Furar Danko Book 02 Page 28

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣


___________________


*3 DAYS CLASS*


Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rarar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rarar kudinne sakamakon  rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni 


Class ze fara ranar jumaa insha Allah 


👉 Masu bukatar tafiya da kudinsu ba scholarship ba, Muna yin study & work ko working visa, a takaitaccen lokaci, working visa Qatar munayi a sati daya, Canada study & working visa a 4 to 5 months, Oman working visa a 7 days insha Allah, Maxico Tour visa 1 month


_________________


.......Har dare Lulu bata sake saka Smart a idonta ba. Suna can sunyi busy shi da su Usman. Sai ma zuwa yamma ne da kewarta ya ishesa ya sa Usman yay masa kiranta a wayar Mamy duk da tsiyar da yeke masa bai kulashi ba. Gaisuwa kwai sukai a wayar ya tambayi AA tana amsa masa cikin basarwar nan tata. Gajeren Murmushi kawai yayi da jinjina jan aji da son tsare girma irin na Lulu. Ya jima baiga mace mai ɗankaren basar da abu ba irinta. Shi kaɗai yake iya gane wacece matar tasa, shiyyasa yake sarrafata a salon da takan zurma ta saki masa jiki batare da ita kanta tana sanin ta zurma ɗin ba. Dan ita Lulu zuma ce, idan kace ma zaka bita da wutar maimakon cin nasara kai wutar zata dawo ta baibaiye ne. Shiyyasa yake amsar zaƙin nata da harbin duka gaba ɗaya sannan ya bita da feshin furanni masu ƙamshi...

        Lulu tayi mamakin ganin irin ƙwarya-ƙwaryar liyafar da aka shirya cikin ƙanƙanin lokaci nan. Ba ita ba hatta su Ammah sunyi mamakin hakan. Sai dai Ammah taji daɗi sosai. Har dare suna abu guda. Bayan sun nitsa ɗin domin su huta ɗin ma gajiya ta hanasu zama a gidan. Lokacin da ya shigo ɗakin musu sai da safe Lulu ma tayi barci saboda alluran da ake mata. Yaronsa kawai yay ma addu'oi da kiss, idon Ammah kuma ya katangesa ga zuwa inda Lulun take sai dai kallo da ga nesa.


      Washe garin cikar sati guda da haihuwar AA suka wayi gari da shagalinsu da kuma isowar Ahmad da Coach, dan Smart yace idan zai iya ɓoyema kowa banda mutanen nan biyu. Yaro yasha addu'a a wajen Coach da Ahmad, Lulu da Smart kuma sun sha sheri wajen Ahmad dan sai da Lulu ta koma ɓoyewa idan taji maganarsa. Duk da bawani yawane da su ba abin dolene ya ƙayatar da mai kallo. Kamar yanda Smart ya faɗa an yankama AA ƙaton ragon turawa, a take kuma aka gashe shi gashi mai ƙyau da tsafta ya shiga jerin abinda za'aci a wajen shagalin. Duk da Lulu na dojewa haka dai dole ta shirya a cikin kayan da Mammy ta kawo mata sabuwar doguwar rigar shadda babba sosai da bazata takura mata ba saboda ciwonta. A kallo ɗaya mai kallo zai san shaddar taja kuɗi, maiƙon da take ma kawai da stones work da aka zuba mata na azaba abin ba'a magana. Bawai an ɗinka kayan bane dan wannan taron, kayan Mamy ne ta ɗinka abinta sai dai bata taɓa sakawa ba. Tunda wannan ta taso sai kawai ta ce Lulu tai amfani da su. Karo na farko Lulu tasa kayan da ba fitet ba a jikinta. Amma sai tai ƙyau sosai musamman da Ummita ta mata ɗauri mai ƙyau sosai, ƙanwar Usman da sai yau suka fara ganinta tai mata kwalliya tana dojewa ta na komai sai da akayi. AA ma an shiryashi cikin wasu tsadaddun kayan yara masu taushi da ƙayatarwa da Abbiensa ya siya masa. Angon jego ma yayi nasa ƙyawun cikin lallausan farin yadi da ya zauna masa ɗas ya fito a cikakken bahaushen sa ɗan Nigeria dan harda hula. Ita kanta Lulu a kallo ɗaya data masa ta sake tabbatar da jiya fa ba yau bace, ƴan maza sun gama cika mazaje sai dai fatan tsahon rai kawai da gamawa da iyaye lafiya. Yanda yake satar kallonta haka take satar kallonsa. Sai dai in sun kama juna ta hararesa ta basar. Yakanyi murmushi ya ɗauke kansa kawai. A haka dai aka fara ɗan taron da iyakar sune sai Dr Lameer da iyalinsa da ƙanwar Usman da boy friend ɗinta data gayyato. Sai abokan Usman biyu da suna ganin Smart suka shaida shi kasancewar su masoya ƙwallo, sun kuma bibiyi wasan link na ƙasar England. Ɗaya ma ɗan can ƙasar ɗinne. Lulu dai tayi mamakin a ina suka kwasosu? Da yanda suke girmama Smart ɗin da wani tattalinsa duk ya ɗaure kanta dan kowa dai yasan waye bature. Sai dai batace komai ba dai ta bar abinta a zuciya tana taɓe baki. Gaba ɗaya taron nasu dai basu fi su ashirin ba. An kuma yisa cike da birgewa da ƙayatarwa, gashi babu wata hayaniya sai ɗan cool music da aka saka na waƙoƙin masoya, duk da dai Ahmad ya saka waƙar data shiga har cikin jini da ɓargon Lulu da Smart ta hausa. Wato (Labarina baya zama nawa ta Salim Smart da KEWA ta Auta Waziri). Amma da farko basu saka ba saboda su Abbah. Sai da sukai addu'oi wa jariri da mai jego dama uban jego sannan. Can cikin lambun Abbah da Daddy da mahaifin Usman suka koma abinsu suka baje suna hirarsu ta dattijai da tarin abinci da aka shirya musu. Yayinda Ahmad da Usman da hali yazo ɗaya a rawar kai suka warware sautin sai dai bamai hayaniya ba. Ansha hotuna kala da iri, sai dai a duk sanda za'ai Smart na naniƙe da Lulu, idan da namiji za'ai tana gefensa ta inda babu kowa bai yarda wani ya raɓar masa mata ba. Tunma su Usman basu farga ba har suka fahimci mutumin nasu fa akwai kishi. Sai suka kama kansu suma yanda bazasu takaloshi ba. Ahmad ne dai kam ya addabesa tako ina da ina, sai dai tunda ya iso AA na hannunsa ya kasa bama kowa. Har cikin rai ƙaunar yaron yake ji tamkar shiya haifa. Yace dai surukinsa ne dan shi da Maryam ɗinsa zasu haifa masa mata. Anyi dariyar zancen nashi, yayin da Smart ya ce, “ALLAH ya shiryeka kai dai. Kadai fara tara ƴaƴa sai ka fara canjawa”.

        “To dama ance maka ban canja bane. Kana ganin har na fara furfura zuwan My Son duniya kuma surukina.” cewar Ahmad yana hararar Smart. Murmushi kawai yay masa da girgiza kai. Taro kam Alhmdllh, sai dai Lulu ana kammala hotuna ta koma ciki wajen Ammah da Mamy da suka basu waje suma saboda yanayin jikinta. Shima dai AA ba'a saki jiki da shi a wajen ba saboda sanyi. Sun ɗan samu gift dai-dai misali, zuwa dare taro ya tashi kowa ya kama gabansa. Gajiya ɗan kai da kawon da suka sha a yinin jiya yasa su Smart wucewa da wuri domin kwanciya.


      Washe gari suka tashi Lulu nata rakin ciwon kai. Sai da Ammah tai mata addu'oi a ruwa tasha aka kama mata kan sannan. Lokacin da su Smart suka iso ya lafa mata. Tana cikin rubutu a littafinta Smart ya shigo da sallama su Ahmad biye da shi. Sai da ta saka mayafi yace su shigo. Sun gaisa da tambayar juna gajiyar taro Ahmad ya ɗan tsatstsokaneta sannan suka fito suka barsu. Smart da tun shigowarsa hankalinsa ke akan book ɗin da takema rubutu sanda ya shigo ta ɓoye. Suna fita ya kai hannu bayanta zai ɗauki littafin tai saurin buge masa hannu tana ɓata fuska. Idanun nan nasa ya kafeta da su babu walwala sam tare da shi. Duk sai taji ta daburce saboda mugun kwarijin ya mata da cika waje. Shima babu wasa a tattare da shi murya a dake ya furta, “Kinada wani abun ɓoyewa ne da kike ganin saninsa a gareni illa ne?”.

      Fuska ta tsuke cikin cuna baki batare data amsa masa ba. Shima sai ya sake dakewa da koma mata Smart ɗin nan mai ɗaukar kai da manna mata hauka sanda yana drivern ta. A kausashe ya furta, “In ma baki son na sani kin makaro. Domin ɗayan littafin ai yana gareni. Banyi niyyar karantawa bane kawai dan nafi son jin komai daga bakinki ba'a rubuce ba.” Da sauri ta ɗago tana kallonsa, ya ɗauke kansa gefe kamar bai ganta ba. Sai kawai taji hawaye sun cika mata ido. Cikin rawar murya ta ce, “Da gaske kakeyi?”.

       “Na miki kama da ɗan wasan kwaikwayo ne da zan miki ƙarya?. Mawaddat ɓoye-ɓoyen nan bazai kaiki ko'ina ba face cigaba da dasa miki damuwar da zata iya maidaki ga abinda kika baro. Mi kike ɓoyewa? Miye baki son a sani? A zatona ko zaki iya cigaba da binnewa kowa abinda kike kallo a sirrinki ni zan kasance ba'a cikinsu ba saboda kasancewata mafi ƙololuwar SIRINKI a yanzu. Amma bazan cigaba da takura miki son sani ba ki cigaba da riƙon abunki in dai nine bazan sake tambayarki ba”. Ya ƙare maganar kamar cikin ƴar fusata zai juya yabar ɗakin. Hannunsa ta riƙo da sauri, hakanne ya sashi tsayawa cak sai dai bai juyo ba, ya dai lumshe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Itama batare data tashi ba cikin shashshekar kukan da ke sukar masa zuciya a hankali ta furta, “Aliyu ban san miyasa kake son ji ba? Babu wani abin sha'awa ko birgewa a son jin abinda ya shuɗe da ga tarihin rayuwata. Babu wani abin alfahari ko ƙayatarwa face baƙin ciki da takaici a cikin jiyana. Taya zan faɗa maka na taɓa kashe mutum da hannayen nan nawa ne?, kuma wlhy ban taɓa jin nadamar aikatawar ba har yau har gobe da ma ƙarshen numfashi na. Aliyu ban san taya kake son na faɗa maka na rasa Nanny na data raineni tamkar uwa ba a dalilin kisan da nayi ba, ta amshi laifin daba nata ba, ta rasa ranta a dalili na, Aliyu alhakinta bazai barni na rayu cikin salama ba...” ta sake sakin kuka mai tsuma zuciya.

       Sosai shima yake haɗiyar zuciya, maƙogwaronsa sai faman kai kawo yake a cikin wuyansa. Idanun maza sun masifar kaɗawa. Da ƙyar ya iya controlling temper ɗinsa tare da firzar da numfashi mai nauyi ya juyo a hankali gareta. Har lokacin hannunta a cikin nasa ya zauna a kusa da ita. Jikinsa ya jawota ya rungume, hakan sai ya bata damar sake sakin kuka tana ƙanƙamesa kamar mai gudun a rabasu. Bai hanata ba, sai tambaya da ya jeho mata kai tsaye. “Taya akai kika aikata kisan kai? Dan nasan kinada dalili mai ƙarfi Mawaddat, bakiyi kalar masu aikata irin wannan laifin bisa son zuciya ba. Please faɗamin miya faru a shekarun baya a tsakaninki da Nanny ɗinki?”.

         Cikin haɗiyar zuciya da shashshekar kuka ta furta, “Johanna itace Nanny na dana buɗa ido na gani a tare da ni tamkar uwa mahaifiya. Duk da dai kafin a kaini gareta na ɗan rayu a Nigeria hannun mahaifina da matarsa, sai dai babu abinda zan iya tunawa a wannan rayuwar saboda ƙarancin shekaru na. Nanny na da nake kira da Mah-mah Ta raineni ne tamkar zinariya, tana bani dukkan gata da uwa ke bama ƴaƴa duk da kasancewarta kafira. Bata taɓa cewa nabi addininta ba balle akai gata tilasta ni. Duk da na kasance mai tsiwa da rashin ji komai nai a gareta abin farin ciki ne, sai taga zan kauce da yawa ne take saurin gyara min duk da bata kasance muslma ba. Daddy na yawan zuwa gareni, dan haka nake ɗauka shi da ita duk iyayena ne, sai da na fara ɗan wayo na fara damuwa akan ƙin kwana da Daddyna keyi a gidanmu idan yazo Germany, ya yarda ya yini da ni a gida koma ya ɗaukeni mu fita yawo amma dare nayi zai wuce masaukinsa. Nakan masa ƙorafin hakan amma sai yay murmushi kawai. Itama idan na tambayeta miyasa Daddyna baya kwana tare da mu kamar sauran abokaina da iyayensu takance min aiki ne ke hanashi hakan.........✍️

No comments