Babu So Hausa Novel Complete

 [11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*


      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_02_*.........Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu. 

      Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.

     Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.


     Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba'ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi, dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.

     Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da  matarsa mai suna Asiya haihuwarsu ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba sai fatan shiriya yake musu. 

      Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar saudia sunje aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa ragamar rayuwar ƙannensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da Mimi. A wannan gaɓar ƴan uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daɗi har cikin ransa.

       Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai ɗan Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ƴan uwansa rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ƙanwarsa Mimi dake fama da ƙaramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ƴan uwan nasa dan kuwa su ko auran Mimi duk da ya basu hakkinsu ƙin zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta'aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane su manta kawai.

        Ɗan shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk iyalansu, dan kuwa a baya basu taɓa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin ƴaƴansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila ɗiyar ƙanwar gwaggo nada yara huɗu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna kiransa da *_Shareff_*. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ƙaramin ciki da take kan laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta mugun tsanarsa saboda huɗubar Gwaggo, ƙinsa take tamkar itace ƴan uban nasa ba mijinta ba. a gefe tana matuƙar jin kishin yana rayuwa a ƙasar waje a ganinta kodai yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matuƙar takaicin ganin su Muhammad sun fara sakkowa akan ƙin ɗan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke ɗaurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai son jama'a da haƙuri, duk da ƙiyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin kishiya ta zama mai haƙuri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daɗin iyayen mijin nata takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai ɗiyar ƴar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haɗata fitinar da aka dingayi da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk maza. sai dai tana da ciki ɗan watanni biyar. Umar dai yaƙi aure, hasalima ya zama fanɗararre a cikinsu sai addu'a. Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba'a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.

     Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba'a faɗaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.

     Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.

      Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri'arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al'amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya ɗauka yaƙi. 

     Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.

         A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa....


        Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.

       A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su'ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma. 

       Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace. Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama. Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi. Yarinya taci sunan *_Juwairiyya_*, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da *_Anam (Blessings of GOD)._*


         Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana maƙale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami'a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na'a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.

       A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.

     Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai.....

      A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.

     Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko'a mafarki bata fatar haɗa zuri'arta dasu Abie a duniya.....


       Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa'aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna'a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da *_MM Shareff_* a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya Shareff bai yarda ya ɗauka ma'aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma'aikatansa damar yin wasan kuma.

     Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo. 

        To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba.........✍


_Ko yaya wasan zai kasance🤔? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO...! MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taɓa zuwa muku da kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taɓo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki a yanzu da rawar da tarbiyyar ƴaƴanmu ke takawa a social media batare da saninmu ba ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da zafinsu suke😉🥰🥰😘🚶🏻._KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.


DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL


IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)

BIYU (400)

UKU  (500)

HUDU (700)


KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


HAFSAT UMAR KABIR

ZENITH BANK

2270637070


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


07040727902


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09134848107KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. 


SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_Ɗan ɗano😋😋_**_MALAYSIA (SABAH)_*..........A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani fara waige-waige a falon. Tabbas ba'a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine. 

            Takun sakkowa da stairs ɗin da'aka kawata adon falon da shi ya sani maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_* a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.

         “Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fashi zuwa Nigeria ki zauna agareki, k idan ma kika ƙuleni ALLAH kin koma can da zama kenan keda ƙasar nan sai yawo”

      Sautin kukan da aka sake fashewa da shi ya sani waigawa da sauri, ƙyaƙyƙyawar budurwa black beauty mai ɗaukar hankali da sam bata kama da matar a yanayin jiki sai na kamannin jini kaɗan. A ƙiyasi na yanayin jiki kai tsaye zance bata wuce shekaru sha bakwai ba. Sai dai a mizanin hankali da sanin masu irin yanayin jikinsu wajen ɓoye shekaru zan iya karyata zuciyata. Amma kai tsaye ban san shekara nawa zan bata ba. Dan sam bata da wani tsaho, tana nan dai ƴar cif-cif ga karamin jiki ga rashin tsayi kamar wata ƴar kanwata can (😂🤣ban dai faɗi suna ba ato😜). Tabbas kyaƙyawa ce, dan duk da kukan da idanunta suka nuna alamun taci hakan bai hana bayyanarsu dara-dara ba duk da suna a cikin farin siririn gilashi. Ga gashin gira da dogon hancinta (kamar na bilyn Abdull🙄 saura wani yace ba haka ba, bansan jealous😒😜). Kai atakaice dai yarinyar masha ALLAH. Sosai hawaye ke cigaba da bin kumatun ta tamkar an bude fanfo. Matar daketa masifar ta sake zuba mata harara a kausashe tace, 

          “Haɗiye min kukan nan kafin nazo na sassafa ki a wajen sakarar banza”.

     Da ƙyar ta shiga ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Sai dai hawayen sunƙi riƙuwa. Cikin rawar murya ta dubi kamilar matar da take kamani da ita a ɗan fisge, “Mamie na tuba ALLAH na daina duk abinda baƙwaso ke da Abie ”.

      “Dainawar taki ko cigaba bazai miki amfanin komaiba ai, dan zuwa Nigeria dai babu fashi tunda kin san abu mai muhimmanci ne zai kaiki. Dolene kije kiyi saves ɗinki a ƙasar haihuwarki kodan gaba zai miki amfani, dan nan ɗin da kika ɗauka ƙasar uwa da uba ta aro ce lokaci kaɗan ya rage mu barta muma ta ishemu”.

       Kuka ta sake fashewa da shi tana daddaga ƙafa. “Ni wlhy bana son Nigeria, zafi, sauro ga shegen hayaniya. Ni basai nayi saves ɗin ba dan bazan taɓa rayuwar Nigeria ba balle har na damu dayin aiki saves yaymin amfani. Please Mamie....”

      Cikin katseta Mamie taja wani tsaki. Kota kanta batabi ba ta nufi wata ƙofa a fusace tana faɗin, “Ki wuce driver ya kaiki wajen gyaran jiki dan Abie ɗinki yace da wuri zaku wuce, kin san kuma baya son wasa da lokaci”.

     Kuka ta sake barkewa da shi kai kace Abie ko Mamie ɗinne aka aiko mata sun mutu. Harga ALLAH bata son zuwa Nigeria dan tana matuƙar wahala da yanayin zafinsu. Ga shegen sauro ɗinnan na kano tamakar kasuwancinsa sukeyi. Uwa uba zaman gidan Uncles ɗinta data tsana saboda mugun halin matar Daddy, na matar ma bai cika damunta ba dan sai ka shiga sabgarta take takuraka. Tafi tsanar babban ɗansa mai shegen baƙin hali da mugunta da har ya zarta uwar tasa. Sam bata ko ƙaunar ganinsa dan basa haɗa ko hanya bare shan inuwa guda, shiyyasa a mafi yawan lokaci idan taji zai zo malaysia take guduwa wajen Aunti Mimi. Da ance kuma zai je wajen aunty Mimi ɗin itama dake aure anan ƙasar malaysia ɗin sai ta gudo ta dawo sabah. Har ya gama zamansa bata yarda su haɗu. Kai itafa a kaf rayuwarta ma bai fi sau uku ta taba ganinsa ba. Tun kuma a ganin farko taji ta tsanesa saboda tsawa da yay mata dan ta fasa glass cup a mistake a gidansu, ita kuma ta murguɗa masa baki yako kama lips ɗin ya murje har sai da sukai kumburi duk da shekarunta basu wuci goma ba a lokacin ta kasa mantawa ta kuma kasa daina jin haushinsa. Hakama haɗuwarsu ta biyu sai da yay mata mugunta, kai idan bata mantaba ma dukansu yay ita da Aysha ƙanwarsa saboda sunje wajen bikin birthday na ƙawar Ayshan ba'a sani ba. Aiko dukan nan ya shigeta dan harda zazzaɓi kasancewar tunda ta tashi da wayonta da hankalinta ba'a taɓa dukanta ba sai shi mugu.........

          Ta jima a wajen tana saƙa mai fishsheta kafin ta haura saman stairs. Cikin mintunan da basufi sha biyar ba ta fito sanye cikin wando da riga ta ɗaura jibgegiyar rigar sanyi data kai mata har gwiwa kasancewar lokacinsa ne, duk da veil data naɗo a kanta kamar yanda larabawa keyi hakan bai hanata jan hular rigar da bakinta keda gashi mai laushi har saman kanta ba. side bag dake hanunta ta saƙala cikin wuyanta sai faman tura baki take. Duk da Mamie na zaune a falon tana yanka tufa ko kallonta batai ba....

      “Mamie na shirya kuɗin to”.

Batare da Mamien ta tanka mata ba ta tura mata card ɗinta na ciran kuɗi. “Na gode ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”. Ta faɗa tana kama hanun Mamie ta sumbata tare da ɗagowa ta sumbaci kumatunta kamar yanda dai larabawa sukanyi. Mamie bata kulata ba, hakan yasa taƙi tafiya idanunta har sun cika da kwalla, dan tunda taga Mamien bata maida mata murtanin sunbar datai mata ba tasan har yanzun tana fushi da ita.

       Haka kawai murmushi ya suɓucema Mamie, ta girgiza kanta da kamo hanun tilon ƴar tata da a kullum cikin jimamin ranar da aure zai rabasu take, dan ta tabbatar hakan na gab da faruwa. A ido zaka ɗauka Anam bata da wani shekaru saboda ƙaramin jiki da ALLAH ya bata. Sai dai kuma a zahiri shekarunta ashirin da uku kenan a duniya. Itama sumbatarta tai da ɗanjan kumatunta, hakan yasa Anam yin ƴar dariyar jin daɗi ta rungume Mamien. Mamie tai murmushi. 

        “To sarkin taɓara tashi kije ko ƙya dawo da wuri”.

     “Okay Mamie bye”.      Batafi awa uku da fita ba sai gata ta dawo, ta kara wani irin ƙyau da kwarjini tabbacin taci gyara tako ina. Dan babu abinda fuskarta keyi sai shining da glowing, ga wani uban ƙamshi mai saka nutsuwar mai shaƙa. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufi ƙyaƙyƙyawan dattijon dake tsananin kama da ita dan shima black beauty ɗinne, amma kasancewar akwai jin daɗin rayuwa baka ganin komai tare da shi sai ƙwarjini da ƙyawun haiba. Ga baƙin sajen fuskarsa daya ƙara ƙawata ƙyawun nasa. Shima dai bashi da wani jiki, dan komai na Anam bashi da maraba da nashi, hakan na nufin dai kamaninta ɗaya da mahaifinta.

      Zuwa tai ta rungumesa ta gefe tana dariyar farin cikin ganinsa. Shima fuskar tasa da murmushi ya riƙo hanunta cikin nasa. “Uhhm Mamana irin wannan ƙamshi haka kamar amarya”. Fuskarta ta ɓoye a kafaɗarsa tana dariya. “Nidai Abie ba wani amarya”. Dariya kawai yayi baice komai ba. A haka Mamie ta fito daga kitchen ta samesu. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon mijin nata abin sonta da ƴar tasu tilo ɗaya a duniya. Anam ta zame veil ɗin kanta tana nunama iyayen nata kanta daya sha gyara masha ALLAH, sai sheƙi yake da ƙamshi gashi da tsaho sosai. Gaba ɗaya kamaninta irin na Abie, gashin kai da gira zuwa gashi ido ne kawai irin na Mamie, sai ko maganarsu dake kama itama.

    Sosai suka shiga yaba ƙyawun da gyaran nata yayi, cikin tsokana Abie ke faɗin, “Mamana kin zama kamar wata amarya da gaske, kodai kawai idan munje na aurar dake ma?”.

    Idanu tai mugun zarowa, sai kuma ta kwaɓe fuska har hawaye na cikon mata ido. Lips ɗinta sai rawa suke tama rasa mizatace. Dariya Mamie da Abie suka shiga yimata, hakan yasata tashi da gudu ta haura sama. “Kin gani kin kunnata”. 

     “Na kunnata ko ka kunna abarka”.

Cewar Mamie tana murmushi. “To aini abin na damuna, idan na tuna wataran aure zatai ta barmu hankalina na matuƙar tashi, gashi shekaru sunyi nisa, kamata yay ma data gama saves ɗin nan kawai a wuce wajen Humairah”.

     Ajiyar zuciya mai nauyi Mamie ta sauke. Murya a raunane tace, “Hakane ya dace, sai dai kuma a kullum cikin korar samarin take ai taƙi bama kowa dama anan ɗin balle Nigeria. A kullum kallon kanta take a yarinya”.

     “To ai yarinyarce, duka yaushe kika haifamin ita. Ni badan auren ya zama doleba dana bar abuta naita kallo kawai”.

      Sosai Mamie ke dariya, cikin riƙe baki tace, “Lallai ashe mu iyayenmu basa sammu kenan da aka ɗakko aka baku. Lallai ashe lokacin auren munada kallo kenan dan za'a sha show rabuwar ƴa da uba”.

     “A zakusha kam. Dan mijin nan zai sha gargaɗi, shiyyasa nafi son ma ta auri ɗan Nigeria dan ƙasar nan ta isheni haka”.

        “To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Ya kawo nagari”. 

  Da amin Abie ya amsa cikin jimami da damuwar rabuwa da tilon ƴarsa.


*_Washe gari_* kamar yanda Mamie ta faɗa hakance ta kasance. Dan kuwa dai Abie da Anam sun wuce ƙasar haihuwarsu Nigeria. Tasha kukan rabuwa da Mamie duk da tasan bazatai shekaran Mamie bataje ba tunda ita sunce bazata zo ba har saita kammala. A jirgi barci ta dinga ramuwa wanda ta gagara yi a daren jiya saboda alhinin yin nisa da iyayenta datai matuƙar shaƙuwa da su take mu'amula da su tamkar ƙawayenta. Sune abokan shawararta, sune abokan kukanta, sune abokan dariyarta, sune abokan rayuwarta. Bata da kamarsu dan su tafi sani fiye da kowa a duniya...........✍

*_Hummm tofa masu karatu, ni kaina wannan littafi banma san mizance ba. Kawai kumuje zuwa muji yaya za'a ƙare da Anam ƴar Malaysia mai gudun Nigeria. (Kai nimafa da za'a kaini Malaysia ɗin nan ba dawowa 9ja ɗin nan zanso yiba. Idan baku yarda ba ku haɗan kuɗin jirgi kuga aiki😎😂👩🏼‍🦯)._**_Ku kasance da Zafafa biyar dan da gaske wannan karon tafiyar tasu ta musamman ce insha ALLAH. Kowanne littafi yazo muku da salonsa na dabban daya dace da buƙatar ku. Sai da ku Zafafa biyar ke amsa sunan Zafafa biyar, dan haka kuɗin na musamman ne a garemu masoya. Idan muka ce na musamman da gaske muna nufin na musamman😘😘😘😄🙏🏻_*
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.


DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL


IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)

BIYU (400)

UKU  (500)

HUDU (700)


KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


HAFSAT UMAR KABIR

ZENITH BANK

2270637070


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


07040727902


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09134848107KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. 


SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_03_*..........Tuni sun tattare kansu a sashen aunty amarya idan ka cire ƴan manya-manyan yaran gidan samari da basu gama dawowa da ga wajen aiki ba da kuma masu shiga school lectures ɗin yamma. Zagaye suke da Anam suna kwasar dariyar hausarta da bata nuna da ƙyau ba. Dan cike take gwamutse da yaren malay da turanci, wai a hakanma Abie na matuƙar ƙoƙarin mata hausar ne shi da aunty Mimi dan Mamie ma ba wani iyawa tai sosai ba harma gara Anam ɗin, tunda dama acan itama ta tashi, ko Nigeria tazo tafi yin turanci da jama'ar gidan. Aysha dake naniƙe da Anam ɗin da suke sa'annin juna dan dama idan tazo bata da ƙawar data wuceta a Nigeria, cike da kulawa take tambayarta dalilin matsar ciki da take famanyi.

       A yatsine Anam ta sanar mata tana jin yunwa ne, dan ta kasa cin duk abincin da aka shirya musu a gidan. Dama can idan sunzo Mamie ce ke musu girki shiyyasa Anam bata da matsala tunda abinda ta saba ci ne, a yanzu ko babu Mamie dole sai abincin Nigeria da har yanzu ta kasa iya ci, ƴan abubuwan da take iya cin ƙalilanne kuma babu su.

      Idanu Aysha ta ɗan waro, cikin harshen turanci take cemata miyasa zata zauna da yunwa bayan abinci da akai domin su tunda sun iske tarin kwanika a sashen Daddy lokacin da sukaje gaida Abie. Sunada tabbacin kuma an shiryasune dan zuwan su Anam ɗin. Fuska a marairaice ta sanarma Ayshan ita bata iyacin duk abincin ba ai. Ba Aysha kaɗaiba duk yaran sai da suka dara, dan sosai ragwantakar Anam ke basu dariya, kodan tana ganinta da ƙaramin jiki ƴar ficika da ita yasa a kullum bata sanin ta girma? Sosai Aysha ta fita girman jiki, sai ma ta saɓeta ta goya dan ita ta kwaso tsayi da garin jikin Mommy mahaifiyarsu.

    Sake ɓata fuska Anam tai kamarzatai kuka, sai faman matse ciki take da cizar lips dan da gaske yunwar takeji, shi kansa Abie yana canne amma hankalinsa na kanta dan yasan bazata iyacin kowanne abinciba da ya gani an tara masa.

      “Am so sorry sweetheart. Kar kiyi kuka faɗi abinda kike so sai a samo miki, ko a kira Yaya ya sayo miki tunda shi yasan inda yake samo abincin naku, dan shima dai ya jima yana wahala kafin ya saba da abincin Nigeria, ko yanzu ma ba komai yake iya ci ba”.

      Fahintar wa Aysha ke nufin za'ama magana ya samo mata abinci ya sakata girgiza kanta, a langwaɓe ta kamo hanun Ayshan cikin nata. “No don't worry rakani wajen Abie na nidai kawai”.

    Batama bari Aysha tace wani abuba ta miƙe har lokacin hanunsu cikin na juna, ɗayan hanunta kuma nakan cikinta. Wando da rigane a jikinta marasa nauyi, wandon irin mai faɗin nan sosai da ƴan Nigeria ke kira a fantama😂, sai fingilar top da tabi jikinta ɗas kamar dan ita aka halicceta, sai siririn veil data sakaya gashinta a ciki sai dai hakan bai hanashi bayyana ta gaba ba saboda veil ɗin daya zama baya.


       Itace ta farayin sallama a hankali cikin sassanyar muryarta, ta dora da faɗin, “Daddy mu shigo?”.

     Murmushi Daddy da Abbah keyi idonsu akan ƙofar. Abba ne ya amsa da “Shigo mana Mamanmu”. Hanun Aysha taja zuwa ciki, sai dai taku uku kacal tai ta tsaya turus fararen idanunta da sukai laushi saboda yunwa tsaye ƙyam akan wanda ke zaune bisa lallausan carpet ɗin falon gab da ƙafafun Abie ɗinta, yayinda hankalin Abie kacokan ke akansa da alama ma bai san da shigowarta ba.

     Sosai ƙirjinta ya harba dan ko kusa batai zaton ganinsa anan ɗin ba, tunma data duro gidan addu'arta shine karma su haɗu kwata-kwata. Zancen Aysha na ɗazun ya tabbatar mata yana ƙasar, hakan kuma na nufin dole su haɗu koda ba yau ba. Amma batai tsammanin yanzu ba. Kamar yanda tai masa kallo ɗaya ta ɓata fuska da gyara yanayinta haka shima yay mata kallo guda duk murmushin fuskarsa ya ɓace, har wani yamutse fuska yay tamkar yaci karo da tutun safiya na cikin sanyi......

      “Mamanmu ƙaraso mana”.

Daddy ya katsesu a tare dan duk yaga irin kallon tsanar da sukaima juna. Shikam ya rasa wannan ƙiyayya ta Anam da Shareff bayan kowa yasan irin dunbin son daya nuna mata tana jinjira har zuwa sanda ya wuce Indonesia, amma a yanzu baka ganin komai sai ƙin juna a tsakaninsu tamkar basu taɓa sanin juna ba. Yitai kamar bata gansa ba taje ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, cikin marairaice fuska tace, “Daddy ina jin yunwa sosai”.

       “Ya salam mamana garin yaya haka? duk abincin dake gidan nan ga wasuma ko taɓawa ba'ai ba kuma dan k kawai aka shirya su”.

      Kanta ta girgiza kamar zatai kuka. “Daddy bana son su ban iya ci ba ai”.

          “Sai ki fara koya yanzu ai”.

Abie ya faɗa kafinma su Abba suce wani abu yana hararar Anam duk da kuwa bai kai zuci ba, dan ransa cike yake da damuwar zamanta da yunwar tunda yasan da gasken ba iya cin tai ba.

     Daddy yace, “A'a ba'ayi hakaba ai. Tunda tace bata iyaba da gaske bata iya ɗinba kuma bataso. A bita a sannu zata koya ci insha ALLAH tunda tana nan. Shareff ka ɗauketa kuje a sama mata abinci dan kaine kafi kowa sanin inda kake ciyo abinda ta iya ci”.

       Tamkar saukar aradu haka Shareff yaji saukar zancen Daddy a kansa. Ya ɗago da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane. Harara Daddy ya zuba masa. “Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.

       Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba. Sai dai fuskar ta sake rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa. 

          “Daddy ni dai nama ƙoshi kawai zansha ko tea to”. Anam da itama ta haɗe fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa ta faɗa baki a tunzure”.

      Maimakon Daddy ya amsa mata sai ya kira sunansa a tsawace. “Shareff Are you daft?”. Kansa ya girgiza kawai yana miƙewa, idonsa a ƙasa yace, “Zanje na sayo kawai.....”

      “Da ita zakaje ta zaɓa abinda take so”.

     Dady yay saurin faɗa cikin katse masa hanzari. Wani irin rumtse ido yay da ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa uwa zai huda shi. Sai dai baice komai ba ya kama hanyar fita. “Basai kaje ɗakko key ɗin mota ba zo ka dauka wannan”. Abbah ya katsesa dan ya tabbatar Mommy ta gansa zata hana itama. Nanma baice komai ba ya dawo ya amshi key ɗin hanun Abban.

       “Maza bishi mamana kuje, ki kuma zaɓo duk abinda kike so kinji”.

    Kanta ta ɗagama Daddy tana murmushi, dan ganin yanda Shareff ɗin keyi yasata jin zama ta bisa kodan ta baƙanta ransa...

        Kasancewar ya fita zafin nama sanda ta iso harabar gidan harya tada motar yana reverse, maimakon ya faka saitin inda take ya ɗauketa sai ya harba motar har bakin gate. Anam tai ƙwafa da taɓe baki, cikin kunƙuni da gurɓatacciyar hausarta tace, “Duk baƙin halin da kake sai naje saika mace idan kasha zuciyanka mugu mai baƙin rai”.

       Oho baima san tanai ba. Cike da wani takun isa tazo ta buɗe murfin ta shiga kanta a gefe. Bawani duban kirki yay mataba a ciki, dan haka bai gama tantance kayan jikinta ba. Tana shiga ya fisga motar da ƙarfi har yanayi kamar zai taka mai-gadi ma, sai da yay tsalle gefe ya bashi hanya cike da mamakin mike damunsa. Dan shi shaidane Shareff mutum ne daya san mutuncin mutane, ko yaya kake a ƙasansa bai yarda ya ƙasƙantaka ba balle wulaƙantaka. Yayi imani da ALLAH ransa a ɓace yake bada son rai yay masa haka ba.

            

      ★ Sosai gidan abincin ya haɗu, ya samu waje yay parking batare da yace da ita komai ba ya fice a motar. Baki taɗan taɓe kaɗan da yima ƙeyyarsa gwalo, sai kuma ta zabura ta buɗe motar tamkar wadda ta tuna wani abu. Yana gab da shiga ta cimmasa saboda da ɗan gudu-gudu take tafiya. Cak ya tsaya, dan haka itama ta tsaya kanta a ƙasa dan duk fitsararta a bayan idone kawai dama.

       “Idan kika bari ƙafarki ta shiga wajen nan sai na ɓallata”. Da yaren malay yay maganar, dan haka komai ya shiga kunnenta tsaf. Baki ta tura fuska a kumbure idonta na tara ƙwalla harya shige tana kallon bayansa ta ƙasan ido. Maimakon ta koma mota sai ta nema waje a gefe tai tsaye tana kallon mutanen dake. a ciki ta cikin glass da aka ƙawata wajen.....

       “Hallo....”

  Aka faɗa a bayanta cikin wani irin sallon daya tilastata ɗago idanunta masu haske, matashin saurayine ƙyaƙyƙyawa fari tas. Sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar karɓarsa ga wani ƙamshi na musamman a tare da shi. A hankali ta janye idanun nata ganin yanda ya tsareta da idanunsa birkitattu. Gefen data maida fuskar ya sake dawowa yana gyaran murya, ta sake ɗauke kanta gefe....

      “Dan ALLAH ki kulani ƙyaƙyƙyawa ”. Ya faɗa cikin marairaicewa da haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Baki taɗan taɓe gefe tana yamutsa fuska da kai hannu ta gyara glass ɗin idonta dake ƙara fiddo ƙyawunta duk da tana sakawane badan gayu ba, kamar bazatace komaiba sai kuma dai ta tanka masa saboda ALLAH daya haɗata da shi. “Ka fara koyan sallama tukunna kamar zaifi bature”. Kansa ya dafe, cike da jimami yace, “Am sorry Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Nan ɗin ma bata amsaba sai da tasha masa ƙamshi tana wani ɗauke kai. “Wa'alaikassalam. kuma ni ba sunana ƙyaƙyƙyawa ba”. “Tabbas sunan shine ya dace dake, sai dai dazanji na yankan zanfi yin farin ciki”. Banza ta masa har kusan minti ɗaya, ganin yana neman matsowa jikinta tai saurin ɗagowa a masife...... 

       A dai-dai nan Shareff ya fito daga wajen hanunsa ɗaukeda ledoji masu tambarin wajen abincin. Duk da idonsa a kansu ya fara sauka sanda yake buɗe ƙofar sai ya ɗauke tamkar bai gansunba. Sai dai ya sake tsuke fuska. Yazo zai giftasu a fisge yace, “Second ɗaya kika ƙara a wajen nan jikinki sai ya faɗa miki”. Daga ita har saurayin da sauri suka maida dubansu garesa dan ita bama ta lura da shi ba da farko. Ko kaɗan bazaka taɓa cewa shine yay maganar ba. Tuno dukan da sukaci ita da Aysha randa sukaje birthday party ya sata zabura da sauri tabi bayansa bakinta a tunzure tana hararar bayansa, da sauri shima saurayin ya take mata baya. Tana ƙoƙarin rufe murfin motar ya riƙe da hanzari..........✍

       KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.


DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL


IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)

BIYU (400)

UKU  (500)

HUDU (700)


KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


HAFSAT UMAR KABIR

ZENITH BANK

2270637070


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


07040727902


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09134848107KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. 


SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_04_*..........Kallon juna sukai cikin ido, tai saurin janye nata saboda wani irin harbawa da ƙirjinta yayi......

     “Please Beauty ko details ɗinki ki bani mana”. Saurayin ya faɗa a marairaice. Ai kafimma ta bashi amsa mai gayya mai aiki ya fisgi motar da ƙarfi. Da sauri saurayin ya saki murfin yana mai yin tsalle gefe dan saura kaɗan ya takashi. Sosai yanzu kam Anam ta firgita, dan har hannunsa ta riƙo batare data sani ba. Tureta yay a jikinsa tare da mika hannu ya rufo ƙofar gefen da take ɗin. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana kiran sunan Mamie da Abie. Bai nuna yama san tanaiba, saima hankalinsa daya maida ga motar dake bin bayansu, sai da suka hau titi sosai hasken solar ya bashi damar ganin fuskar guy ɗin da suka baro ne. Lip ɗinsa ya ciza da ƙarfi yana wani fici-fici da idanunsa, sai ya koma tafiya a slow-slow harya zam saurayin ya ɗan gota su. Gefen titi ya gangara, sai da yaga saurayin na ƙoƙarin dai-daita nasa gudun danya sauka gefe titi shima saboda ganin sun tsaya sai kawai yay warming motar da wani irin karsashi ya sake harbata saman titi tamkar shikaɗaine a kansa. Tabbas da ace akwai ƙasa babu abinda zai hanashi bulama saurayin ita.

       Wani irin duka saurayin ya kaima steering ɗin a ƙulle da kufcewar damar daya samu. Ya kife kansa yana furzar da huci mai zafin gaske, dan harga ALLAH yarinyar ta matuƙar tafiya da dukkan imaninsa.


        Kamar yanda ya fita a fusace haka ya dawo a fusace, ko parking bai gama daidaitawaba da ƙyau ta ɓalle murfin motar ta fice da sauri. Wani irin mugun kallo yabi bayanta da shi, sai kuma ya janye yanayin ƙwafa ya kashe motar ya fito. Zaune ya sameta kusa da Abbah tana zuba surutu, dan har yanzu suna a falon suna hira. Sosai takaici ya riƙe masa maƙoshi, ya harareta yana ɗauke kai da zube ledojin hanunsa gabanta. Fuskarta ɗauke da murmushi kamar ba itace ta gama kuka a hanyaba yanzu tace, “Jazakallahu khairan Yaya Shareff”. Ta ƙare maganar da masa gwalo yanda su Abba basu luraba sai shi. 

         Yi yay tamkar baima gantaba duk da tsaurin idonta na bashi mamaki, sosai ƙanensa ke shakkarsa a gidan, amma sam babu irin wannan tsoron da yake gani a idon ƙanensa tattare da ita. Kai tsaye take abunta garesa, abunda ya fuskanta dukane kawai bata so, dan tun dukan da ya taɓa mata ita da Aysha ta shiga hankalinta a lokacin har tana wasan ɓuya da shi. Sallama yayma su Abie dake saka masa albarka ya fita fuskarsa ɗauke da murmushin daya saka Anam sakin baki tana kallonsa da mamaki. Dan inba Abie ɗin ba da wahala kaga murmushi a fuskarsa, kullum fuska a ɗaure kamar ɗan raka gawa....


         Washe gari da ƙyar Aysha ta iya tashinta danta shirya. Haka tai wanka tanata mitar ita barci bai ishetaba. Shiri tai cikin wando da riga, sai dai anan babu maganar fita a haka duk da  zafi da ranar da akeyi a Nigeria, dole ta ɗaura abaya, Sosai tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. ɓata fuska taketa faman yi dan bada son ranta tasa abayar ba, sai dai yanda Mamie ta gargaɗeta ta dingayi tunda tasan kayan nata duk ba irin na sawar Nigeria ba ne. Shiyyasa ta zubo mata abayoyi kusan goma tanata mita bata kulata ba. Kasancewar akwai sanyin safiya sai bata damu da saka abayar ba sosai.

       Sashen Mommy suka nufa ita da Aysha, sai dai daka kalleta kasan ba'a san ranta bane. To amma kodan Aysha da kunya tace bazataje ba. Mai aiki kawai suka samu a falon tanata aikin gyarawa, suka gaisa Anam na amsasu cike da fara'a, dan haka kawai ita dai Ladi ke birgeta. Bedroom ɗin Mommy suka nufa daga nan, bayan sallama aka basu iznin shiga. Zaune suka sameta a kujerar mirror tana murza ɗauri, ganin aysha ta rissina tana gaisheta itama saita ɗan rissina batare data yarda sun haɗa ido ba. Bata amsa na Anam ɗin ba, sai Aysha data watsama harara... “A ina kika kwana?”.

      “A sashen Mom ne”.

Aysha ta bata amsa cikin ɗari-ɗari dan tasan faɗa zata sha. Aiko kamar jira Mom ta rufeta da faɗa, ta inda take shiga batanan take fitaba. Itadai Aysha haƙuri kawai take bata. A tsawace tace. “Ɓacemin da gani shashasha da bata san ciwon kanta ba”.. Kafinma aysha tai yunƙurin fitowa tuni Anam tai waje ranta fal ƙarin mamakin masifar Mommy ɗin...

      Da sauri tai baya jin suna neman yin karo da mutum. Ta tura baki gaba tare da ɗan matsawa gefe saboda hararar da yake watsa mata. Yana ƙoƙarin raɓata da nufin wucewarsa tai tunanin bugeta zaiyi, kamar ƙiftawar ido yaga ta zura da gudu ta fice. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da girgiza kansa kawai. Anan ɗin ma yana ƙoƙarin shiga ɗakin Mommy Aysha ta fito tana sharar hawaye, rissinawa tai ta gaishesa, maimakon amsa mata sai ya jeho mata tambaya idonsa kafe a kanta, “Mike damunki?”.

     Kanta ta girgiza masa. “Ba komai Yaya Mom ce, dan naje sashen Mom na kwana shine taketa faman faɗa, ni kuma saboda naga Anam ne tunda nasan idan mukazo nan bazata barta ta kwana ba”. Shiru yay yana cigaba da kallonta kawai, batare da yace komaiba kuma sai ya raɓata ya wuce ɗakin Mommy ɗin.

         Anam kam sai da ta tabbatar tabar sashen sannan ta ƙara kumbura baki, sashen Gwaggo ma da tun jiya batako kallaba sai da Abie ya korata sannan ta tafi fuska a haɗe kamar zatai kuka. Bata son kakar tasu dan itama tasan ba sonta take ba. Koda ta shigo sashen tsohuwar a ciccije take. Tamkar bama tasan Anam ɗin ba take kallonta, hakan yasa itama Anam ɗin tsumewa tai kamar bama wajenta tazo ba. Cikin ƙunar rai Gwaggo ta ture ƙaton kofin shayin da take sha gefe tana kallon Anam cike da tsana,

        “Fitsararriya cokalin banza. K ko kunyar kanki bakijiba sai yau kike zuwa gaisheni? Da yake baki da mutunci. to in bakizoba k ai ubanki shi yazo dan uwarki”. 

   Shiru tai taƙi cewa komai, hakan sai ya sake tunzura Gwaggo ta fara bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ko motsi Anam bataiba ballema tai mata gaisuwar da akace tazo tayi, sai da ta tabbatar mintunan da Abie bazai zargi komai ba sun cika sannan ta gaida Gwaggo dake yayyafa ruwan bala'i da zage mata iyaye tai ficewarta batare da ta jira amsa ba. Biyota Gwaggo tayi tana ƙwala mata kira. 

      “Zuwairah!! Zuwairah!! yanzu nan ni kikema wannan ɗibar albarkan? To ko ubanki ai bai isaba, ke ko kakarki ma data haifi uban naki balle ke yarin....”

      “Ki cinye kanki fitinanniyar tsohuwa”. Anam ta faɗa a hankali tana ƙara sauri dan ko muryarta bata buƙatar ji. Taji daɗin samun Abie harya shiga mota, dan haka ta buɗe wuf ta shige duk da bataji daɗin yin tafiyar da wanda ta gani zai jasu ba. Sai da suka fita a gidan gaba ɗaya Abie daya lura bata gaida Shareff ɗin ba ya dubeta ta mirror.....

      “Anam!”.

“Na'am Abie ”.

   “Kin gaida Yayanki kuwa?”.

Ido suka haɗa da shi ta mirror, ita ta fara ɗauke nata idon ganin kallon banzar daya jefa mata. “Abie na gaishesa tun ɗazun ma ai da muka haɗu a sashen Mommy”. Idanunsa da basu gama bajewar kumburin barci ba ya sake ɗagowa ya dubeta. Itako ta ɗauke kanta cike da basarwa. Abie kam daya yarda sai kawai yay murmushi da maida hankalinsa ga lap-top ɗin dake a cinyarsa yana dubawa, ta Shareff ɗince yake nuna masa ayyukan company duk da dama can komai za'ayi yana sanar masa. Sai dai a kullum cikin ƙara bashi wuƙa da nama yake da nuna masa duk yanda yayi dai-dai ne kawai. Koda suka iso inda zatai daidaita komai daya shafi hidimar ƙasar nata bata yarda tako kalla Ya Shareff ba, shima bai shiga sabgartaba dan koba komai yana jin nauyin Abie sannan shi sam baya wasa da yara dama can, itacema kawai za'ace ta ciri tuta a wajensa tana ƙarama.

     Komai da taimakonsa shi da Abie ya kammalu, basu sami nutsuwa ba sai kusan azhar. Maimakon gida sai suka wuce company. Tunda akai

Companyn Anam batazo Nigeria ba, dan haka ta ɗan nutsu a kallon tsarin wajen da yanda ma'aikata keta kaikawo na daidaita kansu tun shigowar motar tasa. Koda suka fitoma sai gaisuwa ake miƙa musu cike da girmamawa da mutuntawa har suka isa katafare kuma haɗaɗɗen office da yaji komai na more rayuwa da saka nutsuwa ga mazaunin cikinta.  Abayar jikinta ta shiga ƙoƙarin cirewa. “Wayyo Abie zafi”.

      Yanda tai maganar ya sashi ɗan juyowa ya dubeta, ai da sauri ya ɗauke kansa ganin kayan dake a jikinta. Wando ne dayay matuƙar fidda surar jikinta da ƴar riga da itama bata ɓoye komai ba. Sun mata ƙyau sosai kuma dai-dai da halittarta ta masu ƙaramin jiki. Har veil ɗin data naɗa bata bari ba sai da ta yaye, ɗaurarren gashinta da yasha gyara ya bayyana, sai dai tuna gargaɗin Mamie yasata warware veil ɗin duk da ba wani girmane da shiba sosai taɗan yafa tana duban sashen da yake....

       “Yaya Shareff Please kasa ac zafi”. Tayi maganar ne tamkar zata fasa kuka, dan da gaske zafine ya taso mata lokaci guda, har wani dimm kanta ke mata. Ta ƙasan ido ya harareta, sai dai baice komaiba ya ɗauka remote ɗin ac dake a desk ɗin office ɗin nasa ya kunna ɗin. Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin jin yanda sanyin ya wani buso mata da faɗin, “Alhmdllhi, Abie ALLAH da kamar ana dafamin fatar jikina fa”. 

     Ƴar dariya Abie yay yana mai girgiza kansa da kallon Shareff dake ƙoƙarin buɗe wajen da yake gudanar da duk ayyukansa na zane. Babu mai shiga wajen sai shi kaɗai, sai ko Fharhan da Khaleel da yakan bama dama a wasu lokutan su kuma Engineers ne, dan company ɗin nasu aikinsa kenan, mai buƙatar zane amasa, idan da gini duk a haɗa, kai dai kawai ka ajiye kuɗi ne kaga biyan buƙata.

      “Babana kaji fa wani shirme, dama zafi na dafa fata ne?”.

       Murmushi ya ɗanyi cikin sanyin muryarsa da shafa kansa yace, “Abie akwai zafinne ai”.

     “Oh ka goya bayanta kenan dai kawai”.

            Murmushi ya sake saki mai faɗi fiye dana ɗazun. Sai dai baice komaiba, saima ɗan hararan Anam data saki baki tana kallonsa ganin murmushi a fuskarsa yayi. Itako ko gezau kallonsa take kamar ta samu hoton bango. Fuska ya ɗan tsuke da ɗauke kansa daga saitinta. Itama sai ta janye tana taɓe baki.

       Tare da Abie suka shiga, yayinda gaba ɗaya hankalin Anam ke ga littafin data ɗauka mai tambarin company ɗin nasu da alama samples ɗin ayyukan sune a wajen. Koda taji shigewar tasu bata maida hankali kansu ba, ta jima tana kalle-kalle, wasu su birgeta wasu ta taɓe baki harta fara hamma. Sai kawai ta zame ta kwanta a kujerar.........✍KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.


DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL


IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)

BIYU (400)

UKU  (500)

HUDU (700)


KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


HAFSAT UMAR KABIR

ZENITH BANK

2270637070


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


07040727902


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09134848107KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. 


SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_Ƙarshen free page_**_05_*   ...........Sun jima a ciki yana nunama Abie abubuwa, yanda yaketa faman bayani da murmushi saika rantse bashi baneba. Dan har dariya sukeyi tare da Abie. Kiran sallar la'asar ne ya fiddosu, hakan yayi dai-dai da shigowar ɗaya daga cikin ma'aikata office ɗin, sannan kuma dai-dai da farkawar Anam data sha barci hankali kwance sanyin ac ya gama ratsata.

        Shigowar ma'aikacin mai suna Abeed tazo masa a bazata, dan hankalinsa gaba ɗaya nakan system ɗin gabansa, sai sallamarsa da buɗe ƙofa ne a lokaci guda suka shiga kunnensa. Da sauri ya ɗago idanunsa batare daya amsa sallamar Abeed ɗin ba ya kai dubansa gareta. Anam da bata san mike faruwaba duk da itama taji sallamar tai yunƙurin miƙewa tana laluben veil ɗinta da nufin ɗan lulluɓama jikinta. Abie ya riga ya shige toilet ɗin cikin office ɗin ɗaura alwala tunkan sallamar Abeed....

       “You are vary stupid!! Zaka shigo min kai tsaye”.

A yanda yayma Abeed tsawar da jefa mata rigar suit ɗinsa dake a jikin hanger ba shi Abeed ɗin ba hatta ita sai da ta zabura. Da sauri ta ɗane kujerar baki ɗaya ta ƙudindune kanta dan sam bata ƙaunar tsawa a rayuwarta. Cikin rufewar ido da manta Abie na'a office ɗin ya sake dakama Abeed tsawa da cigaba da masa masifa. Shi dai yay ƙasa da kansa dan bai san laifinsa ba anan har yanzu, tunda ya san ya yi sallama ya kuma yi knocking....

        “Get out!!”.

Ya sake faɗa a tsawace. Da sauri Abeed yay baya da rufe ƙofar. A fusace ya maida dubansa ga Anam da ke leƙosu ta cikin rigarsa. Ya watsa mata wata uwar harara, cikin gargaɗi mai kaushi,

      “Idan kika ƙara fitowa da wannan ƴan iskan kayan saina kashe fuskarki da marukan da bazata ganuba. Stupid girl! An faɗa miki nan muna buƙatar sune”.

    Baki ta tura gaba duk da ta mugun tsorata da yanayinsa. “To ni Yaya MM wannan duk sune kayana ai, kuma ni su na iya saw.......”

    Ganin ya yunƙuro zai tashi ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera fuska a kwaɓe. Ƙwafa yay da sake watsa mata harara. Abie dake tsaye da ga bakin ƙofa yana kallonsu tun ɗazun basu lura da shi ba yay murmushi, domin kuwa wasu abubuwa masu ban mamaki ya hango a cikin ƙwayar idon ɗan nasa, ya girgiza kai kawai da ƙarasowa ciki. Sai lokacin Shareff ya lura da shi. Ƙasa yay da kansa dan shi gaba ɗaya yama manta Abie na'a office ɗin. Miƙewa yay sum-sum ya nufi toilet batare da ya yarda sun haɗa ido da Abie ba. Shima baice masa komai ba sai binsa da yay da kallo kawai. Anam dake a laɓe sai da taga ya shige sannan ta fito, cikin taɓe fuska ta ƙaraso inda Abie yake tana faɗin, 

     “Uhhm Abie ALLAH Yaya Shareff baida kirki, yanama staff ɗinsa ihu bai masa komaiba kuma”.

    Nanma murmushi kawai Abie yay baice komai ba. Zata ƙara magana Ya Shareff ɗin ya fito tai saurin komawa bayan Abie ta ɓuya. Sai dai hakan bai hanata ganin hararar daya watso mata ba. 


★★★★★


         Washe gari su Abie suka wayi gari da shirin kai kuɗin auren Ya Shareff, wanda dama yana ɗaya daga cikin dalilinsa na zuwa Nigeria, dan data Anam ne kawai turota zaiyi tunda yasan akwai mai iya mata komai ai. Ita dai Anam bata san mike faruwaba ma, dan ta jima bata tashi a barcin safe ba kasancewar daren jiya tunda aka ɗauke wuta ta kasa komawa barci saboda zafi, duk da kuwa Mom ta kawo mata fan ta kunna mata saboda tsaki data dinga zubama su Husna kamar wata dangin tsaka, sai dai kuma fahimtar iya gaskiyarta ne yasa Ikram zuwa ta faɗowa Mom ɗin. Ganin akwatuna har set uku a falon Mom masu shegen ƙyau da tarin kayan sa rana ya sata tambayar Ya Khaleel first born ɗin Mom. Shima dai saurayine zangarere da shi dan yana shekara ta 26 a duniya. Khaleel ƙyaƙyƙyawa ne shima kuma nutsatstse. Sai dai akwai tsare gida da rashin son raini harma yafi Shareff zafi, dan shi Shareff inhar baka shiga gonarsa ba babu ruwansa da kai, sannan yana da sakewa da jama'a fiye da Khaleel. Shine na uku a haihuwa a gidan. Dan sanda Mom ta auri Abba haihuwar Mommy biyu ne. Daga Shareff sai Maheer da take goyo. Duk da Shareff ya bama Khaleel shekaru sosai hakan bai hana ƙaunar juna shiga tsakaninsu ba, dan tunda ya dawo daga Indonesia bashi da wani aboki a gidan kamar Khaleel. Da taimakonsa ya san wajaje da yawa daya manta, sannan tun a baya idan yazo hutu dama shine abokin yawonsa saboda nutsuwar yaron na birgesa. Yafi Maheer hankali sosai da sanin ciwon kansa, dan yanada himma da ƙwazon nema duk da ko maganar aure bayayi ma.

       Duk ɗaurewar Khaleel suna ɗan shiri da Anam, sai dai itama ba wani sake mata yake ba dan miskilanci a jininsa yake. Kamar bazai tanka mataba yanata aikin danna wayarsa sai kuma ya kalleta. “Kayan auren Yaya Shareff ne”.

      “Ya mi?! Dama aure zaiyi!?”.

A yanda tai maganar ya tilastashi sake dubanta da ƙyau, haka kawai yaji dariya ta taho masa. Amma sai ya gimtse.

       “Kinada matsala da auren nasa ne Granny”. (Dan haka yake kiranta mafi yawan lokaci).

     “Kuji Ya Khalel ɗin nan da wani magana. Ni ina ruwana da wani aurensa da har zai zamar min wani damuwa. Ai sai dai nai murna zai tafi can ya barmu mu huta matan ta kwashi baƙin hal......”

     Jin ta gagara ƙarasawa yasa Khaleel fashewa da dariya, dan dama dai tun ɗazun ya lura da Shareff daya fito daga bedroom ɗin Mom. Ita kuma sam ALLAH baisa ta lura ba sai yanzun da yaƙe ƙoƙarin baro corridor ɗin baki ɗaya dan dama kamar ya ɗan tsayane yana sauraren su, amma a zahiri waya yake dannawa. Duk da ba inda take yayo ba da gudu ta afka ɗakin barcin su harda murza key.

     Shiko dama daba inda take yayo ba harara kawai yawatsama Khaleel da faɗin, “Dalla tashi muje ka zauna kana abu kamar wani yaro”.

         Har yanzu dai dariya ƙunshe a bakin Khaleel ya miƙe. Idonsa na duban ƙofar da Anam ta shige. Suna ƙoƙarin fitowa yace, “ALLAH my best yariyar nan sam bata da wayo har yanzu. A hakan wai kuma ta kammala karatu. Bayan rashin wayon ƴan fari a jikinta harda taɓarama na ganin ita kaɗai ce a gaban su Mamie. Jiya fa harda kuka ta dinga yima su Mon wai zafi saida aka kawo fan aka kunna mata”.

      “Mom ɗince ta biye mata mtsoww ”.

Ya faɗa cikin halin ko in kula. Shi dai Khaleel yace, “Gara dai da aka kunna mata dan bata saba da zafin nan bane namu. Su da suke fama da dusan ƙanƙara ma wasu lokutan dan tsabar sanyi. Kaga ko tazo nan dole ta shiga wani yanayi dan kano ogace ta zafi..”

      Komai bai ƙara cewaba yay gaba Khaleel ya bisa.


     Kasancewar da  Mom da Aunty Amarya sai wata ƙanwar Momy da yayarta za'aje yasa Anam maƙalema Mom sai taje. Mom bata hanata ba, dan ita tanada sauƙin kai sosai shiyyasa suke zaune lafiya da Mommy tsahon shekaru, duk da dai itama Mommy ɗin bawai tanada faɗa bane ko rikici, kawai dai ta tsani Mamie ne saboda tun farko akan hakan Gwaggo ta ginata, ta riga ta nuna mata shi Abie ɗan uba ne a cikin su Daddy duk da kuwa ba itace ta haifesu ba. Sai kuma ta kasance mace mai son komai ace itace sama da kowa, sannan a wajenta ake neman komai, a ganinta bazai yiyu ita matar farko a gidan ba, sannan mijinta shine babba ace wata a matan ta fita. Fin da Mamie ta mata kuma ya ƙara ƙiyayyar, itako Mom Abbah bai kai Daddy ba gaskiya, sai dai na waje bazai taɓa fahimtaba kasancewar ana ganinsu kansu a haɗe a koda yaushe kuma suna gida ɗaya ne.

      Kasancewar matar da Shareff ɗin zai aura ɗiyace ga gwaggo halima (ƙanwar daddy), kuma mahaifinta yaya a wajen mommy gawurtaccen ɗan siyasa mai muƙamin babba a jihar ta kano gidane katafare suka iso. Komai yaji na more rayuwa. Fadwa shine sunanta, ɗiya ga Alhaji Sadiq Dakata. Mahaifinta kamar Yayane ga Mommy. Dan da mahaifiyarsa, da Mahaifiyar Mommy da gwaggo duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Zumincine mai ƙarfi a tsakaninsu, dan haka ita da Gwaggo suka zaɓama Shareff Fadwa matsayin mata tunkan ya dawo gida Nigeria. Sunyi hakane a cewarsu dan kar Abie yay tunanin basa auren Anam. Da farko dai Shareff bai maida hankali ba duk da baice baya sonta ba. Sai da Mommy ta masa jan ido sannan ya ɗan ke kula Fadwa ɗin. Fadwa ƙyaƙyƙyawar yarinya ce gwargwado kuma ƴar gata, sannan kuma sele (celebritie) a social media, musamman tictok da istagram harma da twitter. Idan zan zauna fayyace muku wacece Fadwa zamu cinye labarinne a kanta. Kuje zuwa dai lokaci zai nuna muku ainahin Fadwa Sadiq Dakata.

     Sun sami tarba ta girma da girmamawa. Inda babu kunya Fadwa ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su Mom. Yayinda su Abie ke can suna tattaunawa da su Alhaji Sadiq domin tsaida rana. Dama dai shine yace baya son aita jeka ka dawo, su haɗo komai rana ɗaya su kawo har sadaki sai kawai a tsaida ranar ɗaurin aure.

        Su dai su Mom wannan abu ya sakasu jin lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa ƴar gida ce dan sun san wasu a cikin halayenta saboda kowa yasan ƴaƴan gwaggo Halima basu da ƙwaɓa. har cikin rai suna jin tausayin Shareff ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana  ba a mafi yawan lokuta. Amma sauran ƴan uwan Mommy da yake ƴan uwansune suma sai basuji komaiba a lamari, dan kuwa dai basu nuna a fuska ba sai dai in sun barma ransune suna nuna normal ne a zahiri.

       Fadwa tasan labarin Anam a wajen Mommy da Gwaggo da mahaifiyarta. Sai dai bata santa a zahiri ba sosai saboda gwaggo halima ba shiga duk abinda ya shafi su Abie take ba, tasha jin sunzo ƙasar tabi duk hanyar datai mata ta toshe haɗuwarsu sai idan wata fitinar suka shirya da su gwaggo shima ita kaɗai take zuwa babu ƴaƴanta. Hakan yasa yaranta basu wani san Abie ɗin bama balle ƴarsa, shima kuma bawani gama sanin ƴaƴanta yay ba tunda bata bari su raɓesa. Hakan yasa Fadwa bata nuna damuwarta da ganin Anam tare da su Mom ba. Amma dai yanda Anam ɗin ta zama miskila a wajen tana kallon komai ya ɗan ja hankalin su Fadwa da ƙawayenta gareta. Har takai babu kunya Fadwa na tambayar su Mom ina suka samo Anam ɗin?. Murmushi kawai Mom tai da faɗin “Itama ƙanwarki ce”. Daga haka ta tsuke bakinta duk da tambayar bin ƙoƙwanto da ƙawayen Fadwa ke cigaba da jefamasu Mom ɗin. Aunty Amarya dama bata tanka ba dan ita bata da farin jini a garesu kasancewarta kishiyar Mommy.

     Har dai suka baro gidan Fadwa da ƙawayenta basu san matsayin Anam ba. Ita kuma ta miskile ko ruwa bata sha ba a gidan har suka taho. Gwaggo halima ma duk da taga kamanin Abie a jikin ta kuma tasan sun zo bata tanka ba bata nuna komaiba. 

         Anam ma sai da suka ɗakko hanyar gida ta fara yima su Mom mitar Fadwa da ƙawayenta masu shegen rawar kan tsiya da nuna wayewa. Murmushi kawai Mom da Aunty sukeyi dan mota ɗaya suke su uku, ƴan uwan Mom ma na nasu su biyu.

      Bayan sun iso gida kowa yaji ainahin watan bikin a bakin su Abie. Nan da watanni biyu. Sauran yaran gidan nata murna duk da wannan ba shine karon farko da za'ai biki ba. Anyi bikin Rahma dake bima Khaleel, da Binta ƙanwar su Shareff dake bima Maheer. Yanzu Aysha ce a layi kuma sa'ar Anam ce dan watanni ta bama Anam ɗin kawai, itace ɗiyar Mommy ta biyar daga ita sai autoci su twins. Ga Anam kam babu dalili ta wani tsume sai kallonsu take da taɓe baki, har bayan magrib babu fara'a a tare da ita. Rashin walwalar tata yasa koda Aysha ta tambayeta. Sai tace ba komai.

     Sai bayan magrib suna hira duk kusan yaran gidan a falon aunty Amarya, gaba ɗaya hirar tasu ta ta'allaƙa ne akan shirin biki. Sai dai Anam taƙi tako tanka sai faman game take bugawa a waya. Sai dai kuma kunenta duk yana a garesu ne. Jin sun cigaba da damunta ta tashi zaune tana wani taɓe baki da harar Nusaiba mai gwada rehearsal na rawan da zasuyi wai a wajen dinner....

     “Kun wani dage sai tsara events kuke bayan amaryar ma ko aji bata da shi mtsoww!!”. 

   Lokaci ɗaya falon yay tsit duk suka juyo suna kallonta. Hussaina ta ɗan waro ido da ƴar tsiwa tace, “Aiko dai aunty Fadwa nada aji gata ƙyaƙyƙyawa ƴar babban gida bama son jealous”.

       “Jealous!!. K! Hussaina dani kikeyi wai! kowa ma? Ni Juwairiyya ce zanyi jealous ɗin wancan farin ƙasan mai kama da ƴar tallan kasuwa. Baki da hankali”.

      A yanda take maganar a fusace yasa Hussaina tsorata, dan in tsiwa takeji Anam kakartace a iyawa. Amma shirun nata badan tsoron bane kawai, harda wanda idonta ya hango ya shigo falon ne yasa tai shiru. Anam kam da sam bataji ko sallamarsa ba sai faman faɗa take da sule Fadwa iya gaskiyarta. Tsaki ta doka da fisgar tab ɗinta dake hanun Hashim da nufin barin wajen, karaf idonta ya sauka a kansa. Yana tsaye tamkar an dasashi ya kafeta da manyan idanunsa masu razana wanda ya shiga gonarsa. Sosai gabanta ya faɗi, amma da yake ƴar gagiyar bata yarda aga gazawarta a fuska ba sai ta ɗaukesu cike da wani irin sallo da kaɗasu kamar mai harara ta nufi hanyar kitchen domin bi ta baya, dan tana shakkar bi ta gabansa tunda a ƙofar falo yake tsaye. Duk da bai nuna yama ji abinda tace ɗin ba hakan bai hana su Aysha ƙara nutsuwa ba.


         Washe gari Abie yay shirin komawa. Anam ta zauna taita kuka itafa sai dai su koma tare. Yasan halinta akan kafiya, baiyi da wasa ba yay mata fata-fata, sai su Abba ne da aunty Amarya keta lallashinta da Ya Khalel. Shareff kam duk da yana wajen ko tari baiyiba. Yamaƙi nuna yasan abinda akeyi. Sai da zai buɗema Abie baya zai shiga ne ya harareta. Ƙasa tai da kanta ta sake fashewa da kuka.

        Daddy da yaga hararar Shareff na ƙoƙarin shiga mazaunin driver ya dakatar da shi. “Kaga ku wuce da Mamana tai rakkiyar itama”. Kansa ya duƙar ƙasa fuskarsa na sake tsukewa da satar kallon Mommy. Murya a rissine yace, “Daddy zanje wani wajene fa bayan airport ɗin”. 

    “Sai ku tafi tare da ita tama huce kafin ku dawo gida”.

    Sosai takaici ya sake lulluɓesa. Sai dai baice komaiba. Daddy da kansa ya buɗe gefensa ya sakata dan Abie baya ya shiga. Koda suka bar gidan shi da Abie ne kawai keta hirarsu. Itako tai tsit kamar bata a motar, sai ajiyar zuciya take faman saukewa idanunta a lumshe sanyin ac na ratsata. A airport ɗin ma Abie shareta yay har sai da aka fara shelar masu tafiya a jirgin da zaibi sannan yaɗan fara lallashinta da ƙara mata nasiha. Daurewa kawai takeyi, amma ita dai bata ƙaunar zama a ƙasar batare da iyayenta ba. Da ƙyar ya ɓanɓareta a jikinsa domin amsa kira, tana ganin ya shige ta dirƙushe a wajen. Takaici ya saka Shareff buɗe motarsa yay shigewarsa. Jin ya mata key ya sata miƙewa da sauri dan ta tabbatar kaɗan daga aikinsa ya wuce ya barta a wajen. 


      Sunbar airport ɗin kaɗan kiran Momy ya shigo masa. Idonsa ya ɗan rumtse kafin ya kai hannu ya ɗaga. “Kana ina?”. Ta faɗa tunkan yay sallama. “Mommy can gidan mana”. Ya faɗa a tausashe. “What! Al-Mustapha kana da hankali kuwa? Da wannan yarinyar kake nufin kaje?! To ina mai tabbatar maka maza ka sakota a napep ta dawo gidan ko ranka ya ɓaci bansan iskanci”. Ɗan jimm yay na sakanni biyu. Sai kuma ya ɗan saki murmushi. “Okay Mommy ba damuwa”. Numfashi ta sauke a hankali da faɗin, “Yauwa ko kaifa. Bana son wannan karon naji abinda bai minba kaga dai yanzu akwai banbanci da da. Ka kula ka bita a yanda take so dan ALLAH”. Nanma murmushin kawai yayi batare da yace komai ba, sai dai har cikin kunnenta tajisa dan haka tai masa sallama ta katse kiran. Wayar ya ajiye shima ya cigaba da tuƙinsa a nutse har suka iso.

       Da sauri ta waro idanu waje ganin inda suka zo, ta dubesa idanunta nayin ƙwal-ƙwal na tahowar kuka. “Yaya! nidai ka kaini gida bazanje wannan gidan ba”.

       Harara ya zuba mata, batare da yace komai ba yay parking a ƙofar gate ɗin. Sanin abinda zatai nan gaba shine roƙonsa ko guduwa ya sashi dubanta, “Haɗiyemin wannan silly hawayen banzan kafin nai miki dukan mutuwa a wajen nan”.

     Babu wasa a zancen nashi, dan haka ta haɗiye sautin kukan sai dai hawayen kam sun kasa tsayawa. Wayarsa data fara tsuwwa ya ɗauka, ganin mai kiran ya sashi ɗagawa da kaita kunne. “Ina waje”. Kawai ya faɗa tare da yanke wayar. Ko mintuna biyar basu gama cikaba Fadwa ta fito cikin yauƙi da yanga. Wando da riga ne a jikinta parkistan ƙirar Egypt. Sosai kalar kayan ya fidda mata ƙyawunta. Musamman yanda ƙaton gilashin data saka ya kusan mamaye rabin fuskar tata da haska farar fatarta. A hankali Anam taja guntun tsoki da ɗan laɓe baki. Sarai Shareff ya jita, sai dai komai baice mataba har Fadwa takusa ƙarasowa garesu.

     “Fita ki koma baya”.

Yanda yay maganar a dake batare da ya kalleta ba ya sata juyowa ta kallesa. “Are you daft?!”.

     Maganar tasa tayi dai-dai da isowar Fadwa jikin motar tana ƙoƙarin buɗe gaban ta shiga dan batai zaton ganinsa da wani ba ma balle wata.  Da sauri Fadwa taja baya saboda yanda Anam ta buɗe murfin a fusace. Saura kaɗan ta bugeta ma ALLAH dai ya taƙaita abun. Ko kallon inda take Anam bataiba tai ƙoƙarin barin wajen maimakon baya daya bata umarnin komawa. Sai dai kuma Fadwa tasha gabanta da sauri....

     “K! K! Dakata k! Ƴar uban wacece a motar mijina?”.

     Ba kowacce hausa Anam ke ganewa ba, dan haka a yanzun ma bata fahimci furucin farko ba hakan yasata kasa haɗa ma'anarsa dana ƙarshe da ƙyau. Amma a yanda Fadwa tai maganar ta tabbata ba'abune mai ƙyau ta faɗa ba. Wani banzan kallo ta watsa mata kawai dajan tsaki ta ratseta zata sake barin wajen. Hannu Fadwa tasa ta fisgota ta maidota baya a wani irin fusace, kasancewarta mutum mai saurin zuciya da son yanke hukunci sai kawai ta ɗaga hannu da nufin zabgama Anam ɗin mari.........✍*_Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Hajiya Fadwa daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. To ku garzayo cikin tafiyar zafafa biyar domin ganin yaya wannan wasan zai kasance😂. Dan tabbas akwai cakwakiya, idan nace cakwakiya ina nufin cakwakiya ƴar gaske. Yanda Fadwa take a tsaye Anam ɗin ma ba kanwar lasa bace. Littafine daya ƙunshi abubuwa da yawa. Rikicin zumunci, makirci, son zuciya, kishi, cin amana, kai harma da SARAN ƁOYE. Wasa ne kashi-kashi, dake da players daban-daban. Karku bari ayi babu ku, zafafa dabanne masoya, musamman na wannan ƙarnin da zasu zo muku a cikin zafi na musamman. Karna cikaku ku dai ku garzayo kawai._*


    _Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, dan girman ALLAH kizo ki mallaki halak ɗinki, idan baki da kuɗin saye ko baki da ra'ayin saye basai kin damu da karantawa ba dan baya cikin wajib. Mai tunanin siya ko mana mugunta ki fitar kiji tsoran ALLAH karki cutar damu bamu cutar dake ba, idan kinyi shirin haka da gayya ko izgilanci a garemu muna roƙon UBANGIJIN al'arshi mai rahama mai jin ƙai, mai sanya alkairi a zukatan dake ƙudurta sharri ya shiryeki ya ganar dake gaskiya ya kuma bamu kariya daga abinda zuciyarki ke ƙulla miki😊🙏🏻._
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.


DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL


IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)

BIYU (400)

UKU  (500)

HUDU (700)


KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


HAFSAT UMAR KABIR

ZENITH BANK

2270637070


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


07040727902


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09134848107KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. 


SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*     *_Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummarka. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar da ni da su. ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai. Ka ƙara mana lafiya da zaman lafiya a wannan ƙasa. Ka azurtamu da shugaba na gari mafi alkairi a garemu da ƙasarmu_*
*_06_*...........Kafin ta sauke nata data ɗaga Anam ta sauke mata lafiyayyen mari daya saka Shareff ɗago idanu a karon farko ya kallesu. Fadwa tai saurin dafe kuncinta tana kallon Anam dake jifanta da wani shegen kallo na gargaɗi tana huci. Mamaki, al'ajab da tsantsar ruɗanin daya haɗu da azabar zafin mari take kallonta ƴar ficit a gabanta. Ba ita kaɗai ba, hatta Shareff wutar kansa ta ɗauke dan mamakinta da ƙarfin hali dama tsaurin idanu. 

      A fusace Fadwa ta kai hannu da nufin shaƙota. Wani shegen kallo ta sake watsa mata da riƙe ƙugu, babu alamar tsoro kona sisi a idanunta cikin zafin rai da harshen nasara ta nunata da yatsa.

       “Niba takalmi bace, ballantana ƙafafunki suyi tunanin takawa a duk sanda sukaga dama. Respect your self ok? Shashasha”. Ta ƙare faɗa tana barin wajen cikin takun izza...

    Tamkar gunkin da aka dasa haka Fadwa ta kasance tsaye tana binta da kallo, dan da gaske wutar kanta ce ta ɗauke baki ɗaya har tama rasa hukuncin da zatai mata. Kusan taku biyar da barin Anam wajen Fadwa ta dawo hankalinta, zabura tayi zata bita  Shareff da mamaki ya hanashi motsin shima ya buɗe motar ya fito, cikin bada umarni yace, “Ƙyaleta”. Juyowa tai tana kallonsa idonta jajur, hakama fuskarta tayi ɗan ja abinka da fara. Tana bala'in jin shakkarsa, amma sai ta kasa daurewa cikin ɗaci tace, “Soulmate! Na ƙyaletafa kace?”.

      Kansa ya jinjina mata cikin ɗan lumshe idanu da jingina da motar, sosai take masa kallon tunzura, amma tai ƙoƙarin haɗiye dukkan abinda ke bakinta. Batare da tace komai ba ta juya da nufin komawa gida. Hanunta yay saurin riƙowa, tai ƙoƙarin fisgewa amma ya hanata damar hakan. A jikin mota ya jinginata idanunsa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da hawaye ke sauka. Ba abinda Anam tai mata bane ya sata kuka, hanata ɗaukar matakin da yayi ne yafi ƙona mata rai.

    Handkerchief ya mika mata, idanunsa na mata kallo cikin lallashi “Nace miki bazan ɗauka mataki bane?”. Idanunta dake ƙara cikowa da hawaye ta ɗago ta kallesa. Ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. “Bana son ɗaukar mataki cikin fushi akan kowanne irin abu ki kiyaye wannan. Shiga muje”.

         Ƙara ƙuna zuciyarta tayi da kalamansa, kamar tace bazataje ba ta fasa sai kuma ta danne saboda shawaran su Mamanta akan ta danne komai dazai mata a yanzu har ta shiga gidansa. Sannan koba komai tana son sanin wacece yarinyar nan, amma cikin fushi tasan bazai sanar mata ba ɗin. Umarninsa tabi ta buɗe motar ta shiga, idanunsa da suka kaɗa sukai jaa ya ɗan bita da su, sai kuma ya janye dayima motar key yay reverse.

          Kasancewar anguwace da kakan daɗe bakaga abin hawaba yasa har suka cimmata. Tafiya take tana sharar hawaye. Duk da horn da aketa faman mata baisa ta juya ba. Ransa ya ƙara ɓaci, a fusace yay parking tare da fitowa yasha gabanta, kanta ta ɗauke gefe kamar bata gansa ba zata raɓashi ta wuce. 

      Hannayensa ya tura cikin aljihun wandon Jeans ɗinsa. “Idan kika ƙara step ɗaya a wajen nan sai jikinki ya faɗa miki!”. Cak ta tsaya iya taku biyun da tai, wasu irin hawaye masu zafi suka ƙara ciko mata idanu. Motar ya nufa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta. Duka kawai take tsoro, dan haka ta share hawayenta dan bata bukatar da ga shi har budurwar tasa su gani, motar ta buɗe ta shiga. Yay ƙaramar ƙwafa da buɗewa shima ya shiga, ya fisgeta da gudu zuwa kan titi batare daya ƙara kallon kowaccensu ba. Sunyi tafiya kusan na minti biyar dai-dai gidan wani abinci Fadwa ta dubesa, “Please Soulmate banyi breakfast ba”. Shiru yay kamar bazai tanka ba, bai kuma da alamar tsayawa, itama kasa ƙara cemasa komai tayi saboda yanda ya haɗe fuska matuka. Harma ta haƙura sai taga ya gangara gefen titi dai-dai wani restaurant da bama tasan da shi ba. Buɗe motar yay ya fita batare da yace musu komaiba, itama Fadwa sai ta fita tana harar Anam data maida hankali ga latsa waya kamar bata a motar. 

       Suna ƙoƙarin barin wajen yakai dubansa gareta, dai-dai ta ɗago itama suka haɗa ido. Fuska ta sake ɗaurewa tamkar yanda shima ya sake tsuke tasa. A yanayin fusata ta janye nata da ɗan kallar gefen Fadwa. Har suna gab da shiga wajen bata da niyyar fitowa ita, sai da suka shige da kusan minti biyu sannan ta fito dan haka kawai zuciyarta ta raya mata ta bisu koba komai zata ragema Fadwa jin daɗi ai.

    Cikin taku a hankali ta shigo wajen, dai-dai yana magana waiter idonsa ya sauka a kanta harta ƙaraso inda suke, kujera taja ta zauna. Idanun nasa ya ɗauke gefe, tare da yin kamar bai ganta ba ya ɗauka wayarsa ya hau dannawa. Kallonsa ta ɗanyi tana tura baki, batare data kalli inda Fadwa take ba itama ta hau latsa tata wayar cikin kwaikwayon salon da yayi.

      Ta gefen ido ya dubeta, numfashi ya ɗan ja a fisge tare da maida hankalinsa ga wayarsa a zuciyarsa yace (azababbiyar yarinya). 

       Kamar tasan mi yake ayyanawar ta ƙara ɗaure fuska tana hararsa shi da Fadwa da hankalinta itama gaba ɗaya ke kan wayarta da alama akwai abinda takeyi mai muhimmanci.  Isowar waiter ɗauke da tray ya sakasu ɗagowa su duka. Har waiter ɗin ta gama shirya musu abincin tabar wajen idon Anam nakan nasa. Ya ɗau cokali zai fara ci tace, “ALLAH Yaya abincinka yafi nawa nama”.

       Duk yanda yaso basar da ita ya kasa. Ya kafeta da idanu kamar mai harara “Kuɗinki ko kuɗina?”.

  Fuska ta taɓe “Naka ne. Amma kuma ai ina cikin masu cin gadonka idan ka mutu, kaga banda laifi idan nayi magana”.

     Wani wawan tsaki Fadwa ta saki tsanar Anam na ƙara faɗi a ranta.

   “Shiga shanu ba sharo”Anam ta fada cikin sakin siririyar dariyar data sake kular da Fadwa (*Sharo ba shanu* bahaushiyar malaysia😹😆)

     Tattausan murmushi kawai ya saki a karo na farko da cigaba da cin abincinsa. (Batun yanzuba ya fahimci bata da riƙo. Sai dai ya tabbatar wannan sauyawar tata lokaci guda ba'a banzaba akwai abinda ke ranta).

    Fadwa ta kafesa da kallon mamaki, sai dai shi yaƙi yarda ya kalla inda take. Saurayin dake kusa da su da drama ɗin tasu taja hankalinsa tun ɗazun yay ƴar dariya idonsa akan Anam shi kuma. Juyawa tai taɗan kallesa. Ganin shima ita yake kallo ta ɗauke kanta tana harararsa, abincin Shareff ta ƙara kallo, burinta kawai ta yanda naman kan plate ɗin nasa zai dawo nata, ganin hankalinsa nakan wayarsa tace. “Yaya!”.

      “Uhhyim!”.

Ya amsata batare da ya daina abinda yake ba. “Na faɗa maka wani abu?”.

     “Uhhm”

Nanma ya sake faɗa batare daya ɗago ɗinba. Ɗan shiru tai tana nazari. Bayan kusan sakan talatin ta dubesa sai kuma ta ɗan harari Fadwa ta maida dubanta ga ƙofar shigowa. “Lah Yaya wannan ba Aunty bace?”.

     Kamar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin jin kamar tayi maganar a serious. Kallonsa ya kai ga ƙofar duk da bai san wace aunty take magana ba akai kamar yanda itama Fadwa da gaba ɗaya takaici ya turniƙe takai kallonta wajen. Wuff ta kwashi kusan rabin naman daya tsole mata ido ta maida a plate ɗinta. Lokacin da yake juyowa fuska a tsuke harta miƙe a table ɗin ta koma na kusa da su da guy ɗin da duk hankalinsa ke kansu yake.

     Plate ɗin abincin nasa ya kalla sai kuma ya kalleta. Kauda kansa yay gefe saboda murmushin dake neman suɓuce masa. Ya ɗan jinjina kansa dayin ƙwafa. Fadwa dai kallonsa kawai take mamakin tsaurin idon yarinyar nan na nema shaƙureta.

       Saurayin da gaba ɗaya komai na Anam ya gama tafiya da imaninsa shima fuskarsa ɗauke da mayataccen murmushi yake kallonta. Ya sake sakin murmushi ganin duk laumar abincin da zata kai sai da yankan nama. Cikin murya ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai zataji yace, “In ƙara siya miki wani gimbiya?”.

        Kai ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta saci kallon Shareff. Ido suka haɗa, ya zuba mata hararar da hanjin cikinta suka kaɗa, amma saita fuske cikin dakewa. Ƙasa tai da idanunta Tana ƙoƙarin sake kai abincin bakinta kamar bata gansa ba, saurayin ya sake ɗan matsota cikin ranƙwafowa har tana jin hucin numfashinsa yace, “Queen Please”.

      Wani irin cije baki Shareff yayi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe gaba ɗayansa. Gabansu ya iso ya ɗauka wayarta da saurayin ke ƙoƙarin ɗauka. A kausashe yace, “Tashi muje”.

     Kamar bazata ɗago ba sai kuma dai ta ɗago tana kallonsa. “Ni banfa gama ba, ba yanzu muka fara ba, ga budurwarka ma bataci nata ba”.

    “I will slap you in baki tashi ba”.

Miƙewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba yayma waiter nuni tazo. Kuɗinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman rago. Fadwa da ko lauma ɗaya bataiba dama ta miƙe tsam da wayarta a hannu ta fice, bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko jikin mota ya sameta ta haɗe fuska tamau. komai baice mata ba ya buɗe ya shiga, a dai-dai nan aka kawo masa takeaway ɗin da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai saurin buɗewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buɗewa ya fito yana dube-dube.

        Wata shaƙiyyar dariya Anam ta ƙyalƙyale da ita harda kwanciya, tana ganin zai dawo ta haɗiye kayarta da gyara zama ta fuske...

    A dake yace, “Malama dawo nan”.

Ido ta ɗan waro tamkar bata san mike faruwa ba. “Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari taje bane?”.

     Kallon banzar daya watso mata ya sata buɗe murfin ta fita tana danne dariya da ƙyar, ƙasa-ƙasa take faɗin, “Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai tasan ita ƙaramar ƴar iska ce”......


★★★★


         A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin ɓacin ran dake tattare da ita. Tunda Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma yaƙi shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba'aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa ɗauke da ledar takeaway. Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta waje. 

      “Yaya sannu da zuwa”.

Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faɗin, “Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka”. A yanzu kam idanunsa ya ɗago yana kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai hannu ga ledar. “Bara na ɗauka maka to”. Harararta yay, babu shiri taja baya tana tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗagashi sama. “Oh my Friend ya kake?”.

      “Lafiya lau Yayanmu. Good morning”.

      Kumatunsa ya ɗan ja yana murmushi. Kafin ya ɗan kalla falon. “Gentlemen ina Mom ne?”.

      “Tana ɗaki da aunty Rahma tazo”.

“Okay! To kace ina gaisheta.”

     Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef ɗin, cikin raɗa yace, “Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi”.

          Idanu ya ɗan waro waje kamar yanda yaron yayi, “Haba dai?”.

   “ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon ɗina”. “Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci tare”. Duk da ledar ta masa nauyi da ɗan gudunsa ya nufa ɗakin cike da murna yana ƙwala kiran “Aunty Anam! Aunty Anam!!”.

        Idanu yaɗan lumshe a hankali da harɗe hannayensa duk biyu a ƙirji yana murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?. 


        Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haɗiye sauran gulmar da take faɗama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai saurin barin falon tana tura baki gaba. 

     “Shareff kai dawa kaje gidan Halima!!”. Mommy ta faɗa a fusace tunkan yace mata komai. Ɗan jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya ɗago yaɗan dubeta. “Mommy ni ban shiga gidanba ma balle naje da wani”. Harara ta watsa masa. “Wlhy Al-Mustapha ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai bazakajita da daɗi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka ɗauketa kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata walaƙanci a gabanta ko?! Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan haɗa zuri'a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan talla......”. Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ƙasan carpet ya zauna ya ɗora kansa jikin ƙafarta, hanunta ya riƙo cikin nasa murya a sanyaye, “First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaɓinki, idan ma hakane a ransu ai bani kaɗai bane ɗa a gidan ko?!.....”

        “Ko kai kaɗaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane a ransu Maheer ma yafi ƙarfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel saina hana uwarsa yarda”.

       Murmushi ya saki mai faɗi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar da suke masa ce ta sashi buɗe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma yace wani abu Hassan yay saurin faɗin, “Yaya daga aikan Gwaggo muke fa”. Komai baiceba ya miƙe ya fita a falon.


___________________


        A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharɓa saboda jin daɗin ɗan sanyi-sanyin safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an ɗauke wuta bazata sake rintsawaba. Dan ƴar fan ɗin da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya taƙi ɗaukar caji. Gaba ɗaya Mom ta shafa'a da batun fara fitar Anam ɗin yau itama, shiyyasa batai tunanin tadata ba tanata ƙoƙarin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaɓeta da ƙyar..


        Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma, bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haɓaka kamfani yake. Zamansa tsayayyen mutum yasa ma'aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani, dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu masu buƙatar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ƙanensa nata ƙoƙarin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ƙoƙarin kaiwa zaune a ɗaya daga kujerun falon dan bazaka taɓa ganinsa cikinsu yana cin abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining ɗin tana haɗa masa tea ta ƙaraso garesa. Tunkan ta ƙaraso ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mug ɗin. “Good morning First-luv”.

      “Morning dear, how are you?”.

“Alhamdulillahi”.

     “Haka ake so ai. A saka maka Irish ɗin?”.

    “No Mommy wannan ɗin ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight thirty”.

        “To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight ɗin gab yake dayi”.


      Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma'a da laraba zai sayo fruit bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ƙarshen wata zai sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai buƙata kananu yakai kowane sashe. Tun Mommy najin haushi da masa faɗa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan na damunta da ɓata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan haka ya maƙale daga ƙofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaɗa da take masa kuma ransa naso. 

      “Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida  Mom a kaimin mota”.

    Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa school bus ɗinsu. Kafin ya ƙarasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi mai aikin Gwaggo ɗauke da ƙaramin basket. Tunkafin ya ƙaraso ya buɗe motar da key tai ƴar ƙara. “Ranka ya daɗe gashi inji Gwaggo”. Baice komaiba ya amsa basket ya ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yunƙurin shiga motar da yay niyya ya nufi Daddyn ɗin duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da asuba, tare kuma suka fita motsa jiki....

       “Babana har an fito?”.

   “Eh Daddy nama so makara dan inada meeting”.

    “To ai yau da gobe sai ALLAH ko”. Daddy ya faɗa dai-dai da fitowar Anam daga sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka saceta ka gudu. Ta naɗa yololon veil ɗinta tare da ɗora p-cap ɗin samansa, saita goya bag ɗinta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta sauke hular daga kanta tace, “Good Morning Daddy”.

     “Good Morning Maman Daddy. how are you?”.

    “I'm fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daɗi”.

         “Ayya mamana ba'akwai fan a ɗakin naku ba?”.

  “Akwai Daddy, idan suka ɗauke nepa ɗinne fa, fan ɗin da Mom ta bani yaƙi ɗaukan cagi jiya”.

     Kanta ya ɗan shafa da faɗin, “Am sorry insha ALLAH za'a saya miki wata to koda an ɗauke wutan, koma ac za'a sayo dai?”.

      Ƴar dariya tayi da satar kallon  Shareff da tun zuwanta wajen ya haɗe fuska yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban Shareff ɗin, “Kun gaisa da Yayan naki ko?”.

        Baki taɗan tura gaba da ɓata fuska, sannan tace, “Good morning”.

      Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a aljihu da faɗin, “Daddy bara na wuce ina ƙara makara”. 

    Daddy yace, “Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce”.

       Idanu ta waro da ƙyau tana ƙyaƙyƙyafta su. “Daddy Abie yace driver zai dinga kaini”.

     “No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an ɗauka miki wani driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya ɗakkoki ba shike nan ba”.

         Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai, sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata buƙatar haɗa sabgarta da shi. Duk miskilancin Khaleel tafi jin daɗin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai sauƙin kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daɗi.

      Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa “To ALLAH ya bada sa'a. Sai ka wuce da Mamana ko”.  Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan rissinar da kansa ƙasa da fadin. “Mu yini lafiya”. Jinjina masa kai shima Daddyn yayi. “ALLAH yasa. Mamana bishi ALLAH ya bada sa'a”. “Amin Daddy” ta faɗa dabin bayan Shareff da tuni yay gaba abinsa kamar ta make masa ƙeya..........✍


_🤭🤗maza ki make to dan ALLAH_._ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_08_*..........Tunda ya amsa wayar ya turama wadda ta kira da sister ɗinta address ɗin inda suke yaketa lallashinta ko ruwa tasha amma taƙi sai faman sharɓan hawayema takeyi. Hakan yasa yay tagumi kawai yana kallonta. Komai tai birgesa takeyi, Duk da ƙaramin jiki da take da shi kai kasan ba yarinya bace, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci lallai ƴar gatace a gidansu dan saurin karayanta yayi yawa. Hoto ya fara mata yana murmushi batare data sani ba.....

         Tunda ya shigo idonsa ya sauka a kansu. Wani irin baƙin ciki da ɓacin ransa sai suka ƙara ninkuwa. Nufarsu yay rai a ɓace sai dai bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba duk da ya ciskulleta sam babu fara'a. Kamar ance ta ɗago idonta ya sauka a kansa. Babu shiri ta miƙe zumbur dan yanayinsa ya tsorarata, bata manta dukan da yay musu ita da Aysha ba. Wani irin mugun kallo yay mata ya ɗauke kansa ya maida ga saurayin da shima ya miƙe dan ya gansa. Kallon banza da tsana yake masa yayinda shi saurayin yay ƙoƙarin mika masa hannu suyi musabaha yana murmushi duk da yaga kallon banzar amma ya shanye.

    Kallon hannun yay ya wani ɗauke ido da maidawa kan fuskarsa yana mici-mici da idanunsa dan sarai ya gane shine ranar yayta binsu daga wannan restaurant ɗin.....

       “Kana buƙatar ka zauna lafiya?!!”.

    Duk da a yanda yay maganar cike da isar gadara hakan bai hana saurayin sakin murmushi ba da jinjina kansa. Cikin sauƙaƙa tasa muryar yace, “Sosai kuwa babban Yaya. Ai magabatanmu kance zaman lafiya yafi zama ɗan sarki”.

     Kansa ya ɗauke duk da shine ya buƙaci amsar kuma aka bashi. Wani ɗan juya harshensa yay cikin bakinsa cike da basarwa yana sakin murmushi mai harshen damo. Sai kuma ya jinjina kansa da sake maido dubansa ga saurayin fuska a haɗe. “To daga yau, daga yanzu, karka bari na sake ganin wannan fuskar taka a inuwa ɗaya da ita. Inba hakaba......”

    Ya ƙarasa da wani shegen murmushi dimple ɗinsa na loɓawa, yaɗan bubbuga kafaɗar saurayin. Bai saurari amsar da saurayin zai bashiba ya fisgi hanun Anam dake maƙure waje guda zuciyarta kamar zata kifo ƙasa. Da tasan shine zaizo ɗaukar tata data aminta da shawarar saurayin daya buƙaci Aysha ta tura address ɗin gidan shi ya kaita amma taƙi. Jakkarta dake kan desk ɗin ya fusga itama tare da wayarta yay gaba da sake yima saurayin warning da idanunsa dake rine matuƙa fiye da yanda ya shigo wajen.....

      Turata yay a motar ya rufe har saida ta zabura dan kaɗan ya hana ya datse mata yatsun hannu. Ya zagayo mazauninsa tare da figar motar a guje yabar wajen. Yanda yay ɗin yay masifar sake firgitata har sai da ta faɗa gefen hanunsa ta ƙudundune fuskarta tana kiran sunan ALLAH, dan ta zata gabzama motocin gabansu karo zaiyi ma. Ƙuwwww!!! Ya taka birki da daka mata wata razananniyar tsawa. Saurin sakinsa tai tai baya a firgice, sai kuma ta fashe da kuka dan gaba ɗaya ya sake firgitata ta tsani tsawa...

         “Stupid! shut up!!. Idan baki rufemin shegen bakinki ɗin nan ba na fara kashe fuskarki da maruka sai kin suma. Wawuya kawai. K har idonki yay tsurin bin motar saurayi kuje restaurant?! Dama abinda kikazo yi kenan a Nigeriar?!!!”.

      Yanda ya ƙare maganar a matuƙar tsawace ya sake birkitata. Amma sai ta danne cikin ƙarfin hali tace, “ALLAH ya kiyaye danni ba mayyar maza bace”.

      Ya sake watsa mata harara kai kace cinyeta zai da jajayen idanun nasa. Sai kuma yay ƙwafa da ɗauke kansa yana sake tada motar. Ko motsin kirki bata sakeyi tunda ta samu bai maketa ba. Kukan ma ta daina na zahiri na zucici takeyi. Gaba ɗaya jitake tama gama tsanar Nigeria, ita dai gaskiya bazata iya wannan masifar ba, tun farko abinda ta guda kenan amma su Mamie sukaƙi fahimtarta. Itakan duk ma yanda za'ai a satin nan sai tabar Nigeria hidimar ƙasar nan bazata yuwuba.....


       Ko gama dai-daita parking baiyiba ta fita dan mutanen gidan duk suna tsakargida tsaitsaye Gwaggo da Mommy ne kawai babu sai irin su Fawwaz da sunyi barci tuni basu san abinda akeyiba. Aysha ce ta taho da gudu suka rungume juna, sai kuma ta saketa taje ta rungume aunty amarya da Mom. Su Daddy da tuni Aysha ta kirasu suka dawo gida zaman jiran isowarsu suma ajiyar zuciya kawai suke saukewa..

      Mom dake shafa kanta da murmushi tace, “Kukan ya isa haka mana mamana. Tunda kuma an dawo gida sai muce Alhmdllhi. Jeki gaida iyayenki”.

    Babu musu ta saki Mom tana share hawaye ta nufi su Abba. Gaishesu tai hawaye na sake silalo mata, abinka ga ƴan boko kasa daurewa Daddy yay sai da ya ringumeta. “Haba Mamana ina kika shige haka duk kin tada mana hankali”. Ya faɗa yana mai ɗagota a jikinsa. Murmushi tai tana share hawayen da suka ƙi tsayawa. “Daddy na kasa ganewane, idan na tsaida masu keke ɗinnan sai suce basu gane yanda nake faɗa musu gidan ba”. Tausayinta sosai ya ƙara kamashi, kanta Abba ya shafa yana murmushi. “Dole ki dage ki koya hausa a zaman nan Mamana, dan rashin iyawan ya taka rawar gani cikin accident ɗin nan”. 

      “A'a Abba dan ALLAH ni zan koma  Malaysia”.

    “Tsit gurin yay babu wanda ya iya cemata komai. Sai Shareff ne ya wani taɓe baki da barin wajen ko uffan baicema kowaba balle bayanin yanda ya samota dan a matuƙar gajiye yake ga ciwon kan nasama zazzaɓi yake neman komawa. Daddy ya kashe shirun wajen da faɗin, “Kuje ciki tai wanka taci abinci dan tana buƙatar kwanciya da wuri. Mamana mayi magana da safe”.

    Badan tasoba tabi Mom dan bata iya musu ba kuma. Duk da yanda Aysha ke tsoron faɗan Mom haka tabi Anam sashen Mom da ƙudirin su kwana tare, dan jitake kamar kafin safiya za'a ƙara cemusu ba'a gantaba ta sake ɓata.

   

   Washe gari tunkan ma Anam ta kira Abie ɗinta ta sanar masa Daddy ya kirasa sukai magana. Yayma Shareff kuma faɗa sosai kamar zai ari baki. Daga ƙarshe ya kafa masa dokar hukuncinsa shine kai Anam wajen aiki kullum ya kuma ɗakkota. Idan ko wata matsala ta sake shigowa akan Anam to lallai ya kuka da kansa dan sai ya matuƙar ɓata masa rai a gidan.

      Shi dai Shareff ɗin baice komai ba akan hukuncin. Sai Mommy ce tace sam bata yardaba ɗanta ba driver bane ba. Ko kallonta Daddy baiba, ya dai tabbatar mata idan Shareff ya isa yaƙi bin umarninsa. 

       Ai wannan magana ta dagula ran Mommy a safiyarnan. Dan tata masifa ita da Gwaggo data fito tana goya mata baya. Daga Daddy har Abba babu wanda ya sake tofa tasa dan sukam dai yanzu sai dai su kalla Gwaggo kawai tunda sun fahimci bata ƙaunar zaman lafiyarsu da ɗan uwansu, Halima ce kawai ta kasa fahimta sun kuma barta wataran zata gane da kanta musamman da suka san idan akai auren nan na Fadwa da Shareff.


        ★★★★


  Duk yanda Mommy taso hana Shareff ɗaukar Anam hakan bai yuwuba. Dan shi dai haƙuri kawai ya bata da nuna mata illar fushin mahaifinsa a garesa. Ya roƙeta ta kwantar da hankalinta a hankali zai janye jikinsa ya samama Anam ɗin driver kowa ma ya huta. Wannan magana tashi ce taɗan kwantar mata da hankali ta maida kanta ga hidimar shirye-shiryen bikinsa.

      Daga ɓangaren Anam ma taci uban borinta akan malaysia zata koma ta fasa hidimar ƙasar su Mamie suka lallasheta da tabbatar mata cewar idan sukazo bikin Shareff zasu san abinyi. Hakanne yaɗan kwantar mata da hankali ta zauna zaman jiran lissafin kwanakin bikin. Yayinda ta cigaba dabin Shareff ɗin a takure. Shike kaita shike ɗakkota, daga gaisuwa babu abinda ke haɗasu sai harara. Ita kuma tata tura baki kenan da ɗaure fuska ita a dole haushinsa takeji duk da bata da riƙo sam wannan karon dai ta riƙe.


           Yau a gurguje yay shirin tun 7 ma batai ba ya fito saboda wani babban uzirin dake gabansa a office ɗin. Ga baƙi zaiyi akan wani babban project da suke saran samu insha ALLAH. A tsaitsaye ya shiga sashen Mommy suka gaisa koma shayin bai zaman shaba yau dan yaran kansu duk suna ɗaki basu gama shiri ba. Baije sashen Gwaggo ba dan ya gaji da mitarta akan ɗaukar Anam da yake yasan zata ɓata masa lokaci. Aunty Amarya ma a tsaitsaye suka gaisa ya nufi sashen Mom. Bayan sun gaisa da Mom ɗin cikin raba ido da kallon ko'ina na falon yace, “Mom tana ina zan makara?”.

      Da mamaki Mom ɗin ke kallonsa. “Wai kana nufin Anam?”.

    Kansa ya jinjina mata. “Eh Mom, yau zan fita da wuri inada uziri shiyyasa na sanar mata tun ɗazun ta shirya da wuri”.

      “Tab ɗi, to aiko banama zaton ta tashi a barci Babana. Ni kuma ban saniba ai da na tadata ta shirya”.

        Cikin ɓacin rai ya ɗan sake duban agogonsa da rumtse idanunsa. Ganin Mom ta nufi ɗakin yaja ɗan siririn tsoki. “Mom bara naje idan Khalel zai fita su taho tare inada meeting ne mai muhimmanci”.

      “To bara na tasheta dan nasan shima ɗin gab yake da fitowa kuwa”.

   Komai baice ba ya juya ya fita.

         Ba ƙaramin jan ido Mom taima Anam ba kafin ta tashi. A gurguje tai shiri saboda Khalel daya leƙo ya mata gargaɗi. Tasan halinsa shima ba mutunci ya cikaba shiyyasa tai ƙoƙarin shiryawa aɗan gurguje tanata kunƙuni dan barcin bai ishetaba. Tsaf ta shirya cikin kayan NYSE kamar koyaushe, sun mata cif kamar ka saceta ka gudu, ƙaramin baby hijjab tasa yau. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Khalel da gaba ɗaya yake ƙage da fitowar tata hanata zaman shan tea ɗin da Mom ta haɗa mata yayi.

     “Mom Please ki barta tasha a hanya ko a office ɗin, ALLAH idan na makara Yaya zaimin faɗa duk da shine yace na ɗauketa, gashi meeting ɗin nan inada alaƙa dashi nima.”

      “Amma Khalel ta fita bata karyaba? Bayan kasan bako wane abinci take iyaci ba. Kai da Shareff ɗin duk wutar ciki tamuku yawane kawai, amma duka ƙarfe nawane yanzu ɗin? An faɗa muku kowane zai dinga iya uban sakkonku da aiki kamar matching?”.

    “Mom bazaki ganeba wlhy. Please ki barta nidai”.

   Kafinma Mom ta sake magana Anam tace, “Kibari zansha a can ɗin Mom kinsan masifar wancan mutumin tafi ta Yah Khaleel”. Murmushi kawai Mom din tayi yayinda Khaleel ke hararta. 


       Sosai Khalel ya zumbuɗa gudu a hanya, lokacin da suka isa wajen aikin nata har bakwai da rabi ta kusa gotawa. Sai dai sauƙinsa ma babu nisa mai yawa da company ɗinsu dan duk titi ɗaya ne. Baki ta taɓe ganin yanda duk Khalel yabi ya damu kansa tunda suka taho yake mata masifa a mota wai idan tace lalaci zatai to zata dinga hawo motar kasuwa kuwa shi dai baza'a dinga sashi ya jirata ba. Ita dai komai batace ba sai faman ɓata fuska dai takeyi tana cin inibi ɗinta data taho da shi daga gida da buga game a waya har suka iso. 

      “Kije idan an fita break zan kawo miki abinci”.

     Sosai ta waro idanu waje. “Har ƙarfe nawa kenan Yah Khaleel?”.

       Harararta yay yana ƙoƙarin jan murfin data riƙe zai rufe. “Lokacin zuhur mana”.

    “Haba Yah Khaleel one fa kenan? Kaga ƙilama yunwa ya halakani kawai”. 

    Dariya ta bashi amma sai baiyiba. “Naji zan roƙa Ya Shareff idan an tashi meeting zanyi squeezing time na kawo miki”. Kafia tace komai yaja motarsa yay gaba. Tabi motar da kallo tana tura baki gaba.


         Kamarko yanda yay alƙawarin ya cika. Dan wajen sha ɗaya aka kawo mata saƙo. Koda ta buɗe sai taci karo da takeaway na abincin da take tsananin so. Daɗin da taji ya sata tura masa text message na godiya, dan hakan tamkar tarbiyyar su Mamie ne a gareta, indai an mata alkairi komin ƙanƙantarsa sai tayi godiya harma da addu'a. 

        Saƙonta ya shigo wayar Khaleel ne a dai-dai sanda wayar ke a hanun Shareff. Yazo nuna masa hoton wani zane da aka turo masa daga lagos sai kira ya shigo masa a ɗaya wayarsa, bazai iya ɗaukar wayar a gaban Shareff ba shine ya fita. Baiyi niyyar buɗe saƙonba, amma ganin sunan daya turo saƙon ya sashi buɗewa. Shiru yay na wasu sakkani yana kallon saƙon tamkar mai bitar karatunsa, sai faman cizar lip yake, sallamar Khaleel ta sashi danne saƙon ya aunashi a delete gaba ɗaya. Wayar ya miƙama Khaleel batare daya kallesa ba. “Kaje da shi zamuyi magana daga baya kawai”.

        Ɗan jimm Khaleel yay yana kallonsa, dan sanin maganar tasu muhimmiyace, hasalima shine ya damesa da kira tun ɗazun akan yazo duk da yasan suna meeting ne. Amma kuma sai bai kawo komai a ransaba yace, “Okay Yaya. To koma dai na tura maka shi kawai saika sake nazari kafin?”.

         “Okay yayi”.

Ya faɗa a taƙaice kawai. Kasancewar shima Khaleel ɗin miskilin kansa ne sai bai sake tofa komaiba ya miƙe ya fita abinsa. Haka kawai ya samu kansa da binsa da harara harya fice. Tsaki yaja da rumtse ido kamar irin mai takaicin kansa ɗin nan. Ya sake jan tsaki ya miƙe gaba ɗaya yabar table ɗin. Can jikin ƙaton window da aka ƙawata office ɗin da shi wanda ake hango har titi da cikin compound ɗin company ɗin kasancewar a saman upstairs office ɗinsa yake yaje ya tsaya. Ya jima wajen a tsaye hannayensa duka a aljihu yana kallon kaikawon mutane daga titi zuwa cikin company ɗin...


       Da lokacin tashi yay addu'a tai tayi ALLAH yasa Khaleel zai dawo ɗaukarta, har kiransa tayi dan taji sai dai bata samesaba network ya hana. Tun shigowar motarsa wajen tasan addu'arta bataci ba. Ɗan duban Yaseer abokin aikinta kuma shima ɗan hidimar ƙasa ne dake gefenta tai a sanyaye. Ya sakar mata murmushi dabinta da ƙyaƙyawan kallon da yake hanata sakewa da shi. “Ga Yayana yazo bye”.

     Manyan idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta. Shima ya miƙe har lokacin idonsa a kanta. “Haba dai Friend haka ake Friendship ɗin anama juna rowan dangi? Kamata yay kice muje na gaida Yayanmu ai ko? Kullum sai dai naga yazo ɗaukarki baki taɓa gayyata ta na gaisar da shi ba”.

      Murmushi kawai tai batare da tace komaiba. Ganin tayi gaba yay saurin bin bayanta har sai da tafiyarsu ta dai-daita. Kasancewar tinted glass ne yasa Yaseer knocking duk da sarai yasan wanda yake ciki ya gansu. Shiru babu alamar za'a sauke ya ƙara knocking fuskarsa faɗaɗe da murmushi. Zai ƙara na uku Anam ta girgiza masa kai a hankali, dama abinda ta gudar masa kenan shiyyasa taso hanashi tun farko. Tana ƙoƙarin buɗe baki ta bashi haƙuri aka sauke glass ɗin a hankali.

          Kallon daya watsa mata ya sata kauda kanta tana taɓe baki, Ƙara ɗaure fuska yay da duban Yaseer daketa faman shafar ƙeya yana murmushi.... Kafinma yace wani abu Yaseer ɗin yay saurin faɗin, “Good afternoon Yayanmu”.

       Kamar bazai amsaba sai kuma ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha, babu musu shima Yaseer ɗin ya basa suka gaisa, a mamakin Anam harda cema Yaseer ɗin, “Yaya aiki?”. Yaseer ya amsa fuskarsa na sake washewa ga sinne kai yana famanyi kamar wanda ke agaban surukai. Anam ta ɗan taɓe baki tana jinjina kanta, a ranta kuwa gulmarsa take. Tana son ɗagama Yaseer dake ɗago mata hannu nata hanun tanajin shakka, sai da taɗan faki idonsa ta ɗaga sau ɗaya ta fuske. Sai dai batasan yama rigada ya gantaba. Bai daiyi maganaba ya tada motar suka wuce.

       Shiru babu wanda ke magana tsakanin shi da ita sai redion motar daketa karaɗi, ganin inda suka shiga saɓanin gida daya kamata su nufa ya sata kallonsa a sace tana muy-muy da baki alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa. Sai da ta karanta symbol ɗin wajen ta gane Saloon sukazo, mamaki ya sata dubansa dan batasan mi sukazo yi wajen ba. Ido suka haɗa yana ƙoƙarin kai waya kunensa tai saurin ɗauke nata. Shima janye nasa yay da cire wayar daga kunensa hango Fadwa na fitowa a wajen tamkar tarwaɗa. Tayi ƙyau sosai cikin doguwar rigar atamfa, sai veil siriri data yafa iya kanta ta naɗesa a kafaɗa, ga wani uban glasess daya cinye rabin fuskarta sai dai ya mata matuƙar ƙyau kasancewarta fara ƙyaƙyƙyawa. Gefe da gefenta ƴammata biyune suma ƙyawawa kamarta farare tas da su. Yanda suke dariya zai tabbatar maka wata maganar sukeyi dan har ita Fadwan fuskarta cike take da murmushi. A hankali Anam taja siririn tsaki daya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai dai ta wani kauda kai gefe kamar wadda taga kashi. Sarai ya fahimci dasu Fadwa take, amma sai baice komaiba ya buɗe murfin motar ya fita fuskarsa sam babu walwala dan ya tsani taron ƙawayen Fadwa da suka zame mata kamar jela. Idan ka ganta da wannan yau gobe da waccan zaka ganta, na jibima daban ne...........✍


*_Haɗuwar iliya da wargaji😂 kunsan dai ba sauƙi😹😹, ku faɗama yarinyar nan taku yau sai mun rama marinmu ko shi Yayan nata bai isa dakatar damu ba ehe😜🤭._*_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_07_*.........Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma ɗan uwansa magana. Yanata tuƙinsa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaɗi har suka iso. Motar ta buɗe tai ficewarta tana taɓe baki, sai da ta rufe masa ƙofar batare data kallesaba tace, “Jazakallahu khairan” tai gaba abinta. Fusgar motar yay da ƙarfi yay gaba har yana tada ƙura. Hakan yasata faɗin, “Kaji dashi in kayane dai”.


        Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira da marmari har ranta ya fara ƙuna gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun. Sosai ranta yake a ɓace ga yunwa dake bala'in cin hanjinta dan bawani abun kirki taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da strawberry. Ganin yamma na ƙara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la'asar, sai dai ita zafi takeji matuƙa kodan inda ta fito akwai ac ne.

        Ta tare abin hawa yafi sau huɗu amma ta rasa yanda zata musu misalin anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe ƙwalla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ƙaunar wulaƙanci shiyyasa bata wulaƙanta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na wulaƙanta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya ba. Hannu takai a hankali ta share ƙwallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da ƙaunarsu, waɗannan matsalolin na ɗaya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar ƙasa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta.......

        Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruɗeba, dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.

     “Beauty!”. 

  Ya faɗa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi. 

           Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta ɗago ba. Sai ma sake haɗe fuska da tai ta ɗauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda tai ɗin ya tabbatar masa ita ɗince. Buɗe motar yay cike da farin ciki ya fito. “A gafarce ni. Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya koma ta gabanta cikin sake raunana murya. “Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haɗamu daga ni sai k”. Karon farko ta ɗan ɗago ta dubesa, ya sakar mata murmushi. “Dan ALLAH kar kice baki ganeni ba”.

     “Bamma taɓa ganinka ba”.

Ta faɗa da ƙoƙarin barin wajen. Sauri bin bayanta yay. “Please dan ALLAH karkimin haka. Ni ne wanda muka taɓa haɗuwa a GJ restaurant da daddare”. Sarai ta ganesa tun kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake ɓata fuska aɗan fusace tace, “Bani bace Please kabar bina”.

       “Kiyi haƙuri bazan iya daina binki ba wlhy dan kullum cikin addu'a da sadaka nake akan ALLAH ya sake nunamin ke. Ya kuma amsamin sai nayi sakaci da damata”.

   Sosai ya bata dariya a wannan gaɓar, wai sadaka. Dan kawai ya ganta zaiyi sadaka. Hararsa tai zata sake wucesa ya babbake ko'ina. “Dan ALLAH ki saurareni”. Kanta ta dafe dan yanata faman haɗata da abinda bazata iya jayayya ba. Hakan yasa dole ta nutsu ta sauraresa. Bawata magana sukaiba damar kaita gida kawai ya nema. Bata da mafitar data wuce binsa, amma maimakon gida da yace zai kaita sai kawai ta buƙaci ya kaita inda zata sai layin waya. Bai musa mataba, dan a ganinsa hakanma wata damace. 

        Kai tsaye office ɗin mtn dake cikin wata plaza yakaita duk da yasan sun tashi aiki yanzu. Sai dai yanada alfarmar da za'a iya biya mata buƙatarta a wajen. Ilai kuwa tarba ta mutuntawa taga ana masa a wajen, yanda kuma suke gaisuwa da ogan wajen taji a ranta ɗan uwansane ko aboki. 

      “Mutumina wannan ƴar shilar fa haka?”.

    Abokin ya tambaya cike da shaƙiyanci cikin zaurancen hausa da Anam ta kasa gane komai dan shima ya fahimci bata iya hausan ba, saboda yanda yay mata tambaya da hausa ta gagara bashi amsa mai ƙyau. Dole suka koma magana da turanci. Murmushi kawai yay batare daya bashi amsaba, sai ma danna waya da yake faman yi abinsa.

     “Wai ka zama kurma ne?”.

Abokin ya sake tambaya yana harararsa.

       “Sarai ina jinka. Kai dai yi aikinka  kawai ba buƙatar tambayar ne”.

   Dariya kawai abokin yay ya cigaba da ƙoƙarin ɗaukar Anam hoto. Tun a gurin ta ɗora layin akan wayarta, ta kuma tambayesu ko zata iya amfani da shi. Kasancewar abokin nasa babban ma'aikaci sai ya amshi wayar yay ƴan danne-danne ya miƙa mata. “Indai kiran gaggawa kike sonyi da shi bashi nan da mintuna talatin sai kiyi”.

    Godiya ta masa tare da duban saurayin da har yanzu ko sunansa bata sani ba. “Zamu iya tafiya?”.

     “Why note Beauty”.

  Ɗan murmushi kawai tai da mikewa. Shima ya bama abokin nasa hannu suka cafke. “Friend ina zuwa ka jirani Please ”.

     “Ba damuwa”.

Cewar abokin nasa yana dariya.

         

    Ganin sun ɗan gota plaza ɗin tace su ɗan tsaya mintuna talatin ɗin su cika. Bai musaba sai dai ya kalla agogonsa duk gudun kar lokacin salla ya shiga. “Beauty inaga muɗan matsa gaba akwai massallaci sai na shiga nai magrib ko”.

     “Babu damuwa”.

Ta faɗa hankalinta akan wayarta. Tun fitarsa a motar babu abinda take sai irga mintuna har ALLAH yasa suka cika. Kai tsaye number ɗin Abie tahau gwadawa dan ta loda kati daga kuɗinta na bank a ciki. Taƙi samunsa saboda network. Komawa tai kan Mamie itama dai yaƙi tafiya kiran. A take idanunta suka sake cika da ƙwalla, ta kife kanta a gwiwarta tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki. A haka ya dawo ya sameta. Sai dai tanajinsa tai azamar goge hawayen nata ta haɗiye kukan.

     “Beauty ina muka dosa yanzu kenan?”.

           “Abinda nake tunani kenan, dan kona maka kwatance ba lallai ka gane ba. Amma in ban takurakaba ka kaini restaurant ɗin nan kawai ka ajiye zan samu mafita”.

        Kallonta kawai yake cike da nazari. “Na miki wani tambaya mana in bazaki damu ba?”.

    Shiru kamar bazata amsashi ba. Sai kuma taja numfashi da jinjina masa kanta. Gyara zamansa yay sosai yana fuskantarta. “Harshenki ya tabbatar min idan ma ke ƴar Nigeria ce ba'anan kike rayuwa ba? Hakan na nufin ke baƙuwace shiyyasa bazaki iya gane inda zakije ba?”.

       Nanma kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ɗan kallesa ta duƙar dakai. “Karka damu ka kaini inda nace kawai Please”. 

   “Baki son na sani ko?”.

“No, kawai”.

Ta faɗa a taƙaice. Bai sake magana ba ya ɗan rausayar da kansa da yima motar key yana murmushi.


         Koda suka iso kamar yanda ta buƙaci ya tafi ya barta a wajen bai yarda yayi haka ba. Cikin lallashi ya sata suka shiga wajen. Yabi ya takura mata akan ta faɗi mi take son ci amma taƙi, dan Anam nada wani hali inhar bata saba da kai ba bata taɓa yarda ta sake da kai. Shi kansa badan tana neman mafitaba bazata bisaba tun farko ko wane irin naci zai mata kuwa. Haƙura yay ya amsar musu drinks kawai da snacks amma ko kallon natan bataiba balle yasan zataci. 

    Tunanin kiran Aysha ne yazo mata a rai. Ta sake zaro wayarta dake cikin bag ta hau lalubenta. Cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, sai dai harya katse ba'a ɗaga ba. Bata gajiba ta cigaba da kira har wajen 8missed call amma babu amsa. Da ƙyar ta iya ƙoƙarin danne kukan dake son taho mata......


_______________________


      Ko kaɗan baiyi tunanin bazata iya maido kanta gida ba. Hasalima zuciyarsa raya masa take tuni ta dawo ɗin saboda yayi over time a office yau yana aiki, ga kansa na masa ciwo. Daya shigo gidan ma a ɗan gurguje ya shiga suka gaisa da Mommy ya fito. Wanka yayi a gaggauce shima saboda magrib dake kusantowa. Koda ya kammala shiri ya fito a compound ya haɗu da Abbah da Khaleel suma zasu massallaci. Tare suka fice, bayan an idar da magrib basu dawo gidaba sukai zaman jiran isha'i.... 


       Tun kafin su ƙaraso suka hango Mom da Aunty Amarya tsaye cirko-cirko a ƙofar sashen aunty Amaryar. Dukansu sai suka nufi can dan da alama babu lafiya. Shidai kusan shine ƙarshe dama. Daddy da suka haɗu a massallacin ne ya fara jefama su aunty amarya tambayar “Lafiya kuke tsaye anan haka?”. Aunty amarya ta bashi amsa cikin damuwa da ruɗani. “Daddyn Shareff lafiya ba lafiya ba. Anam ce bata dawo gidaba har yanzun. Mubarak yaje har wajen aikin nata kuma maigadi ya tabbatar masa babu kowa a ciki ita ɗincema kusan ƙarshen fita, ta kuma jima a titi kafin yaga wani ya ɗauketa a mota”.

      “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un”. Daddy da Abba suka faɗa kusan a tare. Shareff ma dake daga bayansu gabansa ne ya faɗi, suka haɗa ido da Daddy daya juyo yana masa kallon tuhuma. cikin son danne abinda keson taso masa yace, “Shareff nasan dai kaji mi mamarku ta faɗa ina ka baromin yarinya?”.

      Sosai ƙirjinsa ke luguden duka. Ya girgiza kansa da risinar da idanunsa da sukai sirkin ja kaɗan saboda gajiya da ciwon kai. 

      “Ba girgizamin kai zakaiba ka buɗe baki kai magana!!”. Daddy ya sake faɗa a tsawace.

            Kansa a ƙasa yace, “Ban baro office ba sai kusan 6, shiyyasa nai tunanin ta dawo gida”.

    “Shareff are you out of your senses?!! Har kake gayamin kazata tama dawo gida. Kana da hankali kuwa? Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”.

         “Wai lafiya mike faruwa ne?”.

Mommy da Hassan yaje ya sanarma gidan babu lafiya ta faɗa tana ƙarasowa wajen. Babu wanda ya iya bata amsa saboda maganar da Daddy ya cigaba dayi a kausashe cikin kuma tsananin ɓacin rai....

       “Wlhy na baka nan da zuwa ƙarfe sha biyun dare ka kawomin yarinyata gida, inba hakaba sai ranka yayi mummunan ɓaci Al-Mustapha!!”.

           Cikin sauri Mommy ta dakatar da shi itama a fusace. “A'a Alhaji kamarya da wannan hukunci haka. Shine ya ɓatar da koma wacece ake neman da za'ace ya fita a wannan daren nemanta bay......”

        “Babu ruwanki a wannan maganar, idan kuma kikace zaki shiga wlhy zan sakaki nadama ne!!”.

      Gaba ɗayansu binsa sukai da kallo ganin yanda yabar wajen a matuƙar fusace. Banda Shareff da kansa ke ƙasa. Abba ne ya dubesa da damuwa shima, sai dai cikin sauƙaƙa murya dan bai kai Daddy zafi ba yace, “Son kayi kuskure. Ka manta Anam babu inda ta sani, ko anguwarnan bana zaton ta san sunanta ma, kag........”

     A harzuƙe Mommy ta katse Abba “Anam!!. dama akan wannan tsifatar yarinyar ake wannan tada jijiyar wuyar? Shareff bance ka fita harkar yarinyarnan ba a gidan nan?”.

      Bai iya ya ɗago ya kalleta ba, dan baisan wace amsa zai bataba. Tana ƙoƙarin nufosa isowar Gwaggo ya dakatar da ita. “Wai hayaniyar mi nakeji a gidanne haka kai?”. Duk juyawa sukai gareta. Ganin kowa ya kasa cewa komai Khaleel yace, “Anam ce bata dawo gida ba”.

       “Shine miya faru kuma? Ita ɗin yarinyace?”.

      “Haba Gwaggo ya zakice haka? Nawa Anam ɗin take? Sannan ina ta sani bayan kinsan kamar baƙuwa take a ƙasarnan bama garin kano ba”.

          Harara Gwaggo ta zubawa Abba mai maganar. “Oh to kana faɗaminne ko kana tunamin Abubakar? Gallaƙeƙiyar budurwa da yanzu idan aka sakata ɗaki da namiji zata samo ciki kake sanarmin nawa take? Toni abindama ban ganeba mi'akema hayaniyar anan?”....

      “Titsiye Shareff sukai yaje nemanta kamar shine yace ta tafi yawon tazubar ɗin, dan nasan bai wuci can ɗin ta tafi ba tunda an saba a inda aka fito..”

       “A lallai kuna bukatar Addu'a Abubakar. Shi Mustapha ɗinne ya kaita ya ɓatar da zakuce yatafi nemanta a wannan daren bayan wahalar da yaje ya gama shawowa a wajen aiki ya dawo. Kai Mustapha muje naga ubanda zai saka fita ko nan da gate a daren nan dan.......”

     Sauran maganar ta maƙale ganin kaf wajen babu alamar Shareff ɗin. Su dukansu babu wanda yasan yama sulale yabar wajen. Horn da ƙarar buɗe gate ya sakasu juyawa can gaba ɗayansu. Sai dai kafinma wani yay wani yunƙuri har motarsa ta fice.....


         Wajen aikin nata ya fara zuwa, sai dai kamar yanda maigadin wajen ya faɗama Mubarak shima haka ya sanar masa. Lokacin da yake tafiya a hankali ya dinga tafiya kozai ganta a hanya. Amma ko alamarta babu duk da titin wajen tako'ina akwai hasken fitulun solar. Duk da hakan bai fasa sake bi a hankali yanzun ma yana dubawaba har ƙarshen titin. Ganin har tara ta gota na dare yay fakin gefen titi ya kifa kansa kan sitiyari dan ciwo yake masa matuƙa kamar zai faɗo ƙasa. Dama tuƙin yinsa kawai yake cikin dauriya.


           A gida kowa ka kalla a cikin damuwa yake, idan ka cire Gwaggo da Mommy da suketa bala'i da kowa ya kasa fahimtar dalilin yinsa. Aysha harda kukanta. Dan ansan ko wayarta aka nema baza'a samuba tunda bata da layin Nigeria. Abba da Daddy da Khaleel ma sun fice police station. 

      “Aunty wayarki sai haske yake tun ɗazun”. Hassan ya faɗa yana duban Aysha data zuba uban tagumi tana sauraren masifar Mommy kawai daketa faman kai kawo tsakanin bedroom ɗinta zuwa falo. Kamar Aysha bazatabi takan wayarba sai kuma tacema Hassan “Ciromin daga cajin”. Ciro mata yay, ganin bata san no ɗinba tai tsaki ta ajiye. Duk kiran da aka cigaba dayi har kusan sau biyar bata kulaba. Sai ma ɗaukar wayar datai rai a ɓace zata kashe sai saƙo ya shigo da no din da aketa kiran nata. Guntun tsaki tai ta buɗe dan taga wai waye ma ya addabeta ya barta taji da damuwarta ma itakam. Zumbur ta miƙe da waro idanu, har zata fasa ihu sai kuma tai saurin gumtse bakinta da satar kallon inda Mommy take. Tai saurin haɗiye farin cikinta ta nufi bedroom ɗinsu da sassarfa. Jikinta har rawa yake ta maida ƙofar ta rufe harda saka key tana dailing number ɗin...

      “Blood da gaske kece?”.

Kamar jira Anam keyi ta fashe mata Aysha da kuka. “Ya ALLAH Blood Please kibar kuka, kina ina ne yanzu? Ga gida duk hankalin kowa a tashe da rashin dawowarki su Yaya dasu Abba duk sun fito”. Ta ɗanji sanyi, amma hakan bai hanata jin zafin Shareff ba. Da ƙyar tace, “Zan tura miki address ɗin yanzu bansan inaneba”..... Aysha na katse kiran tai kiransa.


      Har yanzu kwance yake kawai akan sitiyari, yama rasa wane kalar tunani zaiyi shi kam. Ring na wayarsa ne ya katse masa tunani. Yay banza da wayar harta tsinke aka sake kira. Nanma bai ɗaukaba sai ana uku ya ɗago a fusace da nufin cin uwar mai damun nasa yaci karo da sunan Aysha. “Lafiya kika isheni da kira ke kuma?”.

      “Kayi haƙuri Yayah. Anam ce ta kiranifa yanzu da wani number sai kuka take.”

     Idanu ya rumtse da ƙarfi yana sauke wata irin bahaguwar ajiyar zuciya da har Aysha na jinsa. “Turomin number”. Ya faɗa a takaice kawai da katse kiran. Mintuna biyu kacal number ɗin da address ɗin data turo mata duk ta turo masa. Wayar ya cilla gefensa yayma motar key da fisgarta a guje yabar wajen. Tafiyar mintuna ƙalilance ta kawosa wajen saboda uban gudun daya zabga..........✍


_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107

      

*_ALLAH yasa yau a rama mana marinmu😹😹😜🚶🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_10_*


*_BABU SO....!!   AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


Shin ko kunada labarin Yar Zuru mamar ZEE ZEE Mai maida tsohuwa yarinya wadda ta shahara wurin hada kaya kamar haka ❤️kamar su 

Kaza

Zabo

Zakara

Ciccibi 

Zuciya 

Tsimin kankana d rake

Tsimin tabaje 

Zumar dabino d kwakwa 

Zumar gorun tula syrup 

Garuka masu kama jiki kamar su ❤️

Bita zai zai 

Dan wata bakwai 

Madarar mata 

Bata🤐🤐🤐 

Ba kishiya ba Ko mugun mutan d mugun aljani sai sun barki 

Matsin kinfi budurwa 

Kalolin gumba dsauransu 

Address maberar jariri bayan FGC sokoto 

Phone 08068526455

Instergram Yar Zuru mamar ZEE ZEE kayan mata

_________________.........Ido ya ɗan tsura ma atm ɗin hanunta cike da nazari, kusan mintuna biyu harta ƙosa da tsaiwar sannan yay magana.

     “Ina zakije?”.

  Yanda yay maganar babu alamar wasa yasata ɗan ɗagowa a marairaice ta dubesa. “Abu zan siyo”. 

      “Shi abun bashi da suna?”.

   Ƙasa tai da kanta tana tura baki batare datace komai ba. 

“Kin kurumuce ne?”.

      Kamar zatai kuka tace, “Sirrine fa Yaya MM, kuma acan shagonne bada nisa bane”.

            “Koma ciki”.

    “Yaya zanfayi amfani da shine yanzu”.

      Ƙoƙarin zagayeta yay zai wuce da faɗin, “Idan kin matsu da koma miye sai ki faɗa kafin ki fitan”.

     Ƙafarta ta ɗan buga a ƙasa kamar zatai kuka sai kuma ta nufesa da sauri tasha gabansa. “Yaya Shareff dan ALLAH. Wlhy important ne”.

     “Inda important ɗinne da baki tsaya raimin wayo ba. Tashimin a hanya ko nabi ta kanki”.

    Matsawa ta ɗanyi ya raɓata zai wuce. Ganin da gaske tafiyar zaiyi tace “Audiga zan sayo”. Cak ya tsaya daga yunƙurin barin wajen, kamar wanda akaima tilas ya juyo yana kallonta. Sai dai ita nata kan a ƙasa sai faman ɓata fuska take dayin muy-muy da baki alamar akwai abinda take son faɗa koma take faɗar a zuciyarta. Harga ALLAH abinda ya fahimta zatai da audigan da ban. Dan haka ya dalla mata harara.

       “Duk audigan dake cikin First aid box's ɗin gidannan kirasa audigan amfani sai kin fita saya? Bar nan kona mareki, mu nan ba'a mana fitan dare”. Kukane kawai ya rage bata saki ba. Har tayi niyyar yin zuciya sai kuma ta tuna halin da take ciki da wanda zata iya tsintar kanta kafin anjima kaɗan. “Yaya Please zanyi amfani da shine ALLAH”. Ransane ya ɓaci, ya ƙaraso inda take a fusace kamar zai kai mata mari ta zabura gefe. “Ina miki magana kina faɗamin zakiyi amfani da shine”. Ganin ya ƙaraso kanta ta zabura da gudu sai sashen Mom. Baiyi niyyar binta ba, sai dai kawai zuciyarsa ta kitsa masa ya amshe atm ɗin hanunta shiyyasa yabi bayanta. A falo ya sameta tana kumbure-kumbure Mom da su Salim zagaye da ita ana tanbayarta lafiya? Dan babu wanda yasan tama fita.

         “Wai bazakiyi magana bane Anam ana tambayarki kinyi shiru?”.

     Shigowarsa ta hanata bama Mom amsa, duk suka maida hankalinsu garesa yaran na gaishesa. Amsawa yay idonsa a kanta. Batare da yayi magana ba ya miƙa mata hanun fuska a tsuke. Ta fahimci mi yake nufi ta bashi dan haka ta zabura zata gudu. 

     “Kika tashi a wajen nan sai kinyi kukan da baki taɓa yin irinsa ba bani”.

     Mom ta kalla idanunta cike da ƙwalla. Mom data kasa fahimtar inda suka dosa tace, “Babana miya faru ne?”.

    A taƙaice ya faɗama Mom abinda ya faru. Cikin mamaki Mom ɗin ta kalleta dan tasan dai Anam da tsoron dare, itada da dare yayi ko'a cikin gidan akace taje wani sashin aika saita nema ƴan rakiyya. “Anam”. Mom tai kiran sunanta. Ɗagowa tai ta dubeta sai kuma ta maida kanta ƙasa.

     “Ina zakije?”.

   A hankali tace, “Audiga zan siyo”.

Ɗan jim Mom ɗin tayi na nazari. Sai kuma ta girgiza kanta “Yanzu Anam har sai kin tafi siyen audiga basai ki tambayeni ba, idan ma babu ai za'a bada a sayo miki. Amma ko fitama bansan kinyi ba”.

    “Kiyi haƙuri Mom naje naga kina salla”.

    Girgiza kai kawai mom tayi, ta maida kallonta ga Shareff, “Ƙyale shashancin wannan Babana, nasan yanda zatai maka bayanin ne yay mata nauyi”.

     Janye idanunsa yay daga harar Anam ɗin, komai bai sake cewa ba ya fice. Binsa tai da kallo tana taɓe baki, sai dai shi baima san tanai ba.


                     ★★★★★★


   Kamar yanda Daddy ya faɗa game da matso da auren Shareff ɗin hakane ta kasance. Dan shirye-shirye aka cigaba da yi babu kama hannun yaro. Dama ankai komai gidan su Fadwa, sai gidansa daya rage a ƙarasama ayyuka wanda dama kamfaninsa keyin ginin shi kuma ya zana kayansa da kansa. Sosai yay busy a tsakanin, Anam ma wataran sai Ya Khaleel take bi ya sauketa ya kuma ɗakkota. Tana dai shan masifa idan ta makara. Ita dai yitake kamarma batasan hidimar da akeba a gidan, ko anko da aka fitar nata cewa tai bataso ita batason kayan zafin nan sai da Mom ta mata faɗa sosai randa zasuje wajen tela sannan ta yarda tabi su Aysha tanata kumbure-kumbure.


       ★Yau data kasance alhamis daya rage 1week bikin Shareff ƙarfe sha biyu ta baro wajen aiki sakamakon mura da take fama da shi. Dama cikin dauriya ta fita aikin har Khaleel na mata faɗa. Zazzaɓi daya rufeta ya hanata sukuni ga ciwon kai, Yaseer ne ya samu shugabansu yay complain aka bata damar zuwa gida. Karan farko data yarda ta shiga motarsa, dan tayi ƙoƙarin zame masa amma ya ɓata rai. Maimakon ma gida sai ya fara nufar asibiti da ita, taso masa magana ciwon da kanta keyi yasata hakura ta zuba masa ido kawai.

    Basu wani samun tangarɗar ganin doctor ɗin ba, kasancewar akwai sanayya tsakaninsa da Yaseer ɗin. Da ɗan mamaki Dr Jamal ke duban Anam ɗin, daga ƙarshe dai ya kasa daurewa ya jeho mata tambaya. “Anam baki ganeniba ko?.”

       Ɗagowa tai daga kwanciyar datai akan desk nasa ta ɗan dubesa, sai kuma ta maida kanta ta kwantar tana ɗan girgiza masa kai. Shiru yay yana kallonta na wasu daƙiƙu kafin ya cigaba da rubuta musu maganain ya bama Yaseer da tun tambayar da yayma Anam ɗin ya shiga tunani. “Babu wani damuwa Yaseer murane kawai kuje a sai waɗannan drugs ɗin tasha insha ALLAH fiver da headache ɗin zai sauka”.

   Godiya Yaseer yay masa da basa hannu sukai musabaha. Ya bisu da kallo lokacin da suke fita kansa a matuƙar ɗaure. Jiyay bazai iya haƙuriba ya ɗauka wayarsa domin lalubo abokinsa dan tabbatarwa. A kiran farko dai ba'a ɗaga ba, duk da yasan daliline ya hana hakan sai ya kasa daurewa ya sake kira....

      “Ai harna fara tunanin bazaka ɗaukaba nai tracing naka ninazo inda kake”.

      Daga can aka amsa da “Saikace wani ɓarawo”.

    Dariya Dr Jamal yay dakai hannu ya shafi gemunsa. “My Man ai baka da maraba da ɓarawon da ake nema ruwa a jallo yau a wajena. Dan nasan bazan iya haƙuriba”.

        “Ai dama koda yaushe kai ba haƙurinne da kai ba. Miya faru?”.

     “Muje a hakan bani da haƙurin. Wai dama mutuniyar ta shigo Nigeria amma ko labari?”.

            “Malam jeka kai tsaye kan maganarka waye mituniyar? Dan na kula kai baka gajiya da kwashe-kwashe”.

    “Oh ALLAH shaidar da kai min kenan? To Anam nake nufi. Dan yanzu suka bar wajena ita da wani yaro Yaseer ya kawota a dubata”.

          Ɗiff yayi kamar wanda ruwa ya cinye har Dr Jamal na tunanin kota yankene, wayar ya cire a kunnensa ya kalla, ganin yana online ɗin dai ya shiga faɗin “Hello! hello! Bakajina ne?”. 

     Ɗin! Ɗinn! kiran ya yanke, bai wani kawo komai a ransa ba ya ajiye wayar da tabbacin bayaji ɗinne, shawarar daya yanke a zuciyarsa na anjima zaije har gida kawai ya sashi ƙin sake kira.


           ★★

   

     “To Alhmdllhi, indai banyi kuskure ba nan shine gidan”. Yaseer ya faɗa yana duban Anam da tunda suka baro asibiti ta kwantar da kanta jikin sit ta lumshe ido. Shiru bata motsa ba, yaɗan leƙa fuskarta yana murmushi da ɗan bubbuga gefen kujerar. Idanun ta buɗe a hankali ta kallesa. Kamar yanda yake mata murmushi itama saita ɗan sakar masa mai kama da yaƙe....

      “Nan ne ko?”.

Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa da narke mata idanusa. Janye nata tai daga garesa a ɗan daburce ta kalli gate ɗin. “Nan ne, na gode sosai ALLAH ya bada ladan zuminci”. Murmushi ya mata kawai ya buɗe ya fita. Side ɗinta ya zagayo itama ya buɗe mata. “Thanks”. Ta faɗa a hankali da ziro ƙafarta ƙasa zata fito idonta ya sauka akan Shareff da shima fitowarsa kenan daga gida hanunsa riƙe da key ɗin motarsa dake anan waje fake, ita sam bama ta lura da motar ba sai yanzu daya danna key tai ƙara. Ganin yanda ya kafeta da idanunsa ya sata yin ƙasa da nata ta ƙarasa fitowa gabanta na faɗuwa. Ɗan baya tai kamar zata faɗi saboda jiri Yaseer yay azamar kai hannu zai riƙota, dafe motar tai da sauri ta tsaya da ƙafafunta. “Ayya sorry Friend”. Yaseer ya faɗa a hankali yana janye hanunsa da bai kai ga taɓata ba.

     Ɗan satar kallon inda Shareff yake tai, yanzun kam zaune yake cikin motar sai dai ƙafafunsa a waje yana danna waya tamkar bai san da wanzuwarsu a wajen ba.....

     “Wancan ba Yaya bane?”.

Yaseer ya katseta yana fuskantar inda Shareff yake. Kanta kawai ta jinjina masa. “A to bara naje mu gaisa ko?”. Nanma batace komai ba, ganin ya nufi inda Shareff ɗin yake ita kuma gashi kwanciya kawai take buƙata, ga hararar daya mata sai kawai tai shigewarta gida...

         Shiru gidan babu gittawar kowa. Ta nufi sashen Mom da tunanin ko barci suke. Nan ɗinma shiru har ɗakin Mom ta leƙa bata samu kowaba, kitchen ta nufa inda take ɗan jin motsi. Iyami kawai ce tana ƙoƙarin ɗaura girkin rana. Gaisawa sukai kafin ta tambayi su Mom da hausarta da Iyami bawani fahimta take da ƙyau ba. Iyami ta bata amsa da cewar dukansu sun fita harsu Gwaggo amma batasan ina suka tafi ba. Fitowa tai ta shige ɗaki ta kwanta, ko mintuna biyu bata cika ba aka buɗe ƙofar, a tunaninta Iyami ce, sai dai kuma ƙamshin turaren da taji ya sata buɗe idanunta da sauri...

       Ido suka haɗa tai saurin janye nata ta maida ta rufe.

   “Tashi”.

  Sake buɗe idanun tai kamar zatai kuka, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasata kasa musa masa ta tashi zaunen. Hanyar ƙofa ya nuna mata. Saita waro idanunta da suka canja launi na mura ga ƙwalla a cikinsu. 

    “Banda lafiya fa Yaya. Ina zanje?”.

   Ganin ya nufota ta miƙe da sauri hawaye na sakko mata saman kumatu. A falo ta kusa faɗuwa saboda jirin dake ɗibarta, a bazata taji tattausan hanunsa cikin nata. Gaba ɗayansu sai da tsigar jikinsu ta tashi, sai dai babu wanda yay yunƙurin cirewa musamman ita dake buƙatar taimako dama. A haka suka fito har waje, ya taimaka mata da kansa ta shiga mota sannan ya zagaya nasa mazaunin, tana sonyin magana tana jin shakka dan haka tai shiru, saima ta kwanta abinta jikin sit ta lumshe idanu..

       Wani clinic ya kaita dan a dubata. Data sanar masa sunfaje asibiti wata muguwar harara daya wulla mata bata sake magana ba. Doctor ya rubuta musu magani fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsu da faɗin, “To amarya ALLAH ya ƙara afuwa kafin biki”.

     Idanu taɗan waro da kallon Shareff da shima kallonta yake, zatai magana ya harareta yana miƙama doctor hannu. “Thanks you doctor”. 

     “No babu damuwa ango ALLAH ya ƙara lafiya sai ranar ɗaurin aure kuma”.

      Shareff ya saki murmushi yana jinjina masa kai. Yanzu kam bama ta jira sun jera ba tai gaba da sauri, koda ya fito harta buɗe mota ta shiga abinta. Sai da suka baro anguwar gaba ɗaya ya tsaya a wani babban pharmacy ya sayi magungunan da aka rubuta, ya kuma shiga gidan abincin dake gefen pharmacy ɗin yay mata takeaway. Duk batasan hidimar da yake ba saboda tunda suka baro asibitin barci ya ɗauketa, dan haka batasan inda suka dosa ba har sai da suka iso. Gefen kujerar yaɗan bubbuga, a hankali ta buɗe idanunta, ganin har ya fita ta yunƙura ta tashi, fitowa tai tana dube-duben inda suke “Yaya MM ina ne kuma nan?”. Bai tanka mataba, ya rufe inda ta fita yay gaba abinsa. Ƙara bin gidan tai da kallo, dagani dai sabone dan duk ma ga botikan fenti nan a tsakar gidan da kayan aiki, gabanta ya shiga faɗuwa, cikin zuciyarta take tambayar kanta (ina kuma ya kawota nan?).....

       “Idan kika bari na dawo nan ALLAH sai kinyi kuka”.  

    Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafa ta nufi inda yake, koda ya buɗe ƙofar da key matsa mata yay ta fara shiga, ƙamshin sabon fenti dana sabbin furnitures ya daki hancinta. Sosai falon yay mata matuƙar ƙyau, danma ciwon kai ya hanata damar kallon komai da ƙyau. Ganin tana neman kaiwa kwance ya dakatar da ita. “No tashi kici abinci kisha magani first”.

       “Yaya banajin yunwa kadai ban maganin kawai”.

     “Dole kici abinci, kin taɓa ganin ansha magani ba'aci abinci ba”.

Yanda yay maganar babu wasa yasata yin shiru. Ya buɗe mata abincin tare da tura mata gabanta, “Kafin na fito ki tabbatar kinci”. Da kallo kawai ta bisa harya shige ƙofar daya buɗe..... Kusan mintuna goma sai gashi ya fito, ganin ya canja kaya yasa ta kasa haƙuri. “Yaya Shareff ina ne nan?”.

      Batare daya kalleta ba yakai zaune cikin kujera da faɗin, “Gidan ƴan shan jini”. Shiru tai, dan tasan baƙar magana ya mata. Ɗagowa yay yaɗan kalli abincin, ganin taci sai baice komaiba yaja ledan magungunan. Da kansa ya ɓalla ya bata, duk ta amsa tasha dan sam bata tsoron allura bare ƙin magani. Ganin zata kwanta a kujerar ya sashi faɗin, “Tashi kije ciki ki kwanta”. Kallonsa tai kamar zatai magana sai kuma ta haɗiye abunta ganin yanda kicin-kicin da fuska. Ya bita da kallo ta ƙasan ido harta shige, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido ya buɗe yana furzar da ɗan huci. Sai kuma ya miƙe ya fita. 

      Gidan ya shiga zagayawa, dan jiya masu fenti suka ƙarasa na katanga. Bai kuma samu shigowaba sai yanzu. Komai yayi masa yanda yake buƙata, shi kansa ya yaba da gidan duk da shine ya zana abinsa companynsa kuma ya fidda kayan aikin ginashi. Yanzu amarya kawai gida yake buƙata nanda kwanaki bakwai insha ALLAH. Motarsa ya nufa ya ɗauka lap-top ya koma ciki. Haka kawai yake jin nishaɗin zama a cikin gidan yau, saɓanin ƴan kwanakin nan da duk yake jin ransa a dagule, dan kayan sashen nasa ma sai da Mommy ta masa jan ido ya bada damar shirya masa su dan ita da kanta tai order ɗin komai tamkar itace mai aurar da macen ba namiji ba. Komai saida ta haɗa masa. Tunda kuma aka shirya kayan baizo ya zauna kamar haka ba......

    Ring da wayarsa tai ya sashi katse aikin da yake famanyi a laptop ɗin ya ɗaga. A tausashe yace, “Mommy barka da rana”. Daga can Mommy ta amsa masa da “Barka dai son kana ina ne?”. Ɗan jimm yayi kafin yace “Mommy kina son ganina ne?”. 

      “Eh to kusan haka, amma idan zaka iya aika wani gidanka ya kai mana keys ma basai kazo ba. Dan gamu a hanya zamuje dasu gwaggo gidan, sannan Halima tai kirana ma danginmu na wajen baban Fadwa zasuzo da masu Company da zasu shirya kayanta su auna komai, shiyyasa muka yanke shawarar muzo muma ɗin kawai dan babu daɗi dangin uba kawai ko?”.

        Tun fara maganar tata zuciyarsa ke faman bugu da sauri, ya ture laptop ɗin cinyar tasa gefe, cikin dauriya da danne halin daya shiga yace, “Okay Mommy! kuna inane yanzu haka?”.

       “Ai gamu ma mun shigo street ɗin gidan naka kamar dai in ban mantaba”.

     Goshinsa ya dafe yana ambaton “Ya ALLAH a hankali”. 

         “Mi kace?”.

  “No Mommy, canai ALLAH ya kawoku lafiya ai inama gidan nima na shigo ganin aiki daga nan na ɗan huta”.

     “Kaji ja'iri, bama ka bari iyayen naka su kaika ganɗoki muje biki”.

    Ƴar dariyar yaƙe kawai ya mata da faɗin, “Sai kun iso”.


        Da sassarfa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Ya duba Anam dake barci hankalinta kwance harda naɗewa cikin lallausan duvet nashi dako shi bai taɓa lulluɓa da shi ba. Nufarta yay yakai hannu kamar zai tadata sai kuma ya fasa, ya ɗan furzar da huci tare da dafe goshinsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya tabbatar su Mommy suka ganta ya shiga uku, dan baima san kalar ƙurar da zata iya tashi a family ɗin MD Shareff ba yau. Jin horn ya sashi sake ambaton “Ya ALLAH”. Tare da fita a ɗakin domin buɗe musu tunda babu maigadi har yanzu sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu yake saran Fharhan zai kawo shi.....


         Tunda ya buɗe musu gate bakin Mommy da Gwaggo ya sake washewa. Suma dai su Mom fuskarsu da murmushin jin daɗin ganin yanda ɗansu ya gina wannan gida dako maƙiyi ya gani zai yaba ko'a zuciyane. 

      “Kai-kai! Anya kuwa Alhaji ƙarami bazan dawo nan ba irin wannan gida haka?”.

    Gwaggo ta faɗa tana riƙe haɓa dabin ko'ina da kallo. Murmushi yay mata da shafa kansa. “Indai bazaki dinga damuna da kwakwazonki ba sai na dawo dake”. Dariya su Mom sukasa, yayinda Gwaggo tai masa daƙuwa. Nanma murmushi yayi kawai. Da kansa yay musu jagora suka shiga ko'ina suna mai yabawa da masa addu'a, bakin Gwaggo da baya iya yin shiru tace, “Toni abinda ban ganeba anan, Alhaji ƙarami yanaga sashe biyu, gidan kamar na zaman mace fiye da ɗaya! Kar dai kacemin kaima halin Kakanka da ubanka zakai tara mata?”.

      Ganin duk su Mom sun juyo suna kallonsa, har fuskar Mommy ta sauya ya sashi ɗan hararar Gwaggo ta ƙasan ido. “Kai tsohuwarnan kedai bakinki bai iya shiru, kawai dan mutum yayi wadataccen waje a gidansa sai yazam na aure? Nayine saboda ke in kinzo kwaɗayin jar miya”.

        Dariya su Aunty Amarya suka sanya. Mommy ma ta ɗan saki fuska tana murmushi dan tun farkon fara ginin gidan da tazo ta gani ta masa irin wannan maganar ganin sashe biyu da nasa na uku, amma sai yace yayine kawai saboda baƙi. Haka kawai zuciyarta taƙi aminta da shi taita masa bin.....

       “To shikenan muje ka kaimu naka sashen muga namai gida”.

   Gwaggo ta katse mata tunani. Gabansane ya faɗi, zaiyi magana Gwaggo ta nufi ƙofar sashen da basu shiganba wanda tabbacin nasan ne, itama Mommy saita take mata baya. Hakan yasa dole su Mom ma binsu. Da ƙarfi ya rumtse hanunsa da cije lip ɗinsa. Ganin har Gwaggo ta shige yay saurin bin bayansu shima dan ya tabbata target ɗinta na biyu shine bedroom ɗinsa. Kamar yanda yay hasashen kuwa hakane. Dan ko falo bama tagama nutsuwa ta ganiba ta nufi ƙofar bedroom acewarta da nan zata fara a sashen. Shigowarsa tayi dai-dai da ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar.............✍


    *_🙆🏻Yau munga idi wagga tsohuwa babu man kai zata ɓaro aiki. Dangin Anam kuna ruwa, maganin masu bin mazan mutane kenan🚶🏻😂🤭_*

     


_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*.      *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_09_*.........Murmushi Fadwa ta sakar masa, cikin narke murya taima hannunta kiss da hura masa .

      “I miss you my Soulmate”. 

   Kansa kawai ya jinjina da wani ɗan guntun murmushinsa iya laɓɓa. Cikin iyayi da feleƙe ƙawayen nata ke gaishesa idanunsu kamar zasu faɗo a kallonsa. Ɗan tsuke fuska yay yana amsa musu sama-sama. 

        “Baby am sorry na saka wahala”.

Fadwa ta sake faɗa tana sake narke masa har tana saka tsigar jikinsa tashi. Nanma murmushi kawai yay mata da kauda kansa daga gareta dan shi kaɗai yasan halin da dama yake ciki ita kuma tana son sake kunnashi da wani. Cikin motar yay ƙoƙarin komawa da nufin ɗakko mata saƙonta, ita kuma batare da tunanin tare yake da kowaba ta nufi ɗayan side ɗin a zatonta anan ya ajiye saƙon nata ne, tana kuma son ƙara birge ƙawayenta da akaikaice tasa ake musu hoto acan gefe batare daya sani ba....

        Sosai Anam ta cika tayi fam da takaici, tayi yunƙurin buɗe motar ta fita taji ya sakata a lock dan yasan dama abinda zata iyayi kenan tace zata fita kamar wancan ranar. Ya ɗakko ledar dake a back sit ɗin Fadwa ta buɗe ita kuma. Ido huɗu sukai da Anam, ta watsa mata wani kallon banza ta ɗauke kai dajan siririn tsaki da faɗin “Ballagaza” a hankali....

        A yau kam tayi laƙawarin bazata ƙyale ƴar iskar yarinyar nan ba. Cikin jin ɗacin (ballagaza) data kirata dashi tace, “Kin yima ubanki dan uwarki.”

    Duk da Anam bajin hausa take da ƙyau ba tasan zagi, amma sai tayi kamarma bataji Fadwa ɗin ba, taciro Bluetooth daga bag ɗinta ta fara ƙoƙarin maƙalawa a kunne Fadwa ta buge hanun Bluetooth ɗin ya faɗi ƙasa. Ƙafa tasa ta takesa da shegen takalminta mai tsananin tsini......

       “Fadwa!”.

    Shareff ya faɗa a ɗan kausashe.....

“......Amma dai Soulmate kanajin tsakin da taimin ai, ranar na ƙyaleta daboda darajarka, amma yau gaskiya bazan iyaba, ban son raini..!”

    Itama ta faɗa da sauri cikin tarar numfashinsa. 

          Anam data sake cika tai fam tai yunƙurin hanɓarata baya ta futa. (Yo dama a gayama kura gayyar cin nama bayan bidirin nasu ne🤣. Ba'a takali Anam ba ma yaya aka ƙare balle anzo har gida da goron gayyata😂).

      “Idan kika fita a motarnan sai ranki ya ɓaci!!”. Yay maganar a tsawace da fisgota ya maida ya zaunar. Kuka ta fashe masa da shi dan zuciyarta tazo wuya. Baibi takantaba yay yunƙurin fita a motar sai ya hango Fadwa can ta nufi motarta a fusace ƙawayenta na take mata baya. Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma ya furzar da huci mai zafi yaja murfin a fusace ya rufe, na side ɗinta ma shine ya rufosa ya tada motar suka bar wajen dan tuni su Fadwa ma sun fice a wajen har tana bulama mutane ƙura.


         Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi yaja birki da ƙarfi, firgita tai ta ɗago da sauri tana kallonsa. Harara ya watsa mata tare da gangarawa gefen titi ya kashe motar. “Nidai ka kaini gida, kuma saina sanarma Daddy mata na maka kiss a titi da rungumek....”

     Bamm ya bige bakin nata, kukan ƙarya ta sake fashe masa da shi dan ko hawaye babu yanzu sai dai taji zafi sosai. “Har Abba ma saina faɗawa da Abie da Mamie da Mom da aunty Amarya”. Ta sake faɗa da ɓalle murfin motar zata fice. Riƙota yay ya maida murfin ya rufe yasa lock. Takaicinsa da haushin abinda Fadwa ta masa yasa takejin zafinsa batare data san dalili ba, cizo tai ƙoƙarin kaima hanunsa dake riƙe da nata....

       “What!! Ni zaki ciza?”.

   Bata kulashi ba ta sake kaima hanun cizo. Babu shiri tilas ya saketa, yana mai girgiza kansa. A hankali yakai kwance jikin kujera bayan ya kwantar da ita, hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa ya lumshe idanu yana mata kallon ƙasan ido. Tunba yanzuba yasan Anam fitinanniya ce dama, sai dai yayi zaton tabar tsiwa zuwa yanzu, amma tun tana ƴar ƙaramarta boss ce daman. Yasha zuwa hutu ya samu an kawo ƙarar Anam daga school ta naɗi ƴaƴan mutane babu dalili, idan kuma gidansu akazo nanma ta jibga, idan gidansu taje yaran ba tsira sukeba. Ƴaƴan aunty Mimi ba ƙaranar wahalar Anam sukaci ba duk da wasu sun girmeta bata ɗaga musu ƙafa........

       “Nidai ka buɗemin, bazan sake shiga wannan motar ba da akeyin wannan abun....”

      Duk yanda yaso danne murmushin dake son fita ya gaza hakan, gefe ya maida kansa yay murmushin kafin ya tashi zaune sosai fuska a haɗe ya riƙo hanunta dake jikin handle ɗin ƙofar, baki ta buɗe zata saƙi ƙara dan matse hanun yayi yasa yatsunsa biyu ya riƙe lips ɗin nata fuskarsa a tsananin haɗe. Sosai idanunta suka sake firfitowa, ga tsoro ga tsiwa......

       “Haɗiyemin wannan kukan, ki kuma faɗi miye abunda akeyin kona tattakaki”.

    Tsaf ta haɗiye kukan zuciyarta na bugawa da sauri dan kusancinsu yayi matuƙar yawa, kanta ta fara jujjuya masa a hankali. Idanu ya zare mata da sakin lips ɗin nata, “Ai saikin faɗa mara kunya”. A tsorace take amma bakin yaƙi mutuwa. Taja jikinta baya da maƙurewa a jikin ƙofa, “To ka bari muje gaban su Daddy ɗin basai na faɗa ɗin ba....”

     Bakin ya sake kaima ɗalli tai saurin duƙewa da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Ƙwafa yay da komawa jikin kujerar ya lafe yana kallon waje,  kusan mintuna huɗu suna a haka ring ɗin wayarsa ya katse shirun nasu. Iska ya ɗan furzar da kallon wayar, ganin Daddy ya sashi ɗagawa yakai kunne a ladabce yay sallama. 

       “Shareff kuna ina?”.

  Ɗan jimm yay saboda jin muryar Daddyn, sai kuma ya gyara zama da ƙoƙarin yima motar key yana bashi amsa. “Daddy gamu a hanyar tahowa gida”.  “To inna jiranku”. Kafin ya sake cewa wani abu ƙitt an yanke wayar. Shiru yay yana kallon wayar sai kuma ya sake furzar da numfashi. Ruwa ya ɗauka a baya ya miƙama Anam da itama ta ɗago tun ɗaga wayarsa. “Malama anshi ki wanke wannan banzan hawayen”. Baki taɗan tura gaba kafin ta amsa, ta buɗe murfin motar batare data fita gaba ɗaya ba ta wanke fuskar. Bag ɗinta dake kan cinyarta ya ɗauka ya buɗe, zatai magana ya harareta. Komai babu na kayan kwalliya da ƴammata kan ɗan fita da shi a bag sai lipsgloss kawai. Baice komai ba ya maida jakar ya rufe, tissue ya ɗiba guda uku ya miƙa mata sannan ya harba motar saman titi. 

      Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu gida, tunda aka buɗe musu gate ya sake tabbatar da babu lafiya, dan ganin masu baƙaƙen kayan nan yasan Aunty Halima ce a gidan. A karon farko yaji zafin hakan matuƙa, shikenan da abu ya faru tsakaninsa da Fadwa sai iyaye sun shiga ciki, to shikam idan anyi auren yaya kenan kuma?. Ita dai Anam ba fahimtar komai tai ba, dan tun kan ma ya gama kashe motar tai ficewarta sashen Mom a zatonta ma ko baƙi Abba ko Daddy wani yayi. Binta yay da kallo harta shige, ya sauke numfashi a hankali shima yana fitowa. Sashen Daddy ya nufa duk da yasan bai wuce ɓacin rai zai tarar ba.

      Tun kafin ya ƙaraso yake jin hargowar Gwaggo Halima daketa masifa, ya girgiza kansa kawai ya shiga falon da sallama. Da Fadwa dake faman rusar kuka suka haɗa ido, ya ɗauke idanunsa fuskarsa na sake tsukewa. Sosai Mommy ke antaya masa uwar harara, hakama Gwaggo. Daddy dai kallonsa kawai yakeyi cike da nazari. Shiko Abba murmushine ma akan fuskarsa yana sauraren ƴar uwar tasu kuma yayarsa. Ƙasa ya zauna ya shiga gaishesu. Abba ne kawai ya amsa da daɗin rai, sai Daddy daya sauke ajiyar zuciya. Mommy kam da Gwaggo hayayyaƙo masa sukai da masifa kamar yanda Gwaggo Halimar ta rufesa da tata. Shi dai babu wanda yacema uffan a cikinsu, kansa a ƙasa ma yake. Sai da sukai mai isarsu sukai shiru duk da Abbah nata son dakatar da su sunƙi saurarensa.

        “Ina ita mara kunyar dan ubanta? Kai yanzu Shareff ko kishinmu ma bakayi duk yawan ƴan uwanka da muka haifa karasa wadda zakai yawo da ita a motarka sai bare.....”

        Haka kawai maganar ta bashi dariya, amma sai baiyiba yay murmushi kawai da ɗagowa ya ɗan dubi Gwaggon tasa datai maganar. 

    “Eh kalleni da ƙyau mara mutunci, ko kanada wata alaƙa da ita bayan ubanta dake matsayin ɗan uba a cikinmu da har kake wulaƙantamin yarinya akanta?”.

          “Dan ALLAH ya isa haka Halima, maganar yarinya ko matsayinta duk bashi bane ya taramu anan. Kai Shareff miya haɗaka da ƴar uwarka?”. 

    Numfashi ya sauke a hankali da ɗagowa ya dubi Abbah da yay maganar ya sake sunkuyar da kansa. “Abbah ni bansan wani abu ya faruba. Ina office ta kirani tana buƙatar abu, duk da ina buƙatar zuwa na huta kuma tana ƙasa dani na ɗauka nakai mata har inda take badan ina jin tsoronta ba.......”

     “Amma daka tashi zuwa ai da wancan bakwainin yarinyar kazo. Dama ranar da ita kaje gidanmu taimin rashin kunya da marina ka hana na ɗauki mataki kace zaka ɗauka da kanka, yau kuma harda zagina tayi tanamun kallon banza irin like akwai wani abu tsakaninku. Ni gara idan sonta kake ka faɗamin na barmata kai kawai dan bazan iya shearing ɗinka da wancan jakar ba....”

       Idanunsa yay bala'in rumtsewa tare da dunƙule hanunsa da masifar ƙarfi. Daddy dake kallon hanun nasa ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, sai dai kamar yanda tun ɗazun baice komaiba yanzunma baice ba. Fadwa ta cigaba da sakin zance tana kuka har sai da Abbah ya ƙwaɓeta dan sai zagin Abie take da Anam....

      “You're vary stupid. Baki san shi ɗin wanene ba a gareki? Ashe muma zaki iya zaginmu mara kunyar banza......”

     A zabure gwaggo ta tare numfashinsa da faɗin, “Yo Abubakar wane matsayi Usman kedashi a wajenku bayan ɗan uba da zaka balbaleta danta zagesa?”.

        “Haba Gwaggo wane irin magana ne wannan?”. Abba ya katseta ransa a ɓace. Gwaggo Halima zatai magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Bana sonji, daga yau kuma idan na sakeji a cikin ƴaƴanki wani ya zagi Usman to lallai ke kanki sai ranki ya ɓaci tunda akoda yaushe ke hankali baya isa miki cikin jiki. Wannan magana kuma na kasheta anan, sannan Mamana nine nace kullum Al-Mustapha ya sauketa a wajeb aikinta ya kuma ɗakkota tunda shine babba wataran sunan uba zai amsa a garesu. Bana son sake jin ƙananun maganganun nan daga yau, nakuma dawo da bikinsu baya zanje na samu Alhaji Sadiq ɗin, magana ya ƙare ok”.

       Babu wanda ya iya sake cewa komai, sai dai har cikin rai maganarsa ta farko ta zafi wasu a cikinsu, ta ƙarshe kuma ta musu daɗi kusan su duka idan ka cire uban gayya daya shaƙa yay fam. A wannan gaɓar yaji mugun haushin Gwaggo a ransa fiye da koyaushe, dan ya gama gane itace ke assasa tsanar juna a tsakanin iyayensu da ƴan uwansu guda biyu kacal dan kawai suna matsayin ba uwarsu ɗaya ba. Shi ya fara ficewa a falon batare da ko kallon wani ya sakeyi ba.

     Da sauri Fadwa ta mike tabi bayansa har tanayin tuntuɓe zata faɗi. Tana kiransa ko waugota baiyiba duk da sarai yajita. Duk da taji zafi haka ta cigaba da binsa har part ɗinsu, yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tai azamar shan gabansa ta tare ƙofar. Mugun kallo ya watsa mata, sosai hanjin cikinta suka kaɗa amma saita daure ta marairaice masa fuska.

      “Haba My Soulmate yanzu ɗinma wulaƙancin zakamin?”.

          “Bani hanya!!”.

    Yanda yay maganar a tsawace idanunsa har suna firfitowa yasata saurin matsawa. Hannu yasa ya ƙarasa ingijeta ya buɗe ɗakinsa ya shige tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ta sake zabura....


     Acan falo kuwa Daddy ne yay amfani da damar fitar su Shareff ya shiga yimusu nasiha musamman Gwaggo da Gwaggo Halima da Mommy da duk matsalar take daga garesu. Duk da a cikin lalama da son bada shawara yay maganar sai Gwaggo ta fashe da kuka tana matsar ido da fyatar majina wai ta fahimci laifinta suke gani dan bata haifesuba. “Shikenan Muhammadu nadai fahimci laifina kake gani, nidai ALLAH na gani ba inayi bane dan na rabaku da su kamar yanda kuke kallo sai dan kare martabarku da takaicin da uwarsu ta shaƙa mana a gidannan wajen mahaifinku. Babu annamimanci da kutungula da Zuwairah bataiba agaremu, akwai randa har sakinmu tasa mahaifinku yay a daren duk da ana ruwa yace mubar masa gidansa. Akwai randa ta ɗau hanun Halima ta turɓuɗa cikin murhu wuta naci wai dan ta zungurar mata icce. Kai har kusan jefa mahaifiyarku tai a rijiya lokacin tana goye da Umaru. Taya azzalumar mace irin wannan zanso ƴaƴanta kuma na baku goyon bayan kusota duk da abinda taima ƴar uwata. Ai shara'armu da Zuwairah sai dai a lahira, gashinan makirar jikarta ta gadota a komai na makirci. Dan haka bazaku taɓa samun nutsuwaba a gidannan tunda annamimiya tazo jinin munafukai.....” Fyaaaatttt. Ta face majina da ƙarfi da nufar hanyar ƙofa ta fita. 

     Mommy ma tashi tai a fusace tabi bayan Gwaggon tata. Cikin ɓacin Rai Gwaggo Halima ta dubi su Daddy. “Yaya kaji ko, duk da abinda uwarsa taima tamu uwar amma kuke nuna sonsa kamar.....”

      “Halima!!”.

Daddy yay saurin dakatar da ita shima ransa a bace. “Amma Yaya itafa gaskiya ɗayace daga ƙinta sai ɓata. Wlhy wlhy kaji na rantse bazan taɓa son su Usman ba a gidannan. Har duniya ta tashi sunansu ƴan ubane a gareni, bawai ƴan uwa ba”. Fuuu ta figi jakarta ta fice. Duk da kallo suka bita. Abbah ya fara sauke ajiyar zuciya da maido kallonsa ga Daddy da ransa ke matuƙar ƙuna. Ya rasa mizai fassara Gwaggo da shi. Tun basu san kansu ba take ƙulla raba kansu, ALLAH gafurun kuma rahimun ya ganar dasu gaskiya hakan taƙi yuwuwa, amma bata barsun ba har saida haƙanta ya cimma ruwa. Sukazo babu dalili suka tsani ƴan uwansu da basu taɓa masu komaiba su da mahaifiyarsu sai alkairi, ALLAH ya ƙara taimakonsu suka gane suka canja. Gashi yanzu tana son saka ƙiyayya kuma a tsakanin ƴaƴansu, wace irin fitinace wannan, kenan itama data haihu a gidan basu isa su jitu da nata ƴaƴanba......”

           Taɓashin da Abba yayne ya maidosa hankalinsa. Ya sauke numfashi a hankali da ɗago idanunsa irin na Shareff da sukai jajur yana kallon ɗan uwan nasa. Cikin ɗacin murya yace, “Abubakar itace silar komai. Duk wata ƙiyayya tsakanin Umma da Mama itace taita haɗata. Bata barsu sun zauna lafiya ba muma ta hanamu gashi zata hana ƴaƴanmu ma. Yanzu ƴar ɗaya tilo da ALLAH ya bama Usman ma bazata barta tasha iskar farin ciki a cikin namu ƴaƴan ba. Kana ganin Maryamu ta daina zuwa da ƴaƴanta ƙasar nan saboda Gwaggo. Haka kuma zamu cigaba da zuba idanu kenan Abubakar?!”.

      “Bazai yuwu ba yaya. Dolene a wannan karon mu ɗauki mataki. Yaya Halima tafi kowa bani haushi. Sam ta kasa fahimtar halin Gwaggo tamkar ita ɗin ba mace bace ba. A zatona da ake cewa mata sunfi kowa zuminci ita ya kamata ta fara farga da son ganin mun dunƙule abu ɗaya amma da ita ake makamin rusamu. Bazan ɓoye makaba ina tausayin Shareff akan wannan auren. Bazasu barsa ya zauna lafiyaba dan itama yarinyar nan da kake gani shaiɗaniyar kantace Yaya”.

     Sosai zuciyar Daddy ke ƙara tafasa dan yasan duk gaskiya ɗan uwan nasa ya faɗa. Shi kansa yana tausayama Shareff dan yana cikin kwatankwacin irin halin da suke neman jefasane akan mommy. Tunda ya aureta Gwaggo ta hanasu su zauna lafiya saboda kawai tana taƙama ɗiyar ƴar uwartace......


    ★★


Tunda ya shiga ɗakin bai sake fitowaba. Kwance kawai yake a gado ko takalmi bai cireba balle maganar wanka har aka kira magrib. Tashi yay ya nufi bayi yayo wankan a gurguje da alwala. Tsabar bai buƙatar haɗuwa da kowa ta baya yabi ya fita massallaci. Bai kuma dawo ba dan koda akai sallar isha'i can ya koma kan wani dakalin maƙwaftansu ya zauna.....

        

      Tunda suka dawo gidan batabi takan kowaba. Tadai shiga ta gaida Mom sannan ta wuce ɗakinsu. Wanka tayi batare data ko shafa mai ba balle saka kaya ta kwanta da towel ɗin jikinta dan wani irin barci ke rinjayar idanunta kasancewar sanyin ruwan wankan dana jiƙar towel ɗin na ratsata. Barci sosai mai nauyi ya kwasheta, acikin barcin taji kamar abu na binta. A ɗan zabure ta farka ta hau dube-dube. Ganin jini ya sakata zaro idanu da dafe goshi. Shaf ta manta da batun zuwansa duk da sai jibi ya kamata ta gansa ma. Gadon ta ɗan dudduba, ganin bai ɓaciba ta nufi toilet da sauri, towel ɗin dai ya ɓaci kasancewarsa sky blue ya nuna sosai. Tasan yana mata zuba sosai shiyyasa bata wasa, gashi tanata son siyen audiga dama amma shiririta tasata mantawa dan ta saba sai da taga Mamie ta ajiye mata da lokacin yinsa yayi gareta. A gurguje ta gyara jikinta ta fito, baƙar abaya kawai tasa ta ɗauka atm ɗinta tayo waje. Ɗakin Mom ta leƙa ta samu tana salla, bazata iya jiraba dan akwai matsala zai iya sake ɓatata. Yanzunma handkerchief ɗinta sabo tai amfani da shi kafin. A falo ma duk sauran yaran sun fita massalaci kasancewar duk yaran Mom mazane aunty Rahma ce kawai mace, Husna ɗiyar ƙanwartace take riƙo bayan auren Rahama.

        Su Daddy sun riga har sun shigo ciki, hakan yasa bata samu matsalar isa gate ɗin ba duk da batasan a ina zata samo audiga ɗin ba, kawai zatai dai tambaya ko gurin mai shagon layinne da sukan siyo ƙananan abubuwa wajensa koza'a samu kokuma ya faɗa mata inda zata samo....

       Cak ta tsaya tare da saurin ja da baya saboda karo da sukaci, sosai gabanta ya faɗi, ta zabura da zummar komawa da baya tana kauda kai dan har yanzu haushinsa takeji akan abinda ya faru, Juyawa tai da sauri.....

      “Idan kika ƙara stap ɗaya saina karya ƙafafunki”.

           “Wayyo Anam kin mutu kawai”.

Ta faɗa tana rumtse ido da cije lip ɗinta kamar zata fasa ihu. Sai kuma ta juyo tana wani tamke fuska batare data yarda ta sake kallonsa ba, ita ala dole bata son yaga lagonta..........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_11_*.......Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.

      A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya saka aljihu sannan yabi bayansu...

        

       Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan karon.

     Ko'ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma'aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba'aiba ya tsolema kowa ido.

    Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa. 

      “Soulmate!”.

Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.

      Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa da buɗewa a lokaci guda.....

          “Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama'a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.

      Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.

       Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.

      “Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi'ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.

           “To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma'auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.

    “Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.

     “Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet Please”.

     Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.

           Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a jikina”.

      Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.

           “Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.

    “Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.

       Addu'arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa. 


     Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa.... Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a jikinta....

        “you are vary stupid!!”.

Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne. 

     “Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka.......

    “Shut up! Stupid!”. 

Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.

      Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.

        A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.

      

     ★★★★


   Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan ɓuya da Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta shirya tabi bus ɗin su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta faɗama kowa abinda ya faru ba, sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa aiki ta daina samun number ɗinsa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu'amula a wajen aikin nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata. A yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani abu ya samesa ai.

        Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya ɗauke mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za'aje tarbo iyayenta airport sai dai batasan waye zaije ɗakkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman jiransu a gida. Aiko ƙarfe huɗu da rabi na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal abokinsa ɗauke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta harda kukan daɗi su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk wannan kaikawo da ihun yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin ɗansu. Hasalima duk wani ɗawainiyar biki Abie da Mami suka ɗauka. Acewarsu Shareff ɗansu ne, sune suka cancanci yimasa aure ba kowa ba. Hatta lefe da duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu nuna sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma dan uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra'ayin ayi bikin nan da ita, duk da kuwa katanga ɗayace tasan wasuma zasu shigo gidansu a ƴan bikin, amma dai ko yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun gara bane ta faɗa gidan zago😚.


          ★★★


    Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da taren ƙawayenta wayayyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da amaryar ta tara ɗunbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin celebrities da akeji dasu. Amarya tasha ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba'ai mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.


      ★★★


    Bayan sallar isha'i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah ɗiyar Aunty Mimi dake kusan sa'anni dasu Anam ɗin tana can itama za'ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da ta langaɓe wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan ɗin ma faɗa Mom tai mata akan batun ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni huɗu bata cikaba da gama murnar isowar su Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe idan ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta ɗin can ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.

       Washe gari wajen sha biyu yaran gidan kowa da ƙunshi abin sha'awa amma banda Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka shirya suka fita hausa day itako tace bazataje ba. Sai faman baƙin rai takeyi na babu gaira babu sabar. Mamie dai tunda taimata tambaya ɗaya tace bakomai bata sakebi takanta ba. Sai aunty Mimi ce ke faman lallaɓata da lallashinta. Sai tace kawai ita bata da lafiya ne.

       A wannan lokacin Shareff dake gidan batare da Anam ta sani ba ya shigo. Gabantane yay masifar faɗuwa. Ta miƙe zaram da nufin guduwa aunty Mimi ta dakatar da ita cewar ta kawo masa breakfast ɗinsa dake kitchen wanda Mamie dakanta da girka abinta kuma irin abincin ƙasar Malaysia ne. Jitai kamar ta fashe da kuka dan takaici, koda ta kawo ta ajiye masa ƙoƙarin juya tai zata bar wajen ya watsa mata mugun kallo saboda ido da suka haɗa by mistake. Baki ta murguɗa masa itama ta haura sama da gudu.

      “Kai kaji shasha lafiyarki kuwa Mamana?”. Aunty Mimi da bata lura da abinda ya faru ba ta faɗa da mamaki tana kallon hanyar da Anam ɗin tabi. “Babana wai kaga mi yarinyarnan tayi kuwa? Sai kace mai tsoron wani anan?”. Murmushi kawai yay baice komaiba. Ta hararesa. “Kaifa tsiyarka kenan ai magana ka bama mutum amsa da murmushi”.

     “Oh ALLAH small Mom rigima. Ni yanzu mikike so nace anan kuma? Ina ruwana da shirmenta”.

         Hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kai. Yay dariya da shafa kansa yana buɗe kwanikan. Ƙamshin ya sashi lumshe ido murmushinsa na ƙara faɗaɗa. “Lallai na shaida Mamie na kusa dani”. 

     Dariya aunty Mimi ta sanya masa da faɗin, “Makwaɗaicin banza”. Dariyar yayi shima da faɗin “Naji ɗin”. Haka ya fara cin abincin cike da nishaɗi suna hirarsu har Mamie ma ta fito daga sashen Abie ta samesu. Zama tai itama suka ɗora, daka gansu kasan akwai shaƙuwa mai faɗi a tsakaninsa tun ba yanzu ba. Anam na jiyo dariyarsu daga sama taƙi sakkowa har saida ya wuce massalaci sallar azhur. Aunty Mimi kuma ta fita zuwa can cikin gida ita da Mamie.

     Ta idar da salla tana shirin sakkowa ƙasa ta samu abinda zataci suka kusa cin karo da Fawwaz. 

    “A'a autan Mom daga ina haka da gudu?”.

         “Yaya ne yace na kiraki”.

Kafin tace da shi wane yaya ya kwasa da gudu ya fice. Ta girgiza kai tana murmushi. Ɗaki ta koma ta ɗauka abaya kasancewar kayan jikinta wando da rigane marasa nauyi. Duk zatonta Khaleel yake nufi, shiyyasa ta fito hankalinta kwance. Harta nufi gate ɗin shiga cikin gida motar dake fake a tsakanin gidansu da cikin gida tai mata horn. Kamar bazata juyaba sai kuma ta dubi motar ganin an sakeyi alamar da ita ake, tunanin ko Yah Khaleel ɗin ne a ciki ya sata nufar can duk da tasan ba motarsa bace, bama tasan motar ba dan kamar ma sabuwa.

       “Tofa, wai su Yah Khaleel sabuwar mota akayine halan?”. Tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi tana shafa motar har side ɗin mazaunin driver. Kanta tsaye ta buɗe murfin. Duk abinda take dama idonsa a kanta, kuma yana jinta dan ya ɗanyi ƙasa da glass kaɗan. Da sauri ta saki murfin tana ambaton ALLAH tamkar wadda taga wani shaiɗan ko aljani. Ɗaga kafa tai da nufin juyawa ya dakatar da ita.

      “Idan kika bar wajen nan sai na mareki”.

   Tsayawar tayi, sai dai taƙi ta juyo. Hasali ma auna yanda zata arta da gudu takeyi.....

            “Zagaya ki shiga”

     Ta tsinkayi muryarsa a dake. Shiɗin ba abun wasanta bane, musamman a yanda yay maganar babu alamar wasa a cikinta. Ta haɗiye ƙwallar da suka taru mata a ido cikin cije lip tabi umarninsa. Sanyin ac da kamshi na musamman suka ratsata a cikin sabuwar motar da ko leda ba'a cirema kujerunta ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da lafewa cikin kujerar ranta fal tunanin ina zai kaita? Bata da mai bata amsa dan haka taja bakinta ta tsuke ta zubama sarautar UBANGIJI idanu..........✍


     

_🤣Tofa, su Shareffudden ango ko'an fara kidnapping ne bamu sani ba😣, to magana ta gaskiya ƴan team ɗinsa ku faɗa mana gaskiya mu fara rigakafin killace kammu kar'a sakamu a ruɗani😂😆?.__ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: ..........A karon farko ta ɗago ta kallesa da mamaki ganin inda yay parking. Magana take so tayi, sai dai ta kasa. Shi kuma yaƙi cemata komai, sai ma wayarsa daya ɗauka yay ƴan danne-danne yakai kunensa. “Fito”. Kawai ya faɗa ya yanke wayar. Ba'a rufe minti uku ba wata budurwa mai tsananin iyayi ta fito daga shagon saloon ɗin tana tafiya kamar tarwaɗa. Haka kawai abin nata ya bama Anam haushi, taja siririn tsaki da taɓe fuska ta janye idonta. Duk da tayine a hankali sai da yaji, sai dai bai nuna yajinba balle ya tanka, sai ma faman daƙilar waya yake, amma ya buɗe murfin kafarsa ɗaya a waje take.

      “Assalamu alaikum Yah Musty barka da zuwa”. Budurwar ta faɗa murya a lanƙwashe lokacin da take isowa wajen. Kansa kawai ya jinjina mata yana janye kunne ɗaya na earpiece dake a kunnensa. Kamarma bata damu da abinda yay matan ba. Murya ta ƙara tausasawa cike da iyayi tace, “To Bismillah muje ko”.

       Nan ɗinma bai tankaba, sai da yaja wasu sakanni ma sannan yay yunƙurin fita a motar.

    Baƙin ciki, haushi da takaicin ballagazanci na wasu mata ya tokare maƙoshin Anam. Lokaci ɗaya taji tama tsani budurwar. 

         “Sai an fito da ke ne?”.

Ya faɗa cike da gatse idonsa akan Anam. Jitai kamar karta fita ɗin, amma sai yaci darajar Yaya da yake gareta tabi umarninsa. Yanda budurwar batai mata magana ba itama bata nuna tama san da zamanta a wajen ba. Gaba sukai tana binsu a baya, budurwar sai ƙoƙarin dai-daita tafiyarta take da shi tamkar dole, ga baki ta saki sai surutu kai kace hanyar kasuwar wanbai aka buɗe da safe. Sosai wajen Saloon ɗin ya haɗu dan yaɗan birge Anam kaɗan, sai dai bata nuna a fuskaba saima kicin-kicin data sakeyi da fuska duk da gaisuwa da ma'aikatan wajen ke musu na girmamawa daya bata mamaki matuƙa. Wajen zama aka basu, harda ajiye musu abinsha kafin budurwar da taji ma'aikatan sun kira da aunty Deena ta dubesa cike da yauƙi da shauƙi.

          “Sir za'a mata kitso ne?”.

    Bai jita ba, saboda earpiece dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne ɗaya, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska. “Am sorry, nayi magana ne bakaji ba, nace za'a mata kitsone?”. Idonsa ya ɗauke daga gareta ya maida ga Anam datai kicin-kicin da fuska fiye da yanda suka shigo dan ta fahimci ita ya kawo kenan. “Komai ma daya dace kumata”. Ya faɗa a taƙaice da maida earpiece ɗinsa.

        “Ni wlhy bance inaso ba. Kuma kaina a wanke yake, hakama......” Hararta yay yana mai zare kunne ɗaya na earpiece ɗin, tai saurin sake haɗiye maganar tana matso hawaye. Ɗauke idonsa yay kamar baima ganta ba. Tanaji tana gani aka kwance mata kalbar kanta aka saka mata relaxer aka wanke fes. Bayan an rage ruwan da towel akai steaming ɗinsa. Wadda take mata gyaran tambayarta tai tana son kitso ne? Amma tai mata banza. Ganin haka ta juya ga Shareff dake zaune komai anayi gaban idonsa.

      “Sir za'a mata kitson ne ko a barta?”.

        “Barta kawai a mata lalli”.

Yay maganar batare da ya kalleta ba yana maida earpiece ɗin kunensa. 

       Ana fara wanke mata ƙafa da gyaran farcen hanunta ya miƙe ya fita, Anam ta bisa da harara ƙasa-ƙasa tana tura baki. Cikin ƙunƙunai tace, “Gwarama da zakai aure mu huta da baƙin halinka”.

    Murmushi mai mata wankin ƙafa tai saboda jin abinda tace. Lokacin da aka fara zana mata lalle harda ɗaukar video, dan tana son lalli sosai kitsone dai kam saida dambe da Mamie tsaye kanta, dan ko Mamie ce tace zata mata ba yarda take ba da arziƙi. Abie kam lallaɓata yake ko yace a barta sai wani lokaci tunda bata so. 

       Sosai ta fito ras tai ƙyau tamkar wata sabuwar amarya. Sai faman kallon kanta take a manyan mirrors na wajen tana murmushi da ɗaukar hoto kamar ba'itace ta gama rikiciba yanzun. Sai da tai mai isarta sannan ta fito waje kamar yanda Deena ta tabbatar mata Yaya Shareff na nan na jiranta a waje. “Okay”. kawai tace mata tai ficewarta. Deena da yaranta suka bita da kallo baki taɓe. Fuska ta haɗe tamau tana cika baki da iska lokacin da take fitowa, ta buɗe motar ta shiga tana wani kauda kai taƙi kallon inda yake.

        A jiyar zuciya ya sauke a hankali yana ɗagowa daga kwanciyar da yay jikin kujerar, murmushin daya tsaya iya laɓɓansa ya ɗan saki ganin yanda taketa faman kauda kai gefe wai ita a dole haushi take da shi. Hanunsa ya kai ya zame veil ɗin, tai saurin riƙewa tana tura baki. Kallon daya wulla mata ya sata sakin masa babu shiri, sai da ya gama ƙarema gashin kallo cikin ɗan lumshe ido da buɗewa ya maida mata ya rufe. Sosai gashin nata yasha gyara sai ƙamshi mai daɗi da ƙyalli yake.


      Koda suka iso a gate yay parking, tana fita yaja motar yay gaba abinsa. Da harara ta raka motar, sai kuma ta kalli hanunta da ƙafa da sukasha lalli tai murmushi. Gidansu tai shigewarta. Dan cikin gida tun daga waje kana iya jiyo hayaniyar daya sake ɗauka alamar baƙi sun ƙaru kenan. Gidan nasu ma cike ta sameshi da baƙin da suka iso bayan fitarta. Sai su Aysha dake shirin komawa gidansu amarya bayan magrib Arabian night. Tambayarta wanda yay mata ƙunshi suka shigayi kowa na yaba ƙyan da yayi. A takaice tace musu Yayane ya kaita wani waje kawai. Koda suka buƙaci jin wane Yaya a ciki bata amsa musu ba tama shige toilet dan son watsa ruwa kasancewar gab ake da kiran sallar magrib saboda sun jima a wajen ƙunshin nan ba laifi, gashi ko sallar la'asar batayi ba.     

      Ana idar da sallar magrib ƴammatan gidan suka sake ficewa wajen event na arabian da aka shirya amma banda Anam yanzu ma. Dan kwanciyarta taima tana kallo a lap-top hankali kwance kamar bata san bikin da akeyi ba. Har magana Amrah tai mata amma tace karta dameta. Yanda tai maganar cikin masifa yasa kowa bai sake magana ba sukai shirinsu suka fice.


          ★★★★★


Washe gari kam gida ya sake cika danƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi na nesa dana kusa. Abokan Yah Shareff na Nigeria da wajenta duk wanda ya iso anan ake saukarsa gidansu Anam a sashen Shareff ɗin da tuni Abie ya ware dominsa duk da ba zama yake ba a hanunsu yanzun. Duk hidimar da ake Anam na ɗaki batako fitowa sai yunwa ta isheta. Bamai ganin ko fara'arta. Mamie tayi faɗan harta watsar da lamarinta, hakama Aysha fushi take da ita dan ita bataga mi Anam ɗin kema fushe-fushen ba tunda babu wanda ya mata wani abu ai. Aima gaba ɗaya ta tsame kanta daga shagalin bikin tamkar Shareff ba ɗan uwanta ba. Da yamma kusan rabin jama'ar gidan suka wuce gidansu Fadwa amarya kamu amma nanma Anam bataje ba. Kai barci ma suka wuce suka barta tana sha hankali kwance. Koda suka dawo kuma su Aysha nata labarin yanda kamu ya kasance da ƙayatarwa Anam sai tai tsaki tama fice a ɗakin gaba ɗaya. Da kallon mamaki duk suka bita, sai dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da al'amarin nata tunda ansanta da miskilanci da kuma tsanar da sukaima juna ita da ƴan gidan su Fadwa batun yanzu ba.


        *_WASHE GARI* ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa, duk da ba'ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya koma tamkar a hanunsu ne.

      Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa'ointa ma na family ɗin sunata zuwa nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.

     Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin yabawa.

     Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu tafi masallaci”.

      Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi  tace, “ALLAH yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa'a, kuma yasa abokiyar arziƙinka ce har a aljannah”.

    Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa, hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye. 

    Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.

      Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”. Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.

      Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.

   Dariya tayi da faɗin, “A'a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a ɗaura a sa'a.” 

     “Humm” 

kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan Humm ɗin bata magani Yarona”.

       Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan da suka rage na take masa baya.........✍🏻

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_13_*..........Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka, Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya kaimu za'a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya fara shirin tafiya dinner.

     Bayan sallar isha'i aka fara kwasar mutane inda za'a gudanar da dinner, sai dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa. Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a barta ta shana😜). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama'a aka dawo gida.


    WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma, dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai bayan sallar azhar. Anayin la'asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau. Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba...

       Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran abokan ango.....


      ★★


  “Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka kanata jamana aji”. 

        Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay yana harararsa da miƙa hannu, Isma'il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima yana dariya. “ALLAH baza'a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”

       Isma'il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu ragowa”.

      Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu. Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom.  


       Jin gidan ya rage hayaniya sosai ta sakko downstairs. Su Mamie ne kawai zaune da ƙannenta, gaishesu tai kowa na tambayarta ya ƙarfin jikinta. Tace da sauƙi tana zama gefen Mamie ta kwantar da kanta a kafaɗarta. Ko mintuna uku batai da zama ba suka shigo da sallama. Shine a gaba cikin ɗanyar shadda milk color sai ƙyalli take harda hula a kansa. Sai su Fharhan biye da shi. Jitai kusan su dukansu idanunsu akanta suke kamar ta tashi ta arta da gudu, sai dai ta dake dan bata fatan sake tafka abin kunyar datai a ranar ɗaurin aure😝. 

       Sai da suka gama gaisawa da su Mamie Dr Jamil dake jin kamar ya haɗiyeta fuska ɗauke da murmushi yace, “A'a Anam banda ke a kai amaryar kenan?”.

      Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi batare data kallesu ba. “Banda lafiya ne shiyyasa”. Ta faɗa a hankaki tana ƙara sinne kanta jikin Mamie. 

          “Ayya ai ban sani ba dana kawo ɗauki. Yaya jikin yanzun?”.

  “Na samu sauƙi”. Ta faɗa a taƙaice tana ɗan ɗagowa. Cikin idonsa natan suka shige, tai saurin janyewa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi....

      “My son kuje kar dare yayi an bar ɗiyata ita kaɗai, ALLAH yay muku albarka, ya bada zaman lafiya na har abada. Ayi haƙuri ayi haƙuri ayi haƙuri. Mu mata a duk inda muke haƙuri ake damu akan komai dan halittane masu wahalar sha'ani. Banda yanke hukunci cikin fushi, duk abinda aka gani ba dai-dai ba abu asannu a ruwan sanyi a kawo maslaha a cikinsa. Ayi ƙokurin sauke duk hakkin da ALLAH yace duk da bani da damuwa a kanka game da wannan. ALLAH ya azurtaku da zuri'a masu albarka”.

      Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Anam dai ma ta maida hankalinta ga wayarta kamar bata jinsu. Ƴan uwan Mamie ma sun masa tasu nasihar suka sallamesu dan dare na ƙarayi. Dai-dai yana mikewa suka ƙara haɗa ido da Anam data ɗago itama. Wani kasalallen kallo suka sakarma juna. Ta kauda kanta tana taɓe baki zuciyarta na mata zafi. Shima iska ya ɗan furzar yana janye nasa a wani yanayi. Bata sake yarda ta ɗago ba har suka fice Dr Jamal na faɗa mata sai yazo dubiya ta musamman. Bata tankasa ba, sai Aunty Nasara dake kamar ƙanwar Mamie ta bashi amsa cikin dariya.

      Tsam ta mike tabar falon dan ji take wani ɗan zazzaɓi ma na neman rufeta, ta nufi ɗakinta da fatan su Aysha su kwana a cikin gida yau bata bukatar su anan......


*_MONDAY MORNING_* 


          Tana tsaka da barcinta na safe mai daɗi kasancewar bata samu yin na dare ba sosai saboda zazzaɓi mai zafi data sake kwana da shi aunty Mimi ta tasheta akan ta tashi ta shirya za'a aiketa. 

      “Wayyo aunty ina su Aysha ki aika a kira miki su suna cikin gida fa ALLAH bana jin daɗi”.

         Hararta Aunty Mimi tayi. “Ai nasan dasu Ayshan na tasheki. Maza tashi kina ɓatamin lokaci. Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi kamar zatai kuka. Wanka tai da ruwa mai ɗumi dan duk son sanyinta kuma bata wanka da ruwan sanyi. Gudun masifar aunty Mimi ya sata shiryawa a ɗan gurguje cikin shigar da tafi so a ko yaushe wando da riga ta ɗaura abaya pink a sama ta naɗa veil ɗin abayar. Tayi ƙyau sosai sai zuba kamshi take duk da bawani kwalliya tai mai yawa ba. A falon ƙasa ta sameta har su Mamie wanda suka makara nata breakfast. Gaishe dasu tai tana karasawa inda Aunty Mimi take.

      “Yauwa ɗiyar albarka. Ai jeki kawai waje ga Ikram can na jiranki a mota da driver ”.

    “To aunty saƙon fa?”.

“Yana wajensu a motar”.

Kai kawai ta jinjina taima su Mamie sallama ta fita. Baya ta buɗe ta shiga yayinda Ikram ke gaba tanata zubama driver surutu da hausanta da bata iyaba wai ita a dole koyan hausa takeyi. Itace autar aunty Mimi shekararta goma sha uku, kasancewarta girman turai sai take abu kamar wata yarinya ƙarama ga tabara ta autoci. 

      “Good morning aunty Anam”.

Ta faɗa lokacin da Anam ke ƙoƙarin rufe murfi. “Morning dear how are you?”.

    “Am fine, sai ƙafana dake ciwo saboda rawan da mukai a wajen dinner ranar”.

         “Good for you”.

“Kai aunty maimakon kimin sorry”.

    “Tunda ni na aike ki”.

Dariya Ikram tayi. Sai kuma ta shiga bata labarin yanda shagalin dinner ya kasance. Shiru Anam tai mata, da taga zata isheta sai ta buɗe bag ta ɗakko bluetooth ta saka waƙa har suka iso gidan da bazata taɓa iya mantawa ba. Kasa motsi tai balle magana har driver yay horn maigadi ya buɗe masa gate suka shige. Jitai kanta na juyawa, ta dafesa tana ambaton sunan ALLAH. Da tasan nan aunty Mimi zata aikosu da duk ma yanda zatai taƙi zuwa ALLAH da sai tayi. Yanzu kuma tana ƙin shiga wannan akku sarkin zancen zataje ta bazata a fassarata a mai baƙin ciki. Siririn tsaki taja da buɗe motar a fusace ta fita dan Ikram tuni ta fice har driver ya buɗe mata booth suna fidda kayan breakfast da sukazo da shi. Ƙin daukar komai tai sai driver da ikram ɗinne suka kwasa.

        Daga can baya ta tsaya Ikram ta shiga yin knocking tana kiran sunan Yaya Shareff. Sun kai kusan mintuna goma sha  sannan aka buɗe har ta gama yanke shawarar juyawa ta koma. Shine ya buɗe ƙofar Ikram ta riƙo hanunsa cike da shagwaɓa. (Wayyo Yaya ƙafafuna har zafi suke da hannuna”.

      Kanta ya dafa da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya tashi yana buɗewa. Ya matsa mata alamar ta shigo yana maida dubansa ga Anam datai tsaye tana kallon wani waje daban. Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yay magana. 

    “Tsaiwar ta miye?”.

  Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufosa. Harta ƙaraso idonsa na kanta yanzu ma. Ya ɗan matsa mata alamar ta shiga itama. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janyewa da raɓashi ta shige tana murguɗa baki. Shine ya shiga da kayan cikin falon da kansa, Ikram sai faman yaba falon take dan babu ƙarya naira tayi kuka. Itako tana tsaye tamaƙi zama, ta dai jingina da bango tana daƙilar wayarta.

    “Ina kwana”.

Ta faɗa batare data yarda ta kallesa ba. Bai amsata ba, sai hankalinsa daya maida ga Ikram da bakinta yaƙi shiru. Haushi ya ƙara kume zuciyarta, gashi ta fara gajiya da tsaiwar, amma sai ta cigaba da daurewa. Kusan mintuna biyar yana biyema shirmen Ikram tamkar ma ya manta da ita a falon. Ƙaton agogon dake bangon falon ya duba, tare da dawo da kallonsa gareta.

      “Bani plate a kitchen”.

   Kallonsa tai da mamaki, sai kuma ta sake ɓata fuska. “Ni ban san kitchen ɗin ba”. Da hannu ya nuna mata ya ɗauke kansa. Kitchen ɗin ta nufa wani haushi na ƙara turniketa, cikin taɓe baki take bin ko'ina na kitchen ɗin da kallo. Tabbas yayi ƙyau, sai dai hakan ba yana nufin wani abu na cikinsa ya burgeta ba. Abinda ya aikota ta nufa ta ɗauka, sai dai ta nufi sink dan ta ɗauraye, sai ƙunƙuni takeyi da bazaka iya sanin mitake faɗa ba. Juyowa tai tana jan tsaki, da sauri taja baya har plate ɗin na neman suɓuce mata. Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba, ga idanunsa masu kaifi daya kafeta da su. A hankali ya tako gabanta duk hannayensa cikin aljihun jallabiyar jikinsa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin numfashinsa. Sai taji gaba ɗaya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi a wadace...

      “Ya jikin ki?”.

   Yay maganar cikin taushin muryar da bata taɓa ji daga garesa ba. Kasa jurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa. Har yanzu idanunsa a kanta suke, tai saurin janye nata tana girgiza kanta. Muryarta da ɗan rawa tace, “Alhamdulillahi”.

      “Kin tabbatar?”.

   “Nifa zazzaɓi ne dama kawai Yaya MM”.

       Jin baice komaiba ta ɗago ta dubesa, still dai har yanzu idonsa a kanta. (Ya ALLAH! lafiyarsa kuwa?) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin son barin wajen. Amma sai furucinsa ya sakata dakatawa babu shiri.

          “I'm sorry”.

    Kasa yarda tayi daga bakinsa furucin ya fito, musamman da babu alamar shi ɗin ya faɗa a yanayinsa. Sannan bata san dalilinsa na faɗarba. Kamar ya fahimci ƙarin bayani take buƙata sai ya bar wajen cike da basarwa. “Zoki dafamin lipton”. Shiru bata motsa ba, da alama bata tare da tunaninta ma. Ya juyo ya dubeta fuska a tsuke. “Badake nake magana ba!”. Itama fuska ta haɗe, sai dai cikin sanyin murya tace, “Yaya matarka fa?”.  Ido ya tsura mata na wasu sakanni, sai kuma ya janye. “Nasan da ita ai na sakaki. Sannan ganin amarya a kicin irin wannan ranar kema kin san bamai yuwuwa bane”.

      Da hausa yay maganar, dan haka ba komai ta fahimta da ƙyau ba. Amma sunan amarya kawai daya shigo ciki ya saka yanayinta ƙara canjawa. Sai dai bata sake cewa komai ba, ta ɗauka tunkuyar daya fiddo mata domin dafa shayin ta ɗauraye, ruwa ta zuba dai-dai shan mutum ɗaya, tana ƙoƙarin rufewa taji tsaiwarsa a bayanta, kafin tayi wani yunƙuri ya janye hanunta da sake buɗe murfin ya buɗe fanfo ya ƙara ruwan. 

      “Nadai bazan dafama wata ƙatuwa shayi tana kwance tana barci ba”.

  Karon farko ya saki murmushi, sai dai komai baice ba ya rufe mata tukunyar. Zata sake magana ya dakatar da ita. “Zakimin abinda na saki ko tsiwa? Trouble maker!”.

      “Ga babbar Trouble maker can ka bari a ɗaki”. Tai maganar ƙasa-ƙasa yanda bazaiji ba. Da kansa ya kunna mata gas ɗin, ta ɗaura tukunyar sannan ta ɗiba kayan ƙamshi da lipton da duk ya fiddo da kansa ta zuba. Flask daya fiddo a kwali shima ta ɗauka ta ɗauraye tare da kofi duk yana tsaye yana kallonta. Baiyi mamakin yanda take komai a tsaftace da kuma tsari ba, dan sai dai ya bama wani labarin Mamie badai a bashi ba, yasan kuma hakan duk tarbiyyar data samune daga gareta. Yana kitchen ɗin harta kammala komai, ya sake ɗaukar kofuna uku ya ɗauraye da kansa ya haɗa da wanda ta wanke. Bata tanka masa ba, ta ɗauka flask ɗin kawai ta fita. Shine ya ɗauka sauran kayan ya fito da su, samunta yay tanama Ikram masifa akan ta tashi su wuce gida, ashe da wayarsa ya haɗata shi ya tafi neman magana kitchen..

      “Sai kun karya, tunda tace bakuyi breakfast ba kuka fito”.

    Ranƙwashi takaima Ikram ɗin, amma sai ta kauce tana dariya da faɗin, “Wlhy Yaya ita a barci ma aka tasota gara ni nasha tea”. Wani ranƙwashin zata sake kaimata ya zuba mata hararar data sata dakatawa, sai dai tayi gefe da kanta tana ƙunƙuni. 

       “Oya zauna ki haɗamin yunwa nakeji”. Ya faɗa yana ajiye ledar dake ɗauke da kayan tea da abokansa suka rako shi da su a daren jiya tare da kaza. Batai magana ba, shima kuma bai sake maganar ba ya nufi ƙofar fita yasa key sannan ya wuce kitchen. Harara ta dinga zubama Ikram tana haɗa tea ɗin, tsabar mugunta ta zabga masa sugar. Ikram ta mikama nata tana faɗin, “Makwaɗaiciya kawai, daga zuwa gidan mutane”.

     Ikram tace, “Ni banyi kwaɗayiba tunda gidan Yaya ne”. Fitowarsa ta hanata bama Ikram ɗin amsa, ya dire babban plate dake ɗauke da kaza sai turiri take alamar ɗumamata yay. Zata miƙe yace, “Koma ki zauna.” babu wasa a lamarinsa dole tabi umarni, sai dai idonta harya fara tara ƙwallar takaici. Hanyar corridor ɗin da take ƙyautata zaton bedrooms ne ya nufa, cikin jin haushin da babu dalili ta raka bayansa da harara. Wayarta ta ɗauka ta cigaba da daƙila, kusan mintuna uku sai gashi ya fito, zama yay a ƙasan carpet ɗin shima kamar yanda take zaune. Yace, “Bani tea”.

    Batai magana ba, ta ɗauka flask ta zuba masa ruwan zafin akan kayan tea ɗin data haɗa a kofin. Sai da ta juya ta tabbatar sugar ɗin ya haɗe sannan ta miƙa masa. Duk da yaga bata haɗa nata ba sai baice komai ba yaja nasan gabansa da ƙyau, kaɗan ya ɗiba a cokali yakai baki dan yaji yaya test ɗin. “Ya ALLAH!”. Ya ambata da sauri. Tasan tsiyar da tai dan haka taƙi ɗagowa. “Kina hankalinki ƙuwa zaki saka min wannan sugarn?”.

     “Toni Yaya nasan yanda kake so ne?”.

   Idanu ya zuba mata kawai tsahon wasu sakanni. “Idan ma mugunta ce harda kanki zaki mawa, ba wadda take cikin gidan kawai ba, dan duk dodo ɗaya zaku yima tsafi”. Komai bata fahimta a zancensa ba. Wani kofin ya ɗauka ya raba shayin biyu, ya ƙara kayan tea ɗin banda sugar ya sake zuba ruwan zafi. Ikram dake ta faman latsa waya tana shan nata tea ɗin yace ta sakko. 

     Duk yanda Anam ta so nuna ta ƙoshi bai saurareta ba. Haka ya tilasta mata karyawa tare da shi da breakfast ɗin da suka kawo da kazar daya ɗumama. Sai dai ita taƙi cin kazar ko sau ɗaya. Ikram kam komai sai da taji yakai mata sannan tai hamdala. Tayi niyyar suna gamawa su wuce, amma sai taga babu dacewar barin kwanikan, ita ta kwashe komai zuwa kitchen, ta ɗauraye kwanikan da suka ɓata. Koda ta fito bata samesa a falon ba, tacema Ikram ta tashi su wuce gida.

       “Lah aunty Anam Yaya yace mu jirashi zai fito muje tare”.

     Harara ta zuba mata, “Shi kuma driver daya kawomu fa yake zaman jiranmu?”. 

      Fitowarsa ta hana Ikram bada amsa. babu abinda ya canja a jikinsa sai key ɗin mota daya ɗakko, ta ɗauke kanta gefe harya ƙaraso ya amsa wayarsa a hanun Ikram. Suna gaba tana binsu a baya har wajen mota, bataga driver ba, ba kuma ta tambaya ba. Ganin Ikram ta shige baya itama tai yunƙurin shiga....

        “Waye driver ɗinku?”.

   Fuska ta tsuke tana hararar Ikram kamar itace tai maganar. “Malama koma gaba”.

     “Ni dai aunty ki barni anan nafi son baya cikina ya cika da yawa zan kwanta”. A fusace ta ƙara yunƙirin yin magana ya dakatar da ita. “Bana son shirme fa kina ɓatamin lokaci nabar matata tana barci kowane lokaci zata iya tashi, ganina kusa da itane kuma abinda tafi buƙata a yanzun”.

      Tamkar saukar aradu haka furucinsa ya daki ƙirjin Anam saboda da yaren malay yay maganar yanda zata jisa ta fahimta da ƙyau. Idanunta ta rumtse ta buɗe motar ta shiga batare datace masa komai ba. Shima bai sake cewarba ya harbar motar zuwa waje dan maigadi dama ya wangale masa gate tuni........✍


    *_🚶🏻🤕😣askiya kuyima ƴar mitsilarnan taku kashedi ta fita sabargar angonmu.😚_*

     


_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_**_BABU SO.. 👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_17_*........Kasancewar Abie a wajen ya sashi ƙin cewa komai ya ɗauketa gaba ɗayanta ya haura sama aunty Mimi biye da shi. Ɗakin Mamie suka nufa kamar yanda Aunty mimi tace.

     Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfin gaske lokacin da yake ajiyeta akan gado, dan tunda ya ɗakkota ta ɗauke numfashinta da rumtse idanu zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shi ɗimma dake ƙoƙarin dannewar tashi zuciyar bugu take da gudu a ƙirjinsa har numfashinsa na seizing. Ajiyar zuciyar ya sauke tamkar ita, sai dai tasa ta fitane a ɓoye. Sallamar Mamie ta sashi haɗiye abinda ke masa kaikawo, tray ɗin hanunta ya amsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Mamie da kanki”.

      Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, ta harari Anam dake kwance lamo tana sauke ajiyar zuciya. “Mai rakin tsiya yanzu waye yaji daɗin? Nikam zanga yanda zaki ƙare lokacin rainon ciki balle ranar haihuwa, mijinki dai yaga takansa ai”.

     Dariya aunty Mimi ta sanya, yayinda Anam ke tura baki gaba, taɗan saci kallon Shareff sai ko idonta cikin nashi. Sosai ya sarƙeta da su, sai da ƙyar ta samu damar fisgewa tari mai alamar sarƙewar yawu na kufce mata. Wani irin yanayi data kasa bama fassara ta karanto a cikin ƙwayoyin idanunsa, hatta da tsigar jikinta yamutsawa ta shigayi, ga tarin yaƙi tsayawa har sai da Aunty Mimi ta tadata zaune tana bubbuga bayanta. Kamar ba shine sanadin komaiba cike da basarwa ya miƙama Aunty Mimi ruwan, a baki ta saka mata, sai da tasha sosai kafin tarin ya lafa idanunta har sunyi jajir. Sannu Mamie tai mata tana ƙoƙarin ficewa domin nuna kara garesu tunda dai duk suna ƙoƙarin nuna kulawa gareta bai kamata ita saita tsaya ba. 

     Yana daga tsaye har Aunty Mimi ta bata umarnin fara cin abinci bayan ta ɗaura mata tray ɗin akan cinyarta. A hankali ta fara cin abinci, sai ƙunƙuni take a zuciyarta na zamansa ɗakin. Oho bai san tanayi ba, dan babu alamar zai fita ɗin. Aunty Mimi ta miƙe ta fita saboda kiran mijinta daya shigo mata a waya. 

       Shiru ɗakin bakajin motsin komai sai na ƙarar spoon da take juyawa a plate, dan gaba ɗaya tama kasa cin abincin yanda ya kamata, tarasa mike damunta, kunyarsa ko haushinsa, dan abinda ya faru a gidanta ɗazun ya gagara barin zuciyarta. Jin shiru kamar baya ɗakin ya sata ɗan ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka sake haɗa ido. Kanta ta maida ga abincinta tana sake tsuke fuska.

     (Sai kallon tsiya) ta faɗa a ranta. Kamar yaji mitake faɗa ya zura wayarsa a aljihu yana ɗan jan siririn tsaki. “Baki iya komai ba sai kallon mutane laziness”. 

     Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa idanunta cike da tsiwa. “Toni da baka kalleniba zaka san ina kallonka ne.....”

       “What!”.

  Ya faɗa cikin ɗan kausasa murya da waro idanunsa kanta sosai. “K! Wai yaushe na zama abokin wasanki ne a gidan nan?”.

       Ƙin cewa komai tai, sai dai bakinta a sama kamar zai taɓo silin. A ranta ko addu'a take aunty Mimi ta dawo kafin ya fara zazzabga mata maruka. Ganin yana matsota tai saurin faɗin, “Amma matarka ɗazun datai iskanci agaban mutane baka hukuntata ba sai ni, kuma jinina da aka zubar sai na rama”. Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye dake nuna tabbacin abun na ranta kamar zanen dutse har yanzu suka shiga rige-rigen sakkowa. Cak ya tsaya yana kallonta, kuka take sosai kamar wadda aka doka, kusan tsahon minti guda da wasu sakanni ta gagara tsaidasu. A hankali ya rumtse idanunsa, tare da furzar da ƙaramin huci daga bakinsa. Shiru bashi da alamar cewa komai balle lallashinta, itako sai ƙara matso hawayen take wani baƙin ciki da takaicinsa na sake hasalata, tabbas da ace lafiyar ƙafarta ƙalau ɗakin zata bar masa....

       “K sau nawa ina hanaki tarayya da wannan yaron amma kika maidani sauna? Bayan shi ba muharraminki ba itako *Matata ce!*”.

     Karan farko da tunda ta fara kukan ta ɗago jajayen idanunta tana kallonsa cikin tsakkiyar ido. Shima kallon nata yake a tsakkiyar idon......

       Ita ta fara janyewa cikin ƙunƙuni tana faɗin, “Ni dai baza'a rabani da masoyina ba”.

     Sosai kalaman nata suka daki ƙirjinsa. Sai dai kafin yay wani yunƙuri aka dakatar da shi.

    “Mike faruwa anan?”.

   Aunty Mimi dake shigowa ta faɗa cikin dariya. Ita ta fara janye nata idanun, batare da tace komai ba ta zame ta kwanta. Shima numfashi ya ɗan fisga, cikin yanayi kamar mai borin kunya ya ɗaga kafaɗarsa. “Nothing Aunty. Zan wuce gidane goodnight”. Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa. Da kallo ta bisa har ya fice, kafin ta juyo ga Anam dake faman sauke ajiyar zuciya.

     Komai batace mataba, sai da ta tadata zaune ta bata abincin da kanta tare da magungunanta sannan ta fiskanceta da ƙyau. Kai tsaye tace, “Mamana kina son Shareff ko??!...”

        “God for bid Ummie”. 

  Ta faɗa cikin tarar numfashin Aunty Mimi da saurai.

    “Sure?”.

“Yes Ummie”.

Yanda ta bada amsar da ƙwarin gwiwa yasa Aunty Mimin haɗe fuska tana mata kallon sama da ƙasa. Cikin rashin wasa tace, “To *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”*.

        “Kishi kuma Aunty? A dalilin mi zanyi kishinsa?”.

     Ko amsa ɗaya Aunty mimi bata amsa mata ba, sai dai ta kafeta da ido ganin hawaye na ciko mata ido. cikin ɗan ɗage kafaɗa tace, “Okay fine kwanta kiyi barci”.

    Kwanciyar tayi, tana ta faman ALLAH ya kiyaye ta so wannan mutumin a zuciyarta, a fili dai bakinne kawai ke motsawa babu sautin fitar magana......


    ★★


   A hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga kiran Fadwa dake faman shigo masa waya babu ƙaƙƙautawa. Sai da tai wajen bakwai baida alamar ɗauka, ana takwas ɗinne ya fisgi wayar a fusace daga change daya sata yakai kunne. Sai dai baiyi magana ba dan inhar ransa ya ɓaci baya son ya ringa cewa komai....

      “My son!”.

Muryar aunty Mimi tazo masa a bazata. Da sauri ya cire wayar a kunensa ya kalla. Tabbas Aunty Mimi ɗince ba Fadwa ba. Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa. “Yes small Mom ko nayi mantuwa ne?”.

      “Da alama tunda ka tambaya ƙila kayo ɗin”. 

  Ƴar dariya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa. “Aunty kenan, da alama magana kike nema dai kawai”.

         “Kusan hakan, sai dai kai tsaye zan yita, kamar yanda nayi a ɗayan ɓangaren”.

      A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba. “To ina saurarenki mamana!”.

        “Babana kana son Anam ko?!”.

    Da ace ruwa yake sha ko cin abinci babu shakka sai ya ƙware dan abinda Small mom ɗin nasa ta faɗa yazo masa a baza. Ya haɗiyi yawu da sauri jin maƙoshinsa na ƙafewar danshi. Yay ƙoƙarin saisaita kansa kai tsaye yace ni da nai aure sati guda kuma”.

     “Ba labarin aurenka nake tambaya ba, dan nima ban manta lissafin ba. Ka bani amsata kawai”.

          Steering ya ɗan daka yana cije lips, cikin son kauda mata dukkan wani tunani babu ko gargadar murya ya bata amsa.

     “Aunty ni matata kawai nake so, bayan ita babu wata a raina”.

        Shiru Aunty Mimi tai, sai kuma ta saki murmushi mai sautin da har yaji, cikin dakewa tace “Sure?”.

     “Babu kokwanto a maganata Mom”.

“Okay fine. To amma *_BABU SO MIYA KAWO KISHI?!*”.

        “Kishi kuma?! Sai dai na zuminci”.

     Ƴar dariya aunty Mimi tai da faɗin, “Lallai kam”. Tana yanke wayar.

      Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yay baya luuu jikin sit ya kwanta, idanunsa da suka canja launi ya lumshe, tsahon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin shiga gidan. Ga kiran dake shigo masa waya da baya raba ɗayan biyu Fadwa ce amma ya kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan mintuna goma sha biyu har mai gadi ya gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan yay masa horn.

       Da ɗan gudunta ta fito, duk da ranta a ɓace yake saboda kiran da take jera masa yaƙi dagawa sai ta danne saboda shawarar su Sima da take hange mafita a gareta basai ta cigaba da tada jijiyar wuya a wajensa ba. Ta ɗanesa tare da maƙalƙalesa, ko kulada yanayinsa batai ba ta haɗe bakinsu. Ƙoƙarin janyeta yay yana kauda kansa kodan maigadi da yake da tabbacin zai iya hangosu amma ta hanashi damar hakan. Dole yay ta maza ya tura murfin motar da kafarsa ya ɗauketa gaba ɗayanta yay sasheta bayan ya raba bakinsu da ƙyar. A kujera ya zube da ita jikinsa, babu wani ɗaga kafa ta sake maida bakinta kan nasa. Baya buƙatar komai a halin yanzun, sai dai bazai iya ƙin bata hakkintaba koda ace faɗan doke-doke sukai indai ta nema zai biya mata, balle ma baya buƙatar haɗa wata matsala tasa ta waje da cisgunawa iyalinsa  wannan alƙawarine ya daukama kansa insha ALLAH, laifinta kuma zai mata hukunci a lokacin daya shirya. Duk da babu wani karsashi tare da shi ita ke kiɗanta tana rawarta bata damuba, sai da ta tabbatar ta isar da saƙon da take bukata sannan ta barsa tana mai kallonsa cikin ido cike da so da kaunarsa.

    “I love you my Soulmate”.

Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akanta. Batare da yace komai ba ya lakaci hancinta da yatsansa. Sai kuma ya ɗanbi falon da kallo. Ganin komai tsaf yaji haushinta ya ragu a ransa. Ya ɗan rungumota jikinsa da sumbatar hancinta. “Haka nake so na dinga ganinki k da gidan nan a koda yaushe”.

     Kai ta jinjina masa tana murmushi da faɗin, “Zaka sameni mai aikatawa”.

         “ALLAH yay miki albarka bari naje na ɗan watsa ruwa”.

     “Kodai ka fara cin abinci”.

Ɗan kallonta yayi na wasu ƴan mintuna, “Sure baiyi ƙauri ba na yau?”.

         “ALLAH bai yiba”.

   “Okay muje”.

Duk da ba son cin abinci yake ba haka ya dinga turawa, dan babu makusa a girkin sai abinda ba'a rasa ba. Dan kawai ya bata ƙwarin gwiwar cigaba dayi kamar hakan ya yaba tare da saka mata albarka..


       ★★★★★


   Kwanaki sun cigaba da shurawa Anam na samun lafiyar ƙafarta. Tun daga ranar dai bata sake ganin Shareff a ƴan dubiya ba. Sai dai takanji maganarsa yazo gidan ko su Amrah suce mata yazo. Dan kamar da gayya sai ya daidaici lokacin da bata falon yake zuwa. Bata damu ba, dan a wannan gaɓar bama ta buƙatar ganin nasa sam. Tana son ƙara zama nesa da shi dan tunanin da aunty Mimi keyi a kanta ya gushe har abada. Kwanakinta biyar ta take ƙafarta sarai ta koma zuwa aiki. Kullum takan shiga gaida matan gidan cikin gida kamar yanda Mamie ke jaddada mata. Sai dai kuma iyakar Mom da Aunty Amarya kawai take zuwa ta gaida bata shiga sashen Mommy dana Gwaggo. Wajen aiki kam tare suke fita da Khaleel, wataran ya dawo da ita wataran Yaseer ya maidota dan yanzu ta ɗan fara sakin jiki da shi ganin bai nuna mata wata alama data danganci soyayya sai abota kawai. Muzzaffar ma yasha gwada zuwa ɗaukarta a office ɗin amma taƙi bashi fuska sam, hakan yasa ya fara zuwa gida kai tsaye dan shikam dai yaga matar aure. Tun tana noƙewa harta ɗan fara sakewa saboda huɗubar Aysha. Sai dai duk da hakan taƙi yarda ta amsa tayin son sa. Tana dai saurarensa darajar Abbansa abokin Abie ne kuma abota mai ƙarfi tun ƙuruciya dan tare sukai secondary school, a yanzu haka kuma suna ɗan huɗɗar kasuwanci tare. 

       A haka kwanakin hutun Shareff suka cika, Maheer ma ya koma katsina wajen nasa aikin tun satin daya shige. Da farko Shareff baya zuwa gidan da safe sai ya taso aiki yake shigowa ya gaidasu. Sai randa yazo sallama da su aunty Mimi da zasu koma Malaysia saboda yara makaranta ya samu Yaseer ya kawo Anam gida. Kuma har cikin gida Yaseer ɗin ya shigo gaishe da su Mamie, a yanda suka amshesa da alama ba wannan ne ma farko ba kamarma ya zama ɗan gida. Komai baice ba, sai dai koda Yaseer ya gaida shi hannu kawai ya ɗaga masa, daga karshe ma ya miƙe ya fice batare da an kammala sallamar ba. Da kallo kawai aunty Mimi ta bisa tana ƴar dariya, Anam kam ta taɓe baki da sake maida hankalinta ga Yaseer tana dariyar maganar Amrah kamar ma bata san da Shareff ɗin ba. Dan koda ta shigo ta gansa a taƙaice tace “Yaya good evening” tai wucewarta. Shi kuma bai amsa mata ba sai hararar da yabi ƙafafunta da su dan kansa a duƙe yake yana daƙilar waya.

        Washe gari da shi akaima su aunty Mimi rakkiya airport, daga can kuma yay wucewarsa office. Anam kuma suka wuce tare da Khaleel daya buga mata warning ɗin kar ta sake tabi wata mota zai zo ya maidata gida da kansa koda bai tashi aiki ba. Badai tace masa komai ba, amma ta bisa da kallon mamaki. Hakan kuwa akai, tun kan ma a tashi aiki yazo yana zaman jiranta, washe gari ma haka sukai haka har kusan sati biyu da su Mamie suka fara shirin komawa suma. Nan fa hankalin Anam ya tashi, ta dinga kuka da magiyar zata bisu Mamie tace bata isa ba. Daga ƙarshe tai mata kaca-kaca sannan ta dawo lallashi da nasiha. Haka tanaji tana gani suka tafi suka sake barinta a Nigeria ita kaɗai. Cikin gida ta sake komawar dai sashen Mom dan nasu gidan an rufe kuma, ranar haka ta yini sukuku kamar mara lafiya, da ga ƙarshe ma har zazzaɓin sai da tayi. Sai da Khaleel ya samo mata magani.

    Su Mamie juma'a suka wuce, dan haka bata fita ko'ina ba sai monday tai shirin zuwa wajen aiki. A cikin ɗaya a dogayen abaya da Mamie tazo mata da su tai shirin, bayan ta saka kayan hidimar ƙasa a ciki dan sanyi takeji yau. A hankali ƙamshinta ke fita, ga black skin nata na shining exactly cikakkiyar ƴar Africa. Bisa matsawar Mom ta zaman yin breakfast da abinda take iya ci da Mom ta jura girka mata batare da gajiyawa ba. Kaɗan ma taci ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllhi”.

        “Badai ƙoshi ba?”.

  Mom ta faɗa tana kallonta. Murmushi tayi mai sanyi tana jinjina kanta, dan gaba ɗaya ta zama wata sukuku. “ALLAH Mom na ƙoshi, yau kwata-kwata banajin cin komai ne”.

     “Anjima fa zaki iya jin yunwa”.

“To Mom bara naje da shi office ɗin”.

Babu musu Mom ta juye mata a kula mai ƙyau. Sai da ta jira  Khaleel yasha shayi shima sannan, fita yay akan ta samesa waje zai shiga ya gaida jama'ar gidan. Saboda kar yasata binsa zuwa gaida su Mommy da tun kan su Mamie su wuce bata zuwa gaida su, shiyyasa ta noke akan zata samesa a mota. Sai da ya fita da kusan mintuna huɗu sannan ta fito. Waige-waige ta shigayi a harabar gidan babu alamar motarsa, tasan yakan kaita waje wani lokacin, dan haka ta nufi gate idan ya fito kawai sai su wuce.

      A wajen gate ɗin kuwa ta samu motar Khaleel tare da makanike, ta ɗanyi tsai tana kallon motar da tai fakin a kusa da motar Khaleel ɗin. Kamar tasan motar, sai dai ta manta mai ita dama yaushe ta taɓa ganinta.... Horn ɗin da akai ya sata haɗiye sauran tunaninta. Makaniken dake duba motar Khaleel ya ɗago yana kallonta “Hajiya kamar dake ake fa”.

    Ba laifi yanzu kanta ya ƙara buɗewa da jin hausa fiye da yanda tazo, ta jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Da farko bataji zataje ba, sai kuma ta canja shawara da tunanin ko Yaseer ne ya ɓadda kama. Murmushi ta saki akan wannan tunanin tana nufar motar. 

     Yanayin sanyinta a tafiyar ya sashi kafeta da ido cike da nazari, gashi bayan murmushin dake fuskarta babu wani alamun nishaɗi ko farin ciki a tattare da ita. 

    Zuciyarta ta gama yanke mata shawarar Yaseer ne, hakan yasata nufar ɗayan gefen batare da neman sanin waye ba ta buɗe ta shiga cikin ƴar dariya tana faɗin “Lallai ma Yaseer, kana tunanin ɓadda kama zata sa na gaza gane k.....” Sauran kalmomin suka kasa ƙarasa fita a bakinta saboda ƙamshin turaren da sai a yanzu ta samu nutsuwar banbancewa. Da sauri ta juyo batare data ƙarasa rufe motar datai yunƙurin yi ba. Har cikin rai ta tsorata da katoɓararta, amma sai ta dake cikin son kame kanta tace, “Oh Yaya yi haƙuri, ALLAH nama zata Yaseer ne ina kwana!”.

        Shiru kamar bazai amsaba, dan tunda ta shigo bai kalleta ba ko sau ɗaya. Idanunsa da suka surku da ɗan ja ya ɗago ya zuba mata. Ƙoƙarin dannewa da ɓoye tsoranta take a fili, ta kai hannu kan ƙofar da nufin buɗewa ta fice ko zata samu damar shaƙar iska yasa lock.

    (Ya ALLAH, wannan mutumin zai iya cinyeni fa a motar nan wlhy gara na lallaɓa) ta ayyana a zuciyarta. Idanu ta marairaice kamar gaske ta ɗago tana kallonsa, “Yaya kayi haƙuri ALLAH ban san kai bane”. Motar yayma key batare da yace mata komai ba ya fisgeta har yana bulama bakaniken dake duba motar Khaleel ƙasa.

     Sunayen ALLAH kawai take ambata a ranta dan tasan itakan yau sai romanta za'a samu a hanun mugun nan......

     “Mina faɗa miki akan yaron nan kwanaki?!”. Ya faɗa a kausashe dai-dai yana hawa kan babban titi. Kallonsa tai fuska a dake, ta kuma ɗauke da sauri saboda tasa fuskar ma tafi tata dakewar. Cikin ɓata fuska da tura baki tace, “Toni Yaya bamfa san wa kake nufi ba ai”.

     Komai baice mata ba, ya cigaba da driving nasa, sai da suka iso dai-dai wajen nata aikin yay fakin daga ɗan nesa. Da mamaki ta kallesa, “Yaya yanaga ka tsaya na.....?”

        Rinannun idanunsa daya dasa a kanta ya sata haɗiye sauran maganar muƙut, tai ƙoƙarin ɗauke idonta ya hana hakan cikin tsareta da nasa da duk suka firgitata. “Ni kike faɗama bakisan wa nake magana akai ba.”

      Da ƙyar ta fisgi idanunta tai ƙasa da su zuciyarta na bugawa da sauri saboda yanayinsa ya masifar tsoratata. Da sauri ta rumtse idanunta saboda jin yatsun hanunsa a kan haɓarta, ya ɗago fuskarta sosai tare da matsota garesa har suna iya shaƙar numfashin juna. “Buɗesu kona mareki!!”.

      Buɗewar tai da sauri saboda kusancinsu ba ƙaramar rikitata yay ba, hatta shi kansa yana iya jin sautin bugun zuciyarta ta hanyar ɗagawa da ƙirjinta ke ɗanyi da sauri-sauri..........✍  
 _ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko  

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_14_*..........Ko parking bai gamayi ba da ƙyau a ƙofar gida ta buɗe motar ta fice. Ya bita da kallo harta shige gida. Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya saki tare da murmushi. Ikram ta fito tana masa bye-bye. Hanun shima ya ɗaga mata har lokacin da murmushin a fuskarsa. Motarsa ya tada tare dayin reverse yabar anguwar dan baizo da niyyar shiga ko'ina ba tunda ko wanka baiyiba. Ga Fadwa dake buƙatar taimakonsa ya baro tana barcin gajiyar daya tara mata a daren jiya wadda shi kansa barcin bawai ya ishesa bane ba, kawai dai sawun giwa ne ya take na raƙumi.


       Anam batai magana da kowa ba ta haye sama, tasan ɗakinta zai yuwu su Amrah na ciki yanzu, na Mamie ma tana jiyo maganar mutane a ciki. Dan haka tai wucewarta falon Abie. Nan kam kowa bata samuba, hakan ya bata damar kwanciyarta ta saki kuka mara sauti. Kuka tayi sosai bana wasa ba har barci ɓarawo yay awan gaba da ita batare data sani ba. Wajen sha biyu Abie daya shigo ya ganta ya shiga taɓa goshinta da tunanin ko zazzaɓin nata ne ya dawo. Amma sai yaji babu zafi jikinta. Idanu ta buɗe da suka maita nauyi dan kukan data sha. Ta dubi Abie ɗin dake mata murmushi. “Sleeping beauty na ta tashi”. 

      Murmushi tai da tashi zaune. “My Abie good morning”. Ta faɗa a marairaice. “Morning Darling duk gajiyar bikince ta saki zuwa nan ɓuyan barci?”. Fuska ta ɗan ɓata. “Abie su Amrah basa barina nai barci mai ƙyau dan surutunsu. Gashi ƙasa nake kwana dan bana son kwana da kowa ɗakin ma ya mana kaɗan”.

    Murmushi kawai yay da shafa kanta. Sai kuma ya dubi idanunta da suka sake fitowa da ƙyau. “Mamana idanun nan kamar anyi kuka da su?”. Da sauri ta girgiza masa kanta. “Abie rashin barcine fa”. Bai gamsu ba. Sai dai baice komai ba. Itama mikewa tai da faɗin, “Bara naje nayi wanka”. Tai maganar da zuwa ta kama hanunsa ta sumbata. Da kallo kawai ya bita, dan yasan tayi hakane dan karya cigaba da tuhumarta akan kumburin idonta daya tabbatar kukane ya sakasu komawa hakan tunda ba yau ya santa ba.


        Ta fito wanka tana shafa mai Amrah ta shigo ta sanar mata tayi baƙo. Da mamaki take kallonta sai dai batace komai ba. Amrah ma ta juya ta fita abinta. A nutse ta ƙarasa shirinta ranta fal tunanin wanene?. Ba ta da mai bata amsa dan haka ta fesa turare da ɗaukar wayarta ta fito. Tayi ƙyau sosai cikin wando da rigar jikinta, sai siririn mayafi data yana a kanta. A wajenta wannan shigace normal saboda a inda ta tashi, sannan rigar bata kama jikinta ba ta kuma sakko har kan mazaunanta. A falo ta samu su aunty Mimi, har zata zauna Mamie ta harareta. “Bake naji ance anzo nema ba?”. Cikin ɓata fuska tace, “Ni banyi da kowaba fa zai zo Mamie”.

     Aunty Hamida tai dariya. “To ɗiyata kika sani ko a ƴan biki ne wani yay sau da baya?. Tashi kije dan da alama mun kusa dawowa wani shagalin insha ALLAHU”.

       “Hu'um aunty ALLAH ya kiyaye ni karatu ma zan koma”.

    Daƙuwa aunty Hamida tai mata. “Karatun gidan ku, a wannan shekarun naki ai aure ne ya dace ko dan kina ganinki ƴar ficika da ƙaramin jiki? Maza tashi kije ana ɓata masa lokaci”. 

     Badan taso ba ta fito, Mamie na kiranta tazo tasa hijjab bama taji ba dan a fusace take da taikaicin koma wanene.

     

       Dr Jamal dake daƙilar waya ya ɗago fuskarsa ɗauke da murmushi yana kallonta. Itako kallo guda tai masa ta kauda idonta. Kujerar dake gefensa ya gyara mata, ta ƙaraso fuska babu walwala tana masa sallama. Amsawa yay murmushinsa na sake faɗaɗa. “Barka da fitowa gimbiyar mata”.

       “Ina yini”.

Ta faɗa a takaice. 

  “Lafiya lau. Bismillah ki zauna mana”.

          Kamar zatace a'a sai kuma ta zauna. 

    “Kiyi haƙuri nazo babu izini. Sai dai karki manta dama nace zan zo dubiya”. 

     Ɗan murmushin yaƙe tayi, a taƙaice tace, “Babu damuwa”. 

    Idanu ya ɗan kafeta da shi, a ƙasan ransa yana tattaro abinda ya dace ya faɗa. Ɗagowa tai ta dubesa itama fuska a murtike. Ya kauda nasa idon. Cikin zolaya yace, “ALLAH ni sai ma naji ina jin tsoronki kamar”.

      Haka kawai yanda yay maganar ya bata dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa shiko ya kafeta da idanu yana murmushi. A dai-dai nan aka buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo. Su duka sukabi motar da kallo har lokacin kowanne da dariyar kan fuskarsa. Dr Jamal ya faɗaɗa tasa ganin Shareff, itako haka kawai sai da gabanta ya ɗan faɗi.

      Ya kai kusan mintuna huɗu bai fitoba idonsa kafe a kansu, sai dai shi basa ganinsa kasancewar tinted glass ne da motar. Murfin motar ya buɗe ya fito da nufin shigewarsa ya nuna bai gansu ba kawai. Sai dai Dr Jamal daya taso fuska ɗauke da murmushi ya hana hakan. Fara'ar dole ya ƙaƙaro yana mika masa hannu kamar yanda shima ya miƙamasa. “Ango! Ango!! Ƙyallinka dabanne”.

     “Haka dai kace”.

 Shareff ya bashi amsa hankalinsa nakan Anam data ɗauke kai kamar bata gansa ba.

    “Haka ɗinne ma abokina. Dan ko kamshinka yau ya sake bunƙasa fiye da kullum. Muma dai gamu nan fara kafa foundation mukai matsayin nan naku haka nan”.

         Gabansa ne ya fadi, amma sai ya dake ya saki gajeren murmushi. “ALLAH yasa haka to.”

     “Insha ALLAH wannan karon da gaske nake abokina”.

   Nan ɗin ma murmushin yayi kawai da faɗin, “Bara na shiga na gaida su Mamie”.

       “Okay to a fito lafiya”.

Ido suka haɗa da Anam ya wulla mata wani mugun kallo data jima bata gani daga garesa ba ya wuce. Dr Jamal daba lura yay ba ya dawo ya zauna yana dariya. “Kinga Yayan nan naki da gaske angwancin nan fa ya amshesa. Kwana daya kacal harya canja kamar bashi ba”.

       Ƙin cewa komai tayi, sai dai tayi ƙaramin murmushi. Shima murmushin yayi yanaji kamar ya haɗiyeta. Sallamar Amrah ta katsesa daga kallon da yake mata. Duk suka dubeta. Gaishe da Dr Jamal tai, ya amsa cike da fara'a da tambayarta gajiyar biki. Tace masa Alhmdllhi tana maida kallonta ga Anam. “Anam Yaya Shareff yace yana jiranki zai amshi ajiyar daya baki”.

      Kallon Amrah take cike da mamaki da rashin fahimta, sai dai ta rasa abin cewa. Sai Dr jamal dake kallonsu ne ya katse shirun da faɗin, “Inaga jeki kawai ki basa saƙon sai na jiraki. Dan da muhimmiyar magana nazo”.

          Kamar zatace ita babu wani saƙonsa a wajenta sai tai shiru kawai. Ta mike zuciyarta na mata kaikawo da mamakin Yah Shareff ɗin. Yaushe ma har suka fara shiri dazai bata wani ajiyar abu..? Ita kaɗai ta nufi hanyar falon, dan Amrah fita tai dama cikin gida zata ya bata saƙon. Ta shigo ɗan lungun dazai sadata da ƙofar falonsu ya kuma zama hanyar dake tare data garden taji an fusgota. Ihu tai niyyar yi yay azamar rufe mata baki. Sai da ya maida ƙofar ya rufe sannan ya saki mata baki yana binta da wani shegen kallo data kasa fahimtar na minene.

     Baki ta tura tana gyara mayafinta. Ya sake harararta da binta da kallon sama da ƙasa fuskarsa a tsananin ɗaure. “Daga yau na ƙara ganinki da wannan banzar shigar gaban kowane ɗan iska ki tabbatar saina ɓaɓɓalaki na zubar. Ki kuma koma ciki, kona haɗa k da shi na zafafa. Tashi min anan kona kashe fuskarki da mari stupid”.

      Da gudu tabar wajen hawaye na silalo mata. Yaja tsaki mai kauri yana furzar da zazzafan huci daga bakinsa. Fitowa yay daga garden ɗin ya nufi falon shima dan dama ko shiga baiyi ba. Zama yay suna gaisawa da su aunty Mimi da ƴan uwan Mamie dama Abie ɗin. Kasa haƙuri sukai sai da suka tambayesa ko lafiya? Dan yanayinsa ya nuna ransa a ɓace yake. Ya kaƙaro murmushi yaƙe yana shafa kansa. “Bakomai fa auntys karku damu. Gajiya ce kawai da bata gama sakinmmu ba”.

      Mamie dake fitowa a kitchen tai yar dariya.  “To banda abun babana aida basai mun gankaba yau, sai kai zamanka ka huta sosai a gida ko”. Kansa ya shafa yana ƙara risinarwa. “A'a Mamie gara dai nazo na dubaku kuma hankalina zaifi kwanciya ai”. 

     “To shikenan ALLAH yay maka albarka yaya ɗiyar tawa itama?”.

    “Lafiya lau tana gaisheku da muku bangajiya.”

          “Duk muna amsawa”.

Bai wani jima sosai ba ya fito, a waje ya sake samun Dr Jamal. Ya nufesa fuskarsa kadaran kadahan. Shiko Dr Jamal tasa kawace da murmushi. “A'a ango mijin amarya Fadwa har ka fito kenan?”.

       “Eh, ina so na ɗanje na sake hutawa kasan gajiyar biki. Kaima nayi mamakin ganinka anan kai da ya kamata ace kana can kana kwasar barci”.

       “Tab barci ai sai ku angwaye. Muko kwanciya mutum yayta rungumar fillos ai da gajiya. Gara mu fito farautar namu kayan kamar zaifi”.

            “Hakane, amma sai naga baka tafi farautar ba ai”.

     “Kajimun ɗan iska mi kazo kaga inayi? Inama take? Tunda kai akace kana kiranta”.

              Fuska ya ƙara tsukewa da ƙyau yana kallon Dr Jamal ɗin. “Yaka kafeni da idanu kamar naci bashinka?. Tunda kace babu ruwanka ni nazo da kaina na kafa gwamnatina”. Kansa ya kauda yana jan karamin tsaki. Kafin ya dawo da kallonsa garesa. “Jamal amma kasan bana son jan raini ko? Duk manyan mata dake garin nan da suka amsa sunansu mata karasa wa zaka so sai wannan ƴar abar haihuwar jiya”.

      Dariya sosai Dr Jamal keyi, “Oh badai an haifeta jiyan ba? To ni wlhy ko yanzu aka haifota ina son kayata a haka. Yarinyarnan ta haɗa duk abinda nake so ga matar da nake fata ta zama abokiyar rayuwata. Ni bana ganin waɗancan manyan matan sam a idona. Kai dai tunda ka ɗauka taka barni nima lokacina ne”.

     Tsaki yaja mai karfi da barin wajen. Dr Jamal ya bisa da kallo yana murmushi. “A gaishe da amarya sai munzo cin cin-cin”.

     Bai tanka masa ba, bai kuma juyoba ya shige motarsa ya fice. Agogo shima Dr Jamal ɗin ya kalla. Ganin lokacin da Anam taci babu alamar zata fito yay tunanin bara kawai ya wuce ya dawo anjima da dare. Yaran Aunty Hindu dake can gefe suna wasa ya kira babban. Leda dake dauke da kayan ciye-ciye na kwaɗayi ya bashi yakaima Anam ɗin shi kuma ya nufi motarsa.....


______________________________


            Washe gari monday Anam ta koma aiki, Abie da kansa ya kaita. Hakan ya mata daɗi, ya kuma sakata a farin ciki har fuskarta ta kasa ɓoyewa. Da Yaseer ta fara cin karo, wanda rabonsa da zuwa aiki tun randa ya kaita gida. Kallon kallo suka tsaya yima juna, farin cikin da take ciki ya sata fara sakin murmushi. Cikin harshen turanci da mutsukka idanunta take faɗin, “Ko aljani ne kemin gizo”.

     Duk yanda ya so daurewa sai ya kasa. Ya saki murmushi yana gyara tsaiwarsa. “Ba aljani bane ifiriti ne”. Dariya maganar tasa ta bata. Ta ko ƙyalƙyalawa cike da nutsuwa tana kare bakinta da handkerchief. Jiyay gaba ɗaya ya narke a kallonta, harma zuciyarsa na jin anya kuwa zai iya kiyaye dalilin da ya sashi jin zai nisanceta kuwa?... Matsowarta kusa da shi ta katse masa tunani. Har yanzu fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙwara. “ALLAH da gaske naji kewarka Friend. Wane laifi mukai haka ake fushi damu harda tafiya babu sallama?”.

       Hannayensa ya haɗe alamar ban haƙuri🙏🏻, fuskarsa a marairaice sai dai baice komaiba. Cikin ƴar dariyar data ƙara zuwa mata tace, “Shikenan ya wuce muje ciki”.

       Tare suka shiga, suka cigaba da hidimomin gabansu. Koda aka tashi aiki Maheer ne yazo ɗaukarta. Ta nuna farin ciki anan ma dan tunda yazo hidimar biki ta hana su zauna su gaisa da ƙyau. Maheer baida damuwa, yanada sauƙin kai sosai ga barkwanci, sai dai Shareff ya fisa haƙuri nesa ba kusa ba, kawai dai yafisa sakewa da mutanene shiyyasa ake ganin kirkin Maheer fiye da Shareff ɗin.

       Bai wuce da ita gida kai tsaye ba. Sai da suka biya wani joint sukaci kayan kwaɗayi sukai hira sosai sannan. A hanya yake cemata yaushe zata rakasa gidan amarya yaga gida. Cikin taɓe baki ta bashi amsa da “Yah Maheer kaje abinka kai kaɗai kawai”.

          “Miyasa bazakije ba ke?”.

“Ba komai, kuma ni nama riga naje ai”.

      “Idan kin koma ma ai duk cikin zuminci ne”.

   Maimakon ta amsa masa sai ta canja da wata hirar. Shima sai bai sake maganarba har suka isa gida.


        A kwana a tashi ango da amarya sukaci kwanaki shidda da angwancewa. Soyayya ce ake zubawa tamkar babu gobe. Basu da matsalar abinci, dan kullum sai Mamie ta aika musu na safe na rana harda na dare ma, sai da Yah Shareff ɗin da kansa yace a daina kai na daren sannan Mamie ta hutar da kanta. A komai nane suke da juna tamkar su haɗiye kansu. Basu da wata damuwa sai suci suyi ƴar soyayyarsu. Babu inda yake zuwa dan ya ɗauka hutu na sati biyu dama, duk da sati ɗaya yay niyya Fharhan ya takura masa akan biyu dai sannan gajiyar biki ta sakeshi. Ya dauka sati biyun dai kawai badan yana tunanin zama har su cika baije office ba, dan yasan sunada ayyuka danƙam harma da wasu sabbin projects da yake fatan samu wanda zasu fito ne daga gwamnati.

      Yakan je gidansu a kullum da yamma ya gaida iyayensa, sai dai koya shigo wajen su Mamie basa haɗuwa da Anam. Dan a mafi yawan lokuta yakan zone bata dawo aiki ba. Bakuma dan lokacin dawowar tata baiyiba. Kawai dai yanzu Maheer na matukar ɗauke mata hankaline, yama hana Abie kaita da safe shi ke kaita ya kuma je ya ɗakkota, bakuma su dawowa gida sai sun ɗan zaga gari wani lokacin ma sai bayan magrib. Wannan dalilin yasa duk sanda Yah Shareff yazo baya samunta a gidan. Bai dai taɓa magana ba, hasalima bai nuna ya san da wanzuwarta ko saɓanin haka ba. Itako dama ko'a jikinta harma mantawa take da shi yanzun, dan koba komai ta huta da harara da kallon dake matuƙar ƙona mata rai daga garesa.


      Yau ta kasance juma'a. Da wuri Maheer ya ɗakkota a wajen aiki da jaddada mata ta shirya da wuri zatai masa rakkiya wani waje. Batare data tambayesa ba tace to. Ciki ta shige, bayan ta gaida Mamie da Abie ta wuce ɗakinta. Dan aunty Mimi da yaranta sunje Abuja gidan yayan mijinta, amma yau suke saran dawowarsu. Wanka tai ta shirya tsaf cikin kwalliyar doguwar rigar material dan Yah Maheer yace mata tasa kayan hausawa. A lokacin har tana ɓata fuskar cewar ita suna damunta bata son zafi, lallaɓata yay, dan yafi son ganinta a kayan saboda ƙyawun da suke mata. A bikin nan ba ƙaramin son ganin kwalliyarta ya dingayi ba. Koda Mamie tace ta zauna taci abinci catai a'a zasuci a wajen cin abinci Yah Maheer zata raka wani waje. Mamie ta ɗanyi jimm sai kuma ta sauke numfashi, gargaɗi tamata nata kama kanta tare da jin tsoron ALLAH.

       “Insha ALLAHU Mamie bazaki taɓa yin kaico akaina ba, yanda nake a gaban idonki haka zan cigaba da kasancewa a bayan idonki. Domin UBANGIJIN dake azaba ga wanda ya saɓa masa, yake rahama ga wanda ya bisa yana kallona koda ke baƙya ganina”.

     Murmushi Mamie tayi, cike da jin daɗi da alfaharin tarbiyyar da suka bama gudan jininsu tilo duk da suna rayuwa a inda kowa ke ganin dole ne yaro ya lalace, sai dai ba hakan baneba, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. “ALLAH yay miki albarka, ya kuma baki ikon tabbatarmin da hakan”.

     “Amin Mamie na uwa ɗaya tilo”.

Ta faɗa tana sumbatar hanun Mamie sannan tai mata sallama ta fice. 


       Tun tafiyar tasu batai nisa ba sosai ta fara fahimtar inda suka dosa. Taso ta share amma saita kasa. ta dubesa a shagwaɓe “Yaya nifa....” Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar fadin, “Ban son kice komai. Ai ni zaki raka ko”. Shiru tayi badan taso ba. Dan tana ganin girmansa da kima sosai a zuciya da ayyuka. Hira ya cigaba dayi mata, wani ta amsa wani tai murmushi har suka iso. Har ciki ya shiga da motar, kamar yanda ya saba mata a tsakanin nan shine ya fara fita sannan ya zagaya ya buɗe mata fuskarsa dauke da murmushi kamar yanda tata ma ke ɗauke da murmushin mai bayyana haƙora. Tace, “Kai Yaya Maheer shine har da wani ɗan respect?”.

     Dariya ya sanya, idanunsa akan fuskarta yana ji kamar ya haɗiyeta dan murmushi na mata masifar ƙyau. Ƙara risinawa yay irin na respect ɗin yana nuna mata hanya alamar suje. Dariyar ta sake sanyawa da salute nashi itama....


       A hankali ya lumshe idanunsa da ɗaukesu daga garesu yana sakin siririn tsaki dan komai yana faruwa ne akan idanunsa kasancewar yana daga barandar sashensa tare da Fharhan da Khaleel suna magana akan office. Tsakin nasa yasa Khaleel da Fharhan da suma ke kallon su Anam ɗin maido dubansu garesa. Sai dai kasancewar ya riga ya maida ga lap-top ɗin dake cinyarsa yasa basu fahimci da ainahin wa yake ba. Khaleel ya mike yana miƙama Maheer daya iso wajen hannu yana faɗin, “A'a Brother dama nan kawo ashe?”. 

     “Eh wlhy, ai ban san kaima nan din kayo ba damun haɗa tafiyar ma ai”. 

   “Ai babu damuwa tunda ga ƴar rakiya ka samo”.

   Murmushi kawai Maheer ɗin yayi da maida hankalinsa ga Fharhan suka gaisa cikin mutunci dan duk abokan  Shareff suna ɗaukarsu yayu suma.

        “Babban Yaya barka da yammaci”.

Maheer ya faɗa idonsa akan Shareff. Sai lokacin ya ɗago, ya ɗan dubi Maheer ɗin fuska babu yabo babu fallasa. “Daga ina haka?”.

    “Daga gida muke. Yau dai nace bara nazo na gaida amarya na huta da gorinta”.

         “Hakan nada ƙyau”.

Ya faɗa a taƙaice hankalinsa nakan abinda yakeyi dan dama tuni ya maida kansa ga lap-top ɗin. Shima Maheer maida dubansa yay ga Anam data coge can taki karasowa. “Hajjaju ƙaraso mana ku gaisa da su Yaya”.

     Baki ta tunzura, badan taso hakan ba ta nufesu tana ƙunƙuni. A jimlace ta gaishesu, batare data damu dawa ya amsa ba waye bai amsa mata ba tabar wajen. Shima Maheer bayanta yabi sai dai ganin ta sake cogewa alamar bazata shiga falon ba yaja hanunta. Ƙoƙarin amshewa take amma ya hana hakan sai da suka shige ya saketa. Kowa babu a falon sai uban ƙaurin abinci daya gaurayesa, ga falon a ɗan hargitse alamar dai yau bai samu gyara ba koma ba yau ɗin kawai ba. Anam ta yamutse fuska kamar mai tsantsami tana bi ko'ina da kallo a karo na farko dan waccan ranar batai ba. 

      “Ni kamar ƙaurin abinci nakeji fa?”.

      Ya Maheer ya faɗa yana dubanta. Baki ta taɓe da kauda kanta batare data amsashi ba. Shima sai bai sake magana ba ya shiga ƙwala kiran sunan Fadwa a tunaninsa ko ta shiga wani uzirinne a ciki batasan abincin na ƙunewa ba. Kusan sau uku sannan ta fito daga hanyar bedroom hanunta rike da waya tana murmushi, da alama abu take dubawa da yake sakata nishaɗi...........✍_😣😣Wayyo Fady baby ya zaki bamu kunya haba selen mu so kike ƴan uba su sami na faɗa yau🤕. Koda yake munada bakin ramawa🚶__ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO.👉🏻AREWABOOKS🫶🏻_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_15_*..........Da kaurin abincin ta fara cin karo, dan haka ta kwasa da ɗan gudu zuwa kitchen tana faɗin, “Wayyo ni Fadwa yau ma yayi ƙauri”. 

      Daga Maheer har Anam da kallo kawai suka bita, Anam ta taɓe baki da neman kujera ta zauna. Ganin haka shima Maheer ɗin sai ya zauna yana ƴar dariya. “Tofa bama yau aka fara ƙonawaba kenan. Lallai Yaya an shigo abba tuwa ashe. Nikam gaskiya bazan iya haƙuri da mace bata kulamin da cikina ba”. Ya ƙare maganar yana tsare Anam da idanu.

     Idanu ta ɗan waro da ɗage kafaɗarta baki a tabe alamar I don't care, sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya. Ihun da Fadwa ta saki ya hanashi cewa komai ya mike da sauri ya nufi kitchen ɗin. Anam kam maimakon ta tashi sai ta ɗauka waya tana cigaba da dariyarta. A dai-dai nan shima ya shigo falon kasancewar Fharhan da Khaleel sun wuce office saboda sunada uziri. Buɗe ƙofar ta sakata rage dariyar da ɗan kallon ƙofar, sukaima juna kallon ido cikin ido. Nata ta fara janyewa saboda hango wani irin yanayi mai kama dajin zafinta a cikin nasa idanun, itakan ta rasa mitaima Yaya Shareff ya tsaneta a duniyar nan, idan dan tazo gidansa ne ya kwantar da hankalinsa wannan shine zai zame mata na ƙarshe insha ALLAH. Bata sake yarda ta kalla inda yake ba, sai dai har yanzu tanajin nasa idanun a kanta. Hakan ya sakata a matuƙar takura, sai dai kuma ta kasa motsawa balle ko yinƙurin barin wajen tayi....

      Dariyar Maheer ta sakashi janye idanunsa a kanta ya juya garesa, sai yay karo da idanun Fadwa dake tsaye ƙyam a kansa tana masa kallo mai cike da tuhuma. Fuska ya sake tsukewa cikin basarwa ya maida hankalinsa wajen bin falon da kallo. Sosai ransa ya ƙara ɓaci fiye da wanda yake ciki tun ɗazun, duk gargaɗin da yay mata akan karya shigo ya sake ganin falon nan haka da datti batajiba kenan. Ya ɗan cije lip ɗinsa kawai batare da yace komaiba ya juya ya fita. Hakanne yasa Maheer bin bayansa shima. Anam ma mikewa tai, ta zabgama Fadwa dake binta da kallon wulaƙanci harara sannan ta fice tana jan ƙaramin tsaki. 

      Duk da kiran da Maheer yay mata batai niyyar binsu sashen Shareff ɗin ba. Sai dai ganin Fadwa na leƙenta ta window rai ɓace ya sata nufar can tana wani murmushi daya ƙawata fuskarta. A bakin ƙofa ta coge, Maheer ya juyo yana kallonta, cikin tsokana ya wulla mata ƙaramar harara. “Malama wa kikema aikin gadi zaki mana tsaye anan? Zoki zauna jareh”.

     Murmushi kawai tayi itama, batare da tace komai ba ta zauna a kujerar kusa da shi tana satar kallon Shareff dake latsa waya kamar ma bai san da shigowar tata ba. Baki ta taɓe itama ta ɗauka tata wayar ta shiga latsawa. Ba'a rufa mintuna huɗu ba Fadwa ta shigo ɗauke da babban basket dake ɗauke da kuloli da duk abinda maicin abinci zai iya buƙata. Maheer ya miƙe ya karbeta yana dariya, cikin ƙasa da murya yace, “Badai mai ƙaurin zaki bamu ba?”. Harara ta ɗan sakar masa da kai masa ranƙwashi ya kauce, dining ya nufa domin ajiyewa, ita kuma ta nufi inda Shareff ke zaune har yanzu idonsa akan wayarsa. Zama tai kusa da shi tana mai rungumesa tare da manna masa kiss a kuncinsa. “I miss you my Soulmate”.

    Maimakon amsa mata sai ya ɗago ya ɗan saci kallon Anam. A zahiri idonta akan waya yake, sai dai kunenta da hankalinta na tare da su..... “Wai har yanzu fushin kake?”. Fadwa ta faɗa cikin kunnensa hanunta ɗaya na cikin nasa ɗaya na shafo wuyansa zuwa gefen kunne. Hanunta dake kan wuyansa ya janye, a hankali yace, “Miye haka wai, muje ki bani abinci”. Bataso haka ba, sai taji inama ya biye mata kodan ta turama wannan yarinyar haushi. Amma ko yanzu ma bata ɓaci ba, tayi alwashin sai Anam ta daina zuwa mata gida har abada daga yau dalilin abinda ta shiryama ranta zatai mata. Cike da isa da yauƙi tabi bayan Shareff zuwa dining, dama shi Maheer tunda ya dire abinci yaja kujera ya zauna acan abinsa.

        Cikin bada umarni Maheer yacema Anam ta taso suci abinci, ta ɗago tana girgiza masa kai alamar a'a. Hararta yayi, “Kinsan ALLAH idan na taso ɗaukarki zanyi kamar bab.....”

    “You're vary stupid!!”. 

Ya faɗa cikin suɓutar baki idanunsa na wani irin ƙanƙancewa. Furucin da fusatar tasa ya saka Maheer haɗiye sauran abinda ke bakinsa. Anam da Fadwa kam gaba ɗayansu suka zuba masa ido dan yanda yay maganar a fusace duk sai da suka zabura. Waya yakeyi, wayar da kafin zancen Maheer yinta yake da murya can ƙasa dako Fadwa dake kusa da shi tana ƙoƙarin fara zuba masa abinci bajinsa take ba. Hannu takai da nufin taɓashi ya maka mata harara dole ta janye, sosai abun ya bama Anam dariya, tako yi gefe da kanta tanayi sai dai ƙasa-ƙasa. Maheer ya kalleta yana murmushi shima. Cokali ta ɗauka ta saka a cikin abincinsa babu ko ɗar ta kai baki, da sauri ta ɗiba tissue ta tufosa a ciki tana ambaton ya ALLAH. Shima dai Maheer yay cak ya kasa cigaba da tauna na bakinsa. Yayinda shima oga kwata-kwatan ya tufo nasa cikin tissue ɗin daya fisga yana kallon Fadwa rai a ɓace. 

       “Kinada hankali kuwa? Wannan gishirin fa!”.

     Ɗan zabura Fadwa tai baya jikinta na tsuma. Ya sake jan tsaki da miƙewa zai bar wajen tai saurin riƙosa. A fusace ya juyo gareta sai dai saurin rungumesan da tayi ya sashi haɗiye kakkausan furucin da yay niyyar jifanta da shi. Jin bai tureta ba ta ɗago da sauri dan a gareta wannan damace da zata aiwatar da shirinta, babu zato kuwa babu tsammani ta haɗe bakinsa da nata. Da sauri Maheer yasa handkerchief ya rufe fuskarsa yana dariya...

     Faɗuwar abu da tarwatsewarsa kan tiles tare da sakin siririyar ƙarar Anam ya sakashi saurin ture Fadwa yana jan numfashi da ƙarfi. Maheer ma da sauri ya janye handkerchief ɗin dake fuskarsa tare da haɗiye dariyarsa. Kusan a tare suka zabura kanta, sai dai Maheer ya rigashi kai hannu zai riƙo Anam, a ɗan fusace ya fisgo hanun Anam ɗin da Maheer ya kama ta dawo jikinsa, cak ya ɗagata daga dirƙuson da tai ya maida saman kujera, ƙafarta dake fidda jini ya ruƙo yana kaiwa tsugunne gaban kujerar, sai da ya rumtse ido sannan ya tsige yankin kwalbar cup data shigeta. Tako sake sakin ƙara jikinta na rawa dan har cikin ƙwaƙwalwarta taji cire glass ɗin. Handkerchief ɗin hanun Maheer ya fisga ya ɗaure mata ƙafar, sannan ya sake ɗaukarta cak yay waje da ita. Maheer da shima ke a rikice bin bayansu yay da sauri.....

      Sosai zuciyar Fadwa ta kumburo cikin ƙirjinta tamkar zata fashe, itace ta tura kofin da hanunta ya faɗi lokacin da taga Anam zata miƙe a yanda ba kowa ya gani ba musamman ma Shareff data rungume. Tsabar yanayin da take ciki ko kwakwkwaran motsi ta gagarayi har tajiyo fitar motar mijinta. Hajijiyar da taji tana kwasartace ta sata saurin dafe kujerar dining...


      Basu san ba ƙaramin ciwo Anam taji ba sai da suka isa wani clinic dake anan cikin anguwar. Sun fara mata allurar rage raɗaɗi kafin su tabbatar musu ciwo taji sosai kuma sai an ciro sauran kwalbar daya karye a wajen sannan a mata ɗinki. Basu wani ja zancen ba akai mata duk abinda ya dace tana faman kuka da raki. Sai da komai ya nutsa ta samu nutsuwa da daina kuka har sun fita sunyo sallar la'asar sun dawo sannan suka sami damar ganinta. Tausayinta dukansu ya sake kamasu, dan cikin ƙanƙanin lokaci har ƙafartata ta kumbura. Ƙin yarda tai ta kalli ko sashin da Shareff yake. Cike da shagwaɓa tace, “Yaya Maheer ni ka kiramin Mamie da Abie su zo”.

      “A haba dai sarkin rigima. Ni babu wanda zan kira dan maybe ma su sallamemu yanzu mu wuce gida. Wai ni garin yaya ma hakan ta faru ne? Keda ke zaune a kujera?”.

          Fuska ta sake tsukewa matuƙa, taƙi kuma cewa komai sai harar gefen ido data ballama Shareff daya tsareta da idanu shima alamar bukatar son ji. 

   “Ina saurarenki ya akai hakan ta faru?”.

          Nan ma ƙin cewa komai tai, sai dai ta ɗago yanzu sosai ta kalli Yaya Shareff har suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi da zamewa ta kwanta tana son maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata. Maheer da bai hakura da son jiba yay ƙoƙarin zagayawa inda ta juya fuska Shareff ya dakatar da shi. “Malam ya isa”.

   Kamar Maheer zaiyi magana sai kuma ya fasa saboda shigowar Nurse. Sannu tai musu tare da mikama Shareff dake kusa da ƙofa takardar hanunta. “Yallaɓai zaku iya tafiya da ita gida yanzu, ga wannan magungunan sai a saya mata tai amfani da su, ALLAH ya kiyaye gaba”.

    Amsar takardar yay da gyaɗa mata kansa kawai. Sai da Nurse ɗin ta fita sannan ya dubi Maheer dake tambayarsa ko can gida zasu wuce kawai?. Bai ce masa komai ba ya fita a ɗakin, shi kuma Maheer ya koma inda ta juyar da fuskarta. 

      Kallonsa tai da faɗin, “Yaya nidai mu tafi gida kawai, bazan koma gidansa ba, kuma wlhy ta kwana da sanin yanda ta zubarmin da jini sai na rama koba yanzu ba”.

        Ɗan zaro ido Maheer yayi da zama a kujerar dake gaban gadon. Kafin ya samu damar cewa wani abu Shareff da wasu Nurse suka shigo ɗakin. Kallonta yake cikin ido saboda yaji abinda take faɗa. Maheer ma kallonta yake sai dai ya kasa cewa komai dan bai fahimceta ba. Da taimakon Nurses ɗin aka kawota wajen mota, tanata mitar ita dai a kaita wajen Mamie. Bai kulata ba, sai Maheer dake lallashinta. Sun tsaya wani pharmacy ya bama Maheer takardar da atm ɗinsa tare da faɗa masa pin......


       ★★


  Tun bayan fitarsu take auna son kiran Mamah (Gwaggo Halima) sai dai gargaɗinsa akan kai ƙararsa ga iyayenta ko nashi na taka mata birki. Sosai ta kasa zaune ta kasa tsaye balle tsaida shawara. Har cikin ranta tsoro ne da shakku ke cizon zuciyarta dake ayyana mata abubuwa masu dama. Ta rasa miyasa yarinyar nan ke yawan shiga mata hanci ne? Kodai akwai alaƙar da suka jima suna jin tsoron ta kasance ne ta ƙullu tsakanin mijin nata da baƙar yarinyar nan? “Kai ina, wlhy zuciyata bazata iya ɗauka ba”. Ta faɗa a zahiri da ƙoƙarin kauda mummunan zaton dake kawoma zuciyarta farmaki. Ba yau ta fara irin wannan tunanin ba, shiyyasa a koda yaushe take ƙara jin tsanar yarinyar bayan wadda mahaifiyarsu ta cusa musu akan iyayenta da ita kanta, bata son ganin wata alaƙa tsakanin Mijinta da Anam, amma abin tsoron a kullum kusanci take gani a tsakaninsun, kusanci irin wanda tafi shiga tashin hankali da shi a yanzu fiye dana baya.. Tabbas lokaci yayi da zata ɗauki mataki, idan tace mataki tana nufin koma wane irine in har zai nisanta tsakanin mijin nata da wadda takema kallon maƙiyya tun a zamanin tsatson kakanni da suka haɗa kishi.....

       Harta danna kiran Mahmah ta yanke, dan tasan rashin haƙuri da haɗiye abu irin nata, maida akalar kiran nata tayi ga Mommy, bugu ɗaya kuwa ta daga. Ta gaidata cikin ladabi da kwantar da murya. Itama Mommy sai ta amsa da kulawa sosai. Shiru ya biyo baya, Fadwa na tunanin ta inda zata fara...

    Mommy ta katse shirun da faɗin, “Fadwa babu dai wata matsala ko?”. Nan ma shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya da fara kukan da bata san yana makale a makoshinta ba. “Lafiya Mommy”. “A'a Fadwa, ya zakice lafiya kuma kina kuka. Kinga kar kiji komai faɗamin matsalarki kinji, Shareff ne ko?”.

       “Bashi bane Mommy yarinyar nan ce Anam”.

     “Anam!!”.

“Eh Mommy”.

Shiru Mommy tayi zuciyarta na tafasa, taja nannauyar ajiyar zuciya tana mikewa. Falon ta fara zagayawa har lokacin wayar na a kunnenta sai dai ta kasa cigaba da cewa komai kamar yanda itama Fadwa tai shiru. Kusan mintuna biyu sannan Fadwa ta katse shirun da faɗin, “Mommy wlhy ni bazan iyaba. Zuciyata bazata iya ɗaukar cigaba da ganin wannan yarinyar mai ƙirar karuwai na shigomin gida ba. Inba hakaba zan iya kasheta na halaka banza.....”

      Rai ɓace Mommy ta katseta da faɗin, “Shi Shareff ɗinne ya kawota gidan?”.

          “A'a tare da Yaya Maheer sukazo. Yanzu haka daga ta ɗanji ciwon da tana akan sani tayisa dukansu sun kwasheta zuwa asibiti a ruɗe. Kusan awa huɗu kenan har yanzu basu dawo ba. Wlhy Mommy na tsaneta, dan ALLAH nidai ta daina zuwa min gida”.

        Katse wayar Mommy tayi, ranta a matuƙar jagule ta fara laluben number Maheer, harta katse ba'a ɗauka ba, ta sake kira nan ma ba'a ɗagaba. Ranta ya sake ɓaci ta maida akalar kiran ga Shareff. Tana gab da tsinkewa ya ɗaga, cikin girmamawa a gareta da tausasa harshe na ɗa nagari ga iyaye yay mata sallama da faɗin, “Mommy barka da yamma”.

        “Kuna ina?”

Ta jeho masa tambaya batare data amsa gaisuwar tasa ba. Ɗan jimm yay alamar tunani, sai kuma ya kalli Anam dake kwance cikin kujera idanunta a lumshe. Kamar mai raɗa ko tsoron tada jariri a barci yace, “Pharmacy”.

       “Kai da wa?”.

Kallon Anam ɗin ya sakeyi suka haɗa idanu, a marairaice ta janye tana kauda kanta gefe. Numfashi ya ƙara saukewa, cikin sake tausasa harshe yace, “Ni da Maheer ne....”

      “Dawa kuma?”.

Ta tare numfashinsa tun kan ya ƙarasa. Bai iya karya ba, shi mutumne kai tsaye koda ace gaskiyarsa zata ja masa laifi ko matsala zai faɗa ya amsa hukuncin daga baya. Dan haka yace, “Mommy da Juwairiyya ne da taji ciwo”.

       A fusace tace, “Waye Juwairiyya kuma?”.

     A hankali yace, “Anam”.

“Kusameni kai da Maheer”.

Ta faɗa tana yanke wayar. Tsirawa wayar ido yayi kamar mai son ganin Mommyn a ciki, sai kuma ya ɗan girgiza kansa ya ƙara kallonta ya ɗauke kansa yanama motar key saboda hango Maheer na fitowa. Baicema Maheer ɗin komaiba ya canja hanyar zuwa gidansa zuwa amsa kiran Mommy. Shima Maheer ɗin baiyi magana ba a tunaninsa mitar Anam ce ta sashi canja shawara. 

      Gidan su Anam ɗin ya fara tsayawa, sai dai bai shiga da motar ba yay parking a ƙofar gate. Kusan atare suka fito shi da Maheer. Maheer ɗinne ya buɗe mata murfin yana faɗin, “Kefa yau kin zama gimbiya sai dai a ɗaukeki ko?”.

       Kanta ta jinjina masa tana murmushi duk da hango mugun kallon da Shareff ya watso mata. Tana ƙoƙarin miƙa masa hannu duk da tsokanarsa dama tai niyyar yi su Abie suka fito shi da baƙon abokinsa da suka jima basu haɗu ba. Hannun Maheer ya janye ya nufi su Abie ɗin kamar yanda Shareff yayi. Abie dake kallonsu fuska ɗauke da murmushi ya riƙo hanunsu su duka yana kallon abokin nasa. “Waɗan nan yarana ne, Babana Al-Mustapha muna kiransa Shareff. Architect kuma Shugaba mai mallakin companyn da nake maka bayani, sai Barrister Maheer”.

      “Masha ALLAH yaran albarka”.

Murmushi duk sukayi suna mai rissinawa da gaishesa. Ya amsa cike da kulawa yana riƙo hannayensu shima. Albarka ya dinga saka musu kafin ya juya ga motarsa dake fake a gefe yana faɗin, “Ato ga ɗan uwanku ma ai tare muke da shi sai ku gaisa ko”.

       A tare duk suka kalli motar, dai-dai da fitowar Anam daga mota itama cikin matuƙar son nuna dauriya sai dai ta kasa taka ƙafar ta nema zubewa. Da sauri Shareff ya nufeta saboda ratsa kunuwansu da siririyar ƙararta tayi, ya riƙota dai-dai ta kusa kaiwa ƙasa. 

    “Ance ki fitone?”.

“Nifa na gajine ga zafi a motar”.

Kamar zaiyi magana sai ya fasa saboda idanun su Abie dake kansu, yayinda kunnuwansu ke jiye musu bayanin da Maheer ke musu na cewar ciwo taji a ƙafa.

          Ƙoƙarin ɗaukarta Shareff ɗin yake yi tai saurin ja da baya cikin zare idanu da bugawar ƙirji sakamakon ganin wanda batai zaton gani ba. 

    “W...waya kawoka gidanmu?”.

Ta faɗa idonta kar a kansa kamar yanda shima ita ɗin yake kallo. Su kuma su Abie su dukan suke kallo. Tattausan murmushi ya saki yana mai janye idanunsa cikin na Shareff da yay wani irin mugun kicin-kicin da fuska, akan fuskarta ya maida cikin ɗaga kafaɗa yace, “Ina tare da Daddyna ne. Amma badan nasan nanne gidanku ba Beauty ”.

        Sau ɗaya ta kalli abokin Abie ɗin ta maida kanta ta duƙar. Cikin sake faɗaɗa murmushi Alhaji Abu kalla ya dubi ɗan nasa da ƙyau. Kansa ya shafa yana mai kauda kai da sakin ƙaramar dariya. Alhaji Abu Kalla yay ƙaramar dariyar shima da ɗauke idonsa ga ɗan nasa ya maida ga Abie da shima dai murmushin yake da sonjin ƙarin bayani..........✍


_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_18_*


..........Sosai idanunta ke faman marmari ga ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a cikinsu. 

      “Juwairiyya!! Wlhy! wlhy! daga yau na sake ganin yaron nan ko wani ya ɗaukeki a motarsa koya kaiki gida sai na miki mugun dukan da zaki kasa tashi, kuma ki koma gidana da zama stupid kawai”. Ya ƙare maganar da ture fuskar tata gefe. 

     So take ta fashe da kuka amma tana ƙoƙarin son dannewa, sai dai hakan bai hana rawar jikinta bayyana ba. A tsawace ya sake faɗin, “Get out of my car! Kafin na marmashe ƙashinki anan stupid”.

     Da sauri ta ɓalle murfin ta fice tamkar mai jiran umarnin nasa dama. Yaja dogon tsaki da figar motar yay gaba, badan titi bane da sai ya bula mata ƙura, murfin ma sai da yay gaba kaɗan yaja abinsa ya rufe.

     Duk yanda taso ƙoƙarin danne komai hakan ya gagara. Dole ta samu wani dutse a gefen titin ta zauna ta fashe da kuka. Duk abinda kaga Anam ta zauna yima kuka lallai ya taɓata sosai, dan tsiwarta da giringiɗishi bai cika barinta maida abu serious ba, ga kuma yanayin rayuwar data tashi a ciki, ita kaɗai a gidansu sannan a ƙasar da kowa kansa ya sani kawai.

     Ring da wayarta ta farane ya sata share hawayenta ta daga dan tasan su Mamie ne, a kullum tana waya dasu a irin wannan lokaci da kuma in zata kwanta. Video call ne, dan haka ta shiga son ɓoye damuwarta da murmushin farin cikin ganinsu. “Good morning my sweetheart”.

        Dukansu babu wanda ya amsa mata, dan duk da ƙoƙarin da take na ɓoyewa idanunta sun tabbatar musu tayi kuka. Abie yaja numfashi a hankali yana sake kafeta da ido. “Mamana mi yake faruwa da ke? Waya saki kuka? Ko baki da lafiyar ne har yanzu? A ina kike nan?”.

      A karan farko ta saki murmushi dan jin tambayoyin mahaifin nata a jajjere. Samun kanta tai da kasa faɗar gaskiya duk da ƙarya ko ɓoye-ɓoye ba halinta bane, ta sake share hawayen da suka ciko mata ido tana murmushi, “Abie ba komai fa, kawai kewarkuce har yanzu ALLAH. Kuma a wajen aiki nake ban dai shigaba ka gani”. Ta juya masa wayar yanda zai iya hango gate ɗin wajen.

     A jiyar zuciya suka saki shida Mamie, kafin su shiga lallashinta duk da ita Mamie a ranta bata gama yarda da cewar har yanzu kewar tasu bace. Amma sai ta barta a hakan dan tasan Anam da rashin ɓoye-ɓoye koma miye wataran da kanta zata sanar musu. Sai da suka tabbatar sun sakata farin ciki tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ba sannan sukai mata sallama Mamie na faɗin ta gaida mata Yaseer. Farin cikin waya da iyayenta ya taushe abinda Shareff yay mata ta shiga wajen aikinta da walwala kamar yanda ta saba ko yaushe.


      *_MALAYSIA_*


    “Humairah waye naji kina faɗin Mamana ta gaida miki?”.

     Cikin rashin damuwa Mamie tace sirikinka ne duk da dai naga ɗiyar taka bata son a gane hakan.....”

     Cikin sauri ya ɗago yana kallonta, har ya kasa dannewa sai da ya ambaci “Suruki kuma?”.

          Ƴar dariya Mamie tai, “Eh bashi kake fatan ganiba daman?, bayan shi ma ai akwai wasu. Yaron nan Muzzaffar da kuma wani abokin Shareff Jamal. Amma naga hankalinsu yafi zuwa ɗaya da Yaseer ɗin nan kamar”. 

       Jin shiru baice komaiba ta ɗago ta kallesa, kallonta yake kamar mai nazari ko tunani, ta ɗan taɓashi, ajiyar zuciya ya sauke. “Abien Anam akwai matsala ne?”.

      Kai ya ɗan jinjina mata yana gyara zamansa, “Babbama kuwa Humairah, miyasa tun muna Nigeria baki sanar min hakan ba.”

     Sosai maganar tasa ta  sakata kafesa da ido dan mamaki, amma ta kasa cewa komai. Fahimtar hakan ya sashi jinjina mata kai, “Basai kin tambayeni komai ba Humairah, amma idan lokaci yayi ko baki tambayeni ba zan baki amsa da kaina”.

   Gaba ɗaya kanta ya ƙara ɗaurewa ita kam, sai dai rashin sabo dayi masa dagiya yasa ta kasa cewa komai ta bisa da kallo kawai ganin ya miƙe yana kai waya kunensa. Yana gab da shigewa ɗakinsa taji ya ambaci sunan Yaya (tasan Daddyn Shareff yake kira da hakan). Jitai kamar ta tashi ta bisa amma sai ta dake kawai, zata bisa a sannu dan tasan dalilinsa na son hana Anaam ɗin tsayawa da samari bayan kuma duk fatansu kenan ita da shi tunkan ta wuce Nigeria.....


   ★★★★

  

        Sauraren sakatariyarsa kawai yake batare da yana fahintar abinda take faɗa masa ba, idanunsa ma gaba ɗaya nakan kula ɗin daya shigo dashi, wadda baya raba ɗayan biyu Anam ce ta manta ta...

     “Kinga jeki zan nemeki”.

Ya faɗa cikin katse sakatariyar da ke faman zuba bayani cike da yanga da kwarkwasa. Bataso hakan ba, sai dai sanin shi sam baya wasa yasata bin umarninsa. Sai da ta fice da kusan minti ɗaya ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi, yakai bayansa kwance jikin kujerarsa yana mai lumshe idanu. kusan mintuna uku ya ɗauka a hakan kafin ya bude idanun, kular ya ɗauka ya buɗe. Ya tsirama abinda ke ciki idanu tamkar mai irgawa ko lissafa abinda aka sarrafashi da shi. Abincine irin na ƴan ƙasar malaysia, shima yana bala'in son sa a lokacin da ya rayu acan, ko yanzu kuma da yake a Nigeria yakan je takanas ya siya a inda yasan zai samu. Hannu yakai ya ɗauka spoon ɗin dake ciki ya ɗiba dan tabbas wannan ɗin da gani an masa haɗi da girki na musamman ne. Sosai ya lumshe ido lokacin da yake taunawa, koda ya haɗiye sai ya sake ɗiba yakai baki, kamar da wasa sai gashi ya cinyesa tas dan dama bai karyaba ya fito gidan, shayi kawai ya sha, shima sai da Fadwa ta ɓata rai dayin korafin ganin saurin da yake faman yi duk da ta fahimci shi mai fitar wuri ne office sannan ya sha a tsaitsaye ya barota tana tura baki gaba.......

      Shigowar Fharhan ta sashi ture kular gefe yana goge bakinsa da tissue. Fharhan dake kallon kular da murmushi ya kai zaune yana faɗin, “Ɗan gatan madam, abincin ma sai an baka kazo office kuma ba gayyatar masu tayaka ci ka kulle office kai kaɗai”.

     Murmushi kawai yay yana miƙa masa hannu sukai musabaha. “Kai ka cika sa ido wlhy, ka hucema kanka takaici kai auren kaima sai a ringa baka kana zuwa da shi kana hanamu”.

       “A'a karka damu alhaji, ai abun bana gori bane muna hanya da iznin ALLAH”.

    “Haka muke so ai muma. dan kun ishemu a tituna”. 

        Dariya sosai Fharhan yake da maganar ta Shareff, yace, “Kaima yaushe kabar titin. Ba komai zan rama”.

          Shima ƴar dariyar yayi. Cikin komawa serious yace, “Yanzu nake duba saƙonka ta email ai. Mutanen nan ya zasu mana haka kuma?”.

    “Wlhy nima abin ya ɗauren kai, jiya badan karna takurakaba da a daren zanzo na sameka gida tun shigowar saƙonsu, na kira wayoyinka kuma duka switch up”.

            “Mtsoww! Kabari kawai, wlhy ban san madam ta kashesu ba sai da asuba na gani. Amma gaskiya abun nan nasu yayi tsauri, anya kuwa bazamuce mun janye ba”.

     “Amma janyewar sai nake gani kamar akwai matsala Musty. Sakamakon company na buƙatar babban aiki irin wannan a halin yanzun, na biyu mun riga munyi zama da su har munyi signing akan agreement ɗin, kasan kuma turawan nan dai musamman chines ɗin nan da basa wasa da damarsu”.

      Huci ya ɗan furzar yana mai komawa jikin kujera ya kwanta. Har ga ALLAH abubuwa masu yawa ne ke masa kaikawo a cikin rai. Amma duk sai ya haɗiye abunsa yana sake fuskantar Fharhan dake kallonsa. “Ni gaskiya da tafiyar ta zama nine dole zanyi shine matsalata Fharhan”.

      “Oh saboda amarya?”.

Hararsa Shareff yayi, “Ko saboda ita ma ɗin ai inada hujja”.

   “hhhh hakane ango kafa ɗan ɗana. To mizai hana kaje da ita kawai”.

            “Zan so hakan nima, sai dai bazai yuwu ba”.

    “Mi yasa?”.

Shiru kamar bazai amsa ba, sai kuma ya girgiza kansa da furzar da iska ya sake komawa jikin kukera ya kwanta yana ɗan juyata. “Ina hasashen Fadwa nada shigar ciki, sai dai ko ita kanta bana jin ta sani. Yin tafiya da ita a irin wannan gaɓar zai iya zama haɗari”.

         “Masha ALLAH! Alhmdllhi. Lallai wannan angon da gaske sharp shooter ne. ALLAH ya inganta mana”.

      Shareff ya ɗan murmusa da faɗin “Amin” akan laɓɓa. Cigaba da tattaunawa sukai, daga ƙarshe dai shawara ta zauna akan shi zaiyi tafiyar tunda dai wata uku ne kawai insha ALLAH. 

       Bayan fitar Fharhan ya buƙaci shigowar sakatariyarsa, daga haka ya cigaba da ayyukansa har zuwa lokacin break....


        ★★★★


  Duk da bata ɗauki gargaɗinsa da muhimmanci ba sai ta kasa sakewa da Yaseer gaba ɗaya yau. Kullum shike fita da ita su ciyo abinci a inda yasan za'a samu abinda take iya ci. Amma yau saita ɓoyema ganinsa. Daga salla ta maƙale a massallaci taƙi fita. Sai ma ta ɗauka alkur'ani tahau karantawa.

       Sai da ta daidaici lokaci yaja sosai sannan ta fito. Kamar jira tana fitowar wani abokin aikinta yazo ya sanar mata tana da baƙo. Da mamaki take kallonsa dan bata tunanin wani zai iya zuwa wajenta a yanzu. Daga Muzzaffar har Dr Jamal bata tunanin ganin wani anan, garama Muzzaffar yakan zo idan ya daidaici sun tashi yace zai ɗauketa sai dai bata taɓa yarda ba. Kamar bazata je ba sai kuma taga gara taje dai taga wanene.

        Turus tayi lokacin data iso taga mai kiran nata, zaune yake a cikin mota sai dai ƙafarsa ɗaya na waje dan ƙofar a buɗe yake..........✍🏻_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_19_*


.......... Ɗagowa yay daga latsa wayar da yake yana kallonta, dan ƙamshin turarenta da takunta ya sanar masa da zuwanta duk da ta kasa magana. Idanunta ta ɗauke daga kallonsa tana faɗin “Good Afternoon”.

           “Ni kike ma gaisuwa kina juyar da fuska?!”.

    Juyowa tai Idanu cike da ƙwalla tana kallonsa. “Ni wlhy Yaya ban san mina maka ba duk kabi ka tsaneni ka takura ni. Komai nayi a duniyar nan a wajenka ban iyaba”. Ta ƙare maganar da sakin siraran hawaye.

         Kallonta kawai yakeyi ko ƙyaftawa babu. Ji tai kallon ya sake saka mata jin haushinsa, juyawa tai da nufin barin wajen..... 

     “Kika bar wajen nan sai ranki ya ɓaci”.  

    Idanunta ta rumtse tana jin wasu zafafan hawaye da sukafi na farƙo na neman kufce mata. Ita kam ta rasa mita tsarema bawan ALLAHn nan a duniya, tana fatan watanin nan bakwai da suka rage mata su maza suzo ta kammala abinda ya kawota tabar ƙasar nan, dama tun farko abinda ta gujemawa kenan amma su Mamie suka kasa fahimtarta. Haɗiye hawayen tai batare data barsu sun zubo ba sannan ta juyo garesa, yana a yanda yake har yanzu, sai dai idanunsa masu kwarjini da kaifin dake hana ƙarfin halinta tasiri na nan tsaye kanta ƙyam har yanzu. Kasa jurar kallonsa tai, tai ƙasa da nata, shima sai ya janye nasan, juyawa yay kujerar gefensa ya ɗakko ledar dake ajiye. Miƙa mata yay kansa tsaye.

     Ledar ta fara kalla tare da hanunsa dake ɗaure da agogo da zoben azurfarsa da ya jima yana birgeta, har addu'ar damar sace zoben ta taɓa yi a zuwa na karshe da tai kafin wannan.... Saurin ɗagowa tai tana kallonsa jin ya kamo hanunta cikin nasa, ya wani sake ƙanƙance idanu cike da salon kallon da a duk sanda ya jefeta da shi yake firgitata, ta fara son zame hanun a hankali dan gaba ɗaya lakar jikinta neman daina aiki takeyi, kanta ta fara juya masa tamkar mai ciwon wuya, tana son zare idanunta daga cikin nasa amma yaƙi bata damar hakan nan ma, sai kawai ta sakar masa kukan karya.

    Hanun nata ya saki a hankali bayan ya saka mata ledar, kamar wadda ake control da remote fitt ta ɓace a wajen. Tsabar sauri har tintiɓe tayi ALLAH dai ya taimaketa bata faɗi ba ta dafe gate.

           Murmushi ya saki mai ɗan sauti daga ƙirjinsa yana kauda kansa. Ya maida ƙafafunsa cikin motar tare da rufeta yabar wajen.


        Itama koda ta shiga sai da ta samu jikin wata mota ta huta tare da share hawayen ƙaryarta sannan ta buɗe ledar. Shawarma ce da ice-creem sai yogurt da robar ruwa. Haka kawai sai kuma ta samu kanta da sakin murmushi. A fili tace, “Ga rashin mutunci ga kirki idan yaso”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi dan haka kawai drama ɗin tasu ta yanzu take maimaita kanta a zuciyarta tana saka mata nishaɗi. 

       Yau kam tayi aniyar kozai daketa bazata yarda tabi motarsa ba, dan haka kawai ragwantakar data nuna ɗazun a gabansa ke hanata sukuni, sai dai murmushi ya kasa barin fuskarta har Yaseer sai da ya kasa haƙuri ya tambaya. Ƴar dariya kawai ta masa batace komai ba. Ana tashi itace farkon fitowa, bata son bin Yaseer ɗin badan tana jin tsoron tabbatar hukuncin Yaya Shareff ba, ba kuma ta buƙatar shiga tasa motar shima gara ta hau napep. Sai dai kuma cikin rashin sa'a tana fitowa taci karo da motar tasa a wajen gate, kuka kawai ya rage ta fasa ta huta, tai tsaye ta kasa matsawa ga motar har tsahon wasu sakani. Sauke glass ɗin da dariyar Khaleel ta sata sakin ajiyar zuciya, dan tunda ta fito idonsa a kanta. “Ai ba mai motar bane sai ki taho mu tafi farar kura kawai”.

     “Humm ALLAH Yaya bazaka ganeba. Shi Yaya Shareff ɗinne ya cika takura da hana mutane sukuni suji daɗin rayuwa”.

          “Maybe yana tsare mutuncin kayansa ne kar kiga laifinsa”.

 Bata wani gane mi Khaleel ɗin ke nufi ba, saboda da hausa yay maganar ta buɗe ta shiga tana dariya kawai. Shima yasan bata gane ɗin ba dan haka ya dara.


____________________________


        Tun daga waccan ranar Anam ta sake kafa wasan ɓuya da Yaya Shareff, motar Khaleel ta samu matsala, sai kawai ta koma bin school bus na yaran gidan. Kasancewar suna fitar sassafe kafin Shareff daya tsiri zuwa gidan da safe ya iso har sun wuce. Ana tashi kuma zatai wuff ta fito ta tari napep. Motar Yaseer ma dai ta daina shiga duk da yata bibiyarta da son jin ba'asi tana tabbatar masa babu komai.

     Samarinta biyu da sukafi takurama rayuwarta taga sun rage manne mata. Dr Jamal da Muzzaffar. Kowannesu kuma yanada gurbi na musamman data ajiyesa dan koba komai suna sakata nishaɗi a wasu ɓangatorin na rayuwa. Sai dai ta gagara neman jin dalilin kowannensu akan ɗan janye mata da yayi, garama Muzzaffar sukan ɗanyi waya jefi-jefi ko chart wasu ranakun.

       A gidan nasu kuwa bata da wata damuwa sai su Hussaina wataran, dan idan rashin kunyarsu ya tashi sukan mata sai dai bakinsu nashan bugu dan bata ɗaga musu ƙafa. Ta daina zuwa gaida Mommy da Gwaggo sai in ta ritsa sun haɗu a hanya taita sinne kai wajen gaishesu. Ko kallonta basayi, dan a ganinsu ma ƙin zuwa gaishesun ta taimakesu koba komai sukan manta da wanzuwarta a gidan. Hakan baya damunta, takan wataya tsakanin sashen aunty amarya da Mom abinta. Ita da Aysha da sauran yaran gidan kuwa sai sambarka. Hakama Daddy da Abbah a koda yaushe cikin bama rayuwarta kulawa suke fiyema da yaransu, dan kullum da tsarabar da waninsu zai kawo mata gidan da kuma mata nasihar tsare mutuncinta suke.

        Kusan kwanaki goma kenan basu haɗu da Shareff ba, sai a yau da akai sa ranar auran Maheer da sam bata san da zancen auren ba sai da taga akwatina a sashen Mom akace na auren Maheer ne yau za'a saka rana da kai akwatinan. Tayi mamaki sai dai batace komai ba, sai daga baya Aysha ke bata labarin ai Maheer ɗin baya son auren Mommy ce ta takura kamar yanda ta takurama Shareff shima. Auren zumincine da ɗiyar ƙanwarta. Sosai Anam taita mamakin hali irin na Mommy, a ganinta ta cika takurama ƴaƴanta a gidan, musamman Yaya Shareff da Yaya Maheer ɗin. Gashi suna mata matuƙar biyayya fiye da duk sauran yaranta, dan tasha ganin Mommy nama Aysha da su Hussaina faɗa suna ƙunƙuni. Itace ma kema Aysha faɗa da nuna mata illar hakan ga iyaye. Sai kuma gashi masu mata biyayyar sunfi shan wahala a hanunta fiye da su Ayshan da sai abinda suke so sukeyi.

       Batabi takan duk hayaniyar da ake a gidan ba, kasancewar ma a sashen Mom baƙin da zasuje kai kayan suke isowa, saita fito domin wucewarta sashen aunty amarya ta huta dan asabar ne. Kamar ta juya taji, lokacin dataga motarsa na ƙoƙarin yin fakin gab da sashen Mom ɗin, amma sai ta dake ta fuske zata wuce abinta.

       Siririn tsakin da taji anyi dai-dai zata gitta ya tilasta ta juyowa, dan sam baiyi kama da tsakin Yaya Shareff ba. Fadwa ce a tsaye cikin shigar madam getzner shadda da taci uban aiki sai walwali take, tabbas tayi ƙyau sosai. Anam ta sakar mata wani murmushin ƙularwa da kashe mata ido ɗaya ta cigaba da tafiyarta. Kusan ɗan cin karo sukai da Shareff daya zagayo waya manne a kunensa yana magana. Shima dai sanye yake cikin shaddar fara tas datai masa ƙyau da fiddosa a asalin bahaushensa ɗan arewa dan harda hula. Ta ɗan ja baya yayinda shi kuma ya tsaya cak dan gaba ɗaya hankalinsa akan waya yake baima san wainar da suke toyawa da Fadwa ba. Kallonsa tai tana wani ƙyaƙyƙyafta idanu, sai kuma ta tunzura baki gaba ganin kallon nata da yakeyi shima tamkar idanunsa zasu cinyeta. “Good morning”. Ta faɗa tana gittasa da ƴar sassarfa.

      Cikin basarwa ya cigaba da wayarsa, hakan sai yayma Fadwa data tsaresu da idanu daɗi harda matsowa zata rungumesa ya kauce mata yana nuna mata sashen Mom. Cikin shagwaɓa tace, “Ni dai ka gama mu shiga tare ALLAH kunya nake ji”. 

    Sarai yasan ƙarya takeyi, amma sai baice mata komai ba har ya kammala. Gaba yay ta bisa a baya....


       Bata buƙatar zaman tunanin abinda ya shafi waninsu, dan haka tai connecting bluetooth ɗinta ta manna a kunne. A hankali takai kwance bisa grass carpet dake a ɗan ƙaramin garden ɗin dake bayan ɗakin aunty amarya tana lumshe idanunta cike da nishaɗi, dan waƙar da take saurare tana matuƙar sonta, mawaƙin ɗan ƙasar malaysia ne, waƙar ma anyitane da yaren malay sai dai an cakuɗa da turanci. Tayi nisa sosai wajen sauraren waƙar fuskarta shimfiɗe da murmushi, ga idanunta a lumshe sanyin inuwar wajen na ƙara girmama nishaɗinta, bakinta sai motsawa yake a hankali alamar bin waƙar takeyi....

       Jin ƙamshinsa ya ƙara ƙarfi cikin hancinta ya sata kasa cigaba da jurewa ta buɗe ido a hankali batare da tabbacin mai ƙamshin bane a wajen. Sai dai kuma cin karo da shi ɗin tsaye ya sakata ɗauke numfashi na wucin gadi. Da sauri ta tashi zaune duk tana jinta a daburce, hijjab ɗinta dake gefe ajiye ta ɗauka ta rufama jikinta dake sanye da wando three quarter da top ƙarama, zafine ya isheta ta sakasu kasancewar a ɗaki take, sai da taji hayaniyar mutane zasu dameta ta sako hijjab kawai ta fito, ganin babu kowa anan ya sata cirewa ta ajiye dan ta samu iska mai ƙyau ta shigeta. 

        Rigarsa ya ɗan tattare sama ya zauna shima bisa grass carpet ɗin dake a share tas dan aunty amarya kullum cikin kulawa take da wajen saboda tsananin son garden da takeyi. Mace ce ƴar gaye mai son hutu da gudun yawan hayaniya. Duk da Anam taji wani irin da zaman nasa wajen amma sai ta dake abinta. Sai dai ta kasa cigaba da bin waƙar daketa maimaita kanta. Shima da tun zuwansa wajen baice komai ba kallonta kawai yayi na wasu ƴan sakanni, sai kuma ya kai hanunsa kunnenta ya zare bluetooth ɗin ya saka a nasa kunnen. Juyowa tai tana kallonsa da mamaki, ya lumshe idanu ya buɗe tare da kauda su a kanta yana sauraren waƙar.........✍_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

0913484810_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107 ko

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_20_*.........“Waye mawaƙin nan?”.

       Cikin shakku da mamakin ta kallesa. Ganin zai kallota tai saurin janye idanunta a kansa, ta bashi amsa cike da basarwa.

       Ɗan Murmushi yayi dan ya riga ya ganta. “Ya iya waƙa gsky, kuma cikin nutsuwa da ma'ana”.

     Itama Murmushi tai a karon farko tana dubansa. “Shiyyasa nake son waƙoƙinsa sosai nima ai. Bashi da hayaniya, sannan duk abinda zai faɗa yakan dace da furicin zuciyoyi”.

         Tsareta ya ɗanyi da idanunsa, hakan yasa ta kauda nata. “Wane furucine ke dacewa da ma'anar zuciyoyi?”.

     A yanda yay tambayar tamkar mai raɗa ya sata juyowa ta sake kallonsa, sai kuma ta janyesu har yanzu murmushinta bai ɓace ba. “Yaya bai zama lallai tunanina dana kowa yazam iri ɗaya ba ai, zata iya yuwuwa nice kaɗai ke fassara haka ko fahimta a lokacin da nakejin waƙoƙin nasa”.

      “Uhhm nice. Kinga nima sai ki turamin maybe na fahimci irin taki fahimtar ko! Ki samun duka waƙoƙin sa ta WhatsApp”.

           “To ai bani da number ka”.

     Cikin ido yake kallonta, ta risinar da nata dan bazata iya jurewa ba. Shima sai ya ɗauke nasa ya maida ga tsuntsaye biyu dake shan ruwa a ɗan kaskon da aunty amarya kan zuba dan su. “Baki so hakan bane shiyyasa baki da ita”. 

     Murmushi kawai tayi, amma batace komai ba, ta dai cigaba da kallon tsuntsayen kamar yanda shima har yanzu idonsa na kansu. Shiru kusan mintuna uku, tashin tsuntsayen ya sashi katse shirun nasu da faɗin, “Zanyi tafiya zuwa China, kuma zan jima dan zan samu a ƙalla kwanaki ɗari acan ko ƙasa da hakan insha ALLAH”. 

       Mamakinsa ya sata ɗagowa ta dubesa, kasancewar nasa idon na kanta ya sashi ɗan lumshewa alamar tabbatarwa... Bata da zaɓin daya wuce kaɗa masa nata kan itama. “ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada abinda za'aje nema mai albarka. Ya tsareka daga haramun, ya haɗaka da halal”.

     Ajiyar zuciya yaja mai ƙarfi, har takai ta sake ɗagowa ta kallesa, murmushi ya sakar mata, irin wanda zata iya rantsewa bata taɓa cin karo da shi a gareta ba. Ta ɗanyi tsammm tana kallonsa, gaba ɗaya ganin al'amarin nasa take na yau kamar almara. Lakace mata hanci da yay ya sata saurin ɗauke kai cike da kunyar kanta. Ya ɗan murmusa yana gyara zamansa. “Zaki koma gidana k da Aysha ku zauna har na dawo”.

       “What! Yaya ni ɗin?”.

   A yanda tai maganar ya sashi kafeta da idanunsa sosai. “Bazakije ba kenan?”.

     Fuska ta ɓata da tura baki gaba, “To ai ni dai kasan bama shiri da matarka”.  

     “Idan kikaje zama yanzu ai sai ku fara shirin kafin na har abada”.

Ba wani fahimtarsa tai sosai ba saboda da hausa yay maganar, amma sai ta girgiza kanta. “No bazamu taɓa shiri da matar can taka ba. Dan nama kusa fara kai mata naushi idan tana cigaba da min kallon banza. Karta ɗauka tsahonta da girman jiki zai razana ni”.

      Yanda take maganar cike da masifa da tsiwa ya bashi dariya sosai. Ya kauda kai gefe yana murmushi. Kafin ya sake juyowa fuska a haɗe yana kallonta. “Matar tawa zaki nausa?”.

    Batace komai ba, sai dai ta sake tura baki gaba. Zaiyi magana ring ɗin wayarsa ya dakatar da shi, Mommy ce, dan haka yakai kunne cike da ladab yay sallama. 

     “Kana ina ne wai Shareff? Ga matarka sai amai take anan duk ta galabaita kazo kuje asibiti”.

          “Ya ALLAH!”.

    Ya faɗa a hankali yana lumshe ido. “Okay Mommy ina zuwa. Amma bara na kira Jamal kin san yau weekend ne ba lallai mu samu yanda muke so a asibitin ba”.

    “To ya hanzarta dan ALLAH”.

“Okay bara na kirasa ɗin”.

     Koda ya yanke wayar kasa haƙuri Anam tayi, dan bata san wa akace baida lafiyar ba. “Yaya waye za'a kai asibiti?”.

            Yana ƙoƙarin kiran Dr Jamal ya bata amsa kai tsaye. “Fadwa ce keta amai wai, duk ta galabaita”.

    Sosai ta nuna jimaminta kasancewarta mutum mai tausayi. “Ayya ALLAH ya bata lafiya, dama bata da lafiya kuma ka yarda ta fito Yaya?, ai da ka barta a gida tunda kowa yasan ciwo”.

         Numfashi ya ɗan furzar, rashin ɗaukar wayar Dr Jamal ɗin ta bashi damar bata amsa. “Bawai kwance take ba, yanzu ma inaga taji ƙamshin abinda bata so ne shine aman yazo”.

      Kallonsa tai cikin mamakin amsar tasa, sai dai kafin tace wani abu kiran Mommy ya katseta. Ɗagawa yay yana mikewa. “Mommy na kira bai ɗaga ba maybe baya kus... Yauwa gashi ma yana kira ina zuwa”. Yankewa Mommy tai, shi kuma ya samu damar ɗaga kiran Dr Jamal ɗin. Ya ɗan matsa da ga wajen Anam ɗin suna magana. Da kallo ta bisa, sai kuma ta ɗan ɗage kafaɗa da ɗauke kanta cikin ɗan taɓe baki. Hijjab ɗin da taketa faman ƙudundune jikinta ta warware ta sanya da ƙyau itama ta miƙe da nufin komawa sashen aunty Amarya tai kwanciyarta kawai ko ɗan chart tayi da ƙawayenta na Malaysia.

      Ya gama magana da Dr Jamal ya juyo kawai ya hangota har takai ƙofar baya ta kitchen ɗin aunty amarya. Idanu ya tsira mata harta ɓacema ganinsa. Ya ɗan ja numfashi tare da barin wajen shima.


★★★


     A sashen Mommy Fadwa sai sake langaɓewa take ganin yanda Mommy da Mamah suka rikice. Dan itama Mamah (Gwaggo Haliman) tazo wajen saka ranar ta Maheer. A haka ya shigo ya samesu zagaye da ita. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana miƙa masa hannu wai itafa yazo zata mutu. Cijewa yay yayi kamar baiga hanun da take miƙo masa ba, koba komai ai sa raga dan iyayensu. Sannu yay mata tare da zama yana gaida Mahmah. Cikin kulawa ta amsa masa itama. “Dama bata da lafiya ne haka Babana?”.

     Ɗan duban Fadwan yayi ya janye idanunsa. “No Mamah bawai tana kwance bane, kawai dai idan taji ƙamshin abinda bata so ne take amai, amma baima taɓa kaiwa kamar na yau ba”.

    Kallon juna Mamah da Mommy sukai, kowanne zuciya cike da son ƙarin bayani, sai dai sun san ba lallai su samu daga Shareff ɗin ba bara kawai su jira zuwan Jamal. Babu ko wani jimawa Jamal ya iso, Shareff ɗinne ya fita ya shigo da shi. Bayan ya gaishesu ya ɗan yima Fadwa tambayoyi tana amsa masa da ƙyar. Da ga ƙarshe ya bata tsinken gwaji.

     “Inaga yi amfani da wannan mugani ko abinda nake zargi ne. In ba shi din bane sai na ɗeba jininki”.

   Mommy ce ta amsa, ta kamata suka shiga toilet ɗin nan cikin falo. Bayan wasu mintuna suka kawo masa tsinken kamar yanda ya bukata. Murmushi ya saki yana mai kallon Shareff cikin ido, ya ɗauke kansa da maidawa gasu Mommy. “To inaga ma basai ta kaimu da gwajin jininba a yanzu-yanzun, dan abinda nake zarginne dai. Ko zuwa monday zata iya zuwa asibiti ta sameni ALLAH ya inganta ya ƙara lafiya. Bara na bata wannan maganin zai sa ta ɗan samu nutsuwa daga galabaitar da tai nayin aman”.

      Sosai bakunan su Mommy yake a washe, yayinda su Hassan suka cika falon da ihun murna suna faman rungume Fadwa. Shi dai uban gayyar tuni sun fice shi da Dr Jamal, sai dai har cikin ransa yaji daɗi duk da ya jima da zargin hakan a ransa. Dr Jamal ya sake masa Congrat, cikin tsokana yana faɗin, “Lallai abokina ka zama namijin duniya, irin wannan bugu na daga kai sai mai tsaron gida haka. ALLAH ya inganta mana”.

      “Ɗan iska kaji da shi dai. Yanzu ina ka nufa?”.

    “Gida ya kamata na koma, amma tunda ka kawoni nan nima bara naima tawa flower ɗin barruwa”. Ya ƙare maganar yana laluben number Anam. Sarai Shareff ya fahimcesa, dan haka baice komaiba sai ma basar da zance yay kamar baiji ba. Kusan sau uku yana kira ba response, ya ɗan ɗage kafaɗa yana duban Shareff. “Musty inaga yarinyar nan bata kusa da wayar. Bara kawai na wuce na dawo taɗin dare. Yaushe ne tafiyar taka jibin?”.

       “Zan wuce da safe ne dan zan fara shiga Abuja, da ga can zan wuce”.

    “Okay to da yamma zan shigo gida insha ALLAH”.

    Sallama sukai ya wuce, shi kuma ya koma wajen su Mommy da suka dasa sabuwar tarairaya ga Fadwa.


        Dawowar ƴan kai kaya da saka rana ta sake baje labarin cikin Fadwa a gidan. Kowa sai sambarka da fatan saukarta lafiya yake. Gwaggo harda ƴar rawarta. Shi dai Shareff tuni yama bar musu gidan, sai yamma ya dawo suka fita salla da su Daddy. Bayan sun dawo ma tare da su yaci abinci. Ya ƙara tattauna batun tafiyarsa da su, daga karshe suka sakko masa zancen matarsa fa? Nan zata dawo da zama ko gidansu tunda dama ba daɗin jikinta take ji ba dan suma labarin ciki har yazo musu.

      Ajiyar zuciya ya ɗan sauke. Kansa a rissine yace, “Da dai tayi zamanta kawai acan ɗin, nayi magana da Khaleel zai koma kwana acan, Aysha da Anam sai suje suma su tayata zama tunda bawani abu suke anan ɗin ba”.

       Abba dake murmushi yace, “Hakan ma yayi to. ALLAH ya baka sa'ar abinda zakaje dominsa. Ya kuma dawo mana da kai lafiya”.

      Da amin suka amsa shi da Daddy. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu batutuwan daya shafesu da kuma tafiyar tasa.


            ★★★

    Anam bata san mike faruwa akan komawarsu gidan Yaya Shariff ba sai washe gari, dan bata wani bama maganarsa ta jiya muhimmanci ba. Koda taji batun cikin Fadwa kuma batace komai ba. Tadai saka albarka a sa ranar Maheer da akace wata huɗu.

      Da yamma ta dawo aiki Mom ke sanar mata ta haɗa kayanta ita da Aysha zasu je su taya matar Shareff zama kafin ya dawo. Cikin waro idanu da mamaki take duban Mom. “Mom ni kuma? Kin san fa yanda matar nan tabi ta tsaneni ga Gwaggo da Mommy da Mamah a gefe...”

      “Anam duk na kawoma Abbanku irin wannan misalin, amma ya nuna min sun riga sun gama yanke hukunci. Kinga sai kibi umarninsu kawai ALLAH ya kaɗe fitina”..iyayenmu😭🙏🏻_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_21_*
......Sosai Anam taji kamar ta fashe da kuka. Sai dai bata iya jayayya ba. Dan haka tabi umarnin Mom bayan tayi wanka taci abinta ta haɗa kayan da basu wuci kala bakwai ba, sai abinda ba'a rasa ba. Dan tanajin da wahala zamanta yay nisa a gidan basu kwashi ƴan kallo da Fadwa ba. Aysha ce ta shogo, ganin ƴan kayan data haɗa tace bata isaba. Canja jakkan kayan tai zuwa babban akwatinta, ta dinga ɗibo kaya a wadrobe tana zubawa, duk da dakatar da ita da Anam keyi taƙi saurarenta, dan harda kayan da aka ɗinka mata da ko sakasu ta kasa farayi har yanzun. Aysha da taƙi saurarenta taja a kwatin tana faɗin, “Yaya har yazo, kiyi maza ki kammala kin san sa da azalzala”.

      Harara ta wulla mata batare data amsaba. Aysha ta fice tana dariya. Dole itama ta miƙe ta karasa kimtsa abinda ya rage mata. Sannan ta fito yima Mom sallama. A can ɓangaren Mommy sai yanzu tasan harda Anam za'a zauna gidan Shareff. Ranta ya ɓaci, dan haka kai tsaye tace bata aminceba in har itace ta haifi Shareff. Shi dai baice komai ba, sai Daddy ne yace bata isaba, idan kuma tai wasa zai matuƙar ɓata mata rai ne. Ganin sunata cacar baki Aysha taje ta sanarma Gwaggo duk da tasan itama ɗin dai sai a hankali ce. Dandanan ko sai gata tazo, da yake Aysha ta faɗa mata abinda ke faruwa koda tazo sai ta goyi bayan Daddy akan tabar Shareff ɗin ya wuce dasu Aysha dare nayi, ai zaman Anam ɗin acan ba komai bane. Rai ɓace kuma cikin mamaki Mommy take duban Gwaggo. Gwaggo ta kyafta mata ido alamar kartaji komai ta sallama. Shiru tayi kawai amma har sannan ranta na mata suya, sai dai tama ƙagara su tafin taji dalilin Gwaggon nayin haka.

       “Kai tashi ka ɗaukesu ku wuce dare nayi”. Daddy ya faɗa yana duban Yaya Shareff da kamar bashi a falon. Mikewa yay kuwa yay musu sallama. Aysha tabi bayansa suka fice. Bai shiga kowane sashe ba, dan zai dawo da safe musu sallama kafin ya fice tunda bada sassafe zai wuce ba Khaleel ne ma zai kaishi airport. Suma su Ayshan dan yana son suje tun a yau ne ya haɗasu da Fadwa yay musu gargaɗi tunda yasan da gaske za'a dinga samun saɓani ne tsakanin Anam da Fadwa. Aysha ce ta shiga ta kirawota.

        Doguwar riga ce jikinta mara nauyi, sai ƙaramin veil data yana a kanta. Tana riƙe da ƙaramar jakar data haɗa kayanta na ciki da Aysha bata kwaso ba saboda sauri. Ta gaida sa batare data kallesa ba. Ɗauke kansa yay yana amsa mata, tare da buɗe motar ya shiga. Aysha tai wuff ta shige baya, zata shiga itama ya hararesu. “Dalla malamai ni drivern ku ne?!”.

      Aysha ta tura Anam dake ƙoƙarin shigowa. “Blood kefa na barma can ki shiga”. Baki ta buɗe zatai magana ya juyo a fusace. “Bana son shashanci fa, kuna ɓatamin lokaci”. Hararar Aysha dake mata gwalo tayi, batare da tace komai ba ta zagaya ta shiga gaban ta zauna. Motar yayma key ya fice bayan sunyi sallama da maigadi.

     A hankali yake driving ɗin kamar baya so, motar shiru babu mai ko motsin kirki. Dan ita Anam ma har ta fara gyangyaɗi kasancewarta mai barcin wuri musamman idan waje da sanyi. Yanzu kam sanyin acn ke ɗibarta dama ga gajiyar aiki. Karatun alkur'ani ya kunna har suka iso, gidan shiru kamar babu kowa, sai maigadi dake sauraren taskar labarai a redio. Yayma uban gidansa sannu da zuwa bayan ya buɗe masa gate.

      Shi da kansa ya fiddo musu akwatinsansu a booth, Aysha taja ɗaya tana turama Anam ɗaya. Hamma tayi cikin ɗan layin barci ta jingina da motar tana dafe akwatin. Ita da akwatin yayma kallo ɗaya ya ɗauke kai, batare da yace komai ba ya sama motar lock da key ya ja akwatin yay gaba. Baki taɗan tunzura sannan tabi bayansu cikin ɗan layin barcinta. 

      Basu sami kowa a falon ba, hatta da tv a kashe take, Aysha ta kallesa cikin zumuɗi tana faɗin, “Yaya Aunty Fadwa fa?”.

          Gitta ta yay kamar bazai amsa ba, sai da ya kai akwatin ƙofar ɗakin da zasu zauna ya juyo. “Maybe ta kwanta, na barta kanta na ciwo”.

    “Ayya ALLAH ya bata lafiya”.

Amin ya faɗa kan laɓɓa idanunsa akan Anam data zauna a hannun kujera ta kwantar da kanta dan da gaske barcin takeji. “Ki tadata kuje ku kwanta kuma kawai”.

     “Okay Yaya sai da safe”.


   Kasancewar tayi wankanta tayi salla tun a gida suna shiga ɗakin ta faɗa kan gado tai kwanciyarta, addu'a ma sai Aysha ce ta mata tana mintsininta cikin tsokana da kiranta kasa anji sanyin ac. Hannunta ta buge, ta juya taci gaba da barcinta.


________________★


       “Gwaggo nifa wlhy duk kin sani a duhu. Ko kin mance wai yarinyar nan ce dana tsana ita da iyayenta fiye da komai a rayuwata”.

     Murmushi Gwaggo tai irin na makircinsu na tsoffin hannu. Ta dafa kafaɗar Mommy. “Daɗina dake gaggawa. Kema kin san bazan amince da zamanta can ba in babu wani abu a ƙasa. Dan haka kwantar min da hankalinki da safe zakiji komai...”

     “Miyasa ba yanzuba Gwaggo?”.

“Saboda idon mijinki yanzu akanmmu yake.” Kai kawai ta jinjina badan taji sauƙi a ranta ba. Gwaggo tai mata sai da safe ta fice tana murmushin da sam Mommy ta kasa fassarashi a kowane mizani....


      *_WASHE GARI_* 


   Shine ya musu knocking ƙofa da zai wuce massallaci da asuba, sai da ya tabbatar sun tashi sannan ya fice. Ana idarwa gida ya dawo, azkar ma sai da ya zo yayita a gida bayan ya sake tada Fadwa dake barci duk da ya tadata kafin ya fita amma bayan fitarsa ta koma ta kwanta. Tana mitar ita har yanzu kanta ke ciwo ta nufi bayi tayo alwala. Bai tanka mata ba harta zo ta kabbara salla. Bayan ta idar ta tashi ta koma gadon, a jikinsa ta lafe tare da sumbatar laɓɓansa. “Good Morning my Soulmate”.

       “Good morning wife ykk ya baby?”.

     Murmushi tai da kamo hanunsa ta ɗaura kan cikinta, murya cike da shagwaɓa tace, “Gashi har ya fara kewar Daddynsa”. Murmushi ya saki a karon farko, ya sumbaci laɓɓanta shima. Cikin ɗage mata gira ɗaya yace, “Nima cike nake da kewarsa shi da mamansa. Amma karya damu bazan jima ba zan dawo garesa insha ALLAH”. Rungumesa tai sosai, tare da fara bashi wasu zafafan salon da ya sashi biye mata. Bayan komai ya lafa tana kwance a jikinsa idanunsa a lumshe ya kirayi sunanta.

      “Uhhyim”.

  Ta amsa tana ƙara ƙanƙamesa. Cigaba yay da shafa kanta har yanzu idanunsa a rufe. “Jiya nazo da su Aysha da zasu tayaki zama. Koda wasa bana son jin wata fitina. Ki riƙe girmanki da mutuncinki. Idan naji wata fitina kezan fara hukuntawa matsayinki na babba”.

     “Insha ALLAH babu abinda zai faru, Ayshan ita da Hussaina ne?”.

   Kansa tsaye yace, “Da Anam”.

Baima gama rufe baki ba ta miƙe zumbur zaune. Shima sai ya buɗe idanu yana kallonta. Kai take girgiza masa hawaye na ciko mata ido...  “Ni gaskiya bazata zaunamin gidaba, taje kawai Aysha ta isa”. Idanunsa ya kauda yana tashi zaune ya jingina da fuskar gadon. “Karki ɓatama kanki rai a banza. Juwairiyya da Aysha zasu zauna tare dake, shima Khaleel anan zai dinga kwana....”

       “Bazai yuwu ba”.

  “Sai ki hanasa yuwuwar mu gani tunda gidanki ne”. Ya faɗa a fusace yana sauka a gadon. Da sauri ta yayibi bedsheet ta sakko tana ƙudindine jikinta a ciki tasha gabansa. “Dan ALLAH ka tsaya muyi magana. Wlhy iya gaskiyata nake gayama na tsani yarinyar nan bazan iya zama inuwa ɗaya da ita ba har abadan dan zan iya halaka ta”. Sosai yake kallonta cikin tsakkiyar ido. Ya riƙe ƙugu da dukkan hannayensa yana ƙoƙarin danne fushinsa. “Zaki iya halaka ta? To sai dai in ki halakata ɗin, dan babu fashi zata zauna anan tunda ba dake na haɗa kuɗin na gina gidana ba. Ki bari mu rabu lafiya Fadwa!!..” Ya ƙare maganar cikin tsananin zafin rai ya ɗan banjajeta ya ficewarsa.

     Zubewa tai a wajen ta fashe da kuka. Itakam ta shiga uku wannan shegiyar yarinya ta zamewa rayuwarta jaraba. Wayarta ta ɗauka tai kiran Mahmah, sai dai kuma a kashe, Mommy ta kira, bugu ɗaya ta ɗauka. Ko sallama babu balle gaisuwa ta fashe mata da kuka tana faɗa mata ita dai inhar da Anam zata zauna to sai dai ta koma gidan su. Sai da ta gama surutanta sannan Mommy tai magana..

        “Fadwa na fiki shiga ɓacin rai da zaman wannan yarinyar anan gidan, dan a daren jiya banyi barcin kirki ba saboda baƙin ciki. Amma ina son ki kwantar da hankalinki Gwaggo tace tanada plan akan zaman nata....”

      “Mommy Shi plan ɗin baza'a iya aiwatar da shi tana nan ba dole sai ta raɓu da gidana?”. 

    “Nima na faɗa miki ba son hakan nake ba. Amma mu saurari mi Gwaggon zatace zuwa anjima. Yanzu dai ki daure ranki ku rabu lafiya da mijinki bayan ya tafi anjima kaɗan zan zo gidan ai”.

            “Mommy....!”

    “Kiyi yanda nace”. 

Mommy ta tari numfashinta a fusace tana yanke wayar, dan ƙara hasalata Fadwan take ma..........✍_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_22_*


.........Kiran Gwaggo ne ya shigo tamkar tasan mike faruwa. Kamar bazata ɗagaba sai kuma ta ɗaga. Tai shiru taƙi magana. Ban san mi Gwaggon tace daga canba ta tunzura baki da faɗin, “Naji ina kwana”. Amsawa Gwaggo tai daga can sannan ta shiga gaya mata abinda yasa ta kirata. Ajiyar zuciya Fadwa ta saukea hankali da fara share hawayenta. Kamar tana a gaban Gwaggo ta jinjina kanta da yin ɗan murmushi tana mikewa bayan ta yanke wayar. A gurguje ta faɗa banɗaki tayo wanka, ko busar da kan batai zaman yi ba ta saka hula da doguwar riga ta fice. Kitchen ta shiga, ta dafa shayi da soya kwai ta haɗa kayan a tray. Sashesa ta nufa, dan dama jiya ya kwana a sashenta ne saboda ta ya buƙaci hakan. Babu kowa a falon, ta ajiye tray ɗin a centre table ta nufi bedroom ɗinsa. Shigowarta dai-dai da fitowarsa wanka. Yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Zuwa tai ta rungumesa tana kwantar da kanta a gadon bayansa. “Kayi haƙuri mijina na tuba, na fahimci nayi kuskure bazan sake ba”.

        Shiru kamar bazaice komai ba, dan yasan wannan ba kalaman Fadwa bane wanine ya bata su akan harshe. Sai dai kuma shi ba mutum bane mai son zurfafa zargi, dan haka ya kamo hanunta ya zagayo da ita gabansa. Idanu suka ƙurama juna, sai faman sakar masa murmushi take, shiko tasa fuskar kadaran kadahan. “Nace fa kayi haƙuri". Ta faɗa cike da shagwaɓa tana girgiza masa hannu. Cikin ɗan turo numfashi waje yace, “Okay fine ya wuce”. Rungumesa tai, kafin taja hanunsa zuwa gaban mirror. Da kanta ta shafa masa man a jiki tana masa duk wani salon kwarkwasa dazai sashi cire komai a rai kamar yanda Gwaggo tai mata huɗuba. Ta ɗan samu ya biye mata badan komai ba sai dan yana son su rabu lafiya. Yayi ƙyau cikin kananun kaya ga ƙamshi data feshesa da shi na tashi suka fito falo. Zama yay idonsa akan breakfast ɗin data ajiye....

      “Inaga ki kirasu mu karya gaba ɗaya, dan ina son nayi magana da ku”. Kamar zatai gardama sai kuma ta haɗiye, cikin taushin murya tace, “Amma ƙwan iya naka na soya anan fa”. 

       Yanda ta amsa ɗin shima ya sashi tausasa nasa harshen dan yana son su rabu lafiya. “Kiyi haƙuri ki soya musu suma, dan yau tamkar baƙi suke anan”. Maganar Gwaggo tasata amsawa, sai kuma sanin halinsa. Juyawa tai ta fita a sashen gaba ɗaya, ya bita da kallo harta fice. Mintunan da basu gaza goma sha biyar ba ta kammala soya ƙwan ta leƙa ta kirasu batare data yarda tako dubi sashen da Anam take ba. Itama dai Anam ɗin bata ko kalleta ba sai Aysha ce ta gaidata da tasowa ta rungumeta. Anam ta taɓe baki da sake juyar da kai tamkar bata gansu ba.

         Su suka fara shiga falon ita kuma tana biye da su a baya. Yana zaune a inda ta barsa, sai dai yanzu waya ce a hanunsa. Koda ya amsa musu sallama kuma bai ɗago ba.

     “A haɗa a dining ne?”. Ta faɗa tana kallonsa. Ɗan ɗagowa yay ya kalleta ya maida kansa, “No barsa mu zauna nan zaifi balance”. Kai ta jinjina masa. Aysha da Anam suka shiga gaishesa. Ya amsa musu da ɗan sauƙaƙa murya batare daya dubi kowacce a cikinsu ba. Saboda kar Anam ta zauna a kusa da shi Fadwa tai saurin jan hanun Aysha ta zaunar, sai ya zam sun sakashi a tsakkiya, ita kuma inda Anam take zaune sai yazam sunyi facing juna ita da shi. Haka kawai taji abun ya bata dariya, dan tana lura da sanda Fadwa taja hanun Ayshan. A zuciyarta tai dariya, a zahiri kam babu ɗigon fara'a a fuskar tata.

      Aysha ta haɗa mata shayin da ajiye mata gabanta dan taƙi taɓa komai, a hankali tace mata ‘thanks’. Ba wani iya cin komai tai sosai ba har yanzun, dan haka koda Aysha tace a saka mata ƙwai  kanta ta girgiza mata da nuna mata bread ya isa. Ɗagowa yay suka haɗa ido, lokaci ɗaya tsigar jikinta ta tashi. A hankali ta janye idanunta daga cikin nasa, shima nasan ya janye batare da yace komai ba. Fadwa kam bama ta nuna tajisu ba, sai Aysha ce tace “K kullum a baki iya cin abu ba bazaki koyama kanki ba?”. cikin yin ƙasa da murya tace, “Ni bana sonsa ne fa”.

       “To k dama indai abinci ne ai komai bakya so”.

   Hararar Ayshan tayi, batare da ta sake cewa komai ba ta cigaba da juya cokali a shayin tana tsakurar bread ɗin. Ɗagowa kam bata sake yarda tayi ba balle ta haɗa ido da shi har suka kammala. Ita da Aysha suka tattare wajen, suka kwashi kwanikan zuwa sashinta. Kasancewar yace su aje su dawo basu ɓata lokaci ba suka koma. Fadwa suka samu zaune a jikinsa, shigowarsu kuma bai sa ta jaye ba, sai shine yay mata nunin ta zauna da ƙyau da ido. Ganin yanda fuskarsa take babu wasa yasa ta matsawa sai dai ranta bai so haka ba. Oho wadda take dan itan ma bata san tanai ba, dan koda suka shigo Anam bata yarda ta kalli ko sashen da suke ba. A ƙasa suka zauna, ya fara addu'ar da MANZON ALLAH yace muyi a duk sanda muka samu kammu a irin makamancin zama haka kafin ya ɗaura da nasiha a garesu, da ga ƙarshe ya ƙare da gargaɗi mai cike da kurarin tabbatar musu in har yaji wani abun ɓacin rai daga garesu su duka ransu sai ya ɓaci, kowacce ta kama kanta, su su girmama matarsa a matsayinta na Yaya a garesu kuma matarsa, itama ta riƙesu a matsayinsu na ƙannenta kuma ƴan uwansa. Daga ƙarshe ya rufe da jawabin zaman Khaleel a gidan, sai dai shi kwana kawai zai ringa zuwa yayi sai kuma cefane da duk wasu buƙatun gidan su nemesa. Daga haka ya sake rufe taron da addu'a yana miƙama Anam kuɗi, kamar tace a'a amma sai ta amsa tayi godiya, itama Aysha kamar na Anam ɗin ya bata. Cike da zumuɗi ta amshe abinta tai godiya, daga nan ya sallamesu.


        Koda suka koma ɗaki Anam kwanciyarta tai tunda yau babu fita aiki, Aysha kam tai zaman lissafa kuɗinta dayin budget ɗinsu cike da farin ciki duk da dubu goma ne kawai. Barcinta da yay nisa ya saka har Yaya Shareff yabar gidan bata sani ba, koda Aysha ta fito masa rakkiya wajen mota dan da Fadwa zaije har airport cike da makirci Fadwan ke tambayar ina Anam. Aysha tace, “Barci take aunty ko'a taso ta?”. “A'a ki barta kawai kar'a tadata kanta yazo yana ciwo ko”. Duk yana jinsu, sai dai baice komai ba. Sai da Aysha taga fitar motar tasu sannan ta dawo itama ta kwanta dan barcinne a idonta.

        A gidan su yaja kusan awa biyu, yay sallama da kowa sannan Khaleel ya ɗaukesa shi da Fadwa zuwa airport, basu wani jima suna jiraba jirgin da zai kaisa abuja ya keta hazo. Khaleel ya ɗakko Fadwa dake hawaye yana mata ƴar dariyar tsonar shagwaɓar tata. Ganin ya nufi hanyar maidata gidanta tace ita dai ya kaita can gidan zata ɗauka abu wajen Mommy, idan ma yanada wani uzirinne ya barta zata maida kanta gida kawai. Bai ƙiba ya canja hanaya.

  

       Duk yanda Mommy da Fadwa suka so ayi maganar zaman Anam ɗin Gwaggo tace ba yau ba, ransu yaso fara ɓaci, sai dai Gwaggo ta nusar da su gaggawa ba tasu bace. Ita dai ta koma gidanta koda wasa karta nuna rashin son zaman Anam ɗin a gidan daga nan har zuwa sanda zata sanar musu abinda ta ƙulla. Fadwa bawani ta gamsu bane, dan haka batama gama sauraren Gwaggon ba ta figi handbag nata tai ficewarta. Duk da kallo suka bita, Gwaggo ta taɓe baki tana duban Mommy.

      “Idan baki tashi tsaye akan wannan surukar taki ba to lallai ina tabbatar miki nan gaba kaɗan sai tasha kanki. Dan hatsabibiyar yarinyace da kanta kawai ta sani, halinta dana uwarta bashi da banbanci”. 

     Wani bahagon numfashi Mommy taja da ƙarfi tana duban Gwaggo tamkar mai son samo ƙarin bayani akan fuskarta, Gwaggo ta taɓe baki tana miƙewa. “Kinga ni jeki kafin mijinki da shi bai rabo da zargi yasan kina nan, nima kwanciya zan ɗanyi barci bai isheni ba jiya da dare”. Da kallo kawai Mommy ke binta hartai shigewarta bedroom. Itama tashin tai cike da rashin zaɓi ta fito dan tasan Gwaggon tayi hakane dan gujema kowace irin tambaya daga gareta.

      Gwaggo dake laɓe jikin ƙofa tana leƙen Mommy ta taɓe baki, cikin ƙara yamutse fuskarta da tsufa ya gama nuna kansa tai murmushi mai cike da ma'anoni masu yawa da fahimtarta sai dai ALLAH.   


(Mi tsohuwar ga ke ƙullawa ne🙀🙀?)


    ★ A ɓangaren Fadwa kam maimakon gidanta sai ta nufi gidansu, dan ranta gaba ɗaya a mugun ɓace yake, ta tabbatar idan ta koma gidanta a haka tofa tanayin sallama jibgar Anam ce zata biyo bayanta. Mamah (Gwaggo Halima) batai mamakin ganinta ba, saboda babu jimawa suka gama magana da Gwaggo a waya, sai dai su dukansu babu wanda yay tunanin nan Fadwa ɗin ta taho. Hasalima kiranta take son yi sai gata. Kuka ta fashema Mamah da shi, dan haka ta tsaya tana kallonta kawai. 

       “Wlhy Mamah sai dai na dawo nan da zama inhar akace sai ta zauna min gida. Ai dama tun farko haka mukai da shi zan zo nan na zauna har sai ya dawo, amma yana zuwa can gidan aka canja masa tunani, ni na gane Mommy da Gwaggo duk bakinsu ɗay.....”

       “K bana son shashanci, ke ko Fadwa wai sai yaushe ne zakiyi hankali ne? Idan an faɗa miki ki dinga saurara..”

  “Mamah dan baki san abinda ke faruwa bane fa, baƙar yarinyar can ɗiyar wancan mutumin na Malaysia fa aka kawo wai su tayani zama gida ita da Aysha. Na nuna masa ban yarda ba yana neman min azaba da masifarsa. Na faɗama Mommy amma Gwaggo ta nuna wai tanada shiri. Wane shiri gareta? Na fahimci tsohuwar nan bata sona kawai yanzun...”

     “Fadwa!!”

Mamah ta katseta a tsawace. .......✍🏻_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_24_*..........Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu mintuna kamar kowa bazaice komai ba, kusan mintuna uku Amal ta nisa. Cikin ɗan ɗari-ɗari ta fara magana. “Ni dai a nawa nazarin da hange sai naga kamar cikin nan shine matsalarki. Kin san fa wasu mazan basu son da anyi aure ace ciki ɗin nan. Kigafa yanda Shareff ke sonki amma ace haka na faruwa tsakaninku wata baifi uku ba da aure, amma dai bamu san zuciyarsa ba kuma”.

     Ta ƙare maganar da ɗan shafo gefen wuyanta ganin yanda suka tsura mata idanu su duka. Yanzu ma kamar bazasu ce komai ba, harta fara tsarguwa sai Siyyah ta katse fargabarta. 

       “Kuma fa maganar Amal kamar tana a kan hanya. Musamman idan mukai dubi da yanayin mijinki. Anya kuwa cikin nan bashine matsalar ba...”

  Nufashi Fadwa taja da ƙarfi, zuciyarta babu abinda take hasaso mata sai yanayin Shareff a randa Dr Jamal ya tabbatar musu tana da ciki, ƙanensa da iyayensu kowa na murna amma shi bataga ko murmushinsa ba, da suka dawo gida ma baice mata komai game da cikin ba amma yana bata kulawa da duk take buƙata. Kenan in dai maganar ƙawayenta gaskiya ne kulawar yana bata ne kawai domin kar ace baya farin ciki? Ya ALLAH itako yaya akai ta kasa ganewa sai yanz.........

      Sima ce ta katse tunaninta da faɗin, “Fady nima dai ina ganin maganar su Amal nakan hanya gaskiya, dan na tabbatar badan cikin nan ba maybe ma tare da ke zai wuce ku ɗanyi honeymoon ɗinku. Amma gashi ciki ya muku cikas dole yayta maida allura galma a tsakaninku, ta hakanne kuma wannan yarinyar zata samu damar cika burinta akansa. A yanzu ma ɗaukar ciki duk ta wajigaki miji na gudunki inaga kin haihu, wlhy yara haukataki zasuyi ki fita hayyacinki. Baki ga miji hatta da followers naki sai sun gudu, dama kece mai kankaro mana mutunci saboda a yanzu kina cikin manyan tiktokers dake lokaci da kuma tarin followers a arewacin Nigeria, sunanki ya riga yayi zarra, da kin saki video tamkar wuta jaje haka yake danne duk wani posting, kiyi tunani”.

     Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka ciko mata ido saboda maganganunsu sun matuƙar shigarta. Ta sake nisawa cikin ɗacin zuciya batare data kallesu ba. “Naji duk bayanan ku, sai dai ban san yaya kuke so nayi da cikin ba tunda ya riga ya shiga jikina, tun kafin faruwar haka ya kamata na ɗau mataki, amma a yanzu na riga nayi latti..”

      “Bakiyi latti ba Fady, har yanzu kina da sauran dama”.

    Ido ta tsirawa Bibah da tai maganar. Bibah ta jin jina mata kai da cigaba da faɗin, “Da gaske bakiyi latti ba, kwata-kwata cikin ana maganar ko wata biyu bai cika ba, ki zubar da shi kawai, hakan zai baki damar sasantawa da mijinki tare da fatattakar shegiyar yarinyar can a rayuwarsa. Idan ya fara nuna son ƴaƴan da kansa sai ki bama cikin damar shiga hankalinki kwance”.

        Sosai maganar ta doki ƙirjin Anam dake saurarensu ta jikin window, dan a inda take zaune windown ɗakin Fadwa ne, tun kuma shigarsu ɗakin tana iya jiyo tattaunawarsu, sai dai da farko bata maida hankali ba sai da Amal ta fara danganta ciki da matsalar Fadwa. Duk da bata son Fadwa addu'a take a ranta kada ta ɗauki shawarar su Sima........ Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani, Mamie ce, hakan ya sata mikewa a wajen tilas tana amsa kiran dan video call ne.....


       Wayarta da Mamie ta hanata jin ƙarshen hirar su Fadwa, dan dai-dai tana kammala wayar suke fitowa kowannensu fuskarsa ɗauke da dariya. Su dukansu kallon banza suka shiga watsa mata suna jan tsaki, wasun su ma har da jeho mata kalmar zagi. Batako kalli inda suke ba, tamayi kamar bata gansu ba. Koda Fadwa ma ta dawo daga rakkiyarsu bata nuna ta ganta ba itama. 

    Itama ciki ta koma zuciyarta na kaikawo na neman mafita duk da bata san yaya ake ciki ba a yanzu. Fadwa ta karɓi gurguwar shawararsu kokuwa?Ba komai ta fahimta a hirar tasu ba dan ma suna haɗawa da turanci ne shiyyasa na zubda cikin yafi tsaya mata a rai. Ganinta shiru yasa Aysha data fito a wanka tambayarta ko lafiya. “Babu komai” ta bata amsa tana mikewa itama ta faɗa bayi.


     Kusan sati ɗaya dayin wannan magana har Anam ta sakankance Fadwa bata amshi shawarar ƙawayenta ba sai kawai ga Khaleel da yazo ɗaykarta an tashi aiki yake sanar mata Fadwa na asibiti ta samu miscarriage. Tsabar yanda zancen ya daketa batama san sanda ta maimaita kalmar miscarriage ɗin ba cikin waro iro. Da damuwa a fuskar Khaleel ya gyaɗa mata kai. “To ya za'ayi, haka ALLAH ya ƙaddara, wajen 3 na yamma Aysha ta kirani wai Fadwa tace cikinta na ciwo ta rakata asibiti. Suna zuwa likita yace cikintane ke son fita yay mata allura don hana faruwar hakan amma ba'a dace ba. Yanzu haka su Mom ma duk suna can nima dan ɗaukarki na fito dan ta zubar da jini sosai gaskiya”.

       Har cikin rai Anam kejin zafin abin dan ta tabbatar Fadwa da kanta ta zubar da cikin nan, kuma tabbas da likitan suka haɗa baki dan a ɓadda kama wa Ayshan. Jin batace komai ba Khaleel ya dubeta. “Ya naji kinyi shiru?”. Numfashi ta fesar da zuƙa, cikin kauda kai tace, “Ba komai ALLAH ya kiyaye gaba”. “To amin ya rabbi. Amma dai kowa baiji daɗin fitar cikin nan ba. Yaya Shareff ma koda na kirasa kasa magana yayi ya yanke wayar. Sai daga baya na sake kiransa wlhy bakiji muryarsa ba kamar yayi kuka. Hakan yasa na fahimci ba ƙaramin so da ƙwallafa rai yayi akan cikin nan ba fiye da kowa”.

        “Huhmm!”.

Kawai Anam ta iya cewa saboda sun iso asibitin. Duk ƴan gidansu suna a wajen har Mommy da Gwaggo Halima. Ta gaida kowa da tambayar mai jiki ta koma kusa da Aysha. Babu jimawa da zuwansu su Abbah ma suka iso, daga gani daga wajen aiki suka wuto nan suma. Har sannan ba'a bar kowa yaga Fadwa ba. Amma dai doctor yace da sauƙi sun mata allurar barci ne dan ta jigata matuƙa.

       Kasancewar kusan duk daga wajen aiki ko makaranta sukayi nan Daddy yace suje gida haka nan abar wanda zai zauna da ita. Gwaggo da ƙanwar Fadwa ɗin aka bari, sai Gwaggo Halima da tace sai zuwa anjima zata tafi ita. Su dai sallama sukaui musu suka wuce kowa na cigaba da jajanta abun a ransa.


       Washe gari kafin su wuce office nan suka fara zuwa ita da Khaleel, sai Aysha data biyosu dan kawo breakfast. Sun samu Fadwa zaune tana waya da alama ita da mijinta ne, dan sai faman marairaice murya take hatta da Gwaggo dake kusa da ita bawani jinta take ba. Ganin tana waya Khaleel ya fita dan ganin doctor, Aysha tabi bayansa da sauri dan tana son amsar kuɗi a wajensa nayo cefane daya manta bai bada ba. Gwaggo da tun shigowarsu tai kamar bataga Anam ba ta miƙe tana ɓantarar goro. Hanyar fita ta nufa dan so take ta tare Khaleel a waje ta amshi kuɗi itama. Ɗakin ya rage daga Anam sai Fadwa dake waya tana ɗan ɗaga murya yanzu wai dan Anam taji. Anam ɗin kuwa tana ji, sai dai tayi kamar bataji ɗin sai faman buga game take a waya. Lokaci-lokaci takan kai yatsa ta gyara zaman gilashinta.... Tsakin da Fadwa taja lokacin da ta kammala wayar yasa Anam ɗan dubanta. Kallon juna sukai cikin ido, Anam ta janye nata cikin halin ko in kula.....

        Yanda tayi sai ya batama Fadwa rai, duk da halin da take ciki muryarta ko fita bayayi da ƙyau ta watsama Anam harara da jan tsuka a karo na biyu. “Ban cika son ganin wanda ban gayyata cikin lamurana ba, ko kuma ban sani ba ko zargin namu ya zama gaskiya ne lashemin jariri akayi..”

      Da turanci tai maganar, hakan yasa komai ya shiga kunnen Anam. Batai niyyar harta bar asibitin ba tai magana amma sai ta kasa hakan, dan a wannan gaɓar taga ya dace ta bama Fadwa amsa dai-dai da ita. A hankali ta taka gaban gadon tana zira wayarta a aljihun wandon uniform ɗinta na hidimar ƙasa. Babu alamar tsoro ko shakka a cikin idanunta ta tsaya gaban Fadwa dake mata kallon mamaki. Idanunta dake cikin farin gilashi ta lumshe ta sake buɗewa akan Fadwa. “Tabbas jaririnki kam cinyesa akai amma da allurar zubda ciki. Dan haka masu zargin zan basu amsar da suke bukata har shi mai cikin dan yasan ɗansa ko ƴarsa sun salwantane ta hanyar abortion bisa shawarar ƙawayenki masu ɗauraki a hanyar da bazata taɓa ɓullewa da ke ba. Ai ban san ke ɗin cikon bench bace ba sai yanzu. Ki fita a sabgata, idan kuma kikace zaki iya dani wasan biri zanyi da ke a tsakkiyar kasuwa na rantse da ALLAH! Be careful”. Ta ƙare maganar da ɗalla yatsunta biyu a saitin fuskar Fadwa tana wani irin murmushi da kashe mata ido ɗaya.

        Numfashi Fadwa taja da ƙarfi, dan tun fara maganar Anam tai sumar wucin gadi........✍🏻_Wannan yarinya tsaurin idonta yayi yawa kudinga mata fada ta kiyaye Fady babynmu inba hakaba za'ai yakin duniya na 79 a kanta☹️👩🏻‍🦯__ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_23_*.........“Anya ƙwaƙwalwarki na aiki da ƙyau kuwa? Kin san wacece Gwaggo a wajen mu? To muna mata kallone tamkar mahaifiya, domin tana bamu dukkan gata irin na uwa tun mahaifiyarmu na raye. Su kansu su Yaya da suke mata wani abun a yanzu babu abinda ke ɗawainiya da su sai asiri da ƴan uba sukai musu saboda su basa samun koda sakin fuska daga gareta, sai dai Alhmdllhi na gagara a garesu, ƴan uwana ma zan dawo da su hanyar da aka kautar dasu. Bari na tuna miki idan kin manta, shi wannan auren da kike takama da shi Gwaggo ce tai ruwa tai tsaki akan kowa har shi Shareff ɗin da uwarsa, dan haka kisa hankalinki waje guda, na tabbata tunda tace mu bata lokaci akwai abinda take shiryawa. Kema ina so ki kwantar da hankalinki Fadwa, kinga bake kaɗai bace ba, ba'a bukatar duk wani tashin hankali daga gareki yanzun, indai matsalar ƴar Usman ce dake gidanki, ki bamu ƙankanin lokaci, ba gidanki kawai ba, Nigeria gaba ɗaya zata bari, barin da har abada bazata sake waiwayowa ba ita da iyayenta. Sai dai hakan bazai faru ba har sai kin haɗiye komai yazama ba komaiba, inba hakaba tashin hankalinki na nufin samun cikar burin Usman na ganin ya nanama Shareff ita ya aura.....”

     Wani mugun tari ne ya sarke Fadwa, sai da Mamah ta bata ruwa tasha, hawayena sharara a fuskarta. “Mamah dan ALLAH kar kimin baki”. “Ba baki nake miki ba Fadwa, mun jima da fahimtar ƙudirin Usman na son haɗa auren ƴarsa da Shareff, a yanda su Yaya suka canja kuma komai zai iya faruwa idan har ya fiddo buƙatarsa a zahiri. Shiyyasa muke son amfani da zamanta a gidan naki tunda mijinki bayanan mu mata abinda zatama bar ƙasar gaba ɗaya har uban nata bazai sake sha'awar zuwa ba balle tunanin ƙulla wata alaƙa damu”.

     A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya. “To amma Mamah bana ƙaunar ganin yarinyar nan wlhy”. “Haka zaki daure na ɗan lokaci ne, kiyi kamar ma baki san da zamanta a gidan ba, dan so muke ta saki jiki sosai saboda shirinmu yay tasiri”. Har cikin rai bawai ta gamsu bane, dan ba ƙiyayyar wasa takeji a zuciyarta akan Anam ba. Dan kamar an raini zuciyarta da tsanar iyayen Anam ne tun tana ƴar karamarta, hakanne yay tasiri matuƙa tare da cakuɗuwa da kishi ya nunku akan Anam ɗin, dan ko yaya Amrah kan samu sassauci a wajenta duk da itama ba sonta take ba kamar yanda bata son mahaifiyarsu. Sosai Mamah ta zauna ta kara lallashinta da maganganu masu daɗi har ta ɗan huce, kwanciyarta tayi anan sai washe gari ta koma gidanta da yamma.


Aysha kawai ta samu, Anam bata dawo aiki ba. Itama Ayshan ƙin sake mata tayi, sai daga baya kuma mitagani oho mata saita fara janta da hira da tambayar jiya basuji tsoroba dai ko su kaɗai. Aysha bata da saurin fushi, duk da tsumewar da Fadwa ta shigo tana mata sai bata ɗaukesa komai ba. Kanta tsaye fuska da murmushi ta shiga bata amsar basuji ba saboda Yaya Khaleel yazo da wuri, shine ma yake sanar musu bazata dawio ba sai gobe. Murmushi kawai tai, daga haka ta canja hirar.

        Sai kusan ƙarfe bakwai Anam da Khaleel suka shigo, da alama bayan sun tashi aiki can gidan ya wuce da ita, sai da ya gama kimtsowa suka taho tare. Yanda Fadwa bata kulata ba. itama sai batabi takanta ba tai shigewarta ɗaki ta barsu suna gaisawa da Khaleel, tanaji suka zarce da hira bata fitoba sai ma tai kwanciyarta dan dama taci abinci wajen Mom abinta. Har tai barci Aysha bata shigo ba, sai da ta farka ta ganta kwance, dama Aysha a ƙasa takeyin kwanciyarta dan Anam bata iya barci ita da wani a gado, shiyyasa a ranar farko tai kwanciyarta a sofa, ganin hakan yasa Aysha jiya tace ta hau gadon ita zata kwanta a ƙasan dan Anam ɗin kasa barci tai. Alwala tayo tai nafilfilinta sannan ta dawo ta sake kwanciya.

     Koda sukai sallar asuba bata koma ba, shirin fita aiki tai har Aysha na mitar sammakon nata bata dai kulata ba. Lokacin da suka fice ita da Khaleel Fadwa bata fito ba ma. Sai mai aikinta da jiya tazo da ita daga gidansu ce keta faman aikin gyaran falon.....


________________________★


           Yau kwanakin Shareff biyar kenan da wucewa ƙasar China. A zahiri tsakanin Anam da Fadwa babu mai shiga harkar wani. A baɗini Fadwa ta kasa jin zata haƙura da jiran shirin su Gwaggo. Dan kuwa kullum jin ƙarin tsanar Anam ɗin take a ranta musamman idan tana waya da Shareff ya tambayeta lafiyarsu. A yanzun ma har faɗa sukai dan yace taba su wayar su gaisa tace Aysha kawai zata bama wayarta banda Anam. Ya tambayi dalili tace saboda Anam ɗin bata isa ba.

      “Nasihar dana muku kafin na taho bata shigaba kenan? Fadwa miyasa kike son kawo min raini ne akan duk abinda na sharɗanta miki?”.

    “Ni laifina kawai kake gani ita bazaka bincika mitaiba. Yarinyar nan tunda tazo gidan nan sai dai taci ta kwanta tai wanka ta fita. Ko gaidani batayi, kai kallo ma ban isheta ba ina matsayin matar gidan. Ya kake so nayine Soulmate? Sai naita binta tana jana a ƙasa duk da ina sama da ita? Ai Aysha ba haka takeba, zata zauna muyi hira ta taya mai aiki aiki, kai kullum ma itace mai mana abinci, finta tai a gidan da ita bazata zauna ayi da ita ba. Shiyyasa tun farko nace ban yarda ta zaunamin gida ba amma kaƙi saurarata....”

     Ƙittt ya kashe wayar, hakan ya sake harzuƙa zuciyarta sai kawai ta fashe da kuka. Kuka taci har ta gode ALLAH. Tana cikin kukan sai gasu Sima tamkar an jehosu gidan har su huɗu. Anam na baranda zaune tana karatu suka wutota. Yanda basu mata sallama ba itama ko kallonsu batai ba dan ta gane Sima. Turus sukai suna kallon Fadwa da duk ta koɗe ta fita hayyacinta a kwana kaɗan, dama sun bar ganin posting ɗinta ne gaba ɗaya shiyyasa sukazo suga ko lafiya, dan bata cika zama gwanar kiran waya ba ita dama, ko kiranta kai sai ta gadama take ɗagawa.

       “Baby Fady kina lafiya kuwa?”.

Cewar Siyyah da tun randa suka kawo Fadwa ɗin bata sake tako gidan ba sai yau. Komai batace ba, sai wasu hawaye da suka sake gangaro mata. Da sauri Amal takai zaune kusa da ita ta rungumota jikinta tana shafa bayanta cike da lallashi, kusan mintuna uku Fadwa ta fara sauke ajiyar zuciya, hakan yasa Amal ɗagota. Tissue Sima ta ɗibo ta miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta. Bibah da tunda suka shigo batace komaiba sai yanzu ta kalla Fadwa. “Baby Fady kinsa duk jikinmu sanyi, badai namijine ya fara nuna miki butulcinsu na cin moriyar ganga a yada kaurenta ba, kin ganki kuwa duk kin wani yamutse kin fita a kamaninki kamar wata mai ƴaƴa huɗu”.

     Baki ta buɗe zatai magana turaren ɗaya daga cikinsu dake ta faman hawa mata kai ya sata tashi da gudu tai toilet. Da kallo duk suka bita, sai da ta fara kakarin amai ne suka mike a zabure suka rufa mata baya. Da taimakonsu ta wanke bakinta, Sima na yatsine-yatsine ta gyara wajen. 

   “Tabɗi babbar magana. Da alama dai Baby Fady cikine da ke”. Siyyah ta faɗa cikin riƙe baki. Sima ta ƙarɓe zancen da “Wane irin ciki kuma ana zaune ƙalau Shamsiyyah?”.   

      Fadwa da ta fahimci turaren Bibah ne ke hawa mata kai hanunta toshe da hancinta tace, “Bibah turarenki ne matsalata wlhy, buɗe Wadrobe ki ɗau wasu kayan ki canja a fidda waɗan nan karki kashen.....” bata karasa ba aman ya sake tahowa dole da sake mikewa da gudu tai bayi. Yanzu kam yi sukai kamar bazasu bitaba, sai daga baya cikin ƙunkuni Sima tabi bayanta ta taimaka mata. Kodan karsu cigaba da bautar kwashe amai dole suka takurama Bibah ta tashi tai wanka ta canja kaya. Daga haka aka samu sauƙi hankalin Fadwa ya samu nutsuwa harta kira mai aikinta ta kawo musu abinci da kayan ciye-ciye. Ta tambayi Aysha fa? Tace barci take. “Bakar yarinyar nan fa?”. “Ranki ya daɗe tana waje tun ɗazu kamar karatu dai take”. Baki Fadwa ta tabe, cikin bada umarni tace rufemin ƙofar falo bana bukatar shigowarta har sai ƙawayena sun wuce”. “Okay ranki ya daɗe an gama”.

     Bayan fitar mai aiki su Sima suka shiga tambayarta tana da damuwane ko kuwa cikinne ya maidata haka har yazam ba'a ganinta a online gaba ɗaya. Ranta a ɓace yake sosai da abinda ya faru tsakaninta da Shareff yanzu, ga damuwar hanata ɗaukar mataki akan Anam da su Mamah suketa famanyi har yanzun. Ita kuma tanajin cewa bafa zata iya juriyar zaman jiransu ba a halin yanzu tunda har takai mijinta na kashe mata waya dan ta faɗi laifin Anam. Su Sima ƴan amanarta ne da take kallo fiye da kowa a cikin ƙawaye. Bibah da Shamsiyya ƙawayentane tun na ƙuruciya sannan ƴan uwanta ta ɓangaren mahaifi. Dan haka kanta tsaye ta shiga zayyane musu dukkan damuwarta akan zaman Anam a gidan dama abinda take tsoro wanda dukan sunsha cemata dama suna zargin Shareff da Anam na soyayya ne tana gwalisesu.

      Dukan su kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. Dan kowannensu akwai manufarsa a kanta tun ba yanzu ba. Fadwa nada ƙyau gwargwadon iko sun sani, mahaifinta nada arziƙi gwargwado shima sun sani. Sai dai Bibah ta fita ƙyau nesa ba kusa ba, hakama mahaifin Siyyah yafi na Fadwa arziƙi nesa ba kusa ba. Amma ta fisu abubuwa da yawa da suke ganin ya kamata ace sune ke da shi ba ita ba. Hatta su Sima data raini wayewarsu da ɗaukakarsu da kanta kowanne da nasa manufar....  

     Ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya idonta cike da ƙwalla. “Ina son kowannen ku ya bani shawara guda ɗaya akan matsalata domin kaina ya kulle ina neman mafita. Mafita ta gaggawa kafin matsalarmu da mijina tafi haka faɗi dalilin ta”..........✍    _😹😹😹Keda ke a gidan aure, amma kina neman hanyar warware matsalar rayuwar aure a hanun wanda basu taɓayi ba. Bayan kin fisu sanin abubuwa da yawan daya kamata ace a wajenki zasu nema shawara idan sunyi nasu auren. Mata a kula, nasan akwai masu hankali acikin wanda basuyi auren ba da yawa da zasu iya baki ƙyaƙyƙyawar shawara mai ɓullewa. Sai dai ki sani, ba kowacce ƙawa bace zakiyi aure ki barta a titi taso ta ganki cikin nutsuwa da farin ciki a gidan aurenki kema. Hakama wanda suke gidan auren ba kowacce bace zata so ta ganki a samnta. Amma kumuje zuwa muji ko shawarar da Fadwa zata samu ga ƙawayenta ita zata ɓulle da ita🤕🤕🤧.__ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_25_*........“A'a lafiya?”.

Khaleel dake shigowa ya faɗa idonsa a kansu. Baya Anam ta ɗan ja tana murmushi, ta girgiza masa kanta. “Ba komai Yaya ina dubata ne kawai”.

            “Okay tom ai haka yana da ƙyau. Bara nima mu gaisa sai mu wuce kar ki makara”. 

Kai kawai ta jinjina masa. Ta watsama Fadwa harara ta juya ta fice a ɗakin. Da ƙyar Fadwa take iya amsa tambayoyin Khaleel, gaba ɗaya a birkuce take da kalaman Anam. Domin kuwa zancen Anam ɗin na nuna mata tabbas taji duk shirunsu da su Sima kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci zufa ta gama jiƙe mata jiki. Har Khaleel ya fahimci haka ya tambayeta ko jikin ne?. Kanta ta jinjina masa cikin kaƙaro murmushi. “Kawai inaga allurar da sukai mince bata gama sakina ba barci nake ji”.

     “Ayya ALLAH ya ƙara lafiya. Doctor ɗin ma yace zuwa anjima zai sallameki, inaga bara na ajiye Anam a wajen aiki karta makara zan dawo yanzun”.

   Kanta kawai ta iya jinjina masa nan ma. Yana fita ta jawo wayarta cikin rawar jiki. WhatsApp ta shiga, ta haɗa group da sauri tare da adding su Siyyah a ciki. Cikin sa'a ta samu Bibah da Sima a online. Cikin bada umarni tace suyi kiran Amal da Siyyah su hau online tanada magana da su. Duk sun san tana asibiti tun jiya, sai dai basu zo ba kamar yanda suka shirya har sai ta koma gida dan karma wani ya zargi wani abu. Tsoron yin voice note wani yajita ko kiransu ya sata tafa musu duk yanda tai da Anam yanzu. Suma hankalinsu ya tashi amma duk sai suka danne kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinsa.

         Maganar Sima ta sakasu duk maida hankalinsu gareta, dan zancen ya dauki hankalinsu. *Sima* _Inaga ba hankalinmu ya kamata mu tayar ba, idan ita tace kwalba ce uwar sheri sai mu nuna mata muɗin gilasai ne mun fita haɗari. Kafin ta faɗama wani zancen nan dolene mu juya komai kanta, hakan ma zai zama hanya mai sauƙi da zata bar miki gida dan koshi mijinki daba son cikin yake ba na tabbatar sai ya tsaneta._

       Cikin ɗan tsumar jiki ta tafa saƙo tana tagging maganar Sima. _Kinga Sima bar zagaye-zagaye faɗi minene shirin naki kai tsaye kawai dan ALLAH_.

      *Sima* _Kafin ta faɗi kin zubar da cikin mu zamu fara sanarwa itace ta zuba miki maganin zubda ciki._

    *Bibah* _Ta yaya hakan zata faru tunda bamu da wata hujja Sima?!”._

   *Sima* _Muko keda hujja. Doctor zamu samu ya faɗama su cikin ya zube ne ta hanyar magani da aka sha, bayan kowa ya gama ji da ɗaukar ɗumi akan maganar mai-aikinki ta tabbatar musu taga shegiyar sanda take zuba maganin. kinga sai mu samu ƙwaya asa a abinda kika sha na karshe dan ya zama shaidarmu ta biyu, yanda kowa yasan ita da iyyenta ba ƙaunarku suke ba tuni za'a yarda wlhy”_.

              *Siyyah* _Woow gaskiya wannan shawaran yayi Sima. Shiyyasa kike birgeni, dan kuwa na tabbatar wannan maganar bazata zama ta wasaba. Maybe ma a kanta har sai iyayen Shareff sun maidata inda ta fito”._

     A hankali Fadwa ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi, jin motsin kamar za'a shigo ya sata ajiye wayar da sauri ta zame ta kwanta tana fidda numfashi ɗaɗɗaya.


      ★Kamar yanda suka shirya ɗin hakance ta kasance. Dan kuwa bayan dawowar Khaleel Doctor yake sanar masa bayanan bincikensu akan zubewar ciki. Hankalin Khaleel ya tashi a take ya kira Daddy a waya ya sanar masa. Cikin ƙanƙanin lokaci magana taje kunen kowa daya dace, dan haka daga asibiti gidan su Shareff aka wuce da Fadwa. Anan su Gwaggo suka tirketa da tambayoyi. Faɗa musu tai ita wlhy bata sha komai ba dan cikin ya zube. Daga dai gama shan lemo cikinta ya kama ciwo shine tace Aysha ta rakata asibiti, suna kuma zuwa Doctor yace cikin na barazanar zubewa. Yay mata allurar kariya daga hakan amma sai ba'a dace ba. Kan kowa ya kulle da zancen, daga ƙarshe Abbah ya tambayi su nawane a gidan.

        Cikin kukan da take faman sharɓa ta sanar masa su huɗu da mai aiki sai maigadi a waje da Khaleel da sai dare yake zuwa, da safe kuma ya fice. Babu ɓata lokaci aka tattaro kowa har maigadi sai kulle gidan yayi. Su Anam dama daga wajen aiki nan suka yo. Kafin kowa yace komai Gwaggo Halima ta fara zazzaga masifa akan bazata yarda ba, duk wanda ya salwantar mata da jika sai inda ƙarfinta ya kare, Hakama Mommy sai kumfar baki take. Itako Gwaggo sai ta saka kuka tana kafe Anam da kallo...

      Hakan yasa kowa maida hankali kan Anam ɗin. Ta nuna Anam da yatsa tana sake fashewa da kuka. “Kar ku raba ɗayan biyu yarinyar nan ce ta aikata. Lallai ilallah itace da wannan aika-aikar, tunda tana ganin Mustapha ya mata nisa shiyyasa ta ƙulla wannan sharrin na salwantar masa da ɗan tayi. Kai wannan yarinya anyi azzaluma makira, dama yaya ɗan ɗan uba zai taɓa son abokin burminsa da alkairi, dama ni dai dan kar ace an hanata zuwa ne amma naji ajikina wani abu mai muni zai faru, sai dai banyi zaton mai girma irin wannan ba........”

      Abbah ya katseta da sauri cikin ɓacin rai,  “Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce haka. Yaya Anam zatai wannan babban al'amarin nawa take?”.

        “Eh kace haka fa, Abubakar kasan miye mace kuwa? To mace ko ƴar kwana ɗaya ce ta wuce da saninka a fanin makirci da shaiɗanci. Idan kana ganinta karama wlhy sai ta aikata maka abinda mai ɗari bazaiyiba. Kuma idan kitsa mata hakan akayi fa...”

               “Wannan dai maganar bashi da amfani gaskiya a bari dai ayi bincike. Ƙilama ita Fadwan da kanta tasha abint.....”

     “A'a gaskiya Yaya kar kai irin wannan yanke hukuncin. Taya za'ai ciki na jikinta ta zubar”. Gwaggo Halima ce ta katse Daddy a matuƙar harziƙe mai maganar.. Ran Daddy ya ƙara ɓaci amma sai baice komai ba yay shiru. Abba ne ya ƙara dakatar da hargowar Mommy da Gwaggo. Dole sukai shiru aka fara yima Aysha tambayoyi. Bayan ta gama bada amsa aka juya kan Anam da zuciya tazoma wuya da kalaman su Gwaggo Halima duk da ba komai take fahimta ba saboda hausa sukeyi. Tambayarta itama Abbah ya shigayi sai dai ta kasa bada amsa ko guda ta saki kuka....

       “You see! Kun gani ko. Shi mara gaskiya ai ko'a ruwa jiɓi yake. Munafuka dangin tsiya wlhy ko za'a tada yaƙi bazan yarda ba”.

 Mommy ce mai maganar, dan haka Daddy ya katseta a tsawace har sai da Anam ta zabura ita da su Aysha. Fadwa ta watsama mai-aikinta harara cike da gargaɗi saboda hango tsoro da firgici cikin idanunta. Ƙyale Anam Abbah yayi ya maida hankalinsa gamai aikin dan ya fahimci zuciya ce ta tokare Anam ɗin. Tiryan-tiryan yanda suka tsara mata ta faɗa. Ko haɗiyar yawu bata gama ba su Mommy suka hargitse falon da hargowa har suna kaima Anam duka da ranƙwashi sai dai Khaleel ya fara kareta. Duk yanda su Daddy suka so suyi shiru hakan ya gagara. Dole Khaleel yaja hanun Anam suka fice da sauri. Mota ya turata ya tayar yabar gidan a guje duk da kiran da Gwaggo Halima ke masa akan ya dawo da Anam ɗin bai saurareta ba..


 

         ★Kuka take sosai har numfashinta na fisga. Yayinda Khaleel ke waya da Shareff cikin bacin rai da ƙunar zuciya. Shima daga can yana jiyo shashshekar kukan Anam ɗin. Sun jima suna wayar kafin ya miƙo mata. Ƙin amsa tai sai da Khaleel ya ɗaura mata akan kunne yana faɗin, “Yaya Shareff ne fa”.

          “Malama amsa wayar ban son shashanci”. Ya faɗa da alamun ɓacin rai a muryarsa daga can. Amsar tayi, sai dai ta fashe masa da sabon kuka. Shiru bai sake cewa komai ba da alama dai yana saurarenta. Tsawon minti ɗaya taƙi tai shiru ya yanke wayar yana jan tsaki. Kanta ta cusa cikin ƙafafunta tare da sakin wayar ta saki wani sabon kukan. Ba sharrin su Fadwa ya sata wannan kukan ba. Zagin iyayenta da su gwaggo Halima keyi da aibanta su ne ke mata zafi. A hakan ma dan ba komai take iya ganewa ba musamman manya-manyan hausa. Tana matuƙar son iyayenta, bata ƙaunar a aibanta mata su. Amma tunda ta fara wayo ta fahimci waɗanda Abie ɗinta ke kira family nasa basu da wani buri daya wuce cin zarafinsa shi da Mamie da ita kanta dake matsayin ƴar su. Ta rasa mi iyayenta sukaima Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima haka da zafi a duniyar nan?...

      Khaleel da kukanta ke ƙara ƙona zuciyarsa da takaicin su Mommy ne ya shiga lallashinta, da ƙyar ta ɗago idanunta da sukai jajir tana kallonsa. Zatai magana ya girgiza mata kai alamar tai shiru. Shirun kuwa tayi sai dai hawayenta sun kasa tsayawa. Khaleel ya miƙa mata goran ruwa dai-dai kira na shigowa wayarsa. Ganin mai kiran ya sashi ɗagawa babu ɓata lokaci ya kai kunne sa. 

     “Bata wayar”. Daga can aka faɗa cikin bada umarni. wayar ya sake miƙa mata. Bata musa ba ta amsa tana cire goran data sha kusan rabin ruwan cikinsa. A jajjare ta dinga sauke ajiyar zuciyar dake shiga har cikin kunensa daga can.........✍_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_26_*..........Gyaran murya ya ɗanyi bayan yaja wasu seconds yana sauraren yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Bazaki daina wannan kukan ba wai?”. Ya faɗa a hankali tamkar ba shi ba...

      “Na daina”.

Ta bashi amsa wani kukan na sake kufce mata. A karon farko taji yayi murmushi har tana iya jiyo sautinsa a cikin kunnenta, ya ɗanja numfashi da sake sauƙaƙa muryarsa “Ya isa nace ko. Ki ɗauka ruwa ki wanke fuskarki zan ƙara kira”. 

     Cikin jan numfashi tace, “Nace fa na daina Yaya”. Dan haka kawai take jin daɗin yanda yake mata magana da lallashi. 

         “Ni banji kin dainaba ai, tunda ga hawayenki ina gani na sauka a z....” cikin sauri ya haɗiye sauran maganar da dafe goshinsa yana cije lips ɗinsa jin zai saki layi. Itama da ba wani gama fahimtar maganar tasa tai ba cikin rawar murya tace, “Yaya dan ALLAH ka faɗama Abie zan dawo Malaysia, idan nice nace zaimin faɗa shi da Mamie”.

      Furzar da numfashi yayi, cikin ɗan kaurara muryarsa yace, “Bazan sanar musu ba, kuma kema karna sake naji kin sanar dasu wani abu ok”.

    “Amma Yaya kag.....”

“Umarni ne ba shawara ba”. Yay saurin katseta. Baki ta tura da hararar wayar kamar yana gabanta, “To nidai bazan koma gidanka ba, sai dai na koma gidan uncle Jafar da zama (Ɗan uwan Mamie da abie ne).

         “Ashe kuwa zan zane miki jiki da bulalai”.

   “To ni Yaya ya kake so nayi? Sai na dinga zama inda ba'a son ganina kamar wata mara gata”.

      “Waye baya son naki?”.

  “Matarka mana. Kuma ALLAH idan bata fitamin a ido ba zan fito mata da ainahin kalata, dan zan koya mata hankali...”

        Dariya ce ke son kufce masa, sai dai ya riƙeta ya dai saki murmushi. “Uhuyim! Ke har wata kala ce da ke ashe? To faɗamun yaya kalar taki take dan mu kiyaye ni da matata”.

   “To ni ai bance kai ba”.

“A idan zaki koyama matata hankali ai dole ina ciki. Kinga gara mu kama kammu kar truth color ɗinki ta samu barin Nigeria auntynmu”.

        A yanda yay maganar ya saka Anam fashewa da dariya. “Oh oh ya kaga Anam Auntyn su Yaya, gaskiya kowa zaiji a jikinsa ne, yanda kake mana mazurai nawa sai yafi ALLAH Yaya”. Sai ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya.

       Kansa ya ɗan girgiza da shafawa yana sakin murmushi, yasan ta iya surutu, sai dai bata taɓa sakewa da shi ba irin haka. Sai dai yaji surutunta da wani. Ya ƙara sakin murmushi da fesar da numfashi a hankali yana lumshe idanunsa da sake lafewa cikin kujerar falon daya kasance masaukinsa. Haka kawai ya tsinci kansa cikin nishaɗi dayin wayar tasu......


       Yayin da Anam da Shareff ke waya anan acan gidan Mommy ce ke neman wayarsa a fusace saboda hukuncin da Daddy ya yanke cewar Anam bazata bar gidan Shareff ɗin ba kamar yanda suka buƙata har sai ya dawo kamar yanda shima ya buƙata. Amma sai taƙi samunsa anata nuna mata waya yakeyi. Ranta ne ya ƙara ɓaci ganin mintunan dake ta ƙara tafiya amma ana sake jadadada mata ana amfani da layin. Ta tura massege babu reply. Ga Fadwa nata musu kuka ita indai Anam zata koma mata gida to ita bazata koma ba..

      “Wai ni yaron nan da ubanwa ma yake waya hakane? K Hussaina jeki ki gano min Daddynku waya yakeyi”.

   Miƙewa Hussaina tayi tana amsawa da to ta fice. Mintuna kaɗan ta dawo ta sanar mata ba waya yake ba, hira yakeyi ma shi da Abba. 

  “Kai! To da ubanwa yaron nan ke waya?”.

Kuka Fadwa ta sake fashewa da shi. “Wlhy yanzu haka shegiyar yarinyar can ce ta kirashi tana ƙulla mana sharri a wajensa. Na tsaneta, bana sonta. Idan ta koma min gida saina kasheta”.

    Shigowar Gwaggo falon ya hana Gwaggo Halima da Mommy bama Fadwa amsa. Takai zaune tana murmushi idonta akan Fadwa. “In dai bazaki kiyayi gaggawa akan al'amuranki ba kuka yanzu kika fara shi. Da kinyi haƙuri kin cigaba da jiran nawa shirin da ba'akai ga haka ba. Ku kuma kun biye mata. Duk yanda kuke tunanin yarinyarnan tabar gidan Mustapha da ƙarfin tuwo bazai yuwuba, wannan kuma zancen ita ta zubda ciki da kuka ƙulla ƙara kusantata ma da gidan kukayi tunda gashi su Muhammadu sun tabbatar muku yanzuma ta fara zama. Duk wanda ya baku shawarar juya zancen zubewar ciki da ita ta zubar ya baku gurguwar shawara ne ga tabbaci kun gani”.

       Mommy da takai zaune cikin sanyin jiki da maganganun Gwaggo ta dubi Gwaggo Halima. “Maganar Gwaggo haka take Halima. Munyi kuskure nima na fahimta. Da Fadwa ta sanar mana zatai hakan ya kamata mu dakatar da ita mu fara yin nazari, tare da bincikarta wanda ya bata shawarar yin hakan tunda mun san zubewar cikinta bashi da alaƙa da yarinyar da gaske”.

     Itama Gwaggo Halimar ajiyar zuciyar ta sauke. Sai kuma ta jinjina kanta, “Hakane Gwaggo anyi kuskure, ba kuma kowa ya jawo hakan ba sai Fadwa da shegen gaggawarta. Na faɗa mata ta kwantar da hankalinta mu jira naki shirin amma rashin haƙuri yasata yanke wannan hukuncin. Gashi yanzu bai haifar da ɗa mai ido ba tunda abinda take son yay nesa da ita da mijin nata damu baki ɗaya bai tabbata ba. Kuma tabbas zaman yarinyar nan cikinmu ba alkairi bane,  na tabbatar yanda bamu ƙaunar ubanta shima bazai taɓa son mu ba, amma ya kawota cikinmu saboda sharri irin na ɗan uba da baka ganesa sai ALLAH kawai. Gwaggo kiyi haƙuri, yanzu minene mafita?”.

      Baki Gwaggo ta taɓe. “Toni mizance yanzu kuma. Nawa shirin ma ai kun ruguza da shirmen ƴarku. Sai kubar yarinyar ta koma gidan kamar yanda Muhammadun ya faɗa. Zanje na sake sabon shiri a kanta dan wannan karon dole ne muyi shirin da zata koma inda ta fito kuma har abada bazata sake dawowa ba. Kai bama ita da suka haifa ba, har Usman da Maryam (Aunty mimi) bazasu sake waiwayo ƙasarnan ba har abada balle ita karan kaɗa miya”.

    A take fuskokinsu suka washe da murmushin jin daɗi. Fadwa tace, “Amma ni dai gaskiya ayi da sauri. Dan wlhy idan ina ganinta a gidana ji nake kamar na shaƙeta ta mutu. Bana son Soulmate ya dawo ƙasar nan tana gida na”.

       “Batun kafin ya dawo ƙasar nan bazai yuwuba. Domin kin ɓata komai ga shirin yin hakan kuma ai. Dolene muyi ɓadda kamar da zasu cire ɓaranɓaramar da kikai a ransu gaba ɗaya daga nan har zuwa lokacin bikin Maheer, so nake da bikin idan sun zo su tattara ƴarsu su wuce yanda bazasu sake dawowa cikinmu ba har abada. Idan kuma kika ƙara yin wanu shirme to kiyi kuka da kanki bani Hannatu ba kuma”.

     Baki Fadwa ta tura gaba sai dai batace komai ba. Nan su Mommy suka shiga jadadada mata ta kiyaye kar kuma a sake samun wata matsalar kamar yanda Gwaggo ta faɗa. Idan tai haƙuri komai zai zama labari dan suma basu da burin daya wuce Anam ta bar gidan ai. Miƙewa Gwaggo tayi, “To bara nayi nan karma wani ya shigo ya ganni. Shima kuma Mustapha kar wanda ya kirasa akan maganar mu jira muga ko wani zai sanar masa a cikinsu”.

   Duk sun gamsu da hakan. Daddy dake bakin ƙofar yaja da baya a hankali yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa. Dama yazo ne dan ya sake kwantar ma da Fadwa hankali da nuna mata tabar zargin kowa akan zubar cikin ta ɗaukesa matsayin ƙaddara. Amma sai gashi yaji ainahin abinda ma ke faruwa. Bai bari Gwaggo data fito tana murmushi ta gansa ba, sai ma ya juya yabar wajen ya fasa shigar... 


        Washe gari Daddy ya sakasu komawa can gidan Fadwa na ɗacin ran kasancewa da Anam. Khaleel ne ya ɗauke su su huɗu har mai aikinta dan maigadi shi tun jiya ya koma. Anam tai murmushi tana kauda kanta gefe ganin uwar hararar da Fadwa ke zuba mata kamar idanunta zasu zubo ƙasa. Sosai murmushin ya ƙular da Fadwa, sai dai batai magana ba har suka iso.  

        Kiran da Abie yay ma Anam a waya ne ya sata dakatawa su suka shige su uku. Itako ta tsaya anan jikin motar Shareff dake lulluɓe tana amsawa. Ta jima tana wayar kafi. ta nufi ciki itama fuskarta ƙawace da murmushi. Matar gidan kawai ta samu a falo zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jijjigawa da yanka apple. Sai mai aikinta dake gyaran falon. Yi tai kamar bata ganta ba tai ƙoƙarin wucewa........✍🏻

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_28_*...........A haka aka shiga shirye-shiryen bikin Maheer, Anam da Aysha. Yayinda kwanakin dawowar Shareff da ba'a sanar da shi komaiba ke kusantowa. Asabar ɗin daya rage saura sati uku biki Anam da Aysha acan gidan suka yini ana shirye-shirye da tsare-tsare. Anam dai ba shiga sabgar duk wani shirye-shirye take ba, su Fadwa ne dai ƙirjin biki keta kaiwa da kawowa duk da ango Maheer bawai yana ko leƙowa yaji yanda abubuwan ke tafiya ba ne, dan shi ƙiri-ƙiri nunawa yake baya son auren nan.  

        Haka itama Anam Muzzaffar yayi tafiya dan tunda aka fara maganar auren ma bata gansa ba, a wayama sai jefi-jefi dan baya ƙasar yaje wani aiki mai muhimmanci a yankin larabawa.

      Washe gari lahadi Khaleel ya dauketa ita da Aysha kamar yanda yay mata alƙawari zuwa wajen tela. Kayanta takai na ɗinki, Mom ce ta bata su takai ɗinki kusan kala goma sha biyar. Kayane masu ƙyau da tsada har tana mamakin miyasa aka banbantata da Aysha, dan telan nata ma na musamman ne saboda Mommy taƙi yarda Aysha ta kawo nata nan. Bayan sun zaɓi ɗinkunan da take so ya gwadata ya faɗa misu bill ɗin kuɗin. Accaunt number ɗinsa Khaleel ya amsa, ya saka masa rabin kuɗin rabi yace sai ya kammala aikinsa. Daga nan gidan wata ƙawar Mom suka nufa ƴar sudan. Har Khaleel ɗin suka shiga ciki, yanda aka tarbesu ya bada tabbacin Khaleel ɗan gida ne. Sun ƙara tabbatar da hakanne lokacin da wata ƴar budurwa ta kawo musu abinsha tana ta faman sinne kai na kunya, yayinda Khaleel ke faman jifanta da wani kallo. Cikin yanayin tuhuma Anam ke kallonsa tana murmushi, yay murmushi kawai da ɗauke kansa gefe.

       “Uhm to lallai ALLAH ya sanya albarka Yaya Khaleel, amma auntyn tamu fa tayi dan kun dace”.

    Salute ɗinta yayi, hakan ya sakata kwashewa da dariya Aysha na tayata, dan ita ta kasa cewa komai tunda ba wasa yake da su ba. Fitowar matar hamshaƙiya ƴar gayu ya saka Anam haɗiye dariyarta. Suka gaidata cike da girmamawa itama tana amsa musu da kulawa cikin hausarta da bai gama nuna ba. Khaleel dake faman sinne kai ta kalla, “My son wacece a cikinsu?”.

     Anam ya nuna, kansa a risine yace, “Itace wannan Mama”.

    “Masha ALLAHU, ALLAH ya sanya albarka. Kace mata insha ALLAH bazai gagara ba, nima zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zan shigo dan maybe zuwa laraba mu fara, kaga zamu samu kwana goma sha bakwai kenan”.

        “To shikenan insha ALLAHU zan sanar mata”.

  Daga Anam har Aysha babu wanda ya fahimci inda zancen ya dosa. Sai dai ganin akan Anam ɗin ake magana ya tsaya musu a zukata. Ƙagara sukai su fita suyi tambaya. Amma sai matar ta tsaresu akan sai sunci wani abu. Su kaɗai suka ɗanci snacks. Shi dai Khaleel ruwa kawai yasha dan kunya. Ganin haka tasa budurwar nan mai suna Suhaima tai musu packaging ɗinsu dan harda gasashshen nama.

        “Yaya Khaleel mufa kun samu a duhu.” Anam ta faɗa dai-dai suna shiga mota. Murmushi yayi yanama motar key, cikin basarwa yace, “Akan mi?”. 

     “Komai ma”.

“To kuyi addu'a ALLAH ya haskaka muku”. Daga haka yaja bakinsa yay shiru. Duk yanda sukaso jin ƙarin bayani bai basu fuska ba har suka iso gida. Kasa haƙuri Anam tayi sai da ta tambayi Mom. Kai tsaye Mom tace mata gyaran jiki na bikin amare za'ai mata dan taga duk tayi duhu. Murmushi kawai tai dan da gaske itama ta fahimci tayi duhun ko dan fitar da take kullum ne oho. Daga haka bata sake bin ta gyaran jiki ba.


     *_Yau litinin_* da tai dai-dai da saura kwanaki goma sha ɗaya biki. A yau ake saka ran saukar su Mamie Nigeria sai dai Anam bata san da hakan ba. Hasalima ta tashi ne da ɗan zazzaɓi. Wajen ƙarfe sha biyu Muzzaffar yay kiranta a waya. Yanda yaji muryartane ya sashi ruɗewa yace zai zo ya kaita asibiti. Amma sai taki acewarta tasha magani. yata lallaɓata amma taƙi yarda dole ya barta dan yasan mutuniyar tasa ƴar tutsu ce. Koda sukai sallama ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya ta gyara kwanciya. Wani barcin ne ya sake awon gaba da ita saboda maganin da Aysha ta bata tasha. Bata farka ba sai kusan uku. Alhmdllhi zazzaɓin ya sauka dan hakata samu tai wanka ta ɗanci abinci. Bayan sallar la'asar tana waje zaune ita da Aysha sai ga kiran Muzzaffar, kai tsaye ya sanar mata gashi a ƙofar gida. Murmushi kawai tai ta yanke wayar, dan zuwa yanzu kam Muzzaffar ya samu wani gurbi na musamman a zuciyarta duk da sun jima nesa da juna dan baifi kwana uku da dawowa ƙasar ba. Yau ne ya fara zuwa gidan suyi hira, dan haka sai da Aysha ta fita tayo masa iso, anan inda suke zaune da Aysha saman kujerun roba ya zauna. Aysha ta shige ciki ta kawo musa ruwa ta koma domin basu dama...

       “Da alama zazzaɓin nan yaci amanar ango da yawa harfa kin rame dama gaki ba auki ba”.

    Veil ɗinta taja ta ƙara rufe fuskarta tana murmushi. Shima ya murmusa cikin ƙara sanyaya murya yace, “ALLAH da gaske nake madam. Kodai aje asibiti?”.

    “A'a ni naji sauƙi fa”.

“Kin tabbata?”.

Kanta ta jinjina masa. Murmushi ya sakeyi mai faɗi da shafa sajen fuskarsa. “Alhmdllhi ALLAH ya ƙara lafiya to”

     “Amin ya rabbi.”

Shiru sukai na wani ɗan lokaci kafin ta saci kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta maida idanunta ƙasa ranta fal mamakinsa, dan babu rawar kan nan tasa, kuma bai kirata Beauty ba ko sau ɗaya. Murmushi yayi da gyara zamansa. “Madam nifa da magana nazo a bakina yau”.

   Fuskarta ta ɗan buɗe sai dai bata kallesa ba. Ya cigaba da faɗin, “Juwairiyya gaskiya nima aure nake so”. A karan farko ta ɗago kai ta zuba masa dukan idanunta dake cikin gilashi. A hankali ya lumshe nasa ya sake buɗewa. “Wannan kallo ai sai kisa na gagara faɗar abinda ke raina”.

     A yanda yay maganar ya sata sakin siririyar dariya. Hakan yayi dai-dai da buɗe gate da maigadi yayi motar Khaleel ta shigo. Su duka basu maida hankali ba, sai ma dariyar da yake tayata shima yana ɗan duban fuskarta da take kaudawa gefe, yanda yaketa ƙara ƙoƙarin son ganin fuskar tata sai yake ƙara bata dariya harta kasa dainawa....

    

         “Alhamdulillahi lallai yau jama'ar gidan nan zasusha surprise na ganinka Yaya fiye da yanda ƴan can gidan suka sha”. Khaleel ya faɗa yana kashe motar. Bai saurari amsaba ya buɗe gefensa ya fito, zagayawa yay ya buɗe masa fuskarsa ɗauke da murmushi.

      Badan glass dake rufe da idanunsa ba babu abinda zai hana aga tsantsar ɓacin ran dake cikinsu. Tuni sun kaɗa sunyi jajur, duk wani annurin dake saman fuskarsa na farin cikin dawowarsa cikin zuri'arsa ya ɓace ɓat. Cike da izzar da fushi ya haddasa ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito, hakan yayi dai-dai da juyowar Anam dake shirin ɗagama Khaleel hannu.. Hannun nata da numfashinta a tare suka maƙale, ƙirjinta yay wata irin bugawa da batasan dalili ba. A hankali laɓɓanta suka motsa ta ambaci sunansa...

      “Yaya Shareff”.

Duk da akan laɓɓa tai maganar hakan bai hana Muzzaffar gane sunan wa ta kira ba, juyawa yay shima a hankali. Cikin dariya Khaleel ya ɗago musu hannu da faɗin, “Surprise”.

          Murmushin yaƙe ta saki, mamakinta na sake bayyana akan fuskarta, ta miƙe a hankali kamar wadda ƙwai ya fashema a ciki ta nufesu, hakan yasa shina Muzzaffar miƙewa fuskarsa da murmushi yabi bayanta..........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_27_*..........A hankali ta ajiye wuƙar tana murmushi, ta miƙe cike da isa da izza tana magana da shan gaban Anam, “To ƴar wasa da biri, ya akai ke kika zama birin kuma a hannun ƴan wasa?”.

       Idanunta dake cikin gilashi ta ɗago tana kallonta, ta saki ɗan murmushi da kauda idanun kamar bazatace komai ba. Sai kuma ta hurar da numfashi da sake maida kallonta gareta. “Mi kikeci na baka na zuba Madam. Da Juwairiyya kike tare fa, _Juwairiyya Anam Usman MD Shareff_ bana gaggawa akan al'amarina, sai dai ina bama maƙiyi damar da zai sharemin hanyar fagen isar da saƙona. Su kin faɗa musu ni na zubar miki da ciki right? Tom ki jira shi kuma mai cikin yazo ya ɗaura bincikensa akan yanda akai na zubar ɗin, daga haka game ɗin zai fara ok!”. Ta ƙare maganar da kashe ido ɗaya ta rabata ta wuce tana dariyar rainin hankankali.

      Wani irin bugawa ƙirjin Fadwa ya shigayi da sauri-sauri, tabita da kallo harta shige. Juyawa tai ta kalli mai aikinta, ganin aikinta take hankalinta baya kansu tai saurin barin wajen ta nufi bedroom ɗinta. Kai kawo ta shigayi cikin tashin hankali, dan da gaske kalaman Anam sun mugun dukanta, kanta ya kulle harma ta rasa kalar tunanin da zatayi. Tayi waya da Shareff a daren jiya amma bai nuna mata komai ba akan maganar rigimar zubda cikin balle tace ko Anam ɗin ta sanar masa ne. (To mi yariyarnan take nufi?) ta tambayi zuciyarta batare da tasan ta inda amsa zata fito ba. Ganin ta rasa ina zata kama ta yanke shawarar kiran Sima, dan tana da basira sosai, tasha warware mata ƙulluka da ita ta gaza kuncesu musamman da abokan hamayyarta irin su Anam ɗin......


       Sima tazo, sai dai Fadwa ta jata sun fita can garden ɗin gidan dake bayan sashen maigidan saboda kar a ƙara maimaita irin na ranar. Acan suka tattauna. Har Sima ta wuce Aysha da Anam basu ma san da zuwanta ba dan suna can suna kwasar barci. sai yamma sosai suka tashi saboda saurayin Aysha daya kira ta zai zo.....


*******************


          Tun daga waccan ranar Fadwa bata sake shiga sabgar Anam ba. Itama Anam ɗin bata shiga tata ba aikinta ma ya ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta. Babban burinta tayi ta kammala tabar Nigeria ta huta. Bata sake waya da Shareff ba tun waccan ranar shima. Sai dai taga sunayi da matarsa wadda in ta gama Aysha kawai take cewa Shareff ɗin na gaidawa. Takanyi murmushi a duk sanda hakan ta faru, duk da kuwa a ranta tanajin zafi da haushinsa. Sai dai takan ce inma baice yana gaida tan ba sai me.


          ★A ranar wata alhamis da tai dai-dai da zubewar cikin Fadwa Daddy yay kiran Aysha da Anam akan su samesa a gida. Daga wajen aiki Anam ta wuce, inda ta samu Aysha tuni tana can. Basu sami zama dasu Daddy ɗin ba sai bayan sallar isha'i. Cikin kulawa su Abban ke tambayar su babu wata matsala dai ko?. Murmushi Anam tayi, dan kai tsaye tambayar tafi ƙarfi a kanta ne. Tace, “Babu wani damuwa sai na zafi”. Dariya Daddy da Abbah sukai mata. 

         Bayan sun sarara Daddy ya dubesu a tsanake, “Yauwa kun san miyasa muka kiraku nan?”. A tare sukace a'a. Daddy ya jinjina kansa da cigaba da faɗin “Magana ce mai muhimmanci akan aure, yanzu dai kunga kun kammala karatunku, babu abinda ya kamaceku sai aure inba so kuke mu zuba muku ido ku tsufa a gabanmu ba, dan haka muna mai baku umarni ba shawara ba, kowaccenku ta bama wanda yake zuwa wajenta dama yazo mu gana da shi”.

        A ɗan tsorace Anam ta ɗago tana kallon daddy, ganin shima kallonta yake ya sata maida kanta ƙasa. Aysha kam murmushi ne ya suɓuce mata, dan kuwa dama Junaid nata damunta akan hakan, itace taƙi bashi dama saboda ganin yanxu ta Yaya Maheer akeyi ba suba.

       “Mamana yaya dai?”.

 Abba ya katsema Anam dogon tunanin data tafi. Kanta ta girgiza idonta na cikowa da ƙwalla. “Abba babu komai, kawai dai....” sai kuma tai shiru. 

      “Kawai dai mi? Faɗi kanki tsaye kinji Mamana. Maganar aure ba maganace ta wasa ba, shiyyasa muka zaɓi baku damarku duk da hakkinmu ne zaɓa muku mazan aure matsayinku na ƴammata”.

      “Tabbas babu wanda zuciyarta ta aminta zata iya tsaidawa, sai dai kuma bata iya jayayyaba, koda wasa bazata iya ƙin bin umarninsu ba dan batun yanzu ba Abie yasha sanar mata su ɗin kamar shi suke a gareta, idan har taja da su akan koma minene na rayuwa dabai zama saɓama UBANGIJI ba tamkar tayi jayayya da shine. Sannan wani ɓangaren ta sani babu abinda iyayenta ke buri a yanzu tamkar ganin tayi aure, kuma itama a karan kanta tana son taga wannan rana kamar kowace ɗiya mace duk da zatai matuƙar kewar iyayenta a kusa da ita. Abu na gaba kuma burin Abie ɗinta ta fidda miji a ƙasarsu ta haihuwa Nigeria, ta tabbata kuma hakan zaisa su dawo kusa da ita suma duk da can yafi musu kwanciya hankali fiye da nan... A hankali taja numfashi, batare data yarda ta kallesu ba ta gyaɗa kanta alamar amsa umarninsu. Daga Abba har Daddy sunji daɗin hakan, dan haka suka sallamesu akan suna jiransu.


         Gaba ɗaya Anam rasa sukuninta tayi a kwanakin da suka gabata, musamman akan wanda ya kamata ta tsayar matsayin miji a tsakanin samarin dake faman mata kaikawo su biyu. Wato Muzzaffar da Dr Jamal. Daga ƙarshe da ta fahimci zata saka kanta cikin wani hali sai kawai ta kira Mamie domin neman shawararta. Mamie uwace, sai dai ta raini tilon ƴarta da matsayi kala daban-daban bana uwa kawai ba. Shiyyasa Anam bata da wata ƙawa ko aminiya a duniya sama da Mamie, dan ko shawara zatai da Aysha ko Amrah sai ta gama da Mamie, koda abun mai nauyine a gareta tanajin kunya zata rubuta ta bama Mamien a rubuce. Yanzun ma hakan tayi, dan haka koda Mamie ta gama karantawa sai tai murmushi, Abie dake zaune a kusa da ita ta nunawa, shima dai murmushin yayi harda ƴar dariya. Ya amsa wayar yana faɗin, “Nine zan bata amsar daya dace da ita”. 

      Mamie tai dariya da fadin, “Uhhm nidai naga yanda zaku ƙare a wannan rana”. Dariya kawai Abie yayi, ya tafa saƙon ya turama Anam da dama zaman jira take. Shiru tai tana kallon saƙon, zuciyarta cike da wasiwasi. Sai dai kuma a ganinta tunda Mamie tace mata yayi to itama koda son sa bai kai mata har can cikin zuciya ba zata aminta da shi kuwa watarana zata so sa da izinin ALLAH. Sai dai kuma kamar yanda Mamie tace kartai masa magana da kanta bazatayi ba, tunda dama ya jima bai zo wajenta ba bai kuma kira wayarta ba sai lokaci-lokaci sukan ɗan gaisa a chart, shima kullum cikin cemata uzirine ya riƙesa yake.


       ★Kwana takwas dayin wannan magana abin al'ajabi ya sauka a MD Shareff family, ba komai bane kuwa sai baiko da saka ranar Anam da Muzzaffar, Aysha da saurayinta Junaid, za'a haɗe biki tare dana Maheer.

       Su Mommy kasa magana sukai dan mamaki, duk da wani sashe na zukatansu sunji tamkar an musu rahama ne, amma kuma sunajin ɗaci da zafin ganin Anam ɗin zata auri wanda shima ba baya ba, dan mahaifinsa akwai kuɗi, shima kuma Muzzaffar ɗin a karan kansa akwai kuɗin dan wani babban gwaska ne a kamfanib MTN. Duk yanda suka so kuma danne abin a rayukansu kuma kasawa sukai har saida suka haɗu suka tattauna, sai dai a ɓangaren Fadwa ranar har ruwa ta zuba ƙasa tasha. Jitai kaso talatin cikin ɗari na tsanar Anam ya sauka a zuciyarta harta kasa ɓoye hakan. Ita Anam ma data lura da ita sai abun yay matuƙar bata dariya........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_30_*..........Ganin tanata bubbuɗe abincin tana nuna masa ta kurma yay mata nuni da fruit salad kawai. Ta nuna masa abinci, yay mata alamar 1spoon kawai. Yanda ya buƙata haka tai masa, sai dai tasa masa haɗin salad a gefen shinkafar da ɗan yawa saboda tasan yafi buƙatar hakan. Da idanu yay mata alamar ‘thanks’ ta sakar masa murmushi.

         Sun fara cin abincin yay sallama da wanda suke wayar ya ajiye. Harya maida hankali ga abincinsa ya ɗago ya kalla Aysha. “Ina Anam?”. Ya faɗa a taƙaice. “Yaya tana ɗaki bata da lafiya, nayi-nayi ta taso taci abinci amma taƙi kuma ko magani bata sha ba”. Idanu kawai ya zubama Ayshar, sai abincin dake bakinsa da yake taunawa a hankali. Sai kuma ya janye kamar baiso yace, “Kiramin ita”. Mikewa Aysha tai da faɗin to. 

      Da ƙyar ta taso Anam, amma da tace bazataje ba ita abarta. Sai da Ayshan tace, “Kin san dai zai iya zuwa har ɗakin nan ya ɓata miki rai ko”. Kamar bazata tashin ba sai kuma ta tashi tana ɓata fuska ga idanunta jazur. Ya ɗan juya musu baya, dan haka har suka ƙaraso wajen bai ɗago kansa ba. Sai da Fadwa tai magana idonta akan Anam datai gefe da fuska sannan ya ɗago. Kallonta yay da ƙyau ya janye idanunsa. Hakan yasa Fadwa sake yin magana cike da kissa. “Baki da lafiya kuma sai kije ki kwanta da ciwo a ɗaki Anam?”.

    “Uhhm”. 

Kawai Anam ɗin tace a taƙaice, amma ko kallonsu taƙi yi daga ita har mijin nata. Murmushi Fadwa ta sake saki a zahiri, sai dai a ranta daɗin damar data samu takeyi, cikin sake sakin fuskarta tace, “Kije ɗakina saman mirror cikin First aid box akwai maganin zazzaɓi sai ki duba wanda zaki iya sha”.

        Yanzu kam sosai ta juyo ta zuba mata idanu, mamakin kissa da sabon salon Fadwan fes a kan fuskarta, sai dai kafin tace wani abu Shareff da yay kamar bayajinsu ya katseta. “Ki wuce ki ɗakko kizo kici abinci kisha”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa, ta jefama Fadwa dake murmushi har yanzu wani kallon banza ta wuce zuwa bedroom ɗin nata da yau ne karon farko da zata shigesa. Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo tana taɓe baki sannan ta nufi mirror zuciyarta na ƙoƙarin danne abinda ke taso mata saboda kayansu data gani a watse a ƙasa da saman gado alamar ansha bidiri dai. Magunguna ta samu zube akan mirror ɗin wanda har ta ɗauke kanta ta kasa sai da ta sake kallonsu.

     Wani irin mummunar bugawa ƙirjinta yayi lokacin da idonta ya sauka akan sticker ɗin ɗaya daga cikin magungunan. Batama san sanda tai wurgi da maganinba ta fasa ƙara dayin tsalle gefe jikinta na maƙyarkyata. Aysha da Fadwa har rige-rigen isowa ɗakin suke. Yayinda uban gayyar ya shigo a ƙarshe fuskarsa a haɗe. Aysha dai dama kanta tayi, Fadwa kam dariya ta fara sai dai shigowarsa ya sata gimtsewa da sauri itama ta nufi Anam ɗin. Da robar maganin data cillar yaci karo, ya ɗauke kansa da maida dubansa gareta saboda abinda take faɗa tafukan hanunta rufe da fuskarta taƙi yarda Aysha ta buɗe.

      “ALLAH ya isa! ALLAH ya isa ƴar iska wayyo Mamie na ban yafe ba ban yafe ba.....”

    “Ikon ALLAH badai mu bane ƴan iskan ko Anam?!”. Fadwa ta faɗa cikin tafa hannaye da nuna damuwa na makirci saboda ganin ya shigo. Shi kuma ɗakin yabi da kallo har idonsa ya dawo kan robar data cillar ɗin, baima san sanda yakai hannu ya ɗauka ba yawun bakinsa na ƙoƙarin kamewa. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ya buɗe akan Fadwa ransa a ɓace. Sai da gabanta ya faɗi ganin yanda idonsa ya kaɗa yay jazur cikin lokaci ƙanƙani.

      “Kamata ku fita!”. 

Ya faɗa cikin bada umarni ga Aysha. Hanun Anam daketa faman jera ALLAH ya isa har yanzu ta kama suka fice. Sai da suka fice ya tako ya zauna a bakin gadon ya dafe kansa bayan ya ajiye maganin gefensa. Ƙoƙarin danne tsoron dake faɗi a ranta tai ta nufesa, cike da kissa takai hannu kan kafaɗarsa. “Soulmate wlhy na man....”

      “You're vary stupid da zaki faɗamin kin manta. Kinsan suna shigo miki ɗaki zaki ajiye waɗan nan abubuwan a inda idonsu zai gani. Koke da kika saka kanki ajiyewar dole ne sai kin bar stickers nasu a jikinsu saboda baki da hankali!!”.

         Yanda yake masifa ba ƙaramin bugu zuciyarta ke mata ba. Ta shiga girgiza masa kai dan yana yine kamar zai mareta. Ta matso da nufin rungumesa ta basa haƙuri ya tureta ya fice. A falo ya sami su Anam har yanzu tana faman kwarara ALLAH ya isa, Aysha na tambayarta wai miya faru ta kasa bata amsa.

     “Shut up!! stupid!”. 

Ya faɗa a tsawacen daya tilasta Anam gimtse bakinta da janye hanunta dake akan fuskarta har yanzun. Da sauri ta sake maidawa ta rufe ganinsa tsaye a gabansu. “Idan kika ƙara wani magana anan saina mareki, dalla kuwuce kuci abinci”. Kusan a tare duk suka miƙe zuwa dining ɗin, yabi bayansu yana jan tsaki mai ƙarfi. Aysha ta zuba mata abincin, jin yanda yaketa faman jan tsaki a jajjere ya sata cin abincin badan taso hakan ba. Laumarta baifi uku ba tai yunƙurin mikewa ya watsa mata harara. Da sauri ta koma ta zauna kamar zatai kuka. 

        A daidai nan Fadwa ta fito jiki a saɓule, sai dai daka kalleta zaka san tayi kuka. paracetamol ta ajiye gaban Anam tana satar kallonsa, fruit ɗinsa yake sha sai dai fuskar tamkar zatai aman wuta. Kujera taja ta zauna. shiru wajen ya ɗauka babu mai ko tari sai ƙarar cokula. Anam ce ta fara turo nata dan da gaske zazzaɓin nata neman dawowa sabo yake. Aysha ta ɓalla mata magani ta bata. Amsa tai tasha babu musu, tana kammalawa tabar wajen da ɗan gudu-gudu dan karma yace zai dakatar da ita. Itama Aysha sauri-sauri tai ta gama ta gudu ta barsu a wajen......


★★★


        Washe gari duk da ta sake tashi da zazzaɓi tana idar da sallar asuba tahau haɗa kayanta da suka rage, dan tun dare ta tattare wasu. Tambayar duniya Aysha ta mata akan miye take haɗa kaya bata tanka mata ba. Har Ayshan taji haushi tai shiru, tamayi kwanciyarta ta juya mata baya. Koda taji ƙarar jan akwati da fitarta bata motsaba tamayi kamar tai barci ne.

    Taji daɗin ganin babu alamar wani ya tashi a gidan, ko mai gadi ma sai da ta ƙwanƙwasa masa ƙofar ɗaki ya fito ya buɗe mata da mamakin ganinta da kaya. Sai dai yanda tai kicin-kicin da fuska bai bashi damar mata tambayar dake a ransa ba. Duk da nauyin akwatin nata ga wata jikkar data ratayo haka taita jansa har titi. Hijjab din Aysha ne har ƙasa jikinta saboda da kayan barci ta fito. Sai da ta iso har babban titi ta samu napep, ALLAH ya sota ma babu nisa zuwa titin. Kai tsaye ta faɗa masa anguwar dazai kaita. Ya faɗa mata kuɗin tace suje kawai.

       Sanda suka iso gidan ba kowama ya tashi ba musamman yara dake hutawa saboda cikin hutu ake. Da mamaki Mom ke dubanta, ta tura baki gaba da faɗin, “Mom bani two hundred zan bama maigadi a wajensa na amsa naba mai napep.” Komai Mom batace ba ta mika mata five hundred. Fita tai ta kaima baba maigadi amma sai yamaƙi amsa. Dawowa tai ta bama Mom kuɗin tare da faɗawa saman three sitters ta kwanta. Mom dai na binta da kallo. “Lafiya da kaya da sassafen nan?”.

       “Ni Mom na gaji dama da zaman gidan can ALLAH. Kawai na taho ne ni tunda Yayan ya dawo ai”.

         “Hummm”.

Kawai Mom ta faɗa ta ɗauke kanta. Anam kuwa barcine ma ya ɗauketa take a wajen dan jiya kasa barcin kirki tayi, haka kawai ta dinga mafarkin abinda ta gani saboda ta saka abin a ranta harda amai tai kusan sau uku a daren jiya dan ƙyanƙyami abin ya dinga bata. Tunda take bata taɓa ganin halittar namiji ba a rayuwarta koda a hoton ma saboda tsayin daka na tarbiyyar iyayyenta a kanta, duk da kuwa ta tashine a wani yanki da yasha banban da nata. Hatta wayarta tanada matakan tsaro kashi-kashi da idon iyayenta ke akai akoda yaushe saboda bata kariya daga faɗawa tarkon musibar zamani na gane-gane dake zama silar watsa tarbiyyar yaranmu da yawa a wannan zamanin ta hanyar waya..

     Ganin barcin nata zaiyi nauyi Mom tace ta tashi ta koma ciki. Batai musu ba ta mike ta shige ciki ta kwanta. Barcin daya gagareta a daren jiya shi ta samu damar ramawa, dan bata farka ba sai kusan sha biyu da rabi. Wanka ta farayi da alwala tai salla ganin one yayi sannan ta fito dan hayaniyar su Fawwaz dake ɗaukar hankalinta..........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_29_*........“Sannu da zuwa Yaya”. Ta faɗa har yanzu mamaki shimfiɗe akan fuskarta. Idanunsa ya ɗauke daga kanta batare daya amsa ba duk da ba gane hakan ake ba saboda idanun nasa na sakeye a cikin gilashi. Taji haushin yanda yay mata ɗin, sai dai yanayin tsukewar fuskarsa ya sata jin shakka da ƙara ganin kwarjini da fresh daya ƙaro. Muzzaffar ya ƙaraso wajen fuskarsa da murmushi shima yana masa sannu da zuwa. Shima ɗin akan laɓɓa ya amsa masa, koda ya miƙo masa hannu dan suyi musabaha kuma kamar bazai karɓa masa ba, sai kuma ya miƙa nasa shima da ƙyar. Anam ta taɓe baki cikin takaicin shan ƙamshin nasa tana kallon Khaleel da shima yanayin Yayan nasu ya sashi kama kansa, sai dai a ƙasan ransa yana mamakin komawarsa haka dan cikin nishaɗi da farin ciki suka baro gidansu daya fara sauka, kuma da farin cikin ya ɗakkosa a airport.

        Dai-dai suna shigewa ya zare gilashin fuskarsa ya watsa mata wani shegen kallo mai cike da gargaɗi ya wuce. Tai tsamm a waje ɗaya zuciyarta na bugawa da dauri-sauri, amma dan ƙarfin hali sai ta murguɗa masa baki. Muzzaffar kam da kallo ya bisa yana sakin murmushi zuciyarsa na cuɗa masa abubuwa daban-daban duk da ba yaune karon farko daya fahimci wasu abubuwa a idanun Shareff ɗin ba. Numfashi ya sauke a hankali yana nuna mata suje. Itama ajiyar zuciya ta sauke a hankali, jiki a sanyaye ta bisa suka koma wajen zamansu. 


       A ciki Aysha da ke kitchen tana girkin dare ita da mai-aiki ce ta fara leƙowa saboda jin sallamar Khaleel, ta wani zaro ido waje da sakin ihun murnar daya saka Fadwa fitowa zumut daga bedroom. Itama idanu ta zaro na mamaki, dan sam bata san da batun dawowar mijin nata ba. Ya ALLAH, ai tama manta da kowa na falon ta fasa ihun murna da kwasowa da gudunta garesa. Baiƙi bata dama ba, dan shima yayi missing ɗinta, ya ware mata hannaye tako shige jikinsa tare da ɗanesa.

     Dariya Khaleel ya saki yana kauda kansa gefe, hakama Aysha da gudu ta koma kitchen tana dariya ita da mai aiki. Acan waje kuwa Muzzaffar ƙoƙarin yima Anam hira yake yi cike da kulawa amma sam sai ya fahimci hankalinta baya tare da shi, yay murmushi da miƙewa yana faɗin, “Bara na barki madam gobe idan ALLAH ya kaimu da dare maybe zan shigo sai mu ƙarasa, ya kamata kije kema ayi murnar dawowar Yayan dake”. 

      Murmushin yaƙe ta ɗan masa, dan duk suna jiyo ihun Fadwa. Ya miƙa mata ledar da yazo da shi tare da mata bye-bye. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali lokacin daya fice a gate ɗin baki ɗaya, ta ɗan kalla ledar daya bata sannan ta nufi ciki. Har shigowarta Fadwa na ɗane jikinsa, ya wani rungumesa tsam tana hawaye da faɗin wai tayi missing ɗinsa. Sosai ƙirjinta ya ƙara ƙarfin bugun da yakeyi, tai azamar dafe kujera dan jitai kanta ya fara juya mata kamar maijin hajijiya, amma sai tai matuƙar dakewa fuskarta ƙawace da murmushi. Shi kaɗai da idanunsa ke a ƙofar dama ya ganta, ya sauke sassanyar ajiyar zuciya da har sai da Fadwa taji, cikin jin daɗi ta ƙara maƙalƙalesa tana raɗa masa yanda tai tsananin kewarsa a cikin kunensa. Karon farko tun shigowarsa falon ya saki siririyar dariya, a hankali ya ɗan kaima wiyanta sumbata idanunsa na kallon Anam ƙasa-ƙasa. Sai akai sa'a itama dai-dai ta ɗago nata idanun da hasken cikinsu gaba ɗaya ya kore duk da a cikin gilashi suke. Ɗauke idanunta tai tana taɓe baki da juyasu cikin salon ko'a jikina. Numfashi mai ɗaci ya saki da ƙoƙarin dakatar da Fadwa dake ɗan jan hanunsa.

       “Shiiii!!” 

    Ya faɗa cikin wani salo yana ɗaura yatsansa akan bakinta da kashe mata ido ɗaya wanda komai ya ƙara faruwa akan idon Anam data ɗago. Wayarta dake ring ta ɗaga da kaiwa kunenta ta sakin murmushi da ajiye ledar hanunta ta nufi hanyar bedroom ɗinsu cikin ƴar sassarfa. 

     Khaleel da sai yanzu ya lura da ita ya ƙara sakin ƴar dariya dan duk zatonsa shi kunyace itama ta sakata yin hakan. Ledar data ajiye a wajen ya ɗauka yana faɗin, “Ƴar ficikar nan mi kika samo mana haka ne?”. Maganar tasa ce ta saka Fadwa saurin juyowa dan itama bataga Anam ɗin ba, a yanzu kuma har ta shige abunta. Ta buɗe baki zatai magana Aysha ta fito daga kitchen ɗauke da tray. Kai tsaye gaban Shareff da yakai zaune cikin kujera ta dire.

     “Yayanmu sannu da zuwa kazo lafiya? Ya hanya?”.

   Kanta ya shafa kawai batare da yace komai ba. Hakan ya sakata sakin murmushin jin daɗi, ruwan data tsiyaya a kofi ta miƙa masa. Ya karɓa idonsa akan Fadwa da ita sam bata da niyyar hakan ma a garesa... Khaleel daya fahimci kallon da Shareff ɗin yay mata ya dubeta shima. “Madam kina tsaye Aysha ta kwashe ladan daya kamata ki samu, anya kuwa bazamu ƙaro amarya ba a gidan nan dan ba'ai mana tarbar data dace ba”.

      Har ƙasan zuciya maganar Khaleel ta soki Fadwa, ta kalli Shareff dake shan ruwansa tamkar baya jinsu dan hankalinsa na kan tv ne, kallonta ta maida ga Khaleel cikin haɗe fuska. “Yaya Khaleel wane fatan tsiyane wannan dan ALLAH da yammacin nan?”.

         Zama yay yana faɗin, “Naga kamar haka ya kamata muyi ne ai hajjaju, idan kuma baki son amarya sai ki gyara kurenki da wuri”. Da gaske magana ya faɗa mata a kaikaice, amma kuma cikin wasa da murmushi Aysha na tayasa da dariya. Hararar Khaleel ɗin tayi, a karo na farko taji tsanarsa, sai dai batace komai ba taje kusa da mijinta ta zauna fuska a ɗaure. Kofin hanunsa ya ajiye yana miƙewa, bedroom ɗinta ya nufa yana faɗin, “Haɗamin ruwan wanka, ke kuma Aysha kuje ku gyaramin side ɗina”.

      “To Yaya”.

Aysha ta amsa cike da girmamawa. Matar gidan kam takaicin Khaleel ya hanata amsawar, sai dai ta miƙe cike da isa tana gallama Khaleel ɗin harara tabi bayansa. Daga Aysha har Khaleel sunga harar, tana shigewa Aysha tai dariya. “Yaya Khaleel ka sakama Aunty Fadwa jin haushin maganarka fa”. Cikin halin ko'in kula ya ɗage kafaɗa da taɓe bakinsa irin I don't care ɗin nan. Ƴar dariya Aysha ta ƙara saki da mikewa zata nufi waje dan kiran Anam ya sanar mata tana ciki ta shigo...

        “Tabbas na kusa fara shukama Khaleel rashin mutunci a gidan nan in har yana min wannan maganar banzar”. Ta faɗa a fusace tana shigowa ɗakin, dai-dai Shareff na ajiye agogonsa daya cire saman mirror ɗinta idonsa akan wayarta dake maƙale a ɗan sama. Video take ɗauka zatai posting a tiktok ihun Aysha ya sakata fita, ALLAH yasota wayar ta gaji ta rufe kanta. Jin bai tanka mata ba ta ƙara maimaita abinda ta faɗa tana kallonsa. Yanzu dai ya juyo ya kalleta sai dai baice komai ba ya ɗauke kansa yana ƙoƙarin jan necktie ɗin wuyansa.

      “Soulmate kanaji fa ina magana”. Ta faɗa a shagwaɓe da rungumesa ta baya. Kamar bazai tanka mata ba, sai kuma a taƙaice yace, “Miye nawa, maganarku ce”. 

      “Hakama zakace?”. 

   Ta faɗa tana juyowa gabansa. Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akan lips ɗinta, sai kuma yay ƙoƙarin kaudawa amma ta riƙo fuskar tasa, bai samu damar cewa wani abuba ya haɗe bakinsu.....


        Aysha ko koda ta shiga ɗaki sai ta samu Anam duƙunƙune cikin bargo, tana taɓata taji zafi sosai a jikin nata zazzaɓinta ya dawo. Sannu tai mata, ta maida mata bargon ta lulluɓa mata. Ita kaɗai taje tai gyaran, hakan ya sata jan lokaci bata gama ba duk da babu datti sosai saboda sukan gyara lokaci-lokaci. Tana cikin saka turare Shareff ya shigo sanye cikin jallabiya fara tas. Sannu ta masa, ya amsa mata da kai yana bin falon da kallo. Baiyi magana ba dan komai ya masa yanda yake so, ya wuce bedroom ɗinsa baifi mintuna uku ba ya fito ya sake ficewa. Itama kammalawa tai a gurguje ta fito dan kiraye-kirayen salla aketayi.

     Ita ta tada Anam sukai salla, suna idarwa ta koma gado ta kwanta. Kyaleta Aysha tai sai da aka ƙara kiran sallar isha'i sannan ta sake tadata. Koda suka kammala babu yanda batai da itaba akan suje falo taci abinci tasha magani amma taƙi. Dole Ayshan ta barta ita ta fito.  Fitowar tata kusan dai-dai ta fitowar Fadwa daga kitchen tare da mai-aiki. Sannu tai musu dan suna faman shirya abincine a dining, itama tayasu tayi, suna tsaka da shirya abincin ya shigo falon yana waya. Kai tsaye dining ɗin ya nufo dan yana son ya ɗanci abincin yaje ya kwanta da wuri a gajiye yake matuka. Mai-aiki tabar wajen da sauri saboda hararar da Fadwa ta zuba mata. Aysha dai kujera taja masa baya. Zama yay idonsa akan matarsa dan sabuwar kwalliyar tata ta masa ƙyau sosai. Ta ɗan duƙo ta sumbaci gefen fuskarsa. Hannu yakai ya ɗan shafi tata fuskar ya cigaba da wayarsa. Aysha dai ta ɗauke idonta a kansu tun sanda Fadwa takai masa kiss........✍🏻

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_31_*
.........Sai ƙarfe goma da wani abu Fadwa ta baro sashen Shareff, dan tun a daren jiya ta lallashi abunta ya sakko duk da dai yaƙi sakin fuska har yanzun. Amma da yake maza su babu ta ido wani lokacin duk da tsuke-tsuken fuskar tasa hakan bai hanashi ya biye mata ba ya sake murjeta san ransa a daren da safiya ma. Duk kewar kwanakin da sukai ba tare da juna ba sai da ya fanshe kayansa da fatan ALLAH yasa ya samar da madadin abinda ya rasa na tayin cikinsa. A gefe kuma magungunan mata da tasha su Mamah suka ɗura mata sumane suka sake susutar da shi ya kasa kauda mata ido.

       Ta samu mai-aikinta harta kammaa gyara ko'ina, almajirin ma dake zuwa ya share tsakar gidan har yayi ya gama abinsa ya tafi, dama da sassafe yake zuwa shi. Ɗan motsin da taji a kitchen ya sakata leƙawa. Mai aiki ce keta gyaran kitchen ɗin. Cikin girmamawa ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama da tambayarta mita musu na kalaci.

       “Hajiya ai baki faɗi komi za'ayiba, shiyyasa sai na dafa shayi kawai na soya ƙwai”.

   Tsaki taja da buɗe kular da ƙwan ke ciki. Sai kuma ta juyo tana kallon mai aiki. “Wannan ai shirme ne, Soulmate bazaici ƙwai kawai ba. Ita Ayshan yau wani saban salo ne ya hanata fitowa kuyi breakfast ɗin tare?”.

        “Wlhy hajiya ban saniba, badai ta fito ba har yanzu. Itama waccan ɗin yau banga fitowarta ba”.

   Ɗan tsaki taja ta wuce store. Ta ƙwala mata kira da sauri ta sameta, “Ki soya Irish, kuma ban san shirme karki cika masa gishiri. Sai ki ɗumama farfesun jiya dabai ciba zanje nayi wanka”. 

     “To hajiya”.

Fita tai batare data tanka mata ba. Itako ta bita da harara tana ƙunƙuni duk da kuwa ta girmi Fadwa nesa ba kusa ba. Shigewarta babu jimawa Aysha ta fito, kitchen ta nufa kanta tsaye mamakin da gaske Anam ta wuce gida na cinta, dan yanzu tai kiran wayarta Husnah ta ɗaga tace barci takeyi. Suka gaisa da iya cikin girmama juna. 

      “Maman Abu yau duk mun makara kenan ba'ai breakfast da wuri ba ko?”.

    “A'a tun ɗazun na dafa shayi aka soya ƙwai, amma hajiya tace a sauyawa Alhaji bazaici ba”. Cikin ɗan waro ido waje Aysha tace, “Kina nufin Yaya bai karyaba har yanzu? Sha ɗaya saura fa”.

    “Eh ai yanzu hajiyar ta dawo daga wajensa ma”.      

   “Lallai ma Aunty Fadwa, shine ita bazata zauna ta haɗa masaba kuma ta bar miki. Na kula har yanzu bata gama sanin wanene Yaya ba.”

          “Maman Abu dai batace komai ba, dan ita kanta yau ta jinjina wautar Fadwa ɗin duk da tun jiya take mamaki akan duk abinda ya faru. A yanda ta santa da soyayyar Shareff tun suna gida batai zaton zatazo gidan aure tai sakaci haka ba, tunda dai komai na mace Fadwa ta iya nan kuma mahaifiyarsu (Gwaggo Halima) batai sakaciba gaskiya musamman ma akan Fadwa data kasance mace babba. Fatan dai ba raye-raye a wayar nan dake ɗauke mata hankali tazo ta cigaba dayi anan ɗin ba, dan tara ƙawayen data saba tun acan taga har anan kullum cikin zarya suke.

        Da taimakon Aysha aikin ya kammala yanda tasan Shareff zaici a kwanciyar hankali. Suka ɗiba nasu ta shirya na Shareff ɗin da Fadwa. Tana ƙoƙarin fita Fadwa ta fito cikin kwalliya sai zabga ƙamshi takeyi. Gaisheta Aysha tayi. Ta amsa cikin raba hankalinta biyu tana buɗe abincin. Da murmushi ta kalli Aysha. Aysha ta mayar mata batare da tace komai ba. “ALLAH ya kaini ran aurenki shatu. Dama inata zullumi nakai abincin nan ya gane banice nayi ba”. Ita dai Aysha dariya tayi kawai. Fadwa zata ɗauka tray ta amsa da cewa. “Bara na ɗauka sai na gaishesa daga nan”.

       A tare suka nufi sashen nasa, sun samesa a falo zaune yana waya. Aysha da tasan bai cika damuwa da zaman dining cin abinci ba sai ta dire tray ɗin saman centre table. Fadwa kam gefensa takai zaune dan haka ya ɗan kalleta idanu ƙasa-ƙasa dan kwalliya na ɗaukar hankalinsa matuƙa ga mace, Fadwa kuwa gwanace wajen iya tsarawa nan ɓangaren ta ciri tuta dan batajin ganda kamar girki da sauran ayyuka da latsa waya ke hanata nutsuwar yinsu yanda ya dace. Ya ajiye wayar daya kammala yana kallonta da ƙyau, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Aysha dake gaishesa.

       “Kin tashi lfy?”.

    “Lafiya lau Yaya, ya gajiyar tafiya?”.

“Alhmdllhi”.

Ya faɗa a taƙaice. Harta yunƙura zata tashi ya dakatar da ita. “Ku har kun karya ne?”.

      “Yanzu zanje na karya Yaya”.

Ɗan jimm yay kamar bazaice komai ba. Dan har ya ɗauke idonsa a kanta sai kuma ya sake juyowa.

“Har yanzu tana kwance ne?”. 

     Ta fahimci Anam yake nufi. Dan haka ta girgiza kanta. “Tun ɗazun ta tashi ta wuce gida”.

     Fadwa da sai yanzu ta saka musu baki, tace, “Gida kuma? Rijiyar zaki wai?”.

   “Eh aunty, tana idar da sallar asuba kusan 6:30 nama zata da wasa take na shareta sai dana tashi naga da gaske ta tafi shine na kirata Husna tace min tanama barci”.

       Daɗine ya sauka har cikin ƙasan zuciyar Fadwa, ko banza shirinta na jiya yayi aiki tunda Anam ta bar mata gida a kan gaɓa. Amma saboda mazuran da yay jiya sai ta nuna rashin jin daɗinta a yanzu har hakan ya bama Aysha mamaki dan tasan dai ba shiri suke da Anam ba. Zaman nan da akai tare dan ya zama dolene kawai. Shiko mai gayya komai bai ce ba. Sai ma umarni ya bata akan ta tashi ta bashi abinci. Cikin shauƙin farin cikin tafiyar Anam ta miƙe ta fara haɗa masa tea. Aysha kuma ta miƙe ta fice ta basu waje.

     Kusan itace ma ta basa abincin a baki tana zuba masa hirar wahalar da taci lokacin da ta samu miscarriage. A ransa yana jin rashin daɗin rasa ɗan tayinsa, amma ya barma ALLAH tunda dama shine ya bashi bada wayonsa ba. A fuska kam tausayintane sosai sai dai baice komaiba. Rashin maganar tasa yasa ta sake yarda da maganar su Sima lallai da gaske baya buƙatar cikin a yanzu daman. Ta godema ALLAH data farga da wuri ta ɗauka mataki gashi yanzu farin cikin dake neman kufce mata na dawowa gareta.

        Basufi awa ɗaya da yin breakfast ɗin ba ya miƙe ya shiga bedroom, babu jimawa ya fito cikin shirin fita. Kallonsa take da mamaki. “Soulmate badai fita ba ko?”. Yi yay kamar baijita ba, ya kai zaune da ɗaukar wayarsa ɗaya, danne-dannensa yay yakai kunne alamar kira, hakan ya sata yin shiru tana kallonsa har ya kammala. Sake dubansa tai a shagwaɓe. “Dan ALLAH Soulmate fita zakai wai?”. Wayar daya gama ya ajiye gefensa, batare daya kalleta ba ya bata amsa. “Dama munyi dake bazan fita ba?”. Baki ta tura da dawowa kusa da shi ta zauna ta narke masa a jiki. Zata fara shagwaɓa sallamar Khaleel ta dakatar da ita. Kai tsaye ya bashi umarnin ya shigo, maimakon ta tashi a jikin nasa saita sake narkewa har Khaleel ya shigo. Kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa tunda indai taɓarar Fadwa ce ba yau ya fara gani ba. 

       Shareff daya fahimta bata da alamar tashi ɗin, ya dubeta yana ɗan tsuke fuska. “Gyara mana”.

   Baki ta ƙara tura masa, sai kuma ta tashi fuska a murtuke tabar falon ko amsa gaisuwar Khaleel batai ba dan har yanzu haushinsa na jiya na ranta ya mata addu'ar kishiya. Baibi takanta ba shi dai ya gaida Yayansa. Suka mike a tare suka fice dan motarsa Khaleel ɗin ya amso wajen wanki da yakai tun sassafe. Khaleel ne ke driving ɗin, yana gefensa suna hira da gaba ɗaya ma akan company ne. Sai ɗai-ɗai data shafi zamansa a gidansa wanda duk shine ke masa tambaya akan wasu abubuwan.

      Sun fara shiga sashen Daddy inda suka sami iyayen nasu uku zaune suna shan hira. Dan in har Abie na gari to bazaka taɓa rabasu ba sai dai in sun fita aiki, yau kuma babu aikin shiyyasa har breakfast tare sukayi. Bayan ya gaisheasu su duka suke masa fatan alkairi akan abinda yaje yayo cikin kulawa. Yaji daɗin addu'oin iyayen nasa dan su duka yana matuƙar jinsu a ransa. Ya ɗan jima anan tare da su suna hira har Khaleel ya fice ya barsu, sai da aka kira sallar zuhur suka fito suka nufi massallaci. A lokacin Anam nacan cike da farin ciki. Dan bata jima da tashi a barci ba Fawwaz ke sanar mata su Mamie sunzo. Da farko bata yarda ba su Husna harda Mom nata mata dariya. Ganin haka yasa ta mike ta nufi gidansu, tun a gate maigadi ya sanar mata, aiko da gudu ta shiga tana ƙwala kiran Mamie!! Abie!!. A lokacin Abie na can tare da su Shareff zasuje massallaci.

     Bayan an idar da salla koda ya shigo gidan sashin Mom ya fara shiga, suka gaisa har da ƙannensa sannan ya shiga wajen aunty Amarya. Daga can sai sashen Gwaggo data tsaresa yaci birabisko data dafa. Baici ba, amma yace ta saka masa a kula zaije dashi gida yaci. Taji daɗin hakan har cikin ranta, ya fito yana murmushin tsokanarsa da take. Sashen Mommynsa ya nufa inda anan ne ya zauna sukasha hirarsu har take kawo masa ƙarar Maheer da yay biris kamar ba shirin aurensa ake ba. Haƙuri ya bata da tabbatar mata zai kira Maheer ɗin a satin nan zai taho gida insha ALLAH. Taji daɗin hakan har a ranta. Yay mata sallama akan zaije gida sai zuwa dare zai sake leƙowa.

       Daga nan gidan su Anam ya shiga. Inda ya sameta nanuƙe da Mamie da Abie tana zuba surutu tana cin abinci. Suko sun biye mata sai dariya suke cike da farin cikin kasancewa da abarsu. Shigowarsa baisa ta daina surutunta ba. Sai dai taƙi yarda ta kallesa ko sau ɗaya dan tunda taji sallamarsa tai gefe da kanta. Shima kallo guda yay mata ya ɗauke kansa, ya maida hankalinsa gasu Abie. Tayin abinci Mamie ta masa babu musu yace zaici. Kasa haƙuri Anam tai sai da ta kallesa. Ya wulla mata harara ta tura masa baki da ƙyaƙyƙyafta idanu. Fuska ya sake tsukewa cike da gargaɗi a gareta ta taɓe baki. Duk abinda suke Abie na lure da su sai dai yayi kamar baya gani har Mamie ta dawo da abincin. Mace ce da sam bata da son jiki, yau da safe suka iso ƙasar amma bata zauna jiran wani ya basu abincin rana ba bayan na safe da suka samu Mom ta shirya musu. Tayi girkinta kodan farin cikin Anam, dan abinda tafi sone ta girka. Abincin ya faraci a nutse suna hirar China da su Mamie, itako ta daina hirar tana cin abincinta a shiririce tana saurarensu, sai dai sai balla ma Shareff harara take ta gefen ido.

        Sai da aka kira la'asar suka fita da Abie massallaci. daga can ya wuce gida dan tun ɗazun yake ganin kiran Fadwa na shigo masa yaƙi ya ɗaga, saima wayar da yasa a silent.........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_34_*
...........A wajen ƴan biki kuwa dawowar ƴan ɗaurin aure ya sake ruɗa gidajen biyu, bakajin komai sai guɗa da kirarin maroƙa tako'ina. Bakin su Daddy ya kasa rufuwa saboda tsananin farin cikin da suke ciki na sake samun damar aurar da yaransu a karo na uku. Hakama Mommy tana a cikin tsananin farin cikin cikar burinta na sake aurar da Maheer ɗinta a ganinta ta raba ƴaƴanta biyu da ƙaya. Shiko ango Maheer ko walwala baka gani a fuskarsa, dauriya kawai yake na amsa gaisuwar jama'a da taya murna a garesa saboda baya son su Daddy suga kamar bai ɗauka shawararsu ba......

        A ɓangaren Mamie da Abie ma duk da wannan rana ta tilon ƴarsu tazo musu a yanayin da basu gama shiryata yanda suke so ba hakan bai hanasu kasancewa cikin ɗunbin farin ciki ba, dan albarkar auren suke nema mata ba wai tsarabe-tsaraben cikinsa ba. Fatansu ALLAH ya bata zaman kafiya da zuri'a masu albarka ita da mijinta. Suna zaune a ɗakin Abie da take barci suna kallonta fuskikinsu murmushi ya kasa sauka, ga ɗunbin tausayinta da ƙaunarta na ratsasu. Abie ya kauda kai gefe yana murmushi ganin Mamie na sharar hawaye, cikin son danne nasa dake ƙoƙarin sakkowa ya miƙe yana kai waya kunnensa tamkar zaiyi kira ya gudu a ɗakin......

        Ƙananun maganar da suka fara fitowa a bakunan mutane saboda jin yanda ɗaurin aure ya kasance suka fara yawaita a gidan har wasu a dangin Mommy ya fara isa kunnuwansu. Da yawansu mamaki suke nunawa jin yanda al'amari ya kasance dan su dai basu san da wannan aure ba. A cikin ƙanen Mommy da abin ta jisa tamkar saukar aradu ta kasa haƙurin shanyewa kamar kowa ta shiga neman Mommy. Da ƙyar ta samota a sashen gwaggo wajen tsoffi na ƴan uwa da ƙawayen ta da suka taru acan. 

        “Ke ko lafiyarki kuwa Samira kika shigo mana kamar wadda take a rikice”. Gwaggo ta faɗa ganin yanda aunty Samiran ta shigo har tana cin tuntuɓe. “Gwaggo dole kike ganina a haka, wani mummunan labari nake jiyowa yana tashi a gidan nan dana gaza gaskatawa, Aunty dama akwai auren wata bayan Fadwa akan Shareff?”.

      “Samira ban son takale-takalen masifa ina cikin farin cikina wane aure kuma?”.

  “Humm aunty kenan, aure nawane aka ɗaura a gidan nan yau, kidai bincika dan yanzu naji anata ƙus-ƙus wlhy wai dama matarsa ce sai dai yau aka sanar.” A rikice Mommy ta kalli gwaggo, itama gwaggon kallonta takeyi baki buɗe. Cikin ƙarfin hali gwaggo tace, “Nifa sam bamma gane wannan soki burutsun nakiba wlhy Samira”.

       “Nima da nake faɗa mukun na kasa ganewar, inaga bincikawar dai kamar ya kamata kuyi”.

   Suɓucewa plates dake a hanun Mommy sukayi, ƙirjinta na matuƙar bugawa da sauri-sauri. Fitt ta fito ɗakin Gwaggo na ƙwala mata kira amma bata juyo ba. A yanda ta fito ɗin yaja hankalin mutane da yawa suka shiga binta da kallo. Kai tsaye sashen Daddy ta nufa, sai dai koda ta shigo bata samu kowa ba sai kwanikan abinci dake barbaje alamar anci. Har bedroom ta leƙa, nan ma babu kowa a ciki. Da sauri ta shiga laluben wayarta dake cikin handbag ɗin hanunta da take tara kuɗin yinin bikinta dan yau takeyi, hannunta ma rawa yake, tadai samu da ƙyar ta lalubo number Daddy tai dailing. Sai da ta kusan tsinkewa ya ɗauka, babu ko sallama tace, “Daddyn Shareff wani shirme nakeji yanzun, nazo sashenka kuma baka nan?”.

       Kai tsaye ya gano abinda taji ɗin, dan haka a dake yace “Ina waje tare da mutane, idan na shigo sai muyi magana...” ƙitt ya yanke wayarsa tana ƙoƙarin dakatar da shi. Tsananin tsoro ne da firgici ya ƙara saukar mata. Tabi wayar da kallo kamar zata gano Daddy ɗin a ciki. Kai ina bazata iya haƙuri ba sam, akalar kiran nata ta maida ga wani yayansu data tabbatar Daddy baya ɓoye masa komai dan abokinsa ne shaƙiƙi tun ƙuruciya. Bugu biyu ya ɗauka, tai ƙoƙarin shanye tashin hankalinta dan tasan saita lalama Yaya Awwalu zai faɗa mata abinda take bukatar. Bayan ta gaishesa yake cemata tayi haƙuri bai shigo ya mata an ɗaura aure ba wani uzirine ya taso masa amma zuwa anjima zai dawo gidan.

      “A'a babu komai Yaya ai kai mai yine, yanzuma na kiraka ne saboda inji ko kana tare da abokin naka dan zuwa anjima ina son ka ɗan ƙarama Maheer faɗa kasan yaran nan da taurin kai, Shareff ya fisa haƙuri da biyayya tunda kaga shi duk aurarrakin nan zaɓinmu ne amma ko yau bai tada hankalinsa ba akai”.

          Yaya Awwal yay ƴar garan murya irin ta manya da ɗan murmushi, “A'a karki damu shima zai kwantar da hankalinsa ai, kuma hankalinsa aiba ɗaya dashi Mustapha ba. Amma zan shigo ɗin insha ALLAH, yaya jikin shi Mustapha ɗin ma? Dan ina tambayar bangansa ba akace yana asibiti babu lafiya”.

      “Eh wlhy zazzaɓine ya kadashi amma da sauƙi, inagama yau za'a sallamosa tunda ba'a kai amarya babu ango ba”.

    A karon farko yay ƴar dariya mai sauti da faɗin, “Wannan gaskiya ne, ALLAH dai ya basu zaman lafiya da haƙuri da juna tunda duk gidane, sai dai dan ALLAH kiyita ƙara nusar dashi da tausarsa tunda su duka ƴan uwansa ne kar zuminci ya samu matsala azo ana hai hai babu daɗi. Gaba ɗayansu ɗaya suke a wajensa babu wadda tafi wata.......”

        Tunda ya fara jawabin nasa na ƙarshe jikin Mommy ya hau rawa, bazata iya jin ƙarshen zancem ba dan haka ta yanke wayar. Hajijiya taji tana neman ɗibarta, a dai-dai nan Gwaggo da taga shiru bata dawoba ta biyota ta shigo. Salati ta saka da riƙeta da sauri. “Ke ko kina lafiya zaki kashe kanki Nafisa?”.

      Kuka Mommy ta fashe da shi, “Gwaggo sun kasheni, wlhy sunyi a banza, har abada jinina dana Usman bazasu zauna a inuwa gudaba. Gwaggo na rantse yau duk masifar da za'ai a gidan nan sai dai ayi sai Shareff ya saketa, ni Muhammad zai cima amana, ni Muhammad zai yaudara ya zalunta.....”

      “K wai miya farune kin sani a duhu?!”.

  “Gwaggo aure fa suka ɗaurama Shareff da ɗiyar maƙiyana, wai ƴar gidan Usman. Kuma tabbas batun yau ba ma.”

        “Ƴar gidan Usman?!!”.

Gwaggo ta faɗa a razane, Mommy bata amsa mataba ta mike fuu ta fito hanunta dafe da kanta dake juya mata. Gwaggo na ƙoƙarin tsaidata yanzu ma bata saurareta ba. kai tsaye hanyar gate tayi, Samira ta biyita da sauri. “Yaya! Yaya miya faru ne? Da gaske ne ko?”.

    Bata iya bama Samira amsaba ta fisgi gyalenta tai waje, kasancewar anata ɗaukar ƴan biki da kawosu ta samu a napep. Daddy daya hangota da yake suna zaune a ƙofar gidan cikin runfa ya miƙe, sai dai kafin yazo har napep ɗin tabar wajen.......


          ★Tun ɗazun ya farka saboda zuwan gayyar abokansa da sukaje ɗaurin aure. Shidai kallon mamaki yake musu, dan baiyi tsamanin ganinsu haka da yawa ba a waje ɗaurin auren ƙanin nasa. Suko sai faman washe baki suke da tsokanarsa a sigar daya kasa ganewa dan kowa ya kasa fitowa fili yace wani abu saboda ganin Fadwa tare da shi. Ga kuma dama Dr Jamal ya rokesu kar suce komai anan Please. Basu wani jima sosai ba suka fita acewarsu zasuje cin abinci zuwa anjima zasu dawo duk da Doctor yace maybe ma zuwa dare su sallamesa. Bayan fitarsu Fadwa ta dawo kusa da shi. Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska sai yaji wani iri, hannu ya miƙa mata alamar tazo, tai kamar zata noƙe sai kuma ta nufesa ganin yay mata alamar roƙo. Jikinsa ya jawota ya rungume, ya sakar mata sumba a gefen wuyanta tare da ɗaura kansa a kafaɗarta yay shiru. A hankali ta lumshe idanunta da haɗiye kukan dake neman ƙwace mata. 

      “Shii!!”.

  Ya faɗa a hankali cikin kunnenta yana kai hannu ya tallafo fuskarta ya juyo da ita...... Burumm ta faɗo ɗakin kamar an jehota. Su dukansu sukai saurin kallon ƙofar, ganin Mommy ya sashi janye jikinsa cikin jin tsananin kunya, Fadwa kam wani irin takaici ne ya tsargi ranta kamar ta dannama Mommy zagi. Mommy kam da sam hankalinta bama yakai kan yanda suke ɗin ba ta jefa masa takarda da biro saman jiki......

       “Rubuta mata saki uku yanzu-yanzun nan da manyan baƙi yanda iyayenta zasu gani da ƙyau bama ƙanana ba...”

     Cikin tsananin mamaki da rashin fahimta yake duban mahaifiyar tasa. Yayinda ƙirjin Fadwa yay wani irin mahaukacin dokawa tamkar gagarumar aradu ta bada sautin fashewa. Ita dai tasan ita kaɗaice matarsa ai........

          Takarda da biron ya tattara ya ɗauka, a hankali cikin muryar mara lafiya ya dubi Mommy. “First luv ban gane ba. Wazan saka?”.

      “Shegiyar yarinyar da aka ɗaura maka aure da ita a ɓoye mana, inba hakaba zan tsine maka Al-Mustapha, tsinuwa mai muni kuwa da a duniya ko kai bazaka ƙara morar kanka ba balle waninka!!”.

       A kusan tare zuciyarsa data Fadwa ta nema wantsalowa waje. Cikin rawar lips shi yay ƙarfin halin faɗin, “A...Aure kuma? First luv n... Ni aka ɗaurama aure??”.

     Sake fusata ta tambayar tayi, cikin tsananin kaushin murya ta sake bashi umarni batare data amsa masa tambayarsa ba. “Bani da lokacin maka wani bayani anan, dan wlhy zan iya tsine maka Al-Mustapha. Da manyan baƙi cikin sakanni ashirin kacal ka rubuta Kai Al-Mustapha Muhammad Shareff, ka saki ƴarsu Anam Saki uku har abada bakai babu ita. Inko ba hakaba shinuwa zata tabbata a kanka bayan cikar waɗan nan sakannin”.........✍*_🙆🏻Ni balki wannan jidali har ina. Wannan fa shine TA LEƘO TA KOMA!. Shareffuddeen zaɓin Mommy ko zaɓin Daddy?🤐🚶🏻._*

      
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_32_*
...........Itama Aysha a ranar ta dawo gida da dare, shine ma ya kawota tare da Fadwa. Anam najin sanda suka shigo gaida Mamie ta maƙale a ɗaki har suka fita bata leƙo ba. Washe gari Mom tazo da mai gyaran jiki. Ba hajiyan bace zatai mata da kanta, ma'aikatan ta ne, amma saboda Mom tai alƙawarin shigowa kullum ayi a gabanta insha ALLAH. Ita dai Anam bata damu da wannan zancen gyara ba tun amsar da Mom ta bata a waccan ranar, dan haka koda suka korata a falo da zasuyi magana ko'a jikinta tama nufi can cikin gida wajen Aysha dake fushi da ita ta barsu. Da wannan damar su Mamie sukasha hirarsu dan Hajiyar Sudan tasan Mamie ɗin sukan haɗu idan ta shigo Nigeria. 

       


_________________


       Tun daga wannan ranar aka farama Anam gyaran jikin mai inganci. Yayinda a cikin gida aketa shirin biki gadan-gadan babu wasa. Ita da Shareff dai haɗuwa ta gagara. Da zaran taji ya shigo gidan zata bar falo idan har tana zaune ne ma. To yanzu ma gyaran da ake mata babu dare ba rana yasa bama zaman falon take sosai ba saboda dokar Hajiyar sudan. Randa Maheer ango ne dai ya iso ta kasa haƙuri sai da ta fito cike da farin ciki suka gaisa. Sai dai yanayinsa ya saka mata sanyin jiki dan duk ya ɗan rame gashi babu fara'a tattare da shi.

    Washe garin da Maheer ya dawo biki na saura kwanaki goma sha biyar da daddare Shareff yazo gidan ya samu iyayensa a falon Daddy. Sune sukace yazo sunada magana da shi. Bai wani damu ba dan duk zatonsa maganar dai bata wuce akan Maheer ba daya kasa kwantar da hankalinsa akan auren nasa.

       Bayan ya gaishesu Daddy ya fara bayani kai tsaye kamar haka. “Shareff mun kiraka nanne matsayinka na Babba ga duk yaran gidan nan. Da farko dai akan maganar auren ƴan uwanka ne, Maheer ya samemu jiya akan yanada wadda yake so ba wannan da ake shirin masa aure da ita ba, sai dai mahaifiyarku tace bazai aureta ba, hasalima ta haramta masa auren yarinyar. Munyi-munyi da shi yaƙi ya sanar mana wacece, sai dai ya roƙemu mu roƙa masa ita ta amince masa dan ALLAH. To kai tsaye dai mun amsa wannan roƙo nasa, sai dai munce yayi haƙuri a ɗaura wannan ɗin tunda an riga an gama magana karmu kasance ƙananun mutane, munga rauni a tare da shi, duk da baiyi jayayya damu ba. Dan haka munaso ka kasance da shi dan hankalinsa ya sake kwanciya. Sai auren Aysha da shima aka ɗaga kamar yanda dangin ango suka buƙata, duk da dai bakama san da zancen ba dama mun bari sai ka dawo a sanar maka”.

      Numfashi Shareff ya sauke a hankaki, kansa a ƙasa cike da girmamawa yace, “Insha ALLAH Daddy zanyi hakan, ita kuma ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi, duk yanda kukayi dai-dai ne ai”. 

     “Amin ya rabbi. Magana ta gaba kuma akan ƙanwarkane itama Mamana”.

Gabansa ne ya faɗi, amma sai ya cije bai nuna alama ba, sai ma ruwa daya ɗauka ya ɓalle murfinsa ya kai baki.. Daddy ya cigaba da faɗin, “Wasu dalilai sun sa mun yanke shawarar aurar da ita itama rana ɗaya da na Maheer ga wani bawan ALLAH da muke da tabbacin zai riƙe mana amanarta da izinin ALLAH. Itama an gama tsaida komai....”

         Gaba ɗaya ya watso ruwan daya gumtsa har yana fesama Abbah dake a kusa da shi. “Subahanalillahi” Abba ya faɗa yana yana riƙo ruwan dake neman subucewa a hanun Shareff ɗin. Daddy da Abie kam sannu suka shiga masa dan bayan fesar da ruwan tarine mai ƙarfe ya sarƙesa. Idanunsa da sukai masifar kaɗawa da ja cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗago yana kallon Daddy.

      Sannu Daddyn ya ƙara masa hakan ya sashi maida idanun ya risinar. Daddy ya cigaba da faɗin “Karka damu munyi bincike mai zurfi a kansa kafin yanke wannan hukunci, sannan munada dalilai masu ƙarfi akan hakan. A matsayinka na babba saika sanya albarka a lamarin duk da yazo a ƙurarren lokaci ko”.

          Kansa ya ƙara ɗagowa da ɗan haɗiyar yawu yana murmushin yaƙe. “ALLAH ya sanya alkairi”. Ya faɗa a takaice yana maida kansa ya dukar. Da amin suka amsa masa, daga haka suka cigaba da bayanin abinda yasa suka kira san. Bai bar wajensu ba sai kusan goma da rabi, ko'ina bai shigaba dan yasan duk sunyi barci ma yanzu ya shiga mota jiri na kwasarsa ya bar gidan....


       

         ★Ranar laraba aka saka amaryar Maheer a lalle, ga Anam dai babu abinda ya danganci hakan sai baƙi da suka fara cika gida. Sai a ranar alhamis ne da safe Abie da Mamie da Aunty Mimi da Abba da Daddy suka zaunar da ita. Bayan gama mata nasiha suka koma lallashinta, sai dai gaba ɗaya bata fahimtar wani fari ko baƙi a zantukan nasu, dan da alama brain nata ta raba tafiya da ƙwaƙwalwarta wajen yin aiki. har suka gama lallashinta taron ya tashi babu alamar numfashinta na fita daga gangar jikinta, a da kamar bata damu da auren ba, sai a ƙwanakin nan kuma jikinta ke mata matuƙar sanyi, rauninta na bayyana a zahiri. Bata samu damar fashewa da kuka ba sai da Aunty Mimi ta kamota suka komo ciki dan da suna a falon Abie ne.

       Mamie dai kasa tsayawa tai, sai aunty Mimi ce ke lallashinta amma kuka ya gagara tsayawa. Gaba daya ta birkice cikin ƙanƙanin lokaci har takai idanunta sun fara daina gani da ƙyau. Hankalin su Mamie ya tashi, amma basu yarda kowa ya sani ba wani abokin Abie amintaccensa doctor ne na ido yazo ya dubata. Ya tabbatar musu damuwace ta kawo hakan, dan haka ya basu shawarar ai mata allurar barci ta huta. Wannan shine dalilin hana yin kamun amarya a yau da aka shirya sai dai anyi ɗan shagali duk da ba kowa yasan minene ya hana ɗin ba. A take ƙananun magana suka baje gida musamman ga su Mommy.

     Duk da sun kasa gane kan zancen sunji farin ciki, har Gwaggo ta kasa haƙuri sai da tabi diddigin jin ba'asi, jin amarya Anam ce babu lafiya sai gata itada Mommy da Fadwa wai duba Anam ɗin lamarin zam-mamaki. Suna fita kuwa suka sanya dariya. Dan dama tun jiya suke dariya da ƙananun maganar rashin kawo lefen Anam gidan, acewarsu wane aurene haka kamar auren sadaka. Duk da zancen nasu ya koma kunen su Mamie harda su Daddy ma babu wanda yace komai.    

      Suna tsaka da wannan farin ciki Dr Jamal ya kira Fadwa yace tazo gida. Sagale tai tana kallon wayar dan ya yanke, kamar zata share sai kuma dai ganin da number ɗin Shareff ya kirata ta yanke hukuncin zuwa duk da kuwa a cikin tashin hankali suke da shi a kwanakin nan. Tadai danne ne kowa bai sani ba sai kawayenta su Sima dake ƙara tunzurata da tabbatar mata itace mai gaskiya.

        Tasan bama suba duk wanda zataima bayani dole zai bata gaskiya. Dan kuwa ita dai babu abinda tai masa a kwanakin nan ya ɗorama kansa wani irin baƙin rai da yafi halinsa data sani. A gaba ɗaya satin nan baya fita aiki kullum yana gida kwance, da farko ta fara lallaɓashi da son jin minene matsalarsa? sai ya dinga daka mata tsawa da faɗin karta damesa, ta shanye na farko dana biyu ana uku takaici da ɓacin rai yasa tai fushi itama ta sharesa. Sai shekaranjiya da Dr Jamal yazo ya dubasa wai bashi da lafiya, haka ta haɗiye taje ta masa sannu ta kula da shi kuma, amma hakan baisa ya sake mata ba. Zuciyarta ta ƙara tunzura tun a jiya ta haɗo kayan tahowa nan gidan biki, gudunma karya ƙara ɗaukar azaba ya ɗora mata ta sanarma Mommy ta masa magana akan zata dawo nan gidan har sai an gama biki, bata san yaya sukai Da mommy ba tadai kirata tace ta taho, koda taje masa sallama bai tanka mataba sai hannu kawai ya ɗaga mata, itako tai fushi tai fitowarta ta barosa duk da taga kamar baida lafiya, ga wata rama da yayi a ƙanƙanin lokaci. Amma murnar Anam zatai aure yasa takejin dolene ta zam gaba-gaba a bikin nan ai, shiyyasa ta tsallakesa tai tafiyarta........✍*_Tofa, su kawu Sharuffudden mike hwaruwa ne haka da ciwo kuma?🤭🤪🚶🏻_*
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_33_*
.........Mommy ce ta shigo falon tare da aunty Iklima, batare data lura da halin da Fadwa ke ciki ba tafara magana cikin raba hankalinta biyu. “Fadwa a fiddo gift ɗin nan dan yanzu nake son ku wuce gidan wankin amarya ɗin nan ke da Bintu kafin sauran su biyoku a baya”.

      “Mommy inaga sai dai aunty Bintun tayi gaba. Dr Jamal ne yay kirana asibiti”.

    “Asibiti kuma? Mi ake acan ɗin?”.

“Inagafa jikin Soulmate ne, dan nata kiransa dama ɗazun bai ɗagamin ba sai nai tunanin baƙin ran nasa ne bai gama sauka ba”. Ganin tana tafiya tana magana Mommy ta riƙota da sauri. Kafin tace komai Fadwa ta rigata magana da ƙoƙarin yin gaba. “Mommy wlhy hankalina a tashe yake idan na dawo mayi magana”. Sakin nata Mommy tayi, Fadwa ta ƙarasa fita da sauri. Cikin sa'a ta samu napep data ajiye wasu mata.


        Azalzalar mai Napep data dingayi yay gudu ya sakasu isowa da wuri, ta miƙa masa dubu, yana mata maganar ga canjinta bama ta sauraresa ba tai gaba dan a rikice take. Tana tafiya tana kiran Dr Jamal, cikin sa'a ya ɗaga ya sanar mata inda zata samesa, sai dai bata gane ba. Dan haka ya turo mata Nurse ta shiga da ita. 

       Yana kwance samɓal Dr Jamal na gyara masa ledar ƙarin ruwan da ake masa. Ta ƙarasa cikin sassarfa gaban gadon, idanunsa a lumshe suke alamar barci, yayi wani fayau da shi saboda ramar da yayi sosai, wadda ita sai ma yanzu ta sake ganinta a bayyane garesa.... Dr Jamal da gaba ɗaya yake cike da haushinta ya juyo yana kallonsa babu walwala tare da shi. “Fadwa yanzu kinyi dai-dai kenan? Mijinki na a cikin irin wannan halin amma kika tsallake kika tafi gidan biki kika barsa?. Badan ALLAH ya kai Khaleel gidan ba kin san kuwa komai zai iya faruwa?”.

      Kukan da take rikewa ta saki, ta kai duƙe gaban gadon tana kamo hanunsa da babu ƙarin ruwan. “Doctor ni ban san jikinsa yayi tsanani hakaba wlhy, duk ta inda na ɓullo dan nasan damuwarsa ya kasa bani damar hakan..”

           “Amma sai ki sanar a gida tunda ke yaƙi ya sanar miki....”

    Shigowar su Abba ya hanata bashi amsa. Khaleel dake gaba ya watsa mata harara ya ɗauke kansa. Taga harar tasa amma sai ta ɗauke kanta, tare da zare hanunta daga cikin na Shareff. Abba da Abie dai sai maimaita sunayen ALLAH suke a bakunansu, dan yanda Shareff ɗin yay fayau na rama a ƙanƙanin lokaci ya basu tsoto. Dr Jamal ya gaidasu, tare da kwantar musu da hankali akan su masa addu'a dan jikin nasa da sauƙi. Addu'ar fatan ƙara samun sauƙin sukai masa, tare da jajanta al'amarin. Abie ya kalli Fadwa dake gefe tsaye, faɗa ya fara mata akan miyasa bata sanar da kowa Shareff ɗin baida lafiya ba. Shiru tai taƙi tankawa, sai ma fuska data ɗaure tamau dan kamanin Anam data gani tattare da dattijon ya bata tabbacin shine baban Anam ɗin kuma ƙanin Mamansu da suke uba ɗaya. Duk da cikin taushin murya da sauƙaƙawa yake mata faɗan sai ta murguɗa baki, babu wanda ya lura da abinda tayi sai Abie. Maimakon yaji haushi amma sai yay Murmushi kawai. 

    Abbah da jin bata amsawa Abie ɗinba ya dubeta shima ransa a ɓace, baida faɗa amma in aka kuresa shima ɗan babu sauki ne. Aiko ya balbaleta da masifa yana zaginta akan shiru dataima Abie ɗin. Haƙuri Abie ya fara bashi amma yaƙi saurarensa, sai da yayi mai isarsa har Fadwa ta fara share hawaye sannan ya ƙyaleta dalilin dawowar Dr Jamal ɗakin.


      Cikin ƙanƙanin lokaci rashin lafiyar Shareff ɗin ta shiga kunnen kowa. Waɗan da basu riga sun wuce wajen kamu ba sai suka zarto asibitin dubasa. Babu wanda aka bari ya shiga wajensa dan ba'ason masa hayaniya. Sai Mommy data matsa ita da Gwaggo suka leƙasa. Har dare anata shigowa asibitin duba san, dan wandama sukaje gidan kamu daga can nan suka dinga zartowa. Hakan sai ya tabbatarma da jama'a mara lafiyan ɗan dangi ne. Har sha biyu bai farka ba, anata ma ƙara masa ruwa har lokacin, dole kowa ya tattara ya tafi aka bar Khaleel da Maheer a wajensa duk da Fadwa harda kukanta itace zata zauna da shi.  A can gida ma Anam tana kwance rijif da zazzaɓi duk da doctor yazo ya dubata bayan na ido. Haka dai aka kwana zukatan mutane da yawa babu daɗi. 


       Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure duk da rashin daɗin da ake ciki akan ciwon Shareff dan na Anam ba kowa ya sani ba. Da sassafe Fadwa ta wuce asibiti ita da Mommy data zillema mutane da ƙyar. Sun samu ya farka har Maheer ya taimaka masa zuwa bayi yayo alwala. Yana cikin yin sallar daya makara ne suka shigo. Sun ɗanji sanyi a ransu. Suna zaune harya idar, suka shiga jera masa sannu yana amsa musu da kai dan sam baya son yin magana. A dai-dai lokacin suma su Abba suka shigo harda Daddy, kamashi su Khaleel sukai ya koma saman gado, cikin magana ƙasa-ƙasa da bata fita da ƙyau ya gaida su. Cikin kulawa duk suke amsa masa da tambayar ƙarfin jikinsa. Ya amsa musu “Da sauƙi” akan laɓɓansa. Abba ya fara masa faɗa akan ya akai ya zauna da ciwo haka babu wanda ya sani? Sai kace wanda baida kowa?.

       Ɗan murmushin ƙarfin hali yayi na yaƙe, murya ƙasa-ƙasa yace, “Abba zazzaɓine kawai shiyyasa. Kuma naji sauƙi Alhamdulillahi”.

     Abie ya girgiza kansa yana mai dubansa da tausayawa. “Wannan yafi ƙarfin zazzaɓi kawai my son. Kaga kuwa yanda ka rame? Sannan a kwanakin nan gaba ɗaya babu mai ganinka, mu duk mun zata aikine ya maka yawa shiyyasa”.

          Ɗan murmushin yake ya kumayi sai dai baice komaiba anan ma. Idanunsa da sukai wani irin kaɗawa jazur ya lumshe da jingina a jikin filon da Khaleel ya saka masa. Ya buɗesu a hankali ya saci kallon Mommy da Fadwa dake zaune kowa ya zuba tagumi. A hankali ya furta “Mommy inajin yunwa”.

        Kai Mommy ta jinjina masa, tare da taɓa Fadwa datai zurfi a duniyar tunani. Numfashi ta kawo mai haɗe da ajiyar zuciya ta kalli Mommyn. “Kira su Bintu muji wai ba'a kammala abincin bane gashi yace yunwa yake ji”. Da to ta amsa. Tana shirin kiran waya sai ga sallamar Mom da Mamie. Su Abba ne kawai suka amsa da Khaleel. Suka shigo Maheer biye da su ɗauke da basket, sai Mubarak da carton na ruwa. Daga Mom har Mamie fuskokinsu sun kasa ɓoye damuwarsu akan yanayin Shareff ɗin, suka shiga masa sannu da jera masa addu'a su Daddy na amsawa da amin. Mommy da Fadwa dai sunyi kamarma basu san da zuwansu ba. Abba ne ya bada umarnin Maheer ya zuba masa abincin dasu Mom ɗin suka kawo tunda yace yunwa yakeji daman...

        Shigowar Doctor ta sakasu duk suka fito, Daddy ya dubi agogo, ganin lokaci yaja gashi yau juma'a ga ɗaurin aure yace su ai gara su wuce gida ma Khaleel da Fadwa sai su zauna a waje sa, dan dama acan gida sune suka hana kowa zuwa har Gwaggo. Cema mutane akai kawai an ma sallamesa dan haka kowa ya dakata da yunƙurin zuwa aka maida hankali ga shagalin biki. Fadwa da Khaleel aka bar masa, su kuma gaba ɗayansu suka wuce gida, sai dai Maheer bai so hakaba, soyay shima a barsa anan basai yaje ɗaurin auren ba. Amma babu yanda zaiyi su Abba suka korashi, ga Mommy sai zabga masa harara takeyi.....


       ★★ 


  Gidajen biyu duk sun gama cika da jama'a, bakajin komai sai hayaniya da al'ada irin ta biki. Maza duk sun wuce massallaci domin halartar sallar juma'a da ɗaurin aure. Yayinda amarya Anam ke ƙudundune har yanzu taci kuka harta godema ALLAH, zazzaɓi ne mai tsananin zafi tattare da ita. Haushin kowa takeji a gidan, har shi Muzzaffar ɗin da rabonta da shi a zahiri tun randa Shareff ya dawo, saita waya jefi-jefi yake kiranta daga gaisuwa kuma sai yace mata yana da uzuri. badan bata son sa ba take jin haushinsa, kauce-kaucen da yake mata ne yafi komai mata zafi, musamman a kwanakin matsowar bikin. Su Abie sun isa da itane shiyyasa take danne komai saboda farin cikinsu, ko sai bayan sun ɗaura mata aure suka gaya mata bazata taɓa jayayya da su ba saboda matuƙar girma da darajar da suke da shi a gareta. Amma shi mizaisa ya dinga mata kauce-kauce kamar dole akai masa ya aureta bashi yazo yace yana sonta ba?, ya kuma ɗauke ƙafa da zuwa inda take ma sai kace zasuyi auren ƙiyayya?. Hawaye ne suka cigaba da silalo mata a hankali dan bata da ƙarfin yin kuka, a wannan yanayin barci ya saceta saboda allurar barci da doctor ya mata.


         ★Tun bayan barin su Daddy asibitin yaƙi ya sake magana da kowa, Fadwa da Khaleel ma cayay su bashi waje yana buƙatar kaɗaici. Ran Fadwa ya ɓaci sosai har ta kasa shanyewa ta dubesa zatai magana Dr Jamal ya ɗan girgiza mata kai da mata alamar roƙo kar tace komai. Harara ta watsama Shareff tai fitowarta. Shiko Khaleel biyota yay fuskarsa ɗauke da murmushi, yayi tunanin ma asibitin zata bari gaba ɗaya, amma sai ya sameta a waje zaune tana danna waya alamar kira take ƙoƙarin yi. Baice mata komai ba ya kai zaune a kujerar dake kallonta, waya ya ɗauka shima, yana jinta tana faman jan tsaki da alama wanda take kiran bai ɗauka ba. Suna a wajen zaune Dr Jamal ya fito, Fadwa ya kalla dake cika tana batsewa. Yay murmushi da girgiza kansa. “Madam kiyi haƙuri kar kiji zafinsa da yawa, shi mai ciwo haƙuri ake da shi dan bakomai ake masa yaga an masa daidai ba. Zaki iya komaa yanzun ya samu barci, amma ba'a buƙatar motsi mai ƙarfi dan barcin nasa bazaiyi nauyi sosai ba”.

      “Amma Doctor dan mutum na ciwo sai ya dinga dizga mutane kuma. Shi baya ganin ƙoƙarin mu ne?”. “Bawai baya gani bane, yanayin da yake ciki ɗinne sai anyi haƙuri da shi Please. Ki ƙara haƙuri ki koma ciki mu zamuje massallaci ne”. Bata sake cewa komai ba ta tashi ta shiga, su kuma suka fice shi da Khaleel da yaƙi saka baki a maganar tasu dan ƴan miskilancin na kusa..........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_36_*.........Burin Mommy kawai ya kalleta amma yaƙiyin hakan. Tsahon minti guda baice komai ba yana satar kallon fuskokinsu ta gefen idanu. Tabbas ya hango tashin hankali kala-kala musamman a fuskar Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima da Fadwa, ya haɗiye busashen yawu da ƙyar tare da tattaro dukan ƙwarin gwiwarsa da jarumtarsa. Cikin dakewa ya ce, “Baba bani da ja akan hukuncinku”.

       “Kan ubanka Al-Mustapha!!”.

  Mommy ta faɗa cikin suɓutar baki, Murmushi Abba da Abie suka saki kusan a tare, hakama aunty Mimi da Mom da aunty Amarya sai da sukai kananun murmushi. Ɗayan yayanta da suke cema Yaya Kamil ya harareta, a kausashe yace, “Nafisa! Dama kina buƙatar ya bijirema iyayensa ne? A matsayinsu na mahaifa a garesa su zartar da hukunci ki nunama duniya k baki bama ɗanki tarbiyya ba saboda wani banzan tunaninki da hujjojinki? Karna sake jin bakinki a wajen nan, in ba hakaba ranki zaifi haka ɓaci billahillazi!!”.

        Dole tai shiru saboda a maganar Yaya Kamil ɗin babu wasa sam. Baba Ibrahim ya sake maida hankalinsa ga Shareff. “Ka bamu amsa ne a dunƙule Shareff, kana nufin ka amsa auren kenan?”.

       Sai da ya ɗan saci kallon Mommy ta gefen ido, tako zuba masa ido cikin matsanancin ɓacin rai, janye idanunsa yayi ya maida kan Daddy shima ya tsume kamar fuskar tasa zatai aman wuta. 

     “Shareff kai muke saurare, in har a ranka kanajin auren nan cutuwane a gareku ka saki yarinyar nan tun yanzu anan karka saka ku a wani halin da zai wargaza zuminci”. 

     A hankali ya girgiza kansa dake rissine a ƙasa. “Baba ku gafarceni bazan iya sakinta ba tunda an ɗaura....”

      Kukan da Anaam ta fashe da shi ya hana Gwaggo data ɗauki sallami tana tafa hannaye ƙarasawa, hakama Mommy da Gwaggo Halima da suka zaburo. Fadwa ma kuka ta saki mai ƙarfi yayin da Aunty Mimi da Mom da Abba suka saki wata nannauyar ajiyar zuciya, Abie ko murmushi ya saki, shi ko Daddy ya ɗan lumshe idanu. Mamie dai kanta a ƙasa yake babu mai iya gane yanayinta. Albarka su Baba Ibrahim suka shiga sanya masa da suma murmushin ya ziyarci fuskokin su, hakan ya ƙara tunzura kukan Anam da Fadwa....

      “Nidai bana Son sa baba, akwai wanda naima alƙawari zan aura nima, kuma shi nake so!!”. Furucin Anam cikin matsanancin kuka ya daki kunnuwan kowa dake a falon. Cikin sauri da zaburowa Mommy tace, “Shima ai ba son naki yake ba, shegiyar yarinya mai kama da ifiratan aljanu. Yaya ai kaga abinda nake gudun masa tun farko, mizaiyi da wannan mara tarbiyyar yarinyar har tana wani iƙirarin ba son sa take ba fitsararriya.....”

     Hayaniyace ta nema sake kaurewa a falon, yayinda Anam ke rusa uban kuka ita akwai wanda take so. Tsawar da Abie ya daka mata ce ta saka gaba ɗaya hayaniyar kukan Fadwa da Hargowar Mommy data Gwaggo yin tsitt. Anam ta maƙure jikin Aunty Mimi tana sake fashewa da kuka. Baba Ibrahim ne ya kalla Abie cikin murmushi, kansa ya girgiza masa cikin dattako. “Ayi haƙuri Usmanu abita a hankali sai a samu masalaha sahihiya. Tsanani baya kai kowa ga hanyar nasara. Juwairiyya zonan kinji”.

       Da taimakon aunty Mimi ta mike taje gabansa, kusa da ƙafafunsa ya nuna mata, ta zauna tana shashshekar kuka da sharɓar hawaye da gyalen data rufe har fuskarta. Cikin lallashi yace, “Kukan ya isa haka to, maza share hawayrnki”.  Da ƙyar ta iya danne kukan, sai dai hawayen basu bar zirara ba. 

        Cikin lallashi yace, “Faɗa min wa kike so?”.

    Kai tsaye tace, “Muzaffar!”.

 “Miyasa shi Shareffuddeen baƙya son shi?”.

       Shiru tai ta kasa magana, ya ƙara maimaita mata tambayar. 

  “Kawai Baba”.

“Ai shi mutum ba'a ƙinsa kawai Juwairiyya. Amma zan baki wata dama da kuma alfarma kin yarda?”.

          Cikin share hawaye ta jinjina masa kanta. Yay murmushi irin nasu na manya masu basira.

  “Ina so kimin alfarmar yarda a kaiki gidan Shareffuddeen. Daga nan zuwa wata uku in har baki samu wani farin cikin zama da shi ba, kizo ki sanar min, ni kuma na miki alƙawarin da kaina zan saka shi ya sallama miki”.

        Karon farko ta ɗago ta kallesa. Cike da tabbatarwa ya jinjina mata kansa yana murmushi. Ta kai dubanta ga Shareff, cikin sa'a kuwa suka haɗa ido. Wani shegen kallo da taima fassara dana tsana ta hango cikin idanun nasa, sai taji ƙwarin gwiwar cin nasarar shawarar baba ibrahim, dan kuwa ta tabbatar babu wani farin ciki da zata samu daga Shareff ɗin musamman idan ta auna irin tsanar da yay mata a rayuwa. Idan haka ne gara ta amince kodan goge laifinta da su Abie zasu iya gani, cikar wata uku kuma dai-dai da kammala Serves ɗinta kenan......

       “Baki ce komai ba”.

Baba ibrahim ya katse mata tunani.

   “Baba na amince”.

Murmushi ya saki mai ƙayatarwa, hakama abie da Abbah da Daddy duk sai da suka saki ajiyar zuciya. Yayinda Mommy tai ƙwafa sai dai babu damar cewa wani abu.. Baba Ibrahim ya sake ƙara musu nasiha baki ɗaya musamman Gwaggo dake a matsayin uwa garesu su duka a wajen. Hakama Mommy data hau dokin zuciya da yasan bazata taɓa tanƙwasuwa ta sauƙi ba. Itama dai Fadwa da Gwaggo Halima sun sami nasu rabon musamman ma Fadwa da yaketa lallashi dan yasan an mata laifi. Suma dai su Daddyn ya musu nasihar ya kuma ƙara bama kowa haƙuri da fatan komai ya wuce sannan yay addu'a taron ya tashi dan dare ya farayi.....


          ★★Washe gari an tashi ne mafi yawan rayuwuka a ɓace, ga amaryar Maheer ta iso tun daren jiya, tana a sashen Mom kamar yanda Daddy ya sharɗanta. Aunty Halima dai tun daren jiya tabar gidan tare da Fadwa, acewarta dai su Daddy basa ƙaunarta babu ita babu su, Fadwa ma tabar gidan Shareff kenan sai dai ya biyota da takardarta. Komai babu wanda yace mata a cikinsu, sai Gwaggo dake faman matsar ƙwalla tana faɗar maganganu. A haka dai babu daɗin rai akai walima washe gari dan dama ango Maheer shi bai yarda da wani event ko ɗaya ba, butsutsunsa yasa Mommy haƙura duk da taso a sha shagali tamkar bikin Shareff da Fadwa. 

       Shareff ma dai tun a daren ya koma can gidansa tare da Khaleel da Maheer ɗin da suka kwana da shi a can saboda yanayin jikinsa daba gama daidaita yay ba. Itama dai Anam bata kwana da lafiya ba dan tunda sassafe ma sai da Abie ya kaita asibiti da kansa aka bata gado. Dan haka har yamma tana can tare da Aunty Mimi da Abie ɗin, sai su Mom da su Daddy da sukaje daga baya dubata. Wannan ya kawo ƙaracin armashin buɗar kai da akai na amaryar Maheer, bayan sallar la'asar danginta da wasu a dangin Mom sukai mata rakkiya gidan mijinta. Gida yayi ƙyau dan Maheer ma yayi ƙoƙari sai sambarka. Sannan iyayen amarya ma sunyi nasu ƙoƙarin dan kun san dai Mom dama duk inda take na masu manda ne. (Tana bala'in son huɗɗa da masu kuɗi a gidan sanyi🤣).

         Tun a ranar mafi yawan baƙi suka kauce dan uwar bikin a birkice take. Tako'ina Mommy ɗin ta birkicema kowa. Gida yayi lafiya, baƙin da suka rage kalilanne, Hakan yasa koda aka sallamo su Anam daga asibiti sanda suka shigo gidan tsitt yake.


      Washe garin data kasance lahadi sai ga mahaifin Fadwa har gida ya maido Fadwa, babu ragi yay mata tatas a gaban su Daddy ita da Mommy. Fafir kuma yaƙi sauraren zantukan Gwaggo duk da uwa take a garesa. Wannan dattako daya nuna ya matuƙar faranta ran kowa a gidan ciki harda Shareff da aka sashi zuwa gidan. Daga ƙarshe kuma ya bisu da nasihar zaman haƙuri dana riƙe junansu domin samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Bayan wucewarsa su Daddy suka sake zama da Shareff, sun basa umarnin ƙarasa abinda ya rage masa dan nan da sati ɗaya amarya zata tare ɗakinta. Yaso yace suɗan ƙara masa amma baiga wannan damar a fuskokinsu ba dan umarni suka bashi ba shawara ba. Daddy kuma ya turkesa a wajen yace ya biyasa kuɗin sadaki dan shine ya ranta aka biya a waccan ranar. Dole yayma Daddy transfer ɗin kuɗinsa take a wajen sannan ya barsa ya tafi.

       Ƙin shiga wajen Mommy yayi dan wasan ɓuya yake da ita tun ranar, ya aika Aysha ta kira masa Fadwa tazo su wuce. Amma sai Mommy tace a faɗa masa Fadwan ta ƙarfi ce idan yanada ƙarfin yazo ya ƙwata. Murmushi kawai yayi sanda Aysha ta zo masa da amsa, batare da yace komaiba ya shiga motarsa ya fice a gidan dan gwara wannan wasan ɓera da magen da yake da Mommy ɗin akan tunkararta face to face a yanzun.


         ★ Kamar wasa ciwo ya kwantar da Anam sai da aka kwasheta aka koma da ita asibiti a daren yau. Dawowar su Amrah cikin gida yasa su Mom suka sani, dan daga Mamie har Abie da Aunty Mimi duk suna acan asibitin. Duk da dare ya farayi haka Abbah da Daddy suka fita, Khaleel ne ya jasu a motar bayan sun kira Abie sunji asibitin da suke.

        Lokacin da suka iso har an bama Anam ɗin gado amma saka mata ruwa barci ya ɗauketa. Ta rame sosai dayin wani irin fayau da ita, suna cikin jajantama juna Shareff ya shigo, Khaleel ne ya  tura masa sms ya sanar masa sanda zasu taho, dan haka ganin nasa ya bama kowa mamaki har Abie ya kasa haƙuri yay magana.

     “Babana waya saka fitowa a wannan daren haka? Ga anguwarku da nisa?”.

    Ƙaramin Murmushi yay idonsa na satar kalllo Anaam dake barci duk ta koɗe tayi fayau da ita abin tausayi..........✍_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_37_*


.........Kiran sallar farko ya farka, dama ba wani barcin kirki yayi ba, dan bai baro asibiti ba a daren jiya sai kusan ƙarfe ɗaya, shima sai da Abie ya korashi dan suma duk lokacin suka wuce aka bar aunty Mimi kawai da Anam dake barci. Sai da ya watsa ruwa kozai samu ƙarfi sannan yay alwala ya fita massallaci, gari ya ɗanyi shaa ya shigo gidan, ya ɗan ja tsaki dan gaba ɗaya gidan yay masa wani irin girma, yayi niyyar sakama Fadwa ido yaga iya gudun ruwanta amma a yau yaji bazai iya hakan ba, dan ya kula sai ya fito mata ta inda bata zato sannan zasu samu dai-daito. Wayarsa ya ɗauka yana zama bakin gado dayin ƙaramar ƙwafa, aunty Mimi ya kira, bugu biyu kuwa ta ɗauka suka gaisa, ya tambayi yamai jiki tace da sauƙi amma bata tashiba har yanzun dai. 

     “Masha ALLAH, nima zan shirya yanzu zan shigo, ko kuna buƙatar wani abu ne shiyyasa na kira?”. 

    Aunty Mimi ta amsa da “To ALLAH ya kawoka lafiya. Bama buƙatar komai tunda bata tashiba balle aji ko ita tana son wani abu ɗin”.

        “Okay to sai nazo”.

Ya faɗa yana yanke wayar. Bai wani jima ba ya kammala shiryawa ya fice, sai da ya shiga mota ya fara kiran number Fadwa, harta tsinke ba'a ɗagaba, ya sake tsuke fuska ransa na ƙara ƙuna dan ya tsani raini a rayuwarsa. Wayar ya jefa kujerar gefansa yay ma motar key ya fice. 


        Gama wayar aunty Mimi babu jimawa ta farka, da taimakonta taje toilet dake a cikin ɗakin, jikinta sam babu ƙarfi, hakan yasa Aunty Mimi taimaka mata ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi sosai sannan tai alwala suka fito. Murya a karye irin ta mara lafiya tace, “Ummie bazan iya salla a tsaye ba ina ganin jiri”. Taimaka mata aunty Mimi tai ta zauna kan sallaya, dai-dai nan masu gyara ɗakin suka shigo tare da wata nurse. Su dukansu suka gaida Aunty Mimi da tambayar mai jiki, ta amsa musu da fara'a. 

        Gyaran gado mai sharar ta fara, yayinda Nurse ɗin ke tsaye tana jiran Anam ta idar. Sai da tai addu'a Nurse ɗin ta taimaka mata ta koma saman gado, kwancia ta ƙarayi dan gaba ɗaya batajin ƙarfin jikinta. Harta lumshe ido sallamarsa ta sakata buɗewa, kallo ɗaya tai masa ta maida ta rufe abunta fuskarta na sake tsukewa. Gaisheshi Nurse ɗin tai hakama mai sharar, ya amsa sama-sama yana ƙarasawa gaban aunty Mimi ya ajiye ledojin hanunsa. Aunty Mimi dake dubansa da murmushi tace, “Babana mun hanaka barci ko?”.

      Murmushi ya ɗanyi da kaiwa zaune a ɗayan gadon dake ɗakin, ya rissina yana gaisheta kafin ya bata amsa da “Ko badan kuba dole na fito ai yau akwai office”.

        “Tofa ango guda da zuwa office”.

   Idanunsa ya sauke akan Anaam batare daya ce komai ba, cikin son basar da zancen yace, “Har yanzu bata tashi ba?”. Kallon Anaam aunty Mimi tayi, ganin tayi luff kamar bata jinsu tai ƴar dariya. “Yanzun nan tai salla ma, tana komawa saman gadon kana shigowa. Sallamar Doctor ta hanashi cewa komai, tare yake da nurse ɗin ɗazun, ya miƙa masa hannu suka gaisa yana tambayar yamai jiki. Da aunty Mimi ma suka gaisa sannan ya ƙarasa gaban gadon. 

       Cikin tsokana yace, “My patient barcine ko likimo?”. Duk da ta jisa bata motsa ba, sai dai taɗan buɗe idonta ta kallesa ta maida ta rufe. Murmushi yayi da sake faɗin, “Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya. Sister Rabi taimaka mata ta tashi”.

     Da taimakon Nurse daya kira sister Rabi ta tashi, sai langaɓewa take kamar zata saki kuka, cikin lallashi doctor yake mata ƴan tambayoyi akan yanayin jikinta tana bashi amsa, ko sau ɗaya taƙi yarda ta kalli sashen da Shareff yake. Bayan doctor ya kammala ya bada umarnin a bata abinci ko kaɗan taci zai aiko a sake saka mata ruwa da allurai uku, dan suna buƙatar ta samu barci sosai da alamu suka nuna kwana biyu bata samu. Koda ya fice shi da Nurse ɗin bata yarda ta kalli inda yaken ba, saima ƙoƙarin kwanciya da taso yi aunty Mimi ta dakatar da ita. Idanunta ta ɗago cikin marairaicewa ta kalli aunty Mimi, har ƙwalla sun taru dan ma gilashin idonta ya ɗan ɓoyesu duk da fari ne tas, karaf suka haɗa ido, ta sake yin kicin-kicin da ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. Shiko ya kafeta da nasa idanun sai dai shima tashi fuskar tsamm take babu wasa.

    “Ummie jiri”.   

Ta faɗa a hankali.

“Na sani mamana ki daure kici abinci kamar yanda doctor yace sai ki kwanta ɗin. Bata iya musu ba, dan haka tai shiru. Aunty Mimi ta bubbuɗe ledojin da Shareff ya shigo dasu, kayan tea ne a leda ɗaya, ɗayar kuma abincine dai-dai cin mara lafiya kuma abinda Anam ɗin take matuƙar so. Amma da yake daru takeji sai tace ita bata son shi, aunty Mimi sai lallashinta take amma ta kafe ita bata sonsa a kira Mamie ta kawo mata wani.

     Sarai yana jinsu amma bai tanka ba, sai danna wayarsa yake kai kace hankalinsa baya kansu sam. Ana cikin badaƙalar Khaleel ya iso. Cikin shirin office yake, ya gaida aunty Mimi da Shareff ɗin yana ajiye basket na abinci da Mom ta aikosa ya kawo. Kafin ya karasa gaban gadon yana kallon Anaam da ƴar sakin fuska dan shi murmushi ma kakan daɗe baka gani ba tare da shi. “A jiki yayi sauƙi granny tunda gaki zaune, jiya har mun fara ƴar ƙwalla da murnar cin gummba”.

    Murmushi ta saki tana kallon Khaleel ɗin kamar ba ita ke bori ba. “Kai Yaya Khaleel, kai ashe soma kake na mutu?”.

     Murmushi yayi shima a karon farko, “To Granny na sani ko lokaci yayi jikin tsufa”.

          Ta ɗan hararesa tana ɗauke kanta, dariya yayi nan ma. A ɗan shagwaɓe tace, “Yaya mika kawo min?”. 

   “Breakfast ne Mom tace a kawo miki kafin su ƙaraso”. 

   “Na gode”.

Ta faɗa tana maida dubanta ga Aunty Mimi da ke kallon Shareff daya miƙe fuskarsa kicin-kicin kamar zaiyi aman wuta. “Ummie zanci”. Da ga shi har Aunty mimi kallonta sukai, yay mata wani mugun kallo ya ɗauke kansa. Itama harara ta balla masa ta ɗauke nata idon. Sarai yaga harar dan haka ransa ya ƙara ɓaci, batare da yayima kowa sallama ba ya fice abinsa. 

     Daga aunty Mimi har Khaleel da kallo suka bisa.....


        ★Yini guda ƴan dubiya nata leƙowa jefi-jefi, sai dai babu Gwaggo babu Mummy, Aysha ma satar hanya tai ta biyo su Mom da zasu zo tazo ta duba Anam ɗin. Dan Mommy ta hana yaran ɗakinta duka. Shareff dai bai sake leƙowa ba sai kusan takwas na dare, da alama daya tashi aiki sai da yaje gida sannan ya dawo nan dan jallabiya ce a jikinsa. Yanzu ma Anaam yitai kamar bata san ALLAH yayi ruwansa ba, shima kuma daga gaisuwa da yay da Aunty Mimi da wata ƴar uwar Mamie data zo duba Anaam ɗin yaja bakinsa ya tsuƙe. Aumty Mimi suka fita zataima baƙuwar rakkiya aka barsu su biyu. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar babu masu rai, sai ƙarar iskar fanka kawai kakeji, taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa sai faman cin apple ɗinta take da aunty mimi ta yanka mata hankali kwance. Idanu ya ɗan tsura mata amma duk da haka ta ƙi ta nuna tasan da zamansa....

      “A tunaninki wannan rashin kunyar taki zaisa ki samu biyan buƙatar taki?”.

    Shiru babu alamar tama jisa tanata dai cin apple ɗinta, ransa ya ƙara ɓaci, cikin jin zafi da ɗacin da muryarsa ta kasa ɓoyewa yace, “Oh ga mahaukaci na magana ko? K! Ki shiga hankalinki wlhy, inba hakaba zakisha baƙar wahala a banza stupid kawai”.

        Babu ko ɗar a cikin idanunta ta ɗago ta zuba masa su duk da suna cikin gilashi, “Yaya Shareff ALLAH bazai baka damar bani wahalar ba kuwa, dan hanyar jirgi daban ta mota daban. Aure ne dai nace bana so kuma komi za'amun bazan so ba dan inada wanda nake s......”

    Ji kake “bumm!” akan bakinta, sam batama lura da sanda har ya taso ya iso gareta ba. Ya ture hanunta da take ƙoƙarin ɗaurawa saman lips ɗinta ya maye gurbinsa da nasa yatsun biyu, cike da baƙar mugunta ya shiga murzasu. Duk da dukan da take kaima hanun nasa bai janye ba sai da ya tabbatar ya murjesu san ransa sannan ya saki. “Karki fasa rashin kunya, nima bazan fasa ɗaukar mataki akanki ba”. Ya ƙare maganar gab da fuskarta har yana busa mata numfashinsa da iskar bakinsa dake ƙamshin mouth freshener na banana.

      Kuka ke son taho mata amma tanata ƙoƙarin dannesa dan taci alwashin bazata sake barin hawaye akan fuskartaba game da wannan auren, zata ƙwaci kanta da ƙarfinta kuma duk abinda za'ai mata sai dai ai mata bazata zauna zaman aure da shi ba. Shima baibi takanta ba dan harya fice ma abinsa rai ɓace. Taja wani shegen tsaki da ɗaga gilashinta ta share ƙwallar da suka taru a fatar idon dan ta danne sauran ta hanasu tasiri. Koda aunty Mimi ta dawo bata tambayeta ina Shareff ɗin ba, da alama dai sun haɗu a waje ne.

      Daga ita har shi haka suka kwana rai a ɓace. Washe gari ma shine ya fara zuwa asibitin, sai da yaje wajen doctor ya biya komai ya basu sallana sannan ya iso ɗakin. Da aunty Mimi kawai yau ma ya gaisa, ƴar darun tasa na kwance ta juyama ƙofa baya baima san idonta biyu ko barci take ba. Shine ya sanar ma aunty Mimi an sallamesu, tai godiya ga ALLAH sannan ta miƙe ta fara haɗa kayansu. Ya ɗauki kayan ya fita da su, ita kuma ta tada Anaam da dama idonta biyu ta taimaka mata ta shirya sannan suka fito bayan doctor ya shigo sunyi sallama. Tsaye suka samesa a jikin motarsa yana waya da alama a cikin su Daddy ne. Ƙin yarda tai ta kallesa duk da shi tana jin nasa idon a kanta. Aunty mimi zata sakata gaba ta tirje akan ita dai baya take so, kokuma subi napep. 

       Faɗa aunty Mimi ta fara mata dan ta kaita wuya kuma, shiko kamarma bai san sunai ba ya shige motar abinsa bayan ya gama wayar tasa. Dole dai ta shiga gaban bisa tursasawar aunty Mimi........✍🏻_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_35_*_ASSALAM ALAIKUM DEARIES ... BARKAN KU DA KOKARI .. KAMAR KODA YAUSHE. WANNAN KARON MA MUNA BARAR ROKON KU WAJEN TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS DAKE MANHAJAR YOUTUBE_


_YARO NE DAYA TASHI DA SON KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE KUMA KWADAYIN GADON ME SUNAN SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE. A KUMA YI VIEWING DA LIKING. A TEMAKA DA SHARING MA... JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO...💕_


Assalamualaikum dear sisters and brothers.


Welcome to ummu sudais YouTube channel🥰

A channel where the Holy Quran is been recited from different Angles.

Click on this link and listen to the Beautiful recitation that will melt your heart 

https://youtu.be/Lafgc749sK8


Your subscription to our channel is of Great important. Please help us grow our channel by subscribing and liking our videos fisabilillah.

Thank you so much


--------------------


..........Cak numfashin Fadwa ya ɗauke daga ƙirjinta, idanunta suka fara ganin duhu-duhu, tai baya luuu zata faɗi dan wani irin mugun hajijiyace ta lulluɓe ganinta da jinta saboda maganar tazo mata ne tamkar saukar nokiliya.... Laɓɓanta matuƙar rawa suke na alamar sonyin magana, amma bushewar yawun dake taimakawa maƙoshinta ya hanata damar hakan. Sai faman raba idanu take a tsakanin Mommy dake tsaye tamkar bajimar zakanya taga abin farautarta da Shareff da alamu suka nuna shima yayi ƙamewar wucin gadi ne saboda wani dalili na mamakin furicin Mommy ɗin ko wani abu daban da bata hasaso ba.....

     Shigowar Daddy ɗakin tamkar an jehosa ta maido Shareff a tashi sumar tsaywar jinin data riskesa tabbacin hasashen Fadwa, dan shima dai jinsa da ganinsa a take suka rabu da gangar jikinsa baki ɗaya, sai idanunsa ne kawai tsaye ƙyam akan Mommy na tabbacin bashi da maraba da sumamme. 

        “Bazan hanashi bin umarninki ba, sai dai nima a nawa umarnin, wlhy! Wlhy! Wlhy!! Idan har Al-Mustapha ka saki Mamana! Nima  zan saki uwarka dai dai da adadin sakin da ta sakaka ka rubuta!!.......” 

    “Dana haɗa jini da Usman da Ai'sha gara na barka har abadan abidina Muhammad!!”. Mommy ta tari numfashin Daddy a tsawace. 

       “Okay fine! Haka kikace ko?. Kai Al-Musta..........” Shigowar Abba da Dr Jamal ta hana Daddy ƙarasa faɗar abinda ke bakinsa, sai dai wani irin mugun kallo da yake bin Mommy da shi, har cikin ranta yake ratsata, sai dai zuciyarta tayi bushewar da take jin zata iya ɗaukar koma minene daga garesa akan wannan auren da rabashi shine kawai samun nutsuwar ruhi a gareta. Gwaggo ta riƙo hanunta tana faɗin, “Altine kina lafiya kuwa? Kai Muhammadu karka sake cewa komai kumuje gida”.

       Mommy ta fusge hanunta daga riƙon da Gwaggo taimata. “Wlhy Gwaggo babu inda zanje sai Al-Mustapha ya saki yarinyar nan, dan bana buƙatar auren nan ya sake minti guda a kansa!!”.

        Dr Jamal da gaba ɗaya ya rikice cikin roƙo yace, “Dan ALLAH Mommy kiyi haƙuri, bara na basa sallamar sai aje gida wannan maganar bata nan bace ba”. Kafin tace wani abu Gwaggo taja hanunta suka fice, ganin shima Daddy ya fita ya sata yarda ta bita. Abbah ya kama Shareff shi da Doctor Jamal. Wata Nurse kuma ta kama Fadwa da har yanzu babu alamar ta dawo hayyacinta.......


         Sun sami gida ya gama hargitsewa shima. Dan Gwaggo Halima da komai yaje kunnenta gaba ɗaya ta haukace, sai zagin Abie take da tone-tone, dan waje ta fito tana faɗar maganganu marasa daɗi, Abie ya miƙe ya shige cikin gidansa, amma sai ta bisa har can. Jin zagi da tonan asirin yayi yawa Aunty Mimi ta kasa haƙuri duk da kowa ya santa mutumce mara faɗa da son hayaniya. Amma zagin mahaifiyarsu da Gwaggo Halima keyi bazata iya jurewa ba ta fara tayata. Cikin ƙanƙanin lokaci hayaniya mai tsanani ta tashi dan dangin Mommy irinsu Samira tuni sun shigo gidan suna taya Gwaggo Halima.

     Ran Daddy ya ƙara ɓaci, yayinda hankalin Abbah dana Shareff sukai matuƙar tashi su kuma. Da ƙyar Gwaggo ta hana Mommy shiga gidan, yayinda Dr Jamal ya taimakawa Shareff zuwa ciki, wasu mata kuma suka kama Fadwa da zuwa yanzun ta fara kuka sai dai babu uhhm babu uhhm-uhhm. 

      Daddy kam daya faɗa gidan Abie lafiyayyun maruka guda biyu ya sauke akan fuskar Gwaggo Halima. Tamkar ƙiftawar idanu gidan yay tsittt, ya kuma sauke mata wasu biyun da suka saka zukatan mafi yawan mutane girgiza. Gwaggo Halima maiji da kanta, Gwaggo Halima babbar mace hamshaƙiya mai taƙama da tunƙaho da sunan mijinta da muƙaminsa koda a tsakkiyar cikin dangine, yau itace ake saukema waɗan nan marukan, dole ne gida yay tsit. Daddy ya ɗaga hannu zai sauke mata na huɗu Abie ya riƙe masa hannu. Cikin tsananin damuwa yake girgiza masa kai alamar roƙo. Ɗagowa Gwaggo Halima tai tare da ware hannu zata mari Abie taji an riƙe mata hannu tare da murɗesa. Abbah ne da wannan aikin, ransa a matuƙar ɓace tamkar bashi ba.....

    “Ko'a mafarki kikai tunanin wannan kuskuren sai mun tabbatar da nadama a rayuwarki Halima!!”. Kalaman Abbah dake amsa sunan ƙani a gareta sukai matuƙar ratsa kunnuwanta dama duk wanda ke a wajen.

      Sosai fa gida ya ƙara harmutsewa da ruɗewa. Har hayaniyar ta saka Anaam dake barcin wahala farkawa. Tun farko ma Mamie ce da hankalinta ya tashi ta rurrufe windows yanda bazai kawo kunnen Anam ɗin ba, sai dai ƙurar data sake tashi a yanzu tafi ƙarfin ta farko. Da ƙyar aka fidda Gwaggo Halima dake cigaba da ɗurama Abie da Mamie da Aunty Mimi harma da su Daddy zagi daga gidan. Sai dai can cikin gidan ma Mommy ce ke borin sai Shareff ya saki Anam. Shiko ya shige bedroom ɗin Daddy ya kulle kansa sai faman dukan ƙofa take da tabbatar masa zata tsine masa.

       Yana jinta, sai dai baya gane mi take faɗa saboda hajijiyar dake juyawa da kansa. Yana zaune bakin gado hanunsa dafe da kansa hawaye na zirara akan fuskarsa. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin makamancin irin wannan tashin hankaliba. Daddy da gaba ɗaya idanunsa sun rine da ɓacin rai ya fisgo Mommy dake faman jijjiga ƙofarsa tana jaddama Shareff ya buɗe kota tsine masa. Babu zato ko tsammani ya sakar mata nata lafiyayyun marin itama da iyakar ƙarfinsa. Dan tsabar azaba da firgita sai da ta faɗa kan kujerar dake daura da ita hannunta duk biyu dafe da wajen da ya maretan.

      “Muhammad ni ka mara?!!”.

“Idan kika ƙara cewa tak ma, zan iya miki dukan mutuwa ba mari kawai ba!!”.

Kalamansa sunyi matuƙar razana duk wanda ke'a falon. Sai dai shi a garesa babu ko gezau ya sake tabbatar mata ta hanyar faɗin “Idan kuma kinji ƙarya bismillah gwada na tabbatar miki!!”.

     Bakin kuwa tai shirin buɗewa zatai maganar dan zuciyarta ta rigada ta bushe Gwaggo tai saurin toshe mata shi, dan ita kam taga tsantsar wutar bala'in dake ci a cikin idanun Daddy irin wadda bata taɓa ganiba a rayuwarta. Duk yanda Mommy taso Gwaggo ta sakar mata baki taƙi, nanfa suka hau kokawa, sai dai ALLAH ya taƙaita abun a dalilin shigowar yayun Mommy maza da Abbah yay kiransu a waya harda wanda ta kira ɗazun taji komai a bakinsa da ƙanin mahaifin Fadwa.

      A tsakar gida dai ƴan biki masu gudun tashin hankali tuni sun fara zare jikinsu suna guduwa dama Magrib tayi, wanda kuwa zasu kwana anan da ƴan son ganin yaya za'a ƙare na zaune jugum-jugum, ƴan bani na iya kuma nata ƙus-ƙus. Fitowar su Daddy zasu wuce massallaci ya saka gidan ɗaukar tsit dan ko'ina akwai hasken wutar nefa, sai dai wasu basu daina magana ƙasa-ƙasa ba sosai musamman waɗanda ke'a ɗan nesa da su.....


      Bayan sallar isha'i duk wani mai faɗa aji a gidan ya hallara a sashen Daddy ne. Dan hatta Anam da bayan farkawarta kunnenta ya jiye mata wasu maganganun da harta ɗan fahimci abinda ke faruwa da akema jidalin tana wajen. Sai dai kuka take har muryarta bata fita, dan kunnenta ya jiye mata wasu manya-manyan zagi da Gwaggo Halima ta dinga jifan iyayenta da su. Gashi kuma Mamie na kuka ita da Aunty Mimi da babban yaron Aunty Mimi ɗin da Amrah. Tsabar kukan da take har amai tayi dan ji take kamarma ta mutu itakam ta huta, sai dai taci alwashin bazata taɓa zaman aure da Shareff ba itama.....

        Yayan Mommy da suke kira da Baba Ibrahim ne ya gama ƙarema kowa kallo, ganin babu Shareff a wajen ya tambaya. Anan ne Abbah ya mike ya nufi ƙofar bedroom ɗin Daddy. Zaune yake a kan sallaya hanunsa dafe da kansa dake matuƙar sara masa kamar zai faɗi, sallarma da ƙyar ya iya tashi yayita ganin lokaci zai shige dan har magtib ya haɗa. Jin muryar Abba ta sashi miƙewa da ƙyar ya nufi ƙofar ya buɗe, Abba dake kallonsa cike da tausayawa ya ɗan riƙo kafaɗarsa. 

       “Yaya dai Babana kanne ke ciwo?”.

   A hankali ya iya jinjin kan nasa da ɗago idanunsa da sukai jazur ya ɗan kalli Abban. Murmushin ƙarfin hali yay ya maida kansa ƙasa ya risinar. Sannu Abban yay masa cikin tausayawa da riƙosa suka fito, kusan kowa sai da ya zuba masa ido a falon, shi kam bai yarda ya kalla kowa ba ya zauna kusa da ƙafafun Abba. 

       Baba Ibrahim ya buɗe taro da addu'a, kafin ya fara magana cikin nasiha dajan hankalinsu akan muhimmancin zuminci a musulunci da zamantakewar rayuwa. Ya ɗora da faɗin, “Wannan aure a ganina abin alfaharine a gareku dan koba komai ya dunƙuleku ne waje ɗaya a matsayinku na jini guda. Fatan alkairi da ƙarfafa gwiwa kawai ya rage kuyi ga shi Shareffuddeen da nauyin ya rataya a kansa, amma ba wannan shirmen ba, gaba ɗaya yaran nan fa a ƙarƙashin ikonku suke, bazakuyi fatan bijirewar waninsu gareku ba in har kunada hangen nesa. Amma ke Nafisa minene naki na tada jijiyar wuya yaro ya saki matarsa??”.

       Mommy dake cike fam da nasihar Yayan nata ta saki kuka, “Wlhy ni dai Yaya bana buƙatar wannan haɗin, inhar nice na haifi Shareff to ina umartarsa ya saki yarinyar nan hakan zaifi mana zaman lafiya a gidan nan bana buƙatar wannan kwamacalar. Taya yana auren ƴar wajen Halima kuma ace ya auri wannan ai an haɗa husumane dan kishi ba wasa bane, babu wani zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya da hakan zai kawo sai ma wata sabuwar musibar. Kuma wannan ai munafunci ne, inba munafunci ba miyasa zasu ɗaura auren bada sanin kowa ba....”

      “ALLAH ya rabamu da ita. Ban san hujjarki na kawo wannan misalan ba, ba kuma na buƙatar sani, sai dai zan miki adalci ɗaya, shine jin ta bakin shi Shareff da ayanzu ikon zartarwa ke hanunsa akan matarsa, dan nasan su dai su Muhammadu da yardarsu da son su sukai wannan haɗin alkairi, kuma basu ɓoye dan munafuntarku ba sai dan kawo masalaha saboda sanin halinku. Dani kuma aka ɗaura auren tun waccan ranar kafin a ɗaura na ita ɗiyar halima da kike magana, domin kuwa da safe muka ɗaura na ita Juwairiyya iya mu kaɗai batare da sanin ko shi kansa Shareffuddeen ba, kafin a ɗaura na ita wannan yarinya Fadwa bayan sallar juma'a......”

  Baki ta buɗe zatai magana ya ɗaga mata hannu, dole tai shiru dan tana bala'in shakkarsa. Kallonsa ya maida ga Shareff da kansa ke ƙasa har yanzu bai ɗago ya kalli kowa ba, sai dai komai na shiga cikin kunensa kamar kowa, yayinda jawabin na Baba Ibrahim ke shigarsa tamkar almara, taya ya kasa gane an ɗaura masa aure da Anaam? Miyasa kuma aka zaɓi ɓoye masa shima?...... “Shareffuddeen!”. Ya kirayi sunansa cike da kulawa.

      Bai ɗago ba, sai dai ya amsa da “Na'am Baba”. Cikin dasashshiyar muryarsa dake tabbatar da baida lafiya. “Nasan kanajin komai basai na ƙara maimaici ba, iyayenka sun baka mata domin ƙoƙarin ƙara ƙarfafa zuminci a tsakaninsu da ku da suka haifa, shin kai ka amince da hakan a matsayinka na ɗa a garesu ko kuwa kanada ja tamkar mahaifiyarka?”.

      Tsitt falon yayi kowa ya zubama Shareff ido musamman Fadwa, Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima.........✍


_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_39_*.........Alhmdllhi amarya ta iso gidanta lafiya, ta kuma samu tarba daga wajen dangin mahaifiyar su Daddy da suma sukazo suka taru anan domin nuna gata gasu daddy ɗin, duk da tun zuwan nasu ƙawayen aunty Halima dake gidan zagaye da Fadwa suka kirata suka sanar mata. Babu ko kara na tuna cewa dangin mahaifiyarta ne ta kirasu tai musu tas a waya da tabbatar musu zata iya da makircin kowa daya nuna goyon bayansa akan aima ƴarta Fadwa kishiya, kishiyarma ɗiyar ƴar uba. Inna Suwaiba! Wadda ta kasance ɗiyar wan maman su daddyn ce ta amshi waya tai mata tas itama dan in masifa ce ta fita iyawa, ai ko babu shiri ta yanke wayar tana zage-zage.


        Kowa ya yaba sashen amarya tare da jinjinama ƙoƙarin iyayenta, dan tabbas kam sun nunama duniya ita ɗin ɗaya ce tilo a garesu kuma ƴar gata. Cikin raɗa Mom da Hajiyar sudan suka sake yima Anam da keta sauke ajiyar zuciya nasiha. Rungume Mom tayi, muryarta a ɗashe alamar taci kuka mai yawan gaske tace, “Mom ni bana son sa dan ALLAH, Mom karku barni anan zan iya mutuwa”. Mom dake rungume da ita tana shafa kanta tai murmushi. “To kiyi haƙuri, zan samu Abbanku nai masa bayani yanda zai fahimceni, yanzu dai ki kwantarmin da hankalinki kinji”.

     Da sauri ta fiddo fuskarta dake cikin mayafi tana kallon Mom da jajayen idanunta da suka kumbura matuƙa saboda kuka. “Mom dan ALLAH da gaske?”. Hajiyar Sudan Da Mom suka haɗa ido, murmushi sukayi, kafin Mom ta jinjina mata kanta “Da gaske mana. ba Baba ibrahim ma yace nanda wata uku indai da wata matsala zai ɗauki mataki ba”. Sake rungumeta tai tana jinjina kanta fuskarta na bayyanar da murmushin da tunda aka fara badaƙalar auren nan ba'aga irinsaba a fuskarta. Cikin dabara hajiyar Sudan ta fita a ɗakin, dan dama su kaɗaine suka rage mutane duk sun fice kowa na tsoron ya rasa mota. Lallashinta Mom ta ƙarayi, kafin itama ta miƙe cikin dabara da plan ɗin da suka haɗa da hajiyar sudan.

      Hajiyar Sudan ɗin ce ta leƙo tai kiranta wai tazo taga wani abu, miƙewa Mom ɗin tai tana gyarama Anam zama. “Kinga zauna ina zuwa”. Ji Anam tai kamar dabara zasu mata, sai dai kafin tai wani yunƙuri Mom ɗin har ta fice a ɗakin, tun tana irga seconds harta koma minutes, ganinfa alamar mintuna kusan goma sun cika babu alamar motsi ma ya sakata miƙewa da sauri hawaye na ciko mata ido. Tabbas babu kowa a falon, hakama sauran ɗakunan zuwa kitchen, wasu irin zafafan hawaye ne suka silalo mata, ta dafe kujera saboda jiri dake neman ɗibarta, da ƙyar ta iya maida kanta bedroom ɗin da suka barta, ta zube a kan gadon hawayen na cigaba da sauka a guje dan bata da ƙarfin yin kuka mai sauti.....

       

      Gida ya koma tsitt, duk da sashen Fadwa har yanzu akwai wasu ƴan uwan babanta uku na hanun damar Gwaggo halima da su Mommy basu da alamar barin gidan, sun zagaye Fadwa dake kuka suna ƙara mata fanfo dan ba'ace nasiha ba. A kallo ɗaya zaka tabbatar da taci kuka itama har ta godema ALLAH, dan hatta da muryarta ma ta dishe. Gaba ɗaya ji take Shareff ɗin ma ta gama tsanarsa, ko ganinsa bata sonyi shi da duk wanda ya shafesa. Tsoron mahaifintane kawai ya taka mata birki akan ƙudirinta na barin gidan, amma batajin zata iya cigaba da rayuwa da Shareff ƙarƙashin inuwa guda da maƙiyarta, yarinyar datai matuƙar tsana a rayuwarta ace a yau itace kishiyarta, kishiyarta da zata iya shearing da mijinta abin sonta. Kai ina wannan ma maganar tatsuniyace, za kuma ta tabbatarma duniya cewar tatsuniyar ce...


     Duk wannan hidima da akeyi ango Shareff na can gidansu gurfane gaban su Daddy suna sake masa nasiha da jaddada amanar matan nasa a hanunsa domin a yanzu matsayi guda suke amsawa a wajensa. Kuma su dukansu ƴan uwansa ne na jini da basa fatan zuminci ya samu wani nakasu ko rauni a dalilin aurensu. Basu barsa ya baro gidan ba sai da ƴan rakiyar amarya suka koma. Yay musu sallama ya fito. Babu sashen daya shiga, dan shima yasan baida wannan damar a yanzu. Ga kuma kansa na masa matuƙar ciwo ma na hayaniyar da aka sha ga kuma jikinsa da bawai ya gama dawowa dai-dai bane shima dama. Dauriyace kawai da ƙarfin zuciya irin ta maza.

      Duk yanda abokansa suka so masa rakkiya kamar auren Fadwa ƙi yay, dole suka haƙura suka gudu sai Fharhan ne kawai dazai jasa a mota dan shi bama zai iya driving ɗin ba. Da farko tsokanarsa ya dingayi, sai da yaga baya cikin good mood ne ya koma nasiha a garesa, dan kuwa dai shi ɗin shaidane akan abinda Shareff yake ɓoyewa a zuciyarsa tsahon shekaru, sai dai ko'a yanzun ma bai nuna masa yama fahimcesa ba yadai bashi shawarwari kawai. Har suka iso bai dai ce komai ba, sai da zai fita ne yace masa “Thanks” a taƙaice. Da kallo kawai Fharhan ya bisa, sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi.


        Kai tsaye sashensa ya wuce duk da yanada tabbacin zuwa yanzu babu kowa a gidan, ya zube cikin kujera yana furzar da huci mai zafi lokacin da yake kai bayansa ga kujerar. Ya lumshe idanunsa da yake jin sun masa matuƙar nauyi. Kusan mintuna goma ya ɗauka a wajen yana kokawa da abinda zuciyarsa ke saƙa masa, kafin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Wanka ne a ransa, dan haka bai zauna ba ya zame kayan jikinsa ya shige bathroom. Koda ya fito jikinsa kawai ya tsane ya zura jallabiya yasa turare kaɗan. Hakkinsa ne ya duba kowaccensu, duk da kuwa tunda Fadwa ta dawo gidan taƙi yarda su haɗu. Sashenta ya fara zuwa batare da tunanin zai samu kowa ba. Turus ya ɗanyi da mamaki, hatta fuskarsa sai da ta nuna dan bai zaton samun kowa ba. Fadwa da ke kwance ta ɗora kanta saman cinyar aunty Malika tai masa kallo ɗaya ta kauda kanta tana jan siririn tsaki ciki-ciki yanda bazaiji ba. Kallonta yake amma taƙi yarda su haɗa ido, ya ɗan girgiza kansa kawai. Komai baice ba ya fito a falon dan ko sallamarsa babu wanda ya amsa a cikinsu, sai kuma binsa suke da kallon banza....

       “Lallai wannan mijin naki ya cika ɗan iska Fadwa. Yanzu muna amtsayin ƴan uwan uwarsa amma yay mana wannan kallon banzar babu ko gaisuwa ya fice”.

   “Ke ko ya zai gaishemu kansa na hayaƙin asiri Safarah. Ai bayin kansa bane, dole fa su Aunty Nafi (Mommy) sai sun tashi tsaye dan Shareff ya shiga kaidun waɗannan mutanen wlhy”.

    Kuka Fadwa ta sake rushewa da shi tana kiran ta shiga uku. Cikin zafin rai wadda batace komaiba tun ɗazun ta daka mata tsawa. “A gidan ubanwa kika shiga ukun? Idan taƙamarsu asiri da tsubbu gaban iyayen gidansu sukazo. Har miye su? Mi akai akayi wannan ƴar yarinyar da bata wuce ki fetota a hancinki da makirci kawai ba. Danni banga abin ɓata lokaci agareta ba balle kuɗi na neman asiri. Wannan yaƙin da kanki zakiyisa in har kin cika ke ɗin jinin baba yalwa ce (Kakarsu data haifi mahaigiyar Mommy, Gwaggo, mahaifin Fadwa, mahaifiyar Bibah).

       “Aunty Lawusa dolene nai kuka, wlhy shima na tsanesa, bana son ganinsa munafiki ne”.

   Yanda take maganar tana kuka yasa Aunty Malika sake jawota jikinta ta rungumeta. Kuka ta sake fashewa da shi. “Aunty yanzu fa zuwa zai ya kwana da ita, shike nan sun rabani da mijina.....”

      “Basu isa rabaki da mijinki ba, ki kuma kwantar da hankalinki shi bai isa kusantarta ba, bama a yau ba har abada, yanda ta shigo haka zata bar miki gida sai dai ta koma ta cigaba da rabama abokan shashancin nata a ƙasar data fito”.

     Ɗagowa Fadwa tai tana girgiza kai, “Aunty baki san waye Shareff bane, wlhy sam baida haƙuri akan mace, ko faɗa yay da ita zai iya neman biyan buƙatarsa shi babu ruwansa”.

     Dariya aunty Lawusa tayi sai kuma ta haɗe fuska. “Malama ki mana shiru haka, idan shi hrj ne ƙarshen dai maitar mace kenan ko? To bai isa tarayya da yarinyar can ba har abada tunda ya taka abun can da ƙafafunsa”.

  Sosai Fadwa ta zaro idanu “Aunty wane abu wai?”. A tare suka sanya mata dariya, aunty Malika ta fiddo ƴar kwalba a jikkarta har guda 2. Ba kinga nayi turaren wannan ba ɗazun? Na kuma barbaɗe ƙofar falonki da wannan yanzun?”. Kanta ta jinjina mata. Ta dafa kafaɗarta tana murmushi, to wannan da kike gani sunansu *ɗan kaɗafi da ni kaɗai ce mace* mu dukanmu nan babu wacce bata aiki da shi a gidanta, kuma munga biyan buƙata shiyyasa kema muka amso miki, dan haka ki kwantar da hankalinki indai wannan yarinyar ce da ƙafafunta zata bar miki gidanki, ko zasu kwana manne da juna wani abu bazai taɓa shiga tsakaninsu ba”. 

      “Ni wlhy ko gadon ma bana ƙaunar su haɗa aunty, kai ko hanunta bana son ya taɓa riƙewa a gidan nan”.

    “Wannan duk mai sauƙi ne, kedai kawai ki saki bakin aljihu, dan yanzu babu boka babu malam maganin mata sune ke ƙwatar mace, shiyyasa mukayo miki haɗinsu gasu nan na musamman yanzu haka ma Hajarah zata taho miki da wasu daga Niger, Fadwa sai kin koma juya Al-Mustapha inda kike so, balle ke ma da kika gama morewa da samun mabuƙaci, ta wannan hanyar zaki banbance masa tsakanin aya da tsakkuwa ki kuma damƙe abunki dan dama naki ne shi kaɗai. Tun farko su Aunty (gwagg halima da Mommy) sunyi sakaci ai da basu haɗaki da haɗi na musamman ba kafin aure da Shareff bai taɓa kallon wata mace ba, kai auren nan ma da bai sai sun wahal da kansu ba da kansa zai bijire wlhy. Amma ko yanzu bata ɓaci ba muna tsaye kanki”.

   Fuskar Fadwa ta washe da murmushi, ta rungume auntys ɗin nata cike da farin ciki, jitai gaba ɗaya duk wata damuwarta tama gushe, dan tayi imani da duk abinda suka faɗa tunda ita ɗin shaidace akan yanda suke juya gidansu da mazajensu  duk da sunada kishiya, aunty Malika ma su uku ne amma idan kaga yanda mijinsu ke rawar kai a kanta saika ɗauka ita ɗaya garesa ko kuma amarya, sai dai itace ta tsakkiya........✍🏻

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_38_*............Duk da da sauran safiya hakan bai hana ta samu tarba daga mafi yawan jama'ar gidan ba. Musamman ma yaran dan suna shirin wucewa school ne suka iso. Duk sai da suka shiga sukai mata sannu da yaya jiki, bayan wucewarsu shima Shareff yay musu sallama ya fita dan wajen aiki zaije. Mamie da kanta ta taimaka mata tai wanka, bayan ta fito ta ƙara taimaka mata ta saka kaya sannan ta fiddota falo wajen su Daddy da suka shigo dubata. 

     Kanta a ƙasa ta gaishe su duk suka amsa mata da kulawa da tambayar jikinta. Abba ne yay ɗan gyaran murya idonsa a kanta. Ɗagiowa tai a hankali ta dubesu, ganin su duka ukun idonsu a kanta yake ta maida ta sake duƙarwa.

      “Mamana!”.

Abba ya kirata cike da kulawa.

Cikin rawar murya ta amsa masa. Yay ɗan murmushi da sake gyara zamansa. “Kin yarda muɗin iyayenki ne bazamu taɓa cutar da ke ba?”.

    Kanta ta jinjina masa tana haɗiye hawayenta. Ya cigaba da faɗin, “Alhmdllhi naji daɗi da kika fahimci haka, ina kuma fatan ki kasance mai biyayya tamkar yanda shima ɗan uwanki ya kasance amatsayinsa na namiji. Duk da nasan abinda mukayi munyisane akan gaɓar data dace akaran kanku bawai zumincinmu kawai ba. Ki ƙara daurewa ki zama mai haƙuri da biyayya, domin aure dai an riga an ɗaura, ba kuma yanzu aka ɗaurasaba ko jiya, an ɗaurashi rana ɗaya dana ƴar uwarki kamar yanda Yaya ya faɗa ranar a gaban kowa, sai da aka ɗaura naki da safe sannan aka ɗaura nata da azhur, hakan yasa ko shi Shareff bai sani ba, mun kuma ɓoye ne saboda wasu dalilai, hakama a yanzu mun bayyana a gareku da kowa ma saboda wasu dalilai. Dan haka zaki tare ranar juma'ar nan insha ALLAHU a ɗakin mijinki. ALLAH yay miku albarka, ya baku zaman lafiya da zuria masu albarka da MANZON ALLAH zai alfahari da su kamar yanda muke fatan yay alfahari da ku da mu baki ɗaya.”

     Kuka takeyi sosai. Sai tausayinta ya kamasu, kiranta Daddy yay ta rarrafa zuwa gabansa. Hanunsa ya ɗaura saman kanta ya shiga saka mata albarka da mata nasiha mai ratsa jiki tamkar yanda Abbah yay mata. Shi dai Abie bai ce komai ba yana dai kallonta ne kawai. Hakama Mamie da aunty Mimi. Sai da suka tabbatar ta tsagaita da kukan da takeyi sannan suka fice su duka, Aunty Mimi ce ta dawo kusa da ita, jikinta ta jawota ta rungume tana lallashinta, a haka su Mom suka shigo suka samesu ita da aunty Amarya. Suma dai nasihar sukai mata da lallashi. Daga ƙarshe Mom tace hajiyar sudan zata zo ta ƙarasa aikinta tunda wancan yabi iska. 

        Ɗakinta ta koma ta cigaba da kuka har barci ya kwasheta, bata kuma farka ba sai kusan azhar da hayaniya ta isheta. Wanka tai cikin rashin ƙarfin jiki sannan ta fito, ganin akwatuna barbaje a tsakkiyar falonsu ga mutane cike anata kallo ya sata komawa da sauri tana faman tura baki. Amrah ta kira cikin roƙo tace ta kawo mata tea, babu jimawa kuwa ta kawo mata tana tsokanarta da fara bata labarin kayan lefen da aka kawo mata. Duk da bata da ƙarfin jiki haka ta kora Amrah waje ta sakama ɗakinta key dan bata buƙatar jin komai. Saboda ma ta kauda abun a ranta sai ta ɗauki lap-top ta kunna film abinta, tana shan tea tanayi, data gama shan tea ɗin sai ta kwanta ta cigaba da kallon a haka tana jiyo hayaniyar gidan har lokacin sama-sama.


         A falo kam ƴan uwa da abokan arziƙi da makota kowa ya yaba da wannan lefe na girma. Babu fariyya a cikinsa kuma babu ƙaranta, ango Shareff ya taka rawar gani duk da ya haɗa lefen ne a ƙurarren lokaci dan Daddy ne ya bashi umarnin yinsa a cikin kwanaki huɗu kacal. Jiya da dare kuwa sai gashi da akwatina set biyu kamar yanda akayi na Fadwa. Sai dai waɗannan shi da Aunty Amarya suka haɗosu ba kamar na Fadwa ba da Mom ce ta haɗa Mommy ma ta haɗa set ɗaya.

      Bayan watsewar gidan Mamie ta samu zama da Anam. Nasiha tai mata mai ratsa jiki da ɓargo, wadda ta ƙara sanyaya ranta da sake sakata karaya. Ta fahimci kowa son wannan *_Auren ƙadda ko biyayyar?_* nasu yake a gidan, bata da wani mai goya mata baya akan ƙinsa sai Mommy da Gwaggo da Gwaggo Halima. Duk yanda Mamie taso daurewa itama kasawa tai saida tai hawaye, dama dauriya kawai take na rabuwa da tilon ƴarta. Sai dai idan ta keɓe tana kukanta ko kuma agaban Abie da shima dai dauriyar kawai yake sai dai yana lallashinta.


       Washe gari alhamis akaje aka tsantsarama Anam jeren daya girgiza zukatan su Mommy, dan kuwa akwai ƴan rahotonsu a wajen a cikin dangin mahaifiyar su Daddy da suke manne da Gwaggo Halima. Ranar ma dai ƙaramin hauka aunty Halima tazo sukayi da su Mommy a gidan, anan ne ma su Daddy suka san Fadwa na gida bata koma gidan mijinta ba kamar yanda mahaifinta ya sharɗanta. Rai ɓace Daddy ya nema ba'asi, dan shima birkice musu yayi fiye da yanda suke zato da tsammaninsa. Ai fa babu shiri Fadwa ta fadi cewar Mommy da Mahma (Gwaggo Halima) sukace bazata koma ba. Ran Daddy ya ƙara ɓaci, a take yanke yayma Mommy saki ɗaya. Tsitt gidan yayi na wucin gadi dan zuciyar kowa sai da ta girgiza musamman Mommy ɗin dake cika bakin idan ya saketa sai mi daga farko, dan ita a tunaninta fa Daddy cika baki kawai yake babu wani sakinta da zai iyayi. Zai ƙara na biyu Abie ya shiga roƙonsa da magiyar dan ALLAH kar yayi. Yana matukar jin nauyin Abie, dan haka yay shiru batare daya ƙarasa na biyun ba ya bar wajen yana huci. Itama dai Gwaggo jan Mommy tayi sashenta tana faman yimata faɗan katoɓarar tata.

     Ranar dai haka aka kwana gidan rai ɓace, yayinda Abba da kansa ya ɗauka Fadwa ya maida gidan Shareff. Duk abinda ke faruwa a gidan Maheer ya kira Shareff ya sanar masa dan yaje gidan gaishesu ya tadda ƙura ta tashi. Amma sai Shareff ɗin baije ba dan yasan zuwansa ɗin sabon masifane, kuma har yanzu tsoron haɗuwarsa yake da Mommy. Abbah bai baro gidan ba sai da ya haɗasu yay musu nasiha mai ratsa jiki, daga ƙarshe ya sa musu albarka da gargaɗin sake barin wata ɓaraka ta shigo musu da har zasu dinga kawota gabansu matsayinsu na iyaye, ya kamata su dinga juriyar sasanta kansu kamar sauran ma'aurata su riƙe sirrin gidansu. 

        

        Washe gari aka tashi da hidimar sabon shagalin biki, dan kuwa dai Abie ya shirya gagarumar walima dama tunda ALLAH bai cika masa burinsa na gayyatar tarin mutane ɗaura auren tilon ƴar tasa ba kasancewar an ɗaurashi a sirrance ne. Abin zai baka mamaki idan kaga yanda mutane ke ɓullowa tako ina, da wanda invitation ya sama a ranar ɗaurin auren Maheer da wanda ma ba'a gayyata ba. Dan danan fa gidajen suka cika taf.

      Mommy da Abie yay tsaye tun a daren jiyan Daddy ya maidata ɗakinta abin duniya ya gama isarta ita da gwaggo, sai dai Gwaggo ta hanata cewa komai sai danginta da suka iso gidan keta kananun magana akan ɓoye musu auren da akai tun farko, dan zuwa yanzu dai kowa ya shaida Anam itace Uwargida duk da ba addini ne ya wajabta hakan ba, amma ga al'ada irin ta bahaushe mukance wadda aka riga ɗaurama aure itace Uwargida musamman ma wannan da akai rana ɗaya. 

     Gwaggo Halima dai bata leƙo gidan ba ma, tana can itama tana zuba tata tijarar a gidan ta sai dai mijinta ya tabbatar mata ko sawun inuwarta ne ya fita gate a bakin aurenta kuma saki uku yake nufi, wannan shine ya hanata fitowa. Sai daita bada umarnin canja komai na Fadwa a gidan Shareff. Dan tun sassafe akaje aka kwashe kayanta tas na furnitures da labulale da wasu a kayan kicin aka zuba mata sabbi ƙal ƙirar waje wai duk dan dai kar Anam ta fita wani abu dan dukiyar da Abie da Mamie suka zubawa ɗiyarsu harma da Aunty Mimi sai yamaɗiɗi ake da shi a dangi. Wasu ma a waya suka gani sai kuma yau da aketa zuwa ganin amarya da masu zuwa gulma wai dannar ƙirjin Fadwa. (😂Basai an dannemu ba ma ku kwantar da hankalinku mu bama kishi😜).

        

       Amarya Anam data ci kukanta tun daga daren jiya har safiyar yau tayi ƙyau cikin kwalliyar haɗaɗɗen lesirin da Abie ya mata, aka kuma naɗeta cikin alƙyabba kai kace daga gidan sarauta aka ɗakkota. Kuka dai da hawaye na ƙarewa da na Anam amarya sun ƙare, musamman lokacin da walima ke gudana dan manyan malaman addini aka ɗakko suka rugurguza wa'azi akan zamantakewar aure a musulunci da al'adar malam bahaushe. Duk da tasan haƙƙoƙin miji kan matar tasa, dana mata akan mijinta hakan bai hana hankalinta sake tashi ba da sake jinsu a yau a bakunan malamai. Anci an sha kowa ya godema ALLAH. Yanda amarya tai ƙyau hakama ango Shareffuddeen yay matuƙar ƙyau cikin ɗanyar shadda daketa maiƙo ga wani ƙamshi na musamman da kwarjinin da ALLAH ke sama duk wasu ma'aurata a ranar aurensu. Anam dai bata san da zamansa ba sai lokacin da za'ai hoto, bata yarda kuma ta kallesa ba fuskarta na rufe da hular alƙyabba, sai dai kamshinsa ya cika mata hanci matuƙa. Koda aunty Amarya ta buɗe mata fuska ma ƙin kallon sashen da yake tai har aka gama zuba hotuna datai matuƙar gajiya taro ya tashi lafiya gab da magrib. Baƙi sun fara bajewa, yayinda akaima Amarya Anam sabon shirin miƙata gidan angonta. 

      Gaba ɗaya iyayenta zagayeta sukai harda Gwaggo a falo, sabuwar nasiha akai mata mai ratsa jiki, tuni kuka ma ya kama gabansa a idonta, dan zuciyar tata ta bushe ta kasa hawaye sam. Sai dai tana saurarensu daki-daki. Mommy dai babu wanda zaice yaga idonta yau a gidan, amma duk da haka an fita hakkinta an kai mata amarya Anam har sashenta domin yin bankwana da ita a matsayinta na uwa. Sai dai kuma suna shiga ta tashi tai shigewarta ta barsu da danginta da basu da alamar niyyar barin gidan.

       Yanda tai ɗin ya ƙona ran Hajiyar sudan, dan haka batako tsaya tofa wani abuba ta kamo hanun Anam suka fito. Sauran sassan aka zagaya da ita harna Gwaggo data bama kowa mamaki da al'ajab, dan kuwa takarƙarewa tai tanama amarya nasiha. Babu dai wanda yace komai amma ta ciki na ciki.

        Lokacin da akai gurfanar da Amarya Anam gaban Abie da Mamie a matsayin sallama dolene ka tausayama waɗan nan iyaye da tilon ƴarsu. Dan kuwa dai duk dauriya da Mamie keyi daga ita har Abie ɗin sai gasu suna kuka har bakunansu suka gagara furta komai sai addu'a a gajarce, dole dai aka haƙura aka ɓanɓareta jikin Abie da ƙyar aka fiddota ƙofar gida inda motocin abokan ango su Fharhan ke jiransu...........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_40_*
...........Ya jima tsaye a ƙofar sashen tamkar mai nazari, kafin ya ɗaura hanunsa akan handle ɗin ya murɗa a hankali. Ƙamshi dai da aka sani da sashen kowace amarya ne ya fara tarbarsa, ya shiga da sallama kan lips ɗinsa idonsa na zagayawa kan komai na falon. Ya turo numfashi mai ɗan ƙarfi ta hancinsa, cikin tafiya kamar mai irga steps ya nufi bedroom ɗin da yake saka ran samunta, dama 3bedrooms ne a sashen iri ɗaya dana Fadwa ne, sai kitchen, store, falo, bedrooms biyu suna facing juna a corridor guda, ɗaya na a can gefe kusa da dining alamar dai na baƙine. Nan ɗin ma dai sai da yay ɗan jimm sannan ya tura ƙofar, babu kowa, sai dai shima yasha kaya tsaff. Maidawa yay ya rufe, ɗayan ya buɗe.

    Kwance take ta dunƙule waje ɗaya, tare da lulluɓe duka jikinta da bargo. Hawaye take sosai ga rawar sanyi alamar zazzaɓine a jikinta. Ya ɗau tsahon minti uku yana kallonta duk da ba fuskarta ce a buɗe ba kafin ya cigaba da takawa cikin ɗakin sosai fuskarsa a tsume har yanzu da takaicin su aunty Lawusa, dan ma baiji abinda suke shiryama Fadwan ba kenan..

      Isowarsa gab da gadon ya bashi damar jin yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere har tanayi kamar zata shiɗe. Sai kuma rawar sanyin da takeyi har yana iya ganin kaɗawar jikinta duk da a lulluɓe take. Hannu ya kai ya yaye bargon baki ɗaya, hucin zafi sosai ya bugesa.....

    “Shiii!! wayyo sanyi-sanyi....” ta faɗa tana ƙoƙarin riƙo bargon da ya janye ɗin, bai bata damar yin hakan ba, ya kai hanunsa na dama saman goshinta. Sosai kan nata ma ya ɗauki zafi. Zumbur ta miƙe, dan sai yanzune ƙamshin turarensa ya kai ga hancinta, gaba ɗaya tama shafa'a da inda take. Tai saurin gyara glass ɗinta da ya sirranta kumbiri da jaan da idonta sukai tana ja da baya...

    “Kina tunanin hakan da kika zaɓama kanki shine maslaha? Duba yanda jikinki yay zafi, idanunki suka kumbura saboda kukan da bazai miki amfani ba bayan kin san hakan a gareki matsala ce babba. Garama ki nutsu domin kukanki da borinki bazai canja komai ba”.

         Wani irin kuka ne ya kufce mata na takaici da ƙara jin zafinsa. Yaja siririn tsaki da juyawa ya fice a ɗakin. Fillo ta ɗauka ta wurgama bayansa duk da ya riga ya fita sai ya samu ƙofa, ta ƙara ɗaukar wani ta jefa. Sai da ta jefa uku sannan ta zame ta kwanta tana cigaba da kukanta da ita kanta ta gaji da yinsa. Kusan mintuna bakwai ya dawo, akan fillos ɗin data wuwwulo ya fara sauke idanunsa, ya ɗan girgiza kansa kawai ya tsallakesu. Cup ɗin da ɗauke da tea ya ajiye tare da magani, batare da yace mata komai ba ya sake fita, bai jimaba ya dawo da goran ruwa. 

      “Tashi zaune” ya faɗa cikin bada umarni, dan yasan idan yay mata laku-laku bayin yanda yake so zatai ba. A yanzu ɗin ma duk da a yanda yay maganar sai da ya sake maimaita mata a ɗan tsawace sannan ta tashi. Da kansa ya gyara mata filo jikin fuskar gadon ya kuma taimaka mata ta jingina da ƙyau. Kusa da ita ya zauna yana mai kallonta tamkar mai nazari. Ita dai taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa. Numfashi ya ɗan furzar da ɗakko kofin shayin ya miƙa mata. Cikin ɗashewar muryarta tace, “Ni na ƙoshi”.  

      A karon farko ya saki guntun murmushi dan shi dariya ma take bashi, yana dannewa ne kawai. Ya ɗan rufe idonsa ya sake buɗewa a kanta. “Shi borin naki ya shafi har cikinki da lafiyarki kenan?”. Ya faɗa cikin sauƙaƙa muryarsa har yanzu da murmushi akan fuskarsa. Baki ta tura gaba da ƙoƙarin zamewa zata sake kwanciya ya riƙota. Son zame jikinta take amma ya hana hakan, sai ma jawota da yay gaba ɗaya ta dawo jikinsa. Tsuma jikinta ya farayi, murya na rawa tace, “Nidai ka sakeni bana so”.

      “An gaya miki nima ina so ne?”.

 Yay maganar a hankali cikin kunenta. Da sauri taso janye jikinta amma ya hana hakan, murmushin dake son sake kufce masa ya danne, ya ɗakko cup ɗin shayin ya sake miƙa mata, ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla tai ta kallesa, ganin ganda yay kicin-kicin da fuska ta maidasu ƙasa. “Bacci nake ji gashi kina ɓata min lokaci”. 

     So take ya fita ya barta dan haka ta amsa, ya ringa ya gama wucewa, dan haka ta kafa kofin a baki tai masa shan ruwa. Shi da kallonta kawai yake, ta miƙa masa kofin zata sake zamewa ta kwanta ya riƙota. Zatai magana ya harareta, baki ta murguɗa masa a kaikaice sai dai sarai ya ganta, baibi takanta ba ya ɓalla magani da ruwa ya bata. Tana gama sha bata yarda ta kallesa ba tai wuf ta kwanta tare da jan bargo ta rufe har saman kanta. Shima baice mata komai ba ya ɗauka wayarsa yana dubawa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya ɗauka kofin data sha tea ɗin ya fito bayan ya kashe mata wuta....

      A hankali ta sauke ajiyar zuciya dan likimo dama tayi ba barcin take ba. Ta ɗanji ƙarfin jikinta dama akwai yunwa tare da ita, sai dai duk da hakan jiri na ɗan ɗibarta kaɗan-kaɗan. Ƙofar ta tashi ta sakama key sannan ta cire kayan jikinta ta saka masu sauƙin nauyi, toilet ta shiga tayo alwalar kwanciya ta dawo ta haye gadon dajan bargon ta ƙudundune dan har yanzu sanyin bai gama sakinta ba. 


      Daga shi har ita makara sallar asuba sukai, haka ya sashi yin salla a gida, yana kuma idarwa ya koma ya kwanta kamar yanda itama a nata ɓangaren kwanciyar ta sakeyi. Barcine cike da idonta, da alama maganin daya bata yana saka barci.

    Ƙarfe kusan sha ɗaya ta farka. Alhmdllhi babu zazzaɓin hakama ciwon kan. Sai dai jikinta babu ƙarfi kamar yanda zuciyarta babu daɗi. Ɗakin ta gama ƙarema kallo da yaba ƙoƙarin iyayenta duk da batajin zatai tsahon zangon zama a wannan gidan. Ta wuce toilet tana sake tabbatarma kanta taƙaitaccen zama zatai. Da ruwa mai ɗumi sosai tai wanka, koda ta fito har ta gama shiryawa babu motsin kowa, taci alwashin bazata ƙuntata kanta ba, ba kuma zata sake yarda tayi kuka ba zatai yaƙin barin gidanne da ƙarfin zuciya dana ƙwanji, dan haka ta gyara gadonta sannan ta fito falo. Anan ɗin ma komai ya mata ƙyau dan an saka kalar da tafi so ne a rayuwarta. Tai ɗan murmushi tausayin iyayenta na ratsata, da sun sani basu wahal da kansu ba ma. Kitchen ta shiga shima ta ƙare masa kallo har store dake cike da kayan abinci na gara. Ta shiga ɗayan bedroom ɗin nan ma komai abin birgewa. Tunawa da wayarta data baro bedroom ya sata komawa, ta ɗakko ta fito ta tuna bata shiga ɗayan ɗakin dake facing nata ba. Kanta tsaye ta shiga kamar ko'ina, tai turus da ganin wanda batai zaton gani ba a ciki. Zaune yake a bakin gadon da alama yanzu ma ya tashi a barci, buɗe ƙofar ya sashi ɗago idanunsa. Ita ta fara janye nata cike da basarwa taja baya da nufin maida ƙofar ta rufe tana ɗan tsuke fuska da faɗin “Good morning”.

     Bai amsa mata ba, bai kuma janye idanun nasa a kanta ba harta maida ƙofar ta rufe. Cikin ɗan ƙunƙunini da murguɗa baki tabar wajen. Falo ta koma tai zamanta ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kunna wayarta. 

     Agogon dake ɗakin ya kalla, ganin har goma da rabi tayi ya sashi miƙewa ya fito a ɗakin, harya nufi hanyar falo sai ya tsaya cak, da baya ya dawo ya buɗe ɗakin data kwana ya shiga. Bai damu da rashin samunta a ciki ba ya shige toilet ɗinta, wanka yayi tare da ɗaukar cikin sabbin brush ɗinta ya buɗe ɗaya yay amfani da shi. Towel ɗinta ya ɗauro, ya riƙo wani a hannu yana goge jikinsa. Gaban mirror ɗinta ya ƙarasa yana bin kayan kwaliyyar dake kansa da kallo ɗaya bayan ɗaya, iska ya ɗan furzar daga bakinsa, sai kuma ya nufi ƙofa, kaɗan ya leƙa kansa duk da yasan bawai zai iya hangota bane....

     Har yanzu tana falon zaune abinta tana buga game hankali kwance, kai kace ba ita bace ta gama bori da rusar kuka ba jiya da sauran kwanakin da suka gabata. Jin kamar ana kiran sunanta ya sata ɗagowa takai dubanta ga hanyar corridor ɗin. Baki ta murguɗa jin ya ƙara kiranta cikin ɗan daga murya, cikin magana ƙasa-ƙasa da ba'ajin mi take faɗi ta miƙe. Harta nufi hanyar ɗakin data barsa ɗazun ta dakata sakamakon jin gyaran muryarsa a nata ɗakin, idanu ta zaro da riƙe ƙugu tana duban ƙofar, ta cije lip ɗinta na ƙasa cikin takun fusata da tsaurin ido ta nufi ɗakin tana wani ɗaure fuska ita a dole bazata masa ta sauƙi ba........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_42_*.........Tsitt gidan ya koma bayan wucewarsu, sai ta sake komawa sukuku da ita. Cikin dauriya ta ƙarasa saka turaren wutar dasu Amrah suka fiffido mata da fresheners masu ƙamshi ko'ina ya ɗauki ƙamshi dama sannan ta wuce bedroom yin wanka. Koda ta fito shiri tai cikin doguwar riga mara nauyi ta ɗan gyara fuskarta da sakama jikinta ƙamshi ta tada sallar magrib. Bayan ta idar ne wani tsoro ya dinga tsikarar zuciyarta, dan shirun gidan yayi yawa matuƙa, sauƙin ma akwai wutar nepa dan anguwar suna samun wuta sosai. Bata damu da rashin ganin Shareff balle tunanin ya dawo gidan ko bai dawo ba. Tana nan zaune saman sallayar taji tsoronta na ƙara girma, sai ta ɗauka wayarta ta fara karatun alkur'ani a ciki.....


      A daidai nan motar Shareff ta shigo gidan, a gajiye yake matuƙa saboda yau yayi yawo ne sosai cikin wani katafaren aikin babban estate da companyn su ke aikin ginawa. Yana China aka fara aikin, tunda ya dawo kuma ciwo ya kwantar da shi bai samu zuwa ya duba ba sai yau. Kai tsaye sashensa ya nufa, mamaki ya kamashi ganin ko'ina tsaf an gyara, ga wani ƙamshin turaren wuta na musamman na tashi ba irin wanda ya sani ba. Hatta da toilet ɗinsa tsaf yake sai ƙamshi ke tashi, ya ɗan saki huci wani kaso na gajiyarsa na raguwa dan shi mutumne mai tsaftar tsiya da kuma son tsafta. A gurguje ya zura jallabiya ya fesa turare ya fice massallacin anguwar tasu da ake ƙoƙari tada salla....


     Tun daga shigowarsa ta farko har fitarsa a idon Fadwa ne dake leƙe ta window, taji matuƙar farin cikin ganin sashensa ya nufa ba sashen Anam ba. A ranta tace, (anya wannan amaryar kuwa ta cika amarya?) sai kuma ta bushe da dariya ranta fes, musamman data tuna sanda take cin nata amarcin yanda ya dinga nanan da ita kamar ƙwai. Amma sai gashi yau harda fita aiki bai kuma tashi dawowa ba sai yanzu. Gaskiyarfa su aunty Malika hayaƙi ba nata baneba, dole ta kwantar da kai taga da mi shegiyar ta shigo, shima kuma ina ya dosa... Falonta ta sake kalla taga komai tsaf ga ƙamshi na musamman irin wanda ta saka a sashensa na tashi, hakama jikinta babu wata makusa wando da rigar sun matuƙar amsarta. Ta sake sakin murmushi da ɗaukar sweet ɗinta mai ƙamshi ta jefa baki ta koma cikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana daukar ɗan guntun bidiyo da zata poster a tiktok kodan maƙiya da suka tasota gaba da izgilin an mata kishiya a watanni biyar kacal.. Tana tsaka da editin ɗin bidiyon ya shigo falon da sallama. Da sauri ta fito daga tiktok ɗin tana ajiye wayar fuskarta da ɗan murmushi tace, “Sannu da dawowa”.

      Sosai mamaki ya ƙara neman kashesa, dan kuwa ya jima baiga Fadwa cikin irin wannan tsaf ɗin ba ita da sashenta. Cikin ɗan salo ta tashi tsaye tana faɗin, “Soulmate wai mi kake kallo ne haka kamar baƙo a sashen?”.

       A karan farko ya ɗan ware idanunsa a kanta da sakin guntun murmushi, kansa tsaye dan bai iya ɓoye-ɓoye ba yace, “Dama da gaske ne mata idan aka musu kishiya sunfi yin hankali da tattalin miji?”.

    Duk da maganar ta mata zafi sai ta dake, cikin murmushi ta matso kusa da shi ta rungumesa. “Haba Soulmate kamarya? Da bana tattalinka?”. Hannayensa duka biyu yasa ya ɗago fuskarta ya riƙe a tafin hanunsa, yayinda itama nata hannayen ke zagaye da shi sun manne da juna. Kallonta yake cikin ido, kaifinsu na sake narkar da ita a soyayyarsa da ƙaunarsa harma da kishinsa mai tsanani, dan tasan mijinta irin mazan da mafi yawan mata basa kalla su kauda ido ne saboda abubuwa da yawa daya tara musamman miskilanci dake saka mafi yawan mutane shakkarsa har ita a karan kanta... A hankali ya hure idanunta, tai saurin rimtsewa ta sake buɗewa cikin nasa da har yanzu suke a kanta. “Da gaske kin canja, haka nake so ki kasance mai yawan kula akan komai my love. Indai kika riƙe zaki mallaki Al-Mustapha a tafin hanunki cikin sauƙi”.

     Wani irin shauƙin daɗi ne ya ratsata, ta sake rungumesa da jin kamar su dawwama a haka. Lallai kwallin idonka idona ɗin nan yayi, cikin ƙanƙanin lokaci ga aikinsa kai babu abinda zatace da su aunty Safarah sai ALLAH ya biyasu. A hankali ya janyeta a jikinsa, da sumbatar goshinta. “Bara naje naga ƙanwarki itama, dan ina son na zauna daku yanzun nan”.

     Kanta ta gyaɗa masa tana murmushin yaƙe, bai sake cewa komaiba ya fice ransa na ƙara sanyi da canjawar tata......


     Bayan ta idar da sallar isha'i har shafa'i da wutirinta tayi, batajin wata yunwa dan haka ta yanke shawarar shan yogurt kawai da Mamie ta sakko a cikin drinks ɗin da aka kawo mata, fita tai da nufin ɗakkowa ta dawo bedroom ɗin, da tasha zatai kwanciyarta dan ita dama akwai saurin barci. Koda ta ɗakko yogurt ɗin sai ta haɗo da dubulan guda ɗaya dan tana matukar sonsa balle wannan da yasha riɗi da zuma mai ƙyau. Daga wutar falon har ta kitchen duk kashwa tai, sai dai kuma rashin sabo yasa ta manta da rufe ƙofar falon ta wuce bedroom, tamkar jira tana shiga ana ɗauke wuta, dai-dai nan shima ya ɗaura hanunsa a handle ɗin ƙofar falon nata ya shigo. Ƙarar data saki ce ta ratsa masa dodon kunne, karo sukaci a tsakkiyar corridor ɗin bedrooms ɗin nata, sai kawai ta zabura ta sake fasa wata ƙarar. 

       Da ɗan lalube ya samu ya riƙota a cikin duhun ya manneta da jikinsa da lalubo kunenta yana faɗin, “K! Calm down ni ne fa”. Yanda yay maganar cikin raɗa ya saka tsigar jikinta tashi baki ɗaya, ta sake ƙanƙamesa da sakar masa wani shagwaɓaɓɓen kuka....  Baice mata komai ba, sai dai yana shafa bayanta a hankali hawayen na sauka a ƙirjinsa duk da bata kai har can sama ba saboda rashin tsahonta, dan shi sai da ya ɗan ranƙwafo sosai ya samu rungumeta da ƙyau. Maido wuta da akai ne ya sakata haɗiye sauran kukan ta shiga sakin ajiyar zuciya, sai kuma kamar wadda aka cikara ta zabura ta janye jikinta... Bai hanata ba ya saketa, suna haɗa ido tai saurin juya masa baya tana tura baki gaba. Bayanta ya ɗan tsurama ido, sai kuma ya zagayeta ya wuce bedroom ɗin nata. Da mamaki ta wara idanunta da basu gani da ƙyau tana binsa da kallo dan batama san inda glass ɗin nata ya faɗa ba, “Wannfa ai shine ƙarfin rai mai sata da sallama” ta faɗa ƙasa-ƙasa tana harar ƙofar. (Ƙarfin hali ɓarawo da sallama bahaushiyar malaysia😹😜).

       Bin bayansa tai dan taga mi zaiyi mata a ɗakin. A bakin gado ta samesa zaune da wayarta a hanunsa. (Ƙarfin hali....) ta raya a ranta da nufar glass ɗinta dake yashe a ƙasa ta ɗauka ta saka. Dai-dainan ya ɗago ya dubeta ya kauda kai. “Babu abinci a gidan ne?”. 

     Bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka ta gagara cewa komai, sake ɗagowa yay ya dubeta yana ajiye wayar tata. “Baki jini bane?”.

        “Ni ban san zakaci ba shiyyasa naba maigadi, naga da safe da aka kawo baka ci  ba, na rana daya rage ne na bashi na kumace kar Mom ta aiko na dare”.

    “Kin bani na safen ne da kikaga ban ciba” ya faɗa cikin kafeta da ido, kallo ɗaya tai masa ta maida nata ta rissinar dan wani irin girma da kwarjini ya ƙara mata. Sai taji gaba ɗaya tsiwar tata bazata yuwu ba. Shima ɗauke nasa idanun yay a kanta batare da ya damu da rashin amsawar tata ba ya ƙara jeho mata wata tambayar. “K mi kika ci?”.

     Ƙasa-ƙasa tamkar mai tsoron a jita tace, “Zansha yogurt”.

      Maida kallonsa yay ga yogurt ɗin da dubulan data ajiye a bedside drawer, dama ruwa ta tuna bata ɗakkoba ta shirya komawa ɗakkowa aka ɗauke wuta. Jin baice komaiba ta saci kallonsa, “Kaima na kawo maka?”. Ta faɗa ganin har yanzu idonsa akan dubulan ɗin.

     Miƙewa yay batare da yace komai ba, sai da ya ɗanzo gab da ita sannan. Idanunsa a kanta kansa tsaye yace, “Ki kawo, ki kuma haɗo da ruwa”.

         Raka bayan nasa tai da hararar gefen ido, cikin kwaikwayon maganarsa da umarnin nasa ta maimaita abinda yace tana ciccijewa kamar dai yanda yayi. Sai kuma ta taɓe baki ta matsa wajen hijjabin sallarta ta ɗauka ta saka sannan ta fito duk tunaninta yana a falonta yana jira. Sai dai koda ta fito wayam, babu shi babu alamarsa. Cikin mamaki tace, “Wai miye nufinsa? Nakai masa can sashensa ko mi? Hu'umm”. Mi kuma ta tuna oho mata sai ta murgiɗa baki ta nufi kitchen ɗin nata.....


        Tun shugarsa sashen Anam tana laɓe tana leƙe ta wimdonta da kallon agogo, ganin ya wuce mintunan datai tsammani zuciyarta ta sosu, ƙwafa tayi cikin takaici da son danne abinda ke ranta tana cusama kanta huɗubar su Aunty Malika, koda ya fito jitai kamar taje ta kamasa da duka amma babu damar hakan, barin wajen window ɗin tai ta shiga bedroom, ƙara gyagygyara jikinta tai da ƙara turare ta ƙara kwallinta da jambaki sannan ta fito hanunta riƙe da wayarta ta yano siririn mayafi batare da tunanin basu kaɗai bane ita da shi.  Cikin yauƙi da yanga ta nufi sashen nasa tana murmushin data aro ta yafa ma kanta.....

     A dai-dai lokacin Anam da batasan akwai zama ba ta shiga falon nasa bayan tayi sallama da knocking ya bata izinin shiga. Zaune yake a saman 1sitter ya miƙe ƙafafunsa duka biyu saman centre table da lap-top akan cinyarsa yana aiki. Ɗan ɗagowa yay ya dubeta da amsa sallamarta ya maida kansa ya cigaba da aikinsa. Ta ɗanyi mamakin jin falon na kamshi yanzu kuma a gyare tsaf ba kamar ɗazun da safe data shigo ba, sai dai ba huruminta bane hakan sai kawai ta ajiye a saman centre table ɗin gefen ƙafarsa kaɗan. A niyyarta data ajiye ta juya ta fita, sai dai tana ajiyewar kafin ta ɗago Fadwa ta shigo da sallama...........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_43_*........Shine ya amsa sallamar tata, da ɗan ɗagowa yana kallonta. Ta ƙaraso zuciyarta na mata zogi irin wanda aka san kowacce mace da kishi ke saka mata. Amma sai ta dake ta sakarmasa murmushi kamar yanda shima yake mata. Ɗan sumbatar gefen fuskarsa tai da bashi side hug. Nanma murmushin ya ɗanyi da lumshe mata ido irin na godiya...

      Anam taji wani irin tsammm a jikinta, dan tunda aka kawota gidan sai yanzu ne suka haɗu da Fadwa, wani irin ƙululu yazo ya tokare maƙoshinta akan abinda Fadwa tai masa duk da bawai kallonsu take ba. Amma sai ta dake ta fasa ɗagowar datai niyyar yi, goran ruwan ta ɗauka ta ɓalle bakinta, ta tsiyaya rabin glass cup data haɗo da shi ta ɗago ta miƙa masa fuskarta a tsuke...

    “Gashi”.

  Idanunsa ya ɗago ya kalleta, tai saurin janye nata saboda haɗuwa da sukai cikin na juna, sai ta ɗan tura baki gaba jin ya haɗa hanunta da kofin duka ya riƙo, kafin ya zare kofin yana faɗin, “Thanks” a samman lips ɗinsa...

     Ta gefen ido Anam ta dubi Fadwa datai wani zaman ƙasaita tamkar bata ganta ba, lips ɗinta ta ɗan cija na kasa a ranta tana ayyana (Tabbas bana son mijinki bakuma zan zauna da shi ba. Amma kafin nabar gidan nan saina tabbatar miki zama birin wasana a tsakkiyar kasuwa kamar yanda nai alƙawari tunda naga haka kike buƙata) A zahiri kam sai ta saki lallausan murmushi, dai-dai ya gama shan ruwan ya miƙa mata kofin sai akan idonsa. Idanunsa ya ware da ƙyau yana mata kallon mamaki, amma saita kauda kamar bata gansa ba. “A saka yogurt ɗin?”. Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa.

     Kallon Fadwa ya ɗanyi, ganin idonta a kansu itama fuskarta kamar da ɓacin rai amma ta dannesa da murmushi ta ƙarfin tsiya ya sakashi dubar Anam da itama tata ke bayyanar da murmushi har yanzun. “Bari na kammala aikin nan zan sha”. Ya faɗa yana maida kansa ga lap-top ɗin...

      “Okay” ta faɗa a taƙaice da komawa kujerar gefansa ta zauna, har ƙafarta ta naɗe zuwa saman kujerar, hakan ya bama zaman nata damar facing ɗinsa, amma saita maida hankali wajen buga game a waya kamar yanda itama Fadwa dake zaune ta ɗayan gefensa ƙafa ɗaya kan ɗaya itama kujera daban, hankalinta ke kan waya tana duba Comments na mutanenta.

     Aikin yake sai dai lokaci-lokaci yakan ɗan kalla kowaccensu ta gefen ido, dariya suke bashi, dan kowacce ta tsume ita a dole hankalinta nakan wayane bata damu da ƴar uwarta ba, amma a zahiri babu ɗigon walwala akan fuskarsa. Kusan mintuna 17 ya kammala abinda yakeyi, system ɗin ya ajiye da furzar da numfashi yana ɗan lanƙwasa yatsun hannayensa daya haɗe waje ɗaya. Kallonsa Fadwa tai, ta saki ɗan murmushi da faɗin, “Waldon sir!”.

      “Thanks you dear”.

   Ya amsa mata yana sauke ƙafafunsa dake kan centre table ɗin suma ya zauna da ƙyau. Duk Anam najinsu, amma tai biris abinta. Yay ƴar gyaran murya da sake zama serious, hakan yasa itama Anam ɗagowa ta dubesa. Bai yarda ya kalla kowaccensu ba, cikin bada umarni ya fara karanto addu'ar da MANZON ALLAH ya horemu dayi a yayinda wani zama ya haɗamu makamancin hakan, kafin ya ɗora da faɗin, “Ina son ku bani dukkan hankalinku nan.”

    Babu wasa a cikin umarninsa, dan haka duk suka sake nutsuwa kowacce ta ajiye wayar hannunta, sai dai Anam bata canja daga yanda take zaune ba, dan taji daɗin zaman. Itama Fadwa dai tana yanda take ɗin sai muskutawa datai yanda zatafi sakewa da ƙyau.

     “Da farko zan fara da godema UBANGIJIN daya haɗamu a ƙarƙashin wannan inuwa, hikimarsace hakan kuma rubutaccene daga taskarsa tun kafin zuwanmu duniya. Gaba ɗayanku ina horanku da bani haɗin kai na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin gidan nan, ina kuma tuna muku tsoron ALLAH a cikin zaman da zamuyi. Ku dukanku matsayi ɗaya gareku a gareni, fatana ku cicciɗani da bani goyon bayan tsaida adalci a gareku. Ban yarda wata ta haɗa da shirka ko zalinci ba a wannan zaman, duk wadda tai hakan bazan yafe mata ba. Fadwa dake zan fara dan kece babba, duk da a shekaru na tabbatar zakuyi sa'anni koda tsiran zai-zama kaɗanne. Ki riƙe girman da ALLAH ya baki waje zaunar da adalci a gidan nan garemu baki ɗaya, kin fita sanin ilimin zaman gidan nan, kin fita sanin abubuwa akaina a yanzu zaki iya nusar da ita idan kikaga bata fahimta ba cikin sauƙi. Duk wata fitina da zata taso zan iya fara hukuntakine matsayin babba dan haka sai ki kiyaye”.

     Cikin danne komai dake a ranta ta jinjina masa kai da sakin murmushi. “Insha ALLAHU zaka sameni fiyema da yanda kake so a gidan nan Soulmate. ALLAH ya bamu zaman lafiya”.

     “Amin ya rabbi” ya faɗa yana maida dubansa ga Anam da duk take saurarensu. “Juwairiyya!”. Ɗago idanunta tai ta ɗan kallesa batare data amsa ba. Shima bai damu da amsawar tata ba ya cigaba da faɗin, “Ina fatan zaki bani haɗin kai wajen wanzar da zaman lafiya a gidan nan kema, sannan ki ɗauka Fadwa matsayin babba a gidan nan ku zauna lafiya, saɓanin hakan ba yana nufin zan hukuntata bane ita kaɗai, har dake zan haɗa domin matsayinku duk ɗayane a gurina. Abinda baki fahimtaba daya shafi gidan nan ko ni zaki iya zuwa gareta ta sanar miki”. 

      Kanta ta ɗan jinjina da faɗin, “Insh ALLAH”. A ƙasan maƙoshi. 

     “Bana son jin wani abu saɓanin abinda nake fata a gareku, dan yanzu ba da bane, a cikin gidana kuke ƙarƙashin ikona ku duka, zan iya ɗaukar kowanne irin mataki akan duk wadda ta shirya bani matsala ko raina ƴar uwarta. Mu dukammu jini ɗaya ne ku dinga tunawa da hakan a duk sanda shaiɗan ya bijiro muku da wani abu a zuciya ko wasu a cikin dangi. Dan na tabbatar a yanzu kowanne zai iya zama ashana da fetur ɗin cinnama gidana wuta adalilinku, kuma bazan amince ba, zan ɗauka mataki akan duk wacce ta bada wannan fuskar a cikinku da su wanda zasu iya kasancewa zagaye daku wajen haddasa min fitina” Bai jira amsarsu ba ya cigaba da faɗin, “Akan kwana, idan aka cire kwanaki bakwai miye tsarinku?”.

       Anan dai Fadwa ce kawai ta amsa, Anam kam dai shiru tayi. Fadwa tayi matuƙar danne raɗaɗin da takeji ta maye gurbinsa da murmushi, “Ni dai a nawa shawaran Soulmate kwana bibbiyun is ok ai ko?”. 

   “Okayyy!”

Ya faɗa cikin ɗan jan y ɗin da maida dubansa da Anam, taƙi cewa komai, taƙi kuma yarda ta kalla kowa. Sai dai tana jin idanunsa masu kaifi a kanta, kanta ta sake duƙarwa da tura baki gaba dan ita kam kunya ma maganar ke bata, fahimtar hakan da yayi ya sashi ɗauke idonsa da faɗin, “Hakan yayi kawai. Duk mai girki itace zata ciyar da kowa na gidan nan abincin dare, zakuma muci tare anan. Na cire safiya da rana ne saboda mafi yawan lokaci ina fita da wuri, na rana kuma bana gida kowa zata iya ra'ayin kanta amma zata bama maigadina tilas. Sai dai a weekend zakuyi har na safe kamar dai gobe”. Ya ƙare maganar yana kallon Fadwa..

       Sam hakan baima Anam daɗi ba itama, amma batai magana ba. Fadwa dai ta amsa masa da “ALLAH yasa haka shi yafi alkairi”. Ya amsa da amin batare daya damu da rashin cewar Anam ɗin ba dan yasan a komai yanzu baƙuwace dole suyi mata uziri na kunyar zaƙewa akan wasu abubuwan har zuwa sanda zata zama ƴar gida. Daga haka ya rufe taron da addu'a. Anam ta fara miƙewa da nufin tafiyarta dan barcine cike da idonta har goma saura...

      “Bani yogurt ɗin”.

  Ya faɗa cikin katseta da bada umarni yana ƙoƙarin canja chennal a tv. Bata da zaɓin daya wuce dakatawar duk da idonta har lumshewa sukeyi. Amma hakan bai hanata ɗan tura baki ba dajin kamar ta saki kuka. Miƙewa Fadwa tai tana faɗin, “To ni bari naje na kwanta, sai da safenku”. Ta ƙare maganar da matsowa ta ɗan sumbaci gefen fuskarsa kamar ɗazun sannan ta fice tanama Anam ɗin saida safe itama.

       Sosai hakan ya soki zuciyar Anam, harta kasa amsa mata, ɗagowa yay ya ɗan kalleta yaga fuskarta kicin-kicin. Glass cup ɗin data cika da yogurt ɗin ta miƙa masa. Tsaii ya ɗanyi yana kallonta batare daya amsa ba, sai hakan ya ƙara tunzurata, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi ta kallesa. Saurin janyewa tai tana ɗan yamutsa fuska. “Yaya dan ALLAH ka amsa zanje na kwanta barci nakeji”.

         Bai amsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta ba, saita sake dubansa a marairaice kamar zatai kuka. Ɗan murmushin daya tsaya iya laɓɓa ya saki batare data gani ba, amsa yay da sake maida hankalinsa ga television ɗin. Ƙara miƙewar tai yunƙurinyi.

     “Ki jira na gama ki tafi da kayan”.

Ya faɗa batare daya kalleta ba. Ai kamar ta ƙwala kuka taji, amma sai ta koma ta zauna batare da tace dashi komai ba, jin sosai barcin na rinjayar idonta ta naɗe har ƙafafunta a kujerar kamar ɗazun. Kallonsa ya cigaba dayi yana shan yogurt ɗin da cin dubulan ɗin kaɗan-kaɗan har aka kammala hirar da yake kallo a tashar ta NTA da wani babban ɗan siyasa na jihar ta kano. Ya juyo da tunanin itama kallon take sai ya samu harma tayi barci. Kafe fuskar tata yay da kallo na wasu sakkanni kamar mai nazari, sai kuma ya kai hannu ya zare gilashin nata a hankali. Tashi yay ya fita, bai jima sosai ba ya dawo da keys ɗin sashenta a hanunsa ya ajiye...

        Motsawa tai, taɗan buɗe ido kaɗan saita gansa dishi-dishi, da farko ta zata yanar barcin data fara ɗaukarta ce, sai ta rumtse idon ta sake buɗewa amma still taji raunin ganinta a bayyane. Cikin sauri ta kai hannu ta shafa fuskarta, jin babu glass ɗinta ya sata kai hannu ta fara laluben cinyarta zuwa kujerar, dan falon babu fitila mai haske ya kashe. Hanun ta janye da sauri saboda sauka da yay a gurbin da bashi tai hasashen kaiwa ba. Shiko tamkar bai jitaba yay biris. Cike da borin kunya ta sauka a kujerar tana ƙara duddubawa, saida ta tabbatar dai ba gani zatai ba sannan ta dubesa fuska a tsume, sai dai shakkarsa bai hana bayyana cikin tsumewar tata ba.

     “Yaya MM gilashi na fa?”.

“Kin bani ajiya ne?”.

“Toni inma ban bakaba dai ai a falonka ya ɓata”..........✍_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_41_*..........Gaba ɗaya tsiwar dake bakin nata ta maƙale akan harshenta, ta juya baya da sauri tana rumtse idanu ƙirjinta na bugawa da karfi. Duk abinda takeyi yana kallonta ta cikin mirror, cigaba yay da goge sumarsa kamar bai ganta ɗin ba, keys ɗin dake ajiye saman mirrorn ya ɗauka ya miƙa mata. “Je ɗakina ki samomin kaya....”

    Kafinma ya rufe baki tai gaba har tana neman yin tuntuɓe. “Da haƙwaranki zaki buɗe ƙofar?”. Ya faɗa cikin katse mata hanzari. Jitai kamar ta fasa ihu, amma sai ta daure idanu a rufe ta juyo tare da miƙa masa hannunta. Kansa ya ɗan girgiza ya ajiye keys ɗin ya cigaba da abinda yake yi. Kaɗan ta buɗe idanunta, tana tura baki gaba ta ɗauka batare data yarda ta kalli inda yake ba ta fice da hanzari. Haka kawai abin nata ya bashi dariya, amma sai ya haɗiye baiyi ba.

        Baki ta shiga taɓewa tana bin ko'ina na sashen da kallo. Babu dai tarkace babu kuma mugun datti, amma yana buƙatar gyara dan da alama shi yake aikin gyara da kansa tunda taji ance Fadwa na gida sai jiya aka dawo da ita. Bakinta dai bai furta komai ba ta buɗe wadrobe nashi. Anan kam komai a tsare yake, ga kuma ƙamshi kayan nayi. Taja wasu mintuna tana bin kayan da kallo daki-daki kafin dai ta zaɓi wanda suka kwanta mata a rai, cikin ɗan taɓe baki take faɗin, “Ko basu makaba dole ka saka, ko kunyar zama da towel a gabana baiji ba tirr” sai kuma ta taɓe baki, “Mutumin nan fa Sassaƙeƙen ƙato ne fa yasin” tai ƴar dariya da kai hannu ta buge bakinta. 

     Tafiyarta take hankali kwance batare data lura da su ba, daga aunty Malika har aunty Safarah, Fadwa aunty Suwaiba sun saki baki suna binta da kallo harta wucesu, baya Fadwa tai kamar wadda jiri ke neman kwasa ALLAH ya sota akwai bango bayanta “Aunty kenan wajenta ya kwana fa?”. Ta faɗa hawaye na rigegen sakkowa. Su duka kallonta sukai, a ɗan hasale aunty Malika ke faɗin, “To ke kam dai lallai takaicin kishiya zai karki idan baki nutsu ba, kuma in har kika bari ta gano lagonki wlhy kin mutu. Mi kwanan nasa wajenta ya amfana masa tunda gata nan tsaye kan ƙafafunta babu alamar tanada daraja na mace a wajensa. Ashema kina kokwanto akan maganin nan?”.

    “Aunty ki fa......”

Cikin katseta Aunty Safarah tace, “K washe garin da aka kawoki gidan nan a haka kika kasance?”. Wata wawiyar ajiyar zuciya Fadwa ta sauke mai ƙarfi saboda tuno wahalar data sha a hanunsa a daren da aka kawota, washe gari kam komai bata iya hasalama kanta ba sai da taimakonsa, dan ko tafiya sai da taita cin azaba kafin ta dai-daita bayan kwanaki biyu, ta share hawayenta tana murmushi, tabbas ta yarda mijinta bai taɓa yarinyar nan ba, dan babu macen da zataje hanun mijinta a karon farko a ganta a haka, shi ɗin namiji ne, idan tace namiji, tana nufin namijin gaske... (🤕dama akwai mazan ƙarya? Ƴar uwa kisa a ranki kema mijinki namijin gaske ne😚😉).


          Anam da batasan sunai ba koda ta isa sashen nata bayan tayi sallama a ƙofar ɗakin cogewa tai taƙi shiga, sai ƙofar data buɗe ɗan kaɗan ta zira hanunta da kayan a kai. Yana zaune a bakin gadonta yana waya ya hango hanunta, ɗauke kansa yay kamar bai gani ba ya cigaba da wayarsa. Jitai hanunta yana neman sandarewa, ta harari ƙofar tamkar tana ganinsa, cikin tunzura baki ta shiga ɗakin, da baya-baya ta dinga tafiya a hankali harta iso gaban mirror, ido suka haɗa da shi ta ciki daga inda yake zaune dan ya gama wayar, da sauri ta kauda kanta ta ajiye kayan a kujerar mirror ɗin tai gaba. “singlet da boxer kuma fa?”.

     “Yayaaaa!”

Ta faɗa da sauri dajan sunan cikin salon kai bakajin kunya tana juyowa. Suna haɗa ido tai saurin sake juya baya “Ni dai babu ruwana”. Jin motsin tashinsa tsaye ta fice da sauri. Sai da ta gama yima ƙofar harara kala-kala sai kace wata ƴar yarinya sannan ta wuce ɗakko masa. Shima daga can ƙaramin tsaki yaja da faɗin, “Girma ba wayo”.

     Yanzu kam bata kai ɗazu daɗewa ba ta dawo, cikin dakiya da ɗaure fuska ta shigo ɗakin kanta tsaye, har gabansa taje ta ajiye ta juya ta fita batare data yarda ta kallesa ba. Da kallo kawai ya bita a ransa yana raya (anya yarinyar nan bata da aljanu ma kuwa?) rashin mai basa amsa ya sashi sake jan wani tsakin ya ɗauka kayan ya saka. Tana zaune a falon ta wani tsume kamar sarauniya a kujerar mulki ya fito, da farko tayi kamar bata gansa ba, sai da ya ƙara matsowa sosai taji ƙamshin turarenta a jikinsa. “Yaya satar turare ka koma kuma?”. Ta faɗa tana tsatstsaresa da idanu. Shi rasama mizaice mata yayi, zata ƙara magana akai knocking. Ɗauke idonsa yay daga kallonta ya nufi ƙofar ya buɗe. Cikin girmamawa Mubarak ya risina ya gaidashi. Kai ya jinjina masa yana amsawa. 

     “Yaya dama breakfast ne akace a kawo”.

    “Okay ya mutanen gidan?”.

“Kowa lafiya yake”.

Komai bai sake cewa ba ya matsama Mubarak ɗin ya shiga, shi kuma ya nufi sashen Fadwa. Taso sharesa amma kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewar sa namijin tsayayye da bazai ɗauka raini ba ya sata nutsuwa, idanunta a ƙasa tace masa ina kwana. Falon yake ɗan bi da kallo batare daya amsa mata ba, sake gaisheshin tayi a ɗarare, sai dai bai amsa ba yanzun ma, saima tambaya daya jeho mata...

     “Masu zugakin sun tafi kenan?”.

Saurin ɗagowa tai ta kallesa, ganin ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifi ga fuskarsa a tsume matuƙa ya sata saurin maida idanun nata ƙasa sai dai ta kasa cewa komai. Ya furzar da numfashi mai zafi da zurfi. “Daga yau na haramta musu zuwamin gida, idan kuma sukai kuskuren sake zuwa ɗin zan ɗauka kowane irin mataki a kansu. Kema bazance karki ɗauka huɗubarsu ba, amma ki sani idan naci karo da wani hali a gareki saɓanin wanda na sanki da shi kamar jiya zakisha mamaki na”. 

      “Humm” kawai tace a ƙasan maƙoshi, dan ta ɗauka zantukan nasa da suna borin kunya irin mazan da sukaci amanar matansu wajen ƙara aure. Sai dai kamar yanda su aunty Malika sukai mata huɗuba bazatace da shi komai ba, zatabi komai a sannu harta cimma nasara akansa daga shi har amaryar tasa. Humm ɗin tata ta matuƙar zafarsa da ɗaukarta raini, sai dai a yanzu baya buƙatar wani tashin hankali dan haka baice komaiba yay ficewarsa. Sashensa ya nufa, ya ɗauka key ɗin mota da lap-top bag ɗinsa ya sake komawa sashen Anaam, har yanzu Mubarak na nan bai wuce ba, yana tsaye daga bakin ƙofa yace, “Ni na wuce office”.

     Ɗagowa tai ta ɗan dubesa, ganin fuskarsa babu alamar wasa ya sata shanye abinda ke bakinta, a taƙaice tace, “ALLAH ya bada sa'a”. A kan laɓɓa ya amsa mata ya juya ya fita. Miƙewa Mubarak yay shima, “Aunty Anam bara naje nima akwai aiken aunty a wajena kar taita jira”. Fuska ta ɓata cikin damuwa, sai dai batace masa komai ba ta gyaɗa kanta kawai. Tanaji tana gani ya fita ya barta ita ɗaya. Sai taji gaba ɗaya sashen ya mata girma da faɗi na rashin sabo, haka kawai kukan da taketa fatan kartayi ya kufce mata, sai da tayi mai isarta sannan tai zaman cin abincin da Mubarak ya kawo, tana kammalawa barci ya kwasheta a falon batare data shirya hakan ban.

        Cikin barci sautin mahaukacin kiɗa dake tashi a gidan ya karaɗe mata kunne, ta tashi a ɗan zabure tana dafe kanta daya sara mata, a dai-dai nan su Amrah suka shigo falon. Su duka kanta sukai suka rungumeta, cikin dauriya da jin daɗin ganinsu ta janye hanunta tana kallonsu fuskarta da murmushi. Aysha tace, “Uhhm su Blood matar Yaya Shareff, wlhy har kin canja dare ɗaya”.

      Kai kawai Anam ta girgiza tana hararta, Amrah ta kwashe da dariya ita da Husnah. Cikin salon ƙara tsokana Aysha tace, “ALLAH karkiji wasa blood, sai sheƙi kikeyi kamar hasken farin wata, ba kamar matar Yaya Maheer ba da muka tarar wujiga-wujiga da ita tana faman kuka”.

       Kafin Anam da zancen ya tsikara tace wani abu Husnah ta karɓe da faɗin, “ALLAH nima taban tausayi, kamar ma wadda bata cikin hayyacinta, daga ganinta zamuyi sa'anni da ita amma kamar bata da wayo sosai wlhy, ko ƴar 18years bazatai wannan sakaka ɗin nata ba ai balle ita”.

         Amrah da batace komaiba ta ɗan girgiza kanta, “Ni kam sai naga ba laifinta bane wlhy, kamar matsalar daga Yaya Maheer ne, kugafa yanda yaketa mazurai kamar ba shi ba. Anya kuwa auren soyayya sukayi sisters?”.

      Tsitt sukai lokaci guda kowa na nazarin maganar Amrahn, Anam ta fara furzar da numfashi tana faɗin, “Inaga kubar zancen nan haka dan ALLAH kamar zaifi. Wai shi wannan kiɗan daga ina yake fitowa?”. Aysha ce ta taɓe baki da jan tsoki, “Daga ina kuwa inba sashen aunty Fadwa ba, shaggun ƙawayen nan natane su Sima fa kamar a gidan. Halan Yaya baya nan ne ko?”.

      Kai kawai Anam ɗin ta jinjina batare da tace komai ba, ta kuma daƙile maganar duk da ta fahimci tana cin bakunansu. Basket ɗin da suka kawo ta jawo gabanta tana buɗe kulolin ciki, da haka ta ɗauke hankalinsu da zancen abincin babu wanda ya ƙara sakko maganar kidɗan dana gidan Maheer.


     Zuwansu ya matuƙar ɗauke mata hankali, da taimakonsu ta gyara ko'ina duk da babu wani datti, zuwa la'asar wasu daga cikin ƴan uwa danginsu Abie ɓangaren mahaifiya sukazo. kayan gara na fulawane da ƴan abubuwan daba'a rasaba suka kawo mata saboda baƙi da zasu ɗan ringa shigowa ganin ɗakin amarya, harda drinks mai ɗan yawa da ruwan roba. Sai lokacin sukaji sautin kiɗan dake tashi a sashen Fadwa ya tsaya, babu wanda yay magana suka cigaba da harkokin gabansu.......✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_44_*...........Banza yay mata kamar baiji ba, sai ma ƙoƙarin mikewa yake bayan ya latse remote tv ya mutu. Ganin zai bar wajen tai saurin riƙo hanunsa dan in har ta bari ya wuce bazata iya kai kanta ko nan da ƙofar fita ba saboda da gaske bata gani da ƙyau a cikin duhu sai da taimakon glass ɗin.

    “Yaya Please ka bani”.

Hanun nata ya kalla tare da ƙoƙarin juyowa, da sauri ta janye nata a yanayin jin kunyar aikatawa. Kafeta yay da idanu yana ƙarema fuskarta kallo kai tsaye, yayinda ita kuma ta kasa ɗagowa ta kallesan. A cikin ransa  yake faɗin, (Fitsararriya ashe kinada kunya?). A zahiri kam babu alamar wasa tare da shi yace, “Muje ki kwanta”.

      “Ina ɗin?”.

Ta faɗa cikin waro makantattun idanunta da mai kallo a haka bazai taɓa tunanin rauninsu ba saboda girma da hasken dake cikinsu tamkar wadda ke iya hango abinda ke faruwa a kilomita huɗu na gabanta. Gab da ita ya matso har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskarta. Cikin magana tamkar mai raɗa “A inda kike?”.

       Baya taso jan jikinta bugun ƙirjinta na daɗuwa amma sai ya hana hakan ta hanyar tokare hanun kujerar da take jiki da hanunsa. Duk sai ta daburce. Ture hanunsa tai da ƙarfi, tai gaba da nufin guduwa ƙafarsa ta nema taɗeta tai gaba zata faɗi ya riƙota, ɗan fisgota yay ta faɗo jikinsa, baima jira tako maida numfashi ba ya ɗauketa cakk ɗinta yay hanyar bedroom ɗinsa dan ya gaji shima kwanciya yake buƙata. Inko ya biye mata sai dai su raba hali. Watsal-watsal take da son ƙwace jikinta tana faɗin, “Ni wlhy ka saukeni bana so, bana son haka Yaya MM, ALLAH zan cijekaaa!!”. Ta ƙare faɗa da ɗan ƙarfin sautin daya sakashi direta a saman gadonsa da sauri. 

      “Kina da hankali kuwa? Fasan kunne zakiyi?”.

   Mikewa tai cikin sauri da nufin barin masa ɗakin dan ita kam dai bazata taɓa yarda ta kwana a ɗakinsa ba, gidan nasa ma domin yin biyayya da iyayenta ne da son cimma burinta cikin sauƙi zaisa ta zauna har zuwa lokacin data ƙayyadewa shirinta. Bai hanata ba dan tuni ya zare keys ɗin ɗakin, sai ma toilet daya nufa cikin halin ko'in kula. Jin ƙofar a kulle ya sata juyowa da sauri duk da ba fes take iya ganin komai ba amma kasancewar da fitila tana gani fiye da acikin duhu. Sosai hankalinta fa ya tashi, dan abu ɗaya zuciyarta ta iya bijiro mata zaisa yay mata hakan, a gareta kuma shine abu na ƙarshe da bazata iya mallaka masa ba koda a yau zaice zai mata dukan da shine kawai abinda take shakka da tsoro tattare da shi. Haɗiye duk wani fargabanta tai tai tsayuwar sojan badakkare a jikin ƙofar tana dakon fitowarsa. Tsahon mintuna 6 sannan ya fito duk tana lissafa ta hanyar kallon agogon dake bangon ɗakin. Yi yay tamkar bai ganta ba ya hau zame jallabiyar jikinsa. Bayyanarsa a zahirinsa da ga shi sai boxer ya sata juya masa baya da sauri tana ambaton sunan ALLAH. Kayan barci ya ɗakko a wadrobe ya saka harda fesa turare kamarma bai ganta ba. Ya haye gadonsa yana faɗin, “Baƙya buƙatar kwanciyar ne?”.

      Maimakon amsa sai ta fashe masa da kukan ƙarya. “Yaya dan ALLAH ka bani key da glass ɗina na wuce barci nake ji, ALLAH haka babu ƙyau, kuma kaina zai iya yin ciwo”.

    “Idan kin so hakan kenan”.

Ya amsata yana jan bargo cikin halin ko'in kula. Kukan ƙaryar tata ta dakatar zuciyarta na mata zafi, sai dai hango keys ɗin a bedside drawer ɗin inda yake ya saka mata jin sauƙi, cigaba tai da tsaiwa a wajen har kusan minti ɗaya kafin ta nufi wajen cikin sanɗa da tunanin yayi shammatarsa ta warto. Tana gab da isa ya fiddo hanunsa dake cikin duvet ya ɗauke, rigarsa ya ɗaga ya ɗaura saman cikinsa ya maida bargon ya rufe. Ganin ta dakata daga yunƙurin tahowar ya ɗan buɗe ido yana kallonta a sigar da ita bata fahimci haka ba musamman saboda matsalar nata ido. 

     “Gashi anan ki ɗauka” 

  Kanta ta ɗauke idonta na ciko da ƙwalla na gaske a yanzun. Dan tsaf ta fahimci tarko ne ya kafa mata. Hannu tasa ta share hawayenta, sai kuma ta taka da baya-baya ta koma saman kujerar dake a bedroom ɗin ta zauna..........


        ★Tun barowarta sashen nasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai faman kaikawo take hawaye masu zafi na kishin mijinta na ragargazar zuciyarta tamka irin kowacce macen da aka kawowa abokiyar zama, ba ita kaɗai ba, irinta da yawa sukan azaftu matuƙa da rashin barci da ƙunci a irin waɗan nan kwanakin bakwai da amarya takan samu matsayin na amarcinta. Kai wasu ma borinsu har yakan zarta natan, ga masu ƙarancin imani ma kwana suke shiryama zukatansu munanan abubuwa harma da masu aikatawa. To ita dai Fadwa saita kasance a jerin masu azaftuwar ƙuntatama kai da ƙiyasta abubuwa da dama da bai dace zuciya ta ƙiyasta ɗin ba ta kasance duk da su Aunty Wasila sun bata tabbacin hakan bamai faruwa bane ta kasa nutsuwa, sai dai babu tunanin mugunta ko shirka a ciki, ita dai kawai mijinta take hangowa da wata a yanayin da ita kaɗai ta sanshi.

     Tsahon lokaci ta ɓata tsaye jikin window tana kuka da dakon kallon hanyar tsumayen fitowar Anam da mijinta, amma sai saɓanin hakan ne ya biyo baya, domin kuwa shi kaɗai taga ya fito zuwa sashen Anam ɗin, bai kuma ɗauki tsahon lokaci ba ya fito ya sake komawa nasa sashen. Neman zubewa tai ƙasa kuka mai cin rai na kufce mata dajin tsananin tsanar su Daddy da take ganin sun ƙulla wannan aurenne saboda basa ƙaunarta ita da mahaifiyarta dalilin asiri da Abie da Mamie da aunty Mimi sukai na raba kansu tamkar yanda a koda yaushe Gwaggo ke faɗa. (karku ga laifin Fadwa, a haka aka raini zuciyarta, a haka ta girma da ƙiyayyar waɗanda bata da wani tabbataccen laifinsu a zahirin rayuwarta, da yawa iyaye na kuskuren wajen ƙoƙarin fidda matsalarsu da ƴan uwansu ga ƴaƴansu, sun kasa gane hakan yanada matuƙar tasiri ga zukatan ƴaƴan, dan in har akai wasa su ƴaƴan zasu tashine da ƙiyayya mafi muni da tsauri ta waɗan nan ƴan uwan nasu koda ace su daga baya sun haƙura sun yafema juna ne. Shiyyasa mafi yawan zuminci ke ƙara lalacewa da taɓarɓarewa a zukatan kowacce zuria fiye da ƙyamatar kafurci. Tasirinsa ne a tsakanin *_Anam da Fadwa_* duk da suna amsa sunan jini ɗaya, amma tunda ba uwa ɗaya ta haifi iyayensu ba, sun ɗauki hakan babbar tazara da bazata iya basu wata ƙyaƙyƙyawar jituwaba sai ƙyara da hantarar juna kawai. Sai kuma ga *KISHI* ya ratsa, wanda yake zamtowa linzami na rasa imanin *MATA* da yawa a dalilin zafafawa, ko da sunada tabbacin bazasu iya canja ƙaddara ba).

          A jiya kasancewar su Aunty Malika tattare da ita ya sama zuciyarta salama da ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta, musamman da zuciyarta ta dinga ayyana mata Shareff a sashensa ya kwana. Amma yau ganin zahiri ya hanata nutsuwa balle fahimtar kanta da kanta a matsayin abinda bazai iya canjawa ba ko samuwar ikon hanawa tamkar kowacce mace irinta. Kuka taci bana wasa ba, wanda ya jata lokaci mai tsayi har kusan ƙarshen dare sannan barci ɓarawo ya fara rinjayarta. A hankali ta sulale akan gadon ƙirjinta cike da nauyi tamkar yanda idanunta ke tattare da nauyin barci. (Koma dai miye ta bani tausayi, mu ƙiyasta kammu a matsayinta bisa adalci na rayuwa. ALLAH ka bamu kishi mai sauƙi da bazai sakamu a nadama ba🙏🏻😣).


    

          ★A lokacin da Fadwa ke can tana kuka da tunanin kasancewarsu a tsakkiyar lambun fure mafi girman daraja a garesu ba hakan baneba. Anam ta jima zaune akan sofa barci na rinjayarta tsoro na fisgota, sai dai bata da wata mafita ko ƙwarin gwiwa saboda babu ɓarawo mafi iya sata kamarsa. Kujerar 1sitter ce guda biyu, hakan yasa bata samu gamsuwar kwanciyarba duk da ta naɗe dukan jikinta a kanta. Daga inda yake kwance yaka hango yanda take mutsu-mutsu tamkar magen data sha matsa a hanun mafarauta. Guntun murmushi kawai ya saki, akan laɓɓansa ya furta “Azababbiyar yarinya”. Yana lumshe idanunsa dake cike da barci. Kusan mintuna goma ya bata domin barcinta ya ƙara nauyi sannan ya miƙe a hankali ya taka gareta. Cikin dabara ya ɗagata gaba ɗayanta yakai saman gadon ya kwantar yana danne dariya. Shi baima taɓa tunanin tanada nauyin barci hakaba, hijjab ɗin ya zare mata sannan yaja mata bargo shima ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Tsakanin Anam da Fadwa bai san wanene yafi wani daru ba. Itama yaso zuwa sashenta yay mata sai da safe amma tsoron abinda zai tarar ya sakashi haƙura. Bai taɓa tunanin da gaske *MAZA* najin shakkar matansu a irin wannan lokacin ba, dan duk yanda yake jin kansa da mazantakarsa da ƙin ɗaukar shirme sai nauyi da kunyar Fadwa ke zagaye da jininsa duk da auren nasa yazo a cikin wani kashine da yasha banban dana sauran maza mafi yawa irinsa.

     Numfashi ya furzar a hankali da juyowa gaba ɗayansa yana facing ɗinta, kallon fuskarta yake a cikin wani irin yanayi mai sanyi da zungurar zuciya, ya matsar da fuskarsa gab da tata tare da saƙala hanunsa saman jikinta ya rungumota a nasa jikin sosai, kamar wadda aka isarwa da saƙo ta buɗe ido, sai dai rashin ganinsa da ƙyau ya sata jan numfashi ta haɗiye tare da nasa da yake busa mata saman fuska. Jan jikinta tasoyi baya ya ƙara matseta. 

      “Yay......”

Kalmar ta kasa ƙarasuwa a zahiri tamkar yanda taso furtawa sai a cikin bakinsa, ba ƙaramin bugawa zuciyar Anaam tayi ba, duk da abinda takema tsoro kenan tun farko dama hakan bai hanata jin mamaki da shiga bazata ba. Bata da wani ƙarfin ƙwatar kanta, sai ma ƙoƙarin zare mata duk wani kuzarinta da razani yake ta hanyar cigaba da sarrafata a wani salo mai kashe jiki da ruguza dukkan alwashi na duk ɗiya mace mai lafiya. Tun tana iya cijewa harta fara amsar salon nasa dan takai shekarun da gangar jikinta ke a matuƙar buƙatar fiye da hakan ma. Sosai ya fitar da ita daga hayyacinta tamkar yanda shima nashi hankalin ya barranta da gangar jikinsa da zahirin rayuwarsa..........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_45_*
.........Saukar hanunsa a wani sashe na jikinta ya sakata dawowa hayyacinta babu shiri, ta damƙe hanunsa da fisgar kanta baya tana sauke numfashi da sauri-sauri kamar yanda shima yake sauke nasan. Kunya tsoro da firgici suka zagaye zuciyarta a lokaci guda. Jin abin take gin-girin-gin tamkar a mafarki, bargo taja da sauri ta naɗe jikinta da juya masa baya amma sai ji tai ya riƙota, maidota yay jikinsa har yanzu yana kokawa da numfashinsa da bai gama daidaita ba. So take tace wani abu tsoro ya hanata, sai jujjuya masa kai take alamar ya barta. 

       “Ni ba'a juyamin baya yayin kwanciya”.

   Ya faɗa cikin kunnenta da sake matseta a cikin jikinsa yanda bazata iya ko motsi mai ƙyau ba. Bata da zaɓin daya wuce yin shiru, dan tasan babu wani yunƙurinta da zaiyi tasiri tunda ruwa ba sa'an kwando bane. Sai dai kuma bata samu nutsuwar yin barci ba har sai da taji shi yayi..


        Rashin kwanciya da wuri baisa ta gagara tashi alokacin da sanyin asuba ya busa cikin ƙofofin fatar jikinta ya kaima jininta saƙo ba. Ta buɗe idanu a hankali tare da ƙoƙarin yin miƙa da tabbacin ta mance inda take. Rashin gani da ƙyau sakamakon duhun ɗakin ya taimakawa zuciyarta harbawa da ƙarfi irin na razana. Da sauri ta sauke hanunta kan abinda ƙwaƙwalwarta ta bata tabbacin mutum ne. Firgicin lokaci guda ya hanata damar tunawa balle yin nazari tai zaburar data farkar da shi daddaɗan barcin daya riskesa fiye dana farkon dare....

        Cikin zafin nama ya maidata jikinsa ya matse tare da kai ɗayan hanunsa ga makunnar fitila ya kunna. Tabbas badan hakan da yay ba babu abinda zai hanata wantsalawa ƙasa sakamakon gab suke da gefen gado ashe. 

    “Relax!”  

  Ya faɗa cikin sarƙewar muryar wanda ya farka a barci, domin samar da nutsuwa daga mutsu-mutsun data cigaba dayi har yana iya jin yanda zuciyarta ke harbawa da sauri-sauri akan ƙirjinsa. Babu alamar zata nutsu ɗin, dan jin muryar tasa ma da alama sake hargitsata yay a dalilin ganewa da tuna komai mai alaƙa da inda take. Sarai ya fahimci yanzu ba tsoron bane, borin kunyane kawai tattare da ita, dan duk ƙoƙarin da yake na son tama buɗe ido ta dubesa hakan ya gagara, sai faman san zame jikinta take da nashi da kuma ƙoƙarin hana ƙirjinta sauka kan nasa ta hanyar tokare tsakaninsu da hannayenta. Dariya sosai ta bashi, amma sai ya gimtse baiyiba ya matsa kaɗan daga gareta. Damar data samu kenan ta wantsala gefe faɗuwar dai daya gudar mata tun farko sai gata tayita, zafin daya ratsata ya sata sakin ƴar ƙara. Yanzun kam bai iya daurewa ba sai da ya murmusa, batare da yace mata komai ba ya tashi yay shigewarsa bayi har lokacin da murmushin akan fuskar tasa.

        Sai da ta gama ƴan matse-matsen hawayenta sannan tai wuf ta miƙe jin kamar alanar zai fito, key ɗin da idonta ya gani a gadon ta ɗauka ta nufi ƙofa da sauri hijjab ɗinta a hannu da galashinta da shima ALLAH ya bata sa'ar gani. Fitowarsa dai-dai da ficewarta a ɗakin.....


       Bayan idar da salla tagumi ta zabga ranta fal takaicin abin kunyar daya faru a ɗakin Yaya MM daren jiya, ta rintse idanunta dake cikin glass tana cije lips kamar ta tariyo komai ta goge a rayuwa da zuciyarta ko zata samu sukuni. Tamkar tana a gabansa ta murguɗa baki da miƙewa, tana naɗe sallayar tana mita cikin yaren malay. “Idan kaga ma na sake kallon hanyar sashen can naka ba riƙeni na kwana ba kace har abada bazan fitoba ma mana, ko kunya bayaji yana mazurai da zare ido amma zuciyarsa saninta sai ALLAH. Toni an faɗa masa waccan shashashar matar tasa ce dake hauka akansa, mtsoww! Tana wani fiffika ita mai miji kamar ance ana son mijin natane balle ra'ayin zama da shi. Aikin ɓurr miye abin so jikin wannan mutumin mai baƙin hali, sai dai ita ɗin dan dama duk jirgi ɗaya ya kwaso su mtsoww!!”. Haka ta dinga mitar har takai kwance kan gado, kasancewar barci ne taf da idon nata cikin ƙanƙanin lokaci yay awan gaba da ita tsiwa fal bakinta daya tashi sama kamar zai taɓo p.o.p.


         ★★★


     Kamar su, itama dai makarar tata bai hanata tashi yin salla akan lokaci ba, koda ta idar kuma kasa komawa tai ta kwanta kamar yanda tai niyyar yi, sai ta ɓige da kiran wayar aunty Malika dan a yanzu sune ke bata dukkan ƙwarin gwiwar da bata samunta a gun kowa hatta mahaifiyarta data san suma suna a cikin tasu damuwarne game da wannan auren *ƙaddara ko biyayyar* daya sami mijinta da rana tsaka. Cikin muryar barci suka gaisa da aunty Malika... 

      “Fadwa badai kin saka shashanci a zuciyarki kin gagara barci ba? Yanzu saboda abunda baida amfani kika zaɓi hana idanunki barci bayan mun gama miki da matsalar?”.

    “Aunty naso mantawa da komai tamkar yanda kuka faɗa sai dai na kasa. Wlhy na tsaneta shima a yau naji na tsanesa. Tare fa suka kwana a sashensa da ita”. Ta ƙare maganar da rushewa da kuka. Aunty Malika taja tsaki tana tashi zaune. “Lallai Fadwa ke shashasha ce gaskiya, yo duk da nasan cewar baki girmi yarinyar nan ba sai dai kuyi sa'anni kuma ita ɗin girman turaice ai banyi tunanin samunki haka muguwar lusara ba. Har mi akai wai akai wannan tsefatar yarinyar da kaɗan tafi wada tsaho. Fadwa kefa girman Nigeria ce, Nigeria ɗin ma Arewa, arewar ma kano kuma matsayin ƙabilar hausawa. Tunda kika taso a gidanku bayan mahaifiyarki kin sameta tare da wata matarne kafin ta fita tabar gidan, kinga kenan kinsan minene kishiya, kin san ilimin zama da ita tunkan ki buɗe ido kiga wata da sunan kishiyarki. Idan har kika cigaba da zubar da mutuncinki wajen zaman yin kuka ko bari Mijinki yaga lagonki to lallai k baki cika jinin zuri'armu ba.....”

     Cikin tarar numfashin aunty Malikan tace, “Aunty wlhy nayi dukkanin ƙoƙarina, ban aikata wani abu saɓanin wanda kukace nayi ba”.

         Ajiyar zuciya aunty Malika ta sauke. “Haka nake sonki ƴa tagari, ki zama jaruma kuma jajirtacciya a gidanta bawai lusara ba. Kamar yanda na faɗa miki yanzu ba'a bin boka ba'a bin malam akan kishi, kissa da kisisina da magungunan mata sune takubban ƴaƙar kishiya musamman irin taki da babu abinda ta sani sai kauɗi da buɗewar ido a cikin masu jajayen kunne. Kafin duniya ta goge mata idanu ta hango abinda kikema sakaci ki jajirce ki ƙwaci mijinki da wannan damar inba hakaba dare zaiyi miki, dare mai duhun tsiya da tafin hanunki ma sai kin gagara gani balle hanyar ceton ranki. Dan haka yanzu ki tashi ki haɗa breakfast mai rai da lafiya irin wanda baki taɓa masaba, kije ki shirya musu a sashen nasa kamar yanda ya buƙata”.

      Hawayenta ta share, duk da sam wannan shawarar batai mata daɗi ba amma zata jure, dan ita shaidace taga alfanun danne zuciya a jiya, badan ta shanye komai ta maidashi ba komai ba Shareff bazai ko dubeta ba akan abunda ta dinga masa tun daga fara rikicin auren nan. Amma gaskiyar su aunty Malika namiji tamkar yaro yake, duk kunnasan da kai da zarar ka lulluɓesa da kwalba sai kaifinsa ya zama mara tasiri ya koma haska maka zuciya da hasken wutar daka kunna masan. Da layin barci da dauriya ta shirya breakfast mai sauƙi kuma mai daɗi tamkar ba Fadwa mai babbake abinciba. Maimakon ɗauka takai sai ta fara shiga wanka, tsaf ta shirya cikin doguwar rigar lass ta caɓa ado tamkar ita ɗince amaryar, ta baje jikinta da kalolin turarren da tasan yafi so da ƙauna sannan ta fice ɗauke da basket ɗin data haɗa komai cikin yauƙinta da iya taku...

         Fitowarsa da ga bedroom yayi dai-dai da shigowarta. Sanye yake shima cikin ƙananun kaya masu taushi da rashin nauyi yanata bulbula ƙamshi. Ta sakar masa murmushi da faɗin, “Good morning Soulmate”.

      Idanunsa ya lumshe da jinjina mata kansa, laɓɓansa shima da ɗan murmushin. “Morning dear! how are you?”.

      “Alhmdullh” ta faɗa tana kauda kumburarrun idanunta da yakema kallon tuhuma, tasan shi mutum ne mai saurin fahimta, amma zatai duk yanda zatai domin hanasa hakan a wannan karon. Hanunsa ɗaya dake cikin aljihun wandonsa ya zare dai-dai yana ƙarasowa gareta, ya amsa basket ɗin. Batai musun bashi ba. Cikin zolaya da cigaba da kafeta da idanunsa dake tsumata ya kashe mata ido ɗaya.

      “Ai da nasan haka zan dinga samun gatan nan a wajenki dana jima da ƙara aure gaskiya”.

   Har cikin ƙwaƙwalwar kai maganar nan ta soketa. Harta kasa ɓoyewa fuskarta ta canja, amma sai tai ƙoƙarin saita kanta ta hanyar maida abun wasa ta hararesa da juya baya kamar tayi fushin wasa. Basket ɗin ya ajiye ya rungumota ta baya yana ɗaura habarsa akan kafaɗarta da murmushi bisa fuskarsa. “Juyawa Shareff ɗinki baya yana nufin lalacewarsa matata. Amma da gaske wannan aure yamun ranar zama ɗan gatan Fadwa”.

         Ita shaidace bai iya ƙaryaba, ko tace baya ɓoye-ɓoye. Duk abinda ya fito a bakinsa koda mai ɗaci ne shine iya gaskiyar dake zuciyarsa. Ta sani tayi kuskure a baya na gazawar bashi kulawa, duk da taci matuƙar burin hakan a garesa kafin aure......

   Jan hanunta da yay ya katse mata tunani, ya zaunar da ita a kujera yana faɗin, “Kinga jirani anan ina zuwa”. Kafin ta samu damar tuhumarsa harya fice. Ta bisa da kallo zuciyarta na ƙuna har hawaye na ciko idanun nata. Duk da gargaɗinta da zuciya keyi haka ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsa wai ko zata samu sauƙin ranta idan bataga alamar abinda take tsoro ba.....


       ★Da sallama ya shigo akan laɓɓansa idanunsa nabin ko'ina na falon da kallo, yayinda ƙamshin dake tashi ke masa maraba da amsa sallamar tasa. Samun falon shiru bai hanashi cigaba da kutsa kai ciki ba har zuwa bedroom ɗinta. Anan ɗin ma dai tsaf, sai dai babu alamar tana a ciki. Ya ɗanyi jimm na tunani sannan ya fito, falon ya dawo ya nufi hanyar kitchen...

     Tsaye take ta juyama ƙofa baya tanata kici-kicin saita sabon oven da take son ɗumama meat pie da take son yin breakfast da shi. Bluetooth ne a kunenta tana sauraren sabuwar waƙar mawaƙin nata da wata ƙawarta ta tura mata daga can malaysia, hargitsin bikin nan ya hanata zaman ji sai yau ta tuna da ita. Atamfa ce jikinta, wadda akaima ɗinkin fitted gown da yabi jikinta ya kwanta luff da fidda surarta matuƙa tamkar an zanata da pen, daga cinya zuwa ƙasa rigar ta buɗe matuƙa har tana zan ƙasa daga can baya. Bata cika son irin kayan nan ba, amma gargaɗin Mamie da nasiharta ana gobe za'a kawota ya sata daurewa ta tsara zata dinga sakawar insha ALLAH koda ba kullum ba. Bata iya ɗaura ɗan kwali ba, dan haka a maimakonsa saita kawo hula ta saka irin ta zamanin nan mai kama da ɗan kwalin. A jikinta taji tamkar ana kallonta, gabanta ya faɗi ta juyo da sauri dan dama dauriya kawai take na kasancewa ita kaɗai..........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_48_*........Hannunsa daya ɗaga kamar zai mareta ya dunƙule, yanda ilahirin fuskarsa ta canja kammani ya matuƙar girgiza zuciyar Anaam amma ta sake aro jarumatar dole ta baibaye tata fuskar da zuciya da shi.

    “Ita ƙaddarar data kawoki, ita zata dawwamar dake a cikin gidan sai dai ki haɗiyi zuciya ki mutu! idan kuma k kin isa mara kunya ce ƙafarki ta taka ko gate mugani stupid girl”.

    Kafin ta samu damar cewa wani abu ya fice a ɗakin, hawaye ne suka cigaba da rige-rigen sakkowa a kumatunta, zubewa tai a saman gadon ta rufe fuskarta da tafukan hanunta. Taja tsahon mintuna tana kukan kafin kiran daya shigo wayarta ya katse mata shi. Amrah ce, kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga takai kunne batare da tayi magana ba. Daga can Amrah tamkar mai tsoron ajita ta fara faɗin, “Kina jina Anaam?”. A taƙaice tace mata eh kawai. 

      “Ke kaɗai ce?”.

Cike da ƙosawa tace, “K dalla faɗi abinda zaki faɗa”.

   “Mtsoww! K daɗina dake masifa. Ina yarinyar na ƙawar Fadwa da muka gansu ranar da aka kai lefen Yaya Maheer?”.

         “Amrah dan ALLAH ki barni wane shirmene wannan?”.

“K Please karki kashemin waya maganace mai muhimmanci wlhy. Ina dai kin ganeta”.

    “Muje na gane, kamar Bibah suke kiranta”.

        “Yes! Exactly ita fa. Kin san yanzu ana tsaka da rigima a gidan nan kin san Mommyn su Yaya Shareff tana nan har yanzu tanata rikicin sai an raba aurenku, na fito daga gida zanje zan shiga cikin gidan kawai naga Bibah ɗin tare da Gwaggo da Maman Bibah a lungun mai shop ɗin nan, shine fa na lallaɓa naje kamar zan sayi abu a shagon, ki duba WhatsApp ɗinki na turo miki voice recording ɗin dana musu dan naga yanzu ma kin fini gane wani hausan”.

      Kamar Anaam zata gwaleta sai kuma tace mata “Okay” a taƙaice ta yanke wayar. Daga can Amrah bata damuba dan ta saba da halin Anaam tun suna yara, sai dai a yanzu ma ta fahimci kamar a cikin damuwa take dan muryarta da alamar tayi kuka.

      Taso share zancen Amrah ɗin amma sai yayta tsunkulin zuciyarta. Data ɗinta ta buɗe tare da shiga in box ɗin Amrah ɗin. Maganar ya ɗanyi ƙasa sosai, da alama ba gab take da su ba. Earpiece ta saka yanda zataji da ƙyau. Maman Bibah ce ta fara magana cikin alamun ɓacin rai. 

    _“Amma ba haka kikai min alƙawari ba, kin tabbatar min idan shirinki na zubar da cikin nan na Fadwa ya tabbata da Shareff ya dawo zakiyi duk yanda zaki ya aure Bibah, sai kawai naji wai ga wadda ya aura, kin kuma ƙi saurareni tun ranar ɗaurin auren nan, na kira ta waya Gwaggo da kinji muryata sai ki kashe”.

      Da ɗan zafin rai Gwaggo ta amshe da faɗin, “Haba Luba, wace magana kikeyi haka. Kina zaton zan faɗi abinda bazan cika bane, ai ni na fara miki tayin haɗa Bibah da Mustapha saboda ganin dacewarsu, na kuma tabbatar miki kasancewar Fadwa a gidan bazai hanata shiga ba duk da ƴar uwa take a gurinta itama. To amma su Muhammadu sukai wannan sarƙa-sarƙar da kema kin san gwagwarmayar da aketayi na hana faruwarta. Ba yin kammu bane, kuma bamu san sun ɗaura auren nan ba. Amma ki kwantar da hankalinki, ni bana rama alkairi da sharri, Bibah kamar ta shiga gidan Mustapha ne ta gama. Yanzu dai kuje gida zanyi duk yanda zan a satin nan na leƙi gidan naku kinga wani zai iya ganinmu anan, kuma za'a iya zargin wani abu shiyyasa ma nace kada ku ƙaraso gida mu haɗu anan”.

      Mamaki, al'ajabi, ruɗani duk suka dirga a zuciyar Anaam lokaci guda, ba komai ta fahinta a zancen ba, sai dai maganar zubar da cikin Fadwa da su Bibah suka bata shawarar yi ta fahimci cewar Gwaggo ce ta sakasu su bama Fadwa shawaran kenan, sannan Bibah ma son Shareff take kuma Gwaggo ta mata alƙawarin samunsa matsayin miji duk da da wadda ta haifi mahaifin Fadwa, da maman Mommyn Shareff, da Kakar Bibah wadda ta haifi Mamanta da Gwaggo uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Kai kai kai wannan makirar tsohuwa da abin mamaki take, ta ƙyalƙyale da dariya dake tabbatar da ƙunar zuciyarta a bayyane. Cikin bushewar zuciya da cin alwashi ta jinjina kanta.    

        “Yes bazan tafi ba, amma Yaya badan kurarinka ba, sai dan koyama matarka da Mommy da aunty Halima hankali har da kai kanka a dalilin tsohuwar banza Gwaggo, yanzu na ƙara fahimtar matar nan itace take ƙulla komai dake a family ɗin nan tabbas. Zan tabbatar mata *Karen bana! Shike maganin zomon bana* kuwa.. 


      Bayan sallar la'asar sai gasu Amrah, tayi farin ciki da zuwansu matuƙa, musamman Ikram mai shegen surutu da bakinta baya shiru. Suka shiga buɗe kulolin abinci dake a falon wanda ita bama tasan da su ba, sai dai kai tsaye ta gane Fadwa ce ta kawosu tana ciki. Koda suka tambayeta ita ta dafa? Kai tsaye tace musu matar gidan. Amrah dai kasa ɓoye mamakinta tai sai da tace, “Wai kina nufin Fadwa?”.

      “Bayan ita akwai wata matar ne a gidan?”. Ta faɗa batare data kalli Amrah ɗin ba. Harararta Amrah tai da faɗin, “Banza kefa idan kina kan dokin zuciya ba'a maganar arziƙi dake”. Shiru Anaam ɗin tamata hankalinta na kan hotunan su Gwaggo da Amrah ta dauka. Dukansu ta tura cikin wayarta, daga haka suka cigaba da hira. 

      An fara kiran sallar magrib Shareff ya shigo, fuskarsa murtik da alama har yanzu ransa a ɓace yake. Ikram ta sheƙa da gudu garesa dama tun ɗazun take tambayar yana ina Anaam ta mata shiru. Ɗaurewar fuskar ya ɗan sassauta yana shafa kan Amrah. 

    “Autah yaushe kuka zo?”.

Hanunsa cikin nata tana murmushi tace, “Yaya tun around Four. Inata tambayar aunty Anaam kana ina? Taƙi amsani”.

       Kallonsa ya kai ga Anaam ɗin, anyi sa'a itama ta ɗago nata idanun a lokacin. Janyewa tai cikin salo tana ɗan taɓe baki, shima sai ya janye nasan yana ayyana (Zanyi maganinki ne) a ransa. Gaishe sa su Amrah sukai, ya amsa musu yana ficewa da basu umarnin tashi suyi salla. Bai dawo gidan ba sai da aka idar da sallar isha'i. Kai tsaye nan ya zarto domin maida su Ikram gida. Anaam jitai kamar karsu tafi, tai musu rakkiya har wajen motarsa, sai da taga ficewarsu sannan ta nufi komawa suka kusa cin karo da Fadwa.

      Kallon kallo sukema juna, Fadwa ta saki siririyar dariya tanama Anaam kallon sama da ƙasa. “Amarya! Amarya! Ta ango baƙya laifi ko kin kashe ɗan masu gidaaa hhhhh. Uhhm kamar haka ake kirarin ko?”. Tai maganar cikin sigar tambayar rainin wayo ga Anaam dake kallonta ita dai. Dariya Fadwa ta sake kwashewa da shi “Oh sorry amarya, ALLAH kina bani tausayi, dan ban taɓa gamo da amarya irinki ba ko'a hikayoyin marubuta. Dama tsiyar auren cushe kenan fa”. Ta ƙarayin ƴar dariya da matsowa gaban Anaam dake kallonta uwa ta samu tv ko bata fahimtar yaren da take magana da shi. Cikin yin ƙasa- ƙasa da murya murmushi shimfiɗe a fiskarta ta cigaba da faɗin, “Zan baki shawara ƙyauta dana tabbatar zatai miki amfani ƴar turawa, karki bari ki zubar da ƙuruciyarki da lokutanki masu muhimmanci a inda ko kallonki ba'a da bukatar yi, gara ki taimaki kanki, ki tattara komatsanki kibi tsoffinki ku koma inda kuka fito koda baki gama serves ɗin ba, koda yake dama mun san bashi akazo yiba neman miji akazo. Bokanku ya iya aiki tunda gashi kin samu ta hanyar cushe, sai dai kuma akwai matsala mai yawa dan basu jehoki gurbin daya dace ba, gara ki sani tun yanzu, wannan gidan sai ya zame miki tamkar kurkuku mafi muni da ƙuntata a rayuwarki, kina da zaɓin taimakon kanki ko cigaba da zaman cin kwakwa, AL-Mustapha Muhammad Shareff anyisa ne domin Fadwa Sadiq Dakata kawai”. Ta kare maganar da ƙyafta mata ido.

       A karon farko Anaam ta saki murmushi tana girgiza kai. “Hauka maganinka ALLAH, ke kuma sanyin da wannan yanayin yazo miki. ALLAH ya ƙara afuwa”. Tai gaba abinta.

    “Ubanki ne mahaukaci ƴar iska”.

Anaam ta cigaba da tafiyarta tana dariya batare data waiwayita ba. A falo ta zube maganganun Fadwa na dawo mata ɗai-ɗai cikin amsa kuwwa. Tabbas bata da burin yin dogon zango a zaman gidan nan, sai dai ya zame mata dole zaman a yanzu kodan kawo ƙarshen makircin Gwaggo, na biyu zata cika burin iyayenta akan zumincinsu da suketa ƙoƙarin ganin sun toshe duk wata hanya da zata wargazashi. Na uku Fadwa, dolene ta koyama Fadwa hankali ta kuma tabbatar mata sufa *Mata suna suka tara* lokaci shi zai nuna *Zarah*. Na huɗu Mommy, na karshe Shareff, zata tabbatar masa da cewar ita ɗin ba kanwar lasa bace, daga shi har matarsa sai ta goge musu hadda a cikin gidan nan... 

      Ta saki murmushi a karon farko bayan ta kammala rubuta dukkan abinda ta gama lissafawa a cikin wayarta sannan ta mike. A dai-dai nan ya shigo falon da sallama ciki-ciki. Itama ciki-cikin ta amsa masa tana ƙara tsume fuska. Shima dai tasa fuskar a tsuke take, ya ajiye ledar hanunsa yana kallonta tamkar mai harara. “Shi wancan ɗakin da kika bari babu gyara waye zai gyara miki?”.

       Shiru kamar bata jisa ba, ya sake dubanta a harzuƙe.

      “Baki jini bane?!”. 

    Baki ta tura gaba, cikin magana ƙasa-ƙasa da tunanin bazaiji ba tace, “Matar taka ta gyara maka mana”.

    “Tunda ita ta kwanar miki a ɗakin ko”.

Kallonsa tai, dan batai zaton yaji ba, ta kauda idanunta da sauri ganin kallon da yake mata. Ƙafa ta ɗaga da nufin barin masa falon cafka ɗaya ya fisgota ta dawo gabansa. Marmar ta farayi da idanu da ƙyaƙyƙyaftasu, ta fara mutsu-mutsun ƙwacewa ya murɗe hannun. Ƙaramar ƙara ta saki da ƙanƙame masa hannu ta fashe da kuka. “ALLAH zai sakamin, kuma wlhy komi kamin sai na sanar da su Daddy...”

      “Bakin ki bazai mutu ba kenan?”. Ya faɗa da ƙara matse hanun. Wata muguwar wawura ta kaima hanunsa ta ƙallara masa cizo a ƙaramin yatsansa..........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_47_*
..........“Wayyo kaga kasa tayi fushi da abincin fa Soulmate”.

    “Ita ta sani”.

Ya faɗa cikin halin ko'in kula da cigaba da cin nasa. Fadwa zata cigaba da masa magiyar ya bita itama ya balla mata hararar. “Malama idan zaki ci naki kici bana son damuwa”. Shiru tai cikin kama baki kar kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Har suka kammala breakfast ɗin babu wanda ya sake magana a cikinsu, sai dai cikin nishaɗi ta cigaba da cin nata a yanzu, amma a zahiri tayi kalar damuwa dan karya ramfota. 


        ★★★


   Acan rijiyar zaki kam zaman lafiya yaƙi tabbata tsakanin Daddy da Mommy. Duk yanda kowa ke tausarta cikin ƴan uwanta akan ta nutsu abi komai a hankali amma fir ta nuna taƙi fahimta. Ita dai burinta kawai Shareff ya saki Anam. Babu kalar tujarar da su Mamie basa gani daga gareta, sai dai babu mai nuna yama san tanayi su dai fatansu zaman lafiya ga yarinyarsu. Babban abinda ke sake wutar tashin hankali a zuciyar Mommy shine rashin zuwan Shareff gidan, dan kuwa Daddy ya haramta masa sake zuwa gidan a yanzu har sai komai ya daidaita, kowa yasan yayi ne saboda Mommy ɗin. Gwaggo kuwa tunda ta nunama Mommy cewar ta kwantar da hankalinta zata nemo mafita, amma Mommyn ta murje idonta taima Gwaggo tas akan ita bata buƙatar wata mafitarta sai Gwaggo ta koma gefe ta naɗe hannu tai shiru, tayi tamkar ma bata gidan bata san borin da Mommy ɗin ke zubawa ba.

     Ba bori da tujarar Mommy bace kawai ke wanzuwa a gidan, harda Gwaggo Halima dake ganin ƴan uwan nata sunma ɗiyarta gudan jininta rashin adalcin raɓata kishi da ɗiyar ɗan uba. Itama dai bata da burin daya wuce ta ɗakko Fadwa ta dawo gida har sai Shareff ya saki Anaam sannan ta koma, sai dai baban Fadwa ɗin yay mata katanga da hakan. Hasalima ya bata sharaɗin ko gate ɗin gidansa ta taɓa da nufin fita a bakin aurenta da babu dawowa har abada. Dan shi mutum ne da dama baida wasa sam, badan haka ba da ya jima da zama mijin hajiya a gidansa saboda azabar Gwaggo Halima. Hatta da yaransa suna matuƙar shakkarsa, kuskuren da aka samu kawai shine siyasa ta kwashe kaso mafi yawa na hankalinsa har takai a yanzu bai iya saka idanu a kansu. Gwaggo Halima ta nutsu a gidanta cikin matuƙar tashin hankali da baƙin ciki, tasan ko giyar wake tasha bazata taɓa gangancin rabuwa da uban ƴaƴanta ba, domin yin hakan a gareta ba ƙaramin nakasu bane, shiyyasa ta nutsu a gida zuciyarta na mata zafi da raɗaɗi musamman naƙin jin Fadwa har a waya dan Abbansu yayi seizing wayar tata duk dan kar suyi waya, ya kuma hana har ƙanenta zuwa gidan Fadwan wannan shine dalilin da yasa a ƴan gidan su babu kowa a kusa da ita sai su aunty Malika dake matsayin ƙanne ga Abban nata.


        Yau ma dai kamar kullum tun bayan kai Anaam gidan Shareff da tujarar Mommy aka tashi gidan. Sai dai babu wanda ya kulata sai Gwaggo ce da tazo wuya ta fito tai mata tatas a tsakar gidan saboda ita kam dai haukar Mommy ɗin ya fara kaita maƙura. Tun Mommy na ƙoƙarin son nunama Gwaggo irin ɗaci da zafin da takeji a zuciyarta har tayi shiru ta koma kuka...

      “Gwaggo baki san irin zafin da nake ji bane a zuciyata wlhy, ji nake kamar na tsinema Shareff na huta. Ni yaron nan zai wulaƙanta a idon duniya ya nuna ubansa ne ya isa da shi bani ba!!”.

      “Ai taimakonki yay, saboda yin biyayya ga mahaifin nasa ne ya janyowa igiyoyin aurenki cigaba da wanzu har yanzu a gidan nan shi da Usman. Ban san mike damun kankiba Nafisa, ina wayonki ina hankalinki ne? Kinbi kin ruɗa kanki akan ɗan abu ƙanƙani da maganinsa ke'a hanunki cikin sauƙi.....”

          “Gwaggo taya zakice cikin sauƙi? Da'a sauƙine Shareff zai kai iyanzu bai saki yarinyar nan ba har zuciyata ta cigaba da ƙuna?”.

   “Kinbi hanyar da bazai saketa ɗinneba ai. Idan kin shirya cin nasara akan ɗanki sai ki nutsu ki dawo hayyacinki” ta ƙare maganar da miƙewa ta fice tabar Mommy da binta da kallo cikin rashin fahimtar kalamanta........


_________________________________


         Gaba ɗaya yau bashi da ra'ayin fita ko'ina, sai dai hakan bai hanashi yin wasu ƴan ayyuka ba ta cikin system ɗinsa. Zuwa yanzu babu kowa a sashen nasa, itama Fadwa tunda ta fita bata dawo ba. Shi kuma bai nema kowaccensu ba yanata harkokin gabansa har akai kiran sallar zuhur. Shigarsa bedroom ɗinsa domin ɗauro alwala ya sashi jan tsaki, dan yana nan a yanda suka tashi barci suka barshi. Har cikin rai abin ya sosa masa zuciya, yana da mace har biyu a cikin gida amma sashensa ya gagara samun shara. Ba yau ya saba ganin hakan ba, sai dai bazai yarda itama Anaam ta zama haka ɗin ba tunda yaga Fadwa ta fara gyara nata halayen itakuma. Jiya itace tai masa gyara, bazai yuwu kuma yau tayi ba bayan ba itace ta kwana a ɗakin ba.

      Koda ya fito sai da ya leƙa sashin Fadwa dan tabbatar data tashi yin salla kamar yanda musulinci ya koyar da duk magidanci na ƙwarai. Da mai-aikinta data dawo ya fara cin karo a falo, ta zube har ƙasa tana gaidashi. Hannu kawai ya ɗaga mata ya nufi bedroom ɗin Fadwa ɗin. Kwance ya sameta tana ramuwar barcin data hana kanta yi daren jiya, ya ɗan kafeta da ido na wasu sakanni kafin ya tasheta. Ɗagowa tai da ƙyar tana kallonsa cikin rufewar idon barci..

     “Tashi kiyi salla sai ki koma ki kwanta”.

   Da ƙyar ta iya amsa masa da to, yasan kaɗan daga aikinta yana fita ta koma, dan haka ya cigaba da tsaiwa a kanta har sai da ta tashi ta shiga toilet sannan ya fito. Sashen Anaam ya nufa, itama dai bai sameta a falo ba sai bedroom, saɓanin Fadwa ita kwancen kawai take amma ba barci take ba. Taji shigowar tasa amma taƙi ɗagowa ko sau ɗaya balle ta nuna tasan da wanzuwarsa. Tun a kallo ɗaya ya fahimci ba barci take ba, sai dai idanunta sun nuna taci kuka duk da suna a rufe dan ta cire glass ɗin. 

      “Ki tashi kiyi salla”.

  Bata tanka masa ba, kuma bata motsaba ya juya yay ficewarsa. Idanunta ta buɗe ta raka bayansa da harara tana laɓe baki. Sai da yaja kusan mintuna uku da fita sannan ta tashi domin gabatar da sallar, a ranta tana addu'ar zuwan jininta a nan kusa.

        Bayan ta idar da sallar saman sallayar ta cigaba da zama tana sharar hawaye, buƙatar kasancewarta da iyayenta ce ke damunta. Abinda Shareff ɗin yay mata ɗazun a dalilin makircin Fadwa har yanzu yana cizon mata rai. Ta san tun farko dama ya tsaneta, taya bazai goya bayan matar son sa ba koda ace itace mai gaskiya. Itako ta ɗauka alwashin baza'ai nisa ba balle har su sami galabar ƙuntata shi da matarsa, a yau ɗin nan za'ayi mai yuwuwa ita ba shashasha bace...

      Yawaitar ƙamshin turarensa a ɗakin ya tabbatar mata shigowarsa, amma sai tai kamar bata jiba duk da taji sallamar da yayi ciki-ciki. Ta gabanta yazo ya gitta ya zauna a bakin gado ta kusa da ita kaɗan, dan ƙafarsa ɗaya ma akan sallayar take. Ido ya ɗan tsura mata na wasu sakanni, tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata san da shigowarsa ba...

     “K kina ganin ba'a isa ace miki kinyi ba daidaiba kenan? To bari na faɗa miki matata ba abin rainawarki bace, a baya kunyi abinda kuke so k da ita, amma a yanzu bazan ɗauka raina juna daga kowaccenku ba. Dole ne duk mai buƙatar son zama lafiya da ni ta zauna da ƴar uwarta lafiya a gidan nan kuma cikin girmamawa da daraja juna!”.

     Yanda yay maganar a kausashe ya sata jin zuciyarta a wuya, hawaye ne suka shiga rige-rige sakko mata saman fuska, “Ni bance ina buƙatar zaman gidan ba ai, balle naima wata ƴar iska biyayy.....”

    Bummm ya buge mata baki da bayan hannu. Ba ƙaramin zafi ne ya ratsata ba, ta dafe bakin tana kallonsa da idanunta da sukai jazur ta cikin glass, sai dai babu hawaye yanzu a cikinsu sai tsantsar baƙin ciki da ƙunar zuciya. Ya miƙe tsaye yana nunata da yatsa. “Idan kin isa mara kunya a gidan nan ki sake yima matata ko kallon banza kiga yanda zanyi dake mara kunyar banza” 

       Hawayen da take riƙewa suka ɓalle mata, ganin zai fice bata amayar dana cikintaba ta miƙe zumbur, “Idan na zauna kenan har za'ayi yadda za'ayin dani, inda kun kwantar da hankalinku ni dama banzo wannan gidan naku da niyyar zama ba, matar taka kuma wlhy tasa a ranta bashi taci, dan ni naci uwarta iya wasan data ɗau layin muyi, dan bata kai matsayin mace ba a wajena. Itace jaka da har take tunanin mijin nata wani abin a SO ne, ni baka cikin irin mazan dazan iya SO Yaya balle muradin zama a shi gidan, ƙaddara ce ta kawoni nan badan rasa masoya ba. Zan kuma barsa a yanzun nan bari na har abada, dan ALLAH kuyi kwaɗon juna ku cinye......”

         A wani irin mugun fusace ya juyo gareta, dan har ya saka kafarsa ɗaya zai fice a ɗakin batare daya kulata ba, sai dai kalamanta na ƙarshe-ƙarshe sun masa saukar mashi ne a tsakkiyar ƙirji. Ko ɗar bataji da yanayin nasa ba dan itama zuciyar tata irin tasance kuma a wuya take fiye da tasan. Kallonta yake da jajayen idanunsa da suke neman wargaza duk wani ƙwarin gwiwar ta amma ta dake.........✍     
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_46_*
.........Kaɗan ya rage ta hamɓarar da wayarta dake ajiye, Baki ta tura da sakin numfashi mai kauri tana kai hannu saman ƙirjinta dake bugawa da sauri-sauri. Har lokacin bai motsa daga tsaiwar da yay jingine da bango ba ƙafafunsa a harɗe cikin na juna hakama hannayensa, sai dai cike da basarwa ya kauda idanunsa da tun ɗazun suke ƙare mata kallo tamkar ya samu television. 

       “Gaskiya irin haka babu ƙyau, a tsorata mutum idan zuciyarsa ta buga fa?”. Ƙasa-ƙasa take maganar da yaren Tamil (shima yana cikin yarukan ƙasar malaysia, kuma Anam ta iya sosai, sai dai bata san shima Shareff yana jin yaren ba, duk da a yanzu bazai iya magana mai tsaho da shi ba, sai dai komai ka faɗa zaiji zai kuma baka ƙananun amsoshi). Ta ɗan saci kallonsa, sai kuma ta juya cike da basarwa tana faɗin, “Good Morning”. 

      Maimakon amsawarsa tsaiwarsa taji a bayanta, taso ta dake, amma kusancinsu yaƙi bata damar hakan. Sai ta kashe oven ɗin kawai ta juyo da nufin barin wajen, komawa tai da sauri ta lafe jikin kitchen cabinet ɗin tana marmar da idanu, abubuwa da yawa sai tsarga mata suke da ga tsakkiyar kai zuwa ƙafafu saboda tsaretan da yay da idanunsa masu matuƙar kaifi da saka mata shakkarsa a lokuta da dama. Rashin mafita ya sata sake cemasa “Good morning” a karo na biyu. 

      Kansa ya jinjina mata idonsa akan fuskarta da babu kwalliya. Yana matuƙar son yaga mace da kwalliya, musamman jambaki, hakan yana ɗaya daga cikin abinda Fadwa ke tasirantarwa a zuciyarsa. “Mi kikeyi anan?”.

    Ya faɗa cikin dakewa idanunsa har yanzu na yawo a jikinta. Itama dakewar tai, cikin ƙin nuna fargabar kusancin nasu da pretending ɗin daren jiya ta bashi amsa. “Ina warming meat pie ne”. 

     Komai bai ceba, sai dai ya kai hannu zai cire meatpie ɗin daga cikin oven data riga ta kashe, ƙwara uku ne kawai sai cinyar naman kaza ɗaya. Wani plate ɗin ya ɗauka ya rufe sannan ya dubeta. 

      “Muje”.

  Mamaki bayyane a kan fuskarta tace, “Yaya ina kuma?”. 

  “Inda ake saida mutane”.

Tasan baƙar magana ya gaya mata dan haka tai shiru. Har tayi gaba taji ya riƙota, idanu ta rumtse wani abu na tsarga mata, ta juyo a hankali ta kallesa da idanunta dake cikin glass, ganin ita yake kallo shima ɗin ya sata kauda kai bakinta a sama. Jawota yay gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa, tana yunƙurin ɗagawa ya saƙalo hanunsa a ƙugunta ya maidata ya manne. Kusancin fuskarsu ya basu damar shaƙar numfashin juna. Sosai ta ƙwaɓe fuska tana son janye jikinta amma yaƙi bata dama. Sai idanunsa dake yawo a fuskarsa ne ke neman dagula mata lissafi. 

       “Yau ta zama ta ƙarshe da zaki sake tahowa bada izinina ba”.  

Kallonsa tai, sai kuma ta janye idanun da sauri. Shima janyeta yay a jikin nasa ya nuna mata hanya. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa dan gaba ɗaya yaci dukkan ƙudirinta da yaƙi a halin yanzun. Kwarjini da kamewarsa ta saka mata jin kasa masa musu. Kusan a tare suke tafiya duk da yanda take takun a hankali duk dan ya wuceta....


     Sosai ta dinga ƙarema gadon kallo zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ga wani irin zafi da zogin da ƙirjinta yake mata. Jitai bazata iya ƙarasa abinda tai niyya ba, tai saurin fita a ɗakin kanta na wani irin sara mata alamar ciwo. A falo ta zube ta shiga ƙoƙarin saita kanta tun kafin waninsu ya shigo. Sai dai kuma har tsahon mintunan data gaji da irgawa babu ko mai kamarsu, hakan ma ya ƙara sosa mata rai, tana shirin miƙewa ta tafi sai gasu sun shigo kowane da sallama ciki-ciki. Da ƙyar ta iya amsawa batare data kalli Anam ba.  

     Sai da duk suka zauna cikin son danne komai tacema Anam ɗin ina kwana. Anam da tun shigowarta itama bata dubi sashin da take ba tai mata banza kamar bataji ba. Haka dama Fadwa ke buƙata, dan haka tai murmushi tana satar kallon Shareff da yay kamar hankalinsa baya kansu.

      “Amarya nace an tashi lafiya?”.

  Ɗago ido tai a karan farko ta kalleta ta watsar, sake maida hankalinta ga wayarta dai-dai da ɗagowar Shareff ya dubi Anaam ɗin ransa a ɓace, sai dai kuma ya haɗiye fushin nasa da kai hannu kan bluetooth ɗin dake manne a kunenta a zatonsa shine ya hanata jin Fadwa ɗin kuma. Saurin dafe kunnen tayi da kallonsa dan tasan babu abinda take saurare a ciki kawai dai bazata amsawa Fadwa ɗin bane. Ta zareshi gaba ɗaya fuskarta da babu kwalliya na ƙara shagwaɓewa. 

     Hannunsa ya miƙa mata alamar ta bashi, amma sai ta maƙe kafaɗa, cikin muy-muy da baki take faɗin, (Mazuran nan fa dai kowa ya iya ai, niba tsoro nake ba dan kayi), A fili kam sai cewa tai, “Yaya miya faru?”.

      Hararta ya ɗanyi da sake miƙa mata hanunsa. “Karna sake ganinki da wannan abun a lokacin da muke tare baki ɗaya. Ana magana ko jin mutane baƙyayi. Bani nace”.

     A marairaice tace, “Nafa cire”.

Matsowar da yay idonsa tamkar zai faɗo saboda kallon da yake watsa mata mai kama da harara ya sakata zabura tai ɗan baya kaɗan tare da tura bluetooth ɗin cikin rigarta saboda hango murmushin da Fadwa tai na alamar cin nasara, sai kuma tunawa da yanda yay mata da key jiya da dare ya sata ganin itama idan tai haka dole zai barta ai, dan hanunsa dai tasan bazai shiga nan ya ɗauka ba. 

      Tsamm Fadwa ta miƙe ta nufi kicin ɗinsa ranta fes da ganin fushi a fuskarsa, ta tabbatar Anaam ta cigaba da jaa akanta zai saukesa. Laɓewa tai tana leƙensu da kasa kunne da ƙyau dan jin yaya za'a ƙare.

      Cikin bada umarni da ƙara tsuke fuska ya sake miƙa mata hanu “Ciro ki bani da arziƙi”.

     “To ni Yaya dan ALLAH mi zakayi da shi? Badai na cireba shike nan, kuma ai banji bane”.

   “Dama ba lallai sai kinji ba ai, bani”. 

Kanta tai niyyar ɗaukewa taji ya damƙo hannayenta, zabura tai tana waro idanunta dake cikin gilashi gaba ɗaya waje saboda tsantsar firgicin jin ɗayan hanunsa cikin rigarta yana laluben bluetooth ɗin data tura a bra....

      Har taune harshe take wajen faɗin, “Yaya Please w...Wlhy zan baka, tsaya ka tsay...”

    Ko nuna alamar ya jita ma bai ba ya tura hanun nasa har cikin bra.. ɗin ya ɗakko bluetooth ɗin. Zuwa sannan gaba ɗaya jinin Anam ya tsaya cak da daina zagayawa tsabar firgita da abinda yay ɗin. Shiko ƙememe babu alamar kallon abinda yay ɗin da girma tattare da shi. Saina hararta da yayi ya ɗauke kansa.

      Fadwa dake yunƙurin fitowa tai mutuwar tsaye, dan jitai tamkar saukar aradu a tsakkiyar kai, a zatonta yanda ya harzuƙa da farko mari zai saukewa Anaam akan fuska. Jin hawaye na ciko mata ido tai yunƙurin komawa cikin kitchen ɗin

     “K kuma ina zaki?”.

Ya faɗa dai-dai yana saka bluetooth ɗin cikin aljihun wandonsa idanunsa akanta. Amsa ta bashi batare data yarda ta kallesa ba tana wucewa. “Ina zuwa nayi mantuwa ne. 

    “Kin san dai yunwa nakeji”.

“Kayi haƙuri ina zuwa”. 

Ta amsa masa hawaye na sakko mata. Da ƙyar ta iya kai kanta jikin kitchen cabinet ɗin ta jingina saboda jin hajijiya na neman zubdata. Tasan shi din mutum ne kai tsaye, amma batai zaton iya yin hakan a gabanta ba, koda yake ba'a gabanta bane tunda ta tashi, maybe kuma baiga sanda ta fito ba shiyyasa. Da wannan ta bama kanta ƙwarin gwiwar share hawayenta ta goge fuskarta ta sake fitowa.

      Kofuna da plates data ɗakko ta ajiye tana magana cikin ɗan murmushin yake. “Am sorry Soulmate, bismillah ku sakko”. 

     Harta kammala zuba Irish ɗin ma kowa Anaam da har yanzu mamakin Shareff ya kasa barinta bata iya ta sakko ba. Sai da suka fara cin abincin ya ɗago ya harareta sannan. Bataci dankalin ba, meatpie ɗinta ta ɗakko. Yi yay kamar bai ganta ba, sai Fadwa ce tai magana cike da kulawa a gareta. Dan burinta bai wuce ta wanke zuciyar Shareff akanta ba ya tabbatar ta amshi nasiharsa a gabansa, ta hakane kawai za'a fara wasan da zataci nasara akan Anaam dake nuna ƙuru-ƙuru kishinta takeyi, ba kuma zata iya ɓoye abu ba, tabbas hakan nasararta ce ta yaƙarta cikin sauƙi a wajen mijinta. “A'a Amarya bara a haɗa miki tea ko, kamar zai fi ki haɗa da shi”.

       Anaam data kalli kamar rainin wayon Fadwa ya fara yawa a kanta ta ɗago tana mata kallon ido cikin ido. “Madam mind your business abeg. Shin dole ne sai kin sakani a sabgarki ne wai?”. 

     Cikin sauƙaƙa murya da karyar da kai Fadwa tace, “Ayya I'm sorry dear ban.....”

   Ɗagowar Shareff dake hararar Anaam a fusace ta sakata haɗiye sauran maganar bata ƙarasa ba. “Ashe zan fasa bakinki yay jini idan wata maganar banza ta sake fitowa a cikinsa. Ya tana miki magana cikin lalama kina wani botsarewa dan walaƙanci!!”.

     Tuni ta daina tauna meatpie ɗin, babu abinda zuciyarta keyi sai tafasa da kumburowa cikin ƙirjinta, musamman da taga murmushin da Fadwa ta saki tana kallonta. Hawayen takaici suka ciko mata idanu, tsam ta miƙe dai-dai Fadwa na faɗin, “Lah babu damuwa wlhy Soulmate. Inaga bata fahimceni bane ba shiyyasa......”

    Bata gama jin ƙarshen zancen ba tai ficewarta..........✍


*Tofa masu karatu da alama yanzu za'a fara wasan. Wadda ta iya allonta tsakanin Amarya da Uwargida saita wanke.😉😆😝🚶🏻.* 


    _Ni dai anawa gaskiya daga Fadwa har Anaam kowanne salon nasa kishin akwai *Dai-dai* akwai *Laifi*. kumuje zuwa domin fahimtar kuskurensu da dacewarsu gaba ɗaya🤌🏻, dan a wannan gaɓar a zahirin rayuwarmu nake so muyi kallo da zamansu bawai rayuwar littafi ba, kunga kenan wadda ta iya allonta itace star a wajenmu, duk da dai a tsarin labarin muna yinsa ne akan *Anaam* gaskiya, domin itace kamar ke jan zaren labarin, sai dai hakan bashi ke nufin ƙyawawan halayen Fadwa bazasu fito ba ko kuskuren Anaam. Ina fatan zaku fahimceni dan naga wasu sun fara cewa a saki Fadwa. 😌To bara kuji zama daram Fady babynmu ko yaji bazatayi ba garama ku shirya kishi yanzu muka fara da ƴar mitsilarku😎🫣🥱🤪😂👌🏼._
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_50_*..........Tasirin maganganun Gwaggo ya hanata sukuni, ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kuma gagara basu fassarar data dace. Gwaggo dai uwa ce a gareta, domin mahaifiyarta haihuwarta kawai tai da shayar da ita. Dan tun daga yaye da Gwaggo ta ɗakkota bata sake waiwayen gidan mahaifinta ba sai da yawo. Ita ɗin tarbiyyar Gwaggo ce kuma rainonta. Ta samu gata irin wanda alƙalami bazai iya zanawa ba a takkada da ga gareta, domin kuwa a zamanin ƙuruciyarta kosu Muhammad (Daddy) dake ƴaƴan MB Shareff na cikinsa basu kaita jin daɗi ba a hanunsa. Gwaggo wata irin mutum ce da gane zuciyarta sai ALLAH, hakan yasa har Umma Hajarah tabar duniya bata taɓa hankaltuwa da wacece Gwaggo ba. Ba Umma Hajarah ba hatta su Daddy a yanzu basu fahimci kaso talatin cikin ɗari ɗin halayen Gwaggo ba sam, duk wannan faɗi tashin nasu akan zumincin da suke tada jijiyar wuyan ganin bai salwance ba. Tai gajeren murmushi da sauke ajiyar numfashi mai nauyi, dan tabbas mafitar data kasa nutsuwa ta samo akan wannan auren da bazata taɓa yarda da tabbatuwarsa ba tana wajen Gwaggo. A ganinta miya rage? Kawai ta kwantar da hankalin nata bisa shawarar tsohuwar ta kuma bita daki-daki domin cimma nasara. Sai dai a sanin datai mata kota tunkareta a yanzu bazata samu abinda take buƙataba dan haka zata barta har zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu......


         ★Jin kamar motsinsa yasa ta bar wajen da sauri, ruwan ta ɗakko ranta duk a dagule na rashin ƙwaƙwaran hujjar ya ganta ko bai ganta ba. Sai dai wani gefe na zuciyarta na ƙarfafata akan ta dake ta fuske kawai, (haba sai kace ba Anaam ba! karki bada mata mana). Da wannan kurarin ta dake ta koma bedroom ɗin, inda ta barsa nan ta samesa, sai dai yanzu ya warware lap-top ɗinsa a saman stool ɗin mirror daya jawo gabansa alamar aiki zaiyi. Ganin yana ɗan kusa da side drawer na gado saita ɗaura anan, sai faman riƙe rigar take da hannu ɗaya duk da a yanzu ba'a ganin komai jacket ɗin ta rufe ruf. Duk yanda taso zuciyarta nutsuwa ta gagara, ta ɗan saci kallonsa, hankalinsa gaba ɗaya yana ga aikin da yakeyi, hasken screen ɗin laptop ɗin ta haske fuskarsa. Gani tai ya ƙara mata wani ƙyau da kwarjini, ta haɗiyi yawu da ƙyaƙyƙyafta idanu domin abinda take son faɗa mai nauyi ne, sai dai gaskiya bazata iya jurewa ba gara dai ta tabbatar.

    Murya a noƙe tace,  “Yaya MM!”.

“Uhhyim”

Ya amsa mata batare da ya bar abinda yake ba. Sai da ta sake juya maganar a ranta kafin ta furta kamar zatai kuka. 

      “Dan ALLAH in tambayeka zaka gayamin gaskiya?”.

Karon farko ya ɗago ido ya ɗan kalleta, tai saurin sauke nata idanun ƙasa. Idanun nasa ya sake maidawa ga aikinsa. Harta fidda rai da amsawar tasa ma.

     “Malama kiyi maganarki kai tsaye”.

  Baki ta tura gaba da ɗan murguɗawa kaɗan harda masa ƙaramar harara, zuciyarta sai ƙwaɓarta take amma wata na ingizata kuma. Cikin in ina da tsantseni ta cigaba da magana. “Dan ALLAH ɗa..zun da ka shi...go k...a...ga..n..ni k..o?”. Ta ƙare maganar kamar zatai kuka.

       Cak ya tsaya da ga danna keyboard ɗin laptop da yake yi, ya ɗago idanunsa da suka canja launinsu tun ɗazun ya kalleta. ɗan ƙara tsuke fuska yay tamkar abinda take maganar a kai bashi ke neman hanasa sukuni ba, murya a dake ya bata amsa kai tsaye...

     “Kina min talla na ƙara gani ne?”.

Babu shiri ta ɗago da sauri, sai ko idanunta cikin nasa. Ta zabura baya tana zagaya hanunta ta saman kanta “God forbid! Sai kace wata ƴar iska?. Kuma nidai ALLAH ya gani ai tambayarka nayi, dan zuciyata ta kasa nutsuwa nasan ka iya fuskewa da mazuranka bayan kuma k..k..k.....” ta kasa ƙarasawa saboda kallon da yake jifanta da shi mai matuƙar yawan aji-aji na fassara.

     “Ni dai naji, shike nan sai da safe. Dan ALLAH a dinga knocking idan za'a shigo”. Ta ƙare maganar da zagayawa bayansa da hayewa gado tana murguɗa baki. Zaune ta tashi da sauri, muryarta na rawa kamar zatai kuka, “Ni Juwairiyya, nifa kamarma cakai ina maka talla ka ƙara gani!, kenan ka gani ɗin fa? Wayyo Mamie na, ki roƙamin gafarar ALLAH Yaya ya fara komaw......”

        Muƙut ta haɗiye zancen ganin ya hawo gadon, ta zabura zata wulƙita ƙasa ya damƙota. Gaba ɗaya idanunta sukai wiƙi-wiƙi tamkar an kama tsohon kwarto a ɗakin surukarsa. Duka hannayenta ya maida baya ya riƙe da hannu ɗaya, ta shiga girgiza masa kai cikin magiya da roƙo muryarta na rawa tabbacin kuka na gab da zuwa. Ƙafafunta da take turzawa ya sa ƙafarsa ya danne, ya kai ɗayan hanunsa kan igiyar rigar tata, ja ɗaya yay mata ta warware dama ɗaurin zarge tai mata. Rigar ta buɗe, ƙara ta fasa masa, babu shiri ya kai hannu ya rufe bakin. Muƙutt ta haɗiye abinda ya rage bai fito a bakin nata ba, idanunsa da suka ƙara canja launi ya watsa mata, “Ba haka kike so ba na buɗe na gani”.

       “ALLAH ya kiyaye wlhy”. Ta faɗa da sauri tana son motsa jikinta ko yaya amma yayi mata riƙo na gaske. 

    “Idan wannan bakin naki ya sake cewa (tak!) saina yage ɗayar ma silly girl”. Ya ƙare maganar hannunsa na sauka saman wuyan rigar da gaba ɗaya ya bayyana ƙirjinta saboda girmansa, rabin jikin nata ma duk a waje suke gashi ta kamata tsam kasancewar roba ce sannan copy lass mara nauyi.

     Fashewa tai da kuka na tsananin borin kunyar daya jefa rayuwarta a ciki, dan ita harga ALLAH bada tunanin komai tai tambayar ba. Sai da ya tabbatar ya firgita ta sannan ya saketa, wani irin kwakusa ta kaima duvet ta ƙudundune har kanta...

         Ƙara danne abinda ke hargitso masa brain yay da ƙyar ya koma ya zauna. Robar ruwan data kawo masa ya ɗauka, batare da yabi takan kofin ba ya ɓalle murfin ya dasa a baki. Tass ya shanye ruwan yay wurgi da robar yana rumtse idonsa da jijjiga kai tamkar mai girgije ruwan cikin suma. Ture stool ɗin da laptol ɗinsa ke kai yayi yana jan wani bahagon tsaki, toilet ya nufa cikin sassarfa kai kace ingizashi ake da remote.

       Anaam da bata san yanai ba na maƙure cikin bargo tayi luff takaicin kanta da kanta ya gama dabaibayeta. Ji take tamkar ta ciji kanta dan haushi. A gaba ɗaya abinda ya faru sai yanzu take iya lissafa rashin wayonta, mima ya kaita masa tambayar? Ta cije lip da ƙarfi tana kaiwa gado mugun mintsini tamkar shine ya mata laifin.. Jin shirun ɗakin yayi yawa ta ɗan leƙo kanta kaɗan, wayam babu shi a ɗakin, jitai wani farin ciki ya ratsata, ta miƙe da sauri ta dire a gadon, ƙofa taje ta sakama key duk a tunaninta fita yay a ɗakin. Ranta fess ta juyo tana karkaɗa keys ɗin da faɗin, “ALLAH na gode maka daya fita azababbe, sai iya fassara mutum akan abinda ba haka yake ba, kuma ban yafe ba ganinmun jiki da akai da way......”

      Numfashinta ya tafi zuuu ta haɗiyeshi tare da yawu, da ƙyar ta iya ɗago ido kaɗan ta kalla abinda taci karo da shi. Shine ɗin dai ba wani ba, zirr! Zirrr! Zirrr!! Haka jininta ke gudu a cikin jijiyoyinta yana kaima zuciyarta da ƙwaƙwalwa rikitattun saƙwanni masu tabbatar da firgicin mutum a cikin idanu. Miya rage? Kawai ta kwasa da gudu tabar ɗakin nan. Zuciyarta ta ayyana mata cikin ƙarfafawa domin ta tabbatar babu makawa yaji abinda take faɗa ɗin.

     Hannu ya miƙa masa alamar ta bashi keys ɗin. Cikin langaɓe kai da girgiza shi, hannunta ɗaya na tattare da rigarta da taketa faman kare ƙirji. “ALLAH bafa da kai nake ba, kayi haƙuri zan maka bayani yanda zaka fahimta...”

           “Nazo na amsa da kaina kenan?”.

   “A'a wlhy, ni dai ba sai kazo ba, daga nan ma zan maka bayani”.

   Yunƙurin matsota yay, da sauri ta jefa masa keys ɗin ya cafe. Cikin aljihun wandonsa ya zurasu da nuna mata gado. “Wuce ki kwanta”.

      Hankali tashe ta buɗe baki zatai magana....

   “Idan kika furta (A) sai na miki fata-fata a ɗakin nan. Idan kuma kinji ƙarya bismillah”.

     Summ summ ta wuce hankalinta a matuƙar tashe. Ya raka bayanta da wani shegen kallo tamkar idanun nasa zasu wantsalo waje........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_49_*.........Da sauri ya saketa yana yarfar da hanun, tako kwashe da dariya ga hawaye sharɓan a fuskar. “Kaɗan ma ka gani indai nice Yaya”. Ta faɗa cikin riƙe ƙugu da murguɗa baki. 

    Idanunsa da har sun kaɗa alamar cizon ya shigesa matuƙa ya ɗago yana kallonta da kaiwa zaune cikin kujerar dake kusa da shi. Ƙoƙarin barin falon tai tana masa gwalo, zamewa ƙafarta tai a dalilin turza carpet tai baya zata faɗi. Da ƙyar ta samu nasarar dafe kujerar da yake zaune, samun rinjayen jikinta a nasa ya tilasta mata zubewa kansa inba hakaba dole sai ta faɗin. Jikinta har rawa yake wajen son yunkurawa ta tashi ya sake saka ƙafa ya taɗota ta koma. Ya saƙalo hanunsa ta saman ƙugunta ta yanda bata isa sake ko yunƙurin tashin ba, fuskokin su gab suna shaƙar numfashin juna. Idanunta dake cikin gilashi ta shiga ƙyafta masa zuciyarta na wani irin bugu da sauri-sauri saboda bata taɓa tsintar kanta a cikin irin wannan halin tare da namiji ba bayan shi, ta sake yunƙurin tashi gaba ɗaya dan kunya ta gama dabaibaye rayuwarta bakinta cike da tsiwa tana motsashi sai dai bayajin abinda take faɗa. Ƙafarsa yasa ya sake harɗeta da manneta da jikin nasa dai-dai lokacin da Fadwa ke ƙoƙarin shigowa falon ɗauke da ƙaramin basket a hannu, cak numfashinta ya tsaya, sallamar datai niyyar rangaɗawa ta maƙale a maƙoshi. 

      Idon Anaam yaga Fadwa sarai, dan haka ta dakata daga yunƙurin tashi da takeyi duk da tsumar da jikinta ke mata, shiko da bai lura da Fadwan ba saboda baya ya bata kaɗan sai ya kamo haɓar Anaam ɗin tare da sake matso da fuskar tasa gab da tata. Ya ɗan ɗage girarsa ɗaya a sama yana kallonta cikin tsakkiyar ido. 

     “K bakin ki bazai taɓa mutuwa ba ko?”.

      A salon da yay maganar ba ƙaramin tsargawar zuciya ya saka Anaam ba, sai dai tai matuƙar daurewa wajen tura masa bakin nata sabida tunawa da Fadwa a wajen. Lips ɗin ya ɗalla da ɗan yatsa, babu shiri taja kanta baya da ƙoƙarin dafe bakin ya hana hakan ta hanyar buge hanun ya ɗaura nasa lips ɗin akan nata. A matuƙar bazata abin ya zomata. Cikin tsumar jiki ta ƙanƙamesa zuciyarta na luguden daka a ƙirjinta tamkar zata wantsalo dan wannan shine second kiss nata a tsayin rayuwarta duk da kuwa ta kasance girman cikin jajayen fata. Ko saurayi irin na school ɗin nan Anaam bata yarda tayi koda ance ana sonta, sai takai ma tsiwarta da rashin ragowa yasa matasan samarin makarantar tasu na shakkar tararta da abinda ya shafi soyayya, kaɗan daga aikinta ta maka tatas a gaban kowa ita ba ruwanta, hatta da ƙawa ɗaya gareta itama dan hali yazo ɗayane shiyyasa suke shiri, dan itama fitinanniya ce ta bugawa a bangon class. Hakama data shiga jami'a bata shiga sabgar kowanne namiji duk nacinsa kuwa inba akan abinda ya shafi karatu bane ba.

       Ta kowanne ƙofar jininta saƙonsa shiga yakeyi jikinta, ya kashe dukkan wani sauran kuzarinta da yunƙurinta, sai da ya barta dan kansa ta samu damar kife kanta a ƙirjinsa tsigar jikinta na tashi, shekara ashirin da uku ba shekara sha uku bace, itama mutum ce tamkar kowa kuma lafiyayya dake samun ingantaccen abinci mai gina jiki, ga kwanciyar hankali, giɓin rashin mahaɗinne kawai tattare da ita dama. Samuwarsa gareta a halin yanzu kuwa tamkar motso mata dukkan abinda ke ɓoye a cikin jininta ne ko tana so ko bata so.. Hannayensa duka biyu ya ɗaura a saman bayanta, tare da kai bakinsa saitin kunenta murmushin dake ta ƙoƙarin son bayyana kansa a fuskarsa na ƙoƙarin kufce masa. 

       “Daga yau da wannan zan dinga punishment ɗin bakin rashin kunyar tunda shi idan aka faɗa sai ya maida”. 

     Janye kanta ta rinkayi dan yanda yake maganar a cikin kunenta da busa mata numfashi sai yake neman sake hargitsa mata lissafinta. Nasarar janye jikinta ta samu ta silale ƙasan kafafunta, shiko ko'a jikinsa, sai ma umarni daya bata cikin kame murya. 

          “Malama tashi ki bani abinci, muje kuma ki gyara bedroom ɗin can yau komin dare”.

     A yanda take kai a kife cikin cinyoyinta ta gallaro masa harara da murguɗa baki, sai da taja wasu sakanni sannan ta miƙe bisa shawarar zuciyarta, dakewar kuwa tai itama, tai kicin-kicin da fuska ta kuma ƙi yarda tako kalla sashin da yake. Bataga Fadwa ba yanzu, da alama tuni taba kafarta abinci. Haka kawai taji murmushi ya suɓuce mata ta ɗan harari ƙofar tamkar har yanzu tana a wajen ne.  

      Fuskarta a gefe tace, “Nifa banda abinci anan”.

   Ɗan dagowa yay daga latsa wayar da yake ya dubeta, sai kuma ya dubi ledar daya shigo da shi ɗin wadda yasan sarai itama ta gani ɗin. Sake maida kansa yay ga wayar batare da yace komai ba. Jitai kamar ta makesa dan duk tana kallonsa ta gefen ido, batare da ta sake magana ba ta ɗauka ledar ta nufi kitchen tana kwaikwayon yanda yay magana cikin bada umarni shi a dole mai kame girma bayan ya gama tsotse mata baki.

       Bayan wasu mintuna ta dawo da abinda ke cikin ledar cikin plate data juyo sai ruwa da lemo da cup duk ta haɗo a saman tray. Ta ajiye a saman centre table batare data yarda ko sau ɗaya ta kalla sashen da yake ba. ALLAH ya sota ma waya yakeyi, takoyi wuff tabar wajen. Da kallo ya bita harta shige, ya ɗauke kansa da ɗan furzar da numfashi yana cigaba da sauraren Fharhan....


        ★Gaba ɗaya brain ɗinta kusan daina neman yin aiki tayi, kukan da take sonyi dan taji daɗi ma yaƙi fitowa ko ɗigo ɗaya. Tasa ƙafa ta hankaɗe basket ɗin abincin data tafi da niyyar kaiwa Anaam ɗin saboda ganin Shareff ya shiga can, dan koda ya dawo sashenta ya fara shiga ya kai mata ledarta, da tace masa ga abinci cewa yay ya ƙoshi tunda bai daɗe da cin na rana ba. Taji haushi amma ta dake harya barota fuskarta da murmushi, yana fita ta zabgama ƙofar harara da faɗin, “Munafuki” (Ƴan uwana mata a kiyayi zagin miji koda a zuciya😕). Harta zauna zata buɗe ledar daya kawo matan sai kuma ta mike, abincin data shirya domin shi ɗin ta tattara cikin ƙaramin basket ta ɗauka da nufin zuwa ta kaima Anaam a gabansa, Cikin ranta har tana saƙa abinda zai faru dan tayi shirin kunna Anaam ɗin ta yanda yau ko kwana a ɗaki ɗayan ma sai ya gagaresu duk da tasan iya shi ɗinne zai faru a tsakaninsu saboda ta yarda da su aunty Malika ɗari bisa ɗari. Amma maimakon hakan sai tai gamo da abinda ya nema saka zuciyarta faɗowa ta baki, wai yau mijinta, abin sonta Al-Mustapha ne rungume da yarinyar data tsana fiye da komai a rayuwarta yana kissing. Ta rumtse ido da sauri komai na dawo mata tamkar a film, ƙara ta saki dayin cilli da throw pillows ɗin dake a kujerar da take ƙasa, hawayen da take ta faman son zubo mata na rige-rigen sakkowa a bala'in guje.....


     ★Rashin fitowarta har ya kammala wayar ya sashi kiran wayarta, tana zaune a bakin gado abubuwa da yawa na mata kaikawo cikin zuciya da ƙwaƙwalwa. Batare da sanin shi bane ta ɗaga kiran dan bata da wannan number tasa. Shiru batace komai ba, jin anyi shiru daga can ma tai sallama muryarta a sanyaye dan da gaske ya rusa mata dukkan ƙarfin jikinta da kuzari. Numfashi ya sauke a hankali, batare da amsa sallamar tata ba.

       “Idan kika bari na sameki a ɗakin nan komi ya faru kiyi kuka da kanki”.

   Sarai ta gane shine, kafin ta samu damar cewa wani abu har ya yanke wayar, ta dafe kanta dake sara mata kaɗan-kaɗan. Da gaske kunyarsa takeji, kunya irin wadda bata taɓaji akan waninsa ba, abinda yake mata yakan zo a bazata gareta. Sanin halinsa na cika magana idan ya faɗa ya sakata miƙewa ta fito. Kallo ɗaya tai masa bata sake ba, shiko baima nuna yasan da fitowarta ba abincin sa yake ci hankali kwance. Itama sai ta fice.  

       Da gaske bedroom ɗin yana a yanda suka tashi suka barsa, cikin taɓe baki da hura hanci tace, “Uhhm kaima dai ƙazaminne ashe”. Haka ta fara gyarawa ranta fal mita, bathroom dai koda ta shiga ta fahimci an wanke sa, amma hakan bai hanata sake wankewa ba. Tana saka freshener ya shigo, ido suka haɗa tai saurin ɗauke kanta. Shima baice komai ba ya nufi wadrob ɗinsa, ficewa tai dan Alhmdllhi ta gama. Hankalinta kwance ta koma sashinta, da tunanin sun rabu kenan tunda ta masa aikin sai yabi wani sarkin kuma. Ta tattare kayan da yaci abinci ta kai kitchen, ta fito ta kashe komai na wuta ta nufi bedroom ɗinta. Duk da tanajin tsoron kwana ita ɗaya hakan yafi mata sauƙi, insha ALLAH zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zataima Mamie magana a kawo mata mai tayata aiki ko motsinta takeji taji sauƙi. Ranta fal farin cikin babu mai takura mata yau take saka kayan barci. Da sauri ta haɗe ƴar saman kayan barcin nata da bata kai ga ɗaure igiyarba tana waro idanu na mamakin ganinsa, shima janye idanunsa da suka riga suka gama kalle abinda take rufewar yay cike da basarwa. Maƙoshinsa da yay bushewar wucin gadi ya kai hannu ya shafa yana kaiwa zaune a bakin gadon..

     “Bani ruwa mara sanyi”.

Ya faɗa murya a shaƙe.

A hankali ta saki numfashin data riƙe, tamkar jiran umarnin take dama tai wuf ta fice. Jikin ƙofar ta jingina tana sauke nannuyan numfashi idonta a rufe, sai kuma ta buɗe tana ƙarema kanta kallo, a cikin zuciyarta kam kanta take bama ƙwarin gwiwa na baiga komaiba. Ta ɗan buɗe Jacket ɗin tana kallon ƙirjinta da kusan rabi ke bayyane ta sama, dan ƴar rigar cikin ƙarama ce sosai, babu bra kuma a jikinta, hakama wandon iyakarsa rabin cinyarta, sai ya zam saka iya su tamkar mutum baida maraba da zigidir. Ta samance har kusan ƙasa mai santsi da kauri. fuska ta ɗan marairaice da haɗa yatsun hanunta biyu tana jujjuyawa a saitin fuskarta dake a ƙwaɓe kamar zata saki kuka. “Wayyo ni Mamie idan ya gani ya gama dani”. Sai kuma ciki girgiza kan cikin bama kanta ƙwarin gwiwa tace, “Insha ALLAH bai gani ba. Yes bai gani ba”. Ta kara maimaitawa cikin tabbatarma kanta. Sai dai kuma zuciyarta taƙi gamsuwa.........✍


   🤭Idan ma ya gani ba sadakinsa bane, kujimin ƴar iya😝🚶🏻.

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_52_*..........Sake maido da ita yayi da riƙo fuskarta cikin hanunsa da ɗage gira sama. “Faɗi abinda ke ranki mana yarinya. Koba angon bane?”.

      “Kaima kasan bashi ɗin bane ba, dan auren wata uku ne, kamar yau ne zai ƙare”.

   “Oh really?”.

Cike da confidence ta bashi amsa. “Ka rubuta ka ajiye”.

        Wani ƙayataccen murmushi daya nema sumar da ita ya saki, yaja hancinta da kashe mata ido ɗaya har sannan murmushin bai bar fuskarsa ba. “Kin tabbatar zaki iya?”.

     Da ƙyar ta iya jawo yawu mai kauri ta jiƙa bushashshen maƙoshinta tana ƙyaƙyƙyafta ido. “Babu tantama a alwashina Yaya MM”.

          Juyata yay suka koma tsakkiyar gadon, ta koma ƙasa shi kuma ya dawo samanta. ƙara ta saki da ƙoƙarin son turesa sai dai ko gezau, ta fara jan numfashi da fesarwa da ƙyar dan gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa dan mugunta. Ɗan ɗagata yay sai dai ba duka ba, ya kalla cikin tsakkiyar idanunta da har sun canja launin farinsu zuwa ja harda tara ƴan ƙwalla. Murmushi ya kuma saki da shafa lips ɗinta kaɗan da yatsun hanunsa. Ya ɗan kashe mata ido ɗaya da kai bakinsa saitin kunenta ya fara magana kamar mai raɗan. “Wannan bakin naki ne zai kaiki ya baroki yarinya. Idan kikace zaki buga game ɗin nan dani zubar hawaye bata shirya barin idaniyarkiba kenan....”

    Janye fuskarta tayi saboda wani zirrr da takeji a cikin jikinta. Cike da tsiwa da son hana ganin lagonta ta sake maido fuskar “Never for ever, ka rubuta ka ajiye Yaya nanda wata uku zamu koma gaban Baba Ibrahim da kai ka bani sakina, dan ni da kai bazamu taɓa son juna ba, kaima kasan da haka ai”. Itama ta ƙare maganar da salon kashe masa idanu daya nema ɗauke masa numfashi.

     Jin zata zille yay azamar tareta da hannunsa, gaba ɗaya annurin fuskarsa ya gushe, cikin ɗan kausasa harshe da zuba mata idanunsa da launinsu ya canja tsakkiyar nata ya fara magana. “Kuma dole ki zauna da ni yarinya, zan kuma tabbatar miki da hakan ki rubuta ki ajiye”.

            Alwashin nasa ya matuƙar tsaya mata a rai, amma sai ta basar cike da rainin wayo ta saki siririyar dariyar data saka tsigar jikinsa tashi. “Yaya MM kana wasa da wannan Anaam ɗin, amma dai muje zuwa, hausawa kance ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, nanda cikar wata uku zan tuna maka wannan”. 

      “Ni kuma kafin cikar wata ukun zan maimaita miki”. Ya faɗa yana janye jikinsa a nata ya sauka a gadon baki ɗaya. Harara ta dallama bayansa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, harda sakin ɓoyayyar ajiyar zuciya. Ita kanta ta yabama kanta da kanta, dan tasan ba ƙaramin dauriya taiba na riƙe tsoronta. Sai da taga ya fice a ɗakin gaba ɗaya ta dafe ƙirji da rumtse ido. Sai kuma ta buɗe da ɗan mangarin kanta. “Stupid girl! Anaam kina da hankali kuwa?. Wayyo ni ALLAH miya kaini yin waɗan nan cika bakin yanzu idan yaƙi sakin fa?” (Sai ki kaisa kotu) zuciyarya ta bata amsa kai tsaye. (Ya zakiyi da su Abie kuma?) wani gefen ya tambayeta. “Shike nan na mutu” ta faɗa a fili tana sake dafe kanta. Ganin zata zarar da kanta sai ta miƙe cikin murguɗa baki da faɗin, “Koma miye bazan yarda yaci galaba a kaina ba. Kafinma wata uku nayi gaba abina”.


    🤣To bara muga yaya wasan zai kaya ƴar mitsila😝.


        ★★★


   Duk yanda taso danne zuciyarta yau ta musu breakfast kasawa tai, koda maman Abu kuma tace zatayi saita hanata. Kallo ɗaya zakai mata ka fahimci taci kuka sosai dan idanunta har sun nuna. Tun tana kallon agogo da tsumayen shigowar Shareff harta daina zuciyarta na cigaba da mata zafi da raɗaɗi. Da alama ya fita ko sallama bai mataba kenan dan yanzu dai lokacin zuwa office ya gota matuƙa, ta kuma tabbatar bazai zauna har zuwa yanzun bai fitaba dan bai haɗa aikinsa da komai ba. Zuwa yanzu ta yarda kuka rahama ne, dan jiya tayi kuma taji sauƙi da sassaucin zuciyarta. Amma yanzu ya gagara fita ko kaɗanne balle taji sauƙi. Wani irin tsanarsa da haushinsa takeji mara misaltuwa, zuciyarta kuma ta kasa tsayawa waje guda da tunanin abu biyu. Shin maganin su Aunty Malika ne baiyi aiki a kansa ba? Kokuwa dai asirin dasu Gwaggo suka jima suna faɗa iyayen yarinyar nan nayine yafi nasu ƙarfi. Kanta ya kulle, ta rasa ina zata kama. Zafafan hawayen da taketa son fitarsu suka sami damar silalowa saman kumatunta masu matuƙar zafi, daga haka kuka mai cin rai ya kufce mata har ya shigo bata sani ba.. Ƙamshin turarensa dake ƙara yawaita a ɗakin da hancintane ya sakata ɗagowa kaɗan ta dubi ƙofar. Tsaye yake cikin ƙananun kaya masu taushi da sukai matuƙar fidda ƙuruciyarsa ta matashin namiji alamar yau bai fita ko'ina ba kamar yanda tai hasashe. Wani irin damm zuciyarta ta bada sauti a cikin ƙirjinta, abinda zai hana Shareff fita office kam lallai ba ƙarami bane, hawaye ne suka sake ziraro mata, ta sake ɗago ido ta kallesa har yanzu yana a ƙofar tsaye hannayensa duka a cikin aljihun wandonsa idanunsa a kanta tamkar ya samu television. Sakkowa tai a gadon da gudu taje ta rungumesa. Murmushi ya saki mai faɗi, tare da zare hannayensa daga cikin aljihu shima ya rungumeta. Ta saki ajiyar zuciya da sake kanƙamesa. Kusan mintuna uku suna a haka tsaye kafin ya ɗagota, fuskarta ya rike a tafukan hannayensa yana raba idanu akan hawayenta, ya girgiza mata kansa yana binta da wani kallon ƙasa-ƙasa. 

      “Kukan bai isaba?”.

   Ya faɗa idanunsa cikin nata. 

Kasa jure kallon nasa tai dan tamkar yana zuba mata wasu maganaɗisune masu wahalar ja'inja. Tai ƙoƙarin maida idanun nata ƙasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora lips nashi kan nata. A tare suka lumshe ido. light kiss ya sakar mata. Taja numfashi da ƙyar da ajiyar zuciya mai ƙarfi. 

      Murmushi ya saki da kai goshinsa saman nata ya haɗe, “Kin huce ko?”. 

Baki ta tura masa zata kautar da kan nata ya hana hakan. Dole ta haƙura ta tsaya tanata sauke ajiyar zuciya a jere. Sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya saketa suka koma bakin gado. tissue ya miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta. 

    “Kin tashi lafiya?”.

“Alhmdllh”.

Ta faɗa a taƙaice. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar wasu baƙin juna. Taso ta danne komai kamar yanda taga ya basar, sai dai bazata iyaba. Ta ɗan dubesa muryarta na rawa. “Yau bazakaje office ba ne?”.

      Bai iya ɓoye magana ba ko kwana-kwana, dan haka kai tsaye ya bata amsa da “Haba dai Madam, ango a office ai a koro ni. Ko ke ɗin nan ai baƙya so ganina a can ba ko. Ina hutu ne sai monday insha ALLAH”.

           Ido ta tsura masa ko ƙyaftawa babu, “Sati ɗaya fa kenan?”.

    “Kinga sun ragemin mudu ba kamar lokacin naki amarcinba ko? Nima dai inajin kamar zanyi bore na ƙara wani satin akan wannan na more angwancina da kyau, amma bani shawara kar ace na cika son bati”.

         Da yasan yanda zancensa ke ƙona zuciyarta da bai cigaba da yinsa ba. Ta janye idanunta dake cikowa da ƙwalla a kansa tana jan numfashi da haɗiye abinda ya tokare maƙoshinta da ƙyar. 

      “Babie kinyi shiru?”.

Kanta ta girgiza masa hawaye na sakkowa a kumatunta. Ta miƙe batare data bari ya gani ba, toilet ta nufa tana faɗin, “Wannan ai maganar amarya ce ba tawaba ita ya kamata ka samu kaga ko wata guda saiku je a ƙara muku”.

     Ƙofar toilet ɗin data bugo da ɗan ƙarfi ya tsurama ido, zuciyarsa na jujjuya maganar tata da son bata fassara. Ganin zai takura kansa akan son fahinta sai kawai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe bakinsa. Shiru-shiru taƙi fitowa har kusan mintuna biyar, ya kalla agogon dake ɗaure a hanunsa tare da kai dubansa ga ƙofar toilet ɗin da mamaki. “Wai nikam mi kike a toilet ɗin nan haka kizo ki bamu breakfast”.

     Shiru babu alamar zata amsa masa balle fitowar tata. Ya sake maimaita maganar sai dai anan ɗin ma babu alamar motsinta. Miƙewa yay zuwa ga ƙofar cikin ɗan tunzura ya bubbuga. “Wai kina jina inata magana kikai min banza?”.

         Nan ma yitai kamar zata sharesa sai kuma ta buɗe, ganinta ɗaure da toilet ya sashi faɗin, “Wai dan walaƙanci dama wanka kika shiga kika barni anan?”.

     “Toni ai ban san zaka tsaya jirana bane kayi haƙuri”.

Ta faɗa cikin son yanƙwala shi tana nufar mirror. Da kallo ya bita kawai. Sai kuma ta ɗan juyo ta kallesa. “Kana buƙatar wani abu ne?”.

     Bai tanka mata ba, bai kuma janye idanunsa akanta ba, sai dai haka kawai zuciyarsa ta sosu da yanda take masan. Idanunsa ya ɗauke kawai da nufar ƙofa ya fice abinsa... Ta raka bayansa da harara cikin taɓe baki. 


        Shawarar fita neman abinci ya yanke a ransa, sai dai kuma wata zuciya ta ƙwaɓesa dayin hakan dan ba mutuncinsa bane yana da mata har biyu ace yana fita yawon gidajen abinci siyowa. Sai dai kuma ko yunwa zata hakalashi yayi alƙawarin a yanzu dai bazaici abincin na Fadwa ba. Sashensa ya koma, ya zube a kujera hanunsa dafe da kansa. Kusan mintuna uku ya samu zaune shiru, sai da ya tabbatar zuciyarsa ta ɗan nutsu sannan ya ɗauka waya yay kiran Anaam.

      Kammala wankin toilet ɗinta kenan kiran nasa ya shigo mata. Batai saving number ɗin ba duk da ranar ya kirata da ita. Tai ɗan jimm kafin ta ɗaga da tunanin wanene. Shiru babu wanda keda alamar magana a tsakanin ita da shi. Ganin haka a ɗan harzuƙe tace, “Nikam idan mai kiran nan baida abinyi ni ina da”.

       Guntun murmushi yayi. Har cikin rai yake jinjina tsiwar yarinyar nan, ita kowa bata jin shakka na waya ma da batasan ko wanene ba bazata raga masa ba. Ya ɗan girgiza kansa da furzar da numfashi. “Ki samo min tea da wani abu ki kawo min”. 

   Kafin ta samu damar tofa tata ya yanke wayar. Tai takwa-takwa na takaici sai kuma ta tsuke baki da buge wayar.........✍

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_51_*
.........Kwance ta kai tana faman tuttura lips gaba, a zuciyarya kam babu abinda take sai masifa, sai dai babu damar yi a fili. Tashi tai zaune zaram kamar wadda aka tsikara tana kallonsa, ganin ya koma ya zauna gaban laptop ɗinsa.

     “Yaya MM?”.

Shiru ya mata yaƙi ya amsawa, amma tsabar bazata iya haƙuri ba saita cigaba da maganarta kamar sharetan da yay bai zafeta ba.

           “Amma dai can ɗakin zaka koma ka kwana kamar ranar idan ka kammala aikin ko?”.

      Banza yay mata nanma, takaicinta ya bayyana har tana jin tuƙuƙimsa a maƙoshi, harara ta dallama bayansa, cikin jin zafi ta fara ɗaukar pillows ɗin gadon ɗaya bayan ɗaya ta jera a tsakkiyar gadon tun daga farko har ƙarshe tana muy-muy da baki alamar magana take. Ƙarshen gadon ta koma da salon kwanciyar kai da ƙafa ta kwanta badan zuciyarta ta bata nutsuwar haƙurin sake kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya da shi ba. Dan tayi alƙawarin kafin cikar wata ukunnan bazata taɓa bari ya samu nasara a kanta ba.

    Duk abinda take yana jin motse-motsenta sai dai bai juyi ba, aikinsa kawai yake badan yana fahimtar wasu abubuwan ba. Bayan shuɗewar kusan mintuna arba'in da biyar yaji shiru ta daina sukur-sukur da motse-motsen da takeyi, kaɗan ya juyo ya kalleta, a can ƙarshen gado take ƙudindine da bargo ta juya masa baya. Ya maida kallonsa akan pillows ɗin data jera, kansa ya girgiza kaɗan wani ɗan guntun murmushi na suɓuce masa. Hankalimsa ya maida ga aikinsa, wanda ya sake jansa kusan awa guda, ganin two ta kusa ya ga hamma yanata jerawa ya sashi tattara komai ya ajiye. Alwala yayo, ya shimfiɗa abin salla, sallar nafila ya gabatar raka'a biyu, yay addu'oi dan barci sai faman rinjayar idonsa yakeyi. Bai cire shingen datai musu ba yay kwanciyarsa bayan yayi addu'oi. Babu jimawa barci yay awan gaba da shi shima.

     Duk da ta rigashi kwanciya shine ya rigata farkawa, ya yunƙura da ƙyar ya tashi bayan karanta addu'ar barci, shanyayyun idanunsa da har yanzu barci ke cike a cikinsu ya zuba mata ta ɗan hasken lamp dake a ɗakin kaɗai. Yanzu kam ta juyo fuskarta, sai dai tana a inda take kwance tun jiya. Sai da yayo alwala sannan ya tasheta, a ranta ALLAH-ALLAH take ya fice ta sama ƙofarta key, sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fice zuwa sashen Fadwa itama ya tashesu. Koda ta fito kai tsaye ƙofar ta nufa, amma wayam babu keys ɗin alamar ya zare. Ta dallama ƙofar harara da murguɗa baki.

       Sai da gari ya ɗanyi sha ya shigo, har sannan tana zaune tana azkar. Batare da ta yarda ta kallesa ba tace masa ina kwana. A taƙaice ya amsa yana kaiwa kwance dan barci ne fal idanunsa. Jin ya fara sauke numfashi ta ɗan juya ta kallesa, ya juya mata baya, amma ta fahimci barci ne ya ɗauke sa. Itama dai ƙarasa azkar ɗin tai ta koma ta kwanta tunda ba wani aikine da ita ba.....


       ★★★★


  Tsabar yanda ta kwana da abubuwa masu yawan gaske a ranta tana idar da salla sashen Gwaggo ta nufa. Burinta kafin su Daddy daga massallaci su shigo ta shige, dan ita yanzu ko ɗakinsa bata zuwa, shi kuma yaƙi ce mata komai akan hakan. Gwaggo na zaune tana lazimi Mommy ta shigo, kallonta kawai take baki a sage, sai dai kuma batai mamaki ba musamman akan sanin halin rashin haƙuri irin nata. Mommy ta gaisheta kamar yanda ta saba, damuwa ƙarara akan fuskarta.

        “Wai Nafisa kuwa anya hankalinki na jikinki? Wace irin rayuwace wannan duk kin firgita kanki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Da alama yau ko barcin kirki ma bakiyi ba ko?”.

    “Humm Gwaggo ina naga ta barci nikam, kema kin san babu wani barci dazan iya a wannan halin. Ki duba fa kiga Shareff ya ɗauke ƙafa gaba ɗaya a gidan nan tamkar ya manta dani a raye, ko'a waya baya kirana tumma yanzu kenan za'a rabani da yarona. Maheer ma yaƙi zuwa duk da shi nasa bai cika damuna ba nasan fushin banza da wofi ya sakama ransa bayan ni gata naima rayuwarsa. Gwaggo taya zanyi barci a wannan yanayin to? Na kasa gane kan Shareff sam. Son yarinyar nan yake da yake gudun haɗuwarmu ko yaya ne?”.

        Ƴar dariya Gwaggo tai. “Banda abin Nafisa halin namiji kuma kika manta! Shi yanzu Mustapha a wannan gaɓar bake kaɗai ba kowama zai iya rasa gane kansa ai.....”

    “Gwaggo to saboda mi? Ni wlhy kaina duk ya kulle”.

       “Uhhm haka dai, tunda kin ruɗa kanki ba dole kanki ya kulle ba. Kina tunanin duk ƙin da yakema yarinyar zai kawo ido ya saka mata ne a gidansa”.

    Kaɗan ya rage Mommy ta haɗiye harshenta. Cikin in ina da shiga ruɗani take magana. “Gwaggo wai kina nufin ya kwanta da yarinyar nan?”.

          “Har kuwa ki ganta da ciki nan da watanni kaɗan”.

“Aiki dana tsine masa”.

    “Ki tsine masa! Kinga Usman da Ai'sha sunci riba a kammu kenan. Ki kiyayi harshenki da ambaton tsinuwa ya ƴaƴanki saboda kawai ranki ya ɓaci. Ki koyi nutsuwa a duk lokacin da kikaci karo da abinda bai miki ba. Nafisa idan kikai sakaci k da kanki zaki tabbatar da nasarar maƙiyanki akan ƴaƴanki. Yanzu dakin kwantar da hankalinki tun bayan da akai rikicin farko akan auren nan da yanzu mun kai ga mafita. Mustapha da kike gani hatsabibin yaro ne mai shegen zurfin cikin tsiya da wayo. Gaggawa a al'amarinsa ba shi bane mafita, kuma tsananinki ba shi bane zaisa muci nasarar rabashi da yarinyar cikin sauƙi, musamman da matarsa dama ta kasance shashasha, dan nikam sai yanzu nake dana sanin yin wannan haɗin nasu”.

       Da mamaki Mommy tace, “Wani abun ya faru ne Gwaggo?”.

    “Nafisa ai shiyyasa nace ke ɗin ruɗaɗɗiyar mutum ce, yo banda haka halin Fadwa har wani ɓoyayye ne da zaki kasa ganewa. Duk wani baƙin halin Halima shine tare da ƴarta, kodan shi Mustaphan bamai yawan magana bane da kullum zai zauna faɗa miki matsalarta shiyyasa kike kasa fahimtar halinta?”

           “Gwaggo bawai ban fahimci wasu abubuwa bane, dan ni kaina yawan kirana da takeyi kullum tana kawomin ƙararsa ya mata kaza ya mata kaza yana cimun rai, sannan Aysha ta faɗa min ko abinci sai ta gadama takeyi a gidan sai dai mai-aiki, Shareff da ko'a gidan nan baicin abincin masu aiki”.

      “Humm zatayi abinda yafi haka ni na sani. Amma karki damu zamu fara gyara mata zama. Yanzu abinda nake so da ke ki sassautama zuciyarki komai, ki nunama su Muhammadu komai ya wuce kin ajiye makamanki, shima ɗin Mustapha ki kirashi a waya ya sameki ki nuna masa komai ya wuce. Mu kuma daga nan zamu fara namu yaƙin, badai wata uku shi Ibrahim ya bata ba, to duk yanda zamuyi sai munyi nanda wata ukun tabar gidan, babban fata na dai ace bai taɓata ba. Kai koda ya taɓatan ma ba komai”.

     “Gara dai karya taɓatan Gwaggo, danni bana fatan haɗa kowace sabga da Usman balle shegiyar matarsa”.

    Ƴar dariya kawai Gwaggo tayi da faɗin, “To ALLAH yasa haka. Yanzu dai inaga kima Sakina magana yau taje mana gidan taga yaya zaman nasu yake”. 

      “Wannan shawaran yayi gwaggo, bara na sanar mata yanzun nan kuwa”.

     Daga haka suka cigaba da tattaunawa kuma har gari yay haske sannan Mommy ta koma sashenta zuciyarta na ɗan sassauta nauyin da tai kwana biyu. Masu aikinta ta bama umarnin haɗa abincin Daddy. Duk da sun ɗanji mamaki babu wanda yace komai tunda ba huruminsu bane, itako ta shige domin shiryawa tunda dama girkin tane.....


        ★★


    Kusan ƙarfe takwas ta farka. Ganin har yanzu shi barcinsa yake hankali kwance sai ta koma ɗayan ɗakin tai wanka ta shirya a can. Ganin har lokacin baida alamar tashi saita nufi falo ta gyara duk da ba wani datti bane ba. Yunwa takeji matuƙa, dan haka ta haɗa tea ta dawo falon tai zaman sha tana buga game a waya. Koda ta kammala a falon ta cigaba da zama tana game ɗin har kusan ƙarfe tara. 

     “Wai mutumin nan bazai tashi bane? Koya manta yau monday akwai office?”.

   Ta faɗa tana kallon agogon dake falon, miƙewa tai kanta tsaye ta nufi bedroom ɗin. Mamaki ya ƙara kamata ganin har yanzu dai a kwance yake, (Lallai babu lafiya) ta ayyana a ranta tana ƙarasawa gaban gadon, dan ita dai a sanin datai masa na rashin wasa da aiki inda ƙalau yake babu yanda za'ai yakai yanzun yana barci. Fuskarsa ta ɗan tsurama ido dan kwance yake a rigingine. Lumshe idanu tai da sake buɗewa a kansa, ita shaida ce Shareff ƙyaƙyƙyawa ne, ƙyawu irin na masu kwarjini da cikar haiba bawai na fitar hankali ba. ALLAH ya bashi dukkan kamala ta cikakken mutum tamkar wani babba. Baida yawan hayaniya, sannan bai da yawan fara'a. Mutane da yawa kance mata yanada sauƙin kai da daɗin zama, sai dai ita har yanzu bata ganinsu tattare da shi, dan zata iya bugar ƙirji tace babu wadda yatsana a rayuwarsa ƙila sama da ita, ta rasa minene laifinta a gareshi. Ta taɓe baki da juya idonta, a fili ta furta “Yo karya soni ɗin nima ai ba son sa nake ba humhh”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki ta juya zata bar wajen a bazata taji an riƙota. A firgice ta juyo dan ta tsorata, sosai idanunta suka firfito waje dan batai zato ko tsammanin shi ɗin bane tunda taga barci yake. Idanunsa ya ɗan rufe ya sake buɗewa a kanta tare da fisgota ta faɗo kansa.....

      “Wayyo Yaya zaka karyani ne?”.

Komai baice mata ba, sai dai kafeta da idanunsa dake a yanayin wanda ya tashi barci. Ƙoƙarin son zame jikinta take a nasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora hanunsa a bayanta ya tallafeta da ƙyar a saman jikinsa, fuskarta dake a gab da tashi ta kautar gefe saboda yanda yake kallonta tsigar jikinta har tashi take. Ɗayan hanunsa yasa ya maido fuskar tata a saitin tasa har yana jin saukar numfashinta. 

       “Kina yin miye tsaye a kaina?”.

   Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta tura baki da ƙara ƙoƙarin janye fuskarta dan bazata iya jurar kallonsa ba. “Ni to mizanyi? Kawai nazo tadaka ne dan naga lokacin office yana wucewa”.

      Agogon dake ɗakin ya ɗan kalla tare da maido idanunsa a kanta lokaci guda. “Dama ango na zuwa office ne?”.

    Sosai ta yatsine fuska tamkar wadda aka faɗama wani mugun abu. sai kuma ta taɓe baki da sake yunƙurin barin jikin nasa........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_55_*
............“To na gode da gaisuwa”. Ya faɗa da miƙewa zai bar wajen. Riƙosa Shareff yay ya maida ya zaunar. 

    “Wai haushi kaji?”. 

  “Mizaisa naji haushi?”.

Murmushi Shareff yayi da cike lips. Sai kuma yace, “Manta kawai”.

   “Ka gwammace ka cigaba da riƙe damuwarka kenan. Look Musty! Idan kasan zaka iya shanyewa miyasa zakazo min nan to?. ALLAH kana bani matuƙar mamaki. A yanda muka riƙeka sam kai ba haka baneba, ban saniba ko baka yarda damu bane har yanzu oho. Well koma dai minene matsalarkace, mudai har gobe da jibi bazamu daina kallonka matsayi mai girmaba insha ALLAH....”

      “Humm Jamal”.

“Miye wani Humm Jamal. Na jima da fahimtarka ai Shareff kai har yanzu matsayin abokai gama gari muke a wajenka. Mune dai kawai ke ɗaukarka da muhimmanci dan bamu san ciwon kammu ba”.

     “Ya ALLAH ni kamun gurguwar fahimta ne kawai. Yanzu dai ajiye wannan harzuƙar taka gefe muyi magana.”

    Harararsa Dr Jamal yayi ya ɗauke kai. Shareff ya sake yin murmushi kawai.

       “Idan ka gama nuƙu-nuƙun to ina jinka”.

   Kafaɗa Shareff ya ɗan ɗage da taɓe baki, “Bafa wani abu bane babba. Akan auren nan ne dai kawai. Jamal na rasa ina zan ajiye zuciyata naji sauƙi. Mommy bori, Fadwa bori, itama kanta Juwairiyya bori. Duk sun kasa fahimtar komai da suke a kaina yake komawa bawai junansu ba. Jamal ALLAH jinina bana tantama a yanzu haka ya hau sama ƙololuwa”.

     Sosai tausayinsa ya bayyana saman fuskar Jamal, ya furzar da iska shima. Tabbas yaso Anaam, har yanzuma sonta baije ko'ina ba a zuciyarsa. Amma hakan baya nufin baza iya yin sadaukarwa ba. Shareff ya fishi dacewa da ita, sannan ya ɗarashi buƙatar zama da ita saboda wasu hujjoji daya riƙe. Yaɗan kallesa yana jinjina kai. “Tabbas matsalace wannan babba. Musamman ma ta Mommy dan na Fadwa da Anaam duk mai sauƙi ne a ƙarƙashin ikonka suke zaka iya ladabtar da su dole kuma su nutsu.”

     “Dama nasun bawai ya cika damuna bane, kawai dai bana son a yanda suken suma. Amma Mommy da Daddy humm, na rasa ina zan kama Jamal. Ko gidan na kasa zuwa gaishesu kwana uku kenan”.

          “Damuwa dole ce kam, domin Daddy Mommy duk sunada iko da muhimmancin bijirewaka kuskurene, babbar matsalar kuma a ra'ayin da suke mabanbanta, inda ace ra'ayinsu ɗaya ne nakane ya bambanta zaka iya sadaukar da naka ka faranta musu ta hanyar bin nasu. To amma yanzu gaskiya al'amarin akwai ruɗani, inba dai ɗaukar Anaam zakai kubar ƙasar nan ba kawai. Nan da wani gajeren lokaci sai ku dawo sannan Mommy ta huce”.

      “Ita kuma Fadwa fa? Sannan aikina fa? Ita kanta service takeyi miye makomarsa?”.

     Nannauyar iska Dr Jamal ya furzar da faɗin, “Ya ALLAH! ALLAH!”.

Shiru kowansu ya kasa cewa komai, tsahon wasu sakkani Dr Jamal ya katse shirun. “To ko Anaam ɗin zaka ɗauke zuwa wani ɓoyayyen guri a garin nan, inaga hakan zaisa Mommy ta ɗan sauka kafin asan mafita. Danni dai banga ta inda maslaha zata samu ba a yanzu tunda buƙatar Mommy kawai shine ka saki Anaam. Sai dai kuma idan sakin nata zakai.....”

      “Baka da hankali”.

Ya faɗa cikin tare numfashin Dr Jamal. Murmushi Dr Jamal yayi da haɗe hannayensa alamar ban haƙuri. “Understand me, nima nasan hakan abune mai wahala da bazaka iyaba, sannan bama zan so hakan ba. Amma kaje dai kayi tunani nima zan ƙara ko zamu sami wata mafitar datasha banban da waɗan nan na yanzu”.

     Kansa ya ɗan jinjina alamar gamsuwa da hakan, a dai-dai nan kiran Gwaggo ya shigo masa. Yay ɗan jimm kafin ya ɗaga wayar yakai kunnensa da sallama. Daga can ta amsa masa tamkar ba ita ba. Gaisheta yayi, nan ɗin ma ta amsa masa murya a sake. “Kana jina ko Mustapha! Ka kwantar da hankalinka nayi magana da ita. Sai dai wannan wasar ɓuyan da kake damu ba shine mafitaba a gareka inhar kana neman albarka. Ya rage naka kai tunani irin wanda ya dace, na barka lafiya”.

     Wayar ya sauke daga kunnensa, ya girgiza kansa da furzar da huci mai faɗi. “Jamal bara naje kawai”. Ya faɗa yana miƙewa da zura wayar a aljihu. 

    “Wata matsalar ce kuma?”.

Kansa ya girgiza masa. “Wadda ake cikin ce dai. Gwaggo ce”.

   “Gwaggo kuma?”.

“Uhmm! Kasan dai bazataƙi goyon bayan ɗiyarta ba ai.

   Ya gane Mommy yake nufi dan haka baice komaiba. Har inda ya ajiye motarsa ya rakosa, ya buɗe ya shiga sannan ya bashi hannu sukai musabaha. Sai da ya fice Dr Jamal ya iya sauke ajiyar zuciya, tausayinsa yakeji har tsakkiyar zuciyarsa. Al-Mustapha mutum ne mai kyawun zuciya ga kowa dazai zauna da shi. Bashi da matsala komai nasa a nutse yake kuma a tsare, yanada halin manyan mutane, dan a lokuta da dama idan yay abu saika ɗauka tunanin wani babban mutum ne mai shekaru saba'in....


       Maimakon ya nufi gida sai kawai ya zarce wajen aikin da companynsu keyi. A can ya samu Khaleel. Ya danne dukkan damuwarsa da haɗiyesa yana mai kallon ƙanin nasa jarumi da halinsu ke kamanceceniya tamkar uwa ɗaya ta haifesu. Murmushi yay da miƙama Khaleel ɗin dake gaishesa hannu alamar yafi son suyi musabaha. Hannu Khaleel ya bashi suka gaisa, ya mika masa irin hular dake a kan duk wanda ke'a wajen. Babu musu ya amsa ya saka, daga haka suka fara zagaya ginin da ayanzu ya fara bayyana kansa gamai kallo. Tabbas aka kammala estate ɗin ba ƙaramin ƙyau da ɗaukar hankali zaiyi ba. Duk inda suka gitta ma'aikata gaishesa suke da girmamawa shiko yana amsa musu da kulawa. Inda yaga gyara yay magana, inda ya kamata ya yaba ya yaba musu. Hakan sai ya ɗauke kaso mafi yawa na damuwar da yake a ciki har lokacin sallar azhar yayi suka nufi massallaci. Koda aka idar da salla wani gidan cin abinci suka nufa anan kusa da ƙafa. A lokacinne kiran Fadwa ya shigo wayarsa. Ɗagawa yay yakai kunne sai dai baiyi magana ba. 

    Muryarta a raunane cikin kuma ɗari-ɗari tai masa sallama. Amsa mata yay kadaran kadahan, sai duk ta daburce, amma cikin dauriya da in ina tace, “Am sorry dan ALLAH. Wlhy babu ruwana sai da nace karsu je. Ganin bazasuji maganata ba yasa na bisu da tunanin ko kana can.”

      “Is ok”.

Ya faɗa a taƙaice. Ita tasan is not ok a cikin muryarsa. Amma sanin baya son nacin magana saita saki waccan ɗin kamar yanda ya buƙata. “To ga abinci na kammala amma naga baka dawo gida ba har yanzun”.

    “Karki damu gashi zanci a inda nake”.

   Zatai magana ya dakatar da ita da faɗin, “Zanci na dare idan na dawo bye” Ya yanke batare da ya jira amsarta ba. Kiran nata ya ɗan sakama masa jin sassauci, dan garama ita, Anaam ko zai cika duniya da fushi ai bata taɓa nuna masa ta damuba a kwanakin datai gidan nasa duk da yasan sarai tana sane da komai na halin da yake a ciki dangane da aurenta. Yaja siririn tsaki a ƙasan zuciyarsa yana ayyana (Zanyi maganinki vary soon).

      Khaleel da tun shigowarsu yana wajen siya musu abinci ya dawo tare da waiter dake biye da shi. kujera yaja ya zauna. “Am sorry babban Yaya na daɗe”.

     “Don't worry”.

Ya faɗa a taƙaice hankalinsa akan wayarsa. Sai da suka fara cin abincin a nutse Khaleel ya ƙara maida hankalinsa garesa. “Yaya nikam kuna waya da Yaya Maheer?”. Idanu ya ɗago ya zubama Khaleel ɗin, kafin kuma ya girgiza kansa alamar a'a. Khaleel yaja numfashi ya fesar. Ruwa ya ɗauka ya ɗan sha ya ajiye. “Naje gidansa jiya da yamma. Saboda su Abbah suna maganar ya daina zuwa gida gaba ɗaya sannan wayoyinsa duk a rufe. Yaya banji daɗin yanda na samesa ba shida matarsa. Gaba ɗaya Yaya Maheer ya canja tamkar bashi ba. Sam babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninsa da matarsa abin ya tsoratani wlhy”.

      Kasa magana yay ya kuma kasa cigaba da cin abinci har Khaleel yakai aya, sai dai idanunsa gaba ɗaya launinsu ya sake canjawa. “Mike faruwa?”.

     “Yaya komai ma na faruwa, a yanzu haka so take tabar gidan amma mahaifiyarta ta tabbatar mata zata tsine mata inhar ta bari Yaya Maheer ya saketa. Shi kuma yaƙi bata kowacce irin dama wlhy bakaga yanda yake treating nata ba like dai wadda suke rayuwa a.... Mtsoww oh my god babu dai daɗin faɗa kawai. Na fara masa nasiha amma yaƙi saurarena, daga ƙarshe ma a gabana ya mareta wai tana haɗashi da ƴan uwansa, so abin is to much wlhy”.

      Numfashi ya sauke zazzafa ransa duk a jagule. Still dai ya kasa cewa komai kallon Khaleel ɗin kawai yakeyi. A ƙasan zuciyarsa kam yana jin rauni matuƙa. Ya rasa miyyasa Mommy ta kasa fahimtar rayuwa irin ta yanzu ta aure tasha banban data zamanin baya, a da daga maza har mata kowa nada kawaicin iya karɓar aure a duk yanda yazo masa. Amma a yanzu ba haka baneba, auren soyayyar ma yaya aka ƙare balle na tilastawa. Shi kansa dabai jureba za'a samu irin wannan matsalar ne a lokacin data tilastashi auren Fadwa. Amma daya jure yayta gayama ALLAH da tilastama kansa tanada mahimmancin amsar ko minene daga umarninta sai gashi ALLAH ya saka masa son Fadwa ɗin. Sai dai Mommy ta kasa fahimtar shida Maheer za'a iya samun banbancin juriya akan wannan al'amarin. A ganinsa data barshi ya aura wadda yake so da an samu maslaha. Dan gashi abinda takema gudun bai tsallaketa ba tunda ga Anaam dai matsayin matar gudan jinin nata bisa ƙaddarar UBANGIJI da babu wani hannu daya isa gogewata....

     Numfashi ya sauke a hankali saboda taɓasan da Khaleel yayi. Abincin suka cigaba da ci batare da wani ya sake magana ba, sai dai Shareff tsakura kawai yakeyi. Baimaci na kirki ba ya ture gefe. Haka Khaleel ya biya kuɗin suka sake komawa wajen masu aikin. Har yamma yana a wajen, bai tafi ba sai da masu aikin suka tashi. Sai da ya sai kayan fruits ya bama Khaleel ya kai musu can gida shi kuma ya zuba na nasa gidan a mota shima ya wuce. Ana kiraye-kirayen sallar magrib ya shigo, dan haka bai nema kowaba a cikinsu ya wuce sashensa. Ruwa ya fara watsawa jikinsa na ɗumi a gaggauce, ya fito ya saka kaya nanma a gaggauce ya fice massallaci dan har an fara sallama..........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_54_*

.........Ƙara riƙo hanun yay da ƙyau idanunsa masu kaifi na saukar mata da kasalar data mantar da ita wanzuwar su aunty Sakina a falon. Dama haka yake buƙata, ta manta da wanzuwar tasu ya samu damar isar da gargaɗinsa garesu batare daya samu wani tangarda daga gareta ba.

     “Dama haka ake bama miji abu?”.

  Ya faɗi maganar a salon daya nema ɗauke numfashin Anaam na wucin gadi, dan muryar da yay mata magana da ita muryace da zata iya rantsuwa bata taɓa ji daga garesa ba. Da ƙyar ta iya ƙwato kanta, tai ƙoƙarin ajiye masa kayan a hanun kujerar da janye nata idanun daya sargafe a nasa dan ta gama yanke shawarar barin wajen kafin a samu matsala yaga rauninta. Tana daga kafa ya riƙo hanunta tare da jawota sai gata ɗaram a cinyarsa tamkar walƙiya. Kafin tunanin wani abu ya risketa har ya yimata zobe da hanunsa ta hanyar ɗorawa a saman cikinta ya manne bayanta da ƙirjinsa kansa bisa wuyanta yana shinshina da fara magana cikin kunenta da wani salon daya saka tsigar jikinta tashi.. “A haka ake bama miji abu ba'a tsaye ba”. 

      Saukar wata mulmulalliyar ashariya cikin kunnuwansu ta tilastata ƙanƙamesa babu shiri dan da gaske ta tsorata dama gata a tsakkiyar wani firgicin. Harga ALLAH ta manta da su a falon, saɓanin shi da duk abinda yakeyi domin su ɗinne dama. A firgice ta ɗaga ido zata kallesu ya hana hakan, dan kuwa hanunsa ya tura cikin rigarta sai dai akan cikinta ya tsaya.. Ɗan matsawar da yay ta sata saki ƙarar ruɗewa dan a bazata abin yazo mata kuma taji zafi......

      Rige-rigen fita aka farayi tsakanin Hajiya Luba da Aunty Sakina, saboda ƙarar Anaam ɗin fassara daban suka bata.  Aunty Sakina ma harda gwara kai a jikin garu lokacin da suke turereniyar ficewa. 

          Hanunsa da taketa faman kaima mintsini ya janye, ta mike zumbur daga cinyar tasa idanunta taf kunya. Riƙota ya sake yi fuskarsa ɗauke da murmushin ƙeta. “Malama nace na gama n....”

    Hararar data wulla masa ce ta hanashi ƙarasa faɗa ya saki dariyar data ƙara ƙular da ita tana jin zafinsa har cikin maƙoshinta. Sake fisgota yay ta dawo saman cinyar tasa. Ya haɗe hannayenta duk biyu dake son turesa ya danne akan cikinta. “Idan idanunki suka cigaba da harararta daga yau sai na miki haɗiyar ɗan sululu a gidan nan fitsararriya”. Mutsu-mutsunta ta cigaba dayi na son ƙwacewa yaƙi bata dama. Saima lanƙwansota yay ta kwano jikinsa ya kai goshinsa kan nata ya haɗe. Yawu ta fara kokawar haɗiyewa da sauri-sauri ganin yana daidaita lips ɗinsu.

     “Please Yaya dan ALLAH kar kayi bana so”.

    Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya, “Fitinanniyar yarinya minace zanyi to?”.

  Bakinta da take faman karewa da hannu tatura gaba da ƙoƙarin kauda fuskarta ya tare da hannunsa, tare da janye nata hanun ya manne lips ɗinsu. So take ta turesa, amma tasirin abinda yake matan a cikin jini yana barazanar hanata kowanne irin yunƙuri, daɗin daɗawa ya riƙe hanunta ta yanda bazata iya ko motsashi ba. A karon farko ta fara maida masa murtani a yau dan tasirin salon nasa jinin jikinta ya fara amsarsa da ƙarfin gwiwa da wani sirrin ɓoye dake can ƙasan zuciyarta da ita kanta har yanzu bata san da zamansa ba tattare da ita. Hakan tamkar ƙara zugane a garesa da dukkan haƙurinsa, dan kai tsaye zuciyarsa ta fara ingizasa ga kaiwa inda bai gama shirya kai kansa ba. Ring na wayarsa ne ya dawo dasu duniyar da suka jima da yin nisan barin cikinta da lissafi irin na masu hankali. Sakinta yay, zaram ta miƙe kamar wadda take a tsinin allura. Da sassarfa ta bar falon ko waiwayensa taƙi tayi. Da kallo ya bita yana sakin kakkauran numfashi da murmushi, a hankali yakai bayansa jikin makarin kujera ya kwantar yana mai lumshe idanunsa da sake sakin ajiyar zuciya a jajjere yana kai hanunsa ya shapo lips  ɗinsa....


     Tun fitowarsu take faman kaikawo a harabar gidan, dan ko sashen Fadwar sun gagara komawa tsabar mamaki da jinjina ƙwarewar iskancin Shareff ɗin a yau. Yaron da ko ido bai cika ɗagawa ya kalla mutane ba shine yay musu wannan baƙin iskancin. Ina bazata iya haƙuri har sai sunje gida ba, dole ne ta kira Mommy kam ai. Takai wayar kunenta tana faman kaɗa ƙafafu da jijjiga jiki na tsantsar bala'i. Cikin sa'a aka ɗaga mata gab da zata tsinke.

      “Sakina har kun isa gidanne?”.

Mommy ta faɗa tunkan aunty Sakinar tace wani abu. Aiko cikin matuƙar ɗacin murya ta tare numfashin Mommy din da faɗin, “A dole Mustapha kam yafi karfinki wlhy Yaya Nafi! Dan tabbas babu makawa an wanke an basa ya sha.”

     Ƙirjin Mommy ya buga da ƙarfi, sai dai kafin tace wani abu Aunty Sakina ta cigaba da bata labarin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Ta ƙare da faɗin, “Zama dai kam bai gammu ba dan wannan yarinyar tafi uwarta hatsabibanci. Nan gaba babu makawa zaima iya cewa kwanciyar aure zaiyi da ita a gabanki saboda ya tabbatarma duniya shi ɗin tantirine na gask......” Ƙitt!! Wayar ta yanke. Tai saurin cirota a kunenta tana kallo a tunaninta ko kuɗine suka ƙare. Ƙoƙarin siya tai ta banki ta ƙara kiran Mommy ɗin. Sai dai kuma number busy ake nuna mata alamar waya take ko kiran wani.....


       Ring ɗin wayarsa ne ya sake sashi buɗe idanunsa da har yanzu ke'a rufe. Ya kafe fuskar wayar da kallo tamkar mai tsoron ɗauka ganin sunan First Luv ruƙu-ruƙu na yawo. Rabon da suyi koda waya ne harya manta, ya kuma tabbatar gargaɗin da yayma su Aunty Sakina ya risketa ne matsayin saƙo. Bazai iya ƙin ɗaga kiranta ba koda yana jin tsoron dukkan wani furuci daga bakinta, kimarta da girmanta sun wuce a musalta a cikin idanunsa da zuciyarsa. Hannu ya kai ya ɗaga tana gab da tsinkewa, yakai kunen nasa cikin ƙarfafa kai....

     “First luv barka da safiya”.

“First ubanka ba first luv ba. Al-Mustapha wlhy ina gab da jamaka kalmar ALLAH ya i.....”

       “Please First luv, abeg kar kice haka dan girman ALLAH.”

“Idan ka sake kirana da sunannan ALLAH sai naci ubanka. Kuma kazo ina nemanka idan ba hakaba ka bari na tako ƙafata gidanka da kaina yarinyar nan na a ciki wlhy wlhy wlhy kadaiji na rantse ko! Sai na jamaka ALLAH ya isa da manyan baƙi no-no na daka sha dan bakai kaɗai na haifa ba balle ka ɗauramin hawan jini”.

       Harshensa har sarƙewa yake wajen faɗin, “Shi... Shike nan naji zanyi, zan zo, amma kimun alfarma Mommy dan ALLAH sai gob.......”

     “Alfarma ubanka, Al-Mustapha ni kake son tozartawa a idon maƙiyana dai ko? Kana nunama duniya mace ta fini daraja da kima a idonka?”. Ta faɗa tana fashe masa da kuka. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi, ya girgiza kai tamkar yana a gabanta. “Mommy wlhy babu wata mace da darajarta zata ko kama ƙafarki a wajena. Dan ALLAH ki fahimceni Mommy ina a tsaka mai wuya......”

      A fusace ta yunƙuro zatai magana Gwaggo ta fisge wayar. “Nafisa wai kin rasa hankalinki ne halan?! A tunaninki wannan butsutsun naki akan Mustapha shine mafita ta ƙarshe da zakibi wajen raba auren?!!......”

         Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da lumshe idanunsa ya saki wayar a jikinsa batare daya ƙarasa jin abinda Gwaggon ke faɗa ba. Dan kuwa tabbas a wannan gaɓar ta taimakesa taimako irin wanda bakinsa bazai iya maimaita faɗa ba, sosai al'amarin Mommy ke daɗa tayar masa da hankali, ya rasa ta inda zai kama domin shawo kanta akan wannan aure. Har yanzu yarasa gane minene takamaimai laifin su Abie a gareta da take musu irin wannan ƙiyayyar (Niko nace Shareff a haka ta tashi, tun tana ƙaramarta an riga an cusa mata ƙinsu. Haka ɗan adam yake, a duk lokacin daka koyar da shi wani abu ƙyaƙyƙyawa ko mummuna yakanzo ya fika iyawa. Iyaye tabbas muna kuskure, kuskuren da shike saka ƴan ubanci a zukatan ƴaƴanmu tsakaninsu da ƴan uwansu. A kullum baki da aiki saina aibanta kishiyarki gaban ƴaƴanki, baki da aiki sai na zaginta da nuna cutarki take zaluntarki take bata sonki, bata ƙaunarki, maƙiyarki ce kuma a gaban ƴaƴanki. Tayaya kike tunanin bazasu tsaneta su tsani ƴaƴanta fiye da yanda kike tsanarta ba, saboda ke ra'ayin ƙinta ya shigekine da girmanki da hankalinki, idan kin so zaki iya yaƙarsa, suko kin raini zukatansu ne akan wannan ƙiyayyar, dolene su dawwama da ƙinta da ƙin duk wani abinda ya shafeta koda bata aikata musu komai ba na ƙi ɗin. ALLAH ka gafarta mana ka gana damu gaskiya koda bazata mana daɗi ko zuwa dai-dai da son zukatanmu ba).

        Anan falon yabar lap-top ɗin da takardun ya fice, koda ya fito su Aunty Samira sun wuce dan baiga motarsu ba. Motar ya shiga shima ya fita a gidan, dan yana buƙatar yin nesa da su har zuciyarsa ta huce. Haka yake baya son yanke hukunci cikin fushi, ya gwammaci yin nesa da abu a duk lokacin da zuciyarsa ta harzuƙa. Asibiti ya nufa wajen Dr Jamal, sai da ya shigo cikin asibitin sannan ya kira wayarsa..

     Daga can Dr Jamal yace, “Ka shigo mana, ni kaɗaine ma a office”.

   Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yanke wayar, bai cika san buɗe cikinsa ga kowa ba. Amma dai mutane biyunnan sun wuce abokai kawai a garesa aminaine na gaskiya. Daga Dr Jamal har Fharhan abokansa ne tunna ƙuruciya, koda yabar ƙasar kuma basu yarda juna ba. Basu da abokin shawara sama da shi, duk da shi yakan jima basuji nasa cikin ba saboda yanada zurfin ciki matuƙa. Na ukunsu kuwa shine Khaleel, duk da kasancewarsa ƙani a garesa hankalin yaron da nutsuwarsa kansa ya kallesa tamkar aboki, sannan shima Khaleel ɗin bashi da wani amini sama da shi duk da yana amsa sunan yayansa ne.

      Sai da yay knocking aka bashi izinin shiga sannan ya shiga. Dr Jamal na zaune a kujerarsa ya amsa masa sallamar da yay fuskarsa da murmushi. Cikin danne kishin rashin Anaam yace, “Ango kasha ƙamshi”. Harararsa ya ɗanyi ya ɗauke kai, ya zube cikin kukerar dake gaban desk ɗin Dr Jamal ɗin yana furzar da iska mai nauyi. Dr Jamal dake binsa da kallo danya fahimci damuwa a fuskar abokin nasa ya miƙa masa hannu sukai musabaha.

     “Wai yana ganka haka kamar mara lafiya? Ko jikinne har yanzun?”. 

Kai ya girgiza masa, sai dai baice komai ba. Dr Jamal ya tsura masa ido na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe ya ɗakko masa ruwa. Baiyi musu ba ya amsa, murfin ya ɓalle ya kai bakinsa. Tass ya shanyesa yana dire robar da lumshe idanu ya sake lafewa a kujerar yana sauke numfashi. Kusan mintuna uku suna zaune a haka shiru, kafin ya buɗe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya canja ya kalla Dr Jamal daya tsura masa ido...

      “Kai kurwana da ɗaci irin wannan kallo haka”.

Dariya Dr Jamal ya kwashe da shi. “Ɗan wulakanci, inda ni maye ne ALLAH kamun kaɗan a ci ɗan iska kawai”.

     Murmushi yay a karon farko da gyara zamansa. “To zama mayen mana kaga idan zan ciwu a wajenka mara mutunci”.

       Dr Jamal yay dariya kawai. Sai kuma ya miƙe daga kujerar zamansa ya dawo inda Shareff ɗin ke zauna shima ya zauna suna facing juna. “Mike faruwa? Damuwa ta kasa ɓoyuwa a kan fuskarka my Dude”. Nannauyan numfashi ya sauke da ɗan ɗage kafaɗa, “Bani da wata damuwa kawai dai nace bari in gaisheka”. Idanu Dr Jamal ya tsura masa fuskarsa na canjawa zuwa jin haushi........✍_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_53_*
.........Da sallama ta shigo ɗauke da madaidaicin tray mai ƙyau, a samansa  madaidaiciyar butar shayi ce da kofinta ɗaya, sai tea spoon da sugar a ƙaramin bowl. Sai kuma plate dake rufe da robar ruwa ɗaya duk da tasan za'a iya samun ruwan a sashensa. Kaɗan ya juyo daga kallon tvn da yake ya ɗan dubeta, sai kuma ya ɗauke da amsa sallamarta akan lips. Gaba ɗayansu haushinsu yakeji dan kowacce da kalar laifin datai masa, sai dai yafi ganin sassaucin na Fadwa akan wannan tsiwatacciyar yarinyar da har yanzu maganganunta na ɗazun basu daina masa zafi a zuciya da ruhi ba. 

      Ita dai da bata san yanayi ba ma koda ta gama zuba shayin ɗan ɗagowa tai ta dubesa da zata saka sugar. A taƙaice yace, “biyu” ya cigaba da kallonsa. Baki ta ɗan taɓe itama ta jefa masa biyun ta saka cokali. Plate ɗin datai warming sauran naman jiya daya kawo da dare ta zubo a ciki ta buɗe masa, sai sauran meatpie ɗinta da shima dai baiyi komaiba kasancewar a fridge yake shima dai tayi warming ɗin nasa. 

      “Bani waya a bedroom”.

Ya faɗa dai-dai tana ɗagowa alamar ta kammala aikinta. Ganin yanda yake tsume-tsumen fuska ta wuce salin-alin batare da tace komai ba. Babu jimawa ta fito da wayar a hannu. Harya fara cin abincin hankalinsa rabi a tv. Nanma dai tana bashi tai ficewarta tabarsa. 

       Motar da bata san kota wacece ba take shigowa gidan. Bata san wani a gidansu da motar ba, dan haka tai wucewarta batare da maida hankali ba dan maybe baƙin Fadwa ne kona mai gidan...


     “Kinga kallon da yarinyar can taima motarmu ta watsar kuwa Sakina?”. 

     Hajiya Luba ƴar uwa ga Mommy kuma mahaifiya ga Bibah ta faɗa idonta akan Anaam dake shigewa sashenta. Aunty Sakinar ma kallon nata take, tai ƙwafa da ɓalle murfin motar ta fita. “Yaya Luba ba dole tai mana kallon banza ba tunda wanda ya kawota gidan ya nuna mata tafimu, yo ta fimu mana tunda ya zaɓeta sama da umarnin uwarsa ma”.

    “To aikuwa zasu ci ubansu daga shi har ita, dan zamu sauke mata abinda ke kanta yanda uwarta ta mallake ubanta mu anan AL-Mustapha yafi ƙarfin haka. Jiba yanda take yawo da wata ƴar iskar shiga dan ALLAH”.

        “Duk dama ta samu ai ke dai Yaya Luba, muje dai”.

Wanda ya kawosu babban ɗan Aunty Sakina ɗinne, ya girgiza kai duk zuciyarsa babu daɗi, dan shi dai baiga abinda yarinyar tayi ba suke cusa mata wannan zagin, shikam harma ya fara tausayin Yaya AL-Mustapha wlhy.


      Suko sashen Fadwa suka fara nufa, a falo suka sameta zaune tana shan lemun fata, mai-aikinta zaune daga ƙasa itama. Kallon sukeyi na wani horro film sai dai sam hankalin Fadwa ba gaba ɗaya yake akan film ɗin ba. Maman Abu ta miƙe tana musu sannu da zuwa. Da ƙyar suka amsa mata, bata damuba ta nufi kitchen ɗakko musu ruwa dan ba yau ta saba da halinsu ba tunda sanda tana can gidan su Fadwa ɗin ma suna zuwa babu kalar wulaƙancin da basa gani su masu aiki a wajensu su a dole ƙanen masu gida (Karku manta suma ƙanen uba suke ga Fadwa, kuma ƙanen uwa ga Shareff). 

       “Baki da lafiya ne?”.

   Aunty Sakina ta faɗa idonta fas akan Fadwa. Kanta ta girgiza mata kawai. Baki aunty Sakinar ta taɓe. Hajiya Luba ta karɓe da faɗin, “Ciwo ya wuce baƙin cikin miji da kishiya mai kama da karuwai, k yanzu nan Fadwa har waccan ƴar tsefatar yarinyar ce zata razanaki ki koma haka firingau-firingau ido luhu-luhu. Kuka kenan kika zauna kinayi kamar wata sakara?”.

     Hawayen da taketa riƙewa ne suka silalo mata. Aunty Sakina da Hajiya Luba suka ɗauki sallallami da tafi kamar waɗanda sukai gamo. Ita dai Fadwa kanta a ƙasa tana hawayenta. 

  “A to wlhy aiki ya ganki kuwa, yima kishiya kuka. Kishiyarma wadda bata wuci a sati ki kaɗa shegiya ba tabar gidan saboda ke ɗin shashashar ce kika zauna kinamata kuka. To bara kiji, idan zaki dawo cikin hankalinki ki dawo, a duk zuri'armu babu sakarai. Balle ke da mijin nan naki tako ina jininki ne, da ubansa da uwarki uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, da ubanki da uwarsa iyayensu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Gaba da baya aka tsaga jikinku jini iri ɗaya za'a gani, itako fa miye haɗinsa da ita banda ɗiyar ɗan uban ubansa, dalla malama sharemin waɗan nan banzayen hawayen ki tashi ki rakamu sashen shegiyar”.

     Hawayen Fadwa ta share, sai dai kuma tuna yana gidan yasa ta kasa tashi. “Aunty yana nan fa a gida”.

    “Shi wa ɗin?”. 

Cewar Hajiya Luba.

“Shareff! Yau bai fita aiki ba wai hutu ya ɗauka harna sati ɗaya”. Ta ƙare faɗa da rushewa da kuka tabbacin abinda ke cin zuciyarta kenan tun ɗazun. 

     Cikin riƙe baki Aunty Sakina tace, “Iyee wato sati guda, amma uwarsa nacan ko sau ɗaya baije ya gaisheta ba. Shiko dai Al-Mustapha yayi asara. Aini namaji daɗin samun nasa a gidan zanfi jin daɗin cin uban shegiyar yarinyar a gaban nasa sallamamme kawai. Tashi muje ki kaimu, kuma karna sake ganin waɗan nan hawayen banzar kema shashasha”.

      

      Anaam na kwance cikin kujera tana buga game suka faɗo mata ko sallama babu. Da farko tayi kamar ta share dan Fadwa ce ta fara shigowa, sai dai ganin su Aunty Sakina ya sa ta tashi zaune tana danne sosuwar da zuciyarta tayi akan shigo mata kai tsaye da sukai. Ta san aunty Sakina dan sun taɓa zuwa gidanta ita da Aysha. Daga Hajiya Luba har aunty Sakina bin falon suke da kallo baki a taɓe, sai dai acan ƙasan ransu razani ne na gaske, dan ko makaho ya shigo ya laluba yasan annunama duniya yariyar ƴar gata ce.....

       Cigaba da game ɗinta tai domin basu dama su gama kalle-kallen, saiko da sukai iya iyawa sannan suka juyo gareta. 

    “Oh lallai, ga ƴan iska sun shigo ko?”. 

Aunty Sakina ta faɗa murya a sama. A karan farko Anaam ta saki murmushi, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi tana kallonsu, cikin hausarta dabai gama nuna ba ta gaishesu kamarma bata fahimci harzuƙowar aunty Sakinar ba..

          “Uhm lallai kam Shareff ka amshi ruwan dafa kanka. Wato k a dole ƴar bariki”.

     Sarai ta fahimci abinda Hajiya Luban ta faɗa, dan kuwa zuwa yanzu Alhmdllhi hausa ta fara zauna mata a brain da harshe da ƙyau saɓanin farkon zuwanta. Amma sai tai kamar bata fahimci komai ba, fuskarta da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Aunty ku zauna Please bara na kawo muku ruwa”. Bata jira cewarsu ba ta nufi kitchen.

     “Babbar b*r* uba kai. Wai wannan yarinyar tana nufin bama tajin mi muke faɗa ko mi?”.

   Fadwa da batace komaiba tun shigowarsu tana kuma daga tsaye dan bata zauna ba tace, “Hummm! Tana jin komai sarai iskanci ne kawai fa Aunty. Ni dama kun barta dan ALLAH kawai....”

        Harara Hajiya Luba ta zuba mata. Shigowar Shareff a bazata ta saka Fadwa haɗiye abinda zata faɗa babu shiri da risinar da kanta ƙasa, wani yawu mai kauri ya wuce muƙut a maƙoshinta ƙirjinta na bugawa. 

        Idanunsa ya janye a kanta da ƙarasowa cikin falon hannayensa duk biyu a cikin aljihun wandonsa. 

   “Oh dama kana gidan?”.

Aunty Sakina ta faɗa tana hararsa.

Duk da sarai ya jita sai bai amsa ba, sai da yakai zaune cikin kujera da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubesu. “Barkanku da safiya aunty kune a gidan namu?”.

     Sosai ransu ya sosu da salon rainin wayonsa su duka. Sai dai kafin wani yace wani abu a cikinsu Anaam ta fito ɗauke da tray shaƙe da kayan ciye-ciye da ruwa da lemo. Itama dai ta ɗanji wani iri na ganin nasa, amma saita fiske abinta ta ajiye tray ɗin a gabansu tana murmushi. “Aunty ga ruwa to....” 

        A matuƙar harziƙe Hajiya Luba ta tura tray ɗin da ƙafarta tana ballama Anaam harara. “Tunda shine ya kawomu ba, k ki kama kanki wadda ta haifeki ma a tafin hanunmu take balle ke kanki...”

     “Juwairiyya bani lap-top dana bari a ɗakinki”. Shareff ya katse hargowar Hajiya Luba tamkar bai ji mima take faɗa ba. Tsamm Anaam ta miƙe batare da tace uffan ba, ba kuma ta kalli sashen da Shareff ɗin yake ba balle Fadwa ta ɗauka wayarta ta wuce bedroom. 

         “Oh ke ko ga mahaukata suna magana dole ka sata aika. K! Fadwa shaƙomin ƴar iskar yarinyar can na nuna mata wacece ni dan ubanta”.

     Muƙutt Fadwa ta haɗiyi yawu da ƙyar a karo na biyu domin jin umarnin Aunty Sakina tamkar saukar aradu bisa kai. Ta ɗan saci kallon inda Shareff ke zaune a harɗe har yanzu kai kace baima san wainar da ake toyawa a falon ba. Kanta ta girgiza a hankali, so take tayi magana amma ta kasa motsa lips ɗinta sai kawai ta juya da sauri ta bar falon ma gaba ɗaya. (Tabbas Fadwa nada kurari da hayaƙi, amma kuma tanada tsoro bata cika iya jure hatsaniyar faɗa ba. Idan mai karatu bai manta ba kokuma ya lura da ƙyau zai fahimci Anaam ta fita tsiwa, saboda a lokuta da dama takan takaleta faɗa amma a ƙarshe Anaam ɗin ke tsigeta itako sai tai laƙwas. Tabbas a cikin raunanan halayanta wannan yana ciki rashin juriyar hatsaniya, a wani fannin kuma zamu iya kiransa haƙuri😜).

      Daga aunty Sakina har Hajiya Luba baki suka saki uwa sakatar sakarai dan al'ajabin Fadwa. “Oh ni Sakina ato lallai Fadwa kema kin cika asararriyar yarinya, to kodai ba Al-Mustapha ɗin kawai aka shanye ba harda ke ɗin kema?”.

     Maimakon samun amsa daga Fadwa data fice sai Hajiya Luba ce ta amsawa Aunty Sakinar. “A to ga halama kin gani kuwa Sakina. Ƙanƙanuwar yarinya ke juya gida miji da kishiya duka a tafin hanunta.”

       Ƙololuwar ɓacin rai kam Aunty Sakina takai, musamman biris da su da Shareff yayi. Tsabar wulaƙanci ma sai latsa wayarsa yake yana ɗan girgiza ƙafarsa da yay crossing. Anaam dake danne dariyarta da jinjina tsaurin idon mutumin nan ta ƙaraso ɗauke da lap-top ɗin a hannu.  Gabansa gab ta matsa, ta miƙa masa harda takardun data haɗo da su. Idanunsa dake akan wayar ya ɗago yana kallonta, ta ɗan tura baki gaba tana son dangwarar da kayan bisa cinyarsa ya riƙo hanunta. Fuska ta ɗan narke da ƙyaƙyƙyafta idanu tai ƙoƙarin janye hanunta.........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_56_*
.........Bai shigo ba sai da aka idar da sallar isha'i. Ya kwashi ledojin daya bari a mota. Na Fadwa ya fara ɗauka ya nufi sashenta. A falo ya sameta zaune cikin kwalliya da waya a hannu. Ga tv a kunne tana faman aiki. Yana mamakin yanda a koda yaushe waya bata barin hanunta, tun baya maida hankali akan hakan har ya fara sosa ransa, sai dai bazaiyi maganaba a yanzu sai anzo gaɓar data dace. 

      Fuskarta ƙawace da murmushi ta taso garesa. Rungumesa tai da manna masa kiss a kuncinsa na dama. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi dan babu abinda yafi buƙata kamar ɗumin matarsa a yanzu. Ya sani ba ƙaramar jarumta yayi ba, dan rabonsa da Fadwa kusan sati uku kenan cikin na huɗu. Hanunta saƙale a wuyansa fuskarsu gab da juna. Bakinsu take son haɗewa amma ya kauda kai kaɗan dan ya tabbata ya biye mata bazai iya ƙyaleta ba kuma hakan ba daidai bane ba tunda akwai haƙƙin wata a kansa bayan ita ɗin.

     Cikin son basar da ita ya janye hanunta dake saƙale a wuyansa yana faɗin, “Ki shirya abincin”. Jiki a sanyaye ta gyaɗa masa kai, harya nufi ƙofa ta kasa haƙuri. “Har yanzu baka huceba ko? Kana ganin laifi na!”.

      Tsayawa yay, sai da takai aya ya waiwayo yana kallonta. Tai ƙasa da kanta zuciyarta na sake raunana dan da gaske abin ya dameta. Shima ɗin ta bashi tausayi, dan shi shaida ne Fadwa nada tsoro da tsananin gudun ɓacin ransa, wannan halin nata na ɗaya daga cikin abinda ya saka masa sonta. “Zan iya miki uziri ana yau, amma ki kiyaye dan anan gaba makamancin haka ta sake faruwa ni kaina ban san irin matakin dazan iya ɗauka ba har asu kansu, dan bazan ɗauka wulaƙanta matata da hanani zaman lafiya ba a gidana”.

      Bai jira cewartaba ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, zuciyarta na rage cinkushewar da tai......


    Idar da sallarta kenan takai bakin gado, muryar Mamie take son ji duk da sun gaisa ɗazun da safe. Maimakon normal kira saita ji sha'awar kiranta video call. Tana ƙoƙarin yin hakan da ɓare lollipop sweet takai baki ya shigo ɗakin. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janye nata dan wani irin matsanancin kunyarsa ta tsinci kanta a ciki saboda abinda ya faru ɗazun da shi ta yini cikin rai. Inda taken ya ƙaraso ya zauna kusa da ita gab. Batare data sake iya ɗagowa ta kallesa ba tace, “Barka da dawowa”.

     “Uhhumm”.

Ya faɗa a miskile idonsa nabin jikinta da kallo. Kaya ƙanana ne da sukai matuƙar kama ɗan jikinta komai ya fita fili tamkar an zana. Ya janye a kasalance dan dama acan ɗin ma kwalliyar Fadwa ba karamin tasiri tai a ransa ba. Ya yarda matan nasa duk ƴan gayu ne, sai dai Fadwa tafi Anaam son ƙyale-ƙyale, dan da wuya kaga fuskar Fadwa babu kwalliya hakan kuma na matuƙar burgesa. Saɓanin Anaam da zai iya cewa bai taɓa ganin kwalliya ba a fuskar tata ba, sai dai idan ya manta. Idan son samune itama zai so ta dingayi ɗin dan yana da tabbacin zata mata ƙyau.

       “Da rana mi kika ci?”.

   Ya jeho mata tamyar idonsa na kallon bakinta dake juya alawar a ciki batare data riƙe tsinken ba. Yanzu ma bata iya ta kallesa ba, ta damƙe wayarta da take juya a hanunta da ƙyau. Muryarta can ƙasa tace, “Noodles”.

    Ɗan jimm yay da tunanin taya ta dafa. “Dami kika dafa to?”.

  Ɗagowa tai ta dubesa da mamaki. “Kamar ya?”.

     “Nasan baki da gas ai”.

  “Nayi amfani da electric ne”.

Ajiyar zuciya ya sauke na samun nutsuwa, dan gaba ɗaya ya shafa'a ne ma, dama yau yaso a siyo mata gas ɗin a kuma haɗa mata tvn ta.. Duk yanda yaso basar da abinda ke tsikararsa ya kasa. Ƙara matso jikinsa yay a nata sosai da riƙo hannayenta duka numfashinsa na sauka a gefen wuyanta. A take tsigar jikinta ta tashi, taja jikinta baya zata matsa ya rungumota, kallonsa tai fuska a marairaice, sai dai bazata iya jurewa ba tai ƙoƙarin rissinarwa amma sai ya hana hakan ta hanyar tallafo haɓarta..

    “Yanzu tsabar rowa bazaki sammin sweet ɗin ba?”.

Wutar kan Anaam neman ɗaukewa tai, tsigar jikinta ta tashi har tana ƙoƙarin yadda alawar babu shiri. Gaba ɗaya yanayin nasa da muryar dayay amfani wajen mata maganar ya matuƙar rikitata, dan bata taɓa jin irin muryar tare da shi ba. Hannu takai jiki a mace zata zare alawar a bakinta ya riƙe hanun tare da matsota suna kallon juna cikin ido. 

    “A haka nake son sha”.

(Ya ALLAH) ta faɗa cikin zuciyarta, a zahiri kam tuni idanunta sun fara marmarin firgici da tsantsar mamakinsa. Ya kashe mata ido ɗaya da sake kusanta fuskarsu, baya ta ƙara jan jikinta ya bita, ta ƙara matsawa shima ya matsa, ta ƙara ya ƙara, sai kawai ta zube a gadon da ƙokarin tufo alawar waje kawai a ganinta hakan shine mafita gareta. 

     Murmushi ya saki a karo na farko, shanyayyun idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya na bin fuskarta da kallo, ya ɗauka alawar ya saka a bakinsa ya ɓalla kaɗan. “Ni ban iya rowa ba zan sammiki” ya faɗa tare da ɗage mata gira ɗaya yana matso da bakinsa gab da nata. 

    “Ba gashi nan na baka ba”. Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa. 

     “A cikin bakinki nake son sha ni”. “Ban yarda ba”. 

“Ba sai kin yarda ba dama tunda nawa ne”. 

       “Naka? Yaushe ya zam....” Ruff ya rufe bakin tare da tura mata sweet ɗin a nata bakin, ya haɗa da harshenta ya fara tsotsa.  Wani irin miƙewa illahirin gashin jikinta sukai, takai hanunta saman ƙeyarsa da nufin janye masa kai hakan ya gagara. Domin wani irin salo yake mata mai narkar da ita, dole ta lumshe idanunta a hankali ta fara bashi gudunmawa. Sai da suka shanye alawar tas a cikin bakinta sannan ya janye. Kanta ta kauda gefe wata irin kunyarsa mai girma na ratsata. Sassanyan murmushi ya saki da leƙa fuskartata, tai saurin ɗaukar fillo ta ɗora tana murmushi itama. Ƴar dariya yayi da ƙoƙarin tashi tsaye. “Ga tsoro ga tsiwa, kona dawo mu shanye sauran?”. 

        Da ƙyar ta iya fisgar numfashi ta haɗiye, ta bude idanu hannunta dafe da ƙirjinta. Dariyarsa ya danne da ƙyar yana gyara rigarsa da jifanta da wani kallo daya sata janye nata idon akan sa, “Oya tashi muje cin abinci”. Ajiyar zuciyar ta ƙara saki, batare data yarda ta kallesaba ta girgiza masa kanta. “Ni na ƙoshi fa”.

    “Amma kin san zan iya ɗaukarki daga nan har can kuma akwai Matata”.

          Har cikin rai maganarsa ta soketa, to ina ruwanta wayace ba matar tasa bace. Ta murgiɗa baki a zahiri da ɗauke kai gefe tana ƙunƙuni. (Wani yace ba matarka bace balle ka mana burga). Sarai ya jita, amma sai baice komai ba ya ɗan matso kusa da ita. Zabura tai gefe tana tura baki. “To bana tashi ba dai”. Hanya ya nuna mata. Hijjabin sallarta ta zara dayin gaba tana kumbura fuska, ya biyota a baya yana murmushi dan ya gama yanke shawarar ayita ta ƙare kawai ya tabbata haka shi zai kawo masalaha ta ƙarshe da zuciyarsa ke tabbatar masa..


     Sun sami Fadwa harta kammala shirya abinci, a cikinsu babu wadda ta kalli ƴar uwarta, kuma kowacce ta tsuke fuska babu sauƙi. Shi dai ya cigaba da shan alawarsa yana ƙumshe dariya, a zahiri kam shima tashi fuskar a tsuken take. Fadwa dake zuba masa abinci ta ɗago tana kallonsa, da ido yay mata alamar thanks. Ta ɗan saki murmushi, sai dai ta tsurama sweet ɗin bakinsa ido. Fahimtar hakan da yayne ya sashi zarota ya miƙa mata, ƴar kaɗan ta rage a jiki yama kusa shanyewa, hannu ta kawo zata amsa fuskarta da murmushi itama Anaam dake ɗayan gefensa tai kamar zata ɗauka kofi ta tanƙwaɓe hanunsa sweet ɗin ta faɗa cikin miya. Fiskewa tai kamar bataga abinda tai ba, hasalima taƙi kallonsu. Wani irin takaici da baƙin ciki ya turnuƙe zuciyar Fadwa, amma sai batace komaiba. 

      Kallonta yay ta gefe ido shikam dai, sai kuma ya maida ga abincinsa guntun murmushi na suɓuce masa. Ganin har sun fara cin abincin bata da alamar zubawa ya sake ɗagowa ya kalleta. “K bazaki ci abincin ba?”.

Fuska ta ɗan yatsina da taɓe baki, “Ni ban iya cinshi ba”. Karon farko Fadwa ta kalleta, itama fuskar ta yamutse baki a taɓe. Cikin gatse da jin bazata iya shiru ba tace, 

     “Sai ki fara koya ai”.

   Itama a gatsen da taɓe baki tace, “Ba buƙatar hakan”. 

Baki Fadwa ta sake laɓewa da ɗauke kai abinta. Itama sai ta harareta ta cigaba da buga game ɗinta.

     Duk yana jinsu amma yay shiru bai sake yin magana ba, sai ma hankalinsa daya maida ga abincinsa hankali a kwance kamar bai san sunai ba. Har suka kammala dai Anaam bata ci ba, shine ya fara barin dining ɗin ya koma falo ya zauna. Fadwa dake shan lemo a hankali ta saki murmushi, dan da farko tayi zaton zai kama lallashi Anaam ɗinne kamar yanda ta san itama Anaam ɗin tayi ne dan ya lallasheta. Amma sai gashi yay biris. Mikewa tai tana tattare kayan da sakin ƴar karamar dariya. “To mudai wannan amarya ta gidanmu uhumm babu alamar ta cika amarya, hausawa na cewa amarya kota buzuzu ce ɗokinta ake, sai dai mu gata mutum a namu gidan bata da wani fawa”. 

     Da gaske saƙon na Fadwa yana isa har tsakkiyar kan Anaam. Dan kuwa da turanci take maganar hakan yasa komai ta jisa. Zuciyarta ta fara luguden dakan fusata da sukar da kalaman ke mata amma sai ta saki murmushi a zahiri. Babu burin zamanta a wannan gidan hakan yasa bata fatan Shareff ya nema wani abu a gareta, dan hatta kissing ɗinta da yakeyi tayi alƙawarin baza'a sake na huɗu ba. Sai dai tabbas saita shayar da Fadwa mamaki cikin sauƙi batare da ta rasa mutuncin nata da take tattali ba... A yanzu dai batace komai ba har Fadwa na koƙarin barin wajen fuskarta ƙawace da murmushi. cigaba da zama a dining ɗin tai kamar mai latsa waya, a zahiri kam komai ta kasayi tsabar raɗaɗin da ƙirjinta ke mata.....

      “Amarsu mu kuna lafiya”..

Fadwa ta faɗa tana ɗaga mata yatsu biyu da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci gefen fuskar Shareff. Fuskar tata ya shafo shima yana murmushi. Idanunta da suka ciko da ƙwalla ta kauda daga kansu, dama ta gefen ido take kallonsu. Jitai bazata iya barmata ba, dan haka ta miƙe tasha gaban Fadwa dake gab da fita...

       Cike da salon ƙularwa fuskarta ƙawace da murmushi take kallon Fadwa da mamakin yanda ta tareta ya sata diriricewa, to amma a gareta hakan zai zama riba tunda tasan Shareff bazai ragawa Anaam ɗin ba. 

     Anaam data gama fahimtarta ta ƙara sakin murmushi da naɗe hannayenta a ƙirji “Amaryar data kai mace ba'a samunta ta sauƙi ai, saboda tsadarta tafi tsada tsada madam, ki rubuta ki aje a duk lokacin dana sallama wlhy sai kin zama ƴar kallo a wajen mijin naki, idan kin isa mu ƙulla”. Ta ƙare maganar ƙasa-ƙasa tana kashema Fadwa ido.   

   Yawu mai kauri Fadwa ta haɗiya saboda ganin alwashi cikin idanun Anaam, ta saci kallon gefen Shareff sai taga su yake kallo. Murmushi ta saki cike da kirsa. “Ayya Anaam miya faru da wannan magana haka?, ai shi ɗin mijinmu ne mu duka ba nawa kawaiba, kinga kuwa basai mun ƙulla wata yarjejeniya a kansa ba, kuma indai nice wlhy nama ƙara muku sati biyu akan ɗayan”.  

   Anaam dako kallon inda Shareff yake batayi ta saki wata siririyar dariya data ƙona ran Fadwa da tafa hannayenta. “Woow! kai kai kai Uwargida abun birgewa. Muna godiya da wannan ƙyauta mai tsada”. Sai kuma ta kashe mata ido da maida muryarta can ƙasa kamar mai raɗa. “Karki damu kinada kaso, za'a samo miki tukuycin baby da zaina tayaki hira tunda kin hana masa zuwan abokin wasansa yayansa duniya”. 

        Duk da a hankali sosai Anaam ta faɗi furucin ƙarshe kaɗan ya rage zuciyar Fadwa ta wantsalo waje.   “Sautin bai miki ba na ƙara n.....” Da sauri Fadwa ta fice cikin sassarfa daga falon, wani irin zufa na tsatstsafowa ta illahirin ƙofofin jikinta har tana kifawa kamar zata faɗi. Anaam ta danne dariyarta da ƙyar, da binta da kallo harta fice. Sai da Fadwan ta fita da kusan mintuna biyu sannan tabi bayanta zuciyarta fes tunda ta rama.  

     Da kallo ya bita ta gefen ido, ya jinjina kansa da sakin murmushi dan duk abinda ya faru a tsakaninsu yaji. Hatta maganar farko da Fadwa tai a dining, yayi shirune dama dan yaga wane mataki ita kuma Anaam ɗin zata ɗauka. Wato Fadwa a gabansa ne take nuna ita ɗin mutuniyar kirkice, ita kuma Anaam bata iya ɓoye-ɓoye ba sai take nuna nata babu wani munafurci a ciki. idan ya auna da kallonsa da Fadwa takeyi tana magana cikin canja yanayi danta kunnasa ne ya hau kan Anaam kenan kamar yanda taga yanayi a kwana biyun nan idan tai makirci. Lallai mata sai ka barsu, idan kai wasa sai su kaika wuta da sheɗana, dolene ya nutsu wajen ƙara fahimtar halayen kowacce kuwa. 

    Duk yanda yaso cigaba dayin kallon kasa hakan yay, dan kalaman Anaam babu abinda suke sai tsikarar zuciyarsa, dole ya miƙe ya kashe komai ya shiga bedroom ɗinsa. Sabon shirin barci ya sabunta da mulke jikinsa da turarurrukansa masu ƙamshi har kusan kala biyar, haka kawai yake jin saka ɗaya bai gamsar da shi ba. Bakinsa kansa yasha Mouth fresheners kusan kala uku, ya sake duban kansa a mirror ya saki murmushi da kashema kansa ido ɗaya...  _“Dole ne yau a tabbatar min da wannan tsadar da tafi tsadar tsada my girl”_.

       

       ★Ransa fes ya fito hanunsa ɗauke da fresh milk. Kansa tsaye sashen Anaam ɗin ya nufa, baiyi mamakin rashin ganinta a falo ba. Sai da ya fara shiga kitchen ya ɗauka ruwa da glass cup sannan ya nufi bedroom ɗinta bayan ya kashe komai ya rufe ko ina.

     Tunda ta fito a sashensa da murmushi ta iso nata sashen, ya kuma gagara barin fuskarta har tai shirin barci dan dama tayi wankanta, brush kawai tayi ta haye gado batare data ɗaura jacket ɗin rigar barcin ba a kan ta cikin data kasance ƴar fingila iyakar cinyoyinta, sannan hanunta siriri ne. Rufda ciki ta kwanta da jan bargo ta lulluɓe har kanta tana cigaba da sakin murmushi.........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO

Chapter 58

58


........Hanunta take ɗagawa daƙyar tana kai masa ƙananun duka, ya fara ƴar dariya da ƙoƙarin riƙe hannayen nata. Duk yanda yaso su koma barci hakan ya gagara, dan ƙorafinta na zafi da raki ya gagara tsayawa. Ga zazzaɓi mai zafi dake ƙara rufeta bayan sauka ya kamata yayi tunda tasha magani. Dole ya tashi zaune da ita a jikinsa yana ƙoƙarin son su haɗa ido amma taƙi yarda. Bai damu da hakan ba, dan yasan kunya dole ce. Shi kansa wani nauyi yakeji amma yana ta ƙoƙarin ganin ya fuske abinsa..


   “Faɗamin miye matsalarki kuma Noorii na?”.


Shiru ta kasa bashi amsa, sai ƙoƙarin son kauda kanta kuma take yaƙi bata dama. Dole ta buɗe baki muryarta a ɗashe irin ta wanda yaci kuka ya more, dan ko fita batayi da ƙyau. “Inajin zafi mai raɗaɗi, dan ALLAH ka kiramin Mamie ko ka kaini wajenta”.


    A ransa yace, (Ko ɗaya a ciki bazaki samu ba) a zahiri kam wayarsa ya ɗauka zuciyarsa na masa kaikawo akan waya dace ya kira. Har yai dailing number Dr Jamal sai kuma ya katse, text message ya tura masa. mintuna kaɗan kuwa sai ga kiransa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da miƙewa ya fice a ɗakin.


   “Malam ba kirana nace kayi ba, Nurse daka aminta da ita nace ka turamin”.


      Dr Jamal yay murmushi da shafa kai daga can, “Oh to ai ko asibitin ban fitaba shiyyasa nace bara na kiraka naji waye babu lafiya?”. Jimm yay na wasu ƴan sakkani, sai kuma ya furzar da huci a hankali ya furta “Juwairiyya!”.


  “Ayya ALLAH ya bata lafiya, mizai hana ka kaita asibiti kawai sai mu haɗu, dan gaskiya a iya hasashena ban san wace Nurse zan tura maka ba indai irin wadda nasan zaka buƙata ce. Amma Dr Bilkisu na tabbatar ta iso yanzu zatafi kulawa da ita da sanin matsalarta kai tsaye inma mune baka son mu duba maka ita..”


   “Kai ka sani”.


Ya bashi amsa a taƙaice da yanke wayar. Daga can Dr Jamal yay ƴar dariya da ajiye wayar ƙasan zuciyarsa na masa kaikawo amma yana turewa dan yayi alƙawarin mantawa da ita, zai cigaba da mata kallone kawai irin na ƙanwa kuma matar amininsa insha ALLAHU.


    Shawarar Jamal ta masa, dan haka ya taimakawa Anaam daketa hawaye har yanzu ta shirya, shima dai a gurguje yay nasa shirin. Duk yanda yaso tai taku daga bedroom zuwa waje ta kasa, ko bedroom ɗin ta kasa iya ƙarasa fitowa zafi kawai take ambata tana hawaye, gashi duk ta langaɓe masa kamar mara ƙashi a jiki. Dole ya ɗauketa gaba ɗayanta ya fito.....
   ★Ranta fes ta tashi yau kamar yanda ta kwanta sakamakon jin ƙwarin gwiwa daga sirrin su aunty Safarah. Gaba ɗaya cikin yaƙini da imanin maganin da suka batan yayi aiki take. Tana idar da salla cike da karsashi ta shiga kitchen da kanta haɗa breakfast. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama maman Abu ba. Sai dai bata iya cewa komai ba dan ta fahimci uwar ɗakin nata tana a farin ciki, tasan kuma yana da nasaba ne da abinda taga tanayi jiya. Sai taji inama zata fahimceta kuma ta isa ta bata shawara akan abinda take kallo ba komaiba. Taji sanda su aunty Safarah ke tabbatar mata maganin matane suka bata, ita kuma ta aminta da hakan saboda bata da ilimin banbancewa, ta sani Fadwa nada rawar kai da ɗagawa, dan duk wanda ya kwana ya tashi a gidansu yasan ita ɗin boss ce musamman akan ƴan aiki, to amma kuma duk da kasancewarta a haka ɗin bata taɓa tunanin ganinta da wani mugun hali da ya zarta waɗannan ɗin ba, tanaji a ranta kuma da wani zai fahimtar da ita abinda su aunty malika suka bata nada banbanci da maganin mata ƙila bazatai amfani dashi ba duk da bata san zuciyarta ba dai.


   Tana aikin gyaran sashen nata ita kuma tana haɗa breakfast mai rai da lafiya a kuma nutse, dan dama dai shiriritarta da son jiki ke hanata yi ɗin a yanda ya kamata bawai dan bata iya ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko'ina, cike da nishaɗi ta kammala ta koma bedroom ta gyara jikinta. A yau zata kawo duk wani iskanci da jiji da kan Anaam a gidan nan, dan babban burinta tai gaba ta barta da mijinta salin alin.


   Ƙarfe takwas da wasu ƴan mintuna ta nufi sashensa dan tasan ya tashi zuwa yanzu, shi ba ma'abocin barcin safe baneba ma, amma a yanzu tunda yana gida ba aiki zai fitaba tasan ko yaya zai ɗan kwanta.....


    


   Fitowar Fadwa yayi dai-dai da fitowarsa ɗauke da Anaam daga sashenta. Babu shiri taja birki ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku ba, shi sam baimaganta ba dan hankalinsa gaba ɗaya ya tafine ga kallon Anaam yana murmushi, saboda tsokanarta yake akan raguwace ita tana tuttura masa baki da kauda fuskarta gefe. Anaam ɗin kam sarai ta ganta, duk da halin da take ciki hakan bai hanata ganin wannan wata dama bace, ada taƙi yarda ta riƙesa, a yanzu kam saita saƙalo hannayenta a wuyansa duk biyu tana sake sakin kuka da cusa kanta a ƙirjinsa. Shiko da bai san dalilin yin hakan ba sai ya ɗan manna mata kiss a goshi da sakin siririyar dariya. A hankaki yake taku har zuwa wajen motar tasa, ya dureta ƙasa tare da jinginata da motar. 


    “Ina zuwa”.


Ya faɗa yana barin wajen, batace komai ba sai dai idanunta na satar kallon sashen da Fadwa dake binsu da kallo har yanzu kamar a birkice take. Da sauri Fadwa tai baya alamar bata buƙatar ya ganta, shima da yake ALLAH yasa hankalinsa ba wajen yake ba sai bai lura da ita ba ya wuce yanzu ma. Mintuna da basu fi uku ba ya sake fitowa hannunsa da key ɗin motarsa. Sake wucewa yay abinsa batare da yanzu ɗin ma ya ganta ba dai...


   A gaban idonta ya sake ɗaukar Anaam ya saka a mota, shima ya shiga suka fice gidan. Tai baya kamar zata faɗi maman Abu da itama komai ya faru akan idonta ta riƙota. “Hajiya dan ALLAH ki kwantar da hankalinki”. Maman Abu ta faɗa muryarta cike da damuwa itama. Da taimakonta Fadwa ta koma ciki, ta ɗakko mata ruwa amma sai ta hankaɗar da shi ya zube, wasu zafafan hawaye da sai yanzu suka sami damar fita a idanunsata suka shiga rige-rigen sauka a fuskarta. Maman Abu dai batai fushiba, takai zaune kusa da ƙafafunta a ɗarare ta sake faɗin, “Hajiya dan ALLAH karki ɗaga hankalinki, wannan kaɗanne daga halin maza idan suka ƙara aure. Amma inaga ki bincika kiji mike faruwa tukunna kamar zaifi. Koba komai kin jefa tsuntsu ɗaya da dutse biyu. Na farko dai zaki san mike faruwa, na biyu kuma zaiji kunyarki idan fitar bata da wata babban dalili da farar safiyar nan. Amma idan na shiga hurumin daba nawa ba kiyi haƙuri..”


   Idanu Fadwa ta sake rumtsewa da ƙarfi zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi, dan tabbas abinda Shareff yayi ya sake zuzuta zafin daya sauka mata lokaci guda, kishi ya rufe idonta ta kasa ji a ranta wata matsalace ta sakasu fita gidan da safen nan bawai lafiya ba.....


   Waya ta ɗauka da sauri ta fara laluben layin aunty Safarah. Bata tsaya ko gaisuwa ba ta sakar mata kuka. 


   “Subahanallahi Fadwa lafiya kuwa?”.


  “Aunty Wlhy maganin beyiba, yanzu fa da safen nan ya fito ɗauke da ita suna farin cikinsu da dariya suka bar gidan nan. Alhalin jiya babu wani kusanci makamancin hakan tattare dasu. Aunty na shiga uku idan hankalinsa ya koma kan yarinyar nan. Jiyafa taimin alwashin indai ya fara kasancewa da ita saina zama ƴar kallo....”


   “Kinga nutsu ki saurareni Fadwa. A yanzu haka gani tare da Aunty (Gwaggo halima) kuma duk tana jinki, dama nazone zan amsa sako da zamuje wani waje saboda ke”.


   Sunan maman ta fara kira cikin kuka, Gwaggo Halima da tun fara bayanin Fadwa wutar kanta ya ɗauke saboda shi babba duk inda yake babba sunansa, tuni zuciyarta ta hasko mata wani abu ya shiga tsakanin Shareff da Anaam kenan, dukan kokarinsu na hana faruwar hakan bai yuwuba kenan, taja numfashi. “Fadwa kinga nutsu kuka ba naki baneba. Karki damu damun bayanin komai na riga na sani domin ni na aiko su Safarah wajenki dama nace ne karsu faɗa miki. Yanzu ki jira zamu kiraki ina zuwa...”


  Kafin tace wani abu aka yanke wayar, ta zube a bakin gado da sake fashewa da kuka mai cin rai....


   


_______
   Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin, yanzu dai taso nuna jarumtar hanashi taɓata amma ina hakan bai yuwu ba. Dan taku biyu kacal ta nema zubewa tamkar ta fasa ihu dan zafi. Dole dai ya ƙaraso ya ɗauketa.


   “Ni dai Yaya ka saukeni zan iya”.


Ta faɗa tana sharce hawayen dake ambaliya akan fuskarta saboda hango Dr Jamal dake nufosu alamar yasan da zuwan nasu. 


  Murmushi yay da kashe mata ido ɗaya “Da wannan tafiyar tonamin asirin ne zaki iya?”. 


   Idanunta ta rumtse kunyar duniya a kanta, dan gani take kowa zai iya sanin miya faru da ita ne. Da taimakon Dr Jamal suka sami ganin Dr Bilkisu a sahun farko. Ganin Anaam taƙi amsa tambaya ko guda ɗaya a gaban Shareff daya tsatstsareta da ido yasa Dr Bilkisu kallonsa da ɗan murmushi. “Alhaji Al-Mustapha ko zaka ɗan bamu wajene dan naga patient ɗin tawa kasancewarka tare damu ya hanata cewa komai”.


    Ido suka sake haɗawa da Anaam. Tai azamar janye nata da tura masa baki. Mikewa yay yana murmushi batare da yace komai ba ya fita. Ko'a bayan fitar tasa ma sai da Dr Bilkisu ta sha fama sannan Anaam ta amsa mata wasu daga cikin tambayoyin nata tana faman sinne kai, a yanda ta fahimci ta kasa zama da ƙyau tai hasashen abinda Anaam ɗin ke faman ɓoyewa. Batace komai ba ta taimaka mata zuwa gadon da suke duba marasa lafiya, ganin tana neman ɗage mata doguwar riga ta riƙe da sauri tana girgiza kanta...........✍

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_57_*
.........A hankali ya tura ƙofar ɗakin laɓɓansa na motsawa alamar sallama, kamar mai irga steps ɗinsa ya cigaba da shigowa cikin ɗakin idonsa akanta duk da ƙudundune take cikin bargo, zaune ya kai gefenta tare da kai hannu ya yaye bargon. A yanda ta miƙe zumbur da alama bata san da shigowar tasa ba. Idanunsa sukai ƙyaƙyƙyawan ganin daya sakashi jan numfashi a fisge, dan shaiɗaniyar rigar jikinta bata bar komai a sirrance ba, a waccan ranar ya ganta, sai dai a yau rigar tafi bayyana masa komai har idonsa na neman tsolewa. Ita kuma data manta a yanda take komawa tai zata kwanta cikin taɓe fuskarta dan wani haushinsa da takaicinsa ne suka sake kamata. Riƙota yay, ta shiga fisgewa da fashe masa da kukan ƙarya.

      “Ni ka sake min hannu, kuma bana son ganinka ka koma can wajenta ita matar son naka, ƙarewar kiss kace ta cinyeka mana...”

   Sassanyar ajiyar zuciya ya saki, komai baice ba, bai kuma saki hanun nata ba sai dai murmushi ya suɓuce masa akan fuska kaɗan, ta cigaba da turesa da ƙoƙarin kai masa ƴan ƙananun duka a damtsen hanunsa. Bai hanata ba yana dai ta ƙoƙarin danne dariyarsa. Ganin abun nata bana ƙare bane ya rungumeta gaba ɗaya ya tura a jikinsa. Duk yanda taso cigaba da fisge-fisgen ya hana hakan, ya fara kai ma fuskarta da wuyanta kiss har yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba. Ƙarfin kukanta ta ƙara da ture masa fuska amma yaƙi ya daina, sai da yay mai isarsa sannan ya barta da ƙara matseta a jikin nasa. 

      “Shikenan sai bori ya ƙare an biyaki kiss ɗinki, ai ban san kina so bane amarya mai aji, nazo da ƙoƙon bara yau a barni na samu tubarrakin wannan tsadar tsada sarauniyar mata kona samo tukuycin nan da kikai alƙawarin badawa”

    Zabura tayi da nufin turesa tana waro ido sosai waje jin wai ashe duk yaji mita faɗa ɗazun, amma yanda ya naɗeta a jikin nasa yasa baiko motsa ba. A karan farko ya sakar mata siririyar dariya cikin kunnenta da cizonsa da haƙori. Ƙara ta saki kaɗan duk da bawani zafi na azo a gani taji a cizon ba. 

     “Ni dai wlhy ka tashi ka fita yaya, kaje ka ƙarata da matarka ni duk abinda na faɗa iya laɓɓana ne kaima kuma ka san...”

      Ruff ya rufe bakin nata da nashi tare da ƙara matseta gamm ya fara mata wani salo daya nema zuƙe numfashinta gaba ɗaya taja ajiyar zuciya tankar mai shirin shiɗewa. Salo ne da bai taɓa kwatantashi ga wata bama, tun tana da zarrar yin yunƙuri harya ci galaba a kanta ta koma masa laƙwas sai dai ta kasa maida murtani sai ma jikinta dake tsuma. 

       “Yaya Please ALLAH wasa nake mata”. Ta faɗa a wahale tana janye bakinta daya sassauta riƙewa a nasa. Ganin yana neman sake cafkowa ta tura kanta cikin ƙirjinsa ta kanannaɗesa.

    Murmushi ya saki da mata zobe da hannayensa, furzar da ƙaramar iska yay da ɗaura bakinsa kan kunenta. Cikin wata irin kasalalliyar murya mai ɗaukar amon sauti daga bututun gudun jini zuwa ƙahon zuciya ya fara fidda aman sauti “Haba autar mata kiji tausayin yayanki mana ki basa dama ya tabbatar miki ke wacece a aikace. Ko kina buƙatar sai naje ƙasa ne bayan kin gama min ɗaurin da wata ƴa mace bata taɓa yima namiji ba.”

      Kasancewar da yaren malay yake maganar babu shiri ta ɗago ruɗaɗɗun idanunta a dalilin jin furucinsa. Cikin tsakkiyar ido suke kallon juna na kusan mintuna biyu, daga ita har shi tsuma jikinsu yake kowa da abinda ke masa kaikawo a zuciya, lips ɗinta suka shiga motsawa kamar zatai magana amma sai ya hana hakan ta hanyar haɗe goshinsu waje guda. Baya buƙatar bata wani space a wannan gaɓar, dan ya tabbatar hakan zai iya zame masa kuskure wajen tsaiwar amsa ɗunbin tambayoyin daya hanga cikin idonta da bakinta.

     Duk da a zaune suke gangar jikinsu ta kasa ɗaukarsu, dole yakai kwance da ita jikinsa na matuƙar rawa da tsuma irin na an daɗe ba'a haɗuba, daɗin daɗawa kuma ango yake, a yau zai sake zuwa irin duniyar da bazai taɓa mantawa da ita ba duk da a waccan gaɓar shima ɗin ya jigatu, ya kuma wahala kasancewar na farko a garesa, a yanzu kam sai dai ya zama malamin wasu inda ana koyarwa a aji.

       Ya matuƙar rikita hankalin Anaam da wani sabon salo. Ta shiga ruɗani irin wanda baka iya banbance fari da baƙi sam. Ita yanzu ba Anaam ɗin Abie da Mamie bace, wata sabuwar Anaam ce a wata duniya da hasashe bai taɓa kaitaba koda a lissafin hange. Ita ba Anaam ɗin data ɗauka alwashin jiran cikar watanni uku bane na barin gidan Yayanta. Ita ba Anaam bace dake tuna da Yaya MM take tare. Ita ba Anaam ɗin dake tuna bayan ita akwai wata mata tare da shi ba ce, ita ba Anaam ɗin dake buƙatar ɗunbin amsoshin tambayoyinta daga garesa bace, ita ba... Ita ba... Da yawa da bazata iya tunawa ba a karan kanta balle wani tsarinta ko burinta..

     Tuni ya jima da rabata da rigar kamar yanda ya raba kansa da tasa suturar shima, ya naɗesu a cikin bargo tare da mirginawa da su tsakkiyar gadon. A daidai gaɓar da Anaam ta dawo hayyacinta kenan dan a yanzu an ɗauki wani layine daya sata zaburowa a razane ta ƙwalla ƙara da ƙanƙamesa jikinta na rawa ta fara son turesa cikin magiya da roƙo.... Da gaske baya jinta, sai dai rufewar idon tasa bata hanashi fara ambaton addu'ar da MANZON ALLAH ya horar damu karantawaba yayin ziyartar juna........


        Sosai jikinta ke ɓari, tana saki wani irin nishin kuka mai ban tausayi irin na wanda yay matuƙar galabaita da jigatuwa. Muryarta tayi ɗashewar da ba'a iya jin wani furuci daga bakinta. A hankali ya mirgino gareta, a jikinsa ya maidata ya rungume. Lallashinta yake son yayi, hawayenta yake son tsaidawa amma ya kasa. Ƙara tsuma jikinsa yakeyi da wani irin karsashi da zuciya ce kaɗai mai ajiye da wannan kundun sirrin bawai gangar jiki ko kalaman kan harshe ba. Bashi da wani zaɓi face sake matseta a cikin jikin nashi yana mai jujjuya mata kansa duk da a cikin ɗan hasken da suke na lamp bazai wadatar da idaniyar da yake da yaƙinin a rufe take iya ganinsa ba. 

    “ALLAH yayi miki albarka”.

Ya iya furtawa da ƙyar kuma a fisge yana sake matseta tamkar ya tsaga fatar jikinsa kawai ya turata ya huta. Tsahon lokaci ya kasa yanke shawarar abinyi na gaba, itako tana faman cigaba da juya kanta dake a ƙirjinsa laɓɓanta na motsawa a hankali alamar akwai abinda take faɗa da ba'aji, hawayenta masu ɗumi da zafi na cigaba da sauka a ƙirjinsa kai kace zata iya ƙarar da su ne a wannan dare baki ɗaya.

      Jin kamar jikinta ya saki ya saka zuciyarsa harbawa da ƙarfi, babu shiri ya miƙa hannu ya kunna fitilar ɗakin. Sosai firgici ya bayyana akan fuskarsa, yatsunsa biyu ya ɗaura a kan hancinta. Da gaske bata numfashi. Zuciyarsa tai wani uban tsalle tamkar zata fito waje. Kansa ya dafe da cije lips ɗinsa da ƙarfi yana ambaton sunan ALLAH. Sai kuma ya shimfiɗeta saman filo ya fara laluben abinda zai suturta jikinsa. Rigarsa ya samo da ƙyar acan ƙasa, baiko saka botiran dai-dai ba ya sauka zuwa gefen gadon. Ruwan daya shigo da shi ya ɓallema murfi, ya zuba a tafin hanunsa ya shafa mata a fuskarta dake jage-jage da hawaye. Babu alamar zata kawo numfashi. Ruwan ya gumtsa ya fesa mata a fuska. Gaba ɗayanta ta zaburo tare da jan numfashi mai ƙarfi. Da zafin nama ya tallaffota ta koma cikin tafin hanunsa, “Juwairiyya!”. 

Ya faɗa cikin sarƙewar harshe...

     Jin bata amsa ba kamar ma ta ƙara koma masa lakaf ya sake girgiza mata kai ta hanyar rike haɓarta da sake kiran sunanta cikin nutsuwa. 

    “K! Juwairiyya K!?”. 

Siririn kuka ta sakar masa, murya a ɗashe tace, “Zafi, wayyo Mamie na”.

Ta furta da ƙyar da buɗe idanunta kaɗan sai kuma ta maida ta rufe kanta na juyawa kaɗan-kaɗan.

    “Ya ALLAH! ALLAH!!”.

Ya faɗa da sake girgizatan, sai kuma ya mannata da ƙirjinsa ya ƙanƙame ya kama hanunta ya fara murza tafin cikin kulawa. Wani bahagon numfashi ta fusga azabar zafi na ƙara ratsata. Sai dai bata da ƙarfin koda ƙanƙamesa balle gane a halin rayuwa take ko mutuwa. Yasan Anaam nada raki, sannan akwai ƙarancin ƙwarin zuciya na ɗaukar wahala a tattare da ita saboda yanayin rayuwar data tashi. Ita ɗin ƴar gata ce, rainon madara da biscuits da chocolates😝, bata taɓa fuskantar makamanciyar wahala irin wannan ba a rayuwarta. Abinda ta sani kawai taci ta sha ta tafi makaranta, koda ya kama tayi wani aiki bamai yawa bane da zai tabbatar mata da ana wahala a duniya. Gashi kuma yasan baizo mata da sauƙi ba sakamakon tunaninsa shekarunta zasu iya ɗauka, bai san abun ba'a shekarun yake ba dan ƙarfin zuciya da juriyar ɗaukar wahala babu ruwanta da shekaru...


       Sabon ragwanci da raki ya ƙara ɓarkewa a toilet yayin yake taimaka mata wajen samun nutsuwa dan ya fahimci wannan itace masalaha ta farko daya kamata ya bata agaji da ita. Kuka take masa sosai irin wanda yafi na farko dan a ɗazun wahala ta hanata yin kukan. Yanzu kam saita samu damar ɓarje guminta wajen yinsa fiye da abinda takeji. Rashin ƙarfin jiki ya tilastata sallama masa dole yana jujjuyata a yanda yake so cikin ruwan zafin. Koba komai ta ɗanji sassauci, sai dai hawayeta sun gagara tsayawa dan su kaɗai ne abinda take iyayi wajen nuna irin raɗaɗin da takeji da galabaitar da rayuwarta da yayi. A cikin ruwan ya barota ya fito, ya kintsa gadon ta hanyar canja bedsheet sannan ya koma fito da ita. Har cikin rai tausayi take bashi, duk da ya fahimci rakinta ne gaba-gaba wajen sake girmama narkewar tata. Koma dai minene ai shi ya takaloma kansa tunda yasan hali. Tun yana hasashen zatai haƙuri tai shiru sai saɓanin haka ya biyo baya, dan kuwa ƙiri-ƙiri ta hanasu barci sai gabanin asuba da ɓarawon yaci galaba a kanta. Kansa ya girgiza kawai, dan bai taɓa sanin darun yarinyar nan da rikicinta yakai faɗin haka ba sai a yau. Rashin barcin da wuri ya jawo musu makara. Bai fara tashinta ba sai da ya idar da tasa sallar, abinda yake gudunne kuwa ya faru, dan rikice masan ta farayi da kuku wuwu. Haka kawai yake jin nauyi da kunyarta shi kansa, domin yasan dai magana ta ƙare tunda a daren jiya ta gama ganin ƙarshen girmansa duk da matsayin ƙanwa da take da shi a garesa. Da farko ya lallaɓata har tai salla, ganin fa bata san zuru ba ya rumtse ido cike da borin kunya ya balbaleta da masifar da bata kai ciki ba, dan da ƙarfin hali yake yinta kawai....

      “Kin isheni fa da kuka. Idan baki rufamin bakinki da kukan banzar nan ba ALLAH yagalgalaki zanyi da safen nan, dan na fahimci kukan naki harda na rashin ƙoshin dalilin yinsa...”

     Kukan ta sake fashe masa da shi tana duƙunƙune kanta cikin bargo, dan hatta muryarsa razani take saka mata a zuciya. Tsoronsa takeji mai girma da tsananin shakkarsa. Ta cigaba da hawayenta batare da barin sautin kukan na fita ba sai dai yana jin yanda take jaa da shaƙar ajiyar zuciya tamkar zata shiɗe. Tashi yay ya fita, mintuna kaɗan sai gashi da kofin shayi. Yasan halin butsutsunta, dan haka ya ɗaure fuska cikin bada umarni yace ta tashi. Duk yanda taso zama da ƙyau domin shakkarsa ta gagara hakan, dole sai jinginata yay da jikinsa zuciyarsa na raya masa akwai matsala kenan. Da kansa ya bata tea ɗin tana sha da ƙyar, ko rabi bataiba tace ta ƙoshi. Bai barta ba har sai da ta ƙara sha, ya bata paracetamol dan jikinta akwai zazzaɓi. Kwanciya yay da sakata jikinsa yana shafa bayanta, sai kuma ya sumbaci kanta dake a ƙirjinsa da ƙara rungumeta da ƙyau, cikin lallashi ya fara magana a kunnenta...

     “Kukan ya isa haka to mai tsadar tsada uhhmyim. Ko kina so a dinga kiranki raguwa ne? Jarumar mace bata irin wannan rakin da kike yi ai. Bakinki taf da tsiwa amma sai ragwantaka”.

    Kukan ta sake fashe masa dashi da son turesa a jikinta amma bata da ƙarfi, yay murmushi da sake sumbatar kanta. “Oh ashe kinada sauran ƙarfi ma na wani zauna kallonki, bara na sake komawa kawai ko zan ƙara farauto baby na uku, dan insha ALLAHU jiya dai na samar da biyu da zakiyi tukuyci da su.........✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Chapter 59

59


.........Murmushi Dr Bilkisu tayi, cikin sigar lallashi tace, “Kiyi haƙuri dubawa kawai zanyi, dan idan yazam yaji miki ciwo ne ba'a ɗauki mataki ba nan gaba zaki iya fuskantar wata matsalar da ba'a fata. Gara tun yanzu yana a ɗanyensa a ɗauka mataki kinji ƙanwata. Badan Anaam taso ba ta bar Dr Bilkisu ta duba, dan sosai ta dinga lallaɓata da nuna mata illar rashin dubawar harta amince. 


   “Ya ALLAH”. Dr Bilkisu ta faɗa da sakin rigar Anaam ɗin takai hanunta saman goshi tana murzawa. Sosai ranta ya sosu, sai dai kuma ta fahimci matsalar daga jikin Anaam ɗinne. Amma duk da haka an nuna mata mazantaka da yawa da ƙawazuci.


   A tsorace Anaam dake kallonta tace, “Doctor wajen ya daina aiki ko?”. Murmushin da babu niyya Dr Bilkisu ta saki, ta girgiza kanta da kallonta. “A'a bai daina aiki ba ƙanwata, kawai dai anyi ɓarna ne da alama angon naki tsohon tuzurune halan shiyyasa ya gagara binki a sannu. Gaskiya yayi miki ɓarna da yawa da dole sai anyi ɗinki”.


   “Na shiga uku”.


Anaam ta faɗa tana fashewa da kuka. “A'a kinga kwantar da hankalinki baki shiga uku ba. Mata da yawa sunci karo da matsala fiye da taki ma a dalilin first night, ban san mike damun mazan ba da suke muku irin wannan zuwan haka, ko soyayyace ke ingizasu oho, koda yake suma iyaye akwai laifinsu, zaka kai yarinya buduwa gidan miji amma kaita tsumata da kayan mata. Sune suke saka gushewar hankalin mafi yawan mazan har su aikata mummunar ɓarna ga yarinya, a yanzu haka inada irin cases ɗin nan da yawa ga wata can ma kwana uku kenan da mata ɗinki har huɗu kaɗan ma ya rage ita mijin ya kasheta dan a sume aka kawo mana ita tana bleeding kamar mai haihuwa” (Iyaye wlhy da gaske matsalar nan tana cutar da yaranmu, maganar mai ɗinki da bleeding ɗin nan da nake muku ya faru a gaske ALLAH har kuka naima yarinyar, amma koda aka binciki mijin iya gaskiyarsa ya faɗa cewar ya fita hayyacinsa ta yanda ya gagara jin tausayinta balle tuna ita din virgin ce, koda yarinyar ma akaji ta bakinta daga baya akan ko tasha wani abu ne bata ɓoye ba ta sanar da irin kayan matan da aka dinga ɗirka mata har ji ta dingayi kamar ta jawo auren koma ta bashi kanta kafin a ɗaura. Ya ALLAH, iyaye mata a duba dan ALLAH a gyara, ƴarki budurwa ce bata san komai ba, koda ɗan kayan fruit kika gyarata da su zuma da mazarƙwaila sun wadatar ai, sai maganin sanyi da a kullum bana gajiya da tuna muku shine mafi muhimmanci kafin kikai ƴarki gidan aure ki tabbatar bata tare da imfection yafi maganin matar nan da za'a iya cutar miki da yarinya a dalilinsu. Dan mazan da yawa sukan kasa controling kansu ne harsu fatattaka miki yarinya a banza taje yoyon fitsari ya sameta. Dan waccan yarinyar da nake gaya muku sai da yakai ko fitsari bata iyayi da kanta saida taimakon robon fitsari tsahon wasu wattani. Shin riba akaci ko faɗuwa kenan🤦🏻?).


     Kuka sosai Anaam ta dingayi har ba'ajin sautin muryarta a yayin da ake mata ɗinkin, tabbas ita din ragguwace bata wasa ba. Ko yaya abu ya sameta ta dinga raki ke nan balle wannan da ya zame mata makafin ajewa a tarihi dan bata taɓa riskar azaba makamancin hakanba. Shareff yasha tarin ALLAH ya isa da inda tarasu za'ai waje guda buhu-buhu zai ɗiba ya kaima Mommy ajiya saboda tarihi😝😆.


    Sosai ya dinga kaikawo dan yana iya jiyo kukanta da kiran Abie da Mamie da take famanyi, har da wasu a ALLAH ya saka matan da take ambata da ja masa ALLAH ya isa. Sosai hankalinsa a tashe yake dajin ɗunbin tausayinta da takaicin kansa. Da yanada damar dawo da ciwon jikinsa da yayi ko zai samu sassauci a zucyarsa, dan itaɗin wata abace mai daraja a zuciyarsa da baki ko alƙalami ƙaryarsa zanawa. Ita ke kukan amma tare suke raba raɗaɗin a zuciya. Koda aka kammala Dr Bilkisu tasa aka kaita wani ɗaki danta huta yana shigowa ta fashe da kuka wai bata son ganinsa Dr Bilkisu ta koresa. Duk da haushinsa da Dr Bilkisu keji kasa daurewa tai sai da tai dariya. “Tunda patient ɗina bata bukatar ganinka jeka abunka mun sallamaka Alhaji Al-Mustapha. Dan gaskiya kai mai laifine mai girma a wajenmu ɗin”.


   “Gutun murmushi ya ɗanyi iya laɓɓa sai dai bai fitan ba. Ya jingina da bango hannayensa zube cikin aljihun wandonsa ya zuba mata idanu. Bargo taja ta rufe har fuskarta ita a dole bata buƙatar ganinsa ɗin dai. Dr Bilkisu ta janye daga kallonta tana ƙara sakin ƴar dariya itama. Inaga ka bata dama ta huce sai muyi magana a office”.


   Kansa ya jinjina mata kawai. Ta juya ta fita. Cigaba yay da tsaiwa a wajen har bayan minti biyu da fitarta sannan yabi bayanta, har sannan kuma Anaam bata buɗe fuskar taba ɗin.
    A office ɗin doctor batare data kallesa ba ta miƙa masa takardar data gama rubutu a jiki. “Taji ciwo ne, amma mun mata ɗinki. Na fahimci cewa ƙaramin jiki ALLAH ya bata, amma shekarunta sun kai ga hakan. Sai dai kuma yanayin halittarta tana buƙatar bi a sannu, domin masu irin yanayinta zakaga ko'a wajen haihuwa ana shan fama dasu matuƙa saboda jikinsu bashi da wani ƙwarin gaske, sauƙinta ma ita tanada wannan ƙaramin jikinne, da irin raɓo-raɓo ɗin nan take akwai matsala, hakan na nufin ko anan gaba za'a bita a hankali inba hakaba kullum zata dinga shan ɗinki kenan. A yanzu dai zan riƙeta anan gaskiya har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ta samu nutsuwa yanda ya kamata saina baka ita da sharuɗɗa masu tsauri. Muna buƙatar waɗan nan drugs ɗin dana rubuta anan.”


    “Uhhim”.


Kawai ya faɗa yana miƙewa. Dr Bilkisu ta bisa da kallon mamaki, irin miskilan mutanen nan na bata tsoro, sai sun tafka tsiya ka rasa ta inda zaka auna yaya ma sukai. Kiji fa ta gama masa bayani akan kuskurensa ya bita da ‘uhhim’ kawai tsabar miskilanci. Bai san ta ɗaga masa ƙafa bane kawai saboda Dr Jamal. Amma da yaga yanda ake ruwan masifa yau, duk da kwarjininsa shima ya taka rawar gani wajen cika mata ido ko fushinta ta gagara nuna masa akan fuskarta.


    Pharmacy ɗin asibitin ya nufa domin sayo magungunan, sai da aka gama haɗawa zai ɗauka waya dan musu transfer yaji babu wayar a jikinsa, kansa ya dafe yana ambaton sunan ALLAH. Dole ya bar musu maganin akan zaije ya dawo. Ɗakin da take ya sake komawa, saboda yana son jin ko tana buƙatar wani abu. Samu yay tana barci a yanda ya suka barta, ya kai hannu ya yaye bargon data lulluɓe har kanta tare da kaiwa tsugunne gaban gadon. Duk da barci take kumburin idonta bai hana ya bayyana ba, ya saki murmushi yatsansa na kaiwa a saman idanun ya shafa, a hankali ya gangaro har saman fuskarta zuwa lips ɗinta. Yatsansa ya shiga zagayawa a kansu, kafin ya sake matsar da fuskarsa gab da tata murya ƙasa-ƙasa ya furta “Tabbas kin cika mai tsadar da tafi tsada tsada autar mata”. Ya ƙare maganar da manna mata lips ɗinta kiss


  Motsawa tai tamkar wadda ta jisa, ya sake sakin murmushi yana cigaba da kallonta. Tsahon minti biyu sannan ya miƙe tsaye, ɗan ranƙwafawa yay a kanta ya tsotsa lips din nata da sumbatar goshinta ya ƙara miƙewa. Kaɗan ya ɗalli lips ɗin da yatsansa. “Bari muga idan bakin tsiwar zai mutu”. Ya faɗa akan lips ɗinsa har yanzu murmushi bai bar fuskarsa ba....
   Duk yanda mmn Abu ta lallaɓata akan ta koma ciki ta kasa motsawa, dan haka harya dawo gidan tana a wajen zaune ita bamai rai ba ita ba sumammiya ba, har yanzu kuma su Gwaggo halima basu kiratanba. Bai shigo ciki da mota ba, dan haka har ya ƙaraso bata san da shi ba. Yay tsaye yana mata kallon mamaki ganin hawaye share-share akan fuskarta dan ma wasu sun jima da bushewa...


   “Baki da lafiya ne?”.


Ya faɗa yana kaiwa tsugunne gabanta da ɗago fuskarta daya riƙo haɓarta da hanunsa na dama. Maimakon amsa sai kawai ta sakar masa sabon kuka. Sosai hankalinsa ya tashi, dan zuciyarsa ta fara ayyana masa ko wanine ya mutu ma. 


      “Ya salam, wai mike faruwa? Wani ne ya mutu ina magana kin mun shiru?”.


   Hanunsa tai ƙoƙarin turewa zata miƙe ya maidata ya zaunar. “Fadwa....!” 


ya faɗa aɗan tsawace


   “Ni ka ƙyale ni!!”.


Ta faɗa a matuƙar tsawace itama da fisge duka jikinta ta shige ciki a fusace. 


Kallo ya bita da shi ransa na sosuwa da mamakinta, shi yarinyar nan takema tsawa wai?. Kallonsa yakai ga Mmn Abu dake tsaye kanta a ƙasa idonsa cike da matuƙar ɓacin rai. “Mi'aka mata?”. 


     “Nima Alhaji ban saniba, tun ɗazun dai na sameta tana kuka anan lokacin da zaka fita da Hajiya Amarya”.


  Ɗan jimm yay na tunani yana idonsa akan Mmn Abu ɗin har yanzu. Komai baice ba yay wucewarsa sashensa yana jan tsaki. Akan kwanikan abinci da aka ajiye ya fara sauke idonsa, kenan idan lissafinsa yayi dai-dai Fadwa taga fitarsa da Anaam shine take wannan haukar. Ƙaramin tsaki yaja da girgiza kansa kawai ya shige bedroom. Bai jimaba ya fito. Sashen Anaam yaje, ya ɗauka mata abinda za'a buƙata ya sake ficewa a gidan batare da yabi takan Fadwan ba. 
    Tun a hanya ya sayo dukkan maganin, koda ya dawo asibitin har lokacin tana barci, ya ajiye kayan ya nufi office ɗin Dr Jamal. Saida suka fito yin sallar azhar ya ɗan leƙa Anaam, har lokacin barci take, dan haka Dr Jamal yasa wata Nurse shiga ta zauna da ita saboda Shareff yace masa zaije wani waje daga nan tunda yaga ba yanzu zata farka ba....


   Barci tasha sosai, sai kusan biyu da rabi ta farka. Jinta take kamar ana mammatsa mata ƙasusuwa, ga ɗinkin da akai matan nayi mata kamar a takure babu dai daɗi. Nurse ɗin nan ta taimaka mata zuwa bayi kamar yanda ta buƙata. Harda kukanta wajen yin fitsari, wani haushin Shareff na ƙara zuwa mata a maƙoshi. A daddafe ta sake fitowa da taimakon Nurse ɗin, tai salla jiri na ɗibarta na yunwa da rashin jin daɗin jiki. Ta idar da sallar tana addu'ar ya shigo da sallama Aysha biye da shi ɗauke da basket, Aunty Mimi a bayansu. Batai niyyar ko kallonsa ba, sai dai jin muryar Aunty Mimi da Aysha ya sakata ɗagowa da sauri.........✍End of book

Leave a commentPost


Comments


106395735749763123617

Hehhee Ina masu cewa Shareef fyade ya yiwa anam to kuzo kusha kallo😂ga ruwan love


14 hours ago112061044133690897194

Karshen tonan asiri kuwa,anam taji maza,an kashe bakin tsiwan


14 hours agoumarfaruk

Mr sherif tonon asiri kayi ma Anam kenan Dama dai Aunty Mimi tace babu so Miya kawo kishi to ga so nan ya tabbata harda kwanciya a gadon asibiti


14 hours agoContact Us

Arewa Books Publishers


WhatsApp: 09031774742


Email: arewabookspublishers@gmail.com


Navigation

Home

About

FAQ's

Legal

Privacy Policy

Terms of Service

Social

Facebook

InstagramCopyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO

Chapter 60

60


.......Cikin nasa idanun suka shiga, sakamakon kallonta yake shima. A karan farko taji hakan babban abune a gareta kallon tsakkiyar idonsa tai masa koda harara ne. Janyewa tai a kasalance ta maida ga Aysha dake kallonta fuska da damuwa duk da bata san mike damu ƴar uwar tata ba. Dan ita dai tana gida ya kirata a waya wai ta ɗakko kaya kala ɗata ta fito ta samesa an kwantar da Anaam asibiti. Ya kuma mata gargaɗin karta sanarma kowa, Mommy ma tace mata zataje waje Fadwa ne. Hakaɗin tayi shine ta sami damar fitowa dan itama Mommyn na buƙatar aje mata gidan Shareff ɗin duk da tasan ba lallai ta sami abinda take so ga Ayshan ba. Amma tasan ta inda zata dinga binta tana jin koma ai. Amma sai ta kasa kallon aunty Mimi da itama kallonta take duk da bata san mike damunta ba, ya sanar mata dai kawai Anaam babu lafiya, sai dai bai son su Mamie su sani.


    Matsowa Aysha tai suka rungume juna, idon Anaam cike da ƙwalla. 


 “Blood mike damunki?”.


Ɗan satar kallonsa tai shi da aunty mimi, idanunsa ƙyam a kansu, Hawayenta ta share da girgiza mata kai kawai alamar babu komai. 


    “Blood ba'a zuwa asibiti ai babu komai, dan ALLAH ki faɗamin”.


   Katse Ayshan yay da faɗin, “Idan kinji maganin mi haka zai miki?, malama tashi ki bata abinci ban son surutu mara amfani”.


   Badan Aysha taso ba dole tai shiru. Aunty Mimi ta ƙaraso ta zauna saman kujera, gaba ɗaya Anaam ta kasa kallonta, idanunta a rissine tace “Ummi good afternoon”.


   “How are you feeling?”.


  Kasa amsawa tai sai hawaye data matso. Aunty mimi tai murmushi, “Mamana har yanzu baki san kin girma ba, shagwaɓa dai shagwaɓa dai why?” nanma batace komai ba, aunty mimi da zuciyarta ke ɗan hasko mata wani abu ta kalla Shareff, shima kansa yay saurin kaudawa gefe yana shafo bayan ƙeyarsa da hannu. “Humm” tace kawai. Itace ta taimaka mata ta koma saman gadon. Aysha kuma ta fara zuba mata abinci. Takowa yay daga inda yake tsaye ya zauna kusa da ita a gefen gadon. Jitai kamar ta makesa sai dai babu dama. Koda Aysha ta gama zuba abincin shine ya amsa, sake gyara zamansa yay yana fuskantarta da ƙyau, sai dai taƙi yarda koda wasa su haɗa ido. 


  “Ko zaki sha tea ne kafin kici abincin?”. Ya faɗa idonsa a kanta. Girgiza masa nata kan tayi, murya a shaƙe tace, “Bazanci komai ba na ƙoshi”. 


     Komai baice mata ba, ya ɗibo abincin zuwa bakinta yana faɗin, “Hahh!”. 


Sosai ta ƙwaɓe fuska, ta ɗan ɗago cikin marairaicewa tana kallonsa, sai kuma ta saci kallon gefen aunty mimi. Ganin basu take kallo ba ta ɗanji sassauci kaɗan. Kanta ta girgiza masa “Banajin cin komai ALLAH”.


   Ƙasa-ƙasa yace, “Gashi kuma dole sai kin ci! In ba haka ba kuma.....” ya ɗage mata gira ɗaya batare daya ƙarasa faɗaba. Dole badan taso ba ta buɗe bakin ya fara bata abincin da tun a ɗanɗanon farko ta gane girkin Mamienta ne. Kasa ɓoyewa tai. 


   “Yaya wajen Mamie ka amso min abinci?”.


  Kansa ya jinjina mata da kai babban yatsansa ya goge mata mai daya taɓa gefen bakinta. Sai taji kunya ta kamata kasancewar Aunty mimi da Aysha a ɗakin. Shiko babu alamar hakan ya damesa ma ya sake miƙa mata wani daya ɗibo a spoon. A haka Dr Bilkisu ta shigo ta samesu yana bata abincin, a ranta ta ayyana (Maza ga zaƙi ga harbi kenan). A zahiri kam idonta akan Anaam tana murmushi. “Masha ALLAH my patient jiki yayi daɗi”.


   Cikowa idanun Anaam sukai da hawaye, ta girguzama Doctor kanta. “Har yanzu inajin ciwo a wajen”.


  Idanu ya waro da sauri jin zatai masa fallasa, ya daura yatsansa akan lips ɗinsa alamar tai shiru, ta gefe kuma yana nuna mata aunty Mimi da ido. Sai dai kuma bai san sarai aunty mimin na kallonsu ba ita da doctor. Ta ƙunshe dariya da kyar, Dr Bilkisu dai kasa dannewa tai sai da tayi tata.


“Ayya karki damu insha ALLAHU zai daina, idan na sallameku zan baki dukkan dabarun da zasu taimaka miki har ki dawo normal a cigaba da amarci ko”.


   God forbid”.


Ta faɗa a hankali samman lips ɗinta. Da ɗan ɗagowa zata hararesa suka kuwa haɗa ido. Babu shiri ta mayar ta risinar. Har doctor ta gama ƙara duddubata bata sake yarda ta kalla sashen da yake ba dan tuni tace masa ta ƙoshi da abincin. Shima dai kunya ta hanashi sake wani motsi, dan ya san dai aunty mimi ta gama fahimtar komai kuma. Magungunnanta ya bata ta sha kamar yanda Doctor tace. Sai da ya tabbatar komai yayi normal sannan ya mike yana kallon agogon hanunsa. 


    “Small Mom ni zanje gida nai wanka bara na maidaki, inaga sai zuwa anjima zan dawo. Aysha ki kula da ita idan da buƙatar wani abu sai ki kirani a waya. Bana buƙatar wani yasan da zamanku anan, idan hakan ta faru ranki sai yafi nawa ɓaci”.


   Aysha ta amsa masa da to.


“Karka damu Babana jeka kawai harka dawo, bara naga likitar nan. Aunty Mimi ta faɗa kai tsaye tana miƙewa ta fita. (Shike nan na mutu) ya ayyana a ransa da bin aunty Mimin da kallo. Itako Anaam tuni tai kwanciyartama ta juya musu baya. Har tayi zaton ya fice sai ga saukar numfashinsa a cikin kunnenta, da sauri ta juyo dan ta tsorata, hakan ya bawa fuskarsu damar haɗuwa, ƙoƙarin jan tata tai baya ya hana hakan ta hanyar riƙota.


    _“Ina alfahari da ke a wannan rana, alfahari irin wanda zuciya bazata iya ƙayyadewa ba, hannu bazai iya zanawa ba, ke ɗin zinariya ce, idan nace zinariya ina tabbatarwa duniya zinariya a tsakkiyar duhuwar jeji, amsar itace, *Haskenki kaɗai za'a iya gani*”._ 


    Daburcewa tai, sakamakon saukar lips ɗinsa akan nata, ta shiga son ture masa fuska, amma yaƙi yarda da hakan har sai da yay yanda yake so da ita. Yana sakinta sashen da Aysha da aunty mimi suke ta fara kalla, sai dai wayam da alama ma duka basa a ɗakin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke da saurin kauda kanta saboda ido da suka haɗa da shi. Murmushi ya saki mai faɗi da yalwa dan ya fahimci catake su Aysha na a ɗakin.


   Sake ranƙwafowa yay kanta har lokacin murmushi shimfiɗe a fuskar tasa. “A ƙara ko? Nima ban ƙoshiba”.


  Ture fuskarsa tai da sauri tana jan bedsheet ɗin dake a matsayin bargo ta ƙudundune kanta. Murmushinsa ne ya ƙara faɗaɗa, ya girgiza kansa kawai da juyawa ya fice a ɗakin.
   Sallamar Aysha ta sakata sakin ajiyar zuciya, sai da taji ta zauna a kusa da ita sannan ta buɗe kanta. “Da alama dai kin samu sauƙi tunda naga Yaya ya fita yana faman murmushi”.


  (Ba dole ya fita yana murmushi ba tunda ya gama yayyagani) a fili kam sai ta taɓe baki da yunƙurawa zata tashi zaune. Taimaka mata Ayshan tayi ta zauna cikin dauriya dan ƙasanta sosai yake mata zafi zamanma dai tayisane irin na kishingiɗa ɗin nan..


  Aysha ta sauke ajiyar zuya tana kallonta, “Dan ALLAH ki kwantar da hakainki na tabbatar zaki ji daɗin zama da Yaya Shareff insha ALLAHU Blood. Yanada ƙyawawan halaye da lokaci ne zai tabbatar miki da hakan kamar yanda nasan kema kina da su. Hatta Fadwa bana son ki biye mata dan ita kanta komai na ƙiyayyarki tanayine ba'a kan tunaninta ba, tunanin su Mommy shike sarrafata tun farko, amma wlhy inhar kika jajirce sai kin ƙwace komai kuma a hankali Mommy zata fahimceki halayen banzar da Gwaggo ta ɗorata a kai duk zata ajiyesu kodan son da takema Yaya”.


   A karan farko Anaam ta saki murmushi. “Blood wannan ba magana bace ta nan, Please share kawai yanzu dai ya mutanen gidan? Ina kewarsu ALLAH kamar nai tsuntsuwa na ganni ciki”.


   “Aiko bazaki ganki ɗin nan ba, dan a gabana su Abba sukace kar Yaya ya kawoki gida sai bikina”.


   Sosai ta waro idanu waje, “Bikinki fa? Hum'um ALLAH bazan iya ba. Dana koma aiki monday zaku ganni”.


   “Hhhhh ashe Yaya zai ɓalla miki ƙafar baya kuwa”.


  (Yanzu ma ai ya ɓalla min) Anaam ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai tayi murmushi kawai....
  ★★★★
Yanzun ma daya dawo gidan bayan la'asar yaso shareta, sai dai zuciyarsa ta gargaɗesa a kan hakan dan koba komai hakkintane a wuyansa. A falo ya sameta zaune ta ƙurama tv ido. Mmn Abu na daga kitchen tana aiki dafa mata indomie dan duk yau taƙi cin komai sai tea kawai. Sai yanzu da yunwar ta cita ne sosai bayan tayi wanka ta fito falo tasa mmn Abu din ta dafa mata. Kallo ɗaya tai masa ta kauda kanta, sai dai ta amsa masa sallamar da yay ciki-ciki itama akan lips. Motsin mmn Abu a kitchen ya sashi wucewa bedroom.


   “Ki sameni a ciki”.


Shiru kamar bazata bisaba, sai raka bayansa da tai da harara ƙasa-ƙasa. Sai da taja kusan mintuna biyu sannan ta miƙe ta bisa. Tsaye ta samesa ya jingina da mirror. Taima fuskarsa kallo ɗaya ta ɗauke kanta da kaiwa zaune bakin gado. 


  “Ɗazun ina tambayarki mike damunki kin tashi kin barni saboda raini. Ina gargaɗinki da karki tsiro da wata sabuwar ɗabi'ar banza, hakan zai sa mu sami matsala da kowaccenku idan tace zata dinga kawomin raini wlhy”.


     Tasan halinsa, dan haka a hankali tace, “Kayi haƙuri”. Batare data ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla ba. 


  Duk girman laifin dakai masa idan ka bashi haƙuri yakan ɗanji sassauci ko yaya. Dan haka ya furzar da huci kawai. Sai kuma ya sake kafeta da idanun nasa. “Kina fushi da ni saboda na fita da ƴar uwarki, maimakon ki fara neman ba'asin mike faruwa kodan jimawar da kikaga munyi a waje batare da mun dawo ba. Sannan yanayin dana fita da ita a gidan nan yana nuna akwai matsala amma duk kika zaɓi ganin baƙina akan bincikawar!”.


    Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo mata. Tasa hannu ta sharesu. “Ni baca nai kayi laifi ba, amma ya kamata tunda ina a gidan na sani, a ƙalla dai an nuna inada daraja ko yayane, amma ta gabana ka wucefa Soulmate tamkar baka ganni ba saboda ka ɗauka mace a hanunka....”


   “Macen dana ɗauka matata ce, kinga hakan yana nufin babu haramci a ciki kenan, kema kuma nasha ɗaukar taki ai. Ki tsaya a laifin ba'a faɗa mikiba kawai bawai ɗaukarta ba. Sannan wannan ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zanzo ina miki magana koda kuwa laifin na miki ki maimaita irin abinda kikaimin ɗazun, bazan ɗauki wannan salon ba ga kowace”.


   Duk da maganganunsa sun ƙona mata zuciya saita jinjina masa kai kawai. Shima bai sake cewa komaiba yay ficewarsa zuwa sashensa. Har yanzu ba'a kwashe kayan abincin safen ba. Dan haka yay kiranta a waya. Tana ɗagawa ya sanar mata tazo ta kwashesu ya yanke wayar.
    Wanka yay, koda ya fito sai ya ɗan kwanta duk da barci yake sonyiba yana son hutawa dan shi ɗin kansa jikinsa duk ciwo yake masa. Ga yunwa na cinsa kaɗan-kaɗan dan duk yau bai wani ci abincin kirki ba. Lokacin da sukaje salla da Dr Jamal bayan sun fito massallaci gidan abinci sukaje. Amma sai ya kasa nutsuwar cin komai sai doughnut kawai ya ɗanci da drink. Daga nan ya nufi gidansu sai dai bai shiga wajen su Mommy ba ya shiga nasu Anaam da niyyar ɗakko Amrah ta zauna da ita a asibiti sai ya iske bata nan. Mamie tayi masa tayin abinci amma sai yace ya ƙoshi yana sauri ne, amma baiwar ALLAHr sai gata da shi ta haɗo a basket saboda tasan abincin da yake matuƙar so ne. Harda plate da drink da alama tayi tunanin office zai koma dan yace mata yazo ɗaukar wasu takardune zai koma wajen aiki. A sirrance ya sanarma Aunty Mimi suka fito tare kamar zasu cikin gida, hakan yasa Mamie bata sani ba. Abincinne ya kaima Anaam taci shiko baima cin ba duk da yana so..........✍[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_61_*........Aunty mimi ta ɗan jima wajen doctor Bilkisu sannan ta dawo, sai faman murmushi take, a ranta kuwa faɗi take (ƴan banza kukace da bakwa son juna. Yanzu kuma ina ƙiyayyar taje harda ɗinki?). A zahiri kam zama tai tana kallon Anaam daketa faman sinne kai taƙi yarda su haɗa ido sam. “Wai nikam na zama surukarki ne halan Mamana? Tun ɗazu sai wani sissinemin kai kikeyi daga ke har mijin naki wani abu ya faru ne?”. 

       Dariya Aysha ta sanya. “Ummie surukartace ke mana, ba ɗanki take aure ba”. 

   Dariya itama Aunty Mimi ta sanya da faɗin, “Bayan haka ma akwai dai wata a ƙasa ma”. Anaam ta ballama Aysha dake ƙara kwashewa da dariya harara. Sai kuma ta koma ta kwanta tare da lulluɓe har kanta tana murmushi.


       ★Da shirin tafiya massallaci daga can ya wuce asibiti ya fito. Har yayi niyyar ficewarsa sai kuma ya shiga wajen Fadwa. Samunta yay tayi alwala. Yanzu kam ya ɗanga sassauci a fuskarta, sai dai ba'a sake masaba yanda aka saba. (Idan ka biye ta matan nan baka da maraba da ball ɗin ƙwallonsu) ya ayyana a ransa. A fili kam sai ya juya kamar zai koma yana faɗi,

      “Zanje masallaci, daga can zan wuce asibiti”.

    Muryarta a dasashe batare data kallesaba tace, “Bara nai sallar sai na jiraka nima zanje na dubata”. 

  Yanji daɗi har cikin ransa. Dan haka yace, “Okay”. yana ficewa. Da kallo ta bisa, ta sauke ajiyar zuciya da taune lips ɗinta ta haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi. Batai niyyar zuwa ba, Mamanta ce ta kirata tace taje, kuma ta saki ranta duk wani fishi da takeyi ta dainashi hakan zai bama shirinsu damar tafiya yanda suke so.

        Maimakon yin sallar magrib ya shigo sai da yay isha'i, ya iske ta cikin shiri dan haka basu ɓata lokaci ba suka fito mmn Abu biye da su da abincin da Fadwa ta sakata shiryawa wanda tayine saboda maigidan. Sai dai kuma Gwaggo halima tace mata ta ɗaukesa ta kaima Anaam ɗin, itama kuma sai ta yarda da hakan tunda da wuya yace zaici a yanda yake kan dokin zuciyarnan. Shiru motar babu mai magana har suka fito daga layinsu. Ya harba motar saman babban titi. 

      Ɗan kallonsa tai ta gefen ido. Har yanzu fuskarsa ciɗin-ciɗin babu alamar fara'a, sai tuƙinsa ma yake tamkar bai san da zamanta a motar ba. Idonta ya ciko da ƙwalla ta maida kanta gefe tana ƙoƙarin haɗiyesu. A wajen masu saida fruits ya tsaya ya sayi laida biyu yasa a baya, ya kuma tsayawa ya sayi gasashen kifi shima ya saka a baya. 

    “Sorry na saki jira”.

  Kanta ta girgiza masa. 

“Babu komai”.

Bai sake cewa komai ba ya tada motar sukai gaba.

      

         ★Suna kallon film a wayar Aysha suka shigo, Aunty Mimi kuma nakan sallaya tana addu'a dan ta idar da sallar isha'i ne. Sam Anaam bata kawo a ranta ganin Fadwa ba. Sai da Aysha ta ambaci sunata sannan ta ɗago. Kallon juna sukai cikin ido. Kowanne ya janye lokaci guda. Aysha ta sauka a gadon da sauri ganin Shareff na kaiwa zaune kusa da Anaam ɗin yana nunama Fadwa kujera.

     “Kun daiyi salla ko? Da kuka zauna kallon film?”.

     “Eh Yaya munyi”

Cewar Aysha. Oganniyar kam tayi kicin-kicin da fuska sabida wani takaici taji na ganin Fadwa. A tunaninta kawai ya kwashe sirrinta ya faɗama Fadwar ne....

     Murmushi yayi da ɗan leƙa fuskar tata. “Har yanzu fushin ne autar mata?”.

       Cin dauriya da son cusama Fadwa baƙin ciki ta saki ɗan murmushi. Cikin disashiyar muryarta da tura baki tace, “Ni nace ina fushi ne dama?”.

     “Uhm-uhm fa, bayan ɗazun har ana jeramin ALLAH ya isa da juyamin baya”.

     Da sauri ta saci kallon Aunty mimi, sai taga sallama ta sake kabbarawa da alama shafa'i da wutiri zatai, ganin idon Fadwa a kansu sai ta sakeyi murmushi da ɗan kallonsa. Sai dai batace komai ba ta janye dan kallonta yake cikin wani yanayi daya saka tsigar jikinta tashi lokaci guda. Shima murmushi yayi idonsa akanta ko ƙyaftawa bayayi kamar ma ya manta Fadwa na tare da su fa a wajen, ga Aysha kuma da aunty Mimi. 

     “Kar dai a sani yarda babu komi aje can ana kuka a bayan idona. Dan naga  ke kam baki raina abin kuka”.

    Cikin ɗan tura baki tace, “Kuka ai rahama ne”.

    “ALLAH?”.

Ya faɗa cikin sigar tambaya da ƙoƙarin ɗago fuskarta.

    Murmushi tai da ture masa hannu tana kauda fuskarta gefe. Yay ƴar dariya kawai da jinjina kansa.

      Fadwa daketa ƙoƙarin danne hawayen da suka ciko mata idanu ta ɗan dubi Anaam. “Ya jiki? ALLAH ya ƙara afuwa”.

    Ciki-ciki ta amsa mata, batare data yarda ta kalleta ba. Dai-dai nan Aunty Mimi ta idar da salla, Shareff ya juya yana gaisheta. Amsawa tai da kulawa tare da duban Fadwa data ɗauke kai bata da alamar gaishetan ita. Murmushi kawai aunty Mimi tayi “Fadwa kuna lafiya ko?”.

     Yitai kamar bataji ba, Shareff ya kalleta cikin ɓacin rai a ɗan kausashe yace, “Kina cikin hankalinki kuwa? Itace zatama gaisheki?”.

       “Nagafa tana salla ne shiyyasa”. Sai ta juya tana gaisheta. Tsaki yaja mai ƙarfi, yayinda Murmushi ya suɓucema aunty mimi ta girgiza kanta kawai tana amsawa.

  Aysha kanta sai bataji daɗin yanda Fadwa ɗin tayiba. A ganinta koba komai yaci Fadwa ɗin ta danne ta amsawa Aunty Mimi cikin daɗin rai tunda har ta karya ƴancinta ta fara gaisheta, tunda ita ta kasa banbance dai-dai ta gaisheta matsayin babba gareta kuma ƙanwar mahaifiyarta. Sai dai batace komai ba saboda Yayansu. Shiru ɗakin yayi zuciyar Shareff a ɓace. Amma sai ya danne a bisa uzirin suna asibiti, sai dai yaci alwashin taka mata birki dan bazai ɗauka wannan banzan halin ba.

       Fadwan ce ta katse shirun ta hanyar tura musu basket ɗin da ta shigo da shi. “Ga abinci nan ALLAH yasa zaki iya ci, bansan a asibiti kike ba sai yanzu da Soulmate ya faɗa da an miki wanda zai fi dacewa da mara lafiyan ai”.

        Banza Anaam tai mata, sai bayan wasu sakanni tace “Ayya” a taƙaice taja bakinta tai shiru.

    Matuƙa ran Shareff a ɓace yake dan har fuskarsa ta nuna hakan, amma tsarinsa na ƙin yankema mutum hukunci cikin fushi ya sakashi yin shiru. Aysha ma kai kawai ta girgiza. dan ta fahimci inhar a haka Fadwa tace zata rayu a zaman aure lallai zata wahala. Domin fidda kishin mace ƙuru-ƙuru a ƙasar hausa tamkar gogama kanta baƙin fenti ne ga mijin dama kowa, domin al'ummarmu kanyi hukunci da zahiri ne a kowanne al'amari musamman akan kishin gidan malam bahaushe. Aunty mimi kam murmushi kawai tai ta maida hankalinta ga Aysha. 

     Anaam dai kwanciyarta tai ta juya musu baya ma, a ranta tana ayyana saita koyama fadwa hankali wlhy, dan abinda taima aunty mimi ya matuƙar sosa mata zuciya. Aunty mimi suna hira ita da Aysha shi yana faman latsa waya fuskarsa a murtuke. Sai ya kasance ita kaɗaice shiru, sai kuma hakan ya sosa mata zuciya har ƙwalla na cika mata ido, kiran wayarta da akai ne ya kawo mata sassauci ta miƙe tabar ɗakin. Anaam ta rakata da harara, amma sai gilashin idonta ya sirrantasu, juya kwanciyarta tai itama zuciyarta na tauna da raɗaɗin abubuwa kala-kala, sai dai taji sassauci a ranta a yanayin da Shareff ɗin ya nuna ɓacin ransa ga Fadwa kan abinda taima aunty mimi, tasan kuma bawai ya barta hakanan ba zasuyi mai dalili idan sun bar asibitin.

       Shigowar Dr Jamal ce ta saka fuskar Shareff sassautawa. Ya gaishe da Aunty Mimi da juyawa kan Anaam da tambayarta ya jiki sannan suka gaisa da Fadwa da shigowarta kenan. Aysha ma gaidashi tayi. Jan hanunsa yay suka fita, kusan mintuna goma sha biyar sannan suka dawo. Batare daya zaunaba yacema Fadwa ta tashi su tafi dare nayi.

      Fakar idon aunty Mimi yayi ya ranƙwafa kan Anaam ya sakar mata kiss. Zai ƙara na biyu dakai hanunsa saman ƙirjinta tai saurin buge hanun tana waro idanu waje harda ƴar zaburarta. Tsaye ya miƙe yana dariya, sai ko suka haɗa ido da aunty Mimi. Juyawa yay da sauri ya fice yana cigaba da dariyarsa.....


*_WASHE GARI_*.


           Sai wajen takwas yabar gidan zuwa asibiti batare da yabi takan Fadwa ba, tun da suka baro asibiti jiya suke tafka rigima da ita, dan kuwa ya mata tatas akan abinda taima aunty mimi, ya kuma tabbatar mata inhar ta ƙara sai ya mata abinda bata taɓa zato ko tsammani ba daga garesa.

      Gargaɗinsa ya sakata kwana kuka, ta kira gwaggo halima kuma ta hanyar wayar mmn Abu data kira wayar cikin masu aikinsu aka haɗata da maman, zayyane mata komai tayi, suka haɗu sukaita zagin su aunty Mimi wai asiri ne ke cin Shareff ɗin. Amma zata ɗauka mataki ta saurareta.

 

   Ya iske Anaam ɗin na toilet tare da Dr Bilkisu tanayi sit bath. Yana iya jin rakin da take zubawa daga nan, ya girgiza kansa kawai da kaiwa zaune a bakin gadon yana murmushi. A haka Aysha ta shigo hanunta ɗauke da flask ɗin tea. Gaisheshi tayi, ya amsa yana kallon flask ɗin.

     “Daga ina?”.

“Yaya gidan Dr Bilkisu mukaje amso ruwan zafi anan cikin asibitin”.

  Bai sake cewabkomai ba akan hakan. Itama saita ajiye flask ɗin. 

    “Kunyi barci dai babu wata matsala ko?”.

  “Eh Yaya. Ai da yake a magungunan nata kamar akwai masu saka barci harma makara tayi sallar asuba.”

       Bai samu damar bata amsa ba suka fito Anaam na tafiya da ƙyar. Suna haɗa ido ta dalla masa harara dan duk wannan dai bala'in shine yaja mata ai. Shi dai kallonta kawai yake murshi na neman suɓuce masa, tana tafiya kamar wata ƴar kaciya. Doctor ce ta katsesa daga kallon nata. Ya ɗauke kai suka gaisa. Baƴani ta ƙara masa na cewar zatama sallamesu amma sai zuwa anjima kaɗan dai haka akwai abinda zata ɗan jira a kawo mata da zata bama Anaam ɗin. 

    A taƙaice ya mata godiya yana maida hankalinsa ga Anaam daketa faman sauke ajiyar zuciya daga kwancen da take ta juya masa baya. Tai musu sallama ta fice tana faɗama Aysha taba Anaam ɗin abinci amma ta fara da tea mai zafi. Kamar jiya dai koda Aysha ta haɗa abincin shine ya karɓa. Cikin bada umarni yace ta tashi zaune. Taso sharesa, sai dai a yanda yay maganar ya tilastata tashi dole bakinta a sama. Yi yay kamar bai ganta ba. Ya miƙa mata shayin ta amsa kamar zata fasa ihu. Sai da ta gama shanye tea ɗin tas sannan ya miƙa mata abincin, amma sai tace ta ƙoshi. Bai saurareta ba ya fara ɗiba yakai bakinta, ta kalesa kamar zatai kuka. 

     “Nifa Yaya nace na kos...”.

  Ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya wulla mata cikin tsakkiyar ido. Idanunta ta lumshe tsigar jikinta na tashi, dole ta buɗe bakin ya zuba mata. A dai-dai nan Dr Jamal ya shigo. Da alama ma shigowarsa asibintin kenan. Sun gaisa ya tambayi mai jiki, bai jimaba ya fita yanama Shareff dariya da shaƙiyanci da ido. Bai dai kulasaba shi dai.


      Karfe kusan sha ɗaya aka basu sallama. Zuwa lokacin yaje office ɗin Dr Jamal ya dawo. Aysha ta tattare kayansu shi kuma ya kama Anaam ɗin da taso botsare, sai dai ya hana hakan ta hanyar tabbatar mata zai ɗauketa. Dole ta nutsu tana tura masa baki. Yay murmushi kawai da sumbatar wuyanta. Mintsininsa tai ya dafe wajen yana ɓata fuska shima. Sai ta saki dariya da masa gwalo.........✍*😝😜Za'a koma filin wasa🚴🏼*

        

_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Menu

Dashboard

My Library

Create Story

Home

About us

FAQ's

Privacy Policy

Terms of service

Logout


BABU SO

Chapter: 63


Share:


Report


BABU SO

View: 432


Words: 2.3K
Chapter 63

63


.........Tsaf ya shanye jambakin, zaune takai tana sauke numfashi, shima barin wajen yay da ɗan hanzari, tanaji ya buɗe toilet amma bata iya ta ɗago ba. Babu jimawa ya fito da alama wata sabuwar alwalar ya sakeyi. Ƙofa ya nufa batare daya yarda ya sake kallonta ba yana faɗin, “Ki tashi kiyi salla”.


    Iska ta furzar mai ƙarfi da dagowa tana kallon kanta ta cikin mirror, sai kawai ta samu kanta da kai hannu ta shafi lips ɗin nata da sakin murmushi. “Fitinanne”. Ta faɗa a hankali tana mikewa. Itama alwalar ta ɗauro, bayan ta gabatar da salla samun kanta tai da komawa gaban mirror ta sake gyara fuskarta da ƙyau cikin simple kwalliya. Kwalli, lipstick ɗin daya saka mata ta ɗan gyara girarta siririya da ƙara powder. Ita a karan kanta sai da ta tsaya kallon kan nata dan wani ƙyau taga ta kara, tai guntun murmushi da ɗaukar turare ta ƙarama jikinta..
     Ana idar da salla ya dawo gidan, saboda makara salla daya nema yi bai shiga sashen Fadwa ba ya wuce, yanzu kam daya dawo sai ya fara nufar can, wannan ƙa'idarsace, akowace salla in har yana gida sai ya tabbatar da mace tayi hankalinsa ke kwanciya, ko yana office yakan ƙokarta ya kira domin tambayar kinyi salla, hakan ya ƙara ƙarfafa Fadwa domin waya takan ɗauki hankalinta ta kasa tashi yin salla akan lokaci kafin zuwanta gidansa matsayin mata. A bedroom ya sameta ta idar da salla fuskarta duk babu walwala. Ya ɗan tsura mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙaraso ciki sosai. Sau ɗaya ta kallesa ta janye idonsa da masa sannu ciki-ciki.


   “Wani abu ya faru ne?”.


Ya tambaya a maimakon amsa mata sannun da tai masa. Batai magana ba, sai dai ta sake ɗan tsuke fuska. 


  “Nasan kin jini fa”.


Kamar bazatai magana ba sai kuma ta ɗago idanunta dake tara ƙwalla tana kallonsa, “Soulmate karka juyamin baya dan kayi aure, maƙiya zasu iya yimin dariya”.


   Mamaki shinfiɗe akan fuskarsa yake kallonta. “Juya baya kamar ya? Anyi wani abu ne?”.


   “In ma ba'aiba ga hanyar yi nan an ɗakko ai. Tunfa da matarka ta dawo gidan nan yau baka sake leƙoni ba, kana ganin hakan adalci ne? Yaufa ko zuwa kacemin na tashi nai salla bakayi ba, kuma tun ɗazun kana'a sashenta ita dan daga can ka wuce massallaci, gaka nan harda canja kaya alamar yin wanka”.


  “Dama kin saka a ringa miki gadina ne? Ko kuma shiga sashen nata ma akwai wata ƙa'ida ta mintunan da zanyi na fito? Ni da matata kuma kina tuhumata dayin wanka kamar wanda ya ajiye wata karuwa”.


    “Niba haka nake nufi ba, amma dai koyaya ai sai kana adalci. Jiya yini guda kuna tare a asibiti, hakama yau tun fitar safe da kai kuka dawo tare kana a sashenta”.


 Sosai ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa, idanunsa daya tsareta da su har suna canja launi. “Okay ke da sokike na watsar da ita kenan a asibitin nazo na tare a wajenki bayan nine sanadin zuwanta can. Ko kuma dan kar ranki ya ɓaci bazanyi wanka a sashenta ba?. Look Fadwa idan kikace zaki ɗaukemu zuwa wannan layin bazaki taɓa shan lalai a wajena ba. Idan kin manta bara na tuna miki, Juwairiyya matata ce, idan yanzu na shiga inda take ta rayamin kasancewa da ita zan samar da wannan farin cikin nai wanka na fito koda anjima hakan zai ƙara bijiromin idan ma wannan kikema zagaye-zagaye zargin nayi. K da ita duk abu ɗaya kuke a wajena, ina fatan kuma tsaida adalci akan kowaccenku. Duk wacce take da wani tuggu nason rinjayata gareta ita kaɗai na cutar da ƴar uwarta ALLAH ya hanata wannan damar ko wacece a cikinku. Abu na ƙarshe dazan gaya miki shine daga yau ki sani *_Ina son Juwairiyya!_* bawai cushenta akai minba kamar yanda na fahimci ke tunaninki ke kaiki. Yanda na aureki domin so bisa jagorancin iyaye haka itama na aureta, kuma koda ace iyayenmu basu ɗaura mana aure ba ni da kaina *_Zan nema aurenta_*, dan hakan burina ne, hatta wannan gidan da sunanta aka ginashi itama, kema shaidace tunda sashe biyu kika tarar. Kinga sai ki sakama zuciyarki salama, ki nisanta kanki da zama mai fuska biyu a gareni, dan bazan daina kasancewa da ita ba domin farin cikin. Sannan ita bata taɓa nuna damuwa da kasancewata a wajenki ba abinda ke gabanta takeyi, mtsoww stupid har kina faɗamin wai na dinga adalci”. Ya juya ya fice a fusace.


   Da gaske Fadwa tayi mutuwar zaune tun fara maida mata raddi da yayi, ga wata irin zufa dake jiƙa duk sassan jikinta sharkaf. Buga ƙofar da yay da ƙarfi ya sata zabura ta dawo hayyacinta, rawa lips ɗinta suka fara alamar magana take sonyi amma taƙi fita, sai kuma ta mike zumbur tana rarumar wayarta ta kunna fitila duk da kuwa ɗakin akwai hasken wutar nefa. Tabbas maganin data zuba ɗin gashi nan, sannan ya taka kuma ai kamar yanda Aunty Safarah da Mama suka tabbatar mata idan ya taka babu wani magana da zatai ya musa mata. Hakama zoben da suka bata na mallaka har biyu gashi a hanunta, sun kuma tabbatar mata mata da yawa suna rububin saya kuma yana aiki akan mazajensu. Mi (hakan ke nufi?) ta tambayi zuciyarta ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri idonta ƙyam akan zoben mallakar dake a yatsanta tana murzashi da tunanin ko batayi dai-dai bane ɗazun daya sshigo. 


    *_(Mata ku daina ruɗar da kanku da wannan zoben da kuke saya, wai miyasa munada ilimi amma basirarmu ke toshewa akan kayan matane?. Kwanaki nai wata baƙuwa, kamar wasa muna hira sai aka kai har kan illar shaye-shayen maganin mata da wasu mata suka maida tamkar ibada a rayuwarsu har ana ribatarsu da su ana basu kayan tsubbu a zuwan maganin mata kamar dai fadwa. Sai kawai take bani labarin ai wani zobe ma ya shigo wai na mallaka. Ana saidawa dubu uku har sama da haka. Ban ɗauka abin serious ba sai a wajen wani taron suna. Hhh abin dariya, mu anan yankin ma tsabar dukan hancin da akema mata zoben ana saida musu ne a 5k 6k 7k har 10k idan aka tabbatar ke hamshaƙiya ce, kunsan kuma su wannan manyan matan sunfi son ace abu nada kuɗi mai yawa sunfi bashi daraja. Humm abin mamaki wai sai ga mata na mugun rububin zobe kamar ƙiftawar ido ya ƙare, har wasu na shiga damuwa basu samu ba. 🤦🏻haba mata mi muke son mu zama ne wai dan ALLAH? Shin wai mallakar nan mizata amfana miki? Nasan kowace mace tana so mijinta ya sota ya kuma ƙaunaceta, amma sai nakega akwai hanyoyi masu ƙyau da zakibi shi namiji ya soki domin ALLAH. Sannan ku fahimta da ƙyau wlhy namijin bahaushe komin son da yake miki da wahala ya lalace a jikinki koda yaushe kamar wasu a cikin ƙabilun nan. Ɗabi'ar da suke nuna mana kuma ba itace rashin so ba, dan kinga mace na nanaye a media da miji bashike nufin ita ƴar gata bace, dan kinji mijin novel ya lalace jikin mace karki ɗauka dole naki mijin sai ya kasance a haka ki yarda yana sonki. Wani abun ana sakashine kawai dan nishaɗi. Mu kiyayi zantuka ko labarai ga ƙawayenmu su gidajensu kaza kaza ta yanda hankalinki zai tashi kiga gazawar mijinki, wlhy koyaya mijinki yake sunansa jan gwarzo, idan kika nutsu yanada tasa baiwa da kalar soyayya da farin cikin da yake baki kema ba sai lallai irin wancan da kike hange ba. Idan kina cikin wani ƙunci a gidan aurenki ki ɗauka harabawace ke kuma bautar ALLAH kikeyi sakamakonki nagaresa, idan kikai haƙuri sai ya sakaki a aljanna. Amma mu kiyayi zurmawa akan shaye-shayen magungunan matan nan da bamusan kansu ba suzo suna mana illa a banza a wofi, su kansu wasu a cikin masu saidawar basu da ilimi a kansu bamu kawai sukeyi. Ki samu mai inganci wanda kika yarda da hadinsa da mai saidashi ki saya kisha gwargwado bata yanda zaki saka kanki a dana saniba kizo kina jama kanki illa da kwasar imfection a banza a wofi. Kuyi hakuri masu magani nasan akwai nagari acikinku dan kowane sana'a akwai na kwarai akwai na banza. Masu na banzar suke bata na kwarai da disashesu akasa ganinsu a idanun al'umma. amma dan ALLAH mata a kiyaye, zoben nan da sayensa gara ki samu kazarki kici tai miki amfani babu abinda ke tattare da son zuciya dake zama ɗorarre).
    Sashensa ya nufa rai ɓace, ya zube a falo yana cigaba da jan tsaki, shi ya rasa mike damun waɗannan yaran, musamman ma Fadwa, dan Anaam ita kai tsaye take abunta bata iya ɓoye-ɓoye ba. Kuma tunda ya santa haka take, tunda ko'a shigowarta gidan nan ya hukuntata sau da yawa akan yima Fadwa abu amma hakan bai hana ta ƙara gobe a zahiri babu wani ƙumshe-ƙumshe. Itako Fadwa yau ta nuna ita mai kirki ce, musamman idan da Anaam a waje, anjima ya sameta tana baƙin rai da ƙananun magana akan Anaam kaza-kaza. Ya rasa mike damun tunaninta, shi kuma ya tsani wannan banzan halin dan yana kamanceceniya dana munafukai. Ƙwafa yay mai ƙarfi, a ransa yana ayyana zaima tufƙar hanci....
    ★★★
 “Blood zan baki wata shawar dan ALLAH ki fahimceni”. Aysha ta faɗa tana direma Anaam plate na abinci data dafa musu a gabanta. 


   Wayar da take latsawa ta ajiye, da maida hankali ga Ayshan. “Tofa shawarar mi kuma blood?”.


 “Ta zamanki a wannan gidan. Na fahimci gaba ɗaya a haguggunce kike, sai dai na miki uziri domin rayuwace da baki saba da ita ba kuma baki santa ba. Kin tashi a rayuwar da kowa yana komai akaran kansa kuma kai tsaye batare da wani munafunci ba ko boye-boye, dolene a wannan gaɓar kisha wahala sai dai nai alƙawarin bazan bari hakan ta faru ba. Blood daga yanzu dan ALLAH komi Fadwa zatai miki ki daina nuna ƙinsa a gaban Yaya koda ace bai miki ɗin ba, domin na fahimci da wannan makamin take amfani wajen kai miki duka a tsakaninki da Yaya. Ki duba ranar yanda ya nuna jin haushinsa akan abinda kikayi, wlhy ina ganinta sanda take murmushi, hakama yau da muka dawo, dan munafunci hardafa rakomu nan”


  Murmushi tayi da ɗaukar spoon ta fara cin abincinta dan tafi son cinta da zafi. “Amma blood ban katseki ba, miye amfanin kwaikwayon halin wani bayan hanyace mara ƙyau, ɓoye ƙinta kamar yanda take ƙina bashine zaisa na birgeta ba ko shi na birgesa. Tsakanina da ALLAH idan nace zan zauna shanye haukar wannan matar zan kamu da ciwon hawan jini, nafi yarda da kamun na maka a wuce wajen dan nasan itama munafunci kesata yimin wani abun”.


   Sallamarsa ta tilasta Aysha haɗiye abinda tai yunƙurin faɗa, dole ta juya tana amsa masa. Anaam kam kallo ɗaya tai masa ta ɗauke. Shiko kasa ɗauke nasa idon yay a kanta, ko sannun da Aysha tai masa hannu kawai ya iya ɗaga mata. Kujerar dake facing Anaam ya zauna. Hakan yasa Aysha miƙewa a ɗan ɗarare tace, “Yaya a kawo maka abincin?”.


   Abincin ya kalla na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe daga inda yake ya koma kujerar da Anaam ke zaune kasancewar 2sitter ce. “Bara naci kaɗan anan kawai”.


  Cikin jin daɗi Aysha tai murmushi, Anaam kuwa ɗagowa tai idanu a ware tana kallonsa, ya ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya yanda Aysha bazata lura ba, da sauri ta kalli sashen da Ayshar take, sai dai ita hankalinta ma ba kansu yake ba. 


     Spoon ɗin hanunta ya zare da sakin guntun murmushi, yana motsa lips ɗinsa a hankali alamar akwai abinda ya faɗa. Batai tunanin da gaske yake ba, sai ganin ya ɗiba yakai bakinsa tayi. 


  “Wai da gaske kakeyi?”.


Ta faɗa cikin magana ƙasa-ƙasa dan kar Aysha taji tana waro masa idanu da ƙyau.


     Shima ƙasa yay da muryar tasa cikin kwaikwayonta da kashe mata ido yace, “Bayan wannan zahirin kina buƙatar ganin wani ne?”.


  Idanun ta ƙara warowa sosai “Are you ok?”.


 “I'm not...”.


Ya bata amsa a taƙaice yana danne dariyarsa dan da gaske tayi bala'in diriricewa. Tsabar son ƙureta abincin ya ɗibo yakai bakinta. Da sauri takai hannu zata kare. “Idan kikaƙi amsa ALLAH cak zan maidoki jikina sannan na baki wanda na tauna a bakina kuma a gabanta harda tsotse lipstick ɗina”.


    Yanda ta saki baki da hanci tana kallonsa ya sashi dungure mata kai yana murmushi, tana buɗe baki da nufin yin magana ya juye mata shi. Dole tai saurin rufe lips ɗinta dakai hannu ta kare bakinta. Dai-dai nan Aysha da ta wuce kitchen batare da sun sani ba ta dire babban tray data shirya abinci kamar yanda akema kowanne magidanci a saman centre table ɗin gabansu. Lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya, Anaam ta kalleta shiko ya fiske fuskarsa na komawa normal kamar ba shine ke murmushin ba.


    Aysha na ƙoƙarin barin falon Anaam tai saurin faɗin, “Blood ina kuma zaki? Kizo muci abincin mu”. Da sauri Aysha ta shige bedroom ɗin baƙi kamar ma bata jita ba. 


  “Yaya ka gani fa ka koreta?”.


“So take ki samu ladan da mata ke samu kema, tunda garden ɗina kin haɗa baki da doctor ɗin can kar naje barruwa.”


  Maganarsa ta farko kawai ta fahimta. Dan haka cike da basarwa ta bashi amsa. “Matarka ai tana dafa maka ta samu ladan, kaga ya wadatar da kai ai”.


    Shima fahimtar hakan ya sashi juya harshe zuwa yaren Maley.


 “Ke minene naki sunan?”.


   “Kanwarka kaima da kowa an sani”.


    “Really?”.


  “Yap!”.


“Idan suka ganki da tsarabar furen garden sai su cireni a jerin Yayun naki ai ok”.


   “Kai ka san wani garden Yaya”.


“Kema kin sanshi sai dai ƙari. Ni fa janbakin nan ya tsolemun ido a bani na shanye kayana k......”


  Abincin data ɗebo ta juye masa a baki kamar yanda yay mata shima ɗazun, dole ya haɗiye sauran maganar itako ta shiga ƙyalƙyala dariya dan lauma babba ne........✍Next Chapter


Leave a commentPost


Comments

No Comments posted yetContact Us

Arewa Books Publishers


WhatsApp: 09031774742


Email: arewabookspublishers@gmail.com


Navigation

Home

About

FAQ's

Legal

Privacy Policy

Terms of Service

Social

Facebook

InstagramCopyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io


63

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO

Chapter 62


.........A waje suka sami aunty Mimi tare da Dr Bilkisu. Khaleel ne yazo ɗaukarta ita gida zata wuce. Anaam ta shiga zazzame jikinta a nasa amma yaƙi sakinta har sai da ya sakata a mota. Ya ranƙwafo zai sumbaceta ta kauce tana faɗin “Kai yaya wai bakajin kunyar aunty mimi”. 


   Kai ya kaɗa mata da lumshe idanunsa “Ƴar kaɗan”.


 “Kake jin kunyar tata?”. Ta tambaya cikin sigar waro masa idanu. 


“Eh mana ba mamata bace. Ba buƙartar na ɓoye mata muhimmancin autar mata ai”.


    Rufe fuskarta tai da tafukan hannayenta tana murmushi. “Ni dai babu ruwana”


  Murmushi yay da sumbatar kunenta. Ƙarasowar Aunty Mimi wajen ya sakashi ɗagowa. Sai lokacin takejin batare da Aunty mimi zasu tafi ba. Fuska ta kwabe da rokonsa zatabi aunty mimi ama yaki. Sai kawai ta kama hawaye.
   ★Shiru babu mai magana a motar har suka iso gida. Har mai rake ta gani tana so amma ta gwammace tai haƙuri da tace ya tsaya ya siya mata. Itace ta fara fita a motar tun kafinma ya kashe, daga shi har Aysha suka bita da kallo. A ransa ya ayyana (Ni nasan maganinki yarinya).


  Aysha ce ta kwashi kayansu, a dai-dai lokacin Fadwa ta fito daga sashenta dama tana laɓe duk tana kallonsu tun shigowar motar gidan. Tayi ƙyau cikin kwalliya sai baza ƙamshi ake. Tai masa sannu da zuwa Aysha ta gaisheta. Itace ta taya Ayshan kwashe kayan zuwa sashen Anaam ɗin. Sun sameta kwance cikin kujera ido a rufe kamar mai barci, kuka take son tayi akan hanata bin aunty mimi amma yaƙi ya fito, shine tai luff a wajen zuciyarta na suya. Sallamarsu baisa ta buɗe idanun nata ba, har sai da Fadwa tace mata ya jiki. Ciki-ciki ta amsa mata, Fadwan ta nuna kamar bata damuba ta sake mata addu'a sannan ta fice.


   Aysha datai tagumi ta girgiza kai kawai. Tashi tai ta fara gyaran sashen duk da bawani datti bane ba. Harta kammala da falo ta koma bedrooms Anaam na'a wajen kwance, Shareff kuma bai shigo ba. Ayshar ce bayan kammala aikin nata ta fito tace mata ta tashi taje tai wanka ga ruwa can ta haɗa mata. Batare data tanka mata ba ta miƙe. “Ki fara shiga ruwan zafin kamar yanda doctor tace.”


  Kanta kawai ta jinjina mata tai shigewarta. Aysha ta bita da kallo cikin tausayi, dan ita tausayi take bata, saboda ta fahimci abinda Anaam ɗin ke gudu danta jigata a matuƙa a hanun Yaya Shareff ɗin.


  Shigowarsa ce ta katse mata tunani, yabi falon da take bazama turare da kallo, sai dai baice komai ba yakai zaune.


   Burner ɗin Aysha ta ajiye da nufar kitchen, babu jimawa ta dawo ɗauke da ruwan. Zata zuba a kofi ya karɓa goran ruwan, murfin kawai ya buɗe ya kafa kai. Bai ajiye ba sai da ya shanyesa tas, da alama ƙishin yakeji dama. Sai lokacin yace, “Tana ina?”.


  “Tana ciki yin wanka”.


Ƙofar ya kalla na wasu ƴan sakanni, sai kuma ya miƙe. “Ki shirya zuwa anjima saina maidaki gida”.


  Da to ta amsa masa. Shi kuma ya shige corridor ɗin bedrooms ɗin Anaam. Tana faman ƙunƙunin ruwan da Aysha ta zuba mata na sit bath yayi zafi da yawa ya shigo, cikin sauri ta juyo kuma a rikice dan babu komai a jikinta. Daburcewa tai gaba ɗaya tama rasa ina zata saka hannu ta rufe, yi yay tamkar bai ganta ba, ya ƙaraso cikin toilet ɗin. Ruwan da take sirkawa ya sakama hannu, ya ɗago yana kallonta. Juyar da kanta tai gefe da ƙara tsuke fuska. 


   “Humm” 


Kawai yace ya fara ƙara ruwan zafin. 


 “Yayi zafi fa da yawa”.


Ta faɗa da sauri kamar zatai kuka. Dai-dai nan ya ɗago dan ya masa yanda yake buƙata, da sauri ta yunƙura zata fice ya damƙota, ƙoƙarin ture hanunsa ta shigayi tana wani ciccijewa ita a dole bata wasa bace. A karon farko ya saki murmushi, hannun nata ya saki ya damƙe towel ɗin, ta ɗago a matuƙar firgice tana kallonsa. Ido ɗaya ya kashe mata da cije gefen lips ɗinsa shima, dole ta kauda kanta dan salon nasa saida tsigar jikinsa ta tashi. Matsota yay tare da ranƙwafowa bakinsa saitin kunnenta. 


   “Bakin ya mutu ne ƴammata?”.


Fuskarta ta sake kaudawa gefe da son ƙwace hanunta. Sai kawai jitai ya since towel ɗin nata. Ruɗewa tai, tai ƙasa zata duƙe ya ɗagata cak ya dire a ruwan zafin. Azabar data ratsata ta zafin ruwan ta sakata sakin ƙaramar ƙara mai kama da kukan shagwaɓa. Matso da fuskarsa yay gab da tata, saukar numfashinsa akan tata fuskar ya sata ɗan buɗe idanunta dake rufe, dai-dai lips ɗinsa na sauka kan nata, sai kawai jikinta ya hau rawa. Ya cigaba da binta a wani salo daya saka jikinta saki lokaci guda, sai dai bai samu haɗin kanta ba kamar yanda yake buƙata. Bai damu ba ya cigaba da sarrafata a hakan tunda dai saƙonsa na isa kamar yanda yake buƙata. Nisan tafiyar ya sakata tuna azabar da tasha a daren shekaranjiya, ga gargaɗin doctor na ta kiyaye har sai ciwonta ya warke. Kota warke ɗin ba buƙata take ba balle yanzun. Laushin da gaɓɓansa sukai ne ya bata damar janye jikinta, ta miƙe zumbur jikinta na ɓari. Bashi da zaɓin daya wuce shima miƙewar, ta nane da bango tana girgiza masa kai ganin ya ɗago idanunsa da sukai matuƙar canja launi yana zuba mata.


   Hannayensa duk biyu ya dafe da bangon tana a tsakkiyarsa. Ƙasa tai da idanun nata da sauri tana ƙara damƙe towel ɗin data fisga tun miƙewarta ta suturta jikinta. Ƙasa ya farayi da hanun damarsa a hankali har zuwa kan makunnar shower, sai saukar ruwa kawai taji a kansu a bazata harta ɗan tsorata babu shiri ta ɗago, bazata iya jure kallon cikin idanunsa ba, dan wani irin al'amari daya girmi ƙwanyarta take hangowa a cikinsu da har suke neman sare ƙarfin gwiwarta, faɗawa tai jikinsa kawai ko hakan zai bata nutsuwa. Haka yake buƙata dama, ya saki ɗan murmushi da naɗe hanunsa duk biyu a bayanta ya rungumeta ruwan na cigaba da sauka a kansu. Kusan a tare suka saki nannauyan numfashi, cikin dabara ya janye towel ɗin da taketa faman riƙo yay ƙasa da shi, tsam ta matsesa dan bata buƙatar ya ganar mata jiki. Murmushi mai ƙayatarwa ya sake saki da ƙara matsetan shima yana saki wasu zafafan ajiyar zuciya a jere....
    Gaba ɗaya ya ƙulleta da kunya, tai wuff ta fara fitowa daga toilet ɗin da alama bakin tsuwar dai ya mutu, sai dai ko gaban mirror bata kai ba shima ya fito. Tana ƙoƙarin ɗaukar hijjab dan tasa ya riƙesa, saman gado ya wurgasa tareda ɗaura mata towel ɗin hanunsa saman kai ya fara tsane mata jiƙaƙƙiyar sumarta. 


   “Har yanzu fushin ne dai baki huceba?”.


  Tayi kamar bata jisa ba, sai dai taɗan saci kallonsa ta gefen ido fuskarta a kwaɓe. 


  Ya ɗan ɗalle mata lips. “Nifa bana son shariya”.


Bakin ta dafe da janye hanunsa da towel dake saman kanta zata bar wajen. “Ni karka sake kulani, kuma matarka ta daina shigomin sashe ban son gulma. Kuje can ku ƙarata kuma cinye kanku tsabar son kai”.


   Dariya sosai taso kufce masa, amma yay ƙoƙarin dakewa sai dai murmushinsa ya ɗan bayyana. Shima ƙarasawa yay gaban mirror ɗin inda takai zaune saman stool tana ƙoƙarin zuba mai a hanunta. Ta bayanta ya ranƙwafa tare da ɗaura kansa a wuyanta ya dafe duk hannayensa akan katakon mirror ɗin. 


   “Mi matata kuma tayi? Ko zaki huce haushinnne a kanta. Faɗamin, wai *_BABU SO! MIYA KAWO KISHI?_*”.


  Dakatawa tai daga shafa man datai niyyar farawa, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi suka haɗa ido ta cikin mirror. Da sauri ta janye nata tana cuna baki gaba. “Yaya kaima kasan SO ɗin da kishin. Da zaka rarrabe munma wlhy dana biyaka”.


    Murmushi ne ya sake suɓuce masa, yasa hannu ya karɓe man hanunta ya ajiye, sake ƙoƙarin ɗauka tai ya riƙe hannun. Dole ta ɗago tana kallonsa, hakan ya bashi damar da yake buƙata, ya sarƙe idanunta a cikin nasa yanda ya tilasta mata tsaiwa suka kurama juna ido, kallon juna suke irin na tsakkiyar idon nan mai ratsa jinin jiki da bargo ya sunce duk wani ƙwarin laka da jijiyoyi. A hankali lips ɗinsa suka fara motsawa...


    “Kin tabbatar idan na rarrabe mikin zaki biya ni?”.


  Da wani salon zamtowarta jiki a kasalance ta janye idanunta a slowly, shima janye nasan yay da wani salon lumshewa da buɗewa tare da miƙewa da ƙyau ya juyota suna fuskantar juna saboda kujerar na juyawa.


  “Yayaaaa!”.


Ta faɗa a shagwaɓe.


 “Yayoo”.


   Ya bata amsa da sake ranƙwafowa akanta tamkar ɗazun, banbancin kawai yanzu suna fuskantar junane. Turashi ta ɗan farayi amma ko gezau, sai ma hanun daya riƙe ya ɗaura saman fuskarsa daga gefen kunne. “Idan kin isa kalla cikin idona ki maimaita abinda kika faɗa”.


    “Ba buƙatar haka ai Yaya tunda nasan kaji. Aysha fa na gidan nan, kaima kuma matarka nacan na jiranka”.


  “Uhmm Madam pretender ke kuma budurwa tace ko?”.


  “Hu'um nayi me da kai? Kamun tsufa”.


     “Yanda kikai dani daren shekaranjiya mana”.


   Janye hanunta tai da ƙoƙarin juyawa tana faɗin, “Kai dai ka sani”.


  Yanzu kam ƙaramar dariya ya saki mai faɗi da miƙewa sosai akan ƙafafunsa. Yitai kamar bata jisa ba taci gaba da shafa manta yana kallonta kamar ya samu tv. Saukar kiran salla a kunnensu ya sakasa kallon agogon ɗakin, ya ɗan furzar da numfashi dan yasan sai ya sake sabuwar alwala.


   Binsa tai da kallo ta gefen ido, yana shigewa ta taɓe baki da miƙewa tana magana ƙasa-ƙasa. Kaya ta saka sauri-sauri kafin ya fito. Tayi ƙyau sosai dan ƙanan kaya sun zame mata jiki matuƙa, har takai komi ta raɓama ɗan jikinta sai ka ganta kamar ka sace. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa, dan ya tabbata ya cigaba sunan alwalarsa karyayya again. Ita bama tasan yanai ba, powder take ɗan shafama fuskarta da ɗan lipsgloss, dan ko kwalli ba sakawa take ba sai Mamie ta tsaya a kanta. A ransa yake raya da kwalliyar tafi haka daya so, sai dai yasan ita ƴar darun tasa a wajenta hakan normal ne. A haka ɗinma tayi ƙyau sosai. 


   Ita ko sanin kaya yake canjawa yasa taƙi juyowa, harya gama shiryawa cikin wandon jeans blue da pitch shirt mai dogon hannu. Jin tsaiwarsa a bayanta ya sata ƙoƙarin barin gaban mirror ɗin, amma saiya riƙota ta hanyar saƙala hanunsa saman cikinta ya manna bayanta da ƙirjinsa duk da bata kai har can sama ba. Ɗagowa tai tana kallonsa kamar yanda shima yake kallonta. Ganin ya ɗago lipstick da dayan hanunsa ta maida idonta akai. Saman lips dinta ya ɗaura, zatai magana yace mata “shiii!”.


   Shiru ta haɗiye abinda take son faɗar, shi kuma ya fara goga mata. Sai da ya gama ya juyota suna fuskantar juna, bakin ta ɗan tunzura gaba ganin yanda yake kallonta.


  “Nifa shanyewa nakeyi shiyyasa bana sawa”.


 “Oh really? To bara na shanye abuna kafimma ki shanye min”.


Idanunta ta waro waje da zaburowa zatai magana ya samu damar sauke lips ɗinsa akan natan. Dole ta koma tai laƙwas dan bai musu kamun wasa ba........✍


_Shareff adai rage cin amanarmu😚🚶🏻🤕._

reeey

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: 64

BABU SO

Chapter: 64 Share:

Report

BABU SO View: 167 Words: 2K

Chapter 64 64

........Dariya take tana masa gwallo. Fuska ya

 

 ɓata, da harɗe hannayensa a ƙirji irin yayi

fushin nan. Yanda yay ɗin sai ya saka Anaam

shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin.

“Kai Yaya shagwaɓa kuma?! ALLAH kamafi

ƙyau a haka fuskanka so cute”. Ta ƙare

maganar da kashe masa ido dariyarta mai

ƙaramin sauti na bayyana fararen haƙoranta.

Ta nuna lips ɗinta da kaɗa masa idanunta

dake cikin gilashi.

“Indai lipstick ɗin nan ne Yaya ba shansa

zakai ba garama ka haƙura”.

“Oh oh haba princess kiji tausayina mana”.

Yaya maganar da matsar da fuskarsa gab da

tata.

Baya taja dasa hanunta ta kare bakinta,

“Babu wani princess na daɗin baki fa Yaya,

barima kaga na shanye abuna, idan baka

ganiba ai dole ka haƙura”.

Yana ƙoƙarin riƙota ta tura lips ɗinta cikin

baki da sauri.. Idanunsa ya waro sosai yana

kallonta cikin langaɓe wuya. Ta fito da lips ɗin

tana dariya da masa gwalo. “Sai kaci abinci yanzu babu”.

“Ni ko? Yarinya zan rama ne”.

Dariyarta ta cigaba dayi ƙasa-ƙasa, shiko ya

ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin aincinsa

fuskarsa da ɗan murmushi.

“Nifa yaya karka cinye min abinci na”.

Idanunsa ya ɗago yana kallonta, sai kuma ya

 

 ɗibo abinci ya nufi bakinta, “Ba marowaci bane irinki ai hahh”.

Bakin ta buɗe ba musu ya zuba mata, a

hankali ta shiga taunawa da faɗin, “Nima ai

bana rowa”.

“Kika min yanzun?”.

“Baga abincina kana ci ba”.

Murmushi kawai yayi batare da yace komai

ba. Itama bata sake magana ba, ya cigaba da bata abincin shima yana ci. Suna gab da kammalawa wayarsa tai ring, ɗauka yay ya duba, ganin Khaleel sai kawai ya ɗaga. Bata san mi'akace masa a wayarba, sai gani tai ya miƙe da kama hanunta....

Da mamaki take kallonsa zatai magana ya girgiza mata kansa. Baki ta ɗan tura dan ita dai bata ƙoshi da abincin ba, sai dai babu yanda zatai dole ta bisa. Hango Khaleel jikin wata mota mai ƙyau fara tas jingine ya sata zare hanunta cikin nasa, bai ce komai ba har suka ƙaraso. Ita ta fara gaida Khaleel ɗin, ya amsa mata fuska da murmushi sannan ya maida hankalinsa ga Yayansa. Gaisheshi yay

da girmamawa. Ya amsa masa da kulawa. “Daga ina haka mazan fama?”.

Murmushin Khaleel ya faɗaɗa dan yana son Yayan nasa ya kirasa da sunan nan. Wani ɗan ƙaramin gi!   ya ɗakko a gaban motar, ya dubi Anaam dake kallon motar da ita kanta an

 

 naɗeta da zaren gi!. Sai kuma ya sake maida kallonsa ga Share" ɗin da shima dai motar yake kallo. “Saƙone daga Abie. Abawa Granny”.

Idanu ta waro matuƙa da kai hannunta duk biyu saman bakinta, sai kuma ta dubi Share" da shima murmushi ke shimfiɗe akan fuskarsa. Shine ya amsa ya buɗe key na mota ya bayyana. Ai batama san sanda ta rungume Share" da faɗin, “Wayyo Yaya daɗi zai kasheni”.

Rungumeta yay shina da sakin dariya kamar yanda Khaleel shina ke dariyar. Ɗagowa tai ta amsa key ɗin tana kallo, sai kuma ta ɗagasa a saitin fuskar Share" tana kaɗa masa. Murmushi ya sake saki mai faɗi da faɗin, “ALLAH ya sakama Abie da alkairi Congratulations dear”.

Da amin ta amsa, Khaleel ma ya amsa da

kallonta. “Congratulations Granny. Saura

kuma tukuyci na, k ko Yaya wazai bani?”. “Karka damu Yaya Khaleel, saika zaɓa”. Ta

bashi amsa da shigewa motar da Share" ya buɗe mata, daidai nan Fadwa ta fito hakama Aysha. A tare suka ƙaraso wajen, Fadwa da gaba ɗaya ranta ke'a jagule tun maganganun da Share" ya yaɓa mata ta dubi Khaleel fuska a tsuke. Kafinma tai magana ya nuna musu

 

 motar ita da Aysha yana murmushi. “Ƙyautace daga Abie aka kawoma Anaam”.

“Woow!!” Aysha ta faɗa cikin zaro ido da

shafa motar tana kallo, Fadwa kam mutuwar

tsaye tai. Dai-dai nan Share" da Anaam dake

cikin motar suka fito kowanne fuskarsa har

yanzu da murmushi. Khaleel ya miƙa mata

hannu, “Nifa a tafamin tukuycina”. Kafin tace komai Share" dake danna

wayarsa ya miƙa masa, saka details ɗinka”. “Woow da kyau babban yaya da gudu kuwa”. Yanda Yay ɗin ya saka Anaam da Aysha

kwashewa da dariya. Shigar saƙo a wayarsa yasa bai tankasu ba, ya buɗe da sauri, “What!”. Ya faɗa yana ɗago kai da sauri ya kalli Share". “Yaya duk tukuyci?”.

Murmushi Share" yay da kallon Anaam,

“Idan tace a ƙara maka ma sai a ƙara maka

ai”. A salon da yay maganar da ɗage mata gira

ya sakata rufe fuskarta da dukkan tafin

hanunta dan taji kunya. Matsota yay tare da

ranƙwafawa saitin kunenta. “Nima ina jiran

nawa tukuycin yanzun nan, inba hakaba a

gaban Khaleel zanyi.....”

Da sauri ta buɗe idanunta... “Kayi mi?”.

Maimakon amsa sai ya nuna mata lips ɗinsa cikin kashe ido. Sarai tasan zaiyi ɗin, amma sai ta kauda ido da nufin cewa a'a. Akan Fadwa da sam bata san da wanzuwarta a

 

 wajen ba ta saukesu. Sukaima juna kallon ido cikin ido, ita ta fara kauda idonta da sakin wani tattausan murmushi mai ma'anoni da yawa ta maido dubanta ga Share". Murmushi ta sakar masa shima ta ɗan saci kallon Aysha dake a mota hankalinta baya kansu, ta maida ga Khaleel, ganin shi ɗin dai zaiga komai sai ta ɗanyi jimm na tunani. “Yaya Khaleel kalla can”. Ta faɗa da sauri tana mai ɗane Share" a bazata ta manne tausasan lips ɗinta kan nasa lips ɗin.

Numfashinsa neman shiɗewa yay saboda

rashin zaton hakan daga gareta. Baya ta nema

janyewa ya ƙara cafkesu da saka hannu biyu

saman ƙugunta ta zuba masa mintsini a gefen

ciki da janye jikinta kunya kamar ta nutse.. Khaleel daya waiga baiga komai ba ya juyo

da nufin hararar Anaam, ai babu shiri ya sake

maida kansa gefe da sauri yana dafe bakinsa

da sakin siririyar dariya. Aysha da bata san

mike faruwa ba ta fito a motar tana rungume

Anaam da faɗin, “Wayyo blood motar nan ta

haɗu wlhy ALLAH yasa a kashe da kai”. Wani

bahagon tari ya sarƙe Fadwa, cikin sassarfa

kamar zata kife ƙasa dan sauri tabar wajen

hawaye masu azabar zafi na kufce mata. Gaba ɗayansu kallonsu suka maida gareta,

dan sai yanzu ma shi Share" yasan Fadwar

 

 na'a wajen. Cike da son basarwa itakam Anaam ta rungume Ayshar. “Thanks you blood, thanks you”. Shima dai gogan ya basar a binsa kamar komai bai faru ba, ya nunama Khaleel hanya alamar su shiga ciki idonsa akan Anaam. Anyi sa'a itama ta ɗago suka haɗa ido. Baki ta ɗan murguɗa masa. Ya taune lips dinsa da sakin murmushi alamar azakizo hannu. Kafaɗa ta ɗage masa da labe baki irin na i don't care taja hanun Aysha suka koma motar...

Da ƙyar Fadwa ta iya kai kanta sashenta

saboda jiri dake ɗibarta da lulluɓe ganinta

gaba ɗaya. “Subahanalillhi. Hajiya lafiya?”. Mmn Abu ta faɗa da nufo Fadwa da sauri

dake neman zubewa ta tareta. Kuka ta sakar mata kamar wata karamar yarinya, maman Abu duk sai ta rikice. Kamata tai har bedroom. Tana son tambayarta mike faruwa tana jin tsoro, dole ta fito ta barta cikin damuwa. Tadai san labarin kitse baya wuce ƙoƙi dan ta jima da fahimtar Fadwa na cikin jerin mata masu tsananin kishi. Gata da hali irin na ɓoye abu a rai da idan bakai dogon nazari akanta ba saika ɗauka kishiya cutarta take musamman irin Anaam da bata iya ɓoye abinda ke ranta. “ALLAH ya ƙyauta”. Ta faɗa

 

 da komawa kitchen ta cigaba da aikinta.....

Anaam kam da tuni sun koma ciki tana can cikin farin ciki tana waya da Mamie da Abie ta video call. Addu'a take zubama iyayen nata harda hawaye, yayinda suma suke kallonta murmushi shimfiɗe a fuskokinsu da tsananin ƙaunarta da tausayinta harma da alfahari da ita na kai mutuncinta gidan aurenta. Dan aunty mimi ta sanarma Mamie komai, hakama Mamie ta sanarma Abie, shiyyasa ya danƙara mata mota najin alfahari da ita akan riƙe tarbiyyar da sukai mata. Sai dai su kansu sun san sun kaita wani filin gwagwarmayar rayuwane na yankin kaddararta, amma sukanji sassauci da tunawa zumincin ALLAH suke son karfafawa insha ALLAHU sadaukarwarsu bazata taɓa zama a banza da wofi ba..

______________________________

Tafiyar dai Aysha bata yuwu a yau ba, dan tuni Share" ya fice gidan tare da Khaleel yin godiya ga Abie, Anaam kuma sai ta ƙara samun sauƙin jikinta insha ALLAH zai kaita. Sai da suka fara biyawa ta o"ice yin wasu muhimman baƙi, ba wani dogon zama sukai ba sai zuwa monday idan ya dawo aiki.

 

 Takardar da zai basu suje su duba kafin zaman ya nema ya rasa, cikin ɗan dafe kai ya dubu Khaleel da Fharhan. “Inaga fa nama bar file ɗin nan a gida wlhy, Khaleel saika koma

kenan dan dole ne mu basu suje su duba.” “Okay bara naje ai bawani nisa bane”.

“Okay ba damuwa, kafin ka isa zan kira su

ɗakko maka kawai”.

Kansa ya jinjina masa ya fice. Shi kuma ya

shiga ƙoƙarin kiran layin Fadwa. Harta tsinke ba'a ɗagaba, yay mata uzirin ko bata kusa ya sake kira, amma nan ma dai hakan, ya ƙara kira har sau uku sai aka koma danna masa number busy. Ransa ya sosu matuƙa, dan ya gane tana kan sani. Amma sai ya shanye kodan baƙin dake tare da shi ya maida akalar kiran ga Anaam. Gama wayarta da su Abie kenan kiran nashi ya shigo, bugu biyu ta ɗauka har yanzu muryarta cike da farin ciki tai masa sallama. A hankali ya sauke ajiyar

zuciya, ya amsa mata.

“Har yanzu murnar motar ce?”.

“Humm Yaya bazaka ganeba”.

Murmushi yayi, “Okay idan na dawo ai sai ki

ganar dani, yanzu nidai nutsu na saki aiki”. “Okay” ta faɗa kanta tsaye.

“Ki duba a study table ɗina, akwai wani file green a wajen ki ɗaukama Khaleel zai zo ya amsa yanzun”.

 

 “Tom”.

Ta duba a kurkusa inda yace amma bataga

file ɗin ba, sai dai kuma hankalinta ne kawai

bai kaiba saboda ya dannesa da wani book.

Ta shiga bin komai daki-daki da kallo tana

ɗan ɗagawa harda buɗe drawers ɗin wajen.

Saukar idonta akan wani ɗan akwati ya sata

nutsuwa tana kallonsa, harta maida drawer

ɗin ta rufe sai kuma ta sake buɗewa ta ciro

akwatin. “Uhhm su Alhaji Yaya mm mi kuma

ake ɓoyewa anan? Koma dai miye zuciyata na

son gani”.

Tana ƙoƙarin buɗewa kira ya shigo wayarta,

shine dan haka ta ɗaga. Kafinma yay magana

tace “Yaya ban ganiba fa, inata nema kuma

tun ɗazun”.

“Kamarya? Bayan nasan yana nan akusa-

kusa. Ki ɗan ɗaga kayan wajen Khaleel na waje yana jiranki amfani zanyi da shi”.

“Oh sorry kamarma gashi anan ka ɗaura littafi akai”.

“Ok ki kai masa yana jiranki”.

Koda ta kaima Khaleel littafin sashen ta sake dawowa. Dan zuciyarta naga akwatin nan haka kawai batare data san dalili ba. Kiciniyar buɗewa ta shigayi, da ƙyar ta dace ya buɗu bayan ta haɗa da ƴan dabaru. Da

 

 littafi ta fara cin karo, ta ɗan jujjuyashi tana taɓe baki ta ajiye. Sai envelope brown babba. buɗeta tai ta zaro albom na hotuna mai tudu sosai sai dai bai cika girma ba a tsaho. “Hotunan sirri ne kenan su Yaya aka ɓoy....” ta kasa ƙarasa abinda ta faro. Ko'a magagin barci aka tasheta babu gilashi a idonta aka nuna mata hoton babu gargada zata bada amsar itace. Hotone da taga irinsa yafi guda ashirin a gidansu. Hoton ne da aka ɗauketa a ranar haihuwarta tun a asibiti. Tana rungume a hanun Yaya Share" Abie da aunty Mimi sun sakashi tsakkiya suna leƙenta a hannunsa ya babbake ya hanasu gani. Da sauri ta koma na ƙasa, shi kuma a ranar sunanta ne ita da shi, na gaba itace da shi da Mamie da Abie da aunty Mimi. Ta cigaba da buɗe albom ɗin mamaki fal ranta dan ta kasa fahimtar ma'anarsa. Hotuna na gaba sun kasance a gurare daban-daban. Wani wajen ita kaɗai, wani ita da shi, wani har da su Abie. Ranar birthday ɗinta na cika shekara ɗaya. “Ya ALLAH” ta faɗa tana cigaba da kallonsu daki- daki. Jikinta ya ɗan fara rawa ganin hotunan da har tana a shekarar shiga primary, secondray, kai har jami'a ma akwai, bayan zuwa lokacin Share" baya tare da su. Duk wani hoton birthday ɗinta akwaisa, hakama

 

 hotunan bikin salla kona wani taron makaranta kona islamiyya duk akwai. Hoton ƙarshe da yay matuƙar bata mamaki shine na ranar ɗaurin aurensa da Fadwa, itama kuma ranar nata ɗaurin auren da bata sani ba. Rubutun da yay a jikin hoton ya matuƙar firgitata..........

End of book

Leave a comment

          C

Post

omments

No Comments posted yet

    

        Contact Us

Arewa Books Publishers WhatsApp: 09031774742

Email: arewabookspublishers@gmail.com

Navigation

Home About FAQ's

Social

Facebook Instagram

Legal

Privacy Policy Terms of Service

    

 Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: ........ *_Cikar burina shine ganin irin wannan ranar


tare da ke gimbiyar mata, kece sirrin ruhuna, nima


inajin raɗaɗi fiye da wanda na gani a cikin ƙwayar


idanunki. I'm sorry! ranarki tana zuwa_*. 


 Ta haɗiye yawu da ƙyar, da sake maimata


karatun kamar mai bita, dan yayisa ne da yaren


maley ta tabbatar batayi kuskuren karantawa ba.


Zaune takai dan ƙafarta ta kasa ɗaukarta. Ta


cigaba da zaro sauran abinda ke cikin akwatin.


Akwai kashi-kashi na ribbons ɗinta, ta gane


hakanne saboda matuƙar son da takema wasu,


wasu kuwa ta gansu a hotunanta dake cikin albom


ɗin can tun tana yarinya. Sai wani ɗan abunta mai


kamar kwalba cikinsa da taurari da wata suna


yawo, a tsakiyarsu da alkur'ani a buɗe, idan bata


manta ba Mamie ce ta bata shi as gi! ɗin kammala


haddar alkur'anin ta, amma saita nemesa ta rasa a


daga baya duk da kuwa a side drawer na gadonta


yake. Har kuka tayi na rashinsa, kai tsaye kuma ta


zargi mai aikinsu ce ta fasa amma ta ɓoye. Mamie


ce ta kashe wutar a lokacin ta sake saya mata wani


sai dai yasha banban da wannan ɗin dan haka


taita mitar batason sa har sai da Abie ya shiga


zancen ya lallasheta. Ashe Yaya MM ne ya sacesa.


Ta cigaba da kallon abubuwa da dama nata, kuma


masu muhimmanci a gareta data nemesu ta rasa a


lokuta mabanbanta, wanda a iya tunaninta ta rasa


mai ɗaukar mata su, duk da har su Amrah yaran

aunty mimi tasha zarga. Book ɗin ta ɗauka saboda


ji a ranta shima ya shafeta. A shafin farko sunanta


ne da rubutu kamar haka.


 *_Juwairiyya Anaam! kece matar aurena kuma


uwar ƴaƴana da izinin UBANGIJINA. Ni kaɗai aka


haifawa ke, zan kuma rayune domin ke insha


ALLAHU._*


 Ta buɗe shafi na biyu zuciyarta na tsitstsinkewa.


_Da ace wani bawa nada damar tsara labarin


rayuwarsa da wanzuwarsa, zan tsara nawane


kawai domin ke kaɗai a wannan duniyar. Ina


roƙon UBANGIJI ke ɗin karki zama a cikin


ƙaddarar abinda ALLAH bazai mallakamin ba,


zuciyata bazata iya ɗauka ba, ya rabbi ka zama


gatana akowane hali_.


 Haka ta cigaba da karanta abubuwa daban�daban akan rayuwarta da tasa daya dinga


rubutawa tamkar labarin littafi. Mafi ƙololuwar


ruɗa tunaninta da saukar da hawayenta shine a


gaɓar da Mommy ta takura masa auren watanta.


Duk wani tashin hankalinsa ya zanashi da fargabar


karta suɓuce masa. Zuwanta Nigeria da sunan


hidimar ƙasa mafi girman sassauci dajin ƙwarin


gwiwar yin biyayya da cusa son Fadwa a ransa


matsayin sadaukarwa ko UBANGIJI zai masa


tukuyci da samun Anaam. Kukanta ya ƙara ƙarfi


jin cewar ya kwanta jiyyane akan jin za'a aurama


waninsa ita ba shi ba, harda barazanar kamuwa da

ciwon hawan jini daya nema shafar lafiyarsa.


“Innalillahi...” ta shiga ambata da kifewa jikin desk


ɗin nasa ta shiga raira kuka, wani al'amari mai


girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta


jikinta. Sai da tai kuka sosai harta gode ALLAH


kafin ta ƙarasa ganin wasu zane-zane da yayi


wanda duk fuskartace ya zana, kai kace tana


tsayene a gabansa yay zanen. Da kyar ta miƙe ta


tattare komai ta maida masa yanda yake ta maida


a drawer ɗin sannan ta fice jikinta a saɓule.


 Aysha dake zaune a falo tana aikin nata na


tiktok data koya gun Fadwa ta bita da kallo. Ganin


zata wuce bedroom batare data tanka mata ba ta


riƙo hanunta da sauri. Juyowa tai tana kallonta,


hawaye masu ɗumi na sauka mata a kumatu, sai


kuma ta rungume Ayshan tana saki wani marayan


kuka da ita kanta bata gama tantance na minene


ba. 


 Hankalin Aysha ya ƙara tashi, ta ɗagota da sauri.


“Ya ALLAH blood wai miya farune? Yaya ne ya miki


wani abu?”.


 Kanta ta girgiza mata. 


“To minene? Ko dai maganar aurence dai har


yanzu? Da zaman wannan gidan?. Dan ALLAH ki


kwantar da hankalinki Anaam. Ki saurareni a


wannan gaɓar na buɗe miki kanki ta yanda wlhy


sai Yaya Share" ya dawo tafin hanunki ta hanyarsoyayya da bin dokokin ALLAH. Na fahimci rashin


sanin minene kishi da rayuwar gidan malam


bahaushe ke sakaki tafiya a haguggunce a wannan


gidan har Fadwa ke jan akalarki da makirci. Ki


nutsu ki saurareni Please”.


 Bataƙi ta Ayshan ba, suka koma suka zauna cikin


hikima da basirar da ALLAH ya bama Aysha. Da


kasancewar ta tashi a rayuwane ta cikin gidan


yawa dama salon kishin Mommy da Aunty Amarya.


Ga karance-karancen littatafan nan na hausa duk


tana taɓawa ta shiga warware mata abubuwa


masu yawan gaske. Anaam irin mutanen nanne


masu saurin haddace abu idan an faɗa musu,


musamman akan abinda ke wahalar da su, ko


wani abu da basa ƙaunar a kaisu ƙasa. Hakan ya


bata matuƙar gudunmawa wajen fahimtar Aysha


daki-daki babu kuskure. Sosai taji daɗin bayanin


dan haka ta rungume Ayshan. 


 “Na gode blood, nagode, irin godiyar da babu


alƙalamin dazai iya rubutawa. Sai dai ki sani duk


abinda kikaga inayi a gidan nan kamar mara wayo


ba rashin wayo bane sarai ina lure da komai da


binsa daki-daki, sannan akan sani nake aikatawa


saboda wasu dalilai nawa. Idan banyi hakaba shi


kansa bazan gama fahimtar halayyarsaba balle ita.


Tabbas nasan bazan taɓa iya kaiku wayon zama a


irin rayuwar da kuka tashi ba, sai dai koba komai


ina shigowa cikinku nima ina ganin wasuabubuwan. Daliline ya sakani zaɓar yin duk abinda


nakeyi. Sai dai a yanzu kalar rubutun zai sha


banban da kalar takardar. A yanzu lokacina ne,


kisa a ranki lokacin Juwairiyya Usman MD Share"


zai fara a gidan Al-Mustapha Muhammad MD


Share". Nayi alƙawarin bazanyi abinda zai cutar


da kowa ba, sai dai zan nunama kowa kowacce


mace da ilimin zaman gidan aure UBANGIJI ya


halicceta, kuma ko wacece ita ko'a ina ta tashi zata


rayuwu, ta kuma riƙe kambunta na ɗiya mace. A


kwanakin da nayi biyar a gidan nan, na karanci


abubuwa masu dama a cikinsu, zan kuma fara


sharar fadata da su domin samun damar shimfiɗa


mulkina batare da wani datti ya sha gaban cikar


burina ba”.


 “Woow vary interesting my blood. Haka nake


sonki dan ALLAH. Ki haukata mana Yaya Share", ki


kuma dawo mana da Fadwa hanya tabar bin


karatun su Mommy, ta zama mai ra'ayin kanta”.


 Anaam ta ƙyalƙyale da dariya, zuciyarta fes


tamkar an sauke mata dukkan wani nauyi da


ƙuncin da takeji a yau a yanzu yanzu. Basai


amfaɗa ba, da ni da mai karatu duk zamu fahimci


hakan nada nasaba da abinda taci karo da shi


wannda a baya bashi take kallo a fuskar Share"


ba. Sun ƙara tattaunawa sosai akan wasu


abubuwan da dama da Aysha kafin ta miƙe ta


koma sashen Share" domin gyarawa bisashawarar Aysha. 


 Bata jin daɗin jikinta saboda ɗinkin da akai mata


na sakata jinta tamkar a takure, ga tafiyarta har


yanzu bai zama normal ba kamar da. Amma haka


ta jure a daddafe na rashin sabon da wahala ta


gyara ko'ina na sashen nasa, sauƙin ma babu datti


mai yawa. Sai da ta tabbatar ko'ina ya mata da


kamshi sannan ta rufe ta fito. Baki ta saki tana


kallon yanda Aysha ta ƙara gyara sashenta itama.


Ta saki murmushi da harar Ayshan dake tsaye tana


karanta mata taje tayi wanka ta ɗauki ado dan


Yaya Share" na gab da dawowa. Akwai tsoro


tattare da ita na abunda ya faru, amma gargaɗin


likita akan Share" ya bata ƙwarin gwiwar


tabbatarma kanta babu wani abu tunda ko dai


baya cikin hayyacinsa ai baya nema wani abu daga


garetaba zaren ɗinki na a jikinta. Da wannan


tunanin ta faɗa wanka. Koda ta fito tsareta Aysha


tai wai sai ta mata kwalliya. Badan taso ba dole ta


tsaya kuwa Aysha ta zaneta tsaf dasu jaja leɓe da


barbaɗa kumatu na zamani. Turare kuwa har ji


take yana hawa mata kai dan khumras nata sun


sami haɗine na musamman daga hajiyar sudan,


ga kuma *_YERWA INCENSE AND MORE +234 809


521 5215 da miss xoxo tayo mata haɗi da sai ƴar


gata ke samunsa


!


_*. Hakama na kanti duk masu


tsadane da ƙamshi na musamman da aka zuba a


lefe. Ƙanan kayan nata taso sakawa, sai dai Ayshata hanata hakan, acewarta kayanmu na gida sunfi


mata ƙyau. Dole badan taso ba ta haƙura ta shirya


cikin skirt da riga na lass daya zauna mata a jiki


tamkar ka saceta ka gudu. Aysha tai mata ɗauri na


zamani daya saka ita kanta kasa rufe baki sai


faman kallon kanta takeyi a mirror da ƙyalla


hotuna da wayarta.....


 


 A gajiye ya iso gidan bayan idar da sallar isha'i. Ya


fiddo ledojin daya shigo da su na fruits kashi biyu.


Sashen Fadwa ya nufa, ya sameta zaune a falo


ƙafa ɗaya kan ɗaya tanata cika da batsewa. Kallo


ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan ko sallamarsa


bata amsa ba. Ledar ya ajiye batare daya ce ko a


ba yay ficewarsa yana ƙwafa. Dan a yanda ta masa


ya bashi tabbacin tana kan sani taƙi ɗauka masa


wayarsa. Sashen Anaam ya nufa da ɗayar ledar


yanata faman furzar da hucin ɓacin rai......_


# #


Shike nan an shiga tsakaninmu da


Soulmate 


$


, dolene mu koma gidan.... Basai na faɗa ba.

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: jimawa, Anaam dafe da kanta dake mata ciwo


saboda kukan da tasha ɗazun, ga jikinta har


yanzu sam baya mata daɗi irin na shiga


sabuwar rayuwar da ba'a saba ba. Aysha ce ta


amsa masa sallamarsa, ya ƙaraso ciki idonsa


akan Anaam. Ya miƙama Aysha dake masa


sannu ledar hanunsa.


 “Ita wannan lafiya kuwa?”.


“Kanta ne ke mata ciwo, nayi-nayi tasha


magani kuma taƙi”. Zaune yakai kusa da ita,


ya janye hanunta dake dafe da kanta. Kasa


kallonsa tai, dan haka kawai take jin wani irin


matsanancin kunyarsa. Shiko ya matuƙar


shagala ne a kallon kwalliyar dake zane akan


fuskarta, a kasalance yakai hannunsa kan


haɓarta ya ɗago fuskar da ƙyau, hakan sai ya


tilasta mata ɗago nata idanun dake cike da


ƙwalla ta kallesa. Ba ƙaramin jarumta yay


wajen jawo numfashinsa dake neman


kufcema ƙirjinsa ba, ya matsota jikinsa tare


da ɗaura hanunsa saman goshin nata.


 “Wannan idon naki kinyi kuka da shi, ko


muje asibiti ne?”.


Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Kanta ta


girgiza masa da ƙara lafewa a jikin nasa har


hakan ya so bashi mamaki. Dan yasan dai


koshi ya ringumeta turesa take kota janye


jikinta, amma yanzu ga saɓanin hakan yanagani, koda yake tunda abin nan ya faru ya


fahimci ta zama wata shiru-shiru, tsiwar taɗan


ragu kaɗan ko likimo ne, mata sunji maza


kenan. Fitowar Aysha ta sakata janye jikinta,


shima sai ya miƙe yana faɗin, “Bara na watsa


ruwa sai a samo miki magani”.


 Baki ta ɗan tura masa da kaiwa kwance. “Ni


basai nasha magani ba fa”. 


 Juyowa yay daga niyyar barin falon da yayi,


“Oh tunda hakane tashi na fasa barinki anan


ɗin”. 


 Dole badan taso ba ta miƙe, dan ya tsuke


fuska babu alamar wasa, duk da dama dai


tunda ya shigo babu fara'ar tattare da shi.


Aysha da tuni ta koma kitchen yay kira. Fitowa


tai da sauri tana amsawa. 


 “Gyaramin fruits ɗin nan”.


“To Yaya. Ko'a haɗa salad?”.


“Duk yanda kikai is ok”.


Kanta ta gyaɗa masa, shi kuma ya kama


hanun Anaam suka fice. Ta bisu da kallo


murmushi bayyane akan fuskarta. Tana fatan


ALLAH ya hana su Mommy raba wannan


auren har abada. Dan sun kasance abin


birgewa best couple ever matuƙa”.


 Koda suka iso sashen nasa a falon ya zauna,


ya riƙota saman cinyarsa ya zaunar. Yanzun


ma cikin mamaki yaga ta lafe a jikinsa. Ya ɗan


murmusa da shafar fuskarta idonunsa na binfuskarta dake ƙwaɓe alamar rashin jin daɗi


da kallo. 


 “Kodai har yanzu garden ɗin na zafinne?


Noorie!?”.


 Kanta ta sinne a ƙirjinsa da riƙo hanunsa


dake kaiwa jikinta, dan zuwa yanzu ta fahimci


mi yake kira garden ɗin. “Yaya Please ka


daina”.


 “No Aunty babu wannan zancen”.


Ya faɗa cikin kwaikwayon muryarta.


Murmushi ya kufce mata tare da ƙara cusa


kan nata cikin jikinsa. Dan yanda yay maganar


ya matuƙar bata dariya. Shima murmushi yay


da kaima wuyanta kisses. Tsoro ne ya kamata,


tai ƙoƙarin jan jikinta baya amma ya hana


hakan. 


 “Wayyo kaina zai fashe Yaya”.


Dakatawa yay daga ƙoƙarin cusa hanunsa


cikin rigarta. Ya riƙo kannata. “Ayya. Sorry,


sorry”. Sake langaɓewa tai kamar gaske. A


ƙasan ranta kuwa dariyace ke taso mata tana


dannewa. Da gaske kan nata na ciwo, amma


yanda takeyi ɗin yanzu harda pretending. Yin


hakan kuma shine mafita a gareta saboda


ganin yana neman sakin layi, itako a yanzu in


ba giyar wake tasha ba mizai kaita sallama


masa ya kasheta. Ai anyi kenan babu ƙari


tunda abun azaba kawai akesha a ciki. Ita jiya


tunaninta gaba ɗaya akan tayaya wasu matanke iskanci a cikin wannan wahalar? Ko kuwa


su basajin abinda taji da bazata taɓa


mantawaba har duniya ta tashi.


 Zaunar da ita yay a kujerar ya shiga bedroom


ɗinsa. Dai-dai nan Fadwa tai sallama. Anaam


tai kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa


ciki-ciki. Sam Fadwa bataji an amsa ba, sai dai


sanin halin mai sashen da kuma halin da suke


ciki na fushi da juna ya sata shigowa a ganinta


kobai amsa ɗin ba zata shigo. Turuss ta ɗanyi


na ganin Anaam, sukaima juna kallon cikin


ido kowacce ta janye da takaicin ƴar uwarta


da tsagwaron kishi.. Basuyima juna magana


ba, Fadwa ta nema waje ta zauna. 


 Fitowarsa ta saka Fadwa ɗaga kai tana


kallonsa, shima ita ɗin yake kallo da mamaki


a ƙasan zuciya, sai dai a fuska babu ko ɗigon


hakan sai ma janyewa da yay cikin halin ko'in


kula ya nufi Anaam dake kallonsu ta ƙasan


ido. Ita dai bata san sunada wata matsala ba a


gidan. Dan haka bata kawo komai a ranta ba


game da ɗaure-ɗauren fuskar tasu. A hanun


kujerar da take kwance ya zauna, 


 “Tashi kisha. Kimmaci abinci kuwa?”.


 Sai da ta ɗan saci kallon gefen Fadwa sannan


ta ɗan tura baki da narke fuska. “Ni banajin


ci”. 


 “Uhhm baƙya son ci, yarinyar nan ki ragetaɓaran nan naki, yanzu abincin ma sai kin


nuna masa hali? Yanzu dai kinga ba'a shan


magani sai da abinci, faɗamin mi zaki ci?”.


 Kallonsa ta ɗanyi da juya ƙwayoyin


idanunta, sai kuma ta narke fuska da girgiza


kai. “Da gaske bana son ci, barci nakeji kawai”.


 “Uhm-uhm fa, bana son zama da yunwa


sam! Ki dai sha ko fruits ɗin can ne idan Aysha


ta kawo. Zakisha ko?”. Ya ƙare maganar da


ranƙwafowa kanta yana sinsinar wuyanta. Ta


gefen ido ta saci kallon Fadwa, sai taga su


take kallo fuskarta ciɗin-ciɗin kamar zata


fashe har wani jajaja takeyi na alamar ɓacin


rai abunka da fari. Murmushi tai mai sanyi


dakai hannu ta shafi fuskar tasa a ranta tana


faɗin (Ashe kin san akwai ciwo ni kike yi masa


kiss a gabana, zan koya miki iya zaman


duniya). Hanunta da take neman janyewa ya


cafke da sauri yana maidashi akan tattausan


gashin kumatun nasa. “Kin yarda zaki sha?”.


 “Ni dai ɗan kaɗan”.


Ta faɗa a shagwaɓe.


Da ƙyar ya iya jan numfashi, dan shagwaɓar


tata ba ƙaramin susutashi take ba. “Good


girl”. 


 Murmushi tayi da janye hanun. Riƙeta yay, ta


marairaice masa. “Nifa fitsari zanyi”.


 “Okayy to ana buƙatar abokin rakkiya?”.Ta faɗa da zille masa tana ƴar dariya.


Bedroom ɗinsa ta nufa batare da ko sashen


Fadwa ta kallaba. Tana shiga ta zube a


gadonsa dan babu wani fitsari dama. Kawai


dai taba Fadwa space ne. Domin rama abinda


tai mata bashike nufin bazata mata adalci ba.


Kuma koba komai yanzu kawai ta nuna mata


cewar alwashinta tabbatacce ne akan mantar


da Yaya MM ita in har tana a tare da shi.


 


 Shiko daga can da kallo ya bita har saida ta


shige, a hankali ya haɗiye murmushi kan


fuskarsa. Miƙewa yay kamar zai bar falon.


Tasan idan tai wasa da wannan damar zatafi


haka shan wahala. Kamar yanda Mama


(Gwaggo halima) ta faɗa mata ba haka ake


buƙata ba, taje ta shirya dashi kodan


kasancewar gobe ne zata amshi girki, suna


buƙatar tai aiki da wasu fitinannun maganin


mata da aka kawo dominta tun daga ƙasar


sudan. 


 “Dan ALLAH kayi haƙuri” ta faɗa da sauri


tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da tun ɗazun


take son su zubo ko zata samu sassauci.


Ratseta yay zai wuce tai azamar riƙosa. Bai


juyoba amma ya dakata. Ta share hawayenta


hanunta riƙe da nasa. “Dan ALLAH kayi


haƙuri, nasan nayi kuskure. Amma wlhysharrin shaiɗanne”.


 Ransa a ɓace ya dubeta da wani mugun kallo


daya matuƙar neman gigitata. Saurin sakinsa


tai da girgiza masa kai. “Nasan nayi kuskure


amma dan ALLAH kayi haƙuri haka bazata


sake faruwa ba”.


 “Tashi kibar min falo”.


“Please Soulmate dan ALLAH”.


Sallamar Aysha ce ta sakashi haɗiye maganar


bakinsa, ya koma ya zauna da amsa mata.


Itama hawayenta ta shiga sharewa idonta na


satar kallon ƙofar bedroom ɗinsa, dan


zuciyarta raya mata take Anaam na wajen


laɓe tana saurarensu. Sosai takejin raɗaɗi da


ɗacin hakan, amma taci alwashi komi zai faru


a yanzu ɗin bashi ne Anaam ɗin zataci itama


zata rama.


 Aysha ta dire tray ɗin hanunta a gabansa,


fuskarta da murmushi ta gaida Fadwa da taƙi


kallonta saboda kar Aysha ta fahimci tayi


kuka. Kanta kawai ta jinjina mata. Ayshan


bata damu ba, dan tasan halin Fadwa wani


lokacin itama akwai yarfi. Hankalinta ta


maida akan Share!, “Yaya a zuba?”. Kai ya


girgiza mata alamar a'a, sai kawai tai musu


sallama ta fice a ranta tana ayyana akwai


matsala gaskiya, sai dai rashin ganin Anaam


yasa taji wani iri.


 Kusa da shi ta taso ta dawo, “Soulmate......Hannu ya ɗaga mata a fusace. “Fadwa! leave


me alone. Tashi ki fita”.


 Idanu ta tsura masa zuciyarta na mata


raɗaɗi, tasan a cikin fushi yake, kuma shi baya


son yanke ma mutum hukunci cikin fushi. Jiki


a saɓule ta tashi ta fice wasu hawaye masu


zafi da jin matuƙar tsanar Anaam na ƙaruwa a


ranta. Dan a ganin duk an mata hakane


saboda Anaam, ta kuma tabbatar ba haka


iyayen Anaam suka bar Share! ɗin ba kamar


yanda Mama ta sanar mata yanzun.


 Ya jima zaune a wajen zuciyarsa na masa


raɗaɗi da ƙuna, baya son ɓacin rai da


damuwa, yama rasa ina zai kama da halin


matan nasa. Ya samu ita Anaam ɗin ta sakko


ya fara samun kwanciyar hankali ita kuma


Fadwar na neman rikita masa lissafi. dole ne


ya musu sabon shiri na zama da kowacce da


halinta. Yasan duk abinda Anaam zatai tana


yinsane a karan kanta sannan bata da ɓoye-


ɓoye. Fadwa kam ya fahimci akwai zugar


mutane baibaye da ita, dan tun zuwan Anaam


gidan ya fahimci ta ajiye wasu halayenta na


zahiri ta aro waɗansu daban, idan bai tashi


tsaye a kanta ba zasu iya laɓewa a bayanta su


tarwatsa masa farin cikin gidansa, shi kuma


harga ALLAH yana sonta itama. Ya furzar da


numfashi mai ɗaci, tunawa da Anaam dakecikin bedroom ya sashi miƙewa ya nufi


bedroom ɗin. Da mamaki yake kallonta


kwance a gado har tayi barci, ya tsugunna


saitin fuskarta yana sakin murmushi da kai


hannu ya shafa kanta. “Dama fitsarin ƙarya ne


kenan?”.


 Idanu ta buɗe a hankali dan dama barcin


baiyi nisa ba, sai kuma ta maida zata lumshe


da ture masa hannu. Hannun nata ya riƙo


cikin nashi, fuskarsa gab da tata, “Tunda kin


tashi muje kisha fruit ɗin”.


 “Ni na ƙoshi barci nakeji Yaya”.


 “Ni kuma ban yarda ba idan kika sha sai kiyi


barcin”.


 “Uhhum-uhhum”. Ta faɗa tana noƙe


kafaɗarta. Miƙewa yay yana murmushi, ya


ɗagata gaba ɗayanta. Watsal-watsal ta farayi


da ƙafafunta. “Wayyo Yaya! Wayyo Yaya ni ka


saukeni na ƙoshi”.


 “Wayyo Aunty! Wayyo aunty ni bazan


saukeki ba sai kinsha”. Ya faɗa dai-dai suna


kaiwa falon.........End of book

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO

Chapter: 67.........Da ƙyar ya iya lallaɓata tasha fruit salad ɗin, dan da gaske barcine a idonta sosai. Ganin tanata faman lumshe idanu dole ya barta. Itama sai ta miƙe tana ɗaga masa hannu. “Yaya good night”.


  Kafin ya samu damar cemata komai tabar falon da hanzarinta dan bata buƙatar yace zai dakatar da ita. Shima baiyi yunƙurin dakatar da itan ba. ya dai bita da kallo. 
    Kamar yanda ya saba bayan gama duk wata al'adar rayuwarsa yay shirin barci. Yaso yin kwanciyarsa anan amma zuciyarsa taƙi aminta da hakan. Ya fito a nutse yana kulle ƙofar. Sashen Fadwa ya fara nufa dan bazaiƙi sauke nauyin da ALLAH ya ɗaura masa ba komi sukai masa na laifi. Yayi mamakin samunta a falo bata kwanta ba. Sai dai hankalinta gaba ɗaya yana akan waya ne. Ta mugun shagala a yin editing video da zatai posting, wanda ɗauka ce mara daɗi, dan kuwa faɗa suke da wata mai suna Teema. Faɗan kuma ya samo asaline akan ita Teema ɗin ta ɗaura hoton Shareff a shafinta tana bin waƙar soyayya. Sai wasu a cikin followers ɗinta suka ɗakko videon suka dinga tagging Fadwa da gaba ɗaya a yau bata buɗe data ba sai da yammar nan, dan tashin hankalin Anaam ya saka a kwana biyun nan ta rage yin posting akai akai kamar da da arana takan ɗora videos sama da uku. Sima itace ta fara kiran Fadwa ta sanar mata lokacin fitowarta a sashen Shareff kenan. To shine fa tun ɗazu ɗin ake tafka rigima tsakanin Fadwa da mabiya bayanta su Sima. Itama Teema da nata magoya bayan sunama Fadwa izgilin Teema zata shigo itama ata uku kafin shekara ta ƙare. (😜gsky naso ace kuje tiktok kuga rigimar nan guys🤣😆).


   Tsaiwarta a kusa da ita ta sakata wani mugun zabura, daka ganta kasan ta firgita. Ta kife wayar akan kujera a daburce take masa sannu. Idanu ya tsira mata cike da mamaki matuƙa, dan baiga abin zabura ɗin ba anan. Ya maida dubansa ga wayar da take faman ja tana turawa ƙasan throw pillow, zuciyarsa ta ɗarsu a karo na biyu game da ganinta da ɗaukar hankalinta da waya keyi, sai dai na yau yafi ƙarfi dan ƙarara alamun rashin gaskiya sun bayyana akan fuskarta. Komai baice mata ba ya juya ya fice.


  Ta bisa da kallo zuciyarta na luguden daka, dan ta tabbata shirunsa wani abu ne mai zaman kansa. Gaba ɗaya sai hankalinta ya rabu biyu, matsawa tai jikin window, sai ta hangosa zai shige sashen Anaam. Jikin windown ta bari, ta ɗauka wayarta da sauri ta nufi bedroom harda murzama ƙofar key.
    A falo ya samesu Anaam najan hanun Aysha akan sai taje su kwanta a ɗaki ɗaya. Ita kuma Aysha ta dake cewar ita bazata ba a ɗakin baƙi dake kusa da dining zata kwana. Shigowarsa ta sakasu dakatawa daga jayayyar tasu, Aysha kuma ta samu damar zare hanunta ana Anaam tana mata gwalo. 


   Filon dake saman kujera tai saurin ɗauka ta jefama Ayshan, da gudu Aysha ta ƙarasa shigewa ɗakin tana cigaba da dariyarta. “Zan kamaki ne ai yarinya”. Ta faɗa tana kallon Shareff dake kallonta.


    “Barcin kenan?”.


  Kanta ta langaɓe masa gefe fuska a narke sai dai batace komai ba. Cigaba da takowa yay har zuwa gabanta, ya kamo hanunta yana faɗin, “Muje”. Kafaɗa ta noƙe masa. Dan haka ya tsaya yana kallonta. “Miyasa?”. Ƙara narke masa tai murya a karye. “Sai dai ka goya ni”. Ya waro idanunsa sosai a kanta, fuskarsa na sassauta tsukewar da take. “Da ɗinkin zan goyaki?”. 


  “To bakai kaja akayi ba”.


Karon farko ya saki murmushi har haƙoransa na bayyana. Jikinsa ya rungumota da ɗaura kansa saman kafaɗarta. “Muka dai ja akayi”.


  “Dawa?”.


Ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin jan jikinta daga garesa. Ƙaramar dariya ya saki dan yanda tai ɗin kamar wadda aka kirama mutuwa. “Da ke mana, harfa wani kanannaɗeni kike. Ko muje a ƙara yanzu ma? Na san dai ya daina zafin ai”.


     Kukan ƙarya ta sakar masa wai ya mata sharri sai sunje shari'a gaban su Abba. 


  Cikin ɗage gira da ƙoƙarin damƙota ya ce, “Oh really? To kafin muje bara na idasa abinda na fara shari'ar tafi armashi”. 


  Saurin goce masa tai tabar wajen da gudu. Binta yay da sassarfa, cikin saurin ya riƙe ƙofar da take neman rufewa ya shige shima. Sosai ta marairaice fuska, dan da gaske ta ɗauka yin zaiyi. “Please Yaya MM wlhy ni bana so, kawai kaje wajen matarka ka kwanama na yafe”.


     Damƙota yay tare da ɗagata cak ya dire saman gado, watsal-watsal ta shigayi da turasa, hakan yasa suka shiga ƴar kokawa wadda ya ƙyaletane kawai. Ya fara kai mata cakulkule tana dariya da turesa. Shima dariyar yakeyi da ƙoƙarin kaima wuyanta zuwa kirjinta kiss. Da haka yaci nasarar haɗe lips ɗinsu waje guda. Tun tana son kauda kanta har yaci galabar shagaltar da ita ta fara bashi haɗin kai. Romancing juna sukeyi cike da sauka a layin manta matsayin junansu. Da sauri ta damƙe masa hanunsa dake ƙoƙarin zame rigar barcinta da tuni ya sauketa akan ciki dama. Jin yana ƙara ƙasa da ita ta dawo hayyacinta. Dakatawa yay tare da buɗe shanyayyun idanunsa dake cike da fitina yana kallonta, dai dai itama ta buɗe natan dake da raunin gani dan tuni ya zare gilashinta dama. Ƙoƙarin janyewa tai ya sarƙesu cikin nasa. 


   “Why?”.


 Ya faɗa da ƙyar muryarsa a matuƙar ɗashe tamkar mai mura.


     “Akwai ciwo”.


   Ta bashi amsa cikin raɗa itama dan muryar tata ko fita batayi rawa take ma kamar mai shirin sakin kuka. Kansa ya girgiza mata alamar kar tayi, amma kamar ya zugata sai gasu suna zirarowa da gudu. Rungumeta yay tsam a ƙirjinsa tamkar mai tsoron a ƙwace masa ita. 


  _“Zubar hawayenki dai-dai suke da ƙuna mai raɗaɗi a zuciya. Ni mai raunine akan ki Juwairiyya. Da ke kaɗai aka raini wannan zuciyar tun daga ƙuruciya har girma. Nakanfi buƙatar nisantarki a zahiri, amma a baɗini ke ce sirrin ƙwarin gwiwar dukkan wani nasarorina. Nakanji himma da ƙawa zucin jajircewa a karan kaina domin ke kaɗai ƙwalli. Idan na danganta matsayinki a zuciyata da kalmar *SO* kawai nakanji tayi ƙanƙanta da rage miki kimar zamowa ke wacece ɗin. Da ace so kwalba ne da tuni ƙarfin ikonki ya tarwatsashi daga zuciya saboda *GIRMAN KI*. K ɗaya tilo, k ɗaya ƙwalli a tarihin da UBANGIJI ne sarki mai ikon sarrafa zukata kawai ya lulluɓe saboda hikimarsa. Ki rayu dani duk tsanani koda ace baƙya buƙatata a irin matsayin da ke kike da shi a wajena. Na miki alƙawarin nawa ya wadatar damu da har ƴaƴan da zamu haifa.”_


   Maganar yake da harshe, amma ita zuciyarta ce ke neman ɓarkewa gida biyu domin yana karantasune a gareta tamkar maimaici akan abinda ta gani a ɗazun. Taigar jikinta gaba ɗaya ta gama miƙewa, da ace ba rungume take a jikinsa ba babu abinda zai hana ya ga yanda take tsuma. Ya ɗago kanta a hankali tare da daidaita fuskokinsu. Da sauri ta maida fuskarta ta sinne a ƙirjinsa, yay ƙoƙarin sake ɗagowa amma ta hana hakan.


     “Please Babie say something”.


   Kuka kawai ta sakar masa dan zuciyarta mai rauni ce, a yanzu kuma ta ƙara raunana ne fiye da raunin daya kasance halittarta, jiyay gaba ɗaya ma ya rikice, ya tashi zaune da ita a jiki, buƙatarsa kawai ta kallesa, sai dai taƙi yarda tai hakan sam. Dole ya barta, ta sake zamewa ta kwanta tare da jan bargo ta ƙudundune jikinta har kanta. Shiru yay yana kallonta ƙirjinsa na harbawa da ƙarfi. Ya jima tsahon lokaci a haka, kafin ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauri alwala......
   ★A lokacin da Shareff ke a ɗakin Anaam yana raya wannan dare a gaban UBANGIJI a ɓangaren Fadwa dare ta raba tana maida murtanin faɗa ga Teema ta hanyar video, da farko sai tayi recording take posting, da abun ya rikice sai aka koma live. Faɗa ne da tun anayinsa iya kan Shareff sai ya koma ƴar tone-tone musamman akan su Sima. Tuni masu bibiyar faɗan wasu a followers nasu ke ƙara tunzura al'amarin ta hanyar Comments.....
     Sai kusan ƙarfe uku yay addu'a da rufe alkur'anin daya kammala karantawa ya koma kan gadon, tuni Anaam tayi barci, ya tsura mata idanunsa tsahon lokaci. Kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da kaiwa kwance. P.o.p ya tsurama idanu abubuwa biyu na masa kaikawo. Yanayin Fadwa na ɗazun yaƙi barin ransa. Fargaban samun tabbaci daga furucin Anaam na randa aka bayyana ɗaura aurensu na masa amsa kuwwa tamkar a yanzune take faɗar bata sonshi waninsa take so har ma da alƙawarin aure. Juyawa yay yana kallonta da idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Sosai yake jin raɗaɗin kalmar. Ashe da gaske take har cikin ranta ne ba bore bane kamar yanda ya dauka daga baya................✍️

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO

Chapter: 68........Yau ta kasance cikar kwana bakwai na kwanakin Anaam a gidan, miji zai koma hanun Fadwa kenan. Sai dai kuma tunda garin ma ya waye bata ganshi ba. Tunda sassafe ya fice sakamakon kiran daya samu daga Engineer ɗin dake kula da aikin ginin wani ƙaton mall da sukeyi na wasu larabawa da suka buɗe branch anan kano. Shine ya zana mall ɗin kamfaninsu kuma ke ginawa, to yanzu a dalilin wani mai musu zagon ƙasa wata matsala ke neman shigowa. 


    Su dukansu ma babu wanda ya san baya gidan sai zuwan Khaleel tare da mai haɗama Anaam tv. Anaam taji wani iri dan a tunaninta ko abinda ya faru a daren jiya ne ya sakashi fitar tunda sassafe. Amma sai batace komai ba dama duk sukuku ta tashi. Itama Fadwan ta jingina fitar tasa ne akan abinda ya faru jiya da dare, sai dai saɓanin Anaam ita tsorone ya kamata da tunanin kodai ya gano tana tiktok ne? To amma idan hakane ai ba fita zaiba wayarta zai fara bincike. Sosai ta shiga taraddadi, cikin tsaida mafita ɗaya ta nema zuwan su Sima gareta. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu sun iso harda Bibah da Siyyah suka ƙulle a ɗaki suna tattaunawa. Maman Abu ta girgiza kai da jinjina wautar Fadwa matuƙa, abinda duk ya faru tsakaninta da Shareff jiya ta gani, ta kuma fahimci raye-rayen da Fadwan keyi Shareff ɗin bai sani ba. Shiyyasa ta tsorata da tunanin ya ganta a jiya. Inama Fadwan zata saurareta data bata shawarar dawowa kan hanya domin gujema zuwan ranar dana sani, dan ta tabbata waɗan nan ƙawayen nata data bama amanar rayuwarta sune waɗan da zasu fara kaita ƙasa kafin su Aunty Malika. Mata irin Fadwa da yawa rashin alƙiblar kansu ke tarwatsa musu rayuwa da nasarori koda ace akwai wasu ƙyawawan halaye abin dubi tattare da su, kafin su farga taurarinsu ya gama disashewa a idon duk wanda zai kasance zagaye dasu, a lokacin kuma dukkan damanmakinsu sun kufcewa yunƙurinsu da taɗesu ga zuwa nasarar da su suke kallo a cikin idanunsu duk da suna ƙoƙarin cimmatane a cikin kuskure na son zuciya.
    Anaam kam dai sukuku ta yini har yamma akan rashin ganinsa, zuwa la'asar sai zuciyarta ta kasa dauriyar ɗauka dan koba komai shi ba abin yadawarta bane ba. Wayarta ta ɗauka, ta gwada kiransa yafi sau goma kafin tai ƙuru ta danna number da ko saving nata ta gagarayi amma ta gama haddaceta tun a kiran da yay mata jiya bayan ta gama ganin kundin sirrinsa mai ɗauke da sirrikan da ita kaɗai suka shafa.


    A lokacin yana zaune ne ya gama yin liƙis da gajiya da yunwa. Dan duk yau ruwa kawai yake iya kaiwa bakinsa tsabar zafin da kansa ya ɗauka akan al'amarin dake zagaye da su. Bashi ba hatta Fharhan da Khaleel da wasu a cikin staff ɗinsa a jigace suke. Juma'a guda haka ta riskesa ko wanka baiba da kayan dake jikinsa kanana sukaje sallar juma'a. Baiko duba waye mai kiran ba ya kai kunnensa. Can ƙasan maƙoshi tai sallama kamar maijin tsoro. Curo wayar yay a kunensa da mamaki, ganin tabbacin ita ɗince ya maida yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da har tana iya jiyowa. Ta ɗan murmusa daga can, tare da langaɓe kai kamar tana a gabansa.


  “Yayaaa!”.


 Yanda ta ambaci sunan cikin ƴar shagwaɓa ta saka tsigar jikinsa tashi, yaja numfashi a slowly.


  “Uhhum autar mata”.


Ta saki siririyar dariyar data ƙara tunzurashi. “Yaya ka rufamin asiri da sunan nan kar mata sumin duka”.


     Murmushi yayi a karon farko, da ɗan gyara zamansa. “Kice na faɗa da shela ko hakan zaisa su tabbatar ke ɗin ta ƙarshe ce tabbacin Autarsu”.


  “Nidai ba ruwana gaskiya. Wai kaje ina ne?”.


  “Yawo mana”.


“Yawo fa Yaya? Ai nasan baka yawo, kai da kullum kana company ina zaka aiki, ina ka dawo aiki”.


    “Oho shaidar da kikamin kenan?”.


  “ALLAH gaskiya na faɗa. Dan ALLAH ina kaje?”.


“Kina kewata ne?”.


Kamar tana a gabansa ta rufe fuskarta da filo. “Ɗan kaɗan”.


  Dariya yayi kam yanzu har Fharhan na kallonsa. 


 “Wato ɗan kaɗan? Autar mata kiji tsoron ALLAH fa”.


    “To ai nama daina ji yanzu gaba ɗaya”.


  “Oh-oh, maimakon na samu ƙari sai a kwashemin ma duka? Aji tausayina mana diamond girl”. 


     Sosai take dariya sai dai a nutse, (kece farin cikin duniyata) ya ayyana a cikin zuciyarsa yana mai lumshe idanunsa. Ji yake tamkar yaga kansa a gabanta kawai. Daga can Anaam data tsagaita dariyarta da iya gaskiyarta tace, “Am serious gidan babu daɗi dan ALLAH ka dawo”.


    Da ƙyar ya iya danne zuciyarsa dake tsalle-tsalle, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Mi kika tanada min ne?”.


  “Duk abinda kace kana so”.


“Kin tabbata ko minene shi zan samu?”.


     “Ga wani ma tun kafin kazo”. Ta faɗa dayin kissing wayar. Har tsakkiyar kansa yaji saukarsa. Kafin ya samu damar cewa wani abu ta yanke wayar ƙit. Ƙoƙarin dakatar da ita yake amma bataki jisa ba, yay ƙoƙarin sake kiranta taƙi ta ɗaga, hanunsa ya kai yana murza goshinsa da cije lips.
    Itako dariya takeyi daga can zuciyarta cike da farin ciki mai ban mamaki. A haka Aysha ta shigo falon ta sameta. “Blood wai kin san wace kwamacala na gani kuwa?”.


  “A ina kenan?”.


Anaam ta faɗa tana tashi zaune da ƙyau. Cikin tsananin ɓacin rai Aysha takai zaune. “Wai ƴan iskan ƙawayen can na Fadwa fa naga takai sashen Yaya suna masa gyara”.


   “What!! gyara fa?”.


“Wlhy na rantse miki gasu can ma kuwa”.


   Miƙewa Anaam zatai Aysha ta maidata. “Kinga kwantar da hankalinki ba so nake kije ba. So nake kiyi duk yanda zakiyi Yaya ya dawo gidan nan yanzu shine kawai maganinsu. Dan yanzu in bai gani ba su Mommy zasu iya ƙaryatawa tunda ba san laifin Fadwan suke ba”.


   Shiru Anaam tai tana kallon Aysha. Tabbas maganarta haka take, sai dai kuma ta yaya zata saka Shareff ɗin zuwa bayan yanzu suka gama waya ma.......
    A lokacin da su suke shawarar yanda zai dawo gida a garesa ma akwai himmar hakance tattare da shi. Jiyay gaba ɗaya tattaunawar tasu ta gundiresa. Ya miƙe yana tattare takardun gabansa. “Fharhan kubar abinda ya rage zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a ƙarasa. Tunda namayi magana da Abie sai zuwa gobe zamu tattauna da shi yau yana Abuja shi da su Daddy”.


   Mamaki shimfiɗe a fuskar Fharhan yake kallonsa. “Dude amma kaine fa kace sai an ƙarasa komai yau miye na canja shawara?”.


     “Na gaji ne, ga yunwa na neman fara katsamin hanjin ciki”.


  “Uhhmyimm!!. Kodai soyayya malam. Lokaci yayi da zaka bar wani ɓoye-ɓoye ka buɗe mana mu kalla ko ma samu na kwaikwayo”.


     “Banza ɗan sa ido”.


   “Naji ba komai. In ka isa kace ƙarya na faɗa mana. Da an langare ana mana ciwo tunda kaji ka samu sai mukaji tsitt”.


   Spoon dake cikin kofin daya sha coffee ya dauka ya jefa masa. Fharhan yabar wajen da gudu yana dariya. Gaba yay shima yana faɗin, “Munafuki mai barci da ido ɗaya. Haka zaka ƙare rayuwarka a bibiyar tawa bakai aure ba tuzurun banza”.


   “Aniyarka ta bika wlhy, insha ALLAH nanda 2months zaku kaini”. Fharhan ya faɗa daga jikin motarsa yanama Shareff dakuwa.


      Murmushi yay da buɗe mota ya shige batare daya sake tanka masa ba....
   Tafiya yake amma ji yake kamar motar bata sauri, ya ƙara gudu tamakar mai shirin barin garin na kano. Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gidan, horn yayi har sau biyu amma maigadi bai buɗe masa ba. Yay dan tsaki da buɗe motar ya fita ya ƙarasa shiga da ƙafa da niyyar yima maigadin faɗa sai ya samu ashe yana bayi ne. Kansa kawai ya girgiza yay gaba, dan ya gwammace zuwa anjima ya shigo da motar kawai.


   Harya nufi sashen Fadwa ya fasa, kai tsaye nasa sashen ya nufa dan yafi buƙatar watsama jikinsa ruwa kafin komai. Tun a ƴar barandar gaban sashen nasa yaci karo da takalman mata. Mamaki yay matuƙar kamashi wani gefen zuciyarsa kuma na ayyana masa ko Mommy ce da muƙarraban ta, to amma takalman basuyi kama da wanda Mommy zata iya sakawaba dan duk hills ne. Kamar mai tsoron shiga ya tura ƙofar a ɗarare. 


  Dai-dai nan Amal dake goge-goge a falon ta ɗago da tunanin Fadwa ce da taje ɗakko turaren mopping ta dawo. “Yauwa baby kin ɗakk....” sauran maganar ta maƙale a harshenta. Ƙaf yawun bakinta ya ƙafe ta saki towel ɗin hanunta ƙarami da take goge-gogen da shi.


   Ana haka itama Bibah dake gyara bedroom ta kawo jiki zata fito, ai ba shiri ta koma da sauri cikin harbawar ƙirji. Sima dake kitchen ce ta shiga ƙwalama Amal kira, sai dai Amal ta kasa amsawa saboda tsabar firgita datai da ganin Shareff. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa dake cike da gajiya sun matuƙar kaɗawa zuwa launi mai razani. Duk da baice da su komai ba kowacce a cikinsu jikinta rawa yakeyi, Amal sarkin tsoro ta fara daga hannaye sama cikin rantsuwa da rawar murya..


   “Wlhy tallahi ba laifinmu bane ba yallaɓai, Fadwa ce ta sakamu mu taimaketa da aikin, amma ALLAH ba mune muka kawo kammu ba, kuma aikin kawai muke maka ba wani abu ba...”


   “Eh wlhy aikin kawai mukeyi Yaya Shareff”. Cewar Siyyah cikin son karfafa kai dan ita bata ruɗe kamar Amal ba, amma daka ganta kasan a firgice take. Sima kam tuni ta fice a kitchen ta ƙofar baya, itace taje a birkice ta sanarma Fadwa dake kitchen tare da Mmn Abu ana haɗa abincin tarbar Shareff ɗin. Ita kaɗai ta nufo sashin a rikice, sai dai tana ƙoƙarin hana ruɗewar tata a zahiri saboda shawarar Sima.


   Bibah dake bedroom kam taƙi fitowa, da sauri ta shiga kiran Gwaggo a waya. Tana ɗagawa ta sanar mata komai. “Bibah k mahaukaciyar inace da zaki biyema wannan sakarar yarinyar keda ke shirin shiga gidan matsayin matar gida. Duk yandama za'ai karki sake ki yarda Mustapha ya ganki a cikinsu. Inba haka ba kini sai k da shi sai dai kallo”.


   “Gwaggo kar kimun haka dan ALLAH”.


  “To laifinama zaki gani kenan? Yanzu banda ku shashshune taya zaku zauna ƙawa na baku aiki”.


  “Wlhy Gwaggo na biye musu ne kawai dan dan tace ɗakinsa ne, nidai ki taimakeni yaya zanyi na fito gashi can a falo ya tsare su Amal.”


“Humm sai ki jira matar gidan ta shigo, kiyi amfani da wannan damar kiyi wuff ki fita batare daya ganki ba”.


   “To to...to Gwaggo nagode sosai, idan da wata matsala zan kiraki dan ALLAH”.


  “Naji”.


Gwaggon ta amsa tana yanke wayar. Cikin laɓe baki.
     Shigowar Fadwa tayi dai-dai da saukema Siyyah data matsoshi cikin kwarkasa lafiyayyen mari da sai da taga taurari masu maƙata😆😜. Ba ita da aka maraba hatta Amaal sai da ta dafe kuncinta da zabura baya kaɗan ya rage ta faɗa kan kujerar dining.


  “Ya salam! Soulmate mari kuma? Shamsiyya ce fa?”.


   Wani matsiyacin kallo ya jefeta da shi fuskarsa na wani irin fusatar azabar dake soya masa ƙirji. Ƙasa tai da idanunta, amma saita matso garesa cikin dauriya ita a dole tana son fahimtar da shi.........✍

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: BABU SO View: 314 Words: 1.7K

Chapter 69 69

............“Soulmate! Please ka s......”

 

 Da sauri ya ɗaga mata hannu, da karkaɗa mata yatsarsa manuniya lips ɗinsa na rawa alamar gargaɗi. Sai dai ya kasa furta komai saboda takaici.

Dole ta dakata jikinta na wani irin tsumar

tashin hankali, hawaye rige-rigen sakko mata

sukeyi.

Har zai shige ya sake juyowa “Ku kuma na

baku minti ɗaya tak, ku kwashi tarkacenku ku ficemin anan kafin na fara ɓallaku ƴan iska!!”.

Ai har turereniya ake na fita tsakanin Amaal da Siyyah, dai-dai nan Bibah ta fito daga bedroom ɗinsa fuskarta a lulluɓe yanda bai ganta da ƙyau ba. Da gudu itama ta fice. Kansa dake sara masa ya dafe da sauri, jin jiri na neman kwasarsa ya dafe bango da sauri yana ambaton sunan ALLAH, da ƙyar ya iya ƙarasa kai kansa cikin ɗakin ya zube a kujera yanajin raɗaɗi da ƙunar zuciya.....

Fitowar su Amal da gudu daga sashen

Share! ɗin ya saka Anaam da Aysha kallon

juna baki buɗe, Aysha ta zunguri Anaam

“Blood jeki kiga mike faruwa? Naga oganiyar

tasu ita bata fito ba”.

“A'a blood babu buƙatar haka, wannan

tsakaninta da mijinta ne ai. Dama su nafi buƙatar yaci ubansu, amma ita matsalartace ita da shi”.

 

 “ALLAH k banza ce, wlhy idan kece hakan ta

faru a kanki ba ganowaba har dariyama sai

tayi zamanyi”.

Dariya Anaam ta saki da kaima Aysha duka.

“Kefa wlhy muguwa ce”.

“Babu wani mugunta, dan ALLAH kije”. “Okay ina zuwa”.

Ta faɗa da nufar sashen maigidan. Hango Anaam yasa da sauri Fadwa dake ƙoƙarin fitowa komawa ciki, bedroom ɗinsa ta nufa da ƴar sassarfa. Zuwa yanzu ya miƙe yana cire kayan jikinsa, shigowarta baisa ya juyo ya kalleta ba, hakan ya ƙara sanyaya jikinta, amma sai ta danne ta ƙarasa gabansa. Tasanshi mai saurin karayane da ganin hawaye, dan haka ta fara matsosu. “Soulmate dan ALLAH ka saurareni na maka bayani. Wlhy ba.....”

“Get out of my room!! Idan ba hakaba duk

abinda nai miki ke kika saya stupid!!”. ya

dakatar da ita a matuƙar tsawace. “Please Soulmate n...”

Saukar lafiyayyen mari a saman fuskarta ya hanata ƙarasawa. .

Cak Anaam dake ƙoƙarin shigowa ta tsaya, ba ƙaramin harbawa ƙirjinta yay da jin ƙarar marin ba. Wani irin ihun kuka mai ƙarfi da Fadwa ta saki, ya sata toshe kunenta, da sauri ta juya ta fice zuciyarta na bugawa da sauri-

 

 sauri. Shiko baiko nuna yasan Fadwa tanai ba ya shige bathroom abinsa. Hankali tashe Fadwa ta fita zuwa sashenta dafe da fuskarta datai jazur abinka da fara. Mamanta ta fara kira tana kuka, sai dai ba'a ɗaga wayarba, sai kawai ta koma kiran Mommy.

Mommy dake zaune ta kalla wayar taja tsaki, haka kawai takeji a ranta ƙofari Fadwa ta kawo mata. Kamar karta ɗauka sai kuma dai ta ɗaga takai kunne batare da tayi magana ba. Maimakin sallama da kuka ta fara cin karo, Fadwa dake kiran ta shiga uku ta shiga zayyanoma Mommy cewar Share! ya mareta, dan kawai ƙawayenta sunzo Anaam ta tunzuroshi. Dama kwana biyun nan babu abinda yake mata sai wulaƙanci akan Anaam

ɗin.... “Mari!!?”.

Mommy ta faɗa a razane.

Kuka Fadwa ta sake mashe mata da shi,

hakan yasa Mommy yanke wayar da sauri.

Aysha ta kira, cikin sa'a kuwa wayar na'a

hanunta ta ɗaga.

“K faɗamin, mike faruwa Yayanku ya mari

matarsa? Akan ƴar iskar yarinyarnan ne ko?”. Aysha da dama yanzu Anaam ke faɗa mata

cikin tashin hakanli ta taɓe baki. “Wlhy Mommy babu ruwan Anaam. Ƙawayenta ta kawo suna masa wai gyaren sashensa shine

 

 ya shigo ya samesu, harda su Shamsiyya”. “Shine dan bata da kunya ta kirani tana

kawomin ƙararsa, to lallai ya kamata a

wannan gaɓar na takama yarinyarnan birki

dan na kula neman maidani ƴar isaka takeyi.” Aysha tace, “To Mommy bakece ke biye

mataba da su Gwaggo. Kamarma itace kika haifa bashi Yayan ba. Ita Gwaggo Haliman ma ba tanayin komai bane dan ɗiyarta, ki duba akan auren Anaam yanda kika biye mata kuka hau kansa kukaita zagi gashi kinaji kina gani Abba ya hanashi zuwa ki gansa ma amma ita kullum tana waya da ƴarta. Kuma wlhy yanzu kusan kullum su Aunty Malika suna gidan nan kawo mata magani anata zubama Yaya a

abinci....”

“Na shiga uku, magani kuma Aysha?”.

“Wlhy Mommy da gaske nakeyi, to duk

kusancinki dasu Aunty Malika matsayinsu na

ƴan uwanki dasu ake haɗa kan cutar da Yaya,

jiya bakiga abubuwan da suka kawo mata ba

harda zoben mallaka wai bazai sake kallon

wata mace ba a duniya sai ita sai abinda tace

masa ko ke albarka, na rasa yaushe suka

ɗinke da Gwaggo Halima haka har suke abu

batare da ke kin sani ba keda Gwaggo”. “Na shiga uku, ni halima zataci amana ta

haɗa kai dasu Malika a sabautamun yaro

 

 saboda ƴarta tayi farin ciki?....”

Fitt Anaam ta ƙwace wayar daga hanun

Aysha ta kashe. “Blood kinada hankali kuwa?

Ya zaki faɗama Mommy irin wannan

maganar?”.

“Ya bazan faɗa mataba Anaam. Kin san ko

suwaye su aunty Safarah? Wlhy rashin faɗar shine mafi munin kuskure dan hatta ke da kanki sai sun sabauta rayuwarki, ɗan sauran zuminci kuma da muke tattali su ɓarar mana da shi. Ita kanta Fadwa ɗin taimakonta nayi, dan wata ƙungiya garesu ƴan baza'a zauna da kishiya ba, inma an zauna da ita saita koma tamkar babu ita a wajen miji, kina tunanin a hankali bajan ra'ayinta zasu cigaba dayi ba harta koma cikinsu. Koba komai ita ɗin jininmu ce, yana da ƙyau muyi duk yanda ya dace domin ta dawo hayyacinta. Yaya baya son yanke hukunci cikin fushi, amma tunda kikaga yau yakai da marinta to idan takaisa maƙura komai zai iya lalacewa”.

(Aysha kenan, dan ma bakisan akan sani ta zubar da ciki ba akan makircin kakarku) Anaam ta faɗa a zuciya, a fili kam saita kai zaune tana mai dafe kanta.....

A ɓangaren Fadwa kam Mommy na yanke waya kiran Gwaggo Halima na shigo mata.

 

 Sabon kuka ta ɓarke da shi tana zayyana mata

abinda ya faru, harda kiran Mommy datai

amma ta yanke mata waya...

“Kan ubancan, mi Nafi ke nufi Share! ya

mareki ya mari banza?. A to lallai idan tace wannan layin zamubi ni da ita bazatai mana ƙyau ba. Ai dama su Malika sun tabbatar min abinda yafi hakama zai iya faruwa saboda Nafi maciji ce da fuskar tana. Aiko zan tabbatar mata Share! bai mareki a banzaba dan wlhy saina rama miki”. Ta yanke wayar.

★Sai da Gwaggo ta gama sauraren Mommy data isa sashenta a rikice tsaf sannan ta saki murmushi irin nasu na tso!in makirai. Domin kuwa anzo gaɓar da ta jima tana jira kenan. Kallon Mommy tai da dafa kafaɗarta. “Nafisa Halima zata iya fiye da haka domin wannan ƴar tata. Jikina ya fara sanyi da al'amarinta tun lokacin zubewar cikin Fadwa. Karki manta itace ta fara kawo shawarar a sami malamin dazai aiki akan Mustapha da yarinyarnan ta wajen Usman. Abinda yasa naƙi yarda a lokacin na tabbatar idan muka biye mata wataran zata haɗo wani abin a bama Share! yaci a zuwan dan ana son rabashi da Zuwaira ne. Ki tuna Halima ƙudace, domin samun biyan bukatarta rai ba'a bakin komai yake ba.

 

 Tunda kuma ta haɗa kai dasu Malika to komai zai iya faruwa da Mustapha ciki harda rabashi da ke kanki uwarsa, dan kuwa ke shaidace, nice na haɗa auren Halima da Sadiqu, amma gashi nan babu mai cin dukiyarsa daga ita sai ƴaƴanta sai wanda ta zaɓa a dangi. Gasu Muhammadu nan ƴan uwanta tasan yanda zata samesu gefe ta kalallame ta dawo wajenmu tana nuna mana tana tare damu. Kin dai san duk son da Halima zatamana bai kai ya na ƴan uwanta ba tunda ba haihuwarsu nayi ba. Kuma kodan wannan dukiyar dake zagaye da Mustapha ai Halima bataso zaunawa ba tunda tasan yanda ta mallake Sadiqu dolene itama ƴarta ta mallaki Mustapha yanda koke kanki bai isa yaji maganarki ba, danni tawa mai sauƙice kwana nawa ya rage ALLAH na tuba”.

Kalaman Gwaggo ba karamin hautsuna zuciyar Mommy sukai ba. Gaba ɗaya tama rasa ina zata kama ta riƙe a wannan gaɓar. Shigowar kiran Gwaggo Halima ya saka tunaninta katsewa. Ta dubi Gwaggo, “Itace fa take kirana”.

“Ɗaga muji mizata faɗa, nasan dai ƴar tata ta kirata itama ai”.

Dagawa Mommy tayi, ta saka hansfree yanda itama Gwaggo zata iya ji. Daga can Gwaggo

 

 Halima dake a wuya muryarta a shaƙe ta fara

magana batare da ko gaisuwa ba. “Yanzu

Fadwa ke kirana Share! ya mareta, tace kuma

ta kiraki ta sanar miki amma bakice komaiba

kin yanke waya. Kome hakan ke nufi kenan?”. A harzuke Mommy ta maida mata murtani.

“Abinda duk zuciyarki ta baki Halima. Nifa

bazan ɓoye miki ba na gaji da yawan kai ƙarar

Fadwa. Ita kullum bazata iya haƙuri da miji ba

saita kawo kararsa. Ko haka taga wani a

cikinmu nayi? Sannan kin tambayetama mita

masan ya mareta? Taya zata kai masa ƙawaye

ɗakinsa na sirri su gyara saboda rashin sanin

ciwon kai. Ni yamun dai-dai, kinga gobe idan

ta sake saiya mata dukan tsiyama ba mari ba.

Sannan Halima ki sani, dukkan ƙulle-ƙullen

da kukeyi ke da su Malika naji kuma na

sani......”

“To idan kinji kin sani ɗin sai yaya Nafi? Kin

goya bayan ɗanki akan marin da yay yarinyata ma, to wlhy ki sani da hannuna zan rama mata marin da yay mata, idan shi ɗin mahaukacine zan maidosa hankalinsa kuwa. Kuma karki manta duk wani ƙulli da tuggunki a tafin hanunna suke, ko dama wanzami baya son jarfa ne, yanda kika mallakemin ɗan uwa kike tunanin ke naki ɗan bazai mallaku ba. Hhhhh Nafi idan kikace wannan layin zamubi

 

 ni da ke akan Share! da Fadwa wlhy muje

zuwa ɗan halak ka fasa....”

“Halima idan kin isa ke tujararriyace mu

zuba ɗin dan ALLAH, ni dake za'aga mai iko akan wannan auren. Shiyyasa dama ni tun farko ban so wannan haɗin ba kika katsatstsare ke da Gwaggo sai anyisa. Bayan nasa ƴarki bata da tarbiyya ko misƙala zarratin..”

“Matsalarkuce kuma wannan, ni nagama dake kuma muje zuwa ɗan halak ka fasa”. Gwaggo Halima ta faɗa da yanke wayar. Wani jijjiga Mommy tai zata maka wayar da ƙasa Gwaggo ta riƙeta.

“Kefa daɗina dake baki da hankali idan ranki ya ɓaci, ki nutsu, har mi akai kai Halima ne ma. Ai wannan yaƙin namune gaba ɗaya, shiyyasa naita nuna miki ki kwantar da hankalinki akan haukan da kike na tsinema Mustapha a banza saboda farin cikin Halima da ƴarta. To gashi nan tun ba'aje ko'inaba sun fara nuna miki halinsu”.

Kukan takaici da baƙin ciki Mommy ta fashe da shi...........

Ashe haka duniya take ƙafar kazace. Aminai biyu ya hakane   ? Yanzune fa wasan na ainahi zai fara, dan za'ai yunwa muga cikin

   

 kowa       .

 Next Chapter

Leave a comment

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: 70

BABU SO

Chapter: 70 Share:

Report

BABU SO View: 283 Words: 2K

Chapter 70 70

........Wasa farin girki wai amarya da tuƙa

 

 tuwon tiya goma. Ashe rikici a waya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima somin taɓi ne. Dan kuwa ba'a rufa awa guda cikakkiya ba sai ga Gwaggo Halima tazo gidan. Hakan yayi dai- dai da dawowar Daddy daga wajen aiki gidan shima. Yay sagade yana kallon Gwaggo

Halima data ƙaraso garesa tana huci. “Halima lafiya kuwa da magribar nan?”. “Inafa lafiya Yaya, Share! ya buɗe ƙwanji ya

shashsheka ma Fadwa mari amma saboda

son zuciya irin na matarka ta goya bayansa

saboda itace ta haifesa”.

Da mamaki sosai yace, “Mari fa dai? Ya

ALLAH mike damun Share! haka? Wannan ba

maganar nan bace shiga ciki nafara zuwa salla

kafin su Abubakar su dawo”.

A maimakon sashen Mommy ko Gwaggo da

da idan tazo gidan take shiga yau sai ta nufi sashen Mom.....

________________★

Rashin fitowarsa har aka kira sallar magrib yasaka Anaam kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son zuwa dubashi tanajin tsoro. Gani take kamar itama ɗin marin nata zaiyi. Harga ALLAH tana matuƙar tsoron duka a rayuwarta. Koda wani taga ana duka firgicewa take. Ballema har abada bazata taɓa iya

 

 manta dukan dayay musu ba ita da Aysha. Da sauri ta juyo jin motsin buɗe ƙofa. Sukaima juna kallon cikin ido ita da shi, ita ta fara janye nata tana sauke ajiyar zuciya dajin shakkar

kallon fuskarsa dake a matuƙar tsuke. “Ki tashi kiyi salla”.

Ya faɗa a taƙaice da juyawa zai fita. Harya kama handle ɗin ƙofar zai fita ya tsaya cak, juyowa yay a hankali yana kallonta saboda ganin yanayinta. Sai dai baice komaiba ya juya ya fita. Numfashi ta saki a hankali da miƙewa ta shiga toilet domin ɗauro alwala.

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye kuma sashenta ya zarto. Tunda ta idar da salla ta kasa tashi a wajen, babu abinda ke mata kaikawo, haka kawai marin nan na ɗazun da yay ma Fadwa ya matuƙar tsaya mata a rai, duk da kuwa ƙararsa kawai taji bawai yinsa akan idonta ba. Harya ƙaraso gabanta bata san da shigowarsa ba, ya kai tsugunne gabanta, tare da ɗago haɓarta. Cikin idanunsa ta zuba raunannun nata da babu gilashi, bata ganinsa fes yanda ya kamata, amma hakan bai hanata tsaidasu a

tsakkiyar nasan ba... “Mike damunki?”.

Ƙoƙarin janye idanunta tai a cikin nasa ya hana hakan, taso kauda kanta gefe nanma ya

 

 hana, saita ƙara tsuƙe fuska da tura baki. A karon farko ya saki murmushi, tare da kai yatsansa ya ɗalli lips ɗin nata. “K wai baki san shekarunki sun girmi wannan taɓaran ba Autar mata?”.

Hanunsa ta ture zata tashi, yay saurin

damƙota yana dariya, jikinsa ta faɗa, dan

haka suka zube ƙasa gaba ɗayansu. Ƙafarsa

ɗaya ya kwanta, tare da jawota ya kwantar a

cinyarsa ita kuma. Ya tokarar da ɗayar ta

jingina kanta. “Nayi laifi ne wai?”.

Hanunsa dake kan cikinta ta kamo, ta saka

babban ɗan yatsan a bakinta ta ciza. “Wai wai

shiii! Wace mugunta ce muka wannan?”.

Dariya ta ƙyalƙyale da shi. “Noorie muguntafa

babu ƙyau sam sam”. Ka ɗan ta murguɗa

masa baki “Punishment ɗin mai yawo ne ai”. “Shi kuma punishment ɗin mai rashin kunya

fa? yaya ya kamata ya kasance?”. “Sai an binciko a littafin shara'a”.

Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa ta gudu. Riƙota yay yana ƙaramar dariya. “Sarkin wayo ai ni tuni na binciko. Yanzu kuma zan ƙaddamar da shi”.

“Wayyo yaya! Wayyo ni yunwafa nakeji, tun safe banci komai ba.”

“Nima ita nakeji ai”. Ya ƙare maganar da manne lips ɗinsu waje guda. Ko sau ɗaya batai ƙoƙarin hanashi ba, saima gudunmawa

 

 data fara bashi, burinta kawai taga ya huce

daga fushinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama

hautsina masa kwanyar kansa, tun yana binta

a salon jarumta harya fita a hayyacinsa ya

ɗauka wata hanya da ban da karatun da ya

kasance mai girma ga Anaam. A yanzu kam ita

ya nema gigitawa, yayinda shi tuni ya fita

hayyacinsa har baya gane ita ɗinfa ƙanwarsa

ce. Sunyi matuƙar shagala a farantama

junansu ring ɗin wayarsa ya shammacesu. Da

ƙyar Anaam ta iya janye jikinta dake rawa

gefe. Shima nashin rawar yake fiyema da tata,

sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye haka, ya

rimtse ido da ƙarfi ya sake buɗewa saboda

ganin mai kiran. Ko'a turu a kwantosa bai isa

ɗaga wayar nan ba, dan babu makawa sai

Daddy ya gane halin da yake a ciki. Haka ya

barta harta tsinke wani kiran ya ƙara shigowa.

Yanzun ma kasa ɗagawar yay har saida ta

yanke, da ƙyar ya samu iya ɗan dai-daita

kansa bayan wasu mintuna sannan yay kiran

Daddyn Back.

Koda Daddy yaji muryarsa a shaƙe a zatonsa

duk ɓacin rai ne, dan kuwa yasan wanene Share! idan yay fushi. “Ka sameni a gida yanzun nan kai da Fadwa”. Bai jira cewarsaba ya yanke kiran. Shima ɗin baice komaiba ya koma kwance tare da mirginawa jikin Anaam

 

 data juya masa baya ya rungumota da ɗaura

kansa a gefen wuyanta yana shinshina, ga

sanyin tiles na ratsasu dan harya huda

sallayar tana iya jinsa a jikinta shima haka.. Jin saukar hanunsa a ƙirjinta tai saurin

riƙewa. “Yaya kirankafa Daddy yakeyi”. Iska ya ɗan hura mata cikin kunne da ture hanunta ya ɗaura a inda yay niyya tun farko. “Koratama kikeyi kenan?”.

“Eh mana, Daddy ba abin wasa bane ai,

umarninsa yana sama da muradanmu”. Sassanyan murmushi ya saki da sake

ƙanƙameta a jikinsa, a hankali ya furta *_Ina ƙaunarki da yawa_*”. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa saboda yanda yay furucin a cikin wani irin wahalallen sauti. Taja numfashi mai kauri da cije gefen lips ɗinta sakamakon saukar kiss ɗinsa saman wuyanta. Bata iya ta ɗago ta kallesa ba harya fice daga ɗakin. Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya da sake kananneɗe jikinta waje guda wani abu mai girma na tsikarar ƙasan zuciyarta....

A sashen Fadwa kan duk da yaji a ransa itace takai ƙararsa wajen su Daddy bai mata magana ba, umarnin kawai ta samesa a mota ya bata ya juya ya fita abinsa. Taja wasu mintuna kafin ta fito dan har ya kunna mota

 

 ma.

Tafiya suke amma kowanne fuskarsa na gefe,

ita tana kallon mutane shi kuma titi har suka iso. baiyi mamakin samun Gwaggo Halima ba, Fadwa ta nufeta ta rungumeta tana sakin kuka. Lallashinta ta shigayi tana shafa bayanta da fuskarta wai tana neman tabon marin. Abin sai ya girmi kan kowa amma babu wanda yay magana sai Mommy ce taja tsaki da taɓe baki. Share! kam zama yay ƙasa a tsakkiyar ƙafafun Abie da Abba. Kansa a ƙasa batare daya kalla kowa ba ya gaishesu. Haka kawai yakejin tsananin kunyar Abie da Mommynsa fiye da kowa a wajen.

Abba da yaga mulmular da Gwaggo Halima kema Fadwa na neman yin yawa ya magana a kausashe. “K Fadwa tashi ki zauna da ƙyau bama son shashanci”.

Tashin tai zaune, sai a sannan kuma take

gaidasu. Iya su mazan kawai suka amsa.

mommy da Gwaggo babu wanda ya tanka.

Gwaggo Halima tai ƙaramar ƙwafa da ayyana

(Zanyi maganinku) a zuciyarta.. Abie ne ya

buɗe taron da addu'a, kafin ya maida

hankalinsa ga Share! cikin serious matuƙa. “Al-Mustapha miya haɗaka da matarka

harda mari? Bayan wannan ba ɗabi'ar dakaga wani a cikinmu nayi a gidan nan bane?”.

 

 Ƙasa Share! ya ƙarayi da kansa, cikin

matuƙar girmamawa. “Kuyi haƙuri Abie nayi

kuskuren aikata hakan, sai dai saida na

umarceta ta tashi tabar inda nake dan bana

son yanke hukunci cikin fushi, amma taƙi yin

hakan har takai nayi marin”.

“Amma banda abinka Babana ai kai

babbane, da taƙi tashi sai kai ka tashi ka bata

waje tunda kasan baka iya controling kanka a

yanayin fushin. Su mata haƙuri ake dasu a

kowane hali, domin hangenka da nasu sam ba

ɗaya bane ba, sai dai sunada sauƙin sha'ani

kuma ba koda yaushe ake cizawa a kansu ba”. “Hakane Abie, insha ALLAHU hakan bazata

sake faruwa ba......”

“Tama sake faruwar mana. Wlhy da kaina zan

rama mata mara mutunci kawai. Kai yanzu

dan baka da kunya Share! har kanada hanun

ɗagawa ka daki Fadwa a gidanka?”. “Yaya Halima! Ya kamata kiyi shiru abi

komai a sannu”.

“Wane kuma sannu Abubakar, bayan kanaji

yana lallaɓashi saboda ba ƴarsa aka mara ba”. Murmushi Abie yay da girgiza kansa. Cikin

dattako da nutsuwar da kowa ya sansa da ita ya fuskanci Gwaggo Halima. “Ba haka bane Yaya Halima. Da Share! da Fadwa da Anaam duka su ɗin ƴaƴanmu ne, bazamu taɓa sakaci da cutuwar ɗayansu ba ai. Da kinyi haƙuri zan

 

 kai inda kike buƙata nima ai”.

Baki ta taɓe da juya kai gefe. Nanma

Murmushin Abie ya saki kawai ya sake maida

hankali kan Share! da ransa ya ɓaci. “Babana

ina jinka miya haɗaku takai ga mari?”. “Ban taɓa fatan dan na samu matsala da

wata a cikinsu sai munzo gabanku ba. Amma

tunda ita tafi zaɓar hakan a koda yaushe fine.

Fita nai a gida tun safe ina wajen matsalar can

data taso a company, na dawo kawai na samu

ta cikamin sashe da ƙawayenta wai suna min

gyara. A yanda suke komai kai tsaye ya

tabbatar min ba yau ce rana ta farkon hakan

ba. Korarsu kawai nai na ƙyaleta domin ita

tasan bana son yanke hukunci cikin fushi,

amma saita biyoni bayan nace ta ƙyaleni a

yunƙurin farko da tai. Taya zata kawomin

wasu ƴan iska sashe, ta san adadin abubuwan

dana ajiye masu muhimmanci a ciki? Ko

bamma ajiye komaiba ita bazatai tunani da

hankalinta rashin dacewar kai wani can ɗin”. “Inafa zata san abinda ya dace tunda a nuna

mata barbaɗa magani shine kawai zaman aure”.

A harzuƙe Gwaggo Halima ta dubi Mommy

mai maganar. “Nafi wlhy ki iya bakinki domin

zai kaiki ya baroki allura ta tono galma”.

“Yo ta tono mana dan ubanta, abu mai sauƙi

 

 bayan ta tono ita galmar ta turbuɗata cikin

ƙansa yanda ko mayen ƙarfe ƙaryarsa sake

ganinta”.

Aifa nan take falon ya harmutse da hayaniya

tsakanin Mommy da Gwaggo Halima. Mamaki al'ajab sukabi suka sanya Share! cikin madaukakin imani. Yau kuma aminai biyune kema juna tujara haka akan abinda suke ganin shine mafi ƙololuwar alkairi a garesu idan suka ƙulla. Kai duniya ina zaki kaimu ne haka?. Da ƙyar su Daddy suka samu sukai shiru. Gwaggo kam tayi kamar bata a falon tai muƙutt da cuno baki gaba ita a dole takai maƙurar ɓacin ran abinda su Mommyn ke aikatawa. Acan ƙasan ranta kuwa dariya taketa kwasa. Yanzu kam Abba ne ya amshe da zancen yana mai fuskantar Fadwa.

“K shashashar inace da zaki bama ƙawaye damar shiga ɗakin mijinki? Haka kikaga iyayenki na mana? Wace irin mace ce ke da baki kishin mijinki? Ai wannan jama kanki rainine ma wajen su ƙawayen naki da shi kansa mijinkin. To saurara ki jini, daga rana mai kama irin tayau, hakan ta sake faruwa ni da kaina zan hukuntaki sannan shima nasa ya hukuntaki tunda koba aure tsakaninku

Yayanki ne.. Kinaji na da ƙyau?”.

Hawaye ta ta share tana jinjina kanta. “Zan

 

 kiyaye Abba insha ALLAHU. Amma Abba dama fa haushina yakeji, dan dama a kwanakin nan banda wulakantani babu abinda yakeyi saboda ya ƙara aure. Baya ganin kowa a gidan sai ita ƴar gwal.....”

“Shiyyasa kuka dage boka da matsubbata ke

da uwarki domin sabautamin ɗa. Su Malika na

kawo miki barbaɗe-barbaɗe kina faman zuba

masa dare da rana. To wlhy babu lallai babu

dole tun kan ai nisa sai ya datse igiyar auren

tunda bake kaɗaice mace ba a duniya......” “Dan ALLAH Nafisa idan baki sakashi ya

datse igiyar aurensu ba baki cika uwarsa ba,

kuma shi din bai haifuba a cikinki...” “Haka kikace?”.

“Eh na faɗa. bandama ƙaddara mi Fadwa

zatai da wani Share! can. Ko dama kun ƙulla

a haɗasu aure dan ku dinga maidamin yarinya

baiwarku”.

“Hahaha yo baiwa kuma ta nawa Halima.

Sai dai wata kuma dan ita kam ta riga ta gama zama labari”.

Ƙara hargitsewa falon yay, da ƙyar yanzu kam Abie da Abba suka sakasu yin shiru, dan Daddy dai ya mugun shaƙa zuciyarsa har wani zallo takeyi, gata tokare a maƙoshinsa kamar yay amanta ya huta.............

  End of book


End of book

     Leave a comment

  Post

omments

No Comments posted yet

   C[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_71_*
..........Gigitacciyar tsawa Daddy ya daka musu. “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ranta yay mummunan ɓaci, idan kuma kunji ƙarya bismillah marasa mutunci kawai. Ku har kun isa ku maidamu mutanen banza. Ku tashi kufita bama buƙatar zaman kowacce a anan”.

       Cikin ɓacin rai suka mike su biyun suka fice. Daddy ya cigaba da faɗa tamkar zai ari baki, da ƙyar dai su Abie ɗin suma suka taushesa. Haɗuwa sukai akan Fadwa da Shareff ɗin duka sukai musu tatas da faɗa musamman Fadwa a matsayinta na mace. Sai kuma suka koma nasiha a garesu. Daga nan suna jiyo hayaniyar Mommy da Gwaggo Halima, hakan yasa Gwaggo da har yanzu bata tofa nata ba ta miƙe ta fita wai zata tsawata musu. Nasiha Abie ya sake musu ta fahimta data saka zukatansu samun nutsuwa, musamman ma Fadwa da taga an nunama Shareff kuskuren marinta da yayi kuma ya nuna nadamar yin hakan da alƙawarin bazai sake ba. Duk da dai itama tasha nata, sun kuma nuna mata illar biyema su aunty Malika cikin hikima. Basu san babu abinda ke cizon zuciyar Shareff ba kamar maganar su aunty Safara'h ɗin nan. Sai dai baice komai ba dan a samu zaman lafiya, amma yay aniyar da kansa zaima tufƙar hanci insha ALLAHU.

      

        Da ƙyar wajen ƙarfe goma suka baro gidan, dan kuwa rikici ne na gaske ya ɓarke tsakanin Gwaggo Halima da Mommy har sai da Baban Fadwa ya kira waya dan baya ƙasar ne shiyyasa harta samu damar fitowa. Ya kuma janye mata wancan sharaɗin lokacin da zaiyi tafiyar saboda haƙuri data bashi akan komai ya wuce. Ashe akwai wani a gaba. Mommy dai taci alwashin sai ta nunama Gwaggo Halima itace ta haifi Shareff ba wani shege ya haifa mata ba. Haka itama Gwaggo Halima ta tabbatar mata cewa ita bata isa komai ba domin Shareff ɗin ba nata bane ita kaɗai..

     Kuka Fadwa ke masa tunda suka taho, dan kuwa rikicin Mommy da Mamanta ya matuƙar ɗaga mata hankali kuma, tana matuƙar tsoron abinda zai rabata da Shareff, tana masa so ne mai tsanani, wanda takejin in har aka rabasu zata iya rasa har ranta. Ya gaji dajin kukan, saboda shima zuciyarsa a wuya take kuma yanajin ƙuna da raɗaɗin abubuwa masu yawa. Sai dai shi jarumin mutum ne mai maida komai ba komai ba koda kuwa a ce ya zame masa komai. Dan haka har suka iso gida bai ce mata komai ba. Shine ma ya fara fita ya barta a motar, saida ta kai kusan minti huɗu a ciki tana cigaba da kukanta sannan ta fito ta rufe motar. Sashensa ta bisa kai tsaye, yana a falo zaune cikin yanayi na wanda baka iya ganemawa. Cikin jan ƙafa ta ƙarasa gabansa, ta tsugunna tare da dafa guyawunsa.

      “Ina tsugunne ne gabanka a matsayin ƙanwa Yaya Shareff, nasan ni mai laifukace a gareka tari-tari, na kuma yarda nayi kuskuren da kake son na fahimta tun kafin akai ga wannan gaɓar. Wlhy bana son zumincin iyayenmu ya lalace saboda aurenmu......”

    “Garama ya lalace, dan ta hakane kawai dake da su zaku dawo rayuwar hankali irin ta mutane. Ke kam rayuwarki naban mamaki matuƙa, mamaki irin wanda nake shiga kokwanto. Ba haka nai miki zatoba sam-sam a rayuwata ba, amma bazance ki dainaba kiyi tayi, shawara ɗaya zan baki kuma ta ƙarshe. Ya rage naki ki dawo akan ƙyaƙyƙyawar hanya ɗaya tak ki gyara halayenki muyi zaman aure na gaskiya, idan ba hakaba wlhy wlhy zan ɗauki mataki ne na ƙarshe dan bazaki maidani mahaukaci ba. Shawara ta rage gareki, ki cigaba da biyema duk wani mai zuwa gidan nan yana ɗauraki a hanyoyin da shi yake ado da su, koki zama mace tagari ki gina taki rayuwar a karan kanki. Idan kuma kika sake amfani da wani abu na kauce hanya domin mallakata, ko bani wani abu a cikin ruwan sha ko abinci ALLAH ya isa ban yafe ba!”. Ya ture hanunta tare da miƙewa ya shige bedroom abinsa.

     Hawayen da take son su zuba ma sam sunƙi zubar a yanzu, sai dai tasan gaskiya ya faɗa mata, dan kuwa a yanzu tana rayuwa ne da rayuwar su aunty Safarah, a baya komi za'a bata ta zubama Shareff a abinci bata taɓa yin hakan tunma tana gida, duk ma yanda zatai ƙoƙarin hanawa sai tayi, sai dai in Mama ta aikata bada saninta ba. Amma a wannan gaɓar ta rikice, idonta ya rufe saboda kishiya da kanta take aikata komai dan taga haske. Sai dai saɓanin hakan duhu take gani, sannan mai makon mallakarsa suɓuce mata yakeyi, kenan su magungunan na ƙarya sunfi yawa a cikinsu kenan? Ƙalilanne ake dacewa suyi aikin kuma basa wani jimawa sai kaga abubuwa sun ƙwaɓe. ‘Ya ALLAH’ ta faɗa tana mai fashewa da kukan zahiri.


    _____________★


       Harta fara jin barci a jiya bai dawo ba, dan ita bata san tare da Fadwa ya fita ba. Koda ta shirya ɗakin da Aysha ke kwana taje ta kwanta abinta. Ayshan batace da ita komai ba dan tasan yau Shareff ya koma wajen Fadwa. Ta ɗanyi murmushi ganin Anaam ɗin sukuku, ko bata fito ta faɗa ba tasan kewar Yayansu ke nuƙurƙusarta. Sai dai sanin itama Anaam nada halin I don't care wasu lokutan yasa babu wannan alamar akan fuskarta sam. Sai dai kuma koda suka kwanta ta jima batai barci tanata juye-juye. Sai da Ayshan ta ɗauke hankalinta da wasu labarai  sannan ɓarawon yay mata kamun kazar kuku. Ajiyar zuciya Aysha ta saki mai ƙarfi da kai hannu ta riƙo na Anaam ɗin. Tausayinta da ƙaunar ƴar uwarta na ratsa mata zuciya matuƙa....


       ★Kamar yanda ya saba da asuba sai da yazo ya tada su, Anaam ƙin yarda tai ta kalla inda yake taima shigewarta toilet. Juyawa yay ya fita shima yana mai sakin guntun murmushi. Itama Fadwa sai da yaje ya tadasu sannan ya wuce massallaci. Daya dawo bai shiga sashen kowacce ba ya koma nasa sashen ya kwanta dan jiya ya jima bai barci ba yanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zai ɓulloma matan nasa. Barci yasha sosai dan sai kusan goma da wasu mintuna ya iya tashi, baiyi mamakin ganin an gyara ko'ina ba ga ƙamshi na tashi, sai dai yaji sassauci a ransa dan Fadwa ta nuna masa ta yarda ta gyara abinda take shirin ɓararwa a idanunsa. Wanka ya farayi ya shirya tare da baje jikinsa da ƙamshin turarurrukansa masu ƙamshin daɗi. Koda ya fito a falo ya sami Fadwa zaune cikin kwalliya mai ɗaukar hankali. Tabbas ta ɗauka hankalin nasa da gaske, sai dai ya basar abinsa. Gaisheshi tayi, ya amsa a daƙile, bata gazaba wajen sake jero masa kalaman ban haƙuri da tabbatar masa zata canja fiye da yanda yake buƙata. Har cikin rai ya ɗanjin tausayinta, dan yasan ya mata hukunci dai-dai da laifinta  da har idan ita ba ibilisiya bace ya kamata yaga canjin. Huci ya ɗan furzar tare da ware mata hannayensa. Ai da gudu tazo ta shige jikinsa. Ya saki ƙaramin murmushi tare da sauke hannayensa akan bayanta ya fara shafawa alamar lallashi. Hawayene suka dinga silalo mata, ita kanta ta ƙara shaidawa Soulmate ɗinta zuma ne, ga zaƙi ga harbi. Ya ɗagota yana kallon fuskarta har yanzu dai babu fara'ar da take muradin gani a garesa. 

       “Kin san bana son kukan nan ko?”.

Kanta ta jinjina masa tana sharewa, ya raɓata ya wuce yana faɗin, “Ina zuwa bara na duba waɗan can ya suka kwana”. Kanta ta jinjina masa, ta bisa da kallo tana ƙara tsane hawayenta dake sakkowa. Ta san bawai ya gama hucewar bane, amma ko yanzu ta samu sassauci. Zakuma tabi duk hanyar data dace domin ganin ya huce baki ɗaya sun koma rayuwar farin cikinsu....


           A falo ya samesu su duka. Anaam na tsaye riƙe da cup na shayi idonta a tv tana murmushi. “Wato blood film ɗin nan fa zaiyi daɗi, sai dai guy ɗin film ɗin sam baimun ba shegen kunensa uwa na zomaye ALLAH”. Dariya Aysha ta sanya harda ƙyaƙyƙyawa tana leƙowa daga kitchen. “Amma wlhy kinci zarafin mutumin nan, ni banga wani kunen da kike masa sheri da su ba.”

       “ALLAH da gaske yanada kunnuwa gasu nan, ga shegen rawan kai a wajensa uwa dangin makaɗan zamanin jahiliyya, ALLAH an cuceta da aka haɗata da shi”.

        Alamar komawa yay ma Aysha data leƙo zatai magana, tai saurin komawa cikin bin umarninsa harda turo ƙofar kitchen ɗin dan ta tabbatar wata taɓarar za'ai. Rayuwar Yayansu na birgeta tun akan Fadwa, gashi dai mutum miskili da baya ɗaukar raini amma matansa nashan sharafin soyayyarsa. Cigaba yay da tsayawa a bakin ƙofar hannayensa harɗe da ƙirjinsa yana kallon Anaam ɗin kawai. Ita ko sam bata san da zamansa ba amma tanajin ƙamshin turarensa a hancinta wanda take ganin hakan normal ne tunda dama yana shigowa maybe tunna baya ne. Juyowa tai zata koma saman kujera suka kusa cin karo da shi dan ya baro ƙofar. Da sauri ta ɗanyi baya a zabure dan tsoroma ya bata. Cikin zafin nama ya riƙe cup ɗin shayin dake neman antayewa a jikinta.

      Baki ta tura gaba da ƙwaɓe fuskarta da tasha kwalliya. “Kai Yaya ALLAH ka tsoratani”.

     Idonsa akan lips ɗinta ya ɗage mata gira ɗaya, “Kin dai so ki tsorata madam”. Bakin ta ƙara tura masa tana ƙoƙarin janye jikinta. Hanata hakan yay ta hanyar riƙo ƙugunta, ya zuba mata mayun idanunsa cikin nata idon, tare da matso hanunta da nasa dake rike da kofin shayin yakai bakinsa. “Wayyo Yaya ni ALLAH zaka shanyemun tea ɗina”. 

      “K miyasa rowanki yayi yawa ne?”.

  “To kai miyasa kwaɗayinka yay yawa ne”.

    Murmushi yayi da kai yatsarsa ya ɗalle mata baki, “Magananniya da ba'a kadata. Sammin lipstick ɗin shima Please”. 

      “Tab ni ban saka da kai ba ni kaɗai zan shanye abuna”.

    Dariyarsa ya danne da ƙyar, ya ɗan ƙwaɓe fuska da langaɓe kai gefe, “Babie Please mana”.

    “Naƙi wayon”. Ta faɗa dayi masa gwalo tana tura lips ɗin cikin baki. “Ni kikama rashin m ko? Zan rama ALLAH”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Kafin ka rama na ƙara wani rashin m ɗin ma”. Ta zille, riƙota yasoyi amma tai tsalle gefe tana masa gwalo. “Zan rama ne yarinya ai zaki zo hannu. Oya muje breakfast”.. 

      Idanu ta ɗan waro, “Gashifa Aysha na mana anan”.

  “Kin manta tsarina kenan”.

Shiru tai cikin ɗan tauke fuska. Dan ta ƙwallafa rai a abinda Ayshan keyi. Amma sai batai musu ba ta kaɗa masa kai. Tare suka fita, sun iske Fadwa na ƙara gyara dining ɗin. A yau ma babu wacce ta kalla ƴar uwarta a cikinsu. Dan haka ya duba kowacce fuskarsa a tsuke. “Kun gaisa da juna?”.

    Shiru duk sukayi kowanne idonsa a ƙasa dan a serious yay maganar. Fadwa ce tai ƙoƙarin dannewa a shaƙe tace “Kin tashi lafiya?”. Baki Anaam ɗin ta taɓe da amsawa a shaƙen itama. “Alhmdllhi”. Komai bai sake ce musu ba, dan yasan a haka a haka watarana zai ci nasara. Wayarsa da yake latsawa ya ajiye, Fadwa ta fara haɗa masa abincin. A daidai nan Aysha ta shigo da ƙaramin tray. Wani irin ajiyar zuciya Anaam ta saki a hankali. Ya ɗan saci kalonta ta gefen ido sai yaji tausayinta. Ya fahimci tana son abinda Ayshan ke musu amma tabi umarninsa ta taho, shiyyasa yayma Aysha  text yace ta kawo mata. Kasa ɓoye farin cikinta tayi har sai da ta kalla Aysha da murmushi. “Thanks you blood”. Murmushi Aysha ta mata. Itama sai ta sake murmusawa. Har Aysha ta juya zata fita Fadwa tace, “Ki dawo mu karya mana Aysha”.

     “No Aunty gashi can na baro kar a barsa ya lalace shima”. Tai maganar tana nufar hanyar fita da ɗan hanzari dan karma Shareff ya tsaidata. Batama san shi baida niyyar tanka musu ba. Abincinsa yake ƙoƙarin fara ci kawai............✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_72_*
.........Abincin yakeci cike da nazarin kowaccensu. Fadwa nayin komaine a taka tsantsan na gudun yin kuskure fatanta komai ya wuce. Yayinda Anaam ke komanta kai tsaye hankalinta kacokan naga abincin da takeci tamkar ta manta da zaman kowannensu a wajen ma. A haka dai suka kammala Fadwa ta fara gyara wajen, dakatar da ita yay dan haka ta koma ta zauna. Anaam data ɗauka waya yayma magana, itama ta ajiye suka bashi hankalinsu. Nasiha ya fara musu a nutse tare da jan gargaɗi. Daga ƙarshe cikin kaushin murya da tabbatarwa ya ɗan bubbuga table ɗin da yatsansa.

       “Bazan lalace wajen zargi akan ku balle ƙin cin duk abinda kuka bani ba, sai dai zan tabbatar muku, duk wadda ta zuba wani abu koda a ruwan sha ɗinane domin samun wani cikar burinta ban yafe mata ba. Kuma idan na kamata bazan yafe mataba ko iya cigaba da zama da ita duk da babu tsarin rabuwa da ɗayanku a zuciyata. Shawara ya rage naku, kumu haɗu mu zauna don ALLAH cikin soyayya da mutunta juna, ko kuma kowa ya ɗauka layin da yaga zai dace da shi a shirye nake wajen maganin duk wadda take tunanin zata iya fin ƙarfi na. Na ƙarshe respecting juna da kuma iyayenmu. Wlhy idan wata a cikinku ta sake kuskuren yin abinda bai dace ba akan wani ko wata a cikin iyayrenmu sai na sakata nadama ta har abada, ya rage naku ku dawo hankalinku kokuma ku ɗaura daga inda kuka tsaya”.

       Har ƙasan zuciya kausasan gargaɗinsa sun shigesu, sai dai sunfi ratsa Fadwa musamman akan zuba masa magani a abinci fiye da Anaam da wannan gaɓar bama komai ta fahinta ba. Amma dangane da girmama iyayensu da juna ya shigeta matuƙa, dan yanayinsa ya tabbatar musu zai iya komai. Bayan ya sallamesu kowacce ta nufi ɓangarenta tana ƙullawa da kwancewa. Shima fita yay a gidan zuwa can gidansu gaida su Mommy tunda yanzu Daddy ya janye masa sharaɗin hana zuwa gidan. Sai dai koda yaje ya samu Mommy da Gwaggo basa nan. Bai so haka ba, dan yazone takanas ya lallashi mommy ɗin da bata haƙuri akan komai ma daya faru, sannan ya yini da ita yau. Gidan su Anaam ma ya iske Mamie da aunty Mimi sun fita, dole dai ya koma gida dan gwara yaje ya huta kawai shima.


      A ɓangaren Mommy da Gwaggo gidajen su aunty Malika sukaje sukai musu tatas, inda akai hargitsi bana wasa ba har saida takai an gurfana a kotun baba Ibrahim. Shima al'amarin ya ɓata masa rai, dan yajima dajin tsiyatakun da su Malikar keyi a gidajen aurensu. Sai gashi yau suna neman saka Fadwa itama kuma abin takaicin harda haɗin kan mahaifiyarta. Sosai yayima Gwaggo Halima dake matsayin matar ɗan uwansa faɗa, ya nuna mata kuskurenta na son ɗaura ɗiyarta akan bigiren da zai rusa rayuwarta a dunuya da lahira. Suma kuma su Mommy yay musu nasu faɗan, dan tun farko da basu nunama Fadwa komai tayi a gidan aurenta dai-dai bane daba haka ba. Yanzu gashi sun ɗanɗana mata tana niyyar zartasu kuma sun shiga damuwa, ta riga kuma ta ɗanɗana ba lallai abin ya iya barinta ta sauƙi ba.

       Nasihar Baba Ibrahim bata canja komai a jin haushin juna da Mommy da Gwaggo Halima keyi ba. Sai ma ƙara jin zafin juna dan kowacce nada sirrin ƴar uwarta a tafin hannu. Kuma kowacce taci alwashin nunama ƴar uwarta fawa ɗinta akan ƴaƴan nasu da kuma mazajensu da suke amsa yayanninsu. Da haka aka sake rabuwa baran-baran.....


____________________________


          Ga Shareff kam tun yana shashshare Fadwa harya dai ya sakko, mata da miji sai ALLAH. Sai gasu kamar komai bai faruba aka koma faranta ran juna, dan aranar ba ƙaramin rikita Soulmate ɗin nata tai ba, har yaji a karan kasa ta cancanci yafiya. Sai dai tsananin kishin mijinta na nan a zuciyarta. A duk sanda ta tuna akwai wata a yanzu bayan ita tare da shi takanji raɗaɗi mai zafi a zuciyarta. Sai dai ta ɗauka alƙawarin daina biyema su Aunty Safarah, bazata ƙara amfani da wani magani ba insha ALLAHU. Zata tsaya da ƙafafunta wajen kishin mijinta da ƙyautata masa kowacce ta ƙwaci kanta kawai. Dan tayi imani bazata taɓa son Anaam ba a zuciyarta, saboda tunda ta tashi a rayuwa da tsanar iyayenta da ita kanta ta rayu.

      A ɓangaren Anaam ɗin itama sosai take jin kishin mijin nata, dan akwana biyun nan da yake tare da watanta ba itaba tana matuƙar jin raɗaɗi da zafi. Abinda ya sauƙaƙa mata kawai zaman Aysha tare da ita. Amma ko shigowa yay wajensu sai tayi matuƙar dauriya take iya kallonsa har ta sakar masa murmushi. Banbancinsu da Fadwa kawai ita bata zafafa ba. Bata son Fadwa tun fil'azal saboda tunda ta mallaki hankalinta tasan Gwaggo Halima da su Fadwa basa son  iyayenta basa respecting nasu kamar su Daddy. Amma batajin tsananin tsanarta dan ita bata zafafama kanta abu, kawai idan ya ɓata mata rai ta nuna fushintane take anan da kwakwazo a wuce wajen. Daga haka kuma ta watsar zata fuskanci nagaba mai wucewane. Tadai ɗauka alwashin ƙyautatama mijinta da basa tarin tukuycin soyayyar daya jima yana mata tun bata san kanta ba. Duk wuya bazata yarda ta bijirema umarninsa ba ko cutar da Fadwa. Amma zata ƙwaci kanta akowane hali idan akai yunƙurin cutar da ita. 


      Lahadi da yamma mijinta ya dawo hanunta, ya gama kwanakinsa a wajen Fadwa. Da taimakon Aysha suka haɗa abincin dare na gaba daya kamar yanda ya sharɗanta. Ta nufi sashensa domin gyarawa Aysha kuma ta gyara mata nata duk da ma babu wani datti mai yawa kasancewar babu yara ba kuma wasu jama'a ne da yawa ke shiga da fita ba. Duk kaiwa da kawowar da Anaam keyi a sashen Shareff a idon Fadwa ne dake leƙe ta window ɗin falonta. Kai tsaye tasan wannan rawar jikin na Anaam wai za'a tarba miji ba basirarta bace Aysha ce. Tai ƙwafa da cije lips, a ranta tana ayyana yarinya ni dake mu zuba a nan gidan. Oho bama tasan tanaiba, dan koda ta kammala rufo sashen tai harda saka key saboda ya bama kowacce key. Batare data ko lura da Fadwa ba ta nufi sashenta dan ta samu tai wanka tunda tasan a koda yaushe zai iya dawowa gidan tunda ba aiki ya fitaba. Yaje can gidane Mommy ta kirashi duk da a cikinsu babu wadda tasan da hakan. Yadai ce musu zai fita kawai.  


        ★Ransa fes ya iso gidan domin jiya ma yazo ya gaishesu kuma shida Mommy babu wata damuwa. dan koda ya bata haƙuri akan duk abinda ya faru tace masa komai ya wuce a gareta kawai. Yaso yaji kamar ba haka bane a ransa, amma saita kore masa dukkan tantama ta hanyar sakin jiki da shi sukai hira da suka jima basuyi irinta ba. Kuma abin mamaki ko sau ɗaya bata kawo maganar Anaam ba ko abinda ya shafi aurenta. Hakama Fadwa. Sun tattaunane kawai akan auren Aysha da kuma komawar Maheer wajen aiki a yau.

     Sai da ya shiga dukkan sashen mutanen gidan ya gaida kowa sannan ya nufi sashen Mommy a ƙarshe. Tana falonta zaune Hussaina na haɗa mata ƙwaɗon zogale ya shigo. Fuskarta da murmushi ta amsa masa sallamarsa. Ya kai zaune shima fuskar tasa da murmushi. 

      “First love daɗi zakici haka?”.

Murmushi tayi mai nuna haƙora. “Ai gaka kaima kazo sai muci tare ko?”.

    “Harma na fiki lauma”.

Dariya tayi daga ita har Hussaina dake yin tata a ƙumshe. Ya gaida Mommyn, Hussaina ma ta gaishesa sannan tabar falon bayan ta kawo masa ruwa. A kwano ɗaya sukaci zogalan da Mommy cike da nishaɗi. Suna tsaka da cinne Gwaggo ta shigo. 

          “Ja'iri kazo zaka cinye mata ɗan zogalan bayan acan na baka kaƙi ci”.

  Murmushi yay da taɓe baki, “Naki kin saka ƙuli ne itako gyaɗa ta saka shiyyasa”.

    “Oh, da gyaɗar da ƙulin duk ba abu ɗaya bane?”.

    “A wajena ni dai da banbanci”.

Mommy dai dariya take musu kawai.


       Sai da suka kammala Gwaggo da Mommy suka dubi Shareff ɗin cikin komawa serious da ƙyau. Hakan daya ganine ya sashi nutsuwar shima ya maida hankalinsa garesu. 

    Gwaggo ce ta fara magana. “Mustapha abubuwa da yawa sun faru waɗanda basai mun zauna lissafi akansu ba ko sake maimaita batunsu anan gurin. Sai dai waɗanda suke faruwa a yanzu sune abun dubawa. Kayi haƙuri munyi kuskuren tilasta maka auren Fadwa ba'a san ranka ba, sai dai mu munyune domin ƙarfafa zumincin ALLAH. Amma ashe zuciyar uwarta cike take da tsatsa. Tunda har a matsayinka na ɗan ɗan uwanta zata iya neman asiri taba ƴarta ta zuba amaka a abinci ko abinsha ya tabbata zata iya kasheka wataran domin farin cikin ƴar tata. Mudai bazamuce dole sai ka saki Fadwa ba. Amma ka zauna kayi tunani mizai iya zuwa ya dawo nan gaba. Dan hatta cikin datai ɓari kwanaki mun fara zargin yarinyar nan zubar da shi tai tana akan sani”.

     A matuƙar razane Mommy da Shareff suka dubi Gwaggo. Har Mommy ta kasa haƙuri....

     “Gwaggo miyasa zakice haka a ina kikaji wannan maganar kuma?”.

    Baki Gwaggon ta taɓe, “Yo Nafi abin duniya na ɓuya ne, kawai nayi shiru ne ban faɗa mikiba. Amma a jiyyarta da nai asibiti na karanci abubuwa da yawa game da yarinyar wlhy. Sai dai ban tabbatar ita ɗin ta zubarba. Amma Mustapha kaje kayi bincike harka tabbatar da gaskiya. Sai dai kayi komai a sirrance basai ka faɗa mataba a yanzu dan karta toshe duk wat hanyar gaskiyarka. Abu na gaba akan aurenka na biyu ne, mudai ba son auren nan muke ba sam, amma munga kai kamar kana so. Dan haka mun yanke shawarar barinka da matarka ku zauna. Sai dai da sharaɗin zaka ƙara aure. Kuma munma zaɓa maka wadda zaka aura yarinyar kirki da tasan mutuncin kanta, idan ƙyau ne kuma duka matan naka ta fisu. Mun tabbatar zakaji daɗin zama da ita insha ALLAHU duk wani ƙuncinka zata ƙwaranye akan waɗan nan ƴan iskan yaran”.

         Sosai ya tsurama Gwaggo ido ko ƙyaftawa bayayi, babu abinda zuciyarsa keyi sai luguden daka. Ya haɗiye yawu da ƙyar. Harshensa na rawa yace, “Aure kuma gwaggo?”.

      Mommy ta amshe da “Eh aure Babana. Shine zai baka kwanciyar hankali muma kuma ya bamu, dan nidai kasan matarka ta biyu ba zan taɓa sonta ba, amma na haƙura in har kabi umarni na a yanzuma zan barka da ita. Idan kuma ka bijire su duka biyun zaka sakesu ka ƙara auren kuma koda bada zaɓina ba. Dan wlhy itama Fadwa ta fitamin arai. Ko kaunar jin sunan yarinyar nan banayi yanzu. Kuma ina nan saina tabbatar da nunama uwarta kai ɗin jinane ni na haifi abuna kuma. Dan haka kaje kayi shawara daga kwana daya har sati guda muna jiranka. Duk abinda ka yanke sai mu sani.”

      “Amma First love......”

“Bana son jin komai Shareff. Kaje kawai kayi tunani kafin ka yanke hukunci, yarinyar da muke so ka aura itace *_Bibah_* ɗiyar Luba na san dai ka santa”............✍
_ZAFAFA BIYAR_


*_INAYAH_*

_MamuhGee_


*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_


*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_


*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_


*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_


_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾


ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070


SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902


IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: *_Typing📲_*

      *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_
              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718*_73_*
.........Innalillahi.... Kawai yake jerawa a cikin zuciyarsa har ƙarshe. Ya kafe Mommy da Gwaggo da idanu ko ƙyaftawa bayayi. 

     “Katashi kaje kar magriba tayi, gashi kace gobe zaka koma aiki kana da buƙatar yin wasu kimtse-kimtse. Dan bana ma son Daddynku ya dawo ya ganka a gidan nan”.

          Kansa kawai ya iya jinjinawa, ya miƙe jiki a saɓule ya fice idonsa har wani yaji-yaji yakeyi. Da farko maganar Fadwa ta zubar da ciki ce ta dakesa. Sai dai maganganunsu na gaba sun goge na farko dan a ganinsa Gwaggo ta kawo zancen Fadwa ce ta zubda ciki domin baƙantata su sami damar shigo da zancen auren Bibah, amma kuma zuciyarsa taƙi daina masa wasiwasi. Bashi da wani ra'ayin zama da mata ko biyu tun ful'azal. Sai dai ƙadararsa ta zama haka. A yanzu kuma bayajin duk wuya duk rintsi zai iya rabuwa da Fadwa da Anaam. Dan kowacce da irin kalar soyayyar da yake mata a cikin zuciyarsa. Yama rasa ina zai kama ya riƙe ne a zancen nasu......

       Koda ya shigo gidan tsabar yanda zantukan su Mommy suka rikita masa lissafi baibi takan kowa ba tsakanin Anaam ɗin mai karbar girki, da Fadwa mai fita. Kai tsaye sashensa ya nufa. Sai bayan sallar magriba mmn abu ke sanarma Fadwa kamar fa taga motar Shareff. Da mamaki tace “Yaushe ya dawo gidan ban sani ba?”.

     “Inaga lokacin kina ciki ne kina wayar nan”.

     Ɗan jimm Fadwa tai na wasu mintuna, sai kuma ta shiga bedroom ta dan karo turare ta fito. Kai tsaye sashen nasa ta nufa. Cikin taɓe baki take bin ko Ina na falon da kallo tana mai shaƙar daɗaɗan fresheners da Anaam ta baza ko'ina tare da turaren wuta. Bedroom ɗinsa ta nufa dan baya a falon. Fitowarsa a wanka kenan, ya juyo yana kallonta. Taku take cikin gayu da yanga, sosai kwalliyar tata ta fita da ƙyau dan ko makaho ya shafa yasan ita ɗin gwanace wajen zaman zanawa. Ji yay kaso ashirin bisa ɗarin damuwarsa sun ragu. Ya sauke numfashi a hankali tare da buɗe mata hannayensa alamar tazo gareshi. Da sasaarfa ta karasa ta shige. Suka sauke ajiyar zuciya a tare. Sumbatar gefen wuyanta yayi, muryarsa a sanyaye ya raɗa mata “Kinyi ƙyau Babie na”.

       Ajiyar zuciya ta saki da murmushi, ta ɗago tana mai kallonsa, sai kuma ta manna masa kiss a ƙirjinsa. “Nagode Soulmate barka da dawowa”.

   Kansa ya jinjina mata, ya kai hannu ya ɗan shafi fuskarta. Murmushi ta sakar masa da janye jikinta a nasa. Baice komai ba ya karasa gaban mirror domin shafa mai. Itama sai takai zaune a bakin gado tana faɗin, “Kayi wani iri kamar mai damuwa. Ko wani abu ya faru ne?”.

     Ta cikin Mirrorn ya