Sakayyah Book 2 Page 2

 

       


  
*GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 2*



 



 





Spbnɗettett. Cikin ɗan sakin fuska Mommy ta miƙe tare da
cewa.



“Wa'alaikum Salam Hajja Nana sannunku da zuwa”.



Hajja Nana na zama aÉ—aya daga cikin kujerun falon tace.



“Yawwa Aysha sannunki”.



Cike da farin ciki Khausar ta miƙe tare da riƙe hannun Dije
kana ta jata suka zauna akan 2sitter.



Murmushi Mommy tayi tare da juyawa ta shiga kichen.



Ta kawo mu abin taɓa,



Fuska ɗauke da murmushi Khausar dake riƙe da hannun Dije ta
juya tare da kallon Hajja  data zuba mata
Ido, cikin sanyi  tace.



“Maraba Hajja Nana ya gida ya Baffa Liman, Baffa Jauro,Baffa
Sadu, Baffa, Garga Yaya Sadik? Duk kowa da kowa dai”.



Harara Hajja Nana ta watsa mata kana tace.



“Sai yanzu kika ganni wacce ta dameki ai gashi tun
shigowarta kika jata jiki, kuke gaisawa idan kin matsu da sanin yanda suke sai
kije ki duba su da kanki”.



Uhum kawai  Khausar ce
tare da loggobar da kai dan har yau bata dawo dai-dai ba cikin sanyi tace.



“Kai wannan tsohuwa ke dai akwai ki da kishi, da mita ina ce
dai yanzu gashi na gaishe ki amaimakon ki amsa shine sai kin cakaleni”.



Riƙe haɓa Hajja Nana tayi tare da maka mata Harara kana
tace.



“Yo ki riÆ™e abinki mana ko wata tsiyar gaisuwar ki zai
min?”.



Ta ida maganar tare da sauƙa ta ɗauki Cup ɗin tea da Mommy
ta zuba mata kana ta kurÉ“a”.



Taɓe baki Khausar tayi tare da cewa.



“Oho dai ai ko bazai miki amfani ba kin nema bare ma amfanin
zai miki”.



 



Mommy da fitowarta daga kichen kenan tayiwa Khausar alamar
tayi shiru kana ta zauna gefen Hajja Nana cike da girmamawa ta gaisheta tare da
tambayar mutane gida.



 



Miƙewa Khausar tayi tare da riƙe hannun Dije tace.



“Zo mushiga ciki”.



Saurin Kallonta Hajja Nana tayi tare da faÉ—in.



“Dawo ki zauna”.



Tsayawa tayi tare da kallon Hajja Nana still hannunta na
riƙe da Dije tace.



“Toh  me kuma zan
miki?”.



Sassauta murya Hajja Nana tayi tare da faÉ—in.



“Ke kam ki dawo ki zauna mana”.



 



Sake hannun Dije tayi tare da tsare Hajja Nana da ido kana
tace.



“To wai mai zan miki zamuje muyi hiranmu irin na Æ´an Uwanta
kema kuyi hiranku mana ko sai dole na zauna ne?”.



Harara Hajja Nana ta maka mata tare da cewa.



“Wato ke dai daga zuwana sai kinsa mun raba hali, ko ba a
isa ace yi kiyiba sai kinyi musu?”.



 



Kallon Khausar Mommy tayi tare da cewa.



“Ke dai ki dawo ki zauna mana koma menene ai zaki ji”.



Kai ta gyaÉ—a tare da janyo hannu Dije suka zauna gefen Mommy
ya zamana Khausar na fuskantar Hajja Nana.



Hajja Nana kuwa zamanta ta gyara tare da fuskantar Mommy
Cike da isa, gadara, taƙama, Iko, kana da Power da take jin tana dashi akan
Khausar da kuma rigima irin ta tsofaffi tace.



“Alhamdilillah mun godewa Allah daya nuna mana lokacin da
Khausar ta gama karatu lafiya”.



Cikin sauri Khausar ta kalleta tare da cewa.



“An gama karatu lafiya ko kuma anfara taka matsayin karatu?
Ko tsakiyar karatu ma naje ne bare akai ga maganar gamawa?”.



Wani kallo Hajja Nana ta watsa mata tare da cewa.



“Karatun Æ™a'ida kam nasan angama shi tunda kinyi haddar
Alkur'ani kin sauÆ™e sannan kinsan, Ahallari, Kinsan  ishmawi, Kinsan Fiqhu, Kinsan Arbauna, Kinsan
Sira da sauransu yanzu wani karatu ya rage miki”.



 



kallonta kawai take sai data gama jerawa kafin tace.



“Karatu kam wanda ya ragene yafi yawa aisharan fage kawai
nayi acikin karatu”.



Harara Hajja Nana ta watsa mata cikin yanayin zafinta tace.



“A'a sannu Al-huda-huda sarkin karatu dole kika ce sharen
fagi kikayi mana, tunda kin samu anbarki kinyi wannan É—in”.



Sake baki Khausar tayi tare tura baki kana tace.



“Ikon Allah dana samu anbarni nayi da mekike nufi kenan, ko
kuma dama kece zaki tsara min abinda zanyi?”.



 



Gyara zama Hajja Nana tayi cikin ƙanƙance Ido tace.



“Ke ko kunya bakya ji dube ki fa duk kin gama girma agida
shekarunki kusan Ashirin ai wannan ma taumaka miki za'ayi dan kin gama tsufa”.



 



BuÉ—e baki Khausar tayi tare da kallon kanta kana ta kalli
Hajja Nana cike da Isa Hajja Nana tace.



“Kalleni da kyau yo Æ™arya na miki, Æ™annen bayanki nawa aka
Aurar wasu da yara bibbiyu wasu kuma É—addaya ke kam wannan wani sai dai yace
bazawara ce ke dan kin gama girma”.



Wani kallo Khausar ta mata tare da cewa.



“A'a Hajja Nana ya isa haka cin fuska dan wlh bazan
juraba.Wanda suka fini dubu nawa ne basuyi Aure ba, sai dai idan A Rugar kune
ake irin wannan Auren, amma nikam yanzu ma nayi Æ™arama da  Aure.



Mommy kuwa kallon Khausar tayi tare da É—aga mata hannu kana
tace.



“Haka naki Khausar kiyi mana shiru”.



 Sunkuyar da kanta
ƙasa tayi batare da ta sake cewa Uffan ba kawai dai tasan in ba ita ke tare
Hajja Nana ba Mommy kam ba abinda zatace tanaji tana gani za'a tauyeta.



 



Hajja Nana Khausar ta nunata da É—an yatsa tace.



“Ki kiyayeni bada ke nake magana ba fitsararriya mara
kunya!”.



Gyara zama Khausar tayi tare da juya mata manyan Idanunta da
kawar da kai gefe.



Murmushi Dije dake gefen Khausar tayi tare  da riÆ™e hannun ta da ido tayi mata alamar ta
daina.



Gyaran murya Hajja Nana tayi tare da cewa.



“Aysha Ni dake nake magana bada Khausar ba, ya batun maganar
da mukayi tunda Allah yasa tagama yanzu, sannan makon daya gabata Baffanta yazo
daga Adamawa aranan daya zo aranan ya koma”.



Sai kuma ta kalli Khausar tare da watsa mata Harara kana ta
maida kallonta kan Mommy dake sauraronta tace.



“Toh dama ace yazo da niyyar kwana zamu Æ™ara so nan, ayi
magana to amma ke me kikace tsakaninta da Aliyu É—an Uwanta!?”.



Ahankali Mommy ta sunkuyar da kanta ƙasa kana tayi shiru
cikin yanayin sanyinta da Kawaici, da mutumtaka da kuma kamala tace.



“Toh Hajja Nana wannan magana duk yanda kuka zantar ai
hakane  Baffanta shine me Aurar da ita,
dan haka duk abinda ya yanke akanta shine dai-dai”.



 



Jinjina kai Hajja Nana tayi tare da tura kallabin kanta kana
ta gyara zamanta cikin jin daÉ—i tace.



“Shima yace min Insha Allah nan da wata É—aya ko sati uku zai
zo idan ya samu sarari zaizo su zanta da Uban goyon yarinyar, shima abashi
mutuncinsa tunda shi ya raineta tun tana da wata wata uku shi yamata komai”.



Kai Mommy ta gyaÉ—a tare da faÉ—in.



“Bakomai duk abinda kuka tsara yayi Idan har Auren Khausar
da É—an Uwanta Al'khairi ne Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa”.



 



Cikin sauri Khausar ta tura bakinta tare da cewa.



“Ni dai bana sonshi kuma ke dai Mommy ayita Addu'ar
alkhairi”.



Wani kallo Mommy ta watsa mata alamar rufe min baki, shiru
Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa Mommy kuwa kallon Hajja Nana tayi
cikin sanyin murya tace.



“Ni dai Allah ya tabbatar da al'khairi idan al'khairi ne
Allah ya tabbatar ya kuma zaɓa musu abinda yafi zama al'khairi atsakanin su.



Gyara zama Hajja Nana tayi kana tace.



“Ammen,Kuma Insha Allahu ma alkhairi ne”.



Kai Mommy ta gyaÉ—a tare da cewa.



“Adduar da mukeyi kenan”.



Miƙewa Khausar tayi tare da riƙe hannun Dije da alamun ɓacin
rai tace.



“Dije mu tafi”.



 



Harara Hajja Nana ta watsa mata tare da sake tura daurin
Kallabinta gaba kana tace.



“Aikuwa wannan magana ya zama dole ki saurareta tunda batu
ne na Aurenki akeyi”.



Cikin ƙankance Ido Khausar tace.



“Nifa bazanyi Aureba ehe 
ke baki da aiki sai ƙaƙale ƙaƙalen magana ina ruwanki da batun
Aurena!?”.



Afusace  ta kalleta
kana tayi Ƙwaffa tare da cewa.



“Aikuwa dan Ubanki nike da ruwa dake kuma dole kiyu Aure”.



 cikin tsirawa Hajja
Nana ido tace.



“Amma dai na faÉ—a miki ki daina zagin mahaifina Aure kuwa
idan Allah ya nufa zanyi amma ba wanda kike cewa ba kam!?”.



Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauke kana tana kallonta bako
ƙyaftawa sai kuma ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.



“To wa kike so ki Aura?”.



Juya ido Khausar tayi tare da cewa.



“Aini nasan wanda zan Aura, kuma dan haka babu ruwanki dani
sai kace ke lokacin da zaki yi Aure zaɓa miki wanda zaki Aura akayi ba ke kika
zaÉ“a da kanki ba!”.



 



Girgiza kai Mommy tayi tare da nunawa Khausar hanya da hannu
alamar tabar wajen ita har ga Allah bata so ma Hajja Nana ta tsaida Khausar a
cikin mgnar ba in bana tsohuwaba taya zata tsaida Khausar bayan tasan yadda
suke da juna.



Tura baki Khausar tayi tare da jan hannun Dije dake murmushi
sam bata gajiya da kallon Dramer Khausar da Hajja Nana.



Khausar da Dije na isa ƙofar Bedroom ɗin zasu shiga Akuma
dai-dai lokacin Asma'u tayi sallama cike da ladabi tsugunna agaban Mommy ta
gaisheta Cike da kulawa Mommy ta amsa tare da tambayarta ya Umminta ta amsa da
tana lafiya.



Kana ahankali ta maida kallonta kan Hajja Nana dake cin
Inabi tace.



“Hajja Nana inayini fatan kunzo lafiya?”.



Kai Hajja Nana ta gyaÉ—a tare da cewa.



“Lafiya lau Alhamdulillah Allah ya miki albarka kar dai ki
riÆ™a É—aukar hallayar wasu Æ™awaye na tsiwa”.



ÆŠan murmushi Asma'u tayi kana cikin sanyi ta gyaÉ—a kanta
Khausar dake tsaye bakin ƙofa ta wani ɓata fuska tare da kawar da kai gefe.



 



Miƙewa Asma'u tayi ta nufi wajensu Khausar suka shiga
Bedroom cikin É—an sakin fuska da sanyi Asma'u tace.



“A Dije sannu da zuwa ya gida ya mutanen Jauro yaya!?”.



Murmushi Dije tayi cikin yanayin sanyin ta tace.



“Duk lafiya lau?”.



Kallon Dije Khausar tayi kana cikin sanyin tace.



“Ayyah Dije yayan Asma'u Malam Jameel Allah ya masa rasuwa
kwanan nan Æ´an Kidnapping suka kashesa!”.



Cike da tausayawa Dije tace.



“Ayyah Ubangiji Allah yajiÆ™an sa da rahma sukuma Allah ya
tona musu asiri”.



Atare Asma'u da Khausar suka amsa da.



“Ameen”.



Asma'u kuwa Idanunta ne suka ciko da ruwan hawaye.



Cikin sanyi Khausar ta dafa kafaÉ—ar ta kana tace.



“Dan Allah Asma'u kiyi haÆ™uri kin sani babu abinda Yah
Jameel ke buƙata awajenmu face addu'a Insha Allah Yah Jameel na cikin rahamar
Allah”.



Jinjina kai Asma'u tayi kana cikin sanyin murya tace.



“Insha Allah muna yi kuma zamu cigaba dayi”.



Miƙewa Asma'u tayi tare da kallon khausar cikin sanyin murya
tace.



“Toni zan tafi”.



Da sauri Khausar ta É—ago kanta cike da kulawa tace.



“Sauri-sauri haka”.



Kai Asma'u ta gyaÉ—a tare da lumshe Idanunta cikin sanyin
murya daya zame mata jiki tace.



“Wallahi gidan Innayi nake son zuwa dama na biyo ne akan
ince muje ki rakani kuma sai na ganki da baƙuwa, shiyasa nayi shiru bance komai
ba”.



Ajiyar zuciya Khausar ta sauke tare da tsira mata ido cikin
fesar da numfashi tace.



“Ayyah wallahi kuwa badan baÆ™uwar ba ai da naje na rakaki
amma lafiya kuwa?”.



 Kai Asma'u ta gyaÉ—a
tana gyaran zaman hijabinta tace.



“Eh Ummi ce ta aikeni wajen Innayi akan Inje wajen.



Yaya Moddibo yau kusan sati kenan bai sake zuwa gidanmu ba
sannan kuma Innayi ma ta kirata tana faÉ—a mata ko cikin gida baya fita”.



Jinjina kai Khausar tayi cike da tausayinsu tace.



“Allah sarki Malam Moddibo dole ya shiga cikin tashin
hankali da alhinin rashin.



 Yah Jameel insha
Allahu jinin Yah Jameel da hakkinmu ba zai taɓa bari wannan mutanen su samu
salama acikin rayuwarsu ba!”.



Kai Asma'u ta gyaɗa cikin sheshsheƙan Kuka tace.



“Tabbas sun cutar da rayuwar mu, cuta mafi muni sun zalunce
mu kana sun É—auke mana duk wani farin ciki da walwalarmu. Yah Jameel shine
Komai namu Yah Jameel shine fitilar dake haska zukatanmu amma dare É—aya suka
rabamu da wannan hasken kuma jigonmu”.



Cikin sanyi da tausayawa Dije tace.



“Asmau'u kiyi haÆ™uri Allah baya zalunci sannan baya bari ayi
zalunci da sannu Ubangiji zai fallasa asirin wanda suka aikata wannan ta'asar
sannan sai sun wulaÆ™anta wulaÆ™anci mai muni insha Allah”.



Cikin sanyi da Khausar da su kaji mutuwar ya dawo musu sabo
suka hada baki wajen cewa.



“Ameen”.



Miƙewa Asma'u tayi tare da faɗi.



“Bari na tafi dan Ummi tayi ta kiran wayarsa baya É—auka
sannan itama Ummi baki daya bata jin daÉ—in jikinta sosai ta dawo tamkar
majinyaciya.



 Khausar  sai kinga gidanmu baki É—aya duniyar bata mana
daÉ—i”.



Cikin sanyin da rarrashi Khausar tace.



“Ayyah Asma'u am haka rayuwa ta gada Ubangiji Allah ya jikan
Yah Jameel da rahma mu kuma Ubangiji yasa mana dangana azuciyarmu sannan mu
cigaba dayi masa addu'a gatan da zamu nuna masa kenan”.



Kai Asma'u ta gyaÉ—a kana tace.



“in sha Allah, na tafi”.



Kai Khausar ta gyaÉ—a sannan ta kalli Dije tace.



“Muje mu rakata”.



Miƙewa Dije tayi sannan suka fita bayan Asma'u ta yiwa Mommy
da Hajja Nana sallama har bakin hanya suka rakata saida ta samu adaidaita ta
hau sannan suka koma.



 



Asma'u na isa gidan direct Sashen Innayi ta nufa zaune ta
hango Innayi kan barandar ta tayi tagumi da hannunta na dama jin anɓude ƙofa
yasa tayi saurin É—aga kanta ganin Asma'u yasa ta saki Ajiyar zuciya.



Cikin sanyi Asma'u ta ƙarasa tare da zama agefenta cikin
sanyin murya tace.



“Innayi”.



Numfashi Innayi ta fesar tare da tsira mata ido cikin alamun
damuwa tace.



“Na'am Asma'u kin zo ya jikin Umminki!?”.



Kanta aƙasa tace.



“Innayi da sauÆ™i Ina Yah Moddibo fa?”.



Ajiyar zuciya me nauyi Innayi taja kafin ta sauƙe cike da
damuwa tace.



“Asma'u bansan wani irin yanayi Moddibo yake Æ™oÆ™arin shiga
ba baki É—aya ya zama wani iri ya dawo tamkar mara lafiya ya zama abin tausayi
koda fitowa bayayi”.



Sai kuma ta runtse Idanunta cike da damuwa kana ta buÉ—e su
tare da cewa.



“Ko abinci idan bana nuna masa É“acin raina ba baya ci banda
ruwan tea Babu abinda yake sha baki É—aya ya sauya duk hankalina ya tashi na
rasa yanda zanyi.



  Gaba daya Æ™asar nan
tafi raina duniyar ta isheni”.



Sunkuyar da kai Asma'u tayi tana jin hawaye na cika kwarmin
Idanunta.



 



Cikin raunin murya Innayi ta kalli Asma'u tare da cewa.



“Na rasa yanda zanyi da Moddibo É—azun nan ma Abban Jameel ya
fita dalilin zuwansa da yayi masa.



 Nasiyya da kwantar
masa da hankali shine ma muka samu É—azun yasha kunu”.



Numfashi mai zafi Asma'u ta fesar tare da kallon Innayi
tace.



“Ummi ma tace tana som ganinsa baki É—aya ta damu da rashin
zuwansa kuma koda ta kira wayarsa baya shiga bare taji muryarsa, Innayi barin
shiga wajensa”.



Kai Innayi ta gyaÉ—a kana tace.



“Shikenan ba matsala muje”.



 



Miƙewa Asma'u tayi tare da nufar Sashen sa Innayi na biye da
ita.



 Innayin ce ta tura
ƙofar falon suka shiga ahankali Idanun Asma'u suka sauƙa akan Moddibo dake
zaune kan 1sitter Ƙirjinsa Rungume da Alkur'ani yayinda idanunsa ke lumshe suna
tsiyayar da hawaye kana dashash-shiyar muryarsa na rera karatun Alkur'ani.



Cikin mutuwar jiki Asma'u ta zauna daga gefen ƙafafunsa
Innayi kuma ta zauna daga saman kujeran.



Ganin yanda hawaye ke fita Shar-shar-shar a idanunsa yasa
Asma'u fashewa da kuka mai gunji hadda sheshsheƙa.



 



Jin sheshsheƙan Kukan Asma'u yasa Moddibo da idanunsa ke
lumshe saurin buɗewa ganin yanda Asma'u ke kuka da sheshsheƙa yasa yayi saurin
sanya tafin hannunsa yashiga goge hawayen dake saman kuncinsa.



Cikin sanyi Innayi ta kallesa tare da cewa.



“Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.



Ahankali ya ɗago kumburarrun Idanun sa da suka jiƙe da
hawaye kana Eyelashes É—insa sun kwanta cikin sanyi ya kalleta.



Innayi kuwa cikin tsaresa da Ido tace.



“Moddibo za kayi fushi da hukuncin Ubangiji ne?”.



Cikin sauri ya girgiza mata kai tare da cewa.



“Astagafirullah³”.



 



Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta tsira masa Ido tace.



“Toh Meyesa Moddibo baka fita, baka cin abinci sannan baka
walwala, kenan fushi kake da Ubangijin daya bamu Jameelu sannan ya É—aukesa!?”.



Kai ya girgiza mata batare da yace Uffan ba!.



Cikin sanyi da rauni Innayi ta zuba masa Ido baki É—aya Garin
Jahar Taraba da maƙasar Nigeria yafi ta ranta, fesar da numfashi kana tace.



“Toh Meyesa sai dai ka É—auki Kur'ani ka rungume kana karatu
kana kuka”.



Cikin wata dashash-shiyar murya me cike da rauni da tashin
hankali yace.



“Innayi mai zan fita nayi acikin garin Gembulan? Innayi da
waye zan fita? Innayi baki É—aya garin nan ya fita raina bana son garin nan na
tsani garin nan garin nan ya fita min araina”.



Sai kuma ya runtse Idanunsa da ƙarfi yayin da jijiyoyin
kansa suka tashi ruɗu ruɗu dasu kana zuciyarsa ta shiga bugawa da masifar ƙarfi
cikin dauriya ya buÉ—e idanunsa da suka yi masifar Ja yace.



“Innayi duk inda na wulga acikin garin Gembulan zanga kamar
J É—ina na akusa dani, shin Innayi taya zan fara fita da waye zanyi yawo da waye
zanje masallaci da waye zanyi dariya da wa zan dawo gida da wa zan zauna inci abinci!?”.



 



Asma'u kuwa kife kanta jikin kushin É—in da yake zaune tayi
tare da fashewa da wani irin kuka tabbas sunyi rashin da baza su sake samun
kwatankwacin saba sannan kuma anzalince su zalinci mai muni da raÉ—aÉ—i.



Jin yanda Asma'u ke kuka kamar ranta zai fita yasa Moddibo
juyawa ya kalleta cikin sanyi da tausayinta yace.



“Asma'u ki daina kuka ki yiwa J addu'a domin shine abinda
yake buÆ™ata atare damu”.



Innayi kuwa kallonsa tayi har zuwa lokacin hawaye na zuba
daga idanunsa ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.



“Toh Moddibo kaima fa kukan kake ya za ayi Asma'u ba zatayi
kuka ba”.



Kallon Innayi yayi tare da lumshe idanunsa wasu hawaye masu
masifar zafi suka zubo masa.



 Anutse ya goge tare
da cewa.



“Innayi idan har bana samu na rungume Kur'ani ina karatu ba
bana samun damar hawaye suna zubo min, sannan aduk lokacin da hawayena ke zuba
inaji kamar ana zare min wani abu mai nauyi ne acikin ƙoƙon raina, shiyasa
nake  rufe kaina ni kaÉ—ai nayi ta kuka”.



 



A tausashe ya kalli Innayi data tsaresa da ido ya cije Lip É—insa
kana yace.



“Innayi idan har banyi kuka ba menene amfanin Idanuna da
hawayena? idan ban zubar dasu arashin J ba J fa Innayi J É—ina”.



Numfashi Innayi ta fesar cikin sanyi tace.



“To ai addu'a zaka yi masa Moddibo”.



Cikin dashash-shiyar muryarsa daya dishe da kuka da tashin
hankali yace.



“Innayi to ai ina masa addu'a”.



 



Asma'u kuwa ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan
hawaye ta kallesa cikin sanyi tace.



“Yah Moddibo Meyesa ka daina zuwa wajen Ummi?.



Baki É—aya hankalinta ya tashi ta dawo kamar mara lafiya?”.



Girgiza kai yayi tare da kallonta kana cikin sanyi yace.



“Asma'u ki cewa Ummi tayi haÆ™uri insha Allah zan zo amma ina
jin wanin irin yanayi ne taya zan kalli al'amarin tayaya zan iya zuwa wajen
Ummi ba tare da J na kusa dani ba?”.



Numfashi mai zafi ya fesar da karfi kana yace.



“Baki É—aya rayuwa tayi min Æ™unci na rasa madafa, komai ya
min duhu acikin duniyar nan na rasa yanda zanyi da kaina baki É—aya na rasa
yanda zan fuskanci al'amarin”.



 



Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da fesar da nunfashi ta
kallesa tare da faÉ—in.



“Ni dai Yah Moddibo mu tafi, idan har baka jeba Ummi na
cikin tashin  hankali da damuwar
rashinka, koda magana da Ummi ba tayi idan ba mun matsa mata ba amma sai ta
zauna shiru ita kadai afalo baki É—aya gidan ya daina yi mana daÉ—i”.



Ahankali Moddibo ya taune Lip É—insa kana yace.



“Insha Allah zan zo ki cewa Ummi tayi haÆ™uri”.



Girgiza kai Asma'u tayi kana tace.



“A'a Yah Moddibo nidai gaskiya Ummi tace sai dai muje tare”.



Gyara zama Innayi tayi tare da fuskantar Moddibo cike da
kulawa tace.



“Toh ka tashi kuje matuÆ™ar kana son farin ciki da kwanciyar
hankalin Ummin ka, kada ka haÉ—a mata ciwo biyu Moddibo kasan rashin ka awajen
Ummi babban matsala ne”.



Cikin sauri Asma'u tace.



“Wallahi kuwa Yah Moddibo baki daya Æ™uncin ya mana yawa, ba
kai babu Yah Jameel. Baki É—aya zuciyarmu acunkushe yake da damuwa amma ganinka
zai É—ebe mana kewa”.



Cikin sanyi da rarrashi Innayi tace.



“Ka daure kaje ko hankalinsu zai kwanta kuma kaima za kaji
sauki  acikin ranka”.



Ta ida Maganar tare da miƙa masa key tsohuwar motar data
fara saya mishi.



Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da karɓa kana ya miƙe cikin
sanyi ya Murɗa handle din ƙofar



tare da fitowa wajen, cikin sauri ya lumshe idanunsa rabonsa
da ganin haske irin haka ko kuma ya taka kofar falon yau tsawon kwana biyar kenan
ko da sallah agida yake baya fita jam'i kai tsaye inda Motarsa yake ya nufa ya
shiga sannan yaja  suka tafi.



 



Innayi kuwa na ganin tafiyarsu ta kira Number Malam ArÉ—o
bayan ya É—aga tace.



“Dan Allah Malam ArÉ—o idan babu damuwa kazo ina da magana da
kai”.



Kai ya gyaÉ—a kana yace.



“Toh badamuwa Insha Allah zan zo”.



 



Modibbo kuwa suna isa memory sa ya shiga tariyo masa hoton
fuskar J É—in sa cikin sauri ya juya gefen damansa jin kamar sautin murya J É—insa
cikin dariya yana cewa A.J tsayuwar me kakeyi Please kazo mu shiga inga Ummina
kasan dai nayi missing dinta da yawa.



 afili ya furta.



“J kai ko nima ainayi kewarta kuma dan na tsaya jiranka ne
da tuni na taho”.



Murmushi yaga M Jameel ya sakar masa sannan ya janye
hannunsa daga cikin nasa ya juya ya fara tafiya yana jujjuya masa hannu alamar
Byebye.



Da sauri Moddibo ya juya tare da cewa.



“J ina kuma zaka je ba kace ka matsu kaga Ummi ba?”.



Cikin sauri Asma'u dake Kallonsa ta tashare hawayen dake
kwaranya a Idanunta kana tace.



“Yah Moddibo Yah Jameel fa baya nan sannan bazai taÉ“a zuwa
inda muke ba”.



 



Moddibo kuwa ido ya tsirawa Asma'u kamar mai son fahimtar
abinda take faÉ—a sai kuma yayi saurin dafe kansa tare da maimaita Kalmar
Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n shi kansa yasan zuwa zuwa yanzu dai kamar
zautacce yake.



Numfashin ya fesar sannan ya nufi falon bakinsa É—auke da
Sallama Asma'u na biye dashi.



Ahankali idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan
3sitter ta daura guiwar hannunta duka biyu akan cinyarta tayi tagumi tare ta
tsirawa waje É—aya Ido baki É—aya ta rame fuskarta yayi fayau.



Cikin sauri Moddibo ya ƙarasa shiga falon tare da zama
agefenta kana ya janye tagumin da tayi ya maida hannunta kan gwiwoyinta.



 



Ummi kuwa cikin sauri ta sunkuyar da kanta nan take hawaye
suka fara zuba Shar-shar-shar cikin sanyin murya ya kalleta kana yace.



“Ummi dan Allah kiyafemin. Insha Allahu bazan sake nesa dake
ba, kinji Ummina ki daina zubar da hawayenki, dan baza mu iya juran. Kallon
hawayen ki na zuba ba”.



Kallonsa Ummi tayi cikin wata raunan'niyar murya tace.



“Babana idan har baka zuwa wajena ya zanyi?Kana so ka haÉ—a
min zafi biyu alokaci É—aya ne?



Babu Jameeluna sannan kaima baka kusa dani mekake tunanin
zanji arayuwata, kana so inshiga wani hali ne?”.



Cikin sauri ya girgiza mata kai kana muryarsa na rawa yace.



“Insha Allahu bazan sake nesa da keba,  zan kasance atare daku tamkar yanda J ke
kasancewa atare daku, zan sanya ku farin ciki tamkar yanda J É—ina ke saku insha
Allah zan kiyaye”.



Ya kalli Ummi da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a Idanunta
ya É—aura tafin hannunsa akan nata cikin rawan murya yace.



“Insha Allah zan zame muku farin ciki kuma Garkuwa kamar
yanda J É—ina ya kasance agareku Ummi. Asma'u Bashir Insha Allah bazan bari
hawayenku ya zuba ba tamkar yanda J ɗina baya bari su zubo ba nayi al'ƙawarin
zan zame muku farin ciki zan maye muku gurbin J É—ina”.



Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka kasa rarrashin sa
Ummi tayi kawai itama hawaye ya cigaba da zuba daga idanunta haka Asma'u da
Bashir suka riƙa kuka harda sheshsheƙa baki daya Moddibo baya jin zai iya hana
kansa kuka bare kuma ya samu kuzarin rarrashinsu hakan yasa aka rasa wanda zai
rarrashi wani acikinsu.



 



Malam Ahmad da dawowansa kenan ya zuba musu ido cike da
tausayinsu ganin yanda suke kukan kasan daga ainihin zuciyarsu yake fitowa.



Cikin sanyi malam Ahmad ya zauna gefen Ummi ya zamana yana
fuskantar Moddibo, Asma'u da Bashir dake ƙasa cike da tausayawa da kuma rinƙa
rarrashisu da basu baki.



 



Ahankali Ummi ta maida bayanta da jikin kushin É—in ta
jingina hawaye na cigaba da zubo mata Moddibo kuwa kasa yayi da kansa yana jin
wani irin yanayi azuciyarsa shikenan J ya tafi ya barsa bari na har abada.



Kallonsu Malam Ahmad yayi kana ya cigaba da cewa.



“Insha Allahu da yardan Ubangiji Jameelu yana cikin rahama,
salama nutsuwa da kwanciyar hankali domin Jameelu ya kasance bawa mai tsananin
Biyayya ga dokokin ubangiji sannan Jameelu yaro ne me biyayya ga Iyayensa
akullum burinsa yaga ya sanya Iyayensa da shalinsa acikin farin ciki”.



 



Jinjina kai sukayi Atare cike da gamsuwa da maganarsa tabbas
ta ko wanni fanni Jameel bashi da makusa.



Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe kana yace.



“Jameel ya kasance mutum mai tsananin tausayi da temakon
al'umma Jameel baya taɓa kallon mutum acikin halin neman temako sannan ya wuce
batare daya temakesa ba, duk wanda yasan Jameel da addu'a yake binsa na
Ubangiji ya jiƙansa dama mutane masu Kirki da karamci Ubangiji bai fiye barinsu
tagayyaraba sam Jameelu bai cancanci kuka agare kuba, addu'a ya cancanci ku
masa domin da izinin Ubangiji yana can cikin rahmar Allah da yardan sa”.



 



Kai Bashir ya gyaÉ—a tare da share hawayen saman fuskarsa
kana cikin sauri yace.



“Hakane ma Abba abinda kake faÉ—a yanzu shine abinda.



 Yah Jameel ya faÉ—a
min acikin Mafarkina jiya da daddare yace. in faÉ—awa Ummi ta daina yi masa kuka
domin duniyar da yake ayanzu tafi wannan duniyar da muke ciki daÉ—i, nutsuwa,
salama, da kuma aminci”.



Cikin sharce hawaye ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi
kana yace.



“Sannan yace bayason wannan kukan da Ummi ke masa, shikam
addu'a yake buÆ™ata duk wannan koke koken bayaso adaina yi masa.”



Kallonsa ya mayar kan Moddibo tare da cewa.



“Sannan kaima Yah Moddibo acikin mafarkin da nayi da Yah
Jameel yace in Faɗa maka ka cigaba da yimasa addu'a sannan kayi ƙoƙari ka cika
masa wasiyyar da yayi maka ta gefen Innayi ya jadda min kuma ka taya Abbansa
kula da lamuran kasuwancinsa”.



Saurin É—ago kai Moddibo yayi tare da cewa.



“Ummi wani wasiyya kuma J É—ina ya bari akaina??”.



Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da matsanancin kuka
batare da tace Uffan ba.



 



Ajiyar zuciya Malam Ahmad ya sauƙe tare da kallon Ummi dake
sheshsheƙa kana yace.



“Fatima yanzu kuka za kiyiwa Jameelu? shin kinsan Rahman da
Ubangiji ya tanadar wa da duk wa'anda aka zalunta da rabasu da rayuwarsu?



Kada fa ki manta Ubangiji ya tana dar da rahma wa duk
rayukan da aka kashe batare da hakkinsa ba”.



 



Ahankali Ummi ta É—ago kanta kana ta sanya tafin hannunta ta
share hawayen ta Numfashi malam Ahmad ya fesar kana yace.



“ki tuna ni'imomin da Allah yayiwa muminai tanadin su.”



Lokaci É—aya Ummi ta saki murmushi wanda tun bayan sace M
Jameel ba tayi irinsa ba wani irin nutsuwa da salama taji yashigeta lokaci É—aya
tabbas tana ji ajikinta Jameelun ta na cikin rahmar Ubangiji.



 



Moddibo ma murmushi yayi wanda ya fito daga ainihin
zuciyarsa in sha Allah J dinsa yana cikin kwanciyar hankali da salama da izinin
Ubangiji addu'a kawai J dinsa ke buƙata atare dashi Insha Allah kuwa zai cigaba
da masa hakan yasa suka cigaba da hirar rahmar da M Jameel zai kasance da
izinin Ubangiji cikin sakin fuska suka cigaba da hira.



 



Acan gidan Lamiɗo kuwa ƙarfe biyar dai-dai Hajja Nana ta
mike tare da kallon Dije dake zaune gefen Khausar suna hira tace.



“Ke Dije tashi mu tafi”.



Kai Dije ta gyaɗa tare da miƙewa cike da girmamawa Mommy ta
haɗa mata tsaraba sannan ta bawa Khausar ta riƙe suka fito.



Suna fita coumpund É—in Hajja Nana ta kalli Khausar tare da
cewa.



“Insha Allah idan Baffa Jimeta yazo zamu zo tare”.



Ko uffan Khausar bata ce da ita ba haka zalika Mommy, bayan
Khausar sun koma falon ta kalli Mommy cikin sanyin murya tace.



“Mommy yanzu dan Allah biye mata zakiyi?”.



Ahankali Mommy ta zauna tare da kallon Khausar cikin sanyi
tace.



“Yanzu Khausar idan ban biye mataba wa kika tsayar?  sannan tsohuwar nan tunda ta rantse akan dole
sai anmiki aure tofa babu makawa, sannan babu yanda zanyi dole sai an Aurar
dake ke dai kiyi fatan Allah ya miki zaɓin alkhairi, sannan ya baki mijin da
zai barki ki cigaba da karatunki ki kuma cika burin ki”.



Wani abu mai masifar É—aci Khausar ta haÉ—iye cikin raunin
murya tace.



“Mommy nifa Banason sa”.



Kallonta Mommy tayi kana cikin tsareta da ido tace.



“To idan bakya sonsa wakike dashi ko kuma wa kika tsayar
babu wani saurayi dake zuwa wajenki Naseer da ake maganar sa yanzu ya fita
sabgarki kuma hakama yafi min.



 Ni yanzu abinda na
fahimta ma kamar soyayya suke da Amina”.



Khausar kuwa kallon Mommy tayi tare da tura baki kana tace.



“Eh Mommy soyayya suke to amma.



Ni me ruwana dasu ni dai bazan Auri Yah Aliyu ba Naseer kuwa
bana sauraron maganarsa bare insa shi araina”.



 



Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da gyara zaman ta cikin
sanyin murya tace.



“Toh Allah ya mana zaÉ“in alkhairi”.



ta faɗa tare da miƙewa tashiga Bedroom ɗin ta Khausar kuwa
jingina bayanta da jikin kushin tayi tare da lumshe Idanunta.



 



Da yammaci Misalin ƙarfe biyar da rabi Hajiya Bunayya da
Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar'uzu.



Cikin farin ciki Hajiya Lami ta gyara zamanta tare da kallon
Boka Kar'uzu dake taune laɓɓansa na ƙasa duk yayi muni ba kyan gani cikin
sassauta murya tace.



“Na gaishe ka Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban
La'anannu ina mai farin cikin sanar da kai shekaran jiya Alhj ya tafi Saudia
kaga yanzu sai ka shirya ka koma gidana kaje kayi sati ba matsala”.



Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya fashe dashi wanda
yasa ganyen bishiyar dake wajen suka soma zubowa yana mai ƙara wangale
wawakeken bakinsa yace.



“Anjima da daddare zanzo, maza ku tashi ku tafi da Æ™afar
hagu yanzu zanyi manyan baƙi da kukar bulikiya Ɗan Jaƙunana mai ƙaho Atsakiyar
kai da da jela zai Æ™araso”.



Ai cikin sauri suka miƙe suka fita daga wajen kamar yanda ya
faÉ—a.



 



Acan gidan Innayi kuwa zaune suke da Malam ArÉ—o asaman
baranda Moddibo.



Cikin nitsuwa Innayi ta kalli Malam ArÉ—o cikin sanyin murya
tace.



“Toh kaji yanda mukayi dashi, yanzu abinda nake so idan
Allah ya nufa zaka je kasamu Abban Jameelu kayi masa bayani idan yaso sai mu
isar da manufarmu ga mahaifin yarinyar”.



Jinina kai Malam Arɗo yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana
yace.



“Insha Allahu idan Allah ya yarda zan shiga wannan maganar
da iyakacin Æ™arfina zan shigeta da izinin Ubangiji”.



Kai Innayi ta jinjina tare da cewa.



“Toh ba matsala Insha Allah Nagode matuka”.



 



Acan gidan Ummi kuwa bayan fitar Malam Ahmad Moddibo ya
kalli Ummi cikin sanyin murya da damuwa yace.



“Ummi nayi al'Æ™awari da izinin Ubangiji da yardan Allah
sainayi duk yanda zanyi sai an gano waÉ—anda sukayi mana wannan cuta.



“Domin duniya tasan irin baÆ™in zunubin da suka aikata,
sannan akamasu ayi musu hukunci dai-dai da zunubinsu, domin wasu su tsira agaba
kada su sake cutar da wasu  kamar yanda
suka cutar damu, da zukatanmu da kuma ahalinmu”.



Numfashi Ummi ta fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya kana
tace.



“Hummmm?".



Cikin sauÆ™e numfashi Asma'u tace. 



“Toh ammn ta ina zamu fara 
Yah Modibbo!?”.



Ahankali Ummi ta kalleta kana ta kalli Moddibo ta sauke
ajiyar zuciya mai sanyi tace.



“Nima abinda nake tunani kenan, ta ina zaku fara wannan ba
ƙaramin case bane dole yakasance mutum nada ƙwararan hujjoji kafin ya tun kari
lamarin mu kuma bamu da sahihiyar Hujja dan haka mu barwa Allah lamarinsa”.



Jinjina kai Asma'u tayi tare da gyara zaman ta tace.



“Makama É—aya muke da shi batun Khausar”



 



Cikin zurfafa nazari Moddibo yace.



“Kin tabbata Asma'u zata bamu haske kan batun?”.



Kai ta gyaÉ—a masa kana cikin gaskiya da gaskiya tace.



“Na tabbatar Yah Moddibo”.



Kallon Ummi dake Kallonsu yayi kana cikin ƙarfin gwiwa yace.



“Ummi”.



Cikin sanyi da tausayinsa tace.



“Na'am Babana”.



Cikin alamun samun nasara da jin daÉ—i yace.



“Ummi zamu fara bincike”.



Kai Ummi ta gyaÉ—a kana cikin wani irin yanayi tace.



“Nikam ina tsoro Babana ina tsoron kada kaima Azo acutar
mana da kai ina tsoro kada wani abu ya sameka kawai abar maganar nan”.



Cike da mamaki da kuma sanyi Moddibo yace.



“Ummi tayaya”.



Girgiza kai Ummi tayi kana tace.



“Babana Abar Maganar kawai”.



Kai ya gyaÉ—a mata sannan suka dauka wani hiran sosai
kowannen su ya samu nutsuwa sosai sukaji damuwar suya fara raguwa kaÉ—an sai
bayan da Moddibo yayi sallar maghariba kafin yayiwa Ummi Sallama ya tafi.



 



Bayan Sallar Isha'i Malam ArÉ—o ne zaune gaban Abba wanda
baki É—aya ya rame yayi wani iri dashi.



Kallonsa Malam ArÉ—o yayi kana yace.



“Toh Alh kaji yanda akayi kuma shine abinda ya  kawo ni”.



Jinjina kai Abba yayi cikin yanayin sanyinsa yace.



“Nima nasani Jameelu ya faÉ—a min”.



Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.



“Masha Allah abu yazo da sauÆ™i kenan”.



Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyi yace.



“Ba matsala Insha Allah zuwa jibi zamuyi kokari muyi
maganar”.



Kai Malam ArÉ—o ya gyaÉ—a tare da cewa.



“Ayyah Jameelu Insha Allah zamu cika masa burinsa tunda har
yayiwa Amininsa zaɓin mata yayi fatan ya haɗa wannan Auren kafin ya tafi zamu
cika masa burinsa da izinin Ubangiji zamuyi ƙoƙarin cika wasiyyar daya bar
mana”.



Kai Abba ya gyaÉ—a cikin sanyi ya gyara zamansa tare da
lumshe idanunsa kana yace.



“Insha Allah zan tsaya akan lamarin sannan zanyi iyakacin
bakin Æ™oÆ™arina ganin ancika masa duk kan wasiyyar daya bari”.



Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da jinjina kai yace.



“Insha Allah babu damuwa idan Allah yakai mu jibin zanzo ba
matsala”.



Godiya Abba ya masa sannan Malam ArÉ—o ya masa Sallama ya
tafi.



 



Bayan kwana biyu: Moddibo ya fito daga gida jikinsa sanye da
Gezner fari soll yayin da kansa ke sanye da hula tangaran baƙa yalwataccen
sumar kansa irin na Fulanin Usul yana kwance aƙeyarsa fuskarsa tayi fayau
manyan Idanunsa na lumshe yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen
Oud Khareem kai tsaye gidan Ummi ya nufa bakinsa É—auke da sallama ya shiga
coumpund ɗin Abaranda ya hango Asma'u na Morping Jin ƙaran buɗe ƙofa yasa
Asma'u ta juya ganin Moddibo yasa tace.



“Yah Moddibo sannu da zuwa ka iso mana”.



Ahankali ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.



“Ummin fa naji gidan shiru?”.



Tana matse mopan dake hannunta tace.



“Bata nan”.



Kai ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.



“Ke kaÉ—ai ce agida?”.



Girgiza kai tayi kana tace.



“A'a Bashir na ciki?”.



Kai ya gyaÉ—a tare da gyara zaman hular dake kansa kana yace.



“Ina Ummi taje?”.



Ahankali ta jinginar da Moper kana tace.



“Ummi ta tafi asibiti saboda kwanan nan ciwon kai yana yawan
damunta taje adubuta”.



 



Cike da kulawa da kuma sanyi yace.



“Subhanallah toh Allah ya sawwaÆ™e”.



Ahankali Asma'u tace.



“Ameen”.



Moddibo kuwa gyara tsayuwar sa yayi cike da nutsuwa da kuma
sanyi yace.



“Asma'u zo muje ki rakani gidansu.



 Khausar akwai
tambayoyin da nake so nayi mata”.



Kai Asma'u ta gyaÉ—a cike da jin daÉ—in hukuncin da yake son É—auka
tace.



“Toh Shikenan Yah Moddibo bari in kira Ummi in FaÉ—a mata”.



Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yayi ƙasa da muryarsa
yace.



“A'a kada ki faÉ—awa Ummi, 
zata hana mu binciken idan kika faÉ—a mata zata hana amma yanzu kiyi
sauri muje kafin ta dawo yanzu zamu dawo”.



 



Jinjina kai tayi tare da faÉ—in.



“Toh shikenan”,Sannan tashiga ta dauki Maroon hijabinta har
ƙasa kana ta kalli Bashir dake karatun wani littafi na addini tace.



“Bari muje gidan su Khausar nida Yah Moddibo”.



Ta Ida maganar tare da fitowa.



 



Miƙewa Bashir yayi tare da fita kana yace.



“Laa Yah Moddibo Sannu da zuwa”.



Kai Moddibo ya gyaÉ—a kana yace.



“Yawwa Bashir koda Ummi ta dawo kada ka faÉ—a mata can mukaje
kace gidan Innayi muka je”.



Ahankali Bashir ya gyaÉ—a masa kai kana yace.



“Toh shikenan Yah Moddibo sai kun dawo”.



Suna fita suka shiga mota kana Moddibo yaja  suka tafi.



 



Acan gidan LamiÉ—o kuwa cikin sauri Khausar ta fita daga side
dinsu ta nufi sashen Gimbiya Bunayya tun kafin ta ƙarasa shiga tace.



“Ummah!, Ummah!!Ummah!!!”.



Daga ciki Hajiya Bunayya tace.



“Na'am”.



Khausar na karasa shiga tace.



“Ummah Raudat tashigo?”.



Kai Hajiya Bunayya ta gyaÉ—a kana tace.



“Eh tashigo”.



Ƙarasa shiga Khausar tayi tare da Hararan Raudat dake ɓuya
tace.



“Raudat kizo muje in miki wanka amma sai wani bauÉ—ewa kikeyi
tun É—azu kina ta gudu”.



Maƙale ka faɗa Raudat tayi tare da tura ƙaramin bakinta
tace.



“Ni dai na faÉ—a miki bana son wankan nan akwai sanyi”.



Cikin rarrashi Khausar tace.



“To ai da ruwan É—umi zan miki”.



Girgiza kai Raudat tayi tare da tura bakinta tace.



“Ni dai Banason gaskiya”.



Ganin tana son É“ata mata lokaci yasa Khausar ta shiga tare
da janyo hannunta tace.



“Maza wuce muje in miki 
zan baki waya kafin fito kiyi game”.



Bubbuga kafa Raudat tayi cike da Shagwaɓa tace.



“Addah Khausi Ni dai ki Æ™yaleni bana so”.



 



Ahankali Khausar tayi ƙasa da muryanta tace.



“Harda Game É—in bakya so?”.



Ware Ido Raudat tayi tare da ƙyalƙyala dariya kana tace.



“Allah dagaske Addah Khausi zaki bani?”.



Murmushi Khausar tayi tare da lakace mata hanci tace.



“Eh”.



Suna shiga Bedroom É—in Raudat ta zauna gefen gado sannan
Khausar ta mika mata wayar bayan tasa mata game É—in _Subway surf_ ta bata
murmushi Raudat tayi kana ta fara buga game É—in.



Khausar kuwa dogon rigar jikinta ta cire tare da É—aura towel
iya ƙugunta ta shiga toilet.



 



Akuma dai-dai lokacin Moddibo yayi Parking afarfajiyar gida
dai dai nan LamiÉ—o ya fito da motarsa ganin Moddibon yasa LamiÉ—o yayi Parking
din motarsa ya fito cikin sauri Moddibo ya ƙarasa kusa dashi tare da basa hannu
sukayi Musabaha cike da kulawa LamiÉ—o yace.



“Moddibo bar kadai ya gida ya kuma Ƙarin haÆ™urin rashin Jameelu?”.



Cikin sanyin Murya Moddibo yace.



“Alhamdulillah hakuri mungode Allah”.



Cike da kulawa LamiÉ—o yace.



“Allah ya gafarta masa ayi ya masa addu'a”.



Cikin sanyin yace.



“Ameen Mai Martaba Nagode.



 dama munzo wajen
Khausar ce”.



Cike da kulawa LamiÉ—o yace.



“Toh ba matsala Asma'u ku isa”.



Ahankali Moddibo yayi ƙasa da kansa tare da cewa.



“A mai Martaba baza'a a bari daga nan ba”.



Girgiza kai LamiÉ—o yayi 
kana yace.



“Ku shiga ba matsala bari na kira Aysha in FaÉ—a mata”.



Hannu ya sanya a aljihunsa tare da ciro wayarsa yayi
dearling number Mommy tana É—agawa yace.



“Aysha ga baÆ™i Moddibo da Asma'u zasu shigo”.



Cike da kulawa Mommy tace.



“Toh ba damuwa su shigo mana”.



Katse wayar LamiÉ—o yayi tare da yi musu Sallama kana ya
shiga motarsa ya fita.



Moddibo da Asma'u kuwa suka nufi sashen Mommy suna isa bakin
barandar Moddibo ya tsaya Asma'u ta ƙarasa shiga falon tare da cewa.



“Assalamu Alaikum”.



Shiru falon ba Kowa sai dai ko ina tsaf-tsaf kana ga ƙamshin
dake tashi. Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da nufar Bedroom din Mommy tana
cewa.



“Mommy!, Ta Æ™arasa tare da shiga Bedroom din Mommy dake
sanye da hijabi tace.



“Asma'u kun Æ™ara so Ina Moddibo?”.



Kai Asma'u ta gyaÉ—a tare da cewa.



“Eh amma yana waje”.



Mommy na zama gefen gado tace.



“Toh kice masa yashigo mana ya zaki barshi atsaye”.



Kai Asma'u ta gyaÉ—a tare da cewa.



“Toh Mommy”.



Sannan ta juya tare da fita falon ta leƙa ƙofan Falon cikin
sanyin Murya tace.



“Yah Moddibo wai kashigo”.



Ahankali ya É—ago kansa tare da buÉ—e Idanunsa dake lumshe
yace.



“Toh”.



Sannan ya shiga falon da komai ke kintse yana fitar da
sanyayyan ƙamshin ahankali ya zauna akan 1sitter dake fuskantar ƙofar Bedroom
din Khausar.



 



Asma'u kuwa juyawa tayi tare da kallon Moddibo kana tace.



“Yah Moddibo bari in sanarwa Mommy ka Æ™ara so”.



Bata jira amsar saba ta nufi Bedroom É—in Mommy.



 



Khausar kuwa ahankali ta fito daga toilet tare da juya kanta
yalwataccen sumar kanta dake jiƙe ya mannu da wuyanta da kuma gefen fuskarta
dake da damshin ruwa fararen cinyoyinta masu haske da santsi na É—auke da
damshin ruwa.



Ware Ido Raudat dake Game tayi  tare da kife wayarta akan gadon kana ta dira
tare da ficewa da gudu saida ta isa kofar Bedroom din kafin ta tsaya.



Cike da mamaki Khausar ke kallonta kana tana tafiya ahankali
tace.



“Raudat ina kuma zaki je?”.



Tura baki Raudat tayi tare da juya Idanunta tace.



“A ni dai Banason wankan nan da kwai sanyi”.



Sake baki Khausar tayi wato ita Raudat zata yiwa wayau, É“ata
fuska tayi tare da cewa.



“Aikuwa baki isa ba kisa in. Baki wayata kiyi game sannan
yanzu kinga na fito kice zaki gudu”.



Gwalo Raudat ta mata tare da fita da gudu.



 Ware ido Khausar tayi
tare da bin bayanta da gudu dariya Raudat ta ƙyalƙyale dashi tare da nufar
hanyar fita sai kuma ta karya kwana ta nufi Bedroom É—in Mommy.



Khausar kuwa garin zata karya kwana ta nufi Bedroom din
Mommy santsin ruwan dake ƙafarta da kuma santsin tlyes ya jata tayi baya
Suuuuuu ta faɗi a ƙasa kana towel ɗinta ya since ya zame yayi ƙ...!



 



 



No comments