Mijin Malama Complete Hausa Novel

 
*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

*_Arewabooks@Nimcyluv_


*1......*

_Allahamdulillah! All thanks to Allah_ _Subhanahu wata'ala, for the opportunity, and ability to start this book MIJIN MALAMA. Am back_ Bayan kammala littafin *IDAN BA

KE* labarin Yaa Sheikh da Halisa. Nasan You have been waiting for so long, Ma sha Allah i really appreciate for the love's nd care, i wnt to let everyone know, wannan labarin ya fi ƙarfin shekara guda a zuciyar Sarauta, ban sani ba, but I knw one thing duk wanda bai karanta zai yi missing. No complain❌ You guys make me proud Sarautar love's you💞🫣.


A lullume garin yake, sakamakon yanayin sanyin da ake ciki, wanda ya fara tun watan Ogusta zuwa watan da ake ciki na Nuwamba. Hazo ne ya yi wa samaniya ado, ga iska mai ƙarfi dake ta shi tana ƙara haddasa sanyin shiga jika, yanayin hunturun daban yake dana ko wacce shekara. Mafi yawanci lokuta a irin wannan ƙarnin manyan cututtukan da suke gaba da sanyi suka fi ta shi, irin su mura, asthma, sikila, ciwon ido, lamoniya, bushewar fata, haɓo, hatsarurruka a titi da sauransu.


Daidai by pass na First bank  motar su ta tsaya akan titi saboda go-slown da hazon ya haɗa, tafiyar 9min (4.8km) ce tsakanin Lodge Road zuwa Aminu Kano teaching hospital. A hankali ta ɗago kanta dake sunkuye tun shigarta cikin motar, fararen Idanunta dake maƙale cikin farin Glasses mai ɗauke da photochromic ta watsa akan titin a nutse. Da ƙyar ta fisgi numfashi saboda a ƙirji yake tsaya mata.

"Jeederh!"

Latifa dake zaune a mazaunin driver hannunta riƙe da string motar ta kira sunanta, tasan ta ji ta sarai don haka bata buƙatar ta amsa, Latifa ta ci gaba da cewa. "We live by our own destiny, kuma Allah na son mu haka, You should not worry about that"

Sai a lokacin Majeederh ta ɗan juya kaɗan jikinta a kame tana curewa waje guda, ji take kamar ita kaɗai ke jin sanyin, duk da cewa Latifa ta rufe Glasses ɗin motar ta kashe a.c.

Baki ta buɗe ta cikin liƙab ɗinta za tayi magana,sai kuma tayi shiru can dai ta ce.

"Worry?" "Kamar haka na ce" cewar Latifa "Kada ki yaudari kan ki dole kina cikin damuwa, duk yadda ki ka kai da zurfin cikin ki, nasanki tsayin shekaru talatin da biyar, komai da komai naki na sani, After that, I am your friend"


Malama Majeederh jin ta kawai take bata fahimta, gangar jikinta ce kawai a motar, tunaninta, nutsuwarta gabaɗaya sun yi ƙaura daga gare ta. Kalaman Abbu su ne suke mata amsa kuwwa! A kunnuwanta.

Latifa bata gaji ba domin ko Aku zata shafa mata lafiya. "Ki zo ki aure Mijina Majeederh zamu zauna lafiya,na gaji da ganinki haka ba aure, na kasa jure yanayin ke ake faɗawa magana ni nake jin zafinta a zuciyata"


Cikin sauri ta juya ta kalli Lafita a ranta tana ayyanna girman wautar Latifa, corner Lafita tayi da kan motar tare da sulalewa gefen gwalta ta shiga cikin asibitin Aminu Kano kai tsaye!


"Yes,Malama  Majeederh Abdul'aziz Khan" ta ci gaba da driving tana faɗin "Sweetheart ya amince zai aureki, Kinga amintarmu zata sake ƙarfi, ba zan taɓa ɗaukarki matsayin kishiya ba, ki amince Please Please Jeederh"


"Ke da mijinki kuna buƙatar ganin psychiatrist" Malama Majeederh ta furta a nutse cikin sanyin murya. Dariya kawai Latifa tayi tana girgiza kai, a ranta ta saka dole tayi forcing Jeederh ta auri mijinta, parking tayi a inda aka tana da domin ajjiye motoci. Ita ta fara fitowa hannunta riƙe da key ɗin motar sai waya, ganin Majeederh bata fito ba ya sanya ta zagawa just to find what's happening. Hannu Majeederh ta saka ta buɗe murfin motar, tare da zuro ƙafarta waje.

Sai a lokacin Lafita ta lura da yadda farar ƙafar Majeederh ta kumbura har wani ƙyalli take, yanayinta ya sauya gabaɗaya yadda ta kumbura ta buɗe zai bawa kowa mamaki. Da ƙyar ta yunƙura ta fito daga motar can ƙasan ranta tana kiran sunan ALLAH.

"Kamar mai suger? Wannan kumburin ya yi yawa Majeederh, Mami ta gani? Abbu ya gani?" A duk jerin tambayar da Latifa taiwa Majeederh ba wacce ta amsa ko inda take bata kalla ba ta nufi ɓangaren data zo.


Da yake Dr Jamal ya san da zuwan nata domin shi ya bata appointment ya sa kai tsaye ta kira number shi, yana ɗagawa ya ce ta shiga. Latifa ta miƙe zata bita zuwa office a kame ta ce.  "I need Privacy"

"Take your time" cewar Latifa tana watsa hannu. Brown ɗin Abaya ce a jikin Majeederh, wacce ta amshi fatarta, sai babban hijabi daya sauka har ƙasa wajan ƙafafuwanta hannunta sanye da safa, fuskarta rufe da liƙab ga Glasses ɗin da ya yiwa idanuwanta murfi. Babu abinda ake gani a jikinta sai ƙwayar Idanunta ƙafarta kuma hijabi ya rufe. Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, budurwa ce bata taɓa aure ba shekarunta Talatin da biyar ciff a duniya, cikakkiyar Malamar addinin Musulunci ce, ɓangaren boko ba ba a barta a baya ba.

Zaune ta samu Dr Jamal suka gaisa cikin fara'a ya ɗakko wani babban file ya ajjiye gabanta tare da zaro x-ray ya ɗaga sama ya ce.

"Finally, bayan tsayin shekaru biyu yau mun samu damar gano abinda ke damunki"

Wahalallan numfashi ta sauke a ɓoye,tana yiwa Ubangiji kabbara.

Ta juya idanunta alamar tana son jin me bincike ya nuna? Dr Jamal ya ce

"Mun sha wahala, ko na ce muna kan shan, sai dai duk wacce zamu sha bayan taki take"


Idanunta a ƙasa ta harɗe hannu a ƙirji zuciyarta na bugawa da ƙarfi amma ba zaka taɓa ganewa ba, kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin halin jinya. "Ƙari ne ya fito miki a ciki, shi ya haddasa kumburin cikin, shi ne kuma yake girma kullum a cikinki har wasu suke fassara ki, ya yi girman da sai dai ayi miki operation a cire, mun samu issues na wannan domin wata idan ki ka ganta zaki ɗauka ciki ne da ita wata tara"


"When za ayi operation ɗin?" Ta faɗa a taushashe ita kaɗai ta san halin da take ciki, bata iya barci ciwon ya ci ƙarfinta burinta a rabata da shi.

"Wednesday, In sha Allah ki zo gobe da yamma da shirin operation" Shiru tayi domin duniyar ce gabaɗaya tayi mata zafi, kamar ta ɗauki wuƙa ta soka a ƙahon zuciyarta haka take ji, rana zafi inuwa ƙona, gida babu daɗi waje babu, family babu, uban daya kawota duniya shi ne ya jefata cikin wannan halin ba zata taɓa yarda Uba zaiwa ƴar shi asiri bisa ƙudirin zuciyarsa ba sai akanta ta gasgata haka, tana rayuwa da asirin mahaifinta a jikinta tana rayuwa da baƙin tabon daya shafa mata wanda ba kowa ya san da hakan ba. "Malama Majeederh Abdul'aziz Khan!"

Dr Jamal ya kira sunanta. Ta miƙe tare da rungume ƙirjinta kamar yadda ta saba ta jima kafin ta ce.

"Thank you,Dr Jamal"

"Your Wlcm, Allah ya baki lafiya" she just smile and quickly leave the office.

Sai ta daidaita nutsuwarta kafin ta fita, tana zuwa ta samu Latifa na waya kallon juna su kayi tana jin Latifa na cewa.

"Wallahi taurin kai ne da Jeederh banda haka mene abin ƙin amincewa da aurenka Sweetheart?"

Ta cikin wayar Aliyu haydar ya sauke numfashi ya ce.

"Tana da gaskiya"

"Wacce gaskiya Beb? Ni da Majeederh ƙawaye ne mun yi trusting juna don ta auri mijina ai ba wani abu ba ne right?"

Murmushi kawai Aliyu ya sauke mata ta cikin wayar, dake waya biyu yake da su, ɗaya a maƙale a kunnenshi, ɗaya kuma a hannunsa idanunsa zube akan screen ɗin ya kafawa photon Majeederh idanu, gabaɗaya jikinta a rufe yake photon kuma tun tana makarantar Noor-Ul-Iman School.

Latifa jin Mijin nata Aliyu ya yi shiru ya sa ta ce.

"Kayi shiru, ko baka sonta?" A nutse ya ce

"Laɗifa Omar, abar maganar haka ya jikinta?" Ta juya ta kalli Majeederh wacce ta shige tana tafiya a hankali jikinta ya ƙara yin sanyi sosai..

"She's critical condition, tana cikin mawuyacin hali bata son nunawa kawai don Allah Sweetheart kayi conversing nata ta aureka kaga sai mu zauna mu biyu"

Bai ƙara magana ba ya kashe wayar yana rufe idanu, bai taɓa ganin fuskar Majeederh ba, ko surar jikinta ko da yaushe a suturce take kaifin Idanunta shi ke ruruta masa abinda yake ji. "What kind of love is this? Ina Son ki Malama Majeederh Abdul'aziz Khan"

Kashe wayar Latifa tayi tasan Aliyu haydar baya ƙaunar auren Majeederh baya sonta bakiɗaya, ita ce ta takura masa har ya amince.

Da sauri tabi bayan Jeederh lokacin tana tsaye gaban motar jikinta duk rawa yake ta kifa kanta saman motar.

"An very sorry for keeping you waiting, muje ko?"

Jeederh bata kalli Latifa ba ta buɗe motar ta shiga, abubuwa da yawa suke damunta ga ciwon Limoniyarta dake shirin ta shi. Ganin yanayin Malama ya sanya Latifa jan motar da sauri Allah ya taimaka babu go-slow har suka isa Lodge Road.

Babu kowa a unguwar sai wasu samari guda uku wanda suka damu jama'a, tunda Motar su Majeederh ta tsaya samarin suke kallon motar, a kame ta fito hannunta riƙe da waya domin ko jaka bata ɗauka ba, cikin nutsuwarta da kamilalliyyar muryarta wacce ko Latifa sai tayi da gaske take jin me take cewa saboda sanyin muryar da jan aji irin na Malama Majeederh Abdul'aziz Khan bata fiye maimaita magana ba.

"Jazakallah-bil khair Latifa Omar"

"Ur welcome, bari na shiga gida sweetheart ya dawo tuni" jinjina kai tayi.

Jeederh na ƙoƙarin nufar gate ɗin gidan su ka ji saukar muryar wani yana cewa. "Karuwa an dawo ne" wani irin runtse Idanunta tayi, zuciyarta ta buga ƙirjinta ya riƙe nan take ta shiga kokawa da numfashinta.

Samarin su kayi dariya ɗaya daga ciki ya ce

"Maganar gaskiya Yusuf ya faɗa, ana fakewa da addini ana yawon karuwanci gari gari" cewar Kabiru.

Yusuf ya ƙara cewa "Babu mamaki idan ka cire hijabin jikinta tsirara zaka ganta, abun fa duk gaibu ne shi ya sa ban fiya yadda da mace mai hijabi ba, Allah ya isan Muslunci ke fa namanki ya halarta aci kuma.....,"

Kau! Kau! Kau! Aka ɗauke Yusuf da wasu kyawawan tagwayen maruka, Majeederh kasa motsawa tayi saboda riƙewar da bayanta ya yi ta shiga kiran sunan ALLAH. Latifa ta juya da sauri ganin Mijinta Aliyu Sufyan Alhassan ta ce.

"Ka barshi, shi da Allah tabbas yana ji kuma yana gani zai musu hisabi tsakaninsu"

Aliyu ya ture Latifa idanunsa ya rine jikinsa na kyarma ya ce.

"Zan ga uban daya tsaya maka, zaka maimaita maganganunka a gaban alƙali, how dare you insulate my wife like that?" Da sauri Latifa ta ce "Your wife, Aliyu?"

Sai a lokacin ya fahimci sakin layin da ya yi kamar zai tashi sama ya ƙwace key ɗin hannun Latifa tare da shigewa mota ya bar wajan.

Abun ya bawa Lafita mamaki sai bata damu ba tasan zafin zuciyar Aliyu baya iya saita kansa.


Malama Majeederh na shiga bedroom ɗinta toilet ta shige ta sakarwa kanta shower tun daga tsakiyar kanta har ƙasan ƙafafuwanta, bata damu da ciwon Limoniyarta ba hanyar da zata shaƙi iska kawai take nema, zuciyarta a cushe take.

"Allah kana kallo ban taɓa riƙe hannun ko wanne namiji ba, ba a taɓa riƙe hannuna ba, Ubangiji ka shiga cikin lamarin" duk yadda taso tayi kuka amma ta kasa. Latifa ta samu Mami a parlour ta ce "Sannu da gida Mami"

Wani irin kallo tayi mata ta ce "Kici gaba da biyewa yarinyar banza irin Majeederh, wallahi zata ɓata miki tarbiyya kuma zan kira mahaifiyarki na sanar mata" Latifa ta ce

"Haba Mami, a gida ku aibata Majeederh a waje ma haka? Ko tausayin ciwonta bakwa ji, mene laifinta?" Mami ta ce

"Yanzu ke ba a ɗakin mijinki ki ke ba? Shekarar ki goma da aure Ita kuma tana yawan barbaɗa" Ruma dake zaune ta ce

"Ni wallahi kallon mai ciki na kewa Majeederh haihuwa yau ko gobe"

Latifa ta ce "Ko a film da littafan hausa ban taɓa jin Mace ta samu ciki babu ɗa namiji ba, Majeederh ba zata taɓa aikata zina ba,ciwo ne kuma Allah yana iya jarabtar bawansa mumini da haka, i trust with all Majeederh Allah na tare da ita, rashin aure da wuri baya nufin lalacewar tarbiyyar mutum!"

Tana faɗin haka ta fice daga cikin gidan ko wajan Majeederh bata shiga ba.

Tun da Majeederh ta shiga bedroom bata sake fitowa ba, hatta shigowar Abbu ta ji amma bata fito ba, jama'ar gidan ba su damu ba Aaliyyah ce kawai ta shiga damuwa. Wasa wasa har ƙarfe biyu na dare ko abinci bata ci ba, lokacin Aaliyyah na zaune ta kasa barci ta miƙe a hankali ta fita zuwa bedroom ɗin Jeederh taci sa a yana buɗe, a durƙoshe ta samu Majeederh ta haɗa uwar zufa jikinta na rawa da karkarwa daga ita sai rigar barci. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Anti Jeederh jikin ne?" Ta nufeta ganin kamar zata mutu ya sanya ta fita a gigice ta shiga kiran sunan ƴan gidan.

"Abbu, Mami, Anti Ruma, Raihana mun shiga uku Anti Jeederh zata mutu"

Kafin ka ce me duk sun fito tsakiyar Main parlour, Abbu fuska a ɗaure ya kalli Aaliyyah ya ce.

"Kirata nan"

"Ba zata iya fitowa ba" cikin tsawa ya ce "Ban damu ba, tama mutu mana?" Aaliyyah na ƙoƙarin juyawa sai ga Majeederh ta fito abinda basu taɓa gani ba shi ne hawaye akan fuskarta, ko mahaifin daya haifeta ba zai ce ya taɓa ganin kukan Majeederh tana babba ba sai yanzu.

Malama Majeederh ta zube a tsakiyar parlourn "ki faɗa mana mene yake damunki?" Cikin dauriya muryarta na rawa ta ce

"Abbu ƙari ne, haka Dr Jamal ya ce" ya kalleta yana son jin tausayinta amma ya rasa mene ya hana shi jin hakan..

Ta kasa daure ciwon ta ce "Ka tausaya mini Abbu" "ki tausaya kan ki Majeederh!" Cewar Abbu.


Ihu! Ta sanya a karo na biyu, tana ambaton sunan ALLAH. A wannan sa'in rayuwarta na cikin tsauni biyu ne, halin RAI ko MUTUWA. "Ya ALLAH" ta furta jikinta na rawa kamar an jona mata wutar lantarki. "Anti Jeederh mu je asibiti, idan ba a cire miki wannan ƙarin na cikinki ba, tabbas zai iya kai ruhinki zuwa kushewa"

  "La'ilaha illallah!" Ta ce. Ba ta taɓa jin azaba da raɗaɗi irin na yanzu ba, kamar ana hura mata wuta a mararta haka take ji. Wani nishi ta yi mai ƙarfi, Idanunta suka kakkafe tana girgiza kai numfashinta na sama, Aaliyyah ta gigice ta kasa yin haƙuri kawai sai ta fashe da kuka "Kada ki mutu don Allah, kada ki barni Anti Jeederh" banda Aaliyyah ba wanda ya damu. Majeederh ta riƙe hannun Aaliyyah ta sake yin wani nishin mai ƙarfi wanda ya fi na baya sai ga kukan jariri ya cika parlourn, zuciyar Abbu ta buga, aka shiga kallon kallo jikin kowa a sanyaye, Mami tayi ta maza ta ɗaga Majeederh sai ga jariri ya ƙara sa faɗowa ƙasa, sai ihu yake.

   "Mun shiga uku, MAJEEDERH haihuwa kika yi? Jariri nake gani haka? Babu aure babu miji ina aka samu ciki har nake ganin haihuwa?" Ba ta da amsa domin ita kanta ba ta tsammaci ciki ne a jikinta ba, bata taɓa kawowa ɗa take ɗauke da shi ba, me ya sa Dr Jamal ya ce mata ƙari ne? Yaushe ta samu ciki a ina kuma?. Cikin kuka Jeederh ta ce

   "Ban sani ba, ban sani ba, ba ni da masaniyar ciki ne a jikina, ban san ɗan waye ba, ban san  yaushe na samu ciki ba, ban taɓa aikata zina ba, wallahi wallahi ban san cikin waye ba, ban taɓa sanin ina ɗauke da ciki ba".. Cikin fushi damuwa da takaici Abbu ya ce "Allah Ya isa....


*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

*_Arewabooks@Nimcyluv_*


*2.......*

A raunace tana ƙoƙarin danne jaririn ta rarrafa zata riƙe mahaifinta, Abbu ya yi saurin ja baya yana nunata da hannu idanunsa sun yi jawur ya ce "Ɗan shege a cikin gidans? A tsakiyar parlourna Majeederh? Kina ta rayuwa da cikin shege a jikinki kina ce mana ciwo ne, ashe ni mahaifinki ki ka yaudara! Ki ka munafurta?"

Ya dafe ƙirjinsa abinka da farin mutum nan da nan fuskarshi tayi jajir.

"Allah ya isa, Allah ya isa tsakanina dake...,"

"Na shiga uku,Abbu" cewar Majeederh wacce ko motsi bata iyawa ga jikinta gabaɗaya jinin haihuwa ya wanke shi. Aaliyyah kuka take sosai ta durƙoshe gaban Abbau ta ce.

"Don Allah Abbu kada ka tsinewa Anti Jeederh, kada ka aibata ta ka ɗauki ƙaddara wacce zata iya faɗawa kan kowa, idan ka tsine mata da wanne zata ji, Abbu ka...," Tsawa ya dakawa Aaliyyah ya ce "Aaliyyah da wanne suna ki ke amsawa a makaranta?"

Cikin tsoro ta ce "Aaliyyah Abdul'aziz Khan!" Abbu ya nuna Malama Majeederh da hannu ya ce "To daga rana mai kamar ta yau na haramtawa Majeederh amsa sunanta tare da nawa, na zareta daga cikin yarana, na haramta mata dukkan amfani da wani abu daya shafi sunana ni Abdul'aziz ko sunan familyna Khan" Tun da ya fara magana Malama Majeederh ta kafe mahaifinta da idanu zuciyarta ta fara daina aiki, Idanunta ya sauya tare da jirkicewa zufa ke yanko mata ta ko'ina jikinta ɓari yake, da sauri Ruma ta janye jaririn tare da sanya reza ta yanke masa cibiya,ganin Mabiya wato mahaifa bata faɗo ba ya sa ta nemi abu ta ƙulle jikin cinyar Majeederh.

Ruma ta saka hannu zata ɗauki jaririn domin ganin me Jeederh ta haifa Abbu ya ce "Ruma idan hannunki ya ƙara taɓa wannan shegen la'anannan yaron zan miki Allah ya isa kamar yadda na yiwa uwarsa"

"Kayi haƙuri Abbu" cewar Ruma. Mami duk abin da ake tana tsaye a gefe ta kasa cewa komai, idan ta kalli Malama Majeederh sai ta dawo da idanunta kan Jaririn.

Aaliyyah ta zube ta ce "Abbu me ya sa hakan? Zaka bawa Anti Jeederh tikiti shiga duniya da hannunka,bayan komai ta aikata kana da kamasho akai ba ita ɗaya ba, mene ya sanya zaka hofintar da MACE MUTUM kamar Anti Jeederh,ita ɗin haske ce, farin ciki ce ta ji da iya jarrabawar da take ciki ta rashin aure da kallon da jama'ar gari suke mata, kayi bincike Abbu, kada ka yi ladama a lokacin da bata da amfani"

Hannu ya sanya ya ɗauke Aaliyyah da mari yana huci ya ce "Ba zan taɓa ladama akan na rabu da wannan shaiɗaniyyar yarinyar ba, wacce ta cuceni ta cuci tarbiyyar dana bata, babu abin da zan iya cewa Majeederh sai Allah ya isa, ban yafe ba, ban yafe har na koma ga mahalaccina ba zan yafe mata ba" ya juya ya kalli sauran yaranshi da matarshi ya ce

"Ni Abdul'aziz Khan na yanke dukkan mu'amalar dake tsakanina da ƴata Majeederh Abdul'aziz Khan, ko da wasa ta ƙara ambaton sunana a matsayin ni ne mahaifinta wallahi sai na tsine mata, domin ni a wajena bata da maraba da gawa! Duniya ce ki je zaki gani"

Ba fatan gaskiya Majeederh take ba, ba kuma neman afuwar Abbu take ba, domin shi ɗin kaifi guda ne, amma tasan zai yi ladama a lokacin da bata da amfani kamar yadda Aaliyyah ta ce. Burin Jeederh shi ne Allah ya bayyana mata uban Jaririn nan, ko itama zata samu damar tsine masa, tayi masa Allah ya isa kamar yadda Mahaifin daya kawota duniya ya yi mata, ta yi masa mummunan fata a rayuwarshi ta yi masa addu'ar ɗaukewar dukkan wani jin daɗi walwala na tsayin rayuwa, damuwa da ƙunci su mamaye farin cikinsa, duhu ya maye gurbin hasken daya haska duniyarshi.

"Tashi ki ɗauki shegen danƙi ki bar mini gida" Aaliyyah kamar zata haukace ta ce "Mami ki sanya baki don Allah, Abbu ina Anti Jeederh zata nufa? shin tana da gidan da ya fi wannan ne?" Sai a lokacin Ruma ta ce "Aaliyyah kada ki sanya na fara zargin kema kin munafurci Abbu" Aaliyyah ta juya ta kalli Ruma ta ce "Me kike nufi?" Ruma ta ce "Ina nufin abin da kunnuwanki suka je yi miki, kin jima da sanin Majeederh nada cikin shege ki ka ɓoye"

Wani irin mugun kallo Aaliyyah ta watsawa Ruma ta ce "Ki ji tsoron Allah, kuma akwai ƙiyama, Mami do something"

"Something?" Mami repeated. "Don Allah" Aaliyyah ta sake furtawa Idanunta ya kumbura sosai, tausayin Malama Majeederh ya kamata tasan tunda Majeederh ta kasa cewa komai hakan na nufin abubuwa da yawa.

Mami ta kalli Majeederh ta ce "Ki duba Majeederh babu alamar dana sani a idanunta, ni kai na da nake uwarta ta yaudareni, sai yanzu nake mamakin abin da ya hanata aure ashe mu muke hauka ita ta jima da sanin kan ɗa namiji shi ya sa babu littafin aure a  cikin littafan da take wallafawa, kin ja mana abin faɗa"

Da sauri Abbu ya ce

"Ta jawa kanta dai, domin ban haɗa komai da ita ba, ta je hakƙin Addinin Musulunci ma kaɗai ya ishe ta, kafin na buɗe idanu ki fice daga gidan nan"

Zuciyarta tayi nauyi bata da hanyar kare kanta, fatan ta Ubangiji data yarda da shi,kuma take bautawa ya bayyana gaskiya ya wanketa a wajan Mahaifinta ko da ba zai amsheta matsayin Ƴa ba. Ta juya ta kalli Jaririn ko Jaririya domin bata san me ta haifa ba, amma tasan samuwar babyn na nufin wani abu! Only God knows.

Da hannu biyu ta ɗauki jaririn ta miƙe da ƙyar jiri na ɗaukarta, ga wani ciwo da cikinta ke mata har yanzu mahaifa bata faɗo ba. Kanta a ƙasa cikin wata murya mai tsananin rauni wacce ko fita ba tayi sosai sbd yadda numfashinta yake riƙewa ta ce.

"Me ya sa zaka mai dani Gawa bayan da rai a tare da gangan jikina? Bayan da numfashi a ƙirjina? Me ya sa zaka bawa duniya ni Abbu wallahi bana da laifi ban san samuwar cikin ba, ban san waye da wannan alhakin ba, ban san waye yake da sanya hannu wajan ruguza rayuwata ba, ban san waye ya zama silar rabani da Mahaifina, dangina, haɗi da farin cikina ba, zan tafi Abbu ina roƙan ka yafe mini a duk sanda gaskiya ta bayyana ko da ƙasa ta rufe mini Idanu, zan raini kyautar ALLAH, zan raini Raba Gardama shi ne hujjar da zata iya fiddani daga zargi, Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri"

Aaliyyah ta cire hijabin jikinta ta sakawa Majeederh domin rigar barci ce kawai a jikinta, kuka take sosai tana faɗin. "Kiyi haƙuri Anti Jeederh bana da ikon taimakonki na kasa aikata komai kiyi...,"

Kuka ya ci ƙarfinta ta juya da gudu ta shige ɗaki ba zata iya ganin tafiyar yayarta ta ba.

Gently Malama Majeederh ta kalli Mami, ta juya ta kalli Ruma, da kuma Raihana wacce bata ce komai ba har yanzu. Ta jima tana kallon Mahaifinta kafin ta nufi hanyar barin parlourn jiri na ɗaukarta, tana jan ƙafa wacce ko takalmi babu ta buɗe gate tare da ficewa daga cikin gidan, kamar yadda take barin gidansu haka numfashinta ke barin ƙirjinta, ganinta na janye wa, jinta na raguwa, jaririn hannunta na neman ƙwacewa zuwa ƙasa.

Tafiya take jini na bin cinyoyinta, tafin ƙafarta na taka kan titi, tun tana jurewa har ƙafarta ta fara rawa jikinta ya saki ta ƙanƙame jaririn a ƙirjinta, slowly slowly ta fara ganin duhu a Idanunta tayi baya luuu! Zata faɗi a kayi saurin tare ta, ta faɗa jikin mutum ba numfashi a ƙirjinta.


Hospital

A hankali aka buɗe Ƙofar room ɗin tare da mayarda ita aka rufe slowly. Tsaye ya yi a kanta ya zuba mata narkakkun idanunsa ya ɗauki almost 5 minutes yana kallonta kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali zuwa gaban bed ɗin, ya ja kujera tare da zama akai, cikin nutsuwa ya sanya hannu ya ɗauki jaririn dake kwance yana motsi cikin tattausan showel ɗin da aka saka shi. Soyayyar Jaririn ya samu gurbi a zuciyarsa musamman da bai taɓa samun ɗan kansa ba, bai taɓa ganin gudan jininsa ba. "Ohh baby, your Dad is here" ya furta can ƙasa gudun kada ya tashe ta.

"His Dad?" Ta furta cikin magagin barcin dake ɗaukarta domin allurar bai gama sarkinta ba.

Ya ɗago kai da sauri ya kalleta ba ƙaramin harbawa zuciyarsa tayi ba, this is the first time da yaga fuskarta babu liƙab iya tsayin shekarun daya santa.

Kasa magana ya yi domin duk yadda zuciyarsa ke fasalta masa kyanta abin ya shige haka, musamman da tayi maganar kamar wacce bata hayyacinta idanunta rufe gashin idanunta sun kwanta luf luf gwanin sha'awa fuskarta ta ƙara haske.

"Kin farka? Ya jikin"

Muryarsa ta daki dodon kunnenta yanzu kam allurar ta gama sakinta ta buɗe manyan Idanunta da suka kumbura tare da sauke ganinta akan Aliyu Sufyan Alhassan. Ta runtse idanu yau ƙarya ta ƙare fuskarta available, Allah ya rufa mata asiri jikinta a rufe yake.

"Sorry,  In sha Allah komai ya zo ƙarshe zan wankeki wajan Abbu be patient" bata kalle shi ba, domin ƙirjinta ya yi mata nauyi babu wanda ya sake magana har Aliyu ya ce "I love my son, i love both"

"Ka barni" ta furta a kame cikin sanyin harshe. Aliyu ya gyara zama idanunsa akan fuskarta duk da bashi take kallo ba. "You're dreaming, ba zan sake kuskuren baya Jidderh,ba zan sake ba, ina son rayuwa da yarona tare da mother's of the son"

"Ni guba ce, zan iya zama illa ga kowa" ya tari numfashinta ya ce

"Ban dani Aliyu Sufyan Alhassan, ban dani Jeederh"  ta juya ta kalle shi kallon daya kusa zautar da shi hannunta ɗaya a ƙirjinta ta riƙe sosai cikin nutsuwarta da kamilalliyyar muryarta ta kame kanta sosai ta ce. "Baka da haɗi da ɗana, kada ka yaudari kan ka ka duba kusancinmu da Latifa ka barni" "Jeederh idan na barki ki ɗauka na bar duniya, Latifa kuma ta bani full opportunity na aurenki" cikin gajiya wa ta ce "ba zaka saman ba"

"Koda na halattawa kai na zama Uba ga danƙi? Wallahi Majeederh na shirya ɗaukan ko wanne ƙalubale akan ki, kuma idan wannan yaron zai sanya ki aureni zan je court ta mallaka mini shi,wanne Irin mallakawa ma? Bayan blood grp ɗina da na shi ɗaya ne, ko DNA text za a yi zai tabbatar da ni ne uban shi" Wayarsa ce ta fara ringing  sunan Wife ya fito ya ɗan ja tsaki har kiran ya tsinke aka sake kira lokacin Jaririn ya fara kuka, picking call ɗin ya yi tare da saka wayar a hands free.

Muryar Latifa na rawa ta ce "Sweetheart kana ina? 3days without you ina ka je ina ta kiran number ka a kashe" ba yabo ba fallasa ya ce.

"Ya akai Latifa?"

"Wani abu mai kama da almara ya faru, na kasa sanin babin da zan iya sanya Malama Majeederh"

Aliyu ya ce "Just go to the point  Wife" cikin damuwa Latifa ta ce "Majeederh ta haihu,na goya mata baya amma ta bani kunya ta sanya ina yawo da ita har ina kare cikin shege?" Ya tare ta faɗin

"Who told you that?"

"Ruma, ta kirani tun a daren da abin ya faru lokacin na tashi naga babu kai babu motarka, kwana uku kenan yanzu haka Majeederh ta gudu da ɗan gudun surutun jama'a kuma ta shaida ɗan shege ne, Ruma ta ce Majeederh ta bayyana musu cewa daga gidan Abbu ba inda zata sai gidan uban ɗan taci gaba da zaman karuwanci da shi"

Duk maganar da suke Majeederh na ji, tuni ta amshe ɗanta daga hannun Aliyu ta rungume shi,tana jin kawo yanzu shi ne kaɗai ya rage mata, shi zata kalla matsayin wani nata kuma zata kula da shi da dukkan iyawarta har kawo lokacin da gaskiya zata kure ƙarya.

"Ke yanzu kin Yarda Malama Majeederh Abdul'aziz Khan zata iya aikata ZINA?"

"Me zai hana Sweetheart? Tunda ga gaskiya ta bayyana kuma Allah ya isa tsakanina da ita, na gode Allah da ya sanya baka aureta ba, balle mu haɗa iri da shege" "Ba shege bane"

Da ƙarfi ta ce "Wallahi shege ne" cikin tsawa mai firgitarwa ya ce

"Latifa Omar idan ki ka sake sheganta mini yaro zaki sha mamakina, zan miki hauka zan nuna miki true color na" Majeederh ta dafe kanta a hankali ta miƙe bayan ta zare ƙarin ruwan da ake mata, ganin Aliyu ya juya baya yana masifa jijiyoyin kansa na motsawa ta sulale a hankali ta bar room ɗin rungume da jaririn nata.

Kamar mahaukaciya haka ta zama, Latifa ta hargitse tamkar zata cinnawa kanta wuta ta ce "Aliyu Sufyan Alhassan kasan me ka ke cewa? Mene haɗinka da yaron?" Cikin rashin damuwa kuma daman ya shirya amsar ko wanne ƙalubale ya ce.

"Yes that's my name Aliyu, kuma baki taɓa jin nayi hauka ba sai dai ina dab da shirin manna bikin haukan ke, tunda ba soyayyar gaskiya ki ke nunawa Majeederh ba"

Latifa ta zari key ɗin motar ta ce "Don't Tell me kana tare da Majeederh tsayin kwanaki ukun nan?" Ya ware hannu irin he don't care ɗin nan ya ce.

"Yhh, Ina tare da Ɗana da matata, Majeederh is my wife....


08119237616

*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

*_Arewabooks@Nimcylub_*


*3.....*

Maganganun Aliyu suka kusan tarwatsa mata zuciya, idanunta ya rufe kafin tayi magana ya ce "Ko a lokacin da nake yaro, ban taɓa kuka saboda wahala ba, ba kuma zan yi kuka saboda abin da zaki aikata ba, ki sawa ranki ba a haifi Aliyu domin sadaukarwa ba, amma an haifi ni domin bautawa Ubangiji da kuma cimma burukana, bana da burin daya shige zama da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan!" Ya fesar da numfashi ya ce

"Ban taɓa neman abu na rasa ba, kin san yadda nake zama mahaukaci akan abin da nake so....," Da ƙarfi Latifa ta ce "And so what Aliyu? Ni kuma zan tabbatar a wannan karan na zama sanadin da zaka rasa abin da ka ke nema, ka yi ta farauta wacce bata da amfani har zaki ya yi gaba da abin farautar taka, zaka san kuma kaci amanar matarka ni Latifa Omar zaka sani" tayi hanging off na kiran.

Tsakanin ita da Aliyu ba a san wanda ya fi wani shiga damuwa da baƙin ciki ba, shi yana jin baƙin ciki idan ta shegenta ɗan gidan Jeederh, yana jin tamkar gudan jininsa ta shegenta. Latifa Omar tana ganin Majeederh ta munafurceta tayi mata kyakkyawan zato ta ci amanarta, Allah kaɗai ya san lokacin data ɗauka tana bin baza, ko komai nata zai ƙare ba zata taɓa barin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya kasan inuwa guda da Jeederh ba.

Ta dunƙule hannu tare da kaiwa iska naushi cikin zafi ya juya yana faɗin.

"I can't take it any longer Majeederh, dole kiyi haƙuri mu zama abu guda" shiru not respond.

Ya riƙe ƙugu cikin sauke numfashi yana son ya saisaita kan shi ya kasa ya ce. "Ina son na je wajan Dr Jamal, i have something to discuss with him" nan ma shiru sai a lokacin ya juya zai sake kiran sunanta yaga wayam! sai gado da drip yana ɗiga a ƙasa.

Baki buɗe ya tsaya cak yana ƙarewa room ɗin kallo kamar ƙungi.

"What?" Cikin sauri ya buɗe ƙofa ya fita suka ci karo da wata nurse ya ce

"Heee Nurse" "Yes, Sir how can i help you?"

Ya juya idanunsa ya yi ta kallon wajan yana son yaga ta ina zai gano Jeederh. "Sir!" Kiran ya dawo da shi hankalinsa ya ce "Kinga wata yanzu da baby a hannu ta fita?" Ta shiru alamar tunani sai kuma ta ce.

"Yanayinta?" Ya ce "She's beautiful, fara tas yar yellow take tana da jiki zata kai 35 yrs going to 36" Ta kalli hanya ta ce

"Oh Malama Majeederh Abdul'aziz Khan?" Ya ɗaga ya ce "Exlty, where she's?" Ta ce "She Left, alright"

Ya yi baya a fili ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, why? why Jeederh mun shiga uku daga ni har ke" da gudu kuma yabar world ɗin ya nufi reception har zuwa parking lot na hospital ɗin amma babu ko mai kama da ita.

Motarshi ya shiga tare da yi mata key kamar zai tashi sama haka yabar cikin asibitin bakiɗaya wanda ya yi kwana Uku ciff a cikinsa.

Dr Jamal na zaune a office ɗinsa yana operating system sai gumi yake duk da sanyin A.cn dake office ɗin. Bell aka danna ya ce "Come in" buɗe Ƙofar akai tare da shigowa.

"Dr Jamal wai meke faruwa da kai ne, kwana uku baka cikin hayyacinka" ya share zufa ya ce "Tajju ina cikin damuwa"

"Problem?" Tajju ya maimaita. Dr Jamal ya gyara zama ya ce "Ka san Malama Majeederh Abdul'aziz Khan?" Gaban Tajju ya faɗi hakan ya tuna masa da wasu memories ya ce "Uhm, ina jinka" kai tsaye Dr Jamal ya ce "Ta haihuwa, kuma yanzu an nemeta an rasa, kwana kenan bana barci kullum sai na duba all scanning da na taɓa yi mata, wallahi tsayin shekara biyu result bai taɓa nuna mini Majeederh nada ciki ba ko da wasa, infact results ɗin na nuna she's Good, sai a satin nan dana sake mata wani ya nuna mini ƙari ne a cikinta shi ne ya haddasa kumburin Cikin, sai gashi kuma wai ta haihu harta gudu" cikin wata kalar hausa Tajju ya ce

"Innalillahi, subuhana"

Ya yi ta maimaita wa kafin ya ce "Amma tayi aure?" Dr Jamal ya ce

"Ko engagement ba tayi ba balle aure, bata taɓa aure a zahiri ma babu wani ɗa namiji daya taɓa cewa yana son ta"

Tajju ya miƙe ya shiga kai kawo cikin office ɗin da sauri kuma ya fice yana cewa "ina zuwa"

Yana fita mota ya shiga ya nufi gidan shi dake cikin Nassarawa. Tun da ya shiga bedroom yake tunani,akwai muhimmin abu da yake son tunawa amma ya rasa mene? Dr Jamal abokin Tajju ne gabaɗayansu likitoci ne.

A hankali ya ce "Malama Majeederh Abdul'aziz Khan? Ya Allah!"

Kwanciya ya yi nan take barci kuma ya ɗauke shi.

Can cikin barcinsa ya ci wasu maganganu na tashi a kunnenshi a firgice ya farka yana haɗa zufa jikinsa na rawa ya ce.

"Gang" ya miƙe ya ce "Gang team!" a haukace Tajju ya dinga fito da kayan wardrobe nasa cikin sa a wata envelope  ta faɗo ya ɗauka da sauri yana dubawa, har yanzu wani sassan yan ƙamshi ke tashi jikin envelope ɗin, ya duba da kyau idan har ba zai manta ba shekaru biyu kenan da bashi saƙon ya bawa Majeederh, shi kansa ba zai iya tuna abin da ya mantar da shi ba. A hankali ya duba jikin envelope da aka rubuta.


         *_No words to explain, no words to describe, no words to as your forgiveness, Wait for me, I'll be back sooner or later, Please Jee_*


Tajju na gama karantawa ko gyara bedroom ɗin bai ba ya zari key ɗin mota tare ficewa daga cikin gidan, tana ina zai fara? Ina zai ga Malama Majeederh har ya bata wannan saƙon? A fili ya ce "Allah na tuba, ban san me ya mantar dani ba" haka yaci gaba da driving.

Tun safe Majeederh take tafiya fuska rufe babyn ya yi shiru a jikinta, kamar mahaukaciya haka ta zama bata gane komai bata bambance komai, kiran sallar Magriba ya yi daidai da tsayuwarta a gefen wani shago a lokacin kuma babyn ya kama kukan yunwa, ta samu waje ta zauna ta shiga kallon fuskar jaririn ko Allah zai sanya ta gane dawa yake kama, amma abin mamaki komai nata ne, kamarsa ɗaya sak da ita idanunsa ne kawai da bai fiya buɗewa ba yasa bata gama gane ƙwayar tawa ba, ganin kukansa zai sanya hankalin jama'a ya dawo kanta ya sa ta zura shi cikin hijabi bata san me zatai masa ya daina kuka ba can ta tuna abincinsa yana jikinta ta ɗaga rigar asibitin dake jikinta tare da sanya masa nono a baki, babu ruwa ko kaɗan zai azabar zafi, haka ya dinga jan fata jin baya shan komai ya cika ya dinga tsala ihu. Sai a lokacin ta fashe da kuka take rungume shi ta ce.

"Asstagafirullah Ya Allah, ba san komai, na yarda da ƙaddara, Allah ka kawo mini ɗauki albarkacin Annabin rahama" a hankali ta dinga tattaro yawun bakinta tana bawa jaririn yana sha, tun tana bashi har yawun ya ƙafe bai kuma daina kuka ba. Ta miƙe riƙe da shi tare da ƙara sawa wajan shagon tayi sallama can ƙasa kafin tayi magana ta ji saukar muryar Abbu a kunnenta ta juya da sauri ta kalli T.v dake shagon, fuskar mahaifinta tar a t.v yana yi wa ƴan jarida bayani ya ce.

"Me kuke son sani?" Ɗan jaridar ya ce "Shin da gaske ne ƴarka Malama Majeederh Abdul'aziz Khan kan ta haihu? bayan duniya ta san bata da aure? Ko dai tayi aure a ɓoye ne, ko kuma zargin da ake a kanta ya tabbata?" Abbu ya yi dariya sosai yana kallon Ɗan jaridan ya ce.

"Ina da ƴa Majeederh, amma tawa yarinyar ta zama gawa tun tuni bata raye, ban kuma san yarinyar dake amfani da sunana da kuma sunan familyna ba, zan yi amfani da wannan damar wajan yi mata Allah ya isa har abada, zan kuma shaidawa duniya duk inda suka samu yarinyar nan mai amfani da sunana su jefe ta ko kuma suyi mata bulala akan laifin aikata zina, su kuma ɗauki mataki akan amfani da rigar Muslunci tana aikata alfasha"

Ɗan jaridar ya kalli Abbu sosai, da alama ya firgita da maganganun shi ya ce. "Kenan Malama Majeederh ba ƴarka ba ce wacce muke tunani?"

Cikin tsawa Abbu ya ce

"Yara biyar ne kaf duniya, tawa Majeederh ta zama gawa tun da jimawa bana son wata tambaya bayan wannan" a firgice Majeederh ta dafe ƙirjinta da yake wani bugawa jajirin ya nemi suɓucewa ta shiga kokawa da numfashinta, wani abu mai nauyi ya tsaya mata a ƙirji Idanunta suka tsaya ƙam akan fuskar mahaifinta tunani take ko dai da gaske bashi ya haifeta ba? Mai shagon ya girgiza kai ya ce.

"Kai duniya, kai duniya wai yanzu aikata zina ya zama ruwan dare? Matan aure su aikata zina, ƴan mata su aikata zina, zawarawa su aikata zina, mijin aure ya nemi matar wani, matar aure ta nemi mijin wani? ga Fyaɗe daya ya waita, ga matsalar tsadar abin duniya, ga rashin nefa ga rashin ruwan sha, albashi wannan sai a shige wata ba a biya, wani lokacin ma a rage albashin, ga yawan aibata Musulunci yanzu Fisabilillahi a kaf garin nan waye bai san Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci ba ce? waye bai san irin tallafin da take bawa Muslunci ba, waye bai san wa'azin da ta kewa masu aikata alfasha ba, sai gashi ana zaton wuta maƙera sai gata a masaƙa, shi ya sa ake cewa kayi amfani da faɗar Malam kada kayi amfani da abin da yake aikatawa, wallahi ko ki aka bani dama sai na jefe wannan shaiɗaniyyar" Lawan ya girgiza kai ya ce "A'a Bala,  amma dai Allah ya kyauta!" Bala ya ce "Amin, shi ya sa taƙi aure tana ta zuba alfasha, kasan daman duk wani mai aikata zina aure bai dame shi ba, kuma ko ya yi aure ba zai daina yin abinda ya saba ba"

Malama Majeederh bata tsaya neman ruwan ba, ta juya da sauri tare da barin wajan a lokacin ji take kamar ta shiga duniya, kamar ta zama ƙaruwar da suke danganta ta da ita, ji take kamar ta zama sanadin lalata sunan mahaifinta dana familyn da yake nesa ta da shi gudun kada ya ɓaci, zuciyarta ta ƙe ƙashe duk damuwarta ta tsaya, lokaci zuwa lokaci take jan numfashi ta sauke sbd abinda ya tsaya mata a saitin zuciya da maƙo shinta. Tayi tafiya mai nisa sosai kafin ta samu wani waje kusa da wata bola ta zauna ta rungume yaron wanda ya yi shiru, jikinsa ya ɗauki zafi. Ji take kamar ta rataye kanta, ga jinin haihuwa daya gaba ɓata mata jiki a haka barci ya ɗauketa.

Tsaye suke gabaɗaya a parlour Hajia ta girgiza kai ta ce "Me kayi haka Zaki? Me ka aikatawa kan ka haka Aliyu?"

Almustapha ya kalli news paper ɗin ya ƙara ware idanunsa akan photon Bar Aliyu Sufyan Alhassan da kuma photon Malama Majeederh Abdul'aziz Khan dake zaune fuskarta rufe da liƙab. Almustapha ya shiga karanta headline ɗin jaridar. "Bar Aliyu Sufyan Alhassan shi ne ya aikata zina da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, tare da saninta domin su wulaƙanta matar Aliyu wato Latifa Omar kasancewarta aminiyar Jeederh" ya karanta a fili cikin zafin nama da faɗa Almustapha ya ce "Wanne shirme da hauka ne haka Aliyu? Zina? Ɗan shege?" Aliyu ya kalli yayan nasa ya ce..

"Ba shege bane" "To uban mene? Aurenta kayi?" Aliyu ya ce "Ko ɗaya, ina son ta am ready to marry her, ɗa kuma ba shege ba ne" Almustapha ya ɗauke Aliyu da mari ya ce

"Mahaukaci, to kayi gaggawar zuwa gidan jaridar nan ka ƙaryata rubutun su, ina da tabbacin kuma matarka Latifa Omar ce tayi wannan aikin ai a gidan jaridar take aiki"

"Tayi dubun su, ba zai sauya mini ra'ayi ba"

Cewar Aliyu. Almustapha ya ƙara ɗaga hannu zai mari Aliyu,cikin sauri Aliyu ya riƙe hannu ya ce

"Kasan Allah ka ƙara marina zan karya hannunka,ka bar ganin kai yaya na ne, idan kun shirya korata kamar yadda Mahaifin Majeederh ya koreta fine I'll leave the house" abu kamar wasa dambe ya sarƙe tsakanin wa da ƙani cikin ɓacin rai Hajia ta zabgawa Aliyu mari ta ƙara zabga masa mari ta ce "Ka nutsu Zaki, ka nutsu" Aliyu ya fashe da kuka ya rungume Mahaifiyarshi ya ce

"What should I do Hajia? Dame zan ji ne? Wallahi idan kuka matsa mini zan iya aikata komai, Hajia I love Majeederh don Allah ki nemo mini ita, hajia hajia....,"

Da Hajia da Almustapha su kayi kan Bar Aliyu Sufyan Alhassan wanda ya faɗi a ƙasa sumamme...


Government House

Labarai ake ta ko'ina gabaɗaya kuma akan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ne, Human rights sun shiga maganar, ƙungiyar mata ta shiga maganar, shugaban ƴan hisba. Ya sauke ɓoyayyiyan numfashin tare da juyawa kaɗan ya kalli tulin jaridun da aka wallafa, gefe guda kuma yana mamakin gidan Jaridar Hausa lastest News, domin sun fi ko wanne gidan jarida ɗaukan zafi da kuma aibata Malama Majeederh. Sama sama yake kallon photon ta, bai taɓa ganinta ba amma muryarta kullum tana yi masa amsa kuwwa a kunne. "Ham...mad" Hammad ya yi sauri ya rusuna ya ce

"Your excellency" "Waye me wannan Shirman?" Hammad ya ƙara yin ƙasa ya ce "Wata ƴar Jarida ce, Latifa Omar"

Abu-turab ya ce.

"A dakatar da gidan jaridar" with so much respect Hammad ya ce

"With pleasure Your excellency" ya jinjina kai kawai, Hammad ya juya cikin sauri. Kai tsaye akai sanarwar da yawun Gwamna tare da bada umarnin rufe gidan Jaridar. Abu-turab ya kasa komawa gida, tun safiyar yake jiran ya ji ance an samu Malama Majeederh Abdul'aziz Khan amma shiru har biyar na yamma ya yi. Tajju ne ke driving hannunsa riƙe da Envelope yana ta yawo amma bai samu Majeederh ba, gashi har an kwana wani daren na shirin yi kamar ance masa ya juya idanunsa ya sauka akanta tana nan zaune bakin bolar ta ƙanƙame jaririn kamar za a kwace mata shi, ta fita hayyacinta duk jini ya ɓata jikinta, cikin sauri Tajju ya gangara gefen titi tare da yin parking yana Hammadala a ransa ya fito,bai san mene a envelope ɗin ba amma yasan dole yana da alaƙa da wannan jaririn babu ko tabbata musamman yanzu daya tuna wata rana. Yazo daidai tsakiyar titin yana ƙoƙarin tsallakawa wata ƙatuwar tifa tayi awon gaba da shi....


#Bar Aliyu Sufyan Alhassan

#Dr Jamal

#Abu-turab


Na'ima Sulaiman Shu'aibu

08119237616

Not editing

*🌈 MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta


*_Please kuyi following Acct ɗina a arewabooks🫰🏿_*

https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


   *AN SAMU MISTAKE, WANNAN SHI NE FULL PAGE NA 4 KUYI SHARING, A GOGE WANCAN🙏🏿*


*4......*

Mummunan hatsarin ya ja hankalin mutane da yawa, hatsari ne wanda za a iya cewa tsautsayi ne da kuma gangan cin driver da yake driving yana waya. Da gudu babbar mota tayi gaba bayan tayi wurgi da Tajju zuwa gefe guda, nan take kan Tajju ya fashe jini ya fara zuba hannunsa guda ɗaya ya fita fit daga jikinsa ko shurawa bai ba rai ya yi halinsa. Motar dake bin bayan babbar motar data buge Tajju ce ta tsaya, cikin sauri driver da wanda yake gefen mai zaman banza suka fito bakinsu ɗauke da sallati "General kira mana Ambulance" cikin sauri General ya ɗakko wayarsa tare searching asibiti mafi kusa da kuma motar asibitin. Hammad ya ce "Allah sarki, haka rayuwa take Allah ya jiƙansa ya yi masa rahama" General ya amsa da "Amin" da sauran jama'ar wajan suka amsa.

Har Hammad zai juya idanunsa ya sauka akan Envelope dake can gefe guda iska na kaɗata a hankali ya ƙarasa tare da ɗauka, a ransa yana tunanin maybe a samu wani bayanai akan mamacin. Ya ware Envelope ɗin first abin da ya gani shi ne ring irin na al'ƙawarin nan, ya juya ring ɗin sosai sai kuma ya zura acikin aljihu, gently idanunsa ya sauka akan headline na wasiƙar kamar haka.

     *_BAD MAN, THE STUBBORN BOY, CRIMINAL, GANG BOY, THE LEADER_*


Daga wannan rubutun idanun Hammad ya sauka ƙasan headline ɗin inda aka rubuta “The memories, was going on my mind, har abad, nasan ni mahaukaci ne da gaske kamar yadda ki ke faɗa Jee” jikin Hammad ya shiga rawa ganin General na ƙara suwa ya tura wasiƙar Aljihu "Lafiya?"

"Actually, good"

Kafin suyi magana Ambulance ta ƙara su aka ɗauki gawar Tajju tare da sanyata ciki, Hammad ya buɗe ya ɗauki wata number da yaga ana ta kira anyi saving da "Bad boy"

"His phone" cewar Hammad bayan kammala komai Ambulance suka tafi asibiti da shi. Suma su Hammad mota suka shiga driving kawai yake amma tuni ya yi losing mind ɗinsa, fatan sa kawai ya isa Gov. Abu-turab Alƙasim, ya san cewa yanzu ya koma gida kasa jurewa ya yi ya ɗauki Wayarsa tare da kiran keɓantacciyar number Abu-turab kusan kira uku kafin ya ɗauka cikin nutsuwa ya ce.

"Uhm" Hammad ya ce

"Your Excellency, akwai damuwa" a taƙaice ya ce

"Kace komai, banda rasa Majee" cikin ladabi ya ce "Am very sorry for that, amma bamu sameta ba, amma mun sami maganin matsalarta, ɗan waye, cikin waye, yadda aka samu cikin duk yana ciki" Abu-turab ya miƙe daga zaunan da yake ya shiga zagaye haɗaɗɗan parlourn nashi fuskarsa tayi jajir. "Ok, meet me at my house" yana faɗin haka ya kashe kiran. Tafiya kaɗan ce ta ƙara su da su cikin gidan Abu-turab wanda yake zaune tare da iyayensa, sojoji birjik ta ko'ina daka nuna rashin gaskiya zaka ji maza akan ka. Girman gidan ya zarce tunani, motoci kala-kala na kamfani daban-daban.

Ko a jerin masu kuɗi ba kowa zaka samu da wannan haɗaɗɗan gidan ba, gida ne 200by 200 iya compound na gidan zai ja hankalinka balle ciki. Kasancewar ba wanda bai san Hammad ya sa ba wani wahala ya nufi cikin gidan, a Main parlour ya samu Mama na sakkowa daga bene ya yi murmushi ya ce

"Sannu da gida Mama" kallonsa kawai take fuskarta kwance da annuri amma kana ganin sanyin jikinta kasan akwai damuwa, kyakkyawar dattijowa mai nutsuwa da sanin ya kamata,ga ilimi na iya zama da ko wanne mutum ga kyakkyawar mu'amala. "Na ɗauka mun yi laifi yau ne" cewar Mama bayan ta zauna.

"Laifi kuma Mama?" Ta dubesa kafin ta ɗauke kai ta ce "Naga babu ko mai kama da kai, hala wani aikin ka ke" ya shafa kai yana rusunawa ya ce.

"Haka ne kam, ina Yake?"

Ta ɗaga kai zuwa part ɗin dama da yake upstairs ta ce. "Ina son tambayarka dama, meke damun shi? Tunda ya shiga part ɗin sa bayan ya dawo bai fito ba, hatta wajan art ɗin da yake shiga yau shiru, lunch ma bai ci ba na kira phohe number sa na gida a kashe" ta tsare shi da idanu ya ce "Akwai wata tattaunawar sirri da yake da ita, maybe shi ne yake duba muhimman abu kasancewar tattaunawar sai 12 na dare"

Ta jinjina kai tare da faɗin "Allah ya taimaka, kasan ƴar rigimarsa ta hanani sakat ita dai Abbi" Hammad ya yi dariya sosai ya ce "Jiddatul-khairi ai ya saba mata ne" kafin Mama tayi magana sai gata ta fito da gudu ta faɗa jikin Hammad ta ce "Uncle, Abbina" ya ɗauketa ya shiga hawa upstairs yana faɗin

"Daughter me, bari muje muga Abbi sai muje siyan chocolate ko?" Tayi murmushi dimples ɗinta soka loma tana ta masa surutu har suka isa haɗaɗɗan part ɗin da kana ganinsa kasan Gov. Abu-turab Alƙasim ne a ciki. Hannu Hammad ya saka cikin wani screen dake ƙofar nan take ta fito da bayanan Hammad a hankali kuma ƙofar ta buɗe.

Jidda ta ƙwace daga hannun Hammad tayi cikin parlourn da gudu tana kiran sunan Abbi, yana zaune saman kujera daman alrdy ya san da zuwan Hammad ɗin, kayan shan iska ne a jikinsa fara Armless da black ɗin 3 gauter.

Hannunsa ɗaya riƙe da Black tea wanda aka sanya masa zuma a ciki, news yake kallo har Jidda ta faɗa jikinsa hankalinsa baya tare da shi. "Abbina"

Ya ware idanunsa idanunsa da suke a ɗan lumshe ya dubeta "First love" sunan da yake faɗa mata kenan, duk da kasancewarta ƴar shi guda ɗaya. "Abbi"

Ya juya bayan ya gyara mata zama a cinyarsa tare da kallon Hammad yana son ya ji wanne labari ne da shi wanda yake da alaƙa da Majeederh.

"Your Excellency barka da yammaci" jinjina kai kawai Abu-turab ya yi.

"Ga wannan wasiƙar, idan ka karanta sai ka ɗauki matakin daya kamata akai, ita kuma zamu nemota In sha Allah" hannu ya sa ya amshi wasiƙar tare da warewa zuciyarsa na harbawa, bai san mene ya sanya duk abinda ya shafi Malama Majeederh ya ke jinsa har ƙasan zuciyarsa ba, barci ya ƙauracewa idanunsa, ga ciwon kan dake ƙoƙarin kwantar da shi.

Duk Yadda ya so ya daure da riƙe kansa ya kasa ya miƙe tsaye da sauri yana ware idanunsa akan paper ɗin, tsoro,fargaba damuwa da kuma firgicin rashin sanin makomarsa wajan Majeederh ya taro ya haɗe masa waje guda.

Ya sanya hannu ya share zufar daya yanko masa, lokaci ɗaya ya hargitse wani zazzaɓi na neman kawo masa farmaki.

"Your Excellency, lafiya dai?" Ba tare daya kalli Hammad ba ya ce

"Ham...mad" "Yes, Your Excellency"

Ya juya gabaɗaya fuska a haɗe ya ce "Tun yaushe nake baka labarinta?"

Kai tsaye ya ce "Shekaru wajan biyar, tun ranar daka halarci musabaƙar da aka yi ta ƙasa"

Abu-turab ya jinjina kai, Elxty 5yrs kenan, a wannan musaɓar ya ji muryar Majeederh, muryar data sanya masa dafin so a zuciya ta zautar da duk wani tunaninsa, ya wanzu cikin muradinta a zuciyarsa, shi kansa ba zai iya sanin abinda ya sanya bai tun kare ta da wannan maganar ba, samun Majeederh Abdul'aziz Khan a garin nan ba wahala zai masa ba. "Har abada Majeederh kada ta san da wannan wasiƙar" da mamaki fal fuskar Hammad ya ce "Your Excellency amma kamar ba a kyauta mata ba, wannan wasiƙar ita zata fitar da ita daga zargi, kuma ita ce zata gane waye ya aikata mata haka" Abu-turab ya koma ya zauna kawo yanzu yasan Bp nasa tuni ya hau cikin kamilalliyyar muryarsa mai tsafta ya ce "Me ka ke nufi?"

"Ba mu yi mata adalci ba" cewar Hammad.

"So baya buƙatar adalci, kansa kawai ya sani, ayi hakkan ya tsaya ni da kai" Hammad ya kalli Abu-turab yana girmama yadda yaso kansa a fili sbd soyayya,idan har son gaskiya ne ba zai taɓa bari Majeederh taci gaba da zama da zargi akanta ba. "Shikenan, Your Excellency. Maganar meeting naka an gama shirya tattaunawar a guest house ɗinka, da kai da Deputy Governor, Secretary to the state of Government, Chief of staff" hannu bibbiyu Abu-turab ya riƙe kansa kana ya jinjinawa Hammad kai ganin yanayinsa ya sa Hammad cewa "yana da kyau ka huta haka, Jidda zo muje" ta maƙale ka faɗa jikin Abu-turab.

"Abbi baya jin daɗi" Abu-turab ya ware idanuna ya ce "Go"

Ta kwaɓe fuska cikin zafin zuciya ya ce "I said Go Hawwa'u Abu-turab Alƙasim!" Tsawar ta gigita mata lissafi ta fashe da kuka tana ƙanƙame Hammad ta ce

"Uncle" ya ɗauketa yana girgiza yana mamakin sauyawar Abu-turab lokaci ɗaya.

Dukkan abinda ya faru akan idanun Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ya wakana, kasancewar bata fahimta kusan tunaninta duk ya jirkice ƙwaƙwalwarta na gab da fara daina aiki yasa bata fahimci su waye ba, motsi kaɗan zata ƙanƙame jaririnta kamar zata bayar da shi ciki, wani zubin kuma tayi ta surutu ita ɗaya sbd tarin abubuwan da suka cunkushe mata, yunwa ba a maganarta jikinta ya fara tashi sbd jini da rashin wanka.. bata shagala azkar, istigifari da addu'ar neman samun sauƙi wajan Ubangiji bai bar bakinta ba.

Washe gari Abbu ne zaune a parlour da Mami sai Ruma da Raihana wanda aka kira su daga gidan mazajen su, sai kuma Aaliyyah dake zaune tamkar marainiyya Idanunta a kumbure ko gani ba tayi sosai, sai Uncle Isma'il da Uncle Bello. "Yanzu har a ranka kana jin kayi daidai?" Abbu ya dubi yayan nasa ya ce "Majeederh dai ni na haifeta, ni na samar da cikinta na kuma raineta, kuma na dawo na ce bani da haɗi da ita don haka a bar wannan maganar" Uncle Isma'il ya ce "An barta, amma ka bani mamaki a matsayinka na Uba kuma dattijon ƙwarai har ka iya shafawa idanunka toka ka ce wai ka sallamawa duniya Majeederh, sbd kawai kada sunan family da naka ya ɓaci? Familyn bazan sunanka ɗin banza, da rayuwar mace kamar Majeederh ta ɓaci ba gwara duka sunayenmu su ɓaci ba, wata rana dalilinta sunan namu ya samu ɗaukakar damu kanmu ba muyi zato ba, mai ya sanya mu iyaye idanunmu ya kan rufe idan tsautsayi ya samu yaranmu? Yanzu Majeederh ko tana sane wannan abun ya faru ba zaka iya yi mata uzurin akan rashin auren da take da shi ya ja mata wannan ƙadsarar ba? Ita ɗiya macace duk runtsi duk jimawa dole ta ɓukaci ɗa namiji wata rana" Uncle Isma'il ya girgiza kai sbd tsabar takaici ya ce "taya ƙasa zata gyaru bayan mu da kanmu bamu gyara zamantakewar data yaranmu ba, fine ka kori Majeederh zan nemota na riƙeta a wajena....,"

"Yin hakan zai ja mana babban kuskure yaya, duk wanda zai so ta bayana yake bi, don haka a barni kawai" Abbu ya tari numfashi Uncle Isma'il da faɗin hakan. Uncle Isma'il da ransa ya fara ɓaci ya ce "Zan taimaketa kamar yadda take taimakon addinin Musulunci, bawai sbd data kasance ƴarka ba Abdul'aziz Khan" Abbu rai ɓace shi ma ya ce "Kana iya yin haka amma daga ranar babu ni ba kai, ka cire ni matsayin ƙaninka, ka yanke mu'amala ta dakai" murmushi sosai Uncle Isma'il ya yi wanda ya fi kuka ciwo yana girgiza kai ya ce "In sha Allah, idan kero na yawo zabo na yawo tabbas za a gamo Majeederh zata baka mamaki" Aaliyyah dake kuka sosai ta ce "Abbu don Allah ka bawa Yaa Nura dama ya kawo kuɗin aurena, na ga ji da zaman gidan nan na tsani komai dake cikinsa" kai tsaye Mami ta ce "Fitowa za kiyi ki ce kin tsanemu, aure kuma dole sai kin kammala makaranta daman ke ɗaya ki ka rage cikin gidan.." sai a lokacin Uncle Bello ya ce "Aaliyyah aure ki ke so?" Duk kawaicin Aaliyyah ta shanye ta ce "Eh, Uncle"

"Ki faɗawa Nura ya zo ya saman a gida nan da sati mai zuwa In sha Allah zaki bar wannan gidan" yana faɗin haka ya miƙe tsaye ya kalli Uncle Isma'il ya kalli Abbu ya ce "Yaya taso muje, Allah ya bada ladan zumunci Sunan family kuma a rubuta a gaban ƙoshi ana yawo da shi"

Suka fice tare da barin gidan,Abbu ya nufi part ɗin sa zuciya babu daɗi shi kam Majeederh ta zame masa annoba, Aaliyyah ta shige nata bedroom ɗin tana zuwa ta ɗauki wayarta ta kunna network ta shiga facebook inda labarin Majeederh da Bar Aliyu Sufyan Alhassan yake ta trending a media. Ko photon Majeederh ta gani da gudu take skipping ta shige sbd tsaron zagi da mugun alkaba'in da ake mata, tana cikin dubawa taci karo da wani posting photon Majeederh ne sanye da abaya fara mai kyau fuskarta rufe hannunta riƙe da loudspeaker. An yi rubutu a saman photon tare da saka.


*She's Innocent*

_Malama Majeederh Abdul'aziz Khan babbar malamar musulunci da muke da ita a wannan jiha, wacce ta samu damar zama zaƙaƙura wajan lashe musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ita kuma ta ƙara jawo kima da martabar jiharmu, wacce take taimakon marayu, marasa gata take nutsuwar da matan aure akan darajar da aure yake da shi, duk da kasancewarta budurwa. Abin tambayar shin ta cancanci haka kowa? Kai da ka ke zaginta ko ki ke zaginta kina da tabbaci akan abinda ya faru, ko kina da hujja? Ko labarin ƙazan kurege aka baki har kike ɗorawa tare da aibatar ƴar jama'a, ta haifi wasun ku da yawa, ta fiki ilimi tunani da sanin ya kamata, ta fika kusanci da mahalicci amma kazo media ko sallar kirki a rana baka yi ka ɓuge da zagin babbar Malama? Ashe muna rayuwa da dabbobi bamu sani ba? Ko masu aikata zina sai an same su turbi da taɓarya tare da shaidu 4 sannan za a ɗauki mataki. MALAMA MAJEEDERH ABDUL'AZIZ KHAN SHE'S INNOCENT I STAND BY HER SIDE._


#Mrs No name


Wani murmushin jin daɗi Aaliyyah tayi 5 minutes da yin posting ɗin amma comments wajan 1k hakan ya tabbatar mata da Mrs no name yana da followers kuma babban mutum ne tunda har ya iya ɓoye sunan shi, kai tsaye profile ta shiga ya rufe komai da komai ko message ba za a iya yi masa ba, dole sai dai tayi magana ta comment section.

Har aka kwana aka tashi Bar Aliyu Sufyan Alhassan bai farka daga suman da ya yi ba, hankalin Hajia ya tashi tana da Papi tare da Almustapha, hatta korar da aka yi masa wajan aiki bai sani ba.

Misalin 8 na dare wahala tayi wahala jikin jaririn ya yi zafi kamar wuta, a yanzu ji take ko jama'ar gari za su kasheta babu abin da zai hanata fita ta nemi ruwan da zata bawa babyn nata, ta miƙe da ƙyar kusan gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci tana bin gefen hanya harta isa wani wajan da ake siyar da tsire kanta ƙasa tayi sallama, gabaɗaya mutanen da wajan suka dubeta wani ya ce "Baiwar Allah lafiya?" Ta jima kafin ta ce "Ruwa nake nema, zan bawa yarona" wani saurayi ya dinga kallonta kafin ya miƙe tsaye ya ce "Mene na rufe fuskar?" Ta ɗauke kai cikin sa a ya gano rabin fuskarta da jaririn hannun da ƙarfi ya ce "Masiƙa la'ananniyya mazinaciyya ku je feta ita ce Malama Majeederh" yana faɗin hakan ya sauke mata wani dutse a ƙoshinta ji ka ke tauu!! Nan take ya fashe jini ya dinga zuba, kafin ka ce me mutane sun cika kowa ya ɗakko duwatsu suka fara jifanta ta ko'ina ta durƙoshe ta rungume jaririn da jikinta, jama'a sunfi ashirin idan wannan ya jefa mata dutse aka sai Wannan ya jefa mata a baya...


Na'ima Sulaiman Shu'aibu

Nimcy sarauta

08119237616

*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

_*Follow my account👇🏾*_

https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


African Queen products

Sabulun matsi

Garin matsi

Humra

Turaren wuta

Maganin Infection

Ga number wayata...08130269641


*5.......*

Ta ko'ina suke jifa mata duwatsun jikin ƙaramin lokacin suka farfasa mata jiki. Wani saurayi wanda kana ganinsa kasan criminal ne yana da dakakkiyar zuciya ya ɗauki wani dutse tare da faɗin. "Fasiƙa, mazinaciyya, duk yadda akai kema ba ƴar halak ba ce, shi yasa tsayin shekaru talatin da biyar ki ka sa yin aure kina bin mazan aure da samari" yana faɗin haka ya sakar mata dutse a goshinta nan take ya fashe jini ya wanke mata fuska,ta fara gani dishi. Sunayen Allah take kira da neman ɗaukinsa, tsoro ya kamata jin babyn nata ya daina motsi da kukan da yake fatan ɗaya Allah ya sanya jifan bai same shi ba, balle ya yi sanadin mutuwarsa.

"To, wai me muke jira ne? daga ita jar jaririn mu sanya musu fetur a ƙona mazinaciyya mai ci da musulunci, a kuma ƙone mugun iri!"

Wani wanda yake da ɗan hankali ya ce "Amma kana ganin ba muyi kuskure ba? Ai ba jifeta ya dace ayi ba, tunda ba matar aure ba ce, budurwa ce bulala ne ya dace da ita" cewarsa.

Saurayin ya ce "A to mene martabarta da matar aure? Ai auren ne ba tayi niyya ba shi ya sa take ta gantali ta shiga rigar addinin musulunci ta ci zarafin Musulunci da musulmai, ita fa yankata ya dace ayi"

Kafin kowa ya sake magana hasken wata dalleliyyar mota ya haske wajan duk da irin fitilar da suke kan hanya.

Gabaɗaya suka kalla motar mai ƙirar  Mercedes-AMG G63 Ash colour, slowly yake driving  har ya ƙara su wajan, ta cikin motar yake ƙare mata kallo ganinta durƙoshe har yanzu ko motsi ba tayi, ya ja idanunsa ya lumshe wani abu ya daki zuciyarsa zafi da raɗaɗi  yake ji sosai abinda yake ji tsayin shekaru ya ƙara yawa a ƙirjinsa. Ya fesar da numfashi tare da sanya hannu ya ɗan danne gefen zuciyarsa, gently ya gyara Bluetooth na kunnenshi speaking calmly ya ce.

"Meet me at my house right now" Yana faɗa ya ɗauki face mars ya sanya tare da ɗaukan Glasses ya saka a idanunsa, cikin tarin nutsuwarsa da kamewarshi wacce ta riga ta zauna a jikinsa musamman yanzu da izzar mulki ke ɗawainiyya da shi. Ya fito daga motar fuskarsa haɗe duk da babu wanda ya san waye, bai kula kowa ba ya nufeta tare da sanya hannu zai kama nata a firgice ta ɗago idanunta tare da girgiza kai cikin wata murya mai rauni da tausayi ta ce

"Kuyi mini komai, ban taɓa jikina" "ji banza shashasha, uwar mene ya yi saura a jikin banda najasa...,"

Marin da aka sauke masa ne ya sanya ya yi shiru da bakinsa domin har tsakiyar kansa ya ji marin shatin yatsun His Excellency ya fito raɗau a fuskar.

Ya ƙara kai hannu zai riƙe nata hannun domin taimaka mata tayi saurin ɗauke hannu kamar bai son magana murya can ƙasa ya ce "Please Hawwa'u, akwai jama'a"

Ta girgiza kai numfashinta na fita da ƙyar ya ƙara rusunawa shi kansa kamar wanda ya yi jinya ya ce "Haba Jiddo" ganin da gaske take ya sanya ya tattara ƙarfinsa waje guda tare da sunkutar ta gabaɗaya har jaririn sai cikin mota, ya kwantar da ita a baya ya sanya hannu ya zare jaririn tare da ɗaukarsa ya nufi ɓangaren diver. Yana shiga ya yi wa motar key da hannu ɗaya ya fara driving cikin sauri ɗaya hannun kuma ya rungume jaririn, keɓantaccen gidansa ya nufa da ita direct.

Wani tsohuwo ya ce

"To ba ga irinta ba, ɗaya daga cikin kwarton abokin alfashar nata ya zo ya ɗauketa, ai ni duk wani ɗan shege na daina tausyainsa tunda ana sane ake haifarsa"

Haka suka dinga surutu, suna faɗin duk wata mace mai irin shekarun Majeederh wacce ba tayi aure ba to kawai iskanci take tana aikata zina.

Lokacin da His Excellency Abu-turab ya isa gidansa P.a ɗinsa na tsaye yana jiran zuwansa, Hammad ya nufi Abu-turab wanda yake ɗauke da jaririn yana zuwa ya miƙawa Hammad jaririn shi kuma ya koma wajan motar, lokacin Majeederh ta gama sumewa jikinta ya ɗauki zafi sosai a ransa yake istigifari kafin ya tattara ya ɗauketa cak, sanin halin Abu-turab yasa tuni Hammad ya shige ciki da jaririn wani ɓangare ya nufa da ita ya kwantar kan bed, bai tsaya jan aji ba ya samu ruwan zafi da showel ya danna duk inda aka fasa mata tare da yi mata allurar kashe zafi data barci, ya yi mata dressing yana yi yana ɗauke kansa, raunin jikinta bai hana shi ganin asalin kyanta ba, asalin kyawun Fulanin Usul. Zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito ya razana da kyanta sosai shi ya sa ko Hammad bai bawa damar shigowa ba sai da ya gama komai ya sanya mata driving tana ta barcin wahala.

After ya gama ya duba babyn. A hankali ya fito yana dafe kansa sbd ciwon da yake masa yana zuwa ya faɗa saman kujera idanunsa rufe. "Amma yana da kyau ka huta Your Excellency" ya ware Idanu tare da tsiyaya black tea a cup sai da ya shanye ya ce

"P.a, kana tsaya iya aikin ka" "Am sorry sir, bayan p.a you're my best friend hakƙina ne na faɗa gaskiya kuma na kula da kai, idan kana son hakƙin Majeederh tana bawan Allan nan kada ya kama mu yana da kyau a bata wasiƙar ta karanta" ɓacin rai wanda Hammad bai taɓa gani ba ya bayyana kan fuskar Abu-turab, idanunsa da suke a ri ne ya ware akan P.a cikin kakkausar murya ya ce

"Kasan me hakan ke nufi?" Ya shiga kaɗa ƙafa a duk sanda ransa ya ɓaci kafin can ya ce

"She never choice me, ba zata taɓa zaɓata a matsayin miji ba, she most go back to him ba zata gane shekarun da nayu ina jiranta ba" ya miƙe yana kai kawo

"Sunanta na sanya jinina, sunanta na sakawa ƴata Jiddo, ko sunan mahaifiyata ban sanya ba sai nata, shi kaɗai ya isa yasa ka gane, zan iya adalci a mulkina al'ummata, amma ba zan iya adalci akan soyayyar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ba, duk hanyar da zan bi na raba ta da kowa zan yi"

Hammad zai magana Abu-turab ya daka masa tsawa ya ce

"Get out" dole ya fita amma shi a ransa ya san babban kuskure ne su riƙe wasiƙar nan.

"Ya Allah!" Abu-turab ya furta yana ɗaukan gorar ruwa mai sanyi, sai da ya shanye tas kafin ya yi cilli da Robber.

Babyn daman yana wajan wata maid yana ta barci ya ji ruwan zafi da kaya masu kyau ga madara da aka bashi sai numfashi yake saukewa.

Yadda Majeederh ta kwana kan gado haka ya kwana a parlour, lokaci zuwa lokaci yana zuwa a cikin daren sai da ya sanya mata drip uku kansa cewar ruwan na tafiya da sauri. Kiran sallar Subhi ya sa ya nufi bedroom ɗinsa farar singlet ɗin jikinsa ya cire ya sakarwa kansa shower ruwa na saukar masa, alwala ya yi ya shirya cikin ash ɗin jallabiya masallacin dake gefen gidansa ya shiga lokacin ana kuraye kirayen Assalatu....

Assalatun ya yi daidai da farkawar Bar Aliyu Sufyan Alhassan a gadon asibiti ya motsa a hankali yana dafe kansa dake masa ciwo kamar ya rabe gida biyu, dishi dishi ya fara gani kafin ganinsa ya daidaita idanunsa ya sauka akan Hajia ta ce "Zakina, sannu ka ji" ya yi ta kallonta kafin ya juya ya kalli Papa shi ma ya ce "Sannu Haydar, ya jikin?"

"Ba sauƙi Papa" Papa ya ce "Meke maka ciwo?"

Ya mutsa fuska ya yi yana rufe Idanu "Meke damunka? Almustapha kira Dr"

"Babu abinda zai iya"

Almustapha ya ja tsaki ya ce "To ai kun ji, shi fa sam baya tausyain kansa ina can gidana tare da matata ku kirani wai jikinsa ya tashi kamar shi kaɗai kuka haifa? Mene abin so a wajan wata Majeederh tsohuwar ko me?" Aliyu kamar zai kuka ya kalli Hajia ya ce

"Kin ganshi ko?" Hajiya ta ce "Ka fita idanuna Almustapha, kabar mini yaro ya ji da abinda ke damunsa" "I love her"

Cewar Aliyu. "Kayi haƙuri zaka sameta idan rabonka ce" Almustapha kamar ya shaƙe Aliyu haka yake ji ya ƙara yin tsaki ya ce

"Gashi nan an sallame ka daga court ɗin da ka ke aiki, sai ka zauna zaman kashe wando kana jiran wata" Zaki ya kwaɓe fuska ya ce "In sha Allah sai Allah ya ɗora maka son wacce bata son ka" Dariya sosai Almustapha ya yi kafin ya ce

"Ai matata ƴar Aljanna ce ta wada tani da komai na kwanciyar hankali to me zai sanya na fara tunanin  yi mata kishiya?"

Sai a lokacin Papa ya shiga dramar ya ce

"Shi ma tashi matar ai ƴar Aljanna ce"  "Barshi Papa idan ya cika ya zo ya dauki Latifa ya sata a wuta, matar taka duk raguwar mai"

Yana faɗin haka ya juya zuwa ga Hajiya tare da ɗora kansa a cinyarta ya ce "Hajia zuciyata babu daɗi ki taimaka mini" ta shiga lallashinsa ta ce "Yanzu yana da kyau ka shaidawa duniya baka da haɗi da ɗan gidan Majeederh, after that sai ka fara shirin nemanta ko?" Ya kalli mahaifiyar tasa sosai sai bai ce komai ba. Misalin 12 na rana lokacin an sallami Aliyu zuwa gida yana zaune ya faɗa sosai kamar wanda ya yi jinyar shekara kamar daga sama ta faɗo bai kalleta ba, ƙamshin turarenta kawai ya ji ya fahimta "Ya jikin?" A gajarce ya ce "lfy" ta zauna ta ce

"Amma ka fasa aurenta?" Ya dubeta ya ce "Ita wa?" Kai tsaye ta ce "Waccar Mazinaciyyar mana" ya yi murmushin kawai bai ce komai ba ta ce "Magana nake kayi shiru" ya juya gabaɗaya tare da saka hannu ya riƙe fuskarta ya ce "Kina son rabauta ko Wife? Me ya sa ki kewa mijinki haka?" Ta ce "Idan har zaka ƙara aure zaka iya ganin fiye da haka" ya sake ta yana kwanciya jikin kujera ya ce

"Sai dai idan bana raye, Latifa Omar ke baki tausayina ne? Sai fa Majeederh zata zo gidanki ki ke gyarawa, tsafta zero, kwalliyya zero, girki zero, mu'amalar aure zero, aikin ki kawai ki sani, yanzu mene ribarki don ki aibata mijinki? yaran da zaki haifa sune abin zai zamewa tabo not me or Majeederh" ta miƙe tsaye ta ce "Divorce me"

"Never, ki jira zama tare da sweetheart" baƙin ciki ya cika mata zuciya ya zari key car tabar gidan ya bita da kallo.

Tunda ta farka daga nauyayyen barcin ko tari ba tayi ba, tsoran ta buɗe idanu taga su waye akanta take, bata so ta samu ɗauki ba ta so ace mutuwa ce ta risketa.

Mama dake zaune ta zabga tagumi ta ce "Baiwar Allah kenan, Allah ya saka miki" ta goge hawayen Idanunta Hammad ya ce

"Kamar ta farka ai" Mama ta ce "Ato gwara ta tashi ai, ga ɗan yana ta kuka gwanin tausayi" a hankali ta buɗe Idanunta ba tare data kalli kowa ba sai gefe guda, yadda take ji zaka ɗauka kuka za tai ta rusawa amma idanunta a ƙafe komai na tunaninta ya sabunta hanyar da zata bi ta zama cikakkiyar karuwa kawai take nema.

"Sannu Malama, Sannu kin ji" sai a lokacin ta juya ta kalli Mama tana jinjina kai. Gently ta mayar da Idanunta ta rufe daidai shigowarsa yana gyara zama babbar rigar jikinsa, nutsuwa da haiba tattare da shi.

"Barka da zuwa Your Excellency" Abu-turab ya jinjina kai tare da neman kujera ya zauna idanunsa kwance a kanta,daga nan Mama miƙewa tayi. Jin shirun ya yi yawa yasa ta juya cikin sa a suka haɗa idanu tayi saurin ɗaukewa. A ransa ya ce "Ma sha Allah, Tubarkallah" a fili kuma ya furta "Jiddo ya jiki?"

Ta haɗe rai sosai "akwai ciwo?" Nan ma shiru tayi gani take yanzu kowa ya tsaneta. Sosai ya gane bata san waye a gabanta ba domin ƙwayar idanunsa kawai ta kalla. Yana ƙoƙarin magana ya ji ƙarar bindiga na tashi ta karaɗe gabaɗaya gidan, ya buɗe idanu da mamaki yasan akwai securities amma harbin na mene? Hammad ya fice da sauri tsoro ya kama Majeederh ta runtse Idanunta cikin rauni ta ce "Ni za a kashe"

"What? Kisa wake shirman haka" ya ajjiye babyn ta ɗauke ɗanta da sauri ta duba hijabin dake gefe wanda yake sabo ta ɗauka ta saka jikinta jiri na ɗaukarta ta rungume ɗanta tare da nufar wajan domin ta miƙa kanta gare su.

His Excellency Abu-turab Alƙasim ya fito yana kallon Hammadala dake ɓoyewa cikin nutsuwa ya shiga nufar wajan da harbin ke tashi Hammad ya ce "No Your Excellency, kada ka je wani Mahaukaci ne da bindiga yake harbi kawo yanzu ya harbi securities guda uku"

"In my house? Mahaukaci?" Hammad bakinsa na rawa ya ce "Yes Sir, kuma wallahi riƙaƙƙen Mahaukaci ne kayan jikinsa tamkar sun yi shekara ɗari a jikinsa, gabaɗaya jikinsa zane ne kamar na tattoo gashi baƙiƙƙirin...


Na'ima Sulaiman Sarauta

08119237616

*🌈 MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

*_Follow my account👇🏾_*

https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


*6......*

His Excellency Abu-turab ya dubi P.a ɗinsa Hammad ganin yadda jikinsa yake ta rawa kamar wanda aka ce masa ba zasu ƙara samun mulki ba. "Your Excellency abun nan yana neman girmama, mu sanar da securities na Government house" Abu-turab dai bai ce komai a hankali ya ci gaba da takawa har zuwa tsakiyar compound na gidan nasa, ya shiga ware idanunsa akan securities ɗinsa da aka harba wanda suke kwance a ƙasa. Ya ɗaga kai ya dubi wanda yake tsaye ya juya masa baya, cikin nutsuwa ya shiga ƙarewa yaro ko matashin saurayin kallo.

Cikakken namiji ne a tsaye, ya riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya, ɗaya hannun riƙe da bindiga ga jini yana zuba daga hannun, baƙi ne irin sosai ɗin nan fatarsa har sheƙi take gabaɗaya wuyansa zanan tattoo ne kamar wanda aka zanawa macizai, sumar kansa a cure take ta wani murmurɗe kamar indomie ta sauka har wuya, wani irin crazy jeans ne a jikinsa wanda ya yayyage ga wata Armless ɗin riga tayi fata-fata a jikinsa, siffofin mahaukaci bayyane a jikinsa. "Who are you?" Abu-turab ya tambaya cikin kakkausar murya fuska ba wasa.

Wanda aka kira da Mahaukaci gabaɗaya ya juyo, kyakkyawar bugawa zuciyar Abu-turab ya yi in his whole life zai iya cewa bai taɓa ganin kamar shi ba, zubin idanunsa ma daban yake musamman yanzu da idanun suka sauya launi babu mai iya fassara abubuwan da suke nunawa, wanda ya yi masa mugun sani shi ne zai iya me yake ji ko me yake buƙata.  Sosai yake da gashin gira a cunkushe, duk baƙin da yake da shi lips ɗinsa jajir yake. Ya lumshe idanu ya buɗe akan Abu-turab,bai ce komai ba ya ci gaba da ƙare masa kallo sai kawai ya ɗauke kansa.

"Ma ka ke buƙata?" Still bai magana ba. Sai a lokacin Hammad ya ƙara so wajan suka dinga kallon mahaukacin kafin P.a Hammad ya ce

"Hi crazy man, who are you, What do you need?"

Nan ma ya daɗe yana kallon su still bai ce komai ba, Hammad ya kalli Abu-turab ya ce

"Your Excellency Wallahi Mahaukaci ne"

Abu-turab ya jinjina kai yana ƙoƙarin juyawa cikin gidan ya ji saukar muryar mahaukacin  ya ce "Hhhh kai... I want my Jee back, and my son" Hammad da His Excellency Abu-turab suka kalli juna kafin Hammad ya ce

"Who's Jee?" Yaƙi cewa komai sai ƙirjinsa dake ɗagawa. "Your Excellency na faɗa maka Mahaukaci ne, da alama ba a son ya hauro ta kadanga ba" Abu-turab ya yi jima kafin ya ce "Call securities" yana faɗin hakan ya juya zai koma cikin gida wajan Majeederh. Da sauri Mahaukacin ya sha gaban Abu-turab yana ƙare masa kallo idanunsa jajir kamar gauta cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce

"Ina so Jee, i want my babe" "Are you mad? Kai ma haukaci ne?"

Shi dai babu abinda yake cewa sai "Ina so Jee, i want my Jee back babe na" His Excellency ya dubi sauran jami'an tsaron ya ce "Ku fita da shi" kafin su kama shi idanun Mahaukacin ya sauka akanta, tana riƙe da jajirin kamar kullum jikinta rufe da hijabi ya zaro dara daren idanunsa waje ya juya da sauri cikin ɗaga murya ya shiga faɗin "Jee, Jee!"

Tazarar dake tsakaninsu ya sa sam bata ji ba. Ya ƙara sauri kamar zai kifa, yana ƙoƙarin haure motar da ke parking lot aka cilla masa igiya ta ƙafa ya faɗo ƙasa, kafin ya yunƙura an sake cilla masa igiya ta harɗe hannayensa, maimakon ya yi ƙoƙarin dukan securities ɗin sai ya fara buga kansa da tarazon wajan yana faɗin

"Bebe, Jee, Malumana"

Ya dinga faɗa yana buga kansa cikin ƙaramin lokacin jini ya wanke masa fuska ya fara gani dishi dishi.

Majeederh na shirin ƙara sawa tsakiyar parking lot ta ji anyi saurin kama hannunta tare da janta baya, a tsora ce ta juya suka haɗa idanu da Abu-turab baki buɗe take kallonsa, daman shi ne? daman Gwamnan jihar su ne ya taimake ta? "Me ki ke?" Ya faɗa speaking calmly. Ta janye idanunta tare da kame kanta tana son ɓoye fuskarta ta tuna ai bata da wata sauran ƙima da daraja sai kawai ta ɗan ja baya ya tattausa murya ya ce

"Baki da lafiya Jiddo, kina son hutawa" ta juya ta kalli yadda Hammad ke kallon su haka kawai jikinta ya bata akwai wani abu ta ce

"Ni za a kashe?" Ta furta cikin kamilalliyyar muryarta. His Excellency ya buɗe ido ya ce

"No, wa zai kashe Jiddo, na samu baƙi ne da zamu yi meeting koma ciki ko?" Haka kurum ta ji ta yarda da shi kuma ta san waye shi yana kyakkyawar mu'amala ta juya shi kuma ya bi bayanta, tana ɗaga ƙafa zata shiga ƙofar ta ji an ce "Malumana" cak ta tsaya ƙirjinta na bugawa zuciyarta na harbawa a ranta ta ce "Little Son"

Zata juya ya yi saurin faɗin "Meke faruwa?"

Ta ɗan yi jam can ta ce

"Na ji murya" ya ce "A voice?" Bata saurare shi ba ta juya shi ma ya juya har ya sha gabanta ya ce "Akwai jama'a, mu koma ba wata murya, ba wanda ya san kina ciki" ya lallaɓata tayi cikin gidan tana shiga ya rufe ƙofar ya sanya securities a jikin door ɗin.

Yana komawa ya samu ana dambe da shi ya yi jina jina da jikinsa "Duk sanda ya ƙara zuwa shoot him, kuyi masa duka" shigowar wata mota ya sa suka tsaya wasu ma'aikatan asibiti suka fito da wani dattijo wanda yake sanye da ƙatuwar sarƙa mai zanan kurus. David ya haɗe hannu alamar apologies ya ce "Sorry" Abraham sosai ya gane David domin shi ne babban Pasto ya jinjina kai kawai. David ya ce "His name is Abraham Daniel David, My grandson ya samu depression har ya zama taɓin hankali, na yi mamakin yadda na'urar jikinsa ta nuna mana nan, duk yadda akai akwa abinda yake nema, baya zuwa waje babu dalili duk haukansa" Pasto David ya faɗa yana sawa a kunce Abraham tare da sanya shi a mota.

Faɗa akai sosai kafin daga ƙarshe aka danna masa Allura nan take ya fara barci.

Majeederh ta zubawa jaririn nata idanu tana son ƙara fahimtar kamanninsa amma abun ya kwanta mata gashi kullum ƙara juyewa yake kama da ita.

"Kin sanya masa suna ne?" Mama ta tambaya tana miƙawa Majeederh haɗin tea a cup ta lumshe idanu ta buɗe a hankali ta girgiza kai. "To ai yana da kyau ayi masa  huɗu ba, wanne suna ki ke so?" A hankali ta ce

"Ibrahimul-khalil"

"Ikon Allah, Sarkin zuciya da faɗa kenan, ga ƙwazo shi kuma ba rago ba halin su ɗaya da Aliyu Haydar Allah ya raya mana Ibrahimul-khalil" Majeederh ta saci kallon Mama so take ta ɗan saba da ita amma yanzu gabaɗaya zuciyarta na gargaɗinta da ƙara yarda da wani, tunda Latifa Omar ta riga ta sanya mata tsoro ainun a zuciya ta gane babu Aminiyya, Abbu ya sama tabo na har abada wanda ya sa ta fahimci babu wani masoyin ƙwarai ko true love.

"A beautiful name, but why Ibrahimul-khalil?" Ba tayi masa magana ba ya zauna saman kujera kafin ya ce.

"P.a a shirya tsaro na musamman a gidan nan, a duba motsin kowa" Hammad ya rusuna ya ce "In sha Allah, Allah ya taimaki Your Excellency"

Fita su kayi gabaɗaya ya rage daga Mama sai Majeederh da Kalil dake barci.

Aaliyyah na zaune a parlour farin ciki ya kamata gobe za a ɗaura aurenta kamar yadda Uncle Isma'il da Uncle Bello su kayi al'ƙawari.

Abbu taga ya fito ɗauke da tarin takardun Majeederh na makaranta, da shaidar zamuwarta mace ta farko data fara lashe gasar musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa da duk wasu ducoment da Award nata da tarin littafanta. Ta miƙe da sauri ta ce "Abbu me za ka yi da wannan?"

Ya yi mata banza tabi bayansa har zuwa tsakiyar compound gani tayi ya zuba musu fetur ta cilla Ashana ta zare Idanu ta ce.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, me kayi haka Abbu" ya dubeta ya ce

"Har na koma ga mahaliccina ba zai taɓa daina yi wa Majeederh Allah ya isa ba, da haihuwarta gwara ɓarinta Allah ya sanya ta ƙarasa lalacewa har abada,ta ɗakko cutar ƙanjamau Hiv har tayi silar mutuwarta a wulaƙance" Aaliyyah kuka take sosai ta ce "Abbu kana sanya mini tsoro anya kai ka haifi Anti Jeederh?" Ya yi murmushi ya ce "Kowa zai yi zaton haka, wallahi wallahi ni ne uban Majeederh ni na haifeta amma yanzu kaf duniya ba Wacce na tsana sama da ita, a kullum idan na ce ta fito da mijin aure sai ta ce Allah bai kawo ba har cewa take ba wanda ya taɓa cewa yana sonta na zaɓa mata, na sha haɗata da maza daga ƙarshe su gudu ashe su sun riga sun halinta sun gane Fasiƙa ce, Mazinaciyya ce, la'ananniyya ce, Allah ya isa Allah ya isa Ubangiji ya tsine miki Albarka Majeederh" ya fashe da wani irin kuka Aaliyyah ma kukan take. Bar Aliyu Sufyan Alhassan yini ya yi yana neman Malama Majeederh amma ko mai kama da ita babu, yana dawowa gida zazzaɓi mai zafi ya rufesa...

Misalin 1:23 na dare tana zaune rungumeta da Ibrahimul-khalil da yaƙi barci yana ta rarraba Idanu gashi so Ma sha Allah sbd kyau daman ance shegu masu iya kyau ba. Sai ya zame mata abokin hira ta ce "Ina son ka Kalil, yadda na riƙe ƙa amana Ubangiji ya kawo sanadin da gaskiya za tayi halinta, ina jin kamar na shiga duniya na kama hotel....," Gilmawar inuwa ta gani kamar an shige ta ɗan kalli wajan ta juya ta duba lokaci taga ɗaya da rabi na dare saura kafin ta san abin yi an fara buga ƙofar bedroom ɗin da ƙarfi ana faɗin "Jee Jee Malumana...


Na kusa ending free pages. Contact to subscribe.... 08119237616 Whatsapp only.

*🌈 MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

*7.......*


_Complete story Arewabooks👇🏾_

https://arewabooks.com/chapter?id=6219d7896c0de838cd360960


Duk yadda Jeederh ta kai da son kamewa waje guda da riƙe kanta amma ka sawa tayi ta miƙe tsaye hannunta riƙe da Khalil, amma ta kasa motsawa sbd bata ƙara jin saukar sautin da kunnuwanta suka jiye mata ba. Shiru shiru sai kawai ta juya zata koma saman bed ta ƙara jin ance "Jee, Jee Malumana" a wannan karan muryar da aka kira sunan bata fita sosai kamar bai kiran yana cikin wani hali, ƙirjinta ya yi kyakkyawar bugawa, bugawar da sai data runtse Idanunta, me ya sa muryar ke yi mata tsananin kama data Little Son? Me ya sa hatta sunan ya zo ɗaya da wanda ya laƙaba mata sbd bashi da hausar da zai iya kiran complete sunanta Majeederh kamar yadda kowa ke faɗa, iya ƙoƙarinsa da faɗar sunan sai dai ya furta kalmar _Jee_ a sauƙaƙe?

"Yaa Allah" ta furta domin tasan har abada har gaban abada idan akwai he never comes to her, amma meke damunta har haka me ya sa muryar ke mata amsa kuwwa a kunne? "Jeeeee!!!" Ya sake furtawa muryarsa bata fita sosai kamar wacce aka tsikara tayi wajan ƙofa tare da sanya hannu ta murɗa handle, tsaye ta gashi yana zabga ƙamshi daga shi sai wata kyakkyawar Arabian jallabiya brown kallo wacce tayi masa kyau sosai, ya ɗan sakar mata kyakkyawan murmushi kafin ya ce

"Kina buƙatar wani abu ne?" Tayi masa kallo ta ɗauke kai ba tare data amsa shi ba, domin bata da yawon magana Majeederh nada matsanancin aji sosai, wanda kuma halittar ta ce hakan. Gani ya yi tana leƙa waje shi ma ya leƙa yana cewa "What are looking for? Me ki ke kallo?" A raunane wanda kuma ba kowa take son yaga raunin nata ba ta riƙe kanta sosai tana sake rufe jikinta da hijabi ta ce "Allow me to go"

"Where?" Ya amsata da sauri. "Ban son zaman nan, kuma ka bari na leƙa waje" Abu-turab ya ware idanu yana shafa sumar kansa ya ce.

"Me Jiddo zata yi a waje yanzu? 2 saura ok" tayi shiru ya ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin tayi saurin ƙanƙame jikinta waje guda lokacin Khalil ya fara kuka..

Sosai Abu-turab ya rufe ƙofar kana ya nemi waje nesa da ita ya zauna saman kujera ya harɗe ƙafa. Malama Majeederh hankalinta ya rabo wajan kashi uku, ɗaya na waje, ɗaya na kan Khalil dake kuka, ɗaya na kan Abu-turab daya sanyata a gaba tare da kafeta da idanu. Sai ta zama ira bata ƙaunar kallo yana takura ta ainun.

Abu-turab yana ƙoƙarin magana su ka ji an daki ƙofar ya miƙe tsaye tare da kallon Jeederh ya ce

"Sorry, na ce a kawo mini abin shur ina da azumi" bata ce komai ba ita dai.

Ya nufi ƙofa yana fita ya rufe ta, kokawa ake sosai da Abraham Daniel David wanda yake son ta ƙarfi sai ya ɓalle ƙofar, gadai securities da yawa amma sun kasa controlling nasa ya jiwa kansa ciwo amma yaƙi ya yi giving up, wani irin ƙarfi ke zuwar masa. "Abraham" Abu-turab ya kira shi,ya juya kalli Abu-turab.

"Me ka ke buƙata?" Da hannu ya nuna masa bedroom ɗin da Malama Majeederh ke ciki, kana ya nuna ƙirjinsa wajan zuciyarsa ya ce.

"Jeena, nan" Abu-turab ya fahimci Abraham na son shaida masa Jee na cikin zuciyarsa ita kuma yake nema. Cikin nutsuwa yana murmushi ya ce

"My friend zo ka ji" Abraham ya kafe waje guda domin babu na biyunsa a taurin kai. Cikin tattausa harshe ya ce "Ita Jee ɗin bata nan, amma ka dawo gobe zan kaita wajanta" ya faɗi hakan cikin harshen Ingilishi yadda Abraham zai fahimci mai yake nufi.

"Promise?" His Excellency ya ce "Promise" Abraham ya sanya hannu a tsakiyar rigarsa inda ya yage ya zaro wata kyakkyawar flowers  sai ƙamshi take ya miƙawa Abraham yana wani irin buɗe ido ya ce "Malumana"

Ma'ana the flowers is for her. His Excellency ya amsa deep down na zuciyarsa cike da mamakina Abraham who is he to her?.

Securities ɗin za su kama shi ya girgiza musu kai tare da yin gaba yana ɗan tangaɗi yana yin gaba ya ji saukar muryar Khalil na kuka ya tsaya cak, sai ya juya kawai sai su kaga ya yi murmushi ya ce

"My pregnancy"

"An samu matsala" In ji Khamal. Abu-turab ya saka hannu ya tsige flower ɗin tare da zubar da ita ya ce

"Make sure baku sake sakaci ba, i hate noises"

"We're sorry Sir, Hakan ba zai sake faruwa ba, wallahi ta sama ya hauro mahaukaci ne daya kama hannun Captain sai da ya ƙarya shi,ya sha duka sosai wajanmu amma bashi da haƙuri yana da zuciya ban san wani abu giving up ba" His Excellency bai ƙara magana ba ya buɗe bedroom ɗin har yanzu tana zaune saɓanin ɗazo Madara take bawa Khalil, Abu-turab ya jima yana satar kallonta da tayi ƙoƙarin ɗago kai sai ya janye idanunsa ya basar

"Jiddo, we need to talk please" yadda ta ƙara nutsuwa ya san cewa ta bashi dama cikin nutsuwarsa ya ce

"Majeederh kina da hankali, ko ban girmeki ba zamu iya zuwa age mate don haka duk abinda zan faɗa miki ba zai zama cutarwa a gareki ba" ya sauke numfashi ya ɗora da "Don Allah kada ki ji zafinki akan hukuncin da ya yanke miki, iyaye ba a taɓa fushi da su ki ɗauki hakan matsayin jarrabawa kuma ƙaddara wacce babu yadda zaki iya dole sai ta kasance, ba zan miki nasiha akan yarda da ita ƙaddarar ba domin kusan kin fini sani, sai dai na nemi ta barraki a wajanki" ya ƙara yin shiru ya ce "I feel your pain, kafin na zama gwana na sha wahala,ina rayuwa da mahaifiyata after my father's died, dangin mahaifina they are so selfish sun ƙwace komai dana mallaka wajan Abbana, filaye, kadarori all the properties, mun fara yawo yawo a dangi kowa yana gudunmu sbd babu ran mahaifina sun manta alherin da ya yi musu, dangin Mamana basa kusa, na fara dako ina garuwa ban taɓa yarda ba zan iya ba, burina Mamana ta ji daɗi na zama wani abu" ya ɗan sauke numfashi kamar lokacin abin ke faruwa kafin ya zuba mata Idanu ya ce "I was thinking mene ya sa mutane suke manta alheri? Kuma da yawan mutane suke sawa ka zama mutumin banza, ko dana fito takarar House of assembly kin me ne ya faru?" Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalle shi some seconds kafin ta janye ganinta daga gare shi, tana ɗan ɗauke numfashi sbd abubuwan da suka tukare mata bata san ranar faɗawar su ba. Abu-turab smile yana jan idanunsa zuwa sama kafin ya ce

"Cewa akai kada a sake a zaɓeni wai bani da uba, ba wannan ya daman ba familyna sune kan gaba wajan ganin na fasa kujerar da nake nema, kamar yadda suka so ban samu ba, gabaɗaya deligate suka juya mini baya, cikin ikon bayan an cinye tenuwa huɗu cif na sake fitowa takara i won the election, nayi shekara huɗu a lokacin ne na haɗu da ƙaddarata, wacce ta zame mini Dafi a zuciya, ta zame mini wani tabon da bana tunanin zai taɓa gogewa da jikin zuciyata sai dai idan zuciyar ce ta samu abinda take buƙata, Jiddo ban faɗa miki haka domin ki tausaya mini zuwa gaba ba, shi ya sa ma ba zan baki labarin cikakkiyar ƙaddara tawa ba, amma ki sani ko wanne mumini idan har amsa sunansa dole Ubangiji ya jarabce shi da jarrabawa, bafa don ya son mutum yake jarabtar shi ba, sau tarin wanda Ubangiji ya fi jarabta to ya fi samun kusanci da shi, kiyi haƙuri ki ɗauka haka zanen taki ƙaddarar yake, babu mamaki mahaifinki ya fiki jin zafin abun da ya faru kiyi masa uzuri, ki addu'a cikin sauƙi komai zai zama labari" ruwa ya ɗauka ya sha yana sauke numfashi.

"Thank you!" Ta furta cikin kamewarta da nutsuwarta a koda yaushe, da nuna cewa ita ɗin babba ce mai ƙiba da daraja wacce a yanzu ta rasa ko wanne daga ciki.

"It's my pleasure, an kawo Raguna na raɗin sunan baby" "ba buƙata"

"Akwai" ya furta cikin tsare gida.

"Kada ki zama mai son kan ki Jiddo, kada ki zama mai musu after all this am elder than you na je 42 ke kina 35, kin ga akwai respect na girman dana baki" shi kansa mamakin surutunsa yake a yanzu ya manta rabon da ya yi magana mai tsayi, lallai zuciya bata da aji ga abinda take muradi da kwaɗayin zama da shi..

"Khalil na godiya"

"Mamin Khalil fa?" Bata ce komai ba ya watsa hannu ya ce "Alright, i don't need your thanks"

Ganin yadda take kallo agogo ya sa ya fahimci tana son kwanciya ya miƙe tsaye yana shafa sumar kansa ya ce

"Ya Rabb! Good night"

Har ya je bakin ƙofa ya sake juyawa ya zuba mata idanunsa ya ce

"Lailatan sa'ida" ta bisa da kallo har ya fice.

Majeederh Yaronta Khalil ta zubawa idanu wanda yake barci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bata da sanya damuwa a rai, amma kunnuwanta sun kasa manta sautin Abbu da yake cewa

"Allah ya isa Majeederh"

Ta rufe ido da sauri ta buɗe data tuna kalmar "Tamkar gawa haka ki ke a waje na" "Fasiƙa!"

Ƙirjinta ya fara ɗagawa numfashinta na tsayawa ta fara kokawa da iskar dake kaiwa zuwa hunhunta ta miƙe da sauri tare da shigewa Bathroom tana daga tsaye ta sakarwa kanta ruwa mai sanyi shower ta dinga ratsa tsakiyar kanta jikinta ya jiƙe ta mance ciwonta sam, ita da ace ciwon zai zama sanadin tafiyarta lahira da wallahi sai tafi kowa murna da kan ta yarda ta koma wajan wanda ya halicceta ya bata ikon kare mutuncinta amma wani mugu azzalumi ya rusa wannan ƙimar, ya shiga gonar da bashi da ikon ko mallakarta bare ya yi tunanin yin noma ya zuba iri. Ana cewa sai ƴa mace ta bada dama ake cin mutuncinta, kamar yadda kalamar sai bango ya tsage ƙadangare yake samun damar shiga.

"Wata bawa dama?" Zuciyarta ta tambayeta. A fili ta furta "Ba zan yafe ba, ko waye na tsane shi Allah ya hana shi kwanciyar hankali"

Ta cire kayan jikinta tare da ɗaura towel jikinta sai sheƙi yake ko'ina yana glowing tunda hutu take samu. Dirarriyar mace ajin farko, kyawun Majeederh na iya sanya ayi raped nata balle Mutum ya yi arba da surar jikinta. Fitowa tayi ta ɗauki wata push pink ɗin abaya ta sanya tayi rolling kanta tare da tsayawa gaban window tana kallon waje tare da shaƙar fresh air, a hankali ta ƙara buɗe Idanunta domin daga bayan ɗakin da take gate ɗin bayan gidan ne idon ba gizo Idanunta ke mata ba babu shakka mutum take hangowa zaune shi ɗaya ya zuba uban tagumi...

Washegari ta shirya tsaf ita da Khalil tana cikin wata blue black ɗin Abaya tayi rolling kanta da babban mayafi fuskar nan fara fat kamar wacce jini ya ƙarewa ga yawon jiri da take yi da ciwon kai duk dare, ta ajjiye cup ɗin hannunta Mama dake zaune ta ce

"Ko ke fa, ai jego ba zai yiwu babu cin abinci ba, shi ya sa babu ko ruwan nono a jikinki, ina tunanin zan yi wa Haseenatou magana ta zo ta tayaki zama kyafi sakewa"

"Na gode sosai Mama, am ina son tafiya"

"Tafiya zuwa ina? Kina kallon yadda jama'a suke fakon ki kamar kin kashe rai wani bai san meke faruwa ba, kawai jita jita zai ji ya kama ya ɗorawa kansa, Ƴata duk wata daraja mace gidan mijinta idan babu shi ne ake rayuwa cikin gidan iyaye, yanzu an shige zamanin da idan ƙaddara ta faɗawa ɗan ka zaka gujesa, a lokacin ma zaka jawosa jikinka, Malama Majeederh baki da wajan zuwa sama da nan kiyi zamanki ki raini ɗan ki har ki samu mijin aure" Majeederh jin Mama kawai take domin ita ba aure yanzu a shafin rayuwarta, babu ma namijin da zai iya sha'awar zama da ita matsayin miji. Suna zaune aka buɗe ƙofa wata kyakkyawar yarinya ta fara shigowa da gudu hannunta riƙe da teddy tana zuwa ta haye jikin Mama ta ce.

"Uncle ba ni"

"To ƴar gatan Uncle"

P.a Hammad ya shigo da murmushin tare da zubewa ya ce "Ina kwana Mama" Mama tayi murmushi ta ce "Allhamdulillah ya mutum gidan" ya amsa da "Suna lafiya" ta miƙe tsaye ta ajjiye Jidda ta ce

"Bari na shiga na kalli labarai" ya yi mata adawo lafiya cike da ladabi da girmamawa domin yana da tabbacin Malama Majeederh ta girme shi ya ce

"Barka da Safiya Anti Majeederh" idanunta akan Khalil a kullum shi ne abokin wasanta, ya zame mata t.v

Ta jima tana kallon Khalil kafin ta ce "Kana lafiya?"

"Allahamdulillah ya baby" ta juya idanunta kawai bata ce komai ba.

"Jidda ce Mami good morning" ta kalli Pa. Hammad ta ce "Mami ce?" Daga bakin ƙofa aka ce "She's your Mother, jeki gaidata" His Excellency Abu-turab ya furta yana shigowa cikin wata dakakkiyar shadda mai kyau sai zabga ƙamshi yake sosai nutsuwarsa ta gama bayyana kamalar shi.

Jidda tana tsalle da murna ta ce "Mamina"

Ta faɗa tana leƙa fuskar Malama Majeederh.

Jeederh ta yi wa Jidda murmushi tana shafa kanta, P.a Hammad ya yi waje ya bar daga His Excellency sai Malama Majeederh da Jidda.

"Is my daughter, mun rasa mahaifiyarta wajan haihuwarta honestly sunanki na saka mata" da mamakin sosai Majeederh ke jin abun ina ya santa har ya sanyawa yarinyarsa sunanta? Lallai karamcin Abu-turab daban yake, kamar yadda ya ce haka aka yanka rago tare da ƙara yiwa Ibrahimul-khalil huɗu ba da sunan daya samu. Tun daga nesa yake danna horn cikin sauri mai gadi ya buɗe masa ya shigo, a hankali ya sako kan motar cikin harabar gidan nasa, mamakin ganin motoci daban daban a parking lot ya kama shi.

Ya buɗe ya fito yana sanye cikin wani tattausa brown ɗin yadi mai laushi ya ɗora hula jaddara, hannunsa ɗaya ya saka cikin Aljihu har zai tambayi mai gadi baƙi akai ne? Sai kawai ya buɗe ƙofa ya shiga, shiru gidan babu motsin komai sai wani slow music dake ta shi, ga parlourn kaca-kaca sai wari da ƙaurin abinci yake, kwalayen exotic birjik plate ɗin abinci har a saman kujera, nan da nan cikin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya fara juyawa ya toshe hanci da sauri yana haurawa sama tare kiran

"Latifa, Latifa"

Yana ƙoƙarin buɗe Ƙofar bedroom ɗin ta tayi saurin fitowa, ya shiga kallonta frm head to toe, towel ne a jikinta iya qiwwa gashin kanta duk a har gitse ya dubi gefen bakinta ya ga jambaki.

"Lafiya?" Aliyu ya ce

"Su waye a gidan?" Ta ce "Friends ɗina ne, yanzu zasu bar maka gida" ya yi jim kafin ya ce "Yanzu dake da friends ɗin mahaukatan ina ne Wife? Ki kalli gidan nan kamar bola wanne irin abu ne, kema kalleki babu tsafta ba komai irin ƙamshin perfume ɗin nan ma babu, babu mamaki part ɗina ba haka yake ba gyara a haka ki ke ihun kada nayi aure? Ko son ki zai kasheni idan har zaki dinga gallaza mini da ƙazantarki wallahi tsanarki zan yi" ya juya rai ɓace bai taɓa ganin ƙazanta irin ta Latifa ba ta rasa yadda za tayi amma tayi farin ciki domin ita tunaninta ya manta da batun Latifa... Gidan ya yi shiru Mama tana part ɗinta, His Excellency Abu-turab ya fita zuwa Wajan meeting a Government house, securities ɗin na bakin ƙofa. A hankali ya dinga leƙo kansa ta wajan gate ɗin dake kusa da bedroom ɗin Jeederh, shigar yau ta musamman ce gashin kansa ya ƙarya hargitsewa ya kwanto gaban goshinsa, hannunsa riƙe da wani teddy da flower mai kyau rabin faffaɗan ƙirjinsa a bayyane sbd yagewar da rigarsa tayi wandon jikinsa 3gauter ne, ga ƙatuwar sarƙa a wuya. Ya kama gate ɗin tare da dirowa cikin gidan, da sauri ya nufi bedroom ɗin cikin sa a yana kama handle ɗin bedroom ya jisa a buɗe, Abraham ya lumshe idanunsa masu cike da kewa ba sallama ba knocking ya tura kansa cikin bedroom ɗin daidai lokacin ta fito daga toilet tana sanye towel iya cinya...


Not editing

Jiya na yi Busy na je unguwa ga wajan aiki🙏🏿.


An fara biyan kuɗin littafin tuni... Yi magana domin biyan naka 08119237616


*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_  *ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan  gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.*

We have

*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su

*Atampha of all kinds*

*Veils*

*shadda*

*shoes*

*qualitative handbags*

*Jewelries* etc

Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din *09060450181*

Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu


https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo

*🌈MIJIN MALAMA🌈*


*_Arewabooks@Nimcyluv_*


_Please ayi following Acct na sister na👇🏾_

https://arewabooks.com/u/ayshadansabo


*8......*

Kamar an dasa Abraham haka tsaya jikinsa na rawa kansa ya sara sosai, wannan shi ne karan farko daya yi mata kyakkyawan kallo, kallon da ba zai taɓa shafewa a cikin ƙwaƙwalwarsa musamman yanzu da yake cikin yanayin ciwon hauka, haukan kuma bai sanya ya manta wani kyakkyawan gurbi dake zuciyarsa ba.

Ko a baya bai san haka kyan jikinta da surarta yake ba. Malama Majeederh na tsaya gaban mirror ta ɗauki wani body lotion tana dubawa ɗago kan da za ta yi taga mutum tsaye a bayanta ta cikin mirrorn.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ta furta cikin tsoro ta rufe Idanunta domin bata gama tantance waye ba, ta ƙara buɗe idanu ta cikin madubi ga mamakinta hawaye ta gani kwance cikin idanunsa sai a lokacin ta kalli cikakkiyar fuskarsa.

"Little?" ta ce da mamakin domin ita ta gama sanyawa a zuciyarta baya raye a duniya. Yana tsaye bai motsa ba, hawayen idanunsa bai tsaya ba, abubuwa ne da yawa suke son dawowa cikin tunaninsa wasu tsofaffin memories na gilmawa ta cikin jijiyar dake motsawa tunanin ko wanne ɗan adam a cikin ƙwaƙwalwa.

Su yake ya tambayeta "Me take a nan? Ya yaga ta take? Waye ya taɓa ta yanzu ya yanke hannun ko waye, me ta yiwa jama'ar gari? Shin daman haka addinin na su yake, mabiyansa basa yiwa kansa adalci, basu kyakkyawa na ciki ba ina ga bare?"

Bakinsa ya a yi masa nauyi, tunaninsa ya tsaya kamar yadda take kallon cikin idanunsa haka ita ma yake kallonta,irin kallon nan da ba kowa ne ya isa ya fassara ma'anar shi ba.

"Jee" Abraham ya faɗa tare da yin inda take, kafin ta juya da nufin matsawa ko ɗaukan hijabi gaba ta jita nan naɗe jikin mutum ya ƙanƙameta a ƙirjinsa kamar wani zai ƙwace ta, tamkar zakin daya shekara yana neman abin farauta bai samu ba sai yanzu.

Duk yadda da su ƙwace jikinta kasawa tayi, fargabarta ɗaya kada wani ya shigo zargin da ake mata ya tabbata, domin babu wanda zai yarda ba da saninta Abraham ya shigo ba.

"Ka yi hauka?" "No!"

Ya bata amsa, amsar data bata mamaki tasha ce masa "Ka yi hauka ne" kai tsaye zai ce mata "Yes, Mahaukaci ne ni Jee" amma yanzu ya bata amsa da "No!"

Hakan na nufin akwai wani abu a ƙasa.

A lokacin kuma ta lura da yanayinsa, shigarsa, sauyin tunaninsa da kamanninsa everything. Majeederh tsayawa tayi tana kallon Ikon Allah, ba zata iya ciwon baki ba, ba zata iya kokawa ba don haka ta ja idanunta ta runtse ƙirjinta na ɗagawa a saitin nasa ƙirjinsa sosai kuma hakan ke taɓa Abraham, tun tuni ta san Abraham bai san wani abu mai kama da tsoro ba, bai san haƙuri ba, balle ace kayi haƙuri ya yi, bai ladama ba, bai san ya yi laifi ba, taurin kai ba zai taɓa abinda bai niyya ba. Abu ɗaya ne da shi yana da tsananin tausayi baya ƙaunar ganin hawayen mace yanzu zai riki ce.

Mamakin ganinsa kuma ya sata kasa ɗaukan mataki.

"Am not crazy Jee, ni ba mahaukaci ba, am not bad, an kai ni gidan mahaukata, kada ki bari wallahi zan kashe kowa"

Jeederh ta tattara ƙarfinta ta hankaɗe Abraham tare da nufar wajan wardrobe zata ɗauki hijabi cikin saur ya biyo ta tare da riƙe hannunta ya sa ƙafa ya daki wardrobe ɗin nan take ta tsage murfin ya faɗo. Ta sanya hannu ta zabga masa mari, ta ƙara zabga masa mari rai ɓace irin ɓacin ran da ko a gaban Abbu bata nuna ba lokacin daya koreta daga gidansa Idanunta ya kawo ruwa ya kwanta ta nuna shi da hannu tama kasa cewa komai.

Murmushi Abraham ya yi yana shafa fuskarsa wane yatsun hannunta ya kwanta sosai cikin gurɓatacciyar Hausar shi maganar a rarrabe da ƙarfi kuma ya ce..

"Beat me, beat me...If that will make you happy" ya cije baki tare da sanya hannunsa ya hargitsa kansa da zafin nama ya dinga kaiwa ko'ina duka hannunsu ya fara zubar da ji ni ya juya zuwa inda take kamar zai shigeta ya ce

"Idanunki ya bayyana laifina,ni na ce maka I'll be back, sooner or later, bana da laifi Jee babu laifi wajeni" duk ya dagula hausar tashi wacce yasan ta fahimta. Ya kama hannunta ta ƙwace da sauri cikin kakkausar murya da riƙe kanta ba tare data bari ya fahimci halin da take ciki ba ta nuna masa ƙofa ta ce "Out, ka je can kayi haukanka mahaukaci"

"No, am not"

"You're Mad" da ƙarfi ya ce "Am not, you stop listening to me" ya faɗa yana matse kafaɗarta idanunsa kamar za su faɗo ƙasa ya zaunar da ita saman gefen gado, tare da zubewa a gabanta ya ɗora kansa saman cinyarta kamar yadda ya sama, wani irin raunataccen kuka ya ƙwace masa, ya dinga yi kamar wani ƙaramin yaro tunda take bata taɓa ganin hawayensa ba balle kuka yau gashi yana rusa mata kuka kamar ance masa Denial ya mutu ko David ko Kiristi. Ba zata iya tantance lokaci daya shafe yana kukan ba, zuciyarta motsa rauni irin na ɗiya mace ya so kamata tausayi irin na uwa da ɗanta ƙwance akan fuskar Malama Majeederh.

Tana son bashi baki akan ya tashi ya tafi, ya ƙara yin nesa da ita fiye da yadda ya yi ta bashi labarin halin da itama take ciki, tasan faɗa ba zai taɓa yiwa Abraham ba, ko mutanen duniya ne za su taro a nan babu abinda ya dame shi.

A hankali ta sanya hannu zata ƙara ɗaukan hijabi caraf ya riƙe hannun tare da ƙwace hijabin ya zuba mata narkakkun idanunsa wanda sukai jajir while he's still crying.

Hannunta ta sanya duk biyun a fuskarsa ta riƙe cikin kyakkyawan lafazi ta ce "Why? Why?"

"Am sorry!"

Ta dube shi ya ce mata sorry baya yi masa wahala, ya ce Sorry ga jama'a kuma babu uban wanda ya isa.

"Why?" Ta sake tambaya.

"Don't judge me, because of your barracks that I have been doing for years"

Ya fesar da numfashi yana kallon jikinta sosai ba abinda ya dame shi mamakinta yake sai yanzu ya fahimci dalilinta na kwasar tarkace ta zuba a jikinta.

"Jee ban ji komai a small marin da ki kayi mini ba, da gaske Mahaukaci ne ni? Dad ya ɗaukeni sun kai ni gidan mahaukata kullum ana mini injection suna sayawa ina jiwa kai ne ciwo, suna son fasa tunani na" ya sunkuyar da kai kafin ya ce.

"Jesus"

"Ki yarda this time around mu tafi, muyi auren Choci" Sai a lokacin ta share hawayen idanunsa ta ce.

"Little ina cikin masifa, ina cikin jarrabawar Ubangiji, don Allah ka tafi leave me alone"

"I knw everything, Abbu ya barki zuwa waje right? Jama'ar addininki sun wulaƙantaki right, Uhm where's is the baby?" Bata ce masa komai ba har yanzu yana durƙoshe gabanta ya ce

"Meye abun damuwa? Ni nayi miki cikin fa, ni ne baki cikin ke da babyn duk nawa ne barsu kawai" cikin razani tana fito da ido ta ce

"Abraham fita, ka fita na ce kabar bedroom ɗin nan" ya ɗaga ƙafa shi bai ga abin damuwa ba ya ce

"I mean my words ni ne na baki cikin, kawai bani da tabbacin yaushe cikin ya samu tunda al'amarin shekaru biyu baya ya faru kenan kuma yanzu ki ka fito da babyn waje, kawai nayi believing babu wani namiji da zai samu sa a irin tawa balle ya baki ciki"

"Ka cika Mahaukaci"

Gabaɗaya suka kalli bakin ƙofa Abu-turab ne tsaye yana tattara hannun riga, Abraham Daniel David ya miƙe tsaye Malama Majeederh ta tayi toilet cikin sauri ta zura abayar data cire ta ɗora rolling.

"Zan nuna maka Banbancin mai hankali da mara hankali, zan nuna maka tazarar dake tsakanin mai mulki da kuma wanda ake mulka" Abraham dai na tsaye can ya girgiza kai ya ce

"Oh, Go ahead"

"Kasan waye ni a jihar nan?" Cikin shan ƙamshi Abraham ya ce

"Governor Abu-turab Alƙasim" sosai His Excellency Abu-turab ya yi mamaki kafin ya ce

"Haukan ƙarya ka ke yi kenan?" Idanunsa akan ƙofar toilet ya ce

"Daman ai bance Mahaukaci ba ne ni, let me warn you kada ka takura kada ka matsanta,kada ka zurfafa domin You can take it"

"I love her" cewar Abu-turab.. "I am the one who raped her" Abraham ya bashi amsa, yana matsowa dab da shi.

"Zan iya komai a kanta" Wani irin murmushin mugunta Bad boy ya yi kafin ya ce.

"Ita ne dalilin ya sa aka kai ni gidan mahaukata"

Abu-turab ya faɗa shi ma yana matsowa wajan Abraham suka haɗe ko wannensu yana huci.

"Mara tsafta, wanda ya dulmiyya cikin yadanci ha zai taɓa samun Malama Majeederh ba"

Wata dariya sosai Abraham ya yi yana ɗora hannunsa a shoulder ta Abuturab ya ce.

"Ƙarshen samu ni na amshi budurcinta, na ɗauka abinda nake kwaɗayi ne sai dai ko  mintuna arba'in ba ayi ba na fahimci ba budurcinta nake so ba,I want to end my life with her, I want to take my last breath on her shoulder,I lived with her love, I will die on her lap with a smile on my face"

Abraham ya faɗa a hargitse. Abu-turab ya ce "Idan ka dauwama a gidan yari har ƙarshen rayuwarka, sai mu gani ko zaka sameta"

"Kai ka ke tsoron prison, ka duba record, da report na Abraham Daniel David ni criminal nan"

Abu-turab ya ɗaga hannu zai mari Abraham kafin His Excellency ya sauke hannun ji ka ke ƙasss! Abraham ya ƙarya hannun. Wata ƙara ya saki da sauri kuma ya danna wani abu daman Hammad na waje don kada ya shigo ne, yana jin ƙarar ya shigo da sauri ganin Abraham ya sa ya ja da baya.

Securities ɗin da suke cikin gidan gabaɗaya suka shigo part ɗin Malama Majeederh daidai lokacin itama ta fito Idanunta jajir da alama ta saurari komai dake faruwa.

Zufa ce ta dinga yankowa Abu-turab, Majeederh ta tsaya tana kallon Abraham day taso ya tsaya a gaban baki ya buɗe ya ce.

"Malumana, shi ne....,"

Marin data sauke masa yasa ya kasa magana, ta ƙara sauke masa.

"Ka tarwatsa mini farin cikina, jin daɗina kwanciyar hankalina, ka rabani da iyayena i hate you" Abraham ya zare ido domin shi ya ɗauka for now bashi da wani laifi, idan har ta karanta saƙon daya bari before he leave the country.

"Na raineka da hannuna, na baka kulawa kamar yaron dana haifa,daga baya na rasa ka, nayi kuka na shiga damuwa, ban cancanci haka ba, kaci zarafina ka ci mutumcin addinina, ban san ya akai hakan ta faru ba amma zan so ka bayyanawa duniya gaskiya domin na samu sassauci, Abraham Daniel David...".

Ta ɗauke kai shi dai yana tsaye gabanta kamar idanunsa za su faɗo ƙasa, yadda ƙirjinsa ke ɗagawa kai sai sanya a gane zafi da tasirin maganganunta a zuciyarsa.

"Allah ya isa, na tsaneka adadin tsanar da mahaifina ya yi mini zan so ka samu tabbataccen taɓin hankali na har abada" sai a lokacin Abu-turab ya zo ya kifawa Abraham mari amma ko motsawa bai ba Malama Majeederh kawai yake kallo.

"Ku kakkarya mini shi a kuma kai shi prison har ending rayuwarsa"

Securities suka rufe Abraham da duka ta ko'ina da ƙasan bindiga. Da ace babu Majeederh wajan ko kalamanta ba su yi tasiri a zuciyarsa ba da tuni dambe ake da shi. Ana dukansa yana kallonta. Ya miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabinta yaje har gabanta ya sanya mata, shi kansa bai san dalilin sanya mata hijabin ba, amma yana lura da idanun Abu-turab akanta. Wani securities ya sakarwa Abraham ƙasan bindiga akansa nan take kan ya fashe, Majeederh ta runtse Idanunta.

Daidai kunnenta ya ce.

"Jee kin jima da sanin Abraham baya giving up, azabar nan babu inda zata, idan baki yafe mini mun daidaita har mun yi aure babu shakka zan baki ciki na biyu, i don't care" "take him out"

Cewar Abu-turab, Hammad tausayin Abraham ne ya kama shi.

Da ƙyar yake jan numfashi sbd wahala amma bai fasa kallonta ba, har suka isa bakin ƙofa za su fitar da shi idanunsa ya kawo ruwa sai kuma ya yi dry domin ya hango rauni a cikin idanunta kawai bata sani ba ne, da ƙarfi ya ce

"I love you Malumana, I'll be back"


Not editing.

Littafin MIJIN MALAMA na kuɗi ne, kuyi magana a wannan number domin biyan kuɗin 08119237616... Na kusa gama free pages


*Ina Mata 'yan gayu masu son kayan gayu kuzo ga dama ta samu*. _BY JAY_  *ta kawo maku Kayan masu kyau da inganci indai mace tasan  gayu to* _BY JAY_ *ne gurin siyayyar ta.*

We have

*Laces* _(Dubai laces, london laces, Switzerland laces,)_ dan uban su

*Atampha of all kinds*

*Veils*

*shadda*

*shoes*

*qualitative handbags*

*Jewelries* etc

Abun sha’awa ana shine Kayan mu ba a jikin kowa zaku gansu ba dan kaya ne unique na mata yan gayu da suka san kan gayu ku dai kawai ku mana magana ta Wannan no din *09060450181*

Ko kuma ku danna Wannan link din domin samun damar ganin kayan mu


https://chat.whatsapp.com/IBD74Cka3X2E2AqZyg0Nfo

*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv Sarauta

*9......*

Yadda suka ɗaure Abraham a jikin sarƙa zaka ɗauka wani tantirin ɗan fashi ne ko kidnaper, ko irin mutanen nan masu muyagon harƙalloli. Suna zuwa suka cilla shi a mota tare da yiwa motar key.

"Ku daka ta" P.a Hammad ya faɗa yana ƙara sawa inda suke ya dubi Abraham wanda kansa yake sunkuye jini ya ɓata masa fuska.

"Mene matsayina?" Kai tsaye Captain ya ce "Kai P.a ne a wajan His Excellency" Hammad ya jinjina kai ya ce "Good,  kamar matsayin P.a ya fi na mataimakin Gwamna, idan ya tabbata haka ne la shakka zaku bi nawa umarnin" suka kalli juna

cikin kuma rashin fahimta Captain ya ce

"Me kake buƙata?"

Ya ce "Ku kai Abraham gidana, ya zama sirri ni da ku kada ku kuskura akai shi Prison idan ba haka ba, ku ne zaku tabbata a can har ƙarshen rayuwa"

"Cin amana?" "Shi ma ita ya yi" cewar Hammad. Captain ya ce "I can't, dole mu kaisa prison kamar yadda ya umarta"

"Nawa ya baku?"

"Mu ai ma'aikatan gwamnati ne, wannan shi ne aikinmu" Hammad ya yi murmushi mai kyau kafin ya ce "Mu ne Gwamnati ai, baka san inda rana zata faɗi ba gobe" "Kowa ya san ta yamma take faɗuwa" Captain ya tari numfashin Hammad da faɗin hakan.

"Zan baka 10Ms, zan faɗa maka yadda za kayi" ya yi shiru alamar tunani kafin ya ce "Sauran securities ɗin fa?" Hammad ya watsa hannu ya ce "Ɗauke shi, lokacin ya fara" Captain ya dubi abokan aikin nasa, ganin sun yi nesa da su hakan ya tabbatar ba su ji abinda suke tattaunawa ba. Tunaninsa ya rabo gida biyu shin ya amshi kuɗin? Idan ya amsa kuma ya ci amanar Gwamnansa, da ƙasar shi da kuma aikinsa. Amma miliyan Goma ai ba nan ba ce, babu wanda kuma zai sani.

Ya shiga motar, sauran securities ɗin ma haka kai tsaye suka fita daga cikin keɓantaccen gidan na His Excellency Abu-turab.

Hammad ya yi murmushi a fili ya ce "Kaci amnar maci amana kamar babu laifi? Ba zan jure ganin hakan ba, am sorry Best friend"

Abu-turab ya na tsaye da hannunsa wanda aka karya ya dubi Majeederh dake zaune tayi shiru ta sanya hannunta tsakanin cinyoyinta hakan na nufin tunaninta ya girmama har ya kasa ɗaukan ƙwaƙwalwarta. Abu biyu ya fi tsaya mata, kalaman mahaifinta Abbu, da kuma kalmar Abraham "I am the who raped her" hakan na nufin Abraham yaga surarta na ɗiya mace? Ya gama kallonta. Ta rutse idanu tana kiran sunan ALLAH. Yaron cikinta? Ɗan data raina? Ya yi mata Fyaɗe? Ya samar da cikin Khalil, ta ya ya hakan ya faru? Rabonta da shi shekara biyu, shin ciki yana shekara biyu ne? Ya akai har ya yi mata Fyaɗe bata sani ba? Yaushe hakan ta faru.

"Jiddo" Abu-turab ya kirata a ruɗe ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce take shirin yin jijjiga. "Ka da ki sawa kan ki damuwa wani ciwon ya kama ki, don Allah Jiddo listen to me ki bani dama, ki bani dama just one chance, please Jiddo Give me one chance"

Ta ɗago kai a nutse ta faɗaɗa kyakkyawar fuskarta speaking calmly ta ce "Your Excellency"

"Yes, Jiddo"

"Don Allah ka bani waje" ta faɗa murya can ƙasa idanunta na lumshewa.

Ya jinjina kai ya ce

"Zan fita,idan zaki farin ciki" yana faɗin haka ya yi waje yana zuwa wajan ƙofa ya juya ya kalleta sai kawai ya fice yana rufe ƙofar bedroom ɗin. Yana fita ta zame ƙasan lallausan carpet na ɗakin, zuciyarta tayi mata zafi ƙirjinta na ɗagawa sama. Tsoron t ɗaya kada bakin mahaifinta ya kamata ya sanya ta lalace kum ta bi duniya kamar yadda kalamansa suka bayyana haka, mene ya sa ya kasa yarda da ita ya kasa fahimtar ba zata taɓa aikata zina ba, ya kasa amincewa ƙaddara ce ta faɗa mata.

Kuka take son yi ku zuciyarta za tayi mata sanyi amma ta kasa sai ma wani abu daya tsaya mata a ƙasan maƙoshi da ƙyar take jan numfashi. A raunace ta ɗaga kai sama ta ce

"Allah na gode maka, Allah na gode maka da wannan jarrabawa, yadda kayo ni a Musulma mai yadda da ƙaddara Ubangiji ka sanya na cinye wannan ƙaddarar, zuciyata ta kasa jurewa Allah kai kasan abinda yake ɓoye Ubangiji idan rayuwata a wannan duniyar shi ne alheri ka tabbatar dani a raye ka bani haƙurin jure ƙalubalen cikinta, idan mutuwata ita ce hutu a gareni Ya Allah ka ɗauki raina a wannan lokacin, ka yafe mini  kurakuraina ka kula mini da abinda na haifa" Ta rufe idanu tana ƙanƙame jikinta tana jan numfashi da ƙyar ta ce

"Asstagafirullah Ya Allah, Asstagafirullah, Asstagafirullah Ubangiji kana kallo,kana ji, kana gani albarkacin imanin da nayi da kai, albarkacin kare addininka da nayi, Ya Allah ka bani haƙuri kwatankwacin haƙurin da Annabi Luɗ ya yi da mutanensa, ka bani ikon jure yanayin rayuwa kwatankwacin juriyar da Annabi Yusuf ya yi, Allah ka bani ƙarfin zuciya wacce zan fuskanci ko wanne  ƙalubale, kwatankwacin Yadda ka bawa Annabi Sulaiman ƙarfi ikon, Allah ka kula dani kwatankwacin kulawar daka bawa Annabi Musa a cikin gidan Fir'auna... Ya Allah Asstagafirullah!"

Jira take taga ta inda mutuwarta zata fara, amma shiru hakan na nufin rayuwata ita ce alheri a gareta.

Abu-turab na zaune ƙasan carpet ya sanya Mama a gaba hannunsa naɗe da bandeji cikin kulawa ta ce "Abu-turab me ka ke so?"

"Majeederh nake so Mama" ta ce "Nemi Soyayyarta idan ta amince ba zan hana ba"

Ya yi shiru ta ce "Idan baka da abun faɗa jeka, ka sani a gaba" ya kalleta ya ce "Kamar ba zata amince ba" Mama ta dube shi sosai tana duba yanayinsa ta ce

"Idan har baka sanya son zuciya cikin lamarinka ba babu shakka zata amince, ka yarda da kan ka shi ne kawai" tana kallon T.v ta ce

"fight for the truth, fight for your love, idan har ka faɗa mata wahalar daka sha akanta Majeederh zata ji tausayinka, sai dai bana son ta aureka don jin tausayi sai don cewa tana Son ka"

"Tausayi yana zama so"

"Inji ku Hausa ba, babban kuskuren da kuke kenan, gurbin tausayi daban na So daban go and search"

"Mama please ki....,"

Cikin faɗa ta ce "Abu-turab ba zan tilasta ƴar mutane ba, fita ka bani waje" ya miƙe jiki a sanyaye yabar bedroom ɗin, Jidda na nufar inda yake ya daka mata tsawa. Mama ta ce "Na gode Allah tunda ƴarka ce" yarinyar ta fashe da kuka sosai da gudu kuma ta nufi bedroom ɗin Majeederh ta sameta zaune inda take..

"Mami" Majeederh ta zubawa yarinyar idanu sai ta ɗan saki fuska ta ce "Call me Jidda"

"Dady ya ce Mami" Majeederh ta jingina da bed ta kallon yarinyar sosai tayi kama da mahaifinta. Jidda ta ce

"Ina son Daddy, kema kina son shi?" Majeederh shiru ba amsa ta ƙara cewa "Zaki zama Mamina?" Sai a lokacin ta ce "Ai ni Mamin kowa ce come here"

Barrister na zaune looking so worries ya ƙara ramewa ya yi baƙi kamar ba kyakkyawan matashin nan ba mai jini a jika. "Aliyu Meke damunka?" Ya dubi Hajia ya ce "Me kika gani Hajia?" Ta haɗe rai sosai ta ce "Why are you asking my question with a question?"

"Ɗan Najeriya ne fa?" Almustapha ya bada amsa yana hararar Bar Aliyu Sufyan Alhassan. "Lafiya nake" "ƙarya ka ke, na san halinka dole da abinda yake damunka" Aliyu ya rasa me zai ce, ya faɗawa mahaifiyarsa damuwarsa tamkar ya tona sirrin aurensa ne, kuma zata tsani Matarsa Latifa Omar, amma seriously yana cikin damuwa ya mance when last da ya yi mu'amalar aure da Latifa, ya manta rabon da ya ji ƙamshin girkinta kullum abinci da ƙauri ya manta rabon da yag kitso a kanta, ya mance rabon da ya ji kalmar adawo lafiya daga bakinta. Yana buƙatar kasance da matarsa haƙurinsa ya fara gazawa.

Ya riƙe kansa, da mutuncinsa sbd gudun faɗawa halaka, amma irin su Latifa sune suke sanya maza neman mata da aikata zina.

"Ni banga abinda ka rasa a gidanka ba, amma ka sanya wa kanka damuwa akan wata ƴar iska haba Aliyu" Barrister ya kalli Almustapha ya ce

"Mai ɗaki ai shi yasan inda yake masa yoyo, ba zan hana ka aibata Majeederh ba amma ba kowa ake halinsa ba" Almustapha ya kalli Aliyu sai kawai ya miƙe tsaye. A tare suka fice daga cikin gidan nasu, Bar Aliyu ya yi Lodge Road wanda dalilin Majeederh ya kama haya a unhwhaty, shi ma Almustapha ya nufi hanyar gidansa. Maimoon na zaune ita da ƙawarta wacce suke neighbor da ita. "Maimoon kin ji daɗi, Allah ya baki miji wanda yake wada taki da komai na rayuwa" Maimoon tayi dry sosai ta ce "Allah sarki, wallahi bani da matsala da mijina saɓani bai taɓa haɗani da shi ba, yana da haƙuri sauƙin kai, sometimes na fisa rikici ma, gaskiya samun miji kamar Almustapha da wahala, yana da kare hakƙin aure da nasa, kullum cikin kyautatawa iyalansa yake" Maryam tayi murmushi ta ce

"To Allah ya bamu irin taki" "Haba ya bawa ƴan gaba dai, ke kina ɗakin mijinki ai ki ce kawai Allahamdulillah,kin san duk wani kwanciyar hankalin aure shi samun daidaito tsakanin ma'aurata, yarda da juna, haƙuri, tausayi. Ni kam i trust my husband" Shira suka ci gaba da yi. Suna zaune Maimoon ta ji anyi horn ta miƙe da sauri ta ce "To ga ɗan halak nan" Maryam ta ce "A'a zama bai ganni ba, lemme have my way" sukai dry kana sukai sallama.

Maryam na fita compound na gidan Almustapha na fitowa ya dinga kallonta domin bai taɓa ganinta ba. Ya shafa kai lokacin da take cewa "Sannu da zuwa"

"Thank you, can i know you?" Ta ce "Matar maƙocinka ce Habib"

"Oh, you're too beautiful" Mamaki ya kama Maryam sai tayi ɗan murmushi ta ce "Harna kai Matarka Maimoon?" Ya yi murmushi yana kashe mata idanu guda ya ce "Haba waccar Dabbar?" Maryam ta zare ido ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Matarka ka ke kira da Dabba?" Ya watsa hannu ya ce "Yes, Kinga bani number ki please" Number ta bashi ta shige tana Kaɗa masa jiki, ji ya yi kamar ya bi bayanta domin ya tabbatar mijinta baya gari.

Cikin dare Abu-turab na zaune ya samu sanarwar gaggawa an samu motar jami'an tsaron shi a wani gefen hanya, gabaɗaya jami'an sun mutu guda ɗaya ya yi saura Captain shi ma yana gadon asibiti.  Misalin 2 na dare Uncle Isma'il na harabar gidansa yana duba jaridar ranar inda yake ganin cewa Governor yana asibitin Cameron domin duba lafiyar shi, kamar yadda aka samu sanarwar ta bakin mai kula da lafiyarsa. Ji ya yi an tsaya gabansa ya miƙe da sauri da ƙarfi ya ce "Abraham innalillahi,mene ya sameka...


MIJIN MALAMA

Book1 500

Book2 500

Mutum zai iya biyan book1 kafin a fara book2... Idan kuma yana da hali zai iya biyan 1k ɗin bakiɗaya. 08119237616 kuyi magana ta nan.

*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv sarauta

*10...…*


Masu Arewabooks follow my account👇🏾 akwai gift ga wanda suka fi kowa share da comments acan

https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv


Abraham ya zube gaban Uncle Isma'il ya ce "I want to convert to Islam, I want to become a Muslim, how much will I give" Uncle Isma'il da mamaki yake kallon Abraham ɗin, Yaushe ya dawo? Mene ya same shi yaga jikinsa da wannan raunin? Mene ya ja hankalin shi zuwa ga addinin Musulunci duk da sauri irin na mahaifinsa Denial, duk da kasancewar Kakansa Pasto a church ɗin da tafi ko wacce girma.

"Lafiyarka ɗaya? Mene yaja hankalinka zuwa ga Musulunci? Yaushe ka dawo?" Uncle Isma'il ya jerawa Abraham tambayoyin cike da mamakin domin kansa ya riga cushe. Abraham ya kasa cewa komai domin bashi da kalaman da za su iya fahimtar da Uncle halin da yake ciki,

But speaking the truth, he wants to be a complete, pure Muslim. Na gartaccen mutum mai tsafta. Al'amarin daya wakana akan idanunsa sun bashi malam tsoro da tu'ajujji wani abu mai sunun tsoro Abraham bai sani ba. that is the first way he will take to surprise Majeederh.

Uncle ya kalli ko'ina kafin ya tattausa murya ya ce

"Ka bari zuwa gobe sai muyi magana mu shiga ciki" Sai a lokacin cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce "Uncly, Jee"

"Jee?" Uncle Isma'il ya maimaita kenan bai mance da ita ba?

"Abraham Maminka Majeederh bamu san inda take ba, we lost her" Ya faɗa cikin damuwa. Abraham ya ɗago kansa tare da saka hannunsa ya dafa cinyoyin Uncle Isma'il ya ce

"She slapped me, insulted me, said she hates me, babu ni rayuwarta abada" Baki sake Uncle Isma'il ya ce

"Ita Majeederh? Wait a ina ma ka ganta? Mene ya sanya harta mareka?" Ya ɗaga gajiyayyun idanunsa wanda babu ladama ko kaɗan a cikin su ya ce "Tana wajan Governor na garin, his prvt house" Uncle Isma'il ya dinga jinjina kai yana tunanin abinda ya kai Majeederh wajan His Excellency, mutum mai tsananin karamci da tausayin naƙasa da shi Al'ummar shi yana da tabbacin ba zai taɓa cutar da Majeederh ba. Ya duba agogon hannunsa yaga lokacin ya ja, gashi ance ma baya ƙasar yana Cameron. "dare ya riga da ya yi, gashi His Excellency ɗin ma baya ƙasar da nayi masa waya ina so contact nasa kai tsaye ba shamaki"

"Liar, yana nan infact shi ya sa a kai ni prison,  a gabansa Jee ta mareni" Uncle ya yi shiru yana son fahimtar wani abu kafin ya ce "Me kayi mata?" Abraham ya ce

"Wai don na ce ni na bata ciki, am the father of her son, am the one who raped her, na rantse" maganganun Abraham su kayiwa Uncle girma a kunne ya fahimci akwai buƙatar neman Majeederh domin bai taɓa ji Abraham ya yi ƙarya ba, He is a man who stands by his words.

Uncle Isma'il ya ce "Amma me ya sa kayi haka Maminka ce fa?" Ya haɗe rai sosai yana ɓata fuska ya ce "Ni yanzu ban son Mamin, she's my wife to be pls Uncle I need your help, Dadyna baya understanding my feelings, Jee bata duba feelings nawa" ya faɗa cikin damuwa da murya mai rauni.. "Ka aikata babban kuskure acikin tsarin addininmu na Islam, wanda ya sha bamban da naku Addinin na Christianity mabiya Yesu, a tsarin dokokin Muslunci role and regulations ga duk saurayin daya aikata Fyaɗe bulala ake masa, mai aure kuma jefe shi ake, wannan abin ƙazanta ce ma fi muni, ba zan goyi bayan haka ba Abraham, Maminka?"

Uncle ya faɗa rai ɓace. Abraham was just looking into uncle's eye's ya kasa bambance fari da baƙi, yana son fahimtar mene abin kuskure a tarayya da mace? Koda yake shi addinin musulunci ya sha bamban da sauran, komai nasu sai sun kawo hujja, A strong argument.

Ya dubi Uncle a lokacin baka iya gane mai idanun Bad boy ke faɗa sbd launin da suka sauya a taushashe ya ce.

".... I Just gave her i kissed, i Little kissed on her neck, duk abinda ya faru it was a mistake"

"Mistake?" Uncle asked.

"I.... I... I am sorry Uncle"

Was the first time daya bawa wani haƙuri saɓanin Jee, yana mata abu immediately yake cewa "Sorry Malumana"

"Help" "Sai nayi bincike, idan ya tabbata dole ka amshi hukuncin Islama, bi ma'ana bulala, kuma na kafa maka sharuɗa"

"Accepted alrdy"

Uncle ya ce "Tashi muje, zan kira Dr ya duba ka"

Sai a lokacin ƙarfi yazo masa, da ƙyar ya miƙe kansa na juyawa. Cikin gidan shiru kowa ya yi barci Uncle ya nunawa Abraham wani bedroom, ya shiga ya haɗa masa warm water kana ya ɗakko masa wata jallabiya tare da barin bedroom. A daren Uncle ya kira Dr, kana ya kira Uncle Bello akan yana neman sa gobe by 11Am, daga nan ya turawa Abbu message akan umarni yake bashi gobe yazo yana nemansa.

Daga nan zama ya yi tare da buɗe system nasa ya shiga Gmail ya turawa zuwa ga email ɗin Governor Abu-turab Alƙasim na sirri akan yana buƙatar magana tare da full address da muhimmacinsa wajan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan.

Washegari Abraham na zaune watching TV daga shi sai 3gauter da Armless mara nauyi wacce ta haska baƙar fatar jikinsa, gashin kansa sai ya yi kamar an gyara shi yadda ya cukurkuɗe kamar indomie, duk wajan ciwon anyi dressing nasa, idanunsa wanda suke always a haka He is so genius, and so romantic. Kana ganinsa kasan bashi da haƙuri zafin rai da taurin kansa, musamman physquie. Ba komai yake ɗauka ya zuba a brain nasa ba, amma ƙwaƙwalwarsa ta kasa mance ranar, komai ya faru cikin tsautsayi. Unconscious happenings, It is still fresh in his mind, he remembers it every day.

Tsaki ya ja, babu abinda yake so a yanzu kamar barasa ita ce kawai zata ɗauke masa nauyin zuciyarsa.

Jawaad ne ya shiga hannunsa zube cikin Aljihu sai Sona dake bayansa tana cewa "Yaya Jawaad ka fiya ruwa, wallahi ko matarka sai tayi da gaske zata ci kuɗinka, ni mamakin ƴan matan da suke nace maka nake tunda ba komai za su samu ba" Jawaad ya yi murmushi yana zama kusa da Abraham ya ce "Yarinya ai mu akwai kalaman soyayya, mun san ta kan mace da kalma ɗaya take nake sace zuciya, kuɗi kuma ai Abba na zuba miki acct" Sona ta ce "Ni dai ba haka bros kewa sister's na su ba"

"A'a, ba zan goyi bayan ɓarnatar da kuɗi ba, bayan baku san ciwonsa ba" Was abinda ta ce.

"To don Allah ka bani, just 50k" "Yarinya ko ƙwandala, na aure nake haɗawa" Ta kumbura fuska duk abinda suke Abraham na jin su..

"Yaa Abraham kai bani"

Ya buɗe idanunsa ya kalli Sona, kallon ɗaya kafin ya lumshe idanu ya ce

"Nawa?" "50k"

"Done" ta buga tsalle ta ce "Yes, thank you Yaa Abraham" Jawaad ya kalli Abraham sosai ya ce "Ni ma Yaa Abraham ka bani na siyi new car"

Abraham ya watsa masa harara ya ce "Bana ƙarawa mai....."

Ya yi shiru yana zaro idanu alamar bai san ƙarshen karin maganar ba. Jawaad ya buga dariya ya ce "Ba a ƙarawa mai ƙarfi, ƙarfi Anji Hausa fa, wai bayan kayi hijara garin Katsinawa ka je ka koyo mana wasa"

"Mene ga hausa, Sometimes there is difficulty in pronouncing some words"

"Ni dai a bani kuɗin" ya juya ya kalleta ya yi shiru sai kuma ya miƙe yana riƙe kansa he's trying to recovering something, kallonsa suke gabaɗaya ya yi ta zaga ɗakin ya haɗa zufa sosai idanunsa sukai jajir da sauri ya ce

"Joshua" Ya ƙara yin shiru for some seconds kana ya ce "Call this phone" Sona ta ɗauki wayarta ya shiga faɗa cikin sauri in a low voice.

Yana gama faɗa ta danna call, ringing ɗin farko Joshua ya ɗauka yana faɗin.

"Hey, who's on the line?"

Sona ta miƙawa Abraham waya ya amsa tare da sanya handsfree sbd yanayinsa ya fara juyewa, Joshua ya yi ta magana shiru can Abraham ya ce "GANG"

"Bad boy" Joshua ya faɗa miƙewa da sauri yana cewa "Bad boy where are you? Gang team need you"

"Ka haɗa mini Gang team, right now" ya fesar da numfashi cikin murya mai sanyi ya ce "I'll send you a acct number, kayi dropping 500k ciki" daga nan yare suka sauya kana ya kashe wayar ya ce Sona ta tura acct number. Daga nan kuma ya fara losing mind.

Uncle Isma'il ya kalli Abraham ya ce "Go and change your dress, before nan let's talk"

Abraham ya dai kalli Uncle bai fiya gane wasu kalaman ba ya ce.

"Faɗa mini duk abinda ya faru a can gidan His Excellency" ran Abraham ya ɓaci ya ji tamkar yanzu abin ke faruwa in brief ya faɗawa Uncle Isma'il everything. Ya jinjina kai ya ce.

"Ina son ka saurara, ba zanwa Majeederh dole ta so ka kota aureka ba, kuma ina bayan tayi maka hukunci daidai da laifukanka."

"....No please Uncle, I'll die idan ba Malumana"

"Kasan mene matsalarka ta farko, kai ba musulmi ba, ga team na ƴan iska, ga shan barasa, babu halarci a aurenka da Majeederh, amma I'll Adviser you duk da cewa akwai wahala ta samun haɗin kanta, ka zama mutumin ƙwarai kuma ka zauna a gidana har sai lokacin dana amince da gyaruwarka, Kai Kiristan ita Musulma, kuma babbar malama wacce ta girmemaka, ta baka zatarar shekaru goma sha biyar Abraham,ta raineka ta ci kashi da fitsarinka akwai girma, akwai nauyi ko da ace kai Musulmi ne Majeederh nasa izza da kame kai bata ɗaukan raini, babu shakka ko auren akai zata rainaka".

Abraham ya ce "Raini? A sbd ba zan iya bata ciki ba? Ina da ishasshiyar lafiya inma yara 100 zan bata cikin dare ɗaya....,"

"Stop it, what noises ni wan mahaifin Majeederh ka ke faɗawa haka ba kunya? To ɗabi'ata data Majeederh data Addinin musulunci tasha bamban da taku, akwai alkunya tsakanin surukai"

"Mene surukai Uncle?" Shi Abraham bai ɗauka laifi ya yi ba ya kuma kasa gane mene kuskuren shi a cikin maganarsa. Ya suruna cikin raunatacciyar murya ya ce.

"I am sorry, amma mene ya sa zata raina ni wallahi kullum zan iya bata ciki.,,"

"Get out Abraham Denial David, out tunda ba zaka nutsu ba"  "Ka yafe, forgive me please, zan zama Muslunci ka taimaka" Uncle Isma'il ya ce "Mene ya ja ra'ayinka? Bayan iyayenka basa su"

"Shi ne first and simple way da zai mallaka mini Malumana"  Uncle ya girgiza kai ya ce

"Ka fara tsarkake niyyarka, ba a taɓa musulunta sbd wani dalili ko neman yardar wani, ka musulunta sbd ka yarda addinin Musulunci shi ne addinin na gaskiya, ka musulunta sbd ka yarda da Allah da Manzonsa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka yarda da su babu abokin tarayya, ka mance littafin injila ka ɗauki Alqur'ani da hannu bibbiyu"

"Ta zan yarda?" "Ka fara nutsuwa kasan mene ya sa ka ke son Musuluncin yanzu ka je ka shirya, kuma babu kai babu yiwa Majeederh magana, balle uzzura mata ko kai hannu zuwa jikinta yadda ta ce ka barta ta tsaneka to barta, ka ƙaura cewa ganinta, yanzu ne za ka yi faɗa, fight for your love, ka je bata da bazata, bazata ta sabon sauyin da kayi ka zama tsarkake" Abraham ya yi shiru yana tunanin ta ina zai iya all this, ba zai iya haɗa waje da Majeederh ba tare daya taɓa ta ba. Ya miƙe tare da shigewa bedroom.

Babban parlourn a cike yake, Uncle Isma'il, Uncle Bello, Abbu, Mami. Gefe guda kuma Bar Aliyu Sufyan Alhassan ne zaune cikin wani lallausan yadi, Sai Hajia da Papa iyayen Zaki. Daga ɗaya barin Masu garin ne bakiɗaya, Governor Abu-turab Alƙasim da Mama sai Haseenatou wacce ta ƙarasu. Abu-turab cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ɗaukan Idanu take ɗinkin jamper da babbar riga, he was so looking anger na jin meke faruwa. Daga tsakiya Malama Majeederh ce zaune cikin wata blue black ɗin Abaya mai kyau tayi rolling kanta gefen fuskarta a rufe hannunta riƙe da Khalil.

A inda take zaune take jiyo ƙamshin perfume ɗin da har abada ba zata mance ba. Abinda bata sani ba dab da ita Oga Abraham Daniel David ne zaune cikin wani milk ɗin voyel mai manyan zane ana iya hango faffaɗan ƙirjinsa mai ɗauke da zanan tattoo kansa kwance luff yana ƙyalli sai sabga ƙamshin Boadicea The Victorious, idanunsa kafe a kanta babu ko ƙiftawa. Uncle Isma'il ya yi sallama kana yasa aka yi addu'a. Ya gyara zama ya ce.

"Bincike da result ya tabbatar Khalil jinin Abraham ne" a kusan tare Governor Abu-turab da Bar Aliyu suka ce..

"Ƙarya yake ɗana ne" Abraham ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Babu me zarar yi ma Jee ciki kaf cikin ku, I'm lucky ni me sa a ne" duk suka kalli Abraham Abbu kuma ji ya yi kamar ya shaƙe yaron.

"Ba musu za kuyi nan ba, kuna son rusa mini ƴar fahimtar da nayi, His Excellency, Barrister, Abraham na yarda duk kuna son Majeederh, shawara ɗaya zan baku Majeederh ba budurwa ba ce ƙaddara ta faɗa mata" Zaki ya ce "Zan zauna da ita haka"

Uncle ya girgiza kai ya ce "Kuyi faɗa, faɗa na samun soyayyar Majeederh zan ga waye MIJIN MALAMA, zanga mai zarrar sace zuciyarta, Ɗa dai na Abraham ne, ban san ya akayi aka samu cikin ba wanda gabaɗaya yanzu Abraham zai bamu labari anan zamu tabbatar da gaskiyar shi".

"Idan tana da burin dawowa gidana to ta ɗauki shegen yaron nan mai gadon tsiya, wanda ya zo da ƙazanta zuwa gidan marayu, kuma ki zaɓi Abu-turab matsayin mijinki shi ne ya dace dake" lokacin guda Majeederh da Abraham da Aliyu suka kalli Abbu banda Abu-turab daya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya.

"Abbu gidan marayu, ni na haifeshi ina raye kuma zan kai shi gidan marayu?" "Idan kin yarda ni ne ubanki, ni ke da hakƙin zaɓa miki miji" ta runtse Idanunta zuciyarta na bugawa bata san lokacin da ta ce. "Na amince, na amince Abbu albarkar ka nake nema" idanun Abraham kamar za su faɗo. "You're liar, ki auri wani,ni kuma na ci gaba da tarayya dake kina haifar shegu, ba zan barki ki zauna lafiya da wanda kika aura ba" tayi masa banza. Abbu ya kalli Abu-turab ya ce "Idan ka shirya kawo sadaki yanzu a ɗaura auren ka tafi da matarka" Abu-turab ya ce "A shirye nake Abbu" Majeederh na zaune ta ji an ɗagata cak tare da yin sama da ita har jaririn hannunta kafin kowa ya yunƙura Abraham ya yi waje da Majeederh yana zuwa ya saka key ya buɗe ƙofar mota ya cilla Majeederh ciki idanunsa rufe ƙwaƙwalwar taɓin hankalin na motsawa  "Kai Mahaukaci ne?" Ya dubeta yana sunkuyawa dab da ita ya zura mata seat blt ya ɗaurawa kansa. A karo na biyu ta sake cewa "Kai Mahaukaci ne?" Ya buɗe ido ya ce "I don't know, amma yau zan iya bamban cewa ni mahaukaci ne or not? Domin a yau zan ƙara baki wani cikin na kwanta take a karo na biyu, daman wancan i have been drug ban san ya ki ke ba, wannan shi ne aikin hankalina, wanda zan yi na hauka ya fi wannan,zan iya tsayawa tsakiyar titi babbar mota tabi ta kanmu, me, you, and our son duk mu mutu" Majeederh ta runtse Idanunta tasan tabbas zai aikata. Da gudu Bar ya fito Abu-turab na mara masa baya, suna fitowa motar Abraham Daniel David na fice daga cikin gidan da gudu...


End of free pages

In sha Allah a nan na tsaya da free pages mu haɗu a paid grp. Yanzu zamu je asalin labari nan tsakiya ne, book1 shi ne asalin tashin hankalin littafin duk wani abu daya faru a nan ya faru. Book2 anan zamu ji yadda jaruman namu za su yi faɗa akan Majeederh.


Ɗan waye?

Ya akai sai bayan shekara biyu ta haihu?

Dashe akai mata?

Cikin Aljanu ne?

Ko Abraham, ko Abu-turab ko kuma Zakin Hajia? Wa zai ci riba.


Book1 500

Book2 500

Gabaɗaya har mu kammala littafin 1k ne. Zaka iya fara biyan kuɗin book1 kafin mu fara book2.... 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank... Evidence of payment 08119237616. Zamu fara posting as soon as kun kammala payment. THANK YOU💋❤️🥰


Kafin kammalawa Wannan page ɗin gabaɗaya sadaukarwa ne ga HASEENATOU AUTAR MANYA. ELEGANT ONLINE WRITER'S, MIJIN MALAMA GRP 1,2. ALLAH YA SAKA MUKU DA ALHERI☺️🥰.


TALLAH👇🏾

Shin kuna bibiyar littafin *DAUƊAR GORA!* Wanda *HAWA__B__KUMO (REAL-SMASHER)* ke kawo maku? Wai³ this is an emotional story ever,idan ba kya bi maza ki nema ki fara kada ayi babu ke,*DAUƊAR GORA!* Labari ne dake ƙunshe da sarƙaƙiya akan ƙaddarar wata baiwar Allah *AYSHATOU AYATULLAH* wacce tayi fama da matsalar yoyon fitsari at a very young age,she really went through tsananin rayuwa,ƙiyayyar Family'n uba,kowa yana ƙyamar zama da ita,saboda larurar data sameta lokaci ɗaya,ba kuma wai dan haifeta da shi ba,ku nema ku karanta kada ayi babu ku..


*DANƊANO*


       Kallon ƙyama Inna Tabawa matar ƙanin Babanta data kama baki kamar an yi pausing ɗinta ta bita da shi dawani murya take cewa "toh! Yau muke ganin tsiya da wasali.. Ke yanzu da girmanki gotai² sai ki saki fitsari a jikin kayanki? O'ohh! Ikon Allah.. Ni Tabawa na ga abunda ya isheni bai ishi Allah ba" ta riƙe haɓa tana sake jinjina al'amarin,kamar an cillota kuma kamar me jiran ayi da ita,Inna Larai tai wuff ta fito daga ɗaki jin maganganun da Tabawa ke faɗa ta ɗora da faɗin "ai Tabawa in faɗa maki iskanci ne da kuma ganin ta samu masu ɗaure mata,amma babu wani rashin lafiyar dake damun yarinyar nan,samun guri ne kawai.. Allah na tuba yau aka fara yin ciki? Kou a kanta aka fara haihuwa da za'a raina ma mutane hankali ace ta gamu da wani larurar dake hanata riƙe fitsari.. Zallar taɓara ce dai ke damunta,tou kuma kin san abunki da goyon kaka,babu abunda baza tayi ba da sunan larura" hawayen da suka ciko idonta tai saurin sa hannu ta goge,da sauri ta wuce za ta bar gurin,Inna Larai ta kalli yara²n gidan tace "Kaiii! Kui mata ihu kou za ta ji haushi ta dena abunda take,kui mata waƙar me fitsarin kwance ni na saku,duk wanda yayi kuma zan bashi Nera 5-5,manya kuma zan baku 20-20" ihu da tafi suka hau yi,kafin kace me ƙananan yaran gidan sun ɗauko murafen languna da ƙananun gallon suka fara kiɗa. Kamar cikin watan ramadhan lokacin tashe,haka muryoyin yara da manyan gidan masu jin haushinta babu gaira ba dalili suke tashi cikin waƙe suna faɗin "me fitsarin kwance,amalaala! Wace ce? Me fitsarin kwance.. Amalala.. Me fitsarin zaune.. Amalala.. Me fitsarin kwance!" Inna Larai tace "baku kama sunanta ba,ku faɗa ku ɗaga murya kowa yaji,idan tai zuciya gobe ta daina" kamar Inna Larai ta zugasu kuwa suka ci gaba da kiɗa suna waƙa "wace ce? Aya me fitsarin kwance,amalaala! Aya me fitsarin kwance.. Amalala.. Aya me fitsarin zaune.. Amalala.. Aya me fitsarin kwance!!" Ba waƙar da suke yi ne yafi taɓa mata zuciya ba,yanda wasu ciki ke zagayeta har suna kama mata zani suna janta,wasu na dungure mata kai shi ne abunda yafi komai sawa taji ta muzanta a idanun duniya,da wani irin sauri ta durƙushe bakin ƙofar ɗakinta,banda kuka babu abunda take kamar ranta zai fita,bata taɓa jin ta yi loosing hope ba irin yau,zuwa yanzu kam gaba ɗaya rayuwar ma ya fice mata a rai,musamman irin tozarci da wulaƙancin da take kan fuskanta daga danginta,abun yai mata yawan da ciwon zuciya yake neman kamata nan take,daga jiya zuwa yau sosai take cikin barazana/walaƙanci da tsokanarsu,har tunanin fita take kou wani uzuri ya kamata da dole zaisa ta haɗuwa da wani cikin mutanen gidan ba Baba Wada kou su Inna Asama'u ba,wani lokaci har ƙofar ɗakin ake zuwa ai mata ɗan kira...


               #Za ku samu littafin DAUƊAR GORA! Na ɗaya kyauta. For 2 & 3 shi ne na kuɗi akan ₦500,SP 1k,za'a tura kuɗin ta wannan account ɗin 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank,kou a tura zuwa 8165726609-Hauwa Usman Muhammad,Opay digital wallet. Mutanan Nijar/Mali zaku tura dala ɗari,SP jaka ɗaya,ku tura shaidarku zuwa 08165726609. Ku bi zazzafan alƙalamin #REAL-SMASHER domin samun cikakkiyar amsarku game da wannan matsala data taɓo wanda ya zama ruwan dare a ƙauyuka har da birni,labari ne mai cike da fa'idodi wanda sai kun bi za ku fahimci mene ne a cikinsa..

No comments