Furar Danko Book 02 Page 29

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗





           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣




........Ban fara shan jinin jikina ba sai dana ga wani yana yawan zuwa wajen Mah-mah. Atake naji na tsanesa, ko yazo gidan bana kulashi duk iya maganar da zai min, ko abu ya kawo min bana amsa. Idan kuma ya ba Mah-mah ta bani indai nasan shine ya kawo bana ci. Yana shiga damuwa da yanda nake masan har ya kasa daurewa ya sanar da Daddy. A wani zuwa da Daddy yay ne yake sanar min ai Felix yaronsa ne na amana, duk wani kai-kawo akan business ɗinsa na Germany shine ke masa. Yana zuwa wajen Mah-mah Kuma saboda harkar business ɗinne, dan itama akwai abinda take riƙe masa. Wannan zance na Daddy ya sani ɗan sakin jikina da shi, a dalilin haka na gane ashe basu da wata alaƙa da Mah-mah ɗina, A duk sanda yazo suna tattauna harkar business ɗin ne kam da gaske. Hakan sai ya sani sake sakin jiki da shi har ina kiransa Uncle, yakan ɗauke ni randa ba makaranta ya fita dani yawo yayo min shopping kamar hauka. A wani zuwa da Uncle You yayi ne yaga wannan al'amari, cikin tashin hankali naji yanama Daddy faɗan mizai sa ya bar Felix ya shiga jikina har irin hakan a matsayinsa na namiji da Business ne kawai ya haɗa su, miyasa ma ya nuna masa wannan gidan. Shi ya yarda da Mah-mah na shiyyasa damuwarsa a kasancewarta mai kula dani ilimin addini da ake neman tauyeni ne kawai. Amma sam baiji ya yarda da Felix ba sam. Naji haushin Uncle You a lokacin, dan akwai shaƙuwa tsakanina da Felix, Kun san yaro dai. Har Uncle You ya gama min hutu a wannan karon ban saki jiki da shi ba, bai damuba bai kuma daina kulani ba. Tun daga wannan lokacin naga Felix ya daina zuwa gidan. Ba irin tambayar da bamma Mah-mah ba sai tace min yayi tafiya ne mai nisa. Akwana a tashi na fara mantawa da Felix a zuciyata, sai wataran katsam gashi, a lokacin inada shekaru goma sha kusan uku, dan kaɗanne ya rage na ƙarasa tunda har secondary na shiga, duk da dai su kasan karatun nasu bawai kamar namu ne na Nigeria ba, shiyyasa ma na kammala karatuna da wuri gaba ɗaya a ƙarancin shekaru. Zuwa lokacin na manta da shi, shiyyasa ban wani sake masa ba, ga shi kuma na fara hankali. Yaso jana jikinsa amma sam naƙi sake masa, idan ma yazo gidan ko fitowa falo bana yi sam. Ni ban san ashe wannan abun naci masa rai ba har yanama Mah-mah korafi, takanyi dariya tace masa na girma ne yanzu na zama ƴammata na fara kuma mantawa da shi..

       A wata ranar asabar Mah-mah ta wuce wajen ibadarsu sai ni kawai a gida da mai aikinmu. Ina ɗakina na baza books na makaranta ina dubawa, jikina daga ni sai ɗan bomshot da best, kaina ko ɗan kwali babu sai jin mutum nai kawai ya faɗo min. Raina ya ɓaci ganin Felix. Dan ko sanda inada ƙuruciya baya shigamin ɗaki ai, balle yanzu da a iyayin tashi cikin jar fata yake sakani jin na zama ƴammata ni da ƙawayena. Cikin masifa nace mizaisa ya shigo min ɗaki, ya fita bana son shirme. Maimakon ya fitan sai ya tsaya kawai yana kallona, dan gaskiya inada tsiwa sosai tun da ƙarancin shekaru na. Dariya ya shigayi irin ta shaƙiyanci, batare da ya damu da masifar da nake masan ba ya murzama ƙofa key ya nufoni. Da farko na ɗauki al'amarin nasa wasa, sai da naga yana yunƙurin rungumoni jikinsa ne raina ya ɓaci, duka na shiga kai masa ina janye jikina, ganin bazan bashi haɗin kai a yanda yake so ba ya kamani ya ɗaure, hankalina ya tabbatar min da yana son wulaƙantamin rayuwa ne. Ina kuka da roƙonsa da magiya amma bai sauraren ba ya ciremin kaya kaf shima ya cire nashi. Aliyu wlhy ban taɓa sanin minene tashin hankali ba sai a wannan ranar, tsabar tsoratar da nai da ganinsa babu sutura ban san na suma ba, sai da ya ɗiba ruwan sanyi a Despenser ɗin ɗakina ya sheƙamin na farfaɗo. Zaginsa na shigayi cikin matsanancin tashin hankali bayan dawowa a hayyacina ina tofa masa yawu a fuska, shiko ya shiga marina yana dariya, da yaga na ƙi daina zagin nasa marin ma bazai masa ba ya cire belt dinsa ya dinga dukana da ita, tamkar ya samu wata babbar mace yay min duka na hauka, har yanzu da sauran tabbunan dukan a jikina wasu basu ƙarasa ɓacewa ba. Ga jini a sayin inda ya bugeni, ga kumburin fuska data sha mari da fashewar baki, ga haɓo da dukan da yay min a gefen ido duk bai duba wannan ba ya nema haike min. Na riga na suma saboda firgita dan ya na gab da cimma burinsa na suman, shiyyasa ban san yanda akai Mah-mah ta samu nasarar shigowa ɗakin ba, ita ce ta kuɓutar dani batare da ya samu nasara a kaina ba. Kiciniyar kwanceni da dukan da yake mata ya sani farfaɗowa, sai dai kafin ta ƙarasa kwanceni ya kaita ƙasa da duka itama. Ina kuka da zaginsa a saman lips dan ko magana bana iyayi dan wahala ya kekketa mata suturar jikinta ya ɗaureta kamar yanda ya mun, a gaban idona ya keta mata mutuncinta ta hanyar mummunan fyaɗe, ya kuma juyata ta baya nan ma ya wulaƙantata. Suma ta biyu ko a lokacin dan tashin hankali. Ban taɓa sanin ana suma a dawo a suma a dawo ba sai a wannan ranar. Kaina ya dawo yana wata ƴar iskar dariya da tabbatar min sai ya wulaƙanta min rayuwa fiye da yanda yay ma Mah-mah dake kwance cikin jini face-face bata ko numfashi sosai. Ban san yanda akai wani irin ƙarfi yazo min ba na halbesa da ƙafata a gabansa, azaba ta sakashi duƙewa, pen ɗina da nake aiki da shi kafin shigowarsa na ɗauka na buga masa a wuya, banyi tunanin zai iya mutuwa ba, a haukana hakan da zan masa ai zai tashi idan aka kaisa asibiti kamar yanda naga a film yana faruwa. A take ya saki razananniyar ƙara da zubewa a ƙasa hannunsa ɗaya riƙe da gabansa ɗaya ya riƙe wuyansa. Dai-dai nan mai aikinmu ta shigo, ashe matsiyacin aikenta yay kasuwa dan ya samu damar min illa ALLAH ya kawo Mah-mah ta dawo gidan. Ihunsa ya sata shigowa, koda ta shigo taga a yanda muke mu duka ukun sai itama ta fasa ihu da komawa da gudu, itace tai kiran ƴan sanda, abinka da inda akasan kimar ɗan adam, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu sun iso, a gaggauce aka tattaramu duka zuwa asibiti muduka ukun. Ban dawo a yahhacina ba sai bayan kwana biyu, a hakan ma ko yaya namiji yazo kusa dani na dinga firgita kenan harda ihu ina roƙon karya cutar dani, duk wanda ya ganni sai ya tausaya min sosai. Ashe nawa wasane, dan Mah-mah ita gaba ɗaya ma brain ɗinta ta birkice, ga wata irin jijjiga da jikinta keyi, a taƙaice dai kamar ta haukace ma kawai..... Felix Kuwa ashe abinda nai masa ya mutu. Ƴan uwansa sunce bazasu yarda ba tunda kashesa akayi, wannan dalilin ne ya saka aka maida hankali akan bama Mah-mah kulawa harta ɗan dawo hayyacinta, an tattara case zuwa kotu. Daddy bai zo ba, Uncle Yousuf bai zo ba har sai da muka samu kusan sati uku a asibitin, zuwa lokacin an miƙa case kotu har an ajiye ranar zaman shari'a. Ana gobe fara shari'ar Daddy ya iso Germany, ya shiga matsanancin tashin hankali da ɓacin rai akan abinda Felix ya aikata, a ranar bai zauna ba sai da ya samo ƙwararren lawyer, washe gari aka shiga kotu. Mah-mah, bata wani bari shari'ar ta ɗauki lokaci ba ta ce itace ta kashe Felix saboda yayi mata fyaɗe ta ƙarfi. Duk yanda naso faɗar gaskiyar abinda ya faru bani da dama saboda tun a daren jiya ta roƙeni akan kar nace komai, na rufa mata asiri kar Daddy yasan ni Felix ya fara hara, dan hakan zaisa ya kalli rainon da tai min a matsayin sakaci, koma ya ɗauka dama a haka take sakaci da al'amarina tun can baya. Kawai idan anje kotu zatace a wajen cetonta ne Felix yay min wanna dukan. Yanda ta tsara ɗin haka ta faɗa a kotu, bayan gama saurarenta da lawyer da dangin Felix suka kawo alƙali ya yanke hukunci, wannan yanke hukunci ne ya sake birkita ƙwaƙwalwar Mah-mah take a wajen ta shiga wani yanayi irin na masu taɓin hankali sosai, a gaggauce aka maida ta asibiti kamar yanda alƙali ya bada umarni, hakan bai wa dangin Felix daɗi ba, dan ba haka suka so ba, sai dai babu yanda zasuyi. Sashin masu taɓin ƙwaƙwalwa aka kaita, ana kula da ita yanda ya kamata bisa tsayawar Daddy. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa game da halin da ya ga Mah-mah ta shiga ciki, sai dai rashin sanin yanda abin ya faru yasa shi bai yi tunanin da yanzu fa akaina abin zai faru ba, tunda Felix ni yaso ketama mutunci ba, ya ɗauka kawai wajen son ceton Mah-mah ɗin nawa ne kamar yanda ta faɗa na samu wannan mahaukacin dukan, wai dan ma na samu sauƙi sosai a lokacin. Kwanan Daddy uku da zuwa Germany Mah-mah ɗina ta mutu, ta bar duniya tana kuka da sunana bakinta....”

         Kuka ne yaci ƙarfin Lulu, ta sake ƙanƙame Smart da tun ɗazun idanunsa sun kaɗa sunyi jazur alamar yana kukan zuci ne. Sake ƙanƙameta yay shima jikinsa na wata irin tsuma, ji yake kamar zuciyarsa zata fashe, kukanta na sukar masa zuciya da ruhi. Tayi kuka sosai kafin ta cigaba da faɗin, “Wannan al'amari shine sanadin barowata Germany, na fahimci Daddy kamar yana tsoron maidani Nigeria ne a wannan halin saboda su Uncle You, ya maidani U.S, in da aka sake sama min sabuwar Nanny sai dai baƙar fata ce, asibiti aka sake kwantar da ni a can farko dan nima dai ina abu tamkar brain ɗin nawa ya taɓu. Na samu tsahon lokaci ina ganin likita kafin na ɗan rage firgita har Daddy ya saka ni a makaranta. Wannan shine ƙalubale na biyu, sannan sanadin abubuwa da yawa na rayuwata. Na ƙudiri niyyar yin karatu tuƙuru na zama lawyer domin kai ƙarshen irin masu halayyar Felix. Sannan kuma na kasa sakin jiki da kowa a yanzu ciki harda sabuwar Nanny ta. Banda aiki sai kuka, zaman ɗaki, a class bana shiga sabgar kowa. In har babu malami ma ina daga can gefe a takure. Duk yanda Daddy daya kasa tafiya ya barni ke lallaɓani da jana a jiki na kasa sakewa, depression yay min tasiri matuƙa. Wannan yanayin nawa ne ya jawo hankalin Alice da Luna gareni, tun bana kulasu har na ɗan fara amsa musu magana, ba komai ya jawo hakan ba sai ganin suna maida hankali a karatunsu, sannan suna nuna min suma suna cikin damuwa amma suna magance damuwarsu da wasu abubuwa shiyyasa ba'a ganewa........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments