SAKAYYAH Book 3 PAGE 7

                   By

*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 7*



                   NA



*Aysha Aliyu Garkuwa*



*Masu son Maganin infection da maganin mata, ku marmatso wannan account no in ne naku ta ciki zaku turo ku?in ku 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, Sai ki turo shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER'N na 08069423567. akwai sabbin kaya masu zafi suna nan bisa hanya, ki turo ku?inki a saki cikin lissafi. Kayanen mata masu zafi sadidan daga Chadi akwaisu Garukan daka, gumbunan, Tsumummuka, cida Ciccibi Abodi cida kaza ci da jan nama kwanon ?asaitacciyar mace biyar sirri, furar mata, gumbar madara Gumbar kolli mai ?yallin al'khairi gumbar uku al'khairi, gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, gumbar ri?i, garin ma?i garin mel?amhi garin ilanwaddihi garin mallaka, tsumin ri?i tsumin tsirtai tsumin kinfi budurwa, tsumin ri?i, tsumin ta baje Sabaya, matsin mali?i mai masifar matse mace matsin da?i har ma?iga, mai ?an kare kyau. Kullacar sirri al'ajabu shu'umar Humra, da duk sauran kan ?amshi. Ha?in amarya budurwa ko bazawara ha?in mai jego ko uwar gida, akwaisu Available set ?inmu hawa hawane akwai manya akwai ?ananan, ?anan daga 40k ne 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ?arami ha?ina na karshe sai kuma ha?in kwanon ?asaitacciyar mace shi 7k ne shine ?arshen ha?ina kenan... Manyan set ?in kuma daga 50k 60k 70k 80k 90k 100k ke zaki fa?i ha?in nawa kikeso anyi miki kana kimin bayanin yadda kikeso da matsalarki ni kuwa nasan abinda zan ha?a miki, ina araha kam amman ina hana bashi*




Haka dai yinin ranan Didi suka yini da ita kana suka kwana Asma'u kuwa sai da Dr Jameel ya gama duty inda suka tafi tare da barin Dr Esha.


Washe gari da sassafe Asma'u ta zo hannunta ri?e da wani madaidaicin Basket Dake ?auke da Warmer masu kyau bisa ga duk kan alama abinci ne tayi kana kafadarta ma?ake da waya ta ?ara sa shiga ?akin alamar waya take yi sai kuma tace.

“Eh Ummi gata nan ma yanzu na shigo”.

Ta ?are maganar tare da mi?a wa Khausar wayar kana ta ajiye Basket ?in hannunta tana mai gaida Moddibo dake magana da Dr Jameel.

Khausar kuwa cikin sanyi tace.

“Ummi” 

Cike da kulawa Ummi tace.

“Khausar lafiya dai kike jin jikin ki ba abinda yake Miki ciwo?”.

Kai ta gya?a kamar tana gabanta tare da cewa.

“Ummi ba abinda. Yake min ciwo fa”.

Cikin jin sanyi da tausayinta Ummi tace.

“Toh Allah ya rabaku lafiya ”.

Tana ?an lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.

“Ameen ya Allah Ummu kuyi min addu'a”.

“In sha Allahu muna miki kuma zamu ci gaba daya miki yanzu ma mukayi waya da Momynki tace min yanzun jirginsu zai tashi”.

Juyawa Khausar tayi ta kalli agogon wayanta tare da cewa.

“Yanzu ma ai sun tashi tun da gashi har tara da rabi kuma tara dai-dai ma jirginsu ya tashi”.

Cikin sau?e numfashi Ummi tace.

“Toh Allah ya kawo su lafiya”.

Ameen ta amsa suna cikin waya da Ummi taga kiran Hajja Nana ya shigo ta wayarta cikin sauri ta mi?a wa Asma'u wayarta kana tayi picking nata takai kunnenta atake muryan Hajja Nana ya ratsa kunnenta tana cewa.

“Khausar”.

Ahankali Khausar tace.

“Na'am”.

Cike da so irin na Kaka da Jika Hajja Nana tace.

“Ya jikin naki?”.

Tana ?an lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.

“Da sau?i”.

Cikin sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace.

“Jiya mukayi waya da Momy take cewa baki jin da?iba ma tana kan hanya zata zo”.

Kai ta gya?a tana kallon Asma'u dake cire warmers cikin Basket tace.

“Eh lafiya lau ba abinda ke damuna Hajja Nana amma wai ance Theater za'a min”.

Cikin son kwantar mata da hankali kana da son sama mata nutsuwa tace.

“A'a kada ki damu ki kwantar da hankalinki ai Theater ba abinda yake yi nima in Sha Allahu da izinin Ubangiji zanyi ?o?ari in zo”.

Murmushin tayi cikin jin da?i ta gyara zamanta tare da cewa.

“Allah ya kawo min ke lafiya Allah yasa ki same ni araye”.

Cikin rashin walwala Hajja Nana tace.

“Wani irin magana ne wannan in Sha Allahu ma araye zan sameki kar ki karya min zuciya”.

Murmushi tayi tare da fa?in.

“Toh Allah ya kawo ki lafiya”.

Ameen ya Allah ta amsa kana sukayi sallama.

Kallonta ta mayar kan Moddibo dake ri?e da hannunta cikin rauni yace.

“Kina so ki karya min zuciya ko Minha? wani irin kalma ne kike fa?a haka”.

?aya hannunta ta ?aura akan nasa tare da cewa.

“Bakomai Yah Mu'allim”.

Dr Jameel kuwa kallon Asma'u dake tsaye gefensa yayi wacce tunda ta cire Warmers cikin Basket bata zauna ba yace.

“Toh ki zauna mana”.

Ahankali tace .

“Toh bari in sa mata abinci”.

Idanunsa ya zare tare da cewa.

“Dear wa yace Miki idan za'a yiwa mutum Theater yana cin abinci ai baza taci abinci ba sai bayan an fito da ita”.

Kallonsa Khausar yau cikin langwa?ar da kai tace.

“Kuma wallahi yunwa nake ji Dr”.

Idanunsa akan Asma'u yace.

“Ki ?ara ha?uri in Sha Allahu ana fito dake ba da?ewa zaki samu ki ?anci wani abu”.

Rau-rau tayi da Idanunta tare da fa?in.

“Toh shikenan”.

Bayan zuwan Asma'u ba da?ewa Niyna da Innayi suka iso wanda hakan yasa Didi ta samu ta koma gida tayi wanka ta sake shiryawa.


 12:30pm dai-dai suka fito da niyyar komawa Asibitin wanda kuma yayi dai-dai da Jirginsu Ummu ya kusa sau?a hakan yasa tace da Ibraahim dake driving ya wuce da ita Airport kana sai motar Hadimai dake biye dasu wanda sun kai hu?u motar Ajere-Ajere suke tafiya motar Hadimai ?aya agaba saina su Didi sai kuma sauran ukun abaya ?arfe 1:05pm dai-dai suka shiga cikin airport Akuma dai-dai lokacin jirginsu Momy yayi Landing.


Bayan Fasinjoji sun fiffito Momy ta fito hannunta ri?e da Raudhat yayinda wani yaro daga cikin ma'aikatan wurin ke gabanta da troling su.

A hankali take tafiya tana  ?an jujjuya ido alamar tana neman ta inda zataga fuskantar da ta sani, sai kuma tayi saurin juyawa jin Raudhat na cewa.

“Oyoyo Didi Yah Ibraahim Oyoyo”.

Murmushi Momy tayi kana tace.

“A'a gasu can ma”.

Ibraahim kuwa sunkuyawa yayi tare da bu?ewa Raudhat hannu da gudu tajeta ta rungumesa tare da cewa.

“Ina Addah Khausy?”.

Yana ?an Sharking ?in hannunsa acikin nata yace.

“Addah Khausy na asibiti”.

Cike da zumu?in son ganinta tace.

“Toh mu tafi inganta ina son ganinta ”.

Mi?ewa yayi tana ri?e hannunta yace.

“Toh shikenan ”.

Cikin sassarfa Didi ta rungume Momy tare da cewa.

“Momyn Khausar Barka da zuwa”.

Fuska ?auke da Murmushi Momy tace.

“Barka dai ya mai jikin?”.

Suna tafiya Didi tace.

“A'a Alhamdulillah mai jiki tana can anata hira da ita amma yanzu nan da minti arba'in za'a shiga da ita sai muyi ?o?ari mu tafi asibiti kafin a shiga da ita”.

Momy ta gya?a kai tare da cewa.

“Toh shikenan”.

Daga nan suka shiga motoci Madadin su wuce gida kai tsaye asibiti aka wuce dasu.


Dai-dai lokacin kuma Lalla Khadijah da Rahma ne da Asma'u ke tare da Khausar, cikin kulawa Lalla Khadijah ke kallon Khausar ?in jin yadda tayi mgnar a yunwace.

“Ayyah Rahma kije ki tambayi Dr Jameel, zan iya shan tea ne”.

Cikin kula Rahama tace.

“Ai ?azuma naje Lalla Khausar cewa yayi ki ?an ?ara ha?uri”.

Gyara zama Lalla Khadijah tayi tare da cewa.

“Kiyi ha?uri ko Khausar ba komai zuwa yamma dai zaki samu kici wani abu”.

?an kwa?e fuska tayi tare da kallon Asma'u dake cewa.

“Toh ni bari inje in kira Dr suzo su shiga suyi mata mana ta samu taci abinci”.

Ta ?are maganar tana fita.


Su Momy kuwa da Didi tafe suke suna hirarsu, duk da dai duk karfin hali suke.

Raudat kuwa sai surutu take zubawa Ibraahim.


Acan asibitin kuwa lokacin da Asma'u take ta kira Dr zuwa lokacin 1:30pm yayi, haka yasa suka fara shirya komai, nan da nan suka gama shirya komai da komai na asibiti kasancewar ?arfe 2:00 dai-dai za'a shiga da ita ahankali Dr Eshaa ta shiga ?akin hannunta ri?e da wani riga da hula irin wanda ake sawa idan za'a shiga da mutum ?akin C's mi?a mata rigar tayi tare da cewa.

“Gashi zakisa wannan ?in”.

Kai Khausar ta gya?a tare da kar?a kana ta juya ta kalli Moddibo cike da tarin ?aunarta da kuma tausayinta Moddibo yace.

“Insa Miki ne?”.

Langwa?ar da kanta tayi tana rau-rau da Idanunta tace.

“Nikam tsoro nake ji zuciyata bugawa take Yah Mu'allim”.

Kamota yayi kana ya ruggumota jikinsa cikin wata amintacciyar murya mai cike da jin ?ai da tausayi yace.

“Bakomai Minha, ba abinda zai sameki sai alkhairi kinji ko Minha”.

Ya ?arashe Maganar cikin sanyi haka nan yake jin jikinsa ya mutu kana zuciyarsa na tsinkewa ya rasa mai yake masa da?i a duniya.

Ganin haka yasa Dr Jameel da Dr Eshaa juyawa suka fita Ahankali Asma'u ta yun?ura da niyyar fita da sauri Khausar ta ri?o tsintsiyar hannunta tare da cewa.

“Asmeey ina zaki je?,Ki tsaya mana”.

Cikin rauni da karyewar zuciya Asma'u ta kalleta kana tace.

“Khausar abinda kike fa?a yana tayar min da hankali ance Miki bakomai a Theater Nan Amma sai wasu maganganu kike masu tarwatsa lissafi da hargitsa mana nitsuwa”.

Araunane ta sunkuyar da kanta tare da cewa.

“Toh ya za muyi da abinda Ubangiji ya tsara mana Asma'u”.

Cikin ?arfafa mata gwiwa tace.

“In sha Allahu Alkhairi Ubangiji ya rubuta mana”.

Kallonsu tayi sai kuma tace.

“Hmmm Allah yasa”.

Asanyaye Asma'u tace.

“Ameen”.

Shiru ?akin yayi na wasu mintuna katse shirun Khausar tayi ta hanyar cewa.

“Gashi kuma har yanzu Momyna bata zoba”.

Kallon time Asma'u tayi tare da fa?in.

“Ai zata zo kafin a shiga dake in Sha Allahu yanzu naji Didi na waya da Innayi tana cewa sun taho asibiti”.

Sake jingina bayanta da jikin Moddibo tayi kana tace.

“Allah ya kawo su lafiya ta ganni inganta koda ma na karshene waya sani!?”.

Cikin sauri Moddibo ya sake janyota jikinsa ya rungumeta haka nan yaji wani irin rauni tausayi jin ?ai baisan lokacin da shesh-she?an kuka ke taso masa daga ?asa ba yace.

“Minha meyesa?”.

Kai ta girgiza tare da cewa.

“Bakomai fa Yah Mu'allim”.

Haka yaita rarrashinta tare da kwantar mata da hankali yace.

“Bakomai Minha babu abinda zai sameki sai alkhairi lafiya za'a shiga dake afito dake lafiya”.

?an Murmushi tayi tare da cewa.

“Ameen Yah Mu'allim in Sha Allahu ya Mu'allim na daina damuwa amma ina neman yafiyarka iya tsawon rayuwar da mukayi tare tun daga makaranta har zuwa dana kasance ?ar?ashin Inuwar Aurenka idan akwai abinda nayi maka ka yafe min kayi min aikin gafara”.

Cikin sauri ya sake ?an?ameta ajikinsa kana yace.

“Babu abinda kika yimin Minha.

Ni kuma me zakiyi kin aduniya Ni babu abinda kika yimin kuma koma akwai na yafe miki duniya da kiyama”.

Kanta ta sake mannawa da ?irjinsa tare da cewa.

“Nagode Yah Mu'allim”.

Ahankali Dr Eshaa ta sake turo ?ofar ta shigo tare da kallon Moddibo tace.

“Asa mata rigar yanzu fa sauran minti goma a shiga da ita kunga har 1:50 yayi”.

Kai ya gya?a kana ya cire mata rigar jikinta ya zira mata na asibitin sai kuma ya tsugunna ya zare mata skintied dake jikinta ya cire ya ?aura akan gadon da take kwance ya ri?o hannunta yayin da ?afanta ke sanye cikin wani takalmin roba  mai taushi Ahankali ya kama gashin kanta ya nanna?e kana ya tura acikin hular rigar sai kuma ya sakar mata da lallausan murmushi yace.

“Kin kuwa ga yanda kika yi kyau cikin kayan nan kuwa?”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Hmmm”.

Matsowa jikinta yayi tare da tallafo kanta ya manna da ?irjinsa kana ya mata kiss agoshi yace.

“Kinyi kyau sosai tare dani za'a shiga ayi Theater dake kinji Minha”.

Kai ta gya?a tare da fa?in.

“Toh Yah Mu'allim”.

Yana ?an janta jiki yace.

“Ana Miki Theater za'a cire mana ?an mu kina gani muna hira”.

Saurin kallonsa tayi sai kuma ta zaro idanunta tace.

“Yah Mu'allim wani irin Theater ne ina kallo”.

Yana matsa hannunta acikin nasa yace.

“Kawai za'a Miki alluran kashe zafi ne sai ayi Theater kina ji kina gani muna kuma hirarmu Yah Mu'allim ?inki a kusa dake”.

Cikin sauri ta girgiza masa kai idanunta na tara hawaye tace.

“Um-um nikam bana son wannan Yah Mu'allim a cire min hankalina kawai ayi min Theater”.

Ganin alamar hankalinta ya fara tashi ya sassauta murya tare da cewa.

“Haka kike so?”.

Kai ta gya?a dai-dai lokacin Dr Jameel ya karaso yace.

“Bakyaso amiki kina kallo?Idan kina so na sai a jawo Mirror a sama Anuna Miki kina kallo”.

Da sauri ta runtse idanunta tare da manna kanta a dantsen hannun Moddibo tace.

“Nikam ina tsoro nice zan tsaya har acire ?a ajikina?,Nikam bana so wallahi Dr Jameel kawai dai ayi min alluran da zai cire min hankalina gwara ayi min shi ina bacci in na farfa?o in ganni da yaro na”.

Moddibo na shafa bayanta ya kalli Dr Jameel tare da cewa.

“Ayi mata yanda take so”

Kai Dr Jameel ya Jinjina kana yace.

“Toh shikenan ba matsala haka za'a yi mata”

Fita sukayi dai-dai lokacin kuma su Momy suka shigo cikin sassarfa taje ta rungume Momy.

Momy kuwa cikin sauri ta lumshe Idanunta jin hawaye na tsats-tsafowa cikin sanyi da rauni tace.

“Ubangiji Allah ya rabaku lafiya Khausar Allah yasa ayi aikin nan cikin lafiya akan alkhairi Allah ya fitar dake lafiya ".

Araunane ta kalli Momy tare da fa?in.

“Ameen ya Allah Momy Allah ya amsa kiyita min Addu'a Momyna kiya femin idan akwai abinda na ta?a yi Miki na cutar wa ko ?acin rai”.

Da ?an sauri Momy ta mari kumatunta kadan kana tace.

“Me kikayi min?,Ni babu abinda kika yimin Mamana Ubangiji Allah ya fito miki dashi da sau?i”.

“Ameen ya Allah” ta fa?a tare da sakin Momy jin muryan Raudhat wacce suka shigo da Ibraahim da sauri ta risina ta rungumo Raudat cike da farin cikin ganinta Raudat tace.

“Oyoyo Addah Khausy ”.

Rungumeta Khausar tayi tana Murmushi cike da farin ciki Raudat ta cigaba da cewa.

“Addah Khausy wannan kayan fa”.

Kallon jinkinta tayi sai kuma tace.

“Raudat Theater za'a yimin”.

Cikin rashin fahimta Raudat tace.

“Addah Khausy menene kuma Thearter?”

?an murmushi tayi tare da cewa.

“Abinda aka yiwa Momy lokacin haihuwar ku keda Ramadan”.

Jim tayi sai kuma tace.

“Toh Addah Khausy Allah ya kawo miki sau?i da lafiya”

Cikin sanyi da rauni tace.

“Ameen ya hayyu ya ?ayyum”.

Moddibo kuwa Ahankali ya kamo hannunta ya tsayar da ita sai kuma ya juyo da ita gaban Momy yace.

“Momy ayi mana addu'a Allah ya fito damu lafiya ”.

Ahankali Momy tace.

“Ameen ya Allah Moddibo”.

Ahankali Khausar ta sake janye hannunta ta rungume Momy sai kuma ta rungume Didi Dr Eshaa ce ta ?araso tare da cewa.

“Lokaci yayi fa kizo mu tafi Khausar”.

Cikin sanyi ta kamo hannun Asma'u.

Ita kuwa Asma'u tuni take zubda hawaye hakanne yasa ta kauda kanta gefe tare da ruggumeta.

Ganin hakane yasa Modibbo ya kamo hannun Khausar ?in suka juya suka nufi cikin ?akin.


Anutse Khausar ta juya ta fara tafiya Ahankali tana waiwayen su cikin ?arfin hali Momy tace.

“Mene kike tafiya haka kamar Kazar da ?wai ya fashewa aciki, kiyi maza kishiga ayi Miki minti nawa kin fito hankalin ki kwance Mamana kike tafiya kina san?a”.

Juyawa tayi ta kalli Momy cikin sanyi da langwa?ar da kai tace.

“Momy ba san?a nake bafa yunwa nake ji shiyasa bani da ?arfi”.

Jin haka yasa Moddibo ya sau?e ajiyar zuciya tare da cewa.

“Shikenan toh tunda yunwa kike ji”.

Ya ida maganar tare da tsugunnawa ya ?auke ta cak kamar Baby ya rungumeta.


   Raudat dake kallonsu ne ta sanya dariya kana ta buga tsalle tare da fa?in.

”Iyeeee Addah Khausy kin lale kinji da?in ki Yah Moddibo ya ?aga ki”.

Ibraahim dake bayanta ya matsa kusa da ita tare da ?agata sama kana yace.

“Toh kema kiji da?i an ?aga ki”.

Cike da farin ciki ta ri?a ?yal?yala dariya tana cewa.

“Addah khausy Bye bye sai kin fito”.

Juyawa Khausar tayi ta kalleta kana tace.

“Toh Raudy na”.

Su Momy kuwa shiru kawai sukayi tare da rakasu da ido.


Suna shiga ?akin direct kan gado Moddibo ya kwantar da ita Dr Jameel kuwa gefen kanta ya tsaya yana Murmushi yace.

“Mrs Mouley Ya kike?”.

Idanunta akan Moddibo tace.

“Lafiya”.

Yana kallon Norse biyu dake tsaye gefe hannunsa ri?e da wani ?an tiren silver yace.

“Ina yake Miki ciwo?”.

Baki ta Cunno gaba still idanunta na kan Moddibo tace.

“Nifa babu inda yake min ciwo”.

Murmushi yayi tare da fa?in.

”Masha Allah”.

Sai kuma ya matsa kusa da Dr Eshaa ya mi?a mata alluran yace.

“Gashi kiyi mata”.

Kar?a Dr Eshaa tayi kana tayi mata.

Dr Jameel kam sake matsawa kusa da ita yayi tare da cewa.

“Mrs Mouley me kike ji yanzu?”.

Cikin wani irin yanayi data fara tsintar kanta ta lumshe Idanunta tare da cewa.

“Wani irin bacci mai da?i nake ji Yah Mu'allim ”.

Ta ?are maganar tana sau?e sassayan numfashi.

“Masha Allah”.

Cewar Moddibo yana matsa hannunta cikin nasa.

 Dr Jameel kam Murmushi yayi kana yace.

“Asha bacci lafiya”.

Ahankali tace.

“Toh”.

Sai kuma ta sake lumshe Idanunta tare da bu?e su ta kalli Moddibo sai kuma ta juya ta kalli Dr Jameel Ahankali ta sake kallon Dr Eshaa.

Cikin wani irin murya na magagin bacci tace.

“Dr Eshaa”.

Cike da kulawa tace.

“Na'am Mrs Mouley”.

Cikin yanayin baccin dake fusgar idanunta tace.

“Bacci nake ji”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Toh gaki ga Mijinki akusa dake kiyi bacci”.

?an jujjuya idanunta tayi tare da fa?in.

“Ta ina yake?”.

Da hannu ta nuna mata gefenta kana tace.

“Ba gashinan kusa dake ba”.

?yaf?yafta idanunta dake cike da bacci tayi tace.

“Ina yake ban ganshi ba bacci nake ji”.

Dai-dai lokacin kuma alluran ya gama fara aiki ajikinta ta narke idanunta suka tafi luuuuu.

Moddibo kuwa Ahankali ya ?an sun kuyo kanta tare da fa?in.

“Minha! Minha!! Minha!!!”.

Yi tayi kamar zata bu?e idanunta kuma ta kasa kasancewar alluran ya gama game jikinta ya saki sai kuma ta bu?e idanunta cikin magagin bacci tace.

“Yah Mu'allimmmmm”.

Shikenan kuma sai bacci.

Sake sunkuya kanta yayi tare da cewa.

“Minha”.

Dr Jameel dake kallonsa yace.

“Kai ka daina ma kiranta allura ya fara aiki ajikinta bari muzo mu fara aikin mu”.


Momy kuwa toilet dake cikin ?akin da aka kwantar da Khausar ta shiga tayi alwala kana tayi sallar Azahar kasancewar su Didi already sun idar.

Momy kuwa koda ta idar addu'a ta shiga yiwa Khausar kan Allah ya fito da ita lafiya haka ma su Didi, Innayi, Niyna ke tayi.


Ahankali Moddibo ya juya ya kalli Dr Jameel tare da cewa.

“Wai da kai za'a yi Theater ne?Dr Eshaa baza ta iya bane?”.

Kai Dr Jameel ya jinjina kana yace.

“Zata iya amma dole sai da taimakona”.

Ya ?are maganar yana kallon Norse biyu dake tsaye.

Cikin sanyi Moddibo yace.

“Toh shikenan”.

Ahankali Dr Eshaa ta zuge zip Dake gaban rigar yanda baza aga al'amuran ta ba sai cikinta daya bayyana a fili,

cike da kwarewa suka fara Thearter cikin abinda bazai gaxa minti goma sha biyar zuwa ashirin ba suka cire yaro fari ?all kyakkyawan jariri gwanin ban sha'awa.

 Dr Jameel na ?ago shi ya cilla ihu Yararai-yararain alamar lafiyayyan yaro cikin sauri Dr Eshaa ta mi?a hannu zata kar?e shi sai kuma tayi saurin ja baya tana Murmushi ganin yanda Moddibo ya bu?e rigarsa ya tallafi yaron ya manna shi da jikinsa.

Murmushi Dr Jameel yayi tare da yin ?asa da murya a hankali yace

“Wai kai ma ka zama Likita ne?”.

Cikin matsanancin farin ciki da wani irin azabebben ?aunar yaron daya mamaye ilahirin jikinsa yace.

“Ba dole ba”.

Dariya Dr Jameel yayi tare da fa?in.

“Aikam toh yanzu dai a bawa Likitarmu ta gyarashi tukunna”.

Moddibo na sake ?an?ame shi jikinsa yace.

“Wani gyarawa sai na kaiwa Didi ta ganshi”.

Dr Jameel na saka hanglove acikin wani ?an silver dake ri?e hannun Norse's dake tsaye yace.

“Zaka kaisa amma ka bari agyara shi tukunna”.

Kai Moddibo ya gyada tare da mi?awa Dr Eshaa jaririn ta amsa tare da mi?awa Norse's ?in kar?a sukayi kana suka je suka fara gyara jaririn.

Su kuwa Dr da Dr Eshaa nan take suka cigaba da aiki bayan sun gyara sun gama komai suka sa mata plaster kasancewar ba ?inki bane atake suka ?arasa mata komai kana suka balle wani abu daga jikin gadon ya zama dai-dai yanda suke bu?ata,

 kana Norse's ?insu suka fara tura gadon yayinda ?arin ruwan ke ma?e a hannunta.


Cikin sauri Moddibo ya matso ta gefenta ganin kamar ta bu?e Idanunta sai kuma tayi saurin rufe su Ahankali yabi bayan gadon.

Dr Eshaa kuwa juyawa tayi ta koma bayan Norse's ?in dake gyara jaririn karbansa tayi ta cigaba da gyara shi da kanta...


 Su kuma suna fita kai tsaye wajen Didi da Momy suka  nufa.

Momy, Didi, Innayi, Niyna kuwa cikin sauri suka mike hangosu ta window da sukayi Norse's kuwa dakin hutu suka nufa kafin su shiga ma sun bu?e musu ?ofa kawai shiga sukayi.


Akuma dai-dai lokacin Lalla Khadijah da Rahama suka shigo harabar Asibitin wanda dama sunje sun saukowa Khausar da Baby abin bu?atarsu ne.


Khausar kuwa Ahankali ta sake bu?e idanunta sai kuma tayi sauri ta rufe ganin kamar Mutanen da Kai suke tsaye bada ?afafunsu ba kasancewar har zuwa lokacin alluran bai gama sake taba Ahankali ta sake bu?e idanun tana ?an jujjuya kanta Ahankali.

Cikin wani irin matsanancin ?aunarta da matsayin mai girma da take dashi a zuciyarsa ya matsa daf da ita ya ri?e hannunta cikin wata sanyayyar murya mai cike da aminci da sadaukarwa yace.

“Minha”.

Idanunta ta sake bu?e wa sai kuma ta sake rufe wa.

Norse's ?in kuwa zaman gadon suka gyara kana suka gyara mata ?aurin ruwan dake jikinta kana suka juya suka fita.

Kujeran dake gefenta ta wajen kafafunta Momy ta zauna.

Moddibo kuwa kujeran dake gabanta daf da kanta ya zauna yayin da Asma'u Rahama, Lalla Khadijah suka ?aya gefenta.


Ibraahim kuwa bayan Moddibo yake tsaye 


Niynah da Innayi kuwa zaune suke bisa carpet dake shinfi?e.


Fuskarsu ko wannensu ?auke da matsanancin farin ciki.


Anutse Moddibo ya ?aura hannunsa na hagu akan gashin girarta yana ?an kwantarwa yayin da yake motsa la??ansa yana mata addu'a.

Didi kuwa cikin sauri ta nufi waje jin Dr Eshaa na cewa.

“Didi ga mai gida ya ?ara so”.

Cikin sauri da matsanancin farin ciki Didi ta kar?esa kana tace.

“Masha Allah Fatabarakallahu Fi Ahsanil Khali?in Masha Allah”.

Sai kuma ta rungumesa Momy kam baki ?aya hankalinta na kan ?ar ta.


Da sauri Rahama taje ta kar?i Yaron ta zuba masa idanu tana kallon baiwar kyau da Allah ya zuba masa yaro ?ul?ul dashi fari ?al.

Rungumesa tayi tana cewa.

“Alhamdulilah Alhamdulillah nayi yaro Ni zan ri?a masa wanka ina rainonsa”.

Murmushi duk sukayi kana Innayi ta kar?esa ta kalla tare da mi?awa Lalle Khadijah cikin matsanancin farin ciki take masa addu'oi.

Cikin matsanancin farin ciki Asma'u ta leka fuskar yaron tare da shafa kansa tace.

“Baby ka wahalar mana da Maminka bazan ?auke kaba har sai taci abinci tukunna”.

Dariya suka sanya Kana Niyna ta karbi yaron sai kuma duk suka koma suka zauna akan Lallausan Darduma Asma'u kam gefenta ta koma ta zauna.

Ibraahim ne ya amshi yaron tare da rugumeshi tsam a jiki yace.

“Welcome to the world *Keyan*. “.

Ma'ana King kenan.


Murmushi Didi tayi tare da cewa.

“In sha Allah kuwa”.


Khausar kuwa Ahankali ta motsa la??anta a hankali murya can ?asa tace.

“Yah Salam, Yah Mu'allim”.

Kasancewar da sunansa ta tafi kana kuma bayan sunan Allah data kira  da sunansa ta fara farfa?o wa.

Da sauri ya sunkuya kanta yace.

“Na'am Minha”

Still idanunta na lumshe tace.

“Yah Mu'allim”.

Ahankali ya sake sunkuyar da kansa daf nata har suna sha?an numfashin juna yace.

“Na'am Minha”.

Hannunta ta yun?ura kamar zata ?aga sai kuma taji ta kasa fuska ta narke tare da cewa.

“Yah Mu'allim ka ?aga min hannuna”.

Dai-dai lokacin Dr Jameel ya shigo cikin sauri yace.

“Kada ka ?aga mata hannunta ka bari sai ta ?aga da kanta”

Kallonta Moddibo yayi cike da tausayi sai kuma ya gya?a masa kai yace.

“Ki ?aga hannunki mana Minha ai zaki iya”.

Idanunta ta rufe kana ta sake bu?e su cikin narkewan murya da sanyi tace.

“Yah Mu'allim ta ina kake?”.

Cikin tsira mata idanu yace.

“Gani nan Minha gani kusa dake”.

Rufe idanunta tayi ta bu?e tare da cewa.

“Ina Momy”.

Cikin sauri Momy tace.

“Gani nan Mamana gani nan kusa dake ki kwantar da hankalinki”.

?yaf?yafta idanunta tayi tare da cewa.

“Yah Mu'allim ka zauna daidai mana meyesa kake zaune da kan ka?”.

Da mamaki yace.

“Zaune da kai kuma?”.

Murmushi Dr Jameel ya masa kana ya masa alamar alluran ne bai sake taba har yanzu.

Muskutawa yayi tare da fa?in.

“Toh Minha na gyara”.

Motsa idanunta tayi tare da cewa.

“Toh”.

Sai kuma ta bu?e idanunta ji tayi kamar alluran ya fara saketa ahankali ta ?ago hannunta sai kuma tayi saurin sakewa tace.

“Yah Mu'allim ka tayani in ?aga hannu na mana”.

Kai ya girgiza tare da cewa.

“Ki ?aga da kanki mana”.

Momy kam na zaune gefenta ta tsira mata Idanu.


Didi kuwa wayane ma?ale kunnenta cikin jin da?i da girmamawa tace.

“Alhamdullilah Abokinka, Amininka, Jikanka Kuma Sarki mai Jiran gado ya fito duniya”.

Abualeey dake zaune cikin Fada ya gyara zamansa cike da matsanancin farin ciki yace.

”Masha Allah Alhamdulillah Allah ya raya mana shi bisa Imani”.

Cike da jin da?i tace.

“Ameen”.

Kana ya katse kiran.

Abualeey kuwa cikin jin da?i ya juya ya kalli Waziri, Galadima da sauran fadawa yace.

“Alhamdulillah an cirewa Matar Aleeyu ?a namiji lafiya lau ”.

Cikin sauri da jin da?i Galadima yace.

“Alhamdulillah”.

Waziri kuwa juyawa yayi kana yayi Sujudur Shukur tare da cewa.

“Alhamdulillah abu duk yanda ake fata haka ya tabbata magauta basu sami yanda suke soba”.

Kai Abualeey ya jinjina kana yace.

“Idan munyi sallar la'asar sai muje asibiti Mu duba ta”.

Amsawa sukayi daga nan suka ci-gaba da zaman fada.


Agefen Khausar kuwa zuwa yanzu ?arfin jikinta ya fara dawowa Sai dai har yanzu alluran bai gama saketa ba bisa duk alamu maganar da take Sambatune.

Ahankali ta ?ago hannunta kana ta ?aura kan cikinta ta shafa ?agowa tayi ta kalli Moddibo tare da cewa.

“Yah Mu'allim”.

Kallon hannunta yayi tare da fa?in.

“Na'am Minha”.

Idanunta alumshe tace.

“Ina cikina”.

Juyawa yayi ya kalli Kyakkyawan Jaririn dake hannun Ibraahim yace.

“An cire mana Baby”.

Idanunta ta rufe kana tayi Murmushi tare da cewa.

“Yah Mu'allim”.

Hannunsa ya ?aura kanta tare da fa?in.

“Na'am”

Tana shafa cikin tace.

“Ka ganshi?”.

Kai ya gya?a tare da cewa.

“Eh na ganshi?”

Murmushi tayi kana tace.

“Momy na ta ganshi?”

Kai ta gya?a tare da fa?in.

“Eh”.

Murmushi ta sake yi still tana shafa cikin tace.

“Didi da Asma'u fa su ganshi?”

Kai ya sake gya?a wa tare da cewa.

“Kowa ya ganshi”.

Baki ta tura gaba cike da shagwa?a kamar za tayi kuka fuskanta ta shafa kana yace.

“Minha ya akayi”.

Fuska ta sake narkarwa cikin mayen allurar tace.

“Yanzu shikenan kowa ya rigani ganin ?ana”.

Murmushi yayi kana Didi ma tayi Murmushi Asma'u kam dariya tayi tare da cewa.

“Aikam dai kece karshen kallo duk mun riga ki”.

Baki ta Cunno gaba.

Didi kuwa sake matsawa kusa da ita tayi kana tace.

“Kiyi ha?uri ?iyata In sha Allahu zakiga ?an ki”.

Sake narke fuskarta tayi tare da cewa.

“Hmmmm”.

Sai kuma ta jinjina kanta tare da juya kanta gefe tace.

“Yah Mu'allim”.

Ahankali yace.

“Na'am”.

Lallausan Murmushi ta saki tare da cewa.

“Yah Mu'allim ina sonka”.

Kansa ya sunkuyar ?asa tare da sakin Murmushi kana ya ?ago ya manna mata kiss agoshi.


Ahankali ta cigaba da kiransa.

“Yah Mu'allim! Yah Mu'allim!! Yah Mu'allim!!!”.

Duk kiransa da take yi yana amsawa.

Cikin sanyin murya da shagwa?a ta cigaba da cewa.

“Ina sonka! Ina sonka!!,Ina sonka!!!Yah Mu'allim Kasan ina sonka ko?”.

Dariya Asma'u ta sanya tare da cewa.

“Dan Allah kar ki dame mu ai mun san kina sonshi”.

Ta ?are maganar tare da ciro wayarta tana mata video Khausar kuwa jin abinda Asma'u ta fa?a yasa ta Cunno baki gaba har lau kuma cikin mayen take.


     Moddibo kuwa wani Amintaccen Murmushi mai cike da jin da?i gami da shau?i ya saki Sambatu take yi amma yana masifar jin da?in su.

A?age da kuma shau?i yace.

“Na sani Minha?”.

Sake Cunno baki tayi tace.

“Yah Mu'allim kaima  kana sona?”.

Tafin hannunta ya matsa tare da cewa.

“Ina sonki Minha Ina sonki ina sonki Minha”.

Cike da kunya Didi ta koma kan Darduman ta zauna.

Momy dake zaune gefensu kuwa sunkuyar da kanta ?asa tayi.

Lalla Khadijah Rahama Asma'u Dr Jameel kam Murmushi kawai suke suna sake jaddada ?auna da sha?uwar dake tsakanin su sun lura Moddibo yama mance da suna wajen.

Khausar kuwa cikin Sambatu da azabebben ?aunarsa tace.

“Ina matu?ar ?aunarka Yah Mu'allim tun ina JSS one fa nake sonka kasan kafi duk malaman makarantar mu kyau ko ina ka sani ko?”.

Cikin jin da?in gami da farin ciki yace.

“Uhmmm”.

Cikin narkekkiyar murya tace.

“Da gaske fa kafi duk mazan duniya kyau, sajenka mai kyau, ai kasan ina son sajenka ko Habibeeey”.

Lallausan Murmushin mai cike da farin ciki yayi tare da cewa.

“Yesss na sani”.

Cikin tsokana Ibraahim yace.

“Toh ashe fa tsohuwar soyayyace, ashe nima sai in fara aje saje”.

Murmushi sukayi baki ?aya, Asma'u kuwa gefen Dr Jameel daya ri?o hannunta yaja ta ?an matso still tanayiwa Khausar video.

 

Ita kuwa Khausar Jujjuya kai tayi tare da tura baki sai kuma tace.

“Ina sonka har rainafa, kuma ina tsoron kayi min kishiya bana son rayuwa da kai da kishiya Yah Mu'allim kayi min al?warin baza kayi min kishiya ba, kuma ka ?i kayi min al?wari Yah Mu'allim”.

Gashin girarta ya shafa kana ya kwantar kanta ya sunkuya ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ra?a mata.

“Minha aike ta musamman ce arayuwata koda wata mace takasance kusa dani Babu wata mace da zata kai ki matsayi da daraja akusa dani”.

Idanunta ta bu?e ta kallesa kana cikin wata sanyayyar murya mai cike da shau?i da bege ta ?yaf?yafta idanunta tare da cewa.

“Yah Mu'allim ina son ka”.

Murmushi yayi kana yace.

“Naji”.

Kanta ta juya ?aya gefen tare da cewa.

“Didi?,Didi!!”.

Didi dake gefe  tace.

“Na'am Khausar ”

Baki ta tura kana ta marairaice fuska tare da cewa.

“Didi ki fa?a masa ina son shi Dan Allah kar ya yimin Kishiya”.

Murmushi Didi tayi kana tace.

“Shikenan ?iyata kwantar da hankalinki kin ji”.

Sake tura bakinta tayi tace.

“Ina Momyna?,”.

Kallon Momy Didi tayi tare da cewa.

“Gata nan”.

?an bu?e idanunta tayi tace.

“Momy ki matso ta nan mana”.

Mi?ewa Momy tayi kana ta matsa kusa da kanta ta tsaya jin alamun ta kusa da ita tace.

“Momy”.

Anutse Momy tace.

“Na'am”.

Tana ?an Murmushi tace.

“Momy kinga Babyna?”.

Kai Momy ta gya?a tace.

“Eh”.

Kwanciyanta ta gyara tare da cewa.

“Momy kinga yaro na ko?,Didi tace namiji ne?”.

Kai Momy ta gyada kana tace.

“Eh”.

Murmushi ta saki tare da fa?in.

“Momy dawa yake kama?”.

Murmushi Momy tayi tare da juyawa ta kalli Jaririn dake hannun Niyna kana ta juya ta kalleta tare da cewa.

“Da Ramadan yake kama Khausar”.

Wani Amintaccen Murmushi ta saki mai cike da jin da?i kana tace.

“Alhamdulillah Momy na samu mai kama da Ramadan".

Kai Momy ta jinjina tace.

“Sosai ma”.

Fuskarta ta shafa tare da fa?in.

“Momy Kyakkyawa ne kenan?”.

Ta ?arashe Maganar da alamar tambaya kana da Murmushi afuskarta.

Kai Momy ta gyada tare da cewa.

“Kyakykyawane Mamana ?an ki kamar Balarabe”.

Tana Murmushi tace.

“Ai tunda aka ce da Ramadan yake kama nasan kyakkyawane Momy”.

Sai kuma ta Maida idanunta kan Moddibo tace.

“Yah Mu'allim kaji wai ?an mu da Ramadan yake kama, kyakkyawane ko?”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Kyakykyawa ne yama fiki kyau ai?”.

Baki ta tura gaba tace.

“Ni dai bai fini kyauba”.

Murmushi yayi yace.

“Toh naji bai fiki kyau ba Rigimatu, ki Kwantar da hankalinki”.

Asma'u kam sai dariya suke mata.

Haka ta cigaba da surutu da Sambatu har kusan karfe hu?u zuwa lokacin already alluran ya gama saketa ta dawo hayyacinta.


Kallon Moddibo tayi tare da cewa.

“Yah Mu'allim zan tashi zaune”.

Sumar kansa ya shafa tare da cewa.

“Toh ki taushi ki zauna mana”.

Fuska ta narke tare da cewa.

“Ka tayani”.

Cikin yi mata kallo mai ha?e da zazzafan yanayi yace.

“Toh ki tashi ki zauna mana ai likitoci sun hana in tayaki, ki tashi da kan ki mana”.

Baki ta tura  tayi ta ?orafi misalin 4:15 ta mike ta zauna da kanta kasancewar ta tashi ta zauna da kanta yasa Dr cewa Moddibo ya tallafa mata amaida ta ?aki ta taka da ?afanta.

Da ?afanta ta taka aka canza mata ?aki wanda akwai step agabansu suna komawa ?aki Asma'u ta zauna ta gabanta Moddibo kuma nata bayanta.


Kallon Dr Jameel Asma'u tayi tare da cewa.

“Dr”.

Yana gyara abin karfen gadon yace.

“Na'am my Dear”.

Kai ta langwa?ar tare da fa?in.

“In bata abinci?”

Kai ya dafe kana yayi Murmushi tare da cewa.

“Kai ke dai baki ?aya na lura bama ta ?an mu kike ba ta ?awarki kikeyi”.

Dariya Momy tayi kana tace.

“Da gaskiyar ta wa yake ta ?an ku”.

Murmushi Moddibo yayi tare da fa?in.

“Momy harda kema bata ?an mu kike ba wato ta ita kike ”

Cikin sauri Dr Eshaa tace.

“To ai har kaima bata ?an ka kake ba ta ita kake tunda ka ?auke sa a?aki baka sake ?aukar saba kana ri?e da hannunta yanzu dai lokacin sallar la'asar yayi atafi ayi Sallah.

Zuwa biyar a ?an asa mata abinci.

Cheaps ka?an da tea rabin cup”.


To sukace kana su tafi masallaci, su kuwa matan sukayi salla a nan.


Sai ?arfe biyar dai-dai 

 Asma'u ta ?an sa mata cheabis ?an ka?an sai tea rabin cup, kamar dai yadda sukace mata.


 Bisa jagoranci likitoci ta matsa ta ri?a bata ta?a ci.

Moddibo kuwa kanta ya ri?a shafawa tare da cewa.

“Minha kinga muje muyi alwala muyi sallah na roki Allah ya baki lafiya ya raya mana ?anmu”.

Lallausan murmushi ta sakar masa kana ta gya?a kai shi kuma ya zauna gefe, nan dai ta gama ci, kana ta ?an gyara manta.


Dai-dai lokacin kuma Abualeey suka iso, bisa jagorancin Ibraahim m suka nufi dakinta dai-dai lokacin da suka shiga a kuma dai-dai lokacin Khausar ta fara wani irin....



No comments