Furar Danko Book 2 Page 12

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!

        𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣2️⃣



.........*_LONDON_*


       A kwana a tashi ba wuya wajen UBANGIJI. A ɓangaren Smart komai na tafiya dai-dai da fatansa dama na duk masoyansa. Sosai ya ƙara canjawa a komai na halittar jiki, gogewar fatarsa da sake zamansa tsayayyen namiji ƙyaƙyƙyawan, ƙiba dai kam bai ƙara ba, sai ma canji wajen zama dana abinci da ya saka shi ɗan ramewa kaɗan dan yasha wahala kafin ya saba ci, yanayin ramar tasa sai ya sake fidda masa ƙuruciyarsa. Harma wani zai iya ɗauka shekarun da yake amfani da su a ƙwallon sune nasa na gaskiya. Kamar koyaushe Lulu na nan daram a ransa, sai dai ɗammarar da ya ɗaura akan tattara al'amarinta da duk wani wanda ke kusa da ita ya sashi dakewa tamkar a yanzu babu komai dake gaban nasa sai harkar ƙwallo da ibada da sam baya sakaci da ita. Abu ɗaya ke damunsa a kanta shine duk dauriyarsa a kowane dare kafin barci ya ɗaukesa daren nan mafi daraja daya ratsa a tsakaninsu ya dinga masa kai-kawon kenan, wataran har takan kaisa ga mafarkinta a wannan yanayin har sai ya kaisa ga wanka kafin sallar asuba. Wani lokacin kuwa har mafarkin gasu a tare yake da ciki a jikinta kotana shayarwa. Duk randa yay irin mafarkan nan yakan tsinta kansa a cikin nishaɗi duk da yana ganin abune mai wahala da yuwuwarsa ba lallai ba, bai kuma taɓa hasashen zata iya kasancewa da cikin na a haɗuwarsu ɗaya kacal, dan duk da ƙarfafashi da zuciyarsa da su Ammah keyi baya jin hasashensa zai iya tabbata akan sake kasancewar su inuwa ɗaya da ita balle har a kai ga haihuwa kuma. Dan ya jima da fahimtar Lulu nada taurin kai dana zuciya matuƙa akan abinda take ƙi ko take so....

       A yanzu haka su Smart sun fara wasan da suka kwashe tsahon watanni suna training akai. Wasane da gaba ɗaya ƙasar Unitet Kingdom hankalinsu ke akansa, kasancewar ya shafi kowa-da-kowa. _Smart Mawashi no. 9_ da ya kasance wannan ne wasanshi na farko a cikinsu tun a wasan farko ya fara bada mamaki. Inda ya zama mutum na farko da ya jefa ƙwallo a raga. Ba'a ɗauki dogon lokaci ba ya sake na biyu. Babbar magana kenan, dan kuwa fa a wannan rana gidajen jaridu da na tabijin harma da rediyo da yanar gizo na ƙasar ta UK a duniyar ƙwallo ka-ce-na-ce ake akan wannan sabon yaro na Queen City, dan ya girgiza zukata fiye da tunani. Farin ciki da Coach ɗin su ya shiga tare da Teammate ɗinsa da fans a wannan rana ba'a magana. Shi kansa yana cikin farin ciki mara misali, dan daga ƙwallon farko har ta biyu da ya jefa sai da yay sujida wa UBANGIJI. Bayan gama Home mach da sukaci 3-1 sati mai zuwa suka tafi away mach, a wannan rana ma al'amarin sai godiyar ALLAH, dan ranar ma dai Smart ya zira ƙwallo sau ɗaya duk da dai ansha wahala matuƙa da gumurzu. Tofa, abinfa ya fara zama babban al'amari. Dan al'amarin Smart Mawashi ya fara ratsa zukatan turawan ƙasar England. Wasan link ya cigaba da tafiya fiye da yanda Smart ke fata, dan matuƙa team ɗin nasu na taka rawar gani, saboda sune na ɗaya a tebiri, dan sunada maki kusan talatin da biyu, sun kuma bama team dake bimusu tazarar kusan maki goma sha biyu. Suna taka rawar gani ta yanda a duk randa zasu buga wasa zakaga stadium ɗin ta cika maƙil fiye da kowace rana. Smart ya jefa ƙwallaye goma a wasa goma sha biyu da suka buga, sunci wasa goma, sunyi drow a biyu. Haka dai wasa ya cigaba da tafiya cikin nasarori daban-daban tare da ƙalubale. Ranar da za'a buga wasan daya kasance kamar na dabi ko hammaya tsakaninsu  Model Unitet cika iya cika stadium ɗin tayi. Dan duk wani masoyin ƙwallo na ƙauye dana birni a wannan ƙasa dama maƙwaftan ƙasar sun taru domin ganin wannan wasa na da sabon ɗan wasan dake lokaci da Queen City zata buga da Model Unitet ɗin da kowa yasan akwai hamayya mai ƙarfi tun shekarun baya tsakanin team ɗin guda biyu. Bayan kammala al'adu irin na ƴan wasa su Smart suka shigo cikin fili. Bakinsa ɗauke yake da addu'a kamar kullum, yayinda yake sake jin wani irin karsashi da himmar ganin yanda ya tara masoya a ƙasar daba tashi ba. Wasa ya fara gudana yanda ya kamata, sai dai a mamakin kowa yau Smart sai wani jan jiki yake yi, gashi shine lamba tara da kowa zai iya taɓawa. Kaɗan-kaɗan masoyansa dama na team ɗin sa suka fara ƙananun maganar yau kuwa lafiya?. Shi kansa Coach nasu hankalinsa ya fara tashi ganin yanda Smart ke gara ƙwallon a kasalance, sai dai abin jin daɗin sun tare ko'ina har yanzu suma abokan hamayyar tasu basu zira ƙwallo ko guda ba, sunata dai kai hari. A haka har aka je hutun rabin lokaci babu wanda ya zira ƙwallon. Dabaibaye Smart da tambaya Coach yayi akan ko baida lafiya ne yau. Amma sai yay murmushi ya ce lafiyarsa ƙalau kawai dai a haka wasan yazo. Sake jan hankalinsu Coach yay akan karsu bari suyi wahalar banza bayan nasarorin da suka kwararo a baya, saboda in har suka bari Modal Unitet sukaci galaba a kansu zasu sanyaya gwiwar masoyansu ne, dan shi dai yau bai gane komai ga Smart ba. Tofa wasa ya canja salo, dan ana dawowa kowa ya nuna da zafinsa ya dawo. A mamakin kowa sai akaga Smart ya ware kamar bashi ba. Abinka da rainon gero da masara a tsaye yake kan ƙafafunsa babu jin gajiyawa ko nuna rauni, gara ƙwallo yake a fili da iyakar ƙarfin zuciya dana ƙwanji. Cikin mintuna biyu da dawowa su Smart suka zira ƙwallo ɗaya, sai dai bashine ya zira ba. Wannan zira ƙwallo ya sake saka wasan ɗaukar zafi suma Model Unitet team ɗin suka rama a mintuna goma da dawowa. Tamkar an tsirama Smart allura ne shi da Teammate na shi a wannan gaɓar. Bata kashi ake na gaske kowa nason ganin ya sake nasara da kai ɗan uwansa ƙasa, amma hakan bata samu ba sai a kusan mintuna ukun ƙarshe da za'a tashi cikin amincin ALLAH Smart ya saka ƙwallo a raga. Wani irin ihu stadium ɗin ya ɗauka tamkar garin London zai tsage kasancewar yau wasan na cikin gida ne, dan Model Unitet ɗin suma ƴan nan cikin London City ɗin ne. Sakanni ashirin da huɗu saura Smart ya sake jefa ƙwallo ta biyu uku kenan da ɗaya. Ya arrahaman zokaji yanda stadium ɗin ke girgiza saboda matsanancin ihu da masu kallo suka ɗauka. Yayinda teammate ɗin Smart suka wani irin rungumeshi a tsakkiya bayan ya ɗago daga sujidar daya zube ƙasa ga hawayen farin ciki sun wanke fuskarsa. Dolene yay farin ciki, a cikin mintina ukun ƙarshe saura a tashi kacal da kowa ya gama fidda ransa za'a tashi 1-1 amma ya zira ƙwallo har sau biyu, wannan abun yayi kukan farin cikine tabbas..    

       Wannan itace mafarin nasarar tabbatuwar cikar mafarkin Smart a harkar ƙwallon ƙafa. Dan gaba ɗaya ƙasar England da kafafen yaɗa labarai suka ɗauka. Tako ina ƙasar ta ɗauki zance akan wannan sabon yaro da Queen City ta samo a wannan karon. Wanda daga fara wasan link zuwa yanzu ya zira ƙwallaye ɗai-ɗai har goma sha uku kenan. Wannan nasara bata tsaya a iya ƙasar UK ba, hatta da sauran duniyar ƙwallo ma ta kurɗa a cikin labarai dama masu bibiyar wasanni. Inda masana ƙwallo keta ƙara fashin baƙi akan _Smart Mawashi_. Dan al'amarin ya girgiza mutane da yawa kasancewar wannan shine farkon wasan link daya buga a ƙasar ƙetare bayan na ƙasarsa Nigeria a baya. Coach Abdull-Hameed da takanas ya tafi ƙasar England ganin wannan wasa na su Smart yau saboda yanda yake ta nuna musu fargabar yinsa a dalilin jin labarin su waye Model Unitet ɗin shi da Uncle Yousuf da Ahmad harda hawayensa. Yana jin alfahari da kasancewar Smart rainonsa ne. Yayinda shima Smart kejin alfahari da hakan. Koda sukai waya da Ammah sai kawai ya sakar mata kuka. Ita sai ma abin ya bata dariya. Duk irin kafiya ta Aliyunta da taurin zuciya kaga yana kuka ai wannan al'amari ya kai babba a jerin farin cikin sa ko damuwa. Wannan dai tasan na farin ciki ne. Addu'a ta dinga jera masa daga ita har Abba duk da sudai ba sanin kan abun sukai ba.....

        

       (To nima dai yau nace Smarty ina tayaka murna a madadin Lulu ƙamshin mu, harda ma tafin ban girma🥱👏)



          *_NIGERIA_*



   A yau wayar Smart da Abbah ita ta haskakama matan gidan mi ake ciki, dan Umma na tare da shi ne a sanda Smart ɗin ya kira sa kasancewar itace da girki yau ɗin. Ƙagara tai Abba ya gama wayar jikinta har karkarwa yake ganin numbar da aka kira Abban kuma taji ya ambaci Aliyu ta fara da +44.. yana gamawa cikin rawar harshe ta ce, “Alhaji wai wane Aliyu kuma ka samu da lambar wajen ƙasar nan haka?”.

         Kai tsaye cikin rashin damuwa Abba ya bata amsa da cewar, “Aliyu na ma. Ai yana can ƙasar turawa buga ƙwallo. Yanzu haka ma ya kirani ne yana faɗa min sunci wasan da tun kusan kwana biyar kenan yake faɗin mu tayasu da addu'a akai dan wasan nada ƙalibale sosai. To Alhamdullah sunci kuma shine ya saka kwallon har sau biyu bayan har sun fidda rai ga hakan”.

       “Tofa sabon zance, shi Hydar ɗin ne ya tafi ƙasar Turai ƙwallo amma mu da muke a gidan bamu da labarin hakan? To Alhaji wani sabon makirci ne yazo ake ɓoye mana hakan kamar wasu masu baƙin ciki ko mugun hali ko yaya ne!!?”. A hasale Umma ke magar har idanunta da suka kaɗa jajur na tara ƙwalla. 

    Abbah da sai yanzu ma shi ya tuna cewar babu fa wanda yasan ina Aliyun yake bayan shi da Ammah da Bilkisu ya tsurama Ummah idanu da mamakin ganin yanda take kumfar baki. Sai dai maimakon ya mata masifa kamar yanda ta hayayyaƙo masan sai yay yinƙurin son fahimtar da ita dalilin ɓoyewar tasu cikin hikima. Amma abin mamaki Ummah ta birkice masa cikin ɗaga muryar data jawo hankalin jama'ar gidan gaba ɗaya zuwa sashen Abbah. Tun Umma na jidali da Abba a ɗakinsa har fa ta fito tsakar gida ta maida abin kan Ammah. Nanfa Mama itama ta ara ta yafa jin ba'asi, yayinda samarin gidan da sauran yaransu suma dai maganar tai mugun dukansu. Ammah dake da ga falonta zaune shiru kawai tai tana sauraren jidalin da Umma da Mama keyi, sai aunty Amarya dake basu haƙuri da faɗin ita bataga abin tada jijiyar wuyaba anan, kamata yay a kwantar da hankali aji dalilin su Abban nayin haka dan bazasu ɓoye ba ai da gangan dole suna da dalilinsu. Neman dawowa faɗan yay akan aunty Amarya, suna cewa itama ai munafukar ce, tunda tana naniƙe a jikin Ammah dan ƙwaɗayin ganin ƴaƴanta na auren masu kuɗi dole tace haka. Maybe ma tasan da tafiyar Aliyun amma taja bakinta tai shiru saboda makircinta da munafurci. Aunty Amarya kusan halinsu ɗaya da Ammah, itama bata da faɗa sai in an kaita maƙura, dan haka tai musu shiru da ga farko, sai da taga suna neman keta mata mutunci a gaban yaransu itama ta fara zazzaga musu nata masifan. Nan fa gida ya sake harmutsewa har sai da Abbah ya fito da ga ɗakinsa a fusace.......✍️



       _🥱Shin Hajiya Yahanasu babu rami miya kawo rami ne?._





_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments