abdull suka shiga.


       Su Habib dake laɓe suma sunata musu hotuna harda masu video suka shiga tafawa da juna suna dariya ganin motar ta fice. “Wayyo soyayya ruwan zuma”. Cewar Khalid yana dariya.

      Salis yace, “Bari kawai master zai ƙonemu a gidan nan. Babban yaya ashe ya iya soyayya haka kallon tara saura kwata yake mana”.

    Dariya suka sanya su duka kowa na faɗin albarkacin bakinsa cike da shaƙiyancin su. Sai dai zukatansu fal suke da tarin farin ciki dan burinsu dama suga master ɗinsu a cikin nishaɗi da farin cikin rayuwa tamkar yanda suma yake burin ganinsu akoda yaushe.........✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

      

         

        *_Chapter Forty Five_*


  ...........Tunda suka fara tafiya duk sanda Hibbah zata ɗago sai taga idon Master a kanta. Dole ta tilastama kanta daina kallon nasa ta koma sauraren hirarsa shi da Abdull dan wata sabuwar kunya yake sake haddasa mata. Sai idan Abdull ɗin ya ɗan tsokaneta ne takanyi murmushi kawai.

      Ba wata tafiya sukai mai nisa ba. Koda Abdull yay fakin bata fito ba sai da ta bari suka fara fita sannan ta fito a ƙarshe. Ɗan duban Master dake kallon agogon tsintsiyar hannunsa tayi, dan suna gab da shiga gidan ya saka mask a fuskarsa. Dai-dai ya ɗago shima suka haɗa ido. Saurin yin ƙasa tai da nata tana ɗan murza yatsun hannunta waje guda.

      Abdull dake fiddo ledoji a booth yay ƴar dariya yana kallonsu. “Mutanen nan kuna lafiya kuwa? Sai wani abu kuke tamkar wasu budurwa da saurayi”.

    Harararsa Master yayi da faɗin, “To kai banda sa ido miya kawo idanunka nan?”.

         “Ikon ALLAH, sai na rufe idanu saboda karnaga masoya”. Abdull ɗin ya faɗa yana ɗan kallon Hibbah da tai kamar bata a gurin, sai dai sarai tana jinsu. Gaba ɗaya dai hankalinta na'a kallon gidan daya gama ƙyau da haɗuwa sashe-sashe kamar wani ƙaramin estate. A kallo guda zaka fahimci sabone ko tarewa cikinsa ba'ayiba, dan wasu wajejen ma ba'a kammala ginin ba.

       Ƴan sandan dake a cikin gidan tako ina kusan su ashirin suka nufosu fuskokinsu da fara'a. Cike da girmamawa suka shiga ƙame jikinsu suna gaidasu. A yanda sukeyi ɗin zai baka tabbacin suɗin suna ƙasa da master ɗinne. 

     Ɗaya da ga cikinsu ne ya kwashi ledojin da sukazo da shi suka nufi sashen dake can  ƙarshe da alamu suka nuna an ɗan jima da kamalashi. Suna shiga cikin falon Hibbah da ke a bayan Master kirjinta yay wani irin bugawa saboda tozali da tai da Yaya Ammar ya fito da ga kitchen ɗauke da kofi yana faman danna waya dake a hannunsa. Jin takun mutane da yawa ya sashi ɗagowa duk da yasan zagaye suke da ƴan sanda a gidan tun randa aka kawosu. Shima ya wani waro idanunsa waje lokacin da idanunsa ke sauka akan Hibbahn da Master daya cire mask ya koma Isma'il ɗinsa bayan sun shigo cikin falon. Da wani uban gudu ta kwasa har tana ɗan ture Master ta nufi Ammar. Babu wani tunani a ranta ta daka tsalle ta ɗanesa da sakin wani kuka mai ban tausayi.

        Har cikin rai sai da Master yaji wani abu mai kama da kishi ya soki maƙoshinsa. Amma sai yay saurin kaudawa a ransa dan yasan dai Ammar ɗan uwanta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Fitowar Ummi dake magana cikin ɗan faɗa akan kiran da Ammar  yake ƙwala mata yasaka Hibbah saurin sakin Ammar ta nufi Ummin. Itama ɗanetan tayi tamkar zata tsaga jikinta ta koma har Ummi na neman faɗuwa.

        Da masifar ƙarfi Ammar ya shiga ƙwalama su yaya Umar kira su da matansu. Suma sai gasu ko suna sakkowa da ɗaɗɗaya daga saman Upstairs. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya harmutse. Har Hibbah tama rasa jikinwa zata kasance dan farin ciki. Sosai Master yaji tausayinta ya kamashi, dan shi kansa ya sake tabbatar da ɗunbin soyayyar dake tsakanin wannan ahali. Dan yanda Hibbah ke kuka haka su Yaya Muhammad ke faman sharar hawayen kewarta da ƙaunarta.

      Da ƙyar Ummi ta samu suka lafa dan lura da su master ɗin da tayi. wanda su kansu su Yaya Abubakar sai yanzu suka gansa. Sosai mamakin ganinsa ya kamasu, dan kewar Hibbah ya mantar da su mamakin ganinta anan ɗin duk da basusan wanene yasa aka kawosu nan ɗin ba tsahon kwanki huɗu kenan.

         “Isma'il yaya akai kuka san nan?”.

Ummi ta tambaya cikin tsaresa da idanu. A karon farko ya saki murmushi kansa a ƙasa.

      Kafin ya samu damar cewa wani abu Yaya Abubakar daya kafesa da idanu ya kira sunansa cikin alamar kowanto. Guntun murmushi kawai master yayi yana ɗauke kansa. Ganin kallon da suke masa da fahimci sauran wasiwasi a ransu ya ɗan duba Hibbah da ke naniƙe da Ummi da alamar magana ce fal bakinta, hakan yayi dai-dai da satar kallonsa datai niyyar yi batasan shima ita yake kallo ba suka haɗa ido. gargaɗi yay mata da idanu alamar ta kiyayi bakinta. Baki taɗan tura gaba da ɗauke kanta tana sake nanuƙe Ummi da ɓata fuska. 

       Master ma ɗauke nasa idon yay ya maida ga duban Yaya Abubakar dake kallonsa har yanzu yana wani ƙayataccen murmushi dake tafe da ma'anoni da yawa. Murmushin shima Master yayi ya ɗauke kansa kawai. A karon farko yay ƙaramar dariya har haƙoransa na bayyana sosai. Ya kai hannu yana shafa fuskarsa da duban Ummi cikin haɗe hannayensa waje guda🙏🏻.

        “A gafarceni Ummi, ni a haka labarin nawa yazone, nima bada son raina na ɓoye miki hakan ba. Dan kallo nake miki na uwa bayan mahaifiyata. Tun asali haka na tashi cikin ɓoyayyar rayuwa saboda samun cikar burina, sai kum yanayi ya sake ɓoyeni saboda neman martabata. Kuma Yaya Muhammad ku gafarceni yau ga auta nan na kawo muku, insha ALLAH kuma zuwa yanzu babu wani tasiri dake tare ga masu burin cutar da ita ko ku kanku. Nagode da halaccinku gareni. Nasan kunada tambayoyi fal bakinku akan kawoku da akai nan aka ajiye, karku damu insha ALLAH daga yau zuwa gobe zaku fahimci komai, dan haka a yanzu dan ALLAH kuyi haƙuri karku tambayeni komai”

     Ya riga ya gama ɗauresu tunma kafin suce komai, dan haka bakunansu suka gagara ce masa koman domin tuhuma. Sai ajiyar zuciya kawai da suke faman saukewa a jajjere. Master ya maida dubansa ga Yaya Abubakar. “Ayi haƙuri babban Yaya, inaga ya kamata ka bimu mu maidaka wajen aiki yanzun dan kafi kowa buƙatar komawar a wannan gaɓar. Yana gama faɗa ya miƙe da ɗan duban Hibbah ya ɗauke kansa yana kallon agogo.

           Dole yaya Abubakar ya miƙe shima ya fita domin kimtsawa batare da ya iya cewa komai ba tunda Master yace karsu tambayesa komai dan ALLAH. Sai dai kuma a ransa ya gama yarda Isma'il jami'in tsarone tabbas.


       A nan suka bar Hibbah da hakan yay matuƙar sakawa cikin farin ciki, hakama sauran yayunta da su Zahidah. Sai dai duk bugun cikin da suke mata akan son jin wani abu game da Isma'il tayi mirsisi. Sai ma ita dataita musu ciwon baki akan dama sun san Isma'il ne ya saceta shiyyasa sukaƙi nemanta balle damuwa da rashin ganinta. Lallaahinta su Yaya Muhammad suka dingayi. Daga ƙarshe Ammar ya bata labarin komai daya shafi Master, wanda zuwa yanzu itama duk tasan wannan harma da abinda su basu sani ba na kasancewarsa jami'in tsaro. Tana da matuƙar wayo, dan haka taki yarda tayi maganar Abba Halilu a gaban su Zahidah da abinda taji har sai da suka shiga salla ɗakin Ummi su kuma suka tafi sashensu. Wayar Ummi ta ɗauka ta turama su Yaya Muhammad massege akan idan sun dawo salla zatai magana da su a sashen Ummi.

     Suna idarwa kuwa koda suka shigo gidan kai tsaye sashen Ummin suka nufa, inda suka isketa naniƙe da Ummi tanata bata labarin su Habib da baba Saude. Ummi sai dariya take da jin daɗin autarta batai rayuwar ƙunci da damuwa ba ashe. Sai take sake ganin girma da mutuncin master a cikin idanunta da jin kaunarsa a ranta fiye da da can. Zama sukai suma suna sauraren surutun na Hibbah suna dariya, idan Ammar ya musa mata magana idan tayi yace bai yardaba su hau faɗa yana dariya da daɗa tunzurata. Sai Yaya Muhammad ya hararesa sannan ya bata haƙuri.

       Yaya Umar yace, “Auta ajiye wannan labarin naki sai anjima faɗa mana mikike son gaya mana?”.

     Kanta ta jinjina masa tana gyara zama, “Wani abu zan sanar muku akan Abba wlhy kuma da gaske nake. Ummi kindai san bana ƙarya, bakuma nayima mutun sharri dan kince ɗan aikene idan ka aika zai dawo kanka komai tsahon shekaru”.

     Ummi ta gyaɗa mata kai kawai. Hibba tace, “Yauwa Ummi ranar ɗaurin aure da yaya Muhammad ya sakani fita amsa waya............”


            Wani irin zufa ke ketoma su Ummi a jiki da kiɗima tunda Hibbah ta fara basu labari. A fuskokinsu kawai ya isa ka irga yawan tashin hankalin abinda sukeji. Dan numfashin Ummi har fita yake a sarƙe kamar mai Asthma. Hibbah dake kuka rurus itama zuwa yanzun ta faɗa jikin Ummi tana faɗin, “Ummi na tsaneshi, bana son sa, bana son sake ganinsa a rayuwata har abada. Ummi dan ALLAH karki sake zaman aure da shi, yaya kuma ku daina cemasa Abba shi ba abbanmu bane fasiki ne azzalumi mai aikata saɓon ALLAH batare da yaji kunya ba”.

        Cikin rawar murya Ammar yace, “Hibbah kin tabbatar maganar nan taki da gaske kikeyinta?”.

       “Wlhy Yaya Ammar da gake nakeyi, kama tambayi Yaya Isma'il yasan komai shima. Nama san zai sanar daku idan ya kammala abinda yake sonyi”.

       Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un suketa faman maimaitawa zufa na sake gudu a jikunansu. Yaya Usman mai ragon zuciya kam harya fara kuka dan kallon abin yake tamkar a mafarki ƙanin mahaifinsu da aikata homo duk da kasantuwarsa dattijo a yanzun. Ummi kam a take zazzaɓi mai zafi ya lulluɓeta duk da kuwa akwai wani lokaci kafin rasuwar mahaifin su Hibbah data taɓa zargin Abban da wannan ƙazantar akan abokinsa Alhaji Balele. Sai dai gudun karta aikata zato akan abinda bata da tabbas yasata kauda al'amarin ta nema tsarin ALLAH daga sheɗan. Lallai dolene rashin imaninsa ya sake ƙarfi a zuciyarsa. Dubi da yanda yake mata fyaɗe cike da cin zarafi da tozarci a gareta. Su duka babu wanda baiyi hawaye ba hatta yaya Umar mai ƙarfin zuciya, sai suka godema ALLAH ma da yaya Abubakar baya nan baiji wannan kwamacala ba. A fusace Ammar yace, “Wlhy Ummi sai mun tona musu asiri, dan barin irin waɗan nan shaiɗanun a duniya haɗarine da barazana ga matasa, musamman waɗanda suke a halin rayuwa na rashin aikinyi. Dan da kuɗi ake jan ra'ayinsu a gurɓatasu kamar yanda nake hasashen shi kansa halilun baƙin matsiyaci ya shiga”.

     Kai Ummi dake sharar hawaye ta girgiza masa. “Ammar tona masa asirinsa tamkar tona namune. Zai ma iya musawa akan hakan. Idan muka zuba ido ma ALLAH da kansa zai tona asirinsu wa duniya insha ALLAH. Sai dai ban yarda Isma'il yana cikin masu aikata wannan kwamacalarba nima Tanee. Koke kin taɓa ganin wata alamar hakan tattare da shi?”.

         Kai Hibbah ta girgiza, dan batason faɗa musu komai da Master ya sanar mata tunda ya gargaɗeta. “Ummi bana tunanin hakan gaskiya, nafi zarigin akwai dalilin da yasa yake tare da su ɗin tamkar yanda ya faɗa.....”

       “Ko kuma wancan master ɗin daya ɓoye sukema tunanin shine Yaya Isma'il ba. Anya kuwa Yaya Isma'il ba jami'in tsaro bane ba?”.

    Ammar ya faɗa yana duban su Yaya Muhammad.

        Yaya Umar yace, “Nima na fara zargin hakan Ammar, tun ma a randa yayma Junaid dukan nan nakeji a jikina jami'in tsarone ɓadda kama kawai yakeyi a cikinsu kamar”.

     “Koma dai miye muɗan sauraresa muji daga bakinsa to”. Ummi tai maganar tana share hawayen dake sakko mata na baƙin cikin halin Abba halilu har yanzun. ALLAH sarki Hajiya mama, ta ƙyamaceta akan tazo cikin ƙaddara bada aure a tsakanin iyayenta ba. Yau ga ɗan data haifa nan yana aikata aiki mafi muni da yafi wanda mahaifinta ya aikata wajen samar da ita. Haka rayuwa take, shiyyasa karka ƙyamaci abinda UBANGIJI ya ajiye bisa ALƘALAMIN ƙaddarar faɗakarwa ga wasu mutane. Kai dai kazamto mai faɗar alkairi ko kawai kayi shiru.


         Haka suka cigaba da hira gwanin sha'awa. Duk yanda sukasha cikin Hibbah akan jin wani abun mara kyau daga Master taƙi yarda ta faɗa koda da suɓutar baki. Sosai kuma ta birgesu suka sake yarda autarsu ta daɗo hankali kenan.

       Addu'a Hibbah ta dingayi kar Master ya dawo yace su koma gida, cikin amincin ALLAH kuwa sai gashi har dare babu shi babu yaya Abubakar. Taji matuƙar daɗi dan yau koba komai a bayan Umminta zata kwana...........✍



*_Chapter Forty Six_*


...........Duk da a yanayin da aka kawo su Hajiya mama ko'a jikin su A.G, sai ma wani kallonsu suke a wulaƙance. Hajiya mama dake kukan azabar da takeji a jikinta sai makyarkyata take dan kallon fuskokinsu kawai firgita rayuwarta yake.

         Abba kam duk da a yanayin da yaga su Dr Sufi ɗin sai bai kawo komai a ransa ba. Ya duba A.G yana da ga zaune inda yaransu suka zubar da shi. “A.G ya halaka rayuwata, maimakon yaymin aiki sai yayi aiki akaina. Komai ya kwashe min, naira dubu 50 kawai ya barni da shi. Ya tafi da dukkan takardun dana bashi, na rantse bazan ƙyaleshi b......”

      “Kai dalla yima mutane shiru”. Engineer ya katse Abba a harzuƙe. Ya nuna Abba da ke masa kallon mamaki. “Kai Halilu mu mun wuce kai mana wasan kwaikwayo anan. Yanzu kai ka rasa waɗanda zaka ruguza sai mu? Mune zaka cima dunduniya a garin nan bayan mune mukai maka sutura harka fito ake maka kallon mutum. Ka manta randa Balele ya kawoka nan tamkar ɗan dakon kashi. Amma bamu ƙyamaceka ba mukai maka buɗar kai da wanke duk wani datti naka da maƙudan kuɗaɗe. Shine a ƙarshe ka rasa waɗanda zaka halaka sai mu. mu zaka haɗa baki da matsiyacin yaron nan master kuci amanar mu......”

       “Ni ɗin?!!”.

Abba ya faɗa a matuƙar razane har yana fama ciwonsa. Ya dafe ƙafar yana sakin marainiyar ƙara. Cikin rawar jiki ya shiga rantsuwa da ALLAH akan shi bai san wannan magana ta Engineer ba. Dan shi a gaba ɗaya rayuwarsa ma fa sau biyu ya taɓa ganin Master ɗin nan. Zaman farko da sukai ya bashi aiki kuma tare da A.G ne. Sai zama na biyu da sukai tare da su gaba ɗaya.

        R.D ya sake katsesa da faɗin, “Kai maƙaryaci, idan har maganar daka faɗa gaskiyane yaya akai ya auri ƴar ɗan uwanka, sannan kuma matar da kake iƙirarin bakaso da manufa ka aureta ubanwaye ya sata barin gidanka ta koma wani daban? Mun kuma je can ɗaukarsu muka iske babu su a gidan”.

         Abba da zuciyarsa ta fara hawa sama matuƙa yayma R.D ɗin wani shegen kallo, dama can yasan baya sonsa batun yanzu ba. “Amma yallaɓai ya kake magana haka kamar ba'a gabanku mukai komai da yaron nan ba a ranar. Miye haɗina da Asiya dazan ɓoyeta bayan nima nemanta nake ruwa a jallo. Ni kaga ma bansan ina suka koma ɗin ba har yanzu. Haka kazalika bansan an kamasu ɗin ba ma”.

        “Ƙarya kake Halilu. Amma tunda bazaka faɗa ta arziƙi ba zaka faɗa ta yaren daya dace”. Cewar Alhaji Sallau a masife. Kafinma ya cema yaransu wani abu sun rufe Abban da duka shi da Hajiya mama. Cikin ƙanƙanin lokaci falon dama gidan baki ɗaya ya kaure da ihu da kururuwarsu. Abba da ya fahimci halakasu suke nemanyi a kiɗime ya nuna A.G. “Wlhy yasan komai, wlhy shi ya kamata ku tambaya inda master yake dan yafi kowa sanin sirrinsa anan wajen. Na tabbata da shi aka haɗa kai aka yashe mana kuɗaɗe dan nima shi naba takardun kaddarorina, kuma shine ya haɗani dashi, ta sanadinsa na sanshi”.

       A razane A.G yake duban Abba, haka su Alhajin Mande ma a rikice suke kallon A.G ɗin. “Kai munafuki, ya kake neman ƙullamin sharri. Halilu anya ƙwalwar kanka kuwa bata samu matsala ba!!”.

        “Na rantse da ALLAH kai ne”.

Abba ya sake faɗa cikin kuka wiwi. A.G da tuni zufa ta jiƙesa zaiyi magana Engineer ya katsesa cikin tafa hannu yana ƴar dariya. “Jama'a ga maganar Alhaji Sallau fa ta bayyana!”.

      “Ban gane ta bayyana ba! Mi kake nufi?”. Cewar A.G yana kallonsa hankali tashe.

        “Abinda kowa yaji a kunnensa mana A.G”. A matuƙar hargitse A.G ya miƙe ido rufe ya yarfama Engineer wani gigitaccen mari da sai da wutar kansa ta ɗauke. Abinka da jami'in tsaro yasan sirrin cin uban mutum. A razane duk suka miƙe baki buɗe. Har suna haɗa baki wajen ambatar sunan A.G ɗin. 

         A.G da gaba ɗaya ya birkice yace, “Sunana ne. Tayaya wannan mara mutuncin zai duba tsabar idona ya alaƙantani da cin amanarku. Duk iya ƙoƙarin da nake muku akan ɗan iskan yaron nan baƙwa gani har takai yau za'a kalleni da wannan suffar. In ban kashe Engineer ba kuce bani bane A.G”.

      Da sauri Alhajin Mande ya riƙosa. “Haba A.G yada harzuƙa haka daga magana. A gabanka fa Halilu yace kaine minene laifin Engineer?”.

      “Okay bakagama laifinsa ba! To yayi. Kai kuyita dukan Halilu da uwarsa har sai ya faɗi gaskiya”.

    Tamkar ƙyaftawar ido zaratan samarin suka shiga lugudar su Abba har sai da suka suma aka zuba musu ruwa suka farfaɗo. Sake cigaba da dukansu sukai kuma babu ko tausayi balle duban tsufan Hajiya mama. Ganin zasu iya mutuwa Dr Sufi yace, “Nifa ina ganin duka bashi magani, idan kuma kun kashe Halilu ta ina zamu samu wani information kenan”.

      Maganarsa ce ta saka Alhajin Mande dakatar dasu. Da ga Hajiya mama har Abba nishin azabar fitar rai kawai sukeyi. Dan tabbas sun sadaƙar yau kam zasu iya barin duniyar nan ma baki ɗaya.

     Faɗa ya cigaba a tsakaninsu dan sufa sunƙi yarda da rantsuwar da A.G ke kwarara musu akan ƙarya Abba ke masa. Shi kuma ganin sunƙi fahimtarsa ya sake birkice musu kawai har takaisa ga fara dambatawa shi da Engineer da yafi kowa zaƙewa duk da tsufansu....


_________________________


            A ɓangaren Master kam koda suka baro wajen su Ummi kai tsaye station suka nufa dan I.G ya shigo gari suna tare da C.P ma. Yaya Abubakar yayi matuƙar mamakin ganin inda sukazo, musamman daya san ana neman Isma'ill ɗinne ruwa a jallo. Sai dai kuma zargin daya jima a ransa ya sakashi yin shiru domin ganin ƙarshen wasan. Kasancewar Master bada fuskar Muhammad Shuraim yazo musu ba babu wanda yace da shi uffan. Sai dai saboda Abdull da wasu tsiraru ke gaishesu kasancewar sunsan yaron I.G ne. Sai ko shi yaya Abubakar daya haɗu da mutane biyu da ya sani.

         Dama I.G ya shigo ne saboda case ɗin dake a hannun Master ɗin, dan haka sunayin knocking aka basu iznin shiga. Yaya Abubakar da Master suka ƙame kusan a tare domin girmamawa ga I.G da C.P.

        Yaya Abubakar yay saurin juyowa ya duba Master, shima da yake shiɗin yake kallo sai ya sakar masa murmushi kawai ya ɗauke kansa ya maida ga I.G dake magana.

        “C.P wannan shine A.S.P Muhammad Shuraim Aliyu, jami'i ne mai ƙwazo, dan haka na ɗorasa akan case ɗin nan na yaron nan master a sirrance. Bakuma hakan na nufin su waɗancan da suke aiki akan hakan bazasu cigaba ba”.

        “Okay sir”.

Cewar C.P a girmame yana duban Master da ya ɗan sake ƙame jikinsa domin girmamawa ga C.P.

       “A.S.P!”.

“Yes sir”.

Master ya amsama C.P ɗin.

      “Tunda boss ya tabbatar da ƙwarewarka hundred percent muma mun yarda. Ina fatan kasan wannan aikine na gaggawa kuma mai buƙatar jajircewa. Duniya gaba ɗaya ta ɗauka burinta kawai taga Master a hannunmu, kowace hukuma ta tsaro farautarsa take domin ta kasance mai nasara. Kamar yanda wasu daga cikin jami'an mu suka tabbatar da harbinsa har sau biyu bazai kasance yayi nisa ba. Lallai-lallai yana cikin garin nan baije ko'ina ba, dan babu wata hanya da ba'a saka jami'an tsaro ba tun bayan mintuna goma sha bakwai da harbin nasa. Waɗannan mintunan kuma sunyi kaɗan ace ya fita a garin nan. Dan haka munada tabbacin yana cikin garin nan. Akwai teams da yawa dake zagaye da case ɗin nan, dan haka kaima zaka haɗa naka team ɗinne dan bama buƙatar duk waɗan can a naka operation ɗin”.

       “Yes sir!”.

Master ya sake faɗa.

     Sosai yaya Abubakar ya narke a tsaye, dan shikam yau Isma'il ya matuƙar jefa tunaninsa a garari da ruɗani. C.P ya katse masa tunani ta hanyar kiran sunansa.

      Maida hankalinsa yay ga C.P ɗin yana ƙoƙarin dai-daita yanayinsa. Shima yace, “Yes sir”.

        “Zaka taimaka masa a wannan aikin saboda na yarda da ƙwazonka matuƙa, shiyyasa mukasa ya ɗakko mana kai, dan mune muka saka aka ɓoyeku saboda information da muka samu cewar jami'an farin kaya zasuyi amfani da ku saboda ƙanwarka dake a hannun master. Kaga wannan shine amfanin sanar da abu da wuri, da baka sanar min ba da nima zan shiga tawagar masu zargin kasan master kai da ahalinka”.

        Yaya Abubakar da duk suka rikitasa ya ce, “Thanks you sir”  kawai, dan yafi buƙatar jin komai da ga bakin Isma'il, zuciyarsa ta fara raya masa Isma'il rainama su C.P hankali yake kenan suma? Kokuwa wani abu ne daban......

        I.G dake rubuce-rubece jikin takarda ya miƙama Master. “A.S.P a yau zaka dawo filin daga, sai kayi ƙoƙarin haɗa sabon team. Ga wannan file ɗin zaka samu dukan bayanan da zaka buƙata a ciki insha ALLAH”.

    Takardan da file ɗin master ya amsa da faɗin, “Thanks you sir”.

     Daga haka suka fito, Master ya sake salute ɗin I.G cike da wani salo. A waje suka bar Abdull, dan haka ya miƙe suka fice a tare magana fal bakin yaya Abubakar.

       Sai da suka fito da ga katafaren gate ɗin Yaya Abubakar da abu keta masa kaikawo a cikin rai ya duba Master.

      “Anya kuwa Isma'il baka ɓoye mana wani abu? Zuciyata ta kasa riƙe zargin da take maka a wannan gaɓar gaskiya. Dama kai jami'in tsaro ne?”.

      “Jajirtacce ma kuwa! Gwarzo abin kwatance da alfahari ga al'ummar wannan ƙasa.”

     Abdull ya bama Yaya Abubakar amsa kai tsaye yana murmushi da juya sitiyari.

        “Karka yarda da shi”.

Master ya faɗa yana duban Yaya Abubakar dake kallonsa ta mirror yana wani ƙayataccen murmushi dake tafe da ma'anoni da yawa. Murmushin shima Yaya Abubakar yayi a karon farko ya ɗauke kansa yana jinjinawa. “Dama na jima ina wannan zarigin a raina, a randa aka kaimu gidan can kuma na sake tabbatarwa. Jira da sauraren zuwanka kawai nake dama ai. Amma abinda ban fahimtaba anan shine, suma su I.G basusan kaike basaja matsayin master ba kenan?”.

         Shiru Master yay tamkar bazai amsa ba. Sai kuma yay murmushi da kai hannu ya zare mask ɗin fuskarsa. Yaja tissue ya goge real face ɗinsa yana furzar da huci. “Ɗan uwana nake kallonka, dan tunda har kasan wanene Isma'il wannan ma zan iya sanar maka saboda a ƙarshen tattare aikin nan nake bana son abinda zai maidani baya kodan Muhibbat.” ya ƙare maganar da ɗaga idanunsa suka kalli juna da Yaya Abubakar. Murmushi sukayi a tare, master ya sake ɗauke idanunsa. “I.G yasan komai, C.P ne bai saniba.”

        Ko tari kasayi yaya Abubakar yay. dan kuwa a yau ɗinnan ya sake tabbatar da zancen nan na mutane dake kiran Master ɗin Hatsabibi duk da su ɗin bama su gama sanin wanene shi ba. Abdull dake saurarensu yay ƙaramar dariya yana ɗan duban Yaya Abubakar ɗin ta mirror shima. “Yayanmu ai mana afuwa. Wannan surikin naka baida maraba da aljanin kan kuka mai leƙa gidan kowa. Sai kun haɗa da addu'a gaskiya”.

        Mangare masa ƙeya Master yayi, hakan yasasu kwashewa da dariya su duka dan Abdull sitiyarin ya saki sai da Master ya riƙe da sauri. Har yana magana cikin suɓutar baki.

      “Kai ɗan iska karka zubar damu wlhy ban gama angwanci ba, Baby luv na buƙatata a kusa da ita”.

      Abdull ya tsaida motar yana kwasar dariya. Yaya Abubakar ma dai dariyar yakeyi, ransa fal farin ciki duk da sun jima da fahimtar irin son da Isma'il ɗin kema autarsu.. Master ya harari Abdull yana ƙumshe tasa dariyar dan harga ALLAH suɓutar bakice. Cikin borin kunya yace, “Ɗan haɗa gurmi in bazaka tada motarba zamu fita mu barka dan munada abunyi”.

         “A'a miyay zafi na Baby luv. Bara na kaiku nikam kafin ka ƙonemu a titi. Shiru Master yay bai sake tanka masa ba. Yaya Abubakar ma dai sai ya saki zancen ya cigaba da duba file ɗin da I.G ya bama Master ɗin har suka kaisa station ɗin da yake aiki suka ajiyesa bayan Master yay masa bayanin shine zai haɗa musu team ɗin, shi kuma zaije ya ƙarasa tattare abinda ya rage daga nan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu zasu fita operation ɗin. Cike da gamsuwa Yaya Abubakar ya basu hannu sukai musabaha sannan ya fita.


       Daga nan gida suka wuce suma. Inda su Habib suke jiran dawowar master ɗin dan tun a jiya ya sanar musu yau ɗin ranar aiki ce da ga nan har zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu............✍


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*


        *_Typing📲_*


_______________________


*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*


_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya💃🏻._


*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu😂💃🏻*.


_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za'a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya😉💃🏻_.


*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻


Kaza akwai 10k

15k

5k

Tsimi 5k 10k

Matsi 5k

Gumba uku 2k

Zumar gorun tula syrup3k

Garuka 3k

Cicccibi 5k

Zakara 20k

Zabo20k

Humra

Turaren tsugunni

Butar tsarki

Maganin infection

Tsimin tabaje

Turaren al,ajab


*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.



_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_

08068526455


*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*


Zaku iya samun mu amanhajar


Facebook

Istagram


Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.


Sai kunzo🥰🥰🥰🥰💃🏻👌🏻.


_____________________


*_Chapter Forty Seven_*


..........Su Hibbah na baje a falo suna kwasar hira ita da su Zahidah dake ta mata sheri itama cikine da ita, dan ta matsa musu tunda ta ƙyalla ido taga cikunna a jikinsu. Shinefa suma suka tasata gaba da nasu tsokanar Ammar na tayasu da dariya wai wayaga auta da ɗa. Tun tana kai ƙararsa wajen su Yaya Umar harta koma jifansa da throw pillows tana kukan taɓara.

         Hatta Ummi kasa daurewa tai saida tai dariya dan taɓarar autar tata sai ita. Kiran da yaya Abubakar yayma Ummi ne ya sanar mata bazai kwana a gida ba ya sakasu barin Hibbah ɗin suka koma hirar rashin dawowar Master shima. Suna cikin zancen kuma sai ga ɗan halak ɗin ya kira Ummi shima ya sanar mata Hibbah zata kwana anan shi wani uziri ya riƙesu tare da yaya Abubakar. Addu'a tai musu na fatan alkairi baki ɗaya.

      Yana katse kiran kuma ya kira Ammar yace ya haɗasa da Hibbah. Amma ya jata gefe dan yasan halin kayarsa. Da ƙyar Ammar ya danne dariyarsa ya kama hannun Hibbah suka nufi bedroom ɗin Ummi.

      Zatai magana ya manna mata wayar a kunnenta ya fice. Hibbah dake hararar Ammar dake mata gwalo zai fice tace, “Mai kan gwanda kawai”.

         “Nine mai kan gwandan?”.

Sassanyar muryarsa ta daki dodon kunnenta a bazata. Dan tama manta waya Ammar ya saka mata a kunne. Idanu taɗan waro tamkar tana gabansa. “ALLAH shine shaida ni dai bada kai nake ba da yaya Ammar nake”.

        Master dake goge jikinsa dake raɓar ruwan wanka da ga can yay murmushi yana ɗan lumshe ido. “Ki shirya ganinan zuwa zan ɗaukeki”.

       Kamar tana gabansa ta marairaice fuska. “Dan ALLAH ka barni na kawana wajen Ummi”.

      “Idan na barki ni kuma na kwana da wa?”.

     Ƙasa-ƙasa batare da tunanin zaiji ba ta ce, “To da dawa kake kwana?”.

“Okay hakama zakice, to nama fasa barin ki shirya kawai”.

      “Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake ba”.

      Yanda tai maganar da alamar kuka ya sashi danne dariyarsa da ƙyar. “Idan na barki duk bashin da kikaci zaki biyasa in kin dawo”.

      Da yake so take a barta babu tunanin komai tace ta amince.

    Murmushi ya sakeyi yana ƙoƙarin shiryawa. “Okay tunda hakane sai ki fara da sumba ɗaya ƙwaƙwara yanzun nan kona taho”.

      “Ni dai a'a dan ALLAH”.

“Oh to ki shirya ganinan zuw.....”

       Kafinma ya rufe baki ta mannama wayar kiss da yazo masa cikin kunne a bazata. Sai kuma ta yanke wayar ƙitt. Duk yanda yaso dannewa ya gagara sai da yay dariya yana girgiza kansa da ajiye wayar ya cigaba da shirinsa.


         Gudu-gudu yay shiri ya fito dan su Habib na jiransa a falo. Barka da fitowa suka shiga yimasa har yakai zaune. Lap-top ɗin dake ajiye saman centre table ajiye ya ɗauka yana gyara zamansa ƙafa ɗaya kan ɗaya. Cikin maida hankalinsa ga abinda yake a ciki ya fara magana batare daya kallesu ba. “Salis, Khalid, Habib. Kune zaku shiga cikin gidan. Khalid kaine zaka fara bubbuɗe ko ina ta yanda idan ya farka zaiyi tunanin kuskure akai wajen buɗesa. Sannan Salis ka tabbatar ka ajiye dukkan abinda zai iya gani da zai taimaka masa neman su A.G a farko kafin kowa, ko cikin yaransa. Da zarar kun kammala duk wannan Khalid sai kai masa allurar da Abdull ya baka. Kasancewar tanada ƙarfi zai saurin farkawa ya kuma dawo hayyacinsa da wuri. Habib zai amfani da wannan damar ta komawa da ga can ta bayan Windown ɗakin da yake ciki kayi wayar ƙarya akan abinda zaka shirya kansa a halin yanzu. Daga nan sai ku koma tacan sama bayan ƙarfen nan ku ɓuya har sai ya fito a gidan sannan ku kirani”.

      Cikin girmamawa suka amsa masa. da hannu yay musu nunin suje, tare da cilla musu key ɗin mota. Salis ya cafe.

    Sai da suka fice ya ɗago ya duba Adam tare da miƙa masa key ɗin Napep. “Kaje ka jira a bakin layin, da zaran sun kira ya fito ka ɗaukesa zuwa duk inda ya sanar maka zaine. daga nan na sani”.

       “Okay Master”.

Adam ya faɗa shima cike da girmamawa.

     Bayan fitarsa shima yaɗan cigaba da aiki, bayan wasu mintuna ya dubi Musbahu da Idris da Zaidu. “Nasan da ya samu damar fitowa babu wanda zai nema a halin yanzu sai yaransa biyu daya yarda dasu fiye da kowa bayan ni. Dage, da Katafila, Musbahu, Zaidu baku da matsala da hakan, dan kun iya komai nasu, ga wayoyinsu nan sai ku ɗauka, zaku haɗa hannu da Adam wajen kaisa inda su A.G suke”.

       Suma cikin girmamawa suka amsa masa tare da ɗaukar keys ɗin mashin guda biyu da wayoyin suka bar wajen domin zuwa suyi nasu shirin. Ya dubi Idris daya rage, “Kai kuma zamu kasance tare da kai anan domin bibiyarsu da ga nan har zuwa lokacin dazan fita”.

      Kansa ya jinjina masa shima, tare da neman waje ya zauna. Waya Master ya ɗauka, yay kiran yaya Abubakar da ya kammala haɗa jami'an da zasuyi aikin tare a can, bayan sunyi magana akan duk yanda tsarin zai kasance ya ajiye wayar da maida hankalinsa ga Idris.


_______________


        Tafiyar kusan mintuna talatin da wani abu ya kai su Habib inda suka nufa, gida ne madai-daici dake cikin sabuwar anguwa, duk da akwai duhun dare haka suka ajiye motar acan baya da gidan sosai suka ƙarasa da ƙafa. Kamar yanda Master ya tsara musu suyi basu ƙetare magana ko guda ba duk sukayin. Bayan Khalid ya kammala nasa aikin na bubbuɗe ko ina ya shiga ɗakin ƙarshe daya buɗe. Ƙugu ya riƙe yana maibin ɗakin da kallo hannunsa ɗaya rufe da hanci, lafiyayyen ɗaki ne madai-daici mai ɗauke da toilet a ciki, sai gado ƙarami na ƙarfe irin na ƴan makaranta da kwanon cin abinci da kofi. Daka gani dai ɗakin baida maraba dana ƴan prison. Cikin nutsuwa ya tsaida idanunsa akan mutumin dake kwance bisa gadon fuskarsa buzu-buzu da gashi har kansa kai kace mahaukacine. Yayi datti matuƙa, na jiki dana sutura, ga wani wari dake fitowa daga jikinsa mai ban tashin hankali. Sai dai babu alamar yunwa tattare da shi ko kaɗan. Khalid ya ɗanja numfashi da ɗage kafaɗa yana zaro syringe dake ɗauke da ruwan allura a aljihunsa. Matsawa yay jikin gadon yayma mutumin, yana zarewa bai tsaya wasa ba yay wuff ya fito da ga ɗakin yanama Habib ƙaramin fito alamar ya kammala nasa aikin.

      Rufe bakin Khalid keda wuya mutumin ya farka, zumbur yay ƙoƙarin miƙewa, sai dai azabar data ziyarci jikinsa na harbin dake a hannunsa da ƙafa wanda Master yazo yay masa shi a daren shekaran jiya tamkar yanda akai masa ya sashi sakin ƴar ƙaramar ƙara. Sai da ya ɗan ja numfashi sannan ya ƙarasa miƙewa da ƙyar yana cizar lip ɗinsa na ƙasa. Ɗakin yabi da kallo cikin ƙunar rai da zuciya, tsahon shekaru biyu kenan yake a ciki batare da yasan wanda ya kawosa ba. Tun yana gwada ƙoƙarin fita harma ya haƙura yasama sarautar UBANGIJI ido. Ana bashi abinci wadatacce ana kuma kula da lafiyarsa. Amma akan bugar da shi da maganin barci a wasu lokutan ta hanyar abincin da ake bashi. Kamar shekaranjiya, sai da aka buhar dashi sannan aka harbar masa ƙafarsa da hannu. Gigitar shigar bullets da azaba ya sashi farkawa, sai dai baiga wanda ya harbesan ba dan harya fice a ɗakin, sai bayan kusan awa guda ya jigata matuƙa sannan yaronsa daya yarda da shi fiye da kowa ya shigo, cikin wata sabuwar azabar ya cire masa bullets ɗin yana zuba masa maganganun da har yanzu daya farka bazasu bar gigitashi ba.

      Jin kamar ana magana ta bayan window ne ya sakashi nutsuwa yana saurare. Tabbas komai ya shiga kunnensa, tamkar yanda Master yay fata kuma yayi yunƙurin ganin ya gwada miƙewa ya gudu. Cikin azabar zogi da ƙafarsa ke masa da raɗaɗi ya miƙe da ƙyar, dan bayan cire bullets ɗin ko paracetamol Master bai bashiba dan rage zafin ciwon. Gwada buɗe ƙofar yayi, sai ko gata ta buɗe. Jikinsa har rawa yake wajen turo illahirin jikinsa waje sosai dan gani yake mafarki yake tamkar yanda ya saba. Sai dai ganin ya fito falon sosai ya sashi saki wata dariyar ƙunar rai da zuciya. Tare da jerama kansa kirari irin na gawurtattun arnan saman dutsin nan. Cikin tafiyar dake nuna ƙashin kafafunsa sunyi sanyi saboda zaman waje ɗaya ya nufi hanyar fita ƙofar falon, dan ya haƙƙaƙe a ransa yau zai bar gidan nan koma ta halin yaya ne. Duk inda auta (Master yake cema auta) yake sai ya halaka rayuwarsa kafin kowa.

        Ba kai tsaye suka buɗe masa ƙofar falon ba dan karya zargi komai, sai da ya ɗan sha wahala kafin ta buɗe duk tunaninsa ƙwazonsa ne. Daga falon ma zuwa tsakar gidan da ƙyar ya iya isowa ƙofar waje, sai dai itafa a rufe take dan haka yay tunanin haura katanga. Kasancewar dukanin hanyar da zata bashi sauƙi na barin cikin gidan sun bar masa ya samu damar haura katangar tunda dama horarrene ba saboba. Dukan abinda ke faruwa su Habib na kallonsa harya fito cikin layin, ya jima a kwance bayan dirowarsa daga katangar kafin ya ƙara tashi ya fara tafiya cikin haɗa hanya, cikin sauri Habib ya dannama master waya ya sanar masa.

       Sosai Master yay mamakin yanda aikin ya tafi a sauƙaƙe, yanke kiran yay ya maida ga Adam. Adam dake daga farkon layi a napep yana gani ya ɗaga cikin sauri.

        “Maza ka tada napep ɗinka ka taresa gashi nan zai fito”.

     “Okay master ”. Adam ya faɗa yana ƙoƙarin sakama napep ɗin key. Cikin azama yabi umarnin Master. Cikin ɗan shawagi tamkar ya ajiye mutum ya shigo farkon layin, yay reverse kamar zai juya ya fita cikin sa'a ya haske mutumin. Ƙasa yay da fitilar sai kuma ya sake haskashi. Tabbatar da shi ɗinne ya sakashi burga napep ɗin zuwa gabanshi, Cikin hanzari ya fito yana ambaton “Subahanallahi mai gida kana lafiya kuwa?”.

     Hannu kawai mutumin ke iya jinjina masa, cikin matuƙar wahala ya fara magana. “Ka fitar dani a layin nan yanzu-yanzu, ko nawane zan baka saurayi”.

      “Babu damuwa baba, kaga taho muje, ko'ina kakeso zan kaika, ina fatan dai lafiya”.

        Bai iya bama Adam amsa ba harya taimaka masa ya shiga napep ɗin, sai da Adam ya tada napep ɗin suka bar layin ya dubesa daga kwancen da yake a baya. “Yaro ko zaka aramin wayarka?”.

      “Babu damuwa baba gata”.

Kamar yanda Master yay hasashe number *Katafila* kuwa ya fara lodawa a wayar ta Adam ɗin, da farko bata shiga ba kamar yanda suka tsara, sai a na biyu. Koda ta shigan kuma su Zaidu basu ɗaga ba harta yanke. Sai da ya sake kira cikin tashin hankali dan sune kaɗai damarsa a yanzun. Tana gab da tsinkewa Zaidu ya amsa.

         Cikin muryar gawutattun marasa ji irinsu Katafila Zaidu ya fara magana. “Kai waye da duhun daren nan hakane?”.

       Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar mutumin, sanin halin katafilansa baya son jira ya fara magana da sauri-sauri. “Master ne Katafila na!”.

      “What!!?. Kai ALLAH ganganne wannan, gagarar da mukai mukune ta sakaku fara canja layi na yi mana shigo-shigo da oga. To ku sani bazaku taɓa sani kojin komai ba dan oga ya muku zarrah”.

      A karon farko master ya kece da wata shegiyar mahaukaciyar dariya da har ta bama Adam tsoro da mamaki. Duk da a yanda yake haka ya fara jerama Katafila kirarin da shi kaɗaine ke masa shi duk duniya. Cikin nuna alamar mamaki da ga can Zaidu yace, “Kai oga!!”

       “Tabbas nine Katafila. Ka fadamin kuna ina dan ma kuɓuta daga hannunsu, maza faɗamin”.

         “A'a oga, kai dai faɗamin inda zamu sameka gani nan ni da Dage a ɓoye muke muma saboda farautarmu da ake dare da rana tun bayan ɓacewarka”.

       Wani sanyi ne ya ratsashi na daɗi, ya mikama Adam wayar akan yayma su Katafila ɗin kwatancen inda zasu haɗu. Babu musu Adam ya amsa ya kwatanta musu yanda Master ya tsara musu dama tun farko.


          Turyan-tiryan Adam ya isa har inda su Zaidu suke, waɗanda gaba ɗaya sun canja kamanni daka gansu kaga ƴan sara suka zam. Sai wani rangaji suke da magana uwa ta bugaggu. Cikin wata irin zabura master ya miƙe zaune saboda jin muryar su Dage, suma ihu suka buga da faɗawa cikin napep ɗin suka cikuykuyesa a dole su murnar ganinsa sukeyi. Adam ya danne dariyarsa da ƙyar yana toshe hanci, dan tunda ya ɗakko master wani shegen wari ke bugar hancinsa. Su kansu su Zaidu da ƙyar suka iya daurewa warin nan. Harda hawayen drama kuwa sukayi su a dole ogansu ya dawo.

         Adam dake nuna kamar a tsorace yake dasu, cikin marairaicewa yake tambayarsu ina zai kaisu?. Musbahu (Katafila) ya duba Adam ɗin sheƙeƙe ya ɗauke kansa yana maidawa kan master. “Oga ko'ina a hargitse take a yanzu haka. Dan wani na amfani da sunanka yana ɓarna ta maƙudan kuɗaɗe, inaga yanzu babu inda ya dace mu kaika sai wajensu A.G, sune kawai zasu baka mafaka har komai ya lafa”.

           kai kawai master ya jinjina musu, dan har yanzu ya lura basu fahimci akwai harbi a jikinsa ba. “Ni yanzu banda lambar kowa, tayaya kenan zamu sami wani a cikinsu?”.

      Zaidu (Dage) ya zaro ruɓaɓɓar wayarsa, “Ai oga kwantar da hankalinka, inada ita a zane kan kwakuletata bara a danna mas kira”. Batare da ya jira cewar master ɗin ba ya dannama A.G kira. Ba'a ɗaga ba sai da tana gab da tsinkewa. A.G dake a tsakkiyar su Alhajin Mande ana sabon meeting yay musu alamar suyi shiru yana kaiwa kunne.

         Daga nan Zaidu yace, “Hallo yallaɓai Dage ne na master mai jurar wahalar duniya!”.

      “What!?”.

A.G ya faɗa yana miƙewa a zabure. Zaidu dake saurarensa yace, “Yes yallaɓai. Yanzu haka muna tare da oga mun tsintosa acan bayan gari, ya kuma tabbatar mana kai kawai yake son fara gani dan bakinsa da goro...”

       “Kai dalla saurara bana son yaudara. Ni shegen yaron nan zaice yana son gani bayan ya halaka rayuwata, kama tabbatar masa inhar ya bari idona yaga nasa to ko kashinsa wani bazai gane ba ok;. Yana gama faɗa ya yanke kiran.

      Duk da Zaidu yaji mi A.G ɗin ya faɗa sai cewa yay ai yace su ƙarasa yana gidan hutun Alhajin Mande. master dai bajin A.G yay ba, dan haka ya aminta kawai dan yasan su Dage bazasuci amanarsa ba. Zaidu ne ya dinga nunama Adam hanya duk da kuwa shima ya sani sarai.


____________________________


       Dukkan abinda ke faruwa Master yana saurarensu ne tiryan-tiryan da ga gida, dan haka yanajin sun ɗauka master ya miƙe ya hau shiri a gaggauce. Yanayi yana waya dasu Yaya Abubakar da suma ke shiri daga can station. Yayinda su I.G suma ke daga can suna jiran tsammani dan Master ya kirasu akan samun inda ainahin master ɗan ta'adda yake a daren nan. Cikin kanƙanin lokaci Master ya fito cikin shiri yana soke bindigu biyu cikin jikinsa.

       “Idris ka kula da komai yanda ya kamata. Ko yaya ka fahimci matsala da ga su Adam kai saurin sanarmin dan su A.G sun wuce dukan tunanin mai tunani.”

       “Okay Master ALLAH ya bada nasara”.

     Kai kawai Master ya jinjina masa. sai da ya je ƙofa ya tsaya yay addu'a kafin ya fice cikin zafin naman da ALLAH ya azurtashi da shi. Mashin ɗin dake can gefe a fake ya nufa, sai da yay addu'a nanma ya haye samansa yay masa key. Da sauri maigadi dayaji motsinsa ya fito ya buɗe masa gate ɗin.


      Akan hanya Master dasu Yaya Abubakar suka haɗu, su kusan ashirin duk cikin shirin kota kwana. Tun a farkon shiga anguwar datai tsitt alamar mutane sunyi barci suka faka motocin da suke ciki. Duk fitowa sukai, hakama Master ya sauka a mashin ɗin nasa yana sauraren abinda ke faruwa daga can ta ɓangaren su Zaidu ta abin da ke a kunnensa. Cikin tawagar yaya Abubakar ɗaya ya karaso gaban Master ɗin da bullet proof jacket ya saka masa. Yana gyara masa ita suna magana da yaya Abubakar akan yanda zasu zagaye gidan hutun na Alhajin Mande da su A.G ke a ciki suna sabon meeting.......


       Acan ɓangaren su A.G kuwa a kiɗime yakema su Dr Sufi bayanin wai yaron master ne ya kirashi akan ga master ɗin nan yana son zuwa inda suke. A zabure suma suka miƙe har suna haɗa baki wajen ambaton sunan master ɗin.

        Engineer yace, “Anya kuwa ba wata gadar zare yake neman ƙulla mana ba?”.

       “Komaima zai iya dan yaron nan shaiɗanine. Amma karku manta a yanzu muna a gaɓar neman mafitane akan iyalanmu da dukiyoyinmu. Ina ganin kodai yarasa yanda zaiyi ya gudu ko makamancin haka shiyyasa ya dawo garemu”.

        “Tabbas maganarka na'akan hanya R.D, inaga mu bashi damar zuwan amma mu taresa cikin ɓadda kama muma”.

       Duk sun gamsu da zancen Alhaji Sallau, dan haka a take A.G ya danna kiran no ɗin da su Zaidu suka kirasa. Bugu biyu kuwa suka ɗaga sai dai basuyi maganaba. Dr Sufi daya amshe wayar a gadarance yace, “Yazo muna jiransa”.

      Batare daya jira cewar su Musbahu ba ya yanke wayar. Murmushi sukayi suna kallon juna batare da master ya lura ba dan kwance yake har yanzu jikinsa babu ƙarfi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso dan dama dai suna gab. Maigadi da dama yasan da zuwan nasu sunayin horn ya leƙo cikin kare fuska da suka haske masa. “Wane mara mutuncine haka wai?”.

       Dira Musbahu da Zaidu sukayi sunama maigadi kurari, ƴar hararar su yay sannan ya fara maƙyarƙyata irin dai ya tsoratan nan. Zaidu ya kai masa halbi yana zagi da faɗin, “Mara mutunci kaine zaka goya oga har cikin gidan nan kuwa. Maza zoka duƙa ya hau bayanka. Bin umarninsu yayi, cikin rawar jiki yazo ya tsugunna, Adam ya taimakawa master ya hau bayan maigadi. Suna ganin ya shiga cikin gidan suka koma napep Adam yaja suka kauce dan Master daga can yana sanar musu suyi maza subar wajen suna gab da gidan.


       Su A.G na ɓaɓɓoye maigadi ya shigo goye da master yana nishi da ƙyar, zubesa yay ƙasa kusa dasu Abba da zuwa yanzu da ƙyar suke numfashi dan azabar wahala. A.G ne ya fara fitowa da sauri a inda ya ɓuya riƙe da bindiga. Maigadi ya ɗaga hannu sama yana makyarkyata daja baya. “Oga ka rufan asiri ka sauke wannan abar, baƙone gashinan, ya kuma tabbatarmin kunsan da zuwansa”.

     A.G dake tsaye kan master da bindiga yayma maigadi nuni daya fita. Da gudu kuwa ya fice har yanacin tuntuɓe. Bai tsaya a gate ɗin ba yay waje bisa umarnin Master shima.

        A.G dake bin master da kallon mamaki cikin daka tsawa yace, “Munafuki da wannan salon kazo kuma? To ai ka makaro dan zuwa yanzu mu babu abinda zakai ka layance mana”.

         Da mamaki master ke duban A.G ɗin. “A.G kardai kace baka ganeni ba. master ɗinku ne fa, kodan ka ganni da wannan gashin buzu-buzu, ku bani abun aski na saukesa nasan zakufi fahimta ta”.

       Harbin ƙafarsa A.G yayi a fusace. master ya saki wahalalliyar ƙara. A dai-dai nan suma su R.D dake laɓe suka fito kowanne hannu da makami. Zasu fara lugudarsa ya zabura gefe cikin magiya da roƙon su saurareshi. Dan sai yanzune ya tuna cewar su Dage sun sanar masa akwai wani Master dake basaja da shi yana aiki. Ya buɗe baki zai fara musu bayani kawai sukaji an banko ƙofar falon da masifar ƙarfi har sai da suka zabura. Su Master ne da suka shigo cikin gidan da sanɗa. Tamkar ƙyaftawar ido sukaima su A.G zobe a cikin falon.

       Yaya Abubakar ya daka musu tsawa akan su ajiye makaman hannunsu koya fasa kan mutum. Cikin rawar jiki dabin ƴan sandan da kallon mamaki su A.G auka shiga ajiye abubuwan hannunsu suna ɗaga hannaye sama na alamar surrender.

      Master daya kasance shi kaɗai a waje ya shigo falon cikin takun izzarsa da ƙasaita yana tafa hannaye. Gaba ɗayansu suka maida hankalinsu ga ƙofar dan son ganin wanene zai shigo. A wani irin zabure duk sukai baya, domin ganin wani Master ɗin kuma. Suka duba yaya Isma'ill suka duba master na ainahi dake zaune shima yana dubansa. Kafin wani a cikinsu ya sami damar cewa wani abu Master yakai hannu bisa face ɗinsa ya zare mask ɗin dakesa su kallesa a master ɗan ta'adda. Sai ga fuskarsa ta ainahin Muhammad Shuraim da jami'an tsaro suka sani ta bayyana.    

         Master yakai zaune yana wata shaƙiyyar dariya da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya kaɗa musu yatsun hannunsa uku. “Hy! Guys”. Yay magana da muryar master ɗan ta'adda. Cikin sake rikicewa suka dubesa, suka dubi master dake zaune fuska buzu-buzu da gashi. A zafafe master ɗan ta'adda ya nuna Master yana girgiza musu kai, “karku yarda da wannan matsiyacin yaron, bakowa bane face yarona, shine ya ari dukkanin salona yazo muku a suffata bayan ya ɗaukeni ya ɓoy.......”

         “Relax! Relax oga. Miye na zazzari bayan nima da kaina zan iya faɗa”. Isma'il (Master) yay maganar cikin tsantsar rainin wayo da kai hannu saman face nashi ya shafa a hankali.

     “What!!!?”.

A.G ya faɗa cikin rawar jiki har yana neman faɗuwa. Hakama su Alhajin Mande wani irin aradu ne ya saukar musu bisa kawuna cikin ƙanƙanin lokaci, Abba dake kwance duk yanaji da ganin komai ya saki wani marayan kuka ianunsa akan yaya Abubakar sa Master.

            Master dake dubansu yana murmushi ya tsaida idonsa akan A.G. “Haba ɗan sanda ya da firgita haka?! A tunaninka kaine kawai ka iya mufunci da salon makirci nacin amanar ƙasa? No, no my dear akwai ƴan iska a saman iyawarka masu tasowa irina!!!!”.

      Master yakai ƙarshen maganar a matuƙar hargitse yana doka hanun kujera da ƙarfi tamkar face nashi zatai aman wuta. Basu kawai ba, hatta su yaya Abubakar kallon razana suke masa. Dan gaba ɗaya ya juye musu tamkar bahagon zaki, Abba da gaba ɗaya suffar Master ta dawo masa irin ranar daya illata Junaid ya fara rawar jiki da faɗin, “Wlhy shine, shine wlhy A.G. shine ya illatamin yarona!”.

       Ina babuma wanda yasan yanayi duk da kunnuwansu na saurarensa. Yaya Abubakar ya fahimci idan Master yay fushi babu sauƙi, dan koyaya kuke da shi sai kaji shakkar koda kallonsa ne. Ganin Master ya ɗauka bindiga Yaya Abubakar yay saurin nufosa, sai dai kafinma ya iso harya harbata a ƙafar A.G. wata irin gigitacciyar ƙara A.G ya saki da kaiwa ƙasa durƙushe.

          Cikin gargaɗi da waro manyan idanunsa masu tamkar zaki ya ke nuna A.G da ɗan yatsa. “Wannan harbi ne na razana matata da ka dingayi!!”.

        Wani irin kuka A.G keyi na azaba, zufa ta gama wanke jikinsa sharkaf kamar wanda yay wanka. Yaya Abubakar dake ɗan bubbuga kafaɗar Master ɗin alamar lallashi yace, “Please Cool down Shuraim”.

     Komawa Master yay ya lafe jikin kujerar yana saki tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ji yake kamar ya harbesu baki ɗaya tun anan ya huta kawai. Dubansa yakai ga ɗaya a cikin yaransu na ƴan sanda. “A ciremin gashin fuskar wannan”.

        Cikin saurin ɗan sandan yace, “Okay sir”. Yana nufar master da zuciya ta kumesa, ji yake kamar ya miƙe ya damƙi Isma'il (Master) yay gunduwa-gunduwa dashi. Dan babu abinda ke masa kaikawo a rai sai irin ɗunbin ƙaunar daya nuna masa a baya da yarda ta haƙiƙa, ashe shi ɗin jami'in tsaro ne dama. Cike da mugunta ɗan sanda ɗaya ya kama hannayensa ya banƙare ta baya yasa masa handcup, wani ya duƙa ta gabansa ya fara aske gashin fuskarsa dake buzu-buzu. azaba ta saka master fara ihu dan aski ne mai kama da ana tsigar gashin da hannu dan azaba.

        Sauke gashin da aka gamayine tsaf ya bayyana ainahin fuskarsa. Tabbas su A.G sun sake tabbatar da wannan shine master ɗinsu, suna mamakin taya akai basirarsu ta toshe haka har suka gagara fahimtar badashi suke tare ba sai a yau da guri ya ƙure musu. Wayar Master ce ta katse musu tunani.

           Yana zaune har yanzu ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani jinin sarauta. Magana yake cikin fushi da harzuƙa. “Sir a yanzu haka mun sami nasarar kamashi tare da iyayen gidansa, sai dai dalilin gaddamar da sukai mana kowannensu ya samu harbi”. Ya ɗanyi shiru alamar saurare. Sai kuma yace, “Okay sir” yana sauke wayar a kunnensa. Da idanu yayma zaratan ƴan sandan dake tare da su magana. Kamar jira suke suka shiga ɗana kunamun bindigunsu. Rikicewa su R.D sukayi dan tunaninsu kashesu Master ɗin yace ayi. Kafin suyi yunƙurin tashi ƴan sandan nan sunbi ƙafafunsu da harbi tako ina. Cikin ƙanƙanin lokaci falon ya rikice da ihu, Hajiya mama dake a sume ta kawo numfashi, dan duk abinda ake ita bama ta sani ba. Yaya Abubakar kuwa sarai ya ganta ita da Abba ya nuna baima san da zamansu a wajen ba dan Master ya bashi dukan bayanan Abba ya gani.

          Cikin abinda bai wuce mintuna goma ba sai gasu kwance wanwar a ƙasa suna ihu da kururuwar azabar harbin da suka sha, a dai-dai nan ƴan sandan da I.G ya sake turowa suka iso gidan tare da tawagar wasu ƴan jarida duk da kuwa asubahi ma tayi............✍


*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*


_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya💃🏻._


*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu😂💃🏻*.


_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za'a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya😉💃🏻_.


*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻


Kaza akwai 10k

15k

5k

Tsimi 5k 10k

Matsi 5k

Gumba uku 2k

Zumar gorun tula syrup3k

Garuka 3k

Cicccibi 5k

Zakara 20k

Zabo20k

Humra

Turaren tsugunni

Butar tsarki

Maganin infection

Tsimin tabaje

Turaren al,ajab


*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.



_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_

08068526455


*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*


Zaku iya samun mu amanhajar


Facebook

Istagram


Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.


Sai kunzo🥰🥰🥰🥰💃🏻👌🏻.


*_Chapter Forty Eight_*


............Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan ƙasa yau an wayi garine da babban labarin kama master da iyayen gidansa. Duk da kasancewar akwai sauran duhun asubahi hakan bai hana anguwar cika da mutanen cikinta da jami'an tsaro ba. Hakama ƴan jarida da basu yarda a barsu a baya ba. I.G da C.P ma basu zauna ba nan suka nufo dan case ne babba da kowa ke buri akan ganin wannan rana da za'a kama master. Kowa ba'a bari ya shiga gidan ba hatta sauran jami'an tsaro, dan Master da yaya Abubakar sai da suka gabatar da sallar asubahin su, sauran yaransu ma sukayi sannan suka yarda suka buɗema su I.G ƙofa. Duk da I.G ya jima da sanin su A.G a cikin tawagar ta bakin Master a yau daya gansu sai takaicinsa ya sake ninkuwa da tsanarsu. Ya kauda kansa hawaye na ciko masa idanu. (Wai fa manyan mutane daya kamata su bama ƙasa kariyane anan tare da ɗan ta'adda mai ruguza ƙasa. ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnakun da sukayi a tsahon shekarun da suke tare da shi. Akwai irinsu da yawa kuma dake lulluɓe da rigar mutunci suna cin dunduniyar ƙasa. Ta yaya ƙasa zata gyaru bayan manyan cikinta sune masu bada gudunmawar gurɓatar yaran dake ta'addanci. Kullum aiki sukeyi ƴan ƙasa na ganin gazawarsu da tunanin yaudara a dalilin tufkar da suke wasu na warwarewa saboda makullan madafun iko dake cikin hannayensu ta ɓangarori da dama).

         Duk da agalabaice su A.G suke saboda harbin da Master yasa akai musu hakan bai hanasu jin kunyar idon su I.G ba, ga ƴan jarida da aka bama damar shigowa sai ɗaukarsu suke a hoto da video lokacin da ake fiddosu da ga gidan. Master ya bada damar saka hajiya mama a motar asibiti, su Abba kam da su A.G aka tarkatasu zuwa police station jami'an tsaro zagaye da su mota-mota.


_____________________________


         Hibbah da Ammar na zaune a falo tun bayan sallar asuba, Hibbah dake latsa wayar Ammar tana kallon hotunan biki tai wani irin zabura ganin news da ɗumi-ɗuminsa a facebook akan an kama Master. Gaba ɗaya ta rikice dan duk zatonta Master ɗinta ne. Cikin tashin hankali Ammar da yaga yanda ta gigice ya warce wayar ya duba shima, da sauri ya rarumi remote ya kunna ƙaramar television dake a falon, a dai-dai nan su Yaya Usman ke sakkowa da ga sama hakama Ummi. Gaba ɗaya wutar kan kowa ta ɗauke saboda ganin abinda ke faruwa. Hibbah ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya lokacin da ake nuna su A.G da master ɗan ta'adda a galabaice saboda harbin da suka sha. Sai su Yaya Abubakar da Master dake ƙoƙarin zillema ƴan jaridar dake neman titsiyesu nason jin yaya akai suka kama master.

       “Kambu! Da gaske fa Yaya Isma'il jami'in tsarone Ummi”.

     Ammar ya faɗa a zabure yana nuna television ɗin. Hannu Ummi ta ɗaga sama tana godema ALLAH, dan harga ALLAH taji daɗi har cikin ranta, ta share hawayen dake zubo mata na tsantsar farin ciki tana kamo hanun Hibbah ta rungumeta. 


______★


     Cikin ƙanƙanin lokaci duniya ta ɗauka. Hotunan su R.D da Master suka fara yawo a social media ta kowanne ɓangare. Tuni kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa akan wannan al'amari mai ban mamaki, musamman ma da manyan ɓarnakun da su A.G suke aikatawa suka fara fitowa a bakunan wasu mutane da suka san sirrinsu. Waɗanda ada tsoro ya hanasu fitowa su faɗa. Musamman ma'aikatan gidajensu na shakatawa. Sai kuma wasu boyayyun mutane da harkalla ta haɗasu da su A.G ɗin suka cutar dasu ko makamancin hakan. Wannan fa shine allura ta tone garma. Dan kuwa har abinda ma ba'ai zato ba sai gashi yana fitowa. Cikin ƙanƙanin lokaci ƴan bani na iya musamman matasa suka fara yo gangami zuwa police station akan a basu su A.G su halaka. Hankalin su Master ya tashi, dan an rasa wanda ya fara fasa zancen su A.G ɗin na Homo. Sai da suka zurfafa binciken gaggawa aka gano a wani shafi na manhajar facebook maganar ta fito, sun bibiyi shafin kuma sunga an buɗesane a safiyar yau dai-dai lokacin da zancen kamasu A.G ɗin ya fito. Babu wani kuma damar da za'a iya bibiyar mai shafin da ita kai tsaye, dan komai bai saka ba. Email ɗin da akai amfani da shi ma babu wani information tattare da shi. Ana cikin haka sai ga wasu hotuna kuma sun fara yawo nasu Halilu da su A.G ɗin tsirara haihuwar uwayensu suna aikata baɗala fami muni da cizon zukatan masu imani.

     Tuni komai ya sake birkicewa, matasa da dama ƙiris suke jira sun sake harzuƙa akan infa ba'a basu su Abba ba to lallai zasu ƙona ofishin ƴan sandan. Duk yanda su Master sukaso controling mutane cikin sauƙi hakan ya gagara, dole aka haɗa da barkonon tsohuwa mai saka hawaye sannan suka tarwatse, jami'an tsaro ta kowanne fanni suka maye gurbin harabar station ɗin dama titin baki ɗaya. Amma duk da haka fama aketayi da matasa.

         I.G da yaga abin na neman zama babban al'amari dole ya fito yay magana ga ƴan jarida cikin lallashi, ya tabbatar ma da jama'ar gari basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen miƙa su A.G gaban alƙali, dan haka su kwantar da hankalinsu gaba ɗaya suspects ɗin zasu sami hukunci dai-dai da ɓarnar da suka aikata. Zakuma a zurfafa bincike domin cigaba da zaƙulo duk waɗandama suke tare da su da ba'a kamaba a yanzu haka.

       Bayanin I.G ɗin ya ɗan kawo lafawar tarzomar, sai dai fama matasa nata kaikawo a media cewar inhar ƴan sandan basuyi wani abu da wuri ba to lallai su zasu ɗauka hukunci a hannunsu, kuma zasu tabbatar da shi.


        Da ga Master har yaya Abubakar a jigace suke, tun daren jiya suke abu guda babu hutu, ga Master dama ba isashen lafiya ne da shi ba. Dauriyace kawai da jarumta da son sauke aikin nan ya hutama ransa. Idanunsa kawai ka kalla dake cikin mask zaka tabbatar da yana buƙatar hutu, sai dai kuma babu damar hakan. Sai da I.G ya fahimci kamar jiri na neman ɗibar Master ɗinne sannan ya kamosa ya zaunar yana masa faɗa.

        Koda yasa aka samo masa abinci tea kawai ya iya sha, ya samu yasha maganin da Habib ya kawo masa da ga gida da ƙyar bisa taimakon Abdull. dan su tun jiya da suka kammala aikinsu suka koma gida suka koma kallo da jiran news. Sai da suka fahimci Master bashi da niyyar fasa ƙwai akan ƙazantar su A.G ne yasasu buɗe shafi suka saki hotunan su A.G ɗin da suka taɓa samu a camara ɗin Master batare daya sani ba tsahon lokaci. Sai dai kuma kafin su saki nasu sai ga wani shafin ya saki zancen su A.G ƴan homo ne. Hakan ya musu daɗi dan sun samu abokin ritatawa. Yanda garin ya hargitse da yunƙurin mutane na abasu su A.G su halaka ba ƙaramin daɗi yay musu ba a rai da zuciya.

 

            ★★★


    A nan wajen su Ummi ma Ammar da Hibbah suna a cikin kwatankwacin farin cikin da su Habib ke ciki, dan kuwa ita da Ammar ɗinne suka buɗe shafin farko wajen bayyanama duniya su Halilu ƴan homo ne. Kasancewar Hibbah kwararriya ce mai ƙwazo ta tabbatar za'a iya bibiyan shafin koda badaga jami'an tsaro ba tabi matakai na ɓoye kai da bin hanyoyin da labarin zai saurin yaɗuwa ga al'umma. Sai ko gashi bukatarsu ta biya. Dan ko mintuna ashirin cikakku basuyi ba zancen ya fita. Har manya-manyan shafukan sada zumunta na yaɗa labarai irin su bbc suka ara suka yafa suma.


___________________


         Kwatanta muku irin baƙin tashin hankalin da iyalan Halilu da nasu A.G dake hannun Master suka shiga ma ɓata lokaci ne, tsabar firgita na shigar al'amarin cikin kunnuwansu wasu har yanke jiki suke suna faɗuwa musamman akan zancen Homo ɗin nan. Dan masu guntayen hawan jini dana suga tuni sun haura dubu bisa dubu ma ba ɗari biyu ba.

      Dole cikin tashin hankali masu tsaronsu suka kira Master suka sanar masa halin da ake ciki. Yay ƙoƙarin nufar gidan I.G ya dakatar da shi danshi tausayi Master ke bashi matuƙa saboda sanin shima likitan yake buƙatar gani. Wasu jami'an aka tura da motar Ambulance domin kwaso waɗanda ke a halin ciwon. lafiyayyun kuma za'a kawosu station ɗin.  


_________________


         A ɓangaren su A.G ɗin suma an cire musu bullets ɗin dake a jikkunansu tun bayan isarsu station ɗin, sannan aka garƙamesu cikin cells ɗaya na musamman na masu aikata manyan laifuka. Da wannan damar sukai amfani wajen titsiye master cikin bahagon yanayi, zayyane musu komai na yanda akai Isma'il (Master) ya dunƙule rayuwarsa ya maye gurbinsa ya basu. tare da azabobi kala-kala daya dinga gana masa ta hanyoyi da dama da bazai iya tuna wasuba a tsahon shekara biyun nan ma.

      Tabbas sun harzuƙa ƙwarai da gaske, sai dai babu damar ɗaukar mataki, yayinda mamaki, al'ajabi na hatsabibancin Master ya sake kashesu matuƙa. Sosai zukatansu ke zafi da ɗaci, musamman idan suka tuna ɓarna da tabargazar da suka dinga zubawa a gaban Master ɗin da a yanzu sunsan bakin alƙalami ya rigada ya butse. Basu da wani sauran tasiri akan kansu ma balle akan wani. Daga ƙarshe takaicinsu da haushinsu suka shiga saukewa akan Halilu daya gallabi rayuwarsu da kukan azabar da yakesha a jikinsa na dukan da suka saka akai masa da karayarsa data koma sabuwa dan shi Master bai sa an harbesa ba saboda ganin halin da yake ciki.

       Marayan kukan azabar da Halilun keyine da ihu ya saka jami'an dake zagaye da su saurin sanarma C.P da keta kai kawo. Dole yasa aka ciro Halilun daga cikinsu dan gaba ɗaya ya galabaita har numfashinsa na fusga na alamar mutuwa. Cikin hanzari C.P ya bada umarnin a miƙasa asibiti.


_____________________________


       A gaba ɗaya yinin yau ma dai su Master basu samu kansu ba har dare, dan shi zazzaɓi ma ya masa rijif koda yasha magani bai samu ya kwantan ba yanda ya kamata. Sai kusan ƙarfe ɗaya da wani abu na dare bayan sun gama meeting ya samu da ƙyar ya rarrafa gida bisa taimakon Abdull.

      Hakama Yaya Abubakar sai dare ya shiga gida, inda su Hibbah da barci ya gagari idanunsu suka zagayesa suna masa sannu dan kallo ɗaya zai baka tausayi shima tsabar zirga-zirgan da sukasha yau. A bakinsa suka sake jin abinda ya faru da Halilu a hannun su A.G harda Hajiya mama da baisan miya kaita hannun su A.G ɗin ba. Mamaki sukai suma matuƙa sai dai ko kaɗan basu wani ji tausayin Halilun ba balle Hajiya mama. Garama Ummi ta ɗan nuna tausayawarta ga Hajiya maman. Sai ko Master da takejin kamar tai tsuntsuwa taje taga halin da yake ciki dan Yaya Abubakar ya sanar musu shima bayajin daɗi.

      Hibbah dai batace komaiba, sai da tazo kwanciya kuma abun yayta damunta arai. A sace ta ɗauka wayar Ummi datai barci tai kiran layinsa. Sai dai harya tsinke ba'a ɗaga ba. Massege ta tura masa ta kashe wayar ta koma ta kwanta zuciyarta tab bege da ƙishirwar son ganin halin da yake ciki.


*_WASHE GARI_*.


            A yau ɗin ma bada daɗin rai aka tashi ba. Dan dandazon jama'ar gari bisa jagorancin matasa tun farar safiya suka zagaye station ɗin. Su kansu su Master da ƙyar suka iya samun hanyar shiga Station ɗin suka fito dasu A.G da za'a miƙa kotu bisa shawarwarin masana da dattijan ƙasa. Dan kowa ya fahimci jinkirin miƙa su kotu zai iya kawo babbar tarzoma da matasan ke son tadawa tun a jiya.

         Tsabar yanda mutane suka fusata wasu da ƙafa suka ringabin motocin su Master ɗin da wadda aka ɗakko su A.G a ciki dake tafiya a hankali kasancewar titin ma babu sauƙi. Haka suka tafi cikin wannan gangamin jama'a har zuwa kotu.

         Su A.G laifi garesu har a wajen manyan ƙasar ma. Dan shi kansa shugaban alƙalan alƙalai da aka gayyato domin yin shari'ar tasu sun saka Master ya taɓa guma masa uban yasa a accaunt ɗinsa tun a farko-farkon shiga jikinsu da yayi. Rashin sanin Master ne yay waɗan nan yashe-yashen kuɗaɗen har yanzu yasa su gaba ɗaya zarginsu akan master ɗan ta'adda yake. Dan haka aƙali dake cike fam da mikin tabon da aka bar masa ya shirya musu tsaf shima domin acewarsa *RAMUWAR GAYYA TAFI GAYYA ZAFI.*

    

           Duk da shari'arsu shari'a ce buɗaɗɗiya hakan bai hana a bama lauyoyinsu damar fafatawa ba da lauyoyin gwamnati. Sai dai manya-manyan hujjojin da lauyoyin gwamnati ke riƙe da su yasa suka kada nasu A.G tun ma kafin shari'ar tai nisa. Dan dole aka matsi bakunan su Alhajin Mande suka zayyane kaso mafi yawa na daga tsiyatakun da suka aikata da rigunan mutunci da wanda master ɗan ta'adda ya aikata bisa umarninsu. Koda suka kawo maganar yashe asusan mutane ba master ɗinsu bane sam alƙali baima sauraresu ba. Dan ihu da boren dake faruwa ta waje daga jama'ar gari da kuɗin da alƙali yaci na manyan mutane irinsu matar gwamna yasa shi yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na tsahon shekaru ɗari da hamsin-hamsin. A takaice dai kowa yasan ɗaurine na rai da rai wannan kawai.

       Sosai wannan hukunci yayma kowa daɗi a cikin manyan, nan take aka cikuykuyi su A.G da aka hana sake cewa komai akayo waje da su domin miƙasu magarƙama (prison). Duk da wannan hukunci da aka yanke musu hakan bai hana jama'ar gari da sukai ready ɗin fitowar tasu ba fara jifansu da gasu har jami'an da suka fiddosu. Dansu burinsu kawai a basu su A.G su kashe kawai yafi hukuncin zaman gidan yarin a wajensu. Sosai ruwan dutsuna ke sauka a kansu har takai da ƙyar aka turasu mota. Nanma basu tsiraba dan motar mutane suka dinga jifa tako ina suna fasa glasses ɗin. Dole jami'an tsaro suka koma kare kawunansu kawai basu A.G ba. Kafin a bar harabar kotun da anguwarma baki ɗaya dasu an musu mugayen raunuka sunata ihu da kururuwa.

       Dan dole aka canja akalar miƙasu prison aka nufi asibiti dasu domin fara treating nasu. Da wannan damar Master yay amfani wajen yima master ɗan ta'adda allurar guba batare da kowa ya farga ba, yayi kuma hakanne domin ɗaukar fansar iyayensa tamkar yanda yay ƙudiri a ransa tun farko. Bayan anyi treating ɗinsu dole nan ma aka bar asibitin dasu zuwa asibitin cikin prison ɗin saboda tsaro ba tsoro ba. Dan duk da boren nan na jama'a akwai magoya bayan su A.G a gefe musamman ƙasashen ƙetare da suke kallon ƙazantar da su A.G ɗin ke aikatawa wadda jama'a ke tada jijiyoyin wuya a kanta ba komaiba. Za'a kuma iya yin amfani da wannan damar a kuɓutar dasu, duk da kuwa a prison ɗin ma dai bawai sakaran tsaro aka barsu da shiba. An sakasune cikin tsatstsauran tsaro da horo mai tsananin gaske da sai sun gwammaci mutuwa da da rayuwa. A yanda mutane ma suka jigatasu da raunikan ruwan duwatsu da wahala wasu a cikinsu sukai labari.


             Abubuwan sun ɗan lafa kaɗan, sai dai an cigaba da cecekuce a kafafen sada zumunta dana yaɗa labarai musam akan abubuwan da suka biyo baya daga bakunan ahalin su A.G, tun daga kan matansu, ƴaƴansu, zuwa danginsu daketa fitaowa suna nuna ƙyama da nisanta kawunansu da su. Yayinda wasu keshan tsinuwa a wajen tsoffinsu da basu riga sun mutu ba irinsu Hajiya mama dake kwance a asibiti rai hannun ALLAH. Dan da ƙyar take iya gane wanda ke kanta. Sai dai bakinta bai gajiyaba wajen jan tsinuwa da ALLAH ya isa ga Halilu.

     Koda su Ummi ma sukaje dubata bisa tursasawar Ummi ɗin da ƙyar ta ganesu tana darzar kuka da roƙon su yafe mata musamman ma Ummi. Ummi tasha kuka dan duk mai imani yaga yanda ƙafar Hajiya mama zuwa rabin jikinta sukai wani masifar kumbura dole ne ya tausaya mata. Ahakanma wai an samu anyi mata gyaran karayar datai a ƙugun a daren jiya a asibitin. Ba itaba. hatta su likitocin kamsu basu san adadin sumar da Hajiya mama tayi ba saboda azabar wahala. Fitsari kam ai ba'a magana ko fanfon birtzatse ya shafa mata lafiya.

     Ko'a jikin su Hibbah, dan ita hankalintama nakan mijinta da sam bataji ɗuriyarsaba yau ma. sai ganin data ɗan masa a tv sanda ake kotu da su A.G. Bisa jagiorancin Yaya Abubakar shima Abba aka kaisu suka dubashi. dan shima dai prison ɗin za'a miƙasa bisa hukuncin alƙali zaiyi shekaru ashirin a gidan yarin. Anan ko Ummi komai batajiba sai ma kallon kaɗan ka gani dataima Halilun. Hakama su Yaya Usman ko'a kwalar rigarsu tamkarma ba dubiyarsa sukazo ba. Basu wani jimaba suka koma gida abinsu.


___________________________________


       Tun Hibbah nasan ran Master harta cire rai, dan tsahon kwanaki biyar kenan babu shi babu alamarsa. Harma sun bar wannan gidan sun koma gidansu da yau Hibbah ta fara shiga. Duk da damuwar rashin ganin mijinta dake cin ranta haka ta danne ta nuna farin cikinta akan cigaban da yayunta suka samu. Dan ko gida sai sam barka komai yaji gishiri da magi. Sai fatan ALLAH ya sauki su Hafsat lafiya kuma.

        Sarai Ummi na lure da halin da Hibbah ke ciki na kewar mijinta amma ta fuske. Kowa yaƙi mata maganar Master ɗin ma a gidan dan ba'ason sanar mata baida lafiya kamar yanda ya roƙa a ɓoye mata har sai ya warke kan hankalinta ya tashi. Ba kuma dan ciwon ma kaɗai ya nisanceta ba. Harda shirye-shiryen ƙarin girma da zai samu shi da wasu tawagar jami'ai irinsu yaya Abubakar. Dan haka yay tunanin haɗewa da ɗan walimar cin abinci na ƙara'in bikinsu da ba'ayiba dana komawa sabon gidansu da yake fatan suyi rayuwa ta din-din-din shi da sauran ƴan uwansa.

          Sai da Ummi taga damuwar Hibbah na fitowa ƙarara akan fuskartane ta zaunar da ita tai mata nasiha da kwantar mata da hankali akan wani babban uzirine yasa Master ɓuya amma yana nan dawowa daga tafiyar da yayi nan kusa. Ta ɗanji sanyi, amma taji ciwon rashin sanar mata da yayi bai kuma nemeta koda a waya ba balle ta san tanada kima a garesa.

          Da wannan damar Ummi da Mama Jiddah amaryar Sheikh Aliyu Maina da Uwargida ran gida Maimunatu sukai amfani wajen gyare Muhibbat ɗin ciki da bai da kayan gyaran jiki dana fata gangariya da ƙamshi. Tare da zaunar da ita suka fara ɗora mata karatu na musamman akan aure da zamantakewar cikinsa. Haƙoƙin miji akan mace da na macen ma akan mijinta.

       A gefe kuma kayan auren Hibbah da aka shirya tun lokacin auren a gidan da Master ya bada matsayin Muhammad Shuraim tuni an kwashesu an maida inda zasu koma ɗin an jere mata su tsaf.


★★


       A ɓangaren Master ma cike yake da tsanin kewa da buƙatar matarsa. Sai dai yayi ƙoƙari matuƙa ya danne wajen ganin yama Ummi kawaici dan itace da kanta ta buƙaci yabar Hibbah a kaita kamar kowacce mace gidansa ita da su Yaya Muhammad. Bazai iya musa musu ba, dan sunyi matuƙar ƙoƙarin a garesa. Hakan yasashi yin amfani da wannan damar shima yay nasa shirye-shiryen da ƴan ƙannensa bayan jiyyar daya sha ta gajiya da sauran raunin jikinsa.

        Abinda kuma bai sani ba su Habib gagarumin biki suke shiryawa tare da Abdull da su I.G dayay burin hakan akan auren Master sai dai ALLAH bai nufa ba. Dan haka yay ƙudiri da aniyar biyan bashi a yanzu bayan yayi tattaki har gidan Sheikh Aliy Maina sun bada haƙuri akan yanda abubuwa suka faru, kasancewar su Yaya Muhammad suma suna tare da Sheikh Aliy ɗinne akan zaman dama duk sai suka nuna babu komai ƙaddarace ai wadda ta riga fata. Fatansu dai ALLAH yasa hakan shine alkairi ga Master ɗin da Muhhibat a yanzun.


      Al'amarin kamar wasa sai ga Muhibbat ta cika watanni biyu a gida tana jiran tsammani. Tayi wani irin masifar ƙyau da haske dake bama kowa mamaki, su Zahidah na tsokanarta akan cikine. Ita dai bata tanka musu duk da tanajin fargaba har cikin ranta. Dan da gaske watanni biyun nan datai a gida bataga al'adarta ba sam. Sai dai kuma ita sam batajin ciwon komai a jikinta dan haka take fatali da batun nasu.

      Ummi kam a yawan barcin da Hibbahn keyi a kwanakin nan yasata zargin ko cikinne da ita. Sai dai rashin ganin sauran alamomi yasata ajiye zargin nata itama dai.

           A randa Hibban ke cika wata biyu da sati guda a gida aka sallamo Hajiya Mama. Ƙin amsarta su Momy sukayi acan gidan dan haka yaya Abubakar ya kawota nan wajen Ummi. Ummi bata musa ba ta amsheta kodan yaranta da darajar Aliyun ta da bazata taɓa iya manta hallacinsa ba shi da Malam. Ɗaki guda aka warema Hajiya maman ta cigaba da jiyya. Su Yaya Muhammad suka ɗakko mai kula da ita acan ƙauye cikin ƴan uwanta da ƙyar. Ko sau ɗaya Hibbah bata taɓa leƙa ɗakin hajiya mama ba domin dubata. Hakama Ammar da Yaya Umar da sukafi kowa tsanarta. Ummi tayi nasihar harta gaji ta sanya musu ido kawai.


         Shirye-shiryen tarewar Hibbah ake sosai a gidan, dan kwanaki biyu kacal suka rage amarya harta sha lalli ƙafa da hannu, tare da kitso na musamman irinn ƴan maidugiri da wata ƴar da Jiddahn ya Sheikh ke riƙo ta fanin Umminsu tai mata. Gyara kam ta shasa harta gaji, dan bayan gyaran dasu Maimoon uwar gidan yah Sheikh ke mata a ɓangaren mamansu Zahidah ma sun gayyato shahararriyar mai haɗaɗun kayan gyaran jikin nan mai kamfanin *mg's skin care*, tun daga kan mayuka, sabulai kala-kala na maida tsohuwa yarinya. *(08062991549)* akan farashi mai sauƙi da rahusa ta haɗa mata kayyaki na musamman da dorata akan kayan shafa dana gyara na mata masu aji ta kowanne fanni itama tana katalleta.

        Haka kawai yau Hafsat ta tashi da ƙwazabar son yin gasashen kifi saboda ƙwazaba irin tamai ciki. Kasancewar matar Yaya Muhammad ita kuma sam bata shiri da kifin yasa Hafsat tahowa sashen Ummi tayi dan maƙwafta sashen Hafsat da Maimunatu (Kausar) suke. Koda ta gayyaci Hibbah ta tayata ƙin zuwa tai, kamar wasa ƙamshi ya fara sirɗaɗowa falon Hibbah na kwance tana kallo. Da farko dai ta ɗan fara yamutse fuska har Ammar na tsokanarta da cewar gulma. Ƙin kulashi tai dan ita kaɗai tasan mi takeji a tsakkiyar kanta game da ƙamshin kifin nan. Ammar da bai fahimci halin da take a ciki ba ya miƙe yana mata gwalo ya shiga kitchen wajen Hafsat ɗin. Ko mintuna uku baiyi cikakku da shiga ba suka jiyo tamkar gudu a falon. Cikin hanzari suka leƙo dan Hibbah suke zargi dama.


        Hibbah da aman daya yunƙuro mata yaci ƙarfinta dole ta durƙushe tan gab da isa ɗakinta ta sakesa a matuƙar wahale. Kanta suka nufo da gudu cikin tashin hankali da tambayarta lafiya?. Ina bama tasan sunai ba. Dan da alama dai aman baizo da wasaba. Hatta Ummi dake ɗaki tana azkar na yamma da sauri tayo waje. Haka ma mai kulla da Hajiya mama babu shiri ta fito duk suka rufu akan Hibbahr datai matuƙar jigata. Dan ko aman yayi kamar zai tsaya da ƙamshin kifin ya sake shiga hancinta saita sake sabon yun ƙuri.

          Fashewa tai da kuka jikin ta na rawa ta sake mamuƙe hanun Ammar dake riƙe da ita. “Y...ya...ya Ammar banaso ku fita da ki.f.in”. Ta faɗa da ƙyar tana sake sakin sabon kuka. Cikin sauri Hafsat ta nufi kitchen domin fita da kifin, yayinda Ammar ya ɗauka Hibbah ɗin gaba ɗaya sukai ɗakin Ummi dan a samu tabar jin ƙamshin kifin.

        Yanda ta galabaitan dole ne ta baka tausayi, da taimakon Ummi ta gyara mata jikinta a toilet ɗinta da Ammar ya kaita can direct. Kuka take wiwi jikinta duk ya saki harda su ɗan zazzaɓi. Har yanzu kuma jin kamshin kifin take har tsakkiyar ƙwalwar kanta saboda tsaya mata da yay a rai. Ummi data gama gaskata cikine da Hibban ta kamota suka fito a toilet ɗin. Zaunar da ita tai a gado ta fita zuwa ɗakinta ta ɗakko mata wasu kayan. A falo ta wuce Ammar da Hafsat na gyara wajen da Hibbah ta ɓata.

           Ummi na dawowa da kayan ta iske Hibbah harta kwanta. Ɗagota tai ta taimaka mata ta saka kayan tana jera mata sannu tausayin autar tata na ratsata.

        “Ummi ki bani wani abun na shinshina ko zan daina jin ƙamshin banaso zan sakeyin amai”.

     Cikin lallashi Ummi dake murmushi ta shiga shafa kanta bayan ta kwantar da ita a jikinta. “Tanee ki ciresa a ranki kawai shine zaisa kibar jin ƙamshin a hancinki, dan tuni Hafsat ɗin ma ta fitar da shi a sashen nan. Amma faɗamin mikike son ci?”.

        “Ummi banajin yunwa, sai dai kozan samu tumatur masu ƙyau da suka nuna sosai zansha”.

      “Abu mai sauƙi”.

Ummi ta faɗa tana miƙewa bayan ta kwantar da Hibbah. Cikin lokaci ƙanƙanin sai ga Ammar da duk yay kalar tausayi kamar shine mara lafiyan da manya-manyan tumatur masu ƙyau a ƙaramin bowl har kusan goma ya kawo mata. Dan anyi sa'a an kawo musu cefanen dama babu jimawa.

      Sagade yayi yana kallon Hibbah nashan tumatur ɗin cikin rawar jiki tamkar wadda ta samu wani apple ko inibi. A wannan halin su Yaya Umar da suka shigo gidan matansu suka sanar musu suka shigo suka sami Hibban. Su kansu mamakin shan tumatur ɗin suka tsayayi har Yaya Umar na yima Ammar faɗa.

        Amarairaice Hibbah ta ce, “Yaya inasone akwai daɗi”.

       Yaya Umar zaiyi magana Ummi ta ɗan girgiza masa kai. “Karka damu Umar barta tasha. Tunda shi zuciyarta keso shi kaɗai zatasha a zauna lafiya inhar ya zauna.”

        Shiru kawai sukai badan hakan ya musu ba. Hibbah na kammala shan tumatur ɗinta kuwa ta zame ta kwanta dajan bargo tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, nutsuwa na ratsata. Wahalar data sha yasa barci saceta cikin ƙanƙanin lokaci batare data shirya hakan ba.


       Koda ta farka kusan bayan magrib garau ta tashi tamkar ba'ita ba. Sai dai ɗan rashin ƙarfin jiki da takeji shima bamai cutarwa ba. Salloli tayi ta fito falo inda take jiyo hayaniyar yayunta da matansu suna hira. Duk sunyi farin cikin ganinta garas. Suka shiga tambayarta jikinta tana amsa musu cikin shagwabar tata saba musu. Suko da kulawa suketa sake sonjin ko tana son wani abu da zataci. Kanta ta girgiza musu tana kaiwa zaune da faɗin, “A'a yaya ku kwantar da hankalinku zanci duk abinda aka dafa indai babu wancan abun na ɗazu (ko sunansa batason faɗa dan ma karta tuno). Sunji daɗin hakan suka sake mata addu'ar sauƙi mai ɗorewa. Daga haka suka cigaba da hirarsu tana lafe a jikin Umminta da tun ɗazun take cikin tsantsar farin ciki akan baiwar da ALLAH yay mata na albarkar auren ƴaƴan nata biyar reras kusan lokaci guda. Bata yarda tayi zancen cikin dasu ba dan batason ma zancen ya fita har sai Hibbah ta tare gidan mijinta. Shiyyasa tunkan aje ko'ina ta cewa Hafsat ma tai shiru da bakinta ko mijinta karya sani tunda ta lura Ammar shi dama bai fahimci komai ba garan😂.............✍


*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*


_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya💃🏻._


*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu😂💃🏻*.


_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za'a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya😉💃🏻_.


*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻


Kaza akwai 10k

15k

5k

Tsimi 5k 10k

Matsi 5k

Gumba uku 2k

Zumar gorun tula syrup3k

Garuka 3k

Cicccibi 5k

Zakara 20k

Zabo20k

Humra

Turaren tsugunni

Butar tsarki

Maganin infection

Tsimin tabaje

Turaren al,ajab


*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.



_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_

08068526455


*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*


Zaku iya samun mu amanhajar


Facebook

Istagram


Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.


Sai kunzo🥰🥰🥰🥰💃🏻👌🏻.

       


*_Typing📲_*


______________________


*_MATAYEN ƘWARAI SARAKAN ADO DA ƘAWATA JIKI DA KWALLIYA KUNA INA NE?._*


_Maza ku garzayo da gudunku ga mutunuyar taku maida tsohuwa yarinya ta sake dawo muku da sabon salo, sabon sunfarin kayan gyaran jiki na mayika da sabulai ƴan gaske💃🏻._


*Kayan kwalliya na mg's skin care zasu maidaki shalele ƴar ƙwalisa tamkar wata ɗan daren sha biyar koda kina da kishiya ƴar Morocco bata girgizaki ba, balle saurayi ɗan son ƙyale-ƙyale da ƙawa ga burwallensa😂💃🏻*.


_Kayan mg's skin care nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai.


*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻


Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?

Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki

Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘

Soap:3k

Beauty kit:12k

Chat:08062991549

07066210195

Call :07046881166

08064532391

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg's skincare

amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra'ayi🥰

Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲

Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝

Nd guest what🤩

Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃

Pamper your skin🧖‍♀️

Shine like a bride👰🏻

Glow🧚🏻‍♀️


______________________


*_Chapter Forty Nine_*


...........Kamar almara Hibbah ta koma normal, dan cikin ikon ALLAH ma yau da ta kasance ana gobe tarewar tata idan ka ganta bazaka taɓa ɗaukar ta jigata jiya ba. Baƙi sun fara isowa daga ɓangaren dangin Hajiya mama da mai jiyyarta ta sanar dasu ta waya bisa Umarnin hajiya maman ba tare da sanin Ummi ba. Sai abokan arziƙin Ummin na nan cikin gari dake zuwa dan shirin abincin gobe idan ALLAH ya kaimu ɗin, tunda tace biki zatai sosai akan tarewar autar ta. Sannan kuma itace uwar ango ma ta wani fanin dan Isma'il ya cancanci hallaci daga garesu bayan na bashi Hibbah kuma.


_______________


       Su Habib ma da suka dage da shiri daga can ɓangarensu sun ƙagara gobe idan ALLAH ya kaimu tayi Aunty Queen ɗinsu ta dawo gatesu, dan sunyi matuƙar kewarta duk da suna gaisawa da ita su ta wayar Ammar da Master ya basu number. Sun ma zo sun ganta sau biyu bada sanin Master ɗin ba duk da dai Ammar ya gumtsa masa batun zuwan nasu. Dan lokacin shi bayanan ma saboda ƴan tafiye-tafiye da yayi a ɗan tsakanin nan akan wasu ayyukan dayake son kalmashe bakinsu dan hutu yake son ɗauka dogo dazai raɓashe ya ƙwalle da amaryarsa.


*_RANA BATA ƘARYA......_*


       Tabbas rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Dan kuwa a yau aka tashi da gagarumin bikin ƙarin girma daga headquarter na ƴan sanda bisa ƙoƙarin mai gayya mai aiki I.G da wasu manya-manya da suka bada gagaurumar gudunmawa domin girmamawa ƙoƙarin su Master ɗin akan zaƙulo su Dr Sufi dake gidan yari sunacin azabar rayuwa data cututtukan da suka taso musu bisa ƙazantar homo da suka aikata. Dan takai ko a cikin prison ɗin yanzu ba'ako buƙatar son zama kusa dasu saboda shegen warin da sukeyi. master kam shi ba'a ma batunsa. Dan wani irin ƙuraje ke fito masa a jiki na allurar poison ɗin da Master yay masa. Hakama Abba Halilu yana nan yanacin azabar ƙafa da alamun ruɓewarta duk ya bayyana gareshi.


        Wani irin gyara da ado na musamman akaima harabar headquarter ɗin tun a yammacin jiya. Zuwa yau kuwa aka ƙarasa ƙawata ko ina har an fara tarbar manyan baƙi tun kusan ƙarfe bakwai na safe.

         Dan ta ko'ina duk wani mai ruwa da tsaki akan wannan taro yana can yana ƙoƙarin shiryawane domin isowa akan lokaci. Musamman ma amarya mai tariya biyu Hajiya mandiya Muhhibat Aliyu Hamza Gwarzo mai zamani😂😜. Dan wata irin tsadddiyar riga mai azabar ƙyau kalar sararin samaniya su Habib suka aika mata da ita tare da duk wani abinda zai cika adon nata da ƙawatashi. Sai kayan kuma da zatai amfani dasu a wajen ƙwarya-ƙwaryan walimar da suka shirya nacin abinci daga bakwai na dare zuwa goma. Da farko Master da suka sanar masa ya tirje sai da Abdull yasa baki da ƙyar ya taushesa ya amince. Dan koba komai yana son ganin farin cikin ƴan kannen nasa kuma ta wani fanin. Itama mai gayya mai aikin yasan zataso hakan kodan ya goge laifinsa na nanata zancen satota da bata gajiya dayi idan tsiwar ta tashi, tare da ɓoyema ganinta da yayi tamkar almara.


         Cikin ƙanƙanin lokaci mai kwalliya ta tsantsarama Hibbah da zuciyarta ke cike da ɗoki da kewar son ganin mijinta. Sai dai tanata ƙoƙarin dannewa a zahiri. Ana gab da kammalawa Ammar ya shigo yake sanar musu suyi sauri harsu Master sun iso za'a wuce. Babu ɓata lokaci mai kwalliyar ta kammala mata komai ta fito tsaf tamkar wata ƴar daren sha biyar. Ga ƙibar da tayi ta ƙara ƙawata tsarin shigar tata masha ALLAH.

      Ummi kanta da su Zahidah kasa haƙuri sukayi sai da suka tanka wannan ƙyawu da Hibbah tai. Su Yaya Muhammad dake jin wani ɗunbin farin ciki suka zagayeta suna zuba mata ruwan hotuna.

        A haka suka fito da Hibbah harabar gidan inda su Master ya ke tsumayen fitowar ta su. Akan su Habib da ke zagaye da shi cikin shiga iri ɗaya tamkar wasu bodyguard ta fara sauke ido. Taja gajeren numfashi da satar kallon mai gayya mai aiki dake sanye cikin wasu Haɗaɗɗun suit sky blue kalar kayan jikinta. Shi kansa tun fitowar tasu yay mutuwar tsaye yana jan wani hargitsatstsen numfashi da ajiyar zuciya har su Habib na iya jinsa.

     Kunyar Ummi data Yaya Muhammad ta hanashi xuwa ya tareta ya rungume ko zaiji nutsuwar abinda yakeji na ratsa ɓargonsa zuwa cikin jini. Maimakon ya nufi Hibbah sai ya matso kusa da Ummi cikin girmamawa ya gaisheta. Ummi ta amsa cike da fara'a tana sanya masa albarka shi da su Habib da suka ƙaraso suma suna gaida Ummin.

         Ya gaisa dasu Yaya Muhammad ma sama-sama kowa ya shiga mota dan jiransu akeyi. Duk da tsokanar da su Habib kema Hibbah bata iya cewa komai ba dan gaba ɗaya idanun Master sun hanata sukuni. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Suna shiga motar da Habib ya kawosa a ciki ya jawota jikinsa ya rungume. A tare suka saki ajiyar zuciya suna sake ƙanƙame juna har yana mamakinta. Habib dai yi yai tamkar bai gansuba yaja motar suka fice a jere da sauran nasu Yaya Muhammad.

        A cikin kunnenta ya raɗa mata “I miss you so much Baby luv”.

        Hibbah da ɗunbin kewarsa da kunya ke zagaye da ita ta sake cusa kanta jikinsa tana mai shaƙar ƙamshin turarensa da yay mata matuƙar daɗi. Itama a hankali tace, “Ni dai bana kewarka”.

     Sassanyan murmushi ya saku da ɗago fuskarta ya sumbaci goshinta. Kasancewar Habib a wajen ya sashi daurewa bai tsotse janbakin ba. Bai kuma sake magana ba har suka isa wajen taron daya gama cika fam da nutane.

     Tarba ta musamman ta mutunci suka samu. tare da wajen zama da aka tanada dominsu. Ba'a wani ɓata lokaciba wajen fara gudanar da taron daya tara manya-manyan mutane. Inda aka gabatar da abubuwa masu yawa tare da kyaututtuka ga su Master. Aka kuma tayasa murnar aure da kowa ke ɗauka yanzune yayisa. Daga haka akaci akasha taro ya tashi lafiya.

        A yanzu kam dole Hibbah tabi su Ummi suka koma gida tare dan ƙarasa shirin miƙata gidanta nan da anjima. Dan acan ɗinma sun baro baƙi sosai dan ma su Mama Jiddah nan dasu Ummansu Zahidah.


      Kamar da wasa sai gashi anyi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan su Hibbahn, anci ansha an rakwashe an ƙwalle musamman su Habib da suka jone da Ammar sukasha shaftarsu. Zuwa takwas na dare kuma aka haɗu a babban hall ɗin da aka tanada domin gudanar da liyafar cin abinci. Anan ɗin ma ba ƙaramin zauta Master gayun na Hibbah yayi ba. Dan gaba ɗaya ta wani canja masa tamkar ba ita ba. Itama kanta gayun nasa ya matuƙar ɗaukar hankalinta danko sanye yake da shadda ƴar ubansu dataji ɗinkin zamani mai ɗaukar hankali. Anci ansha su Habib sun cashe a filin rawa sai kace wasu ƴan daudu😂. Tun Master na hararsu harya shiga sahun masu dariya duk da ƙoƙarin dannewa da yay tayi. Ƙarfe goma dai-dai taro ya tashi, daga nan kuma aka ɗunguma rakkiyar amarya sabon gidansu inda Master ya ɓoye su Ummi. Zuwa yanzu an gama komai gida ya haɗu matuƙa kai kace wani ƙaramin estate ne. Dansu Musbahu kowa da sashensa matan aure kawai suke jira. Mutane basu wani zauna ba kowa ya kama gabansa akabar amarya da angonta dasu Khalid da suma gajiya ta sakasu kwanciyar wuri a sashin baƙi da suke zaune yanzu kafin matayen nasu su shigo kowa ya koma nasa sashen.


        Master da dama yana gidan abinsa dan tare suka taho da ƴan rakkiyar amarya suna tafiya ya nufi ɗakin Hibbah da kayan tsarabar da aka tanadar mata dan yaga bataci komai ba a wajen liyafar.

     Tana zaune a tsakkiyar gadon tana kwasar kuka kai kace yau ɗin aka fara kawota gareshi. Kayan hannunsa ya ajiye ya nufi gadon yana murmushi, cikin neman tsokana ya ɗaga mayafin yana faɗin, “Haba Hajjaju keda kika dawo wajen mijinki minene na kukan?”.

      Hannu tasa ta ture nasa tana ƙoƙarin juya masa baya ya riƙota yana sakin wata siririyar dariya data nema narkar da Hibbah, dan a cikin kunnenta yakeyi. Ƙoƙarin haɗe bakinsu yakeyi tana ture masa kai cikin bore hardai ya samu nasara. Salon da yake mata da kuma halin da take a ciki yasata miƙa wuya har tana maida murtani. Sai da ya tabbatar ya sakata yin laushi sannan ya barta yana sauke ajiyar zuciya. Kunya ta sata saurin sauka a gadon ta nufi toilet dan fitsari takeji.

          Ta kammala tana ƙoƙarin fitowa sukaci karo da shi zai shiga shi kuma. Hanunta ya kama yana binta da wani kallo ƙasa-ƙasa daya sata kauda kanta daga kallon nasa. “Muje muyi alwala”. Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi tamkar mai gudin ajisu. Ba yanda ta iya dole ta bisa suka koma. koda suka yo alwalar suka fito tare suka gabatar da salla. Yaja musu addu'oi masu tsayi na zaman lafiya da haƙuri da juna Hibbah na amsa masa da amin. Bayan sun kammala duk yanda taso zillewa bai bartaba sai da ya sakata cin abinda ya shigo dashi. Gasasun ƴan shila ne da yogurt dayay mata matuƙar daɗi har tana masa cin zalama da ya bama Master mamaki. Sai dai baice komaiba ya sata yo brush da barin mata ɗakin dan tai shirin barci.

        Har taji daɗi ya fita sai gashi ya dawo tana ƙoƙarin kwanciya. Badan taso hakanba ta kwanta kamar yanda shima kai tsaye gadon ya hawo yay kwanciyarsa hankali kwance.


    Wata irin soyayya ce mai tsayawa a rai da zuciya da Hibbah bazata taɓa mantawa da ita a rayuwartaba Master ya nuna mata a wannan dare. Sai dai ta jigatu matuƙa dan har saida taita masa kuka da magiya amma bai sauraraba sai da ya more kwanakin kewarta tsaf. Tun a daren suka gyara jikinsu suka koma barci, da Asuba suna idar da salla bai sarara ba sai da ya ƙara dan gaba ɗaya ta dagula masa lissafin kansa, saboda gyaran da tasha bana wasa bane ba. Ga ƙaramin ciki a jikinta wanda shi baisan dashi ba yaketa faman bidiri da bireɗensa.

         Yasha taɓara da shagwaɓa dan daƙyar ya lallaɓata suka dawo falo kusan sha ɗaya na safe dan ta samu ta karya. Sun sami ƙayataccen breakfast daga baba saude dasu Habib, tsananin yunwar da Hibbah keji yasata zaman dirshan ta dira kan abincin nan babu sauƙi. Tana gab da gamawa ta buɗe kular ƙarshe da nufin duba abinda ke ciki dan Master yace natane shi bayacin sa. Wani irin dukan kanta ƙamshin farfesun kifin yayi. Cikin zabura ta saki murfin kular tai baya har abin na bama Master tsoro.

     Kanta ta dafe dake juya mata tana masa nuni da hannu akan ya rufe amma bai ganeba. Babu shiri ta saki aman dake taso mata dan ƙamshin kifin sake hauro mata kai yakeyi.

        Da hanzari Master ya miƙe kanta ya riƙota. Ganin aman daya tsaya yake sake taso mata dole ya kwasheta da sauri suka nufi hanyar bedroom. A toilet ya direta yana riƙe da ita harya lafa. Ya gyara mata jikin yana jera mata sannu cikin damuwa da tambayarta dama bata da lafiya ne.?

      Kanta ta girgiza masa a galabaice ga hawaye shaɓe-shaɓe ta sanar masa batason ƙamshin kifi ne. Mamaki ya kamashi dan yasan dai tana cin kifi ai, akwai lokacin da ya taɓa jin su Habib na sanar mata shi baya cin kifi tace saiko ta sakashi yaci wataran saboda ita kifi tamafi sonsa akan nama.

          Saboda laushin da jikinta yayine ya sashi neman number Abdull domin zuwa ya dubata. Babu bata lokaci kuwa Abdull ya iso, sai lokacinne ma su Habib kejin Aunty Queen babu lafiya. Gaba daya suka ɗunguma sashen domin dubata.

         Tun a kallo guda da Abdull yay mata ya fahimci cikine da ita. Amma sai ya bata tsinken gwajin ciki yace su gwada ya gani yanzun. Ana kuwa gwadawa da tsinken ciki ya nuna kansa. Wayyo farin ciki ga waɗan nan ahali ai bama acewa komai. Master kam jin abun yayi tamkar wata almara ko tatsuniya. Ya tsare Hibbah da idanunsa dake canja launi suna tara hawaye. Abdull dake kallonsa ya rungumesa yana mai tayasa murna. Hakama su Habib gaba ɗayansu suka ruƙunkumesa suna ihun murnar zasuyi ɗa.

        Hibbah dai baka gane farin ciki ko akasin hakan tattare da ita. Dan tunda taji ihunsu Salis na hawa mata kai ta rarrafa ta koma ɗaki ta kwanta. Acan Master ya sameta. Ya ƙanƙameta hawayen da yake riƙewa na ziraro masa. Yana hawaye yana murmushi da kissing Hibbah tako ina. Yama rasa ta ina zai bayyana farin cikinsa a rayuwa. Godiya yaketa faman jerama UBANGIJI da kirari a zuciyarsa.


       A gaba ɗaya yinin yau waɗan nan ahali sun yisane cikin wani irin farin ciki mara misali da kwatance. Duk da zuwa azhar Hibbahn ma ta martaye garau tamkar ba itaba. Sai dai ta samu tumatur ɗinta mai yawa tasha dan yanzu bata da abu mafi soyuwa sama da shi.

           Duk da garau ɗin data koma dukan motsinta a idanun Master ne. Kaɗan-kaɗan saiya tambayeta mike mata ciwo? Mitake son ci?. Tun tana cemasa babu komai harta koma tura masa baki irin ya dameta ɗin nan. Ko kaɗan baijin haushi, sai ma murmushi da yakeyi kawai.


_________________________


        Sam Hibbah bata wani laulayi, kifi kuwa tun daga ranar ko su Habib daina cinsa sukai a gidan. Sai wata tsadaddiyar soyayya Master ke nuna mata suna gurzar amarcinsu yanda ya kamata dan cikin nan ba ƙaramin saka masa kwaɗayinta yake ba. Gashi abin ya haɗa da zaman hutu da yakeyi a gidan harna tsahon watanni uku da aka bashi. Tun kwananta uku da dawowa gidan ita ke girkinta da Master, wani lokacin kuma taje sashen su Baba Saude suyi gaba ɗaya, musamman idan Abdull na gidan. Shafta tsakaninta dasu Habib sai abinda yay gaba. Dan ma an sama musu aiki zuwa yanzu ba zaman gidan sukeba sosai sai idan Master na bukatarsu akan wani aikin.

        Komai na Hibbah ya sake canjawa. Ta buɗe ko ina ya cika a jikinta ga ƙiba cikin yana sakata masha ALLAH. Cikinta na watanni huɗu ta fara wani matsanancin laulayi da batayisa a baya ba. Ga shi Master ya koma aiki kuma. Dole Baba Saude ta dawo yini sashen nasu ko yana fita Hibbah ta koma can har sai ya dawo. Dan zuwa yanzu komai bata iyayi sai kwanciya. Ƙarin ruwa kuwa duk bayan kwana biyu sai an mata shi ake samun nutsuwa. Sau biyu Ummi dasu Zahidah na zuwa dubata. Su Yaya Muhammad kam ai basusan adadi ba. Balle Ammar yaji labari wanda kullum babu fashi idan ya dawo school sai ya biyo tanan ya ganta yake iya wucewa gida.


       A cikin wannan tsukun da Hibbah ke dirzar nata laulayin aka saka aurarrakin su Habib da ƴammatansu. Zai kama dai-dai da haihuwar Hibbah insha ALLAH. Bayan saka ranar da kusan sati biyu wani aiki ya tasoma Master zuwa kudancin ƙasar. Dole ya tattara matarsa suka wuce tare dan bazai iya barinta a halin da take ciki ba. Ta tafi da kewar su Musbahu, suma ta barsu da kewarta. Dan hatta Ummi taso Master yabar Hibban anan amma dan karta shigar masa rayuwa tai shiru ta bisu da addu'a.

        Sai kuma tahowar ta saka Hibbah cikin ɗunbin farin ciki dajin daɗi. Dan kai tsaye wajen shakatawa na musamman a bakin ruwa Master ya samar musu masauki. Kasancewar aikin nasa kuma na sirrine ya sai ya koma a real Isma'ill ɗinsa suka sake baje shafukan soyayya da rainon cikinsu da Master ke matuƙar so da ƙauna da fatan fitowarsa duniya lafiya. Ɗan yawon da yake da ita wajaje daban-daban yasata fara samun ƙarfin jikinta, sai dai randa laulayin ya bugar da ita kuma dole ne su kasance a gida. Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gasu da wattani uku da tahowa har sun shiga na Huɗu.

        Taso komawa gida a watan daya gabata dan a farkonsa su Zahidah duk suka haihu kusa da kusa. Sai dai aikin Master dake gab da kammaluwa ya sashi hanata zuwan sai a waya akaita tura mata hoton babys masha ALLAH. Ranar sunayen ne dai da aka haɗe ta birkice masa da kuka harda su zazzaɓi. Sai da ya haɗa da Ummi dasu Yaya Muhammad a masu lallashi sannan ta haƙura. Ammar kuwa ya dage yayta ɗauka mata videon komai yana tura mata. Dan mutane ne sosai suka halarci taron musamman dangin Hajiya mama da ƴan ƙauyen su Ummi. Ita Ummi ma har mamaki da al'ajab abin ya bata. Amma saita ɗau hakan matsayin wani hikima da rahama na UBANGIJI.

       Washe garin suna akai zama na musamman da su kawu ballo game da gida da kayan gadon su Yaya Muhammad ɗin da Halilu yaso handamewa. Duk da dama an raba musu tun lokacin da babansu ya bar duniya sai yanzu aka sake raba abinda ya rage musamman gidan da suka taso dan ance su Momy su tashi. Kuka momy ta dingayi tana neman alfarmar Ummi akan a barsu su zauna Hajiya mama dake kwance tace bata yarda ba. Su Ameera su fitar da miji su Yaya Muhammad su aurar dasu. Ita kuma Momy ta koma can gidan da Mahaifin su Hibbah ya bama Halilu tunkan ya rasu ta cigaba da jiyyar Junaid.

      Dole kuwa haka akayi, dan su Ameera da suka fahimci tsohuwar son tona musu asiri take babu shiri suka kawo ƴan samarinsu da abaya suka raina. Gudun kar wata matsalar ta biyo baya su Yaya Muhammad suka saka bikin a kurkusa. Dan sati uku kacal suka saka. Komai kuma daya shafi kayan ɗaki basuyi ƙyashin yimusu shi ba.


________________


        A satin dasu Hibbah suka dawo a satin aka ɗaura auren su Ameera. Haka taci biki a wahale ta ƙaton ciki Ammar na mata iya shege. Daya kalleta saiya kwashe da dariya. Video kuwa da hotuna yayisu kala-kala. Tun tana kulashi harta daina dan yay bala'in taso rayuwarta gaba shi dasu Habib da ayanzu suka ɗinke abokai shaƙiƙai.

     Bikin dai ba wani armashi yayi ba sosai. Dansu Yaya Muhammad ɗin ma sunfi maida hankali a shirye-shiryen nasu Habib da za'ai satin sama. Wanda Ummi ce matsayin uwar anguma I.G uban anguna. Hatta lefe su Yaya Abubakar haɗa hannu sukai da Master aka haɗa komai na birgewa da nunawa tsara. Ana miƙa amare su Ameera ɗakunansu kowa ya maida hankalinsa akan nasu Habib. Dan Hibbah ma dole ta koma gida dan Master yaƙi yarda akan zata zauna anan har satin bikin. Shi fatansa ma ta haihu lafiya kafin a shiga ruguntsumin taron.............✍

   


*_Chapter Fifty (End)_*


............ALLAH kuwa ya amsa addu'ar tasa. Dan a daren data koma gida kusan ƙarfe uku ta farka da matsananciyar naƙuda da dama kusan sati kenan tanata cinta a tsaye tadaiyi shiru ne kawai dan karya hanata halartar bikin su Amira. A rikice ya miƙe ya kira baba Saude. Wadda tana zuwa ta fahimci haihuwarma ta taho.

     Duk yanda yaso su tafi asibiti hakan bai yuwuba. Dan kuwa dai abin yazo inji mai tsoron wanka. Ansha fama da gwagwagwa kafin ALLAH ya sauki autar Ummi lafiya gab da kiran sallar asubahi. Ta santalo ɗanta namiji mai kama da Ubansa sak. Lokaci da Master ya ɗauki yaron sai ga hawaye na rige-rigen sakkowa kan fuskarsa dan hakan ya tuna masa da randa Mamynsa ta haifi Habib. Ya rungume yaron wata irin ƙaunarsa na rsatsa jini da ɓargonsa. Sai da aka kammala gyara Hibbah tsaf bayan sallar asuba sannan ya shiga ya ganta. Su Habib ma sai lokacin suka sani.

     Wayyo zo kaga murna da ihu. Yaro kuwa gaba ɗaya suka hau rububin ɗaukarsa Hibbah na kallonsu tana dariya da hawaye ita da Master, dan Alhmdllhi batajin wani damuwa a jikinta. Amma duk da haka sai da suka fita asibiti taga likita. Kasancewar babu wata damuwa suka dawo gida da wuri. Inda suka iske matan su Yaya Muhammad dasu Ameera amare cike da gidan. Dan tuni su Idris sun baza batun haihuwar. Hotunan yaro kuwa nata yawo a wayoyin ƴan uwa da abokan arziƙi.


       Master yama yaro huɗuba da *ALIYU HAYDAR, ZAKI GADANGA ƘUSANR YAƘI*. Sosai Hibbah taji daɗi, duk da dai tasan shima sunan mahaifinsa kenan. Ammar kuwa ai cayay shi akaima takwara babu wasu su daddy.

     Tsaye Baba Saude take akan Hibbah hakan yasa Ummi sam bata damu da batun a maidota gida ba tunda biki zasu shiga. Kwana biyu da haihuwa aka dire tarin kayan barka daga su Yaya Abubakar na ban mamaki. Dan har sai da Master yace sunyi yawa ai. Amma suka nuna masa zama su ƙaro kuwa.

     Dole ya tsuke bakinsa yay godiya hakama Hibbah.

      


★★★


      Duk da ɗanyen jego dake a jikin Hibbah haka aka tsunduma hidimar biki, sai dai ita kam babu damar yawan shigi da fici. idan kuwa ta kama dole zaka ganta cikin dogon Hijjab kamar yanda Baba Saude ta tilasta mata sakawa.

     Randa take cika kwanaki shida da haihuwa aka ɗaura gagarumin auren ƙannen Master guda bakwai a babban masallacin juma. Taron aure ne daya samu halartar mutane manya dama jama'ar gari talakawa irinmu yaku bayi. Dan kuwa kowa burinsa nuna halacci ga Master. Zo kaga bakunan anguna uwa gonakin auduga. Sunyi shar dasu abin sha'awa da birgewa.

         Washe gari aka haɗa bikin suna da karasun biki, inda kowa ke nuna bajintarsa. Amaryar jego Hibbah tayi ƙyau harta gaji ita da jariri Hydhar, wanda gaba ɗaya kamaninsa ke rikiɗewa zuwa Habib abin zam-mamaki.

     Iya jigatuwa kowa ya jigatu, anci ansha ankuma raƙashe an ƙwalle yanda ya kamata. Dan kuwa Ammar ma dai yace shimafa auren nan yakeso nanda wata guda kacal, dan maganar gaskiya bazai bari su Habib su ajiye ƴan dugwi-dugwi ba shi yana sake da baki ga Hibbah da ɗa.

    Zuwa dare aka kawo amare ɗakunansu, kowa ya kama gabansa akabar su Hibbah da sauran aiki.


____________________


     Kamar yanda Ammar ya ambata shima kam ALLAH ya amsa masa. Dan bayan bikin su Khalid da wata guda cif aka ɗaura nasa auren da amaryarsa. Hibbah kuwa ta samu nayi. ta tasashi gaba da sheri kala-kala ta rama duk bashin da yaci akanta tsaf.

      Bayan bikin Ammar da kwanaki tara suka wuce Umrah ita da Master ɗinta da Hydhar. Dan Master yace yana buƙatar hutu kasancewar tayi arba'in. Sai da suka fara zuwa ƙasar dubai suka more rayuwarsu na tsahon sati biyu kafin suka wuce saudia domin gabatar da umrah. Daga saudia Canada suka nufa wajen Abdull dake shirin tattaro iyalansa ya dawo gida shima.

     Zokaga murna wajen ƴaƴan Abdull din da matarsa duk da kuwa a waya suka san juna da Hibbah. Hydhar kam ya zama ɗan gata dan koyaushe yana nane da yaran. Da wannan damar su Hibbah da Oganta Master suka sake ɓarje guminsu da gajiya a ƙasar canada.

          satinsu biyu cif a canada suka ruguntsumo da iyalan Abdull suka dawo gida. Inda suka iske rasuwar hajiya mama.


*_AKWANA A TASHI_*


          _A KWANA_ a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rana ta zama dare, dare ya zama kwana, kwanaki sun koma sati, sati sun zama wata. Watanni sun rikiɗe shekara. Kafin cikar wasu buruka shekaru sunta ninkuwa a cikin rayuwar su Hibbah.

        Alhmdllhi zuwa yanzu yaranta uku, hakama su Yaya Muhammad yara uku-uku suke da, dan haihuwar ta cigaba da tafiya musu ne kamar yanda suka fara. Family ya haɗu cif ga Ummi abin birgewa. Hakama ga Master burinsa ya cika. Dan suma su Habib yaransu bibbiyu yanzu suda Ammar. Family biyu sun dunƙule waje guda sun koma zuri'a ɗaya.


     Yau data kasance Friday sauri-sauri Hibbah ke ƙoƙarin kammala ayyukan gidan kafin sojojin gidan su dawo makaranta. Dan Hydhar da yaransu Habib na farko duk an sakasu, sai ɗiyarta ta biyu mai sunan Mamyn su Master suna kiranta mimi. sai na ƙarshen da shima rarrafe yake ko ina mai sunan Master ɗin. Wato Isma'il, suna kiransa Ansar.

      Kasancewar duk juma'a a tare suke haɗuwa da matan su Zaidu suyi girki mai yawa da ake fita da shi sadaka shiyyasa komai bataiba a sashen nata daya danganci abinci. Sai ɗan fruit salad data shiryama Master da fura damammiya da taji kayan haɗi.

       Cikin ƙanƙanin lokaci ta saka ƙamshi ta faɗa wanka, dan Ansar na wajen Sharifat data zama budurwa. Dan ayanzu hakama a wajenta take ta bar hannun baba saude dake fama da ƙafa zuwa na tsufa. Rigimar da yaketa tsilala mata ce tasa Sharifat ɗaukarsa suka tafi can compound inda matan su Adam ke girki. Dan dama ba barinta sukeyi tayi ba ita, sai dai ta duba abinda baiyiba.

     Suna tsananin bata girma kamar yanda suka samu mazajensu na mata itada Masternsu. Ita kuma ta tsare mutuncinta bata bada wata ƙofar da raini zai shiga tsakaninta da wani a cikinsu ba. Yaransu duk ta haɗe da nata tana kulawa da basu tarbiyya kamar yanda suma sukeyi. Koyaya taga saɓanin zai shiga tsakaninsu zatai iya ƙoƙarin ta taga ta gyara komai cikin hikima.......

      Da sauri ta buɗe idanunta saboda jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Ta sharce ruwan dake sauka mata a fuska tana kallonsa dan dama tasan sai shi ɗin. Harara ya sakar mata yana kwance towel ɗin jikinsa ya shigo wajen wankan da dungure mata kanta. “Yarinya kinsan dai kin saɓa doka ko? To wankanki baiyiba sai kin koma farko”.

         Fuska ta ɗan ɓata da turo hanunsa dake ƙoƙarin ɗora mata soson daya haɗama kumfa. “Ban yarda da wayon nan naka ba Daddyn Hydhar. Ai yanzu muka gama waya amma baka sanarmin kana hanyar shigowa gida ba”.

         “Kinma isa”. Ya faɗa da dungure mata kai ya turata jikinsa yana goga mata sosan. Son ƙwace jikinta ta cigaba dayi amma ya hana. Daga haka suka koma kokawarsu ta masoya suna dariya. Har dai takai an koma asalin soyayyar datafi ta kokawar wanka. Cikin nishaɗi da farin ciki suka kammala wankan nasu dana abinda ya biyo baya suka fito yana tsokanarta da fitinanniya.

         Dariya tayi da yarfa masa ruwan hanunta. Cikin ɗaga gira tace, “Kai kuma Master na fitinannun miye sunanka?”.

       “Zona faɗa miki”

Da sauri ta zille ganin zai damƙota. “ALLAH zaka makara salla ga sojojinka can kuma da alama sun dawo suma”.

     Master dake ƙarasawa gaban Mirror yana goge jikinsa fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Aini na ɗakkosu a school. Dan yau ma tare dasu zanje massallaci. Na bar yarda su Habib namin wayo”.

        Ƙarasowa Hibbah tai garesa ta rungumosa ta baya da kwantar da kanta a gadon bayansa tana murmushi. “Ina bayanka big daddy. Dan kuwa dama kullun mitar yaran nan big Daddy bai zuwa dasu massallacin juma'a ne.”

      Hanunta ya kamo ya zagayo da ita ya jingina da mirror ɗin. Yaɗan lakace hancinta da sumbatar lips ɗinta. “Insha ALLAH zan gyara baby luv. Koda kinga ran juma'a ban dawo akan lokaci ba, kiyi azamar kirana ki tunamin alƙawarin sojojina”.

        Rungumesa tai tana murmushi da sumbatar ƙirjinsa. Shima ya rungumetan ransa fes da tarin so da ƙaunarta.

      Da taimakonta ya shirya cikin ɗanyar shadda fara ƙal harda murza hula. Itama ta kimtsa sauri-sauri suka fito tare suna baza ƙamshi. A falo suka iske su Hydhar daketa faman hayaniya har an gama shiryasu cikin nasu shaddojin farare tas irin ɗaya mazansu da matansu. Da gudu sukayo kan Hibbah duk suka rungumeta suna faɗin “Big Mommy Oyoyo”.

         Durƙushewa tai itama cikinsu tana mai rungumesu da faɗin “Oyoyo sojojin big daddy Ya school?”.

       Atare suka amsa mata da Alhmdllh. Ta miƙa hannu ta kamo Mimi dake gefe tana tunzura baki fuskarta duk hawaye. “Kai! Kai waye ya jangwalo min uwa a gidan nan ne?”.

       Duk juyawa sukai suna kallon mimin har Master dake amsa waya. Mimi ta sake taɓe baki tana nuna Sudies. “Yaya Sudies ne ya cimin cake ɗina a wajen Ammi”.

       Katse wayar Master yayi, ya zirata aljihu yana matsawa inda Mimin take. Cak ya ɗauketa tare da sumbatar kumatunta. “Mamyna shine shagwaɓa kuma bai tashi ba sai yanzun?. Maybe rowanki kikai masa shiyyasa ya ɗiba ai.”

      “Big daddy ƙaryane, nima ta shamin juice ne shiyyasa na mincini cake ɗinta”.

     Cewar Sudies yana matsowa kusa da Master. Dire Mimi yayi kusa da Sudies ɗin ya ɗan duƙo gabansu ya kama hanunsu ya haɗe waje guda. “To tunda kowa yama kowa a shirya. A yafema juna kuma”.

     Kallon juna Mimi da Sudies sukayi, Sudies yasa hannu ya sharema Mimi hawayenta. “Sorry sweet heart bazan sake ba ki yafemin”.

      Mimi dake murmushinta mai kama dana Hibbah tace, “Nima sorry yaya Sudies ka yafemin”. Sai suka rungume juna. Tafi su Hydhar suka farayi musu kamar yanda aka koyar dasu. Master dake murmushi ya sumbaci kumatunsu ɗaya bayan ɗaya yana sanya musu albarka.

    Hibbah dake dariyar wannan hali na Mimi da gaba ɗaya ita ta biyo tace, “Mamana to azo amin oyoyo ɗin idan an huce”. Da gudu Mimi tazo ta faɗa jikinta.

         Master yay dariya da faɗin “Like mother like daughter”.

     

     Su Habib dake tsaye suma duk suna kallonsu dariyar suke musu. Suka ƙaraso cikin falon Khalid ɗauke da Ansar daya amso hanun Sharifat. Yana ganin Master ya fara miƙa masa hannu. Amsarsa yay yana faɗin, “Oh my sweet Darling ina ka shigane ban gankaba”. Ya sumbashi kumatun yaron mai tsanain kamanni da shi da kullum ake gaddama a gidan akan waya biyo?. Hibbah da Habib dai sai dai suyi dariya kawai dan sunsan Master ne tamkar yayi kaki ya ajiye.



      Ganin zasu makara salla suka fice. Aka bar Ansar na kwasar kuka shi sai ya bisu. Lallashinsa Hibbah ta dingayi daga ƙatshe ta goyasa dai.


      Ana idar da salla basu jimaba a massallaci suka dawo, can cikin garden aka kai tabarmi aka baje tamkar yanda suka saba. Cikin ado da gayu suma matan su Musbahu duk suka iso garden ɗin, cikin girmamawa suke gaida babban yaya Master. Shiko yana amsa musu da kulawa tamkar yanda ya saba. Gaba ɗayansu har baba saude suka ci abincinsu hankali kwance zukatansu fes da farin ciki. Bayan sun kammala su Hibbah suka gyara wajen yara kuma suka fara wasansu.


     Bayan sallar la'asar kowa yayo shiri cikin kayan ƙwallo su Habib da yaran har Master suka baje a compound suna wasanninsu cike da farin ciki da tsantsar ƙaunar junan da baka isa cewa suɗin ba jini ɗaya baneba. Basu bar wajen ba sai magriba. Sai da sukai har sallar isha'i suka dawo gidan, kowa ya nufi sashensa domin hutawa da iyalansa.


Washe gari gaba ɗayansu suka dunguma gidan Ummi yini. Idan wannan satin sukaje, wani satin sai su Yaya Muhammad da matansu suma da yaransu suzo nan. Lahadi kuma kowa ya ɗauka matarsa su tafi inda yake buƙata. Ko gidansu ko yawon da shi yafi buƙata.✍😭


_Alhamdulillahi_


_To masoya nima dai bara na shaƙata anan dan maganar gaskiya na rubutu. Abinda na faɗa dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladan. Wanda nai kuskure ALLAH ya yafe mana baki ɗaya._


*_Littafin TAKUN SAƘA ƙirkirarren labarine bawai gaske ba. Idan kayi karo da abinda kai kake gani a mahangarsa tamkar bazai yuwu ba sai ka ɗaulesa matsayin nishaɗi da marubuci kansa domin ƙawata labarin sa. Abinda yazo domin tunatarwa kuwa sai ka gwada shi ko zaka dace. Wanda ya baka haushi kayi haƙuri haka rayuwa take dama ba komai akeyi dan birgewa ba. Wanda ya baƙanta ranka ma kayi haƙuri rayuwa akwai zaƙi a cikinta akwai ɗaci. Abinda kaso gani baizo a yanda kaso ɗin ba kayi haƙuri ajizancine irin na ɗan adam mai mantuwa da gaggawa._*


_Akoda yaushe ZAFFA BIYAR na godiya a gareku masoya, yanda baku gajiyaba wajen bibiyarmu, muma bazamu gajiyaba wajen yi muku godiya da ƙaunarku akoda yaushe. ALLAH ya barmu tare, alkairinsa yakai gareku aduk inda kuke a faɗin duniya😘😍😘😍😍😍🤙🏻_.


*Na yafema dukkan wanda ya ɓatan rai a wannan rubutu, nima ina neman afuwa da gafarar kowa dan zata iya yuwuwa wannan shine littafi na ƙarshe da _Bilyn Abdull_ zata rubuta a duniya😭🙏🏻. ALLAH ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. ALLAH yasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin ciki a garemu. ALLAH ka zaunar da ƙasarmu lafiya ka azurtamu da shuwagabanni na gari. Ka shiryemu muma talakawan ka gyara mana zukatanmu gurɓatattu*😭😭😭🙏🏻


_Sai mun haɗu a zafafa na gaba idan da rabon hakan_.


*_BILYN ABDULL CE😘🤙🏻_*


_______________________


TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

No comments