Furar Danko Book 2 Page 11

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲








  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣1️⃣




.......Kasancewar Tajuddeen a gidan ranar ya hana Ummita da Lulu sakewa, dan itama dai Ummitan irin mutanen nan ne masu tsantseni akan addini da rayuwa, balle kuma itama ɗin dai tanada tabo irin na Lulu, koma muce ya zarce na lulun tunda ita an riga an keta mata nata mutuncin a sanadin fyaɗen ma harta haifi ɗa sai dai a yanzu babu shi a raye, abin takaicin kuma mijin yayarta data riƙeta ne wanda ta taso tanama kallon tamkar uba ta aikata mata hakan. Sannan tanada matuƙar wayo da lura akan al'amura na rayuwa. Lulu data rufe kanta a ɗaki saboda kasancewar Tajuddeen ɗin tana shiga saman gado ta kwanta tai shiru cikin nazarin abubuwan da suka faru a yayin fitar tasu yanzu. Sai kuma kamar wadda aka tada ta tashi zaune zuwa gaban mirror ta nufa, kanta ta ƙurama ido na tsawon lokaci, kafin takai hanunta ta ɗage rigarta gaba ɗaya ta ƙurama cikinta da ya ɗan turo kaɗan idanu, sai kuma ta kai hannunta saman shi a hankali ta lumshe idanunta hawaye na ciko mata su, ɓul-ɓul taji ya harba tamkar abin shiri, da sauri ta buɗe idonta da hawaye suka cika taf tana kallon saitin daya motsa ɗin, sai kawai ta saki dariya mai haɗe da kuka. Dan abu uku ne ke mata kai-kawon. Wai ita Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi ce ɗauke da ciki na haihuwa, abinda bata taɓa kawowa a jerin tunaninta ba na rayuwa. Duk da kuwa tanada masifar son yara a rayuwarta, amma bata taɓa kwatantasu gareta anan kusa ba ace matsayin ga nata ba a dalilin tsanar maza da tayi a rayuwarta. Sai kuma wata hikima ta UBANGIJI da ikonsa gashi a yau itace aka tabbatarma zata haihu ɗan mutum matsayin mallakinta. (Mallakinku dai ke da ubansa) wata zuciya ta ayyana mata. Idanunta dake a rufe tai saurin sake buɗewa, dan abinda zuciyar tata ta tsikaro mata yay matuƙar dakar ƙirjinta. (Aliyu) ta sake ayyanawa a zuciyarta tare da kaiwa zaune a kujerar mirror ɗin tamkar cikin gajiyawa. Sai kuma a fili kamar wadda aka tunzuro ta furta, “Ai har abada bama zai san da cikin ba balle zuwansa duniya ko rayuwarsa Mtsowww!!” ta miƙe a ɗan hasale. Kokawa ta shiga yi da zuciyarta akan abinda take ta ƙoƙarin sake tsikaro mata game da Smart ɗin. Cikin tsawa-tsawa kamar zararra tace, “Please and Please bana son damuwa a beg”. Ta ƙara jan tsaki ta shige toilet. (Ni sai ma taban dariya sai kace wadda keyi da wani a gabanta😂🤳). 

          A haka Lulu ta ƙarasa wannan yini cikin wani irin yanayi mai wahal fassara a gareta ita kanta. Sai dai jaɗan-kaɗan hannunta na saman cikinta, yayinda zuciyarta ke cigaba da kawo mata al'amari mai nauyi dangane da kakarta da kawunta da sukaso rabata da shi batare da ko sau ɗaya sun taɓa tunkararta da batun tana da ciki ba ko tunanin zata so abinta. A ganinta wannan babban taka hakkin ɗan Adam ne ai, sannan bataga minene dalilinsu na zubar mata ɗin ba. Dole tana son tasan dalilinsu musamman ma Uncle Sulaiman data rasa dalilinsa na shishshigema rayuwarta a yanzu. Tunda a baya ita dai takan ma haɗa watanni bata ganshi ba. Ganin damuwa na neman cinkushe mata rayuwa ga kayan shaye-shaye sun gagareta sha a yanzu balle tasha ta manta damuwarta ya sata tattare tunanin ta ajiye gefe. Sai ma wani ɗan murmushin takaici ko damuwa za'a kirashi data saki, tare da shafa cikin nata a fili tace, “Wato kai saika nuna min daga jinin wanda ka fito ko?, abu na farko daka fara datse rayuwata da shi shine shaye-shaye, to ya isa a tsaya iya nan inba hakaba a sha ranƙwashi dan bana son shishshigi, shima uban naka yasan ba kanwar lasa bace niɗin tunda ban taɓa raga masa ba akan shiga min hanci daya dinga yi” ta duddungure cikin da yatsanta, zafin da taji ya sata ɓata fuska da sake faɗin, “Garama ka biyo halin Ammah dai zan iya fatan haka ba wannan mutumin mai fuska a turɓune ba uwa ta shanu” daga haka ta fito zuwa falo, dan tasan dai Tajuddeen ya wuce ai yanzu. Ilai kuwa Ummita kawai ta samu a falon tana ƙara gyarawa. Cikin ɗan murmushin da ayau ne ta fara yinsa ga Ummitan ta ce, “Ɗazun mun fara magana amma baki ƙarasa bani labari ba”. Ɗan kallonwa Ummita dake murmushi tayi, sai kuma cikin yanayin signal da idanu ta mata nunin tai shiru da bakinta. Sarai Lulu ta fahimta kuwa, dan haka ta waske da cewar, “Yanzu ni kuwa dama labarin ko dai film ɗin zan nema kawai na kalla da idanuna”.

         Murmushi mai ƙayatarwa Ummita tayi tare da jinjina a kaikaice ganin uwar ɗakin nata ta  fahimci abinda take son ta fahimta ɗin cikin sauri, dan haka itama ta fara bata labarin wani Hausa film da take kallo a YouTube kawai. Sai daga baya Ummita ta ajiye mata ƙaramar takarda. Ɗauka Lulu tayi tana dubawa dan cikin littafi ta saka mata yanda ba za'a gane ba. 

        _“Aunty dole fa sai munyi taka tsantsan, dan inaji a jikina an saka mana recorder a cikin gidan nan da take recording duk wani magana da muke iyayi koda bata shafi komai ba, maybe ma harda cctv camara”._

      Lulu ta jima tana kallon takardar da Ummitan ta ajiye tare da shiga dogon nazari akan abinda tace ɗin dama abubuwan dake faruwa. Wanda ya kamata dama tun farko ta nazarcesu a matsayin ta na Lawyer. Sai dai rashin fahimtar dalilan da zata iya hangar abubuwanne kawai yasa bata kai can ɗin ba, da kuma halin rashin lafiyar da take ciki shima. Zaram ta miƙe daga falon zuwa bedroom ɗinta, tamkar wadda akaima allura ta fara kaikawo tare da tsunduma cikin gidauniyar nazari. Komai take bi dalla-dalla, tun daga randa Dada ta ɗakko ta da ga gidanta har zuwa zamanta Abuja na kwana biyar a hannun Hajiya Shuwa batare da Dada ta barta ta nufi gidan Uncle ɗinta Khamil ba. Zuwansu Canada da kai-kawon da Uncle Sulaiman keyi anan ɗin shi da Tajuddeen. Yunkurin zubar mata da ciki da ɗauke mata passport da yayi daga ita har Ummita, bibiyar ta da taga anayi da canja security ɗin ƙofar gidan da akaiyi da bata isa fita ba daga ita har Ummita sai da izinin Dada, amma kuma ai shi Tajuddeen kai tsaye yake zo musu. Maganar da Dr Olivia tayi yau da Dada, zancen Ummita akan recorder da cctv camara da take hasashe. Tsaf Lulu ta haɗe waɗan nan abubuwan waje guda tare da tattara hankalinta a jikinta ta saka rigar lauyanci. Tana zaune a gado pen da book a hannunta tana rubuce-rubuce akan haɗa wancan da wannan ya bata ma'ana Ummita ta shigo ɗakin da sallama ɗauke da kofin kunun gyaɗa da ya zama abincin Lulu. Sai tururi yake da ƙyamshi mai daɗi. Ummita ta ajiye mata saman coffee table da ɗan kaiwa tsugunne a gabansa ta fara tsiyaya mata a ƙaramin kofi. Cikin raɗa-raɗa ta ce, “Aunty karfa ki tada hankalinki akan maganar nan da kikaga na rubuta tunda bawai mun tabbatar bane ba ko gani da idonmu. Amma ina son daga yanzu mu sake taku a gidan nan musamman akan wannan cikin na jikinki. Aunty duk da ban san miye dalilin son zubar da shi da ake ba ina son ki gane muhimmancinsa a gareki kamar yanda kika faɗa a ɗazun. Dan da ace bai kasance mai muhimmanci ba baza'aita kawo masa hari irin haka ba na san salwantar da shi gaba ɗaya. Sannan ina son ki nutsu a matsayinki na lawyer ki fahimci wanene kawunki da ɗansa da manufarsu, dan tabbas a nawa guntun nazarin na fahimci kamarfa suna amfani da Dada ne kawai a wannan al'amarin, kai shi kansa Tajuddeen ɗin kamar uban amfani yake da shi a kanki kawai wlhy”.

       Tunda Ummita ta fara magana Lulu ta zuba mata idanunta ne kawai. Dan gaba ɗaya lissafin Ummitan yazo dai-dai ne da nata. A hankali itama ta furta “Ummita duk ya akai kika san wannan?”. Murmushi Ummita tayi da ya ƙara fidda ƙyawunta da gogewar data sake yi na zama a turai. Cikin nisawa ta ce, “Aunty kenan. A kanki zan iya yin fiye da hakan, dan ke wata madubi ce ta rayuwata data haska min kaina da ga ruɗanin munana zuwa na MACE MUTUM mai daraja”. Hannu takai ta share hawayen da suka sakko mata, sai kuma tai murmushi mai ciwo. “Aunty ki bari zamuyi magana amma ba'a gidan nan ba, sai dai ki yarda aikine tuƙuru a gabammu wlhy, amma bana son muyisa cikin gaggawa in har muna son kuɓuta da ga wannan tarkon cikin ƙoshin lafiya batare da an rasa wani a cikinmu ba.” ta miƙe a hankali ta nufi ƙofa. Da kallo kawai Lulu ta bita cikin wani irin yanayin sake shiga firgici, dan har wata ƴar zufa-zufa ke tsatstsafo mata a goshi. Sai kuma ta lumshe idanunta dai-dai sanda Ummita take ficewa a ɗakin gaba ɗaya ta zame ta kwanta. A karan farko ta saki lallausan murmushi irin wanda ke tabbatar da Lulu ƙamshi ta dawo kenan da ga barcin daya figeta na wucin gadi ba Mawaddat ta yanzu ba mai yawan karaya da yin sanyi. Dan tabbas a yau Ummita ta zame mata tamkar wata fitilar tochlight data haska mata wajen ajiye ƙafa da ɗaukewa, sannan allura mai ƙarfin gaske da ta zaburar da ita tare da wanke mata idanunta da ke lulluɓe a ɗan watannin nan cikin yanayin barci ruɗani. Laulayin cikinnan da daina shan abubuwanta ya so maidata wata sabuwar Mawaddat ba Lulu ƙamshi ba. Idanunta ta sake buɗewa a hankali ta ƙure p.o.p ɗin ɗakin da kallo. A zuciyarta ta ce, (Tabbas Ummita gaskiya kika faɗa, yanzu ba lokacin gaggawa bane ko burin guduwa. Lokacine na cigaba da kwantar da kai matsayin MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI har sai nasan SIRRIN DAKE ƁOYE. Dolene na fara sanin manufar Uncle Sulaiman a kaina tare da tantance Dada kafin a fara wasan) ta saki wata ƴar siririyar dariya da faɗin, “Mutanen nan wato har yanzu baku san wacece ainahin Lulu ƙamshi ba ko? Karku damu saura ƙiris ku sani har ma ku bama wasu labari. Hhhh” ta sake sakin dariya tana kai hannunta saman cikinta da cigaba da faɗin, “Idan na gama da su kaima zan dawo kan naka UBAN, dan ajiyarka da yay anan ta ƙarfin tuwo bai sha a banza ba duk da yamin sakin dana buƙata salin alin”. Wani ɓul-ɓul cikin yayi kamar ɗazun har sai da ta zabura alamar tsorata, sai kuma ta harari cikin da faɗin, “Idan ba kayi ko kikayi ba ai ba'a tabbatar min jinin gadararre bane. Dan haka a nutsu bana son iyayi okay”........✍️


     _(😂Smart ɗanka ko ƴarka sun higa uku, duk tsiyar da ake maka da alama zata dawo kansu yanzu😂. Tofa dangin Smart kuma sai ku shirya MATA bisa kanku, dan akan cikinku zamu huce komai da kukai mana ehe🚴🚴🚴🥱)._




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments