Abban Sojoji Takun Karshe
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
Zagayeta su kayi gaba ɗayansu,su jahad na ambatar sunanta,fawan ne ya ɗauko masu ruwa a fridge ya dawo ya miƙa ma uncle ɗinsu,kar6a yayi tare da buɗe murfin ya ɗebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskarta,nan take ta farka tana faman yin atishawa,Alhamdulillah suka shiga faɗi suna kallonta,yunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido,
Muryarta na rawa tace"jaj..jahad hos...sana...ku ne?ko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba?
Ba ƙaramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane su,atare suka faɗa jikinta suka rungume juna suna kuka,
Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaɗae ba ma fuskar kowannansu na ɗauke da murmushi,musamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka hajiya azeemarsu har cewa take yi"yanzu nan waɗannan ƴan ukun duka namu ne?ƴa'ƴan mu ne?Allah abun godiya,yau dole in yi nafilar dare don miƙa godiyata ga Allah S.W.A daya nuna mun ƴa'ƴan abusufyan ɗinmu da ranmu kuma da lafiyarmu,Ashe dae da rabon yara suga danginsu,bayin Allah sun sha wahalar rayuwa,amma bakomai har yanzu lokaci bai ƙure mana ba,zamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarku,Zamu baku duk wani jin daɗi na duniya da kuka rasa,zamu gatanta ku,sai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani ƙunci da kuka ta6a fuskanta arayuwarku,waɗanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sunji dama ba'a halicce su cikin duniyar nan ba,
Abbansu junaid ya kar6e da cewa"Ae daga rana irin ta yau su fara ƙirgen kwanakin mutuwarsu,saboda ƙarshen su yazo,sun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEIN!Wallahi thumma tallahi ɗaya daga cikinsu bazai sha ba!' ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar,
Abbas yace"Abba ina ganin yakamata yaran nan suje su kwanta dare yayi sosai,suna buƙatar hutu,in yaso koma menene gobe zamu ida tattauna akai,'
Jinjina kai Abbansu yayi tare da mayar da idanunshi kansu sehrish dake manne da juna suna kuka,
Gyaran murya ya ɗan yi masu,atare suka ɗago suna kallonshi da idanunsu dake zubar da hawaye,
"Kuyi kuka yara bazan hanaku ba,dole kuyi kuka domin kuwa an cuci rayuwarku,an zalunce ku,an ƙuntata maku,an rabaku da mahaifinku na asali kuma an rabaku da danginku,duk akan laifin da baku kuka aikata ba,saboda son zuciya irin na mutanan nan su rasa akan wa zasu ɗauki fansar su sae akan waɗannan bayin Allahn.... 'Shiru ya ɗanyi yana faman sauke ajiyar zuciya,
abusufyan na zuƙunne akusa dasu ya sunnar da kanshi ƙasa,hakanan ya dinga jin kunyar yaran yana ji aranshi tamkar duk shi ne silar jefa su cikin halin da suka shiga,
Su fawan kuwa dasu twins irfan jabeer da sauransu duk suna atsaye kowannansu jikinshi asanyaye kamar waɗanda aka zare ma lakka,lokaci guda sukaji tsananin Son yaran ya kamasu,
duk wannan abun dake faruwa gwaggon katsina,na zaune saman kujera tana ta faman matsar kwalla,har lokacin bata daina tsinar dangin Sayyadi ba,haris sai faman lallashinta yake yi tana buge mashi hannu tana faɗin"ka rabu dani Harisu!abun da ciwo wlh,Zuciyata tafarfasa takeyi,ƴa'ƴan abusufyan ɗina aka wulaƙanta kamar dabbobi?wlh bazan ta6a daina tsinewa Sayyadi ba,munafuki algungumi ɗan wuta,Ya Allah ka tsine ma sayyadi da duk zuriyarshi harda unguwar zomar da ta yanke mashi cibinshi, Ya Allah kayi mana maganinsu,Sayyadi ko ɗan iska,uwarshi ta haifa mana masifa....munafuki lokacin da yake zuwa wurin abu har ƙasa yake zukunnawa ya gaishe Ni,da wata guntuwar jallabiyarshi ta gado,ƙafafun nan nashi kaman shebur sanye cikin silifar ɗan ta shegiya...Muna yi mashi kallon Biri yana yi mana kallon ayaba.....'
sai faman sambatu takeyi abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,can kuma tace"Allah sarki abu,nasan yanzu ta gane cewa Allah ɗaya ne,yarinyar nan akwai taurin kai kamar kwallon goruba ga kafiya,kunnuwan nan nata kamar na Zoman daji falo falo dasu,ba irin jan kunnan da banyi mata ba,amma taƙi ji na,Ae ga irinta nan yanzu majnun ya koya mata hankali yanzu tana can Saman bola tana sambatu baiwar Allah,wama yasan uwa duniyar data shiga.......'
"Sehrish ku tashi ku tafi ɗaki ku kwanta,gobe zamu ƙarasa magana daku," Abbansu ne yayi maganar,
Miƙewa sukayi tsaye tare da yi masu sallama sannan suka wuce ɗakin nata,gaba ɗaya sehrish ta ɗan shiga ruɗu,batasan meya faru ba,amma bakomai yafi ɗaure mata kai ba face ganinsu hosana da jahad,taya akai suka San inda take har suka zo wurinta?abun kamar a mafarki take ganinshi,
Atare suka shiga cikin ɗakin,anan fa suka tsaya suna kallon juna fuskar kowaccen su ɗauke da tsantsar farin ciki mara misaltuwa,
"Sehrish Ashe da rabon zamu sake ganinki a duniyar nan"?jahad ce tayi maganar yayin da hawaye ke sauka a fuskarta,
ta ɗaura da cewa "Sehrish munyi kewarki sosai,munyi kukan rashinki atare damu,munsha wahala sosai,abubuwa marasa daɗi sun faru damu bayan rabuwar mu dake,amma duk wani hali da muka shiga hakan baisa mun manta dake ba sehrish kullum kina aranmu,koda yaushe muna cikin zullumin a wane hali kike?kina raye kuwa?kina jin daɗin rayuwarki?kina da ƙoshin lpy ko akasin hakan ....'
jin wannan maganar ta Jahad yasa ta fashe da kuka mai cin rai,janyota jahad tayi jikinta sosai ta rungumeta,itama hosana ta matsa tare da sanya hannayenta ta bayansu,suka haɗe su ukun,sun jima a wannan yanayin kafin daga bisani suka haye saman gadon su duka ukun suka zagaye junansu suna fuskantar juna a zaune
Sai lokacin sehrish ta buɗe bakinta tare da cewa"inaso ku faɗamun meya faru na daina samun wayar tsohuwa,sannan kuma inason jin yadda akai har ku ka san inda nake,nayi mamakin yadda na manta daku gaba ɗaya acikin rayuwata,nasan ban kyauta maku ba,Amma kuyi haƙuri ku yafe mun........'
ta ƙarasa maganar tare da kai hannunta ta shafo gefen fuskar hosana tana kallonta da idanunta waɗanda suka canza launi sosai,sai lokacin ta gane cewa ashe sune yaran da Marshal Omar ke ruƙo a wurinshi,rashin sani yafi dare duhu,har waya suka yi dasu jahad amma bata ganesu ba,saboda bata acikin hayyacinta,
Jahad ce ta kwashe dukkan abunda ya faru tun daga kan Jefa wayar tsohuwa da hosana tayi acikin Masai da kuma mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu acikin cell,haɗuwarsu da Marshal Omar,zamansu a wurin gwaggon katsina da kuma rayuwarsu agidan Aunty babba,komai ta sanar mata,
Sosai sehrish tayi kuka tamkar ranta zai fita,har zazza6i saida ya lullu6eta nan take,bakomai yafi girgiza ta ba face mutuwar tsohuwa,da kuma zamansu hosana a gidan Aunty babba,abun ba ƙaramin ta6a zuciyarta yayi ba,wani irin ciwon kai ne ya rufar mata mai raɗaɗin gaske,rarrafawa tayi ta koma gefe guda saman bed mattress ɗin ta kwanta tare da janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,Wurinta su jahad suka koma tare da kwantawa kusa da ita,kowanannsu na acikin yanayi,tabbas sunga rayuwa......
Daƙyar bacci 6arawo ya sace su,amma fa dukkansu babu wanda babu zazza6i ajikinshi,
Kowa fa ya manta da cikinshi saboda lamarin su hosana,a gidan babu wanda yaci abincin daren shi,saboda ƙunci da takaicin yadda rayuwar ƴa'ƴan uncle ɗinsu ta kasance,
Lokacin da Azmee ta turo ƙopar ɗakin nasu samun su tayi kwance suna bacci kowacce fuskarta ɗauke da hawaye,bacci sukeyi amma hawayen basu daina zuba daga idanunsu ba,ba ƙaramin tausayinsu taji ba,ta jima tana kallonsu kafin ta rufe masu ƙopar ta koma bedroom ɗinta,
Kwance yake asaman katafaren gadonshi,tunda ya dawo bedroom ɗinshi,ya shiga toilet yayi wanka,ya dawo ya kwanta yana tunanin duniya,juyi kawai yake yi asaman gadon bacci yaƙi ɗaukarshi,har lokacin zuciyarshi bata sauka ba,abun ya dame shi sosae,ya tsani zalunci arayuwarshi,ya tsani mugun mutun mai hali irin na dabbobi,tabbas idan har sayyadi ya bari ya shigo hannunshi sai ya ɗanɗani kuɗarshi,daga baya kuma ya dawo yana tunanin wai yanzu ƴar yarinyar nan da take yi mashi aiki,ashe ƴar uwarshi ce?jinin shi?ɗiyar Uncle ɗinsu?hakan na nufin cewa ita ƙanwarshi ce...?
"Wonders shall neva end'ya furta hakan tare da lumshe idanunshi,nan take kuma ya tuna da hoton da Uncle abusufyan ya basu lokacin da suke a U.s,hakan na nufin cewa Hoton yaran ne ya basu lokacin da suke ƙanana,zan tambayi uncle hoton wacece nai selecting acikinsu,as I promised then zan taimaketa da kuɗi ta sayi duk abunda takeso bazan fasa ba...... '
Wasu dae sunyi bacci a wannan daren yayin da wasu kuma Baccin ya ƙaurace ma idanunsu,a tsaye Abusufyan ya kwana idanunshi sun ƙanƙance saboda raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi,bawan Allah,wlh abunda ciwo,taya ma zai iya bacci?yasha kuka dae,ga wani irin Matsanancin ciwon kai da yake fama dashi,yawo yake ta yi acikin dakin yama rasa tunanin da zai yi yayin da tafin hannunshi na dama ke dafe da saitin zuciyarshi,wani irin bugawa takeyi mashi mara daɗi,
Yana cikin tsayuwar ne har aka kira sallar asuba bai ankare ba,sae da Yaji ana mashi knocking ƙopa,muryarshi ashaƙe yace"Wanene,"
"Ni ne"muryar Abban su junaid ce,
Hakan yasa shi cewa"ƙopar abuɗe take yaya ka shigo daga ciki,".
Tura ƙopar Abba yayi ya shiga ciki yana ganin Abusufyan atsaye yace"dama saida rai na ya bani cewar baka yi bacci ba abusufyan,'
Yayi maganar tare da ƙarasawa ya dafa kafaɗarshi yana kallon fuskarshi da hawaye suka wanke ta sharkaf,
Cikin sanyin murya yace"duk wanda yace maka kayi haƙuri tamkar ya cuce kane!amma ya zakayi abusufyan?dole haƙurin nan shi zakayi,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi na iya zarce na ƙunar wuta,abusufyan bazan ce kayi laifi ba,amma kasan cewa dole ne dama kaga badai dai ba!kayi aure batare da sanin mahaifiyarka ba,baka sanar mata ba balle tasanya albarka acikin auren naku,kunyi komai a6oye kai da gwaggon katsina,sai gashi yau Allah ya bayyana mana komai,nasan kai kanka kayi mamakin ganin Ƴa'ƴanka su duka ukun a ƙarƙashin kulawar gidan mu,kaɗan daga cikin Ikon Allah kenan!kwata kwata yaran basu san suna da dangi ba,garari kawai sukeyi a wulaƙance cikin gari,mu ma haka bamu son cewa akwai wasu ƴa'ƴa waɗanda suka kasance jinin mu ne su ba,babu wanda yasan haka,amma cikin ikon Allah da yake shi hakimun ne,sai gashi silar aikatau ɗaya ta faɗo hannunmu,yayin da silar ciwon ɗaya daga cikinsu da aka kai asibiti Allah ya ƙaddara haɗuwarsu da Omar yayin da shi kuma yaje wurin ɗan uwanshi Dr haris,lamarin ubangiji girma gare shi!gaba ɗaya Allah ya haɗa yaran a wurinmu ta hanyar da bamu ta6a tsammani ba,kamar yadda kai da gwaggon katsina baku yi tsammanin abunda kuka aikata asirrance zai tonu ba,tunda baku sanar mana ba sae gashi Allah ya sanar damu,su kansu yaran basu yi tsammanin zasu haɗu da dangin ubansu na asali ba,su dama basu da masaniya akan wanine ubansu......'
Dakatawa abba yayi da maganar yana kallon abusufyan dake ta faman shessheƙar kuka muryarshi na kerma ya shiga cewa"Ya Allah ka yafe mun kuskuren dana aikata na auren abu batare da sanin mahaifiyata ba da kuma dangina ba......tun farko nine silar jefa rayuwarsu Cikin halin da suka tsinci kansu,da ace ban 6oye ma kowa ba,duk da ammi bazata barni in auri abu ba amma ina da tabbacin cewar Abbanmu salahuddeen zai aura mun ita inna nasanar mashi,iyakaci dae Ammi zata zangwameta ne daga baya kuma nasan zata fara sonta,wlh ni sam tunanin hakan baizo mani ba a wannan lokacin,idona ya makance,kuma ba laifin gwaggon katsina bane,Son da takeyi mun ne yasa ta aikata hakan don ta faranta mun ganin halin da na shiga a lokacin jin cewar Mommynmu ba zata bari in auri abu ba,gashi na mutu akan sonta
kaicona.......'fashewa yayi da wani sabon kukan,dana sani kenan irin wadda ba'ason yinta,abun yayi ta maka ciwo azuciyarka,shiyasa kullum muke cewa Allah ya tsare mu daga aikata aikin danasani,saboda bai da daɗi,ɗaci gare shi,
Ba ƙaramin tausayi yaba Abba ba,tuni shima hawaye suka fara sauka akan fuskarshi,janyo abusufyan yayi ajikinshi sosai ya rungume shi yana lallashinshi,
A ƙarshe yace"Abusufyan ka manta da duk wani abu daya faru dazun,yanzu lokacin farin cikine,yakamata ka nuna godiyarka ga Allah subhanahu wata ala daya nuna maka wannan ranar da ya haɗaka da triplet ɗinka dukkansu da ransu kuma da lafiyarsu!wlh abusufyan dana ga yaran nan amatsayin ƴa'ƴanka kaɗan ya hana in buga tsalle saboda murna.....'yayi maganar yayin da suka raba jikinsu dana juna,
tallabo fuskarshi abba yayi cike da zolaya yace"Kasan me?
Abusufyan ya girgiza mashi kai alamar a'a,
Abba yace"nifa ɗazu dana ga ka firgita da ganin yarinyar nan nayi tunanin cewa ko ka ƙyasa ne,har ina cewa shikenan lokacin barin gwaurantakar abusufyan yayi aduniya ashe ashe uban ne gaba ɗaya........'
Ya ƙarasa maganar yana dariya,murmushi abusufyan ya ɗanyi,
Abba ya kuma cewa"Wai yanzu nan duk aikinka ne waɗannan abusufyan?ashe dae ƙanin nawa bana wasa bane...'
fashewa da dariya abusufyan yayi tare da sunnar da kanshi ƙasa,
Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Abba ba,dama so yake ya sanyashi farin ciki don ya gusar mashi da damuwar da yake ciki,
dafa kaɗarshi abba ya kuma yi tare da cewa"duk haihuwata ya'ya goma sha takwas akan su jahan ne kawai na samu ƴan biyu,amma kai da yake mai sa'a ne,na ku ba irin namu bane sai gashi ka haifa mana ƴan uku reras!ko Ya ammi zata ji in taga ƴa'ƴan mara jin maganar nan nata abusufyan....nasan zata ce shegen bisa zai aika ae,
Wannan karan atare suka fashe da dariya,
Daga bisani Abusufyan yace"yaya hussein inaso naga yaran nan sosai,na damu dasu wlh....'
Wani irin kallon rainin wayau Abba yayi mashi kafin yace"yau naga ikon Allah!ni kake fadama kana son ganin ƴa'ƴanka?Yaran nan fa naka ne halak malak,ae ni nama yi tunanin a wurinsu zaka kwana,saboda suna buƙatarka sosai atare dasu,yanzu basu da burin daya wuce suga mahaifinsu atare dasu,"
Wani irin daɗi ne ya lullu6e abusufyan yace
"Zan iya zuwa wurinsu yanzu"?
Abba yace"Ka bari mu dawo daga masallaci inyaso kai tsaye kawai sai ka wuce wurinsu,"
Fuskar shi ɗauke da farin ciki yace"okey,bari naje nayi alwala,"
Abba yace"muna jiranka a main palour in ka kammala,ka same mu acan,"
Yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da nufar ƙopar ɗakin nashi ya fuce tare da tura masa ƙopar,
Toilet abusufyan ya shiga batare da 6ata lokaci ba,ya ɗauro alwalar,
Lokacin daya fito babban falon anan ya same su kowannansu ka kalla zakaga alamun damuwa a fuskokinsu,wasu ma da alama basuyi bacci ba,musamman Marshal Omar babu alamar yayi bacci adaren jiya,hatta Sgr ma akwai alamun rashin isasshen bacci atattare dashi,taya zaiyi bacci sayyadi na yawo acikin gari,shi fa in ya ƙullaci mutun irin haka har sai yaga bayanshi sannan yake samun kwanciyar hankali,su twins kuwa fuskokinsu sunyi jawur su da fawan,kowa dae da damuwa aranshi,
Bayan sun kammala haɗuwa suka wuce masallaci atare,
Tura ƙopar ɗakin nasu azmee tayi don ta tashe su sallar asuba,ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganinsu ajere suna sallah,kowaccensu na sanye da dogon hijabi a jikinta hijjaban sehrish ne hosana da jahad suka sanya,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,dama indae suna tare su ukun,musamman in akace maka akwai jahad atare dasu tofa basa wasa da ibada,duk da itama Sehrish ɗin ba daga baya ba,amma jahad ɗin itace kan gaba,saboda ita ba'a tashinta sallar asuba da zarar anfara kiran sallar asuba duk nisan baccin da tayi zata farka ne da kanta,abun sama rai ne da kuma sabo da yi,da kuma imanin mutun,
*Murmushi kawai azmee ke saki tana kallonsu gwanin ban sha'awa,ƴa'ƴan abusufyan,jikokin Ammi da salahuddeeen,ƴa'ƴan ƙanin Abban sojoji Abusufyan,ƙanne ga Marshal Da Sgr duk su kaɗae,abun farin ciki abun murna!yanzu su sun zama abunso wlh,yayyansu gaba ɗaya sojoji har goma sha takwas,ko sauro ne yayi gigin Cixon fatar jikinsu sae yaji saukar alburushin bindiga asaman goshin shi* 🤣
Azmee na tsaye tana kallonsu taji alamun motsin mutun a bayanta,jin an dafa ta yasa tayi firgit ta ɗan juya,Hajiya azeema ce jikinta sanye da hijabi blue,hannunta ruƙe da carbi,fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Nazo ganin ƴa'ƴanmu ne,idan ba damuwa ki bani hanya in wuce ciki,"
Murmushi azmee tayi tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,sai da ta shiga ciki sannan azmee tabi bayanta tana cewa"sallah nazo in tashe su suyi,shi ne na same su ashe har sun tashi ma,abun ba ƙaramin burgeni yayi ba dana gansu ajere su ukun suna sallah,'
Murmushi hajiya azeema tayi ayayin da take zama daga gefen gadon su tace"Albishirinki,"tayi maganar tana kallon azmee,
Azmee tace"Goro,"
"Fari ko ja,"cike da zolaya tayi maganar,
"Fari dae,shi ne ke tare da alkhairi,wannan launin jan alamace ta hatsari,"
Dariya hajiya azeema tayi kafin tace"Tab jiya anyi babu ke!Labari da ɗumi ɗuminsa!zazzafan gaske....'
A ƙagare azmee tace"Meya faru"!
A lokacin su jahad sun sallame sallah,suna zaune saman dardumar suna sauraransu,
Nuna su hajiya azeema tayi tare da cewa"Ke wai ashe yaran nan ƴa'ƴan abusufyan ne!!!"
Gaban azmee ne ya faɗi Rasss!saboda yadda maganar ta dirar mata kai tsaye acikin kunnuwanta,
"Wai dagaske"?tayi tambayar cike da mamaki,
Hajiya azeema tace"hmmmm ke dae bari,wani iko sai ubangiji,dagaske fa nake,babu wanda baiyi mamakin wannan abun al'ajabin ba,yara dae ƴa'ƴan ƙaninmu ne sufyan,'
Juyawa azmee tayi tana kallonsu sehrish da sukayi zuru suna kallonsu musamman Sehrish da batasan kan zancen ba,saboda bata a hayyacinta lokacin da akayi maganar,amma lokacin da jahad ke bada labarin rayuwarsu taji komai a kunnanta kuma daga nan ne Sihirin jikinta ya lalace saboda tunaninta daya rinjayi kwalwarta harta tariyo dukkan abunda ya faru arayuwarsu ga kuma addu'ar da Sgr keta yi mata acikin kunne,
Cike da mamaki azmee tace"taya akai hakan ya faru?dama abusufyan ya ta6a aure ne kenan?
Ataƙaice azeema ta bata labarin yadda abusufyan ya auri abu batare da saninsu ba,har suka samu ƙaruwar ƴan uku,'
Wani irin farin cikine ya lullu6e azmee saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa,
"Jahad!dagaske ne abunda kunne na ke jiyo mun"?sehrish ce tayi maganar tana kallon jahad da tsananin mamaki,
Murmushi jahad tayi ta jinjina mata kai alamar eh,ta ƙara da cewar"jiya duk baki a hayyacinki,abun farin cikin nan ya faru,Mun jima muna wahalar rayuwa ashe muna da dangi mai girma irin wannan bamu sani ba,cikin ikon Allah kuma sai gashi Allah ya haɗa mu dasu ta hanyar da bamuyi tsammani ba,ina tunanin addu'ar da muka jima munayi ne Allah ya kar6a mana,Ashe oumman mu sai da ta fara auren uncle ɗin su abusufyan sannan ta auri wannan fasiƙin mutumin sayyadi,da cikinmu ta shiga gidan shi........'
Aruɗe sehrish tace"taya hakan zai yiwu?
Hajiya azeema ce ta katse ta da cewar tabbas zancenta gaskiya ne sehrish!ku ƴa'ƴan ƙaninmu ne Abusufyan,sai da ya fara auren mahaifiyarku sannan Mugun mutumin nan daya ƙuntata rayuwarku ya aureta.......'gaba ɗaya hajiya azeema ta kwashe labarin rayuwar mahaifiyarsu agidan gwaggon katsina da kuma haɗuwarsu da abusufyan har izuwa rabuwar aurensu ta auri sayyadi ta sanar ma Sehrish,'
tun kan takai ƙarshen labarin nata,Sehrish tayi sujjada,tana shessheƙar kuka,saboda tsabar farin ciki,Ashe ita ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan?hakan na nufin su Babban yaya ƴan uwanta ne na jini!haba no wonder ae shaƙuwar dake tsakaninta da junaid tayi yawa,kai kana ganin abun zakasan cewar akwai alaƙa ta jini ajikinsu,ta damu da mutanen gidan sosai,ashe danginta ne su ɗin,
Jikin azmee ba ƙaramin sanyi yayi ba bayan hajiya azeema ta sanar mata irin zaluncin da sayyadi yayi ma su Sehrish,har idanunta sai da suka cicciko da kwalla saboda tausayinsu da taji,ta jima tana tsinar sayyadi acikin zuciyarta,
Muryarta tamkar zatayi kuka tace"dama ina ta son mu samu lokaci Sehrish ta bani tarihinta wllh,ashe haka suka sha ukubar rayuwa bayin Allah,kai koma wanene wannan mugun mutumin ya cika babban azzalumi,saboda tsabar zalunci ya raba yara da mahaifinsu ya kuma ƙuntata rayuwarsu,duniya ina zaki damu.......'azmee na cikin magana,Abusufyan ya turo ƙopar ɗakin bakinshi ɗauke da sallama,gaba ɗaya hankalin su sehrish ya dawo kanshi,shi ma kuma yana ɗago idanunshi suka sauka akan ƴan ukun nashi,kwata kwata ma bai lura da hajiya azeema da kuma azmee dake a ɗakin ba,Su sehrish kawai yake kallo cike da so da ƙauna,ko kyaftawa baiyi,kamar ya haɗiye su haka yake ji,kamar yadda yake jinsu haka suma suke jinsu,sae ƙare mashi kallo suke yi kamar su watsa a guje su rungumo shi haka suka dinga ji,ta wani 6angaren kuwa abun ba ƙaramin yawo yake yi masu akai ba,Wai nan mahaifinsu ne halak malak,ubansu wanda yayi silar zuwansu duniwa,dama suna da uba da dangi a duniya?tambayoyi iri iri suke shiga yiwa kansu,
Ganin sun zubama juna ido tsakanin Abusufyan da kuma su sehrish dake zaune saman darduma suna kallon shi,hakan yasa hajiya azeema tayi masu gyaran murya hankalinsu ya dawo kanta sannan tace"Zaman me kuke yi ne?baku ga mahaifin naku bane?ba zaku zo ku rungume shi ba,kuji ɗumin mahaifinku a jikinku?
jin wannan maganar ta hajiya azeema yasa su miƙewa gaba dayansu jiki na rawa suka ƙarasa wurin shi,
Tunkan su ƙaraso ya buɗe masu hannayenshi alamar su shiga ciki,haɗasu yayi dukansu ya rungume su sosai ajikinshi kamar zai maidasu cikin cikinshi,hawaye ne suka shiga gangarowa a idanuwanshi da kuma idanuwansu sehrish,bai ta6a tunanin zaiga wannan ranar ba,yau gashi ga ƴa'ƴanshi sun dawo wurinshi,tabbas Allah ne ya kar6i addu'ar daya jima yana yi,atare suka ɗago idonsu cike tab da hawaye suka haɗa baki wurin cewa"Abba,"
Har cikin zuciyarshi yaji wani irin sanyi ya ratsa shi,muryarshi akasalance yace"Ku sake maimaitawa banji ba,"
"Abba,"suka maimaita mashi kamar yadda ya umarta,
"Wlh kunyarku nake ji!duk wani abu daya faru arayuwarku ni ne sila,Na cuci rayuwarku,Naji na tsani kaina ƴa'ƴana suna a wani hali na rayuwa amma nagaza taimakonsu,zan iya zuƙunnawa saman guiwaowina agabanku domin in nemi gafararku.....,'tunkan ya ƙara maganar gaba ɗaya ya tafi zai zuƙunna saman guiwowins,cikin sauri suka rurruƙe shi suna cewa"Abba dan Allah kada kayi mana haka bamu so,ka daina ɗaura laifin akanka,dama Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan,dan Allah kada ka zuƙunna agabanmu,mu fa ƴa'ƴanka ne,
Ganin dagaske kneel down zaiyi agabansu yasa suka riga shi zube wa saman guiwowinsu,tsayawa daga tsaye yayi yana kallonsu,Azmee da hajiya azeema duk suna kallon abunda ke faruwa,ba ƙaramin tausayi suka basu ba,
"Abusufyan"! Hajiya azeema ce ta ambaci sunanshi,amsawa yayi yayin da ya mayar da idanunshi akanta,
Anatse ta soma magana"yanzu ba lokacin baƙin ciki bane ko lokacin tuna baya,Lokacin farin ciki ne wannan,dariya yakamata in dinga gani a fuskar kowannanku ba hawaye ba,ko ba haka ba azmee?tayi tambayar tare da mayar da idanunta kan azmee,
Murmushi azmee tayi kafin tace"Wannan haka yake,Abusufyan ina tayaka Murna sosai,nayi farin ciki mara misaltuwa,naji daɗi da sehrish ta kasance ƴarka ce,ko ince suka kasance ƴa'ƴanka ne,lamarin ubangiji da girma yake,babu wanda ya ta6a tsammanin haka,naji ma ina ganin kamannin fuskarka a fuskar sehrish ashe ƴar kace.....'magana take hawayen farin ciki na gangarowa daga fuskarta,
Murmushi kawai abusufyan ke saki,a lokacin harsu Sehrish sun miƙe tsaye suna tsaye akusa dashi,hosana ta rurruƙe hanunshi kamar wani zai kwace mata shi,
Hajiya azeema ce tace"Azmee yakamata mu basu wuri su gana da juna,don na lura da yadda Uban ƴan ukun nan ke zumuɗi akan ƴa'ƴanshi,"cike da zolaya ta ƙarasa maganar tare da miƙewa taja hannun azmee suka fuce suna dariya,
Ajiyar zuciya ya sauke tare da mayar da idanunshi kansu jahad yace"kun samu bacci kuwa jiya?ya tambayesu ne saboda fuskokinsu daya gani duk a yamutse,musamman idanunsu sun ƙanƙance,
Haɗa baki sukayi wurin cewa"Eh,"
Hosana tace"abba,dagaske kaine Abban mu ko?
"Ga zahiri kin gani,"yayi maganar yana yi mata nuni da fuskarshi,murmushi suka saki gaba ɗayansu,
Sun jima atsaye tare dashi suna magana jefi jefi saboda basu saba da juna ba,duk jin abun suke wani iri haka,kamar mafarki ne suke yi ba gaske ba,
"Ku koma ku kwanta,kuyi bacci ku huta,idan har akwai inda keyi maku ciwo ku sanar mun zansa aduba ku yanzun nan....'wannan maganar tashi ba ƙaramin sanyaya masu jiki tayi ba,
"Abba,lafiyarmu qalau,babu abunda ke damun mu,'suka faɗi hakan atare,
Gyaɗa kanshi yayi tare da kama hanya zai juya da nufi yabar ɗakin nasu,
Cikin sauri jahad ta ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Alla kada ka tafi kabarmu,muna buƙatarka a kusa damu,muna so mu kasance tare da mahaifinmu,'
Sehrish ta kar6e da cewa"hakane Abba,ka dawo mu zauna atare dakai,muna buƙatar kyakkyawar kulawa daga wurinka,'
tana kai ƙarshen maganar hosana tace"Abba pls,ko don saboda Ni,"
Wani irin murmushin farin ciki abusufyan ya saki yana kallonta,batare da 6ata lokaci ba,suka wuce saman gadon nasu,a tsakiya suka sanya abusufyan,yayin da suka kwanta gefe da gefenshi,sosai ya rungume hosana ajikinshi,duk in ya tuna labarin yada ta samu ta6in hankalinta nan take sai yaji idonshi sun ciko da kwalla,
"Idan Allah ya kaimu gobe,da kaina zan gyara maku gashin kanku inyi maku kalaba guda biyu,kamar yadda na ta6ayi maku Lokacin da kuna yara,nasan ba zaku iya tunawa ba,'
Jikinsu ne yayi wani irin sanyi, wani irin yanayi suka shiga gaba ɗayansu,
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_
*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*
*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅
Bismillah
Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,
Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,"
Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,
Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,"
on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,
Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,'
cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,'
Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?
"Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa
"kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne....'
Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,
"Wani abusufyan din kuke magana akai,"
Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin,
Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet,
gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,'
A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,
Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam,
"Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle ɗin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri ɗaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa ƴa'ƴanshi ne......'
Hannu ɗaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruƙe da wayarta data kara a kunnanta,
"Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za'ace yana da ƴa'ƴa har ƴan uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!!
6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar
Fashewa da kuka tayi saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daɗin jikinta,
Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta,
Tsoki taja tana jinjina kai tace"dama saida raina ya bani cewa ƙarya take yi mun,tayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukko,Shashasha kawai,
"Mommy kin farka kenan"
Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata,
Juyowa tayi tana kallonta,atsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeans,ta ɗaure sumar kanta da ribbom,yayin da hannunta ke ruƙe da Cup mai ɗauke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,
Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsala,hakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya,
ƙaƙalo murmushin yaƙe Aunty babba tayi tare da cewa"Lafiya naga kina murmushi"?
"Lafiya lou mommy,kawai wani abun farin ciki ne ya faru,nasan cewa muddin kema kika ji,zaki yi farin ciki sosai,'
Murya asanyaye aunty babba tace"Faɗamun daughter har na ƙosa naji wannan abun farin cikin?halan an ƙara maku albashi ne?ko matsayi aka ƙara maki wurin aiki"?
Dariya hafsat tayi tana girgiza kai tace"Mommy baki canka dai dai ba,wannan albishir ɗin da nakeso inyi maki yafi ƙarfin duk waɗannan abubuwan da kika lissafo,kar6i tea ɗin nan ki fara korawa kafin na faɗa maki,"
Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take miƙa mata,a hankali takai cup din bakinta ta kur6i Tea ɗin,kusan sau uku tana kur6arsa,kafin ta ɗan jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tace"daughter dan Allah ki faɗamun wannan wani abun farin ciki ne!wlh duk na ƙosa naji,'
"Zan faɗa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna,'
"Ba inda zanje,idan zaki faɗamun ki faɗamun kawai,Sae ja mun rai kikeyi," tayi maganar tana faman tamke fuska,
Hafsat tace"bada jimawa ba,Na kira Aunty azeema,don in gaishe da ita,Anan take sanar dani cewa ƴa'ƴan uncle abusufyan Sun bayyana...!
Tunkan ta ƙarasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannunta,Ya tarwatse ƙasa,Ruwan tean dake ciki ya fallatsar masu a ƙafa,
ja da baya hafsat ta ɗanyi tana kallonta tace"haba mommy,so kike ki ƙonamin ƙafa ta,daga faɗin abun farin ciki?
Rai amatuƙar 6ace tace"Ki 6ace mun da gani sakarya kawai,Maƙaryatan banza,bazan ta6a yadda da kalamanku ba,duk bakinku ɗaya da Hayaam,'
Ta faɗi hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi sama,ranta duk a jagule,bin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairs,ta6e baki tayi tare da watsa hannayenta tace"I don't care, Ni dae farin ciki nakeyi,Daddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga ƴa'ƴan uncle ɗinmu Abusufyan,tunkan na gansu har naji ina sonsu sosai,in ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi,'
Cike da farin ciki hafsat take maganar,zuƙunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa,
Lokacin da Aunty babba ta ƙarasa bedroom ɗin nasu,har ta ɗaga ƙafarta zata zura acikin ɗakin taji muryar ishaq yana cewa"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!Abba nayi farin ciki sosai,Meyasa tun jiya ba'a sanar dani ba,ae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiya,Amma ina taya uncle murnar ganin ƴa'ƴanshi,kuma ina tayamu murnar samuwar ƴan uku acikin zuri'ar mu,gaskiya bazan ma iya jurewa ba,Zan shirya nazo ne kawai,saboda na qosa naga ƴan ukun mu bayin Allah....
Abba yace"wani abun ma sai kayi tozali da yaran,kyawawan ƴan mata dasu,Yadda kasan photo copy ɗin abusufyan haka suke,kamanninsu sak iri ɗaya da nashi,'
Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yace"Abba kafin na ƙaraso,dan Allah a isar musu da saƙon gaisuwata,Ace yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosai,kuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman,'
"Insha Allah zan sanar masu yanzun nan,Allah ya kawoka lfy,"
"Ameen Abbana,"
Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar,
tashin hankalin da ba'a sama shi date!!!!!!!
Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faɗa mata,Tabɗijancan,
Dakyar ta iya shiga cikin ɗakin,lokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati ɗaya,
Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haɗaɗɗiyar shadda,
Ganin yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewa"Naji abunda ya faru,Hafsat ta sanar dani komai,ina tayaku murna,'ko amsar shi bata tsaya ji ba,ta faɗa cikin toilet,
Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom ɗin yana cewa"Ni yanzu zan wuce Abuja ne,inyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi haka,duk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat,
daga cikin toilet tace"Allah ya sauke ka lpy,in anje agaishe mana da mutanen gidan,"
"zasuji insha Allah," ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga ɗakin.
❤🤍❤
Acan 6angaren kuwa har lokacin suna a falon kan junaid da Uncle abusufyan ya gama fahimtar dashi game da Su Hosana da jahad,
jiki asanyaye yace"Amma meyasa su ba suyi rayuwa atare damu ba?meyasa Abba?uncle why?cike da tuhuma yake maganar yana kallonsu,yayin da fuskarshi ke ɗauke da damuwa,
abban su ne yace"Junaid,mu kanmu bamu san dasu ba,da ace munsan da zamansu da bamu bari hakan ya faru ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,"
Shiru junaid ya ɗanyi yana ƙare ma su Jahad kallo,yaso ace tun fil azal tare da yaran ya taso,da ba ƙaramin kulawa zasu samu a wurin ƴan uwansu ba,Allah sarki rayuwa kenan,Rashin sani yafi dare duhu,su kansu su Sehrish sae dama dama suke da sun san cewa suna da wannan family ɗin daba abunda zai hana su nemi danginsu,Tabbas an cuci rayuwarsu ƙiri ƙiri an rabasu da Ubansu kuma an hanasu danginsu,wata shari'ar dae sae a lahira,
"Nasan yanzu kowa yana jin yunwa,saboda halin da muka shiga jiya babu wanda ya samu damar cin abinci acikin mu,Yakamata yanzu komai ya wuce,Lokacin farin ciki ne,Za'a shirya gagarumar walima saboda ƴan ukun mu,munaso su manta da duk wani abu da ya faru a rayuwarsu kuma su ƙaddara cewa tamkar yau ne suka faɗo duniya,ko ba haka ba"? Ya yi maganar yana kallon matasan gidan dake atsaye,Kowannansu fuskarshi asake,su fawan ne suka haɗa baki wurin cewa"Wannan haka yake Abba,In sha Allah zamu nuna masu soyayyar ƴan uwantaka,har sai sun manta da dukkan wani ƙunci da suka fuskanta na rayuwarsu,' murmushi kawai Abusufyan ke saki don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
Marshal Omar yace "Sannan kuma muna ƙara baku haƙuri game da halin da kuka tsinci kanku,duk da ba laifin mu bane,amma mun ɗaura ma kanmu laifin,Muna neman afwarku,Hosana Sehrish and Jahad,forgive us pls,'
gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi,lokaci guda kuma sukaji wata irin soyayyar ƴan uwansu ta kamasu,
Jahad ce tayi ƙoƙarin cewa"duk wani abu daya faru damu dama can rubutaccen ne!Allah ya riga da ya ƙaddara faruwan hakan,mun gode ma Allah da muka cinye wannan jarabawar,da juriya kuma da haƙuri,yanzu gashi gaba ɗayanmu muna farin cikin wannan rana da Allah ya haɗamu da danginmu,Babban abun farin cikin ma da ya kasance Uncle abusufyan shine mahaifinmu ba waccen fasiƙin mutumin ba.......'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,Janyota Abusufyan yayi tare da rungumeta ajikinshi,yana ɗan bubbuga bayanta,
"Ya Omar," hosana ce ta ambaci sunan shi,tana faman kumshe dariya abakinta,gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu akanta,nuna shi tayi da yatsanta sannan ta nuna kanta,kafin ta haɗe yatsun wuri guda ta ƙullasu,Alamar ita dashi sun zama ƴan uwan juna, ƙayataccen murmushi Marshal ya saki yana kallonta,
Duk wannan abun dake wakana akan idon Sgr dake atsaye,ya goya hannayenshi asaman wide chest ɗinsa,Har lokacin bai sauko ba,hankalinsa fa bazai kwanta ba har sai yayi tozali da YA SAYYADI,
Suna cikin magana muryar azmee ta katse su da cewa"Abba an kammala shirya breakfast ɗin,yakamata ku hallara a dining ɗin," tana magana idonta na akan su jahad fuskar nan ɗauke da murmushi,
Batare da 6ata lokaci ba,gaba ɗayansu suka hallara asaman zungureran dining table ɗin wanda ke shake cike tab maƙil da kayan makwalashe naci dana sha,mutun goma shabiyu yake ɗauka,akwai kuma wanda Abban su junaid yasa aka ƙara cikin wanda aka shirya walimar jiya dasu,Ansanya shi a gefen nasu mai mazaunin mutun shida,Aunty azmee ta jera wasu kayan kalacin asaman shi,anan Abusufyan ya zauna tare da su sehrish jahad da hosana,
Tun daga kan yadda kowa ke zuba abinci acikinshi zai tabbatar maka da cewar ba ƙaramar yunwa suke ji ba,ko azmee basu jiya tayi serving ɗinsu ba suka shiga zuba abincin da kansu,Sgr ne kawai tayi serving ɗinsa sae kuma Abbansu,amma sauran ba wanda ya tsaya jira,wurin yayi tsit bakajin hayaniyar komai,sai sautin Cokulla,kwas kwas kwakwasss,
ɗagowa Marshal omar yayi karaf idonshi yaci karo dana hosana,ta zuba mashi ido ko kyaftawa batayi,kasancewar table ɗinsu na kusa dana juna,tazarar kadan ce,
Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da plate din gabanta,alamar ta mayar da hankalinta kan abunda take ci,
murmushi tayi tare da kai hannu ta dauki lemu tana korawa,
Junaid kuwa duk ya rasa samun natsuwa sam ya gaza cin abincin dake a gabanshi sae faman juya cokalin yake yi acikin plate,duk in ya tuna abunda yayi ma Jahad acikin mota amatsayin Sehrish sai yaji gabanshi ya faɗi rass,fargabar shi kada jahad tayi tunanin ko ɗan iska ne shi,tunda ba sanin shi tayi ba,kar kuma tace zata sanar ma wani abunda yayi mata,tunawa yayi da lokacin daya tsoma harshenshi acikin bakinta ya ƙanƙameta yana kissing lips ɗinta,ba iya nan ba ya tsaya har hannunshi saida ya zura ackin hijabinta
Hankali tashe junaid ya miƙe yana ƙoƙarin barin dining ɗin,hankalin kowa ya koma kanshi,
Har suna haɗa baki wurin tambayar shi ina zashi,
fuskarshi ɗauke da damuwa yace"Abba,bana jin yunwa,dama munyi breakfast tare da Mommy,zanje wurinta yanzu" Abbansu yake ma magana amma hankalinshi na akan Jahad dake shan farfesun da azmee ta zuba mata a plate,da alama ba ƙaramin daɗi farfesun yayi mata ba,duba da yadda ta mayar da hankali akanshi,
"Okey,zaka iya tafiya," ya bashi amsa,cikin sauri junaid ya kama hanyar zuwa bedroom ɗin Abbansu don acan ta sauka,yana tafiya yana waiwayen su jahad aranshi yana cewa"wayyo Allah na,bansan me zai biyo baya ba,nasan cewa dole ta sanar ma Uncle abunda nayi mata,idan ta faɗa mashi shi kuma zai faɗa ma Abban mu ne,Abban mu kuma zai faɗa ma Babban yayanmu ne,shi kuma zaice wuyana ya isa yanka tunda har na iya Sumbatar mace daga nan zaiyi tunanin turani aikin Soja abunda banso,shikenan tawa ta ƙare'
ranta ne ya bata cewar ana kallonta,hakan yasa ta tsagaita daga shan farfesun da takeyi,ta ɗan ɗago idanunta,kai tsaye suka sauka akan junaid dake can nesa dasu yana kallonsu,
Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya ƙura mata ido yana kallonta,aranta tace"bansan meyasa yake kallona ba,tsorana kar ace baisan ganina ne,'
"Allah yasa halinta irin na Sehrish ne,idan takasance mai sauƙin kai irin na rishi ɗina nasan cewa zata rufa mun asiri,amma anya zatayi sauƙin kai?Nasan me zanyi daga yanzu zan dinga ɗaure mata fuska,in nuna kamar na tsane ta,nasan hakan ne kawai zaisa taji tsorona taƙi faɗa masu abunda ya faru atsakaninmu!good idea",
Yana kai ƙarshen zancen zucin nashi ya watsa mata harara tare da murguɗa mata baki,ya juya ya nufi bedroom ɗin abbansu,
Jiki asanyaye jahad ta ɗauke idanunta daga kallon bayanshi da take yi,lokaci guda taji komai ya fita ranta ba don komai ba sai don kallon da taga junaid yayi mata,maganarta ta tabbata,Junaid baison ganinta,tunda gashi ya harare ta kuma hada murguɗa mata baki,
Muryar daddynsu ce ta katse ta da cewa"Jahad,meya faru ne?naga kin daina shan farfesun ina fata lafiya?
firgit ta ɗanyi tare da wurga eye balls ɗinta akanshi tace"Am ok daddy,'
jinjina kansa yayi kafin yace"Ku saki jikinku,kuci abinci sosai,kada kuji komai,nasan baku saba ba,don na lura akwai rashin sabo atattare daku,amma a hankali zaku saba da ƴan uwanku,'
hosana tace"Abba ae ni,nama saba da kowa,baka ga yadda nake ta cika cikina da abinci ba,jahad ce ke jin kunya,ni bana jin kunyar kowa,'
Dariya sukayi gaba ɗayansu,Sehrish na cikin sakin dariyar nan,Karaf idanunta suka haɗu dana Sgr,ɗagowar shi kenan yayi arba da ita,gabanta ne taji ya faɗi rass saboda fuskarshi a murtuke take ba annuri,nan take dariyar da takeyi ta koma ciki,ganin ta zuba mashi ido,yasa shi jefa mata harara,a hanzarce ta kawar da idanunta daga kallon fuskarshi da take yi,jikinta kuma yayi sanyi,ta shiga tambayar kanta dalilin hararar da taga big bro yayi mata,kodai baya farin ciki ne da kasancewarta JININ SA!?tabbas hakan zai iya faruwa,Wataƙil kodan ya saba ganinta a matsayin ƴar aikinsa,baiwarsa,ƙasƙantacciya shiyasa yanzu Yake nuna 6acin ranshi don yana ganinta tamkar a matsayi ɗaya suke dashi,Ƴa'ƴan Wa da ƙani,da alama hakan baiyi masa ba,
"Idan har dagaske ne abunda nake hasashe,insha Allah zan tattara na bar masu gidan,saboda bana son 6acin ranshi,zan iya yin komai don farin cikin shi," ta ƙarasa zancen zucin nata tare da sake ɗagowa a hankali don ta saci kallonshi,adai dai lokacin shima ya ƙara ɗagowa da kyawawan idanuwanshi kai tsaye suka shiga cikin nata,nan take taji gabanta ya kuma faɗuwa rass,kasa janye idanuwanshi yayi daga kallonta da yake yi,a yayin da yake jujjuya spoon ɗin dake hannunsa acikin plate ɗin abincin gabansa,har Yanzu bai daina mamakin kasantuwarta ƴar uwarshi ba,ta jininsa,tamkar a mafarki haka yake ganin abun,ganin ta zuba mashi ido batare da ta janyesu ba yasa shi ɗaure fuskarshi yasha murrr,saboda kada ma yarinya taga fuska har tayi tunanin raina sa don tasamu matsayi,
"U will still remain who u are,wadda take aiki a ƙarƙashina,Matsayin dana baki kenan,"ya fada a ransa
Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"bazasu kara wahala ba,bazan ta6a bari hakan ya faru ba,tunda dae har yaran nan suka bayyana a matsayin ƴa'ƴana,In sha Allah bazan ƙara bari suyi aikin wahala ba,ko cokali bazan ƙara bari ɗaya daga cikinsu ta ɗauko ba acikin gidan nan,rayuwar hutu kawai nake so suyi rayuwar ƴanci," ya ƙarasa zancen zucin nashi a yayin da yake bin kowaccen su da kallo cike da so da ƙaunar ƴa'ƴan nashi,'
Janye idanunshi yayi daga kan nata,kafin ya miƙa hannu tare da ɗaukar Glass cup mai ɗauke da abun sha me sanyi ya kai shi saitin mouth dinsa yana sipping ɗinshi anatse,yayin da sanyin lemun ke ratsa throat ɗinsa,a hankali ya lumshe idanunsa tare da ɗan ware su kaɗan,again suka ƙara sauka akan na sehrish a karo na uku kenan,agaggauce tayi hanzarin janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan plate ɗin abincin dake a gabanta,
Hannu Sgr ya sanya tare da yago tissue ya goge bakinsa,kafin ya miƙe tare da juyawa ya nufi upstairs,Miƙewa Marshal yayi da alama shima ya kammala breakfast Ɗin nasa,shima upstairs ya nufa,
Fitowar Hajiya azeema keda wuya daga cikin bedroon ɗinta,ta jiyo muryar gwaggon katsina tana ta faman sambatu tana cewa"Tsiyarta kenan mutun yazo gidan ƴan gayu,Ni bazan iya rayuwar turawan nan ba,taya za akai ma mutun salalar biredi tare da tea rabin kofi kamar wata ƴar iska ace in sha"?
Tafiya take tana sambatu zaninta a hannu sai ɗan undi ajikinta,kanta kuwa ta kifa wannan ɗaurin ɗan kwalin nata mai kama da helmert,
har zata gifta hajiya azeema tayi gyaran murya tare da ambaton sunanta"Goggo," fuska a yamutse ta juyo tana kallonta,dawowa tayi daga gefenta suna fuskantar juna tace"Yawwa azeema,wai nikam inaso in tambayeki,'
Natsuwa hajiya azeema tayi tare da cewa"ina sauraronki gwaggo,"
"Jiya nayi wani mafarki,ƴa'ƴan abusufyan sun bayyana,wasu ƴan uku kyawawan gaske,da nayi tunanin koda gaske ne abun ya faru amma daga baya na gane ba gaskiya bane,in ba haka ba,yaushe abusufyan ya ta6a yin aure"? Tayi tambayar tana kallon hajiya azeema,wadda ta saki baki tana kallon gwaggon,
Ganin azeema tayi sototo tana kallonta yasa tayi tunanin cewa ko abunda ta faɗa ya bata mata rai ne,
"Nasan dole kiyi mamaki kema,Mafarkin fa kamar dagaske,ɗaya daga cikinsu har tana sharara mana labarin ƙarya waisu ƴa'ƴan wata zainabu ne,kuma ma acikin labarin hada wata hajiya Ameena,in banda shaiɗan ina abusufyan ina ƴa'ƴa"?
Ƙiris ya rage Azeema ta fashe da dariya agaban gwaggon katsina,ganin yadda ta haƙiƙance tana kora mata bayani,kuma babu alamun wasa a fuskarta,
Ƙunshe dariyar bakinta tayi tare da basar da ita tace"Gwaggo Anya kina shan maganinki kuwa?ina Dr harris yake?gaskiya inason ganinshi,'
Tsoki gwaggon katsina taja tare da cewa"Harrisun daya zama ɗan iska,"
Waro ido waje azeema tayi tace"gwaggo harris ne ɗan iska"?
ta6e baki tayi tare da cewa"Zan masa ƙarya ne?ba ɗan cikina bane"?nasha wahalar yima yarona tarbiya amma waccen sauden.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,zanin hannunta takai saitin idonta tana ƙoƙarin goge hawayenta,
Zuru harris yayi wanda fitowarshi kenan kuma atare da saude suka fito,jin maganar gwaggone ma yasa yayi hanzarin cire hannunshi daga cikin na sauden,
Hajiya azeema tace"gwaggo faɗamun me harris ɗin ya akaita,?
Hankali tashe Saude tace"ya harris pls kada ka bari gwaggo ta faɗa mata abunda muka aikata,kasan gwaggo yadda take ɗaukaka abu,inta tashi faɗi saita ƙara ma miya gishiri,'
Dr harris yace"just don't worry ur self,insha Allah bazata faɗa mata ba,"
Faɗin hakan keda wuya gwaggon Katsina tace"Azeema abun da ciwo,yanzu yunwa nake ji,shiyasa ma kika ga nafito ina sambatu,Wurin waccen matar zani,wlh ba azmee ba Allah yasa ramadan ce ita yau saina zazzaga mata rashin mutunci!Ni zata raina ma hankali tunda safe,takawo mun tea rabin kofi da salalar biredi wai in fara da wannan,don ta raina mun hankali,nayi mata kama da kusu ne?
Rai a6ace tayi maganar,aikuwa atare haris da saude suka fashe da dariya,a hanzarce ta juyo sakamakon jin sautin dariyar tasu,nan take ta tsuke fuska ganin shi tare da saude,
Murmushi Hajiya azeema tayi tare da cewa"haba gwaggo baki fahimce ta bane,cewa fa tayi ki fara da wannan tana nufin kafin ki tashi fitowa zuwa yin breakfast ɗin,yanzu haka yana can an shirya mana mu kawai ake jira muje muci namu kalacin,"
Hajiya azeema ta ƙarasa maganar tare da ruƙo zanin hannun gwaggon tace"Bari na taimaka maki ki ɗaura shi,"
Girgiza kai tayi tare da cewa"Barmin shi a hannuna,nafison inji iska na shiga ta ko'ina,"murmushi hajiya azeema tayi kafin tace"hakan ma yayi gwaggo,ae under skirt din ma bamai sharashara bane,yana da kauri,amma duk da haka dae ki ɗaura zanin yadda zaki fito da kyau tunda ga rigarshi kin sanya ajikinki,Kuma kinga Abusufyan na nan,Ga kuma ƴa'ƴansa,bazasu so suga gwaggonsu a haka ba,"
wani irin ƙayataccen murmushi gwaggon katsina tasaki tare da cewa"Kenan dagaske ne Mafarkin da nayi jiya"?
Jinjina kai Azeema tayi tace"Ae suna nan,duk abunda ya faru jiya dagaske ne,ba mafarki kikayi ba,agabanki akayi komai kin dai shafa'a ne,'
Jin haka yasa tayi saurin mayar da zanin ajikinta tana ɗaure shi tana cewa"Allah sarki ƴa'ƴan abusufyan ɗina,bayin Allah,sunsha wahala a hannun wannan fasiƙin mutumin baƙin shaiɗani,Allah mutumin nan ƙaho ne kawai bai fito masa aka ba,amma ina tantama anya ba Irin shaiɗan bane"?
"gwaggo kidaina maganarsa ma,Ni wlh ko zancen shi ma bana so anayi,Na tsani mutumin nan kamar yadda natsani mutuwa ta,"acewar hajiya azeema,tayi maganar ne a yayin da take kama hanyar Zuwa Dining area ɗin nasu,bin bayanta Gwaggon tayi tana cewa"Ae ko sai dai ki toshe kunnanki,don zancen sayyadi ya zama dole,in har ba'a kawo min kansa ba,bazan daina faɗan sunan shi ba,'
Murmushi kawai hajiya azeema tayi,atare suka ƙarasa dining area din,
Gaggaisawa suka fara yi da junansu,su jahad na ganin saude suka tashi atare suka nufe ta,dama Jiya basu samu damar gaisawa da ita ba,saboda yanayin da suka shiga gaba ɗayansu,haɗasu tayi ta rungume ajikinta,cike da farin ciki tace"Ina tayaku murna sosai,nayi farin ciki sosai,Ya harris ya sanar dani komai agame daku,ashe ku jininsu ne,'ta ƙarasa maganar ayayin da take raba jikinta daga nasu,kowannansu fuskarshi ɗauke da murmushi,Jahad tace"Aunty saude kinga ikon Allah ko?munsha wahala sosai,mu kanmu bamu ta6a tunanin cewa muna da dangi ba,amma sai gashi ƙaddara ta haɗamu da ya Omar,Ita kuma ƴar uwarmu Sehrish ƙaddarar aikine ya kawota gidan nan,Muna tare da ƴan uwanmu ba tare da mun sani ba,sae gashi rana ɗaya Allah ya bayyana mana komai,'
Saude tace"Congratulations Once again,ina ƙara tayaku murna sosai da kuka fito daga tsatson wannan Family ɗin,abun alfahari ne wannan"kafin ta mayar da idanunta kan Hosana,Cike da zolaya taja kumatunta tare da cewa"Hosana Kinga yadda kika canza?kamar ba wannan Sha takwas sha taran ba,mai ɗan kai,kinyi kumatu kamar Balon balon,Ga haske gaskiya ya Omar ya Iya raino,"
Fashewa da dariya hosana tayi tana faman sunnar dakai,
"Kiyi ma sister ɗinku mana,Ita bazata taso mu gaisa ba"?tayi maganar tana kallon sehrish dake zaune,tana faman kallonsu ɗaya bayan ɗaya,
Murmushi jahad tayi tare da juyawa tayi mata alamar ta taso da hannunta,
Miƙewa sehrish tayi tare da nufar inda suke,koda ta ƙaraso saude ta sanya hannu tare da janyota ta rungumeta,kafin ta raba jikinta dana sehrish tace"Masha Allah,gaskiya ban ta6a ganin triplet,masu kama iri ɗaya sak kamar taku ba,ina taya ki murna sosai da Allah ya haɗaki da ƴan uwanki,da kuma mahaifinku,da kuma danginku,'
Fuskar sehrish ɗauke da murmushi tace"Ngde sosai,"
"Allah ya tsare mana ku,Ya Albarkaci rayuwarku ya kuma kare ku daga sharrin maƙiya,'
Atare suka amsa mata da Ameen,bama su kadae ba,hadasu Abba dake sauraron maganganun nasu,
Kamar yadda Abba yayi alƙawarin shirya gagarumar walima na bayyanar ƴa'ƴan ƙaninsa Abusufyan,Da kanshi ya fidda date ɗin da za'a gabatar da ita,Kuma tun aranar ya fara kiran Ƴan uwa da abokanan arziƙi yana sanar dasu game da ƴa'ƴan abusufyan da suka bayyana,Babu wanda bai bari ba,kowa kira yake tun daga kan danginsu na Zaria,na damaturu dana sauran states ɗin da kuma waɗanda ke zaune Ƙasashen waje,kowa saidaya sanar mawa,Bayan Abbas ya koma gidane da safe Amani ke tambayarshi meya faru ne jiya ya hanasu zuwa gidansu,Anan ya kwashe duka abunda ya faru game da su Sehrish ya sanar mata,wani irin farin ciki ne ya cika ta,Ba don komai ba sai don sanin cewa plan ɗin Aunty babba ya gama Tarwatsewa,ae tunda taji cewar ƴan mata ne kuma sun kai shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas kyawawan gaske,Nan fa ta kwashe da dariyar mugunta aranta tana cewa Naga yadda za'ae Aunty laila ta cimma burinta,Gida bai ƙoshi ba taya za'a ba na waje,Ae tuwona maina za'ayi,Haba ae xance ya ƙare,
ita kanta Amani ta ƙosa ranar walimar tazo saboda suje gidan,saboda taji cewar Aranar Aunty babba da hafsat zasu zo Abuja,babban burinta taga tashin hankalin da aunty babba zata fuskanta inta gansu,
Ranar walimar kuma yayi dai dai da ranar da Ammi zata zo,tare da wasu daga cikin danginsu,haka zalika captain Najeeb da kuma Talal suma duk a ranar zasu dawo gida,ba don komai ba sai don su sanya ƴa'ƴan uncle ɗinsu abusufyan acikin idanunsu,Kowa ɗokin ganinsu yake yi kamar kamar me,musamman da sukaji irin rayuwar da yaran sukayi a wulaƙance sai suji wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu ya shiga cikin ransu,kuma duk aranar MG Osman da kuma Captain Adam suma zasu dawo gida,wanda tun dawowarsu daga U.s suka tafi sada zumunci,Gaskiya wannan Babbar rana ce,Hakan yasa ma Zamuyi shiri na musamman ni da makaranta littafina don mu halarci gidan amatsayin gayyar soɗi tunda ba'a gayyace mu ba,Sa kaine kawai,
Cikin ƴan kwanakin nan wata irin rayuwar farin ciki suke gudanarwa tare da Daddynsu,kullum yana manne dasu,Da kanshi ya zauna yayi masu kitson kalaba guda bibbiyu akansu kamar yadda ya ta6a yi masu suna yara,koda yazo kan Sehrish,Cike da mamaki yace"Ya akai naga gashin kanki guntu?ko kinyi wani ciwo ne dayasa aka datse maki gashin,"girgixa kai tayi tare da cewa"a'a Laifi nayi ma Babba yaya shine ya yanke mun gashin da almakashi,"
da buɗar bakin Abusufyan sai cewa yayi"Yayiwa kanshi ai," murmushi sehrish tayi duk da batasan me daddyn nasu yake nufi da hakan ba,duk a wannan kwanakin basu je school ba,Abusufyan da kanshi yace kada su damu shi da kanshi zai kaisu makarantar don karma a tuhume su,
A 6angaren Sir Commander haroon kuwa,tamkar munafuki haka ya koma acikin gidan,ba kowa ma ke sanin lokacin da yake shigowa gidan ba,da kuma lokacin da yake fita,Da alama dae akwai wani abu da yake shiryawa a 6oye,
*AMRISH*
Zaune take acikin class ɗin gaba daya ta shiga damuwar rashin ganin Sehrish kwana biyu ko layinta ta kira bata samu,hatta wayar junaid ta jaraba kira shima ba'a ɗagawa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tagumi tayi idonta cike tab da hawaye saboda damuwar da take ciki,taso ace sehrish na nan atlease zata ɗebe mata kewa,tana cikin wannan tunanin har malam ya shigo cikin class ɗin nasu bata sani ba,bayan ya kammala amsar gaisuwa daga wurin student din,kai tsaye ya ƙarasa seat ɗin da Amrish take,hannun shi yakai wanda ke ruƙe da maker ya ɗan bubbugi desk ɗinta,a firgice takai idanunta akanshi,Yunƙurawa tayi tare da miƙewa ganin Ya mu'allim,wanda tun ranar daya ba sehrish Ruwan addu'ar nan bai ƙara zuwa makarantar ba,duk da sun samu labarin cewar Ya tafi Umra ne,shiyasa aka musanya masu shi,
Murmushi ya ɗan saki afuskarshi yana kallonta yace"tunanin me kike yi ne?har na shigo cikin class ɗin baki sani ba?
Muryarta na rawa tace"Ayimun afwa ya mu'allim,Bana jin daɗi ne bansan ka shigo ba,
Jinjina kanshi yayi tare da ɗan kai idanunshi kan Seat ɗin sehrish yace"Ina yarinyar nan take?ƴar family ɗin Salahuddeeen hussein naga kamar bata a class ɗin"?
fuskarta ɗauke da damuwa tace"Batazo ba,yau kusan kwana huɗu kenan bata zo school ba,kuma nayi trying kiran layinta amma bana samu,har brother ɗinta na kira,shima layinsa ba'a samu,'
Jin hakan yasa shi fargabar to kodai wani abu ya faru da yarinyar?Yaso yaji ya tayi da ruwan addu'ar daya bata,shin tasha ko bata sha ba?
Jinjina kanshi yayi tare da juyawa yace"Allah yasa dae lafiya,in har batazo ba,zuwa sati mai zuwa zan je gidansu don na binciki dalilin rashin zuwan nata,'
Jiki asanyaye Amrish ta koma ta zauna,saman seat ɗin nata,jikinta har ya fara kerma saboda tsoran kar ace wani abune ya faru da Sehrish,
A ƙarshe dae ta yanke shawarar neman gidansu don taje ta ganta da kanta.
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
"Allah ya kaimu lpy,Abba,'jahad da sehrish ne suka haɗa baki wurin bashi amsa,
Abusufyan yace"ba abba zaku dinga kirana ba,saboda ana kiran Yaya hossein da Abba,abun zai dinga ruɗa mutane ne arasa gane wani abban kuke nufi,amma ku dinga kirana Daddy,saboda a bambanta sunan,ina fata haka yayi maku?
"Eh daddy,"suka haɗa baki wurin bashi amsa,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,
"Abba ita Oumman mu fa?dagaske ne ta haukace kuma tana saman bola tana hauka kamar yadda gwaggon katsina tace?kuma wanene majnun ɗin da naji gwaggo tace shi ya koya ma oummanmu hankali,'hosana ce tayi maganar,jahad tace"Ke fa matsalarki kenan baki da kan gado,tunda kika ji ance Majnun ae kinsan wa ake nufi,'Murmushi Abusufyan yayi yana sauraronsu,
Sehrish tace"dan Allah ku daina magana,kuna takurama daddynmu bacci fa yake ji,baku ga idanunshi ba,
Mayar da idanunshi yayi kan sehrish data aza kanta asaman kafaɗarshi,kafin ya mayar da idanunshi kan jahad itama tana manne dashi,ga hosana kuma data manne mashi asaman chest ɗinshi,kamar zata koma ciki,Allah kaɗai yasan irin farin cikin da yake ji acikin ranshi,daɗi kamar ya kashe shi,babban burinshi Ammi tazo taga yaran daga zarar ta amince dasu,bai da wata sauran damu,zancen sayyadi kuma ya gama sama ranshi lokacin mutuwarshi yazo,Saboda Case ɗinshi na hannun Zaki da damusa,tabbas sai ya ɗandani kuɗarsa,
"Daddy,bakace komai ba!oumman mu fa muna so mu sake ganinta atare,"muryar hosana ce ta dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga,firgit ya danyi tare da sanya hannunshi ya shafa kanta yace"Kada ku damu,insha Allah komai yazo ƙarshe,Oumman ku duk inda take bi'iznillahi za'a ganota ne,inason komai ya lafa ne,daga ni har ku mu samu kwanciyar hankali sosai,sannan zan fara sanyawa a binciko mun makwabtan nan naku,ina da tabbacin cewa za'a samu wasu bayanai masu muhimmanci a wurinsu,"
Ba ƙaramin daɗi suka ji ba,burinsu oummansu itama tashigo cikin wannan daular suci gaba da rayuwa acikin family ɗin Abbansu,
"Daddy Allah ya taimaka,kuma ya baku sa'a akan duk wani yunƙuri da zakuyi na ganin kun kawo ƙarshen Mugun mutumin nan dashi da duk wani wanda yake da hannu akan cutar da zuri'armu,Allah ya tonu asirinsu,kuma Allah ya bayyanar da Oumman mu da ranta,Insha Allah daga rana irin ta yau zamu kasance kullum muna taya ku addu'a saboda asamu nasarar kama ya sayyadi,'murmushi abusufyan yayi yana sauraran maganar jahad,bayan ta kammala maganar Sehrish tace"insha Allah daddy zamu tayaku da addu'a kuma zamu jajirce wurin ganin mun bada gudummawa wurin binciken gano waɗanda ke da hannu akan cutar da zuri'armu,duk da mu mata ne muna da rauni,amma hakan bazai hanamu miƙewa tsaye ba wurin kawo ƙarshen Ya sayyadi da kuma ire irensa,shaiɗanun dake take masa baya,'
tana kai ƙarshen maganarta hosana tace"Abba don Allah Idan kun gano ya sayyadi,inaso abani damar da zan fasa mashi tsakiyar goshin shi da bindiga,ko in harbi saitin zuciyarshi ta daina bugawa,"
Dariya sosai abusufyan yayi yana sauraron kalaman hosana,
"Hosana,ae idan ya mutu ta hanyar harsashin bindiga sai inga kamar yayi mutuwar sauƙi ne,nafi so ya rayu tamkar matacce,gashi da rai amma baida wani sauran amfani,shi kanshi sai ya dinga roƙon Allah ya ɗauki ranshi ya mutu ya huta,a tunanina ba,amma abunda nake gani yakamata mu shirya mashi mummunan ƙarshe,wacece acikinku zata bamu idea?yayi tambayar yana jiran amsoshinsu,
Kowacce da irin shawarar da take bayarwa akan yadda za'a shiryama ya sayyadi mummunan ƙarshe,bad ending kenan,ba kamar hosana tafi kowa bada mummunar shawara,daga bisani kuma suka fara tsara ma kansu Happy life bayan an kashe ya sayyadi da tawagarsa,zasu fita ƙasashe daban daban yawon shaƙatawa tare da daddynsu,oummansu da kuma ƴan uwansu,araina nace hada mazajanku ko abun kamar zaifi bada citta harda kanunfari.......'
Bacci ne ya ɗaukesu atare manne da juna saman gadon,abun gwanin burgewa uba da ƴa'ƴanshi masu kama guda.
Har wuraren ƙarfe goma na safe basu farka ba,dama sun tara bacci sosai a idanunsu,har Abbansu junaid sai da ya leƙo ɗakin ya same su a baje suna sharar bacci murmushi ya saki,tare da curo wayar shi daga Aljihun rigar jikinshi,hoto ya ɗaukesu kusan guda uku,bayan ya kammala ya maida masu ƙopar ɗakin ya rufe,
Bayan ya fita daga sashen su kitchen ya nufa a lokacin Azmee harta kusa kammala aikin breakfast,yayi mamakin ganinta ita kadae tana ta faman aiki,
Tana ganinshi ta ajiye aikin da takeyi ta ƙaraso gaban shi tare da gaishe shi cikin girmamawa tace"barka da safiya Abba,antashi lpy?jiya sai muka ji abun farin ciki,Hajiya azeema ke sanar dani wai ashe su sehrish ƴa'ƴan Abusufyan ne,Wlh nayi farin ciki sosai,dama na jima ina ganin kamanninta da Shi,'.
Fukarshi asake yace"wllh Alhmdllh,mun Samu ƙaruwar ƴan uku,ni dai ince jiya banganki ba,ae naso ace agabanki akayi komai,kema kiji wannan abun al'ajabin da kuma tashin hankalin,labarin dae babu daɗin ji,Amma ta wani 6angaren kuma mun gode ma Allah da ya bayyana mana yaran nan amatsayin jinin mu,munyi farin ciki sosai,har Walima ma nake so asake shirya mana saboda yaran nan,'
Murmushi azmee tayi tare da cewa"Yaushe kenan?ko yau zamu fara shiryawa ne"?
Girgiza kai Abba yayi alamar a'a sannan yace"Wannan walimar ta musammance,gagarumin shagali za'ayi,akwai buƙatar kwanciyar hankali kafin lokacin,amma zanyi shawara da Abusufyan,idan har muka tsara komai,zan sanar maki,don ku shirya tarbar baƙi,zamu sa aƙaro wadanda zasu tayaki aiki.....'
Tunkan yakai ƙarshen maganar azmee tace"a'a Abba,zan iya ni kaɗai,basai an ƙaro masu aiki ba'
"Okey,ba damuwa naga kina ta wahala ke kadae,wai nikam ina yarinyar nan take ne?wata ƴar fara kanwarsu laila?naga kamar atare kuke aikin girki da ita ko ta koma gida ne"?
Azmee tace"a'a bata koma ba,bata jin daɗin jikinta ne,shine nace mata ta huta kawai,in taji sauƙi taci gaba da tayani,saboda yarinyar akwai son aiki,'
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa"Allah ya bata lpy,bari zanyi ma Kanal yousouf magana ya dubata...'
Cikin sauri azmee tace"A'a....ae na bata magani dama ciwon ciki ne,insha Allah zata warke,'
"Okey,' ya ambaci hakan tare da fucewa ya wuce cikin main palour dinsu,
Zama yayi saman sofa yana murmushi,bakomai yake tunawa ba face yadda yaga abusufyan tare da ƴan ukunsa,aranshi yace"Allah sarki,rayuwa kenan komai mai wucewa ne in bawa yasa haƙuri aransa,junaid tun yana jinjiri rabonshi da mahaifiyarshi,sai gashi jiya rungume da ita yana bacci,ƴan ukun abusufyan tun suna ciki rabonsu da ubansu, tun kafin cikinsu ya bayyana ma,sun sha wahalar rayuwa amma sai gashi komai na rayuwarsu ya canza yanzu tamkar basu ta6a shiga wani ƙuncin rayuwa ba,sannu a hankali zasu manta da duk wata uƙuba da suka sha arayuwarsu,Yau dae gasu can rungume da mahaifinsu suna bacci,Allah sarki,
A ƙarshe kuma yace"Oh,ni kuma gani nan babu mai rungumata,abusufyan nacen rungume da ƴa'ƴan shi,junaid ma na can manne da mommynsu,gaskiya nayi kewarsu sosai......'
"Abba!" karaf kiran ya sauka a kunnanshi a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,bakowa bane face Junaid yana tsaye hannunshi ruƙe da waist ɗinshi,har yanzu shaddar jiya ce ajikinshi,fuskar nan tashi cike da annuri sai faman zabga murmushi yake yi yadda kasan wanda akayi mashi albishir da gidan Aljana,
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e abbansu,yunkurawa yayi zai miƙe tunkan ya ƙarasa miƙewar junaid ya watsa da gudu kai tsaye ya faɗa jikinshi sosai ya rungume shi yana faɗin"I really miss u Abba,'
"Nima junaid nayi kewarka sosai,jiya da tunaninka na kwana araina,'yayi maganar yana ɗan bubbuga bayanshi,
raba jikinsu sukayi dana juna,ganin abbansu na kallon bayanshi yasa shi cewa"Abba mommy ko?
murmushi yayi tare da cewa"Ashe ka gane,ta ina ne?ko ba tare kuka zo ba?
ɗan ta6e baki junaid yayi nan fa hankalin abbansu ya tashi,.
Jiki asanyaye yace"Junaid bazata zo ba ko?Allah yasa dae ba Australlia ta koma ba,dama tunda na ganka kai kadae gabana ya fadi,don nasan halinta,'
Fashewa da dariya junaid yayi ganin yadda Abban nasu ya tashi hankalinshi don baiga mommynsu ba,
ɗaure fuskarshi yayi"oh ka ɗauki abun wasa ko?ba zaka faɗamun ina take ba,'
Yana cikin maganar ya jiyo takun takalminta,baisan lokacin daya janye junaid gefe ɗaya ba,Zuba mata ido yayi yana kallonta fuskarshi ɗauke da murmushi,tsayawa tayi tana ƙare mashi kallo,ba ƙaramin kyau tayi ba saboda kwalliyar da junaid yayi mata,da kanshi ya shafa mata janbaki ya gyara mata jagirar idonta,duk da haskenta sai da yashafa mata hoda,wai don Abbansu ya ganta da kyau,kuma shi da kanshi ya za6a mata rigar da zata sanya,jallabiya ce brown colour mai kyan gaske tayi rolling mayafi akanta,kamar wata balarabiya,tayi haske sosai kamar wata fatalwa,ga tsayi dake gareta kamar Sgr,
Komawa junaid yayi saman sofa yana kallonsu,jira yake yaga mai zasu yi,sun wani ƙura ma juna ido,sae murmushi yake saki,
Cigaba da tafiya tayi harta ƙaraso kusa dashi suna fuskantar juna,
Waro ido waje junaid yayi tare da cewa"Anshiga uku,Abba kaga yadda ka koma agaban mommy,wai dama ahaka kukayi aure Wayyo Allahna'
maganar junaid tasa suka fashe da dariya gaba ɗayansu,shi abunda ya bashi mamaki tsawonta agaban abban nasu,sae yaga abban nasu ya koma mashi guntu,
Sun jima suna sakar ma juna murmushi kafin daga bisani suka rungume juna sosai,kamar zasu zama daya,ba ƙaramin kewar juna sukayi ba,duk da akwanakin can baya yana kai mata ziyara Australlia,daga bayane ya daina zuwa saboda abubuwa da sukayi mashi yawa,
Kasa rabuwa sukayi da junansu,junaid kuwa ya tasa su gaba yana kallonsu kamar wanda ya samu television,
Adai dai lokacin twins suka shigo cikin falon,sakamakon Yunwa data ciwo su,karaf idanunsu suka sauka akan Mommynsu dake rungume da Abbansu,har suna haɗa baki wurin Cewa"Mommy!"
Cikin sauri suka raba jikinsu dana juna,wurga idanunta tayi akansu jahan da ayaan dake tsaye suna kallonta fuskar kowannansu ɗauke da farin ciki,
Da gudun gaske suka ƙarasa inda take gaba ɗaya suka faɗa jikinta,haɗasu tayi duka ta rungume ajikinta,tuni taji hawaye sun cicciko a idanunta,tayi kewar ƴa'ƴanta sosai,muryoyinsu tamkar zasu yi kuka suka haɗa baki wurin cewa"we really missed u mom!ashe zamu sake ganinki acikin gidanmu,'suka ƙarasa maganar ayayin da suke raba jikinsu da nata,
Hawaye tagani a idanunsu,cikin sauri ta sanya hannunta tana share masu hawayen muryarta na rawa saboda kukan daya zo mata daƙyar ta iya cewa"i missed u too my twins,nasan ban kyauta maku..... '
Jahan ya katseta"Mommy abubuwa da yawa sun faru,wanda da ace kina tare damu na tabbatar cewar bazasu faru ba,mun yi rashinki akusa damu mommy,munyi kewarki......'
"Mommy..amma dae ba zaki sake komawa ba ko"?acewar ayaan
Jinjina mashi kai tayi alamar eh sannan tace"nadawo kenan bazan sake komawa ba,I will be with u,for the rest of my life....."
Murmushi kawai Abbansu ke saki yana kallon uwa da ƴa'ƴanta,abubuwan farin ciki dae sai faruwa sukeyi acikin gidan,
"Mommy,kinga junaid ko ya girma sosai,yayi kukan rashinki sosai lokacin da baki nan,amma yanzu nasan cewar zaki bashi kulawa,dan Allah mommy ki bashi kyakkyawar kulawa saboda yafi kowa buƙatarki,'ayaan ne yayi maganar yana kallon junaid dake zaune yana ta faman murmushi,
Itama kallon nashi tayi tare da cewa"Insha Allah ayaan,daga yanzu junaid zai canza gaba ɗaya,zan bashi kyakkyawar kulawa,bama shi kadae ba hada ku gaba dayanku,Amma banga fawan ba dasu Irfan,and kanal yousouf ko duk suna ciki ne"?
Jahan yace"basu tashi daga bacci ba,bari naje na kira maki fawan ɗin,'
Dakatar dashi tayi da cewa"A'a kada ka tashe shi daga bacci,nasan daga ya farka yaji labarin zuwa na zaizo ne,but where is Alexander?
Atare suka haɗa baki wurin cewa"Mommy wanene Alexander kuma"?
Dariya Abbansu yayi tare da cewa"tana nufin Babban yayanku,ae sunan data raɗa mashi kenan ko kun manta,'
"Ae mun saba da kiranshi da babban yaya,mun manta da wannan sunan,shima yana a bedroom ɗinshi,duk bacci sukeyi saboda jiya bamu samu isasshen bacci ba,
Abba ne yayi mata nuni da 3 seater din dake gefensu yace"bismillahi,ki zauna mana ko baki gaji da tsayuwa bane,ko da yake na tuna fa Soja ce matar tawa,'yayi maganar cikin zolaya,
Murmushi kawai tayi tare da samun wuri ta zauna,shima abban nasu ya zauna daga gefenta,wuri su ayaan suka samu saman 2 seater suka zauna,
Cike da kulawa tace"Amma meya hanaku samun bacci da wuri ne?naji kunce baku samu isasshen bacci ba ko wani abu ya faru ne'?
Ayaan yace"abun farin cikine ya faru jiya agidan nan mommy,nasan kin kwaso gajiyar tafiya,idan kika huta nasan cewa Abba zai baki labari anjima,"
Da sauri junaid yace"meya faru ne?dan Allah ayaan ka faɗa mana yanzu kawai,Mommy fa tun jiya tazo ƙasar nan,muna acan tare da ita agidanta ma muka kwana,bata sanar ma kowa ba,sae abban mu,'
Baki sake jahan yace"Wai dagaske?mommy abun ƴar haka ce,wato shine mu ba'a sanar mana da zuwan naki ba,junaid kawai kika sanar mawa,no wonder shiyasa jiya ban ganka ba,abun ya tsayamun araina,ba don abunda ya faru ba na bayyanar ƴa'ƴan uncle ɗinmu daba abunda zai hana mu nemeka a wannan lokacin,duk wannan abun shiya ɗauke mana hankalinmu....."tunkan ya ƙarasa maganar Junaid yace"Ƴa'ƴan uncle?wani uncle ɗin kenan"?aɗan rude yayi maganar,
Miƙewa Ayaan yayi tare da ruƙo hannun junaid yabar wurin tare dashi,sai da suka samu wurin da bakowa sannan yace"kai kasan meya faru jiya"?
Cike da zumuɗi junaid yace"taya za'ae in sani,ni da bana agida,don Allah ka sanar dani har naƙosa naji,'
Ayaan yace"hmmmmm,labari da ɗumi ɗuminsa,ko kasan cewa yarinyar nan Sehrish ɗiyar uncle ɗinmu ce Abusufyan?
Gaban junaid ne ya faɗi rasss!saboda yadda maganar ta dira a kunnanshi,can kuma ya ɗan ɗaure fuskarshi yace"pls Ya ayaan dan Allah ka daina jamun rai,ni dae ka faɗimun gaskiyar abunda ya faru,'
Ayaan yace"kai nifa bada wasa nake maka ba,na ta6a maka wasa irin wannan ne!Sehrish ɗiyar uncle ɗinmu ce abusufyan,
Tur6une fuska junaid yayi tare da ɗan bubbuga ƙafarshi rai a6ace yace"yaushe uncle ya ta6a aure da har zai haifi ƴa'ƴa,kuma ma ƴar tashi ka rasa wadda zaka ce sae sehrish,kaji tsoran Allah ya Ayaan,babu kyau ƙarya,'
Rai a6ace Ayaan ya dunguri goshin junaid tare da cewa"Shashasha,ana ƙoƙarin a fahimtar dakai amma kaƙi yadda,don ubanka kaje ɗakin nasu ka leƙa,zaka ga abun mamaki,'
Turo baki junaid yayi tare da juyawa ya nufi hanyar xuwa ɗakin sehrish yana cewa"mai ƙarya dae ɗan wuta,'
Murmushi ayaan yayi yana kallon bayanshi,yasan cewa muddin junaid yaga Sehrish da ƴan uwanta sai ya haukace masu,farat ɗaya bazaiyi tunanin ƴan uku bane,sae ranshi ya fara bashi cewar Aljanune,
aikuwa,junaid na ƙarasawa kopar dakin,a hankali ya sanya hannunshi tare da tura ƙopar dama a buɗe take,zura ƙafarshi ya fara yi kafin ya ƙarasa shiga bedroom ɗin,koda baby junaid ya shiga ciki bai kai idanunshi kansu ba,sae da ya fara rufe ƙopar ɗakin sannan ya juyo fuskarshi a washe,Karaf idanunshi suka sauka akan abusufyan dake rungume da hosana suna bacci,gabanshi ne ya faɗi rass cike da mamaki yace"Kai uncle tare da rishi ɗina,kwance saman gado suna bacci,Anya kuwa bansamu matsalar idanu ba......'
"Junaid!" Jin an ambaci sunanshi yasa shi juyawa a firgice yaci karo da Sehrish dake zaune gaban mirror tana shafa powder a fuskarta,sae faman sakar mashi murmushi take yi,waro ido waje junaid yayi a tsananin tsorace ya mayar da idanunshi kan hosana dake rungume da abusufyan ya kalleta ya sake juyowa ya kalli wadda ke zaune agaban mirror,
Muryarshi na rawa yace"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Nashiga ukuna!wai meyake damuna ne!meyake shirin faruwa dani ne!kodai nafara gamo da aljanu ne......'bai kai ƙarshen maganar tashi ba yaji an buɗe ƙopar toilet ɗin dakin,da sauri ya wurga idanunshi wurin,
Jahad ce ta fito,jikinta sanye da bathrobe,alamar wanka tayi,
Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,
Hankali amatuƙar tashe junaid ya dinga kallonsu ɗaya bayan daya,idan ya kalli jahad sai ya kalli sehrish dake zaune gaban mirror,sae ya kuma juya ya kalli Hosana dake manne da uncle ɗinsu,
Tunkarar shi jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi,sehrish kuma na cewa"Junaid nice fa,baka gane ni ba,"
Ae ina,a gigice junaid ya fasa wata uwar ƙara wadda tayi sanadiyar tashin Abusufyan da hosana daga dogon baccin daya ɗaukesu,
Da gudun gaske junaid ya damƙi handle din ƙopar ɗakin tamkar zai balle ta,buɗewa yayi tare da watsa wa da gudu har yanayin tuntube,tun kan ya fito daga corridor din dakin,Abbansu da mommynsu dasu twins suka nufo wurin saboda jin sautin razananniyar ƙarar da junaid ya saki,
A sukwane ya faɗo wurinsu,hankalin Abbansu ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yadda junaid ke gudu duk tsigar jikinshi ta tashi,
Daƙyar suka samu suka damƙoshi saboda ƙokarin guduwa yake yi daga cikin gidan,
Hatta Marshal Omar da Sgr sai da suka jiyo ƙarar junaid,duk wani mai bacci acikin gidan sai da ya farka,ɗaya bayan ɗaya suka shiga fitowa suna tambayar ko lafiya,
Jikinshi sae kerma yake yi duk yabi ya firgice,tambayarshi suka shiga yi ko lafiya,
Muryarshi na kerma yace"Abba rishi uku acikin ɗakinta,Abba na mutu wlh aljanune ke bibiyata......'yana faɗin hakan ya sume ajikin Abban nasu,
Tunda sukaji haka ransu ya basu Cewar yaje ɗakin Sehrish ne,Abbansu baiso hakan ba,dama yasan shi firgitacce ne,yaso ace tun farko saida ya fara yi mashi bayani anatse sannan yaje ɗakin nasu,
Ayaan kuwa tun lokacin da yaji junaid ya fasa ƙara,ya ƙumshe dariya abakinsa,saboda yasan tsiyar daya tsula mashi,zaiyi wuya junaid ya yarda cewar Sehrish ƴan uku ne,ba kasafai yake fahimtar irin waɗannan abubuwan ba,sai an zaunar dashi cikin lalama anyi mashi bayani dalla dalla,sannan ake samu ya yadda,
"Junaid ne ko"?abusufyan ne yayi tambayar,yayin da yake daga zaune saman gadon,
Sehrish tace"Shine daddy,ya ruɗe ne saboda ya ganmu mu uku,ya tsorata sosai naso na fahimtar dashi amma sai naga ya watsa aguje,'jin haka yasa abusufyan yin hanzarin saukowa daga saman gadon ya fuce daga ɗakin,
Jikin jahad ba ƙaramin sanyi yayi ba,ganin halin da junaid ya shiga saboda ya gansu su uku,tsoronta kar wani abu ya same shi,ganin yadda ya watsa waje aguje,
"Inaso naje naga halin da yake ciki,bansan meyasa ya firgita ba har haka,"sehrish ce tayi maganar a yayin da take miƙewa daga saman stool,jikinta na sanye da farar riga da dogon wando fari,kanta kuma na sanye da hula fara ta roba,buɗe ƙopar dakin tayi ta fuce tare da nufar inda suke,
Komawa jahad tayi ta zauna saman kujerar gaban mirror,hannu tasa tare da ɗaukar man shafawar sehrish ta buɗe shi tana lakuto shi a hannunta tana shafa ma jikinta,
"Jahad wai meya faru ne?naji sautin ƙara a kunne na," hosana ce tayi maganar,tana zaune tsakiyar gadon sae faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji,
"Ƙanin Ya Omar ne,junaid ya shigo ɗakin nan,ina tunanin ya tsorata ne da ganinmu shiyasa ya firgita,saboda yaga fuskokinmu iri ɗaya dana sehrish,"
sauko da ƙafafunta tayi ƙasa tana cewa"bari naje naga meke faruwa a wajen,"
Da sauri jahad tace"Kada ki fita hosana!sehrish ta fita muddin ya ƙara yin arba dake zai zauce ne,ki bari sehrish tadawo sai muji daga bakinta,idan an fahimtar dashi ya fahimta,sai mu fita atare,
Hosana tace"amma fa Yunwa nake ji sosai aciki na,'
"Bari daddy ya dawo zanyi mashi magana,nasan zai sa ashirya mana breakfast ɗinmu,'acewar jahad,
Murmushi hosana tayi tare da cewa"jahad bakiji irin farin cikin da nayi ba jiyan nan!,wlh inason Daddynmu sosai,tun lokacin da gwaggon katsina tace mu ƴa'ƴan abusufyan ɗinta ne,ta kuma kirashi awaya tabamu mu gaisa dashi,tun daga lokacin nake jinshi araina,na dinga addu'ar Allah yasa ya zama mahaifinmun duk da alokacin nasan wanene mahaifin namu......'
"Nikaina hosana a lokacin,da muka fara waya dashi sai da naji jikina yayi sanyi,naji wani irin yanayi atattare dani ashe dae dagaske mahaifin namu ne,gaskiya munyi dacen uba,yana da kirki sosai duk da ban zauna dashi na wani lokaci ba,amma tun daga kan Fuskarshi zakasan cewar mutumin kirki ne,ashe lokacin da muna yara har zuwa ya ta6ayi ya ɗauke mu yakaimu gidansu yayi mana wanka sannan yayi mana kitson kalaba,bawan Allah,Allah kaɗai yasan yadda yaji acikin zuciyarshi lokacin da wannan baƙin mugun ya rabashi damu,'
Hosana ta ƙara da cewa"Mummuna kawai,fuskarshi kamar ɗuwawu saboda rashin kyau,har naqosa naga yadda Ya omar ɗina zai karairaya ƙasusuwan jikinshi,"ta ƙarasa maganar tana yin nuni da hannayenta,yadda takeso Omar yayi ma Ya sayyadi,
Ta cikin mirror jahad ke kallonta tana dariya tace"ae ba ƴa'ƴa Omar kaɗae ba,baki lura da yadda wannan mai blue eyes ɗin nan yayi ba,wani fari kyakkyawa mai ƙirar nan,har ni sai da na tsorata dashi ganin yadda ya zabura yabar wurin yana huci......'
Hosana tace"ae nagane shi,Ni wlh tsoran idanunshi nake ji, kaman aljani,wai shima yanzu ɗan uwanmu ne ko?duk ƴan gidansu ya Omar ne ko?
"Yayanmu zaki ce,ae yanzu duk wanda kika gani acikin gidan nan,to yayan mu ne,jiya baki lura da wani matashi acikinsu ba wani fari,mai mutunci wanda yazo ya kira mu,lokacin da alAbbansu ke neman mu"?
Murmushi hosana tayi alamar tagane shi tace"daga gani zaiyi sauƙin kai sosai,kuma da alama ba ƙaramin farin ciki yake damu ba,mun gode ma Allah jahad daya haɗamu da dangin mu,'
Lokacin da sehrish ta shiga main palour din nasu,anan ta samu matasan gidan duk tsaitsaye akan junaid,dake kwance saman doguwar sofa ɗin da Abbansu ya kwantar dashi,a lokacin har sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,bakinsa sai faman kerma yake yi kuma har lokacin bai daina faɗin "Rishi guda uku"ba,
Abusufyan yace"bawan Allah,nidai naji an saki ƙara ashe wai junaid ne,bansan time ɗin daya shigo ba,lokacin ina bacci ne,ae da ban bari hakan ya faru ba,da tun lokacin na fahimtar dashi,ashe har yanzu junaid na nan da wannan firgitar tashi,ae nayi tunanin ya daina,'
Shafa gefen fuskarshi abba yayi a yayin da yake zaune daga gefen daman kujerar yace"Ya tsorata ne sosai,ae ni kaina banyi tsammanin zaije ɗakin nata bane,naso ace saida na fara yi mashi albishir sannan yaje wurinsu,'
Jahan dake tsaye yace"Aikin ayaan ne,shine ya tura shi ɗakin nata,'ya ƙarasa maganar yana hararar ayaan dake tsaye yana dariya,
Duk Alexandra na tsaye tana sauraronsu,sam batasan inda zancen nasu ya dosa ba,
Koda sehrish ta ƙaraso,zuba mata ido Alexandra tayi tana kallonta,gaban sehrish ne ya faɗi lokacin da tayi arba da ita,har sai da ta ambaci Innalillahi acikin zuciyarta,ba komae ya firgitar da ita ba face ganin fuskar sgr a fuskar matar,kuma batasan da ita acikin gidan ba, sai dai lokaci guda taji aranta kaman ta ta6a ganin hoton matar,
Cike da mamaki Alexandra tace"wacece wannan kuma"?tayi maganar tare da yin nuni da sehrish wadda tuni ta koma bayan abusufyan ta tsaya,
Jahan ne ya bata amsa da cewa"Ƴan ukun uncle abusufyan ne,'.
"Abusufyan kuma?dama ya ta6a aure ne?
"Eh,ya ta6a aure batare da sanin kowa ba,sai daga baya abun ya bayyana cewar ƴa'ƴansa ne,kuma ƴan ukune kamanninsu iri ɗaya sak,abunda yasa kika ga junaid ya ruɗe kenan,baisan cewa su uku bane,ɗaya ya sani acikinsu,muma sai jiya Allah yasa mukasan da zamansu muka san cewa ƴa'ƴanshi ne,Nasan abba zai sanar dake komai,'
Jinjina kai Alexandra tayi tare da ɗan ta6e bakinta,yayin da ta janye idanunta daga kan sehrish ta mayar dasu kan junaid dake ta faman sambatu,
"Abba pls ku fahimtar dani mana!meyasa nake ganin Sehrish guda uku?ko na samu ta6in hankali ne,'
"Junaid u should calm down ur mind,in baka natsu ba taya zamu fahimtar dakai,"acewar abbansu,
Jin hannun mutun acikin nata yasata yin saurin juyawa,sai lokacin ta lura dashi sam bata ga fitowarshi ba,
"Mommy,"ya ambaci sunanta cikin sanyin murya,cike da farin ciki tace"Fawan!ka farka daga baccin kenan"?tayi maganar ayayin da take janyo shi jikinta,sosai ta rungume shi,
"Mommy tun yaushe kika zo ba'a sanar mun ba?sae dai na fito na ganki unexpected"
"Tun jiya nazo fawan,muna tare da junaid acan gidana muka kwana tare dashi sai yau da safe muka dawo atare,da fatan na sameka cikin ƙoshin lapiya,'
"Alhamdulillah mommy munyi missing ɗinki sosai da sosai,'
"Nima nayi missing ɗinku fawan,'magana suka cigaba dayi atsakaninsu,
Duk wannan abun dake faruwa alexandra bata tanka ma abusufyan ba,shima kuma bai tanka mata ba,tun lokacin daya shigo falon yayi arba da ita,yaga ta kawar da kanta gefe tun daga lokacin shima ya share ta,dama bata shiri dashi,tun lokacin da Abba ya aurota,ya ta6a zama agidan,yanayin yadda take wahalar da yayanshi ne yasa yayi mata rashin kunyar da ta haddasa gaba atsakaninsu,saboda shi bakinshi bai rufuwa muddin yaga tana gaya ma Yayanshi hossein magana saiya mayar mata da martani mai zafi,wannan dalilin ne yasa Abba yace ya tattara ya koma wurin ammi don bazai iya jurar zama dashi ba,kullum haɗa mashi Bomb yakeyi acikin gida,shiyasa abusufyan bai zauna agidan yayan nashi ba,kuma ammi bata kawo shi gidan ba lokacin daya addabeta da rashin jin maganarshi,kawai ta yanke shawarar kai shi gidan hajiya Ameenatu,
Kowa daya fito tun daga kan su irfan jabeer,khaleed da kanal yousouf babu wanda baiyi farin cikin zuwan mommynsu junaid ba,daya bayan ɗaya saida tayi hugging ɗinsu ajikinta,kanal yousouf ne kawai ta manna ma kiss a gefen fuskarshi,ji suke tamkar mahaifiyarsu ce Maryam ta dawo gidan,Allah sarki Allah ya jiƙan rai,tun daga yanayin yadda alexandra ta kar6esu hannu bibbiyu tana rungumarsu ransu ya basu cewar ta shiryu yanzu,da alama babu wannan girman kan nata da kuma Zafin ran nan,
Sehrish dae duk jikinta yayi sanyi tun daga kan irin kallon da taga Mommynsu junaid nayi mata,ranta ya bata cewar akwai matsala,sam fuskarta babu yabo babu fallasa lokacin da Jahan ke sanar da ita cewar ɗiyar uncle ɗinsu ce,
Abbansu na ƙoƙarin fahimtar da junaid,suka jiyo muryar sgr yana tambayar"Meya faru ne!"yayi maganar ne ayayin da yake saukowa daga saman stairs ɗin,jikinshi na sanye da shirt fara ta ɗame jikinshi sai kuma dogon wando jeans,ba ƙaramin kyau yayi ba,
Gaba daya suka juyo suna kallonshi,Marshal Omar na biye dashi abayanshi,atare suka sauko,
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e alexandra lokacin da tayi arba da first born dinta wato Surgeon General Rafayet,gaba ɗaya tagaza rufe bakinta saboda ba ƙaramin so take mashi ba,tana matuƙar alfahari dashi,
Sehrish kuwa tunda taji muryarshi taji gabanta ya faɗi rass,tabbas tayi kewarshi sosai,jiya abubuwan da suka faru ne suka hana takai mashi dinner ɗinshi,tasan cewa daƙyar ne idan yaci wani abu ajiyan nan,
Aranta tace"bansani ba ko yana farin ciki da kasancewata ƴar uwarshi,ɗiyar ƙanin Mahaifinshi,ko yaya yaji aranshi"?
Jahan ne ya sanar dasu abunda ya faru da junaid,
ƙarasawa Sgr yayi wurin Mommyn tasu,ita tafara manna mashi kiss a gefe da gefen fuskarshi sannan shima yayi mata kamar yadda tayi mashi,daga bisani kuma suka rungume junansu,
Abun ba ƙaramin burge sehrish yayi ba,har sai da ta ɗan saki murmushi kaɗan a fuskarta,
"Am really glad to see u mom,"ya furta hakan ayayin da suka raba jikinsu daga na juna,
Shafa gefen fuskarshi tayi tare da cewa"Yanzu ka kyauta mun?tun yaushe rabon dana sanya ka a idanuna Alex?ka daina zuwa wurina,kusan 1 year kenan baka tako ƙafarka kazo ba,'
Ganin hawaye sun cicciko a idanunta yasashi yin saurin ruko hannayenta tare da cewa"pls mom just forget about the past,nasan ban kyauta ba,amma kullum kina araina,kuma ina kiranki awaya muna gaisawa....'
Abbansu ne ya katse firar tasu da cewa"Ashe ba daɗi,Rama mun yayi Nima,ƙiri ƙiri kin rabani da aurena kinsa anata yi mun kallon Tazuru,'
Dariya sukayi gaba ɗayansu,banda sehrish dake tsaye jugum tana sauraronsu,
Matsawa Omar yayi cike da zolaya yace"Oh Mommy abun ƴar wariyar launin fata ce ko?atare da bro ɗina muka fito,amma ko kulani bakiyi ba...'yayi maganar yana ɗan ɗaure fuskarshi,
murmushi alexandra tayi tare da komawa wurin marshal,ta manna mashi kiss agefen fuskarshi sannan ta dafa shoulders ɗinshi tare da cewa"Omar ni bazan iya cewa komai ba,so nake nafara huce haushina akanshi kafin nadawo kanka,dama kaine mai ɗan son zumuncin,duk lokacin da kuka samu hutun aiki kana janyo shi kuzo wurina,amma yanzu duk kun juya mun baya,ni nasan duk shirin Abbanku ne yasan cewa dole nayi kewarku....'
Omar yace"no ba haka bane mommy,rayuwarce sai a slow,bamu manta dake ba,kuma kamar yadda rafayet ya fadi,muna kiran ki fa awaya kullum mu tambayi lpyrki,da ace kin ƙara 1 week baki zo nigeria ba,da kin ganmu munzo,ba don ma aiyuka da sukayi mana yawa ba,ae da mun rigaki zuwa....'
Ba ƙaramin daɗin kalaman Omar taji ba,yasan duk wata hanya da zaibi don ya kare kansu a wurinta,ba kamar SGR ba,shi kai tsaye kawai yake maganarshi ba wata kwana kwana,'
Sai da suka samu natsuwa sosai,sannan suka tattara hankalinsu kan junaid,
"Ina sehrish take ne"?Abbansu ne ya ambaci sunanta,saboda yaga gifcinta a wurin,
Da sauri ta amsa mashi da cewa"Gani nan Abba,"tayi maganar tare da fitowa daga tsayen da take abayan daddynsu,
Haɗa ido sukayi da Sgr,da sauri ta kawar da idonta,zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi,daƙyar ta iya ƙarasawa wurin abban nasu ta gaishe shi,
Bayan ya amsa mata yace"ki fahimtar da junaid,ina tunanin in yaji daga bakinki zaifi yadda cewa ku ƴan uku ne,'
Murmushi sehrish ta ɗan yi tana kallon fuskar junaid wanda ke kwance saman kujerar duk yabi ya rikita kanshi,tunda tayi magana yasan cewa itace saboda yaji muryarta,
Cikin sanyin murya ta soma magana,
"Junaid ka manta kwanaki na ta6a sanar dakai cewa Ina da ƴan uwa?waɗanda nake kira da wayarka?
"Amma ai kince mun baki da wasu ƴan uwa lokacin da muka yi maki magana akansu ni da aunty azmee,"yayi maganar yana faman hura hanci,
"Junaid a lokacin bana cikin hayyacina bansan ya akai na manta dasu ba,amma yanzu nadawo hayyacina kuma Zan iya tuna komai a game dasu,idan baka yadda dani ba,bari na tuna maka,ko ka tuna Yarinyar daka ɗauko a school cikin motarka?tun lokacin saida nayi ƙoƙarin fahimtar dakai cewar bani bace,ni ina a makaranta ka barni,shine dalilin da yasa nasha wahala aranar,'
Jin wannan maganar ta sehrish yasa junaid miƙewa daga zaune,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face,yadda jahad ta kasa sakewa dashi,kuma launin gashin kanta baƙi ne ba irin na sehrish ba,hatta muryarsu ma akwai ɗan bambanci,haba no wonder shi dae ya jima yana tunanin cewa al'jana ya ɗauko a motarshi ashe ashe mutunce,indae dagaske ne xancen sehrish hakan na nufin cewa ƴar uwartace ya ɗauko a motarshi?to kodai sune yaran da Ya Omar ɗinsu yasa su gyarama gidan uncle ɗinsu zai kawosu suyi rayuwa aciki......'bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,Muryar Omar ta katse Hanzarin shi"Junaid!maganar da take faɗa maka dagaske ne!they're triplet,kuma ƴa'ƴan uncle abusufyan ne,dukanmu bamu son da haka ba sai jiya Allah ya bayyana mana komai,'
Yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da kallon fawan yace"Kaje ka kira mun su hosana da jahad suzo ya gansu da idanunshi don ya shaida cewar mutane ne ba aljanu ba,'
Cike da zumuɗi fawan ya wuce bedroom ɗin sehrish a lokacin har jahad ta kammala shirya kanta cikin riga da skirt na sehrish,ba ƙaramin kyau tayi ba,
Kwankwasa ƙopar fawan yayi kafin ya turo tare da cewa"Ya omar nason ganinku yanzu,'jin haka yasa sukayi saurin kimtsawa,duk suka yafa gyala a kansu,
Atare da fawan suka shigo cikin main palour ɗin,
Jerawa sukayi kusa da sehrish duk sun sha jinin jikinsu tsoransu kar ace wani abun ne kuma ya taso,
zuba masu ido junaid yayi yana kallonsu,idan ya kalli jahad sai ya kalli hosana,
A ƙarshe ya tsaida idanunshi kan jahad,ta hanyar gashin girarta ya gane cewa itace ya ɗauko a motarshi,har suka sha Love,
Dafe kanshi yayi tare da cewa"OMG!Abba kenan reesh ƴar uwata ce,jini na,ɗiyar uncle ɗinmu abusufyan!taya hakan ya faru?kuma dama rishi ƴan uku ne su ba ita kaɗae bace!idan har dagaske ne meyasa basu taso atare damu ba!!!!!!!_
Karaf maganganun da junaid ke faɗi suka dira a kunnan Hayaam,wadda fitowarta kenan,yunwa ta korota daga bedroom ɗinta ta gaza jurewa shine ta lalla6a ta fito don ta shiga kitchen,
Gabanta ne yayi wani irin bugu ji kake rasss!rarasss!hankali amatuƙar tashe ta ɗago da idanunta ta sauke su akan Mutanen dake tsaitsaye acikin falon,waro ido waje tayi ganin Sehrish dasu jahad,anan ta tuna abunda azmee ta faɗa mata jiya na cewa ƴan uku ne su,kuma kamanninsu iri ɗaya sak,a fili ta ambaci"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya Allah ka rabani da mugun Ji da kuma mugun gani!nashiga uku Ni yau Hayaam,bari dae na ƙara kasa kunne naji uban da suke tattaunawa,ya Allah kasa korar shaggun za'ayi daga gidan,
"Junaid sehrish ɗin daka sani da kuma waɗannan biyun masu kama da ita sak,ƴa'ƴana ne,ni ne mahaifinsu,Na auri mahaifiyarsu ne ba tare da sanin kowa ba........'ataƙaice Abusufyan ya fayyace ma Junaid komai,
Saboda tsabar kiɗima hayaam ƙiris ya rage ta fasa ƙara a wurin,ta matukar firgita da jin abunda abusufyan ya sanar ma jahad,tashin hankalin da ba'a sama shi date,gudu gudu,sauri sauri hada tuntube wurin komawarta cikin bedroom ɗinta,jikinta sae faman kerma yake yi kamar wadda sanyi ya kama,hannu ta aza asaman kanta tana faɗin"nashiga uku!na bani na lalace!ƙarshe na yazo acikin gidan nan!taya akai haka ya faru duk ina nan sake da baki bansani ba,wai yanzu dagaske yarinyar nan mai aikin gidan dana raina,nake ganinta ƙaskantacciya yar wurin uncle ɗinsu ce Abusufyan,Tabɗijancan,Kallo ya koma sama!kai anya kuwa banyi kuskure wurin sauraran maganar shi ba?
Turo ƙopar da akayi ne yasa ta yin firgit ta juya,
Tana ganin azmee hannunta ɗauke da plate na breakfast ɗin da ta kawo mata,
Jiki na rawa hayaam ta ƙarasa wurinta tare da cewa"Aunty Azmee wai dagaske ne Seh...seh..rish ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan!"
Ƙayataccen murmushi azmee ta saki tare da cewa"Dagaske ne mana!Nima sai da asuba nakejin wannan labarin a wurin Hajiya azeemarsu....'tunda azmee ta soma magana hayaam ta fita hayyacinta,
Har sai da azmee ta ambaci sunanta"Hayaam!naga kamar kin tafi duniyar tunani ne?lafiyarki kuwa?
Murmushin yaƙe ta saki tana ƙoƙarin danne damuwarta tace"Azmee bana jin daɗi ne,zuciyata tafarfasa takeyi ne,"
.azmee tace"Allah sarki,dama saida raina ya bani cewa baki lafiya,To Allah ya sawake,yanzu dae ga wannan ki fara karyawa nasan kina jin yunwa.....'
Wani irin bugu Hayaam takai ma plate ɗin dake hannun azmee nan take yayi gefe guda ya tarwatse ƙasa,snacks ɗin dake aciki suka 6are,
Ita kanta hayaam sai da ta firgita saboda ba'a cikin hayyacinta tayi hakan ba,tsananin 6acin rai ne da ƙiɗimar da tayi,
Hankali tashe azmee tace"Hayaam!!'
Tunkan ta karasa maganar hayamm ta zukunna jiki na rawa tashiga kwashe snacks ɗin dake zube aƙasa tana mayarwa cikin plate din,
Muryarta na rawa tace"dan Allah aunty azmee ki tafi kawai,nagode sosai zanci....'
Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,ganin yadda la66an hayaam ke kerma kamar gandar nama,tasan cewa duk akansu sehrish ne,
"Allah ya baki lafiya,"ta ambaci hakan tare da juyawa tabar mata ɗakin,
Azmee na fita hayaam ta jefar da plate ɗin,
. miƙewa tsaye tayi nan fa tashiga safa da marwa tana zagaye ɗakin,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba face Aunty laila,tabbas ya kamata tayi gaggawar sanar da ita halin da ake ciki,
Jiki na rawa ta ɗauko wayarta dake ajiye saman mirror,tana danna wayar yatsun hannunta na kakarwa,daƙyar ta tsaida hankalinta wuri guda ta danna ma Aunty Babba kira.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_
*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*
*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅
Bismillah
Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata,
Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing,"
Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour,
Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki,"
on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar,
Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,'
cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,'
Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai?
"Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa
"kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne....'
Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi,
"Wani abusufyan din kuke magana akai,"
Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin,
Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet,
gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,'
A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa,
Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam,
"Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle ɗin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri ɗaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa ƴa'ƴanshi ne......'
Hannu ɗaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruƙe da wayarta data kara a kunnanta,
"Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za'ace yana da ƴa'ƴa har ƴan uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!!
6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar
Fashewa da kuka tayi saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daɗin jikinta,
Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta,
Tsoki taja tana jinjina kai tace"dama saida raina ya bani cewa ƙarya take yi mun,tayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukko,Shashasha kawai,
"Mommy kin farka kenan"
Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata,
Juyowa tayi tana kallonta,atsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeans,ta ɗaure sumar kanta da ribbom,yayin da hannunta ke ruƙe da Cup mai ɗauke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,
Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsala,hakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya,
ƙaƙalo murmushin yaƙe Aunty babba tayi tare da cewa"Lafiya naga kina murmushi"?
"Lafiya lou mommy,kawai wani abun farin ciki ne ya faru,nasan cewa muddin kema kika ji,zaki yi farin ciki sosai,'
Murya asanyaye aunty babba tace"Faɗamun daughter har na ƙosa naji wannan abun farin cikin?halan an ƙara maku albashi ne?ko matsayi aka ƙara maki wurin aiki"?
Dariya hafsat tayi tana girgiza kai tace"Mommy baki canka dai dai ba,wannan albishir ɗin da nakeso inyi maki yafi ƙarfin duk waɗannan abubuwan da kika lissafo,kar6i tea ɗin nan ki fara korawa kafin na faɗa maki,"
Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take miƙa mata,a hankali takai cup din bakinta ta kur6i Tea ɗin,kusan sau uku tana kur6arsa,kafin ta ɗan jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tace"daughter dan Allah ki faɗamun wannan wani abun farin ciki ne!wlh duk na ƙosa naji,'
"Zan faɗa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna,'
"Ba inda zanje,idan zaki faɗamun ki faɗamun kawai,Sae ja mun rai kikeyi," tayi maganar tana faman tamke fuska,
Hafsat tace"bada jimawa ba,Na kira Aunty azeema,don in gaishe da ita,Anan take sanar dani cewa ƴa'ƴan uncle abusufyan Sun bayyana...!
Tunkan ta ƙarasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannunta,Ya tarwatse ƙasa,Ruwan tean dake ciki ya fallatsar masu a ƙafa,
ja da baya hafsat ta ɗanyi tana kallonta tace"haba mommy,so kike ki ƙonamin ƙafa ta,daga faɗin abun farin ciki?
Rai amatuƙar 6ace tace"Ki 6ace mun da gani sakarya kawai,Maƙaryatan banza,bazan ta6a yadda da kalamanku ba,duk bakinku ɗaya da Hayaam,'
Ta faɗi hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi sama,ranta duk a jagule,bin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairs,ta6e baki tayi tare da watsa hannayenta tace"I don't care, Ni dae farin ciki nakeyi,Daddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga ƴa'ƴan uncle ɗinmu Abusufyan,tunkan na gansu har naji ina sonsu sosai,in ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi,'
Cike da farin ciki hafsat take maganar,zuƙunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa,
Lokacin da Aunty babba ta ƙarasa bedroom ɗin nasu,har ta ɗaga ƙafarta zata zura acikin ɗakin taji muryar ishaq yana cewa"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!Abba nayi farin ciki sosai,Meyasa tun jiya ba'a sanar dani ba,ae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiya,Amma ina taya uncle murnar ganin ƴa'ƴanshi,kuma ina tayamu murnar samuwar ƴan uku acikin zuri'ar mu,gaskiya bazan ma iya jurewa ba,Zan shirya nazo ne kawai,saboda na qosa naga ƴan ukun mu bayin Allah....
Abba yace"wani abun ma sai kayi tozali da yaran,kyawawan ƴan mata dasu,Yadda kasan photo copy ɗin abusufyan haka suke,kamanninsu sak iri ɗaya da nashi,'
Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yace"Abba kafin na ƙaraso,dan Allah a isar musu da saƙon gaisuwata,Ace yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosai,kuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman,'
"Insha Allah zan sanar masu yanzun nan,Allah ya kawoka lfy,"
"Ameen Abbana,"
Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar,
tashin hankalin da ba'a sama shi date!!!!!!!
Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faɗa mata,Tabɗijancan,
Dakyar ta iya shiga cikin ɗakin,lokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati ɗaya,
Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haɗaɗɗiyar shadda,
Ganin yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewa"Naji abunda ya faru,Hafsat ta sanar dani komai,ina tayaku murna,'ko amsar shi bata tsaya ji ba,ta faɗa cikin toilet,
Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom ɗin yana cewa"Ni yanzu zan wuce Abuja ne,inyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi haka,duk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat,
daga cikin toilet tace"Allah ya sauke ka lpy,in anje agaishe mana da mutanen gidan,"
"zasuji insha Allah," ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga ɗakin.
❤🤍❤
Acan 6angaren kuwa har lokacin suna a falon kan junaid da Uncle abusufyan ya gama fahimtar dashi game da Su Hosana da jahad,
jiki asanyaye yace"Amma meyasa su ba suyi rayuwa atare damu ba?meyasa Abba?uncle why?cike da tuhuma yake maganar yana kallonsu,yayin da fuskarshi ke ɗauke da damuwa,
abban su ne yace"Junaid,mu kanmu bamu san dasu ba,da ace munsan da zamansu da bamu bari hakan ya faru ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,"
Shiru junaid ya ɗanyi yana ƙare ma su Jahad kallo,yaso ace tun fil azal tare da yaran ya taso,da ba ƙaramin kulawa zasu samu a wurin ƴan uwansu ba,Allah sarki rayuwa kenan,Rashin sani yafi dare duhu,su kansu su Sehrish sae dama dama suke da sun san cewa suna da wannan family ɗin daba abunda zai hana su nemi danginsu,Tabbas an cuci rayuwarsu ƙiri ƙiri an rabasu da Ubansu kuma an hanasu danginsu,wata shari'ar dae sae a lahira,
"Nasan yanzu kowa yana jin yunwa,saboda halin da muka shiga jiya babu wanda ya samu damar cin abinci acikin mu,Yakamata yanzu komai ya wuce,Lokacin farin ciki ne,Za'a shirya gagarumar walima saboda ƴan ukun mu,munaso su manta da duk wani abu da ya faru a rayuwarsu kuma su ƙaddara cewa tamkar yau ne suka faɗo duniya,ko ba haka ba"? Ya yi maganar yana kallon matasan gidan dake atsaye,Kowannansu fuskarshi asake,su fawan ne suka haɗa baki wurin cewa"Wannan haka yake Abba,In sha Allah zamu nuna masu soyayyar ƴan uwantaka,har sai sun manta da dukkan wani ƙunci da suka fuskanta na rayuwarsu,' murmushi kawai Abusufyan ke saki don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
Marshal Omar yace "Sannan kuma muna ƙara baku haƙuri game da halin da kuka tsinci kanku,duk da ba laifin mu bane,amma mun ɗaura ma kanmu laifin,Muna neman afwarku,Hosana Sehrish and Jahad,forgive us pls,'
gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi,lokaci guda kuma sukaji wata irin soyayyar ƴan uwansu ta kamasu,
Jahad ce tayi ƙoƙarin cewa"duk wani abu daya faru damu dama can rubutaccen ne!Allah ya riga da ya ƙaddara faruwan hakan,mun gode ma Allah da muka cinye wannan jarabawar,da juriya kuma da haƙuri,yanzu gashi gaba ɗayanmu muna farin cikin wannan rana da Allah ya haɗamu da danginmu,Babban abun farin cikin ma da ya kasance Uncle abusufyan shine mahaifinmu ba waccen fasiƙin mutumin ba.......'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,Janyota Abusufyan yayi tare da rungumeta ajikinshi,yana ɗan bubbuga bayanta,
"Ya Omar," hosana ce ta ambaci sunan shi,tana faman kumshe dariya abakinta,gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu akanta,nuna shi tayi da yatsanta sannan ta nuna kanta,kafin ta haɗe yatsun wuri guda ta ƙullasu,Alamar ita dashi sun zama ƴan uwan juna, ƙayataccen murmushi Marshal ya saki yana kallonta,
Duk wannan abun dake wakana akan idon Sgr dake atsaye,ya goya hannayenshi asaman wide chest ɗinsa,Har lokacin bai sauko ba,hankalinsa fa bazai kwanta ba har sai yayi tozali da YA SAYYADI,
Suna cikin magana muryar azmee ta katse su da cewa"Abba an kammala shirya breakfast ɗin,yakamata ku hallara a dining ɗin," tana magana idonta na akan su jahad fuskar nan ɗauke da murmushi,
Batare da 6ata lokaci ba,gaba ɗayansu suka hallara asaman zungureran dining table ɗin wanda ke shake cike tab maƙil da kayan makwalashe naci dana sha,mutun goma shabiyu yake ɗauka,akwai kuma wanda Abban su junaid yasa aka ƙara cikin wanda aka shirya walimar jiya dasu,Ansanya shi a gefen nasu mai mazaunin mutun shida,Aunty azmee ta jera wasu kayan kalacin asaman shi,anan Abusufyan ya zauna tare da su sehrish jahad da hosana,
Tun daga kan yadda kowa ke zuba abinci acikinshi zai tabbatar maka da cewar ba ƙaramar yunwa suke ji ba,ko azmee basu jiya tayi serving ɗinsu ba suka shiga zuba abincin da kansu,Sgr ne kawai tayi serving ɗinsa sae kuma Abbansu,amma sauran ba wanda ya tsaya jira,wurin yayi tsit bakajin hayaniyar komai,sai sautin Cokulla,kwas kwas kwakwasss,
ɗagowa Marshal omar yayi karaf idonshi yaci karo dana hosana,ta zuba mashi ido ko kyaftawa batayi,kasancewar table ɗinsu na kusa dana juna,tazarar kadan ce,
Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da plate din gabanta,alamar ta mayar da hankalinta kan abunda take ci,
murmushi tayi tare da kai hannu ta dauki lemu tana korawa,
Junaid kuwa duk ya rasa samun natsuwa sam ya gaza cin abincin dake a gabanshi sae faman juya cokalin yake yi acikin plate,duk in ya tuna abunda yayi ma Jahad acikin mota amatsayin Sehrish sai yaji gabanshi ya faɗi rass,fargabar shi kada jahad tayi tunanin ko ɗan iska ne shi,tunda ba sanin shi tayi ba,kar kuma tace zata sanar ma wani abunda yayi mata,tunawa yayi da lokacin daya tsoma harshenshi acikin bakinta ya ƙanƙameta yana kissing lips ɗinta,ba iya nan ba ya tsaya har hannunshi saida ya zura ackin hijabinta
Hankali tashe junaid ya miƙe yana ƙoƙarin barin dining ɗin,hankalin kowa ya koma kanshi,
Har suna haɗa baki wurin tambayar shi ina zashi,
fuskarshi ɗauke da damuwa yace"Abba,bana jin yunwa,dama munyi breakfast tare da Mommy,zanje wurinta yanzu" Abbansu yake ma magana amma hankalinshi na akan Jahad dake shan farfesun da azmee ta zuba mata a plate,da alama ba ƙaramin daɗi farfesun yayi mata ba,duba da yadda ta mayar da hankali akanshi,
"Okey,zaka iya tafiya," ya bashi amsa,cikin sauri junaid ya kama hanyar zuwa bedroom ɗin Abbansu don acan ta sauka,yana tafiya yana waiwayen su jahad aranshi yana cewa"wayyo Allah na,bansan me zai biyo baya ba,nasan cewa dole ta sanar ma Uncle abunda nayi mata,idan ta faɗa mashi shi kuma zai faɗa ma Abban mu ne,Abban mu kuma zai faɗa ma Babban yayanmu ne,shi kuma zaice wuyana ya isa yanka tunda har na iya Sumbatar mace daga nan zaiyi tunanin turani aikin Soja abunda banso,shikenan tawa ta ƙare'
ranta ne ya bata cewar ana kallonta,hakan yasa ta tsagaita daga shan farfesun da takeyi,ta ɗan ɗago idanunta,kai tsaye suka sauka akan junaid dake can nesa dasu yana kallonsu,
Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya ƙura mata ido yana kallonta,aranta tace"bansan meyasa yake kallona ba,tsorana kar ace baisan ganina ne,'
"Allah yasa halinta irin na Sehrish ne,idan takasance mai sauƙin kai irin na rishi ɗina nasan cewa zata rufa mun asiri,amma anya zatayi sauƙin kai?Nasan me zanyi daga yanzu zan dinga ɗaure mata fuska,in nuna kamar na tsane ta,nasan hakan ne kawai zaisa taji tsorona taƙi faɗa masu abunda ya faru atsakaninmu!good idea",
Yana kai ƙarshen zancen zucin nashi ya watsa mata harara tare da murguɗa mata baki,ya juya ya nufi bedroom ɗin abbansu,
Jiki asanyaye jahad ta ɗauke idanunta daga kallon bayanshi da take yi,lokaci guda taji komai ya fita ranta ba don komai ba sai don kallon da taga junaid yayi mata,maganarta ta tabbata,Junaid baison ganinta,tunda gashi ya harare ta kuma hada murguɗa mata baki,
Muryar daddynsu ce ta katse ta da cewa"Jahad,meya faru ne?naga kin daina shan farfesun ina fata lafiya?
firgit ta ɗanyi tare da wurga eye balls ɗinta akanshi tace"Am ok daddy,'
jinjina kansa yayi kafin yace"Ku saki jikinku,kuci abinci sosai,kada kuji komai,nasan baku saba ba,don na lura akwai rashin sabo atattare daku,amma a hankali zaku saba da ƴan uwanku,'
hosana tace"Abba ae ni,nama saba da kowa,baka ga yadda nake ta cika cikina da abinci ba,jahad ce ke jin kunya,ni bana jin kunyar kowa,'
Dariya sukayi gaba ɗayansu,Sehrish na cikin sakin dariyar nan,Karaf idanunta suka haɗu dana Sgr,ɗagowar shi kenan yayi arba da ita,gabanta ne taji ya faɗi rass saboda fuskarshi a murtuke take ba annuri,nan take dariyar da takeyi ta koma ciki,ganin ta zuba mashi ido,yasa shi jefa mata harara,a hanzarce ta kawar da idanunta daga kallon fuskarshi da take yi,jikinta kuma yayi sanyi,ta shiga tambayar kanta dalilin hararar da taga big bro yayi mata,kodai baya farin ciki ne da kasancewarta JININ SA!?tabbas hakan zai iya faruwa,Wataƙil kodan ya saba ganinta a matsayin ƴar aikinsa,baiwarsa,ƙasƙantacciya shiyasa yanzu Yake nuna 6acin ranshi don yana ganinta tamkar a matsayi ɗaya suke dashi,Ƴa'ƴan Wa da ƙani,da alama hakan baiyi masa ba,
"Idan har dagaske ne abunda nake hasashe,insha Allah zan tattara na bar masu gidan,saboda bana son 6acin ranshi,zan iya yin komai don farin cikin shi," ta ƙarasa zancen zucin nata tare da sake ɗagowa a hankali don ta saci kallonshi,adai dai lokacin shima ya ƙara ɗagowa da kyawawan idanuwanshi kai tsaye suka shiga cikin nata,nan take taji gabanta ya kuma faɗuwa rass,kasa janye idanuwanshi yayi daga kallonta da yake yi,a yayin da yake jujjuya spoon ɗin dake hannunsa acikin plate ɗin abincin gabansa,har Yanzu bai daina mamakin kasantuwarta ƴar uwarshi ba,ta jininsa,tamkar a mafarki haka yake ganin abun,ganin ta zuba mashi ido batare da ta janyesu ba yasa shi ɗaure fuskarshi yasha murrr,saboda kada ma yarinya taga fuska har tayi tunanin raina sa don tasamu matsayi,
"U will still remain who u are,wadda take aiki a ƙarƙashina,Matsayin dana baki kenan,"ya fada a ransa
Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"bazasu kara wahala ba,bazan ta6a bari hakan ya faru ba,tunda dae har yaran nan suka bayyana a matsayin ƴa'ƴana,In sha Allah bazan ƙara bari suyi aikin wahala ba,ko cokali bazan ƙara bari ɗaya daga cikinsu ta ɗauko ba acikin gidan nan,rayuwar hutu kawai nake so suyi rayuwar ƴanci," ya ƙarasa zancen zucin nashi a yayin da yake bin kowaccen su da kallo cike da so da ƙaunar ƴa'ƴan nashi,'
Janye idanunshi yayi daga kan nata,kafin ya miƙa hannu tare da ɗaukar Glass cup mai ɗauke da abun sha me sanyi ya kai shi saitin mouth dinsa yana sipping ɗinshi anatse,yayin da sanyin lemun ke ratsa throat ɗinsa,a hankali ya lumshe idanunsa tare da ɗan ware su kaɗan,again suka ƙara sauka akan na sehrish a karo na uku kenan,agaggauce tayi hanzarin janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan plate ɗin abincin dake a gabanta,
Hannu Sgr ya sanya tare da yago tissue ya goge bakinsa,kafin ya miƙe tare da juyawa ya nufi upstairs,Miƙewa Marshal yayi da alama shima ya kammala breakfast Ɗin nasa,shima upstairs ya nufa,
Fitowar Hajiya azeema keda wuya daga cikin bedroon ɗinta,ta jiyo muryar gwaggon katsina tana ta faman sambatu tana cewa"Tsiyarta kenan mutun yazo gidan ƴan gayu,Ni bazan iya rayuwar turawan nan ba,taya za akai ma mutun salalar biredi tare da tea rabin kofi kamar wata ƴar iska ace in sha"?
Tafiya take tana sambatu zaninta a hannu sai ɗan undi ajikinta,kanta kuwa ta kifa wannan ɗaurin ɗan kwalin nata mai kama da helmert,
har zata gifta hajiya azeema tayi gyaran murya tare da ambaton sunanta"Goggo," fuska a yamutse ta juyo tana kallonta,dawowa tayi daga gefenta suna fuskantar juna tace"Yawwa azeema,wai nikam inaso in tambayeki,'
Natsuwa hajiya azeema tayi tare da cewa"ina sauraronki gwaggo,"
"Jiya nayi wani mafarki,ƴa'ƴan abusufyan sun bayyana,wasu ƴan uku kyawawan gaske,da nayi tunanin koda gaske ne abun ya faru amma daga baya na gane ba gaskiya bane,in ba haka ba,yaushe abusufyan ya ta6a yin aure"? Tayi tambayar tana kallon hajiya azeema,wadda ta saki baki tana kallon gwaggon,
Ganin azeema tayi sototo tana kallonta yasa tayi tunanin cewa ko abunda ta faɗa ya bata mata rai ne,
"Nasan dole kiyi mamaki kema,Mafarkin fa kamar dagaske,ɗaya daga cikinsu har tana sharara mana labarin ƙarya waisu ƴa'ƴan wata zainabu ne,kuma ma acikin labarin hada wata hajiya Ameena,in banda shaiɗan ina abusufyan ina ƴa'ƴa"?
Ƙiris ya rage Azeema ta fashe da dariya agaban gwaggon katsina,ganin yadda ta haƙiƙance tana kora mata bayani,kuma babu alamun wasa a fuskarta,
Ƙunshe dariyar bakinta tayi tare da basar da ita tace"Gwaggo Anya kina shan maganinki kuwa?ina Dr harris yake?gaskiya inason ganinshi,'
Tsoki gwaggon katsina taja tare da cewa"Harrisun daya zama ɗan iska,"
Waro ido waje azeema tayi tace"gwaggo harris ne ɗan iska"?
ta6e baki tayi tare da cewa"Zan masa ƙarya ne?ba ɗan cikina bane"?nasha wahalar yima yarona tarbiya amma waccen sauden.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,zanin hannunta takai saitin idonta tana ƙoƙarin goge hawayenta,
Zuru harris yayi wanda fitowarshi kenan kuma atare da saude suka fito,jin maganar gwaggone ma yasa yayi hanzarin cire hannunshi daga cikin na sauden,
Hajiya azeema tace"gwaggo faɗamun me harris ɗin ya akaita,?
Hankali tashe Saude tace"ya harris pls kada ka bari gwaggo ta faɗa mata abunda muka aikata,kasan gwaggo yadda take ɗaukaka abu,inta tashi faɗi saita ƙara ma miya gishiri,'
Dr harris yace"just don't worry ur self,insha Allah bazata faɗa mata ba,"
Faɗin hakan keda wuya gwaggon Katsina tace"Azeema abun da ciwo,yanzu yunwa nake ji,shiyasa ma kika ga nafito ina sambatu,Wurin waccen matar zani,wlh ba azmee ba Allah yasa ramadan ce ita yau saina zazzaga mata rashin mutunci!Ni zata raina ma hankali tunda safe,takawo mun tea rabin kofi da salalar biredi wai in fara da wannan,don ta raina mun hankali,nayi mata kama da kusu ne?
Rai a6ace tayi maganar,aikuwa atare haris da saude suka fashe da dariya,a hanzarce ta juyo sakamakon jin sautin dariyar tasu,nan take ta tsuke fuska ganin shi tare da saude,
Murmushi Hajiya azeema tayi tare da cewa"haba gwaggo baki fahimce ta bane,cewa fa tayi ki fara da wannan tana nufin kafin ki tashi fitowa zuwa yin breakfast ɗin,yanzu haka yana can an shirya mana mu kawai ake jira muje muci namu kalacin,"
Hajiya azeema ta ƙarasa maganar tare da ruƙo zanin hannun gwaggon tace"Bari na taimaka maki ki ɗaura shi,"
Girgiza kai tayi tare da cewa"Barmin shi a hannuna,nafison inji iska na shiga ta ko'ina,"murmushi hajiya azeema tayi kafin tace"hakan ma yayi gwaggo,ae under skirt din ma bamai sharashara bane,yana da kauri,amma duk da haka dae ki ɗaura zanin yadda zaki fito da kyau tunda ga rigarshi kin sanya ajikinki,Kuma kinga Abusufyan na nan,Ga kuma ƴa'ƴansa,bazasu so suga gwaggonsu a haka ba,"
wani irin ƙayataccen murmushi gwaggon katsina tasaki tare da cewa"Kenan dagaske ne Mafarkin da nayi jiya"?
Jinjina kai Azeema tayi tace"Ae suna nan,duk abunda ya faru jiya dagaske ne,ba mafarki kikayi ba,agabanki akayi komai kin dai shafa'a ne,'
Jin haka yasa tayi saurin mayar da zanin ajikinta tana ɗaure shi tana cewa"Allah sarki ƴa'ƴan abusufyan ɗina,bayin Allah,sunsha wahala a hannun wannan fasiƙin mutumin baƙin shaiɗani,Allah mutumin nan ƙaho ne kawai bai fito masa aka ba,amma ina tantama anya ba Irin shaiɗan bane"?
"gwaggo kidaina maganarsa ma,Ni wlh ko zancen shi ma bana so anayi,Na tsani mutumin nan kamar yadda natsani mutuwa ta,"acewar hajiya azeema,tayi maganar ne a yayin da take kama hanyar Zuwa Dining area ɗin nasu,bin bayanta Gwaggon tayi tana cewa"Ae ko sai dai ki toshe kunnanki,don zancen sayyadi ya zama dole,in har ba'a kawo min kansa ba,bazan daina faɗan sunan shi ba,'
Murmushi kawai hajiya azeema tayi,atare suka ƙarasa dining area din,
Gaggaisawa suka fara yi da junansu,su jahad na ganin saude suka tashi atare suka nufe ta,dama Jiya basu samu damar gaisawa da ita ba,saboda yanayin da suka shiga gaba ɗayansu,haɗasu tayi ta rungume ajikinta,cike da farin ciki tace"Ina tayaku murna sosai,nayi farin ciki sosai,Ya harris ya sanar dani komai agame daku,ashe ku jininsu ne,'ta ƙarasa maganar ayayin da take raba jikinta daga nasu,kowannansu fuskarshi ɗauke da murmushi,Jahad tace"Aunty saude kinga ikon Allah ko?munsha wahala sosai,mu kanmu bamu ta6a tunanin cewa muna da dangi ba,amma sai gashi ƙaddara ta haɗamu da ya Omar,Ita kuma ƴar uwarmu Sehrish ƙaddarar aikine ya kawota gidan nan,Muna tare da ƴan uwanmu ba tare da mun sani ba,sae gashi rana ɗaya Allah ya bayyana mana komai,'
Saude tace"Congratulations Once again,ina ƙara tayaku murna sosai da kuka fito daga tsatson wannan Family ɗin,abun alfahari ne wannan"kafin ta mayar da idanunta kan Hosana,Cike da zolaya taja kumatunta tare da cewa"Hosana Kinga yadda kika canza?kamar ba wannan Sha takwas sha taran ba,mai ɗan kai,kinyi kumatu kamar Balon balon,Ga haske gaskiya ya Omar ya Iya raino,"
Fashewa da dariya hosana tayi tana faman sunnar dakai,
"Kiyi ma sister ɗinku mana,Ita bazata taso mu gaisa ba"?tayi maganar tana kallon sehrish dake zaune,tana faman kallonsu ɗaya bayan ɗaya,
Murmushi jahad tayi tare da juyawa tayi mata alamar ta taso da hannunta,
Miƙewa sehrish tayi tare da nufar inda suke,koda ta ƙaraso saude ta sanya hannu tare da janyota ta rungumeta,kafin ta raba jikinta dana sehrish tace"Masha Allah,gaskiya ban ta6a ganin triplet,masu kama iri ɗaya sak kamar taku ba,ina taya ki murna sosai da Allah ya haɗaki da ƴan uwanki,da kuma mahaifinku,da kuma danginku,'
Fuskar sehrish ɗauke da murmushi tace"Ngde sosai,"
"Allah ya tsare mana ku,Ya Albarkaci rayuwarku ya kuma kare ku daga sharrin maƙiya,'
Atare suka amsa mata da Ameen,bama su kadae ba,hadasu Abba dake sauraron maganganun nasu,
Kamar yadda Abba yayi alƙawarin shirya gagarumar walima na bayyanar ƴa'ƴan ƙaninsa Abusufyan,Da kanshi ya fidda date ɗin da za'a gabatar da ita,Kuma tun aranar ya fara kiran Ƴan uwa da abokanan arziƙi yana sanar dasu game da ƴa'ƴan abusufyan da suka bayyana,Babu wanda bai bari ba,kowa kira yake tun daga kan danginsu na Zaria,na damaturu dana sauran states ɗin da kuma waɗanda ke zaune Ƙasashen waje,kowa saidaya sanar mawa,Bayan Abbas ya koma gidane da safe Amani ke tambayarshi meya faru ne jiya ya hanasu zuwa gidansu,Anan ya kwashe duka abunda ya faru game da su Sehrish ya sanar mata,wani irin farin ciki ne ya cika ta,Ba don komai ba sai don sanin cewa plan ɗin Aunty babba ya gama Tarwatsewa,ae tunda taji cewar ƴan mata ne kuma sun kai shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas kyawawan gaske,Nan fa ta kwashe da dariyar mugunta aranta tana cewa Naga yadda za'ae Aunty laila ta cimma burinta,Gida bai ƙoshi ba taya za'a ba na waje,Ae tuwona maina za'ayi,Haba ae xance ya ƙare,
ita kanta Amani ta ƙosa ranar walimar tazo saboda suje gidan,saboda taji cewar Aranar Aunty babba da hafsat zasu zo Abuja,babban burinta taga tashin hankalin da aunty babba zata fuskanta inta gansu,
Ranar walimar kuma yayi dai dai da ranar da Ammi zata zo,tare da wasu daga cikin danginsu,haka zalika captain Najeeb da kuma Talal suma duk a ranar zasu dawo gida,ba don komai ba sai don su sanya ƴa'ƴan uncle ɗinsu abusufyan acikin idanunsu,Kowa ɗokin ganinsu yake yi kamar kamar me,musamman da sukaji irin rayuwar da yaran sukayi a wulaƙance sai suji wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu ya shiga cikin ransu,kuma duk aranar MG Osman da kuma Captain Adam suma zasu dawo gida,wanda tun dawowarsu daga U.s suka tafi sada zumunci,Gaskiya wannan Babbar rana ce,Hakan yasa ma Zamuyi shiri na musamman ni da makaranta littafina don mu halarci gidan amatsayin gayyar soɗi tunda ba'a gayyace mu ba,Sa kaine kawai,
Cikin ƴan kwanakin nan wata irin rayuwar farin ciki suke gudanarwa tare da Daddynsu,kullum yana manne dasu,Da kanshi ya zauna yayi masu kitson kalaba guda bibbiyu akansu kamar yadda ya ta6a yi masu suna yara,koda yazo kan Sehrish,Cike da mamaki yace"Ya akai naga gashin kanki guntu?ko kinyi wani ciwo ne dayasa aka datse maki gashin,"girgixa kai tayi tare da cewa"a'a Laifi nayi ma Babba yaya shine ya yanke mun gashin da almakashi,"
da buɗar bakin Abusufyan sai cewa yayi"Yayiwa kanshi ai," murmushi sehrish tayi duk da batasan me daddyn nasu yake nufi da hakan ba,duk a wannan kwanakin basu je school ba,Abusufyan da kanshi yace kada su damu shi da kanshi zai kaisu makarantar don karma a tuhume su,
A 6angaren Sir Commander haroon kuwa,tamkar munafuki haka ya koma acikin gidan,ba kowa ma ke sanin lokacin da yake shigowa gidan ba,da kuma lokacin da yake fita,Da alama dae akwai wani abu da yake shiryawa a 6oye,
*AMRISH*
Zaune take acikin class ɗin gaba daya ta shiga damuwar rashin ganin Sehrish kwana biyu ko layinta ta kira bata samu,hatta wayar junaid ta jaraba kira shima ba'a ɗagawa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,tagumi tayi idonta cike tab da hawaye saboda damuwar da take ciki,taso ace sehrish na nan atlease zata ɗebe mata kewa,tana cikin wannan tunanin har malam ya shigo cikin class ɗin nasu bata sani ba,bayan ya kammala amsar gaisuwa daga wurin student din,kai tsaye ya ƙarasa seat ɗin da Amrish take,hannun shi yakai wanda ke ruƙe da maker ya ɗan bubbugi desk ɗinta,a firgice takai idanunta akanshi,Yunƙurawa tayi tare da miƙewa ganin Ya mu'allim,wanda tun ranar daya ba sehrish Ruwan addu'ar nan bai ƙara zuwa makarantar ba,duk da sun samu labarin cewar Ya tafi Umra ne,shiyasa aka musanya masu shi,
Murmushi ya ɗan saki afuskarshi yana kallonta yace"tunanin me kike yi ne?har na shigo cikin class ɗin baki sani ba?
Muryarta na rawa tace"Ayimun afwa ya mu'allim,Bana jin daɗi ne bansan ka shigo ba,
Jinjina kanshi yayi tare da ɗan kai idanunshi kan Seat ɗin sehrish yace"Ina yarinyar nan take?ƴar family ɗin Salahuddeeen hussein naga kamar bata a class ɗin"?
fuskarta ɗauke da damuwa tace"Batazo ba,yau kusan kwana huɗu kenan bata zo school ba,kuma nayi trying kiran layinta amma bana samu,har brother ɗinta na kira,shima layinsa ba'a samu,'
Jin hakan yasa shi fargabar to kodai wani abu ya faru da yarinyar?Yaso yaji ya tayi da ruwan addu'ar daya bata,shin tasha ko bata sha ba?
Jinjina kanshi yayi tare da juyawa yace"Allah yasa dae lafiya,in har batazo ba,zuwa sati mai zuwa zan je gidansu don na binciki dalilin rashin zuwan nata,'
Jiki asanyaye Amrish ta koma ta zauna,saman seat ɗin nata,jikinta har ya fara kerma saboda tsoran kar ace wani abune ya faru da Sehrish,
A ƙarshe dae ta yanke shawarar neman gidansu don taje ta ganta da kanta.
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_
*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*
*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅
Bismillah
❤🤍❤
A hankali ya tura ƙopar bedroom ɗinsa tare da shigewa ciki,turus yayi ya tsaya yana kallon junaid dake manne da Mommynsu suna bacci yadda kasan wani jinjiri ya ƙanƙame ta sae faman sharar bacci suke yi atare,murmushi ya ɗan saki tare da wuce wa cikin bedroom ɗin,Rage kayan jikinshi yayi bayan ya kammala ya shige cikin toilet,Within 15mins yayi wanka,sae gashi ya fito ɗaure da towel,tsaf ya kammala gyara jikinshi agaban dressing mirror,kafin ya koma wurin Closet ɗinshi,ya ɗauko wasu lallausan kayan bacci riga da wando farare ya zura ajikinshi,bayan ya kammala shirin kwanciya,ya zagaya ta baya dai dai saitin da junaid yake manne da mommyntasu ya lalla6a tare da hayewa saman gadon,zuba mata ido yayi yana kallonta,kullum koma mashi takeyi tamkar sabuwar amarya,ji yake kamar ma ba'ajima da yin aurensu ba,saboda tsabar son da yake yi mata,ba ƙaramin kewar matar shi yayi ba,har yanzu bai kammala hucewa ba,tunda tadawo kullum da daddare suna manne da juna,a kwanakin nan ba ƙaramin kwanciyar hankali ya samu ba,ya zama cikakken mutun don rashin Alexandra ba ƙaramin gibi yayi mashi ba,kasa janye idanunshi yayi daga kallonta da yake yi,tayi wani irin haske mai kyan gaske,fatarta kamar ta jinjiri saboda tsabar sheƙin da takeyi da daukar ido,bin dogon gashin kanta yayi da kallo wanda ya baje agadon bayanta,a hankali ya mayar da idanunshi akan farar half vest ɗin dake ajikinta,nan take ya fara shiga yanayi na buƙatarta,ga kuma junaid ya riga shi,to ya kenan?
ƙasa ƙasa yayi da muryarshi dai dai saitin kunnan Junaid ya ambaci sunan shi a hankali"Junaid!junaid!tashi ka koma bedroom ɗinka,"yayi hakan ne saboda baison ya tashe ta,yasan inta farka ba lallai tabari ya rabata da junaid ba,jin shiru junaid bai motsa ba yasa shi ƙara ɗan ɗaga muryarshi yace"junaid!junaid!pls get up and go back to ur bedroom,inaso in kwanta ne!"
Shiru junaid ba alamun ma zai farka,hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarshi yace"Junaid!junaid!Ka tashi mana!!"
Duk wannan suratan da Abbansu keyi kaf a kunnan junaid,sarai yana jinshi yayi banza dashi,tun kiran farko da yayi mashi ya farka,koda yaji Abbansu na cewa ya tashi ya koma bedroom ɗinshi zai kwanta,sai ya ƙara ƙanƙame mommyn tasu,don yaci alwashin cewa yau fa abbansu bazai kwana tare da mommynsu ba,ba don komai ba sae don shi aganinshi Abbansu baiyi mashi adalci ba,don me zai dinga kwana tare da Mommynsu bayan shi ne ya dace su dinga kwana tare da ita,Saboda tafiyar da tayi ta barshi tun yana jinjiri,yanzu lokacin shi ne bana abbansu ba,dole ya haƙura yabar mashi,Tashin hankalin da ba'a sama shi date!
"Junaid!nafa son cewa kana ji na,kayi banza ka ƙyale ni!zaka tashi ko saina yi wurgi dakai,"a faɗace Abban nasu yayi maganar yana kallonshi,
turo baki junaid yayi cikin ƙunƙuni yace"Abba,wlh ba inda zani!yau kwana na ne,"
Har saida gaban Abbansu ya faɗi rass saboda yadda maganar ta junaid ta dirar mashi a kunnanshi,Cike da mamaki ya maimaita maganar "yau kwanana ne!"!
Junaid dake maƙale da Mommynsu yace"eh,abba kadaina ma wahalar da kanka,Allah yau ba inda zani,kullum sai kayimun wayau,kana kwana tare da mommy,fisabilillahi Ni da kai waye ya dace ace yana kwana tare da Mommy!!!?
Saboda tsabar takaici sam abbansu ya rasa me zaiyi ma junaid,gashi babu mabugi a kusa balle ya kwaɗe shi,ko ya samu sanyi aranshi,
Ganin junaid ya turje bilhaƙƙi dagaske yake bazai tashi ba,gashi kuma Alexandra tafara mutsu mutsu alamun suna takura mata,kuma baiso ta farka daga baccin saboda gudun karta hanashi kora junaid izuwa bedroom ɗinshi,hakan yasa ya yanke shawarar binshi ta lalama,
Sassauta muryarshi yayi tare da cewa"Pls babyn abbansa,abeg dan Allah ka tashi ka koma bedroom ɗinka,help ur dad pls,bakasan halin da nake ciki ba,pls junaid ɗin Abbansa,"
Ƙara ƙanƙame Mommynsu yayi tare da cewa"wlh Abba dama kadaina yi mun magiyar nan,ni yau tare da mommyna zan kwana,"
Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"to ni a ina kakeso na kwana?junaid baka tausayin Abbanka ko?meyasa zakayi mun haka?yau kuma rigimar akaina zata ƙare"?
ashagwa6e junaid yace"Abba,gaskiya kayi haƙuri nidai babu inda zani,kaje bedroom ɗina ka kwana mana,'yayi maganar tare da ƙara shigewa jikin Mommyn tasu,
Rai a6ace Abba yace"Don ubanka zaka tashi ko bazaka tashi ba!!"?
shiru yayi bai tanka mashi ba,sae ma minsharin ƙaryar da ya dinga ja,don abban nasu yasan cewa bacci ya ɗauke shi,
A daddafe Abbansu ya miƙe daga zaunen da yake gefen gadon,ranshi duk a jagule kamar ya aza hannu aka ya fasa ihu haka yake ji,shi kaɗae yasan halin da yake ciki,bai ta6a sanin cewa junaid bai da wayau ba sae yau,duk yasa ya zama abun ban tausayi,hawaye ne kawai bai zubar ba,amma ba ƙaramin 6ata mashi rai yayi ba,ya jima yana zagaye a cikin bedroom ɗin,yana kallonshi,a ƙarshe ya nufi ƙopar bedroom ɗin tare da buɗewa ya fuce waje,
"Gobe ma anan zan kwana,"junaid ne yayi maganar bayan jin fitar abban nasu daga ɗakin,
"Daughter"! ƙiris ya rage ta saki tray ɗin dake hannunta,don bata tsammaci jin muryar mutun a bayanta ba,bakowa bace wannan face Sehrish wadda ke tsaye a cikin kitchen tana shiryama Sgr fresh fruits tare da coffee,jikinta na sanye da doguwar riga ta bacci mara nauyi milk colour tayi rolling mayafi akanta launin baƙi,
Ganin daddynsu yasa ta sakin murmushi tare da cewa"daddy,dama idonka biyu bakayi bacci ba har wannan lokacin"?
ƙarasa shiga kitchen ɗin yayi yana cewa"taya zan iya baccin?bayan ɗaya daga cikin ƴa'ƴana idonta biyu bata runtsa ba,raina ne ya bani cewar akwai wadda batayi bacci ba acikinku shiyasa na fito don inga wacece ashe kece...."
fashewa da dariya sehrish tayi jin abunda yace,shima dariyar ce ɗauke a fuskarshi,
..tsayawa yayi dab da ita yana kallon kayan marmarin da ta kammala Jera ma sgr,ta gyare tsaf ta yayyanka mashi su,
"Yanzu wannan kayan daɗin duk na wanene?ko ke zaki sha"?yayi tambayar a yayin da yakai hannunshi cikin ƙayataccen tray din wanda ke ɗauke da plate na kayan marmarin ya ɗauki yankin abarba ɗaya tare da turata abakinsa yana sha,
"Bani zan sha ba,na babban yaya ne,"tunkan ta ƙarasa maganar taga ya dakata da taunar abarbar da yake yi yana kallonta fuskar shi ɗauke da mamaki yace"Kina nufin Rafayet kika shiryama wannan?shiya sanyaki ne"?
Jinjina kai tayi tare da cewa"eh daddy,shine ya buƙaci na dinga kai mashi fruit tare da coffee adai dai irin wannan lokacin ƙarfe sha biyu na dare in sun dawo daga aiki....'daƙyar ta ƙarasa maganar ganin yadda fuskarshi ta canza,alamar wani abu baiyi mashi daɗi ba,
"Daddy wani abu"?ta furta hakan tana kallonshi,
shiru yayi jimmm kamar mai nazarin wani abu,kafin daga bisani yace"da sanin Abbanku"?
girgiza kai tayi alamar a'a sannan ta ƙara da cewa"yasan cewa inayi mashi aiki daddy,amma banda tabbacin cewar ko yana da masaniya akan hakan,bansani ba ko babban yayanmu ya sanar dashi,'
ta6e baki Uncle abusufyan yayi kafin yace"Abba bazai ta6a bari ba,bana tunanin cewar ya sani,taya mace kamarki zata dinga zuwa ɗakin namiji a irin wannan lokacin!!?
Gabanta ne taji ya faɗi rass,sunnar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannnunta,
"That's imposssible!!!Banaso gaskiya hakan bai kwantamin araina ba,duk da ɗan uwanki ne shi a yanzu,amma hakan bai dace ace kina zuwa ɗakinshi ba a irin wannan lokacin,in fact ba'a son mace da namiji suna ke6ewa,nasan kinsan da wannan!"
Muryarta na kerma tace"Hakane daddy,
Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Yawwa,ɗauki kayan marmarin ki kai masa,kada ki makara,"
Hannunta na kerma ta ɗauki tray din da sauri da sauri ta nufi hanyar fita daga kitchen ɗin,har ta kusa fita daga cikinsa,muryarshi ta dakatar da ita,
"Sehrish,"
"Na'am daddy,"ta amsa mashi tare da ɗan juyawa ta baya tana kallonshi,
"daga yau!banaso ki ƙara zuwa don kiyi mashi aiki,koda da safe ne ko da rana,Azmee itace mai aikin gidan nan,idan ma da buƙatar masu aikin zansa a ƙaro wasu,amma ba zakuyi aiki wa kowa ba,ina fata kin fahimce ni,'
Tunda abusufyan ya fara maganar gabanta ya shiga faɗuwa,hankalinta yayi mugun tashi,tuni idanunta sun fara canza launi,
Fuskarta ɗauke da damuwa tace"daddy,inajin tsoran shi sosai,bansan taya zan sanar dashi hakan ba,'
Murmushi Abusufyan yayi tare da takawa kusa da ita suna fuskantar juna yace"Bance ki sanar mashi ba,kawai inaso daga yau ki ɗan ɗaga ƙafa daga zuwa part ɗinsa don kai mashi abinci ko yi masa gyara,nasan cewa bazai damu da hakan ba,tunda ga azmee,in ma yayi magana akan hakan ki sanar dashi cewa"NI NA HANAKI!"
wani irin wahalallen yawu Sehrish ta haɗiye a bakinta,sam bazata iya yima daddyn nasu gardama ba,tasan cewa yayi hakan ne saboda tausayinsu da yake ji,baison suna aikin wahala,amma wannan hukuncin da ya yanke mata ba ƙaramin horo bane agareta,Na farko hakan zai nisanta tsakaninta da SGR,ganinshi zaiyi mata ƙaranci,in har ba downstair ya sauko ba,Allah ya haɗasu to bafa zata samu damar ganinshi ba,Abu na biyu kuma hayaam zata samu damar shige masa,don tasan cewar daga ta daina yin aiki a ƙarƙashinsa,hayaam zata kunno kai,na uku kuma batasan me zai biyo baya ba,in har yasan cewar ta daina yi mashi aiki,Shin zai damu ko bazai damu ba.....'
"Zaki iya tafiya,kada ki jima a bedroom ɗin nashi,dare yana ƙara yi,da zarar kin kai mashi,kiyi hanzarin komawa cikin ƴan uwanki ki kwanta kiyi bacci ki huta,
"Toh Abba,zanyi duk yadda kace,"
Murmushi abusufyan ya saki tare da cewa"ki kulamin da kanki daughter,sai da safe,"
murmushin tayi itama bayan ta amsa mashi,batare da 6ata lokaci ba,ta wuce sashen Sgr,kamar wadda aka zare ma lakar jikinta haka take tafiya,ba don komai ba sai don Hukuncin da Daddy ɗinsu ya yanke,Taya zata iya rayuwa batare da tana sanya babban yaya acikin idanunta ba akai akai!anya kuwa zata iya jurewa?wa zai kula mata dashi kamar yadda take kula dashi?tashin hankalin da ba'a sama shi date,
Wani irin farin cikine ya lullu6e hayaam dake la6e wurin kitchen ɗin tana sauraron abunda Uncle abusufyan ya tattauna tare da sehrish,kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha don tsabar farin ciki,ashe munafukar tana la6e ta kasa kunne tana sauraronsu,bakomai ya fito da ita ba daga ɗakinta face yunwar da taciyota,hakan yasa ta lalla6a ta fito don ta sama ma kanta abunda zata ci,anan ne fa tajiyo muryoyinsu suna magana acikin kitchen ɗin,shine tayi masu la6e,ta kwashe duk abunda suka tattauna acikin kunnanta,Lokaci guda ta manta ma da yunwar da take ji acikin cikinta,gudu gudu sauri sauri ta koma bedroom ɗinta,faɗawa tayi saman gadonta tana faman tiƙar dariya,bayan ta tsagaita da yin dariyar tashiga tufka da warwara acikin zuciyarta,
"Idan har inaso in samu nasarar cigaba da zama acikin gidan nan,dole saina haɗa kai da wani!wanda zai taimaka mun,wurin ganin na cimma burika na!tabbas ina bukatar shi,"ta ambaci hakan ayayin da take ƙoƙarin miƙewa daga zaune,
*WANENE SHI*!?
*Surgeon General Rafayet*
A ƙopar shiga bedroom ɗinshi ta tsaya,zuciyarta duk a ƙuntace take,don idanunta acike suke tab da hawaye ba don komai ba sai don hukuncin da daddynsu ya yanke agame da zuwanta part ɗin SGR,yanzu shikenan Yau zata kasance rana ta ƙarshe da zatayi aiki a sashen shi?shikenan bazata ƙara takowa ba da sunan ta kula dashi ba? 😥
Tamkar ta fashe da kuka haka ta dinga ji,dakyar ta daure ta cije tare da zuba sallama,shiru ba'a amsa mata ba hakan yasa ta ƙara daga muryarta,ta kuma zabga sallamar akaro na biyu,shima shiru bai amsa mata ba,hakan yasa ta fara tunanin cewa kodai yayi bacci ne ko kuma yana acikin toilet,don tasan shi akwai yin wankan dare duk in xai kwanta,
Tunani tayi ai shi muharraminta ne a yanzu hakan yasa ta kutsa kai tare da shigewa cikin bedroom ɗin nasa,wani irin daddaɗan kamshi ne ya daki hancinta,mai daɗin gaske,ga ratsa zuciya,lumshe idanunta tayi a hankali tare da sake buɗesu,tana ƙare ma shimfiɗeɗen gadon nashi kallo,kasa janye idanunta tayi daga kallon shi da takeyi,Yana a kwance saman gadon,yayi covering jikinshi da lallausan blanket ɗinsa,dai dai saitin stomach ɗinsa bargon ya tsaya,sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi da alama dae a gajiye suka dawo yau,baccin ma kamar bai shirya mashi ba ya ɗauke shi,duba da yadda yayi kwanciyar,right hand ɗinshi na asaman kanshi ya zagayo dashi ta dayan 6angaren,
A hankali sehrish ke nufar gadon nasa tana tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa akai,saboda rashin kwarin jikinta,ajiye mashi tray din tayi asaman side table ɗinsa,sannan tashiga tunanin,kodai ta tashe shi daga baccin kota ƙyale shi?ta jima tana nazari kafin zuciyarta ta bata shawarar cewa ta tashe shi kawai,ganin cewa ba kayan bacci ne ajikinsa ba,hakan na nufin baiyi night bath ɗin daya saba yi ba,tabbas bazaiji daɗin baccin shi ba,
Zuba mashi ido tayi tana ƙare mashi kallo,anan taga zufa na tsattsafowa a saman dogon hancinsa,da kuma wuyansa,mamakine ya kamata,aranta tace"Zufa kuma?duk da sanyin A.c dake akwai?karfa ace babban yaya bashi da lafiya"?cike da damuwa tayi tambayar,can kuma tace"kodan baiyi wankan daren daya saba yi bane?zai iya yiyuwa hakane,amma fa ina tsoran tashin shi daga bacci,
Bari dai kawai na haƙura kar in jama kaina,don na lura kwanan nan ɗaure mun fuska yake yi,kamar nayi masa wani laifi,'
Tana kai ƙarshen zancen zucin nata,tayi wani kwakkwaran juyi da nufin tabar wurin,cikin rashin sani tayi tuntu6e da doguwar ƙafarsa ɗaya data sauko ƙasan gadon,birkicewa tayi duk yadda taso ta ruƙe jikinta amma abun ya faskara,gaba ɗaya ta tafi ɗungurugum ta faɗa saman jikinshi,
Hankali a matuƙar tashe Sehrish ta zazzare idanunta tana kallon fuskarshi,gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,ganin ya fara motsa idanunshi yasa ta soma kiciniyar miƙewa daga saman jikinsa,sae dai kash bata samu wannan damar ba domin kuwa Sgr harya ware kyawawan idanuwanshi,biji-biji ya dinga ganinta acikin idanunshi,ita kuwa tuni jikinta ya shiga kerma,a hankali yakai hannunshi tare da ɗan Murza idanunshi,kafin ya ƙara ware su da kyau akanta,gaba ɗaya duk tabi ta rikice tuni zufa ta fara tsattsafo mata,ganin cewa dagaske dae ita yake kallo yasa ta ambaton nashiga uku,a hanzarce ta bar jikinshi ta sauka daga saman gadon,la66anta na rawa tace"dan Allah kayi haƙuri babban yaya,wlh ba yin kaina bane,na kawo maka fruits ne kuma banyi niyyar na tashe ka ba,tuntu6e nayi da ƙafarka na faɗo saman jikinka.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda wani irin kallo da taga yana jifarta da shi,sunnar da kai ƙasa tayi tana faman wasa da yatsun hannunta dake ta faman kerma,
"Kneel down," ya furta da wata irin kasalalliyar murya ta wanda bacci bai ishe shi ba,
cikin sauri Sehrish ta zube saman guiwowinta agaban gadon nashi,
"Ur Hands up and close ur eyes," yayi maganar yana yi mata nuni da hannunshi,
Jiki na rawa ta ɗaga hannayenta sama tare da kulle idanunta,sosai ta rufe su,tana matsar kwalla,
"Kada kiyi attempting buɗe idanunki,ko sauke hannayenki if not kinsan mai zai biyo baya,'
Muryarta na kerma tace"bazan buɗe ba,'
"Gud," ya furta hakan a yayin da yake cire blanket ɗin dake rufe da jikinsa,a hankali ya sauko daga saman gadon,tsayawa yayi yana rage kayan jikinsa,sae da ya rage daga shi sae short,sannan ya wuce cikin toilet ya rufe ƙopar,
Saboda tsabar tsoro batama san cewa Sgr ya shiga toilet ba,sae faman shessheƙar kuka takeyi,after some minutes ya fito daga cikin toilet ɗin nasa,jikinshi sanye da bathrobe white colour,gaban dressing mirror ɗinshi ya zauna,ya shiga shafe jikinshi da mai,bayan ya kammala ya feshe ko'ina tass da tsadaddun tururrukan jikinshi,nan take ƙamshin ya gauraye ko'ina na cikin bedroom ɗin,ya jima agaban mirror ɗin kafin ya yunƙura tare da miƙewa ya nufi can cikin bedroom ɗin wurin Closet ɗinshi,
Almost 30mins Sehrish tayi zuƙunne saman guiwowinta jikinta na kerma,
dawowa yayi jikinshi sanye da nigh dress masu kyan gaske,
Wuri ya samu ya zauna daga gefen gadon yana fuskantarta,a hankali ya miƙa hannunshi tare da buɗe side drawer ya ɗauko wannan hoton da Uncle ɗinsu Abusufyan ya ta6a basu lokacin da suna ƴan shekara sha a duniya,zuba ma hoton ido yayi yana ƙare mashi kallo,kafin ya ɗago da idanunshi ya azasu akan fuskar sehrish yana kallonta,da alama nazarin wani abu yake yi a fuskarta da kuma fuskar ƙaramar yarinyar dake acikin hoton hannunsa,so yake ya gano wacece yarinyar dake acikin hoton nan,ƴar ƙaramar yarinya wata zararriya da ita,gashin kanta duk ya tarwatse ya yamutse yayi datti babu gyara,kayan jikinta duk sun fita hayyacinsu sun yage,ga ƙafafunta ko takalma babu,fuskarta kuwa duk tayi jaga jaga da majina,hoton yayi confusing ɗinshi,kokwanto ya shiga yi anya itace a cikin hoton?kodai ɗaya daga cikin ƴan uwanta ne,
"Open ur eyes,"
Jin muryarshi yasa tayi saurin buɗe idanunta wanda ke fitar da kwalla,muryarta na rawa tace"babban yaya dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba,"tayi maganar tana faman shassheƙar kuka,
Miƙa mata hoton hannunshi yayi tare da cewa"Who is she"?
hannunta na kerma ta kar6i hoton daya miƙa mata,Ƙura ido tayi tana kallon hoton,nan take tashiga tambayar kanta ina Sgr ya samu hoton ɗaya daga cikinsu?ita kanta bazata iya tuna waya ɗauki hoton ba,kuma haka zalika bazata iya tantance wacece acikin hoton ba,saboda abun yayi confusing ɗinta,Kamar ita kamar kuma hossana,saboda gashin kan daya harmutse kamar na Mahaukaciya,tasan cewa hosana ce kawai keda irin wannan hargitsastsen gashin,
"Ina sauraranki,"ya furta hakan a yayin da yakai hannunshi tare da ɗaukar cup of cofeen da takawo mashi,ya shiga kur6ar shi anatse,
Cikin en ena tace"Wannan kamar hosana ce,bazan iya tantance wacece ba,'
ɗaure fuskarshi yayi tare da cewa"Oh ba zaki iya tantance wacece acikin hoton ba?what does that mean"
Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Inaji hosana ce,wannan itace gashin kanta yake a haka,"
Hannu Sgr yasa tare da kar6e hoton ya ajiye shi a gefen shi,'
Tsuru tsuru tayi da idanunta,cike da tsoran kar ace ta ƙara wani laifin,
"I want u to tell me..,wannan bastard ɗin menene ma sunan shi?
"Ya sayyadi," ta bashi amsa,
"akwai wasu mahimman bayanai da nakeso naji daga gare ki,hope zaki natsu kiban amsa," jinjina kai tayi tare da cewa"in sha Allah,"
"Awani area kuka zauna a kano?"
"A hotoro ne" ta bashi amsa,
Jinjina kai yayi tare da ajiye cup ɗin dake hannunshi,then ya ɗauki banana yana 6areta a hankali yace"zaki iya tuna address ɗin gidanku kenan"?
"Eh,"
"Okey,' ya ɗanyi shiru bayan yakai ayabar abakinsa ya ɗan gutsireta acikin bakinshi,kafin ya kuma cewa"a labarin da sister ɗinki ta bayar,ta faɗi cewa shi wannan mutumin ya ta6a nemanku,a cikinku akwai wadda ya ta6ayin raping"?
Daram!!!taji gabanta ya faɗi,girgiza kai tashiga yi muryarta har tana harɗewa wurin saurin cewa"babu...bai ta6a samun nasarar yin hakan ba,yadai ta6a yunkurin hakan,"
Shiru Sgr ya ɗanyi sae lokacin ya ɗan ɗago da idanunshi ya kalli fuskarta,gaba daya duk tabi ta rikice jikinta sae faman kerma yakeyi,yanayinta kuma kamar akwai wani abu data 6oye masa,
"Tell me the truth!kinsan bana son ƙarya,even if u hide it to me i will find out soon,so its better ki sanar dani,before naji a wurin wani!!"
Hawaye taji sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta tashi ta watsa da gudu,saboda ta tsani taji ana zancen Ya sayyadi,
ɗagowa tayi da idanunta waɗanda suka rune suka canza launi,kai tsaye suka sauka acikin nashi,cikin shessheƙar kuka tace"bazan maka ƙarya ba,yaso yayi hakan amma Allah bai bashi dama ba,'
"In har dagaske ne abunda kika faɗa,to meyasa kike kuka"?
"Saboda banason ana mun maganar shi,hakan yana tunamin rayuwar da mukayi a baya,"
kawar da idanunshi yayi daga kan fuskarta,sannan yace"Its okey,u can wipe ur tears,amma ba hakan yana nufin za'a daina maki maganar shi bane!dole ta hanyarku ne zamu samu dukkan bayanan da mukeso,before muci nasarar kama shi,'
Hannu tasa tana share hawayenta tace"Allah ya bani ikon Amsawa,"
"U can leave,"ya bata umarnin tafiya,
Tashi tayi jikinta asanyaye ta juya tana nufar hanyar fita daga bedroom ɗin nashi,gaba ɗaya duk jikinta yayi mugun sanyi,wata irin kasala ta lullu6eta,har ta kusa fita daga bedroom ɗin nashi ta ɗan tsaya tare da juyowa a hankali don tayi ma ɗakinshi kallon karshe tunda daga yau bazata ƙara zuwa sashen shi ba,da sunan yi mashi aiki,
Juyowarta keda wuya,idanunta suka shiga acikin nashi,har saida gabanta ya faɗi,kasa tafiya tayi kallonshi kawai takeyi,a yayin da shima yake kallonta,
Kusan 8 mins sannan taji muryarshi acikin kunnanta yace"Lafiya"?
girgiza kai tayi alamar ba komai,kafin tasa kai ta fuce daga bedroom ɗin nashi,
Saukowa downstair tayi,hawaye nata faman zarya a fuskarta,sai da ta goge tears ɗin sannan ta wuce bedroom ɗinsu, a hankali ta tura door ɗin ɗakin ta shiga,Samun Jahad tayi zaune daga gefen gadon ta zabga tagumi,yayin da hosana ke ta faman sharar bacci,
Bayan ta rufe masu ƙopar ɗakin ta koma daga gefen jahad ta zauna tare da ambaton sunanta"Jahad,"
A razane ta ɗago tana kallon Sehrish,sam bataji shigowarta ba,
"Mekike tunani ne"?
Murmushi jahad ta ɗanyi tare da cewa"Ashe kin fita,na farka ban ganki ba,acikin ɗakin,'
Sehrish tace"Naje part ɗin babban yayanmu ne,'
"Wannan mai blue eyes ɗin"? Jahad ta tambaya yayin da take kallonta,
"Eh,Sunan shi RAFAYET,amma suna kiranshi da BABBAN YAYA,"
"Shine babbansu kenan"?acewar jahad,
"A'a bashi bane babbansu gaba ɗaya ba,Akwai wanda suka girme shi sosai,Sunan ne ya dace dashi shiyasa suke kiranshi da haka,"
Jahad tace"kamar bazaiyi sauƙin kai ba,na lura ko magana baisan yi,ni in inama kallonshi tsoro yake bani,araina har cewa nake yi wai shima nan ɗan uwanmu ne,ƙwayar idonshi daban koda yake ga Ayaan nan shima idanunshi ash ne,mommynsu ma nata kalar na babban yaya ne,amma Mommynsu fa kamar bata son ganinmu nake gani ko kin lura da haka"?
Sehrish tace"eh hakane,amma kada kisa ma ranki wannan,idan kika lura abun kamar a jininsu yake ita da babban yaya,in ka biye ta yanayinsu toh bazakayi rayuwa asake ba,duk zaka takure kanka ne,kayi tunanin cewa kamar sun tsani mutane basa son ganinsu bayan ba haka bane,kawai basu cika son magana ba,ko kallon mutane basa son yi,'
Cike da mamaki jahad tace"tofa su kuma haka suke?shiyasa junaid shima baison ganina,har yau fa junaid ko son haɗa ido baiyi dani,in kuwa muka haɗa ido dashi har hararata yake yi ya kuma murguɗa mun baki,Wlh bana jin daɗin abunda yake yi mun,sai inga kamar ya tsane ni ne,abun ba ƙaramin damuna yake yi ba,gashi inason nasamu kusanci sosai dashi,kamar yadda naga kuna shiri a tsakaninki dashi,bansan meyasa ni yake mun haka ba,'
Tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,
Sehrish tace"kai junaid ɗin keyi maki hakan?to ae duk gidan nan babu kamar shi,indai wurin son mutane ne,yafi kowa faran faran da mutane kullum cikin fara'a yake,Junaid fa ko yau kuka fara haɗuwa dashi zai nuna tamkar kun ta6a haɗuwa a baya,kuma yadda zai saki jiki da mutun zaisa kayi tunanin kamar kun share shekaru kuna atare,"
Sosai Sehrish ta shiga kora mata bayani agame da junaid,
Abun ba ƙaramin ɗaure ma jahad kai yayi ba,cike da mamaki tace"To Amma meyasa ni yake mun haka"?
Murmushi sehrish tayi tare da cewa"dole akwai dalili,amma ki barni dashi in sha Allah zan tambaye shi inji,"
gyaɗa kai jahad tayi tare da cewa"Shikenan,dan Allah duk yadda kikayi dashi ki sanar mun,"
sun jima suna fira atsakaninsu kafin bacci yayi awon gaba dasu,ƴan ukun Abusufyan,
Wuraren ƙarfe biyu daidai na dare,wata irin guguwar iska,ta shigo ta cikin windown ɗakin su Sehrish mai matuƙar tsoratarwa da kuma razanarwa baƙi wulik mai tafe da wani irin sauti,wanda ya ciccika kunnuwansu,a firgice hosana ta farka tare da fasa wata irin razananniyar ƙara,wanda yayi silar tashin Sehrish,ita kanta ta tsorata da ganin guguwar iskar nan,ta tattare wuri guda yadda kasan kwarangwal din mutun haka shape ɗinta ya koma bayan ta sauka a dakin nasu,ga yayi ajikinta,
Ƙanƙame Sehrish hosana tayi sosai tana cewa"Wayyo Allahna,mun shigo uku,ina daddynmu yake,menene wannan abun,'
Babu abunda Sehrish ke ambato face"innalillahi wa'inna ilaihirraji'una,yayin da ta ƙura idanunta akan guguwar nan data saukar masu acikin ɗakinsu,
jikinsu sae faman kerma yake yi gaba ɗayansu,hakoransu sae faman rawar ɗari suke yi kaf kaf kaf,saboda wani irin sanyi daya ziyarce su,
ganin guguwar ta tsaya agefen gadonsu,kamar su take kallo don harda ƴan idanu gare ta hakan yasa suka ƙara fashewa da kuka suna faɗin"Wayyo Allah mun shiga uku!"
A firgice jahad ta farka,jin ihun da su hosana keyi,adai dai lokacin hosana na cewa"wlh hada ƴan idanu ke gare ta,mun shiga uku,"
Zuba masu ido jahad tayi tana kallonsu ganin yadda suka kware baki suna kuka,Ga bargo a hannunsu,sun rurruƙe,
A hankali ta mayar da idanunta kan abunda suke kallo,guguwar nan ta gani tsaye da suffar kwarangwal tayi masu ƙuru da ido,
"Jahad kina ganin abunda muke gani kuwa"?Sehrish ce tayi mata maganar,
Jinjina kai jahad tayi tare da cewa"Nagani,mutun ne wannan ba guguwar gaske ba,koma waye yazo ne don ya tsoratar damu ne kawai babu abunda zai iyayi mana,"
Hankali atashe hosana da sehrish suke kallon jahad,jin abunda tace,babu alamun jin tsoro atattare da ita,hankalinta kwance tayi maganar,ganin haka yasa suma suka dakatar da kukan da sukeyi,
"Wama ya sani,ko ya sayyadi ne yazo da suffar guguwar nan don yazo yaga yadda muka koma," jahad ce tayi maganar fuskarta ɗauke da dariya,
Baki asake suke kallonta,sehrish tace"Anya jahad ba macanzarki akayi mana ba?na fara kokwanto anya kece?taya zaki ga wannan tashin hankalin amma ki nuna baki damu ba?guguwa face tayi suffar kwarangwal kuma hada ƴan idanu kuru tana kallonmu ki kalla dakyau,"
Tsoki jahad taja tare da cewa"Nice mana,nifa Allah kaɗai nake tsoro,dashi na dogara,wannan koma menene yazo wlh ni dariya ma halittar take bani,ji idon fa yadda yake jujjuyawa kamar an ɗorashi,' fashewa da dariya jahad ta kuma yi,Kafin ta kalli su hosana tace"abunda za'ae yanzu muja bargo mu lullu6e,mu rabu da ita,idan ta gaji da tsayuwa ta tafi,koda yake ba ƙafafu gareta ba,fiffike zatayi ta tashi,'
Ta ƙarasa maganar cike da nishaɗi,jan bargon nasu tayi,cikin sauri suka gyara kwanciyarsu ta lullu6esu da bargon,saboda tsabar tsoro Bargon da suka lullu6a dashi sae faman kerma yake yi,
"Jahad dagaske,baki ji tsoron wannan abun ba"?kasa-kasa Sehrish ta tambaye ta,
Murya na kerma jahad tace"yanzu haka ma kuka nake yi,wlh atsorace nake,ƙarfin hali kawai nayi,saboda na ta6a jin wani malami yace idan ka nuna kana jin tsoran Aljani shine yake cin nasara akan mutun,shi har faɗama yake yi da aljanu shine nima na jaraba yin irin nashi,'
Duk da halin da Sehrish ke ciki sai da ta fashe da dariya tana kumshe baki,
"Jahad kinja mana bala'e,koma meye yanzu kin ƙara fusata shi da kalamanki,bansan me zai biyo baya ba,"acewar sehrish,
Jahad tace"Addu'a zamuyi kawai,insha Allah ba abunda zasu iya yi mana,'
Muryar hosana suka jiyo abayansu tana cewa"Sehrish dan Allah kuyimun addu'a,ko fatiha bazan iya karantawa ba a halin da nake ciki a yanzu,ga fitsari ya matse ni,'muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
Jahad tace"ki tashi ki shiga toilet mana!kinsan Allah kada kiyi mana fitsarin kwance,'
Fashewa da kuka hosana tayi tana cewa"taya zaki ce in shiga toilet bayan wannan halittar na nan ta ƙura mana ƴan idanunta,Allah ba inda zanje,sai dae ki tashi ki rakani ko kuma inyi shi a wando,'
Har haɗa baki sukeyi wurin cewa"Wai wa zai raka ki"?
"Ke ko sehrish daya daga cikinku ta rakani,"
"Tab,wlh nidai ba inda zanje,sai dai ko Sehrish," jahad nakai ƙarshen maganarta sehrish tace"Ke baki je ba sai ni kike tunanin cewa zan rakata,Ae wlh sai dae tayi shi a wando,ba inda zanje,"
Ganin basu ɗauki maganarta serious ba yasa ta ƙara fashewa da wani kukan mai sauti,
"Dawo tsakiyarmu ki kwanta,zanyi maki addu'ar ɗaukewar fitsari,ae na iya,Oumma ta ta6a koya mana,"fashewa da dariya sehrish tayi tana cewa"kai jahad,ni ban ta6a jin wata addu'a ta ɗauke fitsari ba,'
Tashi hosana tayi tare da komawa tsakiyarsu ta kwanta,tana jiran Jahad tayi mata addu'a kamar yadda tace'
"Rufe idanunki"jahad ta fadi hakan fuskarta ƙumshe da dariya,runtse ido hosana tayi tare da cewa"Na rufe,"
Tofa mata addu'a jahad ta shiga yi a fuskarta,ita kanta me addu'ar batasan me take fadi ba,sae faman motsi take da baki,intayi sosai saita tofa ma hosana a fuskarta,
A ƙule hosana tace"waini sai tofa mun miyau kike a fuskata,kuma ni banji kina addu'ar ba,'
"Ita addu'ar a sirrance akeyinta,ba a bayyanata,kiyi shiru kawai zanci gaba da karanta maki har a samu fitsarin ya ɗauke,
Shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,yayin da jahad taci gaba da karanta mata addu'ar,duk sehrish na sauraronsu,
Abu kamar wasa,bacci ya ɗauki hosana,
"Kamar tayi bacci"?sehrish ta tambaya,
Jahad tace"eh,tayi bacci yanzu saura mu ya rage muyi bacci,'
Sehrish tace"taya zamu iya bacci da waccen halittar a ɗakinmu?inta cutar damu fa"?
Jahad tace"Insha Allah ba abunda zata iya yi mana,muyi addu'a kawai mu kwanta,mu ɗauka kamar mafarki ma mukeyi,"
Kamar yadda jahad tace haka suka haɗa baki suna karanta addu'oi,bayan sun kammala kuma suka shiga karanta ayoyin alkur'ani mai girma atare,cikin lokaci ƙankani bacci ya ɗaukesu,
Yin baccinsu keda wuya wannan guguwar ta disashe daga wurin ta 6ace 6aat.
Tashin hankali,kowaye yazo masu da wannan suffar?
Abunda ya faru bayan fitar abbansu daga bedroom ɗinshi,kai tsaye ya wuce upstairs part ɗin Marshal Omar,jikinshi duk asanyaye haƙika junaid ba ƙaramin 6ata mashi rai yayi ba,da alama sakin fuskar da yake yi mashi ne yana wasa dashi kamar tsaranshi,hakanne yasa raini ya fara shiga tsakaninsu,
Da sallama abakinsa ya shiga bedroom ɗin Marshal,samunshi yayi a kwance yana sharar bacci,bedside lamps ɗinsa ne suka haskaka wurin bed ɗinsa,
Shiga ciki abbansu yayi tare da hayewa saman gadon,ya jingina bayanshi a jikin headboard ɗin gadan,Ranshi duk a jagule yama kasa kwanciyar saboda yasan cewa koya kwanta bazai iya runtsawa ba,ba ƙaramin ƙuntata yayi ba,junaid ya fusata shi sosai,
Kwakkwaran juyi marshal yayi zai gyara kwanciyarshi,karaf idanunshi suka sauka akan Abban nasu,cike da mamaki ya ambaci sunanshi"Abba!"
fuskarshi ɗauke da damuwa yakai idanunshi akan fuskar Marshal yace"Omar,dama ba bacci kakeyi ba ne?"yayi maganar ayayin da yake ƙoƙarin 6oye damuwarshi,
Yunƙurawa Omar yayi tare da tashi daga zaune yana fuskantar abban nasu yace"Abba!meya faru naganka anan?kuma fuskarka da alamun damuwa attare dakai,"?
shiru abbansu yayi na wani lokaci yana deciding akan ya faɗa ma Omar halin da yake ciki ko kuwa ya ƙyale zancem kawai,
"Omar,ashe junaid bai da wayau har yanzu yaro ne shi"?
aɗan ruɗe omar yace"me junaid ya aikata,"?
"Hmmm,ya hanani sakat Omar,ƙiri ƙiri junaid ya shige mun ɗakina,yana can rungume da mommynsa,nayi nayi dashi ya tashi in kwanta amma ya ƙiya,wai har ni yake ce ma Yau kwanan sa ne!"?
Murmushi marshal Omar yayi jin shiriritar junaid,wato yau da Abbansu yake kishi,
"Abba,just calm down ur mind,ka bani 5 minutes yanzu zan dawo,just wait,"
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya kama hanyar fucewa daga bedroom ɗin,
Zugudum abbansu yayi yana jiran dawowar Marshal,
Saukowa downstairs yayi kai tsaye ya wuce bedroom ɗin Abban nasu,a hankali ya tura door tare da shigewa ciki,koda junaid yaji an tura ƙofa sae ya ɗan ɗago da kanshi don yaga wanene,ashe baiyi bacci ba damuwar jahad ta hana shi sak har yanzu a tsorace yake,duk a tunaninsa abbansu ne,karaf idanunsa suka sauka akan Marshal Omar dake shigowa ciki,ae yana ganin Marshal Omar ya qara ƙanƙame mommynshi,don yasan cewa abbansu ne yakai shi qara shine akazo a ɗauke shi,
Omar na ƙarasawa wurin gadon ya Shiga tattara hannun jallabiyar jikinshi,muryar junaid kamar zai kuka yace"Ya omar dan Allah kada ka ɗauke ni,wai ni mai yasa akeso a takuramin.....'bai ƙarasa maganar ba Omar ya ɗaukesa gaba ɗaya ya aza a kafaɗarshi,ya fuce tare dashi daga ɗakin,
Suna tafiya yana kuka kamar ƙaramin yaro,Omar yace"rufe mun baki junaid,banason ƙara jin wani sounds daga bakinka stupid,wai har abba kake cema Yau kwananka ne!tsaran wasan ka ne!ko don kaga yana wasa dakai ne shiyasa ka raina shi?
Ya ƙarasa maganar a lokacin da yake hawa upstairs,
Cikin shessheƙar kuka junaid yace"Ya omar,ni fa ban raina shi ba,saboda me zai dinga zuwa yana kwana tare da mommy,bayan ni ya dace ace ina kwana a wurinta,abba baiyi mun adalci....'
Katse shi omar yayi da cewa"Shut up junaid,'
Tsit junaid yayi yana faman hura hanci,
"Tunda har ka fara kishi da mahaifinka,hakan na nufin cewar zaka Iya aikin Soja!yadda zaka ji daɗin kishin ƙasarka,"
Hankali tashe junaid yace"Am sorry ya Omar,bazan ƙara ba,Zan daina hanashi kwana,'
girgiza kai Omar yayi yana cewa"Ban amince ba,zuwa aikin Soja ba fashi junaid,U.S ma zamu turaka,zanyi ma sgr magana,dama abba kawai muke jira ya amince,kaga yanzu ka 6ata mashi rai nasan cewar a shirye yake daya miƙa ka wurinsu koya huta da shiriritarka,
Turo kopar bedroom ɗinsu yayi ya shige da junaid ciki,Abba na ganin shi ɗauke da junaid,ya ɗaure fuska a cikin zuciyarshi kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,
Sauke shi saman gadon Omar yayi tare da cewa"Maza ka kwanta,"
turo baki junaid yayi yana kallon Abbansu,zuba mashi ido abban yayi yana kallon ikon Allah,
Kwantawa junaid yayi tare da Lullu6ewa da bargo,yayi ƙasa ƙasa da muryarshi yana cewa"abba hankalinka ya kwanta,ka rabani da mommyna,kuma gobe can zan kwana,in kuma aka hanani ɗakinsu sehrish zan dinga kwana,"
Saukowa abba yayi daga saman gadon ya kalli Omar tare da cewa"ngde ssae Omar,Ni zan wuce,mu kwana lpy,"
Fuskar Marshal ɗauke da Murmushi yace"Gud night abbana,"
Har yakai bakin ƙopar fita daga ɗakin ya juyo yana kallon Omar ɗin dake tsaye yana kallon bayansa yace"Omar wai cikin triplet ɗin nan Wacece taka acikinsu"?
Sunnar dakai ƙas Omar yayi yana faman sakin Murmushi,daƙyar ya iya furta sunanta"Hosana,"
Jinjina kai abbansu yayi fuskar nan ɗauke da murmushi yace"batare da 6ata lokaci ba,bayan an kammala walimar jibi zan nema maka auranta a wurin mahaifinta,saboda banason wani daga waje ya gansu yace yana so,nafison dukansu su auri na gida,saboda na yadda sosai da irin tarbiyar dana baku,zaku kula da rayuwarsu sosai,"
"But....Abba Rafayet fa,?shima zaka nema mashi auren ɗaya daga cikinsu in yaso sai a haɗa auren atare!!!!?
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: Sai faman safa da marwa takeyi acikin bedroom ɗinta,gaba ɗaya ta rasa samun natsuwa,hakanan ta dinga jin fargabar zuwa abuja,ga zumuɗin zuwan da takeyi amma kuma tana zullumin abunda zai biyo baya,hakanan ta dinga jin kamar wani abu mara daɗi zai faru,ƙafafunta har sun fara ciwo saboda zaryar da take ta faman yi,tun bayan da ta kammala sallar asuba bata koma bacci ba,Jikinta na sanye da Zumbuleliyar riga doguwa brown,sae guntun hijabin da ta kammala sallah dashi,hannunta na ruƙe da wayarta,wani tunani ne ya fado mata aranta,cikin sauri ta shiga danna wayar dake hannunta,Hayaam ta buga ma waya,nan take kiran ya shiga,batare da 6ata lokaci ba hayaam ta ɗaga kiran,daƙyar take magana saboda ta katse mata baccinta,rai a6ace tace"Lafiya kika kira Ni?bayan kin gama kwashe mun albarka"!
Cikin lallami Aunty babba tace"Dan Allah hayaam komai ya wuce kinji ƙanwata?nasan ban kyauta ba,amma kiyi haƙuri,"
Tsoki hayaam taja tare da cewa"hmmm,halan yanzu kin gasgata maganata ne?shiyasa kika kira don jin ƙarin bayani?
Aunty babba tace"EH,hakane,na yadda da abunda kika faɗamun,tuntuni shiyasa ma na kira ki,"
Hayaam tace"Yanzu ya kenan?ya zamuyi?don gaskiya akwai matsala aunty laila,burin mu bazai ta6a cika ba,muddin yaran nan suna nan!"
Jinjina kai Aunty babba tayi tana cewa"babban takaicina yaran da suka kasance mata ne!har ƴan uku,gaskiya abusufyan bai kyauta mana ba tsakani da Allah,haka ake?kawai sai yaje yayi aure a 6oye batare da sanin kowa ba?wai kuma da sanin ammi kuwa"?
Hayamm tace"Anya,gaskiya ina tunanin Ammi bata sani ba,'
Jin haka yasa Aunty babba cewa"Allah yasa in tazo tace bata amince da yaran ba,kinsanta Jarababbiyace,musamman ma da yayi auren bada saninta ba,Wai shin su yaran ina mahaifiyarsu take ne?tana da asali kuwa"?tayi tambayar cike da son jin ƙarin bayani,
Hayamm tace"Ina fa,ae rannan na tambayi azmee game da mahaifiyarsu,shine take sanar dani cewa mahaifiyar yaran Ƴar fa mai gadin gidan gwaggon katsina ne!basu da wani asali,buzaye ne ƴan niger,"
Aunty babba tace"tabɗijancan aikuwa Ammi bazata ta6a yarda dasu ba,kinsanta ta tsani mutun mara asali,gata ita kaifi ɗaya ce muddin tace bata yarda dasu ba amatsayin ƴa'ƴan Abusufyan to fa korasu zatayi daga gidan,yakamata muyi wani abu akai,tun kafin takai ga zuwa,"
Hayaam tace"meke nan zamuyi?kinsan fa gobene walimar kuma gobe zata zo,"
"Abunda zamuyi shine,Ae ina da numbar Ammin a wayata,zanyi amfani da sabon sim ɗina,wanda ban fara amfani dashi ba,zan kirata na sanar da ita game dasu tunkan taji a wurin wani,"acewar Aunty babba
dariya hayaam tayi tare da cewa"Gaskiya aunty laila kin iya haɗa tuggu,ni sam banyi tunanin hakan ba,wannan ce hanyar da zamu bi wurin tarwatsasu,idan kika kirata awayar ki tunzurata sosai,ki ɗaurata akan network har sai ta amince da kalamanki,ki sanar da ita cewa yaran shaggu ne,abusufyan yayi ma mahaifiyarsu ciki a 6oye,shine suka so su 6oye mata,don karta sani,"
Murmushi Aunty babba ta saki tana cewa"hakan yayi sosai,zan tsara komai yanzu........."tana cikin maganar taji alamar dirar motar ishaq,
Cikin sauri tace"Hayaam inaso ki ɗauko min hoton yaran kafin muzo gobe,zan kashe wayar yanzu ishaq ya dawo,
"Toh aunty laila,zanyi ƙoƙarin ɗauko maki hoton nasu,"
Daga haka sukayi sallama da juna,
Ajiyar zuciya aunty babba ta sauke,har taji wani sanyi a ranta saboda ta samu mafita,
Bayan sun kammala wayar hayaam ta buɗe ƙopar ɗakinta tare da fitowa,cikin sanɗa hayam take tafiya don kar wani ya ganta,a haka har ta ƙarasa bedroom ɗinsu sehrish,tura ƙopar tayi cikin sa'a ta samu ƙopar ɗakin a buɗe,leƙa kanta ta fara yi anan ta same su,suna ta sharar bacci wanda tun bayan sallar Asuba da suka tashi suka koma suna yin baccin,
Murmushi ta saki tare da sa kai ta shige ciki,adai dai bakin gadon nasu ta tsaya tare da ɗago da wayarta dama already a cikin camera take,Saita fuskarsu tayi dama kuma duk suna facing ɗin ceilling,kyakkyawan hoton fuskokinsu ta ɗauka,bayan ta kammala ɗaukar hoton,ta lalla6a batare da kowa ya ganta ba,ta koma bedroom ɗinta,cikin sauri ta tura ma Aunty babba hoton ta whatsapp ɗinta,
❤🤍❤
Wuraren karfe takwas,suka farka daga bacci,sehrish ce ta fara shiga toilet tayi wanka,bayan ta fito daga wankan jahad ta shiga ciki,gaban dressing mirror ta zauna ta gama shafe jikinta,ta feshe shi da turare,sannan ta koma ta ɗauko Jallabiya fara ta zura ajikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,musamman adon dake jikin rigar na stones,shiya ƙara ƙawata rigar,bayan tayi rolling kanta da mayafin rigar,ta fito daga cikin bedroom ɗin nasu ta wuce kitchen,cike da zumuɗin kaima babban yaya breakfast ɗinshi gaba ɗaya ta manta da abunda Uncle abusufyan ya faɗa mata,
A kitchen ta samu azmee,har ta kusa kammala girkin,ganin yadda take ta aiki ita kaɗae yasa sehrish taji duk ba daɗi,muryarta a sanyaye tace"Ina kwana Aunty azmee,"
Juyowa tayi daga tsayen da take gaban gas cooker,fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Lafiya lou ƴan matan abusufyan,fatan kun tashi lafiya"
"Lafiya lou,amma aunty azmee gaskiya banajin daɗi in naga kina aiki ke kaɗae,meyasa baki tashe mu ba,munzo mun tayaki aikin"?tayi maganar yayin da take ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin,
Azmee tace"kada ki damu,na riga na saba da aiki,wannan ba wani abu bane,Abba ma ya nemi daya ƙaro masu aiki amma nace mashi ya barshi kawai,saboda na saba da yin aiki ni kadae,"
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"that's impossible,gaskiya in har ba zaki amince a ƙaro masu aiki ba,to daga yau Ni dasu jahad zamu dinga tayaki aiki,don bazaiyiwu ba kiyi ta wahala ke kaɗai,"
murmushi kawai azmee tayi batare da tace Komai ba,
"Aunty azmee idan akwai abunda kika kammala inaso zan fara kaiwa dining in jera,kinga na rage maki wani aikin,"
"Ban kaiga shiryasu ba,amma sai dai idan zaki kaima Sgr nashi,sae na haɗa maki,ki kai mashi,"
Murmushi ta saki tare da cewa"Toh,"
Shirya mata breakfast azmee tayi acikin ƙayataccen tray,bayan ta kammala,sehrish ta ɗauki tray ɗin tare da fucewa daga kitchen ɗin,
tana cikin tafiya harta kusa hayewa upstairs taji anyi mata gyaran murya abayanta,cikin sauri ta juya don taga Wanene,ganin Uncle abusufyan yasa gabanta faɗuwa,saboda tana kallonshi ta tunano da abunda ya faɗa mata a daren jiya,
Muryarta na rawa ta furta"Daddy,"ƙarasawa yayi wurinta tare da tsayawa dab da ita fuskarshi a ɗaure yace"Me na faɗa maki jiya?tun yanzu zaki fara sa6amun"?
Hankali tashe sehrish tace"a'a daddy,wlh mantawa nayi,bazan ƙara ba,dan Allah kayi haƙuri,"
"Zo ki wuce ki mayar da kayan abincin kitchen,inyaso azmee taje takai masa,"
Jiki asanyaye Sehrish ta juya tare da kama hanyar komawa kitchen,duk wannan abun daya faru akan idon,Mommynsu junaid alexandra,tana tsaye abakin part ɗinsu na downstairs tana kallonsu,
Haka ta koma kitchen da kayan abincin idonta cike tab da hawaye,taci burin ta ganshi yau,amma Uncle abusufyan yayi mata tsiya,
Tamkar wadda aka zarewa laka haka ta shiga kitchen ɗin,Azmee na ganinta dauke da tray a hannu tace"Lafiya naga kin dawo da kayan abincin"?tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,muryarta tamkar zatayi kuka tace"Uncle ne ya hanani zuwa part dinsa da sunan aiki,tun jiya da daddare ya gargaɗeni akan Karna kuskura na ƙara yin aiki a ƙarkashinsa,bansan meyasa ya hanani ba,"
Cike da mamaki azmee tace"to fa!ko meyasa yayi hakan?kuma kin tabbata bakiyi wani laifin ba wanda yajawo har ya hanaki aiki a part ɗinsa"?
"Aunty azmee ni banyi laifin komai ba,"ta ƙarasa maganar a yayin da take ajiye tray ɗin hannunta,
Shiru azmee tayi aranta tana mai mamakin hukuncin da Abusufyan ya yanke ma sehrish,to kodai don saboda basa shiri da Alexandra ne?tabbas zai iya yiyuwa hakane!tunda akwai gaba atsakaninsu,dole kuwa ya hana Sehrish tayi ma Sgr aiki,don bazai ta6a yarda ƴarsa tazama baiwarsa ba,
"Aunty azmee ko zaki iya nema mun alfarma a wurinsa yabarni in cigaba da aiki acikin gidan nan kamar yadda na saba,"muryar Sehrish ce ta katse mata tunaninta,
zaro ido azmee tayi tare da cewa"Ni ƴar ubanwa?na isa in shiga tsakaninki da mahaifinki?bazaiyiwu ba sehrish,shawarar da zan baki shine kawai ki bi Umarnin mahaifinki ki xauna lafiya,Shi kaɗae yasan dalilinshi na yin hakan,kuma in har kika yi mashi biyayya zakiga ribar yin hakan,"
ɗakyar ta iya haɗiye yawun bakinta,ga hawaye sae faman zarya sukeyi a fuskarta,
"Wannan hukuncin da mahaifinki ya yanke,yayi mun dai dai,don koda bai dakatar dake daga yi mashi aiki ba,to ni dakaina zan hanaki!"
Gaban Sehrish ne ya faɗi rass jin muryar Mommynsu junaid abayanta,Azmee kuwa na ganinta tasha jinin jikinta don tasanta sarai bata da mutunci ta wani 6angaren,
Juyawa sehrish tayi da sauri tana kallonta,
A hankali take tunkararsu yayin da take ci gaba da magana"Banason kusancinki dashi ko kaɗan!just maintain a good distance between u and him,In ba haka ba,You will see the trouble!!"Jikin sehrish har kerma yake yi don ba ƙaramin tsoranta takeyi ba,koƙarin 6oyewa a bayan Azmee takeyi,don gani take tamkar Alexandra zata bugeta ne,
Koda ta ƙaraso dab dasu,harara ta wurga ma azmee tare da cewa"Matsa daga gabana,da ita nakeson magana,"jiki na rawa azmee ta janye jikinta gefe guda,aranta tace"tashin hankali ashe har yanzu matar nan,bata canza ba,lallai akwai matsala,"
goya hannayenta tayi asaman ƙirjinta,yayin da suke fuskantar juna ita da Sehrish,saboda tsabar tsoro ƙiris ya rage sehrish ta saki fitsari,ko idonta bata iya dagawa ta kalleta saboda yadda tayi mata tsaye aka,
Wani irin kallo Alexandra ke bin Sehrish dashi,tun daga ƙasa har sama,yatsina fuska tayi tare da cewa"Ur name"?
Murya na kerma tace"Sehrish,"
Jinjina kai alexandra tayi tare da cewa"saboda daddynki ya hanaki aiki a part ɗin rafayet shine kike kuka?why?
..girgiza kai sehrish tashiga yi tana cewa"a'a..ba saboda haka nake kuka ba...."
"Kukan menene toh"?ta sake jefa mata tambaya a karo na biyu,
"Babu komai,"ta bata amsa tana faman zazzare idanu,
Murmushin gefen fuska alexandra ta saki kafin ta kuma cewa"dama ana kuka ne just without any reason?ki faɗamun gaskiya mana,kodai kin faɗa tarkon shi ne"?
Waro ido waje Sehrish tayi hankali tashe tace"a'a ba haka bane,kawai ina kuka ne saboda tsoron hukuncin da babban yaya zai yanke mun in ya gane cewa na daina yi masa aiki,"
Ta6e baki alex tayi tare da cewa"Just calm down ur mind,Bama zai ta6a damuwa akan hakan ba,kiyi ma mahaifinki biyayya,kuma ki nisanta kanki dashi kamar yadda nace,hakan zaifi maki kwanciyar hankali,"tana kai ƙarshen maganarta,ta juya cike da isa tare da fucewa daga kitchen ɗin,
Fitarta keda wuya Azmee ta mayar da idonta kan sehrish saboda ta lallashe ta,amma ina,tuni sehrish ta watsa da gudu tabar kitchen ɗin,
A bakin ƙopar dakinsu ta tsaya tana faman shessheƙar kuka,zuciyarta har wani tafarfasa takeyi mata,dole tayi kuka saboda tasan cewa ta rasa Sgr na har abada,tunda mahaifiyarshi ta nuna bata sonta,zuƙunnawa tayi a ƙopar ɗakin tana cigaba da kukan nata,ta jima zuƙunne a wurin cikin wani irin yanayi mara daɗin ji,tana jiyo muryarsu jahad acikin bedroom ɗin,suna tattaunawa kan wankan da zasu ɗauka gobe ranar walima,hada zancen saloon ɗin da daddynsu yace zai kaisu ayau,
gaba ɗaya taji komai ya fita ranta,don har wani zazza6i taji ya saukar mata ajikinta,ita kaɗae tasan raɗaɗin da takeji acikin zuciyarta,hannu tasa tare da share hawayenta sosai don karsu hosana su gane cewa tayi kuka,bayan ta kammala goge hawayen ta miƙe,tare da buɗe ƙopar ɗakin tashiga ciki,
Jahad na zaune gaban mirror tana shafa powder a fuskarta,hosana kuma na tsaye gaban wardrobe tana cewa"Nama rasa wani kaya zansa yau,saboda inaso in na kammala shiryawa inje in tashi Ya Omar daga bacci don nasan cewa bai kaiga tashi daga bacci ba,"ta ƙarasa maganar tare da ɗan juyawa ta kalli jahad tace"daddy yace yau zai kaimu Saloon ko?to da yaushe zamu fita?donni hada ƙunshi za'ayimun a hannuna,yanzu ma in naje ɗakin ya Omar zan tambayeshi wani kalar ƙunshi yakeso ayimun baƙi ko ja," jahad tace"Soyayya daɗi,kunshin ma sai an tambayi ya omar wani kala yakeso kenan?to gyaran gashin fa?shi bazaki tambayeshi wani kala yakeso ba?
murmushi hosana tasaki tare da cewa"dole ma in tambayeshi wani kalar gyaran gashi yakeso ayi mun,"_
Suna cikin magana muryar Sehrish ta katse su da cewa"Ƴan uwana rabin raina,me kuke tattaunawa akai ne?naji kamar ana gulmar ƴa omar,ko kunnena ne,'tayi maganar tana ƙoƙarin danne damuwarta,gefen gadon ta samu ta zauna,tana faman sauke ajiyar zuciya,
.juyowa sukayi suna kallonta,hosana tace"Sehrish ina kika je,na tashi ban ganki ba,har naji tsoran kada ace wannan halittarce mai ƴan idanu ta ɗauke mana ke"
Dariya sehrish tayi tare da cewa"ni harna manta da wannan abun,koda na tashi daga bacci ban iya tuna abunda ya faru jiya ba,sae naji kamar duk a mafarki ne,"
Hosana tace"Ae taji tsoro ta gudu,yau da daddare in tadawo,zan aro bindigar yaya Omar in harba mata bullet acikin idanunta,"atare suka fashe da dariya jin abinda hosana tace,hada kwatantawa da hannunta yadda zatayi shooting din guguwar,
Jahad tace"Cika baki kawai,kin manta kukan da ki kayi mana ajiya?kinfi kowa tsorata,ba don nayi maki addu'ar ɗaukewar fitsari ba,da ba'asan me zai biyo baya ba....'dakyar ta ƙarasa maganar saboda dariyar da tazo mata,
cike da nishaɗi suke yin firar tasu,kafin lokacin yin breakfast yayi atare suka fita,Hosana ta wuce part ɗin Omar,yayin da su kuma suka wuce dining,Sehrish dae jurewa kawai takeyi,suk ta gaza sakewa saboda rashin sanya sgr a idanunta,gashi bai sauko downstairs ba,saboda Azmee takai mashi nashi a part ɗinsu,kuma sam bai tambayeta akan Sehrish ba,Hakan na nufin cewa Sgr bai damu da ita ba ko kaɗan,dama haroon yace Iskace ke wahalar da mai kayan kara,
Yana kwance yana sharar bacci,hosana ta shiga bedroom ɗin nashi,lalla6awa tayi ta haye saman gadon har wurinshi ta ƙarasa,saitin fuskarshi tana kallon zunzurutun kyawunsa,
Hura mashi iska tayi a fuskarshi,nan take ya ɗan motsa tare da yatsina fuskarshi,murmushi hosana ta saki tare da kai hannu ta toshe mashi hancin shi,aikuwa a gigice ya farka batare da ya sani ba ya tattara dukkanin ƙarfinshi ya cakumi hosana tare da yin wurgi da ita,gaba daya ta tafi yaraf ta kife ƙasan tiles ɗin daga gefen gadon,nan take ta fashe da kuka saboda hancinta daya daki ƙasa,shi duk atunaninshi wani ne ya kawo mashi hari shiyasa yayi mata haka,kuma yana yin wurgin da ita,yaci gaba da baccinsa,dama duk a cikin magagin bacci ne yayi mata hakan,
Cikin baccinshi ya jiyo sautin kukanta tana cewa"Wayyo Allah,hanci na ya fashe,ya Omar ka kashe ni,"
A firgice ya ware idanunshi tare da miƙewa daga zaune yakai idanunshi wurin da sautin kukan ke fita,anan ya samu hosana dafe da hancinta a zaune dirshan tana kuka,
Hankali atashe ya sauko daga saman gadon ya zukunna agabanta yana tambayarta lafiya?garin yaya taji ciwo a hancinta,
Cikin shessheƙar kuka tace"bakaine ka cakume ni ba,kayi wurgi dani daga saman gado na faɗo ƙasa har hancina ya bugu,"
Waro ido waje yayi tare da cewa"Ni kuma dakaina"?
Jinjina kanta tayi tare da cewa"Eh mana,saboda kawai na toshe maka hanci,
🙏🙏🙏
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
❤🤍❤
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Hannu yasa tare da tallabo fuskarta yace"Hosana bada sani na nayi maki hakan ba,laifin ki ne,meyasa zaki toshe mun hancina?so kike na mutu'?
Girgiza kai tayi"a'a,banso ka mutu,ae ni wasa nayi maka ko,"tayi maganar tana satar kallon fuskarshi,
"Faɗa mun me ya kawoki bedroom ɗina har saman gadona"?
A ƙule tace"nifa nazo ne na tashe ka don kaje ka ci abinci,naga kowa ya fito banda kai,kuma zasu iya cinye abincin duka,"
fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Waya faɗa maki za'a cinye abincin,ae ko ban fita ba Azmee zata kawo mun ne har cikin part ɗina,"
Shiru tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,ɗagowa ta ƙara yi zata saci kallonshi suka haɗa ido,ganin yadda yake kallonta ko ƙyaftawa baiyi hakan yasa ta ɗaure fuska cikin shagwa6a tace"Ya omar wannan kallon fa,ka wani tsare ni da ido,"
yadda tayi maganar ba ƙaramin burgeshi tayi ba,ya jima yana kallonta batare da yace wani abu ba,har sai da ta hasala rai a6ace tace"shikenan tunda ba zaka mun magana ba,bari na tashi na tafi,dama ko abincina banci ba,saboda kawai inzo in tashe ka daga bacci,amma ko farin ciki ba kayi ba,'
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ruƙo hannunta cikin nashi"Hosana,so nake ki faɗa mun gaskiya,kina sona da gaske?kuma zaki aure ni? Waro ido waje hosana tayi tana kyakkyaftasu kamar na ƴar tsana jin abunda yace,a ruɗe tace"Ya Omar!aure fa!"_
Jinjina mata kai yayi tare da cewa"eh,aure hosana ko baki shirya ba,"
Turo baki ta ɗanyi tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa,hankalinsa kam harya ɗan tashi saboda ganin yadda ta tsorata don yayi mata zancen aure,dama fargabarsa kada sai anje wurin nema mashi auranta tace bata shirya ba,don yasan ba cikakken hankali gare ta ba,
Lalla6ata ya shiga yi"pls hosana,ki faɗamun gaskiya,zaki aure ni"?
daƙyar ta iya buɗe baki tace"Ni yanzu tashi zanyi in tafi,dama zuwa nayi fa don in tambayeka,wani kalar ƙunshi kake so ayimun baƙi ko ja,"
ya lura cewa batason zancen auren shiyasa ta kawo maganar ƙunshin,cikin sanyin murya yace"Nafison jan lalle zai fi yi maki kyau,kuma ba mai yawa ba ƙunshin,ƴar flower kawai za'a zana maki mai kyau,"
Yana kai ƙarshen maganar,hosana ta miƙe tana faman shan ƙamshi,da sauri ta juya ta bar bedroom ɗin nashi,bin bayanta yayi da kallo har ta fuce,jiki asanyaye ya miƙe tare da nufar toilet ya shige,
Hosana na fita daga cikin bedroom ɗin nashi,a falonsa ta tsaya tana faman zabga murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,Yau ya Omar ya nuna yana sonta harma yanayi mata zancen aure,ta rasa ma wa zata fara faɗamawa,sai faman zagaye zagaye takeyi a cikin falon,
Wuraren ƙarfe biyu da rabi na rana,Abusufyan ya ɗaukesu acikin motarshi kamar yadda yayi masu alƙwarin kaisu wurin saloon da kanshi,hosana da jahad suna a bayan motar duk sun ɗau wankan jallabiya sun laga mayafi,Sehrish na agaban motar kusa da driver seat inda Uncle abusufyan ke zaune yana driving ɗinsu anatse,Su jahad da hosana sae fira sukeyi tare dashi,amma ita ko uffan bata tanka masu ba,dama tunda ta shigo cikin motar Abusufyan ya lura da yanayinta,
gyaran murya yayi mata hakan yasa ta ɗan dago da kanta ta kalle shi,
"Meyake damunki ne Daughter?tunda kika shigo cikin motar nan baki tanka mana ba,ga ƴan uwanki suna ta fira a tsakaninsu amma ban dake".
Muryarta asanyaye tace"Babu komai,"
"ko don saboda na hana ki kai ma Sgr abinci ne"? Yayi maganar batare daya kalleta,
Cikin sauri tace"a'a ba haka bane,kawai bana jin daɗin jikina ne,"
"Ban yarda ba daughter,saboda shi ne yasa kika shiga damuwa,"_
Shiru tayi bata ce komai ba,murmushi abusufyan yayi kafin yace"banyi hakan don na takura maki ba,face don na ɗaukaka darajarki,nasan ba zaki fahimce ni ba a yanzu amma nan gaba da kanki zakiyi mun godiya akan hakan,idan kuma hakan ya 6ata maki rai,kiyi haƙuri,'ya ƙarasa maganar adai dai lokacin da suka ƙaraso wurin Saloon ɗin,parking ɗin motar yayi jahad da hosana suka fita waje,tana ƙoƙarin buɗe motar ta fita ya ambaci sunanta"Sehrish,"juyowa tayi tare da kallon fuskar daddyn nasu tace"Na'am daddy,"
"Murmushi kawai nakeso kiyi mun kafin ki fita,"
fashewa tayi da dariya har fararen hakoranta suka bayyana,duk a tunaninta wani abu mai muhimmanci ne yasa ya kirata,ashe kawai don ya tambayi murmushinta ne,shima dariyar yakeyi,kafin su fita daga cikin motar atare,
**************
Fitowarshi kenan daga wanka,yana cikin shirya kanshi cikin riga da wandon jeans,yaji an kwankwasa ƙopar ɗakinshi,daga muryarshi yayi tare da cewa"ƙopar a buɗe take,"yayi maganar tare da juyawa yana kallon mai shigowar,
Cike da mamaki yace"Ya HAROON!kaine!dama kana nan,"
Shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin nashi yana cewa"Ina nan mana junaid,kaine ka manta dani,kowa ma ya manta dani,"
"Ya haroon ba haka bane,wlh ni ban manta dakai ba,kana araina,"
ta6e baki haroon yayi alokacin da yake tsayawa agaban junaid suna fuskantar juna yace"Ka ƙara kyau da haske,hankalinka kwance baka da wata damuwa,ba kamar ni ba,kullum cikin damuwa nake,zuciyata har nauyi takeyi mun saboda halin da nake ciki amma babu wanda ya damu dani,yau ko mutuwa nayi babu wanda zai damu,sae ma farin ciki da za'ayi,"
Jin wannan maganar ta haroon yasa jikin junaid yin sanyi,wani irin tausayin shi ya kamashi,muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"pls Ya haroon dan Allah kadaina faɗin wannan maganganun,wlh bana jin daɗi,"
"Junaid ƙarya nayi ne?an damu dani acikin gidan nan ne?kowa yayi watsi dani,babu wanda ke damuwa dani,tamkar bare haka nakeyin rayuwata,hatta azmee da take ƴar aiki acikin gidan nan ta fi ni muhimmanci tunda ita ana damuwa da ita,ni kuwa fa?
Hawaye ne suka cicciko a idanun junaid,dama shi akwai tausayi,gaba ɗaya tausayin haroon ya kamashi,saboda duk abunda ya faɗi gaskiya ne,ba'a damu dashi ba,ko zancen shi ma babu maiyi acikin gidan,idan zai share wata a waje babu mai tambayar ina yaje,
"Tamkar maraya ni fa haka nake acikin gidan nan,kalli kaga yadda na koma duk na rame saboda damuwa,gaskiya ni bazan iya cigaba da rayuwa ba junaid,zan kashe kaina ne kowa ya huta," yana kai ƙarshen maganarshi ya juya da sauri zai bar ɗakin,
Da gudun gaske junaid ya rungumoshi ta baya tare da fashewa da matsanancin kuka yana cewa"Meyasa ya Haroon!pls stop saying that,banason jin kana zancen mutuwa,ko kowa bai damu dakai ba,Ni nadamu dakai,ko don saboda ni ya haroon kada ka aikata hakan,idan ka kashe kanka,nima bazan rayuwa ba,zan bi ka mu tafi tare,"
Wannan kalaman na junaid ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,cire hannunshi yayi daga ruƙon da yayi ma waist dinshi,sannan ya juya suna fuskantar juna yace"Junaid dagaske ne ka damu dani?kuma bakaso in mutu"?
cikin shessheƙar kuka junaid yace"Eh ya haroon bana so pls,"
Hannu haroon yasa yana share mashi hawayenshi,kafin daga bisani ya janyo shi ajikinshi tare da rungume shi sosai ajikinshi,kamar zai mayar dashi cikin shi,saitin kunnanshi yakai bakinshi tare da cewa"I love u so much junaid,cos you're so special,in dai zan kasance tare dakai bazan ta6a shiga wani ƙunci na rayuwa ba,kallon ka kawai zai iya sanya farin ciki a cikin zuciyata,daga yanzu inason ka zama abokina junaid,saboda ka dinga ɗebe mun kewa,muna fita yawo atare,don bani da aboki,nifa kowa gudu na yake yi,bansan meyasa ba,'ya ƙarasa maganar tare da janye junaid daga jikinshi,
"Junaid!ka amince zaka zama abokina"?
Jinjia kai junaid yayi tare da cewa"Eh,na amince,amma dan Allah ya haroon kadaina zancen zaka kashe kanka,banjin daɗi banso pls,"
"Shikenan na daina,daga yau kome kakeso ma zanyi,am sorry na sanyaka zubar da hawayenka,"
"Ya haroon ni zanje nayi ma Abba magana akanka,nasan abba zai fahimce ni,"
cikin sauri haroon ya ruƙo hannun shi tare da cewa"A'a junaid,just leave it,banason kowa yasan meke tsakanina dakai,kada kayi ma kowa maganata don ba lalle su fahimce ni kaman yadda kai ka fahimce ni ba,"
"Shikenan bazan faɗa ba,"
"Yawwa junaid ɗina,Yanzu zan barka ka ƙarasa shiryawa,"
Yana faɗin hakan ya juya tare da fucewa daga ɗakin junaid,ya koma bedroom ɗinsa,agaban dressing mirror ɗinshi ya tsaya yana ƙarewa fuskarshi kallo,
A hankali wannan mugun murmushin nashi ya soma bayyana akan fuskarshi,fashewa yayi da dariya kafin daga bisani ya ɗaure fuskarshi,kalaman junaid ya shiga tariyowa,tuni jikinshi yayi sanyi,ta wani 6angaren ji yake tamkar bazai iya ba,amma bai da wata mafita daya wuce wannan!
"Junaid kada ka damu zamu mutu atare,"ya faɗi hakan tare da komawa ya zauna daga gefen gadonshi,
Bayan junaid ya kammala shiryawa,saukowa downstairs yayi har lokacin jikinshi ba kwari,haroon ba ƙaramin tausayi ya bashi ba,A main palor ya samu Abbansu tare da Momnynsu dasu Twins suna fira atsakaninsu,tunkararsu yayi fuskarshi ɗauke da murmushi,suna haɗa ido da Abbansu ya watsa mashi harara,sunnar da kai ƙasa junaid yayi da wurin Abban yaso ya fara zuwa amma wannan hararar da yayi mashi ce tasa ya fasa zuwa ya wuce wurin mommynsu,dukawa yayi tare da manna mata kiss kafin ya rungumeta,fuskarta asake tace"My romeo,"Amsa mata yayi da mommy,a lokacin daya koma wurinsu twins suna gaisawa,Jahan yace"Ina zuwa naga key ɗin mota a hannunka,"
"Zanbi su uncle ne," ayaan yace"Kada ka bari Mommy taji to,in ba haka ba bazata bari kabi su ba,"
"Saboda me"?ya tambaya yana kallonshi,Jahan ne ya bashi amsa da cewa"Saboda bazata barka ba,idan ta tambayeka ina zaka je,sae kace mata gidan abokinka zakaje,"duk wannan maganar da sukeyi a kunnan abbansu saboda yana kusa dasu,kallonsu kawai yakeyi,juyawa junaid ya ɗanyi tare da satar kallon mommyn,idonta na akanshi hakan ya tabbatar mashi da cewar so take taji me suke cewa,'
"Ka tafi kawai,"acewar ayaan,
harya juya zai tafi ya tuna da Abbansu,dawowa yayi tare da zuƙunnawa agabanshi yace"Abba,"ɗaure fuska abba yayi batare da ya tanka mashi ba,
"dan Allah kayi haƙuri abba in na 6ata maka rai,bazan ƙara ba,"
Ta6e baki abba yayi tare da cewa"Junaid kenan,ae ni yanzu babu ruwana dakai,kafi ƙarfi na,"_
Ashagwa6e ya kuma cewa"pls abba,kayi hakuri,ka manta da abunda ya faru jiya,bazan ƙara ba,"
"Naji,tashi ka tafi,ka kulamun da kanka,"
Murmushi junaid ya saki tare da mikewa ya manna mashi kiss a fuskarshi,sannan cikin sauri ya kama hanyar fita,
"Junaid ina zuwa"? Jin muryar Momnynsu yasa shi dakatawa da tafiyar da yake yi,
tsayawa yayi tare da juyawo ya kalleta,
"Mommy gidansu abokina zani je,"
"Kai da wa?waye zai kai ka?
Nuna mata key ɗin motarshi yayi kafin yace"Ni zan kai kaina,"
Jinjina kai tayi tare da cewa"Okey,u can go," da sauri ya fuce daga cikin gidan,
Mayar da idanunta tayi akan abbansu tace"Dama inaso inyi magana dakai,wai meyasa kuka bar romeo yana Driving da kanshi?Also babu wani security guard dake tsaronsa,Shi kadae yake yawonshi,"
Abba yace"Allah xai tsare mana shi,"
Alexandra tace"Nasan da wannan,Amma wannan babban ganganci ne,koda ace kowanne daga cikinsu zaiyi yawonshi batare da security guards ba,amma bai kamata ace kamar junaid ƙaramin yaro yana yawo shi kaɗae ba,ba wani tsaro atare dashi,Especially yadda kowa ya sanya mashi ido,gaskiya ni hakan bai kwanta mun araina ba!!"
shiru abbansu yayi yana nazarin maganarta,
Jahan yace"Gaskiya Abba,maganar mommy gaskiya ne,yakamata ace junaid akwai security guards dake tsaronsa duk inda zaije,musamman a wannan yanayin da muke ciki,bibiyar rayuwarmu akeyi don kawai acutar damu,junaid kuma yafi kowa ƙaranta acikinmu,yana buƙatar security,"
"Abunda nake ƙoƙarin fahimtar dashi kenan,"acewar mommnynsu,
jinjina kai Abba yayi tare da cewa"hakane,zanyi wani abu akai',
daga nan suka cigaba da tattauna a tsakaninsu,
*Boss Bature*
Tun bayan da Hayaam ta tura ma Aunty babba hotonsu hosana,bata samu damar duba hoton nasu ba,ko whatsapp ɗinta bata shiga ba,wayarma tana ajiye cikin bedroom ɗinta,Shirye shiryen zuwa walima kawai sukeyi,atare da hafsat suka fita saloon daga nan za'ayi masu ƙunshi,bayan nan kuma zasu biya Shopping mall,saboda siyayyar da tace zatayi ma Ƴa'ƴan uncle ɗinsu,basu suka dawo gidan ba sai wuraren karfe shida na yamma agajiye suka dawo,kowa ya wuce bedroom ɗinshi,Aunty babba na shiga ɗakinta,kai tsaye ta faɗa saman gadonta ta shiga sharar bacci,Hafsa kuwa saida ta fara yin wanka,ta canza kayan jikinta izuwa riga da skirt marasa nauyi,sannan ta fito falo ta kwashe shopping bags ɗin da suka bari a falo,takaisu ɗakinta,tana cikin dudduba kayan wayarta dake ajiye gaban mirror ta shiga ringing,hannu takai tare da ɗaukar wayar tana kallon screen ɗinta,ganin Sunan Aunty Hayaam ya bayyana akan secreen ɗin wayar,yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta,
"Assalamu Alaikum aunty hayaam,'
Ko amsa mata sallamar batayi ba tace"Hafsat ina Aunty laila take ne?tun da sassafe na tura mata hoton bata duba ba,har nagaji da jira,"
Hafsat tace"yanzu muka dawo daga kasuwa agajiye,tana a bedroom ɗinta ina jin bacci ne ya dauketa,ko inyi mata magana ne"?
Hayaam tace"A'a,kawai idan ta tashi ki sanar da ita cewa na tura mata hoton ƴa'ƴan abusufyan ɗin,ta duba ta whatsapp ɗinta,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,muryarta na rawa tace"hoton ƴa'ƴan Abusufyan dinmu!zan sanar mata kuwa,"
Rejecting call ɗin tayi,da gudu ta fito daga bedroom ɗinta,kai tsaye ta haye upstairs ɗakin aunty babba,tura kopar ɗakin tayi tare da shigewa ciki,a kwance ta samu aunty babba saman gadonta sai sharar bacci takeyi,ga wayarta ajiye agefenta,
Cikin sanɗa takai hannu tare da ɗaukar wayar,ta danna power ɗinta ta kawo haske,ganin akwai password yasa ta ɗan bubbuga kafarta tana cewa"Kai mommy,yanzu dole sae kin tashi sannan zan samu damar ganin hoton babies ɗinmu!gaskiya ni a ƙagare nake,"
Tana cikin maganar,ta tuna da finger print ɗin dake akwai ajikin wayar,nan take zuciyarta ta bata shawarar cewar me zai hana,ta lalla6a ta hau saman gadon,ta dangwalo yatsan aunty babba,kota samu wayar ta buɗe,Good idea,ta furta hakan tare da lalla6awa ta hau saman gadon,cikin sanɗa ta ƙarasa inda aunty babbar take,hannunta ta ruƙo tare da sanya yatsan hannunta a wurin,ya rubuta mata wrong,haka ta dinga bin yatsun hannun aunty babba tana jarabawa,har sai da taci nasarar buɗe wayar,saukowa tayi daga saman gadon,ta tsaya atsaye,hannunta har kerma sukeyi wurin daddana wayar,tsoranta kar Aunty babba tafarka saboda tasan halin Mommyn nata,ta tsani wani ya ɗaukar mata wayarta,kamar mara gaskiya,
Tana shiga whatsapp ɗinta,sai ga wani security ɗin,rai a6ace tace"Mommy kamar mara gaskiya,duk tabi waya ta garƙame da security,"
Allah yaso shima finger print ne,komawa tayi tare da dangwalo yatsan aunty babba,whatsapp ɗin ya buɗe,
Kaitsaye ta shiga chat ɗinsu da Hayaam,anan taga hoton da Hayaam ta tura mata,bai buɗe ba hoton saboda data a kashe take,cikin sauri hafsat ta kunna data ɗin,nan take yashiga loading yana ƙoƙarin budewa,a hankali hoton ya soma bayyana,ƙura ido hafsat tayi tana jiran hoton ya kammala buɗewa,
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake Daram!!Dararam!!tamkar ana buga ganga,Waro ido waje hafsat tayi agigice a matukar razane,tamkar wadda taga Zombie,hankali a matuƙar tashe tace"Kai!!!"
Hannunta har kerma yakeyi wurin yin zooming ɗin hoton nasu ta matso dashi kusa don tagani dakyau,gaba ɗaya tagama kiɗima,wata irin zufa ce ta soma tsattsafo mata agefen fuskarta,daƙyar take iya haɗiye yawun bakinta saboda maƙoshinta daya bushe ƙamas,juyawa tayi ta kalli Aunty baba dake ta faman mutsu-mutsu alamar zata farka daga baccin da takeyi,aikuwa cikin sauri tayi deleting ɗin hoton gaba daya,sannan ta rufe wayar,tayi wurgi da ita asaman gadon,jikinta na kerma ta fuce daga dakin,gudu gudu sauri sauri haka take tattaka stairs ɗin ƙiris ya rage ma tayi tuntu6e saboda yadda jikinta ke rawa kafkaf kamar wadda sanyi ya kama,
Bedroom ɗinta ta koma,tana shiga ta aza hannu akai tana faɗin"Tashin hankali!In har dagaske ne abunda idanuna suka gane mun acikin hoton nan kenan hakan na nufin cewa HOSANA DA JAHAD Suna araye kuma suna a gidansu daddy!taya hakan ya faru?Kenan Ya Omar shine ya ɗaukesu?Ina wannan tsohon mutumin da mommy tasa ya kwashe su da nufin ya zubar dasu?Taya akai hosana da jahad suka kasance ƴa'ƴan uncle ɗinmu!?wacece ita ɗayar yarinyar mai kama dasu sak!dama su ƴan uku ne?Tabɗijancan,akwai matsala,
Komawa tayi gefen gadonta ta zauna tare da kifa hannunta asaman fuskarta,hosana da jahad suna raye,suna gidan abban mu,wayyo Allah na,ina farin ciki sosai,duk da ina tsoran abunda zai biyo baya,Ashe jinina ne su!shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu,mun cutar dasu sosai,mun zalunce su bayin Allah,mutuwa ce kawai batazo ta daukesu ba acikin gidan nan amma sunsha wahala,sun ƙuntata,tabbas Mommy mun shiga uku,idan Abba yaji,daga ni harke ba wanda zai tsira,kwara ni hukuncina mai sauƙi ne tunda na nuna masu soyayya daga baya amma ita mommy itace silar fitar dasu daga gidan nan don azubar dasu,Wayyo Allah na!,
Yatsun hannunta sae faman kerma sukeyi,jiki na rawa ta ɗauki wayarta tare da lalubar numbar junaid ta danna mashi kira,
A lokacin junaid yana tare dasu Uncle abusufyan,dama sai daya fara kiranshi a waya ya tambayi address ɗin inda suke ya bashi,har an kammala yi masu saloon tuntuni,anyi masu ƙunshin jan lalle a hannuwansu,daga can suka wuce shoprite siyayya,bayan sun kammala siyayyar,suka biya gidan Uncle ɗin nasu wuraren 6,saboda su kwaso wasu daga cikin kayansu Jahad da hosana wanda zasuyi kwalliyar walima dasu,
A bayan motar junaid aka sanya trolley ɗin kayan nasu,sannan Sehrish da hosana suka shige motar abusufyan,jahad kuma ta shiga motar junaid,atare motocinsu suka fita daga cikin gidan,
Tunda jahad ta shiga motarshi,ya ɗaure fuskarshi,dama tun wurin siyayyar yake ta shan mur yana murtuke mata fuska,amma hakan bai hana tayi masa magana ba,duk in ta ɗauko abu sai ta gwada mashi ta tambayeshi zaiyi mata kyau,daƙyar yake amsa mata da eh,ko a'a,sai dae kawai tayi murmushi ta girgiza kai,
Kiran Hafsat na shigowa a wayarshi,yace"ki ɗauki wayar,ki amsa wayar sai ki sanyata a handsfree,"
hannu jahad tasa tare da ciro wayar daga aljihun gaban rigarshi,picking call ɗin tayi bayan ta sanyata handsfree sannan tayi Mata sallama,
Muryar hafsat ce ta karaɗe kunnansu"Junaid!kana ina ne"? Gaban jahad ne ya faɗi rass saboda jin muryar hafsat,duk da bata tabbatar da cewar ita bace,amma muryar tayi mata kama da ta sister hafsat,
"Ina akan hanyar komawa gida ne yanzu hakan,"
Hafsat tace"junaid dan Allah so nake in tambayeka,waɗannan yaran ƴa'ƴan uncle abusufyan Ƴan uku ne"?
"Of course they are triplet,"ya bata amsa a yayin da yake ƙoƙarin juya sitiyarin motar,ya karya kwana,
Hafsat tace"Ya sunan su"!
Juyowa yayi ya ɗan kalli jahad da idanunta ke akan shi,kafin ya mayar da idanunshi kan driving din da yakeyi,a jere ya ambaci sunayensu"Hosana Sehrish Jahad"!hafsat na jin haka,a gigice ta kashe wayar,
"kiran ya katse,"Jahad ta faɗi tana ƙare ma wayar kallo,
"May be network ne,idan na koma gidan zan kirata,"
"In mayar maka da wayar"?
"A'a ki ruƙe a wurinki,idan mun isa gida zan kar6a,"
ta amsa mashi da toh,
Gallery ɗinshi ta shiga tana kallon kyawawan hotunanshi da yayi,tare da videos,yawanci duk na ban dariya ne,wasu yana a kwance,wasu ya zullo harshe waje,wasu hotunan ya kashe idanunshi,
Dariya ta dinga yi a yayin da take kallon videos ɗinshi na tiktok,duk yana sauraron sautin dariyarta,wani lokacin har satar kallon fuskarta yakeyi,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,musamman inta tuntsire da dariya,wani sa'in hada kifa kanta saman laps dinta saboda tsabar dariya,murmushi kawai yayi tare da mayar da hankalinshi akan driving ɗin da yake yi,a haka har suka ƙarasa gida,
Bayan hafsat ta katse kiran,ta Kifa kanta asaman pillow ɗinta,tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka,dama ance dana sani ƙeya ce,
Farkawa Aunty babba tayi da wata irin matsiyaciyar yunwa,sae faman hamma takeyi,tashi tayi daga zaune tare da kai hannu ta ɗauki wayarta tana cewa"Ko hayam ta tura mun da hoton?bari na duba na gani,Allah yasa dai bata manta ba,"
shiga cikin whatsapp ɗinta tayi tare da duba chat ɗinsu da hayaam,rai a6ace taja dogon tsoki tare da cewa"Wai dama bata turamun hoton ba!harfa ƙara nanata mata nayi akan ta tura mun hoton amma bata turo ba," ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da wayar saman gadon,
Saukowa tayi daga saman gadon,fita tayi daga cikin bedroom din ta sauko ƙasa,kai tsaye ta nufi kitchen,
Batare da 6ata lokaci ba,ta shiga harhaɗa kayan da zatayi amfani dasu,bayan ta ɗaura girkin,ta ɗebo snacks a plate ta haɗo da coke mai sanyi ta dawo falo,ta zauna,tana ci tana kallo a plasma hankalinta kwance,
jin motsin mutun a gefenta yasa tayi firgit tare da juyawa don taga wanene,ashe hafsat ce atsaye yanayinta kamar na wadda tayi amai da zawo,fuskar nan tayi gwanin ban tausayi,idanunta sun ƙankance saboda kukan da tasha,
"Hafsat!lafiya naga fuskarki tayi jawur?kinyi kuka ne"?
Girgiza kai hafsat tayi tare da cewa"Babu komai mommy,wani film nake kallo acikin wayata,shine ya sanya ni kuka,"
Tsoki Aunty babba taja"shirmen banza,kawai daga kallon film saiki kama kuka kamar wata sakarya,"
murmushin takaici hafsat tayi tare da samun wuri daga gefen aunty babba ta zauna,batare da tace komai ba,
Aunty babba taci gaba da cewa"gaskiya kowane film ne wannan ya ciri tuta tunda har ya iya sanyaki zubar da hawayenki,yadda kike da shegen taurin kai,
"Mommy ba zaki gane bane,"
"Taya za'ae in gane?tunda bakiyi mun bayanin meya faru ,acikin film ɗin ba,ki ɗan bani labari mana,"
Gyara zama hafsat tayi kafin ta soma bata labarin kamar haka"wata matace fa,mijinta ya kawo mata wasu marayun yara donta rainesu a wurinta,tun ranar da mijin ya kawosu gidan shi kuma yayi tafiya,ae kuwa matar nan,ta shiga gana masu azaba,ta hanasu abinci yunwa kamar zata kashesu,har bugunsu takeyi,sannan kuma ta dinga sanyasu aikin wahala,har saida suka kusa rasa rayuwarsu,mommy kinsan meya faru"?
Dakatawa Aunty babba tayi daga shan lemun hannunta da takeyi tace"a'a saikin faɗa,"
"Hmmm,Mommy ƙarshe fa matar nan,tasa aka kwashe yaran nan,aka 6atar dasu saboda kawai kar asirinta ya tonu a wurin mijinta...'
"Hakan da tayi yayi mun dai dai,"Acewar aunty babba,
Murmushi hafsa tayi kamin tace"Ae ban ƙarasa maki labarin film ɗin ba,bayan tasa an zubar da yaran nan,ita duk a tunaninta sun mutu ma,Ashe can wurin gararin rayuwar da sukeyi a daji Allah ya haɗasu da kanin mijinta har ya taimakesu ya kaisu gidansu mijin,da akayi bincike aka gano cewar yaran ƴa'ƴan kawunsu ne wato ƙanin mahaifinsu,"
Aunty babba tace"tashin hankali!ita ko wannan ya zatayi da kanta?
Dariya hafsat tayi tare da cewa"Nima abunda nake tunani kenan!amma Mommy idan kece ya zakiyi,"
shiru Aunty babba tayi tana tunani kafin daga bisani tace"Ae kawai tunkan asirina ya tonu zan gudu ne,a neme ni arasa,amma nikam hafsat wai ya sunan Film ɗin nan ne?tayi tambayar tare da kallon hafsat ɗin wadda itama kallonta takeyi,mikewa hafsat tayi tsaye tare da cewa"An fara kiran sallar magriba,bari naje nayi salla,"
"Amma baki faɗamun sunan film ɗin ba!"Aunty babba ce ta sake nanata mata tambayar da tayi mata,
*AN YANKA TA TASHI* shine sunan film ɗin mommy,yanzu na kalleshi a tashar youtube,tana kai ƙarshen maganarta,ta juya da sauri ta wuce bedroom ɗinta,
Zugudum Aunty babba tayi tana maimaita sunan film ɗin da hafsat ta faɗa mata,wato An yanka ta tashi,
Aranta tace"gaskiya ya kamata in kalli film ɗin nan,Inaso inga yadda matar nan zata ƙare,ko ya mijinta zaiyi da ita?tabɗijancan,akwai badaƙala,"tayi maganar tare da mikewa ta wuce kitchen domin ta duba girkin da ta ɗaura,
Bayan ta kuma fitowa daga kitchen ɗin,upstairs ta wuce bedroom ɗinta,gefen gadon ta zauna tare da miƙa hannunta ajikin drawer chest ta janyo gidan farko,sabon sim ne ta ɗauko tare da daukar wayarta dake ajiye saman gadon,zura sim card ɗin tayi aciki,sannan ta lalubo lambar wayar Ammi wadda tayi copying kan phone,danna mata kira tayi,nan take kiran ya shiga,kusan sau uku kiran na katsewa batare da anyi picking ɗinsa ba,tana kira a karo na hutu Ammi ta ɗaga kiran 😳
ɗan zaro ido Aunty babba tayi kafin ta gyara natsuwarta tare da zabga sallama"Assalamu Alaikum Ammi barka da warhaka,"ta maƙe muryarta yadda ammi bazata iya gane muryar wacece ba,
on the other hand Ammi ta amsa mata da cewa"Wa'alaikumus salam,barkanki dai,zan iya sanin dawa nake magana"a dake take magana,
Aunty babba tace"Nasan bakisan dawa kike magana ba,saboda baki sanni ba,Ni matar abokin Abusufyan ce,wadda ke zaune a ƙasar turkey,"
Shiru ammi tayi tana sauraran me magana,
Aunty babba taci gaba da cewa"akwai wani mummunan abu da abusufyan ya aikata a 6oye baison kowa ya sani,shiyasa na kira don in sanar dake,don banason abunda zai ta6a mutuncin family ɗinku,wannan abun kunya ne,muddin ya fita waje mutane sukaji to fa,zaku rasa duk wata ƙima da martaba da kuke da ita....'
tana cikin magana Ammi ta dakatar da ita"Ya isa haka!banason wata kwanana,ki faɗamun abunda kikeson sanar dani!me Abusufyan ya aikata?wani laifi ne wannan da har kike ikirarin zai ta6a ƙimar family ɗinmu a idon jama'a,"?
Wani irin wahalallen yawu aunty babba ta haɗiye kafin daƙyar ta soma kora mata jawabi kamar haka
"Shekarun baya da dadewa,Abusufyan yayi ma wata fyaɗe,harta samu ciki....."
Wata irin tsawa da Ammi ta daka mata har sae da takusa sakin fitsari a wando,a tsiwace tace"Dakata!ki iya bakinki!kinaso ki shiga tsakanina da ɗana ne!wacece ke,kada kiyi tunanin kin kirani da 6oyayyiyar number,zan iya sa agano munke duk inda kike,"
Muryar Aunty babba na kerma tashiga faɗin"wlh dagaske nake ammi ba ƙarya nake ba,gobe idan kinzo abuja wurin walima,zaki ga yaran,ae suna nan gidan Abba,Sun jima suna 6oye maki gaskiya,saboda tsoron hukuncin da zaki yanke ma Abusufyan,yanzu haka maganar da nake maki,sun gama shirya yi maki ƙaryar cewar yaran ba shaggu bane ta hanyar aure aka haife su bayan ba haka bane,suna nan yaran ƴan uku ne mata,sun girma sosai,' tana kai ƙarshen maganar Ammi tace"Kin gama"?
Shiru Aunty babba tayi tana faman mazurai aranta tace"Wannan tsohuwa badae taurin kai ba,bansan ya zanyi na fahimtar da ita ba,ta cika jaraba,"
tana cikin wannan zancen zucin Ammi ta katse kiran,
Wurgi Aunty babba tayi da wayarta,tare da mikewa tana cewa"Ae shikenan,nasan cewa gobe tana ganin yaran zata tuna da kalamai na,daga nan saita ɗauki hukuncin daya dace,"
❤🤍❤
*Boss Bature*
Zaune yake asaman Sofa mai mazaunin mutun uku,gaba ɗaya ya tattara hankalinshi akan Laptop ɗinshi da yake daddawana anatse,jikin shi na sanye da linen tank top,blue colour tabi shape din jikinsa,sick pack din nan nasa ya bayyana ajikin rigar,trouser ɗin jikinsa kuma white colour ne,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga kowani sashe na jikinsa,
Shigowa Azmee tayi part ɗin nasa da sallama a bakinta,yayin da hannunta ke ruke da tray,amsa mata sallamar yayi batare daya ɗago ya kalleta ba,ƙarasawa azmee tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman empty table din dake a gefenshi,hannu takai tare da ciro plate ta daukko serving spoon tana ƙokarin buɗe warmer,muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"ɗazu da safe meyasa kika kawomin breakfast?kuma kika gyaramun bedroom ɗina,dama kece ke gyara mun part ɗina ne"?
gabanta ne taji ya faɗi rass,muryarta na kerma tace"A'a bani bace,Sehrish ce,"
"Meya hanata yi mun aiki,"?yana magana yana danna laptop dinsa har time ɗin bai ɗago da idonshi ba ya kalle ta,
Azmee tace"Am...um...dama..."bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannunshi,cikin sauri ta shiga taitayinta,
Cike da bada Umarni yace"Call her right now,"
Jiki na rawa azmee ta juya tare da fucewa daga part dinsa,downstairs ta saukko,babu kowa a falon duk suna a bedroom ɗinsu,wasu ma sunyi bacci,
Kai tsaye ɗakinsu Sehrish taje,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kwankwasawa,sai faman knocking takeyi amma ba'a buɗe mata kopar ba,da alama sun jima da yin bacci,
Har sae da ta fidda rai da za'a buɗe mata kopar,tana kokarin juyawa tabar wurin,taji alamun za'a buɗe kopar,Jahad ce ta buɗe ɗakin tana tambayar wanene,
Ganin azmee yasa tayi saurin gaishe da ita cikin girmamawa,
Azmee da nan take ta gane ba sehrish bace tace"kiyi hakuri na tashe ki kina bacci,Sehrish nake nema,dan Allah ki sanar da ita cewa SGR yana nemanta a part ɗinsa,"
Jahad tace"tayi bacci,bari na tashe ta,"tayi maganar tare da juyawa cikin sauri ta shiga cikin ɗakin,
Wucewa azmee tayi ta koma kitchen,cike da zullumin mai zai biyo ba idan Sehrish ta sanar ma Sgr cewa Uncle abusufyan ne ya hanata yin aiki a part ɗinsa,tabbas za'a kwashi ƴan kwallo,
"Sehrish!ki tashi babban yaya yana son ganinki a part ɗinsa,dan Allah ki tashi kije,"jahad ce keta kokarin tashinta daga bacci,sehrish kuwa sai faman mutsu mutsu takeyi,daƙyar ta iya cewa"Wanene ke nema ne'?
Jahad tace"babban yaya,"
Jin sunanshi yasa Sehrish buɗe idanunta ta wurgasu kan jahad dake tsaye,yatsina fuska tayi tare da maimaita sunan nashi"babban yaya?shike nema na,waya faɗa maki"?
"Aunty azmee,yanzun nan bata jima da tafiya ba,naga kamar ma bata acikin natsuwarta,"
Jin hakan yasa gaban sehrish faɗuwa rass,yunkurawa tayi tare da mikewa zaune,ta saukko da ƙafafunta ƙasa,kafin ta miƙe tsaye,saboda tsabar saurin ta fita ko Mayafi bata ɗauka ba,gashi kanta ko kallabi babu,sumar kanta ce da tasha gyara,an mayar mata da gashin mai gazar gazar ya sauko har kafaɗarta,a hankali gashin kan nata ke toho yana fitowa,har ta launin gashin anyi mata dying dinsa ya koma 2 colour,Kayan bacci ne ajikinta riga da wando sharara suke,farare masu laushin gaske,irin waɗanda kana sanyasu ajikinka,Ko baka jin bacci nan take zai zo maka,
Tunkan ta ƙarasa shiga falon nashi take jin ɗar ɗar acikin zuciyarta,tun jiya rabon da ta sanyashi acikin idanunta,daƙyar ta iya yi mashi sallama tare da kutsa kai cikin falon nashi,bai amsa sallamarta ba,har ta ƙarasa inda yake,atsaye muryarta na rawa tace"Gani,"bai dago ba kuma bai tanka mata ba,sae ma cigaba da danna system ɗinshi da yake yi,lokaci bayan lokaci yakan kai hannunshi ya dauki Coffee ya kur6a,zuba mashi ido tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,ba ƙaramin kewarshi tayi ba,sam batayi tunanin ma zai nemeta ba,
sai da ta ƙara cewa"babban yaya gani,Aunty azmee tace kana kira na,"sannan ya soma magana anatse"yau da safe,meya hanaki zuwa part ɗina"?
Shiru tayi gabanta na faɗuwa,batasan amsar da zata bashi ba,saboda tsoran abunda zai biyo baya,
"Kinsan bana maimaita magana,amsarki nake jira,"
Runtse idanunta tayi aranta tana fadin"nashiga uku,!Allah ka kawomin ɗauki,bansan me zan faɗa masa ba,"shirun da tayi mashi ne ya fusata shi,aikuwa a zafafe ya daka mata tsawa,har sai da ta zura da gudu saboda yarda ta tsorata,kama hanyar fita tayi saboda ruɗewar da tayi,hakan yasa ya miƙe tsaye tare da bin bayanta,ruƙo hannunta yayi tare da fusgota ta dawo saitin shi,Waro ido waje tayi tare da ja da baya da baya,har suka ƙure ma bangon,runtse idonta tayi muryarta na kerma tashiga faɗin"Am so sorry babban yaya,I can explain,zan faɗa maka,"
A hankali ya ware blue eyes ɗinshi akan fuskarta,sumar kanta yabi da kallo,yayi mamakin ganin yadda gashin yayi tsayi cikin ƙankanin lokaci har ya kamo kafaɗarta,gyaran gashin da akayi mata ya ƙara fiddo da kyawun fuskarta,mayar da idanunshi yayi akan La66anta dake ta faman kerma duk tabi ta gigice,lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa,moving ya ƙarayi gaba ɗaya yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinshi,lokacin da taji tsinin hancinshi na gogar nata,nan take gabanta ya kuma bugawa daramm,jikinta ya shiga yin kerma ta ko'ina,gaba ɗaya duk tabi ta susuce har lokacin ta gaza buɗe idanunta saboda tsabar tsoro,jin saukar hannunshi asaman ƙirjinta yasa ta yin saurin ware idanunta arazane,kai tsaye suka sauka cikin nashi,face to face,Eyes to eyes,nose to nose,mouth to mouth!!,
A firgice ta janye idanunta daga kan fuskarshi ta mayar dasu akan ƙirjinta,Ashe gaban rigarta ne ta bari a buɗe ta manta bata sanya links ɗin rigar ba,Shine ya sanya hannunshi a wurin yana manne mata su,jurewa kawai takeyi amma ba ƙaramin yanayi Sgr ya jefa mata ba,musamman yadda hannunshi ke nutsewa a cikin boobs ɗinta,ba ita kaɗae ba,hatta shi kanshi daya kai hannunshi wurin saida yayi regretting,saboda wani abu daya dinga jin yana fisgarshi yadda kasan magnet,mayen karfe ba,
daƙyar ya iya zame hannunshi daga saman ƙirjin nata,bayan ya kammala sanya mata links ɗin,Sannan cikin sanyin murya yace"tell me the reason why baki zo yi mun aiki da safe ba!bakisan bana son sharing a aiki na ba!?
Magana yakeyi amma idanunshi sae ƙokarin lumshewa sukeyi tamkar mai jin bacci,wanda kuma ba kowa ne yajawo hakan ba face Sehrish,
Cikin en ena tace"Kayi haƙuri ba laifina bane,Daddy ne ya hanani zuwa"
Cike da mamaki yace"Kina nufin Uncle ne ya hanaki zuwa,"
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,yayin da take ta faman haɗiyar yawu,
. "just without any reason ya hanaki aiki a ƙarƙashi na"?
daga mashi kai tayi alamar eh,
Cije pink lips ɗinsa yayi tare da tsoma hannunshi acikin sumar kanshi yana cakuɗata,ranshi a matuƙar 6ace yace"hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ƙarƙashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!!*
*Tashin hankalin da ba'a sama shi date!*
Gobe walima,suwa suka shirya zuwa💃💃💃💃
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Ranshi a matuƙar 6ace yace"hakan bazai ta6a yiyuwa ba,dole kiyi aiki a ƙarƙashina!ban damu da matsayinshi a wurinki ba,dole ne ayimun biyayya!!!!!!!
Waro ido waje Sehrish tayi tana kallonshi,hankali atashe jikinta sai faman kerma yakeyi,ji take tamkar ta zura da gudu,saboda yadda taga Sgr ya fusata tsoranta kar ya ciro belt ɗin wandonsa ya rufe ta da bugu,tana cikin wannan zancen zucin muryar shi ta katseta da cewa"listen to me!"
Natsuwa tayi tana sauraronshi kamar yadda ya Umarta,
"Banaso na ƙara ganin Azmee tazo part ɗina da sunan za tayi mun aiki,ke nakeso ki kawo mun breakfast sannan ki gyaramun part ɗina,hope u understand?"
Muryarta har kerma takeyi wurin cewa"E zan..na..fahimta,'
Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Okey,yanzu kizo kiyi serving ɗina,then idan kin kammala ki gyara mun bedroom,"babu wasa a fuskarshi yake yin maganar,wato yadda ya tsare Sehrish yadda kasan ƴar cikinshi,ta yi tsuru tsuru,Ni dai bansan ya Sehrish zata ƙare ba,ga umarnin mahaifinta gana kuma yayanta mai matukar tsauri,shin wa zatayi ma biyayya?a sanin mu dai Umarnin Mahaifi shine sama da komai,bayan na mahaifiya,bari mu gyara zama muga yadda wannan Al'amarin zai kaya,
Ja da baya yayi tare da juyawa ya koma saman sofa ya zauna sannan yace"Am waiting for u,"
Jiki asanyaye Sehrish ta ƙaraso inda yake,yatsun hannunta sae kerma sukeyi,a haka ta shiga serving ɗinshi,a plate ta zuba mashi chicken pepper soup ta tura mashi agabanshi,yana ci tana satar kallon fuskarshi,ba ƙaramin mamaki Sgr yake bata ba,ta jinjina ma ƙarfin halinsa na yau,batasan me zai faru gobe ba amma tabbas akwai badaƙala,
Bayan ya kammala cin dinner ɗin nashi,sai da ta gyara mashi bedroom ɗinshi,sannan ta samu ta fito daga part ɗinsa da kayan abincin,a hankali take taka stairs ɗin,ranta a jagule ba don komai ba sai don karya umarnin mahaifinta da tayi,wanda kuma ba komai ne yaja hakan ba face shegen tsoron Sgr da takeyi,da ba don haka ba,da ba abunda zai hana tayi mashi gardama,don a yadda yake da bad temper ɗin nan ta kuskura tace zatayi mashi jayayya,bugu zai kai mata,zuƙunnawa tayi asaman steps ɗin benen tana faman cizon la66anta,a hankali ta furta"sae yaushe ne zan fita daga wannan KURKUKUN ƘADDARAR da nake ciki?yaushe ne abubuwa zasu fara tafiya dai dai arayuwata?daga wannan sai wannan"? Idonta cike tab da hawaye tayi maganar,kafin ta yunƙura tare da miƙewa ta nufi bedroom ɗinsu bayan ta kai kayan kitchen,a hankali ta tura ƙopar tare da shigewa ciki,bayan ta datse ƙopar ta juya,mamaki tayi ganin jahad ruƙe da wayarta a hannunta ta ƙura ma screen ɗin wayar ido,duk a tunaninta zata zo ta same ta tayi bacci,ashe bata koma bacci ba tun bayan da Azmee ta tashe ta,
Ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon a gefenta ta zauna,cike da mamaki take kallon jahad,ganin ko motsi ba tayi,bama tasan ta shigo ɗakin ba,ko menene yaja hankalinta haka?
"Jahad!"Sehrish ce ta ambaci sunanta,a firgice ta juyo tana kallonta,ganin sehrish yasa ta sakin murmushi tare da cewa"Har kin dawo,ae nayi tunanin acan zaki kwana,"
dariya sehrish tayi tare da dungurin goshinta tace"Abun hada tsokana,Nima nayi tunanin zanzo na same ki,kina bacci ashe idonki biyu,me kike yi da wayar ne"?don naga gaba ɗaya yaja hankalinki,"
Ƙayataccen murmushi jahad ta saki tare da cewa"Hmmmm ba zaki gane bane,wani zazzafan hausa novel ne nake karantawa acikin wayarki,dama jira nakeyi kizo in tambayeki a ina zan samu cigaban littafin"?
Cike da mamaki Sehrish tace"Novel kuma?ae ni bana karatun littafin hausa,banma san ya akai kika samu littafin a wayata ba,don gaskiya bana ajiye su,"
Wani kallon rainin wayau jahad tayi mata tare da cewa"Kina nufin duk haɗuwar littafin nan baki ta6a karanta shi ba!hakanan kike ajiyar shi acikin wayarki?
Yatsina fuska Sehrish tayi tare da cewa"nifa bansan dashi ba,may be cikin friends ɗina na makaranta ne wata wurin tura ma wasu ta turamun shi batare da sani na ba,"
jinjina kai jahad tayi tace"gaskiya an barki a baya,tunda uwata ta haife ni ban ta6a karanta littafin me shegen daɗi irin wannan ba,tunda na fara karantashi bakina ke awashe,kamar anyi mun albishir da gidan aljanna,"ta karasa tana daria,
Ta6e baki sehrish tayi tare da cewa"Wai ya sunan Littafin ne?naji sai faman zuzuta shi kike yi,inaso inji sunanshi ne saboda tun daga kan sunan littafi ake tantance in mai daɗi ne ko mara daɗi,"
Ƙayataccen Murmushi jahad ta saki tare da Furta sunan Littafin*A SANADIN MAKWABTAKA*!
Maimaita sunan Sehrish tayi"A sanadin makwabtaka"
Jahad tace"kwarai kuwa,sunanshi kenan,"
Gyara zama sehrish tayi tare da cewa"kawo wayar mu gani,zan jaraba karanta one page naji ya daɗinsa shin yakai Abban sojoji da nake jin friends dina nata faman cewa ya hadu"?
Jahad tace"Ae ya zarce nan,"tayi maganar tare da miƙa mata wayar tace"one page kika ce zaki karanta,zan jira ki kammala don inci gaba daga inda na tsaya,"
Hannu sehrish tasa tare da kar6ar wayar,ta buɗe page ɗin littafin asanadin makwabtaka,a natse ta fara karantashi,"
Zuba mata ido jahad tayi tana jira taga reaction ɗinta,
a hankali murmushi ya fara bayyana akan fuskar Sehrish,daga ƙarshe ma ta fashe da dariya,tunda tafara karanta littafin sae faman zabga murmushi takeyi,ita da tace zata karanta one page sai gashi ta zarce page biyar,ganin abun ya wuce gona da iri yasa jahad sanya hannu ta kar6e wayar tana cewa"Ya isa haka,je ki kwanta,gobe akwai shirye shiryen waleema,"
ɗaure fuska sehrish tayi tare da cewa"wlh baki isa ba,sai da kika fara ɗanɗana mun zuma abakina na lasa daga baya kuma kizo kice zaki hana ni"?
itama jahad ɗin ta tamke fuskarta tace"ae ni na fara karantawa tun farko,ke da bakisan ma da zaman littafin acikin wayarki ba sai da na faɗa maki"
wurga mata harara sehrish tayi tare da miƙa mata hannu tace"Bani wayata,"
Jahad tace"wlh bazan bada ba,sai na kammala karanta littafin nan,"
Abu kamar wasa suka shiga cece kuce,ran sehrish yayi mugun 6aci,aikuwa ta cakumi wuyan rigar jahad,nan fa suka shiga kokowa asaman gadon kamar ƴan wrestling,wani bugu da Sehrish takai ma jahad a kumatunta ne yasa ran jahad ya 6aci,a fusace tayi wurgi da wayar Sehrish,kai tsaye ta faɗi saman tiles,ta daku sosai ji kake taratssss!screen ɗin wayar ya tarwatse,
Tashin hankali,
la66an sehrish har kerma sukeyi wurin cewa"kika fasa mun wayata"?
Girgiza kai jahad tayi hankalinta a matuƙar tashe tace"dan Allah sehrish kiyi haƙuri,wlh bada sanina nayi hakan ba,raina ne ya 6aci saboda naji zafin bugun da kikai man"
Hawaye ne suka cika idon Sehrish cikin murya kamar ta mai son yin kuka tace"Ni babban baƙin ciki na,ba wayar data fashe bane,nasan daddy zai iya canzamin wata,Amma littafin fa?a ina zan same shi,daga ji zai dauke ma mutum damuwa yasa shi nishadi"?
Jahad tace"Am so sorry sehrish,na maki alƙawarin cewa,zan nemo maki shi,nasan baza a rasa me shi ba,akwai wata class mate ɗina sunanta hafsat bature,ta kware wurin karanta littattafan hausa,insha Allah idan muka koma school zan tambayar maki ita,nasan bazata rasa littafin a wayarta ba,idan ma babu littafin to ina da tabbacin cewar tasan marubuciyar shi,sae ta bamu numbar wayarta,"
Jin haka yasa sehrish sakin murmushin jin daɗi,matsawa tayi tare da rungume jahad tace"yawwa jahad,kinyi tunani mai kyau,nagode sosai,yakamata mu kwanta yanzu,dare yayi fa sosai,"
tayi maganar ayayin da ta gyara kwanciyarta,itama jahad ta kwanta,atare su kayi addu'ar bacci cikin ƙanƙanin lokaci baccin ya ɗaukesu,
"Nagode sosai da shawarwarin daka bani,kuma insha Allah ina da tabbacin cewar in muka biyo mashi ta wannan hanyar zamuci nasara akanshi,abun zai zama tamkar wasan kwaiwayo," Acewar Abbansu junaid dake tsaye a bakin ƙopar fita daga ɗakin Uncle abusufyan,Uncle ɗin na a bayanshi fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,da alama sun kammala tattaunawar da sukeyi,
"Nike da godiya yaya Hossain,idan har wannan abun ya tabbata,zanfi kowa farin ciki,"
Juyowa Abba yayi cike da zolaya yace"kada ka manta,gobe ne fa sunan ƴan ukun da aka haifa maka,me zaka yanka masu"?
..sunnar dakai ƙasa Abusufyan yayi yana dariya,yace"Sa za'a yanka masu guda uku,raguna uku,ɗawisu guda uku,ƴan shila guda ɗari uku,kaji guda ɗari uku suma,"
Dariya Abba yayi yana bubbuga kafadarshi yace"Abun ya ƙayatar dani wato komai guda uku kenan za'a yanka masu,idan ma ba uku ba to ɗari uku,dole dae ukun ta fito kamar yadda suke ƴan uku,a ƙagare nake da goben nan tayi,bari na hanzarta zuwa na kwanta,"
"Allah ya nuna mana ita lafiya,"acewar abusufyan daga haka Abba ya bude kopar tare da fucewa yana faɗin"mu kwana lfy,"
Bayan fitarshi,Abusufyan ya koma tare da hayewa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke fuskantar ceiling,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face ABU,a kullum cikin tunanin wani hali take ciki yake,haƙiƙa ya damu da ita sosai,kusan kullum ne sai yayi mafarkinta,dama da yawa idan ka sanya abu aranka,zaiyi wuya bakayi mafarki akansa ba,babban abunda yafi damunshi duk in zai ganta a mafarkin cikin wani irin mawuyacin hali,
"Bakomai ne yasa na damu sosai akanta ba,face sanin cewa ita marainiya ce,bata da kowa a duniyar nan wanda zai damu da ita idan bani ba,da kuma ƴa'ƴan data haifa ba,Abu bata da kowa bata da wanda zai neme ta idan wani mummunan abu ya faru da ita,da ace ƙaddara bata haɗani da Abu ba harna aureta ba,a yau akace ta 6ace,nayi imanin cewa babu wanda zai damu akan hakan,mahaifinta ne kawai shi kuma Allah yayi mashi rasuwa,Allah yajiƙanka baba buzu,haka ya damƙa mun amanarta,duk da yasan halina bana jin magana ga ƙuruciya dake fusgata,yayi mun halaccin da bazan ta6a mantawa ba,kuma Insha Allah zan ruƙe mashi amanar daya bani,bazan ta6a mantawa dashi ba,saboda shine silar komai,gashi har nasamu ƙaruwar ƴan uku tare da ƴarsa,naso ace yana raye nasan zaifi kowa farin cikin ganin jikokinsa,'
Hawaye ne suka soma gangarowa daga cikin idanuwansa masu ɗumin gaske,murmushin takaici ya saki tare da gyara kwanciyarshi,ya runtse idanunshi daƙyar bacci ya ɗauke shi,
A 6angaren Abba kuwa,bayan sun rabu da Uncle abusufyan,yana shiga bedroom ɗinshi,ya tsaya turus ganin junaid kwance yana sharar bacci,ga mommynshi agefe tana bacci itama,girgiza kai yayi tare da cewa"bansan meyasa junaid keyi mun haka ba,ya raina ni wlh,"juyawa kawai yayi tare da fucewa daga bedroom ɗin ya koma upstairs bedroom ɗin junaid ya nufa ya kwanta,ya ƙyale shi ne saboda yana cikin farin cikin gobe walima,baison abunda zai 6ata ranshi,
Wuraren ƙarfe 2 na dare junaid ya farka sakamakon zungurar shi dayaji anyi da sanda,a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare manyan idanunshi masu ɗauke da bacci,ƙasa ƙasa yaji ana ambatar sunanshi Junaid!junaid!aikuwa a tsorace ya sanya hannunshi tare da toshe kunnanshi ya fasa uwar ƙara,kai tsaye sautin ƙarar daya saki ta daki dodon kunnan Alexandra,a firgice ta farka,ganin junaid da tayi a zaune jikinsa sai kerma yake yi hakan yasa ta miƙe tare da janyoshi jikinta tana faɗin"junaid!romeo ɗina what's wrong with u?baka lafiya ne,"duk tabi ta tsorata da halin da yake ciki,
..Muryarshi na kerma yace"Mommy,wani abu zai faru dani,dan Allah ki taimaka mun,banso in mutu yanzu,"
Jin wannan maganar ta junaid ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba,kankame shi ta ƙarayi muryarta na rawa tace"Junaid,kadaina faɗin haka banason ji,babu abunda zai faru dakai indai kana tare dani,nasan cewa mafarki kayi,pls calm down ur mind,mu koma mu kwanta,
ɗagowa yayi daga jikinta,cikin shessheƙar kuka yace"Mommy dan Allah,ki tashi muyi sallah,sai kiyimun addu'a,"
a ruɗe tace"Salla kuma junaid,am not a muslim bana sallah,zan daiyi maka addu'a,"
"A'a mommy nidai ki tashi muyi sallah,kiyimun addu'a,"Ashagwa6e yayi maganar,
"Junaid ka fahimce ni,bakasan cewa niba musulma bace!ko daddynku bai ta6a faɗa maka bane,Ni bana sallah,I don't even know how to do it,"
Jin haka yasa junaid sake fashewa da wani sabon kukan mai sautin gaske yana cewa"Mommy ki tashi muyi sallah,ki tashi mommy!wlh idan baki tashi munyi sallah kinmun addu'a ba mutuwa zanyi,"
Tashin hankali,gaba daya junaid yabi ya rikice mata ya hanata sakat,duk yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita ba musulma bace,bata sallah amma abun ya faskara,junaid ya kurmance mata,
Babu arziƙi ta amince zatayi sallar,tasata gaba yayi ta shiga toilet ta dauro alwala,ko alwalar bata wani iyaba,ruwa kawai ta watsa a fuskarta,ta wanko hannayenta da kafafuwanta tafito,shi ma ya shiga cikin toilet ɗin,wucewa tayi wurin wurin closet ɗinsu,ta buɗe kayan Abbansu ne a jere sai kayan sawar ta,wanda tazo dasu,gaba daya babu hijabin da zata sanya,dakyar ta samu wani mayafin doguwar rigarta mai ɗan tsayi,ta ɗauko shi tare da sanyashi ajikinta,sae yayi mata tamkar hijabi,
tsayawa tayi tana jiran junaid ya fito suyi sallar,lamarin nashi ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ƙiri ƙiri junaid yasata za tayi sallah,ya rufe idonshi ya nuna tamkar baisan cewa ita ba musulma bace,aranta tace"Anya junaid bai samu ta6in hankali ba?in ba haka ma meyasa zai yi forcing ɗina akan inyi salla bayan yasan cewa ni ba musulma bace,Omg!ni bansan ma ya akeyin sallar ba,ko time ɗin baya dana ta6a musulunta ba don Allah nayi ba,ko sallah banyi a lokacin,"
tana cikin zancen zucin nata sai ga junaid ya fito daga cikin toilet yana faman yarfa hannunshi,ruwan alwalar da yayi yana ɗiɗɗigowa ƙasa,
Carpet ɗin salla ya dauko masu na abbansu sannan ya dawo ya shimfiɗa masu shi,
Juyawa yayi tare da kallon Mommyn tasu wanda tayi sototo tana binshi da kallo,
"Ni zan shiga gaba saiki tsaya abaya,"
Dawowa bayanshi tayi ta tsaya,shi kuma ya tsaya agaba,tare da daidaita natsuwarshi,ya kabbara sallar,anatse suka shiga yin sallar atare,tunda suka kai raka'a dayan farko,bacci ya kwashe Alexandra,junaid bai sani ba yaci gaba da yin sallarshi,sai da yayi kusan raka'a takwas sannan ya sallame,
cikin bacci taji an ambaci sunanta da ƙarfi"Mommy"!!a firgice ta farka tare da buɗe idanunta tana kallonshi,muryarta adisashe irin ta mai bacci tace"junaid har mun kammala sallar,"zum6ura mata baki yayi rai a6ace yace"nadai kammala sallar mommy,kin barni ni kaɗae,kina ta bacci,"
cikin lallashi tace"kayi haƙuri romeo ɗina,saida na faɗa maka cewa banyin sallah,nifa ban iya ba,nadai samu nayi ɗaya,dakyar itama na samu nayi ta,don bacci nake ji,"
"Shikenan kiyimun addu'a yanxu,sai muje mu kwanta"
Yadda yayi maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,nan take taji kamar bata kyauta mashi ba,jiki asanyaye ta sanya hannunta tare da ruƙo hannunshi,ta shiga karanta mashi addu'oin,cikin harshen Faransanci,bai damu da yaren da takeyi mashi addu'ar ba,saboda yasan cewa Allah yana ji da kowani irin yare aka roƙesa,"
Ta jima tanayi mashi addu'a tana tottofa masa asaman sumar kanshi,kafin daga bisani suka koma saman gadon suka kwanta,ba ƙaramin kwanciyar hankali junaid ya samu ba,tunda ta tofa mashi addu'ar nan take yaji wani sanyi aranshi,tamkar an bashi ƙwarin guiwa,kuma tunda ya kwanta bacci ya ɗaukeshi bai ƙara jin an zungure shi ba,
DARE YAYI GARI YA WAYE,
Tun bayan Kammala Sallar asuba,Azmee da Saude,Suka fara ɗaura girke girken da zasuyi anan cikin gida,Uban aiki ne a gabansu,saboda Abinci ne kala kala zasuyi,na kasashe daban daban,saukin su ma Naman da za'a yanka basu zasuyi aikinshi ba,An riga da an bada aikin naman already,sai dai kawai in an kammala akawo masu shi Hada snacks sukayi order wanda za'a ci,akwai kuma Naman da Azmee zatayi masu farfesu dashi,da kuma tsiren nama,don ta kware a wannan 6angaren,Sunyi nisa acikin aikin sai ga Hajiya azeema ta shigo,bayan sun gaisa da junansu,itama tace tazo ayi aikin da ita,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,nan suka haɗu su uku,suka tasar ma girkin nan,Cikin ƙanƙanin Lokaci,Wani irin daddaɗan ƙamshi ya gauraye ko'ina na kitchen ɗin,
Hatta main palour ɗin kamshi ya karaɗe cikinsa,gwaggon katsina dake kwance,saman gado,tun bayan sallar asuba ya ɗauketa,tana cikin bacci ta dinga jin ƙamshin abinci nashiga Hancinta,ba arziƙi ta farka tana faɗin"wannan wani irin ƙamshi ne mai tashin mutun daga bacci"?tana maganar tana shinshinar kamshin,saukowa tayi daga saman gadon,jikinta sanye da kayan baccin nan nata na gado,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nata tana tunkarar inda kamshin ke fitowa,
Kamar daga sama suka ji muryar gwaggo tana cewa"Ikon Allah,ƙamshi ya tashe ni daga bacci,ya kawo ni cikin kitchen,don inci daɗi,"
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,kafin suka shiga gaishe da ita,
ƙarasawa tayi cikin kitchen ɗin suna haɗa ido da saude ta watsa mata harara tare da cewa"ya akai kuka bar wannan tana girki?bafa ta iya girki ba,Rannan ta zuba mana Gishirin lalle amatsayin gishiri cikin farfesun nama,gaba ɗaya girkin nan bai ciyu ba,ƙarshe saboda tsoran kar asirinta ya tonu inyi mata faɗa,ta dauki farfesun ba tare da sanin kowa ba taje ta zuba ma karnukan layinmu,kunsan kare da nama nan fa suka lashe farfesun nan tasss suka cinyi shi,aikuwa cikinsu ya kumbura sumtum,sukayi mussai,gaba ɗaya suka mace aka zubdo su,mai karnukan nan yace bazai yarda ba,sai yayi shari'a da Saude,ranar saude har gudawa saida tayi don jin za'a kaita ƙara kotu,yarinya tabi ta burkice mana,daƙyar Harrisu ya biya diyarsu,daba don haka ba,da tuni saude an jima da yanke mata hukuncin kisa....'
Tunkan gwaggo takai karshen Labarin da take basu gaba ɗaya suka fashe da dariya,banda saude wadda ta tur6une fuska,rai a6ace tace"Kai gwaggo,"
gwaggo tace"ƙarya nayi?ko ba haka akayi ba,ki faɗi tsakaninki da Allah in ba ayi hakan ba,ranar fa har gudawa kikayi,kika dinga kuka kina cewa gwaggo ki maishe ni rugarmu,saboda kawai na kashe karnuka shine za'a kai ƙarata kotu,wlh ko shanun baffa na kashe ba za'ayi mani wannan hukuncin ba,sai ku ƴan gayu da kuka ɗauki ran kare da mahimmanci karen da ko hisabi baza'ayi dashi ba,"
Sake fashewa da dariya sukayi,yadda gwaggo take kwaikwayon muryar Saude,ba ƙaramin dariya ta basu ba,saboda hausar irin ta fulanin da basu kware bace,"
fuskar saude tamkar zatayi kuka,batasan meyasa gwaggo keyi mata haka ba,duk in suka shiga cikin mutane saita kunyata ta,wannan labarin da take bayarwa ya jima da faruwa,tun lokacin da Dr harris ya ɗaukota daga rugarsu ya kawota gidansu,lokacin batasan komai ba,ita arayuwarta ba abunda ta bama mahimmanci inba Kiwon shanu ba shi kadae tafi sani,gwaggo kuma bata koyar da ita komai ba,kwana uku da zuwanta gidan ne,ta shiga kitchen ta ɗaura masu girki,tana cikin girkin ta fara neman gishiri zata zuba acikin,gafa gishirin acikin farar roba an zubashi,amma saboda ta saba ganin gishiri kulle acikin leda yasa tayi zaton koba gishiri bane,hakan yasa ta fito ta wuce ɗakin gwaggo don ta sanar da ita cewa babu gishiri a gidan,tana shiga ɗakin gwaggon katsina,ta same ta tana bacci,harta juya zata fita shine taga wasu kullun kaya da aka kawoma gwaggo acikin leda,nan fa ta shiga laluban kayan,ta zaƙulo ledar gishirin lalle ta fuce dashi,duk a tunaninta gishiri ne,dayake kanta a toshe yake,kwata kwata bata lura da lallen dake acikin ledar ba,ita dae kawai gishirin lallan ta ɗauko,taje ta zuba masu acikin girkin,ba don Allah yasa gwaggo ta tashi tana neman gishirin lallanta ba,har saude taji,daba ƙaramin illa zata yi masu ba,karshe dai abun kan karnukan layinsu ya ƙare,tun daga wannan lokacin ne harris ya sanyata a makaranta,da kuma makarantar koyon girki,har ta samu ta kammala secondary,daga nan ne akasamu kanta ya waye,
"Gwaggo me kikeso a zuba maki ne?nasan yunwa ce ta koro ku,"azmee ce tayi maganar,
Gwaggo tace"komi ma da kuka girka,a zuba mun in ɗanɗana inji yaya ɗanɗanon girkin naku yake,don tunda kuka sanya saude acikin girkin nan naku nasan cewa dole a samu matsalar rashin gishiri kodae ta zuqa shi,ko kuma yayi kaɗan,"
murguɗa mata baki saude tayi tare da juyawa ta shige cikin store,tana faɗin"nashiga uku da wannan matar,a haka Haris yakeso in zama surukarta,bansan ya zan ƙare da ita ba,lafiya lou nake yin girkina acan gida,har santi takeyi amma yanzu tazo sai sharri takeyi mun agaban mutane,Zamu koma gida ne,nasan me zanyi mata,ae mun saba dama,"
Saude bata fito daga cikin store ɗin ba,sai da taji fitar gwaggo daga kitchen din,bayan sun zuzzuba mata abincin da suka girka,komai sai da tasa suka zuba mata,a ƙaton tray ta fuce dashi tana cewa"idan na cinye wannan zan dawo a ƙara mun,"
dawowa tayi cikinsu suka cigaba da aiki,azeema tace"sai kin dinga haƙuri da ita,bayin kanta bane,ku tayata da addu'a,Allah ya yaye mata wannan haukan da aka ɗaura mata,"
Saude tace"insha Allah,zamu cigaba da tayata da addu'a,ae yaya harris ya sanar dani komai,na tausaya mata sosai,Allah dai ya tonu asirin waɗanda ke shirya masu wannan maƙarƙashiyar,Allah ya kawo ƙarshensu,"
Azmee tace"ae bazasu kai labari ba,a sannu asannu zasu gane kurensu,"
Suna aiki suna tattaunawa game da irin rayuwar da su sehrish sukayi a baya,
Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin tamkar ba'a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziƙin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buƙaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za'a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar ƙasa da naira dubu ɗari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuɗaɗen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin ɗaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu ɗari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haɗa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai ƙaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan ɗaya,Jahad miliyan ɗaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu ɗan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka'aba ɗakin Allah,harma in roƙe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,
Sehrish na cikin toilet tana wanka,amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi akan Sgr,kalamanshi na jiya ne suka shiga dawo mata acikin kanta,dole tayi aiki a ƙarkashin shi batasan meyasa yake son ganinta a matsayin ƴar aikinsa ba,
Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo muryar jahad,daga waje tana cewa"Sehrish dan Allah kiyi sauri ki fito,inaso nima nayi wankan,kafin asake kiran mu,"
jin haka yasa tayi saurin kammala wankan ta fito,ɗaure da towel a waist ɗinta,shiga ciki jahad tayi,don tayi wankan itama,duk hosana na zaune gefen gadonsu hannunta ruƙe da biro da memo din Sehrish sae faman lissafin kyaututtukan da suka samu takeyi,"
Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"Aiki ya same ki hosana,kowa na ɗokin zuwa yayi wanka amma ke hankalinki na akan kuɗin da muka samu,abunda baki sani ba,idan mukayi wanka mu kayi kwalliya,sae mun samu ninkin abunda muka samu a yanzu,"
Juyowa hosana tayi tare da waro ido jin an ambaci kuɗi tace"dagaske kike sehrish idan mukayi wanka mukayi kwalliya zamu samu fiye da wannan kuɗin da muka samu"?
Jinjina kai sehrish tayi tace"kwarai kuwa,ke dai kawai ki tashi ki fara yin wanka,jahad na fitowa,ki shige ciki,"
Cike da zumuɗi ta miƙe ta koma ta tsaya a kopar shiga toilet ɗin tana kwankwasa ma jahad,
"Ki fito nima in shiga,"
Murmushi sehrish ta saki,dama wayau tayi mata,don taji ɗazu suna magana da jahad tana cewa ita ba yanzu zatayi wanka ba,sae da marece,bayan tun yanzu akeso su shirya,don agansu da kyau,
Gaban dressing mirror ta zauna,tana shafa mai ajikinta,sae faman sauri takeyi saboda taje part ɗin Sgr,kamar yadda ya umarce ta akan taje da safe ta kai mashi breakfast ɗinshi,kuma ta gyara mashi bedroom ɗinsa,light makeup tayi a fuskarta,saboda wannan wankan safe ne zata ɗauka,da anjima Azmee tace za'ayi masu makeover,tamkar brides haka zasu fito,
Bayan ta kammala yin kwalliyar,komawa tayi wurin wardrobe din kayansu ta buɗe tana ƙare masu kallo,dama kullum zata zura kaya ajikinta sai ta tsaya yin ruwan ido wurin za6en kayan da zata sanya,
"Da rana zan sanya shadda lace ɗita,da marece kuma zan ɗauki wankan Swiss lace,yanzu dae bari na sanya wannan Arab gown ɗin,naga sai faman ƙyalli takeyi,in na sanyata ajikina,ba ƙaramin kyau zanyi ba,"ta ƙarasa maganar tare da janyo rigar,golden colour ce,gaba ɗaya jikinta adon stones ne masu ƙyalli da ɗaukar ido,batare da 6ata lokaci ba ta shiga kiciniyar zura rigar ajikinta,daƙyar ta shigeta saboda ta matse ta,gaba ɗaya tabi shape ɗin jikinta,kirjinta ya fito sosai,ga wani uban hips daya bayyana ajikin kayan,dama akwaita da diri sosai,don dai bata cika sanya kayan da zasu bayyana surar jikinta bane,hannun rigar na net ne,dogo ne ya kawo har wrist ɗinta,kana hangen fatar hannunta ta ciki,
siririn mayafin ta ɗauko,ta sanyashi asaman kafaɗarta,wa'iyazubillah,ba ƙaramin wankuwa sehrish tayi ba,juyowa tayi tare da kallon Hosana wadda ta saki baki tana kallonta,tace"Nayi kyau,"
Yadda hosana ta saki baki,tana kallonta ko kyaftawa batayi ba ƙaramin dariya ya bata ba,har saida ta ambaci sunanta,sannan hosana ta iya buɗe baki tace"Wlh kinyi kyau Sehrish sosai,kamar ƴar matan aljanna,"
Dariya Sehrish tayi yayin da ta koma gaban mirror tana kallon kanta,hannu tasa tare da daukar kwalbar turarenta,tabi jikinta ta feshe,sannan ta fuce daga ɗakin,tun da tafito idon kowa ya dawo kanta,abokanan matasan gidan da suka hallara a babban falon,duk saita tsargu,kitchen ta wuce anan ta samu Azmee tana zuzzuba ma saude abinci acikin warmers tana fitarwa waje,wurin baƙi tana kai masu,
Ae tunda azmee tayi arba da ita tashiga zuzuta kyanta,
"Aunty Azmee ni nasan ban kai haka ba,kawai kina hura mun kaine,".
Azmee tace"ae kin zarce duk yadda nake faɗi maki,dama shi mai kyau bai gane yana da kyau,sai in ana faɗi,"
murmushi kawai ta saki tare da cewa"Aunty azmee ina kayan breakfast ɗin babban yaya inaso nakai mashi,"
"Oh kin manta cewa abusufyan ya hanaki"?
"Nasani Aunty azmee,bansan ya zanyi bane,babban yaya jiya yace,baison ki ƙara aiki part ɗinsa,ni kawai yakeso in dinga zuwa inayi mashi aiki,kuma har faɗa mashi nayi akan cewa daddy ya hanani amma yace shi babu ruwanshi,kawai nayi mashi aiki,
Jinjina Kai azmee tayi tare da cewa"Tabɗijancan,aikuwa akwai matsala!don wlh Abusufyan yaji wannan maganar bazai yadda ba,kuma ke in banda abunki kin manta wanene abusufyan a wurinki,mahaifinki fa ne,taya zaki tsallake umarninsa kibi na babban yayanku?hakan na nufin cewa yafi iko dake akan mahaifinki?kina ganin cewa abusufyan zaiji daɗi idan yaji cewa kin cigaba da yi mashi aiki"?
Jin wannan maganar ta azmee yasa jikinta yin sanyi,sunnar da kanta ƙasa tayi,tuni idonta sun ciko da kwalla,
Gyaɗa kai azmee tayi tare da cewa"Nasan don baki da yadda zakiyi ne sehrish,zan shirya maki breakfast ɗin ki kai mashi,amma karki kuskura ki bari Uncle abusufyan ya gani,kuma koda ya kamaki,kada ki sanya sunana aciki,"
Amsa mata tayi da toh,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta shirya mata warmers da sauran tarkacen abincin acikin kayataccen tray ta bata takai mashi,'
Tunda sehrish ta fito daga kitchen ɗin gabanta ke faduwa sai faman waige waige takeyi,tsoranta kar daddynsu ya ganta,cikin sa'a ta haye upstairs batare da taci karo dashi ba,
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin data ƙarasa cikin falonshi,babu kowa aciki,hakan yasa ta tunanin ko bai tashi daga bacci bane,tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinshi,taji muryar namiji a bayanta,
"Ji mana,"a firgice ta juyo don taga wanene,ɗan zaro ido tayi tana kallon matashin daya biyota,acan falo ta ganshi tare dasu kanal yousouf da alama abokinsu ne,
Murmushi ya sakar mata tare da cewa"Am sorry na biyo bayanki batare da saninki ba,nagaza jurewa ne shiyasa na yanke shawarar yin hakan,'
muryar sehrish na kerma tace"Am...um..dan Allah ka jira ni awaje,yanzu zan fito,
"Okey,zan tsaya awaje,but pls don't stay long,"
Ya faɗi hakan tare da juyawa zai fita,har ya sakai zai fita daga falon,ya kuma juyowa tare da kallonta har lokacin tana a tsaye yace"Kin tafi da imanina sosai,zan iyayin komai don na mallake ki,"ya ƙarasa maganar tare da fucewa,
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke aranta tace"Kowanene wannan jarababben,baisan nan part ɗin wanene ba,so yake yaja mun masifa,ya wani kwaso kafafunshi ya biyo ni,'
kamar ance ta juya,idanunta suka sauka kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,fuskar nan kwata kwata babu annuri,daga shi sai short fari ajikinsa,
Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,ƙiris ya rage ta saki tray ɗin hannunta,tuni jikinta ya soma rawa,
"Zoki wuce ciki,"yayi maganar babu alamun wasa a fuskarshi,jiki na rawa ta nufi bedroom ɗin nasa,matsa mata hanya yayi ta wuce,sannan ya kama hanya azafafe ya fito daga falonsa,anan waje ya samu saurayin nan,tsaye yana jiran fitowar sehrish bawan Allah,ya ɗauki wankan suits,sae faman zabga murmushi yake yi,
..jin an ta6a kafadarshi yasa shi juyowa don yaga wanene,gabansa ne ya faɗi Rasss lokacin da yayi arba da sgr tsaye agabanshi ya ruƙe qugu,tamkar zaki haka ya koma mashi,mugun tsoranshi suke ji,saboda ko magana bata ta6a haɗashi da abokanan ƙannenshi ba,labarinshi kawai suke ji a wurin su Irfan,babu wanda baisan Sgr ba,wato babban yaya,
Fuskarshi a tamke yace"Wani ganganci ne yasa ka biyota har cikin part ɗina!"?
Muryarshi na kerma yace"wlh ni ba ita na biyo ba,zuwa nayi kawai don in gaishe ka,dama Jabeer ne yace yakamata muzo mu miƙo gaisuwa wurin babban yayansu,kaji dalilin dayasa na kwaso ƙafata nazo,"
Wani irin kallo sgr ya wurga mashi,jin ya sharara mashi ƙarya bayan yaji duk abunda yake faɗa ma sehrish,
Sunnar dakai saurayin yayi yana faman mazurai,tsoranshi karya kai mashi naushi,
Hannu Sgr yasa tare da ruƙo neck tie ɗinsa yace"menene sunanka"
Cikin sauri yace"Jazz,"
Sgr yace"Jazz ko?let me warn u,ka tsaya a iya matsayinka,in ba so kake ka kwana a gadon asibiti ba,ka rufe idanunka daga kallon matan mutane,hakan zaisa ka zauna lafiya,'yana kai ƙarshen maganarshi yace"just u can leave....."ae tunkan sgr ya ƙarasa maganar,Sir Jazz ya watsa da gudu jiki na rawa ya sauka downstairs,
Ajiyar zuciya sgr ya sauke tare da juyawa ya koma ciki,
a ƙopar shiga bedroom ɗin ya tsaya,yana kallon sehrish dake ƙoƙarin gyara mashi gadonshi,har ta ajiye mashi kayan breakfast dinsa,yadda ta rankwafa shape ɗin hips ɗinta ya fito sosai,ba ƙaramin kyau tayi masa ba,sai yanzu ya gane dalilin dayasa wannan saurayin ya biyota,tunda yaga babban kaya dole ya zauce,baisan cewa babban goro sai magogin ƙarfe,
gyaran muryar da yayi ne yasata yin saurin ɗagowa,tana ganinshi tasha jinin jikinta,ƴan kame kame tashiga yi kamar wata mara gaskiya,ƙarasa shiga ciki yayi tare da samu wuri daga gefen gadon ya zauna,sannan anatse yace"Am hungry,"
cikin sauri ta dawo gaban table ɗin tashiga ƙoƙarin yin saving ɗinshi,coffee mai zafi ta fara miƙa mashi acikin cup,hannu yasa tare da kar6a,yana cikin kur6ar coffeen kamar ance mashi ya ɗago,idanunshi suka sauka akan Boobs ɗinta da suka fito sosai,tamkar zasu fasa gaban rigar,zukunnawar da tayi ne yasa suka yi hakan,
Nan take ya shaƙe,ba arziƙi ya ajiye cup ɗin dake hannunshi,gaba ɗaya duk yabi ya susuce ya shiga yin tari,tamkar maƙoshin shi zai 6allo,ganin haka yasa sehrish dakatawa daga yin saving ɗinshi da takeyi,tashiga yi mashi sannu,
daƙyar ya samu ya daidaita natsuwarshi,muryarshi ashake yace"Ke!ina scarf ɗinki yake"?
Muryarta na kerma tace"gashi nan agefenka,da zanyi gyara ne,na ajiye shi anan don karya takuramin,
Harara ya ɗan watsa mata tare da cewa"ɗaukarshi ki yafa,banason na ƙara ganinki haka kina yawo,"
"Toh,"ta amsa mashi,sannan ya kai hannunshi a gefenshi ya ɗauko mata mayafin ya miƙa mata,tana kokarin kar6a ta aza hannunta asaman nashi,ɗagowa yayi da idanunshi kai tsaye suka shiga cikin nata,agigice tayi saurin kawar da nata idanun,
Tunda yake arayuwarshi wata ƴa mace bata ta6a jan hankalinshi ba,da surar jikinta,harya shake irin haka ba,mata dayawa suna kawo mashi kansu,wasu har cire kayansu sukeyi don suja ra'ayinshi,amma basu ta6a cin nasara ba,donshi bashi da wannan Sha'awar ko kaɗan,akan sehrish ne kawai ya ta6a ganin wani sauyi,A ranar da suka faɗa saman gadon shi atare,har yau yana mamakin wannan abun,
*Aunty Babba*
Tuni sun kammala shirinsu na zuwa abuja,wankan shadda ta ɗauka,doguwar rigace ta kashe ɗaurin ɗan kwali abun sai wanda ya gani,Hafsat kuwa Code lace ta sanya ajikinta,riga da skirt milk colour,su aunty babba hada trolley na kayan sawa,ta sanya abayan boot ɗin motarsu,dama tace in taje sai tayi sati biyu,hafsat dae kallonta kawai takeyi,ita kadae tasan me zai biyo baya,hafsat ce take tuƙin motar yayin da aunty babba ke zaune agefenta,
kafin su fita daga garin Kaduna,Hafsat tace"Mommy,yakamata mu tsaya a kasuwa ki saya mana niqabi,"
aunty babba tace"Niqab kuma?daughter me zamuyi da niqabi sai kace wasu munafukai,"
murmushi hafsat ta saki tare da cewa"Mommy zaiyi mana amfani sosai,tunda nace maki mu sayi niqabi akwai dalilin dayasa nace maki haka,'
.....guntun tsoki aunty babba tasaki tana cewa"Ni ba wani niqabin da zan siya,kedai in kina buƙata ga hanya nan kije ki siya,"
Parking ɗin motar tayi,adai dai bakin wani shopping mall,
"Ni zanje in siya,kina bukatar wani abu"?
"A'a adawo lafiya,"
Fita hafsat tayi daga motar,kusan 15 mins sai gata tadawo hannunta ruƙe da sabon niqab,ta siyo,komawa tayi cikin motar,sannan ta tashi motar,suka miƙi hanya,
A 6angaren Amani kuwa tuni ta kammala shirinta,sun ɗau wankan lafaya itada Amal,Abbas da kanshi ya ɗaukosu acikin Motarshi,
Wuraren ƙarfe biyu da rabi na rana,wasu matsiyatan motoci haɗaɗɗun gaske,suka shigo cikin layin gidan,irin motocin nan na jigunan masu kuɗi,masu rai da numfashi,su huɗu ne motocin tare da security guards suke,kowace mota soja ne ke driving ɗinta,har suka ƙetara gate ɗin gidan,
A jere motocin suka tsaya,da gudu wani soja,jiki na rawa yazo ya buɗe mata ƙopa,
Tunkafin ta fito daga cikin motar,hayaƙin tabar da take sha ya fara fesowa waje,tashin hankali da ba'a sama shi date !Ko wacece Wannan
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Ƙarasa fitowa tayi daga cikin motar,jikinta na sanye da wani jigunannan lace,anyi mata riga da zani,rigar takai har guiwarta,ta coge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsiya,tun daga kan wuyanta zuwa hannayenta,duk zinari ne,tsohuwa mai ran ƙarfe,hajiya Ammi kenan Ummu Hossein,Ummu Azeema,Ummu Abusufyan,kaka ga su junaidu da kuma sehrish,fara ce tass bafullatanar asali doguwa kuma siririya,tsufanta bai hanata yin gayu ba,tsohuwar soja ce wadda tasha gwagwarmaya,kuma itace mace ta farko a lokacinsu data fara ruƙe muƙamin Major General,kaifi ɗaya ce ita,mace mai wuyar sha'ani,mutum mai tsananin haƙuri ne kawai zai iya jurar zama da ita,hannunta ɗaya na ruke da sandar karfe ta alfarma,yayin da ɗayan kuma yake ruƙe da sigari,tana tafiya tana busa ta,har ta hanci hayaƙin ke fitowa,
Babu wanda yayi tunanin cewar zatazo da wuri,bata sanarma kowa ƙarfe nawa zata zo ba,duk sunyi tunanin sae wuraren marece zata ƙaraso,Atare da MG Osman da Captain Adam suka zo,sae Hajiya Sarah ƴar wurin yayanta Modibbo,tare da ya'yanta mata su biyu Yasmeen da noor,dukkansu ba zasu wuce shekara ashirin da biyu ba,tunda matasan gidan sukaji zuwan ammi nan fa kowa yasha jinin jikinshi don sun san zuwanta bai cika zama alkhairi ba,duk in tazo sai wani abu ya faru,wannan karan basu san dame tazo ba,gaba ɗayansu sun hallara a main palour ɗin suna jiran ƙarasowarta ciki,mutun ɗaya ne bai fito wurin tarbarta ba,bakowa bane face Abusufyan,tun da yaji zuwanta ya kasa samun sukuni,sae faman safa da marwa yakeyi acikin bedroom ɗinshi,jikinshi nata kerma ba don komai ba sai don zullumin abunda zai biyo baya,idan tayi arba da triplet ɗinshi,duk da yayi ma kanshi alƙawarin cewar,koda ace ta koresu to tabbas ƙafarsu ƙafarshi,bazai ƙara barin rayuwarsu ta wulaƙanta ba,duk inda zasu je zai kasance atare dasu,
hayamm kuwa tana la6e jikin window tana leƙen Ammi,tun fitowarta daga mota,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta saboda tana sa ran cewar tuggun da suka shirya,zaiyi aiki,
Lokacin da suka shiga falon,nan fa kowa ya shiga miƙa gaisuwa,abun da zai baka mamaki,ko amsawa wannan batayi kamar mai fama da ciwon baki,sai dae ta ɗaga masu hannu,Azmee ce ta kaisu ɗakunan da aka gyara masu,domin su sauke gajiyar da suka kwaso,kafin zuwa anjima,kowa sai da ya kara zuwa gaishe ta ɗaya bayan ɗaya har ɗakin data sauka,mutun uku ne kawai basuje gaishe ta ba,Sgr,Abusufyan sae junaid wanda bai kaiga fitowa ba daga bedroom ɗinshi,
Mg Osman kuwa a nan falon suka zauna tare da Marshal Omar,suna gaggaisawa,saboda anjima ba'a haɗu ba sunyi kewar junansu sosai,
Hayaam tana ƙoƙarin zuge glass ɗin windon da take leƙe sai ga Motar Abbas tayi parking cikin gidan,tsayawa tayi tana jiran ganin su wanene kuma suka ƙara zuwa,kodai Aunty laila ce ta ƙaraso ne,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,Abbas ya fito daga cikin motar,daga bisani kuma Amani da Amal suka fito atare daga cikin motar,
Ƙura ido Hayaam tayi tana ƙare ma Amal kallo,cike da mamakin wacece wannan Kyakkyawar yarinyar da Amani tazo da ita,A iya saninta dae Amani bata ta6a haihuwa ba,balle harta haifi ƴa kamar wannan,duk yadda taso ta gane wacece yarinyar nan amma hakan ya gagara,kwakwalwarta a toshe take,saboda tsabar mugunta irin tasu tun Amal na ƙarama suka canza mata kamanni saboda uƙubar da take sha a hannunsa,dole hayamm ta kasa gane wacece ita,
"Hayam!"muryar Azmee ce ta karaɗe kunnanta,da sauri ta rufe glass ɗin windown tare da juyowa tana kallon Azmee,shigowarta kenan ɗakin jikinta na Sanye da jallabiya baƙa,anyi mata kwalliyar zanen flower blue,veil ɗin data yafa ma blue ne,ba ƙaramin kyau azmee tayi ba,ta wanku sosai,
Ƙarasawa hayaam tayi wurinta tana faɗin"Aunty Azmee sae yanzu za'a tuna dani?yunwa kamar zata kashe ni,kowa yana rayuwarshi acikin gidan nan sai ni duk a ƙuntace,"
"Ke kika so ki ƙuntata kanki hayam,Sgr yanzu haka ya manta da cewar ya koreki daga gidan nan,zai iya yiwuwa ma ya manta dake gaba ɗaya,kuma kinga yau ranar Walima ne mutane duk sunzo,ba dole bane ya ankara dake ba,bama haka ba mutumin da kafin ya ɗaga ido ya kalli wani aiki ne a wurinsa,don haka ina baki shawarar ki daina kullan kanki,"
Tun kan azmee ta ƙarasa maganar hayaam ta soma washe baki,la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"An..aunty Azmee kina nufin sgr ya manta da laifin da nayi mashi kuma zan iya fita inyi yawo na acikin gidan nan kamar kowa,'
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"Of course,amma fa hayaam koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara yunƙurin zuwa sashen shi!duk yawon da zakiyi ki tsaya a downstairs babu ruwanki da abunda ya shafi upstairs ina fata kin gane"?
yatsina fuska tayi tana fadin"dama ni Aunty azmee me zai kai ni,waccen karan ma tsautsayi ne da ƙaddara,"
"Sannan kuma,kada ki kuskura ki ƙara shiga shirgin Sehrish!kinsan dai yanzu tafi ƙarfinki nesa ba kusa ba,ƴar masu gida ce ita,kuma shalelen daddynsu,ga kuma yayyanta maza muddin kikace zaki ta6ata wlh zaki ta6o ma kanki ne,akanta sae abaki Red card na barin gidan nan,"
ta6e baki hayaam tayi,tana faman hura hanci,maganar ba ƙaramin ƙona mata rai tayi ba,don bata da yadda zatayi ne,
Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta kama hanyar fita tana faɗin"Yakamata kiyi wanka,ki shirya saiki fito ayi shagalin dake,"
Cikin sauri ta ruƙo rigar Azmee tace"Aunty Azmee don Allah ki taimakamun wlh yunwa nake ji,tun jiya da daddare rabona da Abinci,"
"Its Okey,zan kawo maki yanzu,"
Komawa ciki hayaam tayi tana jiran azmee ta kawo mata abinci taci,kafin tayi wanka ta kimtsa,
bayan su Amani sun shigo cikin main palour ɗin,anan suka zauna suna gaisawa dasu kanal yousouf,kafin tabar wurin tare da Amal,wurin Azmee taje suka gaisa tayi masu kwatancen ɗakin Hajiya Azeema da kuma na gwaggo,duk saida tabisu ta gaishe su,hatta ɗakin Abusufyan saida suka je,sukayi mashi Allah sanya Alkhairi,daga nan suka dawo kitchen,lokacin Azmee tana haɗa ma Hayaam lunch ɗin da zata kai mata,
Juyowa tayi jin sallamarsu tace"har kun dawo"?
Amani tace"Eh,duk naje nayi masu Allah sanya alkhairi,yanzu abunda ya rage mun inason zuwa wurin dasu yaran suke,bansan a wani ɗaki suke ba,'
Azmee tace"Ae suna nan ɗakin da Sehrish take,ae kinsan ɗakinta wanda ke a kusa da namu,yakamata kuje wurinsu,'
Murmushi Amani ta saki aranta tace"ba dole inje ba,ni da nakeson na gyara tsakanina da Sehrish,"
A fili kuma tace"okey,nagane ɗakin bari muje wurinsu,"
Juyawa sukayi atare da Amal suka nufi ɗakinsu sehrish,abakin ƙopar ɗakin suka tsaya,Amani ta kwankwasa ƙopar,jahad ce ta buɗe kopar,ba ƙaramin kyau tayi ba,wankan swiss lace ne ajikinta wanda aka haɗa da bazin shadda,stones work ne ajikin kayan wanda ya ƙara fito da ɗinkin sosai,
Murmushi Amani ta sakar mata tare da cewa"Sehrish ce ko"?ta tambaya ne saboda Abbas ya sanar da ita cewar kamanninsu ɗaya sak,
Martanin murmushin jahad ta mayar mata kafin tace"A'a,ba ita bace,tana ciki in kira maki ita ne,"ta ƙarasa maganar tana kallon Amal wadda itama jahad ɗin take ta kallo,
Amani tace"bari mu shiga daga ciki,sai mu gaisa,"
Matsa mata hanya jahad tayi suka shiga cikin ɗakin,
A lokacin Sehrish na kwance saman gadon ta ɗan kishingiɗa,tana hutawa,saboda ba ƙaramin gajiya tayi ba,sun sha zurga zurga,gashi Anjima za'a fara walimar bayan Sallar la'asar,shiyasa ta dawo ɗaki don ta huta,kafin lokaci yayi,ganin Amani yasa ta miƙewa daga zaune tana kallonsu,
Wuri Amani ta samu daga gefen gadon ta zauna,Amal ma ta zauna,tun kafin ma Amanin tace wani abu sehrish tace"Sannunku da zuwa,"hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Amani ba,tayi tunanin zata ga akasin haka ne,
"Yawwa,fatan mun same ku cikin koshin lafiya"?
Sehrish tace"Lafiya lou Alhmdllh,"
Amani tace"kin gane ni ko"?murmushi kawai sehrish ta saki,taya za'ae ta manta da matar da tace zata iya rasa ranta idan ta cigaba da shisshige ma matasan gidan,
"Ina fata dai baki ruƙe ni aranki ba?dan Allah ki manta da komai dana ta6a faɗa maki,komai ya wuce,yanzu zumunci ya ƙullu atsakaninmu,ko wancen karon ma da nayi maki wannan maganar,wlh bada wata manufa na faɗa maki hakan ba,"
Jinjina kai Sehrish tayi tare da cewa"babu komai,ae ya riga ya wuce,"
Ba ƙaramin daɗi Amani taji ba,juyawa tayi tare da kallon jahad dake tsaye tace"zo ki zauna mana,inaso muyi fira tare daku,"zagayawa jahad tayi ta 6angaren hannun hagu ta zauna daga gefen gadon,
Amani tace"ina cikon ta ukun take ne?Abbas ya faɗamun cewa ku ƴan uku ne,"
Jahad tace"hakane,hosana ce babu,taje wurin yaya Omar ne" shiru Amani ta ɗan yi tana maimaita sunan hosana a cikin zuciyarta,kamar ta ta6a jin sunan abakin wani,"ke ya sunanki"?
"Ni sunana jahad," jinjina kai amani tayi tare da cewa"Suna mai daɗi,amma nifa bansan komai ba,agame daku,sehrish kawai nasani tana aiki a gidan nan,"
Jahad tace"ae mu muna a wurin ya Omar ne,shi ya taimake mu a lokacin da muke cikin mawuyacin hali,bayan ƙaddara ta rabamu da ƴar uwarmu,"
..A ruɗe Amani tace"Hannun Ya Omar"
Jahad tace"eh,"
Cike da son jin ƙarin bayani Amani ta kuma cewa"Kun zauna a kaduna ne"?
Ita kanta jahad sai da gabanta ya faɗi jin Amani ta ambaci kaduna kai tsaye,taya akai tasan cewa sun zauna a kaduna,
Daƙyar ta iya bata amsa da cewa"Eh,mun zauna acan,daga baya ne Ya Omar ya dawo damu Abuja,gidan daddynmu,"
Tashin hankali,miƙewa amani tayi da sauri jikinta na rawa tace"Ga Amal nan ƙanwata ce,in ba damuwa ta zauna a wurinku,"
Amsa mata sukayi da toh,cikin sauri ta fuce daga ɗakin,kallon juna jahad da Sehrish suka yi atare,duk sun lura da yadda Amani ta ruɗe,
"Wacece wannan Sehrish"?jahad ce tayi mata tambayar,sehrish tace"matar yaya Abbas ce,Aunty Amani,"
Taso ta ƙara tambayarta,amma saboda Amal dake zaune a wurin yasa tayi shiru,tabbas ta so taga kamannin Aunty babba kaɗan a fuskar Amani,duk da Amani tafi kyau sosai,kuma ita bata da jiki irin na Aunty Babba,miƙewa jahad tayi tare da cewa"Zan fita yanzu zan dawo,"
Sehrish tace"adawo lafiya,"
Bayan jahad ta fita,Sehrish ta kalli Amal dake zaune,rashin sabo yasa ta kame kanta wuri guda,
Murmushi tasakar mata tare da cewa"ki saki jikinki mana,naga duk kin gaza samun natsuwa,ko dan bamu ta6a haɗuwa bane?"
Sunnar da kai Amal tayi tana murmushi,wata irin kunyace da ita,daƙyar ta iya cewa"banta6a zuwa nan ba,yau nafara zuwa,bazan iya sakin jikina ba,tunda bansan kowa anan ba,"
Sehrish tace"Ae kuwa yanzun nan zansa ki saba dani,da farko dai ki dinga kirana da Aunty Sehrish,saboda ina kallon ƙaramar fuskar nan taki nasan cewa na girme ki,tsawo ne kawai gare ki,amma a shekaru ba zaki wuce sha huɗu ba,ko nayi ƙarya"?
dariya Amal tayi tana girgixa kai tace"A'a bakiyi ƙarya ba,shekarata sha huɗu amma na kusa kai shekara goma sha biyar,nan bada jimawa ba,"
"Kice zamu zo yanka cake ko"?acewar sehrish,
Amal tace"Eh,zan gayyace ku idan lokacin yayi,"
Sehrish tace"Nima na kusa cika shekara sha takwas,banma sani ba ko na kai shekara sha takwas ko ban kai ba,nifa banma son ranar da aka jefo ni duniya ba,ni dai kawai na ganni ina yawo na ne....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda dariyar da Amal ta kwashe da ita,abu kamar wasa sai gashi cikin lokaci ƙankani sun saba da juna,nan suka zauna suna ta fira atsakaninsu,
Amani kuwa tun bayan da ta fita daga ɗakinsu sehrish,tarasa inda zata tsoma kanta,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,Aunty babba ta sanar da ita cewar tasa an zubar da yaran da Omar ya kawo mata,kuma tace mata ƴan biyu ne yaran,hakan na nufin cewar jahad ne da hosana a wurinshi?kamar yadda jahad ta sanar da ita cewa su A wurin yaya Omar suke,indae dagaske hakane to taya akai Yaran suka dawo wajen Marshal Omar bayan tasa an zubar dasu!?kodai Omar ya sanya ɗan leƙen asiri ne acikin gidan?tabbas hakan zai iya faruwa,indai kuwa hakane Watan cin uban Aunty laila ya tsaya,Zuwa maiduguri ba fashi,
Acewar Amani wadda ke ta faman yin safa da Marwa a tsakanin corridor ɗin ɗakunansu sehrish,daga bisani tace"Allah yaso ni ban tsoma hannu na ba,a wurin cutar dasu ba,ashe da rabon aure na yayi lasting,Aunty babba kam ta shiga uku,taja ma kanta bala'e,kwara ma da hakan ya faru,da nayi niyyar ɗaukar ma Amal fansa,amma yanzu na fasa,zan zuba idone kawai inga yadda dramar nan zata kaya,"ta ƙarasa zancen zucin nata,fuskarta ɗauke da murmushi,ba komai take hangowa ba face yadda rayuwar Aunty babba zata ƙare,........'
Bayan fitar jahad,kitchen ta wuce ta shirya lunch acikin tray,kamar ita zata ci,upstairs ta wuce dashi,adai dai ƙopar ɗakin junaid ta tsaya tare da sanya hannunta ɗaya,ta ɗan bubbuga ƙopar ɗakin,wata murya taji daga cikin ɗakin ta amsa mata da cewa"Wanene"?muryar kuma bata junaid bace,
"Ni ce," ta bashi amsa ataikace
"Kece wa"?
"Jahad,"shiru taji anyi mata kafin,harta fidda rai da za'a buɗe mata,tana ƙoƙarin barin wurin taji alamun ana buɗe ƙopar,tsayawa tayi har ya kammala bude kopar,ganin fuskar wani daban bata junaid ba yasa tasha jinin jikinta,musamman yadda taga fuskar mutumin a murtuke babu fara'a ko misƙala zarratin,
"Wa kike nema"?
Muryarta na rawa tace"Wurin junaid nazo,naga ban ganshi ba duk yau,"
"Shine kika zo kawo mashi abinci?yace maki yana jin yunwa ne"?shiru jahad tayi masa batace komai ba,da alama dae wannan ba ƙaramin masifaffe bane,
"Wuce ki shiga,"ya faɗi hakan tare da matsa mata hanya ta wuce ciki,shi kuma ya fuce daga ɗakin,
jikinta sai kerma yakeyi saboda tsoran mutumin da tayi arba dashi,hakanan taji tsanarshi aranta,kuma sam baiyi mata kama da mutanen kirki ba,
Lokacin da ta ƙarasa shiga ɗakin a kwance ta samu junaid,daga shi sai farar shirt da short fari a jikinshi,ya kwantar da kanshi asaman pillow,idanunshi na arufe,ajiye mashi tray ɗin tayi asaman front table ɗin gadon nasa,sannan ta samu wuri daga gefen gadon ta zauna tare da ambaton sunanshi"junaid,"
A hankali ya buɗe idanunshi tare da azasu akan fuskar jahad,yanayin shi ya nuna tamkar baijin daɗin jikinshi,idanunshi kansu sun marairaice,
Bai tanka mata ba sae da ya gama ƙare mata kallo sosai,saboda ya tantance wacece acikinsu,tashi yayi daga zaune sannan yace"Jahad ko"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan ta ƙara da cewa"duk yau ban ganka ba,shiyasa nace bari nazo na duba ka,hada abinci ma nazo maka dashi,duk da bansan ko kana jin yunwa ba,"
"Thanks for your caring,duk yau babu wanda ya damu dani,sai ke kawai,naji daɗi sosai,"yayi maganar tare da sauko da ƙafafunshi ƙasa,hannu yakai zai ɗauki jug,ta riga shi ɗaukar jug ɗin tare da cewa"bari na zuba maka,"dakatawa yayi ta tsiyaya mashi lemu mai sanyi acikin cup,sannan ta miƙa mashi,yasa hannu ya kar6a,tare da kai cup ɗin saitin bakinshi yana kur6a,
binshi tayi da kallo,yayi wani irin haske fari fat,kamar mara jini a jiki,hakanan ta dinga jin wani irin tausayinshi na shigarta,ga tsananin ƙaunarshi da takeyi kamar kamar me,
Har ya kammala shan lemun bata sani ba,juyawar da zaiyi suka haɗa ido dashi,kawar da idonta tayi gefe guda tare da yin saurin cewa"Kamar baka lafiya ko"?
"Me kika gani"?
"Kawai yanayinka na gani,kamar na wanda bashi da ƙoshin lafiya,"
"Lafiyata ƙalou,don inajin yunwa ne shiyasa kika ganni haka,amma da zarar naci na ƙoshi,zan dawo dai dai,"
"Kasan kana jin yunwa amma meyasa baka tashi ka nemi abinci ba"?tayi maganar a yayin da take janyo plate ta shiga zuba mashi fried rice aciki,
"Tun safe fa naketa yin bacci,ni kaina bansan ya akai nayi bacci mai tsayi ba,kuma dana tashi jikina duk ba ƙwari,shiyasa bansamu na sauko downstairs ba,saboda kasalar data baibaye ni,
"Kuma baka sha wani abu ba?kamar maganin bacci"?
Shiru junaid ya ɗanyi yana tunani kafin yace"a'a bansha komai ba,amma ya haroon ya kawo mun wani tea a cup wuraren ƙarfe takwas yace mun insha,kuma saida na tambayeshi maganin menene yace mun maganin ƙara kuzari ne,shine nasha,tun daga lokacin nidai ban ƙara sanin meke wakana ba,yanzu ma da kika ganni a kwance tashi na kenan,kuma shi ya tashe ni,yace mun in tashi inyi wanka in shirya,lokacin walima ya kusa,"
ɗagowa jahad tayi tare da kallon fuskarshi tace"Wannan mutumin daya fita yanzu shine Ya haroon"!?
ɗaga mata kai yayi alamar eh,
ta kuma cewa"Wanene shi?don ban ta6a ganinshi ba a gidan,"
Junaid yace"Shima yayan mu ne,bai cika zama gida bane shiyasa baki ta6a ganinshi ba,"
"Kada na cika ka da surutu,ka fara cin abincin,"
Maƙe hannayensa yayi tare da cewa"Hannu na ciwo yakeyi mun,"murmushi ta saki tare da kai hannu ta ɗauki cokali tana faɗin"bari na baka abaki to,"
ɗebowa ta dinga yi tana tura mashi abakinshi yana Ci suna fira,gwanin ban sha'awa,a haka harta samu yaci abincin sosai,sannan ya tashi ya shiga toilet wanka,zama tayi tana jiran fitowarshi saboda yace ta jira shi,su fita atare,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,a sannu a sannu dai junaid ya fara sakewa da ita,Allah sarki
*Boss Bature*
Bayan Sallar la'asar,kowa ya ɗauki wani sabon wankan,Amani da kanta tayi masu Jahad makeup ita da Hosana da Sehrish,gaba ɗayansu suka sanya Swiss lace ajikinsu,wanda aka ɗinka masu shi domin su sanya a aranar walimar,riga da skirt ne ba ƙaramin kyau kayan sukayi masu ba,sun wanku iya wankuwa,yadda kasan dollar wurin kyau haka suka koma,Suna acikin ɗakin nasu Su huɗu hada Amal,in aka haɗa da Amani sun zama su biyar kenan,zama tayi tana ƙarasa gyara masu ɗaurin ɗan kwalin da tayi masu,
A Can ciki kuwa Matasan gidan duk sun hallara,Azmee da Saude ne suke ta ɗawainiyar bin kowani table dake a wurin suna Jejjera abinci kala kala,daga bayane hayaam ta samu damar fitowa daƙyar,tun tana ƴan kame kame kamar mara gaskiya har dae ta fara sakewa,tashiga tayasu Azmee kai ma baƙi lemu,
A hankali Motarsu Aunty Babba,ta shararo izuwa cikin gidan,a dai dai parking space,hafsat ta tsayar da motar,tare da juyawa ta kalli fuskar Mommyn nata dake ta faman jan minshari,tunda suka taho ta kama bacci acikin motar,hannu hafsat tasa tare da bubbuga kafadarta,a firgice Aunty babba ta farka tana fadin"Har mun ƙaraso ne,"
Hafsat tace"eh mana,gamu acikin gidan ma,kin barni da driving kina ta sharar bacci,'
Yamutsa fuska Aunty babba tayi tare da buɗe motar tana faɗin,wlh agajiye nake,ga baccin ma bai isheni ba,kuma yunwa ma nake ji,'
Bayan motar ta tsaya tare da buɗe Boot ɗin motar,ta curo trolley ɗin kayansu,tare da saukko dashi ƙasa,
Sai da hafsat ta sanya niqabin da ta siya a hanya sannan ta buɗe motar ta fito,hannunta ruƙe da ƴar purse ɗinta,ganinta da niqabi yasa Aunty babba jan guntun tsoki tare da fadin"Yau naga ikon Allah,kamar wata Munafuka,kin nace dae yau sai kin sanya wannan baƙin abun a fuskarki,kamar wata ƴar shi'a"
"Mommy ba zaki gane bane,"
Tayi maganar tare da kama hanyar shiga cikin gidan,bin bayanta aunty baba tayi tana fadin"ba zaki zo ki kar6i trolley ɗin ba"
"Haba Mommy,Duk aikin driving ɗin da nayi,kuma sai na wani ɗauki trolley,ae ke yakamata ki janyoshi,tun fa da muka kamo hanya kike ta bacci,kika barni da aiki,nima agajiye nake bazan iya ɗaukar shi ba,"
"Kar Allah yasa ki ɗauka toh,"suna tafe suna magana har suka shiga cikin Main palour ɗin,Hayaam najin sallamar Aunty babba,ta wani saki ihu har saida hankalin kowa ya dawo kanta,da gudu taje ta rungumota tana faɗin"Wayyo Allah aunty laila,tun dazu nake ta baza ido inga zuwanku amma shiru,har na fara fidda rai da zuwanku ashe kuna hanya,"tayi maganar tare da raba jikinta daga na aunty babba,fuskar nan awashe Aunty babba tace"Mezai hana mu zuwa,naso na sanar maki wlh mantawa nayi,koda yake bacci fa nayi a mota,hada ƙarin haka yasa ban samu na kira ki awaya ba,'
"Gaskiya nayi kewar ku sosai,"acewar hayaam tayi maganar a yayin da take mayar da idanunta akan Hafsat dake sanye da niqabi,a ruɗe tace"Kai!wai hafsat ce sanye da niqabi,"
Hannu hafsat ta sanya tare da ɗan ɗage niqabin tace"Nice mana,gaba ɗaya hankalinki na akan mommy dayake kinfi damuwa da ita,"
Washe baki hayaam ta kuma yi tare da rungumo hafsat ajikinta tana faɗin"Sorry bangane ki bane wlh,kema ce kin sanya niqabi kamar wata mara gaskiya,"
Suna cikin magana muryar Azmee ta katse su da cewa"maraba da manyan baƙi,Yau su hajiya laila ne a gidan namu,wata sabon gani,yau za'ayi ruwa da ƙanƙara,"
Dariya sukayi gaba ɗayansu,kafin daga bisani Aunty babba tace"Ae wannan zuwan na musamman ne,Har sai kun gaji damu Allah,"tana magana hafsat na zungurinta alamar ta daina faɗin zasu jima,amma zafin ɗumi yasa ko lura batayi ba balle ta ankare,
"Ae tunda na ganku da trolley ɗin kayan nan nasan cewa zaku jima mana anan,wataƙil ma har sai an aurar da ƴa'ƴan namu tukunna,kunga sai ayi agabanku,'
Gaban aunty babba ne ya faɗi rass,a razane tace"Auren wasu ƴa'ƴa kenan"?
dariya azmee tayi tare da cewa"Ƴa'ƴanku mana na wurin Abusufyan,"
ɗaure fuska Aunty babba tayi tana fadin"haba dae,wani aure kuma ana zaman lafiya,daga ganin yaran kuma sai ki fara yi masu fatan yin aure,duka nawa suke,bana ji ance ƴan shekara sha bane,'
kafin azmee ta kuma cewa wani abu hafsat tace"Dan Allah mu shiga ciki mu zauna,wlh agajiye nake,gashi ko salla ma ba muyi ba,"
Atare suka ƙarasa shiga ciki,bayan sun kammala gaisawa da mutanen dake zaune a babban falon,daga bisani hayaam takaisu bedroom ɗinta,suna shiga ciki hafsat ta cire niqabin data sanya,tai wurgi dashi saman gadon,tashige toilet don ta ɗauro alwala,a ƙagare take da tayi arba dasu jahad,duk da tsoran karsu canza mata,musamman in suka tuna abubuwan da sukayi masu a gidansu,tana cikin toilet tajiyo muryar hayaam tana fadin"Tun jiya fa na tura maki hotunan nasu,baki gani bane,kuma har hafsat saida na kira a waya na sanar da ita don ta tunasar dake,'
Aunty babba tace"Gaskiya ni banga wani hoto ba da kika turamun a whatsapp ɗina,mu barma zancen tunda dae gani acikin gidan zan gansu da ido,batare da nasha wata wahala ba,'
Hayaam tace"Ae yanzu haka suna can cikin ɗakinsu tare da Amani...'
Cike da mamaki Aunty babba tace"Amani kuma?Ubanme ya haɗata dasu da har take shiga ɗakinsu?Oh ni yau naji ikon Allah,wannan shisshigi da kutsu irin na Amani,"
"Nima azmee ce ke sanar dani cewa tana a ɗakinsu wai tanayi masu kwalliya,ni duk bama wannan bane damuwata ba,Akwai wata kyakkyawar yarinya fara da Amani tazo da ita,na rasa gane wacece yarinyar nan,kuma fuskar yarinyar sak irinta amanin ce,"
Aunty babba tace"To fa,ko ina tasamu yarinya,zai iya yuwuwa fa daga gidan marayu Abbas ya ɗaukko masu ita don su raina,kinfa son cewa basu ta6a haihuwa ba,'
"Bari naje ciki,kada azmee taji ni shiru,ina ɗan tayata aiki ne,'acewar hayaam
Harara Aunty babba ta watsa mata tare da cewa"dama aiki na turoki kiyi acikin gidan?shiyasa naga duk kin zabge,nida zanzo inga ko'ina na jikinki ya cicciko,amma sai uban ƙasusuwan wuya,kamar wadda tayi jinya,'
Tsuke fuska hayaam tayi tana faɗin"Bakisan halin dana shiga bane,shiyasa zaki ce haka,tunfa da Sgr ya kore ni daga gidan nan,ban ƙara samun kwanciyar hankali ba,kullum ina ƙumshe acikin ɗaki saboda tsoran kar muyi arba dashi,ga ciwon yunwa dake damuna,ba don azmee ba ae da tuni na jima da sheƙawa,itafa ce take kawomun abinci har ɗakina,wani lokacin in ta manta bata kawo mun ba,sae dai fa in dare yayi kowa yayi bacci in saci hanya inje kitchen in ɗebo abinci,gaskiya nasha wahala sosai,
"Laifinki ne hayaam,kina zaman zaman lafiyarki acikin gidan nan,Amma kika toƙano masifa,kirasa wa zaki kaima hari sai Sgr,ae wlh ki godema Allah dabai kakkaryaki ba,nikaina nayi mamaki da kikace iya korarki yayi kawai,'
Tur6une fuska hayaam tayi tare da juyawa tana fadin"Ni dae mu bar maganar ae yariga da ya wuce,kuma ma ae ya yafe mun,bakiga yanzu ina yawo na hankali kwance acikin gidan ba,"
Aunty babba tace"Allah yasa dagaske ne cewar ya yafe maki ɗin,sai kiyi taka tsantsan kafin mu samu Allah ya cika mana burin mu,don wannan karon da shirina nazo,Bazan bar gidan nan ba,har sai naga an shafa fatihar aurenki,keda Sgr,"
Cike da farin ciki hayaam ta sanya tafin hannunta tare da rufe fuskarta tana sakin dariyar farin ciki,
"Aunty laila kina ganin hakan zai yiwu kuwa?ga Yaran nan ƴa'ƴan abusufyan,wlh ba ƙananu bane balle ace basu isa aure ba,Sun kaifa sha Takwas inaji,kuma wlh bakiga surar jikinsu ba,matane sosai,ni tunda nagansu ma duk sai naji na tsani kaina,kuma kinga su ƴan gidane za'a iya tunanin haɗasu auren Zumunci...'
Tunkan ta ƙarasa maganar aunty babba tace"Impossible!wlh bazai ta6a yiwuwa ba!Muddin ina numfashi ɗaya daga cikinsu bazata ta6a auren Sgr ba,kwara ma Omar abra saita haƙura amma Allah sgr ya Haramta agaresu na haramta masu shi,da bala'e sai ya aureki,ko anaso ko ba'aso,babu wani shege daya isa ya hana wlh,babu shi,"yadda Aunty babba ke cika baki tana magana ba ƙaramin dariya ya so yaba hafsat ba dake acikin toilet tana sauraronsu,ita batasan halin da suke ciki ba,sae faman kuri take tana cika baki,
Ita kuwa hayaam sae faman washe baki takeyi,gaba daya ta miƙa yardar ta ga Aunty babba,ae gani takeyi zata iya aikata komai don ta mallaka mata Sgr,
Bayan fitar hayaam daga ɗakin Hafsat ta fito daga cikin toilet din,idonta na akan Aunty babba data ɗan kishingiɗa asaman gadon,
"Mommy yakamata kije kiyi sallah,kinsan fa yanzu za'a hallara gaba ɗaya wurin waleemar yakamata ki hanzarta yin sallar,"
yatsina fuska tayi tare da cewa"Anya zan iya yin sallar nan kuwa,nagaji sosai,zuwa anjima dai nayi sai in haɗa da magriba duka inyi,"
girgiza kai kawai hafsat tayi batare da ta ƙara cewa komai ba,don ba yau ta saba yin haka ba,ita kanta hafsat ɗin zamanta dasu jahad ne ta fara yin sallah cikin lokacinta,
Zaune yake agefen gadonshi ya zabga uban tagumi,tun bayan da suka dawo daga sallar la'asar,yadawo ɗakinshi atakure,turo kopar ɗakin nashi Abba yayi tare da shigowa ciki,ba ƙaramin tausayi abusufyan ya bashi ba,wuri ya samu tare da zama daga gefenshi sannan yace"Bana faɗa maka cewa ka kwantar da hankalinka ba?jibi yadda duk kabi ka tukura kanka,"
ɗagowa yayi tare da kai idanunshi kan abba,muryarshi asanyaye yace"bansan ya zanyi bane,hankalina yaƙi kwanciya wlh,bansan wane hukunci Ammi zata yanke mun ba,ni tsorona kada tace bata yarda cewar da aure na samu su jahad ba,kasan halinta yaya hossein,tana da wuyar sha'ani,"
Abba yace"hakane,amma insha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na fahimtar da ita,kaima kasan cewa bazan ta6a bari yaran nan su tozarta ba akan idon kowa,Ammi tana buƙatar hujjoji masu ƙarfi kafin ta gasgata abu,zamuyi kokari wurin ganin cewa munyi amfani da hujjojin da muke dasu a hannu wurin fahimtar da ita,abunda nakeso dakai yanzu ka saki jikinka,nasan cewa da anjima kaɗan idan ta farka daga bacci zata fito nan babban falon,so nake kazo da ƙwarin guiwarka ka gaishe da ita,kasan kun jima baku haɗu ba,kuma dama can kai mai laifi ne a wurinta,'
fuskar Abusufyan cike da damuwa yace"Hada ƙarin hakan yasa nake fargabar haɗuwa da ita,Ni kullum mai laifi ne a wurinta,ko kirana ma bata ɗagawa,tunda nabar nigeria shekara goma sha,amma mommy bata ta6a ɗaukar waya da sunan zata kira ni ba,kuma ko na kirata bata ɗagawa,ni ina ganin kamar bata so na ne,shiyasa takeyi mun haka,'
ruƙe hannunshi abba yayi acikin nashi"abunda kake tunani ba haka bane,zanma iya cewa tafi sonka fiye da kowa,kuma ta damu da kai sosai,babban laifin da kayi mata shine naƙin sanar da ita dalilin da yasa kabar Nigeria,ammi batasan komai game da tafiyarka ba,tayi kewarka sosai,don akwai lokacin da ta kirani a waya,kuka ne kawai batayi ba a lokacin,saboda ka tafi batare da saninta ba,wannan dalilin ne yasa take fushi dakai,amma yanzu ina da tabbacin cewar in har muka sanar da ita dalilin tafiyarka,zata fahimce mu,kuma zata kar6i yaran nan hannu bibbiyu,kuma zata yafe maka"
Jiki asanyaye abusufyan yace"Allah yasa,dana fi kowa farin ciki,"
Murmushi abba yayi tare da miƙewa tsaye ruke da hannun abusufyan yana cewa"Tashi muje ciki,nasan yanzu haka triplet ɗinka suna nan,sun ɗau wanka suna jiran daddynsu don suyi hoto tare dashi,"
Jin haka yasa Abusufyan sakin fara'a a fuskarshi nan take yaji damuwarshi ta ragu saboda an ambaci ƴan ukunshi,
atare da abba suka fito daga cikin ɗakin,adai dai lokacin Hajiya Azeema da gwaggon katsina da saude suma duk sun fito,kowa yasha kwalliya a fuskarshi,ga harris shima tare da Marshal Omar duk sun hallara anan falon,A jere su Sehrish suka fito su uku Ita dasu jahad hosana,sae Amal dake abayansu tare da Amani,
Ae tunda suka shigo cikin falon hankalin kowa ya dawo kansu,yadda kasan wasu taurari haka suka bayyana,kai tsaye wurin abusufyan suka nufa,haɗasu yayi su duka ya rungumesu sosai,bayan ya sakesu,suka gaishe da Abba tare dasu Marshal Omar dake tsaitsaye a wurin,Hannu abba yasa tare da jan kumatun hosana yace"Amaryar Omar,irin wannan kyau haka,"da sauri tasa hannu tare da rufe fuskarta,tana dariya,kawar da kai gefe Omar yayi yana ɗan sakin Murmushi,da zasu bashi dama da ba abunda zai hana ya rungumota don ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,matsowa kanal yousouf yayi kusa dasu yana fadin"Uncle ni wacce za'a bani acikinsu tunda ya Omar yayi kamun tashi,kada su ƙare ni in rasa,"dariya sukayi gaba dayan su,Uncle abusufyan yace"Layi zaka bi,don mutun ko da kuɗinshi saida rabonshi," Abba ya kar6e da cewa"kwarai kuwa,sae wanda ya dage da sallar dare zamu bamawa,"
daga bayansu suka jiyo muryar junaid yana cewa"Kamar ni kenan,duk gidan nan babu wanda yakai ni tashi yin sallar dare,"ya ƙarasa maganar tare da ruƙe qugunshi,fuskar nan ɗauke da wannan kyakkyawan murmushin nashi,yayin da idanunshi ke akan jahad,
fashewa suka kumayi da dariya,kanal yousouf yace"haba junaid,cewa zakayi duk gidan nan babu wanda yakai ka,sharar bacci idan dare yayi,mutumin da daƙyar ake tashin shi sallar asuba shine yake cika baki yana faɗin yafi kowa sallar dare,"
bubbuga ƙafa junaid yayi cike da shagwa6a yace"Kai yaya yousouf dan Allah ka daina faɗin haka,kada kasa araina ni,"
"Raini kuma na yaushe junaid!agabansu fa kake bubbuga ƙafa kamar ƙaramin yaro kana shagwa6a,a haka kake cewa kar araina ka,wace mace ce zata so ta auri shagwa6a66an namiji irinka?acewar kanal yousouf,
Tur6une fuska junaid yayi yana faman zumbura baki,juyawa yayi tare da kai idanunshi kan abusufyan yace"Uncle,ae dai zaka bani kyautar ɗaya ko"?
Abusufyan yace"mezai hana junaid?ko sisi bana buƙata,duk wacce kakeso acikinsu,zan baka ita kyauta,basai ka biya sadaki ba," gwalo yayi ma kanal yousouf yana fadin"ae dae Uncle yace zai bani,kuma a kyauta ma,"
Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba,duk wannan rashin wayon da Junaid ke yi akan idon jahad,zubama sarautar Allah ido tayi,aranta tace wai dama haka yake?saboda ita bata ta6a ganin junaid na shagwa6a agabanta ba,hada su gwalo ɗabi'unsa kamar na yaron goye,kaɗan kika gani
Cike da nishaɗi sukeyin firar tasu,adai dai lokacin General ishaq da Abbas suka shigo cikin main palour ɗin,sae faman sakin fara'a suke yi,ƙarasa shigowa sukayi kai tsaye suka nufi inda su Abba ke tsaye,gaishe da abba sukayi,kafin su jahad suka haɗa baki wurin gaisar dasu,
Fuskar ishaq ɗauke da murmushi yace"Masha Allah,nama rasa abunda zance,yanzu wannan duk namu ne"?yayi maganar yana nuna su hosana,Abba ne ya bashi amsar cewa"Naku ne ishaq,halak malak Allah ya mallaka maku,gasu nan harsu uku,"
Abbas yace"kamar yadda Allah ya nuna mana wannan ranar da ranmu kuma da lafiyarmu,ina fata Allah ya ƙara haɗamu a ranar auransu kamar haka dae........' haɗa baki su Abba suka yi wurin cewa"Ameen,"banda abusufyan wanda ya sunnar da kanshi ƙasa yana murmushi,Sehrish da jahad kuwa duk kunya ta gama rufesu,
Abba yace"ko baku son auren ne"? Shiru su kayi suna faman ƙumshe dariya,
"Sun ma isa suce basa so?ga yayyansu nan duk tazurai,ae dole su bada hadin Kai asamu a rufa ma juna asiri," cike da zolaya ishaq yayi maganar,yayi matuƙar basu dariya,
Adai dai lokacin Aunty babba ta shigo cikin falon ita da hafsat,😲
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Tofah nan fa kowa ya shiga tunanin wata hujja ce Sgr ke da ita?kanga wayar yayi a kunnansa,then Calmly ya furta"Ku ƙaraso ciki,"jin haka yasa kowa kai idanunshi kan ƙopar shigowa falon,don ganin su wanene zasu shigo ciki,
Bada jimawa ba,wata haɗaɗɗiyar Wheel chair Golden Colour mai ɗauke da wani dattijo tsoho tukuf fari tass hatta sumar kanshi furfura ce fara tass babu zaren gashi ko ɗaya daya kasance launin baƙi,hatta gashin girarsa dana idonsa fari ne tass duk furfura ta mamaye ko'ina,wani matashi ne ke ruƙe da ita yana turashi a nutse,tashin hankali ae koda Ammi tayi Arba da mutumin dake a saman wheel chair ɗin nan,hankalinta gaba ɗaya ya tashi haikam,ba ita ba Hatta su Abba dasu Gwaggo da Azeema sunyi matuƙar mamakin ganinshi,saboda a iya saninsu baya qasar,a Saudi Arabia yake da zama,amma sai gashi yau Unexpected yazo,wannan wani irin zuwan bazata ne?
Lokacin da matashin ya ƙaraso dashi ciki Ammi ta tabbatar da cewar dagaske dae shine,a kiɗime ta miƙe tsaye muryarta na in,ina ta ambaci sunan shi"Mo...moddibo"
Wani irin kallo tsohon ya wurga mata,kallon zakiyi bayani,gwaggon katsina kuwa wani irin farin ciki ne ya lullu6e ta,saboda tasan cewa tunda Modibbo ya tako da ƙafafunsa yazo Nigeria to tabbas za'a samu maslaha,saboda duk duniyar nan babu wanda ke taka ma Ammi burki in ta burkice sai Shi!mugun shakkar shi take ji,saboda shi tamkar Ubane agareta,a hannunshi ta taso,shiyasa yasan hanyoyi da dama da zai iya tankwarata,kuma duk wasu halaye nata da ɗabi'unta nashi ne sak ta ɗaukko,amma shi da ya manyanta ya ajiye wannan jin kan,'
Bayan saurayin ya tsayar da wheel chair ɗin,Modibbo ya yunƙura tare da miƙewa da sandar hannunshi,cikin sauri suka bashi wuri,ya samu wuri ya zauna a hakimce saman sofa,nan kowa ya shiga gaishe dashi suna yi mashi sannu da zuwa,fuskar nan tashi asake yake amsa masu,ba ƙaramin daɗin zuwan modibbo suka ji ba,bayan ya kammala kar6ar gaisuwarsu ɗaya bayan ɗaya,
Sannan Ammi tace"Yaya sannu da zuwa,ya gajiyar tafiya"
Fuskarshi aɗaure yace"Gajiya tabi jiki,ae ba yau nazo ba,tun shekaran jiya ina ƙasar nan,zuwa ne kawai banyi ba,kuma ba don kowa nazo ba sai don saboda ke!"
Jin haka yasa ta koma ta zauna,jiki asanyaye,
Cikin sauri Abba ya kalli su fawan tare dayi masu alamar su tashi su bar wurin,"mikewa su kayi dama Jahan a ƙagare yake daya bar wurin,duk ji yake kamar ya ɗosa mazannansa akan wuta,atare suka miƙe tare da barin wurin,Ya rage daga Gwaggon katsina,Abbansu,hajiya Azeema,General ishaq,da Cg Abbas,Uncle Abusufyan,marshal Omar da Sgr,bayan su kuma sae su Jahad dake zaune ƙasa,duk sunyi zuru rayuwarsu a hannun Allah,basu san su wanene waɗannan tsoffin ba,amma sun tsorata dasu,musamman Ammi data tayar masu da Hankali,har tana ƙoƙarin korarsu daga gidan,
Bayan su jahan sun shiga ciki,ya fashe da dariya hada dafe ciki yana faɗin"Dama ance GABA DA GABANTA ALJANI YA TAKA WUTA"💥
Junaid kuwa,bedroom ɗin Abbansu ya wuce,anan ya samu mommynsu tsaye agaban drawer,jikinta sanye da doguwar riga,tana ƙoƙarin sanya mayafi akanta,
Sam bata lura dashi ba,har saida ya ƙarasa bayanta tare da rungumota,hannu tasa tare da janyoshi ta dawo dashi ta gabanta,a shagwa6e ya ambaci sunanta"Mommy dama kina a ɗaki,bakisan meke faruwa ba a babban falo,"
Hannu tasa tare da shafa fuskarshi tace"Romeo,bani da alaƙa da abunda ke faruwa acan,yanzu faɗamun naga fuskarka kamar akwai damuwa,"
"Mommy,ba Ammi bace take son korar su Jahad daga gidan nan ba,"
"To menene damuwarka aciki don ta kore su"?
Sakin baki junaid yayi yana kallonta kafin ya ɗaure fuskarshi yace"Haba Mommy,ƴa'ƴan uncle ɗinmu fa ne,taya ba zan damu ba,uncle fa yana sonmu sosai,muma dole mu so ya'yanshi,kuma su jinin mu ne,nidai wlh banso ta koresu,kuma Allah koda ace ta koresu,wlh saina bisu.....'ya ƙarasa maganar yana zum6ura baki,
Hannu tasa taja kumatunsa"Ni kuma an gaya maka zan barka ne?zansa a ɗauke mun kaine,in kaika U.s mu cigaba da rayuwarmu acan,ko ba zaka bi mommynka bane,"
Bubbuga ƙafarsa yayi tare da cewa"I wanna fallow u Mom,amma Allah sai dai mu tafi mu duka tare dasu sehrish,jahad da hosana,"
"Dole dai saina je dasu"?
ɗaga mata kai yayi alamar eh,janyo shi tayi ta rungumeshi ajikinta,"don't worry dear kome kakeso zanyi,indae hakan zai faranta maka rai,yanzu mu zauna ka tayani fira,inaso mu tattauna wata magana dakai mai mahimmanci,"
Komawa sukayi tare da zama daga saman gadon,suka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu,
*Aunty Babba*
Lokacin da suka faɗa cikin ɗakin suna murna ita da hayaam,tsayawa sukayi daga tsaye,suna tattaunawa,Aunty babba tace"Ae dama saida raina ya bani cewar Ammi bazata barsu su zauna a gidan nan ba!gaskiya matar nan ta burge ni wlh,yadda ta zagesu tass ta kirasu da shaggu hakan ba ƙaramin nishaɗi ya sani ba,in banda ma shashasha irin Abusufyan taya zaka kawo ƴa'ƴa daga sama kace ya'yanka ne,kuma kayi tunanin cewa kowa zai yarda dakai?Ae ni wlh tayi mun dai dai matar nan,"
Ta ƙarasa maganar tana faman sakin shu'umin murmushin nan nata,
Hayaam tace"Nima ba ƙaramin burgeni tayi ba,naci dariya lokacin data korasu suka watsa aguje suna kuka,ƴan jakar uban,yanzu sai muga ina zasu dosa,dama su kashe kansu kawai su huta muma kuma munsamu natsuwa," cike da nishaɗi take maganar tana watsa hannu alamar ita ko ajikinta,
"Dama abunda yasa nake son Ammi ta koresu,kinga na farko zasu fita daga cikin zuri'arsu ne gaba ɗaya,babu su babu auren ɗaya daga cikin ƴa'ƴan Abba,saboda Ammi bazata bari su auri bare ba,balle kuma yaran da ta ambaci sunansu da shaggu,Secondly kuma wannan korar da tayi masu,zai hana Ishaq da Omar su tuhume ni akan tonan asirin da waccen Zararrar taso tayi mun a bainar jama'a,kinga riba biyu kenan,"
Tana kai karshen maganarta,hayaam ta ɗaura da cewar"wannan haka yake Auntyna,mu ɗin jinin nasara ne,duk abunda muka sa agaba sai munga bayanshi koma uban menene shi,"
Dariyar mugunta Aunty babba ta kuma saki kafin tace"Bazan ƙyalesu haka nan ba,saboda Omar zai iya bin bayansu don ya taimakesu,dole in samu wanda zaibi takansu da mota su mutu kawai,kowa ya huta,"
Hayaam tace"faƙat!kinga babu su a duniyarma balle ayi dasu,"
.......duk wannan surutan da suke yi,Amani na la6e a ƙopar ɗakinsu wadda bata idasa rufewa ba,tana recording ɗin muryoyinsu a wayarta,don taci alwashin saita tarwatsa duk wani plan nasu,Ni boss nace kinyi mun dai dai,
*Boss Bature*
The genius
❤🤍❤
bari mu leƙa falo muga meke wakana,shin ansamu cigaba ko kuwa ana nan yadda ake?
Natsuwa su kayi gaba ɗayansu,wurin yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta,kowa ya natsu ya nabba'a tamkar ɗalibai ne agaban ya sayyadi,bafa sayyadi mijin abu ba,ina nufin malami,kar ayimun wata fahimta,
"Waɗannan sune ƴan ukun Abusufyan ɗin"modibbo ne yayi maganar yayin da idanunshi ke akan Su jahad dake zaune sunyi zuru zuru,'
Har suna haɗa baki wurin cewa"Sune,"
Jinjina kai yayi tare da mayar da idanunshi kan Ammi yace"Ki kace yaran shaggu ne ko?Wata hujja gare ki na cewar bada aure ya haifesu ba?
Fuskarta aɗaure tace"Ina da hujja,saboda nice mahaifiyarshi,kuma ni bansan an ɗaura mashi aure da kowa ba,"
Girgiza kai modibbo yayi,sannan yace"hannunki ya taso ne?ko kuwa wurin ki kaɗae za'a iya ɗaura mashi aure ne"?
Shiru tayi batace masa uffan ba,cigaba da magana yayi"don haka baki da wata hujja ta cewar abusufyan yayi aure ko baiyi aure ba,ya samu ƴa'ƴa,wlh Aisha kin ban mamaki!wai har yaushe ne zaki ajiye waɗannan makaman yaƙin naki ne?ke fa yanzu ba yarinya bace,kin tara ya'ya da jikoki amma har yau bazaki ajiye wannan zafin ran naki ba,sai yaushe ne ya'yanki da kuma jikokinki zasu ji daɗin zama dake ne?yanzu ni ba misali bane agareki?ko bakisan wanene modibbo ba?kinfi kowa sanina bani da wasa ko miskala zarratin,duk wani kangararre acikinku,keda ƴan uwanki nine nan nake tankwarashi,amma yanzu saboda na manyata,na tara ya'ya da jikoki,duk na ajiye waɗannan ɗabi'un,Na canza kaina ne ba don komai ba sai don saboda ya'yana da kuma jikokina suji daɗin zama dani,kuma suyi alfahari dani amatsayina na kakansu,bawai su dinga tsoro na ba,suna gudu na harma su dinga yi mun fatan mutuwa,kamar ke ɗin nan dai.....'yayi maganar yana nuna ta da sandar hannunshi,sunnar dakai Ammi tayi tana faman jinjina kai,
Canza harshe modibbo yayi izuwa harshen fulatanci,yayi hakan ne saboda kada faɗan da zaiyi mata ya zama tamkar tozarci ne agaban jikokinta,
"Gaba ɗaya kin takurawa rayuwar ya'yanki,da ta jikokinki,kin hanasu sakat,ko irin wasan dake tsakanin kaka da jikan nan bakya yi masu,kullum burinki ki ƙuntata rayuwarsu,shin menene ribarki idan kinyi hakan? Ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,kafin yaci gaba da cewa"Yanzu jibi yaran nan ƴan wurin fatima,hakanan kika ɗaura karan tsana kika ɗaura masu sai kace ba jininki ba!in ma saboda mahaifiyarsu ne,ke kin ta6a ganin inda laifin wani ke shafar wani ne?in kuwa haka ne ae da dukkanmu mun shiga uku,saboda wancan zaiyi sata ne a ɗaura maka laifin bayan bakai ne ka aikata ba,"
Katse shi tayi cikin harshen fulatanci tace"Amma yaya modibbo ni meyasa ya'yana basu jin maganata ne?basu ɗaukeni mahaifiyarsu ba,suna yin abu gamon kansu batare da sun sanar mun ba,Hossein ya ƙetare ƙasar nan yaje yayi aure batare da sani na ba,sai dai kawai na ganshi da mata ya dawomin,matar kuma ma farar fata ba jinsun mu ba,sannan kuma Abusufyan shima yayi aure batare da sani na ba,saboda me zasuyi mun haka ne?
anzo dai dai wajen,acewar modibbo gyara zama yayi sannan yace"kin manta yadda akai kika auri salahuddeen ne?to idan kin manta bari na tuna maki,dama duk wanda ya bijire ma iyayensa ko ba daɗe ko ba jima sai shima yaga ba dai dai ba,na farko bada sa hannun iyayenmu ba,kika shiga aikin Soja,babu irin yadda ba'ayi dake ba don ana ganin bai dace dake ba,ba kaman daya kasance ke bafullatana ce,amma kika ƙeƙashe ƙasa kikace sai kinyi aikin soja,a ƙarshe da aka takura maki,shine kika tattara kayan ki kika dawo gidana da zama saboda kina tunanin cewar ni zan goya maki baya don ki samu abunda kikeso,da kika zo wurina a lokacin na nuna cewar nima bazansa hannu na ba acikin lamarin tunda har iyayenmu sun nuna basu so,a ƙarshe sai kika gudu batare da sanin kowa ba,kika shiga aikin Soja,sae dai kwatsam muka ganki da kakin Soja ajikinki,ko ba haka akayi ba"?
Wata irin zufa ce ta shiga wankowa a fuskar Ammi sam bata ta6a tsammanin cewa wannan ƙaramin kuskuren data aikata na bijirema iyayensu,zai dinga bibiyar rayuwarta bane,
"Akan wannan aikin sojan da kika shiga,babu wanda baiyi kuka dake ba,saboda kafiya,da taurin kai irin naki,ga jinkai dake gareki,iyayenmu basu isa su baki umarni kai tsaye kiyi abu ba,sai sun biyo ta wurina saboda shakkarki da suke ji,bayan wannan kuma,baki sanar ma kowa ba game da salahuddeen lokacin da kuka fara soyayya dashi ba,sai daga baya ne muka fahimci shi ya hure maki kunne har kika bijire mana kika shiga aikin sojan,hakan kuma yasa duk muka ki amincewa da farko ki aure shi,amman da yake Allah ya kaddaro aure tsakaninku ba yadda muka iya dole muka kyale ki ko don kafewar da kika yi da kuma rabon itama Ameena anan zata samu mijin, ko ba haka akayi ba"?
Jinjina kai Ammi tashiga yi yayin da idanunta suka cicciko tab da kwalla amma bata bari sun zuba ba,
Gwaggon katsina kuwa,sae faman sakin murmushi takeyi,tana faɗin"kwarai kuwa,haka akayi,"Abban su junaid kuwa da hajiya azeema duk jikinsu yayi mugun sanyi,sae yanzu suka gane daga inda matsalar take,dama duk in mutun yaga rayuwarshi tana tafiya ba dai dai ba,kuma bai akaita wani zunubi,toWlh ya binciki kanshi!ya tuhumi kanshi ahankali zai gano dalili,
Su jahad dae suna nan tsugunne sun kasa kunne suna sauraronsu,sai dai subi bakin modibbo da kallo,daga bisani in Ammi na magana subi ta da kallo saboda basu iya fulatanci ba,haka Marshal Omar dasu ishaq duk basa jin fulatanci,haka zalika Sgr baya jin harshen nasu,dama shi ko hausa daƙyar ya koye ta,kuma har yau in yana magana da harshen hausa sai ka gane cewar ɗan koyo ne don sam hausarsa bata nuna ba shiyasa bai fiye yin magana da hausa zalla ba saiya haɗa da turanci ko spanish,amma kuma hausar tashi ba ƙaramin daɗi takeyi ma mutane ba,
Murmushi Modibbo ya ɗan saki kafin yaci gaba da cewa"ina fata yanzu kin tuna komai"?
Siraran hawayen da take 6oyewa ne suka gangaro a saman fuskarta,muryarta ƙasa ƙasa tace"Na tuna,"
Modibbo yace"Tunda kin tuna bari na ƙara ɗaura ki akan hanya,irin abunda kika aikata ne yasa shima ɗan cikinki da kika haifa yaje yayi aure batare da saninki ba,saboda gudun kada ya fara sanar dake ki hana shi yin auren,hossein ya auri Alala..kunzandariya...."kasa ƙarasa maganar yayi saboda bai iya ambaton sunanta ba,abun yaso yaba Sgr dariya,amma ya basar da ita tare da gyara mashi sunan yace"Alexandra ne sunan,"
Modibbo yace"yawwa ɗan gari,bazan dai iya Ambaton sunan nata ba,a barshi a fatima,tunda ae ta ta6a musulunta,kuma muna sa ran zata ƙara musulunta insha Allah,"
Suka ɗanyi dariya,kafin ya ɗaura da cewar"Hossein ya auri fatima batare da saninki ba,saboda yasan halinki sarai kin tsani jinsin da ba naki ba,gudun kar ya sanar dake kiƙi amince masa yasa shi yin hakan,sannan......"modibbo bai ƙarasa maganar ba,ammi ta kuma katse mashi hanzarinshi da cewa"Yaya modibbo amma ae ni harsu biyu sukayi mun haka!bayan ni,ni kaɗai ce na bijire ma iyayenmu haka,"
wannan maganar ta Ammi yasa shi yin dariya,tare da girgiza kai yace"in kikayi wata maganar kina tunamin da ƙuruciyarki wlh,dama ita irin sakayyar nan tamkar ramuwar gayya haka take,kuma ita ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,sakamakon abunda kika shuka ne,yasa kika girbi kyakkyawan sakamakon da ya zarta nakin,kuma tunda har kika iya ƙyale hossein bayan laifin daya aikata maki na auren bare kuma farar fata ae yaci ace kin yafe ma Abusufyan tunda shi da ƙuruciyarshi ya auri yarinyar,kuma hada sa hannun gwaggonshi,kuma kinsan wacece ita a wurinki,da mahaifinmu da nata uwa daya uba daya,kuma saboda yardar da kikayi da itane yasa kika damƙa mata amanarshi,ita kuma ƙaunar da take yi maki ne ya shafi ɗanki da kika haifa,hakan yasa ba zataso wani abu ya cutar dashi ba,Yaro ya nuna yana son ƴar mai gadin gidansu,ke kuma kin tsani auren bare mara asali,gashi shi kuma yaron ya kwallafa rai akan yarinyar,don lokacin da ita Aminatu taso ta sanar dake game da yarinyar balbaleta kikayi da masifa,kina cewa karta kuskura ta bari alaƙarsu tayi nisa,ta raba tsakaninshi da yarinyar,a ranar saida Abusufyan ya suma jin za'a raba shi da abunda yakeso,wannan dalilin ne yasa hajiya ameenatu ta aura mashi yarinyar batare da ta sanarma kowa ba,sai ni ɗinnan da nake magana,"
ɗagowa Ammi tayi tana kallonshi cike da mamaki,
Jaddada mata maganar yayi"kwarai kuwa ta sanar dani,nasan da zancen auren,kuma aranar da aka ɗaura auren Abusufyan da zainabu abu,ina ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren batare da sanin kowa ba,ita kanta hajiya ameenatu batasan na halarci ɗaurin auren nasu ba,a iya waya kawai ta sanar dani,sae kuma akaci sa'a ina da wani taron manyan malamai da zamu halarta anan jihar kano,wannan ne babban maƙasudin daya kaini garin harna shaida wannan ɗaurin auren....."
Ae tunkan modibbo yakai ƙarshen maganar wani irin murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskar kowannansu,saboda yayi maganar ne cikin harshen da zasuji,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya abusufyan ya shiga saukewa,nan take yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarshi,duk da yayi mamakin zuwan modibbo wurin ɗaurin auran nashi saboda bai ganshi ba,amma tunawa da irin dubban al'ummar dake a masallacin kuma ya kasance ranar juma'a ne ana kammala salla aka ɗaura auren nasu,tabbas bazai iya tantance kowa dake a wurin ba,amma ko a lokacin bayan an ɗaura auren sun koma gida sai da baba buzu ya kirashi gefe guda yake sanar dashi cewa"Wani babban malami,yayi mashi alheri bayan sun fito daga masallaci,kuma yana tunanin cewar Kamar jininsu ne saboda yaga kamannin Hajiya ameena a fuskarshi,a lokacin Abusufyan bai gane wanene ba,sai yau da modibbo yayi maganar nan kwatsam ya zancen ya faɗo mashi aranshi bayan ya shiga zurfin tunani,tabbas kuwa modibbo ne,
Murmushi modibbo yayi tare da kallon Abusufyan yace"nasan zakayi mamaki,saboda nazo ɗaurin auren ka batare da sanin kowa ba,uzuri ne ke gare ni a lokacin shiyasa ban nemeka ba,don nasan muddin ka ganni a lokacin saika nace akan in tsaya,"
ya ƙarasa maganar tare da mayar da idanunshi kan Ammi,tun kafin ya kuma cewa wani abu,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Amma yaya kasan da maganar auren nashi shine ba'a sanar dani ba?saboda me?
"Saboda halinki"! Kai tsaye ya bata amsa,
"Tabbas naso in sanar dake ko alokacin,saboda kinsan cewa ni bana jin shakkarki,hajiya ameenace ta rokeni akan cewar karna sanar dake,saboda hakan zai iyasa ki fusata harma ki yanke ma Abusufyan hukunci mai tsanani,kuma a ƙarshe zumuncin dake tsakaninki da ita ya tarwatse,dana nace akan zan sanar dake har kuka saida tayi mun,wannan dalilin ne yasa ban sanar dake ba,kuma ana haka daga baya kwatsam naji labarin mutuwar auren Abusufyan ɗin,hada ƙarin haka yasa akabar zancen gaba ɗaya,ashe yarinya ta fita da cikinsa ta auri wani,to kinji dalilin dayasa mu kanmu bamu san da ya'yan nashi ba,har suka kai wannan girman a hannun mijin da ta aura daga baya,"
Dakatawa yayi da maganar,falon yayi shiru na wani lokaci,kafin ya mayar da idanunshi kan Sgr dake zaune,yace mashi"ka kunna mata audio din nan daka kunna mun itama ta saurare shi,"
"Okey,"ya amsa mashi tare da,daddana wayar hannunshi,ya shiga audio din tare da kunnashi,sannan ya miƙe tare da ƙarasawa kusa da kujerar da Ammi ke zaune ya miƙa mata wayar,yatsun hannunta na kerma tasa hannu ta kar6i wayar tashi,ta ajiye asaman hannun sofa ɗin tana sauraronshi,wannan audio din na labarin da abusufyan ya bayar ne da kuma Labarin dasu sehrish suka bayar na irin ukubar da suka sha a hannun ya sayyadi,ashe ranar da abun ya faru,Sgr ya ɗauki audio na maganganun da sukayi kaf acikin wayarshi,tabbas shi ba ƙaramin jami'in Soja bane!yana Aikinsa wani lokacin tamkar jami'in sirri,Na jinjina masa,da irin baiwar da Allah yayi mashi da kuma irin kwazon dake gare shi,ta ko ina Sgr ya haɗa,shiyasa nace maku shi ɗin komai nasa Extraodinary ne~~~
Miƙewa junaid yayi tare da ruƙo hannun Mommynsu yace"Shikenan mommy tunda mun kammala discussion din,ki taso muje falo pls,kada kice baki zuwa,in ba haka ba raina zai 6aci,wlh ko abincin dare bazanci ba,indai kika ƙi zuwa gaishe da modibbo,"
Cike da mamaki tace"Modibbo?kana nufin mahaifin maryam oummunsu Omar?
daga mata kai yayi alamar eh,
Shiru tayi tana wani tunani,a iya saninta modibbo mutunne mai mutunci sosai,saboda shine ya taka ma Ammi burki a lokacin da taso Abba ya sake ta,tabbas bazata ta6a mantawa da halarcin da modibbo yayi mata ba,
Ganin ta miƙe yasa junaid sakin murmushi yace"mommy zaki ko"? Jinjina mashi kai tayi alamar eh,
Janyo hannunta yayi har suka ƙaraso falon,ganin hankalin mutanen dake acikin falon gaba daya yana akan Audio din da ammi ke saurare,hakan yasa itama ta samu wuri ta zauna,junaid ma ya zauna gefenta,yayin da idanunshi ke akan su sehrish,sam basu lura dashi ba saboda hankalinsu duk ya tashi,a sakamakon Audio din da aka kunna,saboda sun tsani jin labarin rayuwarsu,ko miskala zarratin,
Kowa ya natsu yana sauraron audio ɗin,lokacin da Abusufyan ya kammala bada tarihin rayuwarshi da abu,sai next audio ɗin ya shiga wanda Jahad ke bada labarin rayuwarsu,nan take hankalin AMMI yayi mugun tashi,jikinta har tsuma yakeyi,tuni wasu siraran hawaye suka shiga zarya a kuncinta,ita kanta Alexandra jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,tunda take arayuwarta bata ta6a jin tausayin wani ɗan adam ba,daga ita har ammin kamar yadda sukaji tausayin waɗannan bayin Allahn ba,Very heart touching story,wanda duk wani mai imani In ya saurareshi dole ya zubda hawaye,in ma baiyi kuka ba,
Ganin yadda hawaye ke sintiri akan fuskar AMMI yasa Omar ya cire hanky daga aljihunsa ya miƙa mata,dama kamar yasan cikin buƙatarshi take,a fuskarta ta kifa hankacif ɗin,ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai,kowa yayi mamakin yadda Ammi ke kuka,cikin shessheƙar tace"ku kashe mun audio din nan ya isa haka,kunnuwa na bazasu iya jurar jin wannan tashin hankalin ba,'
dama Audio ɗin yazo ƙarshe,junaid ne ya mike ya ɗauki wayar,tare da miƙa ma babban yayansu ita,ya kashe audio ɗin,
"Shiyasa akeso ko da yaushe mutun ya kasance mai sauƙin kai,kada ya cika tsaurara al'amurransa,yanzu da ace banzo ba,da shikenan,haka zaki kora yaran nan,ke baki tsaya kinyi bincike ba,kuma baki saurari bayani daga gurin kowannansu ba kawai kin tashi kin yanke hukunci,sai daga baya kuma kizo kina danasani"
daƙyar ammi ta iya furta"Astagfurullah Allah na tuba!ka yafe mun,rashin sani ne yasa na kirasu da shaggu,game da halin da yaran nan suka tsinci kansu,duk laifin mahaifinsu ne,shine silar komai,duk da daman Allah ya ƙaddara faruwar hakan babu wanda ya isa ya hana,amma Abusufyan bai kyauta ma rayuwarsu ba,meyasa bai sanar ma kowa ba don aɗauki mataki?saboda kawai yayi mashi barazana?Amma dai Allah ya tsine ma fasiƙin mutumin nan,Wlh bazan barsu ba,saboda me laifin kakansu zai shafe su?wannan wata irin mugunta ce mara kan gado,?bai tsaya a iya kan ya'yan salahudeen ba,hada jikokin duka yake ɗaukar fansa akansu,?kuma shima salahudeen ɗin daya kashe mahaifinsu ae don saboda mugayen laifukan da aka kamasu dashi ne,ɗaukar fansar ta mutun ukuce suke ɗauka,mahaifinsu da kuma mahaifiyarsu,da kuma wannan ɗan koran nasu,dukkansu Allah zai toni asirinsu,'
Jinjina kai modibbo yayi yana sauraronta saida takai ƙarshen maganarta,tukunna yace"ba komai ne yasa na tako nazo ƙasar nan ba,face don abu uku,kuma ina fata zaki bani haɗin kai domin asamu maslaha atsakaninku gaba daya,saboda baza a ta6a cin nasarar gano waɗannan masu ɗaukar fansar ba,har sai ku na cikin gidan kun fara haɗa kanku,in ba haka ba,munafukan dake shirya maku zagwan ƙasa zasu samu nasarar cin galaba akanku,ta hanyar rarraba kawunanku,saboda ni inaji araina cewar masu shirya wannan maƙarƙashiyar suna ATARE DAKU!sun shiga cikinku,suna acikin rayuwarku!'
Wannan maganar ba ƙaramin jijjigasu tayi ba,don sai da kowannansu ya ɗago yana kallon fuskar modibbon,
"Nasan zakuyi mamaki amma nan gaba sannu a hankali zaku shaida maganata,yanzu dae bari inyi abunda ya kawoni,"
"AISHA" Ya ambaci sunan Ammi,muryarta asanyaye ta amsa mashi da Na'am,
"Banaso in ƙarajin wani ƙorafi akanki!wannan ne na farko kuma wannan ne na ƙarshe!idan har kinaso ki zauna lafiya,to ki gyara tsakaninki da ya'yanki!da kuma tsakaninki da Jikokinki,na uku kuma shine tsakaninki da surukarki fatima,"ya ƙarasa maganar yana nuna Alexandra da sandar hannunshi,ɗagowa ammi tayi tare da kai idonta kan Mommynsu junaid wadda itama kallon nata takeyi,kawar da kanta tayi gefe batare da tace komai ba,
Cigaba da magana modibbo yayi,"Allah ma mukanyi masa laifi kuma ya yafe mana,balle mu ƴan adam,fatima bata yi maki laifin komai ba,tun farko koda kike mata magana take mayar maki saboda kin nemi cin zarafinta ne!wanda kuma ba kowa ne zai iya jurewa ba,balle ita da take jar fata,yanayin rayuwarsu ko ince tarbiyarsu ba irin tamu bace,don da a ƙasarsu ne kikayi mata haka zata kaiki ƙara kotu ne a yanke maki hukunci,babu ruwanta da Cewar ke surukarta ce,sannan kuma bai kamata ki nuna mata ƙiyayya ba,duk maison naka ae masoyinka ne!ɗanki fa takeso,kuma saboda son da take mashi tabar iyayenta da kowa nata tazo ƙasar nan,inda bata san kowa ba,ko tsoron acutar da ita batayi ba,bakowa ne ma zai iya wannan kasadar ba,don haka yakamata ki so fatima saboda masoyiyarki ce,ba maƙiyiyarki ba,idan don ta kasance farar fata ce,damu dasu shin ba Allah bane ya halicce mu ba?ya banbanta mu ne?ko wani yafi wani ne"? Ya ɗan jinkirta da maganar yana kallonta,
Kafin ya ɗaura da cewar"Yakamata ki ajiye wannan gabar dake tsakaninki da ita,Yanzu fatima ta wuce suruka a wurinki,tamkar ƴ'a take a wurinki,tunda ta hayayyafa da ɗanki,yakamata kiyi alfahari da ita saboda itace ta haifa maki ɗaya daga cikin jikokinki wanda duniya take alfahari dasu,waɗanda suka ɗaukaka darajar mu a idon duniya,"
Nauyayyiyar ajiyar zuciya Ammi tasaki tare da gyaɗa kai tace"Insha Allah komai ya wuce,"
Murmushi Abba ya saki ranshi fari tass kamar an yi mashi albishir da gidan aljanna,
"Sannan kema Fatima inaso ki ajiye dukkan wasu makaman yaƙin ki,kibi surukarki tamkar mahaifiyarki,kiyi mata biyayya amatsayinta na wadda ta tsugunna ta haifi uban ya'yanki,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Nima a wurina komai ya wuce,dama saboda ƙiyayyar da take nunamin ni da ya'yana ne yasa nima nake ƙinta,amma daga yanzu insha Allah babu wanda zai ƙara jinkan mu,"
Tana kai ƙarshen maganar junaid yace"Gaskiya,wannan sulhun bai cika yadda akeson shi ba,Mommy da Ammi basu ta6a yin koda musabaha ba,yakamata yau su tashi su rungume junansu ta hakan ne zamu gane cewar sun shirya da junansu,"
Gaba ɗayansu suka saki murmushi,miƙewa Alexandra ta farayi kamin Ammi itama ta miƙe,suka ƙarasa tare da rungume juna,tafi su Abba suka shiga yi wanda hakan yaja hankalin sauran matasan gidan,har suka firfito cikin falon don suga me ke wakana,ae koda su kayi arba da Ammi da Alexandra rungume da juna,nan fa suka shiga sowa,abun ba ƙaramin farin ciki ya sanyasu ba,musamman su Fawan don sun jima suna jiran wannan ranar tazo,ashe da rabon zasu ganta da idanuwansu,
"Ki yafe mun duk abubuwan da nayi maki,kuma inaso ki sani ba don bana sonki bane yasa nayi maki hakan ba,kawai haline irin nawa,da kuma sharrin shaiɗan" Ammi ce tayi maganar ayayin da take raba jikinta daga na alexandra,fuskar kowanansu ɗauke da siraran hawaye,
Murmushi alex ta saki kafin tace"Allah ya yafe mana gaba ɗaya,inaji kamar nafi kowa farin cikin wannan ranar,"tayi maganar fuskarta ɗauke da dariya,suna cikin rahar nan sukaji ana ɗaukarsu hoto ket ket!!
Da sauri suka waiga don su ga wanene,ashe wai fawan ne ya ɗauko camera ɗinsu,yana ɗaukarsu hoto yana faɗin"yau a daily trust dole su buga wannan gagarumin labarin,zazzafan gaske,Ammin mu wato kakarmu a yau ta rungumi surukarta wadda ta kasance mahaifiyarmu bayan sun dade suna shan gwagwarmaya ,"
Dariya sosai su kayi,ganin ya sanyasu raha,yasa shi cewa"Abba mu shigo ciki a ƙarasa tattaunawar tare damu?
Fuskar Abbansu ɗauke da murmushi yace"why not,a yanzu an sasanta komai,an samu maslaha,zaku iya zuwa ku zauna,"
Jin haka yasa suka ƙaraso ciki,gaba ɗayansu ne hada su twins jabeer,khaleed irfan dasu kanal,wuri suka samu suka zazzauna a ƙasa,
Junaid yace"Yawwa Amminmu,yanzu saura Uncle ɗinmu bawan Allah,yayi missing ɗinki sosai yakamata shima ki rungumeshi,ko yaji sanyi aranshi,"ya karasa yana langa6ar da kai.
Juyawa Ammi tayi tare da kallon abusufyan wanda ke a zaune,idonshi na kallon ƙasa,
Gyaran murya ta ɗan yi mashi,ya ɗago da idonshi ya kalleta,cike da zolaya tace"So kake sai nace ka taso"?
Fashewa yayi da dariya,kafin ya miƙe da sauri ya faɗa jikinta,sosai ta rungume shi ajikinta,tana ɗan bubbuga hannunta a bayanshi tace"nayi kewarka sosai,ka sani kuka Abusufyan,fiye da tunaninka,hakanan ka tafi ka barni shekara da shekaru...."tana maganar hawaye na fita a idanunta,
ɗagowa yayi daga jikinta,idonshi na fitar da kwalla yace"Ki yafe mun Ammi,nasan ban kyauta maki ba,nayi maki abubuwa da dama wanda bakyaso,nasan cewa hada haƙƙinki ne ke bibiyar rayuwata shiyasa ma harya shafi ya'yana,...."
Hannu tasa tana share mashi hawayenshi tace"Na yafe maka abusufyan,dama ni burina shine ka dawo kusa dani,kuma Alhamdulillah,gashinan ka dawo cikin yan uwanka,naji daɗin hakan sosai,Allah ya ƙara haɗamun kanku,"
gaba ɗaya suka amsa da Ammin,
"AMMI saura su rishi,su baki rungumesu ba,kalli fa kiga yadda duk suka shiga damuwa,bayin Allah,"
junaid ne ya sake yin maganar yana raku6e fuska,alamar tausayi
Kallonsu Ammi tayi,sun cunkushe wuri guda kamar kifin gwangwani,musamman Sehrish jikinta har lokacin sae kerma yake,a hankali Ammi ta taka izuwa inda suke,ta zuƙunna agabansu,sannan takai hannunta tare da shafa fuskokinsu,kafin tace"dole in nemi yafiyarku,saboda na jefebku da mummunan kalma,bisa rashin sani,ina mai matuƙar baku Haƙuri akan abunda ya faru a rayuwarku!ba laifinku bane laifin wasu ne akeso a ɗaura maku shiyasa aka biyo ta hanyarku duk don a ƙuntata mana,amma nayi maku alƙwarin cewa ɗaya daga cikin waɗanda sukayi sanadiyar wulaƙanta rayuwarku,Wlh bazai sha ba!daga rana irin ta yau zansa a fara bincike akansu har sai Allah ya tonu asirin kowannansu,kuma nayi maku alƙawarin cewa,zansa akawo maku wannan fasiƙin mutumin har inda kuke don ku wanke mun mummunar fuskarshi da tafukan hannayenku,"
Jin wannan maganar ta Ammi yasa Hosana fashewa da dariya,har white teeth ɗinta suka bayyana,dimples ɗin fuskarta suka lotsa,Jahad ma murmushi ne ya bayyana a fuskarta,sehrish ce kawai batayi murmushi ba,da alama kamar akwai wani abu dake damunta,duba da yanayin jikinta dake ta kerma,
Ruƙo hannayensu ammi tayi tare da miƙar dasu tsaye sannan ta haɗasu duka ta rungumesu sosai,ajikinta,
Wani irin matashin murmushi ne ya bayyana a fuskar kowannansu dake a falon,haƙika sunji daɗin wannan ranar,tsakaninsu da Allah sai godiya daya bar Modibbo a raye har zuwa wannan lokacin,saboda shine silar komai daya faru ayanzu,da bai zo ba da akasin hakan ne zai faru,
Addu'oi' Ammi ta shiga karantowa tana tottofa masu akawunansu,a ƙarshe tace"Allah yayi maku ALBARKA,"suka amsa mata da Amin,
Komawa su kayi kowa ya zauna,itama ammin ta zauna,bayan kowa ya natsu Modibbo yace"ko akwai mai magana acikinku"?
Da sauri Abbansu junaid yace"Ina da magana,"
Modibbo yace"faɗi kai tsaye muna sauraronka,"
"Yawwa kawuna,dama akan maganar fatima ne da Abusufyan!har yanzu basu shiri a tsakaninsu,tun wani sa6ani da suka ta6a samu a lokacin baya,to har yanzu basa jituwa,yakamata aduba lamarin,'
Sunnar dakai ƙasa Abusufyan yayi,kamar yadda itama alexandran tayi,
"Ae yanzu ko banyi masu magana ba,zasu shirya kansu ne ko don zumuncin dake a tsakaninsu,da kuma ƴa'ƴayensu,"
Murmushi kowannansu,yayi abusufyan yace"Insha Allah komai ya wuce a wurina,dama can ni ban ta6a ruƙeta araina ba,nasan rashin kunyar da nakeyi mata ne a lokacin baya yasa take fushi dani har yanzu,amma ina neman afuwarta,"
Yana kai ƙarshen maganarshi,Alexandra tace"Nima komai ya wuce a wurina,Allah ya yafe mana baki ɗaya,kuma ya ƙara haɗa kawunanmu,"
Wani irin ihu junaid ya fasa,saboda tsabar farin ciki,hankalin kowa ya koma kanshi,ganin sun zuba mashi ido yasa shi sanya tafin hannunshi ya rufe fuskarshi,saboda kunyar data rufe shi,ƙasa ƙasa yake sakin dariya,bakomai ne yasa shi wannan farin cikin ba,face Shiryawar da Momnynsu tayi da Uncle ɗinsu,ko ba komai zai samu amincewarta wurin auren ɗaya daga cikinsu,💃
"Gobe da safe zan wuce damaturu,tunda naci nasarar haɗa kawunanku,ina fata zaku kasance a haka ko bayan tafiyata," atare suka amsa mashi da cewa"Insha Allah,"
"Amma mun jima bamu haɗu ba,bazaka ƙara kwanaki ba"? Ammi ce tayi maganar,
murmushi modibbo yayi kafin yace"kada ki damu,tun da dai na shigo ƙasar zaku dinga ganina ne akai akai,insha Allah,"
Alhamdulillah,The end🥱🤣😂😅 nan bada jimawa ba,zan rubuta hakan insha Allah,nasan wasu har gabansu ya faɗi rass.........
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk mai son karanta littafin Abban sojoji,kai tsaye ya tuntu6eni ta numbar wayata 08103884440_
Special thanks to hafsat Usman Abubakar🥰,
"Koda ace baka samu zuwa ba,xamu zo nan damaturun,dama mu ya dace ace mun je can gaba ɗayan mu bayan komai ya lafa,ko don saboda ƴan ukun abusufyan,zamu je dasu don suma suga danginsu dake acan da kuma na zariyya,dana sauran state,"acewar ammi,
Modibbo yace"hakan ma yayi,Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku,"suka haɗa baki wurin amsa mashi da ameeeen,
Duk wannan abun dake faruwa Aunty babba da hayaam suna acikin ɗaki,kowannansu ya dafi waya sai danna yake yi,gaba ɗaya tunaninsu ya tafi akan cewa An kori su sehrish,hakan yasa hankalinsu ya kwanta luf,
miƙewa zaune aunty babba tayi daga kishingiɗen da take,fuskar nan a washe tace"Oh ni ƴasu,ko ina waɗannan ƴan ukun suka dosa yanzu?
Hayaam tace"Wama ya sanin masu,suna can suna gagari acikin gari,ƙarshenta ma a samu wata babbar mota zubin ɗan gotte tayi mana awon gaba da kawunansu,"
Fashewa su kayi da dariya,sai da suka tsagaita dayin dariyar Aunty babba tace"duba mun ƙarfe nawa yanzu,agogon wayata ba saiti,"
"kusan Ƙarfe tara fa yanzu,gashi ko abincin dare ma ba mu nema ba,"
Tsoki taja"mtsww,wannan wani irin gidane!A tunani na Azmee ya kamata ace ta kawo mana dinner ɗin mu har cikin ɗaki,ni bansan menene amfanin matar nan ba a cikin gidan nan,bata wani aiki,sae dae ta dafa masu abinci,ta zauna taci ta ƙoshi ta tara tumbi,ta mayar da gidan kamar na ubanta,"
Hayaam ta ɗaura da cewa"Ae kwanaki har magana taso ta gayamun,saboda waccen korarriyar yarinyar,Sehrish take da suna ko wa ma......."dakatawa tayi da yin maganar sakamakon turo ƙopar da taji anyi,atare suka kai idanunsu wurin,
Azmee ce ta shigo hannunta ɗauke da tray,koda su kayi arba da ita,nan fa suka shiga yin ƴan kame kame na rashin gaskiya,
Basu amsa mata sallamar da tayi masu ba,ƙarasawa tayi ta ajiye masu tray ɗin a ƙasa,sannan tace"abinci ne na kawo maku,bansan ko kuna buƙata ba,naga baku fito kun nema ba,shine nace bari na kawo maku a ɗaki,"
Washe baki suka shiga yi,hankalinsu harya kwanta,da alama bataji gossiping ɗinta da sukeyi ba,
"Mun gode sosae Azmee,wlh kina ƙoƙari sosai acikin gidan nan,ke kaɗae kike duk wasu aikace aikace na gidan nan,shekara da shekaru,baki ta6a gajiyawa ba,kin mayar da dangin nan tamkar naki,bansan meyasa har yanzu kike tare dasu ba,wahalar tayi yawa,yaci ace yanzu kin nemi miji kinyi aure,amma in kika cigaba da zama a haka,rayuwarki zata ƙare ne a matsayin baiwa kuma bazawara,ba wani cigaba,"
Tunda Aunty babba tafara magana azmee ta zuba mata ido tana kallonta,batare da ta ƙyafta idanunta ba,har sai da Aunty babba takai ƙarshen maganar,sannan tace"Bani da amsar da zan baki Laila,amma inaso ki sani dangin nan basu ɗaukeni kamar yadda kikayi tsammani ba,kuma ni bana gajiya da aiki a ƙarƙashinsu,saboda sunyi mun halarcin da bazan ta6a mantawa ba,"
Juyawa azmee tayi da sauri ta kama hanyar fita daga ɗakin,harta ruƙe handle ɗin ƙopar zata buɗe muryar aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"har yaushe ne zaki cigaba da danne abunda ke zuciyarki?
"Mekenan"!azmee ta tambaya a yayin da ta juyo da kanta tana kallonta,
"Azmee nafa son komai!na son cewa akwai wanda kikeso acikin gidan nan!saboda kin ta6a sanar dani a lokacin baya,ko kin manta"?
Baza kunne hayaam tayi tana sauraronsu,
"Hakane,na ta6a sanar dake,amma yanzu babu wannan a zuciyata,kuma ko a lokacin dana so shi,saboda irin kyautatawar da yake yi mun ne,kuma da tausayin shi da nakeji,na rashin matarshi a kusa dashi,Amma yanzu Alhamdulillah,uwar ƴa'yanshi tana a kusa dashi,babu wata sauran damuwa,
Murmushi aunty babba ta saki tare da miƙewa daga zaunen da take a gefen gadon,ta tunkari azmee tana cewa"Yanzu ke sai ki haƙura dashi?baki kwaɗayin ki aure shi,ki samu ƙaruwa dashi,ko don ki samu gado acikin gidan nan"? Da alama Aunty babba so take ta tunzura azmee,
Girgiza kai azmee tayi"ni bani da buri akan tara dukiya,bana kwaɗayin abun duniya,saboda sanin cewa komai na tara ƙarshe a gidan duniyar nan zan barshi!albashin da nake samu acikin gidan nan ya isheni in ƙarashe rayuwata dashi,"
Ta6e baki aunty babba tayi,fuskar nan ɗauke da shu'umin murmushin nan tace"Yanzu shikenan kin za6i ki ƙarashe rayuwarki a ƙarkashin wasu kenan?ke baki da ƴancin kanki?wlh azmee bakisan ciwon kanki ba,ban ta6a ganin ƴar wahala irin ki ba,kin ƙuntata rayuwarki,kin ƙasƙantar da kanki,duk don saboda ki faranta ma wasu!har yau babu wani cigaba a arayuwarki,yakamata ace yanxu kin mallaki katafaren gida naki na kanki,kin kuma mallaki mota,kinje hajji da umrah,kin kuma je yawon shaƙatawa dubai da sauran ƙasashe,haba azmee yakamata kiyima kanki adalci,wlh kina cutar kanki,Nidai shawara nake ba......"
Tsawar da azmee ta daka mata ne yasa ta kasa ƙarasa maganar,ba ƙaramin razana tayi da tsawar ba,tamkar ba abakin azmee ta fito ba,
"Ke baki isa ki tunzurani ba,laila!ki iya bakin ki,in ba so kike kija ma kanki ba,ki tsaya a iya matsayinki,nima in tsaya a nawa,idan ki kayi kuskuren shiga gonata wlh ranki zaiyi mugun 6aci," tana ƙarasa maganar,ta janyo ƙopar da sauri ta fuce,
"Hmmmm Aunty laila,matar nan fa ba zaki ta6a iya canza mata ra'ayi ba,don na lura itama kaifi ɗaya ce,"
Jinjina kai aunty babba tayi aranta tana mai mamakin irin yadda azmee ta daka mata tsawa,sai kace batasan matsayinta agidan Ba,!
Komawa tayi cikin ɗakin ta zauna dirshan a gefen gadon,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,taso ace taci nasara akan azmee ko don su sami haɗin kanta wurin Cimma burinsu,guntun tsoki taja tare da cewa"Ƴar wahala,sai kace tafi kowa tsoron Allah,kullum haka zaki ganta da cazbi a hannunta tana yawo,"
Ta ƙarasa maganar tare da mayar da idonta kan tray ɗin abincin da azmeen ta kawo masu,yatsina fuska tayi tare da kai hannu ta buɗe warmer ɗin,dambun shinkafa ne yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,a plate ta zuba masu nan suka zauna,suna ci ita da hayaam kamar wanda yunwa ta koro,
Azmee kuwa bayan fitarta daga ɗakin nasu,jiki a sanyaye ta wuce ɗakinta,kalaman aunty babba ba ƙaramin 6ata mata rai su kayi ba,zuciyarta ta sosu sosai,daure wa kawai takeyi,da ace bata kai zuciyarta nesa ba da ba abunda zai hana ta wanke fuskar laila da mari!
Sam ta manta da hafsat dake kwance a ɗakinta,baiwar Allah tun bayan fitarta daga ɗakin hayaam,ta wuce ɗakin azmee batare da sanin kowa ba azmee ce kaɗae tasan cewa tana a ɗakinta,anan tayi wanka,ta kuma ci abinci ta kwanta,saboda wani irin zazza6i daya saukar mata ajikinta,kwata kwata zuciyarta ba daɗi,tayi danasanin rayuwarta fiye da a ƙirga,idanunta na tsananin son ganin Su Jahad,amma tsoran tunkararsu takeyi,gashi har tsaraba tayi masu don ta basu hmmm,duk in ta tuna irin uƙubar da suka sha a hannunsu,sae ta fashe da matsanancin kuka,tun azmee na rarrashinta har ta gaji ta ƙyaleta,idanunta sun kumbura suntum haka la66anta ma,bakomai take yi ma fargaba ba,fa ce irin hukuncin da Mahaifinta zai yanke mata,don kuwa tasan muddin yaji abunda suka aikata masu jahad,Wlh ba zasu sha ba,su dukan su sae sun fuskanci mummunan hukunci a wurinsa,gaba ɗaya tayi nisa cikin zurfin tunani,taji shigowar azmee cikin ɗakin,buɗe idanunta tayi tana kallon azmee dake shigowa,yanayin yadda taga fuskar azmee ya tabbatar mata da cewar tana cikin damuwa,gefen gadon ta zauna zugudum yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,
"AUNTY AZMEE" muryar hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacinta,juyawa tayi bayanta tare da kai idanunta kan fuskar hafsat dake kawance,ƙoƙarin 6oye damuwarta tayi kafin tace"har yanzu bakiyi bacci ba?
Miƙewa hafsat tayi daga zaune,sannan tace"Bazan iyayin bacci ba aunty azmee,inajin tsoron abunda zai biyo baya,nasan cewa daddy bazai ƙyaleni ba,"ta ƙarasa maganar tana faman matse kwallon dake gangarowa akan fuskarta,
"Kidaina sa damuwa aranki hafsat,a yadda kika bani labarin irin ruƙon da kuka yi masu jahad,da farko atare kuka azabtar da rayuwarsu ke da mahaifiyarki amma kuma daga baya kin nuna masu soyayya,ina mai tabbatar maki da cewar wannan soyayyar da kika nuna masu daga baya itace zata cece ki a hannun mahaifinki...."
"Taya kike tunanin hakan zai zame mun mafita aunty azmee?bayan ni ce dakaina,na ɗauki su jahad acikin mota ta,na fitar dasu daga cikin gidan,na damƙa su a hannun wannan mugun mutumin wanda mommy tasa ya zubar mata dasu a daji!"tana magana hawaye na zuba a fuskarta,
"Amma Ae kin sanar dani cewar,Mommynki yaudararki tayi akan cewar gidan marayu zaki kai su ashe zubar dasu take so ayi,"
"Hakane aunty azmee,amma ae su hosana basu son da haka ba!nasan cewa sun tsaneni yanzu,kallon mayaudariya suke yi mun,kuma ba kowa ne ya jawo mun haka ba,fa ce Mommy,"
Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da wani sabon kukan,
"Ga shawara"! Cikin shessheƙar kuka Hafsat tace"Ina...sauraronki,koma wata irin shawarace inaso,"
"Gobe da safe tun kafin Abbanki ko Omar suyi yunƙurin tunkarar Su jahad akan maganar,ke ki fara yin hanzarin zuwa wurinsu ki nemi yafiyarsu sannan kiyi masu bayanin cewar bada saninki ba,wannan mutumin ya ɗauke su ya kaisu daji don ya zubar dasu ba,Mommynki ce ta yaudareki akan cewar gidan marayu zai kai su....."
"Aunty azmee kina ganin in na faɗa masu hakan zasu yarda dani?hosana fa tana da ta6in hankali,daƙyar zata fahimce ni,"
.."kada ki damu,zasu fahimce ki,ki kwantar da hankalinki kawai,kamar kina acikin jirgi mai ya qare,"murmushi hafsat ta ɗan saki,har taji sanyi aranta,fatan ta Allah yasa gobe in taje wurin su Jahad,su fahimce ta,
Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu kafin daga bisani,azmee tabar ɗakin hafsat kuwa bargo taja ta lullu6e kanta,sannu a hankali bacci ya ɗauke ta,
Acan falo kuwa bayan komi ya lafa,Ammi tace"Yakamata kowa yaje yayi sallah,ya kwanta ya huta,"amsa mata suka yi da toh,sannan kowannansu ya miƙe tare da nufar Bedrooms ɗinsu,atare Su jahad suka miƙe,saida suka fara yi ma su ammi sallama,ta amsa masu fuskarta asake tare da tunasar dasu akan in zasu kwanta kar su manta suyi addu'a,a ƙarshe dae falon ya rage babu kowa cikinsa,irfan shiya jagoranci Modibbo har zuwa ɗakin da zai zauna kafin gobe,Bayan ya kaishi ɗakin,Azmee ta shirya mashi kayan tea takai masa,kamar yadda ya buƙata,
*Boss Bature*
🤍❤🤍
A 6angarensu sehrish kuwa,bayan sun koma bedroom ɗinsu,alwala kowannansu yayi sannan su kayi salla atare,bayan sun kammala suka haye saman gadonsu,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauki Jahad da Hosana,banda sehrish wadda bacci ya ƙaurace ma idanunta,tabbas ɗazu ta tsorata sosai da Ammi ta koresu,abun ya razanar da ita,ta kuma ji matuƙar tausayin Daddynsu,duk in tazo rufe ido,fuskarshi take gani a lokacin daya fashe da kuka yana faɗin cewa sai dai ta tsine mashi amma sai yabi ƴa'ƴan shi,bazai bari rayuwarsu ta wulaƙanta ba,tabbas ba ƙaramin so yake yi masu ba,yana tsananin ƙaunarsu fiye da tunaninsu,lokaci guda abunda ya faru a babban falo ya shiga dawo mata acikin kanta,mikewa tayi daga zaune,ta jingina bayanta a headboard din gadon,yayin da hannayenta ke rungume da pillow,a hankali tashiga tariyo abunda ammi tayi,na bijirema umarnin iyayenta,wanda hakan yasa ita ma ƴa'ƴanta suke bijire mata,Wannan abun ba ƙaramin tsoratar da sehrish yayi ba,saboda tunawa da Umarnin da mahaifinta ya bata na hana ta zuwa sashen sgr da sunan yi mashi aiki,amma taƙi bin umarninsa,hakanan ta dinga jin gabanta na faduwa,runtse idanunta tayi tare da buɗesu a hankali,wasu siraran hawaye ne suka shiga gangaro mata a fuskarta,a hankali la66anta suka soma motsi,ƙasa ƙasa take magana,matsar da kunne na nayi don inji me take cewa,
_Ya Allah ka yafemun!bani da hankali nayi kuskure,saboda kawai son wanda baisan inayi ba,saboda na faranta ma wanda nakeso,naƙi bin umarnin mahaifina,wlh bazan ƙara ba,inajin tsoron nima ƴa'ƴan da zan haifa suƙi bin umarni na,bana fatan hakan ya faru,zan daure nayi mashi biyayya_
Tafin hannunta tasa ta goge hawayen dake zuba a idanunta,bakomai idanunta ke hango mata ba,fa ce kyakkyawar fuskar SGR,tabbas yau yayi masu abunda ba zasu ta6a mantawa ba arayuwarsu,yana da matuƙar kirki sosai,bakowa ne zai gane hakan ba farat ɗaya,shi na musamman ne,samun mutun mai irin kyakkyawar zuciyarshi a wannan zamanin da muke ciki,zaiyi matuƙar wuya,
Zuro ƙafafunta tayi ƙasa daga saman gadon,ta miƙe tsaye,jikinta na sanye da riga da wando na bacci,milk colour,takawa tayi izuwa gaban door ɗin dakin,ta buɗe bayan ta fita ta janyo masu ƙopar ta rufe,
A hankali take tafiya,ga wani irin sanyi dake ɗan ratsa sassan jikinta,amma sam bata jin sanyin,saboda daɗinshi take ji,zura hannayenta tayi acikin aljihun wandon jikinta,kai tsaye ta wuce main palour din,wayaam taga babu kowa kamar yadda tayi tsammani,da alama ma mutanen gidan duk sunyi bacci,hakanan taji tana marmarin tasha Cornflakes acikin wannan daren,juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen,within minutes ta fito hannunta ɗauke da Cup,ta cika shi da cornflakes haɗi na musamman tayi mashi,ta zuba uwar madara da bornvita duka ta sanya,ta kuma Tsula sugar,'
Dawowa tayi falon,ta zauna saman sofa tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,nace sannu ƴar masu gidan,
Motsa cornflakes ɗin ta shiga yi,da cokalin hannunta sae faman jujjuyashi takeyi aciki,kafin daga bisani ta shiga ɗebowa tana kaiwa abakinta tana sha,tana taunarsa kunnuwanta na motsi saboda daɗin da yayi,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba fa ce junaid,abokin shiriritarta,murmushi tayi tare da cewa ɗan uwana rabin raina nasan yanzu haka yana can yana sharar baccinshi,da ace idonshi biyu da atare zamu sha wannan cornflakes din,i really missed u junaid,rashin kwanciyar hankali yasa,mun nisanta da juna,amma insha Allah tunda komai ya dai²ta,yanzu bamu da sauran wata damuwa,zamu dinga fita yawan shaƙatawa atare mu dukkan mu,
Ita kaɗae abunta sai faman sambatu takeyi,kamar wata zautacciya,tana cikin shan cornflakes ɗinnan,ta wutsiyar idonta ta hango mutun a tsaye ƙiƙam,aikuwa hankalinta yayi mugun tashi,kasa juyawa tayi saboda tsoron kar ace dodo ne,tuni jikinta ya fara kerma,dama gata da shegen tsoro,zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunaninta wanene mutumin data hango tsaye a upstairs,tsabar tsoro ya hana ta juyawa ta kalleshi da kyau,wani irin wahalallan yawu ta haɗiye,ajiye cup ɗin dake hannunta tayi,sannan ta lalla6e tare da saukowa daga saman sofa ɗin,ta durƙushe ƙasa tayi sujjada,kamar maiyin sallah,duk don saboda kar dodon ya ganta,a hankali ta shiga rarrafawa a ƙoƙarinta na tabar falon,ta koma ɗakinsu,
Shikuwa mutumin dake tsaye goye da hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuba ma sarautar Allah ido yayi,abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,tsoran yarinyar harya so yayi yawa,ko kallon inda ya ke bata yi ba,ta wutsiyar ido kawai taga inuwarsa amma ta sama ranta cewar wani mugun abunne,sam baiso ta tsorata ba,don bada niyar wannan yazo wurin ba,
Wani abune ya faɗo mashi aransa,cikin sauri ya koma cikin part ɗinsa,jimmm kaɗan sai gashi ya dawo hannunshi ɗauke da wayarsa,tsayawa yayi tare da saita wurin da take yana ɗaukarta video kasancewar akwai haske sosai a main falo din,
Ba ƙaramar wahala sehrish tasha ba,da wannan rarrafen ta ƙarasa har wurin da zata shiga corridor ɗin ɗakinsu,gaba ɗaya zufa ta wanke mata fuskarta,tana ƙokarin shiga,wani abu ya faɗo mata aranta,tsayawa tayi tana tunanin kodai ta juya taga wanene shi tunda dae ta iso wurin da zata shiga ɗakinsu,koma menene ai bai isa ya cutar da ita ba,da zarar ta juya taga dodo ne,sae ta watsa da gudu ta shige ɗakinsu,taja ƙopa ta rufe,fakat,
Jikinta na kerma,amma ahaka ta daure ta ɗan juyo da kanta,takai idanunta saman upstairs din,ae batasan lokacin da taƙarasa juyowa gaba ɗaya ba,ta baza idanunta donta tabbatarma kanta abunda take gani,ƙura ido tayi tana son gano wanene saboda yayi mata nisa,wannan hasken fatar nashi ne ya fara sa ta tunanin kamar sgr ne,ƙara zuba ido tayi anan ta hango wannan doguwar sunar kan tashi,tabbas kuwa shine,ajiyar zuciya ta shiga saukewa a fili tace"Ashe babban yaya ne,nasha wahalar banxa,Allah yasa dai ban zubar da cornflakes ɗina ba,
ganin tana kallonshi,yasa ya janye phone dinsa,ya kashe camera ɗin ya tura wayar a short pocket dinsa,da hannu yayi mata Alamar taxo,
Waro ido tayi tare da nuna kanta,don ta tabbatar in ita yake kira,nuna ta ya kuma yi da hannunshi,
Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba rasss,tsoranta kar ya tuhumeta akan meya hanata zuwa part ɗinsa kai mashi Cofee don yau bata je ba,
Miƙewa tayi kamar wata mara gaskiya,haka ta tunkaresa,kamar an zare mata lakar jikinta,a hankali take tattaka matattakalar stairs ɗin,harta ƙarasa ɗan nesa dashi tukunna ta tsaya,tunda ta saci kallonshi sau ɗaya,tayi arba da faffaɗan ƙirjin nan nashi,gashi babu shirt ajikinsa,Shorts ne kawai black colour ya sanya,kuma ma dai ba ƙaramin kyau yayi masa ba,
Ganin ta tsoge wuri guda,yasa shi moving ya ƙarasa inda take dab da ita,don har saida ta ɗan ja da baya,saboda ƙure matan da yayi,
Lokaci guda tarasa natsuwarta,sai ƴan kame kame take,a ƙarshe ma ta zura hannunta acikin sumar kanta,tana ɗan sosawa,ƙamshin turaren jikinshi ba ƙaramin illa yake yi mata ba,saboda wani yanayin da take tsintar kanta aciki,
gaba ɗaya idanunshi na akan lips ɗinta,mutsu mutsun da takeyi da bakinta,ba ƙaramin tafiya yake yi dashi ba,
Almost 5 mins suna a haka sannan ya buɗe baki da wannan Sexy voice ɗin tasa yace"Meyasa baki yi bacci ba"?
Muryarta na kerma tace"bana jin bacci ne,"
"Okey,that's y You came out to disturb those who are sleeping"?
sunnar dakai ƙasa tayi tana girgiza mashi kai,alamar a'a,ganin ta dage sai faman sosa gashin kanta takeyi,yasa shi kai hannunsa ya damƙo wrist ɗin hannunta da ta zura acikin sumar kanta yace"ƙaiƙayi kike ji ne"?
A ruɗe tace"eh,"
Jinjina kanshi yayi tare da sakin hannun nata,
.."lemme help u.......'ɗagowa tayi a razane jin abunda yace,ko amsarta bai tsaya ji ba,ya sanya hannunshi tare da zagayo dashi ta gefen waist ɗinta ya tallabota sosai, ya janyota gaba ɗaya ta faɗa asaman wide chest ɗinsa,nan fa hankalinta yabi ya tashi,ta susuce ta zauce ta rasa uwar ubanta,a hankali ya ɗago da right hand dinsa,ya tsoma shi acikin lallausar sumar kanta,wani irin massage ya shiga yi mata,wanda ya haifar mata da wata irin matsananciyar kasala ajikinta,ita kanta batasan lokacin da ta zagaye waist ɗinshi ba da hannayenta duka,ta ƙankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinshi,yana jin yadda numfashinta ke fita da zafi zafi,tausasan la66anta sai gogar masa fatarsa suke,sosai sehrish ke shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinshi,tana jin kanta a wata irin duniya,wadda ba kalar tamu ba,just like in the dream haka take kallon lamarin,ta rasa gane wai shin SGR sosa mata kanta yake yi ko kuwa,saboda daɗin dake ratsa jikinta yafi ƙarfin a kirashi da daɗin susa kawai,tamkar zata zauce haka take ji,ga wani irin abu dake yi mata yawo a jikinta tamkar zufa,'
Duƙar da kansa ya ɗanyi tare da kai hancinsa ya cusa sa shi acikin sumar kanta,ƙamshin man da take shafama kanta ne ya daki hancinsa sosai ya shaƙe sa,lumshe idanunsa yayi tare da ɗan ware su a hankali ya buɗe su,kafin ya mayar da la66ansa asaman fatar kunnanta,tamkar mai yin whispering haka ya shiga yi mata magana"tell me What did you do in the kitchen when you entered"? Yayi maganar tare da raba jikinshi daga nata,idanunshi tamkar na mai jin bacci,
"Cornflakes na haɗa,saboda in sha,"ta bashi amsa a yayin da idanunta ke kallon yatsun hannunta data haɗesu wuri guda tana wasa dasu,.
"Okey,ɗaukomin cornflakes ɗin,inaso nasha nima,"
Batare da musu ba,ta juyawa da sauri da sauri ta sauka downstairs,a nan saman table,ta ɗauko cup ɗin da ta ajiye,sannan ta dawowa upstairs ɗin ta kawo mashi,miƙa mashi tayi,ya sanya hannu tare da kar6ar kofin,spoon ɗin ya ɗauka tare da ɗan jujjuya shi,kafin ya ciko cokalin yana ƙokarin kaiwa bakinsa yaji tace"Kamar yayi yawa,'ɗan ɗagowa yayi da idanunshi ya kalli fuskarta da sauri ta kawar da nata idanun gefe,saboda taga ya ɗebo da yawa ne kuma mouth ɗinsa is too small shiyasa tayi mashi magana,a ganinta cokalin bazai iya wuce wa ba,ta cikin bakinsa,amma sai gashi ya shanye abunsa,bayan ya tauna cornflakes din,ya ɗan dakata tare da cewa"Bana shan sugar sosai,sannan milk ɗin ma tayi yawa acikinsa,meyasa kika sanya da yawa har haka"?
. shiru tayi tana faman wurga ido,
Miƙa mata cup ɗin yayi tare da cewa"Kar6i kayan ki"hannu tasa ta kar6a,sannan tace"Zan iya tafiya,"?
Hanya ya nuna mata tare da cewa"na ruƙe ki ne"?
Ajiyar zuciya ta sauke,kafin ta juya da sauri da sauri ta sauka donwstairs,duk yana binta da kallo,kitchen ta shiga a tsaye ta ƙarasa shanye cornflakes din ta ajiye cup ɗin,sannan ta fito tare da kai idanunta Upstairs taga in yana nan,a tsaye ta same shi,idanunshi a lumshe,
Juyawa tayi ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinsu,adai² corridor din ta kuma tsayawa tare da ɗan waiwayawa don taga in yana nan koya tafi,Again ta ƙara ganinshi a tsaye kuma da alama ita yake kallo,ranta ne ya bata cewar kodai tayi masa bye bye da hannunta,may be ya mayar mata da martani,
ɗaga hannunta tayi tare dayi mashi bye bye,abun mamaki sai gashi ya ɗaga mata hannu yana yi mata bye bye din shima,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,har batasan lokacin da ta fashe da dariya ba,da gudu ta juya tare da faɗawa bedroom dinsu,
Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya koma cikin part dinsa,bayan ya shiga bedroom ɗinsa,toilet ya fara shiga,bada jimawa ba,ya fito tare da hayewa saman shimfiɗeɗen gadonshi ya kwanta,tare da janyo pillow ya rungume shi asaman wide chest dinsa,yayin da blue eyes ɗinsa ke kallon haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakinsa,ya rasa gane meke damun shi,amma tabbas yana jin missing ɗin wani abu sosai atattare dashi,yana tsananin buƙatar wani abu,wanda baisan menene shi ba~~~~~~~
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk mai son karanta littafin Abban sojoji,kai tsaye ya tuntu6eni ta numbar wayata 08103884440_
Special thanks to hafsat Usman Abubakar🥰,
"Koda ace baka samu zuwa ba,xamu zo nan damaturun,dama mu ya dace ace mun je can gaba ɗayan mu bayan komai ya lafa,ko don saboda ƴan ukun abusufyan,zamu je dasu don suma suga danginsu dake acan da kuma na zariyya,dana sauran state,"acewar ammi,
Modibbo yace"hakan ma yayi,Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku,"suka haɗa baki wurin amsa mashi da ameeeen,
Duk wannan abun dake faruwa Aunty babba da hayaam suna acikin ɗaki,kowannansu ya dafi waya sai danna yake yi,gaba ɗaya tunaninsu ya tafi akan cewa An kori su sehrish,hakan yasa hankalinsu ya kwanta luf,
miƙewa zaune aunty babba tayi daga kishingiɗen da take,fuskar nan a washe tace"Oh ni ƴasu,ko ina waɗannan ƴan ukun suka dosa yanzu?
Hayaam tace"Wama ya sanin masu,suna can suna gagari acikin gari,ƙarshenta ma a samu wata babbar mota zubin ɗan gotte tayi mana awon gaba da kawunansu,"
Fashewa su kayi da dariya,sai da suka tsagaita dayin dariyar Aunty babba tace"duba mun ƙarfe nawa yanzu,agogon wayata ba saiti,"
"kusan Ƙarfe tara fa yanzu,gashi ko abincin dare ma ba mu nema ba,"
Tsoki taja"mtsww,wannan wani irin gidane!A tunani na Azmee ya kamata ace ta kawo mana dinner ɗin mu har cikin ɗaki,ni bansan menene amfanin matar nan ba a cikin gidan nan,bata wani aiki,sae dae ta dafa masu abinci,ta zauna taci ta ƙoshi ta tara tumbi,ta mayar da gidan kamar na ubanta,"
Hayaam ta ɗaura da cewa"Ae kwanaki har magana taso ta gayamun,saboda waccen korarriyar yarinyar,Sehrish take da suna ko wa ma......."dakatawa tayi da yin maganar sakamakon turo ƙopar da taji anyi,atare suka kai idanunsu wurin,
Azmee ce ta shigo hannunta ɗauke da tray,koda su kayi arba da ita,nan fa suka shiga yin ƴan kame kame na rashin gaskiya,
Basu amsa mata sallamar da tayi masu ba,ƙarasawa tayi ta ajiye masu tray ɗin a ƙasa,sannan tace"abinci ne na kawo maku,bansan ko kuna buƙata ba,naga baku fito kun nema ba,shine nace bari na kawo maku a ɗaki,"
Washe baki suka shiga yi,hankalinsu harya kwanta,da alama bataji gossiping ɗinta da sukeyi ba,
"Mun gode sosae Azmee,wlh kina ƙoƙari sosai acikin gidan nan,ke kaɗae kike duk wasu aikace aikace na gidan nan,shekara da shekaru,baki ta6a gajiyawa ba,kin mayar da dangin nan tamkar naki,bansan meyasa har yanzu kike tare dasu ba,wahalar tayi yawa,yaci ace yanzu kin nemi miji kinyi aure,amma in kika cigaba da zama a haka,rayuwarki zata ƙare ne a matsayin baiwa kuma bazawara,ba wani cigaba,"
Tunda Aunty babba tafara magana azmee ta zuba mata ido tana kallonta,batare da ta ƙyafta idanunta ba,har sai da Aunty babba takai ƙarshen maganar,sannan tace"Bani da amsar da zan baki Laila,amma inaso ki sani dangin nan basu ɗaukeni kamar yadda kikayi tsammani ba,kuma ni bana gajiya da aiki a ƙarƙashinsu,saboda sunyi mun halarcin da bazan ta6a mantawa ba,"
Juyawa azmee tayi da sauri ta kama hanyar fita daga ɗakin,harta ruƙe handle ɗin ƙopar zata buɗe muryar aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"har yaushe ne zaki cigaba da danne abunda ke zuciyarki?
"Mekenan"!azmee ta tambaya a yayin da ta juyo da kanta tana kallonta,
"Azmee nafa son komai!na son cewa akwai wanda kikeso acikin gidan nan!saboda kin ta6a sanar dani a lokacin baya,ko kin manta"?
Baza kunne hayaam tayi tana sauraronsu,
"Hakane,na ta6a sanar dake,amma yanzu babu wannan a zuciyata,kuma ko a lokacin dana so shi,saboda irin kyautatawar da yake yi mun ne,kuma da tausayin shi da nakeji,na rashin matarshi a kusa dashi,Amma yanzu Alhamdulillah,uwar ƴa'yanshi tana a kusa dashi,babu wata sauran damuwa,
Murmushi aunty babba ta saki tare da miƙewa daga zaunen da take a gefen gadon,ta tunkari azmee tana cewa"Yanzu ke sai ki haƙura dashi?baki kwaɗayin ki aure shi,ki samu ƙaruwa dashi,ko don ki samu gado acikin gidan nan"? Da alama Aunty babba so take ta tunzura azmee,
Girgiza kai azmee tayi"ni bani da buri akan tara dukiya,bana kwaɗayin abun duniya,saboda sanin cewa komai na tara ƙarshe a gidan duniyar nan zan barshi!albashin da nake samu acikin gidan nan ya isheni in ƙarashe rayuwata dashi,"
Ta6e baki aunty babba tayi,fuskar nan ɗauke da shu'umin murmushin nan tace"Yanzu shikenan kin za6i ki ƙarashe rayuwarki a ƙarkashin wasu kenan?ke baki da ƴancin kanki?wlh azmee bakisan ciwon kanki ba,ban ta6a ganin ƴar wahala irin ki ba,kin ƙuntata rayuwarki,kin ƙasƙantar da kanki,duk don saboda ki faranta ma wasu!har yau babu wani cigaba a arayuwarki,yakamata ace yanxu kin mallaki katafaren gida naki na kanki,kin kuma mallaki mota,kinje hajji da umrah,kin kuma je yawon shaƙatawa dubai da sauran ƙasashe,haba azmee yakamata kiyima kanki adalci,wlh kina cutar kanki,Nidai shawara nake ba......"
Tsawar da azmee ta daka mata ne yasa ta kasa ƙarasa maganar,ba ƙaramin razana tayi da tsawar ba,tamkar ba abakin azmee ta fito ba,
"Ke baki isa ki tunzurani ba,laila!ki iya bakin ki,in ba so kike kija ma kanki ba,ki tsaya a iya matsayinki,nima in tsaya a nawa,idan ki kayi kuskuren shiga gonata wlh ranki zaiyi mugun 6aci," tana ƙarasa maganar,ta janyo ƙopar da sauri ta fuce,
"Hmmmm Aunty laila,matar nan fa ba zaki ta6a iya canza mata ra'ayi ba,don na lura itama kaifi ɗaya ce,"
Jinjina kai aunty babba tayi aranta tana mai mamakin irin yadda azmee ta daka mata tsawa,sai kace batasan matsayinta agidan Ba,!
Komawa tayi cikin ɗakin ta zauna dirshan a gefen gadon,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,taso ace taci nasara akan azmee ko don su sami haɗin kanta wurin Cimma burinsu,guntun tsoki taja tare da cewa"Ƴar wahala,sai kace tafi kowa tsoron Allah,kullum haka zaki ganta da cazbi a hannunta tana yawo,"
Ta ƙarasa maganar tare da mayar da idonta kan tray ɗin abincin da azmeen ta kawo masu,yatsina fuska tayi tare da kai hannu ta buɗe warmer ɗin,dambun shinkafa ne yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,a plate ta zuba masu nan suka zauna,suna ci ita da hayaam kamar wanda yunwa ta koro,
Azmee kuwa bayan fitarta daga ɗakin nasu,jiki a sanyaye ta wuce ɗakinta,kalaman aunty babba ba ƙaramin 6ata mata rai su kayi ba,zuciyarta ta sosu sosai,daure wa kawai takeyi,da ace bata kai zuciyarta nesa ba da ba abunda zai hana ta wanke fuskar laila da mari!
Sam ta manta da hafsat dake kwance a ɗakinta,baiwar Allah tun bayan fitarta daga ɗakin hayaam,ta wuce ɗakin azmee batare da sanin kowa ba azmee ce kaɗae tasan cewa tana a ɗakinta,anan tayi wanka,ta kuma ci abinci ta kwanta,saboda wani irin zazza6i daya saukar mata ajikinta,kwata kwata zuciyarta ba daɗi,tayi danasanin rayuwarta fiye da a ƙirga,idanunta na tsananin son ganin Su Jahad,amma tsoran tunkararsu takeyi,gashi har tsaraba tayi masu don ta basu hmmm,duk in ta tuna irin uƙubar da suka sha a hannunsu,sae ta fashe da matsanancin kuka,tun azmee na rarrashinta har ta gaji ta ƙyaleta,idanunta sun kumbura suntum haka la66anta ma,bakomai take yi ma fargaba ba,fa ce irin hukuncin da Mahaifinta zai yanke mata,don kuwa tasan muddin yaji abunda suka aikata masu jahad,Wlh ba zasu sha ba,su dukan su sae sun fuskanci mummunan hukunci a wurinsa,gaba ɗaya tayi nisa cikin zurfin tunani,taji shigowar azmee cikin ɗakin,buɗe idanunta tayi tana kallon azmee dake shigowa,yanayin yadda taga fuskar azmee ya tabbatar mata da cewar tana cikin damuwa,gefen gadon ta zauna zugudum yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,
"AUNTY AZMEE" muryar hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacinta,juyawa tayi bayanta tare da kai idanunta kan fuskar hafsat dake kawance,ƙoƙarin 6oye damuwarta tayi kafin tace"har yanzu bakiyi bacci ba?
Miƙewa hafsat tayi daga zaune,sannan tace"Bazan iyayin bacci ba aunty azmee,inajin tsoron abunda zai biyo baya,nasan cewa daddy bazai ƙyaleni ba,"ta ƙarasa maganar tana faman matse kwallon dake gangarowa akan fuskarta,
"Kidaina sa damuwa aranki hafsat,a yadda kika bani labarin irin ruƙon da kuka yi masu jahad,da farko atare kuka azabtar da rayuwarsu ke da mahaifiyarki amma kuma daga baya kin nuna masu soyayya,ina mai tabbatar maki da cewar wannan soyayyar da kika nuna masu daga baya itace zata cece ki a hannun mahaifinki...."
"Taya kike tunanin hakan zai zame mun mafita aunty azmee?bayan ni ce dakaina,na ɗauki su jahad acikin mota ta,na fitar dasu daga cikin gidan,na damƙa su a hannun wannan mugun mutumin wanda mommy tasa ya zubar mata dasu a daji!"tana magana hawaye na zuba a fuskarta,
"Amma Ae kin sanar dani cewar,Mommynki yaudararki tayi akan cewar gidan marayu zaki kai su ashe zubar dasu take so ayi,"
"Hakane aunty azmee,amma ae su hosana basu son da haka ba!nasan cewa sun tsaneni yanzu,kallon mayaudariya suke yi mun,kuma ba kowa ne ya jawo mun haka ba,fa ce Mommy,"
Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da wani sabon kukan,
"Ga shawara"! Cikin shessheƙar kuka Hafsat tace"Ina...sauraronki,koma wata irin shawarace inaso,"
"Gobe da safe tun kafin Abbanki ko Omar suyi yunƙurin tunkarar Su jahad akan maganar,ke ki fara yin hanzarin zuwa wurinsu ki nemi yafiyarsu sannan kiyi masu bayanin cewar bada saninki ba,wannan mutumin ya ɗauke su ya kaisu daji don ya zubar dasu ba,Mommynki ce ta yaudareki akan cewar gidan marayu zai kai su....."
"Aunty azmee kina ganin in na faɗa masu hakan zasu yarda dani?hosana fa tana da ta6in hankali,daƙyar zata fahimce ni,"
.."kada ki damu,zasu fahimce ki,ki kwantar da hankalinki kawai,kamar kina acikin jirgi mai ya qare,"murmushi hafsat ta ɗan saki,har taji sanyi aranta,fatan ta Allah yasa gobe in taje wurin su Jahad,su fahimce ta,
Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu kafin daga bisani,azmee tabar ɗakin hafsat kuwa bargo taja ta lullu6e kanta,sannu a hankali bacci ya ɗauke ta,
Acan falo kuwa bayan komi ya lafa,Ammi tace"Yakamata kowa yaje yayi sallah,ya kwanta ya huta,"amsa mata suka yi da toh,sannan kowannansu ya miƙe tare da nufar Bedrooms ɗinsu,atare Su jahad suka miƙe,saida suka fara yi ma su ammi sallama,ta amsa masu fuskarta asake tare da tunasar dasu akan in zasu kwanta kar su manta suyi addu'a,a ƙarshe dae falon ya rage babu kowa cikinsa,irfan shiya jagoranci Modibbo har zuwa ɗakin da zai zauna kafin gobe,Bayan ya kaishi ɗakin,Azmee ta shirya mashi kayan tea takai masa,kamar yadda ya buƙata,
*Boss Bature*
🤍❤🤍
A 6angarensu sehrish kuwa,bayan sun koma bedroom ɗinsu,alwala kowannansu yayi sannan su kayi salla atare,bayan sun kammala suka haye saman gadonsu,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauki Jahad da Hosana,banda sehrish wadda bacci ya ƙaurace ma idanunta,tabbas ɗazu ta tsorata sosai da Ammi ta koresu,abun ya razanar da ita,ta kuma ji matuƙar tausayin Daddynsu,duk in tazo rufe ido,fuskarshi take gani a lokacin daya fashe da kuka yana faɗin cewa sai dai ta tsine mashi amma sai yabi ƴa'ƴan shi,bazai bari rayuwarsu ta wulaƙanta ba,tabbas ba ƙaramin so yake yi masu ba,yana tsananin ƙaunarsu fiye da tunaninsu,lokaci guda abunda ya faru a babban falo ya shiga dawo mata acikin kanta,mikewa tayi daga zaune,ta jingina bayanta a headboard din gadon,yayin da hannayenta ke rungume da pillow,a hankali tashiga tariyo abunda ammi tayi,na bijirema umarnin iyayenta,wanda hakan yasa ita ma ƴa'ƴanta suke bijire mata,Wannan abun ba ƙaramin tsoratar da sehrish yayi ba,saboda tunawa da Umarnin da mahaifinta ya bata na hana ta zuwa sashen sgr da sunan yi mashi aiki,amma taƙi bin umarninsa,hakanan ta dinga jin gabanta na faduwa,runtse idanunta tayi tare da buɗesu a hankali,wasu siraran hawaye ne suka shiga gangaro mata a fuskarta,a hankali la66anta suka soma motsi,ƙasa ƙasa take magana,matsar da kunne na nayi don inji me take cewa,
_Ya Allah ka yafemun!bani da hankali nayi kuskure,saboda kawai son wanda baisan inayi ba,saboda na faranta ma wanda nakeso,naƙi bin umarnin mahaifina,wlh bazan ƙara ba,inajin tsoron nima ƴa'ƴan da zan haifa suƙi bin umarni na,bana fatan hakan ya faru,zan daure nayi mashi biyayya_
Tafin hannunta tasa ta goge hawayen dake zuba a idanunta,bakomai idanunta ke hango mata ba,fa ce kyakkyawar fuskar SGR,tabbas yau yayi masu abunda ba zasu ta6a mantawa ba arayuwarsu,yana da matuƙar kirki sosai,bakowa ne zai gane hakan ba farat ɗaya,shi na musamman ne,samun mutun mai irin kyakkyawar zuciyarshi a wannan zamanin da muke ciki,zaiyi matuƙar wuya,
Zuro ƙafafunta tayi ƙasa daga saman gadon,ta miƙe tsaye,jikinta na sanye da riga da wando na bacci,milk colour,takawa tayi izuwa gaban door ɗin dakin,ta buɗe bayan ta fita ta janyo masu ƙopar ta rufe,
A hankali take tafiya,ga wani irin sanyi dake ɗan ratsa sassan jikinta,amma sam bata jin sanyin,saboda daɗinshi take ji,zura hannayenta tayi acikin aljihun wandon jikinta,kai tsaye ta wuce main palour din,wayaam taga babu kowa kamar yadda tayi tsammani,da alama ma mutanen gidan duk sunyi bacci,hakanan taji tana marmarin tasha Cornflakes acikin wannan daren,juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen,within minutes ta fito hannunta ɗauke da Cup,ta cika shi da cornflakes haɗi na musamman tayi mashi,ta zuba uwar madara da bornvita duka ta sanya,ta kuma Tsula sugar,'
Dawowa tayi falon,ta zauna saman sofa tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,nace sannu ƴar masu gidan,
Motsa cornflakes ɗin ta shiga yi,da cokalin hannunta sae faman jujjuyashi takeyi aciki,kafin daga bisani ta shiga ɗebowa tana kaiwa abakinta tana sha,tana taunarsa kunnuwanta na motsi saboda daɗin da yayi,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba fa ce junaid,abokin shiriritarta,murmushi tayi tare da cewa ɗan uwana rabin raina nasan yanzu haka yana can yana sharar baccinshi,da ace idonshi biyu da atare zamu sha wannan cornflakes din,i really missed u junaid,rashin kwanciyar hankali yasa,mun nisanta da juna,amma insha Allah tunda komai ya dai²ta,yanzu bamu da sauran wata damuwa,zamu dinga fita yawan shaƙatawa atare mu dukkan mu,
Ita kaɗae abunta sai faman sambatu takeyi,kamar wata zautacciya,tana cikin shan cornflakes ɗinnan,ta wutsiyar idonta ta hango mutun a tsaye ƙiƙam,aikuwa hankalinta yayi mugun tashi,kasa juyawa tayi saboda tsoron kar ace dodo ne,tuni jikinta ya fara kerma,dama gata da shegen tsoro,zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunaninta wanene mutumin data hango tsaye a upstairs,tsabar tsoro ya hana ta juyawa ta kalleshi da kyau,wani irin wahalallan yawu ta haɗiye,ajiye cup ɗin dake hannunta tayi,sannan ta lalla6e tare da saukowa daga saman sofa ɗin,ta durƙushe ƙasa tayi sujjada,kamar maiyin sallah,duk don saboda kar dodon ya ganta,a hankali ta shiga rarrafawa a ƙoƙarinta na tabar falon,ta koma ɗakinsu,
Shikuwa mutumin dake tsaye goye da hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuba ma sarautar Allah ido yayi,abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,tsoran yarinyar harya so yayi yawa,ko kallon inda ya ke bata yi ba,ta wutsiyar ido kawai taga inuwarsa amma ta sama ranta cewar wani mugun abunne,sam baiso ta tsorata ba,don bada niyar wannan yazo wurin ba,
Wani abune ya faɗo mashi aransa,cikin sauri ya koma cikin part ɗinsa,jimmm kaɗan sai gashi ya dawo hannunshi ɗauke da wayarsa,tsayawa yayi tare da saita wurin da take yana ɗaukarta video kasancewar akwai haske sosai a main falo din,
Ba ƙaramar wahala sehrish tasha ba,da wannan rarrafen ta ƙarasa har wurin da zata shiga corridor ɗin ɗakinsu,gaba ɗaya zufa ta wanke mata fuskarta,tana ƙokarin shiga,wani abu ya faɗo mata aranta,tsayawa tayi tana tunanin kodai ta juya taga wanene shi tunda dae ta iso wurin da zata shiga ɗakinsu,koma menene ai bai isa ya cutar da ita ba,da zarar ta juya taga dodo ne,sae ta watsa da gudu ta shige ɗakinsu,taja ƙopa ta rufe,fakat,
Jikinta na kerma,amma ahaka ta daure ta ɗan juyo da kanta,takai idanunta saman upstairs din,ae batasan lokacin da taƙarasa juyowa gaba ɗaya ba,ta baza idanunta donta tabbatarma kanta abunda take gani,ƙura ido tayi tana son gano wanene saboda yayi mata nisa,wannan hasken fatar nashi ne ya fara sa ta tunanin kamar sgr ne,ƙara zuba ido tayi anan ta hango wannan doguwar sunar kan tashi,tabbas kuwa shine,ajiyar zuciya ta shiga saukewa a fili tace"Ashe babban yaya ne,nasha wahalar banxa,Allah yasa dai ban zubar da cornflakes ɗina ba,
ganin tana kallonshi,yasa ya janye phone dinsa,ya kashe camera ɗin ya tura wayar a short pocket dinsa,da hannu yayi mata Alamar taxo,
Waro ido tayi tare da nuna kanta,don ta tabbatar in ita yake kira,nuna ta ya kuma yi da hannunshi,
Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba rasss,tsoranta kar ya tuhumeta akan meya hanata zuwa part ɗinsa kai mashi Cofee don yau bata je ba,
Miƙewa tayi kamar wata mara gaskiya,haka ta tunkaresa,kamar an zare mata lakar jikinta,a hankali take tattaka matattakalar stairs ɗin,harta ƙarasa ɗan nesa dashi tukunna ta tsaya,tunda ta saci kallonshi sau ɗaya,tayi arba da faffaɗan ƙirjin nan nashi,gashi babu shirt ajikinsa,Shorts ne kawai black colour ya sanya,kuma ma dai ba ƙaramin kyau yayi masa ba,
Ganin ta tsoge wuri guda,yasa shi moving ya ƙarasa inda take dab da ita,don har saida ta ɗan ja da baya,saboda ƙure matan da yayi,
Lokaci guda tarasa natsuwarta,sai ƴan kame kame take,a ƙarshe ma ta zura hannunta acikin sumar kanta,tana ɗan sosawa,ƙamshin turaren jikinshi ba ƙaramin illa yake yi mata ba,saboda wani yanayin da take tsintar kanta aciki,
gaba ɗaya idanunshi na akan lips ɗinta,mutsu mutsun da takeyi da bakinta,ba ƙaramin tafiya yake yi dashi ba,
Almost 5 mins suna a haka sannan ya buɗe baki da wannan Sexy voice ɗin tasa yace"Meyasa baki yi bacci ba"?
Muryarta na kerma tace"bana jin bacci ne,"
"Okey,that's y You came out to disturb those who are sleeping"?
sunnar dakai ƙasa tayi tana girgiza mashi kai,alamar a'a,ganin ta dage sai faman sosa gashin kanta takeyi,yasa shi kai hannunsa ya damƙo wrist ɗin hannunta da ta zura acikin sumar kanta yace"ƙaiƙayi kike ji ne"?
A ruɗe tace"eh,"
Jinjina kanshi yayi tare da sakin hannun nata,
.."lemme help u.......'ɗagowa tayi a razane jin abunda yace,ko amsarta bai tsaya ji ba,ya sanya hannunshi tare da zagayo dashi ta gefen waist ɗinta ya tallabota sosai, ya janyota gaba ɗaya ta faɗa asaman wide chest ɗinsa,nan fa hankalinta yabi ya tashi,ta susuce ta zauce ta rasa uwar ubanta,a hankali ya ɗago da right hand dinsa,ya tsoma shi acikin lallausar sumar kanta,wani irin massage ya shiga yi mata,wanda ya haifar mata da wata irin matsananciyar kasala ajikinta,ita kanta batasan lokacin da ta zagaye waist ɗinshi ba da hannayenta duka,ta ƙankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinshi,yana jin yadda numfashinta ke fita da zafi zafi,tausasan la66anta sai gogar masa fatarsa suke,sosai sehrish ke shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinshi,tana jin kanta a wata irin duniya,wadda ba kalar tamu ba,just like in the dream haka take kallon lamarin,ta rasa gane wai shin SGR sosa mata kanta yake yi ko kuwa,saboda daɗin dake ratsa jikinta yafi ƙarfin a kirashi da daɗin susa kawai,tamkar zata zauce haka take ji,ga wani irin abu dake yi mata yawo a jikinta tamkar zufa,'
Duƙar da kansa ya ɗanyi tare da kai hancinsa ya cusa sa shi acikin sumar kanta,ƙamshin man da take shafama kanta ne ya daki hancinsa sosai ya shaƙe sa,lumshe idanunsa yayi tare da ɗan ware su a hankali ya buɗe su,kafin ya mayar da la66ansa asaman fatar kunnanta,tamkar mai yin whispering haka ya shiga yi mata magana"tell me What did you do in the kitchen when you entered"? Yayi maganar tare da raba jikinshi daga nata,idanunshi tamkar na mai jin bacci,
"Cornflakes na haɗa,saboda in sha,"ta bashi amsa a yayin da idanunta ke kallon yatsun hannunta data haɗesu wuri guda tana wasa dasu,.
"Okey,ɗaukomin cornflakes ɗin,inaso nasha nima,"
Batare da musu ba,ta juyawa da sauri da sauri ta sauka downstairs,a nan saman table,ta ɗauko cup ɗin da ta ajiye,sannan ta dawowa upstairs ɗin ta kawo mashi,miƙa mashi tayi,ya sanya hannu tare da kar6ar kofin,spoon ɗin ya ɗauka tare da ɗan jujjuya shi,kafin ya ciko cokalin yana ƙokarin kaiwa bakinsa yaji tace"Kamar yayi yawa,'ɗan ɗagowa yayi da idanunshi ya kalli fuskarta da sauri ta kawar da nata idanun gefe,saboda taga ya ɗebo da yawa ne kuma mouth ɗinsa is too small shiyasa tayi mashi magana,a ganinta cokalin bazai iya wuce wa ba,ta cikin bakinsa,amma sai gashi ya shanye abunsa,bayan ya tauna cornflakes din,ya ɗan dakata tare da cewa"Bana shan sugar sosai,sannan milk ɗin ma tayi yawa acikinsa,meyasa kika sanya da yawa har haka"?
. shiru tayi tana faman wurga ido,
Miƙa mata cup ɗin yayi tare da cewa"Kar6i kayan ki"hannu tasa ta kar6a,sannan tace"Zan iya tafiya,"?
Hanya ya nuna mata tare da cewa"na ruƙe ki ne"?
Ajiyar zuciya ta sauke,kafin ta juya da sauri da sauri ta sauka donwstairs,duk yana binta da kallo,kitchen ta shiga a tsaye ta ƙarasa shanye cornflakes din ta ajiye cup ɗin,sannan ta fito tare da kai idanunta Upstairs taga in yana nan,a tsaye ta same shi,idanunshi a lumshe,
Juyawa tayi ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinsu,adai² corridor din ta kuma tsayawa tare da ɗan waiwayawa don taga in yana nan koya tafi,Again ta ƙara ganinshi a tsaye kuma da alama ita yake kallo,ranta ne ya bata cewar kodai tayi masa bye bye da hannunta,may be ya mayar mata da martani,
ɗaga hannunta tayi tare dayi mashi bye bye,abun mamaki sai gashi ya ɗaga mata hannu yana yi mata bye bye din shima,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,har batasan lokacin da ta fashe da dariya ba,da gudu ta juya tare da faɗawa bedroom dinsu,
Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya koma cikin part dinsa,bayan ya shiga bedroom ɗinsa,toilet ya fara shiga,bada jimawa ba,ya fito tare da hayewa saman shimfiɗeɗen gadonshi ya kwanta,tare da janyo pillow ya rungume shi asaman wide chest dinsa,yayin da blue eyes ɗinsa ke kallon haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakinsa,ya rasa gane meke damun shi,amma tabbas yana jin missing ɗin wani abu sosai atattare dashi,yana tsananin buƙatar wani abu,wanda baisan menene shi ba~~~~~~~
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Gaba ɗaya Aunty babba idonta bai hango mata su hosana ba,kutsa kai kawai takeyi cikin falon,hafsat dai tana la6e a bayanta,cike da fargaba,
Ƙarasawa sukayi wurinsu,daga bayansu Sehrish suka tsaya,hakan yasa bata samu damar ganin fuskokinsu ba,sai faman washe baki take yi,gaishe dasu Abba suka farayi,fuskar kowannansu awashe,"Ishaq shine baka sanar dani zuwansu ba,"acewar Abba,General ishaq yace"Ni kaina bansan sun karaso ba,nadaisan munyi dasu kan cewa zasu taho,"
Abusufyan yace"masha Allah hafsat ta girma sosai,ba don ina ganin hoton ta ba,da bazan iya gane ta ba,
Sunnar da kai ƙasa hafsat tayi tana murmushi ƙasa ƙasa,yayin da zuciyarta ke a cunkushe,
duk su hosana basu ɗauki muryarta ba,amma da zarar tayi magana sai sunji tamkar sun ta6a jin muryar matar dake magana,
"Muna taya ka murna Abusufyan,ƴa'ƴa har ƴan uku Allah ya albarkaci rayuwarsu,Alla ya.........'bata ƙarasa maganar ba sakamakon juyowar da sehrish tayi,Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake daram!!!dararam!!!yadda kasan ana buga ganga,Saboda tsabar kiɗima bata san lokacin da ta furta"Kutumar Uba...."gaba ɗaya hankalin kowa ya dawo kanta,jin ashar ɗin data buga,Hakan yasa Jahad da Hosana juyowa atare,Waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe,lokaci guda duk tabi ta gigice ta ruɗe ta rikice ta fita hayyacinta abunda batayi tsammani ba,la66anta har kerma sukeyi wurin nuna su da hannu tana ƙoƙarin tayi magana amma kermar da bakinta keyi ya hanata cewa komai,
Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin matar da ta azabtar da rayuwarsu,ta ƙuntata masu ta kusa halakasu,hosana kuwa a matuƙar tsorace ta faɗa bayan Marshal Omar ta ƙanƙame shi tana faɗin"Ya Omar,bansan ganinta,tsoranta nake ji,itace matar da ta azabtar da rayuwarmu,itace tasa aje a jefar damu cikin daji,har wannan tsohon mutumin ya kusa cutar dani,don Allah ya Omar ku kureta,azzaluma ce macuciya ce,bata tsoran Allah,bata da tausayi kuma bata da Imani,
Hankalin kowa dake a wurin ya dawo kansu,gaba daya Abba dasu Abusufyan da sauran mutanen dake a wurin duk sun ruɗe sun gaza gane inda zancen nata ya dosa,Ishaq kuwa tun da yaga jikin Aunty babba na kerma,zufa na keto mata,ranshi ya bashi cewar tabbas ta aikata wani abu ne,saboda yasan halinta,muguwace kuma bata da gaskiya,Bashi ba hatta Marshal jikinshi yayi mugun sanyi,musamman da yaji hosana na fadin ta cutar da rayuwarsu nan ya fara tunanin Wasu abubuwa da yake zargi a lokacin baya,da kuma maganar da major ya ta6a sanar dashi na cewar baya son ya shiga tsakaninshi da matar Yayan shi,
hannu Aunty babba ta aza akanta tana faɗin"Shikenan An yanka ta tashi,amaimakon ta mutu,nashiga ukku ni laila,Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wani tsautsayi ne da ƙaddara suka kawo ni gidan nan,'
Tunda Abbansu junaid yaji hakan yasan cewa tabbas akwai wani abu daya ta6a faruwa a tsakaninsu,koma dae menene bai kamata,su tuhumeta ba agaban ƙannen mijinta,a bainar jama'a kuma,ko ba komai Matar babban yayansu ce,
"Ya Omar dan Allah,tabar wurin nan wlh bansan ganinta,kashe mu take son yi,shiyasa ta biyo mu har nan,"gaba ɗaya kukan hosana ya cika kunnuwansu,'
Wani irin wahalallan yawu Aunty babba tazo haɗiyewa,nan take ta yanke jiki a wurin ta faɗi asume,da sauri hafsat ta tsugunna tare da tallabo ta,tana jijjjigata,
Gaba ɗaya duk sun kashe ma ishaq baki yama rasa abun cewa,tsananin baƙin ciki da takaici ya hanashi cewa uffan,jikinshi sae faman tsuma yake yi,burinshi kawai yaji abunda suka aikata ma yaran,da har suka tsorata da ganinsu,tabbas sai sunci Ubansu,muddin yaji wani da ba dai dai ba,don bazai yarda suja mashi tozarta ba a idon ƴan uwanshi,
Aunty Azmee ce ta taimaka wurin ɗebo ruwa suka yayyafa ma Aunty babba a fuskarta,ae tana farfaɗowa kamar wata zautacciya tayi zumbur ta miƙe,ko waiwayonsu ba tayi ba,ta watsa aguje,tayi cikin gidan,Allah kaɗae yasan inda ta kutsa kanta,
A fusace General ishaq zai bi bayanta,Abbansu junaid yayi saurin ruƙo hannunshi tare da cewa"kada ka bita,yakamata mubi komai a sannu,yanzu bamu kaɗai bane a wurin nan ba,akwai ƙannenka kuma akwai bare a wurin nan,"
Jinjina kanshi kawai yayi ba don ya haƙuri ba,
Batare da sanin kowa ba,hafsat ta zame jiki daga wurin,saboda wani irin mugun kallo da taga Daddynta nayi mata,bashi kaɗae ba hatta Marshal kallon tuhuma yake yi mata,hakan ne yasata ta sulale tabar wurin,sauƙinta ma basu ambaci sunanta ba,amma tasan dole sunanta ya fito aciki,kuma daddynta in ya tashi yanke hukunci hada ita zai haɗa ya yanke mawa,tabbas tayi dana sanin biye ma mahaifiyarta wurin cutar dasu hosana,gayanan sunja ma kansu,
Ruƙo hannun hosana yayi tare da janyota,ta dawo ta gabanshi,fuskarnan tayi jawur,sae faman kuka takeyi tana faɗin"ya Omar a koreta tabar gidan nan,bana son ganinta,bata da Imani,itace ta rufe mu acikin store tayi mana horon yunwa,ta dinga bugunmu da bulala,kuma ta dinga samu aiki,har gadon asibiti sai da aka kwantar dani.......'
Cikin sauri Omar ya sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki,cikin lallashi yace"its ok hosana,na fahimce ki,zansa sojoji su koreta daga gidan nan hakan yayi maki,"
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan yace"kada na sake jin kukan ki to,ya isa haka,kalli fa ki gani duk kin 6ata kwalliyarki da hawaye,"
Curo handkerchief Abusufyan yayi daga gaban aljihunsa,ya ruƙo hosana,tare da sanyashi a fuskarta yana goge mata hawayenta,"Daddy matar can bata da Imani ko kaɗan,taso ta kashe ni,dan Allah ku sakar mata karnuka su rakata bakin gate,tabar gidan nan,"
Muryar abusufyan tamkar zaiyi kuka yace"Kiyi haƙuri kinji hosanata,zansa a koreta kamar yadda kikeso,amma yanzu kiyi shiru da bakinki,ki daina magana,banason ganin hawayenki,"
"Daddy bakasan yadda nakeji bane,zuciyata tafarfasa takeyi,raɗaɗi takeyi mun kamar ana rura garwashin wuta acikinta,wlh daddy waccen matar bazata ga Manzon Allah ba,sai ta shiga wuta,'
Hankali atashe Marshal ya daka mata tsawa har saida ta dawo cikin hayyacinta,fuskarshi a daure yace"kar na sake jin kince uffan a wurin nan,surutun ya isa haka!banace za'a kore ta ba,"
Saboda tsoratar da tayi da tsawar da yayi mata ne yasa ta faɗa jikin daddyn nasu ta ƙankameshi,tana faman sauke ajiyar zuciya,'
jikin kowa yayi sanyi,musamman Ishaq,bawan Allah duk yabi ya takure kansa,idanunshi sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai,
Abba ne yayi ƙoƙari wurin dawo dasu daidai daga yanayin da suka shiga,daƙyar aka samu hosana ta zauna itama amma duk da haka tana yawan firgita wannan ya ƙara tabbatar masu da cewa ba ƙaramin Abu Aunty laila ta aikata masu ba,wuri kowa ya samu ya zauna agaban table ɗin dake a wurin wanda ke shaqe da abinci kala kala,nan fa kowa ya shiga bama cikinsa abinci,jikin Sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,saboda ta gane dalilin dayasa su jahad suka tsorata da ganin matar,wato itace matar da Omar ya kaisu gidanta,wadda ta azabtar da rayuwarsu,kamar yadda jahad ta bata labarinta,kowa ya lura da yanayin yaran,sun kasa sakewa suci abinci sosai,ƙarshe sai dae Abusufyan ya dinga binsu one by one yana sanya masu abinci abakinsu suna ci,a haka har ya samu suka ci sosai,bayan sun kammala cin abincin,Junaid ya ɗaukko Camera ɗinsa,nan fa aka shiga ɗaukar hotuna,abun gwanin burgewa,Happy family,kowa sai da ya fito Hajiya azeema,su gwaggon katsina Saude,Dr harris,hatta ƴan matan da hajiya sarah tazo dasu,sae da suka fito akayi masu hotuna,mutun uku ne kawai babu a wurin Ammi wadda kowa ke fargabar fitowarta,bayan ita sae Haroon wanda ke ƙumshe acikin ɗakinsa,Sgr kuwa baya cikin gidan,tun wuraren ƙarfe uku yabar gidan,
Anyi masu hoto tare da mahaifinsu sun sanyashi atsakiya,sae wanda akayi masu tare da Abbansu junaid tare dashi kanshi junaid ɗin,kowa saida yayi hoto tare dasu,hatta Su twins da fawan dasu irfan,kowannansu sae da yayi hoto dasu,sun sha hotuna ba ƙadan ba,
Basu suka kammala ba sae wuraren sallar magrib,sannan kowa ya shige ciki domin yin alwala,
Kamar jira jahad takeyi su shiga ɗaki ta rufe hosana da faɗa,tamkar zata bugeta,"Sai yanzu na tabbatar da cewar ke cikakkar zararriyace baki da hankali,meyasa ba zakiyi shiru da bakin ki ba?don me zaki tona mata asiri agaban mutane"?
Fashewa da kuka hosana tayi tana faɗin"kada ki ƙara cemun zararriya,kuma naje na tona mata asirin,Ni bazan ta6a yafe mata ba wlh,kamar yadda ta cutar da rayuwarmu itama sai ta fuskanci sakamakon abunda ta aikata mana,'
"Hosana,karna sake jin kin tada wannan maganar,idan ba so kike ranki ya 6aci ba,"
"Wlh saina faɗima Daddy da Abba,kuma saina faɗa ma yaya Omar,sai dai duk abunda zai faru ya faru,'
rai a6ace tayi maganar,cakumar rigarta jahad tayi,tare da yin wurgi da ita,ta faɗa saman gadon tana kuka,fitowa Sehrish tayi daga cikin toilet,ganin jahad na ƙoƙarin bugun hosana yasa tayi saurin zuwa tare da ruƙo hannunta"karki kuskura kice zaki hukunta hosana!abunda tayi dai dai ne,koda ace ita bata faɗa masu ba,to ni saina faɗa masu abunda waccan matar ta aikata maku,saboda bata da Imani,muguwace ita,muddin akace za'a cigaba da yafe ma mutane irinta to tabbas bazasu ta6a canza halinsu ba!Suna buƙatar a ladabtar dasu,a hukuntasu,idan suka aikata ba dai dai ba,Ni hakan da hosana tayi ta burgeni,!"
Shiru jahad tayi,ta wani 6angaren zancen sehrish gaskiya ne,muddin ba'a ɗauki mataki ba akanta taga an ƙyaleta to tabbas bazata ta6a canzawa ba,amma yanzu idan suka hukunta ta dole nan gaba taji shakkar ƙara yin irin kuskuren da tayi abaya,
"Kin faɗi gaskiya sehrish,ni banyi tunanin hakan ba,kuma koda nake yi ma hosana faɗa,saboda 6arin zancen da tayi ne agaban mutane,bai kamata ta yi magana akan idon kowa ba,in ma faɗin ne Ya Omar yakamata ta sanar mawa,sae su yanke mata hukuncin da suka ga ya dace da ita,"
Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke idonta daga kan sehrish ta mayar dasu kan hosana dake baje saman gadon tana kuka,nan take taji bata kyauta mata ba,hawa saman gadon tayi tare da janyota jikinta,tana lallashinta,daƙyar ta samu tayi shiru,daga bisani suka tashi domin yin sallar magrib,
*Aunty Babba*
Tunda ta watsa a gujen nan,ɗakin hayaam ta faɗa,jikinta sae faman rawa yakeyi,zagaye tashiga yi a ɗakin tana tunanin hanyar da zata bi ta gudu daga cikin gidan tun kafin ishaq ya waiwayeta,tsoranta karya bata takardar saki,don bata shirya yin zawarci ba,hannu ta aza aka tana fadin"Nashiga uku ni laila,na jama kaina masifa da bala'e,Ina zan tsoma raina inji daɗi,"tana cikin zancen zucin nan,hafsat ta shigo ɗakin,kamar jira takeyi nan ta shiga balbaleta da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba,
"Don ubanki ki faɗa mun taya akai yaran nan suka rayu!nasan kinsan komai munafuka algunguma!"hafsat na ƙokarin buɗe baki,Aunty babba takai mata naushi a kumatunta,har sai da le6enta ya ɗan fashe,idonta jawur ta ɗago tare da kallon Mommyn nata idanunta cike taf da hawaye tace"Mommy!ni kika buga saboda zunubin da bani na aikata ba?
A faɗace Aunty babba tace"Zanci ubanki ko ki rufe mun baki,wlh hafsat kin cuce ni!Allah ya isa tsakanina dake!ae kinsan da zaman yaran nan acikin gidan nan, shiyasa don munafunci kika sanyo nikabi uban meyasa baki sanar dani ba tuntuni don inyi takaina!Kece kika tseratar dasu daga hannun baba alamu,in ba haka ba taya akai har suka kawo kansu cikin gidan nan"!?
Girgiza kai hafsat ta shiga yi yayin da idanunta ke fitar da wasu irin hawaye masu ɗumi,cikin shessheƙar kuka tace"banta6a dana sanin kasancewarki mahaifiyata ba sai yau!Kin jefani acikin masifa kin kuma zo kina neman ƙala mun sharrin cewa ni na tseratar dasu daga hannunshi,wlh Mommy bakiyi ba!duk wasu magayen ɗabi'u da halayen dana ɗauko naki ne,baki ta6a cemun nayi badai dai ba,baki bani tarbiya mai kyau ba,kullum gur6atamun tunani na kikeyi,saboda kar in dauko halayyar mahaifina,Ni banta6a ganin uwa irinki ba,Yanzu gashi nan daga ni harke wa gari ya waya?kuma inaso ki sani mommy,Ni bansan komai agame dasu hosana ba,bansan ya akai suka dawo hannun Ya Omar ba,Na faɗa maki hakan ne ba don ina jin tsoranki ba,sai don kisan cewar Bani na aikata hakan ba,Allah ne Ya Kamaki,ba yadda banyi ba don ki kyale yaran nan karki salwantar da rayuwarsu kika ki,kuma ni ce da hannuna na goge hotunan da hayaam ta tura maki a wayarki,saboda nafi son ki tako da ƙafafunki don ki gir6i abunda kika shuka......"
..saboda tsabar tsuma jikinta har kerma yakeyi,shaƙo wuyan rigar hafsat tayi da ƙarfin gaske,gadan gadan kasheta zatayi,kiciniyar kwace wa hafsat tashiga yi,suna cikin wannan halin,Amani da hayaam suka faɗo cikin ɗakin da gudun gaske sukayi kansu,daƙyar suka kwaci hafsat daga hannun Aunty babba,dafe maƙoshinta tayi tana faman yarfa hannu tana ambaton"ruwa!ruwa'
Da sauri hayaam ta fita waje,sai gata ta dawo da bottle water a hannunta mai sanyi,miƙa ma Hafsat ruwan tayi,jiki na rawa ta cire marfin robar tare da yin wurgi dashi,ta kafa robar abakinta tana kwankwaɗar ruwan,hayaam ce ta zauna a wurinta,tana lallashinta,
Rai amatuƙar 6ace tashiga fadin"ae da kun barni na kasheta don ubanta,wlh hafsat baƙin cikinki bazai ta6a kashe ni ba,Muguwa kawai,nafi kowa dana sanin haihuwarki,Ni ina kokwanton cewar Anya ba'a asibiti akayimun musanyarki ba,"
Fashewa da dariya Amani tayi tana tafa hannayenta,
Nan take Aunty babba ta ɗaure fuska,tana jifarta da harara,
Tsagaitawa tayi daga yin dariyar da takeyi masu sannan tace"Wannan abun daya faru nafi kowa farin cikinsa,tamkar na zuba ruwa a ƙasa na sha,"
"Amani baki da hankaline?kinsan me kike faɗi kuwa?wannan abun fa ya shafi kowannanmu,bai kamata ki dinga yi mana dariya ba,"Acewar Aunty babba,
wurga mata harara amani tayi tare da cewa"yadai shafe ku!karki kuskura ki ƙara mentioning ɗina aciki,domin kuwa bansan anyi ba,lokacin da kuka tsara muguntarku kuka cutar dasu,kunyi shawara dani ne?Kuma ae har shawara saida na baki akan ki daina azabtar da yaran amma kika ƙi ji ke ga shugabar azzalumai,wlh baku da imani zuciyarku ta bushe,kwakwalwarku a toshe take,tamkar ana zuba maku dussa acikin kawunanku saboda ɗabi'unku sak irin na kafuran farko ne,....."
Waro ido waje Aunty babba tayi tare da faɗin"Ni kike faɗama wannan maganar!"
Amani tace"Kwarai kuwa dake nake,Muguwa macuciya kuma Azzaluma,zuciyarku ta ƙeƙashe Zalunci kawai kuka sa agaba,daku da uwarku Mammy,tsohuwar banza me shegen son kuɗin tsiya,wlh kunji haushin rayuwarku,shegen kwaɗayin abun duniya,ga baƙar zuciya,ga dogon burin tsiya ko tsoran mutuwa bakwayi..."
Tunkan amani ta ƙarasa maganar Aunty babba ta kwashe ta da tagwayen maruka,ji kake tasss tatasss!'kafin Aunty babba ta janye hannunta daga kan kuncin Amani,itama ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta kikkifa mata maruka a jere kusan uku ji kake fass tasss taaasss!
dafe kumatu aunty babba tayi yayin da idanunta sukayi jawur,tunda take arayuwarta ba'a ta6a yi mata irin marin da Amani tayi mata ba,hasalima Amani shakkarta take ji,amma sai gashi yau ta cire yatsunta guda biyar cuf,ta kikkifa mata maruka,
Koda ganin haka,sae hayaam ta miƙe tare da ɗaga hannu zata sharara ma Amani mari,aikuwa hafsat ta yunkura tare da miƙewa ta damƙo hannun hayaam tana faɗin"baki da hankaline?matar da ta iya ɗaga hannu ta mari mommy har sau uku,itace zaki mara?kina tunanin cewa zaki iya rama mata ne," dariya Amani tayi tare da cewa"ki barta inga ƙarshen rashin kunya,wlh dai dai nake da kowane shege acikin ku,Bana jin tsoranku a yanzu,tun ranar da Amal ta sanar dani komai game da ukubar da kukeyi mata tun daga ranar na ɗaura ɗamarar yin yaƙi daku,"
Hankali tashe hayaam da aunty babba suka kalli juna jin ta ambaci sunan Amal,
Hafsat ce tace"Amal na wurinki ne"!?
Jinjina kai amani tayi tare da cewa"Amal tana wurina!itace yarinyar dana zo da ita cikin gidan nan,kun so ku kashe mun ƙanwata,Amma Allah bai baku nasara akanta ba,Amal ta tako da ƙafafunta ta kawo kanta har cikin garin nan,"
Shiru duk sukayi suna sauraronta,
"Haƙƙin Amal kaɗai ya isa ya jefa rayuwarku cikin masifa,laifin me Amal tayi maku da har kuka wulaƙantar da rayuwarta?yarinya ƴar ƙanƙanuwa amma kukayi mata taron dangi wurin azabtar da ita,saboda tsabar mugunta irin taku,ƙiri ƙiri kuka hanani ganin Amal,ku ka yi mun ƙaryar cewar Amal ta 6ace ba'a ganta ba,mugaye kawai ashe gidan makwabtanmu kuke kaita kuna rufeta,duk in nazo har in bar garin,tana can arufe kamar akuya,ko abinci ma baku bata,wai ku wasu irin mutanene?wace irin zuciya gare ku...?
Kasa ƙarasa maganar Amani tayi saboda kukan daya ciyota,nan take ta fashe da wani irin matsanancin kuka,ba ita kaɗae bama hatta hafsat sai da ta zubar mata da kwalla,baƙin ciki kamar ta binne kanta,abun kunyar da mommynta ta aikata ba ƙaramin illa yayi ma zuciyarta ba,
Hayaam kuwa sae faman mazurai takeyi ita da aunty babba sunyi wuƙi wuƙi,basu da abun cewa,dama ance rana dubu ta 6arawo,rana ɗaya ta me kaya,
"Wlh kaɗan kuka fara gani!haƙƙin Amal da kuma haƙƙin waɗannan bayin Allahn da kuka cutar bazai ta6a barinku ku zauna lafiya ba,in har ba zaku canza waɗannan munanan ɗabi'un naku ba,mugunta da kwaɗayin abun duniya,dogon buri,rayuwar ƙarya,duk ku kadae gashi har yau Allah bai ta6a baku nasara ba,mutumin da bai ta6a sa Allah alamurransa ba taya zaiga dai dai"?
Tsoki Aunty babba ta buga tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace"zo ki fuce ki bamu wuri tun kafin ranki ya 6aci a wurin nan!shashasha kawai kina tunanin cewa kalamanki zasu iya tankwarani ne?duk duniya ba ayi mutumin da zai zauna yanayi mun nasiha ba,wlh ba ayi shi ba,"
Girgiza kai amani tayi tare da juyawa a fusace tabar ɗakin tana faɗin"Jiki magayi,"
Komawa Aunty babba tayi yaraf ta zauna gefen gadon tana faman cizon yatsa,miƙewa hafsat tayi tare da fucewa daga ɗakin,
Fitar ta keda wuya,Hayaam ta dawo gefen aunty babba ta zauna tana faɗin"Yanzu menene mafita"?
..fuskarta a hargitse tace"mafita ta wuce mu gudu salin alin batare da sanin kowa ba,"
"Saboda me zamu gudu?hakan na nufin cewa sun ci nasara akanmu kenan"?
"Hayaam ba zaki gane ba,ina tsoran in sake yin arba da hosana ne,bata da hankali,zata ci gaba da tona mun asirine a bainar jama'a"
"Amma Aunty laila,taya akai yaran suka zauna a wurinki har hakan ya faru?meyasa baki kashesu ba tun lokacin"?
Guntun tsoki taja tare da kawar da kanta gefe cike da takaici tace"sai yanzu nake danasanin barinsu araye,meyasa ban kashesu ba tun lokacin da suke a wurina ba?wancan shashashan mutumin dana bama aikin zubar mun dasu a daji bansan ya akai yayi sakacin da har suka ku6uta daga hannunshi ba,kuma tun ranar dana bashi su nake ta jaraba kiran wayarshi akashe kullum har na gaji na daina kira,duk shi ya kwafsamin wlh,yanzu yawo acikin gidan nan ma ya haramta agareni,Allah yaso Hafsat ta siya niqabi a kasuwa,zan kar6e shine in sanya a fuskata saboda gudun kar waccen mai ta6in hankalin cikin sun ta ganni.....'
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci,zurfin tunani ta shiga yi kwatsam ta tuna da maganar nan da hajjaju ta ta6a sanar da ita kwanakin baya can da suka wuce lokacin su hosana na a gidan,
"Idan kin toshe waɗannan hanyoyin,ita kuma waccen ɗayar hanyar da ta riga isa inda baki so fa ya zakiyi da ita'
Jinjina kai Aunty babba tayi tare da faɗin"Allah ya isa tsakanina da hajjaju,sarai tasan komai game da rayuwar yaran nan amma taƙi sanar dani,babu yadda banyi da ita ba,amma taƙiya saboda tsabar baƙin hali irin nata,da tun farko ta sanar dani cewa ƴan ukune yaran akwai ɗaya dake aiki a gidan da tuni nasan abunyi,
wannan masifar har ina"?
"Amma kina ganin Ammi zata barsu ne acikin gidan nan?Jiya munyi plan ɗin cewa zaki kirata a waya ki sanar da ita cewa yaran shaggu ne,kin sanar da ita hakan," ta ƙarasa maganar tana kallon fuskar aunty babba wadda ke a hargitse,jin maganar hayaam yasa ta ɗan jinkirta,kamar me nazarin wani abu can ta ɗan washe baki tare da cewa"Hakane!Wannan ita kaɗae ce hanyar da ta rage mun,jiya na kira ammi a waya kuma na sanar da ita cewar Abusufyan ne ya ta6a yi ma wata fyaɗe harta samu ciki ta haifesu,ina da tabbacin cewar AMMI bazata barsu su zauna ba,dole ta koresu ƴan jakar uban,wlh na tsani yaran can,na tsani mahaifinsu duk shine silar komai,ya tashi yayi aure batare da sanin kowa ba,gayanan ya jefa mu acikin masifa,ni duk bama wannan ba,taya akai AMAL ta gudo daga gida tazo Abuja wurin waccen baƙar munafukar?ta ya akai Mammy da Abrah su kayi gangancin da har AMAL ta gudu daga gida ta dawo wurin Amani?
Hayaam tace"Nima abunda nake tunani kenan,don ko aranar da zan bar gidan Amal na ƙunƙume aɗakinmu,zazza6i ya rufeta,Ni babban baƙin cikina ma,muna nan sake da baki,Amal na iya zuwa ta aure wani daga cikin matasan gidan,kinga ae shikenan mukuma tamu ta ƙare,maƙiyanmu za suyi ta cin nasara akan mu,'
"Insha Allah hakan ma bazata faru ba,in har ɗaya daga cikinku ke da abra bai auri ɗaya daga cikin matasan gidan ba,to sai dai ayi Ragas,Uban kowa ya rasa,itama Amal ɗin tarasa,ita kuma waccen ƴar iskar sai nayi silar mutuwan aurenta,tunda har ta iya ɗaga hannu ta kikkifamun mari,wlh saita gane kuranta,kuma wlh billahil azeemu,muddin Ishaq ya sake ni,itama sai Abbas ya sake ta,inyaso sai muyi zawarcin atare,"ta ƙarasa maganar tana faman sakin huci,tayi danasanin zuwanta gidannan!
*Boss Bature*
❤🤍❤
turo ƙofar ɗakin da ammi ta sauka akayi,Azmee ce ta shigo hannunta ɗauke da kakkauran tea ɗin data haɗa mata,a zaune ta same ta saman darduma jikinta sanye da hijabi,yayin da hannunta ke ruƙe da cazbaha,da alama sallah ta kammala yi,
Cike da girmamawa azmee ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe ta,"Ina yini Ammi,ya gajiyar tafiya,"
da buɗar bakinta sae cewa tayi"Ina Abusufyan yake"?
Azmee tace"sun fita sallar magrib,amma nasan yanzu suna kan hanyar dawowa gida,nan bada jimawa ba nasan zasu shigo ciki,"
Jinjina kai tayi tare da kai hannu ta ɗauki cup ɗin da azmee ta miƙa mata,abaki takai cup din ta kur6e sa kusan sau uku sannan tace"Idan sun dawo,kice su jira ni a palour gaba ɗayansu,inason ganinsu,"
Tuni Azmee tasha jinin jikinta,aranta tace"tashin hankali,'a fili kuma tayi saurin cewa"Za'a sanar masu,"sannan ta mike ta kama hanyar fita daga ɗakin,har azmee ta ruƙe handle din ƙopar zata fita,muryar Ammi ta katse mata hanzarinta da cewa"Next time idan zaki haɗamun tea,bana son sugar yayi yawa,sannan madarar tafi bornvitan yawa,da fatan za'a kiyaye,'
"insha Allah za'a kiyaye,ko akwai wani abu da kike buƙata"?
"Idan ina buƙata zan sanar dake ne,basai kin tambaye ni ba,zaki iya tafiya,"
jinjina kai azmee tayi kafin ta buɗe kopar ɗakin ta fuce,babban falo ta nufa tana tafiya tana jinjina wa izza irin ta Ammi,saboda tsabar masifa,ko bornvita azmee bata zuba a tea din ba,madara kawai ta sanya mata amma saboda hali irin na ammi,da ba'a iya yi mata gwaninta,ta buga warning akan madara tafi bornvita yawa,ko ta ina taga bornvitan"?akan tea ma tayi ƙorafin anyi ba dai dai ba,inaga In taji abunda Abusufyan ya aikata batare da saninta ba,tabbas akwai matsala,rayuwarsu sehrish tana cikin garari,don wannan guyababbiyar matar bazata barsu su zauna lafiya ba,acikin gidan nan,
Jin sautin muryoyinsu,yasa Azmee dawowa daga zurfin tunanin da ta shiga,dawowarsu kenan daga masallaci kowa bakin shi ɗauke da sallama suka shigo cikin Main palour din,Abba ne tare da Abusufyan sae junaid atare,bayansu kuma su Abbas ne da ishaq,Mg Osman da kuma Captain Adam,sai kanal yousouf da kuma Marshal wanda ke tare da Dr harris,a bayansu kuma akwai Fawan,twins,jabeer,irfan,khaleed dukansu dai suka shigo ciki,
ƙarasawa Azmee tayi wurinsu tanayi masu sannu da dawowa,daga bisani ta isar masu da saƙon ammi,nan fa kowa ya shiga fargabar dalilin tarasu da Ammi tace ayi,musamman Abusufyan yafi kowa shiga damuwa,tsayawa su kayi a tsaye kowa yana ta zullumin fitowarta,Abba dae sai ƙarfafa ma abusufyan gwiwa yake,akan ya jure,kada tsoro ya hanashi yi ma Ammi bayanin komai yadda zata fahimta,
Jin takun takalminta kwas kwas!yasa su yin saurin kai idanunsu akanta,fuskarta na manne da farin glass,kwata kwata babu annuri a fuskarta,yayin da hannunta ke ruƙe da sandar nan ta alfarma,Ƙarasowa tayi tare da samun wuri ta zauna saman 3 seater,sannan ta aza ƙafarta ɗaya bisa ɗaya,tare da kallonsu tace"Ku zauna,"
A ƙasa su fawan suka zauna,yayin da Abbansu junaid,da abusufyan suka zauna asaman ɗayar 3 seater ɗin,ishaq da abbas suka zauna asaman 2 seater,Dr harris da Omar suka zauna a ɗayar 2 seater,dama 2 set ne na sofa a babban falon,manyan ne suka zauna saman kujerun,yayin da ƙananan daga kan Kanal yousouf suka zauna aƙasa,
Tsit falon yayi na wani lokaci,kai kace mutuwa ce ta gifta,ko motsin mutun bakaji a wurin,kowa ya kame kanshi,
ɗaya bayan ɗaya Ammi ta dinga binsu da kallo,kowa sae faman noƙe kai yake,shi dai abusufyan ya gaza sakewa,don ko idonshi bai ɗago ya kalle taba,
ɗaga sandar hannunta tayi tare da nuna Ayan tace"wannan dogon gashin fa?sai kace wani ɗan daudu meyasa baka aske shi ba?
cikin sauri Ayan yace"ƙuraje ne ke fitomun akaina duk in nayi yunƙurin aske gashin"
Ta6e la66anta tayi,kafin ta janye idonta daga kan Ayaan ta mayar dasu kan fawan,sunnar da kai ƙasa yayi yana ƴan kame kame,
"Ƴa'ƴan fatima kenan,ba zaku ta6a canzawa ba,yadda kasan sun haɗa jinsi da ibliss,ji bi ɗan iskan askin dake akanshi,hada kala ma ka canza mashi kaiga ƙeƙasasshe ko"?
Fawan akeyi ma faɗan Amma Abbansu ne ke jin maganar har cikin zuciyarshi,bakomai ya ɗan 6ata mashi rai ba,sai kalmar data faɗi na cewar kamar sun haɗa jinsi da iblis,abun ya tsaya mashi arai,jurewa kawai yakeyi,
ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga sharrance su,har sai da tazo kan junaid wanda keta faman sakin murmushi kamar wani zautacce,
"Iko sai Allah!kai zonan,"da sandar hannunta tayi mashi nuni da yazo,miƙewa junaid yayi ya koma ƙasan kujerar da take ya zauna,hannu tasa tare da jan kunnanshi tace"Bakasan nazo bane?kowa na zuwa ya gaishe ni,amma banda kai,Abbanku ya sangarta ka ko?shiyasa ka fara jin kanka wani shege,"dafe hannunta yayi yana dariya yace"Ammi dan Allah ki sakarmin kunne na,Da zafi fa,Abba kana gani ko,"?
"Me Abban naku zai iya yimun bakasan cewa ni na tsugunna na haifesa ba,"
Zumbura mata baki junaid yayi tare da murguɗa mata baki,
"Fiye da haka ma zaka iya yimun tunda ubanka ya ɗaure maka mazauni,dole ka murguɗamun baki,ae bazan bar gidan nan ba,sae nasa an tura ka aikin soja,sannan hankalina zai kwanta,"
Bubbuga ƙafa junaid ya shigayi yana yi mata ƙunƙuni,hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bata ba,amma bata bayyana hakan akan fuskarta ba,"
Shiru ta ɗanyi na wani lokacin kafin tace"kai irfan,tashi ka kiramun gwaggonku,tare da Auntynku Azeema inason ganinsu,"cikin sauri irfan ya miƙe tare da barin wurin ya wuce ɗakinsu gwaggo,
Bada jimawa ba,sae gashi ya dawo tare da gwaggo da hajiya azeema abayan shi,duk wannan surutun na gwaggon katsina,yau tsit kake jin bakinta,sae faman wurga ido take,wuri suka samu suka zauna,a saman sofas ɗin dake cin mutun ɗaya,
Bayan kowannansu ya natsu,Ammi ta tsayar da idanunta akan Abusufyan,wanda tunda suka zauna a falon,bai ɗago ya kalleta ba,
gyaran murya ta ɗan yi tare da ambaton sunanshi"Abusufyan"a firgice ya ɗago yana kallonta,bawan Allah harya fara haɗa gumi,ga yatsun hannunshi dake ta kerma,duk wasu alamu na rashin gaskiya sun bayyana a tattare dashi,Abba sai tausarshi yakeyi yana faɗin"ka kwantar da hankalinka,ka natsu dan Allah,duk kabi ka firgice,hakan ma zaisa taƙi yadda da hujjojin da zamu bata,"ƙasa ƙasa yake yi mashi maganar don karta ji shi,
ɗakyar Abusufyan ya iya amsa kiran da tayi mashi"Na'am Mommy,"
"Meyasa kabar ƙasar nan,batare da ka sanar mun ba?laifin me na aikata maka da har kake gudu na?sai kace bani na haifeka ba?bansan me ka ɗaukeni ba,'
muryarshi na rawa yace"Kiyi haƙuri Ammi,Nima bada son raina na tafi na bar ƙasar nan ba,nasan ni mai laifine a wurinki,ki yafe mun....'saukowa yayi daga saman sofa ɗin ya dawo ƙasa ya zuƙunna yana bata haƙuri,
"idan har dagaske kasan cewar kai mai laifine,meyasa da ka dawo Nigeria bakazo gida ka same ni ba,don ka nemi yafiyata ba"?
Shiru yayi yayin da idanunshi ke cike tab da kwalla,gaba ɗaya ya rasa inda zai tsoma ranshi,babbar damuwarshi shine,yadda zai fara yi mata zancensu sehrish,
..hmmmm ta furta sautin tare da mayar da idanunta kan gwaggon katsina tace"Saboda yardar da nayi dake ne yasa na ɗamƙa maki Amanarshi,don ki ladabtar mun dashi,a tunanina zaki canzamin shi,ashe bansan nayi aikin banza ba,"
ɗaure fuska gwaggon katsina tayi,alamar ranta ya 6aci,
"Ammi dan Allah komai ya wuce,just forget about the past,haba dan Allah,komai ya wuce mana,taya za'a zauna ana ta faman nanata abunda ya riga ya faru.,.,.."
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abunda Jahan ke cewa,yadda kasan wanda yasha giya haka ya shiga sambatu yana faman jan guntun tsoki ƙasa kasa,yunƙurawa Marshal yayi da nufin ya buge masa baki,Ammi ta dakatar dashi"basshi ya ƙarasa,ba laifinsa bane,gado yayi wurin Uwarsa,ae ni bansan yaushe ne ƴa'ƴan fatima zasu fara girmamani ba,amatsayina na wadda ta haifi ubansu,"
Rai a6ace jahan ya miƙe zai bar wurin Abbansu ya daka mashi tsawa tare da korosa yace"Koma ka zauna,Allah yasa inga ka ƙara cewa uffan a wurin nan,"
Komawa yayi gefen ayaan ya zauna yana faman hura hanci,
Jinjina kai Ammi tayi tana kallonshi tace"Nan gaba fa,in ban bi asannu ba,bugu yaran nan zasu fara kaimun,To Allah ya kyauta gaba,"
Abba yace'Insha Allah hakan ma bazata ta6a faruwa ba"
Shidai abusufyan har lokacin yana zuƙunne asaman guiwowinsa,cike da zullumin me zai biyo baya,
"Uncle ka tashi ka koma ka zauna,jikinka sai kerma yakeyi,Ammi fa ba abunda zata iyayi maka,"Sakin baki abbansu yayi yana kallon junaid dake magana,yana ƙoƙarin kashe wutar da jahan ke ƙoƙarin kunnawa shi kuma zai hura wata wutar,
Girgiza kai Ammi tayi tare da wurga ma Abbansu harara tace"Bazan iya zama agidan nan ba,yaranka sunfi ƙarfina,"sunnar da kai ƙasa abba yayi kafin ya ɗago yana kallon junaid da yayi maganar ya ɗan jefa mashi harara,
Suna cikin wannan Zaman sai ga hosana ta shigo cikin falon,tana neman warin ɗan kunnanta daya faɗi,'tashin hankali,gaba ɗaya hankalin kowa ya koma kanta,abusufyan kuwa arazane ya ɗago yana kallonta,ammi duk bata lura da ita ba har sai da Hosana ta buɗe baki tayi magana"Daddy ɗan kunnena ya faɗi a falon nan ban ganshi ba,'juyawa ammi tayi tare da kai idanunta kan hosana dake tsaye tana magana,a wani slow ta sanya hannu ta zame glass ɗin dake a fuskarta,tashiga ƙare ma hosana kallo,cike da mamaki tace"Ina kuka samu matashiyar yarinya acikin gidan nan"?sunnar da kai ƙasa Abusufyan yayi yana faman zare ido zuciyarshi tamkar zata faso kirjinshi ta fito saboda razana,
Shiru kowa yayi mata aka rasa wanda zai buɗe baki ya bata amsa,
Jin sunyi banza da ita yasa ta kira hosana da hannunta"Zo nan,"
Shiga ciki hosana tayi tare da tsayawa agaban Ammi tace"Gani,"
"Wanene mahaifinki a wurin nan"tayi maganar tana nunasu da sandar hannunta,
...murmushi hosana ta saki tare da ɗaga yatsan hannunta ta nuna abusufyan sannan tace"Gashi nan,shine daddynmu,ni dasu Sehrish da Jahad,"
..a wayance Ammi tace"Oh harku nawa ne a wurinshi"?
Hosana tace"Ƴan ukune mu,ko in kira maki su jahad ki gansu?"
Cike da mamaki Ammi tace"kira mun su in gansu,"da gudu hosana ta nufi ɗakinsu don ta kira su jahad,
Tashin hankali,
Wani irin gumi ne ya shiga fesowa daga jikin abusufyan,gaba ɗaya duk yabi ya kama kansa,jikinshi sae faman kerma yakeyi,bashi kaɗae ba hatta sauran dake a wurin zaune,kowa saida yasha jinin jikinsa,musamman Kallon da Ammi ta dinga binsu dashi ɗaya bayan ɗaya,kallon tuhuma,
Lokacin da hosana ta faɗa corridor ɗin ɗakunansu,hayaam na tsaye a wurin,tana ganinta tasha gabanta tare da cewa"daga ina kike"?
Murguɗa mata baki hosana tayi kafin tace"Ni bansan wacece keba,ki bani hanya in wuce,su jahad zan kira,wata tsohuwa ce fara tass take son ganinsu,"
Jin haka yasa hayaam ta gane cewa cewa AMMI ce ke son ganinsu,shu'umin murmushin nan nata tasaki,kafin ta matsa ma hosana hanya ta wuce,jinjina kai hayaam tayi tana faɗin"hada wani zumuɗin Ammi ta kirasu,basu son cewa watan korarsu daga gidan yayi ba,"tana ƙarasa maganar ta nufi ɗakin da Aunty babba take,tana shiga ta sanar da ita cewar ga Ammi can tasa a kira mata ƴa'ƴan Abusufyan,jiki na rawa Aunty babba ta taso,suka fito daga ɗakin domin suje yin la6e,don su ga irin korar karen da ammi zatasa ayi ma su Sehrish,
Bada jimawa ba,Hosana ta fito hannunta ruƙe dana sehrish,ɗayan hannun kuma ruƙe da hannun Jahad,jikinsu na sanye da hijab don tunda su kayi sallar Magrib basu ciresu ba,hosana ce kawai ta cire hijabin jikinta,ta yafa mayafi akanta,
da sallama a bakunansu suka shigo cikin falon,ya salam ae tuni Abusufyan ya zauna ƙasa dirshan yana lazimi,Abba kuwa sae faman jinjina kai yakeyi,gwaggon katsina kuwa tana ganinsu jahad ta shiga zare na mazurai don tasan cewa ƙarshe abun kanta zai ƙare ita da ta sanya mashi hannu ta ɗaure mashi mazaunai wurin yin auren batare da sanin Ammi ba,kowa dai yashiga zullumin abunda zai biyo baya,
Aunty babba kuwa suna la6e ita da hayaam sun kasa kunne suna jiran jin mai zai biyo baya,jikinsu sae faman tsuma yakeyi,
Zuba masu ido Ammi tayi tana kallonsu,one by one,ganin yadda matar ta ƙura masu ido yasa duk suka sha jinin jikinsu,daƙyar suka iya haɗa baki wurin gaishe da ita"Ina yini,"
Bata amsa masu gaisuwar tasu ba,sae nuni da tayi masu da sandar hannunta alamar su zauna,wuri suka samu agaban kujerar da su Omar ke zaune,suka zauna daga ƙasa tare da lankwashe ƙafafunsu,zaman cin tuwo,
Nuna Sehrish tayi da sandar hannunta tace"Ya sunanki"
Jiki asanyaye sehrish ta bata amsa da cewa"Sunana Sehrish,"
Ammi ta kuma cewa"wanene mahaifinki"?
wurga idanunta tayi akan Abusufyan ta nuna shi da hannu tare da cewa"Gashi nan,shine mahaifinmu"
jinjina kai Ammi tayi tare da kallon abusufyan wanda keta faman zubda gumi a fuskarsa,duk sanyin A.c din dake akwai a falon,
...hmmmm janye idanunta tayi daga kan Sehrish ta mayar dasu kan Jahad tace"Kefa ya sunanki"?
"Sunana jahad,"
"Wanene mahaifinki acikinsu,"
Juyawa jahad tayi tare dakai hannu ta nuna abusufyan tace"Shine daddynmu,"
Rai amatukar 6ace Ammi ta daka masu tsawar da ta gigitasu gaba ɗayansu duk suka razana,a tsiwace tace"Kowa ya zuba mun ido yana kallona,ba zaku faɗamun a ina kuka samo su ba?taya akai Abusufyan ya zama ubansu!"
Abba ne yayi ƙoƙarin buɗe baki yace"Ya'yanshi ne dagaske,kamar yadda suka faɗa Ammi,"
Aruɗe Ammi tace "Ni kake faɗama cewa ƴa'ƴanshi ne?kada ku raina mun hankali ta gidan ubanwa Abusufyan yayi aure da har zai haifi waɗannan balagaggun ƴan matan!"?
Fashewa da kuka hosana tayi,sehrish da jahad kuwa tuni hawaye sun soma wanke masu fuskarsu,jikin Marshal ba ƙaramin sanyi yayi ba,haka zalika sauran dake zaune a wurin,
"Abusufyan!ka faɗamun taya akai ka samu yaran nan?Na yarda cewa ƴa'ƴanka ne koda basu faɗamun da bakinsu ba,saboda ina ganinsu nasan cewa Jinina ne su,ko ba don kamanninka dake akan fuskarsu ba,So nake naji TAKUN hanyar da aka Same su!?nasan halinka tun fil azal baka rabuwa da mata,ka faɗamun gaskiya,ka ta6a yin mu'amala da wata ƴa' mace ne har ta samu cikinka"?
A kiɗime abusufyan ya shiga yi mata rantsuwa yana faɗin"Wlh Ammi tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,Nasan cewa zaiyi wuya ki yadda dani,amma wlh saida na auri mahaifiyarsu sannan na same su,ga gwaggonan itace shaidata,"
Tamkar zata rufashi da duka haka tashiga balbaleshi da masifa"Bazan ta6a yadda da kalamanka ba,karka kuskura ka ƙara cewa ta hanyar aure ka same su,in ba haka ba saina ci maka mutunci a wurin nan!dama najima ina zarginka abusufyan,banta6a tunanin zakayi mun haka ba,ka cuce ni,bazan ta6a yafe maka ba,rashin jin maganarka har yakai ka kawo mun Shaggu acikin zuri'ata,bazan ta6a lamun ta ba......'
Rai a6ace gwaggon katsina ta katse mata hanzarinta da cewa"Ya isa haka,babu laifin abusufyan acikin wannan lamarin,Nice na aura mashi yarinyar da ta haifa mashi waɗannan ƴa'ƴan,don haka kidaina ambaton sunansu da shaggu saboda baki da hujjar yin hakan,bazan ta6a yarda a tozarta ƴa'ƴan abusufyan ɗina a gabana ba ehe," kowa yayi mamakin yadda gwaggon katsina ta mayar ma Ammi martani,tamkar wata mai cikakken hankali,
"Dan Allah Ammi ki daure ki fahimce shi,rashin sanar maki da basuyi ba,shine babban kuskuren da Abusufyan da gwaggo suka yi,Gwaggo ta aikata hakanne saboda son da takeyi ma abusufyan wannan dalilin ne yasa ta aura mashi mahaifiyarsu batare da saninki ba,saboda tasan halinki,kin tsani auren bare,gashi shi kuma abusufyan ya kwallafa rai akan yarinyar,wannan ne yasa ta aura mashi ita,saboda gudun karya faɗa halaka..... "Wani irin kallo da Ammi ta jefa mashi ne yasa shi dakatawa da yin maganar da yake,wato Abbansu junaid,
Aunty babba dake la6e ita da hayaam suna sauraronsu,saboda tsabar farin ciki kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha,burinsu kawai Ammi ta koresu Jahad,
Kowa saida ranshi ya 6aci a wurin nan,saboda yadda ammi ta haƙiƙance akan cewar bazata kar6i shaggu ba acikin zuri'arta,a ƙarshe tace"na riga da na yanke hukuncin korarsu daga cikin zuri'ata,banason ganinsu,kuma duk wanda yayi yunƙurin binsu acikinku wlh saina tsine mashi yabi duniya,kuma zan yafe shine acikin ƴa'ƴa Na,
Wani irin matsanancin kuka su jahad suka fashe dashi,haka abusufyan ma kuka yake yi tamkar ƙaramin yaro,ƙiri kiri za'a rabashi da ƴa'ƴanshi,su Abba kuwa gaba ɗaya jikinsu yayi mugun sanyi,Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,haka zalika sauran kowa hankalinshi yayi mugun tashi,
Su aunty babba kuwa dake la6e,jin an kori su sehrish,yasa suka daka uban tsallen farin ciki,saboda tsabar dariyar mugunta,hada hawaye,da gudu suka koma cikin ɗaki,suna faman dariya,burinsu ya cika,
"Ku tashi ku fuce daga cikin gidan nan tunkafin insa ayi waje daku,"jiki asanyaye suka miƙe tsaye jahad ta ruƙo hannun sehrish da jahad acikin nata,tafiya sukeyi kamar wanda aka zarewa laka,yayin da hawaye ke gangarowa daga idanuwansu,yunƙurawa abusufyan yayi da sauri zaibi bayansu,aikuwa abba yayi hanzarin damƙo rigarshi ya janyoshi,ya dawo da shi saman sofa din,a haukace ya shiga kiciniyar kwace kanshi yana fadin"Ka barni yaya hossein wlh sai dai ta tsinemun amma bazan bari rayuwar ƴa'ƴana ta wulakanta ba,duk inda zasu je ƙafata kafarsu,"ganin abusufyan na ƙoƙarin zaucewa yasa su Marshal Omar dasu ishaq da abbas suka rurrukeshi,sai faman hargowa yakeyi,yana kokarin kwacewa don yabi bayansu sehrish,
bazasu iya jurar ganin halin da mahaifinsu ke ciki ba,hakan ne yasa suka fuce waje da gudu suna kuka,tamkar ransu zai fita,sae faman shessheƙar kuka sukeyi,
Suna cikin wannan yanayin Motar SGR,ta shararo da gudu cikin gidan,a tsiyace su kayi parking ɗin motar,tunkan Amstrong ya buɗe mashi motar,ya sanya kafarshi tare da harba murfin motar,ya fito daga ciki,kai tsaye ya nufi wurinsu Sehrish dake a tsaye suna kuka,kwata kwata basu lura dashi ba,sae dai suka ji an ruko hannayensu,Jahad da hosana,a firgice suka ɗago suna kallonshi,"ku wuce mu shiga ciki,"yayi maganar tare da jan hannunsu,sehrish ma tabi bayansu suka koma cikin falon,jin sallamar Sgr yasa hankalin kowa komawa kansu,ganin ya dawo dasu sehrish yasa kowa ya shiga sauke ajiyar zuciya,Zuba mashi ido Ammi tayi tana kallon ikon Allah,
ƙarasawa cikin falon yayi tare ce masu sehrish"Ku samu wuri ku zauna,"jiki asanyaye suka samu wuri ƙasa suka zauna,suna faman sauke ajiyar zuciya,
Zama sgr yayi asaman sofa,tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,yayin da yake fuskantar Ammi wadda ta zuba ma sarautar Allah ido,
Sai da ya mula yasha iska sannan ya soma magana
"dama saida raina ya bani cewa hakan zata iya faruwa,that's the reason why na tanadin hujja ɗaya kuma kwakkwara wadda zata wanke zargin da kikeyi akan abusufyan da kuma waɗannan triplet ɗin,"
Ƙarasa maganar yayi tare da sanya hannunshi cikin aljihun wandon jeans ɗin dake ajikinshi,ya zaro wayar shi,
*mu haɗu On monday don jin yadda zata kaya,*
_har yanzu wasu basu gode mun akan long page ɗin da nake sawa,in banda ma rashin godiyar Allah irinta ɗan adam,a ƙalla yawan one page da nake sawa Yayi fiye da 3 page na wasu masu rubutan,Allah har mamaki nakeyi in naga page ɗin wasu writers din,duk read More 3 ne amma ni kaga page mai read more 9 har 12 ina sakawa,ƙaramin page ɗina shine zaka ga read more 6,zama nakeyi inyi rubutu kamar zan kashe kaina,amma wasu saboda rashin godiyar Allah suna zuwa sunayi mun complain ɗin wai adinga posting sau biyu?a iya sanina Vip ne ma ake sanya 2 page,amma ni ina sanya maku kusan 3 page a hade duk da hakan baiyi maku,idan so kuke sai in dinga raba maku shi uku,saboda na lura hakan yafi maku,kunfiso ku ganshi arabe,bakomai ne yasa ma nakeyin page masu tsayi ba face don in samu intakaita labarin saboda yana da tsayi,idan kuma aka cigaba da raina abunda nake sanyawa wlh zan mayar dashi ne read more uku in tafi dai dai da kowa👍_
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Saman Gadon ta haye ta kwanta tare da jan bargo ta lullu6e,zuciyarta cike da wani irin farin ciki,sai faman sakin kayataccen murmushi take,daƙyar bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,❤
Wuraren sallar asuba,jahad ta farka tare da tashin su hosana,atare bayan sunyi alwala su kayi salla,bayan sun kammala suka koma saman gadon suka dasa wani sabon baccin don bai ishe su ba,
Ƙarasowa hafsat tayi ƙopar bedroom ɗin nasu,jikinta sanye da dogon hijabi,hannu tasa ta ɗan bubbuga ƙopar ɗakin,shiru ba'a buɗe ba,ƙara bugawa tayi,bugun ya isa cikin kunnan sehrish,cikin bacci tace"Wanene"?
Hafsat tace"Ni ce,"
"Kece wa"? Sehrish ta tambaya a yayin da ta miƙe tare da tunkarar ƙopar ta buɗe,Tun daga ƙasa har sama sehrish ke bin ta da kallo don batasan wacece ita ba,amma tabbas ta ta6a ganin fuskarta,kuma jiya taga gifcinta acikin gidan,ga kuma kamannin fuskar Yaya ishaq a fuskarta,
ƴan kame kame hafsat ta shiga yi,muryarta na inda inda tace"am...um..jahad.." katse ta sehrish tayi da cewa"ba ita bace,Ni sunana sehrish,jahad tana ciki tana bacci,"
"In ba damuwa inason ganinta,"
Matsa mata hanya sehrish tayi,ta shiga cikin ɗakin nasu,rufe ƙopar sehrish tayi sannan ta koma ciki itama,sae faman kallon kallo suke ita da hafsat,duk tabi ta kama kanta,kana ganin fuskarta zaka fahimci cewar bata da gaskiya,
Wuri ta samu gefen gadonsu ta zauna,idanunta na akan su jahad da hosana dake ta sharar bacci,
Muryarta a sanyaye tace"in ba damuwa,dan Allah ki tashe su daga baccin inason yin wata magana dasu mai mahimmanci,"
Batare da musu ba,Sehrish tace toh,sannan ta haye saman gadon tana ambatan sunayensu,gami da bubbuga ƙafafuwansu"jahad!hosana!ku tashi ana son ganinku,"
cikin bacci hosana ta buga tsoki tana fadin"dan Allah a ƙyale ni,kar a takuramin,"
Jahad kuwa tuni ta farka,tana faman mutsustsuka idanuwanta,wurga idanunta tayi kan sehrish tace"Wai lafiya"?
"Wannan ce ke son magana daku,"tayi maganar tana nuna hafsat dake zaune,
Juyawa jahad tayi tana kallonta,cike da mamaki ta ambaci sunanta"Aunty hafsat!" sunnar dakai ƙasa hafsat tayi,fuskarta dauke da matsananciyar damuwa,daƙyar ta iya amsa mata"Na'am jahad,"tashi zaune jahad tayi,suna fuskantar juna ta sake ambatar sunanta"Aunty hafsat,"
"Kinsanta ne"? Sehrish ce tayi tambayar,jahad tace"Niko na santa,itace ɗiyar wannan matar da nake faɗa maki wadda ta azabtar da rayuwarmu,kuma wannan itace ta ɗauke mu acikin motarta,ni da Hosana ta kai mu hannun wannan mugun mutumin wanda ya kai mu daji har yayi ƙoƙarin cutar da Hosana,"
Jin wannan maganar yasa ran sehrish ya 6aci,harara ta wurga ma hafsat tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace"Dan Allah malama tashi ki fita ki bamu wuri!bamu son ganinki!mugaye kawai Azzalumai,kun cutar da rayuwar ƴan uwana,saboda son zuciya irin naku,basuyi maku laifin komai ba,Amma kuka tsangwamesu,saboda kunga basu da gata,Insha Allah sai kunga sakayyar da Allah zaiyi masu,kuma sai kun ɗanɗana irin uƙubar da kukayi masu,"
Hawaye ne suka shiga zarya a fuskar hafsat,dama saida ranta ya bata cewar dakyar ne su yafe mata,
Janye idanunta tayi daga kan sehrish ta mayar dasu kan Jahad,cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ku yafe mun Jahad,nasan mun cutar daku,amma inaso ku sani bada son raina ba,na kaiku wurin wannan mutumin,Mommy ce ta sanar dani cewa Gidan marayu za'a kaiku,shiyasa har na ɗauke ku,kuma nayi hakan ne saboda tsoran karta halakar daku acikin gidan nan don ba yadda banyi ba akan ta kyale ku amman ta kiya,shiyasa ma na amince da akaiku gidan marayun ashe zubar daku tasa ayi,'
"Ba zamu ta6a yarda da kalamanki ba,saboda tun farko baki nuna kina son mu zauna acikin gidan ba,ke da mommynki,shiyasa kuka haɗa baki ke da ita,kika fara yaudararmu kina nuna kamar kina son mu ashe,so kuke ku fitar damu daga cikin gidan,saboda rashin Imani Aunty hafsat kika damƙa mu a hannun wannan mutumin,to bari kiji Ya Omar ya kashe shi har lahira!!
Gabanta ne ya faɗi rassss!hankalinta yayi mugun tashi,a kiɗime tace"Ya kashe shi!"
Jahad tace"kwarai kuwa Ya Omar shi ne ya kama shi da hannun shi acikin gidan gonarsa,lokacin da yake ƙoƙarin keta haddin hosana,aikuwa ya fasa mashi kai,anan wurin ya zama gawa,'
Tana kai ƙarshen maganarta sehrish ta ɗaura da cewar"tun yanzu kwara kusan inda dare yayi maku!don wlh Ya Omar bazai sassauta maku ba!muddin yaji cewar kune kukayi silar da har wannan mutumin ya ɗauki su jahad ya kaisu daji,sannan ku fara tunanin irin hukuncin da kuma zaku fuskanta a wurinshi!"
Wani irin wahalallan yawu hafsat ta haɗiya,tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,ba don komai ba sai don jin cewa An kashe mutumin nan!tun da har Omar zai iya kashe rai akan su hosana,tabbas ba ƙaramin so yake masu ba,kuma akansu zai iya hukunta kowa,yanzu su menene sakamakonsu?
"Baku da wata mafita,shawara nake baku tun kafin hosana tayi maku tonan asiri,kwara kusan abunyi,don tace saita sanar ma Daddy da Ya Omar abunda kukayi mana!" jahad ce tayi maganar,
Gaba ɗaya duk sun bi sun tsoratar da ita,la66anta har kerma suke wurin rokonsu tana cewa"Dan Allah ku yafe mun,wlh nayi dana sanin duk wani abu da mu kayi maku,har ga Allah ni bada sanina ba,mommy ce ta shirya duk wannan,Allah shine shaidata,bazan yi maku ƙarya ba,"sosai hafsat ke kuka,
Ruko hannun jahad tayi acikin nata tana fadin"jahad nasan kina da sauƙin kai,dan Allah ki yafe mun,wlh nayi nadamar abunda mu kayi maku ni da mommyna,nasan naƙi ku da farko amma daga baya naso ku sosai,kuma nayi kukan rashinku atare dani,lokacin da nagane cewa Mommy ba gidan marayu tasa akaiku ba,har faɗa sai da mu kayi da ita,ko isasshen bacci bana samu a lokacin saboda tunanin wani hali kuke ciki......"ƙarasa maganar tayi tare da sanya hannu tana share hawayen dake zuba a kan fuskarta,
Shiru su kayi da alama jikinsu ya ɗanyi sanyi,Sehrish tace"Jahad,idan kinyi niyya ki yafe mata,'jinjina kai jahad tayi tare da cewa"Ni dama ban ruƙe ki araina ba Aunty hafsat,na yafe maki Allah ya yafe mana gaba ɗaya,"
Amsawa tayi da "Amin,sannan tace"Hosana fa?dan Allah ku tashe ta inaso in nemi yafiyarta,"
Hannu Sehrish takai tare da bubbuga ƙafarta,farkawa hosana tayi,idanunta sunyi suntum saboda bacci,
"Hosana ki tashi,ga Aunty hafsat nan tana son magana dake,"jin an ambaci sunan Aunty hafsat yasa ta wartsakewa ta miƙe daga zaune,koda idanunta su kayi arba da fuskar hafsat,nan take ta murtuke fuska rai a6ace tace"Ni bana son ganinta,na tsaneta kamar yadda suka tsane mu ita da Mommynta,Aunty hafsat muguwace bata tsoron Allah,itace takai mu wurin wannan mummunan mutumin wanda yakusa kashe ....."katse ta jahad tayi da cewa"pls hosana just forget about the past,forgive her pls,Aunty hafsat tayi nadama,kuma bada son ranta ba ta kaimu wurin mutumin nan ba,Mommynta ce ta shirya wannan,"
Maƙe kafaɗa hosana tayi alamar bata yarda ba,harara ta wurga ma hafsat ɗin tana murguɗa mata baki tace"Allah saina faɗama Ya Omar da daddy,ko kukan jini zatayi sai dai tayi,amma saina faɗa,saboda rashin Imani kamar wasu dabbobi haka kuka rufe mu acikin store babu abinci ga ƙishin ruwa,ko iska babu,amma ko ajikin ku mu rayu ko mu mutu wannan ba matsalarku bace,zafi kamar zai kashe mu,adaren ranar da muka kwana a store,ba don jahad tayi mun fifita ba da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya don rashin imani ku kuna can kuna shan A.c,wlh saina faɗama daddy....."fashewa hosana tayi da kuka,hada bubbuga ƙafarta,daga gani abun ba ƙaramin ciwo yake yi mata ba,ya tsaya mata arai,
Gaba ɗaya jikinsu yayi wani irin sanyi,musamman hafsat,duk yadda taso ta shawo kanta amma abun yaci tura,hosana ta rantse ta maya akan cewar saita faɗa ma Ya Omar,hatta jahad sai da taso ta lallasheta,amma ina ƙarshe sai ta dinga ƙoƙarin bugun jahad din,
Ganin haka yasa sehrish kallon hafsat tare da cewa"dan Allah kiyi haƙuri ki tafi kawai,hosana batasan ganinki,idan tana kallonki haukanta zai iya tashi,"
Jiki asanyaye Hafsat ta mike,tana tafiya tana waiwayonsu yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,a haka har ta isa ƙopar ɗakin ta buɗe ta fuce da gudu tana kuka,
Hannu Sehrish tasa tare da janyo hosana ta rungumeta sosai ajikinta tana lallashinta,da ƙyar ta samu hosana tayi shiru,sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,komawa su kayi suka kwanta kowa da abunda yake saƙawa aranshi,
*Aunty Babba*
Suna kwance ita da hayaam sai faman sharar bacci sukeyi suna jan minshari yadda kasan bijimayen sa,sun cika gadon su biyu kawai,babu wanda ya farka acikinsu balle suyi tunanin yin sallar asuba,can cikin bacci Hayaam ta dinga jin ana bugun ƙopar ɗakin nasu tamkar za'a balle ta,dogon tsoki taja tana faman yatsina fuska alamar an takurata,a ƙule tace"Wai dallah wanene ke buga ƙopar ɗakin nan"!?
Muryar hafsat tajiyo daga waje cikin shessheƙar kuka tace"Ni ce,ki zo ki buɗe mun ƙopa,"
Jiki na rawa hayaam ta saukko daga saman gadon ta ƙarasa tare da buɗe ƙopar,gabanta ba ƙaramin faduwa yayi ba ganin fuskar hafsat sharkaf da hawaye,hankali atashe tace"Meya faru ne kike kuka"?
A tsiwace hafsat tace"Ba dole inyi kuka ba!kun jefani cikin masifa!ki bani hanya na wuce,Da Mommy nake so inyi magana,"tana faɗin hakan ta bangaje hayaam tare da wuce wa ciki,duk tabi ta ruɗe,wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare ma hafsat maƙoshinta,lokacin da tayi arba da Aunty babba,baje saman gadon tana sharar bacci,wato hankalinta kwance ita,batasan wainar da ake toyawa ba,
Da karfi ta ambaci sunanta"Mommy!Mommyyyyyyyy!
A firgice Aunty babba ta farka,agigice ta tashi zaune tana faɗin"Lafiya hafsat kike mun irin wannan kiran"?
"Ina fa lafiya mommy!ashe ke kina nan kina sharar bacci,ni kin barni cikin tashin hankali,jiya ko isasshen bacci ban samu ba,saboda tunanin hukuncin da Ya Omar da daddy zasu yanke mana..."
Jin wannan maganar yasa Aunty babba fashewa da dariya tana tafa hannu,
Hakan ba ƙaramin fusata hafsat yayi ba,muryarta na rawa tace"Mom...my dariya ma kike yi"?
Aunty babba tace"to me kikeso inyi in banda dariya,ke bakisan meya faru ba jiya"?
Zuba mata ido hafsat tayi tana kallonta,
"Hayaam zo ki faɗa mata da alama batasan meya faru ba,ae mu yanzu bamu da sauran damuwa,hankalinmu a kwance yake kamar muna cikin jirgi gobara ta kama," tana magana tana faman washe baki,
Ƙarasowa inda hafsat take a tsaye,hayaam tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli hafsat tare da cewa"ke bakisan cewa jiya Ammi ta kori su Jahad daga gidan nan ba?korar ma korar wulaƙanci,ae shiyasa kika ga mun saki baki muna bacci hankalinmu kwance,saboda bamu da sauran damuwa yanzu,"
Wani irin kallo hafsat ta wurga mata tare da cewa"Amma dae a mafarki hakan ya faru ko"?
Aunty babba tace"Wani mafarki,jiya agabanmu Ammi ta korasu,da gudu suka fita daga gidan nan suna kuka,"
Tsabar takaici ya hana hafsat cewa komai,
Hayaam tace"Ae kawai ki kwantar da hankalin ki kema,babu mai tuhumarki akansu,Yaran da yanzu ba'asan ma inda suke ba,"
"Mommy!dama tunanin da kuke kenan?shiyasa baku damu ba,ko kaɗan"
""Kwarai kuwa akan me zamu damu"?
Hannu hafsat tasa tare da dafe kanta,tana faɗin"Ya salam!Wlh Mommy idan mafarki kike toh ki farka!domin kuwa jahad da hosana suna acikin Gidan nan!babu inda suka je!!
Wani irin bugu zuciyar Aunty babba tayi ji kake daraam,a ruɗe tace"Kamar ya kenan"?
"Mommy Jahad da hosana suna nan!Yanzu haka daga bedroom ɗinsu nake,naje ne domin in nemi yafiyarsu akan laifin da muka aikata masu,"
Saboda tsabar tashin hankali har suna haɗa baki Ita da hayaam wurin cewa"Jahad da hosana suna acikin gidan nan!!!"
Jinjina kai Hafsat tayi kafin ta ɗaura da cewar"mun shiga uku mommy,mun ja ma kanmu bala'e da masifa!Ashe Ya Omar shine ya taimake su hosana acikin gidan Gonar mutumin nan,kuma a dai dai lokacin da yake ƙoƙarin yin raping ɗin hosana!
Hannu Aunty babba ta aza aka tana fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"
Hayaam kuwa sai faman zazzare ido take,
"Mommy,bugu da ƙari,a nan wurin Ya Omar ya tarwatsa kan mutumin nan ya mutu har Lahira,"tunkan hafsat ta ƙarasa maganar Aunty babba ta saukko daga saman gadon,hannayenta asaman kanta take fadin"Nashiga ukuna,Na bani na lalace,na ru6e!hafsat dan Allah ki faɗamun gaskiya,!dagaske baba alamu ya mutu!kuma Omar ne ya kashe shi saboda su Hosana!ashe shiyasa kenan naita neman number wayansa daga baya ban samu,wannan wata irin masifa ce!,
Zarya tashiga yi acikin ɗakin tana faman cizon yatsa,Hayaam tace"Aunty laila don Allah ki kwantar da hanlinki...."
Hankali tashe Aunty babba tace"taya zaki ce in kwantar da hankalina?bayan ga kashi cike a wandona,ni bansan wani irin hukunci Omar zai yanke mun ba" tana magana zufa na gangarowa a fuskarta,
Ita kanta hayaam,duk a tsorace take duk da ba ita ta aikata laifin ba,amma ta razana da jin cewar Omar ya kashe mutumin da Aunty babba tasa ya zubar mata da yaran,
"Yanzu hafsat menene mafita"!tayi maganar muryarta tamkar zata fashe da kuka,
Kafin hafsat tace wani abu hayaam ta rigata cewa"Ni ina ganin kawai Aunty laila,ku tattara kawai kubar gidan nan ke da hafsat,"
Wani irin kallon rainin wayau hafsat tayi mata tare da cewa"Mu tattara mubar gidan nan fa kika ce?ke kuma fa?ko kina tunanin cewa In asirin mu ya tonu,ke bazai shafe ki bane?tun wuri kusan inda dare yayi maku ke da Mommy!saboda kune baku da alaƙa da gidan nan!Ni kuwa ba inda zanje saboda nasan cewa duk hukuncin da daddy zai yanke mun bazai ta6a korata ba a gidan nan,saboda Ni ƴarsa ce,nan kuma gidan kakana ne,"
Zuru zuru hayaam tayi jin abunda Hafsat tace,Aunty babba kuwa batasan ma me suke magana akai ba,saboda kanta ya ɗau chargy,sae faman zagaye ɗakin takeyi,ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,
"Wlh da nasan yaran nan suna acikin gidan nan,da tun jiya da daddare zanbi dare,in taushe masu hanci da pillow har sai sun bar duniya don ubansu,yara sun zame man bala'e!"
Girgiza kai hafsat tayi tana kallonta,har yanzu dae babu alamun dana sani atattare da ita,
"Tunda nake ban ta6a shiga tashin hankali ba arayuwata sai akan waɗannan yaran!komai nasa agaba sai naci nasara akanshi,amma waɗannan tsinannun yaran sun tarwatsa mun duk wani plan ɗina,Ba kowa nafi jin haushi ba,face Ubansu,duk shine silar daya auri uwarsu a 6oye harta haifo mana mugun abu,Allah danasan da zaman yaran tun suna cikin ciki zansa a markaɗe munsu,don karsu duniya,'
"Mommy dan Allah kidaina wannan soki burutsin!kin ishemu da surutu kamar wata zautacciya,duk waye ya jefa mu cikin halin nan in ba ke ba?maimakon ma kiyi tunanin sama mana mafita,Sai wasu sambatu kike marasa kan gado,ni bazan iya jurar jin waɗannan munanen kalaman da kike jifar su jahad dashi ba,inaso ki sani su ɗin ƴan uwana ne,"
Juyowa Aunty babba tayi tamkar zata rufe hafsat da bugu,"Don Ubanki Har ni zaki faɗama cewar ƴan uwanki ne!sun fini kusanci dake ne?Ko ciki ɗaya kuka fito tare dasu ne?
"Wlh mommy da ace ciki ɗaya na fito dasu dana fi kowa farin ciki,tun daga kan halayansu da ɗabi'unsu zai tabbatar maka da cewar mahaifiyarsu ta basu tarbiyyar daya dace,kuma ita mai kyakkyawar zuciyace shiyasa ƴa'ƴanta ma suka kasance masu kamar yadda take,Ni ce dai nayi babbar asara,dana fito daga jikin ki!gashi nan yanzu sai danasani nake....."kasa ƙarasa maganar tayi,a hanzarce ta watsa da gudu tabar ɗakin,saboda yadda taga Aunty babba ta tunkarota azafafe,yadda ranta ya 6aci ɗinnan komai zata iya aikatawa,
ƙafafunta ne suka fara yi mata raɗaɗi ba arziƙi ta koma daga gefen gadon ta zauna,idanunta sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai,zuciyarta sae faman tafarfasa takeyi mata,tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito waje,zama hayaam tayi daga gefenta,kowannansu yayi zuru zuru,
"Aunty laila!ni ina ganin kawai ki gudu batare da sanin kowa ba,in ba haka ba,inajiye maki tsoron abunda zai biyo baya,"
Cike da takaici Aunty babba tace"Hayaam naso ace hada Amani muka aikata wannan laifin,saboda banaso taci galaba akaina,yanzu in ishaq ya sake ni,ni kaɗae zanyi zawarci na,bakowa nafi jin haushi ba face hosana!mahaukaciyar banza,ina zaman zamana lafiya na,ta nemi tozarta ni agaban kannen mijina,wlh in har ta tona mun asiri,ni kuma sai nayi silar mutuwarta!!!!!!!!!!!!!!
"Dan Allah Aunty laila kidaina kira mana mutuwa,muji da abunda ke damun mu,duk yadda za'ae yanzu kada ki bari kuyi arba da hosana ɗin, yunwa nata cinsu,amma saboda gudun haɗuwarta da Omar ko Ishaq,yasa ta gaza ko ɗan leƙawa waje,
Bayan fitar Hafsat tashi suka yi suka zura Hijabs ajikinsu,sannan suka fito atare suka nufi ɗakin daddynsu,kamar yadda Sehrish ta basu shawarar su je su gaishe da daddynsu da Ammi da su hajiya Azeema,
Abusufyan na kwance saman gadonshi yaji ana knocking door ɗin ɗakinsa,miƙewa yayi tare da ajiye wayar hannunshi saman side drawer,ƙarasawa yayi yasa hannu ya buɗe ƙopar,zuba masu ido yayi yana kallonsu,sam baiyi tsammanin zai gansu ba,abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba sunsha hijabai ajikinsu,sae faman murmushi suke sakar mashi,
"My triplets"ya ambaci hakan tare da basu hanya don su shiga ciki,rufe ƙopar yayi bayan sun shiga daga ciki,
Saman gadonshi hosana ta haye,jahad da sehrish kuwa a ƙasa suka lankwashe ƙafafunsu suka zauna,
Wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana kallonsu,
"Ina kwana daddy,an tashi lafiya,"
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Lafiya lou my daughters,Nayi mamakin ganinku,waye acikinku ya bada shawarar azo agaishe ni ne"?yayi maganar yana kallon fuskokinsu,
Jahad ce ta nuna sehrish da hannu,
"Kinyi tunani mai kyau,dama yanzu nake shirin zuwa in taso ku,don muje ku gaishe da Modibbo,da Ammi da sauransu,abunda ya dace ne,kullum da safe ku dinga zuwa kuna gaishe dasu,"
Atare suka haɗa baki wurin cewa"In shaa Allah zamuyi hakan daddy,"
Juyawa yayi tare da kallon hosana dake kwance,hada rufe ido tana minsharin ƙarya,don yayi tunanin cewa bacci ne ya ɗauke ta,
Hannu yasa tare da jan kumatunta,nan take ta fashe da dariya,shima dariyar yayi kafin daga bisani,yace"ku tashi mu tafi ɗakin Ammin atare don ku gaisar da ita,
Saukowa hosana tayi daga saman gadon,ya ruqo hannunta dana jahad,suka jera tare suka fuce,
Suna tsaye a ƙopar ɗakin Ammi,sae ga Junaid,yana hangosu ya shiga sakin murmushin nan nashi,jiki na rawa ya nufi wurinsu,Gaisar da Abusufyan ya fara yi"Gm Uncle,"cike da zolaya Abusufyan yace"a haka zan baka auren ƴa ta?kana gaisar dani daga tsaye sai kace wani tsaranka ba wani respect"?jin haka yasa junaid saurin duƙawa ƙasa,sannan yace"Ina kwana Uncle"?
Dariya su kayi gaba ɗayansu,ganin yadda ya zuƙunna,
"Lafiya lou in law ɗina,ko kaifa,miƙe tsaye toh tunda ka ƙaraso sae mu shiga ciki atare,"mikewa yayi fuskarshi a washe,duk a tunanin Abusufyan junaid wasa yake yi masa yawan zancen zai bashi auren ɗaya daga cikinsu,baisan dagaske shi kamu yake yi ba
da sallama a bakunansu suka shiga cikin ɗakin,koda ammi taji muryoyinsu,da sauri ta kashe tabar da take zuƙa,ta sanya ta acikin Ashtray dake ajiye ƙasa,da ƙafarta ta tura shi ƙarƙashin gado,duk akan idon Abusufyan abun yaso ya bashi dariya,lallai Ammi ta kimtsu tunda har ta fara jin kunyar jikokinta su ganta tana zuqar sigari,
A saman carpet,kowannansu ya zauna tare da lankwashe ƙafa,Abusufyan ne ya fara gaisar da ita"Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya?Ya gajiyar tafiya"?
"Lafiya lou Alhamdulillah,"ta amsa mashi,Sannan su Jahad suka haɗa baki wurin miƙa gaisuwarsu,da murmushi a fuskarta ta shiga amsa masu ɗaya bayan ɗaya,a ƙarshe ta tsayar da idanunta kan Hosana tace"Kin tashi lafiya"?
Murmushi hosana ta saki tana faman noƙe kai tace"lafiya lou,"
Janye idonta tayi daga kan hosana ta mayar dashi kan junaid tace"Sarkin Murmushi,Angona nakaina naga kayi kyau sosai ka kuma ƙara haske,faɗamun menene sirrin"?
"Kishiya zanyi maki ne"yayi maganar yana murmura mata ido,ɗan waro ido waje tayi tare da cewa"Wacece ita"?
ɗagowa yayi yana kallonsu,Sehrish har sai da ya gano jahad sannan ya nuna ta da hannu yace"Gatanan,"
Ammi tace"Kin shirya yin kishi dani ko"?
Girgiza kai jahad ta shiga yi alamar a'a,
"To kaji bazata iya kishi dani ba,sai ka haƙura da auren gaba ɗaya,don ni bazan zauna da kishiya ba,"
"A'a wlh Ammi sai dai ki haƙura dani in aurota,"
Yadda yayi maganar ba ƙaramin dariya ya basu ba,don har saida suka dara,
Ammi tace"wato Ni zaka juya ma baya ko?saboda ka samu zankaɗeɗiyar budurwa sabuwa gal cikin leda,Ni kuma nayi maka tsufa,"gyaɗa kai tayi tare da cewa"bakomai na haƙura,"
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,mayar da idonta tayi kan Abusufyan"Yanzu ya ake ciki game da zancen Mahaifiyar yaran nan"?
Jin an sako zancen abu yasa shi gyara zama,sannan yace"Muna nan muna shirya waɗanda zasu je kano domin binciko gidan da suka zauna acikinsa,saboda muna sa ran zamu samu wasu muhimman bayanai a wurin makwabtansu,"
Jinjina kai Ammi tayi"hakan yayi kyau,banason a tsaya 6ata lokaci nafi son ayi komai tun da wuri don ba'a san halin da take ciki ba,"
"In sha Allah zamuyi hakan,daga nan suka miƙe tare da yi mata sallama suka wuce ɗakin Modibbo,ba ƙaramin daɗi yaji ba daya gansu,sun jima a wurinshi,kafin daga bisani suka wuce ɗakin gwaggon katsina,sun sha barkwanci a wurinta,daƙyar suka samu tabarsu suka fito,ɗakin hajiya azeema suka wuce,sun jima a wurinta suna shan fira,ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ɗakunansu kafin daga bisani,Lokacin yin breakfast yayi suka hallara gaba ɗayansu a dining,kowa saida yazo banda Sgr,saboda yasa ma ranshi cewar za'a kawo mashi ne har part ɗinsa,Azmee ce takai mashi,saboda Sehrish ta sanar da ita cewar,bazata samu damar kai mashi ba,tana so tabi Umarnin mahaifinta ne,
Lokacin da Azmee ta shiga part ɗinsa,yana daga kishingiɗe saman Sofa mai mazaunin mutun ukku,jikinshi na sanye da jallabiya,shigowa ciki tayi gabanta na faɗuwa don tasan cewa dole ya tuhumeta akan me ya hana sehrish zuwa,lalla6awa tayi ta ajiye masa tray ɗin a asaman table,gudun karya tuhumeta yasa tayi saurin ja da baya zata gudu tabar ɗakin,har takai baƙin ƙopar ɗakin tajiyo muryarshi yana fadin"ke zo nan,"dakatawa tayi da tafiyar hannunta dafe da saitin zuciyarta,jiki asanyaye ta dawo ta tsaya agabanshi,kwata kwata idanunshi na a lumshe,wayarshi na ajiye asaman wide chest ɗinsa,
dakyar ta iya cewa gani yalla6ai,
"Bana ce kar na sake ganinki a part ɗina ba da sunan aiki?ko bata faɗa maki bane"?
Shiru azmee tayi,tana faman zazzare ido,ranta ne ya bata cewar kawai ta sanar dashi gaskiyar zance,
Don haka tace"Sehrish ta sanar dani cewar bazata ƙara aiki a part ɗin ka ba...."tunkan ta ƙarasa maganar ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu,nan take azmee tasha jinin jikinta,
"Ita da bakin ta,ta faɗi hakan"?
Muryarta na kerma tace"Eh,
Ya kuma cewa"ta faɗa maki dalilin yin hakan"?
"Eh,tace tana son bin Umarnin mahaifinta ne,"
ɗan ciza gefen la66ansa yayi tare da cewa"its Okey,just leave........" da sauri azmee ta juya tare da kama hanya ta fuce daga part ɗin nasa,
Wuraren ƙarfe goma sha biyu modibbo ya shirya tafiya,Kanal yousouf ne tare dasu Irfan suka kai shi har Airpot ya hau jirgi,
Yinin Ranar Aunty babba na ƙumshe a cikin ɗakin Hayaam,tsoro ya hanata fitowa waje,da yunwa ta addabe ta Hayaam ce ta ɗebo mata abinci ta kawo mata a ɗakin,hosana kuwa kar take dasu,don taci alwashin sai ta tona masu asiri wurin daddynsu,da kuma Ya omar,
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,jin Cewa sgr bai nemeta ba,duk da ta damu akan son ganinshi,jurewa kawai takeyi,
A ranar Talal Da captain najeeb suka ƙaraso,murna a wurin ƴan uwansu kamar zasu haɗiye su don farin ciki,musamman junaid daya kasance rival ɗinsa ne ya dawo wato Talal,da yake shima autane a ɗakinsu Omar,
After 1 day
*Boss Bature*
Around 2:00 pm,
Zaune take a hakimce saman 2 seater,jikinta na sanye da turkish dress Riga da wando,a launin fata fara ce amma hasken nata hada na bleaching tayi 6au sosai,babbar mace ce a ƙalla zata kai shekara 35,gaba ɗaya idanunta na akan plasma tv din da take kallo aciki,yayin da hannunta ke ɗauke da cup na coffee,lokaci bayan lokaci take kur6asa,ta aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,wuyan kafarta na sanye da ziririyar sarƙa,sai faman karkaɗa kafar takeyi,Tana da manyan idanu dara dara,ga dogon hanci wanda ke manne da nose ring,kai kana ganinta zaka san cewar cikakkiyar ƴar bariki ce,
Jin ringing din wayarta dake ajiye asaman hannun kujerar da take ne yasa ta Ajiye cup din hannunta asaman madaidaicin table din dake a kusa da ita,sannan tasa hannu ta dauki wayar,hidden number ce aka kirata da ita,picking call ɗin tayi ta kanga wayar a kunnanta,cikin harshen fulatanci take magana,
Tana cikin yin wayar taga inuwar mutun tsaye akanta,ɗagowa tayi a hankali don taga wanene,sauke ajiyar zuciya tayi ganin Amrish ce,jikinta na sanye da uniform,ta goya school bag dinta a abayanta,dawowarta kenan daga school,fuskarta a ɗaure kwata kwata babu annuri acikinta,
Rejecting call ɗin tayi tare da ajiye wayar asaman sofa din,sannan ta mayar da hankalinta sosai akan Amrish,
"Welcome back my daughter,Am really glad to see u,"
Tayi maganar tana buɗe mata hannunwanta don tazo ta rungume ta,rai a6ace tace"Mommy na tsani ganinki wlh,banason ki,saboda baki da halin kirki,so kike ki kashe mun rayuwata da hannunki,"tana maganar hawaye na gangarowa akan fuskarta,
Maimakon ta nuna damuwarta akan hakan sai ma ɗan ta6e la66anta tare da cewa"Kamar yadda baki so na,Nima haka bana son ki,donni a tsarin rayuwata ban shirya haihuwa ba saboda bana son ƴa'ƴa don su takura ne,na samu cikinki batare dana shirya ba,babu yadda banyi ba don na zubar da cikin,amma ya liƙe ya nace sai ya zauna a mahaifata,a ƙarshe nayi deciding zuwa ƙasar waje a markaɗe mun shi,mahaifinki ya hana hakan,nayi takaici a wannan lokacin kamar nayi suicide,"
Hankalin Amrish ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abunda mahaifiyarta ke faɗi da bakinta,tuni wasu zafafan hawaye suka shiga wankowa a saman fuskarta,cikin shessheƙar kuka tace"ki faɗamun!Su wanene iyaye na!don ina da tabbacin cewar bake kika haife ni ba,"
Fashewa da dariya matar tayi yayin da take karkaɗa kafafunta,
Jin tayi banza da ita yasa ta daka mata tsawa tare da cewa"Mommy ki faɗamun su wanene iyaye na?In ba haka ba zan je na kashe kaina!"
Yunkurawa mommyn tayi tare da mikewa tsaye ta daddage ta kifa ma Amrish mari tare da cewa"Sai me idan kin kashe kanki!?wa kikayi ma asara!shashasha kawai,"
Fashewa da kuka Amrish tayi yayin da zuciyarta ke tafarfasa tace"Mommy yau ke da kanki kika mare ni"?
Dogon tsoki taja tare da cewa"Har kashe ki ma zan iyayi,Saboda kinyi mun tsawa,ko iyayena da suka haife ni basu ta6a gigin daka mun tsawa ba,balle ke ƴar dana haifa,idiot"
Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta ɗauki wayarta,sannan tabar falon tana fadin"kafin gobe in samu gawarki dan Allah,"tayi maganar cikin halin ko in kula,
Da gudu Amrish ta watsa,izuwa bedroom dinta dake a upstairs,datse ƙopar ɗakin tayi,bayan tayi wurgi da school bag dinta,ta shiga neman igiyar da zata shaƙe kanta don ta mutu,ganin bata samu ba yasa ta buɗe kopar ɗakin,ta fita,bada jimawa ba sai gata ta dawo cikin ɗakin hannunta dauke da insect powder,buɗe murfin tayi da sauri sauri ta daga robar tare da zazzagawa acikin bakinta,
Mommyn na acikin bedroom ɗinta,ta jiyo wata irin razananniyar ƙara mai rikitarwa,sakin wayar dake hannunta tayi,da gudun gaske ta fito daga bedroom ɗinta dake a downstairs,tamkar za tayi tuntu6e ta fadi kasa haka take gudun,lokacin da ta ƙarasa bedroom din Amrish,hannu tasa ta dinga bubbuga ƙopar tana faɗin"AMRISH!AMRISH!!baki da hankali ne,bakisan wasa ba,me kika aikatawa kanki!ba zaki zo ki buɗe mun ƙopa ba!!Amrish gaba daya duk tabi ta rikice,
Shiru amrish bata buɗe mata ƙopar ba,hakan yasa ta dawowa wurin window ɗin ɗakin ta buɗe ta don ta gane ma idonta,
A gigice ta fasa uwar ƙara tare da aza hannyenta asaman kanta tana fadin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!na shiga uku!!!!zubewa tayi ƙasa saman guiwowinta tana faman zabga kuka,hawaye jaga jaga a fuskarta,tana cikin wannan yanayin,taji shigowarsu Zeenat da sofia ƙawayen Amrish cikin falon gidan,mikewa tayi da sauri har tana tuntu6e ta saukko downstairs,tunkararsu tayi tana fadin"Nashiga uku!!Amrish ta kashe kanta!!bansan ya zanyi da rayuwata ba!!
Kallon juna sukayi hankalinsu a matukar tashe suka haɗa baki wurin cewa"Am...Amrish!!meya faru da ita!taya akai ta kashe kanta!!!
Kasa bude baki tayi don tayi masu magana,da hannu ta dinga nuna masu bedroom ɗinta,nan suka gane cewar tana acikin ɗakinta,da gudu suka nufi upstairs ɗin,itama tabi bayansu,nan fa suka shiga ƙoƙarin 6alle ƙopar ɗakin nata,
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋 Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
❤🤍❤
Daƙyar suka samu ƙopar ta buɗe nan suka same ta a kwance rai hannun Allah,wani irin ruwan kumfa kumfa ne ke fitowa daga bakinta,gaggawar ɗaukarta su kayi,su biyu suka cuccu6eta sai cikin motar Mommyn,da kanta tayi driving ɗin motar,yatsun hannunta nata kerma tana yi tana dan bugun steering,Su zeenatu kuwa dake a back seat na motar,sae kuka sukeyi suna jijjigata don karta mutu basu isa asibitin ba,
Suna ƙarasawa asibitin,da sauri suka cuccu6eta suka shiga da ita mommyn na fadin"Emergency pls doc,nurse....!"reception Nurses ne suka kar6eta da sauri da sauri suka shiga da ita ɗaki,anan aka kwantar da ita,doctors suka taru a kanta.
Zama sofia da Zeenatu su kayi asaman waiting seat,yayin da Mommyn Amrish ke ta faman zarya a corridor din,jikinta sai faman kerma yake yi,sam bata ta6a tunanin cewa Amrish zata iya yunkurin kashe kanta ba sai yau da ta tabbatar mata,tasha faɗin cewa zata kashe kanta in bata faɗa mata wanene mahaifinta ba,bata ta6a ɗaukar abun serious ba,sae yau,ta tsorata da irin hukuncin da Amrish ta yanke wa kanta,
"Mommy wai meya faru ne?Nasan cewa Amrish bazata ta6a yunƙurin kashe kanta ba,batare da anyi mata wani abu daya 6ata mata rai ba!"
Zeenat ce tayi maganar,yayin da idanunta ke fitar da hawaye,
"Ni banyi mata laifin komai ba,kan dai maganar nan ce da take yawan faɗamun na cewar ta tsane ni bata sona,in faɗa mata su wanene iyayenta ko ta kashe kanta,ta 6ata mun raine yau saboda tayi mun tsawa shiyasa na kwashe ta da mari sannan nace taje kafin gobe in samu gawarta,shine fa ta fusata har ta aikata hakan,"
Cikin shessheƙar kuka zeenat tace"meyasa ba zaki iya lallashinta ba?saboda me zaki sa hannu ki mare ta?kuma kika furta mata cewar taje ta kashe kanta bayan kinsan cewa ita yarinyace ba wayau tacika ba,yanzu gashinan kinja zamu rasa ta gaba ɗaya"cike da takaici Zeenatu ta ƙarasa maganar tare da komawa saman waiting seat ɗin ta zauna tare da kifa kanta saman laps ɗinta tana cigaba da matsar kwalla,hannu sofia tasa tana ɗan bubbuga bayanta,ɗagowa tayi da idanunta waɗanda suka rune jawur dasu,daƙyar ta iya buɗe baki tace"Mommy yakamata ki sanar da yayanta halin da ake ciki,tun kafin rai yayi halinsa,"
A tsananin tsorace Mommyn tace"bazan sanar da kowa ba,idan ma ta mutu bazan bari wani ya sani ba,guduwa kawai zanyi in yaso daga baya sunji labari,don wlh bazasu ƙyaleni ba,"
"Saboda me kika ce haka mommy"?
"Zeenat mubar zancen kawai,ni kaɗai nasan halin da nake ciki,"tayi maganar tare da kifa kanta jikin bangon da take tsaye,
Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,
"Amma mommy meyasa kike 6oye mana abubuwa da dama game da Amrish?har yau bamu ta6a ganin mahaifinta ba,bayan wannan bamu ta6a ganin wani acikin dangin ku ba,sae mutun ɗaya kawai,yayanta dake zuwa wurinta ...."
Kasa ƙarasa maganar tayi saboda ganin irin juyowar da mommyn Amrish tayi a ruɗe,la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"Kar na kuskura na ƙara jin kinyi mun wannan maganar!baida amfani sanin wanene mahaifin Amrish!Ni ɗin nan ni ce Mahaifinta kuma ni ce mahaifiyarta!!
Shiru sofia tayi,batare da ta ƙara cewa Komai ba,,,,,,,,
Ranar dae A asibiti suka yini har dare ya ritsa dasu,
*Boss Bature*
❤🤍❤
Fitowarsa kenan daga cikin toilet jikinshi na sanye da bathrobe,hannunsa kuma na ruƙe da short towel yana ɗan matse sumar kanshi,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga jikinshi,tamkar wanda aka tsamo daga ruwan turare,saboda ƙamshi,gaban dresssing mirror ya tsaya yana ƙarasa tsane sumar kan tashi,ɗan dakatawa yayi tare da wurga eye balls ɗinsa ta cikin mirror yana kallon Shimfiɗeɗen gadonsa,bedsheet ɗin duk yayi squeezing,ga blanket ɗinsa dake a cukurkuɗe saman gadon,komai ya hargitse ba don komai ba sai don rashin mai gyara,2 days kenan ba'a gyara mashi part ɗinsa ba,a ƙa'ida duk rana sai an canza mashi bedsheet da Blanket amma yau har 2 days ba'a musanyasu ba,mutun ne shi mai tsaftar gaske,ga ƙyanƙyami,gashi ko kaɗan baijin zai iya ɗaga yatsanshi da sunan zai gyara bed ɗin nasa,ba don komai ba,sae don saboda kasancewar shi mutun mai matuƙar Ji da kanshi,a wurinshi wannan tamkar ƙasƙanci ne da matsayinshi ya zuƙunna da sunan zai gyara bedroom ɗinsa,tamkar ƙaskanci ne namiji yayi aikin da mace ya dace tayi shi,ko ba don wannan ba shi tun yana yaro ko tsinke wannan acikin gida kawar masa shi akeyi,sam bai iya aikin gida ba,wanka ne kawai yakeyi ma kanshi,amma da zarar ya fito daga toilet akwai masu taimaka mashi wurin yin dressing na Outfits ɗin da zaisa,
Yana cikin tsayuwar nan,Yaji sallamar Azmee daga cikin palour ɗinsa,bai amsa mata sallamar ba,hannu yasa tare da ɗaure igiyar Bathrobe ɗinsa sosai,sannan ya juya tare da nufar ƙopar fita daga bedroom ɗin,adai dai bakin ƙopar ya tsaya tare da goya hannayenshi asaman wide chest ɗinsa,
Azmee kuwa tunda taga ya fito gabanta ya shiga faɗuwa,dama zuwa tayi don ta gyara mashi part ɗinsa,
"Where's she"? Ya tambaya batare da ya aza eyes ɗinsa akantaa ba,
Tunda ya ambaci hakan ta gane cewa akan sehrish yake magana,don haka tace"Tana a bedroom ɗinsu,"
"Okey,call her right now,"
Yayi maganar cike da bada Umarni sannan ya juya tare da shigewa cikin bedroom ɗinsa,.
Juyawa Azmee tayi da sauri ta fuce daga part ɗin nasa,downstairs ta saukko kai tsaye ta nufi ɗakinsu Sehrish,hannu tasa tare da knocing ƙopar,a lokacin duk sunyi nisa acikin baccinsu,can cikin bacci Sehrish taji bugun ƙopar ɗakin nasu,buɗe idanunta tayi a hankali sunyi mata nauyi saboda wani irin bacci da take ji,jikinta a kasalance ta yunƙura daƙyar ta sauko daga saman gadon ta buɗe ƙopar tana tambayar wanene,
Tunda taga Azmee taji gabanta ya faɗi rass,duk da batasan meya kawota ba,
"Aunty azmee lafiya?tayi tambayar tana yin hamma,
Azmee tace"ina fa lafiya,Sgr ne ke son ganin ki,yace in kira mashi ke yanzun nan"
Daram taƙara jin gabanta ya faɗi,"nashiga uku ni yau,"ta faɗi hakan tana yarfa hannu,
"Yakamata kiyi sauri kije tun kafin ya hasala,don da alama yau ranshi a 6ace yake,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta bar ƙopar ɗakin nasu,
Jiki a sanyaye sehrish ta koma cikin bedroom ɗin nasu,gaban wardrobe taje,ta buɗe ta ɗauko mayafi ta yafa shi asaman kanta,kayan bacci ne ajikinta,
Fitowa tayi daga ɗakin,ƙafarta na sanye da slipper,tana tafiya cike da zullumin me zai biyo baya,ba komai take hangowa ba face tafin hannun Sgr,ya wanka mata mari,har runtse ido takeyi saboda ganin abun take kamar dagaske,tana ƙoƙarin giftawa ta babban falon ta wuce sama,kwatsam Abusufyan ya fito daga bedroom ɗinsa ya hango gifcinta,tsayawa yayi yana ƙare mata kallo daga inda yake,jinjina kanshi yayi tare da lalla6awa yabi bayanta,cikin sanɗa batare da ta sani ba,
Hayewa tayi saman stairs ɗin,sannan ta wuce part ɗinsa,bakinta ɗauke da sallama ta shiga ciki,babu kowa a falon nasa,tsayawa tayi a tsakiyar Sofas ɗin,don bazatayi gangancin shiga bedroom ɗinsa ba,ƙwara daganan idan taga ya harzuƙa ta watsa da gudu,amma in can ciki ne zai iya kama ta,
Tana cikin tsayuwar nan zuciyarta na ɗar ɗar,taji motsinshi da sauri takai idanunta kan ƙopar bedroom ɗinsa,gabanta ne ya faɗi rass ganin shi a tsaye,hannunshi ɗaya ruƙe da waist ɗinshi,yayin da yake sanye cikin sleeping dress white color ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,Amma fuskar nan fa babu annuri ko misƙala zarratin,
Da hannu yayi mata alamar tazo,hakan yasa ta nufi wurinshi ɗan nesa dashi ta tsaya sannan tace"Gani,"
Hakan da tayi ba ƙaramin 6ata mashi rai yayi ba,maimakon tazo kusa dashi saita tsaya nesa dashi,
"Ni kike so in ƙaraso inda kike"!?
Girgiza kai tayi alamar a'a,jinjina kanshi yayi tare da matsa mata hanya yace"shiga ki gyara mun bedroom ɗina,"
kasa motsawa tayi saboda alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta na cewar bazata ƙara zuwa part ɗinsa ba,da sunan yin aiki,saboda umarnin mahaifinta,
Ja da baya ta ɗanyi tare da girgiza mashi kai gabanta na faɗuwa ga tsoro amma ahaka ta daure ta cije tace"daddy ya hanani,"
Wani irin kallo da yayi mata ita kanta saida ta girgiza,tausasan la66ansa har kerma sukayi wurin furta"Ni kike faɗama cewa Daddy ya hanaki"?
..shiru tayi tana faman zare ido,hakan ya ƙara fusata shi,gadan gadan ya tunkarota,ƙoƙarin juyawa tayi amma ina kafin tayi wani yunƙuri tuni ya ruƙo mayafinta nan take ya zame ƙasa,kwakkwaran damƙa yayi ma gashin kanta,hakan yasa tayi screaming saboda Zafin da taji,
Jijjiga kan nata yayi,tamkar wata Ƴar babyn roba haka ya ɗaga ta gaba ɗayanta da hannu guda,kuma ta hanyar gashin kanta daya damƙa,wutsil wutsil tashiga yi da ƙafafunta,hawayen azaba na gangarowa akan fuskarta,fashe mashi da kuka tayi muryarta na rawa ta shiga faɗin"Wayyo Allah na!Babban yaya dan Allah kayi haƙuri ka sauke ni ƙasa,wlh bazan ƙara ba,zan gyara maka ɗakin,'
Zuba mata ido yayi yana kallonta tun daga ƙasa har sama,wata ƴar ƙarama da ita,mamakinsa a ina ta samu ƙwarin guiwar gaya masa magana batare da jin shakkarshi ba,
"Babban yaya dan Allah ka sauke ni!Wayyo Allah da.. daddy,nashiga uku,zai kashe ni,gashin kaina zafi,zai cire mun gashina,"saboda tsabar kuka hada majina,fuskarta tayi jaga jaga da hawaye,sai da ta galabaita sosai sannan ya saki gashin kan nata,gaba daya ta zube saman guiwowinta saboda jikinta da ba ƙwari,
Zura hannayenshi yayi acikin aljihun dogon wandon dake ajikinsa,sannan yace"Tashi ki shiga ciki,ki gyaramun bedroom ɗina"
Jikinta na kerma ta miƙe da sauri da sauri ta tunkari ɗakin nashi tana faman shessheƙar kuka,tana ɗaga ƙafarta zata shiga ɗakin taji an dakatar da ita,
"Karki kuskura ki shiga ɗakin nan"!!!! Rass taji gabanta ya faɗi jin Muryar daddynsu,a firgice ta juyo don ta shaidawa idanunta,
Shigowarshi kenan cikin palourn yayi maganar,a wani sukwane Sgr ya wurga eye balls ɗinsa akanshi,takawa yayi har zuwa gabanshi ya tsaya suna Facing ɗin juna,sannan yace"meyasa kake son takura rayuwarta ne?yarinyar nan ba ƴar aiki bace,ƴata ce!kuma ni ne na bata Umarnin cewa ta daina aiki acikin gidan nan!akan me kakeso ta fifita Umarninka akan na mahaifinta?matsayinmu ɗaya ne a wurinta ne"?
Wannan maganar ta Abusufyan ba ƙaramin Fusata shi tayi ba,Yadda kasan zaki haka ya shiga fitar da huci ta hancinsa,ya ma rasa amsar da zai ba Uncle ɗin,saboda zuciyarshi da ta hasala,don har bugu zai iya kai mashi,muryarshi na kerma yace"Un...cle!Are u telling me dat matsayinmu ba ɗaya ba a wurinta!"jinjina kanshi ya shiga yi yana fama ciccije la66ansa,ran manya ya 6aci,yaci gaba da cewa
"Of course our position is not the same,but she's my younger sis,ina da right ɗin da zan sanyata aiki tayi mun,why kake so kajamin raini a wurinta"! daƙyar voice ɗinshi ke fita saboda tsabar 6acin rai zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi,
"Ba raini nakeso naja maka ba a wurinta!tabbas ƙanwarka ce ita halak malak,kuma kana da ikon da zaka sanyata abu tayi maka,wannan gaskiya ne,amma Ni mahaifinta na hana haka!ban amince ba,tayi aiki a ƙarƙashin kowa ba,Azmee itace mai aikin gidan nan!ita yakamata ace tana yin duk wani aikin daya dace,idan ma Aikin azmeen ke baka so,Zan iya sawa a ƙaro wasu masu aikin da zasu rika yi maka,amma ba ƴa taba,saboda ita ba ƴar aiki bace......"tunkan ya ƙarasa maganar Sgr ya daka mashi wata irin gigitacciyar tsawa,a tsiwace yasa hannu tare da toshe ears dinsa yana faɗin"ENOUGH!Enough!banason ji,banaso,she must execute my Command,that's may final say" ya karasa maganar yayin da idanunshi ke aruntse ruff ya rufesu
Abusufyan yayi ma tsawar,amma gigitar da sehrish tayi,tamkar zata zauce,ƙanƙame jikinta tayi,cike da fargaba,
Zuba mashi ido abusufyan yayi yana kallonshi,a hankali ya zame tafin hannayensa daga toshe kunnuwansa da yayi,a hankali ya ɗan ware blue eyes ɗinsa,tare da juyawa ya kalli wurin da Sehrish ke tsaye a ƙopar ɗakinsa yace"Wuce ciki ki gyaramun bedroom ɗina"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,wannan ƙarfin halin na Sgr ba ƙaramin mamaki yaba Abusufyan ba,a tsananin tsorace ta wurga idanunta kan daddynsu don taji me zaice,
"Karki kuskura ki sanya ƙafarki a ɗakin nan!idan har na isa dake"!!wannan shi ake kira da tashin hankali,zazzare idonta tayi tana kallonsu,ta rasa Umarnin wa zata bi,A zarihi dae tafi tsoran Sgr,a baɗini kuwa tafi son tabi umarnin mahaifinta saboda sanin matsayin da yake dashi a wurinta,sa6a mashi zai iya haifar mata da gagarumar matsala a rayuwarta,haka zalika sa6ama sgr ba ƙaramar matsala zaija ma kanta ba,ta rasa inda zata tsayar da kwayar idonta,idan ta kalli Sgr sai ta kalli abusufyan,kowannansu ita yake kallo,daga ganin fuskar Abusufyan zaka san cewar hankalinsa ba a kwance yake ba,babban abunda yake fargaba shine Sehrish taƙi bin Umarninsa,duba da yadda ta gaza motsa jikinta,tabbas zai kunyata sosai kuma darajar da yake da ita ta mahaifinta zai zube ne a idon sgr,zai cigaba da ganin kanshi ne amatsayin Sarki,wanda ke bada Umarni kuma dole abi,
Wata irin tsawa sgr ya daka mata,wadda har sai da jikinta ya girgiza sosai tabi ta rikice,a fusace yace"won't u go in!"
Yana rufe bakinsa,Abusufyan yace"idan har kika kuskura kika shiga ciki,zan yafe ki ne acikin ƴa'ƴana,babu ni babu ke!"
Jin wannan maganar yasa ta fashe da matsanancin kuka,baiwar Allah tana a cikin tsaka mai wuya,yarfa hannunta tashiga yi tana faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un Ya Allah ka kawomun ɗauki!daddy!!babban yaya!!bansan ya kukeso inyi da kaina ba!!dan Allah ku ƙyale ni!kubarni in ba haka ba zuciyata zata iya bugawa in mutu,"
Tuni jikin Abusufyan yayi wani irin sanyi,idanunshi suka cika tab da hawaye,tsananin tausayinta ne ya kamashi,kamar yaje ya rungumota ajikinshi ya lallasheta,Amma yaci alwashin cewa bazai ta6a bari Sgr yaci nasara akanshi ba,
A 6angaren Sgr kuwa,ya gama hasala tunda yake a rayuwarshi bai ta6a bada umarni aka tsaya yi mashi jayayya ba sai yau,sau ɗaya yake bada command kuma dole abi batare da anyi mashi musu ba,runtse idanunshi yayi tare da tura yatsun hannayenshi cikin sumar kanshi yana cakuɗata,yayin da yake ɗan cizon lips ɗinsa,wani irin huci ke fita daga hancinsa,wannan ɗabi'arsa ce aduk lokacin da ranshi ya 6aci sosai,steps uku ne matakin hauhawarshi,idan yakai step na ƙarshen the most dangerous kenan don tamkar aljani yake komawa kuma kowaye gabanshi bai gani tamkar makaho yake komawa,a wannan step ɗin idan ya damƙi mutun a hannunshi yana bugunshi sae yaga gawarshi,kuma babu mai iya control ɗinsa har sai lokacin da Allah yasa zai dawo hayyacinsa,amma zaiyi wuya yakai wannan step ɗin sai in ya damƙi mai laifi zai hukunta shi,iya step na biyu yake tsayawa,mataki na farko shine zaka ga yana huci yana zagaye wuri,na biyu kuma Shine yake cizon la66ansa sosai,ya runtse idonshi ya kuma cusa yatsun hannunshi acikin sumar kanshi yana faman sakin huci tamkar mayunwacin zaki,
Jini ne ya shiga ɗiɗɗigowa daga saman pink lips ɗinsa hakan ba ƙaramin tayar ma sehrish da hankali yayi ba,ita da bata saba ganin yana yi ba,Abusufyan kuwa hankalinshi kwance saboda yasan sgr sarai tun yana yaro yasan shi da wannan baƙar zuciyar,idan ya cije la66ansa har sai ya fasa su,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shessheƙar kuka tashiga cewa"Dad..ddy dan Allah ka ce mashi ya daina,yana fasa la66ansa da kanshi,!"Shi yake fasa la66ansa amma raɗaɗin ita take jinshi ajikinta saboda tsabar ƙaunar da takeyi mashi,
Da wata irin murya ya kuma cewa"ki wuce ciki nace,karki bari na ƙara maimaita maki hakan!" saboda tsabar ruɗu ta juya zata shiga ɗaƙin,aikuwa abusufyan ya daka mata tsawa,a ruɗe ta juyo tana kallonshi yayin da hawaye ke fita a idanunta,hanya ya nuna mata da hannunshi yace"Zoki wuce"
A tsorace take kallon Sgr wanda idanunshi ke arufe,sosai ya runtse su,ganin haka yasa tayi tunanin watsawa da gudu tabar ɗakin don tabi Umarnin mahaifinta,tasan cewa kafin ya buɗe idanunshi tabar falon,
Daddagewa tayi da gudun gaske ta watsa aguje ta nufi hanyar fita daga falon,sae dai ina kafin ta ankara sgr ya zabura a hargitse yabita,abusufyan na ƙokarin taroshi aikuwa yayi wurgi dashi gaba ɗaya,yayi gefe guda ƙasa,A zafafe ya damƙi waist ɗinta,wani irin ruƙo yayi mata ruƙo bana wasa ba,ya ɗaɗɗagota sosai ya manna ta da jikinshi,bedroom ɗin shi ya nufa da ita,wannan ƙarfin halin har ina,ran abusufyan ba ƙaramin 6aci yayi ba,miƙewa yayi da sauri ya tari Sgr kiciniyar kwace Sehrish ya shiga yi da hannunshi,nan fa suka kacame ma juna,
"Subhanallahi me nake gani haka"!!muryar Abba ce ta karaɗe kunnuwansu,gaba ɗaya suka juyo kowa na huci suna kallonshi,a lokacin Sgr ya saki sehrish daga hannunshi,da gudu ta miƙe tana kuka,ta nufi wurin Abba,gaba daya ta faɗa jikinshi,rungumeta yayi yana ɗan bubbuga bayanta,yayin da idanunshi ke akan Sgr da Abusufyan,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,yadda sgr ya manta wanene abusufyan a wurinshi,har yake ƙoƙarin yin dambe dashi,hauka maganinka Allah,
"Abusufyan da hankalinka kake kokoyi da Rafayet kamar wasu tsararrakin juna?duk akan menene kuke wannan faɗan"?
Yayi tambayar tare da mayar da idanunshi kan Sgr wanda ke tsaye har lokacin sama yake bai sakko ba"Rafayet ka bani mamaki!ka rasa dawa zakayi dambe sae Kawunka,ƙanin mahaifinka!Anya baka fara shaye shaye ba?nafara zarginka," afusace ya juya tare da shigewa cikin bedroom ɗinshi yaja ƙopa ya rufe,
"Bansan me rafayet ya ke ɗaukar kanshi ba,Taya zan ba yarinya umarni A matsayina na mahaifinta sannan yace dole saita take umarni na don tabi nashi?saboda haka fa ya ke ƙoƙarin buguna sai kace wani tsaransa"da alama ran abusufyan ya 6aci sosai,yana maganar yana nufo inda su Abban suke tsaye shi da sehrish,hannunta na ruƙe cikin na abban,wani irin zazza6i ne ya rufar mata mai zafin gaske,ga ciwon kai mai tsanani da take fama dashi,duk don saboda tashin hankalin da suka jefa ta ciki,kuma har lokacin kukan take yi,
Sam Abba baiji daɗin abunda ya faru ba,"kayi haƙuri Abusufyan abunda yayi bai kyauta ba,duk da ba laifinsa bane irin rayuwar da aka saba mashi da ita kenan tun yana yaro,komai yi mashi akeyi,kuma in ya bada Umarni bi akeyi duk don tsoran kada ranshi ya 6aci,"
Gyaɗa kai kawai Abusufyan yayi tare da cewa"babu komai,Ae nasan halinshi sarai shiyasa banji zafin abun sosai ba,inayi mashi uziri ne,"
Ya ƙarasa maganar tare da kallon sehrish wadda ke ta faman matse kwalla,suna haɗa ido dashi ta sunnar dakai ƙasa,
"am really sorry my daugher,banyi hakan don na 6ata maki rai ba,"
Cikin shessheƙar tace"Ammm..ma daddy,cewa fa kayi zaka yafe ni acikin ƴa'ƴanka,idan har nabi umarninsa,"
Murmushi ya ɗan saki akan fuskarshi kafin yace"wasa fa nake maki,banda hankali ne,ae koda ace kin bi umarnin nasa bazan faɗi hakan ba,zan dai ji ɗaci araina,na faɗi hakan saboda ina gudun ki ƙi bin Umarni na,"
"Daddy nidai banason wannan wasan,dan Allah kada ka ƙara faɗamun hakan," yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya yaso ya basu ba,don har sai da ta bubbuga ƙafafunta ƙasa,don ya tabbatar da cewar bataso,
"In sha Allah bazan ƙara ba,kinyi haƙuri ko"?
ɗaga mashi kai tayi alamar Eh,
"Wato kun sasanta tsakaninku,ni kuma kun barmun yaro na,cikin wani hali ko"?Abba ne yayi maganar cikin zolaya,hada ɗaure fuskarshi,
Abusufyan yace"Yaya ai kai kaɗai kasan yadda zaka shawo kanshi,don yanzu duk wanda yayi gigin zuwa wurinshi,ba ƙaramar matsala za'a samu ba,"
Murmushi Abba yayi kafin yace"Shikenan zanje in lallashi abuna,kai kuma kaja ƴarka ku wuce ku bamu wuri,"
Hannun Sehrish Abusufyan ya ruƙe,tare da janta suka bar part ɗin yana dariya,
A bakin ƙopar bedroom ɗinsa ya tsaya cike da zullumin taya zai shawo kan sgr,hannu yasa yayi knocking ƙopar,shiru Sgr bai buɗe masa ƙopan ba,hannu yasa ya ƙara knocking ɗin ƙopar yana kiran sunanshi"Rafayet!ka zo ka buɗe mun ƙopa,inason magana dakai,"shiru bai ji motsinshi ba,babu alamun zai buɗe masa ƙopar,kwantar dakai abba yayi ajikin ƙopar cikin lallashi ya soma magana"haba rafayet ɗina,ni fa ne abbanka,so kake yau in gaza runtsawa?idan har bakazo ka buɗe mun ba anan zan kwana,"ya ƙarasa maganar tare da zuƙunnawa ƙopar ɗakin nashi,abu kamar wasa ya fara gyangyaɗin bacci,duk in ya ɗan farka sai ya ambaci sunan Shi Rafayet ka buɗe mun ƙopa,so kake na kwana anan?
Duk wannan surutan da Abbansu ke yi kaf a kunnan sgr,wanda ke zaune saman front chair na dressing mirror ɗinshi,ya kifa kanshi asaman Dressing mirror,gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi side by side na fuskarshi,zuciyarshi ba ƙaramin tafarfasa take mashi ba,ranshi yayi mugun 6aci wai har shi zai bada Command aƙi bin umarninsa?bakowa yafi ji ma haushi ba fa ce Uncle ɗin nasu,don me zaiyi iko da Sehrish?saboda kawai ya haifeta?wani irin huci ne ke fita akanshi tabbas sai ya nemi matsayin dake asama dana mahaifinta ba don komai ba sai don yayi iko da ita,akan idon mahaifinta kuma,
Yana cikin yin wannan zancen zucin yaji Muryar Abbansu kamar ta wanda yasha giya,saurarawa yayi yana sauraron waƙar da Abbansu ke rera masa daga waje,tun yana yaro idan aka 6ata mashi rai,ya fusata da gudu yake shiga bedroom ɗinsa ya rufe ƙopa,idan abbansu naso ya sauko daga fushin da yake yi sai yazo ƙopar ɗakinshi yana kwankwasawa yana raira masa waƙa,cikin ƙankanin lokaci yake saukowa daga wannan fushin,
Jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,ɗan ɗagowa yayi da kanshi ya wurga eyes ɗinshi kan agogon bangon dake a manne ƙarfe kusan ɗaya na dare,Abbansu na waje yaƙi tafiya,kuma in har bai buɗe mashi ƙopar nan ba,to anan wurin zai kwana,saboda ya ta6a yi mashi haka,miƙewa yayi jikin shi babu ƙwari ya ƙarasa tare da jan ƙopar ya buɗe mashi,jin an buɗe ƙopar yasa Abbansu miƙewa jiki na rawa,suna haɗa ido da sgr,yasa hannunshi a idanunshi yana yi mashi kukan ƙarya wai ya barshi a waje,sanyi ya bugeshi,hakan da yayi ba ƙaramin dariya yaso ya ba Sgr ba,
Juyawa Sgr yayi tare da shigewa cikin bedroom ɗin,abban yabi bayanshi,a gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna,
"Yanzu faɗamun,me yake damunka"?
Shiru ya ɗanyi tamkar bazai tanka masa ba,daƙyar ya iya buɗe bakinshi yace"Abba,Uncle ya gama dani!har ni zan ba yarinyar can Umarni,ya hanata,don kawai yana taƙamar cewar shi mahaifinta ne"?yana magana muryarshi na shaƙewa saboda tsabar 6acin rai,
"Rafayet!ni bansan me zance maka ba,ka san dai inason farin cikinka,duk wani abu da kake so ni mai iya yi maka shi ne,amma banda wannan!zan iya iko da Abusufyan amma bazan iya iko da ƴarsa ba,shi mahaifinta ne dole tabi Umarninsa tayi mashi biyayya,bijire mashi zai iya sa ta fuskanci matsala arayuwarta....."
Bai ƙarasa maganar ba Sgr yace"That means ba wanda ya isa yayi iko da ita sai shi kawai?kenan Ni bani da wani matsayi a wurinta?bamu isa mu sata abu ba tayi kenan?
Jinjina kai abbansu yayi tare da cewa"Hakane!maganar gaskiya babu wanda ya isa yayi iko da ita a halin yanzu bayan mahaifiyarta sai kuma shi"
"Abba babu wani sama dasu wanda zai iya iko da ita fiye da mahaifanta"?yayi maganar ranshi a ɗan 6ace yana kallon Abban nasu,
Gyara zama abbansu yayi,fuskar nan tashi ɗauke da wani 6oyayyen murmushi yace"duk duniyar nan bayansu mutun ɗaya ne!wanda zai iya yin iko da ita,fiye da iyayenta!'
"Wanene shi"?ya tambaya Yana jiran jin amsar da Abban nasu zai bashi,
"MIJINTA,shine wanda zai iya yin iko da ita fiye da iyayenta!Mahaifinta zai iya kiranta tazo gida mijinta ya hana,kuma dole ta hanu,ko tana so ko bataso,"
Hannu Sgr yasa tare da dafe gefen kanshi,yana faman sauke ajiyar zuciya,muryarshi ƙasa kasa yace"Abba!babu wata hanyar sai wannan"?
Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa"that's the Only solution,"!
Ya ƙarasa maganar yana kallon fuskar SGR,Acikin zuciyarshi kuwa Allah Allah yake akan ya amince zai auretan,Shikenan burinshi zai cika ganin cewa Rafayet yayi aure,
"She's too young for me,Ni bazan iya auren yarinyar da ko Secondry school bata kammala ba,wannan abun kunya ne agare ni,da matsayi na in aureta?da wani ido duniya zata kalleni"?
Zuru Abbansu yayi yana sauraronshi,wato Sgr har yanzu yana nan da wannan ji da kan nashi,
Hannu Abbansu yasa tare da dafa shoulder ɗinshi sannan yace"Rafayet!nima ban goyi bayan hakan ba!idan har ka aureta girmanka zai faɗi ne!Amma ga wata shawara"?
ɗan ɗagowa yayi da idanunshi masu ɗauke da bacci ya kalli abban nasu"Wane shawara ne wannan"?muryarshi a akasalance yayi maganar,
Abba yace"Me zai hana kuyi auren yarjejeniya atsakaninka da ita yarinyar"?
"Kamarya kenan"?
Ƙayataccen murmushi Abbansu ya saki yana kallonshi kafin ya ɗaura da cewar"Wata nawa ya rage maku ku koma U.S"?
"Remain 3 Months,"ya bashi amsa,
Abba yace"Yawwa,before 3 months ɗin nan su cika,me zai hana ka aureta,a matsayin Contract marriage,don tayi maka aiki kawai na tsawon wata uku,kamar yadda kake so da zarar time ɗin ya cika,kawai saika bata divorce letter ɗinta,Amma ya kake gani"?
Shiru Sgr ya ɗan yi yana nazarin maganar Abban nasu,kafin yace"Abba bacci nake ji,i will think about it before tomorrow,"
"Ba damuwa,kafin gobe dae yakamata kayi tunanin abunda ya dace,zan jira jin amsarka da safe," ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya fuce daga ɗakin nashi,
Blanket ɗinsa yaja ya lullu6e jikinshi har zuwa neck ɗinsa,maganar Abbansu ce ke tayi mashi yawo acikin kanshi,ga bacci yana ji amma yaƙi ɗaukarsa,sae faman juyi yake yi asaman gadon,tabbas in ya aureta zaici galaba akan Uncle ɗinsu Abusufyan,yana so ya dinga commanding ɗinta akan idon mahaifinta kuma ba yadda zaiyi dashi,na biyu kuma Yana so yarinyar taci gaba da aiki a ƙarkashin ikonshi,har zuwa lokacin da zai koma U.S!!idan har yana so hakan ya faru kenan dole sai ya aureta!?OMG!
"That could not be possible for me as a Surgeon General to marry a young girl who has not even finished her secondary school,"ya furta hakan tare da jan blanket dinsa ya rufe fuskarshi daƙyar bacci 6arawo yayi awon gaba dashi,
*Boss Bature*
Saukowa down abba yayi fuskar nan tashi ɗauke da murmushi,anan ya samu abusufyan tsaye yana jiranshi,yana ganin ya tunkare shi,
"Ina sehrish ɗin take ne"?
Abusufyan yace"Tun ɗazu ta wuce ɗakinsu,Nima kai nake jira muyi sallama kafin inje in kwanta,Amma ya kuka ƙare da rafayet ɗin?ina fata dai ya sauko daga fushin nan nashi"?
Fuskar abba ɗauke da murmushi yace"daƙyar na shawo kanshi,yanzu haka ma ya kwanta,sae kayi haƙuri da surukin naka,"
Dariya abusufyan yayi kafin yace"ae ni bansan ya zamu ƙare da rafayet ba,lamarin ya fara bani tsoro,ƙoƙarin buguna fa yake yi ne?ahaka zan zama surukinsa?yana yi mun kallon tsaransa?Lokacin dana shiga ɗakin nasa samun shi nayi fa ya damƙi gashin kanta ya ɗaga ta sama kamar wata ƴar babyn Roba,yarinya sae kuka take tana bashi haƙuri amma ko ajikinshi,"
Abba yace"Ae rafayet sae addu'a,amma abun nashi ƙara gaba yake yi,yana ji Da ƙarfin nan nasa,bakowa zai iya jure zama dashi ba," suna tafiya suna fira har suka zo ƙofar ɗakin Abba,anan su kayi sallama da abusufyan ya wuce nashi ɗakin,
Fuskarshi a washe ya shiga ɗakin kamar ance ya ɗaga idanunshi karaf suka sauka akan Junaid dake baje saman gadon yana bacci,ga Mommynsa agefe,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,daga fitarsa har ya shigo ɗakinshi,Anya kuwa junaid shi kaɗai ne?yaro kamar mai iska,har leƙa ɗakinshi yayi ya same shi kwance yana sharar bacci shi da Talal,amma yanzu daga dawowarshi ya same shi a ɗakinshi,
Cike da takaici ya shiga cikin ɗakin,gefen gadon ya zauna tare dasa hannu ya bubbugga ƙafarɗarshi""Junaid!junaid"! Da ƙarfi yake ambaton sunan nashi,yatsina fuska junaid ya shiga yi yana faɗin"Wai wanene ke son takuramin"!
Yayi maganar yana ɗan ware idanunshi masu ɗauke da bacci,
Harara abbansu yaa jefa mashi tare da cewa"Ubanka ne,buɗe idonka ka gani mara matunci" koda yaji muryar. abbansu sae ya ƙara tamke fuska,yana faman murguɗa masa baki,Abba yace "Eyyyeh!ni kake murguɗa ma baki," zumbura masa baki yayi,hada sa hannu ya toshe kunnuwansa don karma yaji muryar abban nasu,
"Nasan maganinka yaro"yayi maganar tare da kai hannunshi saman side drawer ya ɗauko bottle water ɗin dake ajiye a sama,buɗe murfin robar ya shiga yi yana faɗin"Zaka tashi ko saina watsa maka ruwan nan,"
Wuri wuri yayi masa da ido,yana jira yaga in dagaske abban nasu ruwan zai watsa mashi,
Jin yayi banza dashi yasa shi ɗebo ruwan a murfin robar,ya watsa masa shi da sanyinsa asaman fuskarshi,aikuwa a gigice ya tashi zaune jikin shi na kerma,hankalin abbansu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda ya tsorata daga watsa mashi ruwa a fuska,abu kamar wasa sai ga junaid yana kuka hawaye jaga jaga a fuskarshi,
Tsawa abbansu ya ɗan daka mashi tare da cewa"Yi mun shiri rigimamme kawai,"
Wannan maganar da abbansu yayi ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,saukowa yayi daga saman gadon yana shassheƙar kuka yace""kuma Allah tunda ka kore ni,ɗakinsu sehrish zanje na kwana,"yayi maganar tare da bubbuga ƙafarshi ya fuce,
Sakin baki abbansu yayi yana kallonshi har ya fuce daga ɗakin,girgiza kai kawai yayi tare da gyara kwanciyarshi,
Junaid kuwa bayan fitarshi daga ɗakin Abbansu,bedroom ɗinsu sehrish ya wuce kai tsaye,cikin sa'a ya samu ƙopar ɗakin a buɗe,hannu yasa ya tura door din,sannan ya shige ciki,
Sun cika gadon su uku abunsu,sae faman sharar bacci sukeyi banda mutun ɗaya wadda ta rufe idanunta tamkar maiyin bacci, gaba daya hosana ta yaye masu bargon da suka lullu6e dashi,dama ita bata iya kwanciyar bacci ba,zaiyi wuya ta kwanta batare da ta faɗo ƙasa ba,dalilin dayasa suke sanyata tsakiya kenan saboda gudun karta faɗo,sehrish na kwance a left hand,hosana tana a middle ɗinsu,yayin da jahad ke a right hand,saitin inda yake tsaye,hannu yasa tare da kashe masu hasken ɗakin da sehrish ta bari a kunne,lalla6awa yayi ya haye saman gadon,gefen jahad ya kwanta, tare da ja masu bargon ya lullu6esu duka,cikin ƙankanin lokaci bacci ya ɗaukeshi,tabbas Sehrish taji lokacin da aka kashe masu hasken ɗakinsu,amma batayi tunanin ta buɗe idanunta ba don taga wanene,saboda halin da ta shiga,Zuciyarta ba tayi mata daɗi ga hawaye sae faman shararowa suke yi daga cikin idanunta,babban abunda ke damunta shine wani hali sgr yake ciki?Yayi bacci ko idonshi biyu?bataso abunda ya faru ba,sai dae ba yadda ta iya dole tabi umarnin mahaifinta da wannan zancen zucin bacci ya sace ta,
tashin hankali,Junaid fa ya shige acikinsu sae faman sharar baccinsa yake,sun manne ma juna shi da jahad,duk a tunaninta sehrish ce,hada ƙara rungumoshi ajikinta,
*mu haɗu on monday donjin yadda zata kaya don kuwa akwai ƙura! Amrish zata Rayu ko kuwa akasin hakan?Wai ma wacece Amrish ɗin nan?su waye iyayenta?shin Sgr zai amince da auren sehrish?a yadda yake jin kanshi ɗin nan?Me zai faru idansu jahad suka Tsinci junaid acikin ɗakinsu saman gadonsu?*😨😱
*Su aunty babba manya Naki na nan tafe*🤣[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: *💋 Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Wuraren ƙarfe 3:00 na dare,Jahad tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci zata gyara kwanciyarta,aikuwa taji an ƙanƙameta sosai an matse ta,numfashinta har wani kokawar ɗaukewa yake yi,ƙoƙarin janye jikinta ta shiga yi amman hakan ya faskara,saboda ruƙon da akayi mata bana wasa bane,cikin baccin ta dinga faɗin"Sehrish!ki sake Ni!kin matseni,numfashi na zai ɗauke" daƙyar sound ɗin ke fita saboda throat ɗinta da ke abushe,saboda thirsty da take ji,tun tana ambaton hakan ƙasa kasa har takai ga ɗaga muryarta "Sehrish!!dan Allah ki sake ni,baki ji nace kin matse ni ba? Shiru babu mai bata amsa domin kuwa duk bacci suke yi,
Jahad kuwa tuni ta gama galabaita hakan yasa ta tattare iya ƙarfinta na ƙarshe ta ingije junaid daga jikinta,ya ɗan yi baya,hakan yasa ta samu sarari,hannu tasa tare da zame bargon ta fiddo da kanta,tana faman sauke ajiyar zuciya,zufa duk ta wanke mata jikinta duk da weather ɗin nasu akwai sanyi,matsuwar da tayi ne yasa ta zubda gumi,juyawa ta ɗan yi tare da kallon gefen hannun hagunta,kasancewar akwai hasken electric bulbs ɗin da suka gauraye gidan daga waje da kuma na corridor ɗinsu gana main palour,Sune suka ɗan bama ɗakinsu haske,duk da an kashe Globe ɗin ɗakin nasu,dama kuma Sehrish ta lalata bedside lamp ɗin ɗakin,lokacin baya data kwala ma Haroon a goshinsa,
Ƙura ido jahad tayi tana ƙare masu kallo,gani take tamkar idonta ba dai dai suke nuna mata ba kamar mutun biyu ne kwance a gefen hagunta,hannunta ta miƙe tare da yaye masu Sehrish bargon da suka rufa dashi,gabanta ne ya faɗi rass!ganin Sehrish ga kuma hosana baje suna ta sharar bacci,nan take hankalinta yayi mugun tashi,wani irin tsoro ne ya lullu6eta,tabbas akwai mutun ɗaya 6angaren damanta,wanda suka kwana rungume da juna a ƙanƙame,wanda yayi silar taushe numfashinta,tashin hankali! kasa juyawa tayi don taga wanene saboda tsabar tsoro,sae dai ta zura hannayenta dake ta faman kerma ta laluba don taji in da gaske wani ne kwance a wurin,Sumar kan junaid ta shafo da hannunta,a razane ta zame hannunta,la66anta na kerma ta shiga furta"La'Ila ha'illah Anta subhanaka,Inni kuntu minazzalumin,"daga bisani ta shiga faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!!,
Muryarta na kerma ta shiga kwalama su sehrish kira kaɗan kaɗan don kada aljanin ya farka,"Hosana!Sehrish!!dan Allah ku tashi!Mutum mutumi acikin ɗakinmu saman gadonmu!ina tunanin Aljani ne ya faɗo ɗakinmu don ya cutar damu,Wayyo Allah na" babban tashin hankalinta aljanin na akusa da ita,in ma cutar dasu yazo yayi toh ta kanta zai fara tunda itace a kusa dashi,
Tuni zufa ta gama wanko mata a fuskarta,numfashi kanshi daƙyar take fitar dashi don kada aljanin yaji yasan cewar idonta biyu,
"Sehrish!Sehrish!!hosana!wai ba zaku tashi ba?dan Allah ku tashi kuga abunda na gani,asaman gadon mu,"tana magana hawaye na sauka daga idonta,don ita ta riga ta sallamawa kanta cewar ajalinta ne yazo,
Duk wannan surutan da Jahad ke yi kaf a kunnan Sehrish,wadda ke lamo tayi nisa cikin zurfin tunanin da take yi,Duk a tunaninta Jahad mafarki takeyi shiyasa take sambatu,wannan dalilin ne yasa bata motsa ba,kuma bata tanka mata ba,idanunta ne kawae ke arufe amma idonta biyu,likimo kawai tayi,
Jahad na cikin wannan yanayin taji an aza mata hannu asaman waist ɗinta,a wani irin Firgice ta fashe da wata irin gigitacciyar ƙara,wadda tayi silar tashin hosana daga bacci,hatta sehrish sai da ta razana,a tare suka tashi zaune ita da hosana suna kallon Jahad dake ta ihun neman agaji,ai koda Hosana da sehrish suka ga hannun mutum a saman qugun jahad,a gigice suka duro daga saman gadon da gudun gaske har suna tuntu6e wurin tunkarar ƙopar ɗakin don su buɗe ta su gudu,jahad kuwa sam taƙi motsawa,sai ihu take tana kuka,waɗanda take tunanin cewa zasu taimaketa sun gudu sun barta asaman gadon ita kaɗai,jikinsu sae faman kerma yakeyi burinsu su buɗe ƙopar su gudu amma taƙi buɗuwa,hakan yasa Sehrish watsawa da gudu,ta shige toilet taja ƙopar ta rufe,ganin haka yasa hosana tunkarar wardrobe ɗinsu,ta buɗe gidan ƙasa da babu kaya sosai acikinsa sae bedsheets,Ta faɗa ciki tare da jan murfin wardrobe ɗin ta rufe shi,kowa yayi ta kansa kenan,duk wannan budurin da akeyi Junaid bai sani ba,domin kuwa ba ƙaramin abune ke iya tashinshi daga bacci ba,irin mutanen nan ne masu nauyin baccin tsiya,
Jahad na cikin wannan halin na firgici,taji an aza mata ƙafa asaman jikinta,firgitar da tayi ne yasa tayi wurgi da junaid gaba ɗaya,ya tafi dama yana dab da bakin gadon,aikuwa ji kake timmmm!ya ƙundumo ƙasa kanshi ya bugu sosai saman tiles,
raɗaɗin da yaji ne yasa shi farkawa daga baccin,ya fashe da matsanancin kuka,
Gaban jahad ne ya faɗi rass!!jin sautin kukan Junaid,rarrafowa tayi ta dawo gefen gadon tare da ɗan leƙawa don ta tabbatar ma kanta abunda kunnuwanta ke ji,Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonshi,yadda kasan wani jinjiri ya 6are baki sai kuka yake yi,da ƙarfi ta ambaci sunanshi"JUNAID"dakatawa yayi daga yin kukan da yakeyi jin an ambaci sunanshi,wurga idanunshi yayi akan jahad,yayi mata wuri wuri da ido yana kallonta,
Muryarta na rawa tace"juj..junaid!dama kai Ne?me kake yi acikin ɗakin mu?
cikin shessheƙar kuka yace"Nifa Zuwa kawai nayi don in taya ku kwana,"
...zuba mashi ido kawai tayi tana kallon fuskarshi don abun ya fi ƙarfinta,
Daga cikin toilet ta jiyo Muryar Sehrish tana ce wa"Jahad wai dagaske junaid ne?Naji kin ambaci sunanshi"?
A ƙule jahad tace"Bansani ba,ku fito ku gane ma idonku,kunaji ina kukan neman taimako amma duk kuka watsa a guje kuka barni,yanzu da wani mugun abunne ba junaid ba,da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya,"
buɗe ƙopar sehrish tayi tare da fitowa daga cikin toilet ɗin,hosana ma ta buɗe wardrobe ɗin tare da fitowa daga ciki,suka tunkari inda junaid yake kwance yana faman sauke ajiyar zuciya,sae faman lumshe ido yakeyi,saboda baccin dake a idanunshi,
"Junaid!" sehrish ce ta kira sunanshi,ware idanunshi yayi akanta yana kallonta,
.."junaid me kake yi a ɗakin mu?waya kawo ka?anya baka fara shan ƙwaya ba"
Harara ya wurga mata tare da murguɗa mata baki yace"bansani ba,duk kun bi kun takura rayuwata,hakanan kawai ina baccina kun tashe ni,laifi ne in na kwana aɗakinku,ni ba ɗan uwanku bane"? Sakin baki sukayi suna kallonshi,hosana tace"wlh saina faɗa ma Daddy da Ya Omar,ince ka shigo ɗakinmu ka kwanta mana asaman gadonmu,ƙato dakai,"tana kai ƙarshen maganarta,junaid yace"idan kin tashi ki faɗama Kaka ƙarewar daddyn,mai kan kurciya kawai" wannan maganar ba ƙaramin fusata hosana tayi ba,jikinta har rawa yakeyi wurin dauko pillow daga saman gadonsu,ta buga mashi asaman fuskarshi,koda ganin hakan,sehrish ma ta ɗauko pillow ta shiga taya hosana,jahad tace"wlh nima bazan ƙyale ka ba,junaid saboda ka bani tsoro,kuma babu kyau ma tsoratar da musulmi,"tasa hannu ta ɗauko pillow itama,nan fa suka tasa junaid kamar sun samu jaki,suka dingi jibgarshi da pillows,tun yana yi masu magiyar su daina har ya sake fashe masu da kuka yana bubbuga ƙafafunshi,suna cikin bugun nan nashi,suka ji tsit junaid ya daina motsi,cikin sauri Jahad ta kalli jikin pillown hannunta,Ɗigon jini ta gani,ɗagowa tayi da nufin ta nuna ma su Sehrish aikuwa karaf idonta ya sauka akan pillown dake hannun sehrish da hosana,duk ɗigon jini ne ajikin pillown hannunsu,Tashin Hankali!
Gaba ɗayansu ba ƙaramin kiɗima suka yi ba,ƴan hanjin cikinsu suka kaɗa,zagaye shi su kayi a zuƙunne suna kallon fuskarshi,
Fashewa hosana tayi da kuka tana faɗin"Wlh babu ruwa na!bani na kashe junaid ba!"maganar da tayi ba ƙaramin tsoratar dasu tayi ba,tuni ido ya raina fata,daga wasa!?
Jijjigashi suka shiga yi atare suna ambaton sunanshi"Junaid!junaid!!!ka tashi!dan Allah junaid ka tashi!!Wayyo Allah munshiga ukun mu!!dan Allah baby junaid ka tashi," ko motsi wannan junaid baiyi ba,matsawa sehrish tayi tare da kanga kunnanta asaman hancinshi don taji in yana numfashi,ɗufff taji babu numfashi da sauri ta sanya tafin hannunta asaman kirjinshi saitin zuciyarshi nan ma taji zuciyar tashi tadaina bugawa,a wani irin sukwane ta ɗago da idanunta waɗanda sukayi luhu luhu cike tab da hawaye tana kallonsu Jahad da hosana,jiki a mace tace"ZUCIYAR JUNAID BATA BUGAWA HAKAN NA NUFIN MUNYI SILAR MUTUWAR JUNAID"!!!
Girgiza kai jahad ta shiga yi tana cewa"Junaid bai mutu ba,dan Allah ki daina faɗan hakan,kada ya tabbata dagaske,"tayi maganar a yayin da take kai hannu tana tatta6a fuskarshi"junaid!junaid!ka tashi dan Allah ka tashi junaid,"
Ganin yaƙi motsi yasa suka fidda rai da cewar junaid zai tashi,kifa kai sukayi su duka ukun suna shessheƙar kuka,ɗan ɗagowa jahad tayi tare da kai idonta kan fuskarshi,Abun mamaki sae ga murmushi ya bayyana akan fuskarshi,dimples ɗinsa guda biyu sun lotsa,Wani irin ihun farin ciki ta saki tana fadin"Bai mutu ba!junaid wasa yake yi mana,gayanan yana murmushi,'jin haka yasa su sehrish saurin ɗagowa da kawunansu suna kallonshi,sae faman wangale baki yakeyi yana dariya,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,
"Junaid"sehrish ce ta ambaci sunanshi,a hankali ya buɗe manyan idanunshi yana kallonsu one by one,sai faman 6a66aka dariya yakeyi,
Har suna haɗa baki wurin cewa"Kai junaid!meyasa zakayi mana haka?wlh ka tsoratar damu sosai,"
"Wanda yasa kuka bugeni,ko tausayina bakuji,kun wani taru akaina kuna jibgata kamar kunsamu jaki amale,shiyasa nima na rama da gangan na ɗauke numfashina don kuyi tsammanin kona mutu"yayi maganar yana murguɗa masu baki,Ajiyar zuciya suka shiga saukewa,
"Junaid dan Allah kayi haƙuri,bazan ƙara bugunka ba,kada ka faɗama kowa,"acewar hosana,
Harara ya jefa mata tare da ƙara tamke fuskarshi,
Cikin sanyin murya jahad tace"junaid baka da lafiya ne?mun ga jini ajikin pillow lokacin da muke bugunka,kuma da alama daga hancinka muka gogo shi,"
Shiru ya ɗan yi yana kallonta kafin yace"Lafiyata ƙalau Ni,nose bleeding ne ba wani abu ba dama ina yawan yinshi,yafi zuwa mun da daddare,shiyasa baku ta6a gani ba"
"Amma ka faɗama Abba ko wani game da nose bleeding din"? Girgiza kai yayi alamar a'a,da alama baison maganar,don haka yace"pls nidai mubar wannan zancen,kusan yadda za kuyi dani don Allah bazan iya komawa bedroom ɗina ba,tsoro ma nakeji,"yayi maganar ashagwa6e,
Jiki asanyaye jahad ta kalli su sehrish tace"kuje ku kwanta,bari ni na rakashi ɗakin nashi," mikewa su kayi atare da ita da hosana suka koma kan gadon suka kwanta,tare da jan bargo suka lullu6e,
Miƙewa daga zaune junaid yayi yana cewa"Allah sai dai ki goyani,don na riga dana faɗa maki cewa ƙafafuna ciwo suke yi mun bazan iya taka stairs ba,"
Murmushi jahad tayi tare da cewa"shikenan,zan goya ka amma ka bari sai munje wurin benen tukunna in goya ka," amsa mata yayi da toh,sannan ya mike tare da ruƙo hannunta cikin nashi yace"Tashi muje,"mikewa tayi suka fita atare,suna tafiya tana satar kallon gefen fuskarshi kamar wani zautacce sai faman sakin murmushi yake yi,hakanan ta dinga jin gabanta na faɗuwa,lamarinsa ba ƙaramin mamaki yake bata ba,kokonto ta shiga yi anya wannan ɗigon jinin da suka gani na ha6o ne? Yanayin yadda abun ya afku tamkar ba jinin ha6o bane,tabbas akwai dae wani abu dake damunshi wanda baison kowa ya sani,
Tana cikin zancen zucin nata taji yace"Mun ƙaraso wurin stairs ɗin,yanzu ki goyani,ki kaini har bedroom ɗina,kuma ki kwantar dani,"
Amsa mashi tayi da toh,sannan ta zuƙunna,ya daddage ya haye saman bayanta,tare da kwantar da kanshi luff kamar wani jinjiri,zagayo da hannayenshi yayi ta saman stomach ɗinta,hakan ba ƙaramin yanayi ya jefa ta ba,ji tayi tamkar bazata iya miƙewa tsaye ba,saitin kunnanta taji daddaɗar muryar nan tashi mai haɗe da shagwa6a"jahad ki tashi mu tafi,bacci nake ji,"
Daƙyar ta iya mikewa tsaye goye dashi abayanta,hannu tasa ta tallaboshi sosai,sannan ta haye saman benen,tana tafiya tana tangal tangal har ta ƙaraso ɗakin nashi,hannu tasa ta ɗan tura ƙopar sannan ta shige ciki,Talal suka samu kwance yana ta sharar bacci,ƙarasawa tayi tare da sauke junaid saman gadon,ya gyara kwanciyarshi,bargo taja ta rufe mashi body ɗinsa zuwa neck ɗinsa,tana ƙoƙarin juyawa tabar wurin,taji ya ruƙo hannunta cikin nashi,jimmm tayi tana jiran jin me zaice mata,
"Jahad"ya ambaci sunanta da wata irin murya ta mai jin bacci,
"Na'am,"ta amsa mashi kiran a yayin da take juyowa" murmushi ya sakar mata tare da sanya yatsan hannunshi acikin dimple ɗin fuskarshi yace"Kiss me pls," bakomai ya faɗo mata aranta ba,face abunda ya ta6a faruwa atsakaninsu,cikin motarshi,daga zuwa manna mashi kiss a side face ɗinsa,bakinta ya goce izuwa cikin bakinsa,a ranar zauce mata yayi,
Maƙe masa kafaɗa tayi alamar bazatayi mashi kiss ɗin ba,bubbuga ƙafarshi ya shiga yi yana yi mata shagwa6a,hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba,saboda wani irin kyau da yake bayyana akan fuskarshi aduk lokacin da yake shagwa6a,tamkar tayi hugging ɗinshi ajikinta haka ta dinga ji,
"Baza kiyi mun ba ko"?yayi maganar.yayin da idanunshi ke ƙoƙarin lumshewa,
"Shikenan,zanyi maka,amma ka rufe idanunka," da sauri ya rufe su yana jiran jin la66anta asaman fuskarshi,tsayawa tayi asaman kanshi,tana karanto addu'o'i tana tattofa mashi akan fuskarshi,daga ƙarshe ta haɗe yatsun hannunta guda biyu na hannun damanta,a hankali ta aza yatsun nata asaman la66ansa,sannan ta furta sautin kiss ɗin da bakinta,wani irin farinciki ne ya lullu6e junaid,duk a tunaninshi bakinta ne ta aza asaman nashi,baisan cewa wayau tayi mashi ba,tasa yatsun hannunta amatsayin la66anta,
rufe mashi fuskarshi tayi da bargon,sannan ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin,
"I Love u so much jahad," muryar junaid ce ta katse mata hanzarinta,dakatawa tayi tare da ɗan juyawa tana kallonshi,yana acikin bargon ya furta mata wannan kalmar,
"Kina sona jahad"?
Wani irin ƙayataccen murmushi ne ya sauka akan fuskarta,bata bashi amsar tambayarba,cikin sauri ta fuce daga ɗakin nashi,ta koma bedroom ɗinsu ta kwanta zuciyarta cike fal da farin ciki,ta ji daɗin kalmar da junaid ya furta mata,duk da bata da tabbacin cewar ko dagaske yake yi mata," da wannan tunanin bacci ya ɗauketa,
*Boss Bature*
🤍❤🤍
Washe Gari,
Kwance take asaman katifarsu,ta saki baki tana ta sharar baccinta,sae faman jan minshari takeyi kamar Ragon layya ga miyan bacci dake gangarowa ta cikin bakinta da ta bari a buɗe,tana cikin baccin nan taji Ringing ɗin wayarta da ƙarfin gaske har cikin dodon kunnanta,hannu tasa tare da toshe kunnanta tana faman buga tsoki,alamar an takura mata,bata ɗaga kiran ba,har ya katse kuma sai ga wani kiran ya ƙara shigowa,a hargitse Abra ta miƙe ranta a matuƙar 6ace,tasa hannu ta dauki wayar dake ajiye gefenta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta Cike da masifa tace"Wai Uban wanene ke kirana tunda sanyin safiya"?
Kafin ta rufe bakinta taji ance"Ubanki ne!" har sai da gaban abrah ya faɗi rasss,cikin sauri ta janye wayar daga kunnanta tare da kallon screen ɗin wayar don ta shaida mai kiran nata,Sunan Aunty babba ta gani,yatsina fuska tayi kafin ta mayar da wayar a kunnanta,"ina kwana aunty,an tashi lafiya"
Rai a6ace Aunty babba tace"Ruƙe gaisuwarki,sakarya daƙiƙiya zaman uban mi kike ke da Mammy da har kuka bari AMAL ta gudo daga mai duguri tazo Abuja wurin Amani?!" jin wannan maganar yasa abrah ta zabura,don har sai da ta daki ƙirjinta da hannunta,Hankali atashe tace"Aunty laila dagaske Amal tana abuja wurin Amani!"
"Ƙarya zan maki ne?Kuna nan sake da baki har yarinya ƙarama tayi maku wayau ta gudu,Yanzu baki ga yadda Amal ta koma ba,Yarinya ta zama ƴar hutu kamar wadda ta taso a gidan naira,Tamkar bata ta6a shan wahala ba,Irin rayuwar dana so ace ke kika same ta,sae gashi ƴar kishiyar da muka tsana ita ta samu wannan damar,ina nan dake in har mu kayi sake AMAL sai ta auri ɗaya daga cikin ƴa'ƴan Alexandra,"
Saboda tsabar takaici Hannu ɗaya abra ta aza asaman kanta tana faɗin"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!
Aunty babba tace"kaɗan ma kika gani!duk laifinku ne!da alama su Amani sunfi mu Jinin Nasara,shiyasa suke ta cin galaba akan mu,"
Muryar abra tamkar zatayi kuka tace"Wlh aunty laila har shawara sai da naba mammy tun kafin amal ta gudu nace mata mu 6alle ƙafarta guda ɗaya,don ta zama gurguwa kinga in mukayi hakan ba yadda za'ae ta gudu,Amma saboda shegen son kuɗi irin na mammy tace Wai mu barta da ƙafafunta,saboda tana so Amal ta auri mai kuɗi don ta rinƙa tatso mana kuɗi a wurinta,Yanzu gashi nan Mammy taja mana"
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci kafin Aunty babba tace"Abra inaso kiyi gaggawar tattara kayanki kibar gidan nan!kema ki dawo Abuja gidan surukanmu da zama!wannan kaɗae ce hanyar da zamu iya cin nasara akansu,"
"Aunty in dawo nan fa kika ce?Aunty hayaam fa?zata dawo gida ne"?
"Bazata dawo ba,zama ma yanzu ta fara shi har sai an shafa fatihar aurenta da Babban yayansu,kawai abunda nakeso dake,ki tattara kayanki ki dawo gidan da zama,saboda ni bani da tabbacin cewar zama na zaiyiyu acikinsa,atakure nake,"
Jinjina kai Abra tayi tamkar tana agabanta tace"Shikenan Aunty laila,da yaushe kikeso inzo nan ne?kuma ya zamuyi da mammy?kinsan fa bata da lafiya tana can kwance,"
Dogon tsoki Aunty babba taja tare da cewa"Wake ta wani mammy?ae kawai ki tattara kayanki yanzun nan ki biyo motar Abuja ta kawoki,Ita kuma mammy Allah ya bata lafiya shine kawai,"
Fuskar Abra ɗauke da murmushi tace"aikuwa yanzun nan zan shirya,zan ma iya sa ɗaya daga cikin samari na,ya kawoni gidan don duk suna da Mota,"
Aunty babba tace"Yawwa cikin sauƙi ma,ki kira ɗaya daga cikinsu,ya kawoki,"
"In sha Allah Auntyna," abra ta amsa mata kafin sukayi sallama,
Duk wannan wayar da Aunty babba keyi kaf a kunnan Hafsat da hayaam dake kwance saman gado,ita kuma tana zaune asaman Stool dake agaban mirror,
"Mommy wannan abun kunyar har ina?taya zaki ce abra tadawo gidan nan da zama?bayan ga hayaam kuma!Nan fa gidan surukanku ne ba gidan ƙanin mahaifinku ba...." a fusace Aunty babba ta jefa ma hafsat wayar hannunta cikin sa'a tasamu gefen goshinta,dafe wurin hafsat tayi saboda zafin da taji,
Rai a6ace tace"Hafsat ki fita daga idona in rufe!kina yimun shisshigi acikin lamurrana,Ina ruwanki da zaman su Abra acikin gidan nan?ke zaki ciyar dasu ne?ko saman kanki zasu zauna ne"?
Shiru hafsat tayi batare da ta tanka mata ba,hayaam dae bata sanya masu baki ba,saboda gudun rashin kunyar hafsat don bata raga ma kowa acikinsu,
Wuraren ƙarfe tara,Azmee da Saude suka kammala girke girken breakfast na gidan,yanzu ta samu sauƙi wurin yin aiki don Saude ba ƙaramin taimaka mata takeyi ba,dayake itama kwararriyace wurin iya girki tana son yin girki,bayan sun kammala,Azmee ta shiga jera mata Warmers acikin tray tana kaiwa saman dining table,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala jera abincin,
ɗaya bayan ɗaya matasan gidan suka shiga fitowa daga bedroom ɗinsu,su Kanal yousouf,Irfan jabeer khaleed twins,fawan,sune waɗanda suka fara hallara daga baya,Abbansu tare da Mommynsu junaid suka fito,kafin wani lokaci kowa ya fito,hadasu Dr haris su Captain adam,najeeb talal da kuma junaid,da sauransu duka dai,Mutun ɗaya ne bai fito ba,bakowa bane fa ce Surgeon general Rafayet,
Bayan matasan sun hallara Azmee taje ɗakinsu Sehrish ta taso su daga bacci,atare suka fito bayan sunyi brush su uku kowacce sanye da hijabi ajikinta,tun ta sallar asuba ce da suka sanya ajikinsu basu cireta ba,bacci yayi awon gaba dasu,
Gaishe dasu Abba suka fara yi,fuskar kowannansu ɗauke da murmushi haka suka shiga amsa masu gaisuwar,daga bisani suka shiga gaisar da yayyensu,kowa da irin yadda yake amsa masu gaisuwar cike da zolaya,don wasu ma hada kwaikwayon Muryarsu,hakan ba ƙaramin nishaɗi ya sanyasu ba,
Komawa su kayi tare da samun wuri suka zauna a dining chairs ɗin da Abusufyan ke zaune,atare suka haɗa baki wurin cewa"Daddy ina kwana?ka tashi lafiya,"
ɗagowa yayi tare da kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya kafin yace"Lafiyalou Alhamdulillah!"
Natsuwa kowa yayi,yayin da Azmee da saude suka shiga zuzzuba masu abincin,kowa na faɗin abunda yake so yaci,
Gyaran murya Abba yayi tare da kallon azmee yace"An kai ma Ammi nata breakfast ɗin"!?
azmee tace"Eh nakai masu,a ɗakin gwaggo don acan tace mun zatayi kalacinta,ita da ƴar uwarta,"
Murmushi ya ɗan yi don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
"Azeema fa"? Ya kuma tambayarta,
"Itama tana atare dasu,can ɗakin gwaggon,"
Jinjina kai abba yayi kafin ya kuma cewa"Aunty saratu fa?da ƴanmatan ta suma ankai masu nasu"?
Saude ce ta kar6e da cewa"Ni nakai masu a ɗakinsu,"
Abba yace"Aikin ku yayi kyau,"ya ƙarasa maganar tare da kai hannu ya ɗauki plate ɗin dake hannunsa yaci gaba da cin abincinsa da azmee ta zuba mashi,
Abbas yace"Azmee banga su Amal ba?ko ankai masu nasu ne"?yayi maganar ayayin da yake ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunshi,?
"Na kai masu a bedroom ɗinsu," ta bashi amsa,
Ganin Abbas ya tambayi iyalinsa ne yasa Ishaq yin gyaran murya yace"Azmee wai ni ina ƴata hafsat ne?ko an manta dasu ne?naga ban gansu ba!?
"Ni kaina inata so in tambayesu,tun shekaran jiya rabon da in Sanya su a cikin idona,tamkar basa a cikin gidan nan"!Acewar Abbansu,
"Bari na kirasu,"Azmee ta faɗi hakan tare da juyawa ta nufi ɗakinsu laila,
abinci take ci,amma hankalinta ba akwance yake ba,Yau tunda ta tashi daga bacci gabanta ke ta faɗuwa rasss!rasss!mafi yawancin lokutta in taji gabanta na yawan faɗuwa to tabbas wani abune zai faru da ita!mai kyau ko mara kyau,sam takasa cin abincinta,sae faman jujjuya cokalin hannunta takeyi acikin plate ɗin dake agabanta,
A hankali ta ɗago da idanunta tare da azasu akan Hosana dake ta faman cunkusa Burger acikin bakinta,yadda kasan zata 6ara bakin ko gajiya da Ci ba tayi,Allah sarki rayuwa kenan,Allah mai yadda yaso,kamar basu bane waɗannan yaran ba,masu yawo babu takalmi a ƙafafunsu,kawunansu babu ɗan kwali,Kayan jikinsu duk a yayyage,babu mai son su,rayuwarsu a wulaƙance kowa gudunsu yakeyi,Amma yanzu komai ya canza!Yanzu gasu acikin danginsu,kowa sonsu yakeyi,suci mai kyau su sha mai kyau,su kwana a mai kyau,suturar sawa ma sai sun za6i wadda suke so su sanya ajikinsu,duk mai yajawo wannan, haƙuri!sun rungumi ƙaddararsu sun cinye jarabawar da Allah yayi masu,basuyi gajan haƙuri ba,kullum cikin kai kukan su wurin Allah suke,saboda sun san cewa shi kaɗai ne zai iya share masu hawayensu,duk irin ƙuncin rayuwar dasu Sehrish suka shiga,basu ta6a ƙasƙantar da kansu ba don suyi bara,ko su siyar da mutuncinsu don su samu kuɗi,kamar yadda wasu mutanen keyi,
Janye idanunta tayi daga kan hosana ta mayar dasu kan jahad,wadda ke ruƙe da bread a hannunta,tana goga mashi butter,abun ya ɗaure mata kai kowa sai cin abinci yake yi hankali kwance,amma ita takasa Cin nata,to ko dai bata da lafiya ne? ta ƙarasa zancen zucin tare da juyawa,karaf idanunta suka sauka akan Fuskar Abusufyan wanda ke kallonta,har sai da ta ɗan razana kaɗan,sunanshi ta ambata abakinta a hankali"daddy,"
..murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa"Daughter,tun ɗazu ina kallonki,kin ƙi cin abincinki,kin tasa ƴan uwanki gaba kinata kallonsu ɗaya bayan ɗaya,faɗamun meke damunki ne'?
"Daddy am not feeling well,gabana sai faɗuwa yakeyi,bansan meyasa ba,shiyasa ma nagaza cin abincin"muryarta akasalance tayi maganar,
Jahad tace"Daddy,jiya ma batayi wani isasshen bacci ba,"
"Saboda me"?yayi tambayar yana kallonta,
"Nikaina bansan meyasa ba,kawai bana jin daɗi ne,"
Jinjina kai yayi tare da cewa"Kada ki damu in sha Allah wannan faɗuwar gaban da kikeji Alkhairi ne zai faru dake,"
"Allah yasa haka ne daddy" ta ƙarasa maganar tare da kai hannu ta ɗauki cup of tea ɗin dake agabanta,ta shiga kur6arsa a hankali,ba don tana jin daɗinsa ba,
Suna cikin cin abincin nan,sae ga Azmee tare da hafsat,sun shigo dining area ɗin,Aunty babba na a bayansu ta sanya Niqab a fuskarta,hayaam dai bata fito ba,saboda gudun karsu haɗu da Sgr a wurin,da hannu Azmee tayi masu nuni da su zauna a inda su Jahad suke,saboda nan ke akwai empty chairs guda biyu da suka rage,da yake table ɗin mai mazaunin mutun Shida ne,
Tunda suka zo wurin,idon kowa ya koma akan Aunty babba dake sanye da niqabi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,sai da suka fara gaishe dasu Abba,sannan suka samu wuri suka zauna,hankalin Aunty babba sam ba'a kwance yake ba,bata so fitowa ba,Azmee ce ta sanar da ita cewa Ishaq yace su fito dining suci abinci,tayi mata hakan ne saboda ta rama Wulaƙancin da sukayi mata,
Daƙyar ta iya gaishe da Abusufyan,batare daya ɗago ya kalleta ba ya amsa mata,hafsat tace"Uncle ina kwana,"?
"Lafiya lou hafsat,ashe kuna acikin gidan,ae nayi tunanin kun koma Kaduna ne,"
Murmushin yaƙe tayi,sae faman zazzare ido takeyi,duk sunbi sun tsargu,ita da mommynta,ita dai Sehrish ta zuba ma sarautar Allah ido,so take taga ta yadda Aunty babba zataci abinci da niqabi a fuskarta,ba ita kaɗae ba hatta jahad abunda take jira kenan,Ishaq kuwa tuni ranshi yayi mugun 6aci,sarai yasan cewa da gangan ta zura niqabi a fuskarta bayan tasan cewar abinci zata ci,alamun rashin gaskiya duk sun bayyana atattare dasu,ita da hafsat,
Serving ɗinsu Aunty azmee tayi,ta tura masu plate ɗin abincin agabansu,hafsat dai tayi kokarin cin abincin,kaɗan kaɗan take tura chips abakinta,Aunty babba kuwa kamar gunki haka ta ƙame saman kujerar taƙi motsi,fargabarta kada hosana ta gane cewa itace,
Murmushin mugunta sehrish ta saki,tare da yin gyaran Murya tace"Aunty,ki cire niqabin mana,in ba haka ba,bazaki ji daɗin cin abincin ba,gashi yana ta hucewa,bazaiyi maki daɗin ci ba inya salafce,"
Mazurai Aunty babba tashiga yi ta cikin niqabin,ƙululun baƙin ciki kamar ta shaqo sehrish ta rufe ta da bugu,ƙin magana tayi saboda gudun kar Hosana taji Muryarta,ta kara tona mata asiri,hakan yasa Jahad cewa"Na ji tayi shiru,kodai bacci ne bai isheta ba"?tayi maganar tana faman ƙumshe dariya abakinta,sehrish tace"inaji tayi bacci ne a zaune,bari na cire mata niqabin don tasha iska kada numfashinta ya sarƙe," yunƙurawa Sehrish tayi tare da kai hannu zata zame niqabin dake a fuskar Aunty babba,ae kuwa a firgice Aunty babba ta zabura ta miƙe tsaye tana faɗin"Karki kuskura ki ta6amun niqabi na," rai a6ace tayi maganar,aikuwa Hosana najin Muryarta,ta daddage ta fasa uwar ƙara,tare da yin wurgi da kofin dake a hannunta,a gigice ta miƙe tana ƙokarin guduwa,gaba daya hankalin kowa ya dawo kanta,Omar ne ya miƙe da sauri ya ruƙo hannunta yana tambayarta lafiya,
A tsorace tashiga fadin"Banason ta!na tsane ta!wlh ya Omar muguwace matar nan,tazo nan ne don ta kashe mu,dan Allah ku koreta daga gidan nan,wayyo Allah na....."ta fashe da matsanancin kuka,tashin hankalin da ba'a samashi date!nan fa kowa ya miƙe tsaye yana bin Aunty babba da kallo,saboda tsabar ruɗu muryarta na kerma tashiga cewa"wa...wallahi Billahil azimu Ni bansanta ba!bansan laifin me na aikata mata ba,yarinyar nan fa mahaukaciya ce tana da ta6in hankali,shiyasa take wannan sambatun...."tunkan ta ƙarasa maganar Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa"karki kuskura ki ƙara kiran ƴata da sunan mahaukaciya!in ba haka ba ranki zai 6aci a wurin nan ne!hosana bazata ta6a tsangwamar mutun hakanan ba batare daya aikata mata wani mugun abun ba," ya karasa maganar tare da jan dogon tsoki,
"Ya Omar dan Allah ku sakar mata karnuka su fiddata daga cikin gidan nan,wlh babu Allah aranta!so take takashe maka hosanarka,"cikin shesshekar kuka take maganar,Marshal sai ƙokarin rufe mata bakinta yakeyi don ta daina amma ina hosana taƙi rufe bakin,don har cizon hannunshi takeyi,in yayi ƙoƙarin toshe mata baki,Aunty babba kuwa sae faman zabga salati takeyi,jikinta sae kerma yakeyi,tuni zufa ta jika ta sharkaf,ƴan hanjin cikinta kuwa sae faman kaɗawa sukeyi,hankalin General ishaq ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kada ace wani mugun abunne laila ta aikata ma yarinyar da har take tsoron ganinta,
Lalla6awa Aunty babba tayi da gudu tabar dining area ɗin ta koma cikin dakinsu,tana shiga ciki ta aza hannayenta asaman kanta tana faɗin"Na shiga uku!Na bani!na lalace!Waccen mahaukaciyar yarinyar tana son taja mun bala'e ina zaman zaman lafiyata,"tana magana tana cizon yatsan hannunta,"Aunty laila meya faru,"hayaam ce tayi mata tambayar,
"Hayaam ta faru ta ƙare!yarinyar can ta gama dani!"muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,hannu tasa tare da zame niqabin fuskarta,tayi wurgi dashi ƙasa,sannan tashiga zagaye ɗakin tana faman cizon yatsanta,
"Dan Allah kowa yayi haƙuri ya koma ya zauna,ina tunanin ciwon hosana ne ya motsa,ba wani abu ba shiyasa take ta sambatu,"Omar ne yayi maganar don ya kwantar masu da hankalinsu,
Fashewa da wani sabon kukan hosana tayi tana faɗin "Wlh ya Omar Ni da hankalina,da tunani na!nasan me nakeyi,wannan matar itace ta...."kasa ƙarasa maganar tayi saboda tsawar da Omar ya daka mata "Shut up hosana!bana son na ƙara jin maganarki a wurin nan!in ba haka ba saina sa6a maki," tafin hannunta tasa tare da toshe bakinta,tana yin kuka ƙasa kasa,
"Ka daina yi mata tsawa Omar,tabbas akwai abunda akayi ma yarinyar nan,wanda ya ƙona mata zuciya shiyasa take wannan sambatun,ya kamata mu lallasheta,muji menene matsalarta"? Acewar Abba,
Ishaq yace"hakane,In ba damuwa Inason ganinka Omar tare kuma da yaran,"
Ya ƙarasa maganar tare da shigewa gaba,Omar yabi bayansa hannunshi ruƙe dana hosana,jahad kuma na abayansu,
Bayan tafiyarsu,kowa ya koma ya zauna,wasu suka cigaba da cin abincinsu,wasu kuma suka bar dining ɗin waɗanda suka ƙoshi da abincin kenan,wurin yayi tsit kowa da abunda yake saƙawa aranshi,
A 6angarensu General ishaq kuwa,a farfajiyar gidan suka zauna saman wasu ƙayatattun kujeru na shakatawa,kowa ya zauna,Hosana da jahad suna fuskantar Ya Omar da kuma ya ishaq,
Gyaran murya ya ɗan yi tare da kallonsu yace"dalilin dayasa na buƙaci ganinku,saboda inason jin menene alaƙar dake atsakaninku da Laila matata?shin taya akai hosana ta santa da har take tsoran ganinta"?
Kafin su bashi amsa Omar yayi hanzarin cewa"Ae farko sun ta6a zama a wurinta,Ni na kaisu gidanka,a lokacin kayi tafiya,na damƙa amanarsu a wurin laila,saboda ina da tabbacin cewar zasu samu kyakkyawar kulawa a wurinta,tun da ita mace ce,zasu fi sakewa a wurinta,"
Tunda ishaq yaji hakan gabanshi ya fadi,saboda yasan halin laila sarai,bata da mutunci,saboda mugun halinta yasa masu aiki suke gudun gidan,duk ƴar aikin da sukayi ƙarshe guduwa takeyi daga gidan saboda masifarta,
janye idonshi yayi daga kan Omar dake magana,ya mayar dasu kansu jahad da hosana,yace"Ina sauraronku?A zaman da kukayi tare da laila me ya faru?
Jahad tace"babu komai,munyi zaman lafiya tare da ita,"tana rufe bakinta hosana tace"wlh ƙaryane!jahad ƙarya takeyi maku,batason ta faɗi gaskiya ne,"ta ƙarasa maganar tana matse kwallar data zubo mata a idanunta,
"Jahad!kinsan banason wasa!faɗamun gaskiyar abunda ya faru acikin gidan,bayan na barku," Marshal ne yayi maganar fuskarshi a ɗaure babu alamun wasa tattare dashi,hakan ne yasa jahad ta natsu ta shiga kora masu bayani,
"Ya Omar,tun lokacin da ka tafi kabarmu a gidan,Aunty laila ta rufe mu acikin wani tsohon store,babu ci babu sha,iska kanta daƙyar muke shaƙarta saboda wurin a ƙuntace yake,babu window,ga ƙwari dake yawo acikin store ɗin,ranar acikinsa muka kwana,hosana ko bacci bata samu ba......"gaba ɗaya jahad ta kwashe duk abunda ya faru dasu agidan Aunty babba,tun daga A har Z ta sanar masu,a ƙarshe ta fashe da kuka,
Ishaq kuwa ba abunda ke fitowa daga bakinshi sai kalmar innalillahi'wa inna ilaihirraji'un,'Muryarshi har kerma takeyi wurin cewa"Omar meyasa ka kaisu gidana ne?wlh da ace ka sanar dani tunda farko,da banbari ka kaisu wurin laila ba,saboda nasan halinta,hakanan nake zaune da ita,matar nan bata da imani!muguwace!yanzu ni bansan ya zanyi ba!da wani ido zan kalli Abusufyan da sauran ƴan uwana idan sukaji wannan Zaluncin da laila ta aikata ma Yaran nan!!
Yana magana,huci na fitowa daga bakinshi,ranshi yayi mugun 6aci idanuwanshi sunyi jawur,
Marshal Omar kuwa saboda tsabar 6acin rai,ya gaza buɗe baki yayi magana,tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu saboda takaicin abunda laila ta aikata ma su jahad,yaran da ya damƙa mata amanarsu,sai yanzu ya gane dalilin da yasa duk in yaje gidan a lokacin da suke wurinta,sai yaga fuskokinsu babu walwala ashe bayin Allah azabtar dasu takeyi,
Daƙyar ya iya buɗe baki yace"Amma Laila ta cuce Ni!ban ta6a tunanin zatayi mun haka ba,Meyasa zatayi mun haka?laifin me kuka aikata mata?kawai saboda taga baku da gata ne,don nace mata marayu ne ku shine ta ƙuntata rayuwarku?Ashe itace ta sanya wannan fasiƙin mutumin ya ɗauke ku acikin motarshi don ya zubar mata daku acikin dajin,har yayi ƙoƙarin Yima hosana fyaɗe acikin gidan gonarshi.... " sai yanzu ya gane dalilin da yasa Major yaƙi sanar dashi gaskiyar lamarin daya afku,koda ya tambayeshi a lokacin baya sai cewa yayi yalla6ai banso in shiga tsakaninka da Matar yayanka ne,Ashe mugun abu ta aikata masu,
A fusace Ishaq ya daki table ɗin dake agabansu,ya miƙe azabure yana ƙokarin zame belt ɗin wandonshi,a ƙoƙarinshi na ya shiga cikin gidan yayi ma Aunty babba bugun tsiya,
Da sauri Omar ya ruƙo hannunshi,"Ya ishaq,ba anan yakamata ka yanke mata hukunci ba,koba komai ita uwar ƴa'ƴanka ce,mutuncinta zai zube agaban kannenmu,da sauran mutanen gidan,inaso taci albarkacin wannan,"
Runtse ido ishaq yayi wani irin huci ke fita daga bakinsa,damƙar hannun Omar yayi tare da janye shi daga ruƙon da yayi mashi,ko waiwayenshi baiyi ba ya shige cikin gidan,
Jiki ansayaye Omar ya mayar da idanunshi kan su hosana dake tsaye,wani irin tausayinsu ne ya lullu6eshi,matsawa yayi tare da janyosu ya rungumesu ajikinshi,tamkar ya zubar masu da hawaye haka yake ji,Yayi danasanin kaisu wurin laila,bakomai ne yaja hakan ba fa ce rashin sani,cikin sanyin Murya yace"kuyi haƙuri ku yafe mun,duk laifina ne dana kaiku wurinta,wlh danasani kai tsaye Abuja na kawoku gidanmu,Ni duk atunanina zaku fi samun kulawa a wurinta,ƙaddarace kawai ta riga fata,Amma wlh da ace kun sanar dani tun lokacin da nake zuwa gidan,da saita ɗanɗani kuɗarta," ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga nasu,
Jahad tace"Ya Omar kadaina ɗaura ma kanka laifi,dama can Allah ya ruga da ya ƙaddara faruwar hakan,kuma yanzu ae komai ya wuce,ni wlh ba don hosana ta fara tona mata asiri ba,da babu wanda zaiji wannan maganar abakina,don har gargaɗin hosana nayi akan kada ta sanarma kowa amma bataji ba,"
Murmushi Omar ya ɗan yi tare da kallon hosana dake ta faman sauke ajiyar zuciya,ruƙo hannunta yayi cikin nashi sannan yace"Hosana tayi mun dai dai jahad!idan har aka biye ta taki,bazaki ta6a bari a hukunta mara gaskiya ba,saboda tausayinki,abunda nakeso ki gane jahad,Irin waɗannan mutanen masu baƙar zuciya,idan har ba'a dinga hukunta su ba,to basu ta6a gane kuskurensu,balle har suyi nadamar abunda suke aikatawa su daina," jinjina kai jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Hakane ya Omar,kayi gaskiya,Sehrish ma ta ta6a fadamun hakan,lokacin da nayi ƙokarin hukunta hosana akan tonan asirin da taso tayi ma matar Ya ishaq,' sun jima atsaye suna magana kafin daga bisani Omar ya ruƙo hannayensu tare da shigowa dasu cikin gidan,
Hankalin aunty babba fa yaƙi kwanciya,babban abunda takeyi ma fargaba shine kada Hosana ta tona mata asiri agaban surukansu,kusan sau uku tana shiga toilet saboda cikinta daya katsa,har wurin ƙarfe 2:30,bata daina safa da marwar nan ba,acikin ɗakin,ƙafafunta har sai da suka fara yi mata raɗaɗi sannan ta samu wuri ta zauna daga gefen gadon tana faman sakin huci,shigowa hafsat tayi cikin ɗakin,fuskarta jawur sae faman kuka takeyi,aunty babba na ganinta ta miƙe hankalinta a matuƙar tashe ta shiga tambayarta Meya faru,Cikin shessheƙar kuka hafsat tace"daddy ne,Yayi mun faɗa sosai akan abunda muka aikata masu hosana,har mari na sai da yayi,kuma yace daga yanzu babu ni babu shi,In nemi wani uban,!"
Hannu aunty babba ta aza asaman kanta tana ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!wayyo!nashiga uku!shikenan Hosana ta gama dani ta tona mun asiri wurinsu ishaq,Wayyo Ni laila,Zawarci ba fashi," tana magana tana cizon yatsanta,
Fitowar hayaam kenan daga cikin toilet taji suna wannan maganar,jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,babban abunda take ji ma tsoro shine Ishaq ya saki Laila,saboda tasan cewa muddin ya saki aunty babba,to zamanta a gidan ya qare!!tunda bata da wata aƙala dasu,!Tashin hankali,ishaq bai ta6a gigin ta6a jikin hafsat ba,duk irin girman laifin da take aikatawa,amma yau akansu hosana Tasha mari,idan har hakane menene hukuncin aunty babba?ita da ta ɗauki nauyin shirin gaba daya,OMG!! Rungumota hayaam tayi ajikinta tana lallashinta,daƙyar ta samu hafsat tayi shiru,
*Boss Bature*
❤🤍❤
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Wuraren ƙarfe shida na marece,ta fito daga cikin toilet,jikinta na sanye da towel fari ta ɗaure shi a saman ƙirjinta,da alama wanka tayi aciki,jahad ta samu zaune saman gadonsu,hannunta ɗauke da wayarta tana ɗan daddanawa,tsayawa tayi a ƙopar toilet ɗin ta ruqe ƙugunta tare da ɗan ɗaure fuskarta tace"Jahad!bana hanaki ɗaukarmin waya ba?kin manta abunda ya faru ran nan?kika kusa kashe mun waya gaba ɗaya!,yanzu da ace ta lalace dashi kenan wa zai siyamun wata"?
Fuskar jahad ɗauke da murmushi tace"Daddy mana!ae yace zai siya mana Phones gaba ɗayanmu,hada ke ma zai canza maki wata,hada ma laptop xai siya mana,"
Washe baki Sehrish tayi tare da cewa"Wai dagaske"?
"Eh,mana,shi da kanshi ya faɗi hakan,Kuma yace next week zamu koma school da kanshi zai mayar damu,don kada wani ya ɗaga mana yatsa,"ta ƙarasa maganar fuskarta dauke da dariya,sehrish kuwa tunda jahad tayi maganar school ba kowa ya faɗo mata aranta ba,face ƙawarta AMRISH,lokaci guda ta faɗo mata acikin ranta,nan take kuma taji gabanta ya faɗi rass,
Ganin fuskarta da alamun damuwa atattare da ita,yasa jahad kiran sunanta"Sehrish,meya faru ne?maimakon inga kina farin ciki?ko baki son komawa school ne?baki gaji da zaman kashe wando ba acikin gida?
Muryarta asanyaye tace"ba haka bane jahad,kawai na tuna da wata school friend ɗita ne,Nayi missing ɗinta sosai,Yarinyar tana sona sosai,itace take ƙarfafa mun guiwa akan in ringa yin karatu,in daina bacci a class,Gaskiya banyi mata adalci ba,sam na manta da ita,ni nasan cewa amrish ta neme ni har ta gaji,"
Jahad tace"Eyya,gaskiya baki kyauta mata ba,gashi sunan ku shigen iri ɗaya ke da ita,ni tun kafin ma in ganta har naji ina sonta,saboda tana son ƴar uwata sosai,Amma meyasa ba zaki jaraba kiranta ba tunda ga waya ko baki da numbarta ne?
"Ina da numbarta,kinsan kwanakin nan hankali na duk ba'a kwance yake ba,tun lokacin da muka daina zuwa school,ban ƙara bi takan wayar ba,sai ma na ganta a hannunki ne sannan nake tunawa da cewar ina da waya,Allah sarki Amrish ɗina,bansan wani hali take ciki ba,gashi bansan gidansu ba,"
Mikewa jahad tayi ta nufi wurin da Sehrish take tsaye,mika mata wayar tayi tare da cewa"Ki jaraba kiranta mana,sai mu gaisa,"
Kar6ar wayar Sehrish tayi,ta shiga cikin contacts ɗinta,ta lalubo numbar amrish,sae dai kash tana kiran layin taji wayar akashe,ɗayan layinta na Airtel ta kira shima akashe yake,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
"Bansan meyasa ba'a samun layinta ba,amma mu bari da anjima sae mu jaraba kiranta mu gani kilan ta kunna wayar,"tayi maganar tare da miƙa ma jahad wayar ta kar6a,sannan ta koma gefen gadon ta zauna,ita kuma ta wuce gaban wardrobe tana lalubar kayan da zata sanya,
Turo ƙopar ɗakin nasu hosana tayi,da sallama abakinta,juyowa sehrish tayi tana kallonta haka itama jahad,
Nuna Sehrish tayi da yatsanta manuni,kafin tace"RISHI KIZO INJI DADDYN MU YACE KI SAME SHI A ƊAKIN SHI,KADA KI WUCE MINTI BIYAR"
Rasss!taji gabanta ya faɗi,
"Hosana dagaske ni daddy ke kira?kuma ni kaɗai yace inzo"?
"Eh,ke kaɗae yake son gani,"
Cikin sauri ta juya tare da zura hannunta cikin wardrobe ɗin,ta lalubo wasu pakistan riga da wando,rigar fara ce,har guiwa daga ƙasanta kwalliyar duwatsu ne,wandon kuma pink colour ne,bai da kwalliya ajikinsa,irin falazun nan ne burgujeje,mayafin kayan ta yafa Shima pink colour,gaban madubi ta koma ta ɗauki flower bomb ɗinta,ta feshe jikinta dashi,sai da ta fara kallon fuskarta a mirror ta ɗan sakarwa kanta murmushi,sannan ta kama hanyar fita daga ɗakin,
Jahad tace"Allah yasa alkhairi ne!kullum in daddy zai kiramu atare yake kiranmu amma yau ke kaɗae kawai yake son gani,"ta ƙarasa maganar tana nuna bayan sehrish da hannunta,
Murmushi kawai ta saki kafin ta buɗe ƙopar ta fuce,
Da sauri da sauri take tafiya don karta wuce minti biyar ɗin da Hosana tace,tana ƙarasawa baƙin ƙopar ɗakin takai hannu kenan zata buɗe,taga an ja ƙopar daga cikin ɗakin,da alama wani ne zai fito,zubama dogayen yatsun hannunshi ido tayi,farare tass ya ruƙe handle ɗin ƙopar dasu,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga ɗakin,nan take ta gane Cewa BABBAN YAYA NE,mamaki ta shiga yi mai ya kawo babban yaya a ɗakin daddynsu?bayan sa6anin da suka samu a tsakaninsu,ko sun shirya ne,?
Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,SGR ya ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin Abusufyan,wankan suit ne ajikinshi farare,kyau iya kyau,
Tsayawa yayi cak kamar an dakatar dashi,Sehrish kuwa tuni gabanta ya shiga faɗuwa,tun daga ƙasa har sama yabi ta da kallo,Yarinyar ko ƙafaɗarshi tsayinta bai kai ba,
Daƙyar sehrish ta iya buɗe baki tace mashi"Ina yini"
Tamkar bazai amsa mata ba,don har sai da ya wuceta ya ɗan yi nisa sannan taji yace"Lafiya,"yana faɗin hakan ya ƙara gaba,su babban yaya irin wannan shan ƙamshi haka,
Jiki asanyaye ta shiga cikin ɗakin da sallama abakinta,A zaune ta samu Uncle abusufyan,daga gefen gadonshi,juyowa yayi tare da kallonta fuskar nan tashi ɗauke da murmushi yace"Daughter,"
"Na'am daddy,ta amsa mashi tare da ƙarasawa,ta samu wuri saman sofa ɗin dake fuskantar gadonshi ta zauna,suna facing ɗin juna ita dashi,sannan tace"gani daddy hosana ce ta sanar dani cewa kana nema na,"
"Eh hakane,ni na ce ta kira mun ke,"
Natsuwa tayi tana jiran jin me zaice mata,sae faman wasa takeyi da yatsun hannunta,
"Gobe yaushe"?yayi tambayar yana kallonta,
..fuskarta ɗauke da murmushi tace"Friday," jinjina kanshi yayi tare da cewa"Masha Allah,Juma'a babbar rana,zaifi kyau in aka kafa tarihi aranar juma'a,ina tunanin kamar zai yi wuya a manta dashi,ko ba haka ba daughter?
Dariya sehrish tayi kafin tace"gaskiya ne daddy,juma'a itace babbar rana,duk abunda ya faru a ranar friday,zaiyi wuya a manta dashi,"
Abusufyan yace"Shiyasa nake so gobe na ɗaura maki aure,ko bakya so"?
Da sauri tasa tafukan hannunta tare da rufe fuskarta,tana dariya,
"Na ƙosa na fara ganin ƴan jikoki na," cikin zolaya yayi mata maganar,
"Dan Allah daddy,ka daina faɗin haka wlh kunya nake ji," cikin shagawa6a tayi maganar har lokacin bata zame tafin hannunta daga saman fuskarta ba,
Miƙa hannu Abusufyan yayi tare da janyo drawer chest ɗinsa gida na tsakiya,ya ɗauko wani small box Golden Colour mai shegen kyau,sae faman ƙyalli yake yi yadda kasan da Zallar Zinari akayi shi,
Ruƙo shi yayi a hannunshi yana jujjuya shi,ɗan ɗagowa yayi yana kallon sehrish wadda ta rufe fuskarta,
Gyaran murya yayi mata tare da cewa"Buɗe fuskarki mana," a hankali ta zame hannunta daga kan fuskarta,kai tsaye idanunta suka sauka kan small box ɗin dake hannun Daddynsu,ɗan zaro idanunta tayi tana ƙare mashi kallo,akwatin ya burgeta sosai,jikinshi sae ƙyalli yakeyi mai matuƙar ɗaukar ido,da jan hankali,cike da zumuɗi tace"daddy wannan fa?wlh yayi kyau sosai,ban ta6a ganin irin shi ba,"
Ƴar dariya Abusufyan yayi tare da cewa"koya burge ki ne"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Jujjuya akwatin yayi tare da cewa"Sadakin wata Ne,aka biya da Gold,"
Waro ido waje sehrish tayi cike da mamaki tace"daddy!dagaske ka ke dowry ne aka biya da Gold,but daddy who's she? Dariya abusufyan ya kuma yi ganin yadda tabi ta ruɗe da jin abunda yace,
"Dagaske nake ba wasa ba,sadakin wata Mai sa'a ce,Jinin nasara,"
"Daddy,can i see it pls"?
Miƙa mata small box ɗin yayi hannunta har kerma yake yi wurin kar6arsa,janyewa Abusufyan yayi fuskar nan tashi ɗauke da dariya yace"Da hannun hagu kuma?hannu biyu zaki sa ki kar6a,sannan in zaki kar6a ki tabbatar da kinyi bismillah,don Abun yayi albarka,"
Murmushi sehrish tayi tare da gyara natsuwarta,sannan ta miƙa hannanyenta duka biyun,tayi bismillah kafin ta kar6e shi daga hannun abusufyan,wani irin sanyi ne taji ya ratsata,jujjuya akwatin ta shiga yi tana ƙare mashi kallo,yana da nauyi duk da ƙarantar shi,hakan ya tabbatar mata da cewar,abune mai daraja acikinsa,ƙoƙarin buɗe akwatin ta shiga yi,da sauri Abusufyan ya dakatar da ita"kada ki buɗe shi,ki adana shi a wurinki,bana so kowa ya gani,kuma kada kowa yasan inda kika ajiye shi,"
Abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,
"Amma daddy,sadakin wata ne fa?kuma naji ka ce in ajiye shi a wurina,saboda Me"?
Bai bata amsa ba,sae ma kwantar da bayanshi da yayi saman gadon nashi,ya ɗan kishingiɗa,ya aza kansa saman pillow,yana kallonta,ta zuba mashi ido tana jiran jin amsar da zai bata,
Ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abusufyan,ya jima ahaka suna kallon kallo shi da Ƴar tashi,kafin yace"Zaki samu amsar tambayarki,amma ba yanzu ba,ki bani lokaci zan neme ki,yanzu zaki iya tafiya,"ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanyar fita daga ɗakin,
Tamkar wadda aka zarewa lakar jikinta,haka ta miƙe jiki ba kwari,wani irin faɗuwar gaba kawai take ji,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta,tana tafiya tana waiwayen daddyn nasu,daya zuba mata ido yana kallonta,tabbas akwai wani abu da yake 6oye mata,sai da takai bakin ƙopar ɗakin,tana ƙoƙarin buɗe kopar ta fita,taji ya ambaci sunanta
"SEHRISH" da sauri ta juya tana kallonshi,
"Game da abunda ya faru tsakaninki da babban yayanku,Nasan ranshi ya 6aci sosai,ya baki Umarnin kiyi mashi aiki,amma na hanaki a matsayina na mahaifin ki,inaso kije ki bashi haƙuri,'
Waro ido waje sehrish tayi a ɗan tsorace tace"daddy in bashi haƙuri fa ka ce?wlh tsoro nake ji,jiya ranshi ya 6aci sosai,idan na kuskura naje wurinshi yau karya ni zaiyi nasan,"
Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba,fuskarta tamkar zatayi kuka,
"Don't worry ur self,SGR bazai ta6a gigin bugunki ba,saboda ba halayyarsa bace,"
Haɗiyar yawu tayi,tana sauraronshi,ɗan dakatawa yayi da yin maganar,kafin ya ɗaura da cewa"daga yanzu inaso,ki cigaba da aiki a ƙarkashinsa....' tunkan ya ƙarasa maganar Sehrish tace"Amma daddy,ka hanani zuwa part ɗinsa fa"
"A yanzu na soke wannan!inaso ki yi mashi biyayya,ki bishi sau da ƙafa,komai yake so kiyi mashi kawai!part ɗinsa kuma koda wani lokaci zaki iya zuwa ki shiga,even in the midnight,indai ya buƙaci ganinki ki je kawai,"
Gaba ɗaya Abusufyan ya gama ruɗar da ita,la66anta har kerma sukeyi wurin cewa"dad..dy!bangane me kake nufi ba,dan Allah ka fahimtar dani,"
"Ki tafi kawai kiyi duk abunda nace maki,idan lokaci yayi zan sanar maki,"
Juyawa tayi tare da zura ƙafarta,tabar bedroom ɗin nashi,lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu,ya ƙurama ceilling ɗin sama ido yana kallonshi tamkar mai karanta wani abu ajikinshi,tunani ya shiga yi acikin zuciyarshi,ya shiga tariyo abunda yaji a kunnuwansa,
_Na amince zan aureta,bana son abun ya ɗauki lokaci,bana son taron mutane,kuma banaso kowa ya sani,saboda ba auren dundundun bane,nan da wata uku zan sake ta,zan aureta ne ba don ina sonta matsayin matata ba,sae don tayi mun aiki kafin na bar nigeria_
Hannu Abusufyan yasa tare da ɗaukar wata takarda dake ajiye saman side drawer ɗinshi,zuba ma takardar ido yayi yana kallonta,Agreement paper ce (Takardar yarjejeniya)mai ɗauke da signatures na mutun uku,"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da zura ta cikin drawer chest ɗin daya fiddo akwatin nan da ya bama sehrish ya sanya takardar aciki ya ajiyeta,sannan ya mayar da ita ya datse,rufe idanunshi yayi bakowa bane ya faɗo mashi arai ba face ABU,nan take yaji kewarta ta lullu6e shi,Allah sarki abu,tana raye kota mutu?
A 6angaren Sehrish kuwa bayan fitarta daga bedroom ɗin Abusufyan,a ƙopar ɗakinsu ta tsaya,warware mayafin da ta laga akanta tayi,sannan ta lullu6e small box ɗin dake hannunta don kada wani ya gani,tura ƙopar ɗakin tayi sannan ta shiga daga ciki,babu kowa acikin ɗakin,sautin ruwan da taji ne daga cikin toilet ya tabbatar mata da cewar Jahad ce ke wanka,cikin sauri ta lalla6a gaban dressing mirror ɗinsu,ta zuƙunna gaban drawer ɗin dake ɗauke da mirror ɗin,ta janyo gida na ƙarshe,ta tura small box ɗin acikinsa can ƙurya ta turashi,sannan ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,miƙewa tsaye tayi har lokacin bata daina mamakin abubuwan da Uncle ya faɗa mata ba,abun ya ɗaure mata kai sosai,
Safa da marwa ta shiga yi acikin ɗakin,takasa zama saboda yanayin da ta tsinci kanta aciki,
*Boss Bature*
❤🤍❤
AMRISH,
Tun jiya da daddare data farka,tana bullayi asaman gadon bayan an samu nasarar ceto rayuwarta,doctor yayi mata allurar bacci bata ƙara farkawa ba,yini tayi a kwance tana bacci kamar matacciya,hankalinsu zeenatu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,musamman Mommyn Amrish ɗin,bata ta6a tunanin amrish zata rayu ba,amma cikin ikon Allah sae gashi taji sauƙi sosai,poison ɗin da tasha bai kaiga yi mata illa ba,sunyi gaggawar kaita asibitin kuma likotoci sun taru akanta wurin ceto rayuwarta,wannan ne yasa bata jigata ba sosae,amma still da sauranta don ba ƙaramin galabaita tayi ba,yanzu haka ma ƙarin ruwa ne aka sanya mata,
Mommynta na zaune asaman plastic chair din dake agaban gadonta,fuskar nan tayi jawur da alama ba ƙaramin kuka tasha ba,ga rashin baccin da basu samu ba adaren jiya,gaba ɗaya hankalinta na akan Amrish dake kwance magashiyan tana bacci,
Zeenatu na a zaune daga gefen gadon da amrish ɗin take kwance,duk sunyi zuru suna kallonta,tunda safe Sofia ta koma gidansu,ita kaɗae ta rage saboda tace bazata koma gidansu ba har sai Amrish taji sauƙi sun koma gida,
Suna cikin zaman nan,kwatsam Amrish ta buɗe idanunta ta zazzaresu a wani irin firgice ta sanya hannu ta fizge robar ƙarin ruwan da akeyi mata,hankali atashe Zeenatu tace"Mommy amrish ta farka!ta cire ƙarin ruwan da aka sa mata,"jin wannan maganar yasa Mommyn yin firgit ta dawo cikin hayyacinta daga zurfin tunanin da ta shiga,sai dai kafin suyi wani yunƙuri,tuni Amrish ta diro daga saman gadon,ta watsa aguje,zeenatu na ƙoƙarin tarota,takai mata wani kakkwaran naushi a saitin Cikinta,nan take zeenatu ta zube ƙasa hannunta dafe da cikin,ta fasa uwar ƙara tana faɗin"Wayyo Allah na!cikina!nashiga uku,
Ko waiwayonta amrish batayi ba,hanyar fita kawai ta nufa,da gudu ta fice daga ɗakin,bin bayanta Mommyn tayi tana yarfa hannu a ruɗe take faɗin"Help!help!!dan Allah jama'a ataimaka a taro mun ita!mara lafiyace zata gudu,'
Da gudu wasu nurses suka bi bayan amrish,hada wasu daga cikin masu zuwa dubiya,
"Amrish dan Allah ki tsaya!wai meke damunki ne!bakiji ina magana ba!ina zaki je ne!," hankali tashe mommyn ke magana,amma ko sauraronta amrish bata yi ba,duk wanda ma yayi ƙoƙarin tarota bugu take kai mashi kamar ƴar wrestling,gashi wani irin ƙarfine da ita kamar na Doki,in ta daki mutun sai ya kusa zaucewa,duk yadda suka so su kama amrish,amma abun yaci tura,domin kuwa 6att suka neme ta suka rasa acikin asibitin,saƙo da lungu babu inda basu duba ba,amma babu ita babu alamarta,ko mai kama da ita ma babu,nan fa hankalin kowa ya tashi,hatta security guards ɗin dake tsaron gate ɗin asibitin,sae da aka tambayesu,sun tabbatar da cewar basu ga fitarta daga asibitin ba,sae dai ko a wani wurin ta 6oye,Hatta Cctv footage sae da aka bincika,amma ba aga ta hanyar da Amrish tabar cikin hospital ɗin ba,kuma ba'aga wurin da ta 6oye ba,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,yarinya kamar mai iskokai?babban abunda zai baka mamaki ƙarfin daya zo mata,mutumin dake kwance magashiyan a gadon asibiti,amma ya tashi farat daya da irin ƙarfin nan a jikinshi❓
Saboda tsabar tashin hankalin da Mommyn Amrish ta shiga,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume,sai dai nurses suka cuccu6eta aka shiga da ita ciki,suka kwantar,itama zeenatu sae da suka kwantar da ita don kuwa ba ƙaramin buguwa tayi ba,naushi ɗaya tayi mata aciki,amma sae da jini ya zuba a bakinta,
*ANA WATA GA WATA!JAMA'A INA AMRISH TA SHIGA NE*?😳😳😳
*Aunty Babba*
Fitowarta kenan daga cikin toilet tana faman dafe cikinta,ɗagowa tayi tana kallon hayaam dake zaune gefen gadon ta zabga uban tagumi da hannayenta biyu,Hafsat kuwa na asaman gadon kwance ta lullu6e da bargo jikinta sae kerma yake yi,wani irin zazza6ine mai zafi ya rufar mata,tunda rana tagaza motsa jikinta,abun gwanin ban tausayi,
Kwatsam!sukaji an banko ƙopar ɗakin nasu,dafe ƙirji Aunty babba tayi tana kallonshi,sae faman huci yakeyi yadda kasan mayunwacin zaki,da ƙafarsa ya tura ƙopar ɗakin ta rufe,hayaam na ganinshi a razane ta haye saman gadon,jiki na rawa ta wuntsila daga ƙasan gadon ta 6oye,tana faman zazzare ido,
Cikin inda inda ta ambaci sunan shi"I..ishaq!"
A zafafe ya ƙarasa inda take,kwakkwarar damƙa yakai ma wuyanta,ya shaqeta sosai,yadda ko ihu bazata iyayi ba,saboda tsabar raɗaɗin da taji nan take ta saki fitsari a wando,wani irin gumi ne ya shiga tsattsafowa daga gefen fuskarta,idanunta sunyi jawur cike tab da kwalla,ƙwayar idon tamkar zata zazzago ƙasa,
A ruɗe hafsat ta fasa uwar ƙara,ganin abunda daddynta ke ƙoƙarin yi,gadan gadan so yake ya kashe Mommynta,da gudun gaske ta duro daga saman gadon tana kuka,
"Kafin ki kashe su!Ni zan fara kashe ki!muguwa kawai!Nayi danasanin aurenki laila!nayi danasanin saninki da nayi,Nayi danasanin haɗa zuri'a ɗaya dake,Allah ya isa tsakani na dake!Na tsaneki!kin fita araina!ban sonki!bansan ganinki!"daƙyar sautin muryarshi ke fita saboda tsabar 6acin rai,a fusace ya buga kanta jikin bango,nan take Aunty babba ta baje ƙasa a sume,'
Juyawa yayi tare da aza idanunshi akan hafsat dake tsaye tana faman zabga uban kuka fuskarnan tayi jaga jaga da hawaye hada majina,nunata yayi da yatsan hannunshi sannan yace"dake da uwarki!ku tattara kayanku ku bar gidan nan!tun kafin inyi sanadin mutuwarku!muguye kawai waɗanda ba Allah aransu,"
Hannu hafsat ta aza akanta tana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!"
Juyawa ishaq yayi da sauri zai bar ɗakin,da gudun gaske ta ruƙo rigar jikinshi tare da zubewa saman guiwowinta tana kuka tana yi mashi magiya akan,karya koreta,
"Daddy dan Allah kayi haƙuri ka yafe mun!wlh ba laifina bane,nasan mun cutar dasu,amma inaso ka sani daga baya na ƙaunace su,Daddy ka yarda dani Mommy itace take azabtar dasu,kuma itace tayi silar barin....'bata ƙarasa maganar ba sakamakon bugun daya kai mata da ƙafarshi,da sauri ta dafe gefen bakinta daya buga wurin har ya fashe,jini ya shiga ɗiɗɗigowa,dogon tsoki ishaq yaja tare da cewa"Kada ki kuskura ki ƙara kirana da sunan daddy!don ni ban haifi wata ƴa mai suna hafsat ba!tunda har kin za6i ki bi mugun hali irin na mommynki,don haka gaki ga ita,duk in da zata je ƙafarki ƙafarta,karku kuskura Dare yayi maku acikin gidan nan!don wlh sai kunyi danasanin haihuwarku da akayi acikin duniyar nan!don bazan raga maku ba,tamkar ban sanku ba,haka zan hukunta ku!kuma idan ta farka daga suman da tayi ki sanar da ita cewa NI ISHAQ NA SAKE TA,!!!!
Wani irin bugu zuciyar hayaam tayi ji kake daramm!!kamar an buga ganga,nan take ido ya raina fata,sae faman mazurai takeyi abayan gadon da ta la6e,Na shiga uku Ni hayaam An saki Aunty laila!Shikenan komai ya ƙare komai ya lalace!mun gama yawo!!
Ya ƙarasa maganar tare da kai hannu tamkar zai 6alle ƙofar ya fuce,Amani dake la6e tana sauraronsu da gudun gaske ta watsa,sae cikin ɗakin da suka sauka,Tana shiga cikin ɗakin ta daka tsalle,bakinta awashe saboda tsabar dariyar mugunta hada hawaye ke fita a idonta,Amal dake zaune saman gado tana buga game a wayar amani,ganin yadda amani keta dariya kamar wata zautacciya,yasa ta ɗan dakata da buga game ɗin tare da cewa"Aunty Amani meya sanyaki farin ciki har haka"?
Daƙyar ta iya dakatawa da yin dariyar tace"Amal ba zaki gane bane,Wani buri da nake dashi ne ya cika ayau ɗin nan!!waɗanda suka jima suna ƙuntata rayuwarmu,tun yau zasu fara gir6ar abunda suka shuka," tana magana tana dariya,
Murmushi kawai Amal tayi tare da mayar da hankalinta kan game ɗin da take bugawa,
General ishaq na fita daga ɗakin,hayaam ta lalla6a ta fito,yadda kasan lagwanin fitila haka take tafiya,jikin taƙaura yayi la'asar wannan hada magriba ma,zuƙunnawa tayi gaban Aunty babba dake baje ƙasa,ta fashe da wani irin matsanancin kuka,Hafsat na kuka itama tana kuka,babu mai lallashin wani,kowa takansa yake yi,
Cikin shessheƙar kuka hafsat ta soma magana"Allah ya isa tsakanina dake Aunty hayaam,kun cuci rayuwata duk don saboda ku ne mommy ta aikata abunda ta aikata don taga ta cika muku burinku,gashi nan yanzu abun ya shafe ni,kunja daddyna ya kore ni,Ni bansan ku wasu irin mutane bane!sam baku da zuciya kare ya lashe,kun nace kun liƙe dole sai kunyi arziƙi da gumin wasu,ku bazaku tashi ku nemi na kanku ba,sam babu Allah aranku,mugunta kawai kukasa agaba,shiyasa har yau babu wani cigaba acikin lamurranku!wlh yanzu ma kuka fara gani!indai bazaku koma ga Allah ba,,ku tsaya a iya matsayin da Allah ya ajiye ku,ku daina hangen na wasu,wannan dogon burin da kwaɗayin abun duniyar ba inda zai kai ku face ya jefa ku ga halaka....."
Itadae hayaam bata tanka mata ba,saboda bata da abun cewa,har wani zazza6i take ji ajikinta,saboda tsabar tashin hankalin da take ciki,komai ya jagule masu,
Miƙewa hafsat tayi,jiki ba ƙwari ta ƙarasa tare da janyo trolley ɗin kayansu da suka zo dashi,janshi tayi izuwa gaban wardrobe ɗin hayaam,ta buɗeta,kayansu dake aciki tashiga fitowa tana ninkesu,Cikin trolley ɗin take jerasu,
Miƙewa hayaam tayi tana tunanin inda zata samu ruwa ta yayyafa ma Aunty babba,saboda babu ruwa acikin ɗakin,kuma tana jin tsoron ta fita waje suci karo da mutumin,tana cikin wannan tunanin ta tuna da akwai fanfo cikin toilet,da sauri ta shiga ciki a tafin hannayenta ta tarbo ruwan,da sauri da sauri tazo ta yarfa mata shi a fuskarta,dogon numfashi Aunty babba taja,tun kafin ta buɗe idanunta ta shiga fadin"Ruwa!Ruwa!" jin haka yasa hayaam yin tunanin ta fita waje ta samo mata ruwan,buɗe kopar dakin tayi cikin sanɗa ta fito tana tafiya acikin corridor din dakunan nasu,cikin sa'a ta taras babu kowa a main palour din,ƙarasawa tayi wurin fridge ɗinsu,ta bude jikinta na kerma ta ɗauko robar ruwa,da gudu ta koma cikin ɗakin,
Ƙarasawa tayi tare da taimaka ma Aunty babba ta tashi zaune sannan ta miƙa mata bottle water ɗin,A tsiyace ta 6alle murfin robar,ta kafata a bakinta,yadda kasan zata haɗa da robar duka ta cinye,abun kamar yaƙi,ta damƙi robar,sae kwankwaɗar ruwan take,kwatt!kwatt!!har sae da ta shanye ruwan duka tass,sannan ta saki robar ƙasa,sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi,hannunta na dafe da kakkauran wuyanta sae faman Murzarshi takeyi,wurin sae raɗaɗi yake yi mata kamar an barbaɗa mata attarugu,idanuwan nan nata sunyi jawur luhu luhu,sae da tadawo cikin hayyacinta sosai sannan ta kalli Hayaam tare da cewa"hayaam meya faru dani ne?ya akai na ganni akwance ƙasa?
Kafin hayaam ta buɗe baki tayi magana,tuni hafsat ta katse mata hanzarinta da cewa"Mommy!kina nufin cewa kin manta duk abunda ya faru?idan ma kin manta bari na tuna maki,Dadddy ne ya damƙi wuyanki ya shaqeki,sannan ya bugaki ajikin bango har saida kika suma,"
Shiru aunty babba tayi tana tariyo abunda ya faru,
"kuma yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan,kada mu bari dare yayi mana,bayan haka kuma ya dankara maki saki ɗaya"rai a6ace hafsat ke maganar,
Wata irin mahaukaciyar dariya Aunty babba ta kwashe da ita kamar wata zautacciya,hakan ba ƙaramin mamaki ya basu ba,miƙewa tsaye tayi tana gyara ɗaurin ɗankwalinta tace"Da sauƙi ma,Ni nayi tunanin wani mummunan hukunci zai yanke mun,sai me don ya kore ni?sakin ma da yayi mun wlh ko ajikina,yayi a banza Ae akwai sauran igiyoyi guda biyu,Ni nasan cewa muddin Abbansu yaji cewar ya sake ni,sae yasa ya mayar dani,Ae ni wlh gaba takaini gobarar titi A jos!" To fa,
sakin baki hafsat tayi galala tana kallonta,ba ita kaɗae ba hatta hayaam abun ya ɗaure mata kai,sunyi tunanin cewa in taji ishaq ya sake ta,xata haukace masu ne,amma sae gashi ko ajikinta!zuciyar ta bushe,
Sae faman tiƙar dariya takeyi kamar sabon shiga a fagen hauka,lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta,tare da kallon hayaam tace"Maza ki tattara kayanki,don atare dake zamu tafi,"
Hankali tashe hayaam tace"Ni kuma?saboda me zamu tafi atare"?
Shu'umin murmushin nan nata tasaki kafin tace"Saboda inaso,muje wurin bokan nan baba ibliss!wannan karan ba fashi,Dole in kawo ƙarshen auren Amani!kamar yadda zanyi zawarci itama haka nakeso tayi shi,sannan waccen mahaukaciyar yarinyar da tayi silar tona mun asiri har ishaq ya sanya hannunshi ya shaqe mun wuyana na kusa sheqawa barzahu wlh saina yi Ajalinta!!!sannan kuma aurenki da Sgr ba fashi!Wlh ko ta halin ƙaƙa!ko suna so ko basa so sai an ɗaura shi!In har kika ga ba'ayi auren nan ba!To sai dai in bana a doron duniyar nan!ko kuma shi RAFAYET ɗin Ya daina numfashi ne acikinta!sai dai kowa ya rasa wlh!da alama har yanzu basu san wacece Ni ba!zan nuna masu true colour ɗina!Ni dasu shege ka fasa!!" tana magana tana fitar da huci,
Mugun abu kokayi bacci?yace idona biyu 👀!ANA WATA GA WATA,
Zuru hafsat tayi tana kallonta,abun yafi ƙarfinta,lamarin Mommyn nata sae addu'a,tunani ta shiga yi anya Mommynta bata fara shaye shaye ba?kodai tana da iskokai ne?
Suna cikin wannan tsayuwar,aka kwankwaso ƙopar ɗakin nasu,a tsiwace Aunty babba tace"Wanene"?
"OMAR NE" koda jin muryar marshal Omar nan fa kowa ya shiga taitayinsa,
"Hayaam je ki buɗe mashi ƙopa,muji dame yazo!in shima zuwa yayi don yaci mutunci na to bismillah!kowani shege dai dai nake dashi,"kamar wata ƴar daba haka take maganar,
Buɗe mashi ƙopa Hayaaam tayi,tun daga irin kallon da taga Omar ya watsa mata tuni tashiga ƴan kame kame tana sunnar da kai,
Shiga cikin ɗakin nasu yayi,yayin da idanunshi ke akan Aunty babba wadda ke tsaye ta ruƙe qugu,sae faman jijjiga jikinta takeyi kamar wata ƴar bori,
Janye idanunshi yayi daga kanta ya mayar dasu kan hafsat,wadda ke tsaye ruƙe da trolley ɗin kayansu,ganin yana kallonta ne yasa ta ɗukar da kanta ƙasa cike da jin kunyarshi,
"Ina zaki je ne"? Yayi maganar fuskarshi a ɗaure,
Muryarta na rawa tace"dad..dy ne yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan kada mu kuskura mu bari dare yayi mana anan,"
"Ban da ke!su kaɗai zasu tafi,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,har ta gaza rufe bakinta saboda tsabar farin ciki,"
Mayar da idanunshi yayi kan Aunty babba dake tsaye ruqe da qugu yace"Major na awaje yana jiranku,idan kun kammala shiryawa ku same shi,Nayi mashi magana zai kai ku hotel ɗin da zaku kwana kafin gobe da safe sae ku wuce maiduguri,Amma fa in kuna so kenan,sannan kuma....'ya ɗan dakata da yin maganar tare da zura hannunshi cikin aljihun jeans ɗin dake ajikinshi ya zaro bendir ɗin kuɗi na ƴan dubu dubu,a ƙalla zasu yi dubu ɗari ɗaya,ya miƙa masu,jiki na rawa hayaam ta kar6e kuɗin tana yi mashi godiya,
...murmushi Marshal Omar ya saki tare da cewa"No,ba sai kin gode mun ba,nayi ne don Allah,'
Yana kai ƙarshen maganar ya juya tare da fucewa daga dakin yana dariya gami da girgiza kanshi,
Bayan fitarshi aunty babba ta buga tsoki,tana faman hura hanci tace ma hayaam"maza ki shirya mana kayanmu,naji ana kiran sallar magrib,zae fi mu lalla6a mu fuce daga gidan batare da kowa ya ganmu ba,nasan duk sun tafi salla,"
Amsa mata hayaam tayi da toh,sannan ta juya tare da shigewa cikin toilet,
Hankalin hafsat ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana faman sakin murmushi,dama babban tashin hankalinta shine idan tabi su Aunty babba maiduguri bazata iya rayuwa cikin gidansu ba,sau ɗaya ta ta6a zuwa,bataji daɗin zama agidan ba,muggan talakawa ne,babu wani abu na more rayuwa acikin gidan,sae ma abun haushi da takaici da zaka taras,
Kusan minti Goma shabiyar sai ga aunty babba ta fito daga cikin toilet ɗin,da alama wanka tayi,xanin atampar jikinta ne tayi ɗaurin gaba dashi,ya jiƙe sharkaf saboda ta ɗauraye shi acikin toilet da ta shiga,
Batare da 6ata lokaci ba,suka shirya tsaf ita da hayaam,dogayen riguna suka sanya ajikinsu,sannan suka aza mayafi daga sama,kama hanyar fita daga ɗakin sukayi,ɗan juyowa aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace"sannu hakima yayi maki dai dai wato hankalinki kwance zaki rabu da Mommynki ko rakiya babu"?
Miƙewa hafsat tayi tare da bin bayansu,suka fuce daga cikin ɗakin,ta ƙopar baya suka bi don kada wani yaga fitarsu,a waje suka samu Major tsaye jikin motarshi,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,yana ganin sun fito da sauri ya buɗe masu motar,
"Allah ya kiyaye hanya mommy,in sha Allah gobe da safe kafin ku wuce maidugurin zan kiraki a waya,"
Harara aunty babba ta watsa mata kafin tace"Munafuka!Hada wani raku6e fuska kamar irin zakiyi kewata ɗinnan!Ae kada ki damu ki sha kuruminki in dai ni ce zan dawo ne!nan bada jimawa ba,"tayi maganar tare da kutsa kai ta shiga cikin Motar,
"Aunty hayaam Allah ya tsare hanya,Ni dai zan wuce ciki,"
Murmushin yaƙe hayaam tayi,tare da janyota ta rungumeta,daga bisani ta shiga cikin motar,batare da 6ata lokaci ba,Mojar ya shiga mazaunin driver,yayi ma motar key,yaja ta da gudun gaske,Fashewa da kuka hayaam tayi tana leƙen gidan ta cikin gilashin motar,aunty babba sai lallashinta takeyi tana cewa"ke fa banzace,menene abun kuka anan?karki wani damu kanki,Ae babu inda zamuje,ko cikin garin nan bazamu bari ba,Ni nasan me nake shiryawa,AI YANZU WASAN YA FARA,
Cikin shessheƙar kuka hayaam tace"Aunty laila bazaki gane bane,wlh banson inyi nesa da gidan nan!ji nake kamar zan rasa shine gaba ɗaya,na kwallafa raina akan Sgr,duk da bana ganinsa amma zaman da nakeyi acikin gidan nan,yana kwantar min da hankalina,at lease muna kusa da juna,ko ba don haka ba,A yanzu ni banajin zan iya rayuwa acikin gidanmu,kwara nan gidan wlh,kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwana a mai kyau,duk da atakure nake kwara nan ɗin da can gidan mu,Jarabar mammy kaɗae ta isa ta Ramar da mutun,babban takaici na,korar wulaƙancin da nayi ma Sofwan nasan cewa yanzu kona nemi taimako awajensa bazai kulani ba,"hannu tasa tana share hawayenta,
Tsoki aunty babba taja mtsww kefa matsakarki kenan!nace maki ki kwantar da hankalinki,ba inda zamuje amma duk kin bi kin tashi hankalinki,sannan in dai akan sgr ne ni nayi maki alƙwarin cewar saina mallaka maki shi,in dai kika ga sgr bai aureki ba to ki tabbatar cewar rayuwarshi a tazuranci zata ƙare,kuma naji kina maganar wani sofwan,uban me zaiyi mana?Ko kin manta cewar Muna da jari atare damu?daga ke harni babu namijin da zai kallemu ya kawar da kansa,Allah ya bamu hasken fata,ga dogon gashi,duk wani abu dake jan hankalin ɗa Namiji ae muna dashi Allah ya bamu,Kinga kuwa muna da hanyar da zamu samu kuɗi,don biyan buƙatunmu,'
Gaba ɗaya duk wannan surutun da sukeyi a kunnan Major,ya kasa kunne yana sauraron su,Sae faman ƙumshe dariya yakeyi acikin bakinsa,abun ban haushi abun ban dariya,
*Boss Bature*
❤REESHRAF❤
A hankali take hawan upstairs ɗin,yayin da zuciyarta ke tariyo mata abunda daddynsu ya sanar da ita,na cewa taci gaba da aiki a part ɗin SGR,kuma tayi mashi biyayya sau da ƙafa,me hakan ke nufi?small box ɗin da daddynsu ya bata,dowry ɗin wanene?ya sanar dani cewa sadakin wata ne,amma dai koma wacece wannan ba ƙaramar mai sa'a bace,halan tafi kowa kyau a duniya ne?shiyasa Aka biya sadakinta da Gold,dama ni wlh,'
Kamar wata zautacciya,sae faman surutai takeyi ita kadae abunta,
Ƙarasa hawa up din tayi,kai tsaye ta wuce part ɗin babban yaya,bata tashi jin faduwar gaba ba,sae da tazo ƙopar shiga falonsa,sannan ta tsaya tana karanto addu'o'in neman tsari,duk don kada ta fuskanci hukunci a wurinsa,bayan ta kammala addu'ar,ta shafa asaman fuskarta da kuma jikinta,kafin tasa ƙafarta ta shiga cikin falon cike da kwarin guiwa,sauke ajiyar zuciya tayi ganin babu shi acikin falon,sae dai daddaɗan ƙamshin turarensa,mai ratsa zuciya,bin falon nasa tayi da kallo,kusan 3 days kenan babu gyara,dama da shirin aiki tazo,wuce wa cikin bedroom ɗinshi tayi,nan ma babu shi aciki,da alama basu dawo daga sallar magrib ba,may be sae after isha,ko kuma ƙarfe goma sha biyun dare daya saba dawowa gida,
Shimfiɗeɗen gadonshi tabi da kallo,zanin gadon duk yayi squeezing,ga blanket ɗinsa ma nannaɗe asaman gadon,bai ɗaukeshi ba,
Hannu tasa tare da zame mayafin sarin dake ajikinta,ta ɗaure shi a qugunta,kwantacciyar sumar kanta na ɗaure acikin ribbon,saman gadon ta haye tare da sanya hannayenta tashiga ƙoƙarin tattaro bedsheet din nasa,Zancen zucin da takeyi ne ya fito fili,
"Matar babban yaya ta shiga uku,na tausaya mata Allah,mutun kullum fuskarshi a daure,kamar ta sa,babu fara'a ko kaɗan,in tayi mashi laifi kuwa zata sha zallan kwaɗi,in kuwa ta fusata shi,ɗaukar ta zaiyi kamar haka,
Tayi maganar tana tattaro bargonsa,ta ɗaga bargon sama tare da yin wurgi dashi,sannan tace"Ya jefar da ita,ko kuma yayi mata irin yadda yayi mun jiya,kamar wata ɗiyar Roba haka zai ruko wutsiyoyin gashin kanta,ya ɗaga ta sama!yana jujjuyata,
Tana cikin wannan sambatun nata,taji anyi mata gyaran Murya,a wani irin firgice ta juya don taga WANENE
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Waro ido waje tayi tana kallonshi,la66anta har rawa sukeyi wurin furta"bab..babban..yaya," tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,babban abunda ya tayar mata da hankali shine batasan tun yaushe yake tsaye abakin ƙopar ɗakin ba!in kuwa har ya jima a tsaye to tabbas yaji duk abunda tace,
Yana tsaye a bakin ƙopar,ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,farar shirt ce ajikinsa mai dogon hannu tare da wandon suits ɗinsa fari,hannun nan nashi na sanye da agogon diamond ɗinsa,Ya ɗaure sumar kansa ta baya,fuskar nan babu annuri ko misƙala zarratin,ya ɗaureta tamau,a hankali ya furta"On My bed!"
Jiki na rawa Sehrish ta sauko ƙasa daga saman gadon,cikin in ena tace"am..umm..dama gyara gadon nake yi,shine na hau sama don in samu in tattaro zanin gadon da bar....'
bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita"Shut up!banason jin komai"ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin ɗakin,kama hanyar fita daga ɗakin tayi,muryarshi ce ta kuma katseta da cewa"are u done"?
"A'a bangama ba,"ta bashi amsa,
"Okey,"ya ambaci hakan a yayin da yake zame agogon dake hannunshi,
Komawa ciki tayi,sannan taci gaba da gyaran gadon,tana jin lokacin daya shige cikin toilet,da alama wanka zaiyi,ajiyar zuciya ta sauke aranta tace"Allah yaso ni baiji abunda nace ba,dana shiga uku yau,nasan cewa dole ya sanyani tsallan kwaɗi,"shaf shaf ta kammala gyara tamfatsetsen gadon,ta canza mashi bedsheet,ta kuma canza mashi bargon da zai lullu6a dashi,in ya tashi kwanciya,bayan ta kammala gyara bedroom ɗin,ta dawo falo,nan ma ta shiga gyara mashi falon,Cikin ƙankanin lokaci ta kammala gyaran,ko'ina ya koma tamkar sabo,sae ƙamshi ke tashi,
Fitowa tayi daga part ɗin nashi,ta wuce kitchen don ta shirya mashi dinner ɗinsa,a kitchen ta samu Azmee ita da Saude,sun kammala dinner suna gyara kitchen ɗin,gaishe dasu ta fara yi,fuskokinsu a sake suka amsa mata,
"Aunty azmee a shirya mun dinner ɗin babban yaya,inaso zan kai mashi ne,"
Murmushi Azmee tasaki tare da cewa"Masha Allah,ki ce Anyi welcome back kenan,"
Dariya sehrish tayi har fararen hakoranta suka bayyana,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"ae daddy,Ya amince na cigaba da zuwa part ɗinsa,inayi mashi aiki,"
"Amma naji daɗin jin hakan sosai,yanzu bari na shirya maki dinner ɗin,"
Amsa mata tayi da toh,sannan ta tsaya tana jiranta,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata a warmers da sauran food stuffs asaman tray,ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi tare da kama hanyar fita daga kitchen ɗin tana faɗin"nagode Aunty azmee,"
Babu kowa a main palour ɗin,yawanci duk basu kaiga dawowa cikin gidan ba,wasu kuma suna acikin ɗakunansu,tana cikin tafiya hannunta ɗauke da tray,taji maganar mutun abayanta,
"Ƴar shila,"a ɗan firgice ta juya don taga kowanene,gabanta ne ya faɗi Rassss!cike da mamaki take bin shi da kallo yaushe rabon da ta sanyashi acikin idanunta harta manta,ita duk a tunaninta ma an tura shi aikine,ashe yana nan cikin gidan,
Fuskar nan tashi ɗauke da wannan shu'umin Murmushin nashi,ya ƙarasa tare da cin burki ya tsaya tagabanta,Face to face suka fuskanci juna,
Jikinshi na sanye da rigar ankara har guiwarsa,sae wandon jeans,sumar kan nan nashi yayi mata ɗan iskan gyaran gashin nan daya saba yi,an saisaye gefe da gefe na kan,tsakiyar kuma anbar sumar a tsaye ba ladabi,
"Nayi kewarki sosai,abubuwa da yawa sun faru,bansamu isasshen lokacin da zamuyi magana ba,naso nazo na taya ki Murna na kasancewarki ƴar wurin Uncle ɗinmu Abusufyan,abun ya ƙayartar dani,"
Sakin baki sehrish tayi tana kallonshi,abun ya ɗaure mata kai,Yadda yake tsara kalami kamar ba wannan mashayin giyar ba,wata irin natsuwa wadda bata saba ganinshi da ita ba,har wani kyau ya ƙara,yayi haske abunshi,duk da ramar da ya ɗanyi,
"Naji kinyi shiru baki ce komai ba"
Jin muryarshi yasa ta dawo daga zurfin tunanin da tashiga,muryarta a ɗan ruɗe tace"amma kaine dagaske?ko an yi musayarka ne,"
Wani ƙayataccen murmushi ya saki na gefen fuska,kafin yace"Ni ne mana HAROON ɗin da kika sani,koda yake na canza a yanzu,nayi ma kaina karatun ta natsu,saboda inaso in zama mutumin kirki,kamar kowa,inaso na shiryu,don na samu mace ta gari,a kwanakin baya kin ta6a yi mun nasiha akan cewa kinaso nazama tamkar ƴan uwana,naji daɗin maganar nan da kikayi mun,kuma nayi amfani da hakan gashi yanzu ni kaina inajin daɗin sauyawar da nayi,"
Zuba mashi ido sehrish tayi tana ƙare mashi kallo har yakai ƙarshen maganar tashi,tayi matuƙar mamakin jin abunda haroon ke faɗa mata,kokwanto ta shiga yi anya haroon ba wani plan yake shirya mata ba?
Ganin ta tsaya tana kallonshi yasa shi gane cewar kokwanto takeyi akanshi,Cikin sauri yace"nasan zaiyi wuya ki yadda dani,saboda sanin da kikayi mun ada,amma na canza ayanzu fiye da tunaninki,"
"Amma na daina ganinka acikin gidan nan"?
"Masallaci nake kwana,shiya sanya baki cika ganina ba,yanzu bana jin daɗin zama ko ina,in ba masallaci ba,acan nake rayuwata,in kinga na fita daga cikin masallaci to wani abu mai muhimmanci ne ya fidda ni,kinsan na tara zunubi sosai shiyasa nake kusanta kaina da ubangiji sosae,saboda in samu yafiyarshi...."
Yanayin yadda haroon yayi mata maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,domin kuwa har hawaye sun taru acikin idanunshi,wata siririyar ƙwalla ce ta gangaro cikin idonshi,da sauri ya sanya hannu ya shareta,
"Yaya haroon,ka daina zubar da kwallarka,tunda dai har ka shiryu ka koma ga Allah,zai kar6i tubanka ne,fata na shine Allah yasa ka daina duk wani abu mara kyau da kake aikatawa,"
Tana kai ƙarshen maganarta,yace"In sha Allah nadaina,bazan ƙara ba,Ni dai yanzu babban burin da nake dashi arayuwata shine in samu mace tagari inyi aure,zan fi samun kwanciyar hankali,"
"Kada ka damu,in sha Allah zaka samu,"
Tana kai karshen maganar ta kama hanya da sauri ta nufi upstairs,
Bin bayanta da kallo haroon yayi har sai da ta 6ace ma ganinshi,fashewa yayi da dariya,a fili yace"Mata kenan!zuciyarku da rauni take,wannan alƙawari ne na ɗaukar ma kaina,Sai na cimma burina ko da ace shikaɗae ne abunda zan aikata kafin in bar duniya,"yana faɗin hakan ya wuce bedroom ɗinshi,
Sehrish kuwa,tun bayan da tabar wurin,zuciyarta ke cike tab da tausayin Haroon,bakomai take tunawa ba fa ce fuskarshi,yadda yayi mata magana yau ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,sanya ƙafarta tayi acikin falon Sgr,sannan ta shiga da sallama abakinta,ganin bai fito falon ba,yasa ta wuce bedroom ɗin nashi,sanin cewa ya shiga wanka,yasa ta shiga cikin bedroom ɗin kaitsaye batare da yin sallama ba,
Gabanta ne ya fadi rass!!ganinshi tsaye gaban mirror daga shi sai short ajikinshi,hannunshi ruƙe da comb yana taje doguwar sumar kanshi,
Juyawa tayi da sauri zata koma falon,ta cikin mirror ya hangota,gyaran Muryar da yayi ne yasa ta ɗan dakata daga ƙoƙarin da takeyi na fita daga bedroom ɗin nashi,
"Where are u going?"
Muryarta na kerma tace"Falo,dama dinner ne na kawo maka,"
"Okey,idan kin kai abincin falo,kizo inason ganinki"
Da sauri ta amsa mashi da toh,fita daga cikin bedroom ɗin tayi,a saman table ta ajiye mashi tray din kayan abincin,sai da ta bada kusan minti 10 sannan ta koma bedroom ɗin nashi,A lokacin har ya kammala zura sleeping dress ɗinshi,Red colour sun fito da natural beauty dinshi,gefen gadonshi ya zauna,tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,yana karkaɗa ƙafarshi ta hannun dama wadda ya aza asaman ta hagun,yayin da hannunshi ke ruƙe da wayarshi yana daddanawa
Da yatsan hannunshi yayi mata nuni da tazo gabanshi,cike da fargaba ta ƙarasa tare da tsayawa a tsaye tana faman zare ido,
"Haka ya dace ki tsaya gabana?C'mon Kneel down"!
Hankali atashe ta zube saman guiwowinta,jikinta nata faman kerma,
Tun kafin ya kuma cewa wani abu,tayi saurin cewa"Am sorry babban yaya,daddy yace na baka haƙuri game da abunda ya faru jiya,dan Allah kayi haƙuri,"
Banza yayi da ita tamkar baiji abunda tace ba,gaba ɗaya hankalinsa na akan wayar hannunshi,sae da ya mula yasha iska sannan yace"Wanene SA"?
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,hannu ta aza akai tana fadin"Innalillahi!nashiga uku,"ƙasa ƙasa tayi maganar tuni ido ya raina fata,
"Idan har kika bari na maimaita tambayar da nayi maki,jikinki ne zai gaya maki",
Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Wlh babban yaya ba dakai nake ba,su6ul da baka ne nayi bansan nace ba,kuma Allah bakai nace ma sa ba,Ni kawai nasan dai nace kullum fuska a ɗaure kamar sa,Kuma fa waƙa ce nake rairawa..."
Bata ƙarasa maganar ba,ya katseta da cewa"Just one answer nakeso!ki faɗamun menene ma'anar kalmar SA da kika faɗi,if not u will be in serious trouble,"tashin hankali!
Nan fa sehrish tashiga mazurai,shin tayaya zatayi mashi bayanin cewa shanu take nufi da sa!tabɗijancan,hauka ma takeyi da zata sanar dashi ainihin mai kalmar SA ke nufi,ta fahimci cewa baisan menene SA ɗin ke nufi ba,shiyasa har ya tambayeta don yaji ma'anarta,yadda zaiji daɗin hukunta ta,
Shirun da tayi mashi ne ya 6ata mashi rai,tsawa ya daka mata wadda ta firgitar da ita,a ruɗe tace"SIR na Yalla6ai nake nufi,wani malamin mu ne na makaranta,muke kiranshi da SA,kuna kama dashi sosai,kyakkyawa ne shima,shiyasa nace fuskarka irin tashi,"
Guntun tsoki SGR yaja,kafin yace"Tashi kiban wuri,"da sauri ta miƙe,ta fito daga bedroom ɗin nashi,gaba daya ma tabar masa part ɗin,don ta lura yau kamar asama yake,
Bedroom ɗinsu ta koma hannu tasa tare da tura ƙopar ta shiga ciki,Jahad ta samu a zaune saman gadon nasu hannunta ruƙe da wayarta,ta ƙurama screen ɗin wayar ido da alama wani abu take karantawa wanda yaja hankalinta har bata ji shigowar Sehrish ɗin ba,hosana kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita,tana kwance naɗe cikin bargo,
Kamar daga sama taji an fisge wayar,a ɗan firgice ta juya don taga wanene ganin sehrish yasa ta sauke a jiyar zuciya tare da cewa"Ashe ke ce,wlh har kin bani tsoro,ƙoƙarin hawa gadon sehrish tayi tana cewa"Halan karatun Novel ɗinne?tayi maganar ayayin da ta aza idonta kan screen ɗin wayar,Ganin rubutun ƙur'ani yasata cewa"Oh ashe karatun qur'ani kikeyi hakan yayi kyau sosai,'
"Ina kika je ne?tun ɗazu ina jiranki,kizo muyi fira don bana jin bacci yanzu,"
Shiru sehrish ta ɗan yi da alamun damuwa a fuskarta,hakan yasa jahad ta kuma cewa"faɗamun meya faru ne?na tambayeki kinyi shiru baki bani amsa ba,ko akwai wani abu ne dake damunki"?
Shaking head sehrish ta ɗan yi kafin tace"bakomai jahad,naje part din babban yaya ne,nayi masa gyaran ɗaki dana falo,shiyasa na jima ban dawo ba,'
Jinjina kai jahad tayi tare da cewa"amma duk da haka akwai sauran wani abu da ki ke ƙoƙarin 6oye mun,ko kin manta cewa ni ƴar uwarki ce,rabin ranki,koma nace ranki gaba ɗaya"
Dariya sehrish tayi jin abunda jahad tace,
"Jahad,akwai abunda ke damuna amma na barshi acikin zuciyata ne kawai,saboda baida amfani kona furta shi,kawai ki tayani addu'a "
Ruƙo hannunta jahad tayi acikin nata,sannan tace"in sha Allah,rishi zan tayaki da addu'a,dama kuma kullum cikin yi maku addu'a nake yi gaba ɗayanku,"ta ƙarasa maganar,jikinta asanyaye saboda tunawa da mahaifiyarsu,a hankali taci gaba da magana"Ko wani hali Oumman mu take ciki a yanzu?nadamu sosai akan rashin mahaifiyarmu a kusa damu,baiwar Allah bazan ta6a mantawa da wasu kalami nata ba,tana yawan cewa ina sonku sosai ƴan ukuna,a duk lokacin dana kalleku,sai inji wani sanyi ya ratsa zuciyata,ku kaɗae ne dangin da nake dasu a duniyar nan,ina addu'a akan Allah ya raya mun ku......."kasa ƙarasa maganar jahad tayi saboda hawayen da suka shiga gangarowa daga cikin idanunta,ita sehrish nan take taji hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,
Sehrish ce ta ɗaura da cewar"babu tabbacin cewa zanyi tsawancin kwana,baƙin cikin wannan mutumin ma kaɗai ya isa ya halakar dani,zanyi kuka sosai,naci buri akan naga girmanku amma zaiyi matuƙar wuya hakan ya faru.........."duk wannan zancen da suke yi gaba daya kaf kalaman da mahaifiyarsu ke yawan faɗi masu ne,tun suna yara,dama kuma yaro akwai shi da ruƙo,in ya ruƙe abu aranshi da wuya ya manta shi har girmanshi,kuka sosai suka shiga yi babu mai lallashin wani,cikin shessheƙar kuka jahad tace"Oumman mu ta ta6a sanar dani cewa mu ba ƴan uku bane,Ƴan shida ne ɗaya ta mutu,biyu kuma Ya sayyadi ya kwashe su ya siyar ma ƙungiyarsu don ya samu kuɗi ........"hannu tasa tana share hawayenta a yayin da takai ƙarshen maganarta,,
Girgiza kai sehrish ta shiga yi yayin da hawayen idanunta ke cigaba da zuba,
"Jahad,wannan maganar ba gaskiya bace,nacewa mu ba ƴan uku bane!daga baya Oumma ta tabbatar mun da cewa mu ƴan ukune ta haifa,Ya sayyadine yayi mata ƙaryar cewar mu ƴan shida ne ta haifa,ɗaya ta mutu biyu kuma ya kwashe su ya siyar ma ƙungiyarsu,da farko ta yadda da kalamanshi saboda ta sanar dani cewa a lokacin da ta haife mu ba'a hayyacinta take ba saboda matsanancin ciwon nakuda daya taso mata gashi ita kadai ce a gidan,sae dai kawai ta farka a gadon asibiti,taga jarirai guda uku a gefenta,a yayin da shi kuma yake tsaye akanta,batasan meya faru ba,wannan dalilin ne yasa ta yarda da maganarshi daya faɗa mata,Ashe yayi hakanne kawai don ya ƙona mata rai,dama kuma rabi da kwata na kalaman ya sayyadi ƙaryane,zaiyi wuya ya faɗi gaskiya a bakinshi,mugun maƙaryaci ne,hakanan ma yana iya tsara ƙarya,ya mayar da ita tamkar gaskiya,don haka ki cire wannan aranki!"
Wata nauyayyiyar ajiyar Zuciya jahad ta sauke,muryarta ɗauke da tsantsar farin ciki tace"Har hankalina ya kwanta wlh,bakiji yadda naji ba,ashe ƙaryane ba gaskiya ba,Amma gaskiya mutumin nan baya tsoran Allah,ni fa duk a tunani na dagaske mu ba ƴan uku bane,akwai wasu suna nan a raye,kullum zullumin da nakeyi shine Suna ina?A wane hali suke ciki su ma?kamannin fuskarsu irin namu ne sak ko kuwa?Ashe duk ƙanzan kurege ne,Ya sayyadi dai ya shiga uku,in ya mutu yana aikata waɗannan mugayen halayan nashi,'
Sehrish ta ɗaura da cewa"ae wannan mutumin bazai kai labari ba,irinsu tun a gidan duniya suke fara gir6ar abunda suka shuka,ƙaddara ce kawai tasa Oumman mu ta aureshi,Ashe shima da wani mugun nufin ya aureta,In sha Allah asirinshi sae ya tonu,kuma Ammi tayi mana al'ƙawarin cewa in aka kamoshi sae mun wanke mata mummunar fuskarshi da mari,Ranar kawai nake jira,in da rai da lafiya,nasan rayuwarmu a hannun Allah take,amma zan roƙi Allah akan ya nuna mun wannan lokacin,koda ace shikaɗae ne burina na ƙarshe da zan cika kafin in bar duniya!!"
Jahad tace"Ni dai koda ace bana raye aka kamo ya sayyadi,alhakin marina na akan ki,Ki haɗa da nawa duka ki kifa mashi su a fuskarshi,"
"Allah shikaɗae yasan wanene gawar fari acikinmu jahad,nima idan bana raye,Alhakin Marina na akanki Jahad,ki haɗa da nawa da naki ki kifa mashi su a fuskarsa,"ta ƙarasa maganar tana nuna ma jahad yadda zata kifa ma ya sayyadi mari a fuskarshi,
"Allah ya kiyaye in ta6a fatar fuskarshi da hannuna!wannan ƙazamin mutumin,sai dai in sanya glove a hannuna,"jahad ce tayi maganar,tare da 6ata fuskarta,
Sun jima suna fira atsakaninsu,kafin daga bisani,jahad ta kwanta,Sehrish kuma ta wuce toilet,bayan ta fito tayi alwala tayi sallah,komawa saman gadon tayi tare da ja musu bargo ta lullu6esu hadi da tofa masu addu'oi.
*Aunty Babba*
A 6angarensu Aunty babba kuwa,sam bacci ya ƙaurace ma idanunta,tsabar baƙin ciki ne ƙumshe acikin zuciyarta,tagaza samun natsuwa,tun bayan da Major ya ajiyesu a hotel ɗin,suka shiga ɗakin da aka kama masu,bata samu ta zauna ba,sae faman safa da marwa takeyi acikin ɗakin,Hayaam kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita asaman gadon,
Allah kaɗae yasan mugun abunda take ƙullawa acikin ranta,don kuwa taci alwashin cewa,a gobe goben nan zasu wuce dajin nan na enugu inda wannan ƙasurgumin fasiƙin bokan yake,Wato Baba Ibliss,kuɗi ne matsalarsu,amma ta yanke shawarar cewa zata siyar da sarƙar gold ɗinta da kuma awarwaron sarƙar,hadda Earrings duka zata siyar don su samu tunkarar Bokan,
*Allah yaba mai rabo sa'a*
*Boss Bature*
❤🤍❤
*A washe garin Juma'a,
Cikin bacci Sehrish ta dinga jin sautin waƙa ƙasa kasa"Takusa Aure ƙara faɗa breaker!ta kusa aure ƙara faɗa breaker,"sae faman mutsu mutsu takeyi acikin bargo,ga baccin bai isheta ba,gashi kuma an takura mata,Ranta yayi mugun 6aci,shiru kawai tayi acikin bargon tayi lamo tana tunanin wani shaiɗani ne tunda sanyin safe yake raira masu waƙa acikin ɗaki,ta kasa gane muryar wacece kamar hosana kamar kuma Muryar jahad,a ƙarshe ta tsayar da tunaninta akan cewa Hosana ce,saboda itace gwanar iya raira waƙa,da wuya kaji waƙa a bakin jahad sae dai karatun ƙur'ani,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,taji an ƙara Volume hada ma kiɗa gangan gangan acikin kunnanta"Takusa aure ƙara faɗa breaker!takusa aure ƙara faɗa breaker,"
a fusace sehrish ta yaye bargon da ta lullu6a dashi,karaf idanunta suka sauka akan hosana,dake zaune saman front chair ɗin dressing mirror ɗinsu,ta dage da iya ƙarfinta na ƙarshe,sae faman kiɗa takeyi da hannayenta,
"OMG!!!" pillow ta raruma ta daddage ta jefa ma Hosana,cikin sa'a ya samu tsakiyar kanta,amma ko ajikinta da alama bata ji pillown ba,lalubo wani pillow ɗin sehrish tayi da ƙarfi ta wurga mata shi,Ya daki kanta,a firgice hosana ta juya don taga menene,pillows ta gani guda biyu a ƙasa,a hankali ta ɗago da idanunta kan wanda ya jefo mata da filon,
Daƙuwa Sehrish tayi mata da hannunta"Ungo nan don ubanki!Dama sai da raina ya bani cewa kece,Saboda baki da hankali,Mahaukaciya ce ke,Tunda sanyin safiya kin addabi mutane kin takurawa rayuwarsu,saboda tsabar rashin hankali waqa kike rairawa hada kiɗa,maimakon ki kama azkhar ɗin safe kinayi abakinki,.....".
Muryar jahad ce ta katse mata hanzarinta da cewa"Wai dama hosana ce ke raira mana waƙa da kiɗa!Nifa nayi tunanin cewa ko ringing ɗin wayarki ne,Amma dae hosana baki da hankali bakisan ciwon kanki ba!shiyasa har yanzu haukan naki ƙara gaba yakeyi,babu abunda zai hana in yiwa Daddy magana akai ki asibitin mahaukata,don abincika notikan kwakwalwarki da suka kwance a ɗauɗaure maki su,"tana magana tana kwatanta yadda za'a ɗaure mata notikan kan nata da hannunta,
Tashin ta kenan itama daga bacci,Kiɗan hosana ne ya farkar da ita,
Tunda suka fara maganar hosana ta zuba masu ido tana kallonsu tsabar bakin ciki ya hanata tanka masu,zuciyarta sae faman tafarfasa takeyi,arayuwarta ta tsani ace mata zararra ko mahaukaciya,fuskarta tacika fam ta kumbura kamar alkubus,a ƙule tace"Ni ce Zararra ko?kuma mahaukaciya"?
Har suna haɗa baki wurin cewa"Eh ance zararra kuma mahaukaciya kiyi abunda zakiyi,"hakan da sukayi ba ƙaramin tunzurata sukayi ba,miƙewa tayi daga saman kujerar,ta shiga nannaɗe hannun rigarta,hakan ya tabbatar masu da cewar dambe zasuyi,
Tana kammala naɗe hannun rigar,ta danƙara da gudu,ta daka uban tsalle ta haye saman gadon,kafin suyi wani yunƙuri,gaba ɗaya ta haɗe kawunansu ta bugasu jikin na juna,ƙara suka saki saboda zafin da sukaji,Ransu yayi mugun 6aci,Aikuwa gaba ɗaya suka tarar ma hosana suka shiga bugunta,ita ma kuma ta shiga kai masu naushi bana wasa ba,dama tafisu ƙarfi,don bala'e suna kuka suna faɗa su duka ukun,gashi babu mai rabasu,
hafsat ce ta nufo bedroom ɗin nasu tun kafin ta ƙaraso ƙopar ɗakin,taji sautin kukansu da kuma sautin buge bugen da sukeyi,
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,bugun ƙopar tashiga yi amma arufe take,sun datse ƙopar tun jiya da daddare da zasu kwanta
Next page na nan tafe,amma fa in mutun najin bacci ya kwanta,don zai iya kai 10,😟
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,bugun ƙopar tashiga yi amma arufe take,sun datse ƙopar tun jiya da daddare da zasu kwanta,tana cikin bugun ƙopar ɗakin nasu sai ga Azmee ta shigo corridor ɗin ɗakin nasu,da alama daga kitchen take,ganin hafsat a ƙopar ɗakinsu sehrish tana ta faman yi masu magiya akan su buɗe mata ƙopar,yasa azmee yin hanzarin ƙarasawa kusa da ita tana tambayar ko lafiya,tun kafin ma hafsat ta bata amsa ta jiyo sautin kukansu Jahad acikin ɗakin,kuka fa bana wasa ba,hankali atashe azmee tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Meke faruwa ne!meyasa su ke kuka"?
Fuskar hafsat ɗauke da damuwa tace"Wlh bansani ba,zuwana kenan najiyo sautin kukansu hada ma buge buge da alama faɗa suke atsakaninsu,Ni tsorona ma kada su lahanta junansu,'
A ruɗe Azmee ta shiga bugun ƙopar tana kwala masu kira"Jahad!Sehrish!hosana!wai bazaku daina ba!Me kukeyi haka!kuzo ku buɗe ƙopar nan tun kafin ranku ya 6aci," duk wannan kwakwazon da azmee keyi a banza domin kuwa babu mai sauraronta,hasalima basu son tana yi ba saboda basu a hayyacinsu,
"Hafsat!kije ki sanar da Daddynsu ko wani daga cikin yayyensu game da abunda ke faruwa,su taimaka suzo ko ƙopar ce a 6alle,tun kafin yaran nan su halaka kansu,"acewar Azmee wadda hankalinta ya gama tashi,
Da gudun gaske hafsat ta fita daga corridor ɗin ɗakin,A main palour ta samu Mommynsu junaid tare da Abbansu da kuma Hajiya Azeema suna tattaunawa,wurinsu ta tunkara tana faman yarfa hannu idonta cike tab da kwalla,
Tun kafin tayi magana suna ganinta suka miƙe tsaye suna tambayar ko lafiya,
Muryarta na kerma tace"Su jahad ne,suke faɗa acikin ɗakinsu,gashi can suna ƙoƙarin halaka kansu,munyi munyi su buɗe ƙopar sunƙi buɗewa sae dai sautin kukansu kawai da muke ji,"
Tun kafin ma ta karasa maganar,Jiki na rawa suka nufi ɗakin nasu,hajiya azeema hada tuntu6e saboda tsabar sauri,a ƙopar dakin nasu suka tsaya,bubbuga ƙopar ɗakin Abbansu ya shiga yi a tsawace yake ambaton sunayensu,amma shiru babu wadda ta amsa masa,sae dai sautin kukan nan da suke ji na tashin hankali,
"Ina ganin bari na kira mahaifinsu wata'ƙil idan yayi masu magana sun ji maganar shi,'Abba ne yayi maganar tare da zura hannu cikin aljihun wandonshi ya ɗauko wayarshi,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin lalubo number Abusufyan,ya danna mashi kira ta soma ringing,
Hajiya Azeema da Alexandra duk sun bi sun ruɗe,
"Ni babban tashin hankalina ma kada yaran nan su illata kansu,Wlh abun ya tsoratar dani sosai ya tayar mun da hankalina,"Hajiya azeema ce tayi maganar,fuskarta tamkar zata fashe da kuka,
Hafsat kuwa tana acikin main palour ɗin,Sae faman kuka takeyi,kwatsamm taji takun takalmi,da sauri takai idanunta wurin MARSHAL OMAR ne ke saukowa daga upstairs da gudun gaske ta tunkare shi tana fadin"Ya Omar,gasu jahad can suna faɗa acikin ɗakinsu,kuma sun kulle ƙopa,anyi anyi su buɗe sun ƙi su buɗe....."
Jin wannan maganar yasa hankalin Omar mugun tashi,da sauri ya nufi bedroom ɗin nasu,lokaci guda kowa na gidan labarin abunda ke faruwa yaje musu,hatta su Junaid dake ɗakunansu suna bacci sae da suka tashi,su fawan twins,dasu Irfan,hada Dr hariis da gwaggon katsina,da Ammi,dukkansu kowa fa amma banda Sgr dake a bedroom ɗinshi,
A ƙopar ɗakin nasu sukayi cirko cirko,Abusufyan yafi kowa shiga damuwa bawan Allah,kamar ya zauce haka yake bugun ƙopar ɗakin nasu yana roƙonsu akan su daina kokoyin da sukeyi suzo su buɗe mashi ƙopa amma shiru babu wanda ya tanka mashi,Haka Marshal Omar ma,Tamkar zai 6alle ƙopar haka ya dinga bugun ƙopar ɗakin nasu,amma duk abanza,Junaid kuwa tuni ya fashe da kuka,yadda kasan wani ƙaramin yaro,
Cikin shessheƙar kuka Gwaggon katsina tace"nashiga uku..Wayyo Allah na,wlh nasan duk sharrin Ya sayyadine bazai barsu hakanan ba,yanzu haka shine ya shiga tsakaninsu,Ya Allah kayi mana maganin wannan baƙin shaiɗanin....'kuka takeyi hada majina,
Lokaci guda sukaji shiru tsit cikin bedroom ɗin nasu babu wani gunjin kuka,hakan ya tabbatar masu da cewar wani mummunan abunne ya faru dasu,nan fa kowa ya shiga kallon kallo,yayin da zuciyoyinsu keta bugawa da karfi,
Jiki asanyaye Abusufyan ya zame ƙasa,tare da aza hannayenshi saman kanshi,yayin da bakinsa ke furta kalmar"Innalillahi wa'Inna ilaihirraji'un,'
"Abba,ina ganin kawai a 6alle ƙopar," acewar kanal yousouf,
Omar yace"Nima abunda nake tunani kenan,amma ƙopar fa ta cije sosai,na buga na buga amman ko motsi batayi,duk irin ƙarfin da nake dashi,"
Cikin shesshekar kuka junaid yace"Bari naje na ɗauko zarto sai a datse kubar,"
Ya ambaci hakan tare da watsawa da gudu ya nufi weapons Room ɗinsu (ɗakin ajiye makamansu,"A rufe ya samu ɗakin,sam ya manta cewar key ɗin yana a wurin babban yayansu,sae da yayi arba da ƙopar a rufe sannan yasha kwana ya dawo da gudu ya haye upstairs ɗin,
Faɗawa part ɗin SGR yayi,a rikice ya shiga bedroom ɗinshi,a lokacin Sgr na kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi yana bacci,
Junaid baibi takanshi ba saboda a ruɗe yake,side drawer ɗinsa ya tunkara,ya shiga bubbuɗeta yana neman key ɗin,duk inda ya duba babu key ɗin,saman gadon ya hau,yana kiran sunanshi"Babban yaya!Babban yaya!pls wake up!babban yaya ka tashi dan Allah,'
Cikin bacci rafayet yaji muryar junaid dake ta faman kiran sunanshi,a hankali ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka kan fuskar junaid,ganin hawaye jaga jaga a fuskar junaid yasa Sgr yin hanzarin miƙewa daga zaune,hankalinshi aɗan tashe yake kallon junaid,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunanshi"Junaid!what are u crying for?meya faru ne?.
"Babban yaya,key nake nema na weapon's room,inaso in ɗauko saw ne,za'a 6alle ƙopar ɗakinsu Sehrish"
Cike da mamaki Sgr yace"For what reason?wani abu ya samu door ɗin da za'a 6alleta"?
Ganin bai fahimci inda zancen nashi ya dosa ba,yasa shi yi mashi bayanin abunda ke faruwa,
Saukowa Sgr yayi daga saman gadon nashi,junaid na biye da bayanshi suka fito daga part ɗin nasa,da sauri da sauri suke saukowa down stairs,
Lokacin da suka shigo Corridor(doguwar hanyar) da ɗakunnansu sehrish suke a jere,Hankalin Sgr ya ɗan tashi musamman daya ga dandazon matasan gidan,ga kuma su Abbansu kowa atsaye cirko cirko,fuskokinsu sun nuna alamun damuwa atattare dasu,'
Abbansu na ganinshi yayi saurin ruƙe hannunshi yana fadin"Yawwa rafayet,nasan zaku iya kai da Omar,dan Allah ku haɗu ku 6alle ƙopar nan,ko mun samu muga meke faruwa aciki,'
A hanzarce kowa ya dare ya basu wuri,da iya ƙarfinsu Na ƙarshe suka daddage suka kaima ƙopar wani irin kwakkwaran bugu ji kake daraamm!nan take Sakatar ciki ta zame da kanta,ƙopar ta buɗe,gaba daya suka afka ciki,
Ba ƙaramin girgiza sukayi ba,gaba dayansu musamman Abusufyan,abunda suka gani yayi matuƙar tayar masu da hankali,Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!!!wannan shine abunda suke ambato a bakunansu,
Sun tarwatsa komai na bedroom ɗin nasu,ɗigon jini jinin da suka gani shi yafi komai tayar masu da hankali,
Jahad ce kwance ƙasan gadon saman tiles,damtsen hannunta duk sawun cizo ne,wurin duk ya farfashe,hatta saman kumatunta cizon ne,daga can saman gadon kuwa hosana ce,baje hannunta dafe da kanta ta toshe kunnuwanta sae faman mutsu mutsu takeyi da ƙafafuwanta,alamar idonta biyu,Sehrish kuwa basu san ina ta lula ba,
Zubewa Abusufyan yayi agaban Jahad dake kwance,hannu yasa yana jijjigata yana ambaton sunanta saboda ya gane itace,hawaye sae faman sintiri sukeyi akan fuskarshi,
Jikin kowa yayi sanyi,zukunnawa Abbansu yayi agaban Abusufyan din yana kallon jahad dake kwance,Sawun haƙoran dake asaman fatar jahad ya tabbatar mashi da cewar faɗa ne ya 6arke a tsakaninsu har sukayi kokoyin nan,
"Ina tunanin suma tayi ne,wani ya ɗauko mun ruwa dan Allah,"Abbansu ne yayi maganar,da sauri fawan ya fuce daga dakin,ya nufi babban falo don ya ɗauko masu ruwan da za'a yayyafa mata,
....a hankali Sgr yake bin ɗakin nasu da kallo,sunyi mashi kaca kaca,damben daga saman gadon nasu ya fara,Hatta bargon lullu6arsu duk sun jefo shi ƙasa,zagayawa yayi ta dayan gefen gadon,6angaren hannun hagu,tunkan ya ƙarasa ya hango ƙafafun mutun,hakan ya tabbatar mashi da cewar cikon ta ukunsu ce,ta wuntsila ta baya,lokacin daya ƙarasa wurin a kwance ya samu Sehrish,gefen bakinta ya ɗan fashe,ga kuma sawun haƙora asaman ƙirjinta,da kuma damtsen hannunta,zuƙunnawa yayi agabanta yana ƙare mata kallo,
"Rafayet!wacece anan?ko cikon ƴar ukun tasu ce"?Ishaq ne yayi maganar ganin rafayet ɗin zuƙunne a wurin,
"Itace," ya bashi amsa atakaice,da sauri Abusufyan ya miƙe tare da sauran suka nufo wurin don suga a wani hali take ciki,
Tun kafin su ƙaraso Sgr yayi saurin kai hannunshi gaban rigarta yaja rigar ya lullu6e mata ƙirjinta daya fito sosai,
Fashewa da kuka gwaggon katsina tayi tana fadin"Wayyo Allah ƴa'ƴan Abusufyan ɗina!ni nasan cewa ba yin kanku bane,Wlh sai Allah ya saka maku,Bayin Allah sunji jiki,kowanene yayi masu wannan ɗanyen aikin,jibi yadda aka ciccije masu fata,Yanzu haka ya sayyadine yazo masu da suffar kura yayi masu wannan aika... aikan,' Harris ne ya katseta da cewa"pls gwaggo kibarmu muji da abunda ke damunmu idan ma kina magana ƙara masu zafin ciwon kikeyi,
Jin haka yasa tayi saurin rufe bakinta,tana cigaba da matsar kwalla a idonta,
"Abun ya ɗaure mun kai!garin yaya haka ya faru?gaba daya kowannansu sawun cizo ne a fatar jikinsu",Abbansu junaid ne yayi maganar,a yayin da suke tsaye gaban sehrish,Sgr kuma na a zuƙunne,
Hafsat ce ta basu amsa da cewa"lokacin da nazo ƙopar dakinsu,naji sautin Kukansu acikin ɗakin da kuma sautin bugu kamar suna dambe a tsakaninsu,ina tunanin cewa faɗa sukeyi a tsakaninsu,'
Jinjina kai marshal Omar yayi tare da cewa"Tabbas sunyi sa insa a tsakaninsu ne har abun yakai ga fada,Kuma wannan cizon dake asaman fatar jikinsu,ba kowa bace tayi masu shi ba fa ce HOSANA!saboda nima ta ta6a cizo na a kwanakin baya,da ranta ya 6aci a asibiti,ta cije ni kuma ba ƙaramin zafi naji ba a lokacin,"
Abba yace"No wonder!in kuka lura babu sawun cizo a fatar jikinta,indai itace kwance asaman gadonsu,ku kalli jikinta dakyau,kuma bata jigata ba,kamar yarda ƴan uwan nata suka jigata,"
Suna cikin maganar nan,Fawan ya shigo hannunshi ɗauke da robar ruwan daya dauko masu a fridge,da sauri kanal yousouf ya kar6i bottle water din,ya 6alle murfin,tare da tarbo ruwan a tafin hannunsa na dama,ya watsa shi a fuskar jahad,Nan take taja dogon numfashi tana ambaton sunan Allah abakinta,ajiyar zuciya suka shiga saukewa,da sauri Abusufyan ya dawo wurinta,tare da zukunnawa agabanta,ya ɗago da ita ajikinshi yana ambaton sunanta"Jahad!Jahad!"koda jahad ta buɗe idanunta tayi tozali da fuskar Daddynsu saita fashe da matsanancin kuka tana cewa"daddy kaga abunda hosana tayi mana?kawai daga magana ta hau bugunmu ni da Sehrish,duk tabi ta gartsa mana ciwo a fatar jikinmu....'tana magana hawaye na zuba a idanunta,
Runtse ido Abusufyan yayi tare da buɗesu a hankali,abun ba ƙaramin ta6a mashi zuciya yayi ba,
Hannu Omar yasa tare da kar6ar Robar ruwan dake hannun Kanal yousouf ya taka izuwa inda Sgr ke a zuƙunne ya miƙa mashi ita,Kar6a Sgr yayi tare da kur6ar ruwan abakinshi,ya fesar dashi akan fuskar Sehrish,a firgice ta farka gami da mikewa zaune tana faman zazzare idanunta,one by one tabi su da kallo,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin Sgr,ga kuma su hajiya azeema tsaye duk akanta,tafin hannuwanta tasa tare da rufe fuskarta,tana kuka,
"Wani ya ɗauko min FA box a medical room"Sgr ne ya ambaci hakan,da sauri irfan ya fuce daga ɗakin don zuwa ɗauko akwatin,ruƙo hannun Sehrish Hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita gefen gadon,"sannu kinji,yi shiru ki daina kuka,"cikin lallashi takeyi mata maganar,
Hawa saman gadon nasu Hafsat tayi,tare da kai hannunta ta ɗago da hosana ajikinta,sae faman kerma jikinta yakeyi,ciwonta ya motsa,da alama an rabu da shan magani,duk a tunanin su abun yayi sauƙi,ashe da sauranta,tabbas hosana tana buƙatar ganin likitan mahaukata,
A faɗace Omar ya daka masu tsawa gaba dayansu yace"wai duk menene yajawo hakan!ba zaku buɗe baki kuyi ma mutane bayani ba!"
Cikin shessheƙar kuka Sehrish tace"Hosana ce,tunda sanyin safiya tafarka,tana raira mana waƙar takusa aure ƙara faɗa breaker,kuma hada kiɗa take raira waƙar duk ta takura kunnuwanmu,har muka farka daga bacci,Don munyi mata faɗa shine ta naɗe hannun rigarta ta hau mu da bugu da cizo kamar ta samu jakuna....'
Cike da mamaki kowa ke kallon sehrish dake kora masu bayani,Ishaq yace"Wai yanzu duk don saboda wannan ku ka kusa illata junanku?gaskiya akwai gagarumar matsala babba ma kuwa,'
Abbas yace"dama da wuya kaga ƴan biyu ko ƴan uku suna zaman lafiya a tsakaninsu,zakaga suna tsananin son junansu,amma ta wani 6angaren basu jituwa,don akwai labarin dana ta6a ji shigen irin wannan daga kokowa suka kashe kawunansu,"
Jin wannan maganar ta Abbas ya ƙara daga masu hankali,Abba yace"in sha Allah,ba zamu bari hakan ta faru ba!tunda abun har yakai ga faɗa da jima juna ciwo,dole a raba masu wurin kwana,shine kawai mafita,"
"Abunda nake ƙokarin cewa kenan"acewar hajiya azeema,
Ammi dai abun yafi ƙarfinta daga ita har Alexandra da hajiya Saratu suna atsaye sun zuba ma sarautar Allah ido,Lamarin yaran yayi matukar daure masu kai,
Dawowa cikin ɗakin nasu Irfan yayi hannunshi ɗauke da First aid box ɗin,ya ƙaraso tare da miƙa ma Sgr akwatin,hannu yasa ya kar6e shi tare da ajiye shi a ƙasa,
Sannan ya zauna,daga gefen gadon,suna fuskantar juna shi da sehrish,wadda ke ta faman shessheƙar kuka,wani irin kallo daya jefa mata,tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa,
"Close ur eyes,"da sauri ta rufe idanunta kamar yarda ya umarta,tana ji yasa mata audiga a wurin ciwon yana goge mata jinin,a sannu ya shiga yi mata dressing din ciwon da taji,bayan ya kammala da ita,Abusufyan ya ruƙo hannun jahad,ya dawo da ita gefen Sgr ya zaunar da ita,cikin lokaci ƙankani Sgr ya kammala yi mata dressing ɗin itama,
"Ita kuma hosana ya zamuyi da ita?kodai asibiti zamu kai ta?Acewar Abusufyan,
Omar yace"Rafayet zai iya duba mana ita anan gida ma"
"Omar am not a psychiatric doctor,though i've experience about their work,zan iya duba ta,Amma a ƙa'ida,psychiatric doctor ya kamata yayi checking ɗinta,bazan shiga aikin da banawa ba,"kaji turawa,ƴan bin ƙa'ida,
Jinjina kai Omar yayi fuskarshi ɗauke da murmushi,ya juya tare da kallon Dr harris dake tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi yace"Bismillah,"yayi maganar yayin da yake yi mashi nuni da hosana wadda ke kwance ajikin hafsat,idanunta sun birkice sae farar kwayar idon kawai,yatsunta kuwa sae faman kerma sukeyi,hada na kafafunta,
Kallonta kawai Dr harris yayi batare daya ta6a jikinta ba,ya faɗi sunan allurar da take buƙata ayi mata,
Da sauri Omar ya ciro wayarshi tare daddana wasu numbobi,ya kira Dr Emran na asibitin Sgr,kiran na shiga emran ya ɗauka,don haka Omar ya miƙa ma Dr harris wayar don suyi magana,
Bayan sun kammala wayar,ya dago tare da kallon Marshal yace"Ya sanar dani cewa within 15 mins zaizo tare da allurar da kuma medicine ɗinta,"
Omar yace"Okey,Allah ya kawo shi lafiya,
"Ku kwanta saman gadon,itama mara lafiyar a kwantar da ita before doctor din yazo,Azmee ki shirya masu breakfast dinsu,yanzu haka ma Yunwa ce ke Cinsu,shiyasa su kayi wannan damban," sae yanzu ammi ta tanka masu,saboda tsabar gatanci maimakon asamu wanda xaiyi masu faɗa da tsumagiya a Zane su, amma kowa ya rufe ido,sae lalla6a su akeyi,diyanso kenan,shalelen abusufyan,
miƙewa sgr yayi daga zaunen da yake,sannan yayi masu nuni da su kwanta,a hankali kowaccensu ta kwanta yadda kasan waɗanda suka yi wata suna Jinya don sunji jiki,a hankali Hafsat ta janye Hosana daga jikinta ta kwantar da ita,har lokacin bata dawo hayyacinta ba,sae faman fari takeyi da idanuwanta,yatsun hannunta dana ƙafafunta sae kerma suke yi,
Haɗa baki su fawan su kayi wurin yi masu ya jiki,kafin daga bisani matasan suka fita daga ɗakin nasu tare da Ammi da hajiya saratu,Ya rage daga Sgr sae Marshal Omar,Hajiya azeema da kuma abusufyan da kuma gwaggwon katsina sae hafsat,Azmee ta wuce kitchen don ta shirya masu breakfast ɗinsu,within 15 mins,Dr Emran ya ƙaraso gidan,a cikin motarshi yazo,tun a waje ya haďu da dr Harris tare da kanal Yusuf a tsaye,dama shi suke jira,fitowa yayi daga cikin Motar hannunshi dauke da Ledar maganin Hosana da kuma injection din da xa'ayi mata,gaisawa suka fara yi fuskar kowannansu dauke da murmushi,canal Yusuf ne ya kar6i Ledar da Emran din yaxo da ita,sun so ya shigo daga ciki suyi breakfast atare dashi,Amma ya sanar dasu uzurinshi,hakan yasa suka ƙyale shi,sallama sukayi da juna sannan suka koma ciki da sauri,
Cikin bedroom din nasu,Dr Harris ya shigo ganinshi yasa Omar da Sgr suka bashi wuri donya ƙarasa gaban gadon,batare da 6ata lokaci ba,ya ɗura ruwan allurar acikin syringe,aikuwa kamar akan idon Hosana yana kai hannu zai ruƙota ta zabura,tashiga yan buge²,ganin haka yasa sgr da Omar matsawa kusa dashi,sae da suka rurruketa dakyar aka samu yayi mata allurar,yana kammala yi mata allurar,nan take zufa ta Shiga tsastsafowa daga jikinta,Kafin wani lokaci tuni bacci yayi awon gaba da ita,hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,
Juyawa dr Harris yayi tare da kallonsu Omar yace"in sha Allah,Zata ji sauƙin jikin nata,sannan idan ta farka,ga medicines ɗinta nan,bayan taci abinci,akwai direction ajikin kowani magani sae a duba,idan za'a bata,"
Amsa mashi sukayi da toh,Omar yace"aikin ka na kyau dr,"sannan ya mayar da idanunshi kan hajiya azeema tunkafin yayi mata magana tace"Zan kula dasu,idan tafarka zan bata maganin da yardar Allah,"murmushi ya saki tare da juyawa ya kalli sgr,"Muje ko?time karya ƙure mana,naga yanzu har 12 ta kusa,nan da wani lokaci xa'a shafa fati.....'bai ƙarasa maganar ba ganin irin kallon da rafayet ya jefa mashi,Dariya Omar yayi yana faɗin"Sorry bro,kada ranka ya 6aci mana,Yau fa ranar farin ciki ce agaremu,murmushi yakamata a gani akan fuskokinmu,ɗanyi murmushi mana,cike da zolaya Omar keyi mashi magana,shi kuwa Namijin sae faman tamke fuska yake yi,daga bisani suka fita daga ɗakin atare da dr harris,
Komawa hajiya azeema tayi tare da samun wuri gefen gadon ta zauna tana kallonsu,duk sun rufe idanunsu kamar masu yin bacci,
"Bismillah gwaggo ku zauna mana,"azeema ce tayi maganar tare da yi mata nuni da saman bedside drawer dinsu,jiki asanyaye gwaggon katsina ta karasa ta zauna saman drawer din,ita dae har yanzu bata yarda Cewar Hosana ce ta ciccijesu ba,
"Azeeme yanzu kema kin yarda cewa yarinyar nan itace da kanta ta gartsa ma ƴan uwanta cizo har haka?Ni nafi tunanin cewa Ya Sayyadine yazo da suffar kura yayi masu wannan aika aikar,mutumin nan fa ba ƙaramin Taƙadari bane,banbancinshi da shaiďan kaho ne kawai da babu,"wannan maganar da gwaggon katsina tayi ba karamin dariya tabasu ba,
Girgiza kai hajiya azeema tayi fuskarta ɗauke da dariya tace"gwaggon shagali,ae in ma shine to ta Allah ba tashi ba,ki kwantar da hankalinki,Sayyadi yake kowa,ba abunda ya isa yayi masu bi'iznillahi,"
Washe Baki gwaggo tayi da alama taji dadin abunda Azeema tace mata,
"Allah yayi mana maganin la'ananne,"
Azeema ta amsa mata da ameen,
Sae wuraren karfe sha biyu da rabi Hosana ta farka jikinta da sauki sosai,kuma tana bude ido ta fashe da kuka tana ambaton sunansu sehrish da jahad,sae da aka nuna mata su sannan hankalinta ya kwanta,
Tuni azmee ta kawo masu breakfast ɗinsu acikin dakin,da taimakon Hafsat da kuma hajiya azeema suka ci abincin,bayan sun kammala cin abincin,Hajiya azeema da gwaggo suka bar dakin,ya rage saura hafsat ita kaɗai,gyara masu bedroom din nasu ta Shiga yi,komai yadawo normal Ba kamar daba da suka hargitsa dakin,bayan ta kammala gyaran ɗakin,wuri tasamu saman side drawer dinsu ta zauna tana kallonsu,
"Hosana ki ji tsoran Allah,jibi yadda kika raunata mu sae kace ba yan uwanki ba,"jahad ce tayi maganar ranta a6ace,
A kule hosana tace"ae laifin ku ne,saboda me zakuyi mun rashin kunya?ni ba yayarku bace?oumma tace ni ce babba acikin ku,saboda majnun ya faɗa mata cewa ni ce na fara zuwa duniya,sae da na shaƙi iskar duniya da minti biyar sannan ke kika zo daga ke kuma sae waccen uwar tsiwar" "dakyar take magana,saboda har yanxu jikin nata da sauranshi,
Guntun tsoki sehrish taja"karki kara ce mun uwar tsiwa,in ba haka ba zan nuna maki kalar nawa haukan,mara mutunci kawai,kuranya mai cin naman ýan uwanta..."
Tunkan ta ƙarasa maganar,da Sauri jahad ta toshe mata bakinta,"Dan Allah ya isa haka,da alama baki ji jiki ba,shiyasa kike ƙoƙarin tsokanota,salon Kija mana jinyar ta koma a gadon asibiti,"
Hafsat dake zaune tana sauraronsu,sae faman kunshe Dariya takeyi,
*Boss Bature*
❤🤍❤
Gaba ďaya matasan gidan,kowa ya Shiga yin wankan juma'a,Kafin wani lokaci duk sun shirya halarta Sallar Juma'a tsaf,kowa ya ɗauki wanka na mutunci wankan shadda,abun sai wanda ya gani,bakowa ne yasan da zancen ɗaurin auren babban yayan nasu ba ko acikin matasan gidan,manyan su ne kawai suka son da ɗaurin auren,sauran kuwa koda zasu san da auren sai dai suji a masallaci a yayin da ake sanarwa.
Zuba mashi ido Alexandra tayi ganin yadda yake ta rawar jiki,yaci uban ado cikin farar shadda,ya zura malunmalun,ya sanya sabuwar hula akanshi,ga agogo sabuwa ya Sanya a hannunshi,ga haɗaɗɗun takalma masu tsadar gaske ya zura a kafafunshi,sae faman sakin Fara'a ya keyi kamar wani sabon ango,yana tsaye agaban mirror hannunshi dauke da kwalbar Turare sae bin jikinshi yakeyi ko ina yana feshe shi saƙo da lungu na jikinshi tamkar zai ƙarar da turaren dukansa,
Abun ya ɗaure mata kai cike da mamaki tace"Darling,irin wannan daukar wanka haka?kaji tsoran Allah kodai kishiya Zaka ƙaromin ne"? dariya abbansu yayi tare da ďan juyawa ya kalli wurin da take zaune gafen gadonsu,ta kura mashi ido ko kyaftawa batayi,
"Ni da nake da Alexandra,Me zanyi da wata ya' mace?Ni na isa ma nayi maki kishiya?kefa ta dabance ko acikin mata,shiyasa lokacin da kika tafi kika barni nagaza samun natsuwa,kuma naqi kula kowa,saboda son da nake yi maki,"
ƴar hararar wasa ta jefa mashi tare da cewa"daɗin baki zakayi mun ko?
"No,ba haka bane,am serious fa,taya zanyi aure baki sani ba?kamar dai wani munafuki,wannan fa wankar sallar juma'a ne,ko kin manta cewa Yau juma'a ne"?
Shiru ta ɗanyi tana kallonshi,kafin ta ɗan ta6e bakinta tare da cewa"Okey,natuna,nidae duk da haka ban yarda dakai ba Allah,ji nake kamar na bika masallacin nan,"
Dariya sosai abba yayi,bayan ya tsagaita da yin dariyar yace"Ashe kina kishi ne?shine kuma kika tafi kika barni,ba kiyi tunanin cewa zan iya ƙara aure ba,a bayan idonki ba"?
"Ae nasan cewa ba zaka iya ƙara aure ba,that's why ban damu akan haka ba,nasan wanene mijina,kuma na yarda da irin son da yake yi mun,bazai haɗa ni da wata ba," acikin zuciyarta kuwa cewa takeyi"Mutun ma ya kuskura yayi mun kishi,da kuwa na tashi gidan nan da bomb,kowa ya rasa,"
Suna cikin magana,sae ga junaid ya faɗo cikin ɗakin,jikinshi na sanye da farar shadda,sae ƙamshi ke tashi ajikinshi,hannunshi na ruke da hularshi,mommynsu na ganinshi ta miƙe jiki na rawa,ta rungumoshi tana shafa sumar kanshi,
"My baby boy,U look so beautiful,Har ma kaso kafi daddynku kyau,"ta ƙarasa maganar a yayin da take raba jikinta daga nashi,
Ashagwa6e yace"Mommy,yanzu kina nufin Abba ya fi ni kyau?kallar ni fa dakyau ki gani tun daga ƙasa har sama,son kowa ƙin wanda ya rasa,"
Dariya sukayi gaba ɗayansu,Abbansu yace"To fa!junaid kishi kake dani"?
Turo baki yayi yana faman ƙunƙuni,irin na shagwa6a66un nan,
Alexandra tace"wasa nake nima,kafi shi kyau nesa ba kusa ba,"
Ƙayataccen murmushi ya saki jin abunda tace,
Mayar da hankalinshi yayi kan abban nasu tare da cewa"Abba mu tafi,kada lokaci ya ƙure mana,"
"Toh,Uban sauri,mu tafi," yayi maganar tare da ruƙo hannunshi,
"Madam mu zamu wuce"
Murmushi tasaki tare da ɗaga masu hannu tace"Adawo lafiya,in anje anyi mana addu'a,"
Junaid yace"kada ki damu mommy zanyi maki addu'a akan Allah yasa daddy ya ƙara maki kishiya,"
ɗan zaro ido waje tayi tana kallonshi,da sauri yaja hannun abbansu suka fuce suna dariya,
A main palour Matasan gidan suka hallara ga6a dayansu,sae ƙamshi ke tashi,kowannansu fuskarshi na ɗauke da murmushi,musamman abusufyan,shigowa abba yayi cikin falon hannunshi cikin na junaid,tunkan ya ƙaraso ya lura cewa babu Rafayet acikinsu,
Kowa sai tambayar ina babban yaya yake,saboda sun saba tafiya masallacin juma'a atare,gaba ɗayansu suke hallara a babban falon nasu duk juma'a before su wuce masallaci,shiru babu rafayet,sae Faman duba agogon hannuwansu sukeyi suna kallon lokaci,har sai da Marshal Omar yace"bari naje bedroom ɗinshi yanzu haka bai kammala shiryawa bane,"da sauri ya tunkari upstairs ɗin yana ƙoƙarin hawa saman benen,Suka jiyo sautin takalmansa,
Gaba ɗayansu suka ɗaga idanunsu sama suna kallonshi,Cike da tsananin mamaki,tunda suke arayuwarsu basu ta6a ganin sgr ya sanya shadda ajikinshi ba,this is the first time daya fara sanya shadda ajikinshi,tabarakallahu ahsanul khaliƙin,Getzner ce sky blue mai ɗaukar ido,wadda sehrish ta ta6a ɗauko mashi a kwanakin baya,donya sanya amma yaƙi sanyawa,To yau dai itace ya sanya ajikinshi,Babu hula akanshi amma ba ƙaramin kyau sumar kanshi tayi ba,yayi mata gyara na musamman,hannunshi kuwa na sanye da Wannan diamond watch ɗin tashi,yayin da ƙafarshi ke sanye da penny loafers,tunkan ya ƙaraso down stairs din ƙamshin turarenshi ya gauraye ko'ina,yadda kasan tauraro acikin taurari haka ya bayyana,tafiya yakeyi gently tamkar baisan taka ƙasa,fuskar nan tashi aɗaure babu fara'a ko miskala zarratin,sae kace ba yau zai angwance ba,
A hankali yake tattaka stairs ɗin, yayin da yake manna links ɗin hannun rigarshi,koda ya ƙaraso cikin falon,batare daya kalli kowannansu ba,ya nufi hanyar fita daga main falo ɗin,Murmushi abbansu ya saki aranshi yace"Rafayet kenan"
batare da 6ata lokaci ba,Suka fito waje gaba dayansu,dama already motocinsu na nan a jere,Nan kowa ya buɗe motarshi ya shiga,A jere motocin suka fuce daga cikin gidan ɗauke da jiniya,
*💃💃💃ALHAMDULILLAH, A YAU JUMA'A DUBBAN JAMA'A SUN SHAIDA ƊAURIN AUREN RAFAYET SALAHUDDEEN HOSSEIN,TARE DA AMARYARSA SEHRISH SALAHUDDEEEN ABUSUFYAN💃💃💃*,
bayan kammala sallar juma'a aka ɗaura auren nasu,Sae dai muce Allah ya basu zaman Lafiya atsakaninsu❤
*Finally Rafayet weds sehrish*🥳🥳🥳😘
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina 08103884440❤_
Fitowarta kenan daga cikin toilet taji gabanta ya faɗi rasss!da sauri takai hannu ta dafe saitin zuciyarta,ƙamewa tayi abakin toilet ɗin batare da ta motsa ba,jahad dake zaune saman darduma,da alama ta kammala sallah,jikinta na a sanye da hijab Maroon colour,ta ɗaga hannayenta sama tana addu'a,tunkan ta kammala ta lura da halin da Sehrish ke ciki,tana shafa addu'ar da sauri ta miƙe ta tunkareta,
"Sehrish!lafiya meya faru ne? A ɗan ruɗe ta tambayeta,
Sehrish kuwa sam ta gaza buɗe bakinta tayi magana,saboda yanayin da ta shiga,gaba ɗaya jikinta yayi wani irin sanyi,
Ruƙo hannunta jahad tayi tare da cewa"sehrish!wai lafiya?ki amsa mun mana"?
Lumshe ido sehrish tayi a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya,daga bisani ta ɗan ware idanunta tana kallon fuskar jahad,dake tsaye agabanta,
"Ko kin fama ciwonki ne"?
Girgiza kai sehrish tayi alamar a'a,tukunna tace"Jahad,ina fitowa daga cikin toilet ɗinnan,naji gabana ya faɗi rass,kuma naji jikina gaba ɗaya yayi mun sanyi,bansan meya jawo hakan ba,"
"Ki cigaba da ambaton Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un acikin zuciyarki,In sha Allah babu abunda zai faru dake fa ce alkhairi,"ta ƙarasa maganar tare da janyo sehrish ɗin har izuwa gefen gadonsu ta zaunar da ita sannan tace"Ki kwantar da hankalinki,bari na ɗauko maki kayan da zaki sanya,".
Amsa mata tayi da toh,kafin ta mayar da idanunta kan farin towel ɗin dake sanye ajikinta ta ƙura mashi ido tana kallonshi zuciyarta cike fal da fargaba,ita kanta batasan dalilin faruwar hakan ba,
Jin an turo ƙopar ɗakinsu yasa tayi saurin ɗagowa don taga wanene,Hajiya azeema ce ta shigo hannunta ruƙe da shopping bag fara fuskar nan ɗauke da murmushi kamar wadda akayi ma albishir da gidan aljanna,murmushi sehrish ta saki da sauri ta miƙe tsaye tana gaisheta"Ina yini Aunty azeema,"
Bata amsa mata gaisuwar ba sae cewa tayi"me nake gani haka?Amarya sanye da towel,ko baki san cewa an ɗaura ba"?
A ruɗe sehrish tace"Aunty azeema,bangane me kike nufi ba,naji kince an ɗaura"?
dariya azeema tayi tare da cewa"su6ul da baka ne fa,Bansan ma na faɗa ba,inaso ince ko an ɗaura abincin lunch ne,ashe azmeen bata a cikin ɗakin nan,"
"Ina yini Aunty azeema,"jahad ce tayi maganar a yayin da take ƙarasowa wurinsu hannunta ruƙe da wasu riga da wando na turkey,da ta ɗaukko ma sehrish,
"Lafiya lou jahad,in ce ko ke zaki sanya waɗannan kayan na hannunki,"
Girgiza kai jahad tayi tare da nuna sehrish tace"A'a bani zan sanya ba,Sehrish na ɗauko masu don ta sanya"
Cike da Zolaya Aunty azeeema tace"kin ta6a ganin inda Amarya ta sanya waɗannan kayan a ranar ɗaurin aurenta"?
Cike da mamaki suka haɗa baki wurin cewa"AMARYA KUMA!!"?
da sauri Azeema tace"Kai,mantawa fa nakeyi,wani film na kalla yanzu,to yarinyar cikin film ɗince aka ɗaura ma aure,a yau juma'a batare da saninta ba,abunne ya tsayamun arai shiyasa nake ta sako zancen,"
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,Jahad tace"Amma gaskiya na tausaya mata Aunty,meyasa za'ayi mata aure batare da saninta ba?To idan ita bata son Mijin da aka aura mata zata iya kashe kanta fa,'?yanayin yadda jahad tayi maganar fuskarta da alamun tausayi,
Sehrish tace"Nima abunda nakeson cewa kenan,zai iya yiwuwa akwai wanda take so,hakan ba ƙaramin illa zaiyi mata ba,"
Murmushi hajiya azeema tayi tana kallonsu,har sai da suka kai ƙarshen maganar tasu,sannan tace"kun ce wani abu anan,amma idan mijin ya kasance kamar babban yayan ku fa?kuna tunanin akwai macen da zata iya rejecting ɗin aurenshi"?
Kallon juna suka kuma yi,kafin jahad tace"Gaskiya zaiyi wuya Aunty azeema,ae babban yayanmu na daban ne shi ko acikin maza,zan iya cewa ma duk macen da ta mallake shi ba ƙaramar mai sa'a bace,ƴar baiwar ce,kuma ita jinin nasara ce,da ƙafar dama ta shigo duniya,"
Dariya sosai hajiya azeema tayi,jin yadda jahad ke zuzuta SGR,
"Duk da ance abincin wani gubar wani,Zai iya yuwuwa ita yarinyar bata ra'ayin namiji irinsa,ba wai don bai kai ba...."
Katseta hajiya azeema tayi da cewa"kamar ya kenan"?
Sehrish taci gaba da cewa"yanzu kamar ace ita yarinyar,tafi son baƙin namiji dogo,sannan wanda baya tara sumar kai,kuma tafi son namiji mai yawan fara'a a fuskar shi,ko kuma ace ita yarinyar tafi son ta auri wanda bai ruƙe da muƙamin soja,Ya abun zai kasance?zatayi farin ciki idan ta samu kamar babban yayanmu,amma ta wani 6angaren baiyi dai dai da ra'ayinta ba,"
Tana kai ƙarshen maganar,Azeema tace"kamar ke kenan!kina nufin bakison namiji kamar babban yayan ku"? Tayi tambayar cike da fargabar amsar da Sehrish zata bata,
Sunnar dakai ƙasa sehrish tayi tana wasa da yatsun hannunta,yayin da fuskarta ke ɗauke da ƙayataccen murmushi,wannan ya tabbatar mata da cewa Tana RA'AYINSA,
Dariya hajiya azeema tayi tare da ɗago da shopping bag ɗin dake hannunta ta miƙe ma sehrish,
"Wedding gown ce aciki,tare da takalmanta,Zuwa bayan la'asar,da zarar an kammala sallar,Zanzo in taimaka maki wurin sanya rigar,sannan da kaina zanyi maki kwalliya,"
A ruɗe sehrish ke kallonta don bata gane inda zancen nata ya dosa ba,ita kanta jahad abun ya ɗaure mata kai,
Ganin yadda suka saki baki suna kallonta,yasa tayi saurin cewa"Oh,na manta ban sanar daku ba,Wani wasan kwaikwayone zamu yi yau acikin gidan nan don nishadi,that's why we choose you to be our bride in the drama,"
Wani irin farin cikine ya lullu6e sehrish,cike da zumuɗi ta kar6i bag ɗin,tana fadin"Amma abun zai ƙayatar sosai,dama inason inga na sanya wedding gown,Ashe da rabon yau in sanyata,
Jahad tace"gaskiya abun zai bada citta,yau kam zamu sha hotuna,"
"Har ma video idan kunaso zaku iyayi,Ni bari na wuce kitchen wurin Azmee,".
Tana ƙoƙarin fita,ta tuna da hosana da sauri ta juyo tare da kallonsu tace"Ya jikin hosana?naga sae bacci take tayi tunda nashigo,da alama jikin yayi sauƙi kenan"?
Jahad tace"eh,taji sauƙi sosai,"
"To,ku ya jikin naku"?
"Ae mu munji sauƙi,"suka haɗa baki wurin bata amsa,
Jinjina kai tayi tare da kama hanyar fita tana cewa"Allah ya ƙaro sauƙi,"
Suka amsa mata da cewa"Ameen,"
A saman gado sehrish ta ajiye shopping bag ɗin,sannan ta kar6i kayan da jahad,ta ɗauko mata batare da 6ata lokaci ba ta zura riga da wandon ajikinta Red colour ne ba ƙaramin kyau suka yi mata ba,gaban dressing mirror taje wurin da ta ajiye ribbom ɗinta before ta shiga wanka ɗaukarsa tayi tare da zura shi acikin hannunta,sai da tafara tattara gashin kafin ta sanya ribbom ɗin ta ɗaure shi tamau,
"Ko dai in tashi hosana,tayi wanka itama?kin ga ko sallah batayi ba,"acewar jahad,
Sehrish tace"ko baki tasheta ba,Yunwa zata tayar da ita,kibarta kawai,kada ki tado mana jangwamgwam,"
"Baiwar Allah ni tausayi take bani,duk in na tuna yadda ta samu ciwon haukanta,sai inji idanuna sun cika tab da kwalla,"acewar jahad,
Sehrish tace"Ni kaina ina tausaya mata sosai,Amma inaji araina cewa,Wata rana hosana zata dawo cikin hankalinta ne,sannu a hankali,Haka muke fata in sha Allah,
Suna cikin magana,Jiniyar motocin dake shigowa cikin gidan ta karaɗe kunnuwansu,da ƙarar gaske har cikin dodon kunnuwansu,
"Su babban yaya ne suka dawo daga sallar juma'a,bari in leƙa inga wankan daya ɗauka yau,!"
Cike da farin ciki sehrish tayi maganar tare da juyawa ta nufi window,jahad ma tabi bayanta,janye labulan sukayi sannan ta zuge masu glass ɗin,Baza idanunsu sukayi suna kallon abunda ke wakana a farfajiyar gidan,
Da gudun gaske motocinsu ke shararowa saman titin da zai kawo ka har wurin parking space na gidan,tun daga bakin gate titin ya fara,
"Wlh abun kamar a shirin film" jahad ce tayi maganar,abun ba ƙaramin burgesu yayi ba,
Lokacin da motocin suka ƙaraso ciki,a wani slow suka tsaya a jere,
"Ko wanene zai fara fitowa,bari mu zuba ido muga wankan su babban yaya,"acewar sehrish,
Jahad tace"Ni har na ƙosa,in ga wankan da daddynmu ya dauka yau da kuma wankan Baby junaid,"
Suna cikin magana,wani gabjejen soja mai ƙirar samudawa,ya buɗe motar farko,Abbansu junaid ne ya fito,other side ɗin kuma Uncle Abusufyan ne,fuskokinsu ɗauke da murmushi,yadda kasan Gonar auduga,
Bayansu kuma sae motar da ke bin bayan tasu,Abokin Abbansu ne Tafeeda tare da abokin Omar,Adams da kuma shattima,daga motarsu sae motar Marshal Omar,zuba ido su Sehrish su kayi suna kallon Ya Omar dinsu,ganin ya fito daga cikin motar ya kuma zura hannayenshi acikin motar,jimm kaɗan sae gashi ya kinkimo junaid tare da aza shi asaman kafaɗarshi,
Waro ido waje su sehrish sukayi Jahad tace"Mun shiga uku!meya faru da baby junaid ɗinmu?kodai bashi da lafiya ne?kalli fa yadda ya Omar ya ɗaukoshi asaman kafaɗarshi,"
"Yanzu haka rigimarshi ce,nasan junaid sarai,har goyashi zai iya cewa ayi,yadda yake jin kanshi kamar jinjiri,"Sehrish ce tayi maganar fuskarta ɗauke da dariya,
Jahad tace"wannan fa ba abun dariya bane,tunda kika ga an ɗaukoshi asaman kafaɗa to tabbas akwai abunda ya faru dashi,nidai Allah yasa kafiyarshi ƙalau,
Sehrish na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,ta hango Amstrong ya fito daga cikin motar Sgr,da sauri ya zagaya tare da buɗe mashi motar,zuba ido tayi tana jiran fitowarshi,
A hankali ya zuro ƙafarsa ɗaya waje,almost 5 mins,tukunna ya ƙarasa fitowa daga cikin motar gaba ɗaya,
Gabanta ne taji ya faɗi rass!ba ita kaɗae ba hatta jahad ya tafi da imaninta,a rude sehrish ta shiga yarfa hannu tama rasa abunda zata ce,just speechless,
Jahad ce tayi ƙoƙarin cewa"Tabarakallahu Ahsanul khaliqin!gaskiya babban yayanmu duniya ne!Irin wannan ɗaukar wanka haka!Ni tunda nake a rayuwata ban ta6a ganin mutumin da shadda tayima kyau sosai irin Babban yayanmu sae kuma Ya Omar,Wankan shadda ba ƙaramin kyau yake yi masu ba,ko don suna da ƙirar jiki mai kyau ne,!koda yake shima fa Ya yusouf ba ƙaramin kyau shadda takeyi mashi ba,kinsan shi wani irin sanyin kyau ne dashi na miskilai,hatta su twins da fawan kowa ma yana yin kyau idan suka sanya shadda amma ba kamar yaya Rafayet ba,da ya Omar,junaid kuwa na dabanne shi,"
Jahad sae faman zuzuta su takeyi,duk a tunaninta Sehrish na sauraronta,batasan cewa sehrish ta lula wata duniyar ba,gaba ɗaya Sgr ya tafi da Imaninta,ya janye hankalinta,babban farin cikinta shaddar daya sanya ajikinsa,saboda tana kwaɗayin son tagan shi sanye cikin kayan hausawa,kuma ta gane cewa shaddar nan ce wadda ta ta6a dauko mashi a kwanakin baya,Ya ƙi sanyawa saboda baya sanya kayan hausawa sai nasu na turawa,
Yadda kasan tauraro acikin taurari haka ya bayyana,fuskar nan babu annuri,ya tamketa tamau,kamar wanda aka ɗaura ma aure da Mutuwa,hannunshi na ruƙe da hular da abbansu ya sanya mashi kafin su shiga masallaci,don a ganshi da mutunci,amma ɗan tahalikin nan kamar jira yakeyi a kammala sallar,suna fitowa daga masallacin bayan ɗaurin auren ya tumbuƙe hular,don shi arayuwarshi ya tsani duk wani abu da zai rufe mashi sumar kanshi,ba ƙaramin ji yake da ita ba,zaiyi wuya kaga Sgr da hula akanshi,sai dai Facing cap ko kuma in ya sanya jacket mai hula ajikinta shine zakaga ya sanya hula,hatta shaddar dake ajikinshi atakure yake da ita duk da shi kanshi ya shaida irin kyan da yayi acikinta,ya saba da kayansu marasa nauyi shiyasa yake jinshi duk atakure,Ƴan uwanshi kowa farin ciki yake yi gashi ya hana kowa ya furta kalmar nan Wato ango kasha kamshi,ya tsani yaji an ambaci hakan,ko kuma a kirashi da sunan Ango,kowa so yake ya ɗanyi mashi wasa da dariyar nan da ƴar zolayar nan da akeyi ma angwaye amma rafayet ya hana hakan!yaƙi jinin akirashi da sunan ango,
Gaba ɗaya suka tunkari ƙopar da zata sadaka da babban palourn gidan,"
Jiki asanyaye sehrish ta zuge glass ɗin windown,ta gyara labulen,
Zuba mata ido jahad tayi tana kallonta,ganin yadda ta sauya lokaci guda kamar wadda aka zarewa lakar jikinta,
Gefen gadon ta koma ta zauna,sam tagaza samun natsuwa acikin zuciyarta,ganin rafayet da tayi ya fama mata ciwon dake acikin zuciyarta,
"Sehrish wai meya faru ne?Yanzun nan fa muke raha dake,amma lokaci guda kin canza,ko baki lafiya ne"? Ta ƙarasa maganar,tare da samun wuri gefen sehrish ɗin ta zauna,
Muryarta tamkar zata yi kuka tace"bakomai,kawai zuciyata ce har yanzu bana jin daɗinta,"
"Dan Allah ki kwantar da hankalinki rishi,Ki saki jikinki,ko zaki kwanta ne?ki ɗan samu bacci may be Ki samu natsuwa acikin zuciyarki,"cike da kulawa jahad keyi mata maganar,
..Sehrish na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,suka ji an kwankwaso ƙopar ɗakin nasu,
Da sauri Jahad ta miƙe tare da tunkarar ƙopar tana tambayar wanene,
Daga waje taji ance"Daddynku ne"
Jin haka yasa jahad yin saurin buɗe mashi ƙopar,
Shigowa ciki Abusufyan yayi fuskarshi ɗauke da ƙayataccen murmushi,zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi baki asake,from head to toe,irin kallon ƙurullar nan,
A ruɗe tace"daddy!kaine!"
Dariya ya ɗan saki tare da cewa"Ni ne mana,me kika gani"
A susuce tace"Wow daddy kayi kyau Over,kamar matashin saurayi ɗan shekara ashirin da biyar,"
Wannan maganar ta jahad,ba ƙaramin dariya ta bashi ba,ta wani 6angaren yaji daɗin yabon da tayi mashi,
Miƙewa Sehrish tayi jin maganar daddynsu nufo wurinsu tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Masha Allah,daddy kayi kyau sosai Allah,kamar irin sabbin ƴan dubu dubu ɗin nan,kasan yadda suke da ɗaukar ido,ga kyau,gasu da burgewa,"
Fashewa da dariya Abusufyan ya kuma yi bakin shi yaƙi rufuwa sai faman hura mashi kai sukeyi,
daƙyar ya samu ya tsagaita da dariyar yace"har kun tuna mun da mommyn ku,duk in naje ɗaukarta daga islamiyya in aka tashe su,Ƙawayenta suyi ta santin wankan da na ɗauka,Har leƙena akeyi ta cikin mota ana nuna ni ga mijin abu nan yazo,Ya iya ɗaukar wanka,ya haɗu sosai,Mommynku ta tsani taji suna yabona,abun haushi yake bata,idan na kuskura na fito daga mota ina jiranta,haka zasu zagaye ni suna kallona,harma suyi mun magana mu gaisa,da zarar abu tazo fuskarta a ɗaure,a fusace take ruƙo hannuna ta tura ni cikin mota,mu tafi,hakan ba ƙaramin dariya yake bani ba Inajin daɗin kishina da takeyi sosai,amma kishin da takeyi mun yajawo rabuwarmu da ita ba don naso ba......"kasa ƙarasa maganar yayi,saboda wani abu da yaji ya taso mashi mara daɗin ji acikin zuciyarshi,tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,
tsananin tausayin Abbansu ne ya kamasu duk jikinsu yayi sanyi,daƙyar jahad ta iya buɗe baki tace"daddy,dan Allah kayi haƙuri da duk abunda ya faru tsakaninka da Oumman mu,nasan cewa abun yana yi maka ciwo acikin zuciyarka,Oumman mu bata kyauta maka ba,gashi sanadin hakan ta jefa rayuwarta cikin haɗari da kuma rayuwarmu,sau dayawa takan zauna tayi ta kuka,musamman da daddare ko runtsawa bata iya yi,kullum cikin ambaton sunanka takeyi tana cewa haƙƙin Abusufyan ne yake bibiyar rayuwarta,na cutar dashi sosai,Mijina yana so na amma na butulce mashi,saboda baƙin kishi na,nayi danasanin rabuwa dashi sosai,Ya Allah ka yafemun,mu lokacin duk bamu san abunda take nufi ba...."tuni hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,itama sehrish hawayen ne suka soma shararowa daga cikin idanunta,Hannu Abusufyan ya sanya tare da janyo su ya rungumesu sosai ajikinshi,sae lokacin ƙwallar dake cike taf cikin idanunshi ta shiga wanke mashi fuskarshi,muryarshi a kasalance ya soma magana"Oummanku yarinya ce sosai,Ko a lokacin ban ruƙe ta a raina ba,saboda akwai ƙuruciya sosai atattare da ita,Nasha wahala sosai akanta,saboda Allah ya jarabce ni da tsananin sonta,ina sonta sosai,har yanzu soyayyar da nake yi mata na nan yadda take,babu abunda ya canza,Nayi kukan zuciya a lokacin dana rasa ta,kamar in zauce,lokacin dana ji zancen aurenta da sayyadi,Allah kaɗae yasan ƙuncin dana ji acikin zuciyata,bakomai nake tunawa ba,fa ce Amanarta da mahaifinta ya damƙa mun,ya yarda dani sosai baba buzu,yasan cewa banajin magana,ga ƙuruciya dake ɗibana amma a haka ya toshe kunnuwansa Ya aura mun ƴarsa,Naji daɗi sosai,A lokacin kamar kamar me,Allah ya jiƙanshi,
Atare suka amsa mashi da Ameen,ɗagowa dasu yayi daga jikinshi yana ƙoƙarin kai hannu ya share hawayen dake zuba akan fuskarshi,da sauri suka riga shi sanya tafukan hannyensu suna goge mashi hawayenshi,
Murmushi ya saki,don ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba,
"Dama nasani wata rana zaku share mun hawaye na,gashi Allah ya nuna mun ranar da raina kuma da lafiyata,"
Yayi maganar tare da sanya hannayenshi duka biyu,asaman fuskokinsu yana share masu hawayensu,bayan ya kammala goge masu hawayen,yace"oh namanta,ban baku tsarabar masallaci ba,"da sauri ya zura hannunshi cikin aljihun wandon jikinshi,
Farar leda ce ya curo mai ɗauke da dabino da goro,
Miƙa masu yayi tare da cewa"hada aya da kwakwa nasiyo maku amma ta hosana ce ita kaɗae zan bamawa,wannan dai gashi ku raba a tsakaninku,"
Kar6ar ladar jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi,sehrish tace"dama na lura kafi ji da hosana,"
Abusufyan yace"eh mana,saboda itace autarku a yanzu,nafi sonta,kuma nafi ji da ita,"
Zumbura baki sehrish tayi tare da cewa"yanzu duk irin cizon da tayi mana a jikinmu baka gani ba?
"Nagani mana,ae gwaggo ta tabbatar mun da cewar ba yin kanta bane,Ya sayyadi ne yazo da suffar kura yayi maku wannan aika aikar....."karasa maganar yayi tare da fashewa da dariya,suma dariyarce ta kufce masu,
Wucewa cikin ɗakin nasu,yayi tare da zama daga gefen gadon yana kallon hosana dake kwance tana bacci,baki a buɗe,
Da sauri ya sanya hannunshi,a cikin aljihun ya curo ledar dake ɗauke da yankakkar kwakwa da ƙullin aya acikinta,
Kwakwar ya ciro,cike da tsokana ya zurata cikin bakin hosana,cikin bacci hosana ta kama kwakwar ta shiga taunarta abakinta,
Dariya sosai sukayi abun ba ƙaramin nishaɗi ya basu ba,
Wuri suka samu suka zauna,suna kallon tsokanar da Daddynsu ke yi ma Hosana,
gaba ɗaya ta cinye kwakwar daya sanya mata abakinta,wata kwakwar ya kuma curowa,tare da zura mata abakinta,kamar wata kura haka ta kama kwakwar tana gartsa,tana taunewa acikin bakinta,
"Daddy,ɗan janye kwakwar mu gani ya zatayi,"acewar jahad,
A hankali ya shiga ƙoƙarin janye kwakwar daga cikin bakinta,ta cije ta da haƙoranta,yana ja tana rurruƙeta,dariya sosai Abusufyan yake yi abun ba ƙaramin nishaɗi yake sanyashi ba,
Da ƙarfi ya janye kwakwar aikuwa a firgice hosana ta farka,fuskarta a yamutse,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,muryarta a kasalance ta ambaci sunanshi"daddy!"
"Na'am,hosana,"ya amsa mata,yunƙurawa tayi dakyar ta miƙe daga zaune tana ƙare mashi kallo kafin ta kwantar da kanta asaman kafaɗarshi,tana faman lumshe ido saboda baccin da tasha,
"Kin tashi lafiya?ko baccin bai isheki bane?
A shagwa6e tace"Ya isheni,yunwa ma nake ji,Cikina babu komai,gashi ko wanka banyi ba,Su jahad duk sunyi wanka basu tashe ni ba,balle inyi nima,"ta ƙarasa maganar tana kallonsu sehrish dake a bakin gadon,murguɗa masu baki tayi tare da harararsu,
"Shikenan,bari in na fita yanzu zanyi ma azmee magana,sae ta shirya maki lunch ko"?
..ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Miƙa mata ledar kwakwar yayi"kar6i nan,tsarabarki ce,ta masallaci kada ki ɗanma kowa kinji ko"?
Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i ledar daga hannunshi
"Nagode sosai daddyna,kuma bazan ɗan masu ba,"
Wurga mata harara jahad tayi tare da cewa"Sannu ko?daddynmu zakice ba daddyna ba,ae bake kaɗae bace a wurinshi ba,"
Gatsina mata hanci hosana tayi tare da ƙara rungumo Abusufyan ajikinta don suji haushi,hakan ba ƙaramin dariya ya bashi ba,
"Daddy,ƙamshin turaren jikinka akwai daɗi sosai Allah,"tayi maganar tare da sanya hancinta ajikin rigar shaddar jikinshi tana shaƙar ƙamshin turaren kamar wata mayya,
"Idan kinaso ma,zan ɗauko maki kwalbar turaren gaba ɗaya,sae ki dinga shafawa kema hakan yayi maki"?
Girgiza kai tayi"a'a daddy,kabarshi kawai,Ya Omar ya hanani shafa turare,idan na shafa wannan turaren zaiyi ƙamshi sosai,kuma idan Yaji bazaiji daɗi ba,zaice hosana bakijin maganata ko?to daga yau babu ni babu ke,ni bazan zauna da mai kunnan 6era ba,'
Fashewa da dariya su jahad sukayi,tuni hosana ta ɗaure fuskarta tana harararsu,Abusufyan yace"yayi kyau babyn Omar,yana da kyau ki dinga jin maganarshi,kina yi mashi biyayya,kada ranshi ya 6aci,"
Cike da jin kunya hosana ta janye jikinta daga na Daddynsu,ta janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,
Wayar Abusufyan ce ta shiga yin ringing,har lokacin fuskarshi ɗauke da murmushi,yace"Bari na shiga ciki,zansa azmee ta shirya maku launch,"
"To daddy,"suka amsa mashi da sauri ya fuce,
*JUNAID ROMEO*
Tashin hankalin da ba'a sama shi date,Tun wurin ɗaurin aure da junaid yaji sanarwar ɗaurin auren Babban yayansu,tare da Rishi ɗinsa,acikin masallacin ya yanke jiki ya faɗi a sume,saboda baisan da zancen ɗaurin auren ba,kwatsam yaji ana sanarwar,
A bedroom ɗinsa Omar ya kwantar dashi,bayan sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,koda ya buɗe idanunshi yaga Abbansu ga kuma yayyansu Isha da Abbas,ga Marshal Omar da sauran matasan duk suna tsaye akanshi,Fashewa yayi da matsanancin kuka mai cin rai,Cikin shesshekar kuka yace"Wayyo Allah na!Wlh an cuce ni,Abba kana sane da cewar ni ke son sehrish amma ka aura ma babban yayan mu ita,wlh bazan yarda ba,Ae ni na fara sonta,don me za'a aura mashi ita!ashe baku sona,hakanan kuke nuna mun soyayya,Wlh nidai bazan yarda ba,abba ka cuce ni sau nawa ina faɗa maka cewar inasonta,Ita nake da burin in aura amma....." bai ƙarasa maganar ba,Omar ya daka mashi tsawa wadda ta gigitar dashi,
"Rufe ma mutane baki junaid!shashasha kawai!Abban ne kaka cewa ya cuce ka?kai ko kunyar yin zancen aure agaban mu baka ji?ubanwa zaiyi maka aure da ƙananun shekarunka?kai da ita waye zai raini wani in anyi maku auren"?
Tafin hannayensa ya sanya tare da rufe fuskarshi,yana cigaba da kukan kuma hakan baisa ya daina sambatun da yake yi ba,
"Ya omar ba zaka gane bane,Abun da ciwo,wlh ina sonta sosai,ina son rishi,kuma itama tana sona,wlh ba babban yayanmu take so ba,Ni take so,don me za'a aura mata shi..."
A zafafe Omar ya zabura zai kai mashi mari a kan fuskarshi,da sauri Abba ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Kuyi mashi uziri,wlh nasan yana sonta sosai,banta6a tunanin cewa junaid ya san so ba,ni duk a tunani na wasa yake yi mun,ashe dagaske yakeyi,dole yaji ciwo acikin zuciyarshi saboda ya saba da ita sosai," muryarshi a sanyaye yayi maganar,Abun ya ta6a mashi zuciyarshi,tsananin tausayin junaid ne ya kamashi,
Shi kanshi marshal Omar jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,kowa yasan da irin shakuwar dake atsakaninshi da sehrish amma ba suyi tsammanin cewar dagaske sonta yakeyi ba,
Hatta su ishaq dake tsaitsaiye cirko cirko agaban gadon nashi ba ƙaramin tausayi ya basu ba,duk yabi ya burkice,fuskar nan tayi jawur da ita,jijiyoyin jikinshi duk sun bayyana,
Adai dai lokacin da Abusufyan ya ƙaraso kopar ɗakin junaid ɗin,kasa shiga ciki yayi saboda jin maganganun da sukeyi aciki,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin cewar junaid sehrish yake so,kuma adalilinta ne ya suma a masallaci,
Duk yadda suka so su shawo kan junaid da lallashi don yayi shiru abun ya faskara,hancinsa har ya fara bleeding,hankalinsu yayi mugun tashi,
Matsawa sukayi kusa dashi suna lallashinsa,Ja da baya ya dinga yi asaman gadon har ya ƙure ma head board ɗin gadon,sautin muryarshi ashake saboda tsabar kukan daya sha,
"Ku rabu dani,bana son ganin kowa!ba kunfi so na mutu ba!to zan mutu ne yanzun nan sae hankalinku ya kwanta,"
Hawaye ne suka cicciko tab a idanuwan kowannansu,
"Junaid dan Allah kayi haƙuri,Allah ya riga daya ƙaddara faruwan hakan,dama can ita ba matarka bace," Acewar Abbas,
Girgiza kai ya shiga yi yana cewa"yaya abbas,bazaku gane bane,bakusan yadda nake ji acikin zuciyata bane,tafarfasa take yi mun,wlh bazan iya jurewa ba,inason rishi sosai,idan har kuna so kuga farin ciki na,to akwance ɗaurin aurenta da babban yayanmu a aura mun ita shine kawai,in ba haka ba mutuwa zanyi,Wayyo Allah rishi ɗina,"yana magana yana shessheƙar kuka,
Abbas yace"Calm down ur mind junaid,akwai mata da yawa agari suna yawo kyawawan gaske,ga ƙanwar matata nan Amal,baka ganta ba ƴar ƙarama dai dai kai,idan kayi hakuri zaka samu wadda tafi ta ma,"
Bubbuga kafafunshi yayi asaman gadon tare da cewa"Ya Abbas wlh banson kowace mace in ba ita ba,Sehrish itace juliet ɗina ita kawai nakeso,kodai aban rishi ko kuma in haɗiyi zuciya in mutu,"to fa,!junaid ya tashi hankalin kowa,yaƙi saurarar kowa,yau an ta6a romeo shugaban ƴan soyayya,
Cikin lallashi Abbansu ya ambaci sunanshi"Babyn Abbanshi,"
Wani irin kallo ya wurga ma abban nasu idanuwan nan sunyi luhu luhu saboda tsabar kukan daya sha,
"Ni ba babynka bane,Romeo ɗin mommynsa ne,saboda baka sona Abba,"ya karasa maganar yana faman matse kwallar dake sharara daga cikin idanuwanshi,
Shiru Abbansu yayi bai ƙarasa maganar tashi ba,junaid yafi jin haushinshi akan kowa,saboda yasan da cewar yana sonta amma ya ɗaura mata aure,duk da shi bai ɗauki maganar tashi serious ba,sae yau daya haukace masu,
Turo ƙopar Abusufyan yayi jikinshi duk ya mutu,tsabar tausayin junaid ne ya kamashi,
Juyowa suka yi suna kallonshi,matsa mashi hanya sukayi ya wuce,har izuwa gaban gadon junaid din,
Zuba mashi ido yayi yana kallonshi,duk ya fita cikin hayyacinshi ya zama abun ban tausayi,wannan ya tabbatar mashi da cewar ba ƙaramin son sehrish yake yi ba,
ɗagowa junaid yayi tare da kallon Uncle ɗin nasu,Cikin shessheƙar kuka yace"Un..cle!hada kai aka ɗaura ma rishi ɗina aure da babban yayan mu,bayan kunsan cewa ina sonta sosai,"
Hawa saman gadon abusufyan yayi tare da janyo junaid ya rungumoshi ajikinshi yana ɗan bubbuga bayanshi da hannunshi,cikin lallashi yace"Junaid,Ni bansan cewa kana sonta ba,da banyi kuskuren aura ma rafayet ita ba,kasan cewa inason ka sosai,kowa ma yana sonka,kuma zamu iya yin komai saboda farin cikinka,hatta rayukan mu ma zamu iya badawa domin ceto rayuwarka,balle kuma ƴar uwarka?sae ita zata gagara?"
"Amma..uncle..meyasa ku ka ɗaura mata aure da babban yayan mu?maimakon ni"?daƙyar yake magana,
"Kayi haƙuri junaid,dama Allah ya ƙaddara cewar ita ba matarka bace,Matar babban yayanku ce,"
ɗagowa yayi daga jikin Abusufyan din fuskarshi jaga jaga da hawaye hada majina,yana kallon uncle ɗin yace"yanzu kuna nufin cewa,babu ni babu rishi?in haƙura da ita kawai?kun za6i ku rasa ni kenan"?
ruƙo hannunshi abusufyan yayi tare da sassauta muryarshi yace"haba junaid,in sha Allah ba zamu rasa ka ba saboda sehrish,ae ba ita kaɗai bace ba,Ko ka manta cewar su ƴan ukune?kuma kamanninsu ɗaya,Idan kayi haƙuri zan baka auren ɗaya daga cikinsu,"
Da sauri Marshal Omar ya katse mashi hanzarinshi da cewar"Wacce acikinsu,"?
dariya abbansu yayi ganin yadda omar ya ɗan tashi hankalinshi,
Abbas yace"Uncle,kada fa kayi mashi alƙawarin auren ɗaya daga cikinsu,saboda junaid bai da wayau baisan wasa ba,kuma koda za'ayi mashi aure ba yanzu ba,sae yayi hankali nan da in ya kai shekara talatin,"yana kai ƙarshen maganarshi,Ishaq ya ɗaura da cewar"Bazai yiwu ba ayi ma junaid aure a yanzu,bayan ga yayyensa nan duk sun manyanta kowa na bukatar aure,yayi haƙuri dai akwai matar abokina na nan,yanzu haka tana dauke da ciki,idan ta haifi jinjirin muka ga mace ce,sae ayi masu magana,su ajiye mashi ita,in ta girma lokacin yayi hankali sai a aura mashi ita,"
Suna cikin maganar nan,Junaid ya sume,a jikin Abusufyan,a ruɗe abusufyan ya shiga jijjiga shi yana kiran sunanshi"Junaid!Junaid!!"
Hankalin Abbansu atashe yace"Duk laifinku ne!meyasa bazakuyi shiru da bakinku ba,gashi nan ya ƙara sumewa,kuma ina da tabbacin cewar maganganun da kuke gaya masa ne suka ƙona mashi rai,"
Hannu Omar yasa tare da ɗauko bottle water ɗin dake ajiye saman side drawer dinsa,ya cire murfin tare da mika ma abusufyan,A hannu ya tar6o ruwan sannan ya watsa mashi a fuskarshi,
Dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,
Shafa fuskarshi Abusufyan yayi tare da cewa"Junaid,"
Tunkafin ya buɗe idanunshi yace"Uncle mutuwa zanyi,"
"Junaid dan Allah kadaina kira mana mutuwa,Indai kan sehrish ne,NI NAYI MAKA ALƘAWARIN CEWA ZAN AURA MAKA ƊAYA DAGA CIKINSU IN HAR TANA SONKA,"
Muryarshi a kasalance yace"Uncle nasan wasa kake yi mun,kada kayi mun alƙwarin da bazaka iya cika mun ba,Zan haƙura kawai in rungumi ƙaddarata,"_
Wannan maganar da junaid yayi ba ƙaramin kashe masu jiki tayi ba,
Tuni hawaye suka cicciko a idanuwan Abusufyan,muryarshi na kerma yace"meyasa kace haka junaid"?
"Uncle,bani da wayau,ni yaro ne har yanzu,kowa yana yi mun kallon sakarai,kuma bani da aikin yi,a haka zaka bani auren ƴarka""?
A hankali wasu siraran hawaye suka shiga gangarowa a saman fuskar Abusufyan,daƙyar ya iya buɗe baki yace"Junaid!duk rashin wayonka baka kaini ba lokacin da ina yaro,bana jin magana har sa'insa nake yi da Mahaifiyata,na iya rashin kunya saboda ni bana jin kunyar kowa,ni ina mu'amala da mata muje party,muje night club,Ka faɗamun ɗaya daga cikinsu wanne kake yi?
"Ko ɗaya bana yi"ya bashi amsa,
Murmushi abusufyan yayi kafin ya cigaba da cewa"kana da kyakkyawar zuciya junaid kai mutumin kirki ne,kana son kaga farin ciki a fuskar kowannan mu,saboda me Ni zan gaza sanya ka farin ciki?Duk da banajin magana amma ahaka Mahaifin Oummansu Sehrish ya bani auren ƴarsa,Nima don haka daga yau ka sanya aranka cewar na baka Auren JAHAD!idan ma akwai mai sonta cikin yayyenka sai dai yayi haƙuri yabar maka,
Wani irin Farin Ciki ne ya lullu6e junaid,lokaci guda ya nemi kukan da yake yi ya rasa,bashi kaɗae ba hatta sauran ƴan uwan nasa dake tsaye a wurin ba ƙaramin daɗi suka ji ba,Musamman Abbansu,Yaji daɗi har cikin ranshi,
Cike da zolaya abusufyan ya kallesu tare da cewa"Ko akwai mai ja acikin ku ne"?
Fashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu,tare da haɗa baki aurin cewa"Mu mun isa?Uba ya mallaka ma ɗansa auren ƴarsa?waya isa yaja daku?ae magana ta ƙare"
Sae lokacin junaid ya fashe da dariya har fararen haƙoransa suka bayyana masu ɗauke da matsakaiciyar wushirya siririya,mai kyan gaske,
"Surukina,fadamun me kakeso yanzu"?
Cikin shagwa6a junaid yace"Maganin ciwon kai,sannan ina jin yunwa sosai,"
"Bari inyi ma jahad magana takawo maka,hakan yayi maka"?
Cike da jin kunya junaid ya rufe fuskarshi da tafukan hannayenshi,yana dariya ƙasa ƙasa,
Zolayarshi suka shiga yi,har sai da suka sanya shi farin ciki sosai,sannan suka bar cikin bedroom ɗin nashi,ya kasance shi kaɗae ne acikin ɗakin kwance asaman gadon,kamar wani zautacce sae faman sakin murmushi yake yi,bakinshi yaƙi rufuwa,
Turo ƙopar ɗakin nashi,akayi da sauri yakai idanunshi wurin,Azmee ce ta shigo hannunta ruke da tray,lunch ne ta shirya mashi,ƙarasawa tayi tare da ajiye mashi tray ɗin saman front table din gadonshi,
Mikewa yayi daga zaune,yana gaisar da ita,
"Ina yini Aunty azmee,ya aiki,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Lafiya lou junaid Alhamdulillah,"
Ta karasa maganar tare da ɗaukar plate ta buɗe warmer mai dauke da chicken pepper soup serving spoon ta sanya tana ɗaukar cinyar kazar tana sanya mashi a plate,kallonta yakeyi sae ya dinga ganin kamar jahad ce,saboda tsabar son ya ganta musamman da yaji an mallaka mashi ita,
"Idan ka kammala ci,ga magani nan Uncle ɗinku ne yace na baka kasha,"tayi maganar tana nuna mashi maganin dake ajiye asaman tray ɗin,
"Nagode sosai Aunty azmee,"
"Na lura kamar kana cikin farin ciki sosai yau,"_
Murmushi ya saki tare da cewa"Aunty azmee,Am so,so happy today,Uncle abusufyan ya bani auren Jahad,Ya mallaka mun ita,"
Waro ido waje Azmee tayi cike da mamaki tace"Wai dagaske"?
ɗaga mata kai yayi alamar eh,Hannayenta ta daga sama cike da tsantsar farin ciki tace"Alhamdulillah!Allah na gode maka!ashe dae ina da rabon ganin aurenka junaid,Allah ya nuna mana lokacin,"
"Ameen ameen,"ya amsa mata,
"Dan Allah kaci abincin nan sosai,kaci ka koshi angon jahad,"
Rufe fuskarshi yayi yana dariya ƙasa ƙasa, itama dariyar ce ɗauke akan fuskarta har ta kammala zuba mashi abincin,sannan ta kama hanyar fita daga ɗakin,sae da junaid yaji alamun ta bar bedroom ɗin nashi sannan ya buɗe fuskarshi yana faman sakin murmushi
*Haroon*
Motarshi na qoqarin shiga cikin hotel yaji an ambaci sunanshi"Ya Haroon,"gabansa ne ya faɗi rass jin Muryar mutum mai mahimmanci a wurinshi,da sauri yaci burki tare da zuge glass ɗin motar a slow,
Tsaye take jikinta na asanye da Uniform,yadda kasan mahaukaciya,gashin kanta duk ya tarwatse ya hargitse,babu gyara,ƙafafunta babu takalma,tayi buɗu buɗu da ita,waro ido waje haroon yayi yana kallonta,tamkar a mafarki,kusan minti 5 kafin ya buɗe motar,ya fito har lokacin kayan jiya ne ajikinshi,a hankali yake tunkararta yana ƙare mata kallo,ita kuwa da gudun gaske ta tunkareshi,faɗawa tayi saman ƙirjinshi tare da zagayo da hanneyenta ta bayanshi,ta ƙanƙame shi sosai,lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka,
Lumshe idanunshi yayi tare da sanya hannunshi abayanta,yana ɗan bubbuga bayan nata,a hankali ya ambaci sunanta"AMRISH"
Boss tabarku da tunani,Bashin friday ne na biyaku,kowa yasan cewa weekend banayin posting,Don haka mu haɗu On monday,in Allah yakaimu da rai da lafiya,don jin Yadda zata kaya👍
*SALON NA DABANNE🔥*
*kada fa ku manta har yanzu muna acikin Littafin Abban Sojoji ne Takun ƙarshe wanda Ni hafsat Bature Na rubuta*
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina pls banda kiran waya,bana amsa shi,Just message za'ayi mun ta whatsapp in sha Allah zan amsa,don bana shariya indai ina online 08103884440❤Masu kirana ƙarfe goma na dare kuna son jamun wlh😡_
Cikin shessheƙar kuka ta amsa mashi"na..am yaya haroon" raba ta yayi daga jikinshi tare da sanya hannayenshi ya tallabo fuskarta,daƙyar take iya buɗe idanunta waɗanda ke jike sharkaf da hawaye,zuba mata ido yayi yana kalllonta,fuskarta duk ta kumbura tayi haske,gashi ta ɗan yi rama wannan ya tabbatar mashi da cewar tana cikin matsananciyar damuwa,yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana idonshi ya sauka akan hannunta,kanula ya gani,a ruɗe yace"Amrish!Wannan fa?faɗa mun meya faru?Kinyi rashin lafiya ne"?
daƙyar ta iya buɗe baki tace"Poison nasha,Saboda na gaji da zaman duniyar nan,Mommy ta 6atamun rai,ba ta sona ba ta damu dani ba......".
Bata ƙarasa maganar ba,yaja hannunta izuwa wurin motarshi,buɗe mata motar yayi ta shiga back seat ta zauna sannan shima ya shiga mazaunin driver,shiga cikin Hotel ɗin ya ƙarasa shiga da ita,bayan yayi parking ɗin Motar ya fito ya buɗe wurin da amrish take ya shiga daga ciki,
Cikin sanyin Murya yace"faɗamun abunda ya faru tsakanin ki da ita"?
Nan ta labarta mashi abunda ya faru tsakaninta da mommynta tun daga farko har ƙarshe,
"Amrish!ashe baki da hankali?saboda kawai ta gaya maki wannan ƴar maganar sai ki nemi kashe kan ki?suwa kika yi ma asara?
Shiru tayi yayin da idanunta ke cike tab da kwalla,
"So kike narasa ki ko"?da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a,
"Bazan ƙara ba,yaya haroon mommy ce ta 6ata mun rai,kuma ni bansan zama wurinta,Na tsaneta bata kwanta mun araina ba,dan Allah kada ka mayar dani wurinta,ka kaini gidanku kawai in zauna tare daku,"
Waro idonshi ya ɗan yi kafin yace"gidan mu!in kaiki a matsayin wa?so kike kija mun?yayyena fa gaba ɗayansu maza ne kuma sojoji ne,bazaiyiwu ba ki zauna acan,"
Fuskarta tamkar zata yi kuka tace"Ya kake so nayi da rayuwata ne?ni babu wurin da nake jin daɗin zama,Ka kaini kawai gidan ku in zauna,idan ina ganinka sai hankalina yafi kwanciya,amma ni bazan koma wurin mommy ba,in ba so kake ka rasa ni ba gaba ɗaya,"tayi maganar aɗan shagwa6e,
Shiru ya ɗan yi yana tunanin mafita,don kuwa ya santa da baƙar zuciyar nan ta gado,in har yaƙi yi mata abunda take so to tabbas zata aikata abunda ta faɗa ne,
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kallonta yace"It's Okey,zan kai ki gidan mu amma kafin nan,Ki fara zama a wurina,Ni abunda ya ɗaure mun kai,taya ya har kika gano inda nake?"
Sae lokacin ta ɗan saki murmushi akan fuskarta,kafin tace"Ae nasan duk wani wuri da kake zuwa,kaine baka sani ba....".
"Wato bibiyata kikeyi ko"? Dariya tayi,tana ɗaga mashi gira,
"Zanyi maganinki,mai ɗan kumatu,"
Sosai ya shiga zolayarta,har sai da yaga farin ciki akan fuskarta,atare suka fito daga cikin Motar hannunshi acikin nata,wucewa yayi da ita VIP,inda room ɗinsa daya kama a hotel ɗin yake,bayan sun shiga ciki wanka ya sanyata tayi sannan ya daukko mata kayan da zata sanya ajikinta,dama ɗakin nasa na sharholiyarsa ne,akwai duk wani abu da mace zata buƙata,tunda nan yake kawo ƴan matansa da samarinsa duka dae,bayan ta kammala shirya kanta,order ya bada na abincin da zataci,
Bayan an kawo mata abincin,taci ta ƙoshi,sannan yace ta kwanta ta huta,Cikin ƙankanin lokaci bacci ya ɗauke ta asaman gadonshi,
Safa da marwa ya shiga yi acikin ɗakin tunanin shi,taya za'ae yakai amrish gidansu!?Yasan cewa ba wani abun tashin hankali bane,kuma in ya kaita zasu kar6eta hannu bibbiyu,amma bazai bari su ganshi ba da sunan wanda ya kawota,in ba haka ba zai zama abun zargi a wurin ƴan uwansu,
Sae faman zirga zirga yakeyi acikin ɗakin,lokaci zuwa lokaci yakan ɗan juya ya kalli amrish dake kwance saman gadon nashi,hankalinta kwance sae sharar bacci take yi,bai ta6a ganin yarinyar da ta yarda dashi ba kamar amrish,kwata kwata ba ta jin tsoranshi don ta rungumeshi,ba wani abu bane a wurinta,duk da shi ya koya mata hakan,har kwana saman gado ɗaya suna yi da ita,amma wani abu bai ta6a shiga tsakaninsu ba,sae dai ƙawayenta su Zeenatu,babu wadda bai yi lalata da ita ba acikinsu,kuma har yanzu yana tare da kowaccensu,duk in ya buƙace su zasu kawo mashi kansu ne,
❤🤍❤
After La'asar,
Tsaye take agaban dressing mirror tana ƙare ma kanta kallo yadda kasan wadda za ta je gasar Kyawun duniya,Wedding gown ce a jikinta fara ƙal,tabi shape ɗin jikinta,hips ɗinta ya fito sosai kamar zai fasa rigar haka daga saman rigar net ne,sosai fatar ƙirjinta ta fito mai matuƙar jan hankali,Daga bayan Rigar lace tattoo ne wanda ya ƙara fito da kyawun rigar,fuskarta na ɗauke da light makeup,ta shafa jan baki red colour,Hannunta na sanye da haɗaɗɗiyar wrist watch ta diamond da Aunty azeeema ta saka mata,mai haɗe da ring da kuma chain ƴar ziririya fara,ga earrings ɗinta,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fitowa daga jikinta Kamar wadda aka tsamo daga cikin ƙogin turare,gaba ɗaya bedroom ɗin nasu Ƙamshin turarenta ne ya karaɗe ko'ina,ƙafarta na sanye da stilleto,matsiyacin high heels ne mai shegen tsini,shima launin rigar jikinta ne,ƙafafunta sun fito ɗass acikinsa,
"Wow masha Allah,Tabarakallahu Ahsanul khaliƙin!"hajiya azeema ce ta ambaci hakan,jahad kuwa hannunta na ɗauke da Wayar sehrish ta shiga Camera sae video take yi mata,ita ma hosana hannunta na ruqe da wayar hajiya azeema I phone 13,Sun taru sai video suke ɗaukar sehrish,
Ƙoƙarin juyowa tayi da sauri hajiya azeema ta dakatar da ita"Kada ki juyo yanzu,bari na aza maki net ɗin nan asaman kanki zai ƙara maki kyau sosai,Bayan ta kammala sanya mata mayafin sannan tace"Sannu a hankali zaki juyo ba da sauri ba," a natse Sehrish ta soma juyowa a wani slow,Hosana na kallonta ta cikin camera sai faman sakin Murmushi take yi,
Hajiya azeema tace"Yawwa My photographers ku ɗaukarmun ita da kyau,ta fito sosai acikin Video ɗin,yadda zanji daɗin ɗaurawa a status ɗina,
Ƙarasa juyowa sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da ƙayataccen Murmushi,ita kanta tasan tayi kyau over,Zuciyarta cike fal da farin ciki,kamar wadda akayima albishir da gidan Aljanna,dama hannunta akwai zanen jan lallen da akayi masu na walima,yana nan raɗau a hannunta bai goge ba,ta ruƙe yar purse ɗinta a hannunta,
Tun daga ƙasa Hosana ta fara ɗaukarta ta cikin camera ɗin har izuwa saman fuskarta,
"Turn ur back,yadda zasu ji daɗin ɗaukarki da kyau,"acewar Azeema,
Juyawa sehrish tayi a hankali suka ɗauki bayan,sannan ta sake juyowa,Jahad sae faman zuzuta ta take yi tana cewa"wlh yadda kasan Amaryar Gaske,Sehrish kinyi kyau sosai kamar dollars"
Dariya hajiya azeema tayi jin abunda jahad tace,
tace"Wato kuɗi sune suka fi komai kyau kenan?shiyasa ake kwantanta su da mutumin da yayi kyau ko"?tayi maganar tana kallon Jahad dariya sukayi gaba ɗayansu,
Suna cikin rahar nan wayar hajiya azeema tayi ringing,sunan Abba ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,da sauri hosana ta miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar bayan ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnanta,
Tun kafin tayi sallama taji muryar abba yace"Azeema kina ina ne"?
"Ina a ɗakinsu sehrish ne yanzu haka,na kammala yi mata kwalliya ne harma ta sanya rigar amaren...."
Katse ta yayi da cewa"Karki kuskura,kice zaki kai yarinyar nan ɗakin Rafayet!".
Hankalinta atashe tace"Saboda me Yaya hossein"?tun daga kan muryar Abba ta tabbatar da cewar yana cikin matsananciyar damuwa,
"Tun farko sai da na faɗa maki cewar wannan auren na sirri ne,kuma na faɗa maki dalilin dayasa ya aureta ba don yana sonta ba fa ce don tayi mashi aiki,.." a ɗan ruɗe hajiya azeema ta dago tana kallon Sehrish,jikinta ne yayi wani irin sanyi har cikin zuciyarta taji babu daɗi,
Da sauri tace masu"Ina zuwa" tana faɗin hakan ta fuce daga ɗakin,a nan cikin corridor din ta tsaya,Muryarta asanyaye tace"Yanzu yaya kana nufin cewa yarinyar nan bazata tare aɗakin Mijinta ba!"
"Azeema so nake ki fahimce ni,!ki natsu ki saurare ni,!rafayet wani irin bauɗaɗɗan mutunne mai wuyar sha'ani,Wlh bazai bari yarinyar nan ta zauna a part ɗinsa ba,da sunan amaryarshi,Yanzu haka zancen da nake yi maki,Ya hana uban kowa ya ɗauki hoto tare dashi!gaba ɗaya babu wanda ranshi bai 6aci ba saboda rafayet!"
Muryar hajiya azeema tamkar zatayi kuka tace"Amma ba'ayi ma yarinyar nan adalci ba!Meyasa tun farko ba'a shawarce ta ba?kafin a ɗaura mata aure dashi!yakamata ace tasan da zancen auren da za'ayi mata da kuma dalilin yin auren!me kuke tunanin zai faru idan har yarinyar nan taji cewar an aurar da ita ne don tayi aiki kawai a ƙarkashinsa"?
Shiru Abba yayi batare daya ce mata komai ba,
Jinjina kai kawai hajiya azeema tayi tare da cewa "Shikenan kawai,Zansa ta cire rigar dana sanya mata,Amma dae banji daɗi ba,Kuma in sha Allah rafayet sai yayi danasanin yin hakan da yayi!"tana kai ƙarshen maganarta,tayi rejecting kiran,Tuni idanunta sun cicciko da kwalla,Ranta yayi mugun 6aci,
"Aunty azeema!"hosana ce ta ambaci sunanta,da sauri takai idanunta ƙopar ɗakin nasu,tsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi tace"Munata jiranki,Kince zamu je kai amarya,"
"Kada ki damu hosana,Yanzu zan shigo ciki,"
Amsa mata tayi da toh,sannan ta koma cikin ɗakin,Kusan 15 mins hajiya azeema tana tsaye batare da ta motsa ba,sae da zuciyarta ta lafa,sannan ta wuce cikin ɗakin nasu,
A tsaitsaye ta samesu suna jiran dawowarta,gaba ɗaya duk sai taji ba daɗi,Musamman yadda taga Sehrish sae faman sakin Murmushi takeyi,tsananin tausayinta ne ya kamata,Shin wata irin rayuwa yarinyar zatayi a ƙarƙashin Sgr?mutumin da baisan Soyayya ba,Tabbas zata sha wahala a hannunshi,Domin kuwa zai mayar da ita tamkar baiwarshi ne,su yaya hossein sunyi kuskuren aura mashi ita,da sunan tayi mashi aiki,wannan tamkar ƙasƙanci ne,kuma yarinyar bazata ji daɗi ba,ranta zai 6aci sosai idan ta gano cewar aure akayi mata,auren ma na sirri,tamkar wata mara gata,babu walima babu wani party,babu taron mutane,babu wedding pics,dole abun ya ta6a Zuciyarta,na biyu da sa hannun iyayenta suka aura mata shi da sunan tayi aiki a ƙarƙashinsa ba matsayin matarshi ba,tabbas an gama cutar da ita,
Mamaki abun ya ba su Jahad ganin hajiya azeema tayi tsaye agabansu,kuma ta ƙurawa sehrish ido tana kallonta,Kamar mai nazarin wani abu,
Jahad ce ta ambaci sunanta"Aunty azeema,"
Firgita tayi lokaci guda ta ɗan saki murmushin yaƙe tare da cewa"Am sorry fa,wlh na shafa'a ne,Yanzu mai ya rage mana muyi"?
Hosana tace"Kai amarya mana,ki faɗa mana a ina zamu kai rishi ɗin,"
Hajiya azeema tace"Ae wannan shirin drama ne!ba dagaske ba,A nan zakuyi wasan ga wayata ma idan kuna buƙatar yin hotuna,Ni yanzu inaso zan wuce ciki ne,"
Da sauri Hosana ta kar6i wayar daga hannun hajiya azeeman,sallama tayi masu da sauri ta fuce daga cikin ɗakin,
"Kamar yanayinta ya canza ko"?jahad ce tayi maganar tana kallon sehrish,
"Nima na lura da hakan,Hosana wanene ya kira ta a waya nasan kinga sunan daya bayyana akan screen ɗin,Zai iya yiwuwa wani abu aka sanar da ita wanda ya 6ata mata rai,"acewar sehrish,
Hosana tace"Ni dai naga Sunan Yaya hossein,amma bansan wanene ba,"
"Sunan Abbansu Junaid ne,Allah yasa dae ba wani abu ya faru ba,"sehrish tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,
"Kodai naje najiyo mana abunda ke faruwa cikin gidan"?Hosanar tayi tambayar tana kallonsu,
Jahad tace"A'a,babu ruwanki,tunda ba kiran mu akayi ba,"
Cigaba da ɗaukar hotuna sukayi acikin ɗakin,Shigowa junaid yayi fuskar nan tashi ɗauke da murmushi,Suna ganinshi suka haɗa baki wurin cewa"Baby Junaid!"
Ɗaure fuskarshi yayi tare da ɗan turo bakinshi ashagwa6e yace"Ni ku daina Kirana da sunan baby,In ba haka ba,ran kowa zai 6aci a wurin nan,"ya ƙarasa maganar tare da aza idanunshi kan Sehrish dake tsaye tasha Kwalliya abunta,sakin baki yayi galala yana kallonta,a ruɗe ya ambaci sunanta"Reesh,"
Murmushi Sehrish ta sakar mashi,tare da yi mashi fari da ido,sannan tace"Na'am,Junaid ya kaga wankan nawa,"?
daƙyar ya iya cewa"reesh,yanzu kina sane aka ɗaura maki aure da babban yayan mu bayan kinsan da cewar Ina sonki"?
Gabanta ne ya faɗi rassss!!Ba ita ba hatta su Jahad da hosana a ruɗe suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma,da Babban yayan mu!"
Shi kanshi junaid ɗin sae da gabanshi ya faɗi,tunani ya shiga yi anya Sehrish tasan da auren kuwa?Yanayin yadda ya ga ta razana ya tabbatar mashi da cewar batasan da zancen auren ba!acikin ranshi yace"meke faruwa ne?Mommy batasan da auren babban yaya ba,kuma itama rishi dasu jahad basu san da auren ba!Abba ya 6oye masu kenan!aikuwa saina tona masu asiri kowa yaji,dama ya 6ata mun raina yau,duk irin amanar dake tsakanina da Abba ya rasa dame zai sakamun sai da wannan,"
"Junaid dan Allah kayi mana bayani dalla dalla yadda zamu fahimta!"acewar jahad,
Kallon fuskar sehrish yayi ganin ta zuba mashi ido tana kallonshi,kalmar daya furta masu ce take ta maimaitawa acikin zuciyarta
"nidai baza aji mutuwar sarki abakina ba,Abba yace kar na faɗama kowa cewa an ɗaura aurensu,"yayi maganar tare da sanya hannu ya toshe bakinshi,
Hankali atashe suka shiga kallon juna atsakaninsu,
"Don Allah junaid ka faɗamun auren wa aka ɗaura"? muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,
"Sehrish kiyi haƙuri bazan iya sanar dake ba,Amma idan kina son samun ƙarin bayani,kije wurin Uncle ki tambayeshi,
Jiki na rawa sehrish ta kama hanyar fita da sauri Hosana tabi bayanta,suka fita atare,
Matsawa yayi kusa da jahad,tare da ruƙo hannayenta yace"Jahad!Albishirinki"?
"Goro,"ta bashi amsa fuskarta ɗauke da murmushi,
"Fari ko Ja"? Wurga ido ta ɗan yi sama kafin tace"Fari,"
"Uncle ya bani aurenki,"jin wannan maganar yasa hankalin jahad ya tashi,lokaci guda ta ɗaure fuskarta,tare da fisge hannunta daga cikin nashi,
Gabansa ne ya faɗi,ganin yadda ta canza mashi lokaci guda tsoranshi kada ace jahad ba son shi take yi ba,
"Jahad baki sona?bakison ki aure ni ko"?
Shiru jahad tayi tana ƙare mashi kallo daga ƙasa har sama,
Tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,fargabarshi wata amsa jahad zata bashi,in har bata amince ba shikenan zai rasa damar da yake da ita,na mayar da gurbin rishi ɗinsa daya rasa,
Motsi ta soma yi da la66anta daƙyar ta iya cewa"Junaid!dagaske kake mun ko wasa?tell me the truth pls,i know u are just teasing me,'
Girgiza kai yayi tare da cewa"Am serious jahad,Bazan 6oye maki ba,da farko sehrish nake so sosai,in har ba zaki manta ba,lokacin dana ɗauko ki a school matsayin sehrish,idan zaki iya tunawa sunanta nake ambata a matsayin ke,nayi tunanin itace shiya sanya na sanar dake abunda ke acikin zuciyata,Amma yau batare da sani na ba,A masallaci naji sanarwar ɗaurin Auren Sehrish da babban yayan mu,har sai da na kusa zaucewa ƙarshe a masallacin na yanke jiki na fa....."
A razane jahad ta katse shi da cewa"Wai dagaske an ɗaura auren Sehrish!kuma da babban yayan mu!?
ɗaga mata kai yayi alamar eh,kafin ya ɗaura da cewa"Ni kaina bansan da zancen auren nasu ba sae a masallaci dana ji ana sanarwar,abun ba ƙaramin ta6a zuciyata yayi ba,na shaqu sosai da sehrish,
Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,jin zancen auren Sehrish da Sgr,ta rasa gane a wane yanayi take ciki,farin ciki ko kuwa akasin hakan!babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda aka 6oye masu ba'a sanar dasu ba,Ko meyasa?Yanzu shikenan an ɗaura auren rishi ɗinsu?ta zama married woman?
Runtse idanuwanta tayi tare da sanya hannu ɗaya ta dafe gefen goshinta,a hankali ta furta"Ya salaam,"
"Jahad,inason naji amsar tambayar da nayi maki"?muryarshi a kasalance yayi maganar,don ya qagara yaji amsar da zata bashi,
A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar junaid,tana kallonshi tace"junaid Daddy da kanshi ya baka aure na?kuma ya tabbatar maka da cewar bada wasa yake maka ba"?
Bubbuga ƙafafunshi yayi saboda hasalar da yayi,a ƙule yace"eh mana,shi da kanshi ya mallaka mun ke agaban kowa da kowa,yaji tausayina ne saboda halin dana shiga,"
.....fuskarta aɗaure tace"Meyasa daddy zai yi mun haka?nace mashi ina sonka ne?kuma ya rasa ma wazai ba aure na sai kai?junaid kayi mun ƙanƙanta!Ni bazan iya zaman aure dakai ba,nafison namijin daya mallaki hankalinshi ba shagwa6a66e ba sangartacce irinka...."tun kafin takai ƙarshen maganarta,hawaye suka fara wanke mashi fuskarshi,cikin shessheƙar kuka yace"au haka ma zaki ce jahad?shikenan babu komai,"da sauri junaid ya juya tare da nufar kopar ɗakin nasu gwanin ban tausayi,
Yana ƙoƙarin kai hannu ya buɗe ƙopar,da gudu jahad ta faɗa bayanshi tare da rungumoshi sosai tana dariya,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya junaid ya sauke,kwantar da kanta tayi asaman bayanshi,magana ta soma yi mashi anatse"junaid,ko da yake yanzu na canza maka suna,Ka tashi daga junaid ka koma Babyn jahad,Ina fata hakan yayi maka,"
Tafin hannayenshi ya sanya tare da share hawayenshi,wani irin sanyi ne ya ratsa cikin zuciyarshi,Calmly ya ambaci sunanta"Jahad,Kin amince da aure na?a yadda nake?zaki iya haƙuri dani?ki zauna dani amatsayin Mijin ki uban ƴa'ƴanki kuma"?
Lumshe idanunta tayi yayin da hancinta ke shinshinar ƙamshin turaren jikinshi,
"I accept ur love junaid,I love u so much,nayi farin ciki sosai da daddy ya baka aurena,a ashirye nake dana baka kulawar daya dace junaid,"
Saboda tsabar farin ciki bakin junaid yaƙi rufuwa,hannunta ya ruƙo tare da zagayo da ita,ta dawo gabanshi suna facing ɗin junansu,zuba ma juna ido sukayi na wani lokaci,batare da sun sha Wahala ba,Sun amince ma junansu kowa ya samu abunda zuciyarshi ke muradi,janyota yayi ta faɗa asaman ƙirjinshi,zagayo da hannayenshi yayi ta bayanta,sosai ya rungumeta,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi,lokaci guda suka kamu da tsananin son kasancewa da junansu,
*Boss Bature*
❤🤍❤
"Rafayet!Ka 6ata mun rai!ka ƙuntatamun!Amma kai ko ajikin ka?meyasa zakayi mun haka"?Abbansu ne yayi maganar a yayin da yake tsaye acikin bedroom ɗin Sgr,Idanuwanshi sun cika tab da hawaye,
"Abba,don me zaka tashi hankalin ka akan auren nan!You know the reason why I married her,Saboda inaso taci gaba dayin aiki a ƙarƙashina,ni ban shirya yin rayuwar aure ba,Babu wannan a tsari na," yana magana huci na fita a bakinshi,saboda tsabar 6acin ran da ya ke ciki,ji yake gaba ɗaya sun takura rayuwarshi,ba don komai ba sai don saboda sun nemi Alfarmar ya taimaka yayi koda hoto ɗaya ne shi da Sehrish don su ajiye na tarihi,
Gyaɗa kai Abbansu yayi tare da cewa"A haka kakeso kai ayi maka biyayya,bayan Ni ban isa na sanya ka abu kayi mun ba,narasa gane kai wani irin mutunne!ka ce yarinya bazata zauna a part ɗinka ba!kuma ba zaka ɗauki hoto ba atare da ita,nasan meyasa kayi hakan!saboda kada hotonku ya shiga duniya a dinga nunata a matsayin matarka!saboda kai a wurinka wannan ƙasƙancine aganta a matsayin matarka,saboda ka fi ƙarfin ta ko"?
Yayi maganar ranshi a 6ace,Sgr kuwa ko ajikinshi,yana daga tsaye agaban dressing mirror ɗinshi ya juya ma Abbansu baya,har lokacin bai canza kayan jikinshi ba,babu wanda baizo yayi mashi magana ba akan ya amince da buƙatar mahaifinsu amma yaƙi yarda,hatta Ishaq da Abbas sunyi sunyi har sun gaji sun ƙyale shi,haka Marshal Omar sunyi barambaram dashi,saboda ya 6ata masu rai,
"Zan tafi na bar maka ɗakin ka,Amma inaso na ƙara tunasar dakai cewa Abusufyan ya baka tsawon wata ɗaya kacal akan ka canza ra'ayinka game da auren yarjejeniyar nan,Zaka iya soke shi in har kana so acikin ƴan kwanakin nan,Amma idan har ka bari wata ɗaya ya wuce baka canza ra'ayin ka ba,duk abunda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa ka kuka da kanka!kuma babu ruwana Na zame hannu na aciki,
A fusace Sgr ya juyo tare da kallon Abban nasu yace"bazan ta6a canza ra'ayi na ba akan hakan!Idan ma yana tunanin hakan to ya daina!Bana buƙatar wani time nayin tunani!wata uku na cika zan sallame ta ne!
Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,ta wutsiyar idonshi ya hango mutun atsaye,a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,
Sehrish ce atsaye tana kallonsu,gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa,domin kuwa taji duk abunda suka ce kaf acikin kunnanta,Jikinta har kerma yakeyi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa akan fuskarta,
Jin shessheƙar kukanta yasa Sgr Juyawa tare dakai idanunshi wurin da take tsaye a ƙopar ɗakin nashi,tun daga ƙasa har sama yabita da kallo,
A hankali Abbansu ya ambaci sunanta"Sehrish!"
Juyawa tayi da gudun gaske tabar ƙopar ɗakin nashi,gaba ɗaya tabar part ɗin nashi,saukkowa tayi downstairs,Su fawan ne tsaitsaye acikin babban falon,koda suka ji shessheƙar kukanta sae hankalinsu ya koma akanta,kowa ya shiga tambayarta lafiya,
Bata tsaya sauraronsu ba,da gudu ta wuce bedroom ɗinsu,tana shiga ciki ta samu junaid da jahad azaune gefen gadonsu suna shan soyayya,jin shigowarta yasa suka mike tsaye hankali atashe suka shiga tambayarta Lafiya,
Bata basu amsa ba,kai tsaye ta nufi toilet ta buɗe ƙopar ta shige ciki,da ƙarfi ta datse ƙopar,sannan ta tsugunna ƙasa tana kuka tamkar ranta zai fita,
Gaba ɗaya Jahad da Junaid suka nufi ƙopar,Suna kwankwasawa suna kiran sunanta"Sehrish!Sehrish!dan Allah Rishi ki buɗe mana kopa!
Turo kopar ɗakin nasu akayi,Abusufyan ne tare da hajiya azeema suka shigo ciki hankalinsu atashe,basu jima da shigowa ba,sai ga Abbansu junaid,dama tunda yaga ta watsa aguje tana kuka ya biyo bayanta,
A bakin kopar shiga toilet ɗin suka tsaitsaya cirko cirko
"Dama nasan abunda zai biyo baya kenan!"acewar hajiya azeema,
Abusufyan yace"Ni bansan waya faɗa mata ba,Naso ace ni na fara sanar da ita,"
Fuskar Abba a yamutse yace"wlh bansan da ita ba!Yanzun nan fa naganta a ɗakin Rafayet,muna cikin magana dashi akan zancen auren nasu,kawai naji shessheƙar kukanta,ashe duk taji abunda muka ce,"
Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,musamman Abusufyan har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata,
Ƙoƙarin lallashinta suka shiga yi amma ina,Sehrish taƙi sauraron kowa kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita,tana jin muryoyinsu a waje sai faman yi mata magiya sukeyi akan ta buɗe masu ƙopar,
Junaid duk yabi ya ruɗe sam baisan cewa abun zai ta6a zuciyarta ba har haka,Ita kanta jahad ba ƙaramin tausayin Sehrish taji ba,kowa sai da yasha jinin jikinshi,babban abunda suke ji ma tsoro kada ta illata kanta,
Bakomai ne ya ƙona mata rai ba,Fa ce abunda kunnuwanta suka jiyo mata,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,komai ya fita aranta,tabbas tana son Sgr sosai har cikin ranta,kuma babu abunda ya canza acikin zuciyarta,tayi farin ciki mara misaltuwa na kasancewarta matarshi,wannan babbar kyauta ce agareta,sae dai kash bataso ya aureta batare da yana sonta ba!Sam bata ta6a ra'ayin hakan ba,tafi son ta auri wanda take so kuma yake sonta,bawai wanda takeso ba,Shi baya sonta,bugu da ƙari kuma ya aureta ne don taci gaba da aiki a ƙarkashinshi na wata uku kacal!
"Idan ba damuwa inaso ku ɗan bani wuri in shawo kanta,"hajiya azeema ce tayi maganar,
Abusufyan yace"kina ganin zaki iya shawo kanta kuwa?
"Ku je kawai,Ni nasan yadda zanyi da ita,ku ɗan bamu wuri,"
Kama hanya sukayi gaba ɗayansu hadasu jahad suka bata wuri,kamar yadda ta bukaci su fita daga dakin,
Zuƙunnawa hajiya azeema tayi abakin ƙopar toilet ɗin,Saboda ranta ya bata cewar sehrish tana zuƙunne a ƙasa,ta gane hakan ne ta hanyar sautin kukan nata,
Cikin lallami ta ambaci sunanta"Sehrish,"
Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"
"Inason magana dake!dan Allah ki bani haɗin kai,kada ki bani kunya,inaso kizo ki buɗe mun ƙopar nan!,"
Miƙewa sehrish tayi,jikinta sai faman kerma yake yi,daƙyar ta iya sanya hannu ta buɗe kopar toilet ɗin,
Sauke ajiyar zuciya hajiya azeema tayi tare da mikewa tsaye tana kallonta,fuskar nan tayi suntum da ita,gaja gaja da hawaye,idanun sun kumbura,janbakin da ta shafa duk ya 6ata mata fuskarta,mascara ɗin da aka shafa mata asaman eye lashes ɗinta,duk ya jike sharkaf da hawayenta ya 6ata fuskar da baƙin,kayan jikinta ne kawai basu 6aci ba,
Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita daga gefen gadon nasu,itama ta zauna suna fuskantar juna,
"Haba amaryar babban yaya,kuka bana ki bane,Farin ciki ya kamata na gani akan fuskarki,"cike da zolaya hajiya azeema tayi mata maganar hada jan kumatunta,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shesshekar kuka tace"Am...amma..Aunty azeema..meyasa za'ayi mun haka?saboda me za'a ɗaura mun aure tare da babban yayanmu batare da an sanar dani ba?Nasan cewa sun isa dani!Amma yakamata ayi mun adalci,Auren wata uku fa?kawai saboda buƙatar kanshi"?
Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi cikin sanyin murya tace"Inaso na tambayeki wani abu,amsa ɗaya kawai nakeso ki bani,kuma ki faɗamun gaskiya,'
Dakatawa sehrish tayi da yin kukan tare da mayar da hankalinta kan Aunty azeema tana sauraronta,
"Inaso ki faɗamun gaskiya,Shin kina son Sgr ko bakya son shi ne"?
Shiru sehrish tayi yayin da idanunta ke akan yatsun hannunta da ta harɗesu wuri guda tana murzasu,
"Kinyi shiru baki ban amsa ba"?
ƙasa kasa tayi da muryarta tare da cewa"bazan 6oye maki ba Aunty azeema,ina son Yaya rafayet sosai,fiye da yadda nake son kaina,"
Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi,dama saida ranta ya bata cewar tana sonshi,
"In har dagaske kina son shi bai kamata kiyi kuka ba don an ɗaura maki aure dashi,"
"Aunty azeema ba baƙin ciki nake yi ba,bakomai ne ya 6ata mun rai ba fa ce irin auren da akayi mun dashi,Saboda kawai nayi aiki a ƙarƙashinshi,na tsawon wata uku?meyasa za'ayi mun haka?idan aka barni ma zan iya yin aiki a ƙarkashinshi ba sai ansa ya aure ni ba,ba bisa son ranshi ba,tunda ba sona yake yi ba,ni kaɗaice nake ɗawainiya da son shi tun kafin nasan wanene shi,Wahala kawai zansha a hannunshi,Ni ban ta6a son na aureshi ba batare da yana Sona ba,"
Jinjina kai hajiya azeema tayi tare da cewa"hakane kin faɗi gaskiya,ba'ayi maki adalci ba,Ni kaina bansan dalilin yin auren ba sai daga baya nake ji a wurin Abbanku,Amma kiyi haƙuri dan Allah kada hakan yasa ki bijire ma iyayenki,kiyi masu biyayya in sha Allah zaki ci ribar yin hakan,"
Batare da musu ba Sehrish tace'Shikenan,in sha Allah zanyi masu biyayya,kamar yadda kika ce,kuma koda baki faɗamun haka ba,Ni bazan yi kuskuren bijire masu ba,"
Murmushi hajiya azeema tayi tare da sanya hannunta ta shafa gefen fuskar sehrish,
"Good girl,Naji daɗi sosai da kika amince zakiyi masu biyayya,Ni kuma nayi maki alƙwarin cewa atare zamu yaƙi sgr,acikin waɗannan watannin guda uku kacal,Zamu canza mashi ra'ayinshi,don ya gane kuskurenshi,kinsan ance DUK ƘYAN TAKALMI ƘAFA CE KE TAKASHI,So nake ki take mun wannan tsadaddan takalmin da ƙafafun nan naki ya taku sosae,"
Sae lokacin Sehrish ta fashe da dariya,har hakoranta suka bayyana,maganar da hajiya azeema tayi mata ta ƙarshen nan ba ƙaramin dariya ta bata ba,
Cigaba da magana hajiya azeema tayi"domin aikin mu yayi kyau muna buƙatar mu shirya plan A da kuma plan b zuwa c,zamu fara jaraba plan A,idan har akaci nasara akan shi kinga basai mun buƙaci plan B ba,Abunda nakeso dake yanzu shine muna buƙatar satar amsa,kuma ke kaɗae ce zaki iya samo mana wannan satar amsar da muke buƙata a wurinshi,
A tsorace sehrish tace"Ni kuma!"hajiya azeema tace"kwarai kuwa,ba wani abun tashin hankali bane,just akwai bukatar musan me yake so da kuma abunda baya so don mu kiyayesu,Ni dae a iya sanina Sgr mutunne maison abi umarninshi ba'ayi mashi musu,yafi so ayi mashi biyayya abishi sau da ƙafa,sannan mutunne shi mai tsaftar gaske,ya tsani ƙazanta,bayan haka kuma Yana son abinci mai daɗi,shiyasa yake cin girkin azmee saboda tana da tsafta kuma ta iya girki,yakama ki koyi kalar girke girkenta,"
"Ae na fara koyo a wurinta,Kuma na iya waɗansu,amma zanyi mata magana akan ta ƙara koyamun wanda ban iyaba,"
"Yawwa haka nakeson ji,ki dage sosai,Nidae ta 6angarena zan baki gudummuwa sosai,""
Sun jima suna fira atsakinsu tamkar ba uwa da ƴa ba,har sae da aka fara kiran sallar Magrib,sannan aunty azeema tayi mata sallama,
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta samu ƙwarin guiwa sosai a wurin Hajiya azeema kuma taci alwashin zata ɗaura ɗamarar zama da sgr,har na tsawon wata ukun
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 12 na dare,tana a tsaye cikin ɗakinsu,sae faman zagaye zagaye takeyi,tana jiran dawowar Sgr,tun bayan sallar isha'e bai dawo cikin gidan ba,har lokacin wedding gown ɗince a jikinta,ta gyara kwalliyar fuskarta,sannan ta daure gashin kanta da ribbom,
Jahad da hosana sun jima da yin bacci ita kaɗae ta rage batayi bacci ba,zuciyarta cike take da damuwa,sam tagaza samun natsuwa babban abunda takeyi ma fargaba shine taya zata fara tunkarar SGR a matsayin Mijinta?shin zata iya jure zama dashi?tasan cewa dole ta fuskanci ƙalubale dayawa a wurinshi,
Tana cikin wannan zancen zucin taji shigowar motocinsu,ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa gefen gadonsu ta zauna tana jiran su ƙarasa shigowa cikin gidan,
Almost 30 mins,sannan ta miƙe tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito waje,babu kowa kai tsaye ta nufi kitchen,batare da 6ata lokaci ba,ta shirya mashi dinner ɗinshi a saman ƙayataccen tray ta ruƙo shi da hannayenta,a hankali take tafiya saboda tsinin takalman dake a ƙafafunta,bata saba tafiya da irinshi ba,babu kowa a main palour ɗin hakan yasa ta wuce upstairs part ɗinsa,
Da sallama abakinta tashiga falon,babu kowa aciki sae dae kamshin turaren nan nashi,kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi tayi,a bakin ƙopar ta tsaya tare da yin sallama"Assalamu alaikum"
"Who's there"abunda taji yace kenan,
daƙyar ta iya cewa"Ni ce"
"Okey,Come in"
A hankali ta zura ƙafarta cikin ɗakin nashi,samun shi tayin kwance asaman katafaren gadon nan nashi na mulki,ko takalman ƙafarshi bai cire ba,still shaddar ce ajikinshi,
Ƙarasa shiga ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table,kamar wata mara gaskiya ta juya zata kama hanyar fita daga ɗakin muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Baki iya gaisuwa bane?"
dakatawa tayi tare da ɗan juyo ta saci kallon fuskarshi,A lumshe ta samu idanunshi tamkar maijin bacci,
Muryarta na rawa tace"Ina yini"
Ta6e la66ansa yayi tare da cewa'zonan""
Jiki asanyaye ta tunkareshi,da hannu ya nuna mata gaban gadon nashi,sannan yace"kneel down"
Tattare rigar jikinta tayi,tare da zubewa saman guiwowinta,
"Kukan me kikeyi ɗazu?ko don saboda kinji abunda muke tattauna da Abba ne?"
Girgixa kai tayi'a'a ba haka bane,""
"Okey,"
Shiru ya ɗanyi na wani lokacin kafin yaci gaba da magana"Na aureki ne saboda inaso ki cigaba da aiki a ƙarƙashin ikona!Idan har bakya ra'ayin hakan zan iya sakin ki,"Ya ɗan dakata da yin maganar yana jiran jin amsarta,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina 08103884440❤_
Not edited,
"zan cigaba da aiki a ƙarƙashin ka,"ta ƙarasa maganar,tana faman sauke ajiyar zuciya,
"Good,"ya furta hakan tare da miƙe wa daga zaune,Ya jingina bayanshi a jikin pillow,har time ɗin idanuwanshi na a lumshe bai buɗesu ba,
"Now you are under my control, you must follow my rules,"dakatawa yayi da yin maganar,tare da kai hannu ya zaro hanky daga front pocket na rigar shaddar jikinshi,
Miƙa mata yayi tare da cewa"Oya,goge wannan fentin dake a saman lips ɗinki,from now bana buƙatar naga make up a face ɗinki,in dai zakiyi aiki a part ɗina,"
Hannu tasa ta kar6i hanky ɗin,tare da kaishi saman lips ɗinta,a hankali ta shiga goge jan bakin da tasha fa,
Cigaba da magana yayi"i won't restrict ur life,You still ave ur right,don na aure ki ba hakan yana nufin zaki ɗauki kanki as a married women ba,No just normally zakiyi rayuwarki,Kuma zaki iya kula duk wanda kikeso koda namiji ne i don't care about that,'
Zaro ido waje sehrish tayi tana kallon fuskarshi,cike da mamakin jin abunda yace mata,Lamarin sgr ya fara bata tsoro,sae ka ce ba musulmi ba!da aurenta kuma ya amince mata ta kula duk wanda takeso?Anya bai fara shaye shaye ba?kodai yana da Iska ne ajikinshi?Abun yayi confusing ɗinta sosai,
"Idan ma kina da tsafta ki ƙara akan wadda kike da ita,part ɗina ya kasance kullum a tsaftace ya ke,"
Kasa kunne sehrish tayi tana sauraron shi,guiwowinta har sun fara yi mata raɗaɗi,magana yake yi tamkar baisan motsa la66ansa,balle har yayi sauri ya kammala ko ta samu ta miƙe,
"Banason wani ya ƙara girkamin abincin da zanci,da hannunki zaki girka mun,sannan ba kowani kalar abinci nake ci ba,Ki nemi bayani a wurin Asmee,"
Dakatawa ya ɗanyi da maganar,hannu ya miƙa tare da ɗauko wayarshi dake ajiye saman side drawer ɗinshi,ya shiga daddanata,
Ganin haka yasa sehrish tayi sauri Zama dirshin a ƙasan,kota rage raɗaɗin da guiwarta keyi mata,
"Where's ur phone"?yayi tambayar tare da ɗan dakawata,da dannar wayar da yake yi,
Da sauri tace"na barta a bedroom ɗinmu,"
"Okey,"ya ambaci hakan tare da kai hannu ya buɗe drawer chest,memo ya ɗauko tare da biro,Ya buɗe empty page,a natse ya shiga yin rubutu asaman paper ɗin,.
Zugudum sehrish tayi,aranta tana tunanin ko taya zata iya gane hand writting ɗinshi?kwanakin baya,daya ta6a yi mata rubutu bata iya gane komai ya rubuta ba,har haroon ya yaudareta,
Bayan ya kammala rubutun,Yayi tearing paper ɗin tare da miƙa mata,hannu tasa ta kar6a,
"Phone number ɗina ne,Cos at anytime zan iya kiranki,even in the midnight indai ina buƙatar wani abu"
Amsa mashi tayi da toh,
"Your work will start from tomorrow!U can leave now,"
Jiki asanyaye sehrish ta miƙe dakyar take ɗangyasa ƙafarta tana tafiya,har sae da takai bakin ƙopar bedroom ɗin nashi sannan ta ɗan dakata da yin tafiyar,juyowa tayi tare da aza idonta akanshi,a lokacin harya sauko daga saman gadon,yana ƙokarin cire kayan jikinshi,da alama wanka zaiyi,
Gyaɗa kai kawai tayi tare da sanya ƙafa ta fito daga bedroom ɗin nashi,
Bata tashi jin hawaye ba,sae da ta hau saman staircase din,tana taka benen a hankali,bakomai yafi ƙona mata rai ba fa ce abunda ya ce mata,Zata iya kula duk wanda takeso koda Namiji ne shi bai damu ba,tsabar takaici kamar ta haɗiyi zuciyarta haka take ji,taci alwashin saita koya mashi hankali,kuma zata jajurce ne wurin ganin ta gudanar da aikinta kamar yadda yakeso,daga baya kuma ta shiga tunanin komai yasa ya hanata shiga part ɗinshi da makeup?mai jan bakinta yayi mashi ne da zaisa ta goge?da alama so yake ya dinga ganinta kamar gardi,shiyasa yayi mata hakan,
Ƙarasa saukowa tayi daga saman stairs din,sannan ta tsaya tare da juyawa tana kallon upstairs ɗin"
In sha Allah,Wata rana Sai kayi kneel down agabana,Kamar yadda ka saba sanya ni in duka agabanka,koda baka zubar da hawayenka ba,zakayi kukan zuciya ne wanda yafi ciwo,Wannan alwashine na ɗaukarma kaina,In har ban tabbatar da faruwar hakan ba,To ni ba jinin Abusufyan bace da abu!!kuma ban cika mace ba,"
Tana magana hawaye na shararowa akan fuskarta,ranta ya 6aci sosai
*ATAƘAICE*
Acikin waɗannan ƴan kwanakin Sehrish ba ƙaramin jiki taji ba,domin kuwa sgr baiyi mata da sauƙi,Aiki takeyi tuƙuru,ba ƙaramin ƙoƙari take yi ba wurin ganin ta kiyaye duk wani abu da zai haɗa ta dashi,Aranar monday abusufyan ya mayar dasu school,da kanshi yakaisu acikin motarshi,basu samu matsala ba,sae dai an wuce su abubuwa da dama,Domin kuwa suna dab da fara'a Exams,abubuwa duk sun haɗe mata,ko karatu takeyi hankalinta na akan agogo,don kada ta shiga lokacin aikinta batare da ta sani ba,tun da sanyin safiya take shiga part dinshi tunkafin ma ya tashi daga bacci,ta gyara mashi toilet ɗinshi da falonshi,bayan ya tashi daga bacci ya shiga wanka,ta zauna ta gyara bedroom ɗin nashi,Sannan ta shiga kitchen ta haɗa mashi breakfast ɗinshi,Mafi yawancin lokutta a makare take zuwa makaranta,Saboda aikin sgr,Sae yaga damar sallamarta tukunna,abun ba ƙaramin 6ata ma abusufyan rai yakeyi ba,sae daga baya ya dinga danasanin ƙulla auren yarjejeniyar da sukayi,kullum Shi yake ja masu yin late a school,saboda dole sai sun jira sehrish ta kammala aiki a part din sgr,sannan su wuce school,baiwar Allah suna dawowa daga school da zarar tayi sallah,ko abinci bata ci,indai sgr na a cikin gidan sae ta fara zuwa ta gyara mashi part ɗinshi ta kuma kai mashi lunch ɗinshi,ta kuma yi serving ɗinshi abincinshi har sai ya mula yasha iska tukunna ya sallame ta,sannan fa take samun damar cin abincinta,Cikin lokaci ƙankani sehrish ta soma fita hayyacinta,Duk ta rame,kullum ne sai ta farka tsakar dare,ta zauna tayi ta kuka ba wanda ya sani,ita kaɗae tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta,gashi in tayi kuskuren yi mashi laifi,Hukunta ta yakeyi da tsallan kwaɗi,babu wanda bai fara jin tausayinta ba acikin gidan,shiru kawai sukeyi,bakomai ne ya jawo mata hakan ba fa ce rashin Hajiya azeema domin kuwa tun sati daya da yin auren,Tabar ƙasar izuwa dubai inda tasaba yin harkokin kasuwancinta,Amma tayi mata alƙawarin cewa bazata wuce One month ba zata dawo nigeria saboda ita kawai,Duk da haka kullum sai sunyi waya da ita,kuma tana ƙara ƙarfafa mata guiwa,kullum tana kara tunasar da ita akan cewa Karta kuskura ta karaya tun yanzu,Taci gaba da hakuri wata rana sai labari,mahaƙurci mawadaci ne,Sannan ta dage da addu'a kuma taci gaba da kyautata mashi,sgr bai tsaya a iya nan ba,idan dare yayi dama wannan ƙa'ida ne saita kai mashi coffee da kayan marmari around 12,toh yanzu takai ga,sae tana bacci wuraren 1:30 na dare ko biyu,ringing ɗin wayarshi ke tashinta daga bacci,daga ta ɗaga zaice mata Coffeee,yana furta hakan zai katse kiran,Dolenta ne ta tashi takai mashi ga bacci a idanunta,duk in taje part dinsa a wannan lokacin zata same shi ne yana yin nafilfilin dare,ko kuma ta same shi bayan ya kammala yin sallar yana karatun alƙur'ani,a rana ta farko data fara ganinshi yana karatun kur'ani abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,Ita duk a tunaninta babu ilmin addini akanshi,Ashe kullum saiya tashi in midnight don yayi sallar dare da kuma karatun alƙur'ani,tun daga ranar da ta fara ganinshi yana yin sallar nan,itama sai ta koma yin sallar daren da karatun al'kur'nin,saboda su dinga samun ladar atare,tunda ya katse mata baccinta,
A 6angaren Amrish kuwa,Daƙyar haroon ya samu ta amince zata koma wurin Mommynta da zama,Da kanshi ya mayar da ita gidansu,Sannan ya gargaɗi mommynta akan ta kiyaye 6acin ranta,itama amrishi ɗin sai da yaja mata kunne akan karta ƙara yunkurin kashe kanta,da haka ya samu ya sasanta tsakaninsu,har ta koma school,Ranar da suka haɗu da sehrish a makaranta kamar zasu haɗiye junansu saboda tsabar farin ciki,sun sha kuka sosai,saboda sunyi kewar junansu,abun ba'a magana,
Soyayyar junaid da jahad kuwa kullum ƙara ninkuwa takeyi acikin zukatansu,sun shaƙu sosai koda yaushe suna manne da junansu,baya gajiya da ɗaukarta su fita shan ice cream,Junaid ya iya soyayya sosau,yaci sunanshi romeo,saboda ya iya caring,ga zumuɗi kamar sabon ango,A ƙagare yake da aɗaura mashi aure da jahad,Bawan Allah duk safiyar Allah sai yayi shiga ta mutunci yaje gaisar da Abusufyan,hakan ba ƙaramin daɗi yakeyi ma abusufyan ba,tun daga haka ya gane cewa junaid zai ruke mashi ƴarshi dakyau duk da ƙuruciyarshi,amma yana da hankali sosai,
A 6angaren Marshal Omar kuwa,Hosana ta tada mashi 6alli,saboda sehrish tayi aure ita bai aure ta ba,duk yadda yaso ya shawo kan hosana akan ta bashi lokaci amma yarinyar nan taƙi yarda,ƙarshe tace mashi in har baije anyi maganar aurensu ba,zata tona mashi asiri ne,gabanshi ya faɗi ya shiga tunanin wani asiri ne hosana take ikirarin zata tona mashi,koda ya matsa mata akan ta faɗa mashi abunda take 6oyewa,sae cewa tayi ae Ya ta6a yi mata fyaɗe hada nuna mashi Zoben diamond ɗinshi daya manta a ranar,kuma tace zata sanar dasu Abbansu ne,Hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,ƙoƙarin fahimtar da ita ya shiga yi akan cewa shi fa ba fyade yayi mata ba,kawai tsautsayine yasa yayi ƙoƙarin raping ɗinta a lokacin,daƙyar ya samu ya lallasheta,sannan ta haƙura,a hakan ma sai da yayi mata alƙawarin cewa za'a daura masu aure,
lokacin da Haroon Ya ji Auren Sehrish da sgr,tamkar zai zauce saboda tsabar tashin hankalin daya shiga,don shi dagaske son Sehrish yake yi,daga baya ne ya gano cewar Auren Nasu na wata uku ne,tunda yaji hakan sai hankalinshi ya kwanta,Kuma yaci alwashin cewa Sai ya samu soyayyar Sehrish,in ba haka ba sai yabi duk hanyar da zai bi wurin ganin ya biya bukatarshi da ita,don ya jima da kwaɗayin son kasancewa da ita,tashin hankali,
Wannan kenan
A ranar wata Juma'a ne,Allah yayi ma modibbo rasuwa,Mutuwarshi tayi matuƙar girgizasu gaba ɗayansu,Musaman Ammi kamar zata zauce don kuwa har suma saida tayi lokacin da saƙon mutuwar nashi ya isar masu,Rashin lafiya yayi na rana ɗaya kuma Allah ya kar6i abunshi,Sunji mutuwarnan kamar kamar me,Ashe babu rabon komawarshi saudiya,duk da yaci nasara akan abunda ya kawo shi nigeria ya haɗa kan zuri'arsu,ya ƙulla zumunci mai ƙarfi atsakaninsu,Allah ya jiƙan Modibbo,
Gaba ɗayansu suka shirya zuwa Damaturu domin halartar jana'izarshi,Banda su sehrish saboda Exams da sukeyi a school ta Second term,amma matasan gidan dukansu abbansu ya tattarasu sun tafi can,gidan ya rage daga Azmee sae su sehrish,baƙaramin daɗin tafiyar sgr sehrish taji ba,Duk da ranta na bata cewar daƙyar zai wuce 1 week bai dawo cikin gidan ba,ta dan samu hutu,Kullum daga taji dirar mota jiki na rawa zata je ta leƙa ta window taga wanene ya dawo,Fargabarta kar ace shine ya dawo,da zarar taga bashi bane,Daɗi take ji,duk da tayi kewar shi sosai,Ko bacci takeyi sai ta dinga jin muryarshi acikin kunnanta yana cewa"Oya kneel down" har mafarkinshi takeyi,❤
Yau Ya kasance wata ɗaya cuf da yin aurensu,batare da sgr ya soke yarjejeniyar ba,yanzu kwana biyar kenan da tafiyarsu Damaturu,dama abbansu yace sai sun zaga dangi,tunda sun jima basu je sun sada zumunci ba,
*Boss Bature*
❤🤍❤
Wuraren ƙarfe 3 na rana,sehrish na kwance saman gadonsu,tayi nisa acikin baccinta,baiwar Allah ba ƙaramar gajiya ta kwaso ba,Yau suka kammala Exams ɗinsu,tunda suka dawo daga school Ko Uniform ɗin jikinta bata samu ta cire ba,ga yunwa na cinta amma ahaka ta kwanta saboda baccin da take ji,
Jahad kuwa tana a garden suna video call da junaid,tun bayan da suka tafi,kullum ne saiya kirata video Call,idan suka fara wayar nan sai sunyi fiye da one hour suna magana,Idan da daddare ne kuwa ya kirata suna kaiwa har wurin asuba,basu runtsa ba,Soyayyarsu ba ƙaramin burge sehrish takeyi ba,wani sa'in sai taji dama itace take samun irin kulawar a wurin sgr,ɗan tahalikin nan tunda suka tafi kullum ne saita tura mashi Text message amma babu reply,bai ta6a mayar mata da amsa ba,kuma hakan baisa ta daina tura mashi ba,
Cikin bacci ta dinga jin jiniyar motoci acikin kunnanta,A firgice ta farka tana faman zare ido,tsoranta kada ace Sgr ne yadawo Cikin gidan,Sai da tadawo cikin hayyacinta sosai sannan ta gane cewa ashe wayarta ce ke ringing,Wata irin nauyayiyar ajiyar zuciya ta sauke,Hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman pillow,sae hamma takeyi saboda yunwar da take ji,duba screen ɗin wayar tayi,Sunan Daddy ne ya bayyana,Murmushi ta ɗan saki tare da answer kiran,ta kara wayar a kunnanta,
"Assalamu Alalikum daddy,"
Muryar abusufyance ta amsa mata da cewa"Wa'alaikum salam,Daughter ya kike?tun ɗazu inata jaraba kiran wayar jahad line busy,ke ma kuma na kira wayarki kusan sau biyu tana ringing ba'a ɗaga ba,dafatan kuna lafiya,"
"Bacci nakeyi ne shiyasa banga kiranka ba,Jahad kuma tunkafin na kwanta,ta sanar dani cewa junaid ya kirata,nasan yanzu haka dashi takeyin waya a garden,"
"Okey,hosana fa?tana ina ne?itama na kira layinta a switch off,"
"Daddy hosana fa,bata amfani da wayarta,tun ranar daka siya mana su bata ƙara bi takanta ba,tafi mayar da hankali akan laptop ɗinmu,yanzu haka ma kallo takeyi acikinta,"_
Abusufyan yace"Na kira ne dama don inji ya ku ke,"
Murmushi tayi kafin tace"Alhamdulillah daddy,muna lafiya,fatan kaima haka"?
.."ina lafiya nima,Ya Exams ɗin taku?kunyi abun kirki ko?
dariya ta ɗanyi tare da cewa"Yau dai muka kammala,Result muke jira yanzu,amma fa daddy kasan a ƙurarren lokaci muka koma school,duk an wuce mu a karatu,duk yadda kaga result ɗinmu kawai kayi shiru da bakinka,ka sanya mana albarka,"
Tana jiyo muryar abusufyan ta cikin wayar yana dariya,bayan ya tsagaita da yin dariyar yace"Oh,kina nufin cewa ba kuyi abun kirki ba ko?oh ni abusufyan kada ace ƴa'ƴana basu da ƙoƙari,"
"A'a daddy ae ba laifinmu bane,yakamata ayi mana uziri,saura fa two weeks a fara exam ka mayar damu school,"
Abusufyan yace"hakane kuma fa,baki tambayeni yaushe zan dawo ba?ko bakiyi missing ɗina bane"?
Muryarta da ƴar shagwa6a tace"I really missed u alot daddy,kamar na janyoka ta cikin wayar nan,inyi hugging ɗinki,"
Dariya yayi sosai kafin yace"this Week zamu dawo ae,zuwan bazata zanyi,kuma a washe garin ranar da nadawo zamuje kano,Zan ɗauki ɗaya daga cikin ku mu tafi kano,saboda inaso muje gidan makwabtan nan naku ya ma sunansu?
Da sauri tace"gidansu maman sadeeq"?
Yace"eh nan nake nufi,zamu je ne domin munyi bincike akan mahaifiyarku,Nasan zamu samu ƙarin bayani a wurinsu,"
Wani irin farin cikine ya bayyana akan fuskar sehrish,fuskarta dauke da murmushi tace"daddy inaso dan Allah ku tafi tare dani mana,"
"Kina tunanin cewa Babban yayanku zai bari na tafi tare dake ne"?
Shiru tayi tuni idanunta sun ciko da kwalla,muryarta tamkar zatayi kuka tace"Amma daddy,ni ya kamata a tafi tare dani,saboda zanfi gane kwantancen gidan nasu,"
"Shikenan idan har kinason mu tafi tare dake,toh ki fara sanar da babban yayanku,idan har ya amince zamu tafi atare,in kuwa ya hanaki zuwa sai dai ki haƙura mu tafi tare da Jahad,"
Jikinta ne yayi sanyi harma ta fidda rai don kuwa tasan cewa Daƙyar ne sgr ya barta ta tafi kano,
Cikin sanyin murya tace"Shikenan daddy,zan jaraba tambayarshi idan ya dawo,Allah yasa yabarni,wlh dana ji sosai,"
Sun jima suna waya dashi kafin sukayi sallama,ajiye wayar tayi asaman side drawer,sannan ta sauko daga saman gadon,direct ta wuce toilet domin yin wanka,within mins ta fito jikinta sanye da bathrobe,ta saki gashin kanta a bayanta,yanzu tsayinshi yakai har mid back ɗinta,
Gaban mirror ta tsaya,tare da ruƙe qugunta,bakowa bane ya faɗo mata a ranta ba fa ce Sgr,a duk lokacin daya sanya bathrobe ɗinshi ba ƙaramin kyau rigar take yi mashi ba,yadda kasan donshi akayi rigar,
Hannu tasa tare da janyo gashin kan nata,ta dawo dashi ta gabanta,tana kwaikwayon yadda sgr yakeyi in ya fito daga wanka,ta daure fuskarta kamar yadda yake tamke fuskarshi,a ƙarshe ta fashe da dariya,
Tana cikin rahar nan,hosana ta turo ƙopar ɗakin nasu,Ta cikin mirror take hangenta,Hannunta na ruke da system ɗinsu,jikinta na sanye da doguwar riga ta material,
"Sehrish ga lunch ɗinki can a dining,Aunty azmee ta ce idan kin gama baccin lalacin naki kije ki ci,"
Ta ƙarasa maganar a yayin da take zama daga gefen gadon nasu,
Juyowa sehrish tayi tare da kallon hosana tace"daddy ya kira wayarki a switch off,wai ina kike ajiye ta ne"?
Yatsina fuska hosana tayi kafin tace"Oho,nima bansan inda take ba,nemanta na keyi ruwa ajallo,dan Allah ki tayani nemanta,inaso in kira Ya Omar,nayi nayi da jahad ta kira munshi amma taƙiya,dama kece mai ɗan mutuncin,"
Harara sehrish ta watsa mata tare da cewa"Sai yau kikasan da haka?bayan kinsaba cewa nafi kowa tsiwa,bayan duk acikinmu ni ce innocent,"
Marairaice mata fuska hosana tayi,"pls rishi komai ya wuce,dan Allah ki bani aron wayarki yanzu dai in kira Ya omar,2 days banji Voice ɗinshi ba,Ni fushi nakeyi dashi ma,ko ya kira yaji ya nake,amma bai kira ba,"rai a6ace tayi maganar,
"Kada ki isheni da surutu,don nasanki bakya gajiya,ga wayar nan ki ɗauka,salon ki cinyemun katina,"
Cike da zumuɗi hosana ta ajiye system ɗin asaman gadon,sannan ta ɗauki wayar da sauri ta fuce daga ɗakin,
Gaban wardrobe ta koma tare da buɗewa,tana neman kayan da zata sanya,shirt ce ta ɗauko off shoulder Ash colour tare da dogon wandon Jeans,batare da 6ata lokaci ba ta zura kayan ajikinta,bayan ta kammala sanya kayan ta koma gaban mirror, tana shafa powder,sannan ta ɗan shafa lip gloss,murza la66an tayi,tana cikin sharce sumar kanta,Jahad ta turo ƙopar ɗakin,
Hannunta ruƙe da wayarta,fuskar nan awashe sae faman sakin murmushi take yi,
Juyowa sehrish tayi tare da kallonta tace"Sai yanzu kika kammala shan Love ɗin?Ni wannan soyayyarta ku tana ɗaure mun kai wlh,ko gajiya bakuyi,yadda kasan Romeo da juliet,kullum kuna a manne da juna,"
Jahad tace"da alama baƙin ciki kikeyi mun Allah,"
"In rasa dawa zanyi baƙin ciki sae dake?kin manta wa nake aure?Ni fa matar Surgeon general ce,ke fa?Ni har kunya ma nake ji,ki rasa dawa zakiyi soyayya sae wannan shagwa6a66an..."
Tunkan takai ƙarshen maganar jahad tace"Auren da yanzu saura 2 month ya mutu!dashi har kike tutiya,"
Gaban sehrish ne ya faɗi rasss!lokaci guda jikinta yayi wani irin sanyi,yayin da idanunta suka ciko tab da kwalla,
Ita kanta jahad,bataso ta faɗi hakan ba,ranta ne ya 6aci saboda ta tsani a kushe mata baby Junaid ɗinta,Wannan ne yasa har ta faɗi maganar da tayi,
"Jahad!ni kike faɗa ma haka"?
Da sauri jahad tace"dan Allah kiyi haƙuri,wlh bansan na faɗi hakan ba,raina ne ya ɗan sosu,"
"Kinayi mun fatan aurena ya mutu kenan"? Tayi tambayar hankalinta aɗan tashe
"Dan Allah rishi kidaina faɗin wannan maganar,nace maki ba a son raina na faɗi hakan ba,"tayi maganar tare da ƙarasawa wurin sehrish ɗin,ta ruƙo hannunta,
"Pls kada ki bari hawayen nan sun fito daga cikin idanunki,kinsan cewa bazan ta6a yi maki fatan aurenki ya mutu ba,kuma wlh ban faɗi hakan ba donna 6ata maki rai ba," fuskar jahad tamkar zatayi kuka saboda tausayin sehrish,
Tuni hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace"kin faɗi gaskiya jahad,bai kamata inyi prouding da aurenshi ba,Ni sam na manta ashe yau saura 2 month babban yaya ya sake ni,ni nama ƙosa ya sake ni in huta,'
Hannu jahad tasanya tana share mata hawayenta"in sha Allah Babban yaya bazai ta6a sakin ki ba,banayi maku fatan rabuwa da junanku,Nafison ku kasance atare na har abada,Daso samu ne kawai wani abu ya shiga atsakaninku,Ana saura sati daya auren ya mutu,aga kina amai kinga shikenan babu zancen saki,Sae dai a fara tanadin suna,"cike da zolaya jahad tayi maganar,aikuwa nan take sehrish ta fashe da dariya,
Ganin tafara dariya yasa jahad taci gaba da tsokanarta"gaskiya naƙosa in ganki da ciki,cikin ma na babban yayanmu,Wayyo Allah na bansan wani irin farin ciki zanyi ba aranar,zanso naga babynku,wlh ba ƙaramin kyau zaiyi ba,idan ya biyo kowannanku,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Najima ina burin wannan ranar,bazan 6oye maki ba jahad,inaso inga nima na haifi ɗan babbyna,Amma nasan ba yanzu ba,"
"Dont worry ur self,Very soon zaki haifa ma babban yayanmu twins ko triplet,tunda muma triplet ne,nasan acikinmu baza'a rasa wadda zata haifi ƴan biyu ba ko ƴan uku,"Acewar jahad,
Shiru sehrish ta ɗanyi tana murmushi,duk da tasan abune mai wuya amma taji daɗin maganar nan ta jahad,
"Inaso naje naci abinci,yunwa nake ji,"
Ta ƙarasa maganar tare da kama hanyar fita daga ɗakin,Bin bayanta jahad tayi da sauri tare da ruƙo hannunta cikin nata,
"Mu tafi atare,nima ae banci abincin ba,"
Dining suka nufa,Wuri suka samu asaman dining chairs ɗin kowa ya zauna,Tray ne mai faɗi azmee ta ajiye masu asaman dining ɗin,Warmers ne guda biyu babba da ƙarama ta miya ajiye asaman shi tare da plate,sae drinks data ɗauko masu,
Da yake mutanen gidan duk basu nan shiyasa bata girka abinci dayawa ba kamar yadda ta saba,ita kanta ta ɗan samu hutu yanzu,
"Munyi waya da daddy,"sehrish ce tayi maganar a yayin da take ƙoƙarin buɗe warmer ɗin,
"Ya faɗa maki ranar da zasu dawo ne"?_
"A'a bai faɗamun ba,sai dai yayi mun albishir mai daɗi,"
Cike da zumuɗi jahad tace"Wani albishir kenan"?
Murmushi ta ɗanyi a lokacin ta kammala buɗe warmer ɗin,wainar shinkafa ce acikinta,
"Ya sanar dani cewa da zarar sun dawo daga damaturu,A washe garin ranar zasu tafi kano,wurin nemo oumman mu,"
Maimakon taga farin ciki akan fuskar jahad,sai taga idanunta sun ɗan ciko daa kwalla,
"Meyasa bakya farin ciki ne"?
"Sehrish farin ciki fa kika ce?Bana Farin ciki,Idan har kika ga nayi farin ciki,toh An samu oummaan mu ne da ranta kuma da lafiyarta,ina fargabar abunda zaibiyo baya,idan suka je nemanta,Kinsan yadda oumman mu take tsananin son mu sosai,Amma lokaci guda aka nemeta aka rasa,tsorona kada ace ya sayyadi ne yayi mata wani abun,dama yasha faɗin cewa zai kashe ta idan har bata daina bin ƙwaƙƙwafin da takeyi mashi ba....."dakatawa jahad tayi da yin maganar,jikinsu duk yayi sanyi,
"Addu'a yakamata muyi mata akan Allah yasa su samota,Amma nikaina ina fargabar a wani hali zasu same ta,"
Duk sunsha jinin jikinsu,zuba masu wainar tayi acikin plate,sannan ta buɗe ƙaramar warmer ɗin,Miyar ganye ce,taji ganda lu6u lu6u acikin,Tuni ƙamshinta ya gauraye wurin,
Daƙyar suke iya cin abincin,kamar waɗanda akayi ma dole suci,
*HAROON*
Fitowarshi kenan daga cikin bedroom ɗinshi,yana ƙokarin barin wurin,Yaji an ambaci sunanshi"Haroon"!gabanshi ne ya fadi,duk a tunaninshi Amrish ce ta kuma biyo shi,da sauri ya juya don yaga wacece,tun daga ƙasa har sama ya soma binta da kallo,Jikinta na sanye da atampa,riga da skirt ne sun matseta sosai,gaba ɗaya surar jikinta ta fito ɗass,bakowa bace wannan fa ce Hayaam,fitowarta kenan daga ɗakinsu na hotel da Omar ya kama masu,Ashe tun ranar basu tafi ba,Zama suka cigaba dayi acikinshi sun ƙara biyan kuɗin ɗakin,don aunty babba taci alwashin cewa babu inda zasu tafi,daga abuja sai Enugu wurin bokan nan,Yanzu haka kuɗi suke harhaɗawa,duk ta siyar da gold ɗinta,yanzu ma shirye shiryen tafiya sukeyi,
Sakin baki haroon yayi yana kallonta,da wata irin kasalalliyar Murya yace"Ke!me kikeyi anan"!?
Cike da kwarkwasa Hayaam ta ƙarasa gabanshi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Kayi mamakin ganina ne?nikaina bansan da zamanka anan ba,yanzu kawai ina fitowa na ganka,kana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinka,"
Lokaci guda haroon ya saki wannan shu'umin murmushin nashi,a wayance yace"Amma nadaina ganinki a gidanmu,nayi tsammanin cewa kin koma gidanku ne?but me kikeyi acikin hotel ɗin nan"?
Shiru ta danyi tana tunanin abunda zata faɗa mashi,
Shi kuwa gogan gaba daya ya aza kwartayen idanuwan nan nashi akan Ƙirjinta,
"Naji kin yi shiru,idan ba damuwa mu shiga daga ciki mana,"yayi maganar yana nuna mata ƙopar daƙinshi,
Gaba yayi tabi bayanshi,buɗe masu ɗakin yayi suka shiga ciki,
A gefen gadonshi suka zauna,suna fuskantar juna,
"Kinyi kyau sosai,"yayi maganar yana wasa da harshen shi asaman la66ansa,
Murmushi hayaam tayi,batare da tace mashi komai ba,
"Ko kina buƙatar abunsha ne kona ci haka insa akawo maki"?
Girgiza kai tayi"a'a,a ƙoshe nake,bana jin yunwa,
ta6e bakinsa ya ɗanyi,kafin ya kuma cewa"Ƙamshin turarenki yayi mun,"
Dariya tayi tare da cewa"Allah ko"?
"Da zaki bani dama ko sau ɗaya ne,just inaso in ɗan shaƙi ƙamshinne a hancina,"
Batasan wanene haroon ba,saboda tasan halayen matasan gidansu,tayi tunanin cewa shima duk irinsu ne,hakan yasa tace mashi"Mezai hana,"
Matsawa yayi kusa da ita,tare da kai hancinshi saman fatar ƙirjinta,yana ɗan shinshinar ƙamshin turaren,nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,zagayawa yayi da hannunshi ta bayan rigarta,abu kamar wasa,ya zuge zeep ɗin rigarta a hankali,saboda tafara fita hayyacinta,
ɗagowa yayi da hancinshi izuwa saman wuyanta kamar wani maye,haka ya shiga shinshina wuyan nata,da wata irin kasalalliyar murya yace,"Wannan turaren na wani company ne"
Shiru tayi batare da ta bashi amsar tambayarshi ba,dama da biyu yayi mata maganar don yaji idan har lokacin tana acikin hayyacinta,Shirun da tayi mashi ne ya tabbatar mashi da cewar,tafara fita hayyacinta,
Bata ankara ba,taji hannunshi ta cikin rigarta saman boobs ɗinta,A zabure ta kwace kanta daga jikinshi tare da ja da baya,tana ƙokarin gyara rigarta,ɗagowa tayi tana kallonshi,Murmushi ta gani akan fuskarshi,
Hakan ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ma,duk a tunaninta mutumin kirki ne shi ashe shima ɗan harka ne,
Miƙewa tayi da sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin,Hannu tasa ta ruƙo kopar zata buɗe,taji ƙopar adatse,hakan yasa tayi saurin juyawa tare da kallonshi,Nuna mata key ɗin yayi a hannunshi yana dariya,
Fuskarta aɗan ɗaure tace"pls,ka buɗe mun kopa inaso na tafi,Aunty laila na jirana,"
Mikewa haroon yayi tare da takawa izuwa gabanta ya tsaya,sannan yace"Ganinki da nayi gaba daya kin tayarmun da sha'awata,na kwaɗaitu da son kasancewa tare dake,kallo ɗaya da nayi maki na gane cewa ke ba ƙaramar ƴar bariki bace,Don haka kada ki 6oye mun true colour ɗinki,kizo kawai muyi harka,"
Zuba mashi ido tayi tana tunanin ta wata hanya zata 6ullowa haroon don ta samu ta tsere mashi,bakomai take ji ma tsoro ba fa ce aunty babba,saboda ta hanata kula maza,'
"Koda ace ina kula maza,bazan kula irinka ba,Kuma ni ba ƴar iska bace kamar yadda kake tsammani,Ka buɗe mun kopa in fita,in ba haka ba zanyi maka illa,"a tsiwace tayi maganar hada rufe idanunta,
Dariya haroon yayi tare da sanya hannushi ya ɗaga wandon jikinshi,ya tura key din acikinsa,sannan yace mata"Zoki ɗauki key din idan kin isa,ƙaramar ƴar tasha kafin kiyimun illa ni zan illata ki idan har baki taimaki kanki ba"
Tsabar takaici ne ya cika hayaam,tayi danasanin yi mashi magana,da duk hakan bata faru ba,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina pls banda phone call just message ta whatsapp,08103884440❤_
*Aunty Babba*
Guntun tsoki taja,yayin da idanunta ke kallon agogon dake manne acikin ɗakin,kusan ƙarfe 6 na marece babu hayaam babu alamarta,har ta fara gajiya da jiranta,tun ɗazu take traying numbar wayarta amma Still Switch off,hakan ba ƙaramin 6ata mata rai yayi ba,tunani tashiga yi ko ina ta shiga?daga zuwa curo kuɗi a banki shiru kake ji wai malam yaci shirwa,
Ruƙe qugu tayi tare da yin ƙwafa,ta koma gefen gadon ta zauna,tana jiran shigowarta,tuntana sa ran dawowarta harta fara fidda rai,lokaci sai gudu yake yi har wurin ƙarfe 7,hayaam bata dawo ba,duk tana azaune har 8 ta buga,
"Allah yasa ba gantalin nata ta tafi ba,daga zuwa curo kuɗi a banki kamar na aiketa wata uwa duniya,tabi duk ta rufe layinta,Mtsww"ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki,
Yayin da aunty babba ke zaman jiran hayaam,ita kuma tana can rai hannun Allah a ɗakin haroon,Lokacin daya hanata fita daga ɗakin ya zura key a wondonshi yace ta taimaki kanta,tayi tsammanin cewa zata iya kwatar kanta saboda tasa ba gara sofwan saurayinta,hakan yasa cikin salon wayau ta zura hannunta acikin jakarta,batare da ya ankare ba,Ta curo kwalbar turare ta fesa mashi asaman fuskarshi,kai tsaye ya ta6a idanuwanshi,raɗaɗi yasa yayi saurin kai hannu yana murza idanun nashi,ganin ya fita hayyacinshi yasa tayi ƙoƙarin zura hannunta acikin wandonshi,aikuwa batayi wani aune ba yayi mata ƙwaƙƙwarar damƙa,Ya yayyaga kayan jikinta da hannunshi,tundaga tsaye ya fara biyan buƙatarshi da ita,cikin rashin imani haroon yayi mata kaca kaca,Karshe yayi wurgi da ita saman gadonshi,Ya tu6e kayan jikinshi kamar yadda ya cire nata gaba ɗaya,sannan yabi ya danneta kamar wani bakure haka yakai mata Hari,wa'iyazubillah duk yadda taso ta ƙwaci kanta amma hakan ya faskara,Tun tana ihu tana kuka har bakinta ya mutu ƙarshe ta sume....."
*Boss Bature*
❤🤍❤
*SEHRISH*
Wuraren ƙarfe 10 na dare,tana a kwance saman gadonsu,ta ƙudundune cikin bargo,bacci harya fara ɗaukarta,tajiyo ringing ɗin wayarta,a hankali ta zame bargon tare da miƙa hannu ta dauki wayar dake ajiye saman mattress din,daƙyar ta iya buɗe idanunta masu ɗauke da bacci,ƙurawa screen ɗin ido tayi yayin ta zuciyarta ke bugawa,Sunan My Boss Man ne ya bayyana da manyan haruffa,Gabanta ne yayi wani irin bugu rass!lokaci guda ta miƙe daga zaune tana faman zare ido,hannayenta har kerma sukeyi,Amsa kiran tayi tare da kara wayar a kunnata,Tunkafin tayi sallama Sexy voice ɗinshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Am back,"yana faɗin hakan yayi rejecting call ɗin,
Yadda kasan gunki haka sehrish tayi kasaƙai,fuskarnan tamkar ta fashe da kuka,ɗan hutun da ta samu na kwana biyu ya ƙare,
Jiki asanyaye ta sauko daga saman gadon bayan tayi wurgi da wayar saman mattress ɗin,Sleeping dress ne ajikinta white colour masu ɗige ɗigen baƙi ajikinsu,sunyi matuƙar yi mata kyau,Riga da wando ne,
Kaitsaye ta nufi wurin windown don ta leƙa taga idan dagaske ya dawo din,hannu tasa ta janye labulen tare da zuqe glass ɗinta,
daga inda take ta hango motorshi a parkin space,wannan ya tabbatar mata da cewar ya dawo yana a cikin gidan,hannu tasa tare da dafe goshinta a hankali ta furta"OMG!"
Gyaɗa kawai tayi tare da cewa"Ae shikenan,Za'a koma ƴar gidan jiya kenan,
Juyawa tayi ta nufi shoe rock ɗinsu,flat shoe ta ɗauko ta zura a ƙafafunta,sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin,buɗe kopar ɗakin tayi bayan ta fita ta datse ɗakin,
Fitowa tayi daga corridor din ta wuce kitchen,gidan tsit babu kowa,duk babu daɗi,tayi kewarsu sosai,musamman ɗan baby junaid ɗinsu,
Batasan ko zai buƙaci abinci ba,tun da yanzu ya dawo,Hakan yasa ta hado mashi Coffee kawai don tasan dole ya bukace shi,a cikin plate ta aza cup ɗin,ta fito daga kitchen ɗin,ta nufi upstairs,tunani tashiga yi ko ina su jahad suke,yanzu haka suna a ɗakin aunty azmee dama kwana biyun nan,duk in dare yayi suna zuwa fira ɗakinta,wani lokacin acan bacci yake ɗaukarsu,sae wurin asuba suke dawowa dakinsu,
A hankali take taka staircase ɗin harta haura sama,wuce wa part ɗinshi tayi,a baƙin kopar shiga falon ta tsaya,kamar yadda tasa ba,sae da fara karanta addu'o'in neman tsari daga sharrinshi sannan ta shiga ciki da sallama abakinta,
Babu kowa acikin falon,bedroom dinshi ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar,sallama tayi mashi,daga ciki taji ya amsa mata,tare da bata Iznin shiga,
Shiga cikin ɗakin tayi cike da fargabar ganin fuskarshi,agaban mirror ta same shi tsaye,yana sanye da bathrobe,jikinshi da alamun danshin ruwan da yayi wanka,bata samu damar ganin fuskarshi ba saboda ya juya mata baya,
Ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi coffee ɗin saman table sannan tace"Sannu da dawowa babban yaya ya gajiyar tafiya"?
Tamkar bazai amsa mata ba,har sai da ta fidda rai da zaiyi mata magana sannan yace"Am ok,"ɗaya daga cikin abunda ke ƙona mata rai kenan,Saita saki baki tayi mashi magana mai tsayi ya bata amsa in short,
"Ga coffee nan,bansan ko zaka buƙaci wani abu ba,bayan wannan,"
"No,need,"ya ambaci hakan tare da juyowa ya koma daga gefen gadon ya zauna,tsayawa tayi saboda tasan halinshi,in har bashi ya sallameta ba,toh bata isa ta tafi ba,
Ɗagowa tayi ahankali ta saci kallon fuskarshi,yayi haske sosai la66an nan nashi sunyi pink tamkar ya shafa jan baki,ya ɗaure fuskar tamau kamar wanda aka aiko ma saƙon mutuwa,
Mayar da idanuwanta tayi akan fatar ƙirjinshi,ganin yana ƙokarin dagowa yasa tayi saurin kawar da idonta gefe guda,
Hannu yasa tare da daukar Cup of coffee din,sae faman tiririn zafi yake yi,saitin bakinsa yakai cup ɗin a hankali yake kur6arshi,
ɗan dakatawa yayi da shan coffee ɗin batare da ya ɗago ya kalleta ba yace"Ɗaukomin sleeping dress ɗin da zan sanya,"
Amsa mashi tayi da toh,Sannan ta juya,kamar ance ya ɗago idonshi karaf ya sauka akan Wandon jikinta,ɗigon jinin daya gani ne yasa shi yin wurgi da Cup ɗin hannunshi ya faɗi ƙasa ya fashe,wani irin tashin zuciya ne yazo mashi,da gudun gaske ya mike tare da tunkarar toilet ya faɗa ciki,
Hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,batasan meyasa shi jin amai ba,ita dae kawai taga yayi wurgi da cup kuma ya nufi toilet,tuni tasha jinin jikinta,tsananin tsoro ne ya bayyana kan fuskarta,tunkafin ma taji meyasa shi yin amai,
Gaban Basin ya tsaya,sae faman kakarin amai yakeyi,tamakar ƴan hanjin Cikinshi zasu fito waje,Wani irin ƙyanƙyami ne dashi,gaba ɗaya duk yabi ya burkice,almost 8 mins yana acikin toilet ɗin,tanajiyo sautin aman da yake yi,zugudum tayi tana jiran fitowarshi,
Hannu yasa tare da buɗe ƙopar toilet ɗin ya fito,jikinshi sae kerma yake yi saboda tsabar 6acin rai,idanuwanshi har sun canza launi,
A zafafe ya tunkareta,ganin haka yasa sehrish tashi ga ƙoƙarin ja da baya,tana ƙoƙarin guduwa daga bedroom ɗin nashi, damƙo wuyan rigar jikinta yayi,tare da janyota yayi wurgi da ita,ta bugi bangon ɗakin,
Raɗaɗin da taji ne yasa ta fashe da matsanancin kuka,ware hannayensa yayi da nufin ya mare ta,runtse idanuwanta tayi da sauri tana kuka,
Yarfar da hannun yayi gefe guda,tsabar 6acin rai ya hana ya buɗe baki yayi mata magana balle har tasan laifin data aikata mashi,cikin shesshekar kuka tace"Dan Allah kayi haƙuri bansan laifin dana aikata maka ba,"
Tamkar ya rufe ta bugu haka yake ji,daƙyar ya iya buɗe baki yace"karki kuskura ki ƙara shigomin part ɗina da wannan ƙazantar a jikinki!ki tsaya har saikin kammala"
a ruɗe sehrish tashiga tunanin wata ƙazanta ce yake magana akai,da sauri ta shiga bin jikinta da kallo,a ƙoƙarinta nata gano abunda ya kira da ƙazanta,
. hakan ba ƙaramin fusata shi yayi ba,a fusace ya buga mata tsawa wadda tayi matuƙar girgizata,ta zaburar da ita kuma ta tsoratar da ita,Nan take taji zubar jini acan under ɗinta,tare da matsanancin ciwon mara lokaci guda ya farmata,Sae lokacin ta gane cewa period ɗinta ne yazo mata,jinin ne ya fara zuwa shiyasa batayi noticing ɗinshi ba,sae daga baya raɗaɗin ciwon ya taso mata,
Dogon tsoki yaja,tare da juyawa ya nufi cikin ɗakin,
Sehrish kuwa tuni ta soma fita hayyacinta,idanuwanta sunyi jawur da su,kamar daga sama yaji tace"AMMA BAKA DA IMANI"_
gabanshi ne ya faɗi rass,dakatawa yayi da yin tafiyar tamkar antokare shi,
"Tunda nake arayuwata banta6a ganin mutun mara imani mara tausayi ba irinka!Jinin daka gani ajikina lalura ce bani na ɗaurama kaina ba,nikaina bansan dashi ba,da bazan bari ya zuba ajikin kayana ba balle har ka gani,duk irin ƙoƙarin da nakeyi wurin ganin na faranta maka rai baka ta6a gani ba,Nifa ba tsoranka nake ji ba!Allah kaɗae nake tsoro,Idan taƙamarka ƙarfi kazo ka buge ni,kaga in zan mutu,Na rayu da wanda yafi ka rashin Imani da tausayi,Kuma na jure zama dashi,naga tashin hankalin daya fi wanda nagani a wurinka,kuma duk na jure hakan....."
Tashin hankali,Sanƙamewa sgr yayi atsaye,hankalinshi yayi matuƙar tashi,a arazane ya juyo don ya tabbatarwa kanshi da abunda kunnuwanshi ke juyo mashi,Jikinshi sae faman tsuma yakeyi,abun yayi matuƙar girgizashi,abun Yayi mugu mugun ɗaure mashi rai,Zuba mata ido yayi yana kallonta cike da mamaki,
"Dame ka ke taƙama ne?kaifa mutunne ɗan adam,mai hannu biyu mai ƙafa biyu,hancin ɗaya,da baki ɗaya,idanuwa guda biyu kamar nawa,Wanda idan yayi bacci sai yarda akayi dashi,idan ya mutu kuwa duk kyanshi duk mun dukiyarshi duk ji dakanshi acikin farin yadi mafi arha za'ayi mashi sutura,ƙarshe ya zama abincin tsutsa,"
Waro ido waje sgr yayi hankali atashe yake kallonta,tunda yake arayuwarshi wata ƴa mace bata ta6a tsayawa agabanshi ba,kamar haka tana gaya mashi magana,Ido cikin ido batare da jin shakkarshi ba,yadda kasan mai iskokai haka sehrish ta rufe shi da faɗa,abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,har ya fara tunanin kodae Tasha ƙwaya ne?to ae ko wanda yasha ya bugi da giya bai ta6a kallon cikin idonshi ba ya gaya mashi magana,
"Burin ka kawai ka wulaƙanta rayuwata,shiyasa ka aure ni don in cigaba da aiki a ƙarƙashinka,Inayi maka biyayya ne ba don inajin tsoranka ba,kaima ka sani,ni ba baiwarka bace baiwar Allah ce,Kuma idan yau naga dama zan iya barin gidan nan,kuma baka isa ka dawo dani ba,dana so tuntuni wlh dana tafi nabar gidan nan,Ƴanci nane,"
.. Tana magana hawaye na shararowa asaman fuskarta,with confidence takeyin maganar,batare data girgixa ba,
"Zan tafi kuma kada kayi tunanin cewa idan na kammala ƙazantar zan dawo part ɗinka da sunan aiki,Bazan ƙara zuwa ba,kuma kada kayi tunanin cewa zanji tsoranka in gudu daga gidan nan ko inzo in baka haƙuri,Wlh bazan ta6a karaya ba,ka yi duk abunda kaga dama,ƙarshe kace zaka hukuntani ko,Idan ka tashi dan Allah kada kabarni da raina,ka kashe ni,"
Ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki,a fusace ta juya tabar cikin bedroom ɗin nashi,
Sai lokacin sgr ya runtse idanunshi,la66ansa sae kerma sukeyi kaf kaf,saboda tsabar 6acin rai,Hannunshi ya cusa acikin sumar kanshi ya shiga cakuɗata,gaba ɗaya ya hargitsar da gashin kan nashi,Cizon la66ansa ya shiga yi,nan take le6en ya fashe jini ya soma ɗiɗɗigowa daga jikinsu,Zuciyarshi har wani boiling take tana burning,wani irin zafi ne ya taso mashi gadan gadan,jiri ya dinga gani acikin idanunshi harya fara tangal tangal zai faɗi ƙasa,
Daƙyar ya iya takawa izuwa gafen gadonshi ya zube ƙasa saman guiwowinshi tare da aza kanshi saman gadon,Tashin hankali Ran manya ya 6aci sosai,ƙoƙari yakeyi ya dakatar da bad temper ɗinshi saboda gudun karya aikata kisan kai,don muddin yakai matakin ƙarshe zaibi bayanta ne kuma sai yayi mata mummunar illa,
A hankali ya shiga furta"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un"!ya ambaci hakan kusan sau talatin,
Sehrish kuwa bayan ta fita daga part ɗinshi,daƙyar take ɗaga ƙafafunta saboda matsanancin ciwon marar da takeyi,Gaba ɗaya duk wannan maganganun da ta gaya ma Sgr ba'a cikin hayyacinta tayi su ba,batasan ma ta furta mashi su ba,Zafin raɗaɗin ciwo ne yasa ta zazzaga mashi masifa,dama kuma a ƙule take dashi saboda ya ƙuntata mata sosai,kuma ya kira jinin da takeyi da ƙazanta abun yayi matuƙar ƙona mata rai,hada ƙarin hakan yasa ta balbaleshi da faɗa,
Tun tana tafiya da ƙafafunta har suka gaza ɗaukarta,ƙarshe a bakin shiga corridor ɗin ɗakinsu,ta yanke jiki ta faɗi ƙasa saman tiles tana birgima,hannunta dafe da mararta,gashi babu wani a kusa balle ya kawo mata agaji,
Kamar yadda sehrish ta kwana waje saman tiles,haka sgr ya kwana zuƙunne saman guiwowinsa,kanshi na asaman gadonshi,Aranar bai runtsa ba,bacci ya ƙauracewa idanuwanshi,
Wuraren sallar asuba,Jahad ta fito daga ɗakin azmee tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinsu,idonta suka sauka akan sehrish dake kwance a ƙasa,gashin kanta duk ya rufe fuskarta,da ƙarfi ta ambaci Sunanta SEHRISH,da gudun gaske ta ƙarasa tare da zubewa saman guiwowinta agaban sehrish ɗin,
"Innalallahi'wa'innalairrahiji un,Sehrish!meya faru dake ne!nashiga uku!Aunty Azmee!!!"duk tabi ta ruɗe,musamman data ga jini ya 6ata wandon sehrish ɗin,sai tayi tsammanin kodai taji wani mummunan rauni ne,Jijjiga jikinta tashiga yi tana cigaba da kwalama Azmee kira,
"Aunty azmee!Hosana!dan Allah kuzo ku dubamin!meya faru da sehrish ne!"
A ruɗe ta miƙe tare da tunkarar ɗakin azmee,tura ƙopar tayi ta faɗa ciki a hargitse,Adai dai lokacin Azmee ta kammala sallar asuba,juyowa tayi tana kallon jahad ganin hawaye asaman fuskarta yasa ta miƙe da sauri ta tunkareta tana tambayarta
"Jahad lafiya meya faru ne"
Muryarta har shaƙewa takeyi wurin ambaton sunan sehrish"Aunty azmee sehrish!bansan meya faru da ita ba,gata can kwance a ƙasa bata motsi,ga jini a jikin wandonta....."tunkan taƙarasa maganar Azmee ta zabura da gudu ta fita daga ɗakin,itama jahad ɗin tabi bayanta da sauri,
Ƙarasawa azmee tayi wurin da sehrish take akwance,ta zuƙunna tana ƙare ma jikinta kallo,tsananin tausayinta ne ya kamata,Allah kaɗae yasan tun yaushe take kwance a wurin cikin halin ha'ula'e,
Hannu tasa tare da shafa fuskarta,busassun hawayene asaman fuskarta,la66anta duk sun bushe ƙamas dasu,
ɗagowa tayi tare da kallon jahad dake tsaye tana kuka,
"Ki kwantar da hankalin ki,ina tunanin suma tayi ne sakamakon Ciwon cikin da tayi,Jinin dake ajikinta na al'ada ne,"
Jin haka yasa jahad ta tsagaita da yin kukan,har hankalinta ya ɗan kwanta duk da akwai sauran damuwa atattare da ita,
"Aunty azmee duk laifin mu ne ni da hosana,da ace bamu tafi mun barta a ɗaki ita kaɗai ba,da duk hakan bata faru ba,Allah kaɗae yasan tun yaushe take kwance a wurin nan,"
"ɗaukomin ruwa,in yayyafa mata,"
Da sauri jahad ta nufi fridge dinsu,hannunta har kerma yakeyi wurin yin saurin ta buɗe,bottle water ta ɗauko,sannan ta dawo wurin azmee ta miƙa mata,kar6a tayi ta 6alle murfin ta ɗan kur6i ruwan abakinta sannan ta fesar dashi asaman fuskar sehrish,
Dogon Numfashi taja,tare da sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,muryarta ƙasa ƙasa tashiga fadin"Cikina zafi,Ciwo yakeyi mun!dan Allah abani magani nasha,kada na mutu,"
"Jahad dauko mata magani,yana nan ajiye saman drawer ɗina,"juya jahad tayi da gudu ta nufi ɗakin azmee,
Hannu azmee tasa tare da ɗago da kan sehrish ta azata asaman laps ɗinta,kafa mata ruwan tayi abakinta,a hankali tashiga kwankwaɗar ruwan,dama makoshinta a bushe yake,
Dawowa jahad tayi hannunta ɗauke da maganin ta miƙa ma Azmee, bayan ta kar6a ta curo mata shi guda biyu ta sanya mata abakinta,tare da ruwan ta haɗiya,
Bayan ta kammala sha,ta mika ma jahad robar ruwan"ki mayar dashi a fridge,bari na taimakata mu shiga daga ciki,"
Dakyar ta cuccu6i sehrish,don ma ba wani nauyi ne da ita ba,cikin bedroom ɗin nasu ta shiga da ita,Jahad tabi bayansu,
Toilet tashiga da ita,jahad sae faman zirga zirga take yi acikin bedroom ɗin nasu,duk wannan budurin da akeyi hosana nacan ɗakin azmee naɗe cikin bargo tana bacci,
Muryar azmee tajiyo daga cikin toilet ɗin tana yi mata magana"Pad zaki miko mun,tare da pant ɗinta,"_
Jiki na rawa jahad,ta ƙarasa gaban wardrobe ɗinsu,wurin kayan sehrish ta ɗauko mata pant,sannan ta haɗo mata tare da pads,
Abakin ƙopar toilet din ta tsaya tare da ɗan knocking kopar,zuro hannu azmee tayi ta kar6i kayan,
Komawa jahad tayi saman gadonsu,ta zauna tana jiran fitowarsu daga cikin toilet ɗin,
Within mins,Azmee ta fito daga cikin toilet ɗin,hannunta dafe da sehrish,duk ta rurruketa gudun karta faɗi,Waist dinta na ɗaure da farin towel,sae faman cizon la66anta takeyi,saboda raɗaɗin da take ji har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,
Asaman bed ɗinsu Azmee ta kwantar da ita,jahad ta yafa mata bargo asaman jikinta ta lullu6eta,
"Sannu sehrish,Allah ya baki lafiya," acewar jahad,
Dama ance ciwon ƴa mace na ƴa mace ne,su da suka son zafin abun gashinan sun taimaka mata,saboda suma sunayi kuma sunsan cewa lalurace,sannan sunsan irin raɗaɗin da takeji ajikinta,dayawa Wasu mazan basu son ya abun yake ba,tunda bayi sukeyi ba,shiyasa har suke ganinshi amatsayin ƙazanta,kuma basu yi ma mata uziri,aduk lokacin da sukayi kuskuren da jini ya bayyana ajikinsu,Wasu mazan nake nufi ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,Haka matan ba,bakowa bace ke taimakon ƴar uwarta ba,acikin irin wannan yanayin na period,
"Sannu Allah ya baki lafiya,"azmee ce tayi maganar,yayin da idanuwanta ke akan sehrish,wadda ta runtse idanunta tana ta faman ciccije la66anta,
Bata bar ɗakin nasu ba,har saida bacci ya ɗauki sehrish sannan tayi masu sallama,
Kwanciya jahad tayi agafenta,suna fuskantar juna,zuba mata ido tayi tana kallonta,cike da so da ƙauna,
A haka har bacci ya dauketa,
A 6angaren Sgr kuwa,ko sallar asuba bai samu ya halarta ba,Acikin bedroom ɗinshi yayi sallar,komawa yayi saman katafaren gadonshi ya kwanta yayin da blue eyes dinshi ke kallon Ceilling,Kalaman sehrish ne suka shiga dawo mashi acikin zuciyarshi,bakomai ne yafi tsaya mashi aranshi ba fa ce kalmomin nan guda biyu da ta kirashi dasu,MARA TAUSAYI MARA IMANI!sannan kuma tayi comparing ɗinshi da wannan fasiƙin mutumin, yaji raɗaɗin abun sosai acikin zuciyarshi,tayi matuƙar ɗaure mashi kai,Ko a ina tasamu ƙwarin guiwar gaya mashi magana?duk irin yadda take jin shakkarshi?yarinyar da ko cikin idonshi tsoran kallo takeyi,balle har ta ɗaga mashi yatsa,
Gyara kwanciyarshi yayi,ya koma yana fuskantar right hand ɗinshi,sannu a hankali bacci ya dauke shi batare da ya shirya yin shi ba,
Wuraren ƙarfe Takwas na safe,jahad na cikin bacci,taji shessheƙar kuka acikin kunnuwanta,buɗe idanuwanta tayi tare da wurgasu wurin da take jin sautin kukan,Sehrish ta gani zaune ta jingina bayanta a head board ɗin gadon,sae kuka takeyi kamar wadda ta rasa wani mai mahimmanci arayuwarta,
Da sauri jahad ta miƙe zaune,tana kallonta tace"Sehrish!lafiya kike kuka?ko haryanzu ciwon cikin ne"?
Girgiza kanta tayi alamar a'a,
"To ki faɗamun meke damunki ne"?da damuwa a fuskarta tayi maganar,
Cikin shesshekar kuka Sehrish ta soma magana,
"Jahad!na shiga uku!najama kaina bala'e,Jiya nayi ma babban yayanmu rashin kunya,batare da sanina ba,wlh sai yau da safe na tuna duk abunda ya faru,nasan cewa bazai ƙyaleni ba,Dole ya hukunta ni"ta karasa maganar tare da sa hannu tana matsar hancinta,
Hankali atashe jahad tace"Sehrish!kodai mafarki kikayi ne?ae babban yayanmu bai dawo ba,kin manta sun tafi damaturu ne"?tayi maganar tana ƙoƙarin fahimtar da ita,
"Wlh jahad ba mafarki nayi ba,jiya ya dawo acikin gidan nan,yana nan a part dinsa,"
Hannu jahad tasa tare da dafe saitin zuciyarta adan tsorace tace"Munshiga Uku!garin yaya har kikayi mashi rashin kunya?kuma kina acikin hayyacinki babu magagin bacci atare dake"?
"Bana acikin hayyacina jahad,zafin ciwone yasa na balbaleshi da masifa,har ina nuna shi da yatsa..."kaf ta kwashe duk abunda ya faru a tsakaninsu ta sanar ma jahad,
Hannu jahad tashiga tafawa tana faɗin"wlh babu ruwana!sehrish kin shiga uku,mai kwatarki a hannunshi yau sai Allah,hukuncinki yafi ƙarfin ayi maki shi acikin gidan nan sai dai yakai ki can headquater dinsu,"
Jin wannan maganar,ya ƙara ɗaga hankalinta,fashewa ta kuma yi da kuka,
Lallashinta jahad ta shiga yi"Am sorry,zolayarki nakeyi,amma gaskiya sehrish Anya baki sha Codine ba?Yo ni ko giyar wake nasha,ae bazan iya tunkarar babban yayanmu ba,balle har in gaya mashi irin zafafa kalaman da kika yada mashi,"
Cikin shesshekar kuka tace"dan Allah jahad ki bani shawara,kodai in gudu in bar gidanne?kinga su daddy basu nan,zai iya kashe ni,"
Shiru jahad tayi tana saƙa wani abu aranta,sehrish kuwa ta zuba mata ido tana jiran jin shawarar da zata bata,
"Kinsan me!kada ki kuskura kije bashi haƙuri,Dama kin faɗa mashi cewa kada yayi tunanin zaki gudu kibar gidan ne,ko kuma zaki zo bashi hakuri,Sannan kuma kince mashi ba zaki ƙara zuwa part dinshi ba koda ace kin kammala ƙazantar ne,Inaso ya tabbatar da cewar dagaske kike mashi bada wasa ba,hakan zaisa abun ya tsaya mashi acikin ranshi kuma zaiji shakkar ƙara faɗa maki irin waɗannan kalaman saboda gudun kar girmanshi ya faɗi,sannan idan yaga kwana biyu baki je yi mashi aiki ba,ina da tabbacin cewar zai nemeki ne,Amma muddin kika je bashi hakuri,wlh sai kinyi danasani ne,"
"Amma jahad,rashin kunya fa nayi mashi,yakamata na bashi hakuri in ba haka ba Zai gane cewa ina acikin hayyacina na gaya mashi magana,kuma zai dinga yi mun kallon mara kunya ƙarshe ma ya tsane ni gaba daya,"
Murmushi jahad tayi tare da cewa"indai bazai ta6a lafiyar jikinka ba toh da sauki,ƙwara yayi maki kallon mara kunyar,akan dai kije bashi haƙuri,nasan bazaki fahimce ni ba,A yanzu amma nan gaba zaki ga amfanin yin hakan da kikayi,"_
Zugudum sehrish tayi tana doubting akan abunda jahad ta faɗa mata,Anya kuwa jahad ba hanyar banza takeson ɗaurata ba?in ba haka ba saboda me zata hana ta zuwa bashi haƙuri,bayan itace mai laifi,A matsayin shi na mijinta kuma yayanta,bai kamata tayi mashi hakan ba,sannan kuma taƙi zuwa bashi hakuri,
Shigowar azmee ne ya katse mata zancen zucin nata,atare suka juya suna kallonta,
"An kammala breakfast,yana a dining yana jiranku,"
Ta karasa maganar tare da kai idanunta kan sehrish tace"Ya jikin naki"?
"da sauƙi alhamdullah,nagode ssai da irin kulawar da kuka bani,"
"Kada ki damu ae duk yiwa kaine,Amma naga kamar hawaye akan fuskarki,Ko haryanzu akwai ciwon ne"?
"A'a,naji sauƙi sosai,"
Murmushi azmee ta saki,kafin ta juya ta fuce daga ɗakin,
"Jahad kije kawai kuyi breakfast ɗin,Ni zan zauna a ɗakine,kada mu haɗu da babban yaya,Don nasan bazaiyi mun da kyau ba,"
"kada kisa damuwa aranki mana,duk kin bi kin tashi hankalin ki,Da yunwa zakiyi ta zama ne?bazaki ci komai ba"?
Shiru tayi ba tare da tace komai ba,
"Okey,zan kawo maki breakfast ɗin aɗaki sai kici hakan yayi maki"?
Ɗaga mata kai sehrish tayi"Eh,ki kawomin anan,zan fi samun kwanciyar hankali,akan in fita wajen,"
Saukowa jahad tayi daga saman gadon,ta buɗe kopa ta fuce daga dakin,
Ajiyar zuciya sehrish ta sauke,tunani ta shiga yi ko a wani hali babban yaya yake ciki,Yayi bacci jiya ko baiyi ba,Allah yasa dai kalamanta basu ta6a mashi zuciyarshi ba,
shigowa jahad ta kumayi hannunta ɗauke da madaidaicin tray,kayan tea ne sai chips da sauran abunda baza a rasa ba,Asaman drawer ta ajiye mata shi,sannan ta juya ta fuce daga ɗakin,
Matsawa tayi kusa da trayn,sannan takai hannu ta ɗauki cup of tea ɗin tana ɗan kur6arshi,
Cikin ƙankanin lokaci ta kammala yin breakfast ɗin nata,
Zama tayi cike da fargabar abunda zai biyo baya,
Ranta ne ya bata cewar,ta jaraba kiran aunty azeema ta sanar da ita abunda ya faru atsakaninta da sgr,may be ta samu shawara mai kyau a wurinta,
Da sauri ta ɗauki wayarta dake ajiye saman gadon,contact ta shiga ta lalubo numbarta,ta danna mata kira,tana fara ringing,Azeema ta ɗaga kiran nata,
Tunkafin tafara magana hajiya azeema tace"2 days ba hello ba hi ko?har kin fara mantawa dani ko,"
Murmushi sehrish tayi tare da cewa"ba haka bane,Aunty azeema kusan kullum ne saina nemi layinki,amma baya shiga,"
Azeema tace"Hakane fa,nifa wayata indai bani na kira mutun ba,da wuya ne a same shi,kullum busy nake,"
Shiru sehrish tayi tana tunanin ta ina zata fara kora mata jawabi,
"Ina sauraronki,Har yanzu ba wani cigaba a zamanki dashi"?_
Nan fa sehrish ta samu ƙwarin guiwar sanar da ita duk abunda ya faru atsakaninsu daren jiya,
Tayi tunanin aunty azeema zatayi mata faɗa ne,amma da buɗar bakinta sai cewa tayi"Very Good!hakan da kikayi mashi yayi mun dai dai wlh,"
Sakin baki sehrish tayi tamkar tana agabanta,kusan bakinsu ɗaya da jahad,
"Kada ki kuskura kije bashi haƙuri!nafi so ya gasgata kalamanki"
Cike da mamaki sehrish tace"Aunty azeema dagaske kike?kada na bashi haƙuri"?
"Ƙwarai kuwa,ina goyon bayan hakan ɗari bisa ɗari,kuma kada ki kuskura kije part dinshi da sunan aiki,Ki rabu dashi,dama ae yace kada ki koma mashi har saikin kammala kazantar kibarshi a hakan,kada ki wani ji tsoro,"
Lumshe ido sehrish tayi tare da ware su fuskarta da dan murmushi tace"Shikenan aunty azeema bazanje ba in sha Allah,"
"Namanta ban sanar dake ba,nafa dawo nigeria,tun jiya amma na wuce damaturu,bazan samu zuwa nan ba yanzu saboda abunda ya faru na rasuwar modibbo,amma kada ki damu zan bada saƙo ta wurin junaid,naji yace zai biyo Abusufyan idan ya tashi dawowa,zan bashi ya kawo maki har gida,Sannan zanyi maki bayanin yadda zakiyi amfani dasu,koda ta wayane,"
"Nagode sosai Aunty azeema,Allah yasaka da alkhairi,Amma yaushe zaki dawo nan?don nayi kewarki sosai,"
Dariya hajiya azeema tayi tare da cewa"Very soon zan dawo,"
Sehrish tace"to shikenan,Allah ya kaimu lokacin,"
"Ameen my daughter,"
Sun jima suna waya kafin daga bisani ta ajiye wayar,har hankalinta ya kwanta,duk da akwai sauran fargaba atare da ita,
saukowa tayi daga saman gadon,Wardrobe ta nufa,hannu tasa ta buɗe,Arab gown ce ta ɗauko pink colour,tare da mayafinta shima pink ne amma bai ciza ba,kamar na rigar,zura kayan tayi ajikinta,sannan ta koma gaban mirror ta zauna,zuba ma mirror din ido tayi tana kallon fuskarta,ta cikin madubin,yayin da zuciyarta ke tariyo mata abunda ya faru adaren jiya,
A 6angaren Sgr kuwa,wata irin matsiyaciyar yunwa ce ta farkar dashi daga bacci,saukowa yayi daga saman gadon,Jallabiya ce ajikinshi,wuce wa yayi wurin closet ɗinshi,withins mins ya shirya kanshi cikin jeans da t shirt Maroon colour,rigar ta fito da surar jikinshi saboda ta ɗanyi tighting ɗinshi,Ƙafarshi na sanye cikin Canvas sneakers,
fitowa yayi daga part ɗinsa,Ya nufi downatairs,a natse yake taka staircase din har ya sauko down,Su jahad na zaune ita da hosana saman Sofa mai mazaunin mutun uku,suka jiyo takun takalmanshi,
ɗagowa sukayi atare suna kallonshi,lokacin da ya ƙaraso wurinsu,da sauri suka haɗa baki wurin gaisar dashi,
Batare daya kallesu ba,Ya amsa masu gaisuwarta su,fuce wa yayi daga cikin main palour ɗin,Kaitsaye Motarshi ya nufa,Amstrong na ganin shi da sauri ya ƙarasa tare da buɗe mashi motar ya shiga daga ciki,sannan shima ya bude driver seat ya zauna,
Kafin ya tashi motar,ya ɗan dago tare da kallonshi ta cikon mirror yace"Sir,Where are we going"?
"Restaurant,"ya bashi amsa atakaice,
Shiru amstrong yayi batare daya tashi motar ba,Hakan yasa shi cewa"what are u waiting for"?
Cikin harshen turanci amstrong yace"Sir,kayi haƙuri da abunda zance,Amma zuwa restaurant ba naka bane,da matsayinka aganka a restaurant ka je cin abinci?kaida ya kamata ace a gida ake girka maka,idan ba damuwa zanje nakawo maka,ka koma ciki pls"
Tunda ya soma magana sgr yayi shiru yana sauraronshi,saboda amstrong yana ɗaya daga cikin waɗanda suke Control dinshi,"
Amsa mashi yayi da okey,sannan ya buɗe motar ya fuce,
Duk wannan abun dake faruwa sehrish na tsaye a wurin window tana leƙen motarshi,taga lokacin daya shiga cikin motar,kuma sai taga ya fito daga ciki,
Aranta tashiga tunanin ko lafiya,
Dawowa cikin gidan yayi,Part ɗinshi ya koma ya zauna saman sofa yana jiran dawowar Amstrong,dan bala'e ga abinci acikin gidan amma yafi ƙarfin yayi ma wani magana ya kawo mashi abincin,tunda ya ƙori mai aikin tashi,
Cikin minti goma sha biyar,Amstrong ya shigo cikin gidan hannunshi dauke da ledojin,Su jahad na ganinshi suka shiga gaisar dashi,fuskarshi ɗauke da murmushi ya amsa mashi,sannan ya wuce upstairs sashen sgr,
Yana barin wurin da gudu jahad ta nufi ɗakinsu,tura kopar tayi ta shiga ciki tana faman ƙwala ma sehrish kira,
tsaye ta same ta hannunta ruke da wayarta,ganin jahad ta faɗo ɗakin babu sallama yasa tace"Lafiya"?
Jahad tace"Yanzu naga wannan sojan wanda yake yin driving ɗin babban yayanmu,Hannunshi dauke da ledojin kuma na restaurant ne don naga sunan ajiki,"
Cike da mamaki sehrish tace"to fa!ko meyasa ya aika akawo mashi abinci bayan ga wanda aka girka agida"?
Jahad tace"Yanzu haka saboda abunda ya faru atsakaninku ne jiya,shiyasa yaƙi cin abincin gidan,"
Jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,
"Yanzu haka,saboda yana ƙyamar girkina ne saboda ina yin period,shiyasa bazaici abincin gidan ba,"acewar sehrish,
Jahad tace"Amma ae bake kikayi girkin ba,Aunty azmee ce ta girka,Gaskiya nafi tunanin cewa wani abunne daban yasa bazaici abincin gidan nan ba,"
Murmushi sehrish ta ɗanyi tare da cewa"kinsan Allah babban yaya bazai iya cin abincin nan ba,Ina nan dake ƙarshe sai dai azubar da shi abanza"
Jahad tace"Mu zuba ido mu gani,zaici ko bazaici ba,"
***
Excuse sir!muryar amstrong ce ta dawo dashi daga zurfin tunanin da ya faɗa,
Muryarshi a kasalance yace mashi"Come in,"
Shiga ciki yayi tare da ajiye mashi asaman table dinshi,Sannan ya sara mashi,kafin ya fuce daga ɗakin,
Kusan minti 5 bai motsa ba,kamar ba yunwa yake ji ba,Hannu yasa tare da curo bugger daga ciki,yana ƙokarin kaita a bakinshi ,Ya tuna da jinin daya gani ajikin wandon sehrish,aikuwa nan take Ya sake ta ta faɗi saman table din,Wani irin yunƙurin amai ne ya taso mashi,da sauri ya miƙe ya nufi cikin toilet,ya shiga kwara amai agaban basin,Ba ƙaramin galabaita yayi ba,ƙyanƘyami ya hana yaci abincin ga yunwa na cinshi,har zazza6i ya fara kamashi,
Tap ya kunna ruwa ya shiga kwararowa,tarba hannayenshi yayi ya shiga kuskure bakinsa,kafin ya wanke face ɗinshi,
Fitowa yayi daga cikin toilet,yana faman sauke ajiyar zuciya,komawa yayi saman gadonshi ya kwanta,wasa wasa Zazza6i ya rufe shi,temperature ɗin jikinshi yayi zafi sosai,
Kasa samun natsuwa sehrish tayi,tunda taga an kira sallar magrib da isha'e,sgr bai fito daga part ɗinsa ba,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankalinta yayi ba,jiki na rawa ta fito daga ɗakinsu ta wuce kitchen,Anan ta samu azmee tana ƙarasa gyara kitchen din ita da hosana,
Ganinta yasa azmee tace"Ya jikin naki"?
"Da sauƙi aunty azmee,sai dai...."shiru ta ɗanyi bata ƙarasa maganar ba,
Tunkarota azmee tayi tare da ruƙo hannunta suka ja daga gefe sannan tashiga tambayarta meya faru,
"Aunty azmee,wani abu ya faru jiya tsakanina da babban yaya ban sanar maki ba,"
"Faɗamun meya faru,Allah yasa dae ba wani laifin kika aikata masa ba,"
Nan sehrish ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar mata,
"Ya salaam,' azmee ta ambaci hakan hankalinta aɗan tashe tayi maganar,
"Wlh aunty azmee ba laifina bane,bana acikin hayyacina ne,shiyasa nayi mashi rashin kunya,"
Muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
Cigaba da magana tayi"Ni babban abunda yafi tayar mun da hankali,har aka kammala sallar magrib da isha'e,banga ya fito daga cikin part dinshi ba,kuma inajin tsoran in tunkare shi,saboda nasan dole ya hukunta ni,kuma nayi shawara da aunty azeema tace kada na kuskura naje bashi haƙuri,haka jahad ma tace mun,"
"Sehrish idan kikace zaki ɗauki shawarar Azeema,zata kaiki ta baroki ne,saboda ita wata irin wayayyiyar maca ce,Bazan hana ki ɗauki shawararta ba,amma inaso ki tuna matsayinshi a wurinki,Yayanki ne shi kuma Mijinki,jiya ya kwana da fushinki acikin zuciyarshi haka yauma ya tashi da fushinki,tabbas zaki jefa kanki cikin matsala ne,in har bakiyi hanzarin neman afuwarsa ba,Yakamata kije ki bashi haƙuri,kuma ki sanar dashi cewa ba a hayyacinki kike ba!"
. "yanzu aunty azmee kina nufin inje in bashi haƙuri"?
"Eh,haka nake nufi,"
"Amma fa yace mun kada na kuskura na ƙara zuwa part ɗinshi har saina kammala period ɗina,"
"Kada ki damu da wannan kije kawai,in sha Allah babu abunda zai faru,"
Tashin hankalin da ba'a sama shi date,Shin shawarar wa kuke tunanin zatayi ma sehrish amfani?Shawarar Azeema da Jahad,ko kuwa shawarar Aunty Azmee,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana ta whatsapp dan Allah banda kiran wayar,bana ɗagawa 08103884440❤_
Nagode da shawararki Aunty azmee,in sha Allah zanyi amfani da ita"
"Yawwa haka nake son ji" azmee tayi maganar tare da komawa cikin kitchen,Sehrish kuwa bata wuce part ɗinshi ba,bedroom ɗinsu ta wuce,sam takasa samun natsuwa,ta rasa shawarar wa zata ɗauka acikinsu,bakomai yafi sata fargaba ba,fa ce abunda zai biyo baya idan tayi kuskuren zuwa sashen shi,
Har wuraren ƙarfe goma sha biyu na dare bata runtsa ba,tana zaune saman gadon nasu,yayin da wayarta ke ruƙe a hannunta,Hosana na kwance a gefenta tana bacci cikin bargo hankalinta kwance,Jahad kuma na can ɗakin azmee,
Wani tunani ne yazo mata acikin zuciyarta,da sauri ta shiga contacts ta lalubo layin Aunty azeema,ta danna mata kira,cikin sa'a ta ɗaga kiran nata,
Kara wayar tayi a kunnanta,tare da yi mata sallama,
"Assalamu Alaikum,"
Aunty azeema tace"Wa'alaikum salam daughter,me kikeyi har yanzu baki yi bacci ba,"?
"Na kasa yin bacci ne,ina cikin damuwa"acewar Sehrish,
Azeema tace"kodai duk fargabar babban yayan naku ne?
"Ba haka bane,Aunty azeema,na ɗan shiga damuwa ne,yau babban yaya bai fito daga part ɗinshi ba,har akayi sallar La'asar da magrib,bai fito ba,"
Maganar sehrish ta ɗan tashi hankalin hajiya azeema,
"Amma ya ci abinci kuwa"?
Sehrish tace"baici abincin gida ba,ɗazu dai yasa an kawo mashi abincin restaurant,amma bani da masaniya akan yaci ko bai ci ba,"
Shiru hajiya azeema tayi na wani dan lokaci,haka itama sehrish ɗin,Kowa da abunda yake saƙawa aranshi,
"Kina jina"muryar hajiya azeema ce ta katse mata zancen zucin da ta shiga,
"Ina sauraronki Aunty,"
"Gaskiya akwai matsala,saboda ba ƙaramin abu bane zai hana Sgr zuwa masallaci ba,Ina da tabbacin cewa zuciyarshi ta motsa,Allah kaɗae yasan halin da yake ciki,gashi babu kowa agidan idan baku ba,dama ace su Abbanku suna nan ne ko Omar zasu iya shawo kan matsalar,Amma yanzu haɗari ne wani ya tunkare shi,tunda ba'asan halin da yake ciki ba,wani irin zafin zuciyane dashi idan ya fusata kowa tsoran tunkararshi yake yi,Amma idan akaci sa'a,Ya yanke jiki ya faɗi ya suma a lokacin da zuciyar tashi ta motsa,to tabbas koda ya farfaɗo bazai tashi da wannan fushin ba......"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar,tana sauke ajiyar zuciya,
"Yanzu ya zamuyi kenan"?sehrish ta tambaya,fuskarta dauke da damuwa,
"Abunda za'ae yanzu shine,inaso kije part ɗin nashi kiga a wani hali yake ciki,Amma fa kada ki bari ya ganki,a 6oye zaki je,in ba haka ba a tsinto ƙasusuwanki a dakinshi,"ta karasa maganar cike da zolaya,
Dariya sehrish ta dan yi duk da tsoron daya kamata,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Shikenan Aunty azeema,zanje in sha Allah,"
Azeema tace"yawwa daughter,idan kin dawo duk abunda ya faru ki sanar dani pls,"
"Toh Aunty,"
Daga nan sukayi sallama,saukowa daga saman gadon Sehrish tayi,bayan ta ajiye wayar saman side drawer,ta zura slipper ɗinta dake ajiye nan ƙasan,ta gyara mayafin jikinta sannan ta fito daga dakin nasu,
Tunkafin ma ta hau upstairs din gabanta ke faɗuwa rass rasss,tamkar wadda zata tunkari wani zombie,
A hankali take taka staircase ɗin harta samu ta haura sama,tana tafiya tana ambaton"La'ilah ha illa antas subhanaka inni kuntu minazzalimin,"har tazo bakin ƙopar part dinshi,kamar wata 6arauniya haka ta leƙa cikin falon,ganin baya ciki yasa ta sauke ajiyar zuciya,cikin sanɗa ta zura ƙafarta ciki,a hankali take tafiya,gudun kada yaji sautin takalminta yasa ta zuƙunna tare da ciresu ta ruƙesu a hannunta,
A ƙopar bedroom ɗinshi ta tsaya,har lokacin bata daina ambaton La'ila ha illah anta subhanala inni kuntu minazzalimin,acikin zuciyarta ba,saboda tsabar tsoro,zuciyarta tamkar zata fito daga ƙirjinta,saboda bugun da take yi mata,daraam!daraaam,
A hankali ta ɗan zura kanta tare da leƙawa cikin ɗakin nashi,
Kwance yake saman gadon,gangar jikin na asaman gadon,yayin da head ɗinsa zuwa wuyanshi suka zuro daga gefen gadon,Sumar kanshi ta zubo har saman floor,
Gabanta ne ya faɗi rasss!tun daga kan yadda yayi kwanciyar ta gane cewa babu lafiya,gaba ɗaya zufa ta wanke jikinshi tamkar wanda ya watsa ruwa ajikinshi,ta ko'ina zufar ke tsastsafo mashi,gaba ɗaya ga66an jikinshi sun sake,
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,batasan ko bacci yake yi ba,ko suma yayi,Allah wa'alamu,
Zura ƙafarta tayi yayin da gabanta ke ci gaba da faduwa,Shiga cikin bedroom ɗin tayi,har zuwa wurin gadon nashi,Yanayin kwanciyar tashi ma,Zata iya haifar mashi da matsanancin ciwon wuya,saboda yadda ya yi sadda kai,
Zuba mashi ido tayi tana kallon fuskarshi,daga gani ba ƙaramin jiki yaji ba,
Tunani ta shiga yi,kodai ta ɗaukko ruwa ta yayyafa mashi,duk da bata da tabbacin cewar ko suman yayi ne,amma ga dukkan alamu ya suma ne...... ,
Da sauri ta juya ta koma palour,fridge ta nufa da sauri sauri ta buɗe shi ta ɗauko robar ruwa,Sannan ta dawo cikin ɗakin nashi,Tashin hankali,Tsayawa tayi tana tunanin taya ma zata fara yayyafa mashi ruwan batare daya ganta ba?kyau tana watsa mashi ta watsa da gudu kafin ya murmure,
Jikinta sae kerma yake yi,a haka ta buɗe robar ruwan,ta tarfa ruwan a hannunta,Ja da baya ta ɗan yi,sai da taba da interval sosai a tsakaninsu,daga inda take ta yarfa mashi ruwan akan fuskarshi,yaraf!ya saukar mashi,Aikuwa nan take ya shiga sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,da gudun gaske sehrish ta 6oye acikin labulen ɗakin nashi,zuciyarta na ɗar ɗar,
Sannu a hankali ya buɗe blue eyes ɗinshi,yana faman sauke ajiyar zuciya,bin kasan bedroom ɗin nashi yayi da kallo,kafin yayi yunƙurin mayar da kanshi saman Gadon nashi,saman pillow ya aza kanshi,yasa hannu yana murza wuyanshi saboda raɗaɗin da ya ji a wurin,lumshe idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu,jikinshi babu ƙwari amma zazza6in ya sauka daga jikinshi,dakyar ya iya miƙewa daga zaune,ya jingina bayanshi a head board ɗin gadon,Yayin da idanuwanshi ke a lumshe,
Sehrish dake 6oye bayan curtains ɗin ɗakin,tana jin duk wani moving ɗinshi,ta toshe bakinta da hancinta da tafin hannunta,saboda gudun kar ya gane akwai mutun aɗakin nashi,
Almost 15 mins yana a zaune bai motsa ba,tun da yake a arayuwarshi bai ta6a shiga matsanancin halin daya shiga ba irin na yau,kamar wani mara gata,sae kace ba Surgeon General ba,Yau ya ɗanɗani zafin kadaici,duk a sanadin kalaman da sehrish ta gaya mashi,
Saukowa yayi daga saman gadon,Ya tsaya atsaye tare da sanya hannu ya tu6e shirt ɗin dake ajikinta,Yayi wurgi da ita saman gadon,Zame belt ɗin wandonshi yayi ya jefar dashi saman rigar,sannan ya zame dogon wandon,Ya rage daga shi sai short light blue,
yana tafiya cike da rashin ƙwarin jiki,a haka har ya buɗe toilet ya shige ciki,Sehrish na jin motsin buɗe kopar toilet,Jiki na rawa ta lalla6a,saɗaf saɗaf ta fito daga cikin bedroom din,Hannunta riƙe da bottle water din,Saman fridge ta ajiye robar ruwan sannan ta kama hanyar fita daga falon,Har ta kai bakin kopar dakin ta juyo ta kalli kayan Breakfast ɗin da Armstrong ya kawo mashi,nan ta gane cewa bai ci komai ba,
Fitowa tayi daga part ɗin nashi,ta saukko downstairs da sauri ta nufi ɗakinsu,bayan ta shiga ciki ta ɗauki wayarta,tare da danna ma Aunty azeema kira,nan take ta ɗaga kiran,
Da sauri ta sanya wayar a kunnanta,tun kafin tayi magana Hajiya azeema tace"Ya ake ciki ne?
Sehrish tace"Naje part ɗin nashi,na same shi a sume saman gadonshi,gaskiya ba ƙaramin jiki yaji ba,nasamu dae na yayyafa mashi ruwa batare da ya ganni ba,na lalla6a na fito daga ɗakin nasa,naji ya shiga toilet da alama wanka zaiyi,Amma fa naga kayan abincin da aka kawo mashi daga restaurant,Da alama bai ci komai ba,"
Hajiya azeema tace"Good!,naji daɗi da bai ganki ba,Kuma naji daɗin suman nan da yayi,saboda zai samu sauƙi acikin zuciyarshi,duk da nasan dole ya ƙullace ki a aranshi,"
Murmushi sehrish ta ɗan yi kafin ta kuma cewa"duk yau baici komai ba,"
"Kada ki damu da wannan,ita yunwa bata da hankali,Ina nan dake wannan abincin da ya bari wanda aka kawo mashi na restaurant,Shi zai nema ina nan dake,yanzu dae ki kwanta kiyi bacci',
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,
"Ki kwanta kiyi bacci,Sae Allah ya kaimu gobe zamuyi magana," sallama sukayi da ita,Sehrish ta kwanta saman gadon tare da ajiye wayarta saman stomach ɗinta,yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling ɗin dakin,
Sgr kuwa,bayan ya fito daga wankan da ya shiga,jallabiya ya zura ajikinshi ash colour,har wani jiri yake gani saboda tsabar yunwar da ya ke ji,ba arziƙi ya dawo palour saman sofa ya zauna,tare da kai hannu ya ɗauki burger ɗin nan,da ya ajiye saman table,Turata yayi cikin bakinsa ya shiga cin ta har yana shaƙewa,a ƙa'ida baya cin abincin da ya sha iska wanda aka bari a buɗe,Amma yau ba kanta,Ci kawai yakeyi,tass ya cinyeta,Miƙewa yayi da sauri ya nufi wurin fridge don ya daukko drink din da zaisha,hannu yakai tare da ɗaukar bottle water ɗin da Sehrish ta bari asaman fridge ɗin,6alle marfin yayi ya kafata a bakinshi yana kwankwadar ruwan,sae da yayi rabin ruwan dake acikinta,sannan ya dakata da shan ruwan da yake yi,Sai lokacin ya ankara da inda ya ɗauki robar ruwan,Shiru ya ɗan yi tare da zubawa robar ruwan dake hannunshi ido yana kallonta,Shi dai yasan bai ajiye ruwa asaman fridge ba,tunani ya shiga yi,Yanayin yarda ya farka duk da akwai zufa ajikinshi,amma tabbas yaji Saukar ruwa akan fuskarshi wannan ya tabbatar mashi da cewar wani ya shigo cikin part ɗinsa,Hannu yasa tare da buɗe fridge ɗin ya saka robar ciki,Sannan ya ɗauki coke mai sanyi,
Komawa yayi saman sofa din,ya zauna tare da kai hannu ya buɗe daya daga cikin ledojin,take away ya curo ya buɗe shi Chips ne aciki duk yayi sanyi,amma ahaka ya shiga turashi acikin bakinshi yana ci,bai ta6a shiga yanayi irin wannan ba a rayuwarshi,tass ya cinye duk wani abu dake a wurin,bayan ya kammala cin abincin,mikewa yayi ya koma cikin bedroom ɗin shi,ya ɗauko wayarshi,Sannan ya dawo saman sofa ɗin ya kwanta tare da miƙar da ƙafafunshi saman hannun kujerar,
Zubama screen ɗin wayar ido yayi yana kallonshi batare da ƙyaftawar ido ba,yama rasa wa zai kira yaji sanyi aranshi,numbar Abbansu ya lalubo ya danna mashi call,Ringing din farko Abbansu ya ɗaga kiran nashi muryarshi da alamun bacci yace"My son,Me kake yi har yanzu baka yi bacci ba"?
batare da ya amsa mashi tambayarshi yace"Daddy,when zaku dawo?gida duk ba daɗi,"
Tsananin mamakine ya kama Abbansu,Yau Sgr da kanshi yake cewa Gida babu daɗi saboda basu nan,ta wani 6angaren kuma yaji daɗin hakan sosai,
"Kayi missing ɗinmu ne"?Abba ya tambayeshi,
muryarshi akasalance yace"Yeah,especially you,I missed u so much,"
Farin ciki ne ya cika Abbansu,kamar ya janyoshi ta cikin wayar ya rungumeshi,
"Pls Daddy,just come back home,if not zan biyoku damaturun ne,in yaso saimu dawo atare,"
Sgr na jiyo sautin muryar Abbansu yana tiƙar dariya,
"Are u laughing at me"?
Tsagaitawa Abbansu yayi da yin dariyar yace"dole nayi dariyar Farin ciki mana,Yau ya kasance rana ta farko daka nuna kayi kewarmu sosai,naji muryarka wani iri tamkar zaka yi kuka,tell me what's wrong with u,wani ya ta6a mun kaine"?
Sgr yace"bana jin daɗin zuciyata ne,ko zaka sanyani farin ciki?
Abba yace"yanzun nan kuwa,bari na tuna maka wani abu,lokacin da kana ɗan jinjiri dakai cikin towel,kyakkyawa da kai,Na ƙwallafa rai sosai akan ka, kai kuma ga kyuyar tsiya,ka ƙi jinin baƙin mutun ya ɗauke ka,koni da nake mahaifinka ban isa na ɗauke ka ba,in ba bacci ya ɗaukeka ba,Sae in lalla6a in shiga ɗakinka,In zauna saman gadon in zuba maka ido inta kallonka,araina ina cewa Yanzu wannan mallakina ne,Allah ya bani Halak malak,Haka zan tasaka gaba ina kallonka,da zarar ka farka kuwa,mukayi ido biyu,kamar kaga wani 6arawo haka zaka fasa ihu kana ambaton sunan Mommynka,"
Lumshe ido Sgr yayi yana sauraron Abbansu,fuskarshi asake tamkar zaiyi murmushi,wata irin natsuwa yaji acikin zuciyarshi,
"Amma daga baya,saboda irin kulawar da nake baka sae ka gane cewa ni mahaifinka ne,kuma inason ka sosai fiye da kowa,sae gashi da kanka,kake zuwa wurina don in ɗauke ka,mu tafi yawo atare,"
jikin Sgr ba ƙaramin sanyi yayi ba,kalaman Abbansu sunyi matuƙar ta6a mashi zuciya,
"Amma ni sai inga kamar baka sona,baka damu dani ba kamar yadda na damu da kai...."
Tunkan ya ƙarasa maganar Sgr ya katse shi da cewa"Daddy kadaina faɗan hakan bana jin daɗi,duk duniya bani da tamkarka,kaine mahaifina,Jigona kuma ginshiƙi na,Abun alfaharina,madubin dubawana....".
Wani irin farin cikine ya lullu6e Abbansu,bai ta6a jin irin wannan yabon daga bakin Sgr ba,sai yau har ya fara tunanin anya kuwa cikin hayyacinshi yake gaya mashi waɗannan kalaman?ko kuwa ya ɗan kora wani abune,Gashi ya saki jiki sai surutu yake yi mashi kamar ba wannan miskilin ba..."
"Pls Rafayet,ka maimaita mun kalaman nan daka faɗamun,inaso nayi recording ɗinsu,"
fashewa da dariya Sgr yayi,hakan ba ƙaramin ɗaurewa Abbansu kai yayi ba,
Cike da mamaki yace"Rafayet,dariya kakeyi mun,dan Allah faɗamun kodai kasha kwaya ne yau,"
"Daddy bansha komai ba,lafiyana ƙalou,kawai ina jin daɗin waya da kaine,ka bari idan ka dawo gida zan sake maimaita maka sai kaji a kunnanka,"
Cikin raha sukayi wayar gwanin ban sha'awa hira irin ta da da mahaifi suka yi wadanda suke cikin begen juna,a karshe sukayi sallama,sauke ajiyar zuciya yayi tare da aza wayar saman chest ɗinshi,wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi,still kalaman Sehrish nadawo mashi acikin ranshi,waɗannan kalaman dae su suka fi ta6a mashi zuciya,Mara tausayi mara Imani,da kuma danganta shi da ya sayyadi,
Tariyo abunda ya faru tsakaninsu ya shiga yi cikin ranshi,Yadda ya damƙo wuyan rigarta tare da yin wurgi da ita ta bugi bango,har ta fashe da kuka saboda zafin da taji,da kuma munanan kalaman da ta jefa mashi,da alama nazarin wani abu yake yi,dangane da abunda ya faru jiya atsakaninsu,
Ya jima asaman Sofa ɗin,kafin daga bisani ya koma cikin bedroom ɗinshi,darduma ya dauƙo ya shimfiɗa tare da kabbara salla,Sae da ya fara biyan bashin sallolin da baiyi ba,sannan ya ɗaura da yin nafilfilin daren daya saba yi,bayan ya kammala ya ɗauki qur'ani ya shiga karantawa,nan take yaji natsuwa tazo mashi acikin zuciyarshi,bashi ya kwanta bacci ba,har sae wuraren ƙarfe biyu na dare,sannan ya haye saman gadonshi ya kwanta,bacci 6arawo yayi awon gaba dashi,
Itama Sehrish,sae da tayi sallar daren,kafin ta kwanta bacci,
Abunda ya faru daren jiya da Aunty babba ta zauna zaman jiran Hayaam....
tunda ƙarfe goma ta buga hayaam bata dawo ba,nan hankalinta yayi mugun tashi,fitowa tayi daga bedroom ɗinsu,ta shiga zarya acikin hotel ɗin,ko Allah zaisa taga gifcinta,amma shiru babu ita har receptionists taje ta tambaya ko sunga fitarta suka tabbatar mata da basu ganta ba,ƙarshe da ta gaji da biɗiɗin nemanta,komawa tayi ɗakin nasu zuciyarta a ƙuntace ta kwanta,duk da halin da ta shiga na rashin hayaam,hakan bai hanata yin bacci ba,harda minshari,
Haroon kuwa tun da ya kammala yi mata wannan aika aikar,ya tattara yabar Hotel ɗin ya gudu gaba ɗaya,don kuwa daƙyar in hayaam zata ƙara moruwa,Ya naƙasata sosai,a saman gadon ya barta a yashe,
Wuraren Sallar asuba,Wayar Aunty babba dake ajiye gefenta ta soma ringing,can cikin bacci ta dinga jin ringing ɗin wayar,dama ta kwana da tunanin hayaam zata iya kiran ta in ta buɗe wayarta,hakan yasa ta farka da sauri takai hannu ta ɗauki wayar,duba screen ɗin wayar tayi da 6oyayyiyar lamba aka kirata,cike da mamaki tace"To fa,waye ya kirani a irin wannan lokacin da 6oyayyiyar number?kodai hayaam ce ta kira,bari na ɗaga na ji,
Picking call ɗin tayi ta kara wayar a kunnanta,
Tun kafin tayi sallama taji ance"Madam,barka da warhaka"
gabanta ne ya ɗan faɗi rass,amma ta dake tace"yawwa,dan Allah wanene ke magana,"
"Babu bukatar ki sani,dama na kira ne don in yi aikin lada,Nasan kina ta neman hayaam ido a rufe,to hayaam dae a halin yanzu addu'arki take buƙata,idan kina son sanin inda take,yanzu zan turo maki da message na address ɗin inda take,sae ki hanzarta zuwa don ki kai mata agaji,Allah ya bata lafiya,idan ta samu ciki dan Allah a ajiyemun abuna,inaso" yana faɗin haka,yayi rejecting kiran,"
Waro ido waje Aunty babba tayi,a hargitse ta saukko daga saman gadon hannunta riƙe da wayar,jikinta har kerma yakeyi,zarya ta shiga yi acikin ɗakin tana jiran shigowar saƙon,
A fili tace"Allah yasa dae hayaam ba wani taje taba ma kanta ba yayi amfani da ita,Sae da naja mata kunne akan ta daina kula maza,amma da ya ke karya ce gaya nan tana son ja mun bala'e,ina zaman zaman lafiyana,"
Tana cikin wannan zullumin,taji ƙarar shigowar message da sauri ta duba top of the screen ɗin wayar,
"Vip,Room 34,"shine abunda taga an rubuta acikin message ɗin,kuma babu numbar wanda ya tura,anyi hidden number,
Sai da tayi zurfin tunani sannan ta gane cewa numbar ɗakin hotel ne aka turo mata,hakan na nufin cewa hayaam tana acikin hotel ɗin,
Jiki na rawa ta ƙarasa wurin trolley ɗin kayansu dake ajiye,gefen wardrobe,buɗe wa tayi ta dauko mayafi ta lullu6a asaman kanta,
Sannan ta tura kopar ɗakin ta fito,tafiya takeyi cike da zullumin abunda zai biyo baya,sae bin ɗakunan dake a wurin takeyi tana bin numbobin jikinsu,cikin sa'a batare da tasha wahala ba tazo kan numbar ɗakin da aka turo mata,sae da ta duba dakyau taga Room 34 ne,Hada key aka ajiye mata ajikin ƙopar,wannan ya tabbatar mata da cewa da gangan aka sanya key ɗin,saboda in tazo ta buɗe ta shiga,
Gabanta sae faɗuwa yakeyi,a hankali ta sanya hannunta ta ɗan murza key ɗin ɗakin ya buɗe,cike da fargaba ta tura ƙopar ɗakin a wani slow kopar ta soma buɗewa ƙiiiiiii,tun kafin ma ta sanya kafarta acikin ɗakin ta hango pant yashe a saman tiles,Rass taji gabanta ya faɗi,wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,dakyar ta shiga cikin ɗakin,karaf Idanuwanta suka hango mata Bra din hayaam dake sagale ajikin mirror,tun daga nan tasha jinin jikinta,wurga idonta tayi gefen hagunta,Handbag ɗin hayaam ta hango yashe a kasa,da alama wurgi akayi da jakar kayan cikinta suka watse akasa,hada wayarta ma duk screen ɗin ya fashe,
..arazane Aunty babba takai idonta saman gadon,mutunne a kwance an lullu6e shi da bargo,
A tsananin tsorace ta ƙarasa gaban gadon,sanya hannunta tayi tare da zame bargon a hankali,tana buɗe bargon da sauri ta mayar ta rufe,saboda tashin hankalin da ta gani,hannu ta aza akai ta fasa ihu tana faɗin"Nashiga uku!Wayyo Allah na,Hayaam wani marar imanin ne yayi maki wannan aika aikar!hayaam waye ya yashe ki haka!La'ila ha'illallahu muhammadur rasulillahi!Amma kowaye wannan anyi haihuwar asara,Uwarshi ta haifo mana Bala'e" ta inda take shiga bata nan take fita ba,Muryarta har shaƙewa takeyi saboda tsabar baƙin ciki,tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu,
..a karshe ta fashe da matsanancin kuka,tare da hayewa saman gadon,tana cigaba da sambatu,da alama ta fara zaucewa,
"mun shiga uku mu yau,Wllh dana san haka zata faru da bamu zauna a hotel ɗin nan ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata,Hayaam kowaye wannan ya gama damu,ɗan jarin da muke taƙama dashi ya kwashe komai babu,ya yashe ki,ya karya mana tattalin arziƙin da yayi mana saura,Ya takaita mu don ubanshi,wlh koma wani jarababben ne,Sae Allah ya toni asirinshi,Ni na ta6a ganin jaraba irin wannan,bai bar komai ba,yayi mata wanwar ɗan jakar uban,haihuwar asara haihuwar titi,haihuwar kwararo...."kasa ƙarasa maganar tayi,wani irin ƙululun baƙin cikine ya tokare mata maƙoshinta,nan tashiga yin kakarin amai,ta saukko daga saman gadon agalabaice ta nufi toilet ɗin cikin ɗakin ta shiga,Sosai tayi amai tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito waje,ta jima acikin toilet ɗin kafin ta fito,tana tafiya ƙafafunta na harɗewa,
Fitowa tayi daga ɗakin ta koma ɗakinsu,Trolley ɗin kayansu ta buɗe,Jallabiya ta ɗaukowa hayaam tare da Mayafi,Sannan ta koma can ɗakin,taci wahala haka ta kinkimi hayaam ta shiga da ita toilet,wani wurin ma ajikinta,baya ta6uwa sae dai anje asibiti duk ya jagule babu kyan gani,hatta la66anta duk sun faffashe hada busasshen jini,nipple ɗinta na right breast kuwa,sai jini yake yi,ƙiris ya rage ya 6alle,haƙika haroon ya cutar da ita,ya zalunce ta,Da mugunta yayi mata hakan,Dama babu Imani aranshi,duk ya faffasa mata skin ɗinta da Nails ɗinshi,saboda baya yanke akaifa,doguwar ƙumba ne dashi,
Aunty babba tasha kuka,Tuntana kukan fili har ta koma yin kukan zuciya,wanda yafi ciwo,Sai da ta nemi taimako a hotel ɗin,sannan ta samu aka ɗauki hayaam,Suka kaita wani private hospital saidai sam bata sanar dasu haƙiƙanin abunda ya sameta ba don tasan karshe reporting za'ace ayi wurin yansanda ita kuma bata son asirinsu ya tonu har abun ya kai kunnan su Ishaq,tafi son in hayaam din ta farfado ta fadi wanda yayi mata hakan don ta tabbatar ba da karfi aka jata dakin ba don wanda ya kira ta ya sanar da ita halin da take ciki har sunan hayaam din ya ambata hakan kuma na nufin ya santa ne,
Tunda aka shiga da ita ciki,Likitoci suka taru akanta,Aunty babba na zaune zugudum saman waiting seat,tashin farko sae da suka fara kar6ar kuɗin gadon kusan Naira dubu 50,Sannan za'ayi mata aiki ciki da waje a ƙalla za'a cajesu kuɗi kusan Dubu ɗari biyar,Bayan haka akwai alluran da za'ayi mata ajikinta kuɗinsu ya kai kimanin dubu 20,
Abun yayi matuƙar girgizata,ita babbar damuwarta,ba halin da hayaam ke ciki ba,Kuɗinsu da suke tattalawa zasu je wurin boka,Har an yashe kusan rabinsu,wasu mutanen dai ba imani aransu,ɗaya daga cikin halin ɗan adam kenan,Duk yadda take da hayaam same parents,Amma harta fara tunanin guduwa ta barta a asibitin saboda gudun kar su talauta ta,Kuma ta yanke shawarar zata yi ma Abra magana tazo su tafi wurin bokan tare da ita,Tunda ita hayaam ta gama lalacewa,babu wani amfanin da zata yi mata,ƙarshe ma taja masu asara,yini tayi a asibitin tana zirga zirga,Yayin da zuciyarta ke saƙa mata,ta gudu tabar asibitin,tun da ta samu ta biya mata kuɗin aikin Can su ƙarata,
Har wuraren ƙarfe Goma na dare,lokacin an kammala yiwa hayaam aikin,Amma bata farfaɗo ba,tsayawa Aunty babba tayi abakin ƙopar shiga ɗakin tana kallon hayaam dake kwance,hancinta na sanye da Oxygen,
Komawa tayi saman waiting seat din,inda tabar handbag ɗinta,ɗaukar jakar tayi ta buɗe ta,biro ta curo tare da memo,aza takardar tayi saman kujerar sannan ta soma rubutu Kamar haka
_Hayaam sae dai kiyi haƙuri,Wlh bazan iya cigaba da zama acikin asibitin nan ba,duk laifinki ne,Sai da na gargaɗeki akan karki kuskura ki ƙara kula wani ɗa namiji,amma da yake ke karyace ba'a raba ki da maza,Gashi nan kin jawowa kanki wanda yafi ƙarfinki,Ya gama dake yayi maki kankat,babu abunda yayi saura ajikinki balle har insa ran zakiyi mun amfani,Shiyasa na yanke shawarar zanyi ma Abra magana,zamuje wurin bokan tare da ita,Don bazan bari burina yaƙi cika ba har su Amani suyi nasara,In dana gode ma Allah bake kaɗai bace ƙanwar da nake da ita ba,Wlh dana ji kunya_
Tana kammala rubuta short note ɗin,Ta ɗauki handbag ɗinta,Sannan ta shiga cikin ɗakin da aka kwantar da hayaam ɗin,A gefenta ta ajiye wasiƙar,Sannan ta curo bandir ɗin kuɗi dubu hamsin ta ajiye mata a gefenta,a hankali ta furta Allah ya baki lafiya hayaam,Idan kuma kin riga mu gidan Gaskiya,Allah ya jiƙanki da rahama,
Tana kai ƙarshen maganar,da sauri ta juya tabar ɗakin,batare da 6ata lokaci ba,ta gudu tabar asibitin,
Rayuwa kenan,
*Boss Bature*
❤🤍❤
Tunda sanyin safiya ringing ɗin wayarta ya farkar da ita daga bacci,cikin bacci takai hannu tana laluban wayar harta samu ta cafkota,janyota tayi cikin bargon tare da buɗe idanunta masu ɗauke da bacci,Sunan Mommy Azeema ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,da sauri ta miƙe daga zaune,har time ɗin doguwar rigar jiyace a jikinta pink ɗin nan,picking call ɗin tayi ta kara wayar a kunnanta,
"Assalamu alaikum,"
On the other hand Aunty Azeema tace"Babyn Rafayet,kin tashi lafiya,"
Murmushi sehrish ta ɗan yi tare da cewa"lafiya qalou Alhamdulillah,"
"Yawwa my Daughter,dama na kira ne about abunda ya faru a tsakaninki da Rafayet,"
Natsuwa Sehrish tayi tana sauraronta
Ci gaba da magana tayi,"Jiya na hana ki bashi haƙuri,Saboda nasan cewa yana cikin fushi,kuma haɗari ne ki tunkareshi a wannan lokacin,kafin nan abunda nakeso in sanar dake,duk yadda kike tunanin rafayet ba haka yake ba,mutunne shi mai ƙyanƙyami sosai,kuma yana da zuciya shiyasa a lokacin ranshi ya 6aci ne sosai,har yayi yunƙurin bugunki,kinsan in ran mutun ya 6aci zai iya aikata komai ba'a hayyacinshi ba,sae yadawo cikin hankalinshi kuma yazo yana danasani,Akwai ire irensu,Ni nasan ba ason ranshi yayi maki hakan ba,don ba halinshi bane wulaƙanta mace,Zuciya ce ta fisge shi har yayi wurgi dake,ya kuma yi yunƙurin marinki......"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar na wani lokaci kafin ta ɗaura da cewa"Kin riga da kin faɗi abunda ke cikin ranki ba'a hayyacinki ba,ina mai tabbatar maki da cewar yanzu zai yi ƙoƙarin gyara mu'amularshi dake ne,Saboda ki daina yi mashi kallon mugu,Amma fa idan har kina son hakan ta faru dole sai kinje kin bashi haƙuri,sai daga baya na zauna nayi wani tunani,muddin baki bashi haƙuri ba,to akwai gagarumar matsala,tunda bai fara sonki ba,zai iya aikata komai daga ciki hada divorce tun kafin ma lokacin ya cika kin ga mu kuma ba haka muke so ba,Kuma idan kin bashi haƙuri ba hakan yana nufin cewa kin zubda ajinki bane,Darajarki zata ƙara daukaka a wurinshi,zai san cewa tabbas kina da hankali sosai tunda har kinsan kiyi laifi kuma ki nemi yafiya,kawai abunda nake so dake koda kinje bashi haƙuri karki nuna cewa ba'a hayyacinki kikayi maganar ba,"
Zuru sehrish tayi tana sauraronta,hankalinta yayi mugun tashi,Shin ta yaya zata tunkari Sgr da sunan zata bashi haƙuri?
"Aunty azeema,still akwai matsala,Babban yaya ya hanani zuwa part ɗinshi fa,saboda period ɗin da nake yi,Nasan idan ya ganni zai tuna da jinin da ya gani ajikin wandona ƙarshema yayi mun korar kare in bai bugeni ba,"muryarta tamkar zata yi kuka haka tayi maganar,
"Kada ki damu da wannan,In sha Allah babu abunda zai faru dake,sannan idan zaki je part ɗin nashi,ki gyara jikin naki sosai,Kuma ki shafe shi da turare"
Gyaɗa kai kawai tayi tare da cewa"Shikenan zanje in sha Allah,duk yadda mukayi dashi zan sanar maki,"
"Okey,saina ji ki,"
Tayi rejecting kiran,Ajiye wayar sehrish tayi saman gadon,Saukkowa tayi tare da nufar toilet ta shiga,Cikin mintina tayi wanka ta fito jikinta sanye da undy taja shi saman ƙirjinta,hannunta ruƙe da Short towel,Goge ruwan jikinta tayi dashi,bayan ta kammala,ta zauna gaban mirror tana shafa body cream ɗinta,Bayan ta gama ta shafa powder afuskarta,tare da murza man baki,Comb ta ɗauka tana sharce gashin kanta,
Turo kopar akayi,ta cikin mirror ta kalli wurin ƙopar don taga wanene,Jahad ce ta shigo hannunta ɗauke da plate meat balls ne aciki tare da Cup na coffee,
"Allah yasa nawa ne,"acewar Sehrish,
Murmushi jahad ta saki tare da cewa"Naki ne mana,nayi tunanin ma baki tashi daga bacci ba," tayi maganar tare da nufar wurin mirror ɗin ta tsaya,hannu tasa ta ɗauki meat ball din guda daya tace"Buɗe bakinki in saka maki,kiji idan yayi daɗi,"
Buɗe baki Sehrish tayi,Jahad ta tura mata shi cikin bakinta,taunarshi ta shiga yi tana jinjina kai alamar daɗinshi yana kai mata karo,
"Baby junaid nayi mawa,Ya kika ji ɗanɗanon"?
.Sehrish tace"Bangane ba,wani junaid ɗin bayan basu nan?ko kin manta ne"?
Jahad tace"Ae munyi waya dashi,Ya sanar dani cewa,Yau ko gobe zasu dawo,Amma basu duka ba,Shi dai yace bazai iya jure rashina ba,In ma basu dawo dashi ba,ko a ƙafa ne sai ya tako,"
..fashewa da dariya Sehrish tayi,itama jahad ɗin dariyar ce akan fuskarta,
"Gaskiya junaid na dabanne,yaci sunanshi Romeo,ga kuma juliet ɗinshi tsaye agabana,"
Tayi maganar tana nuna Jahad dake atsaye,
Murmushi jahad ta saki tare da cewa"Oh Ni sehrish,Wlh bansan ya zamu qare da junaid ba,idan munyi aure,Kina ganinshi ɗan ustazi ko,ba ƙaramin jarababbe bane,"
Sehrish tace"gaskiya sai kin jure don kula da junaid ba abu bane mai sauki,a kwanakin baya can da jimawa,lokacin daya gane cewa ni mace ce,Mun ta6a yi dashi zamu haɗu a garden,Ni kuma na manta,kinsan Allah tun wurin magrib junaid ya zauna a garden ɗin nan yana jiran zuwana,maimakon da ya ji ni shiru ya dawo cikin gida,sae yaƙi shigowa saboda munyi alkawarin haɗuwa dashi,Ni kuma na manta,ɗan tahalikin nan,tsakar dare akayi ta nemanshi aka rasa,ashe yana can garden yana jirana,ga asthma ɗinshi ta tashi,da ace ban tuna ba naje wurin nan ba,da Allah kaɗae yasan abunda zai faru dashi....."
Jin wannan maganar ba ƙaramin tayarwa jahad da hankali tayi ba,
"Kice Majnun zan aura ba Romeo ba,junaid bashi da hankali wlh,"acewar jahad,
Sehrish tace"yana da hankali mana,Junaid yana da mutunci sosai,ya kyautatamun sosai,bazan ta6a mantawa da halaccin da yayi mun ba,ina taya ki murna jahad,idan har kika auri junaid,babu ke babu yin aikin wahala,zan so naga rayuwar aurenku,tamkar comedy haka zata kasance,Zaki samu nishaɗi sosai,"
Ba ƙaramin farin ciki jahad taji ba,sae faman sakin murmushi takeyi,
Hannu sehrish tasa tare da ɗaukar cup ta kaishi bakinta tana kur6ar coffee,sae da ta shanye sannan taci gaba da ɗaukar Meatballs ɗin tana jefawa a bakinta,Duk jahad na atsaye ta ruƙe mata plate ɗin,
"ki zauna mana,ƙafafunki basu ciwo ne"?
"A'a,So nake in koma kitchen,Ina taya Aunty azmee aikin gida ne,"
"Hosana fa?tunda mukayi sallar Asuba,dana koma bacci ban ganta ba lokacin dana farka,"tayi maganar a yayin da takai hannu gaban mirror,ta yago tissue tana goge bakinta,
Jahad tace"Tana a dining,kinsan ta bata gajiya da ci,Ae ina tausayin Ya Omar,Don hosana saita ƙarar mashi da duk wani tattalin arziƙin da yake dashi,Gashi don ubanta ko girki bata wani iya ba,ci kawai ta sani,"
Dariya Sehrish tayi sosai kafin tace"Sauƙinta ma,Ya Omar mutunne mai haƙuri,Kuma yana da kyakkyawar zuciya,Shi kaɗai ne zai iya control ɗinta,Amma fa zaiyi fama wlh,"tayi maganar tare da miƙewa ta koma gaban wardrobe,
Buɗewa tayi tana neman kayan da zata sanya ajikinta,
Suna cikin magana,Hosana ta faɗo ɗakin tana kuka,bakinta cunkushe da Donuts,Ga wani a hannunta ta ruƙo,ɗayan hannun na ruƙe da wayarta,
Juyowa sukayi atare suna kallonta,hankali atashe suka tunkareta har suna haɗa baki wurin cewa"Hosana,Me ya faru!me kikeyi ma kuka haka?Wani ne ya rasu"?
Ɗaga masu kai tayi alamar eh,
Gabansu ya faɗi rass,A sukwane suka kalli juna,kafin suka mayar da idanuwansu kanta,
"Hosana faɗamun!waye ya rasu!"jahad tayi maganar jikinta na kerma,
Sehrish tace"ki buɗe baki kiyi mana magana,ko wani ne bashi da lafiya,"?
Sae lokacin ta taune donut ɗin bakinta tana matsar kwalla tace"Yayi Hatsarin Mota ya mutu"!
Kallon juna sukayi atare kafin su kuma mayar da idanuwansu kanta,arazane suka haɗa baki wurin cewa"Wa?
..cusa donut ɗin hannunta tayi acikin bakinta,Cikin shessheƙar kuka tace"wani Mai yin comedy,Yanzu nake gani acikin wayata,yayi hatsarin mota ya rasu"
Sauke ajiyar zuciya su kayi atare,Duk atunaninsu wani ne ya rasu Cikin waɗanda suka tafi damaturu,
"Hosana ba kuka zakiyi mashi ba,Addu'a yakamata kiyi mashi don ita yake bukata,Allah ya jiƙanshi,Ya gafarta mashi zunubban shi,Allah yasa aljanna ce makomarshi,Amma idan kikayi mashi kuka to ke ba cikakkiyar masoyiyarshi bace,"
"Nadaina kukan,Idan nayi sallah zanyi mashi addu'a,"
ta ƙarasa maganar,tana cigaba da taunar donut ɗin dake a bakinta,sannan ta juya ta fuce daga ɗakin,
Jiki asanyaye Jahad ta koma gefen gadonsu ta zauna,Sehrish kuma ta koma wurin wadrobe ɗin,Tana ɗaukar kayan da zata sanya,
"Hosana ta tayar mun da hankalina sosai,Jikina duk yayi sanyi,"
"Kin gane wa take nufi ne"?sehrish tayi mata tambayar,ayayin da take zura skirt ajikinta,
"Kamal Aboki take nufi mana,Wanda yayi wannan comedy ɗin nan,na matar soja,yana rera waƙar india shi da wani,akwae ma wani wanda yake cewa gayuna kun ga Alert,su kuma sauran sai suce a'a,kin tuna shi"?
Shiru sehrish tayi tana ƙoƙarin tuna comedy ɗinsa,can tace"Nagane shi,ya iya comedy sosai,Na ta6a ganin video ɗinshi a wayar Amrish,dayake ita mayyar kallon Comedy ce,Ni kinsan bancika amfani da waya ba,"
Jahad tace"naji mutuwarshi sosai,ya tsaya mun araina,rayuwar kenan kana taka Allah yana nashi,shiyasa wasu mutanen in suna aikata abunda suka ga dama har mamaki suke bani,sun manta cewa duniyar nan ba wurin zama bane,Jin daɗinta ƙalilan ne,da zarar ka mutu za'a kai ka grave ɗinka,daga kai sai Halinka,mai kyau ne ko mara kyau,idan na tuna cewa zan mutu in bar duniyar nan,ko inaso ko banso sai inji komai ya fita raina,ina rage duk wani dogon burin da nake dashi akan duniyar nan,Kuma ina ƙara kusanta kaina wurin Allah,...'
Sehrish tace"Wata rana muma babu mu,masu karanta labarin ma babu su,Mai bada labarin ma babu ita,Allah yasa dae mu cika da kyau da imani"_
Jahad ta amsa mata da"Ameen" sannan ta miƙe tare da nufar ƙopar fita daga ɗakin tana cewa"Ni zan wuce wurin Aunty azmee,kada mu barta da aiki ita kaɗae,"
"Nima idan na kammala shiryawar zanzo na tayaku aikin"acewar sehrish,"
Shaf shaf ta kammala shirya kanta,Cikin Skirt red colour,Asymmetrical Yana da baza ajikinshi,Gaban skirt ɗin bai kai bayanshi tsayi ba,yayi matuƙar yi mata kyau,Halter shirt ta sanya ajikinta white colour tayi tighting ɗinta,Red & white abun ba'a magana,Takalma ta zura a ƙafarta t-strap yana da ɗan tsini amma ba sosai ba,Launin skirt ɗinta ne,komawa tayi gaban mirror ɗin,ta ɗauki kwalbar turarenta tabi jikinta ta feshe ko'ina,saƙo da lungu,nan take ƙamshin ya gauraye ko'ina,bata sanya mayafi akanta ba,sai gashin kanta da yayi mata rumfa abayanta,
Fitowa tayi daga ɗakin,ta shiga cikin palour bata samu kowa ba,Suna can cikin gidan suna gyare gyare,
Tunda ta hau saman staircases(matattakalar bene)gabanta ya shiga faɗuwa,lokacin da ta ƙarasa part ɗin nashi bata shiga daga ciki ba,
Gabanta sae faɗuwa yake yi rass rass!leƙawa tayi ciki babu kowa Sae dae kayan abincin nan daya ci,'
Runtse idanuwanta tayi tare da ɗaga hannayenta izuwa saitin fuskarta,
"Ya Allah Kana ganin baiwarka,acikin wani hali na firgici da tsoro,Allah ka tsare ni,Wllh idan naga ya nufo ni zai bugeni,Sae in watsa da gudu,Amma takalmana masu tsini ne,kada suja inyi tuntu6e in faɗi ƙasa,"
Dakatawa tayi da yin zancen zucin nata,Sannan ta ɗan buɗe idanuwanta tana ƙara leƙa cikin palourn nashi,
Jaraba yadda zata bashi haƙuri ta shiga yi,
_babban yaya,Am sorry bazan ƙara ba,nasan nayi maka laifi,amma banyi hakan da niyyar na 6ata maka rai ba,Ba yin kaina bane,kuma ba hali na bane,Allah shine shaidata,ni bana yi ma na gaba dani rashin kunya,tsautsayine kawai da ƙaddara,A iya nan zan tsaya na baka haƙuri,saboda ka hanani shiga part ɗinka,har saina kammala period ɗina,Shiyasa bazan samu damar shigowa daga ciki in baka haƙuri ba_
Tana cikin tsara yadda zata sanar dashi,Kwatsam taji ƙamshin turarensa acikin hancinta,gabanta ne ya faɗi Rasss!waro ido tayi waje,ta zazzaresu,hankalinta yayi mugun tashi,
Kasa juyawa tayi ta kalli bayanta,saboda tana da tabbacin cewar,SGR YANA TSAYE ABAYANTA!Ashe baya cikin part ɗin nasa,Tashin hankalin da ba'a sa mashi date! Ko ya sehrish zata ƙare!?
Sanƙamewa tayi a tsaye,ko motsi ta gaza yi,jira kawai take taji yayi wurgi da ita,
"Excuse me,"muryarshi ce ta katseta,jiki na rawa taja gefe guda,yayin da idanuwanta ke kallon ƙasa taƙi yarda ta ɗago balle har su haɗa ido dashi,jikinshi na sanye da kaftan shirt har guiwa tare da trouser ɗinta brown colour,ya saki sumar kanshi ta baya,wani irin daddaɗan ƙamshine ke fitowa daga jikinshi,Slowly ya wuce cikin palourn batare da ya kalleta ba,abun ya yi matuƙar bata mamaki,tayi tsammanin tashin farko zai daka mata tsawa ne ya shako wuyanta,Sae gashi ko kallon inda take bai yi ba,Wuri ya samu saman Sofa ya zauna,tare da jingina bayanshi a jikinta,
Tunani Sehrish ta shiga yi Ko ya ji abunda tace ko baiji ba Oho,Allah Wa'alamu,ranta ne ya bata cewar ta juya ta tafi kawai,tunda ba damar ta shiga ciki,ya riga da ya hanata,tana ƙoƙarin barin wurin,kwatsam taji yace"Zo nan,"
Rasss taji gabanta ya faɗi,nan take taji fitsari ya matseta,daƙyar ta daure ta cije,ta dake sannan ta juya ta shiga cikin palourn,nesa dashi ta tsaya,saboda gudun kar ya shaƙota,
Idanuwanshi na akan agogon hannunshi daya dafa sofa hand dashi,
"Laifin me na aikata maki,da har na cancanci a kira ni,da mara IMANI mara TAUSAYI"?he said calmly,
Wuƙi wuƙi sehrish tayi da ido,sae faman murza yatsun hannunta take yi,batasan amsar da zata bashi ba,
"Also,kinyi comparing ɗina da wannan fasiƙin mutumin,Why"?
Shiru tayi tana ta faman mazurai,
Miƙewa yayi daga zaunen da yake gadan gadan ya nufi wurinta,ja da baya Sehrish ta shiga yi tamkar ta watsa da gudu tabar falon sai dai ba dama,har saida suka ƙurewa bangon falon sannan ta tsaya,tare da ƙankame jikinta,tsoronta kada yace zai bugeta,
Rumfa yayi mata da faffaɗan ƙirjinshi,duk tabi tasha jinin jikinta,Acikin zuciyarta sae faman ambaton La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin takeyi,gaba ɗaya ƙamshin turaren jikinshi ya hanata sukuni,ga fargabar da ta shiga,
"look at my face!nayi maki kama da mara tausayi,Mara imani"? Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,dakyar ta iya buɗe baki tace"A'a,“
"But Why u said so"?
Girgiza kai ta shiga yi,batare da ta furta komai ba,
"Shekarunki nawa"?
Muryarta na kerma tace"Na shiga sha takwas,"
Gwauron numfashi ya saki tare da zura hannunshi na dama cikin sumar kanshi a hankali ya furta"Ya Allah"!abun yayi mashi ciwo,ƙaramar yarinya na so ta caja mashi kwalwa,
Zame hannun yayi daga cikin sumar,tare da dafe bangon da tafin hannun,
"In my life,Wata ƴa mace bata ta6a gigin gaya mun magana ido cikin ido ba,batare jin shakkata ba,Sae ke,"yayi maganar yana nuna ta from head to toe,
Hankalin Sehrish yayi mugun tashi,Hukuncin da zai yanke mata kawai take jira,"
"A ina kika samu ƙwarin guiwar yin hakan"?yayi tambayar yana kallon fuskarta,
Shiru tayi,tana faman haɗiyar yawu,
Jinjina kanshi yayi tare da ja da baya ya juya,Saman sofa ya koma ya zauna,
"Come close"ya furta hakan yana nuna mata gefen table ɗin dake agabanshi,
A hankali ta tako tazo gabanshi ta tsaya,sae lokacin ta ɗan saci kallon fuskarshi,karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna,irin kallon da taga yanayi mata ne yasa tayi saurin duƙar da kanta ƙasa,ta ƙurawa takalman ƙafarta ido,
"Don't judge me,till u know me well,"
Jinjina kanta tayi,batare da ta ɗago ba,
"Idan har akwai abunda nake maki,Wanda yasa kike yi mun kallon wicked,mara tausayi mara Imani,lemme know,"
Da sauri tace"babu komai,"
"I don't trust u,If u can't say it,ki rubuta mun a Text message"
Abun yayi matuƙar ɗaure mata kai,yadda tayi tsammani ba haka ta gani ba,kokonto ta shiga yi anya Sgr ɗin da ta sani ne kuwa?kodae mafarki take yi ne,ta kasa yarda cewa da gaske ne shi yake yi mata,
A hankali ta furta mashi toh,
Juyawa tayi ta kama hanyar fita daga falon,tafiya take yi tana wasi wasi acikin zuciyarta,
"Idan ina takura maki ne,Remain just 2 months na bar ƙasar,Zan sallame ki ne,kiyi rayuwarki kamar yadda kika saba,".
dakatawa tayi da yin tafiyar ta ɗan juya tare da kallonshi,
ba ita yake kallo ba,idanuwanshi na a lumshe,ci gaba da magana yayi"Ki dawo ki ci gaba,da yin aikin ki a part ɗina,"
Tayi matuƙar yin mamakin abunda yace mata,hatta kalamansa ya tausasasu bakamar yadda yake yi mata magana ba ada,
"Am waiting for my breakfast,then bedroom ɗina yana buƙatar gyara,"
"Amma ka hanani yin aiki a part ɗinka ayanzu,"
"Nayi cancelling,"
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke,ta wani 6angaren taji daɗi sosai,duk da bata ji daɗin kalaman da ta faɗa mashi ba a jiyan nan,da alama sun ta6a mashi zuciyarshi sosai,
Komawa cikin falon tayi,gaban table ɗin sa taje,ta kwashe ledojin nan da aka kawo mashi na restaurant,
Sannan ta juya ta nufi ƙopar fita daga falon,tana tafiya tana waiwayenshi har wani ƙara leƙen fuskarshi takeyi,Saboda abun ya ɗaure mata kai sosai,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Batare da 6ata lokaci ba,ta shirya mashi breakfast ɗinshi,takai mashi a falonsa,yadda tabarshi haka ta same shi a zaune,Sae da tayi serving ɗinshi ya ci ya ƙoshi,Sannan ta wuce bedroom ɗinshi,Ta shiga gyara mashi,lokacin da ta kammala gyara Bedroom ɗinsa da Toilet,ta fito palourn, Komawa cikin bedroom ɗin yayi after some minutes ya fito jikinshi sanye da trouser na army tare da shirt,tana cikin gyaran yazo ya wuce ta,Gyara palourn tayi ko'ina yayi fess sae ƙamshi dake ta tashi,turo mashi ƙopar falon ta ɗan yi,Sannan ta saukko down da sauri ta wuce bedroom ɗinsu jiki na rawa,Don a ƙagare take da ta sanar Wa Aunty Azeema,
Tura ƙopar ɗakin tayi tare da sa ƙafa ta shiga ciki,jahad ce kwance saman gadon Kunnanta manne da waya,suna waya da junaid,juyowa ta ɗan yi tare da kallon ƙopar don taga wanene ya shigo,Ganin Sehrish yasa ta mayar da kanta inda take fuskanta taci gaba da yin wayar,
Wayarta dake ajiye saman drawer ta dauko,contact ta shiga ta lalubo layin hajiya Azeema ta danna mata kira,Wayar na shiga ta ɗaga kiran ,
"Daughter,ya ake ciki ne?tun ɗazu nake tasa ran ganin kiran ki,"Aunty Azeema tace,
Murmushi sehrish ta ɗan saki tare da cewa"Yau babban yaya yayi matuƙar bani mamaki,Abun da ban ta6a tsammani ba,'_
"har na ƙosa naji meya faru,ae tunda naji muryarki,nasan cewa an dace,halan bai yi maki komai ba"?
"Baiyi mun komai ba,ƙarshe ma cewa yayi in rubuta mashi duk wani abu da yake yi mun wanda bana so in tura mashi ta message da ya tambaye ni abunda yake man nace ba komae,Sannan kuma yace in ci gaba da aiki a part ɗinsa,"ta ɗan dakata da yin maganar,tana jiran jin me Auntyn zata ce,Sautin dariyarta tajiyo ta cikin wayar,
"Dama sae da raina ya bani cewar Rafayet,bazai yi maki komai ba,Gaskiya naji daɗin hakan sosai,wannan ma wani matakin nasarar ne,Yanzu me kika yanke shawara akai"?
Sehrish tace"game da me kenan"?
"Ina nufin me zaki rubuta mashi"
"Nikaina,bansan me zan rubuta mashi ba,amma ki bani shawara,"ta ƙarasa maganar tare da samun wuri,saman drawer ɗin ta zauna,tana ci gaba da sauraronta,
"abunda nakeso dake,kada ki ji tsoron komai,ki natsu ki kwantar da hankalinki,ki rubuta mashi duk wani abu da kika sani wanda baki so yana yi maki,wannan dama ce kika samu,"_
Ajiyar zuciya ta sauke tare da gyaɗa kai tace"shikenan,Zan rubuta mashi yanzu,"
"Yawwa my daughter,take care of ur self for me,Sai kinji daga gare ni,"
Daga nan sukayi sallama tayi rejecting kiran,
Juyawa tayi gefen hagunta tare da kallon jahad tace"Juliet,inason magana dake,idan kin kammala wayar,"
Juyowa jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Ae mun kammala yin wayar ma tun ɗazu,wayarce kawai ban cire a kunne na ba,saboda ban gajiya da jin Voice ɗinshi,Expecially idan yanayi Mun shagawa6ar nan tashi,kamar in janyoshi ta cikin wayar,in manna mashi kiss,"
Fashewa Sehrish tayi da dariya,gami da girgiza kai,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Gaskiya ne,Juliet Matar Romeo,abun naku azimunne,"ta ƙarasa maganar a yayin da take komawa gefen gadon ta zauna,kafin ta kuma cewa"Am looking for ur advise,My lovely sis,"jin haka yasa jahad ta miƙe zaune daga kwancen da take,ta jingina bayanta jikin head board ɗin gadon,tana facing sehrish sannan tace"Shawarar me kike so in baki ne"?
Calmly sehrish tace"yau naje bama babban yaya haƙuri,Kinsan meya faru"?
Hankali aɗan tashe jahad tace"Sae kin faɗa,"
Murmushi sehrish ta ɗan saki kafin ta cigaba da cewa"bai yi mun komai ba,ko yatsa bai ɗaga mun ba,Yanzu haka ma zancen da nake maki,Yace na rubuta mashi text message na duk abunda banso yana yi mun,"_
Wani irin ihun farin ciki jahad ta saki tare da furta"Yess!yess!"da alama abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
"Wlh naji daɗi sosai!dama nifa koda nace kada kije ki bashi haƙuri saboda tsoran karya Bugeki ne,Amma yanzu Alhamdulillah,komai ya wuce,gashi har an samu ci gaba,"
"Yanzu me kike ganin ya dace na rubuta mashi?Mommy azeema tace kada naji tsoran komai na rubuta duk abunda nake so ya daina yi mun,"
Murmushi jahad tayi,tare da cewa"ta kwana gidan sauƙi,Ae yanzun nan zamu tsara mashi text message,Amma inaga kamar mu rubuta mashi ta whatsapp ko?zaifi tsayi rubutun ba kamar na text message ba,
Sehrish tace"Ni damuwata ma,kada musha wahalar rubutawa yaƙi karantawa,Saboda na ta6a tura mashi message,bai rubutomin reply ba,"
Jahad tace"kinsan shi mutunne mai jama'a,mutun mai farin jini irinshi bazai rasa dubban saƙonnin Masoyanshi ba,Shawarar da zan baki shine,Idan kin rubuta mashi message ɗin saiki jaraba kiran layinshi,idan ya ɗaga saiki sanar dashi cewa kin tura mashi,"
Jinjina kai Sehrish tayi,"kin kawo shawara mai kyau,"
"Yanzu dame dame Yake yi maki wanda bakya so"?Jahad tayi tambayar tana kallon fuskar Sehrish dake kallonta,
"Abu na farko,nidai bana son wannan tsawar da yake yi mun,na biyu bana son tsallan kwaɗin da yake sanya ni don ba ƙaramar wahala nake sha ba duk in nayi shi,Na uku kuma,banason yana hana ni zuwa part ɗinshi da make-up a fuskata....,"haka Sehrish ta shiga lissafa mata abubuwan da bataso,Bakomai yafi bama jahad dariya ba,fa ce Make-up da sehrish tace bata so yana hanata,cike da zolaya tace"in banda abunki,bashi kike yiwa kwalliyar ba?kuma yace bayaso,sae ki daina kawai,Kinsan ba ko wani namiji bane keson wannan ƙyaleƙyalen namu na mata,wani namijin ma baison ƙamshin turare,kowa fa da irin nashi ra'ayin,"
Harara sehrish ta ɗan wurga mata tare da cewa"Amma lokacin baya before wedding ɗinmu,ina yin make-up in shiga part ɗinsa bai ta6a hanani ba,sae bayan da aka ɗaura auren,"
Jahad tace"saboda yanzu ne yake da cikakken iko akan ki,Shiyasa ya hana ki,'
Ta6e baki sehrish tayi kafin ta mayar da idanuwanta kan wayar,Ta shiga whatsapp ɗinta,Contact ɗinsa ta nemo wanda tayi mashi saving da *My Boss man*,ta shiga Cikin Chat ɗinsa,sau ɗaya ta ta6a yi mashi sallama,bai duba ba,"
A hankali ta soma rubuta mashi saƙon,
"Sehrish,me zai hanaki ki ɗan rubuta mashi cewa,ya dinga sakar maki fuska,koda bazaiyi murmushi ba"?
Wani bazawarin kallo sehrish ta jefa ma Jahad,a ƙule tace"idan ya tashi cin ubana,ae baki a kusa balle ki kawo min agaji,Ni na isa in sanya wannan fuskar tashi,ta dinga yi mun murmushi,?kina ganin ko su Abba in yana tare dasu baya murmushi,shifa naturally haka face ɗinshi take,a tamke,"
Dariya jahad tayi tare da kai hannu ta dafa shoulder ɗin Sehrish "Kada ki damu My own sister,Very soon fuskar yaya rafayet,zata koma kullum a washe,amma fa sai ranar da kika haifa mashi baby,"
Fashewa tayi da dariya,jin abunda jahad tace mata,
Can kuma tace"Anya,Babban yaya yana son ƴa'ƴa kuwa?irinsu fa kamar basu damu da haihuwa ba,yawanci ma basu son matansu su haihu,Akwai wani American film dana ta6a kallo,Bature ne mutumin har yakai shekara 80 bai ta6a haihuwa ba,Saboda yana da wani ɗan karensa,shiya ruƙa a matsayin ɗansa,yawanci kuma zaki ga basu son haihuwa da yawa,ɗaya zuwa biyu,sae kiga sun kwallafa rai akan ƴa'ƴan nan,"
Jahad tace"Amma shi Half cast ne!(ruwa biyu)ba dole bane komai ace irin nasu ya ɗauko,Duk da yafi ƙarfi ta 6angaren Mommynsu,kuma acan ya taso duk ɗabi'unsa da halayansa,in kika lura irin nasu ne,Amma daga gani kamar zaiso ƴan babies,ke in ma baiso,to akan ki zai fara son ƴa'ƴa,"ta ƙarasa maganar tana dariya
Murmushi sehrish tayi a yayin da idanuwanta ke akan screen ɗin wayarta,har tayi nisa cikin rubuta mashi saƙon,
"Jahad,bansan meyasa kikeso in samu ciki ba,kullum baki da zance sai na in samu ciki,in haifa ma babban yaya baby,bayan kinsan cewa nan da wani ɗan lokaci auren zai mutu,"tayi maganar muryarta a sanyaye,
Jahad tace"saboda na ta6a yin mafarki ne,kuma acikin mafarkin na ganki da ƙaton ciki,sai gashi kuma kin haihu,Kinsan me?tayi tambayar batare da tajira amsar sehrish ɗin ba taci gaba da cewa"babyn da kika haifa Triplets ne kuma dukkansu maza ne,Ƙwayar idonsu blue ce kalar ta babban yayanmu,gashin kansu ma kwantacce ne irin nashi,hasken fatarsu da komi irin nashi ne.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda jin saukar pillow da tayi asaman fuskarta,wanda Sehrish ta jefa mata shi,
"Maƙaryaciya kawai,daga jin wannan ƙirƙirarran labari ne,babu wani mafarkin da kika yi,"_
Dariya sosai sukayi,ba ƙaramin nishaɗi suka samu ba
Bayan ta kammala rubuta mashi saƙon,Miƙa ma jahad wayar tayi don ta duba ta gani in akwai abunda ya dace su ƙara,Kar6ar wayar jahad tayi tana karanta message ɗin har yazo karshe,Sannan tace"komai yayi yadda akeso,tura mashi sakon sai ki kirashi,"
Tura saƙon sehrish tayi bayan ta kunna WI-FI ɗinta,nan take saƙon ya isar mashi,phone call ta shiga tare da danna mashi kira,
Kusan sau biyar tana kira ba'ayi picking ba,
Jahad tace"mu haƙura zuwa anjima yanzu haka suna aikine,"
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 6 na marece,wata danƙareriyar mota tayi parking a cikin wani katafaren hotel,a parking space motar ta tsaya,jim kaɗan wata matashiyar budurwa ta fito daga cikin motar,jikinta na sanye da riga bubu ta material,ƙafarta kuwa na sanye cikin high hills,ta coge ɗaurin kallabin nan na rashin ɗa'a,Sae faman taunar cingam takeyi abakinta,
Hannunta na ruƙe da ƴar purse ɗinta,ta sagala mayafin asaman kafadarta,
....fitowa wani matashi yayi daga gaban motar,daga ganinsa zakasan cewa ba ƙaramin shege bane,kuma tantirin ɗan iska,
Zagayawa yayi tare da buɗe boot ɗin motar ya ɗauko mata trolley ɗin kayanta,sannan ya kalleta tare da cewa"Babe,Mu shiga ciki ko?in ɗan taka maki"
Murmushi Abrah,ta saki tare da nuna mashi hanya tace"bismillah,"gaba tayi yabi bayanta,suna tafiya yana yi mata sambatu,"Gaskiya zanyi kewarki sosai baby,bansan ya rayuwata zaka kasance ba,idan babu ke,zan zama tamkar maraya,"_
Abra tace"hmm,dama ka daina yi mun wannan daɗin bakin naka wlh,Don na sanka,mayen mata ne,Allah kaɗai yasan yawan matan da kake mu'amala dasu,Ni bansan ma tanawa bace,"_
"Subhanallah,Zargina kikeyi ma kenan?babu kyaufa,"
"Ba zarginka nake yi ba,zahiran na gani ae,"suna magana suna tafiya har suka shiga cikin reception,mutane ne ke ta safa da marwa a wurin,Batare da sun sha wahala ba,ta hango Aunty babba tana tunkarosu,Fuskar nan aɗaure babu annuri,Amma tana hango saurayin da Abra tazo dashi,nan take ta ɗan saki fuskarta,ƙarasowa tayi wurinsu,
"Sannunku da zuwa ya gajiyar tafiya,"
Saurayin ya amsa mata"Alhamdulillah,Mun same ku lafiya,"
"Lafiya lou,"kafin ta mayar da idonta kan abra tace"Wanene wannan kuma?yakamata a gabatar mun dashi,ko da yake bari mu shiga daga ciki,'tayi maganar tana yi masu nuni da hannunta,
Saurayin yace"kash,bazan samu shiga ciki ba,ina sauri ne zan wuce wurin wani uncle ɗina dake anan,Urgently yake nemana,"
Aunty babba tace"Amma banji dadi ba,duk irin wannan ɗawainiyar da kayi mana,bazaka shigo daga ciki ba ka huta,ko lemu ne ka ɗan sha,'
"Kada ki damu Aunty,Idan kuka dawo daga tafiyar zanzo ne sai mu gaisa dakyau,"
"Aunty wannan shine Bobby ɗin da nake baki labarinshi,Yana da kirki sosai,Saboda yana kyautatamun,"ta ƙarasa maganar,fuskarta dauke da murmushi,
Aunty babba tace"Ma sha Allah,naji daɗin ganinka sosai,Allah dae ya nuna mana ranar aurenku,Musha biki,'
Murmushi ya saki yana faman shafa keyarshi da hannunshi,
"Bari mu shiga daga ciki,Sae munyi waya,"acewar Abra,
"Okey babe,ki kulamun da kanki,Sae kinga saƙona,"
Ya ƙarasa maganar tare da juyawa yabar reception din,Aunty babba tayi gaba Abra tabi bayanta,Har izuwa cikin ɗakin da ta kama,
Suna shiga cikin ɗakin abra ta saki trolley din kayan,ta faɗa saman gadon ta kwanta tana faman sauke ajiyar zuciya,
Daga gefen gadon Aunty babba ta zauna,tare da kallonta tace"kun sha tafiya,toh ya ku ka baro su mammyn'?
"Tana can,rai hannun Allah,ae na faɗa maki cewa bata da lafiya,Amma da sauƙi dae,tunda tana ɗan mikewa har ma ta zauna,Matsalar dae babu mai kula da ita,Shima Abie ya tattara yana shi yana shi yabar gidan,yanzu ita kaɗai ce acikin gidan,bansan ya zata ƙare ba,"hankalinta kwance take yin maganar,
Shiru Aunty babba ta ɗan yi,batare da ta janye idanuwanta daga kan fuskar abra ba,
"Aunty kinyi shiru,ba kice komai ba?wai nikam Ina Aunty hayaam ne'?nayi tunanin zan ganku atare ne,kuma nayi mamakin ganinki a hotel"
Harara ta ɗan watsa mata tare da cewa"in ba a hotel ba,a ina kikeson ki ganni ne?Ko bakisan cewa aure na ya mutu ba"?
...ƙumshe dariya Abra tayi,
"Kiyi mai isarki lokacinki ne ƴar rainin hankali,Muna nan cikin tashin hankali,ke kina can kina holewarki,wato kin samu duniya ko"?
Turo baki abra tayi tana fadin"matsalar kenan fa,yanzu nasha wahalar tafiya,ko ruwa ban sha ba,Amma zaki fara yi mun faɗa,Allah in naji ban iyawa,sae dai ki neme ni ki rasa,"
Sakin baki Aunty babba tayi tana kallonta,kafin tace"lallaine wuyanki ya isa yanka,fiye da haka ma zaki iya faɗamun,"
murguɗa baki abra tayi tare da cewa"na tambaye ki Aunty hayaam amma baki ce komai ba,tana ina,"?
Ta6e baki Aunty babba tayi kafin tace"Ae hayaam ni kaina bansan inda take ba,kinsanta bata gajiya da yawo,yau kusan kwana uku banganta ba,sae dai ta kirani mu gaisa,Amma ni kona kirata a kashe nake samun wayarta,"
Saboda rashin tsoran Allah,Aunty babba ta zauna tana shirgawa Abra ƙarya,don tasan cewa muddin Abra taji cewa,hayaam na kwance gadon asibiti ba lafia,baza ta ta6a yarda suyi tafiyar nan da ita ba,Sai ta tsaya tayi jinyarta,kuma in taji cewar ta bar ƴar uwarta a asibiti babu mai kula da ita,to tabbas ranta zai 6aci sosai,"
"Kai Aunty hayaam,ita ma dae kamar wadda taci ƙafar kare,bata nan bata can,"
Aunty babba tace"Ni duk ba wannan ba,Kinsan dai dalilin dayasa nace kizo ko"?
"Eh nasani,"ta bata amsa,
"Yawwa,Jibi nakeso mu shirya mu tafi,lokacin kin huta sosai,"
Yatsina fuska Abra tayi,tana ɗan gatsina hanci tace"Oh ni,yanzu haka zamu kwasa mu tafi wurin boka har enugu,cikin dajin Allah,Kamar waɗanda basu da mafaɗi,Kuma dae babu tsoran Allah..... "
Tunkan ta ƙarasa maganar Aunty babba tace"Rufe mun baki,Uwar surutu sai kace aku,Duk ba don ku akeyi ba?don rayuwarku tayi kyau," fuskarta aɗaure tayi maganar,
Zumbura baki abra tayi,tare da yin ƙasa ƙasa da muryarta tace"mutun yayi sallar dare mana,ya roƙa wurin wanda ya halicce shi sai wani boka can"
"Me kikace"Aunty babba tayi tambayar tana kallonta,Don tajiyo ƙusƙus ɗin da take yi,
Abra tace"Ni Bance komai ba,idan ma nayi magana to akan abinci ne,yunwa nake ji,"ta ƙarasa maganar tana shafa stomach ɗinta,
"Okey,bari nayi mana order,sae muci atare,don nima banci komai ba,"
Wuraren ƙarfe 7,Motoci guda biyu suka shigo cikin gidan a jere,a lokacin Jahad da Sehrish suna a kitchen tare da Aunty azmee suna tayata aiki,Azmee na agaban gas cooker,Sehrish da jahad,suna yanke yanken kayan lambu,
Jin dirar motacin nan yasa Sehrish saurin cewa"Ga babban yaya nan ya ƙaraso gida,"
Jahad tace"Anya kuwa shi ne?Junaid fa ya sanar dani cewa yau ko gobe zasu dawo,Allah yasa su ne,kada abunda na haɗa mashi ya lalace,"
Murmushi sehrish ta saki,tana cewa"Mrs romeo,Ae koda bai dawo ba,mu zamu cinye kayan daɗin da kika haɗa mashi,".
Muryar azmee suka jiyo daga bayansu tana cewa"Nima hadani za'aci daɗin,"
Dariya su kayi gaba dayansu,
Jahad tace"idan zaki ci Aunty azmee babu damuwa,Amma Allah koda bai dawo yau ba,ƙwara na zuba shi a dustbin da dai inba su rishi suci"
Harara sehrish ta ɗan watsa mata da yake suna facing ɗin juna na,tace"saboda baƙin hali irin na ɗan adam,'
"Aunty azmee ina da tambaya dan Allah,"acewar jahad,
Azmee tace"Allah yasa na sani,"
Murmushi jahad ta yi tare da cewa"Tsakanin babban yaya da Junaid waya fi wani kyau,"
Har sai da gaban azmee ya faɗi rass,Saboda girman tambayar da tayi mata,jinjina kai tayi na wani lokaci kafin tace"tashin hankali,Kuma ni kike so in amsa maki tambayar,"
Jahad tace"Eh,saboda nasan kinsan menene kyau,zaki iya fadin wanda yafi kyau acikinsu,"
Sehrish tuni ta dakata da yankar lettuce ɗin da takeyi,hannunta ruke da wuqa,duk ta qagara taji amsar da azmee zata basu,
"Ni ko a school,ban ta6a haɗuwa da question mai wuyar Amsawa ba irin wannan,To ae dukkansu kyawawane na bugawa a jarida,Junaid kyau rafayet kyau,"
Dariya sukayi jin yadda azmee keta nanata maganar,da alama sun caza mata kai,
"Amma ni a ganina,kamar junaid yafi kyau,saboda shi fuskarshi kullum asake take,Kuma wannan murmushin nashi ba ƙaramin kyau yake ƙara mashi ba,"acewar Sehrish,
Jahad tace"Amma ae bai kai yaya rafayet tsayi ba,duk da shi ma dogone,kuma baida irin surar jikin babban yayan mu,"
Sehrish tace"Ae da ace shima junaid ɗin zai dinga motsa jiki,in a short time zaki ga ya koma kamar babban yayan mu,ae su maza daga sun fara ɗaga ƙarfe Jikinsu ke buɗewa,"
Azmee tace"hakane kema kince wani abu anan,Gaskiya dukkansu zan iya cewa babu wanda yafi wani kyau,idan don saboda murmushi zaisa junaid ya ɗare rafayet a kyau,to ae shima rafayet ɗin idan yayi murmushi sai kin kusa zaucewa,kilan bai ta6a yin murmushin bane kun gani,sannan kuma ga surar jiki ta ko'ina dae su duka biyun sai dai ace ma sha Allah..."zugudum sehrish tayi tana sauraron abunda azmee ke cewa,aranta tace"Kutmelesi,Su Aunty azmee har ansan su babban yaya nada kyawun sura,da kyakkyawan murmushi,ba dai kalle mun mijina takeyi ba,"ta ɗan yi maganar hada tamke fuska,can kuma ta fashe da dariya...,
Suna cikin tattaunawar nan,Suka jiyo Muryar Junaid yana sallama,aikuwa jiki na rawa jahad ta ajiye knife din dake hannunta,da gudun gaske ta fito daga kitchen din,
Yana a tsaye,jikinshi sanye da shadda brown colour,hannunshi ruke da trolley,fuskar nan ɗauke da ƙayataccen murmushi,duk a tunaninta shi kaɗai ne,hakan yasa ta nufe shi da gudu zata rungume shi,ƙiris ya rage ta ƙarasa,Sae ga Marshal Omar da Uncle abusufyan sun shigo,da sauri taci burki,tana faman sauke ajiyar zuciya,Fashewa junaid yayi da dariya yana kallonta,saboda ya gane abunda taso tayi,Su uncle sunyi mashi buƙulu,
.....hannu tasa ta rufe fuskarta,tana dariya,
Murmushi marshal ya saki,haka shima abusufyan ɗin,Jahad sarkin kunya,
Fitowa sehrish tayi daga cikin kitchen ɗin,fuskarta ɗauke da murmushi,da sauri ta ƙarasa wurin abusufyan,hugging ɗinshi tayi tare da cewa"sannu da dawowa Daddy,ya gajiyar tafiya,"?ta ƙarasa maganar tare da ɗagowa daga jikinshi,
Hannu yasa tare da shafa fuskarta yace"lafiyalou My Daughter fatan na same ku lafiya,"yayi maganar yana miƙa ma jahad hannu,cike da jin kunya ta ƙarasa wurinshi,ya rungumota ajikinshi,
Marshal Omar yace"Oh ni,babu mai yin hugging dina,daddynku kawai kuka sani,babu komai nasan da hosana na nan,da gudu zata bani hug" dariya sukayi gaba ɗayansu,haɗa baki sukayi wurin gaishe dashi,Ya amsa masu fuskarshi a sake,
"Lah ya Omar,"muryar hosana ce ta katse su,ɗagowa su kayi gaba ɗaya suna kallonta,Da alama daga bacci ta taso,sae faman lumshe ido takeyi,
Kai tsaye ta tunkarosu,kamar yadda yayi tsammani,ko Daddynsu bata runguma ba,wurinshi ta wuce,ta rungumeshi tare da kwantar da kanta saman wide chest ɗinshi,'
Jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"Hosana ko kallo ban isheki ba ko?,hankalinki na akan Omar," Yayi maganar yana kallonta,
Murmushi ta saki tare da ɗagowa daga jikin Omar ta koma wurinshi,zata rungumo shi da sauri yaja da baya yana cewa"bana so,babu ruwana dake,ki koma wurin Omar ɗin,Ae ni baki damu dani ba,burina kawai in dawo gida don saboda ke,Amma shine kika watsa mun ƙasa a ido,"
Dariya suka shiga yi gaba dayansu,hosana kuwa bubbuga ƙafa ta shiga yi muryarta tamkar zata yi kuka tace"pls daddy,let me hug u,wlh nayi missing ɗinka sosai,kawai dae nayi alƙwarin cewa,zan fara tarbar Ya Omar ne kafin kai,kuma banso in karya alƙawarin dana ɗauka,"
Abusufyan yace"ae gashinan ko?Dama na yafe mashi ke,Ni ga ƴan tagwaye na nan,su da suka damu dani,'yayi maganar yana nuna su sehrish,
Zumbura baki tashiga yi,tana murmura masu baki,
Ruko hannun Omar tayi tare da jan shi tace"Mu tafi ya Omar,kayi wanka kaci abinci,Sannan ka kwanta ka huta,"Bin bayanta Omar yayi fuskarshi ɗauke da Murmushi,
Girgiza kai Abusufyan yayi tare da cewa"Allah ya shirya min ke Hosana,Abun naki sai addu'a,"
Ya ƙarasa maganar tare da ruƙo hannayensu Sehrish suka wuce cikin palourn,sun ɗan zauna anan suka ƙara gaisawa da daddyn nasu kafin daga bisani,suka barshi ya wuce bedroom ɗinshi don ya huta,
Wuraren ƙarfe 12 na dare,lokacin har sun kammala dinner ɗinsu tuni,Sun koma cikin bedroom ɗinsu,batare da 6ata lokaci ba,Su ka shirya cikin kayan baccinsu,sun kwanta ajere cikin lallausan bargonsu,
Kwankwasa ƙopar ɗakinsu akayi kwankwan,
"Wanene"?jahad ce tayi tambayar,saboda itace ta rage idonta a buɗe,
"Zo ki buɗe mun kopa,"da sauri ta saukko daga saman gadon jin muryar junaid,
Hannu tasa tare da buɗe kopar,Yana tsaye cikin sleeping dress dinsa white colour,hannunshi ruƙe da Shopping bag,".
Junaid dama ba kayi bacci ba?tayi tambayar tana ƙare mashi kallo,sae hamma yake saki,
Ashagwa6a yace"Na fara bacci mana,Mommy azeema ce ta tashe ni,saboda kawai wannan saƙon na rishi da tace na kawo mata,"
Yayi maganar yana nuna mata ledar hannunshi,
"Eyya,Amma banji daɗi ba,but am sorry,kawo saƙon na ajiye mata,don har bacci ya ɗauketa,"
Miƙa matar bag din yayi,ta sanya hannu ta kar6a,sannan ta juya zata shiga ciki,da sauri ya ruƙo hannunta tare da janyota ta faɗo jikinshi,hugging ɗinta yayi tightly tare da cewa"I really missed u my Juliet,"
Lumshe ido jahad tayi tana shaƙar ƙamshin turaren jikinshi tace"I missed u too my Romeo,"_
Kiss ya manna mata asaman cheek dinta,sannan ya raba jikinta daga nashi,tare da juyawa yabar bedroom ɗin,
Har sai da ya 6ace ma ganinta,Sannan ta tura kopar tare da shigewa ciki,A gefen gadon daga ƙasa ta ajiye bag ɗin,batare da ta buɗe taga menene aciki ba,ta haye saman gadon ta kwanta fuskarta dauke da murmushi,
"Jahad har yanzu yaya rafayet bai dawo ba"!?
Muryar Sehrish ce ta katse ta,da sauri ta juya left hand ɗinta tana kallonta,a rufe ta samu idanuwanta tamkar mai yin bacci ashe likimo tayi,
"My own sis,ashe bakiyi bacci ba,"?
"Idona biyu jahad,baccin ne yaƙi zuwa,"
Jahad tace"Yakamata kiyi bacci,kinsan da anjima idan babban yaya ya dawo zai tashe ki ne,so it's better ki kwanta yanzu,ko kin samu bacci na minti 30,"
"Ae baccin ne yaƙi zuwa,"tayi maganar tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta,
"Wanene ya shigo ɗakin nan?ko daddy ne,"?
"Junaid ne,ya kawo saƙo yace naki ne,Inji Aunty azeema"jin haka yasa sehrish miƙewa daga zaune,tana faɗin"ina sakon yake,"
Hannu jahad tasa tare da ruƙo hannun bag ɗin,ta ɗago da ita,izuwa saman gadon ta miƙa ma Sehrish,hannu tasa ta kar6a,tare da ajiyeta agabanta,tana faman yin hamma,kamar mai jin yunwa,
Buɗe shopping bag ɗin tayi,tare da ɗan leƙa kanta tana kallon kwalaben dake acikinta tare da robobi,aranta tace"ko na menene wannan,bari dai na ajiyesu,zuwa gobe nasan zatayi mun bayani akansu,"ta ƙarasa maganar tare da matsawa ta ajiye bag ɗin saman side drawer,sam bata son bacci ya ɗauketa,saboda tasan cewa lokacin dawowarshi yayi harma ya wuce,jingina bayanta tayi ajikin head board din gadon,Sae faman yin hamma takeyi tana gyangyaɗi amma taƙi yarda bacci ya ɗauketa,tana yi tana kallon wall clock,kusan ƙarfe ɗaya,amma basu dawo cikin gidan ba,duk yadda taso ta hana bacci ɗaukarta,amma hakan ya faskara a zaune ta fara baccin,itama jahad tuni bacci yayi awon gaba da ita,Hosana dama tuntuni ta ƙundundune cikin bargo tana sharar baccinta,
A round 1:30 na dare,Motarsu ta shigo cikin gidan da gudun gaske ta shararo har izuwa parking space,tsayar da motar Armstrong yayi tare da fitowa,da hanzarinsa ya zagaya tare da buɗe mashi kopa,a hankali ya zuro da ƙafarshi,after some minutes ya ƙarasa fitowa daga cikinta,Hannunshi na'a dafe da forehead ɗinsa yayin da idanuwanshi ke a lumshe,da alama babu cikakkiyar lafiya atattare dashi,tun daga kan yadda yake fitar da numfashinsa,
"Sorry sir,idan ba damuwa zan iya taka maka,mu shiga daga ciki,naga kamar ba zaka iya ƙarasawa ba".
A hankali ya furta"don't worry ur self,Zan iya tafiya da kaina"yayi maganar tare da kama hanya ya wuce cikin gidan,tsayawa armstrong yayi yana kallonshi har saida yaga shigar shi kopar falon gidan,Sannan yabar wurin motar,
Babu kowa a main palour ɗin,dakyar yake tafiya har ya samu ya hau saman staircases ɗin,Ya wuce part ɗinsu,hannu yasa ya tura kopar,ya shiga daga ciki,Direct ya wuce bedroom ɗinshi,zame t-shirt ɗin dake ajikinshi yayi tare da yin wurgi da ita saman gadon,daƙyar yake fitar da numfashi mai hucin zafi,idanuwanshi kansu daƙyar yake iya buɗe su,.
Hannunshi yakai tare da ruƙo belt ɗin wandon jikinshi ya cireshi,ya duka ya cire takalmansa,sai da ya rage daga shi sae Short ajikinshi,yana ƙoƙarin zame safar ƙafarsa,kira ya shigo cikin wayarshi,hannu yakai tare da daukarta,inda ya ajiyeta saman side drawer dinshi,duba screen ɗin wayar yayi,da hidden number aka kirashi,Abun yayi matuƙar daure mashi kai,muddin aka kirashi da hidden number sai Ainihin sunan mai number ya bayyana,amma wannan kiran a haka ya shigo mashi,
Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnanshi,Shiru ba'ayi mashi magana ba,shima kuma bai tanka ba,yana ƙokarin rejecting kiran yaji shessheƙar kukan mace,kuka fa sosai tamkar zai fasa screen ɗin wayar,da sauri ya janye wayar daga kan kunnan shi ya zuba ma screen ɗin wayar ido yana kallonshi,cike da mamakin wacece wannan ta kirashi tana raira mashi kuka a irin wannan lokacin"? Rejecting kiran yayi,yana ƙoƙarin ajiye wayar,text message ya shigo wayarshi,on the top of the screen message din ya bayyana,
Karanta saƙon ya shiga yi kamar haka,
_Rafayet bazan ta6a bari na rasa ka ba,Zan iya yin komai akanka don na mallake ka,koda kuwa kisan kaine,Na jima da sha'awar son kasancewa tare da kai,alƙawarine wannan na ɗaukarwa kaina_
Bai damu da saƙon daya gani ba,Saboda yasha haɗuwa da ire-irensu,sun yi nacin har sun gaji sun daina,Amma wannan baisan dame tazo ba,hada ikirarin zata iya yin kisan kai akanshi,koma wacece wannan ba ƙaramar ƴar daba bace da alama,
wurgi yayi da wayar saman gadonshi,Sannan ya juya daƙyar yake ɗaga ƙafarshi har ya samu ya shige cikin toilet,
*Sehrish*
Firgit ta farka lokaci guda ta miƙe a hanzarce ta wurga idanuwanta kan agogo,ƙarfe kusan 2 na dare,durowa tayi daga saman gadon hankalinta aɗan tashe,sai da ta fara zuwa window ta leƙa taga Motarsu,sannan ta fito da sauri,riga da wandone ajikinta,kanta kuma na sanye da mayafi ta ɗaureshi amatsayin kallabi,tafiya takeyi tana sambatu ga bacci da bai bar idanuwanta ba,
Kitchen ta shiga,jim kaɗan ta fito hannunta ruƙe da tray,Coffee ne asaman shi tare da Fruit,tana ƙokarin hawa upstairs taji ance"Sannu da ƙoƙari," Cak ta tsaya da tafiya,yayin da zuciyarta tayi wani irin bugu ji kake rasss!,a hankali ta juya don taga wanene yayi mata maganar,Waro ido waje tayi ganin babu kowa a babban falon,kuma tabbas taji anyi mata magana,ranta ne ya bata cewa kodai kunnuwanta ne suka jiyo mata hakan,tuna wannan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce part dinshi,a bakin kopar shiga bedroom ɗinshi ta tsaya ta fara yin sallama,jin bai amsa mata ba yasa tayi tunanin ko bacci ya ɗauke shine ko kuma ya shiga cikin toilet ne,
Sanya kafa tayi ta shiga cikin ɗakin,Ƙarasawa tayi wurin table ta ajiye mashi tray ɗin,Sannan ta ɗan jinkirta tana jiran fitowarshi daga cikin toilet ɗin,har lokacin bata daina yin hammar bacci ba,idanuwanta kuma na rufewa,da alama baccin zata cigaba da yi atsaye,
Tana cikin tsayuwar nan tajiyo sautin aman shi daga cikin toilet,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,bakomai ya faɗo mata arai ba,fa ce abunda ya faru tsakaninta dashi a daren shekaranjiya,kada ace har yanzu ƙyanƙyamin jinin daya gani ajikinta ne yake sa shi yin amai,Nan take taji jikinta yayi wani irin sanyi.........."bata ƙarasa zancen zucin nata ba,Taji motsin fitowarshi daga toilet,
Tsautsayi da ƙaddara ne yasa Sehrish yunƙurin juyawa don taga a wani hali yake ciki,Aikuwa A gigice ta fasa ƙara,firgitar da tayi ne yasa ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume,Da sauri Sgr ya koma cikin toilet,tare da jan kopa ya rufe,sam baiyi tsammanin akwai mutun a bedroom ɗin nashi ba,Shiyasa ya fito a naked ɗinsa,babu kaya ajikinshi,Sehrish taga abunda yafi ƙarfin idanuwanta,
Bada jimawa ba,ya kuma fitowa daga cikin toilet ɗin,Waist ɗinshi ɗaure da towel,ya saki sumar kanshi ta baya,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,yadda ta yanke jiki ta faɗi a sume saboda kawai taganshi babu kaya ajikinshi,kamar taga wani mugun abu?ko kaɗan baiji kunyar komai ba da ta ganshi a haka din,sae ma mamakin sumewarta da yayi,sam baya jin ƙarfin jikinshi,Ƙarasawa yayi wurin da take a sume ƙasa,ya zuƙunne saman guiwarsa ɗaya,Hannayensa ya sanya tare da ɗaukkota ya kinkimota A saman shoulder ɗinshi,A ƙoƙarinsa na yakai ta bedroom ɗinsu,yana ƙoƙarin miƙewa tsaye da ita dauke a kafaɗarshi,Cikin rashin sa'a ƙafafunshi suka harɗe a jirkice ya saki jikinshi gaba ɗaya suka faɗa saman katafaren gadon nashi yaraff nan take mayafin da ta rufe hair ɗinta dashi yabar kanta,kwantacciyar sumar kanta ta tarwatse asaman gadon,
Tunda suka faɗa saman gadon sehrish ta farfaɗo sakamakon ruwan daya Yarfo mata asaman fuskarta,Ruwan sumar kanshi ne daya fito daga wanka bai tsaneta ba,numfashin mutun ta dinga ji da ɗumi duminsa asaman fatar ƙirjinta,tarasa gane maiya faru da ita,meya ke faruwa ne?taji an danneta,wani irin nauyi tamkar an ɗaɗɗaure jikinta haka ta dinga ji,
A hankali ta buɗe idanuwanta,kai tsaye suka fuskanci ceilling,gabanta ne ya faɗi rass,hannu tasa don taji menene ajikinta,kai tsaye hannunta ya sauka akan lallausar sumar kanshi,shafa sumar ta shiga yi,lokaci guda ta tuna cewa a ɗakin Sgr take,A matuƙar tsorace ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet,"shiru bai amsa ba,hakan ba ƙaramin ruɗu ya sanyata ba,
ƙoƙari yake don ya tashi daga jikinta,Amma hakan ya faskara,a karo na biyu yayi yunƙurin miƙewa,ɗagowa yayi da kanshi yana faman cizon la66ansa,a hankali ya ware sexy blue eyes ɗinshi,kai tsaye suka sauka akan ƙirjin sehrish,Nan take ya tsinci kanshi da bin surar kirjinta da kallo,gaba ɗaya rigar jikinta ta zamo,sakamakon faɗawar da sukayi saman gadon da hannunshi ya zame rigar batare daya sani ba alokacin da yake ƙoƙarin ɗaga jikinshi daga nata,dukiyar fulanin nan nata a tsaitsaye dasu tubarkalla ma sha Allah full ɗinsu,gwanin ban sha'awa,
Lokaci guda yabi ya susuce,ya tsinci kanshi a wani irin yanayi,Sehrish kuwa tunda ya ɗago da fuskarshi,hankalinta yayi mugun tashi,duk tabi ta ruɗe ta firgita,jikinta sae kerma yake yi,Sam bata lura da abunda yake kallo ba,sae faman lumshe idanuwanshi yakeyi yana buɗesu a hankali,yayin da maƙoshinshi ke motsi,kamar yana swallowing wani abu,wata irin zufa ce ta shiga tsastsafo mashi a gefen fuskarshi,ganin haka yasa ta ƙara tsorata,saboda tunawa da abunda ya ta6a faruwa a tsakaninsu,lokacin da haroon ya bata allurar nan,tuna wannan yasa hankalinta ya ƙara tashi,la66anta sae kerma sukeyi,a hankali ta furta"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..."sautin muryarta ne yaja hankalinshi,mayar da idanuwanshi yayi akan fuskarta,wani irin kallo ya shiga bin ta dashi,
Moving face ɗinshi yayi saitin fuskarta,da sauri ta runtse idanuwanta yayin da ta ke ci gaba da ambaton hakan,numfashinsu ne ya shiga haɗuwa dana juna,tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta,taji tausasan la66ansa asaman nata la66an,tongue ɗinshi ya zura acikin bakinta,lokaci guda Sehrish tabi ta rikice ta susuce,ta fita hayyacinta,kamar yadda shima ya fita nashi hayyacin,haɗa bakinsu su kayi cikin na juna,suna exchanging saliva ɗinsu,hot french kiss ya shiga mata,tun daga kan lower lip ɗinta ya soma tsotsarshi sosai,laushinsu yasa shi ƙara zabura,gaba ɗaya yabi ya rikice,hannayenshi kuwa tunda ya damƙi boobs ɗinta dasu,ya shiga murzarsu,gaba ɗaya ya kara susucewa,ya zauce ya soma sakin nishi,almost 30 mins ya zame mouth ɗinshi daga nata,ya mayar dashi saman nipples ɗinta,ya kama tamkar jinjiri ya shiga sucking ɗinsu,bada wasa ba,Jikinshi har wani kerma yake yi,tamkar wanda ya shekara da yunwa atattare dashi,raɗaɗin da tafara ji ne ya dawo da ita cikin hayyacinta,a lokacin har yana ƙoƙarin Zame towel ɗin jikinshi bcos all he needs at dat moment was to do it,da alama ya manta halin da amaryar tasa ke ciki na rashin yin salla,a wani irin firgice da iya karfinta na ƙarshe,ta daddage ta ingije Sgr daga jikinta,a wani irin kasalance yayi gefe guda yana faman sauke ajiyar zuciya,jikinta sam babu ƙwari haka ta miƙe da sauri ta dira daga saman gadon,har tana tuntu6e wurin ƙoƙarin guduwa daga bedroom ɗin nashi,tamkar wadda zombie ya biyo,ko mayafinta bata tsaya dauka ba,boobs dinta ma da hannuwanta ta tar6esu sai daga baya ta janyo rigarta da ta zame kasan stomach dinta,ta zura hannun rigar,gudu gudu sauri sauri tabar part ɗinshi,duk ta bi ta ruɗe ta rasa in da zata dosa,Allah dae ne ya kawota ɗakinsu,don kuwa bata cikin hayyacinta,lamarin ya girmi tunaninta,a wani sukwane ta faɗa bedroom ɗinsu,a edge of the bed ɗin,ta zube jikinta naci gaba da yin kerma,hakoranta har gamewa suke yi dana juna kaf kaf,tamkar wadda sanyi yayi ma mugun kamu,ƙanƙame jikinta tayi yayin da idanuwanta ke rurrufewa,wata irin matsananciyar sha'awace ta rufe ta,
Ita kenan,A 6angaren Sgr kuwa tun bayan da ta bar part ɗinsa,bai iya motsa koda yatsansa ba,jibgewa yayi saman gadon tamkar kayan wanki,ga wani irin raɗaɗi da yake ji a kasan mararsa,abun da bai ta6a yi ba arayuwarshi yau ya ɗanɗana ma kanshi,bazai iya tantance meke faruwa dashi ba,wata irin kasalace ta rufeshi,ya jima yana juye juye asaman gadon,cikin wani irin mawuyacin hali kafin Allah ya kawo mashi sauƙin jikin nashi,har bacci yayi awon gaba dashi,
*Boss Bature*
Wuraren sallar asuba,azmee ta kwankwaso ƙopar bedroom ɗinsu,kwankwan,dogon numfashi Sehrish taja tare da buɗe idanuwanta,waɗanda suka canza launi izuwa ja,tamkar wadda tayi ciwon ido,har cikin kunnanta take jin bugun ƙopar ɗakin nasu,amma ta kasa buɗe baki tayi magana,
Jahad ce ta farka daga bacci tana tambayar wanene,Muryar azmee tajiyo daga waje tana cewa"Aunty azmee ce,Lokacin sallah yayi,bansan ko kun tashi ba,"
"Yanzu muka tashi Aunty azmee,muna godiya sosai,"juyawa azmee tayi tare da barin ƙopar dakin,
"ku tashi rishi lokacin sallah yayi,dan Allah a hanzarta tashi,Sallah tafi bacci da minshari alkhairi,"cike da zolaya takeyin maganar kamar yadda ta saba yi in zata tashe su,zura hannunta tayi abayanta tana ƙoƙarin lalubo sehrish dake kwanciya abayanta wayammm taji babu kowa,ranta ne ya bata cewar kodai ta shiga toilet ne,gyara kwanciyarta tayi tana jiran fitowar sehrish daga toilet ko ta samu itama ta shiga tayi al'walar,duk wannan surutun da jahad keyi A kunnan sehrish tana sauraron Muryarta,
Lalla6awa tayi da rarrafe ta nufi toilet,daƙyar ta iya miƙewa tsaye,a hankali ta tura kopar ta shige ciki,batare da tabari jahad ta ankara da ita ba,
After some minutes,ta fito jikinta ɗaure da towel,jin motsin fitowarta,yasa jahad saukowa daga saman gadon,
Ta nufi wurinta,tunkan ta ƙarasa wurinta taga alamun ruwa ajikinta,yana ɗiɗɗigowa,fuskarta ɗauke da mamaki tace"Wanka da asuba"?shiru sehrish tayi batare da tace komai ba,
Jahad ta kuma cewa"da ruwan sanyi kikayi wanka ne?naga jikinki yana ta kerma,"nan ma tayi shiru bata tanka mata ba,
A hasale tace"Sehrish magana fa,nake yi maki,"
Muryarta a kasalance tace"Jahad,Am not feeling well"tayi maganar tare da wucewa izuwa gaban wardrobe,
"Meya ke damunki ne"?jahad tayi tambayar tana binta da kallo,
Shiru tayi ba tare da ta bata amsar komai ba,gyaɗa kai jahad tayi kafin ta wuce cikin toilet,don ta lura kamar sehrish batason zancen,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
*AMAREN BANA*
*DR MMN YUSUF (LIKITAR MATA)* 🩺💉💊🚑
07069711327 call or Whatsapp
*Shawara gareki amarya* 🧕👈🏼 *akan babbar matsalar da take damun mu ta addabemu watau ciyon sanyi ( infection)*
Shin kinsan illar da sanyi yake da ita ajikinki kuwa?? hmmm sanyi Yana haifar Mana da matsaloli Kashi Kashi ciki kuwa harda rashin kwanciyar hankali agidan mazajenmu , miyasa yanzu matsaloli sukayi yawa agidajen aurenmu ne ??? Wannan tambaya ce da kowacce mace yakamata tayiwa kanta saboda yadda abun yazama ruwan dare ,musamman duba da iyayenmu kakaninmu Sam basu fuskanci irin wannan matsalar ba to mu mi yake kawo Mana rashin zaman lafiya da mazajenmu ne duk da mafi yawanmu auren soyayya mukayi sa'banin iyayenmu da mafi yawa auren Hadi ake masu Amma sunfimu kwanciyar hankali shin Ina matsalar take ne ??????
Tabbas duk maccen da take da ciyon sanyi to zataci gaba da fuskantar matsaloli agidan aurenta , saboda sanyi Yana tafiyar da duk wata ni'imar mace yana hanata jin sha'awar mijinta Yana Hana jin Dadin auratayya tsakaninta da mijinta , zata dinga jin ciyo wajan saduwa wani lkcn har da mijin ma zafin zai rinka ji a maimakon yaji Dadi , kinga kuwa doli akwai k'atuwar matsala musamman in kinada kishiyar da zaiji Dadi a wajanta,
Ciyon sanyi Yana haifar da ciyon Mara Mai tsanani Yana Hana haihuwa idan yayi yawa ajiki yanasa mace budewar gaba Koda kuwa budurwace wadda Bata taba sanin namiji ba to sanyi kansa gabanta ya bude ,yanasa tusar gaba, kuraje, kaikyin gaba, da sauransu ,
Shawarata anan itace kowwace amarya Budurwa ko bazawara ta tabbatar tayi amfani da maganin sanyi kamun komai ,saboda duk.gyaran da zakiyi to aikin banza ne matukar kinada sanyi to ba gyaran da zaiyi maki wani tasiri yadda akeso zai kasance kinyi 'barnar kudinki a banza ne kifara yin maganin sanyi kamun kiyi komai ,
Ina matan da suke cewa duk abunda zanyi amfani da shi na kayan Mata bayamun aiki ????? To kusani bakomai ne matsalar ba sai (infection) matukar kinada sanyi to ba abunda zakiyi amfani dashi kiga aikinsa saidai kiyi ta barnar kudinki a banza ba biyan bukata👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Wannan yasa nazo maku da sahihin Kuma ingantaccen maganin sanyi na Mata da maza , maganine da yake fara aiki cikin gaggawa matukar kikayi amfani dashi to kinyi bye bye da matsalar sanyi da izinin Allah ,kina fara amfani dashi to kema zakiji canji ajikinki ,
Na Sha ne da sabulun tsarki da Wanda Zaki dafa kina tsarki sai Kuma oil Wanda Zaki rinka shafawa ,
Na.maza Kuma gari ne Wanda za'a rinka dafa mashi cokali daya atace asha ruwan da ikon Allah kun rabu da matsalar sanyi kenan , don Yana da kyau in kinada sanyi to.kiyi magani keda mijinki tunda abune da ake dauka kar kiji sauki shikuma yanada shi kinga anyi ba'ayi ba kenan ,
TAKUCE YAR MUTAN SOKOTO MMN YUSUF MAI KAYAN MATA 😍😍😍😍😍😍😍
Don samun ingantattun magunguna na nemini ta wannan number 07069711327 pls in Baki shirya siya ba kibari sai kin shirya kimun magana pls🤗🤗🤗🤗🤗🤗
*RISHRAF*
A cikin kitchen ta ƙarasa shan kukan nata,ta matse ƴar kwallarta,kafin ta shirya mashi dinner ɗinshi,Asaman Tray tana kan hanyar komawa upstairs,Kwatsam Sai ga haroon ya faɗo cikin falon,ba daga waje ya shigo ba,Acikin gidan yake,amma batasan daga ina yake ba,har sai da gabanta ya faɗi lokacin da tayi arba dashi,yayi jaga-jaga dashi ya jigata sosai,daƙyar yake iya ɗaga ƙafarsa idanuwan nan sunyi jawur dasu tamkar garwashin wuta yadda kasan na Mujiya sun yi luhu luhu,Jini sai ɗiga yake yi daga hancinshi,
Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,musamman da ya ƙaraso wurinta,duk tabi tasha jinin jikinta,
Tsayawa yayi kusa da ita yana kallonta,nuna mata fuskarshi yayi da yatsan hannunshi yace"haka kike so ko"?
Sunnar da kai ƙasa tayi,jikinta yayi wani irin sanyi,
"Saboda kawai na mareki,Shine aka yanke mun wannan ɗanyen hukuncin,bansan meyasa kowa yake ƙi na ba,An tsane ne ba'a son rayuwata,yau idan na faɗi na mutu alhakina bazai ta6a barinku ba" yana magana yana share hawayen dake shararowa akan fuskarshi,Wani irin tausayinshi ne ya Kamata,
"Nasan nayi laifi,Amma sau ɗaya na mareki su kuma har sau uku suka mare ni,Bayan wannan Hada wani horon aka ƙaramin,just because of You!Kuma laifi kika yi mun,Kin haɗani da dabba dole raina ya 6aci,ni kaina bada son raina na mare ki ba,Kin ƙuleni ne,"
Tuni idanuwanta suka cicciko da kwalla,muryarta na kerma tace"Dan Allah kayi haƙuri ya haroon....".
Bata ƙarasa maganar ba ya katse ta"Haƙuri fa kika ce?hmmmmm,bansan shi ba,Wlh tunda har suka ta6a lafiyar jikina sae uban kowa ya ɗanɗani kuɗarshi acikin gidan nan!Irin ƙuncin da suka ƙumsa mun acikin zuciyata sai sun ga martanin da zan mayar masu,Sun ta6o ma kansu bala'e da masifa,Zaman lafiya ya ƙare acikin gidan nan!Zan kashe musu farin cikinsu na har abada,Zan ƙuntata rayuwarsu,Zanyi silar da zuciyar wasu zata buga,"
Gabanta ne ya faɗi rass,gaba ɗaya tabi ta razana da kalamansa,Cos in a serious matter yayi maganar,babu wasa a kalamansa,
Jan ƙafarshi yayi daƙyar yake ɗangyasawa,kama hanyar zuwa part ɗinsu yayi,
Har yayi nisa da tafiya ya ɗan dakata tare da juyowa ya kalleta,adai dai lokacin itama ta juyo tana kallonshi,
Nuna ta yayi da yatsanshi"ke kuma!ki kuka da kan ki"!
Yana ambaton hakan yasa kai da sauri yabar wurin,
Tashin hankali!
Jikinta har kerma yake,tray ɗin hannunta da ta ruƙo kamar zai faɗi ƙasa,dakyar ta iya ɗaga ƙafarta,jiki amace kamar wadda aka zarewa laka,
Lokacin da ta shiga bedroom ɗin nashi,Har ya fara yin bacci,ƙarasawa tayi ta ajiye mashi dinner ɗinsa asaman table,kasa tashin shi tayi daga baccin,sam babu natsuwa atattare da ita,Kalaman haroon sunyi matuƙar girgizata,har cikin ranta take jin fargaban abunda haroon zai shirya masu,Wannan lokaci ne mai haɗarin gaske a rayuwarsu,tayi zurfi acikin tunaninta,Shessheƙar kukan da take yi ne ƙasa ƙasa Sounds ɗin ke kai mashi cikin kunnanshi,a hankali ya ɗan buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci,direct suka sauka akanta,zuba mata ido yayi yana kallon ikon Allah,Hawaye wasu na bin wasu fuskarta ta jiƙe sharkaf,ta shiga wani irin yanayi na tsoran halin da zasu shiga,
"Lafiya"?yayi maganar a yayin da yake ƙoƙarin miƙewa zaune,jin tayi shiru bata bashi amsa ba yasa shi kai hannu ya daki table ɗin gabanshi,A firgice ta dawo cikin hayyacinta zuba mashi ido tayi tana kallonshi,da sauri ta sanya tafin hannunta tare da wiping tears ɗinta,
"Hawayen menene asaman fuskarki"?
da sauri tace"babu komai,"
"Saboda na hana ki zuwa Kano"?
Girgiza mashi kai tayi alamar a''a,
"To na menene"?
Shiru tayi saboda ba ta da amsar da zata bashi,taso ace zata iya sanar dashi game da kalaman Haroon Wata'ƙil suyi ƙoƙarin dakatar dashi,Amma ina bazata iya ba don bata san miye zai aikatan ba,jin tayi mashi shiru yasa shi miƙewa tsaye ya koma wurinta ya tsaya,Hannu biyu yasa ya tallabo fuskarta,
"Tell me whats wrong with u?who touch u"?
girgiza mashi kai ta ƙara yi"babu komai,Bana jin daɗin jikina ne,'
"ina ke maki ciwo"?
Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,Ae yasan cewa tana period,tuna haka yasa tayi saurin cewa"Marata,ke yi mun ciwo,Amma da sauƙi,"
ta ƙarasa maganar tare da ɗagowa don ta saci kallonshi,idanuwanshi na akanta tamkar zasu lumshe saboda yanayin da yake jin kanshi a lokacin,
Zame hannuwanshi yayi daga kan fuskarta,ya mayar dasu saman waist ɗinta,gabanta ne ya faɗi rass,tunani ta shiga yi komai zai yi mata,ɗaukarta yayi cak tare da sauketa saman katafaren gadon nashi,hakan ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba ga wani irin tsoro da taji,
Ja da baya yayi ya taka izuwa wurin switch ya kashe light ɗin ɗakin gaba ɗaya nan take furniture ɗin ɗakin suka Soma bada haskensu different colours,hatta gadonshi da ya kwantar da ita,tunawa tayi da lokacin da ta ta6a kashe light ɗin ɗakinsa,ranar tayi mamaki sosai abun ya ruɗar da ita kuma ya ƙayatar da ita,Yadda komai na kayan ɗakinshi ke ƙyalli suna bada haske launi launi daban daban da zarar an kashe hasken ɗakin,
daga inda take kwance take hangen fuskarshi ba ƙaramin kyau yayi mata ba,gaban dressing mirror ɗinshi ya tsaya,ya zura hannayensa acikin trouser pocket ɗinsa,ya jima tsaye a wurin,kafin ya dawo saman gadon daga gefe ya zauna,Da kanshi ya shiga yin serving abincin yana ci atsanake,
Lumshe ido Sehrish tayi,tunda take a arayuwarta bata ta6a jin bed mattress mai ɗan bala'en laushi da daɗin kwanciya ba irinta Sgr,irin gadon da mutum ko baya jin bacci ya haushi,nan take baccin zai zo mashi,
tun tana kallonshi biji biji har ya kammala cin dinner ɗin nashi ya miƙe ya wuce cikin toilet daga nan ta fara bacci sama sama,lokacin da taji motsi ta ƙara buɗe idanuwanta,samunshi tayi a tsaye saman Darduma yana yin nafilfilin daya saba,Abun ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba,komai nashi burgeta yake yi ba kaɗan ba,a hankali bacci ya ɗauke ta,
tana cikin baccin nan,taji daddaɗan ƙamshin turaren nan nashi acikin hancinta,Slowly ta buɗe idanuwanta Unexpected eyeballs ɗinta suka sauka cikin ƙwayar idonshi a matuƙar tsorace ta buɗe baki zata yi ihu da sauri ya sanya tafin hannunshi ya rufe mata bakin,
Ta tsorata ne da ganin yadda blue eyes ɗin nashi ke shining kuma sunyi blue sosai,dama idan dare yayi kalarsu tana ɗan ƙara cizawa,
"It's me,"a hankali ya furta mata hakan,lokaci guda ta shiga sauke ajiyar zuciya,kallon junansu suka shiga yi,launukan hasken ɗakin dake ƙyalla fuskokinsu ba ƙaramin ƙayatar da abun yayi ba,
A hankali ya zame tafin hannunshi daga bakinta ya maye gurbinsu da tausasan la66ansa,sosai ya shiga kissing lower lip ɗinta,har izuwa upper,gaba ɗaya Sehrish ta soma fita hayyacinta ɗago da ita yayi tare da zagayawa da hannunshi ta baya ya zuge zip ɗin rigar jikinta ya soma shafa bayan romantically,kafin ya ƙarasa zame rigar zuwa saman stomach ɗinta,Lokaci guda yabi ya susuce saboda halittar ƙirjinta ba ƙaramin fisgarshi sukeyi ba,tayar mashi da sha'awarshi suke yi gaba ɗaya,duk da yana ƙoƙarin Controlling ɗin kanshi saboda period ɗin da takeyi,da sauri sauri numfashinsu ke fita,ga wani irin dumi da temperature ɗin jikinsu yayi,moving hands ɗinshi yayi izuwa saman mararta a hankali ya shiga shafa wurin,hakan ba ƙaramin gigitar da ita yayi ba,Lumshe idanuwanta tayi yayin da wasu siraran hawaye ke fitowa daga cikinsu,mayar da harshen shi yayi cikin bakinta,gaba ɗaya suka kacame ma juna,ita kanta batasan ta zura hannayenta cikin sumar kanshi ba,Duk ta hargitsar da ita,ta cukuikuye mashi ita,zame tongue ɗinshi yayi daga cikin mouth ɗinta,passionately ya shiga bata hot kisses asaman wuyanta,runtse idanuwanta tayi sosai kamar ta fasa ihu haka take ji,A wata irin duniya ta fara jin ta wadda bata ta6a ziyarta ba sai a wannan karon,da Yayan Romeo ya fara sanyanta a hanyar zuwanta,
Hucin numfashinshi ta dinga ji asaman wuyanta ya lumshe idanuwanshi yana jin wani irin feelings,da bai ta6a ji ba arayuwarshi,ɗan ta halikin nan ya jima yana cutar rayuwarshi saboda ego,almost 30years duk da bai ƙarasa ba,babu aure ba soyayya ta kowace hanya ya haramta ma kanshi mace,But this time around ya fara dawowa cikin hayyacinshi,ya jima bai motsa ba,almost 15 mins,kafin ya mayar da mouth din sa saman nipple ɗinta,kamawa yayi a hankali ya shiga sucking ɗinshi,A ruɗe Sehrish ta zabura,gudun kada tayi mashi irin na jiya yasa ya rufeta gaba ɗaya babu ta hanyar da zata tsere mashi,Sosai ya shiga biyan buƙatar shi da ita,sama sama cikin wani irin yanayi na shauƙi Bacci ya ɗaukesu a rungume da juna,ƙanƙame fa irin sosai ɗinnan,
A 6angaren jahad kuwa ta gaza runtsawa,tunda Daddynsu yace mata ta shirya gobe zasu je kano,kwata kwata bata son zuwa kano,Har acikin ranta ta tsani zuwa garin saboda rayuwar da suka yi acikinshi,Ga fargabar halin da zasu tsinci mahaifiyarsu aciki,Araye ko a Mace?Ko a wani mawuyacin hali na rayuwa,ga kuma babynta Junaid,basu jima da yin waya ba har kuka saida yayi mata akan cewa karta tafi tabarshi saboda ya shirya masu outing gobe,Abubuwa da yawa sun bi sun cunkushe mata,tsaye take acikin ɗakin sai faman safa da marwa ta ke yi,ta gaza kwanciya,har wuraren ƙarfe ɗaya jahad bata runtsa ba,Hosana kuwa tana ƙudundune cikin bargo,hankalinta kwance baiwar Allah,ita da babu cutar so ajikinta,
Ta jima a haka kafin daga bisani ta samu Solution na matsalar,komawa tayi saman gadonsu ta kwanta tare da jan bargo ta ƙudundune,taso ta jira dawowar sehrish amma shiru bata dawo ba,bata damu da hakan ba saboda tana da tabbacin cewa duk inda take tana acikin ƙoshin lafiya,
*Junaid Romeo*..
In midnight (Cikin tsakar dare)
*Wuraren ƙarfe 2:30 na dare*
Yayi nisa acikin baccinshi yaji an ambaci sunanshi da ƙarfin gaske da wata irin murya mai matuƙar razanarwa,tashin hankali,A firgice junaid ya ware idanuwanshi shi kaɗae asaman gadonshi,Gabanshi ne ya faɗi rass!sakamakon Mutun daya gani tsaye agaban mirror ɗinshi sanye da baƙar jallabiya mai hula,a wani irin firgice junaid ya miƙe zaune tare da toshe kunnanshi ya fasa ƙara mai sautin gaske yana ambaton sunan Daddynsu maimaikon sunan Allah,
Sosai ya shiga ja da baya,Hankalin shi a matuƙar tashe la66ansa na kerma ya shiga faɗin"Daddy!Mommy!Ya Rafayet!ya Omar!kuzo ku taimake ni!nashiga uku!dodo acikin ɗakina!Kashe ni zaiyi,'
Ƙwayar idonshi tamkar zata faɗo waje saboda tsabar tsoro,
Mutumin dake tsaye agaban madubin,wasu irin zaƙwa zaƙwan Akaifune a hannunshi,tsininsu tamkar na wuƙa,Ga uban gashi ajikin fatar hannunshi,juyowa yayi junaid na ganin fuskarshi ya rikirkice ya ruɗe,uban gashi ne ta ko'ina asaman fuskarshi,Ga wasu irin dogayen haƙora dake gareshi har sun sauko daga bakinshi,Idanuwanshi kuwa wa'iya zubilla,
Gadan gadan ya tunkari junaid,A wani irin Sukwane,junaid ya wuntsilo daga saman gadon har yana tuntu6e wurin ƙoƙarin fitowa daga cikin bedroom ɗinshi,fisgar ƙopar yayi dama a buɗe ya barta,da gudun gaske ya fito tare da nufar bedroom ɗin Sgr yana kuka,Sai dai kafin ya ƙarasa wurin part din nashi,Sai ga wannan Mutumin ya bayyana,A gigice junaid ya fasa ƙara ya canza hanya ya nufi part ɗin marshal Omar,Nan ma kafin ya isa,Sai ga mutun ya ƙara bayyana,A galabaice ya sauko daga downstairs,bawan Allah Ya rasa wurin wa zashi,gashi duk ihun da yake yi yana kuka babu mai jin shi,
*Junaid*!
Muryar jahad ce ta katse shi,da sauri ya juya wurin da sautin ya fito,a tsaye take tana kallonshi da gudun gaske ya nufeta tare da faɗawa jikinta ya ƙankameta yana faɗin"dodo!dodo!"
Bugun ƙafarshi da akayi ne yasa shi yin firgit ya farga daga baccin da yake yi,Duk zufa tabi ta jiƙa jikinshi sharkaf,kukan da yake yi acikin mafarkin har azahiri yake yinshi hannunshi rungume da pillow,
Biji biji ya fara gani acikin eyes ɗinshi kafin idon nashi su washe,
A hankali ya ambaci sunanta"Aunty Azmee,"yayi maganar tare da tashi daga zaune yana kallonta,
"Meya faru dakai ne junaid?tunda nashigo nagan ka kana ta koke koke cikin bacci,"ajiyar zuciya ya sauke tare dakai idonshi kan wall clock ƙarfe 9 na safe,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,Ko sallar asuba baiyi ba,
Cike da damuwa yace"Aunty Azmee wani mummunan mafarki nayi wallahi,Na tsorata sosai,Amma dana farka na ganki sae hankalina ya kwanta,Allah na gode maka da ya kasance ba gaske bane,da yanzu shikenan Na rasa rayuwata,"
Zama azmee tayi daga gefen gadon mashi,cike da kulawa tace"Junaid!Anya kayi addu'a kafin ka kwanta bacci?
girgiza mata kai yayi alamar a'a
"Ni nasani ae,tun lokacin baya nake fama dakai akan yin addu'ar bacci before ka kwanta,amma kaƙi jin maganata,"
Muryarshi tamkar zai yi kuka yace"Aunty azmee,wlh inaso nima na dinga yin addu'ar,amma bansan meyasa ba,karatu baya zama cikin brain ɗina,bazan 6oye maki ba,ban iya komai ba,ko a karatun sallah iya surori biyarne akaina dasu nake yin sallah,amma bayansu wlh ban iya wani abu ba,komai na karanta bai zama acikin kaina,"
Tsananin tausayinshi ne ya kama azmee,har cikin ranta ta damu da halin da junaid yake ciki,tana jinshi tamkar ɗan cikinta,
"Junaid ita addu'a,zaka iyayinta da ko wani irin Yare,Allah yana ji kuma zai amsa maka ne,Inaso ka dage da yin addu'a,nima kuma zan tayaka in sha Allah,"
Ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,
"In sha Allah Aunty Azmee zan dage da addu'a,nagode sosai da irin kulawar da kike bani,"
Murmushi azmee ta saki tare da cewa"kada ka manta fa,nifa na shayar dakai,Na so ka sosai junaid,tun lokacin da kana jinjirinka,ban mantawa Abban ku ya ke kawomin kai,
yini kake a wurina,lokacin yayyanka na zuwa aiki wasu kuma ba su kammala secondary ba,mu kaɗai muke kasancewa acikin gidan,Inyi maka wanka,in shafe maka jikinka da mai in gyara maka sumar kan ka,sannan in canza maka kaya,idan na kammala yi maka wannan,sai in shayar da kai,har bacci ya ɗauke mu saman gado,Kasan me"?
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"a'a sai kin faɗa,"
Taci gaba da cewa"idan na farka naga babu kai a kusa dani kamar in zauce...."
"Saboda me"?Yayi tambayar da ɗan mamaki a fuskarshi,
"Saboda na tsani araba ni dakai,Su fawan da zarar sun dawo daga school,har ɗakina suke zuwa su ɗauke ka,"
Fashewa yayi da dariya sosai har dimples ɗinshi suka lotsa,Bayan ya tsagaita da yin dariyar yace"Ni bansan meyasa kowa ke sona ba,Ina da farin jini sosai,ko yau muka haɗu da mutun cikin ƴan mintina sai ki ji yace ina burgeshi,"yayi maganar with proud,
Murmushi Azmee ta saki,kafin tace"Because of ur Glamorous personality,kana da kyakkyawar zuciya,shiyasa ka ke sace zuciyar mutane cikin ƙankanin lokaci,"
..cike da zolaya yace"Shiyasa jahad ta zauce akan sona,"yayi maganar yana dafe saitin heart dinshi,
Dariya azmee tayi tare da miƙewa tsaye tana cewa"Ga breakfast can yana jiran ka a dining,Jahad ba ta nan balle ta kawo maka a ɗakinka
Dafe saitin zuciyarshi ya kuma yi hankali a ɗan tashe yace"Aunty Azmee kina nufin cewa,Juliet dina bata nan?yanzu saida Uncle Abusufyan ya tafin mu da ita ko"?a shagwa6e ya ƙarasa maganar yana ɗan bubbuga ƙafarshi,har cikin ranshi baiso tafiyar jahad ba,Yaci burin su fita shan ice cream yau,
Fucewa Azmee tayi daga cikin ɗaƙin tana dariya,
Saukowa yayi daga saman gadon jiki asanyaye ya wuce cikin toilet,
*Boss Bature*
❤🤍❤
*Marshal Omar*
Fitowar shi kenan daga cikin toilet,Waist dinshi ɗaure da towel hannunshi kuma na ruke da wani short yana goge ruwan dake ɗiɗɗigowa daga jikinshi,
"Ya Omar"muryar hosana yaji acikin kunnanshi,da sauri ya juya don yaga ko itace,Kwance ya sameta saman gadonshi ko kayan baccinta bata cire ba,
Cike da mamaki yace"Kee!me kike yi acikin bedroom ɗina"?
"Ya Omar nifa zuwa nayi kawai don na gaishe ka"tayi maganar a ɗan shagawa6e,
"Haka ya dace kizo gaishe dani?ko sallama babu,kawai sai dai na fito daga toilet na same ki a kwance saman gadona,"Yayi maganar fuskarshi aɗan daure,
Murguɗa mashi baki tayi tare da cewa"Ae ɗakin Mijina ne"
Harara ya watsa mata"waye mijin naki?Allah ya kiyaye in auri mai ɗan kai irin naki,"
Gwalo tayi mashi tare da cewa"Oho dai,a haka ka gani kuma kake so,"_
ƙiris ya rage ya fashe da dariya,amma sai yayi saurin kawar da dariyar don kada taga kamar ma wasa yake yi mata,
"Get out from my bedroom!"a ɗan tsawace yayi maganar tare da nuna mata hanyar fita daga bedroom ɗin,
Maƙe mashi kafaɗa tayi,"Wlh ba inda zani ya Omar,Kazo ka ɗauke ni,ka fitar dani idan ba ka son gani na,"
girgiza kai kawai yayi tare da ƙarasawa gaban mirror dinshi,
"Kaya fa zansa,pls ki fita daga waje idan na kammala saiki dawo,kin ji My baby"
"Ae wlh ba inda zani je,Ae ba wani abu bane don ka sanya kaya agabana,tunda aure zamuyi,"
Shiru yayi bai kara tanka mata ba,
Jin yayi banza da ita yasa ta kuma cewa"Ya Omar"shiru yaƙi amsa mata kiran nata,
Ci gaba da magana tayi"Wai ya Omar,idan munyi aure,to taya zamu haihu muma"?
Banza yayi bai tanka mata ba,
Bata damu da hakan ba,sai ma ci gaba da maganar tayi,
"Ya Omar,kana ganin nima zan iya haihuwa?Kuma ma Taya za'ae na samu cikin"?
Hauka maganinka Allah,ya furta hakan acikin Zuciyarshi,
"Ji ya Omar ina magana ka wani share ni,idan baka faɗamun ba,to taya zan sani,"?
Ƙin tanka mata yayi,a hasale tace"Shikenan tunda ba zaka bani Amsa ba,wlh idan Daddy ya dawo zanje in tambayeshi ne,don ni bazan bari ayi abun kunya ba,Ayi mun aure bansan komai ba,
A ƙule ya juyo tare da kallonta yace"Ke,Tashi ki fuce mun daga ɗaki"
Maƙe mashi kafaɗa ta kuma yi"anƙi a fita Ya omar,"
Abun ya ɗaure mashi kai,ita ko shakkarshi bata ji,neman ma abunda zata yi mashi ya bugeta take yi don tasan cewa bazai iya ta6a lafiyar jikinta ba,
"Idan kanaso in fita cikin lalama,to ka fara faɗamun taya zan samu ciki idan munyi aure"
"Shine abunda kikeson sani"?yayi tambayar yana kallonta hadi da dage mata gira,ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Aikuwa Nan take ya sanya hannunshi ya zame towel ɗin daya ɗaure qugunshi dashi,
Tashin hankali! A gigice Hosana ta fasa wata irin razananniyar ƙara,Kafin kace me kamar walkiya haka tabar ɗakin da gudu tana kuka,ta firgita sosai
Mayar da towel ɗin yayi ya ɗaure waist ɗin sosai,sai faman tiƙar dariya yake yi,har da dafe cikinshi,
"Maganinki kenan,nasan daga yau ba zaki sake yi mun irin wannan question ɗin ba,Yarinya sai kace mai iskokai,Ni bansan ya zan ƙare da ita ba,A haka dai nakeso,kuma zan kula da abuna"ya ƙarasa zancen zucin fuskarshi ɗauke da murmushi ya wuce wurin wardrobe ɗinshi,sai daga baya ya dinga tunanin kada hosana fa taje ta faɗa ma wani abunda ta gani tunda ba hankali gareta ba,Tuna wannan yasa yayi saurin ɗauko jallabiya ya zura ajikinshi,da sauri ya sauko downstairs yana nemanta,
Azmee ya hango tana jera kayan abinci asaman Dining na breakfast dinsu,da sauri ya tunkareta,tunkan ya ƙarasa wurinta tajiyo takun takalmin mutun,ɗagowa tayi tare da kallonshi,ganin Marshal yasa ta saki fuska tare da gaisar dashi,
"Barka da safiya Omar,an tashi lafiya,"
A gaggauce ya amsa mata"lafiya lou,amman pls ko kinga gifcin Hosana,"?
"kamar dai naso naga giftawarta,lokacin ina ƙoƙarin fitowa daga kitchen,kuma naji kamar shessheƙar kuka ta ke,"
"Ina kike tunanin ta shiga ne,"
Shiru Azmee ta ɗan yi tana tunanin wurin da taga hosana ta nufa,
"Yawwa,ina tunanin bedroom ɗinsu ta nufa,"
Tunkan ta ƙarasa maganar ya kama hanya da sauri da sauri ya nufi ɗakinsu,a buɗe ƙopar take hannu yasa ya turata,tunkan ya shiga ciki,Ya jiyo shessheƙar kukan Hosana,Yana yin sallama taji muryarshi da gudun gaske ta sauko saman gadonsu ta faɗa toilet ta datse ƙopar,tana ci gaba da yin kukan,
..Sehrish na kwance saman gadon,ta ƙudundune cikin bargo,tun da Asuba da ta farka asaman gadon Sgr lokacin ya shiga toilet domin yin alwala,ta saɗaɗa tabar bedroom ɗin nashi,ta dawo ɗakinsu,
Kaitsaye ya wuce ƙopar toilet ɗin ya tsaya tare da ambaton sunanta"Am really sorry Hosana,nasan ban kyauta maki ba,ke ce kin takuramin that's why nayi maki hakan,kuma ni fa amsar tambayarki kawai na baki ba wani abu ba,
Cikin shessheƙar kuka yaji tace"Ya Omar baka da kunya wlh,Ni babu ruwana dakai,Wlh bansan ganinka,bansan ganin wannan abun naka"
Hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,
A ruɗe ya shiga faɗin"hosana!baki da hankaline?so kike ki tona mun asiri,har wani ya ji mu?kin manta ni zan aureki,"?
A tsiwace tace"wlh saina faɗama daddy idan ya dawo,ince ka nuna mun abunka,"
Hannu yasa tare da dafe kanshi,ya furta"Wayyo Allah na,Ni Omar,naja ma kaina,"
Ƙasa ƙasa yayi da muryarshi cikin lallashi ya soma magana,
"My Hosana pls,ki yafe mun,bazan ƙara ba wllh,kome kikeso zanyi maki,"
"Wlh ya Omar,ko kukan jini zaka yi saina faɗama daddy cewa kai ɗan iska ne,Ni bazan aure ka ba,"
Tsawa ya daka mata tare da cewa"Ki faɗima duk wanda zaki faɗimawa ƴar rainin hankali,Wlh kuma kika kuskura kika faɗama wani sai na sa6a maki,kuma babu ni babu ke,Ƙasar ma zan bari gaba ɗaya in tafi can in auri baturiya,".
Rai a6ace ya juya tare da barin ɗakin nasu,
Sai da taji alamun fitarshi daga ɗakin,sannan ta wanko fuskarta ta,ta buɗe ƙopar toilet ɗin ta fito waje,abun ya dameta sosai buɗe ƙopar ɗakin tayi ta fuce,A dining ta same shi zaune shi da junaid suna yin breakfast,Azmee na yin serving ɗinsu,
Kamar wadda aka zarewa lakar jikinta haka ta ƙarasa ta samu wuri kusa dashi ta zauna,
"Aunty Azmee ina kwana"?fuskar Azmee ɗauke da murmushi ta amsa mata,"Lafiya lou Jahad,kin tashi lafiya...."da sauri junaid yace"Aunty azmee wannan ce jahad?kalli fa ƴan kumatun fuskarta ki gani,Hosana ce,"
Dariya azmee tayi,shi kanshi Omar yaso ya ɗan dara,ita kuwa tsuke fuska tayi tare da jifarshi da harara tace"ina ruwanka da kumatuna"?
murguɗa mata baki junaid yayi dama basu jituwa atsakaninsu,Ƴar tsama sukeyi,
juyawa ta ɗan yi gefenta tare da kallon Marshal,Ya tamke fuskar nan babu annuri acikinta,
Saitin kunnanshi takai bakinta cikin sanyin murya tace"Ya Omar bazan ƙara ba,kuma bazan tona maka asiri ba,dan Allah kada ka tafi ka barni,"
side smile yayi tare da cewa"Its okey,nima wasa nake yi maki,bazan iya tafiya nabarki ba,"
Murmushi ta saki,har hankalinta ya kwanta,
Hannu Azmee takai zata ɗauki plate ta zuba mata abinci,ganin ta zura hannunta acikin plate ɗin Omar suna ci atare yasa ta fasa,Abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,
*KANO TA DABO TUMBIN GIWA KODA ME KAZO AN FI KA* acewarsu ba,Don ni ban yarda ba,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Bayan *Jahad* ta fito daga toilet, hijab ta ɗauko cikin wardrobe ta zura ajikinta,wurin gadonsu ta koma ta haye sama tare da kai hannu tana bubbuga hosana,
"Get up hosana,Time ɗin sallah yayi,"
hosana bata motsa ba,sae ma cigaba da jan minsharinta da tayi,
"Hosana ki tashi mana!ba zaki tashi ba wai,kullum sai kin bani wahala idan nazo tashin ki daga bacci"tayi maganar fuskarta a ɗaure,
Hosana kuwa,gyara kwanciyarta ta ƙara yi,har wani ƙara jan minsharin takeyi da ƙarfi don ma jahad tasan cewa tayi nisa a baccinta,alhalin tun a first call da tayi mata ta farka,
A ƙule jahad tace"kada Allah yasa ki tashi,kuma saina faɗa ma ya Omar cewa baki yin....."tunkan taƙarasa maganar,hosana ta diro daga saman gadon da gudun gaske ta nufi toilet ta buɗe ta shige ciki,dariya jahad tayi sosai kafin ta sauka daga saman gadon ta koma ta shimfiɗa carpet ta kabbara sallah,
Sehrish kuwa tana a ƙudundune cikin bargo tayi lamo tana faman sauke ajiyar zuciya,kokwanton abunda ya faru tsakaninta da Sgr takeyi,ta kasa gasgata abunda ya faru last night,shin dagaske ne ko kuwa mafarki ne tayi,Don tasan cewa hakan zai yi wuya ya kasance gaskiya,Abun ya matukar ɗaure mata kai,ya caza mata brain ɗinta,tana cikin wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita,
*Junaid Romeo*
Bude ƙopar bedroom ɗinsa yayi tare da fitowa daga ciki,Still kayan baccin jiya ne ajikinshi,ya kara wayarshi a saman kunnanshi,hakan na nuni da cewar waya yake yi,Ashagwa6e yake magana yana faman tura baki,
"Abba pls come back Soon,nafiso na ganka a kusa dani,"ya ɗan yi maganar yana bubbuga ƙafarshi ƙasa,
On the other hand,Abbansu yace"ka ji tsoron Allah junaid!Nafa gano ka,So kake in dawo gida,saboda ayi maganar aurenka ko"?
Murmushi junaid ya saki yana ɗan sosa ƙeyarshi da ɗayan hannunshi"eh dan Allah Abba,nidai duk atakure nake,Allah jina nake kamar a prison,Ayi mun aure kawai in ana son zaman lafiya,"
Abba yace"idan ba'ayi maka auren ba fa"?
Ƙuƙuni ya shiga yi ƙasa ƙasa yana cewa"zan addabi kowa ne,in kuma kama ɗaki a hotel....."
Bai ƙarasa maganar ba,Jin dariyar Abbansu ta cikin wayar,ashe duk yaji abunda yake cewa,
"Junaid wa kayi mawa?kasan cewa yayyenka gaba ɗaya soldiers ne,Wlh kayi kuskuren yin badai dai ba,kai kasan inda za'a kai ka,".
Jin wannan maganar ta Abba yasa shi ɗaure fuskarshi,
Yana tafiya yana waya,da alama part ɗin Sgr zai wuce,saboda can ya nufa,
Lokacin daya shiga falonsa,babu kowa,a saman sofa ya zauna,sai da ya kammala yin wayar da Abba,Su kayi sallama,Sannan ya miƙe tare da wuce wa bedroom ɗin Sgr,
Sallama yayi mashi,jin shiru yasa shi shiga cikin ɗakin kaitsaye,a kwance ya same shi saman katafaren gadon nashi,ya lullu6e jikinshi har zuwa chest ɗinshi,jallabiya ce sanye ajikinshi,tun daga kan yadda yake yin baccin nashi zai tabbatar maka da cewa,yana cikin kwanciyar hankali da natsuwa,
Lalla6awa Junaid yayi ya ƙarasa kusa da gadon,yana ƙoƙarin hawa idanuwanshi suka sauka asaman bargon Sgr,turus yayi ya tsaya yana kallon ikon Allah,Ya jima yana tunanin kome ya jawo hakan,abu dai gashi nan kana ganinshi ta cikin bargon,hawa sama yayi har zuwa saitin fuskarshi sannan ya tsaya tare da furta sunanshi a hankali"Babban yayanmu,"shiru bai amsa mashi ba,ƙara ɗaga murya yayi'babban yaya,"
Hannu ya kai tare da shafa gefen fuskarshi ya sake cewa"Babban yaya..,"
Har cikin dodon ears ɗinsa yaji kiran nashi,daƙyar ya iya ware blue eyes ɗinshi,biji biji ya fara gani kafin idanuwan suka ɗan washe,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunan shi"Junaid,"
Murmushi junaid yayi tare da cewa"nazo ne don na takura maka,Jiya na jira naga dawowarka,amma baka dawo gida ba,har bacci ya ɗauke ni,'_
Zuba mashi ido Sgr yayi yana kallonshi,
Hakan yasa junaid ya ɗan tsuke fuskarshi yace"haba yaya rafayet,in zauna in tayi maka zuba kamar parrot maimakon ka mayar mun da martani saika zuba min ido kana kallona,"
a hankali ya lumshe idanuwanshi kafin ya sake ɗan waresu akan Fuskar junaid ɗin,
"Me kake so ne"?
Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"Yanzu babban yaya sai inason wani abu zanzo wurinka?jiya fa na dawo daga tafiya,ko farin cikin ganina ma baka yi ba,"
Ruƙo hannunshi Sgr yayi tare da janyoshi ya kwantar da kanshi saman ƙirjinshi,yana ɗan shafa bayanshi yace"Am glad to see you,Ya gajiyan tafiya,?kayi mun tsaraba"?
Ashagwa6e junaid yace"Eh mana,munyi tsarabar fura,da zuma,da sauransu dai,idan kanaso zan yi ma rishi magana ta dama maka fura kasha,Wlh akwai daɗi sosai,nima in nasha kunne na har rawa yake yi,'
Ya ƙarasa maganar tare da ɗagowa daga jikinshi,da buɗar bakin Sgr sai cewa yayi"you mean tafi abun da nasha last night daɗi"?
A ruɗe junaid yace"babban yaya,me kasha jiyan?Ae ni bansan shi ba balle in san cewa ko yafi furar daɗi,
Shi kanshi baisan ya furta hakan ba,it was just slip of the tongue,saboda ya kwana da abun aranshi,kuma yanzu haka ma shi yake tariyowa acikin brain ɗinsa,abun ya tsaya mashi arai,yadda har surar jikinta taja ra'ayinshi har ya fita hayyacinshi ya fara romancing ɗinta,ƙiris ya rage jiya ayi abun kunya,
(Allah yaso bai ƙarasa headquater ɗin ba,da shikenan an buge boss,(in jini ba,don na lura wasu in ina kara wannan bayanin suna tsammanin cewa Sune sukeyin zancen zucin,sometimes ina ƙarawa da nawa bayanin)
"Yaya rafayet,"junaid ne ya ambaci sunanshi,ganin ya shiga zurfin tunani, hankalinshi yayi wani wurin,mayar da idanuwanshi yayi kan junaid tare da cewa"don't disturb me pls,Inaso na ɗan huta junaid,"
Ranshi ya ɗan sosu,jiki asanyaye ya juya zai sauko daga saman gadon,Sgr ya dakatar dashi"Wait,'ɗan tsayawa yayi tare da juyawa yana kallonshi,
"Tell me what do u want from me"?
Shiru junaid yayi yana lissafin adadin kuɗin da zai kar6a a wurinshi,Don sunyi da jahad zasu fita yawo,gashi ƴan kuɗaɗen acct ɗinsa duk sun ƙare,Yayi broke,'
ɗaga yatsun hannunshi yayi yana yin lissafin,hakan ba ƙaramin dariya yaso yaba Sgr ba,dama sai da ranshi ya bashi cewar wani abu ne ya kawo shi bedroom ɗinshi,tunda sassafe ko wanka bai yi ba,balle aje ga maganar breakfast,A tsiyacen shi yazo,
"Zan koma bacci,tunda naga lissafin na ka bamai ƙarewa bane,"
Da sauri yace"pls babban yaya kada ka koma bacci,yanzu ma daƙyar na tashe ka,".
ta6e lips ɗinshi yayi tare da nuna wurin dressing mirror ɗinshi da hannunshi,Yace"idan kuɗine kake buƙata a wurina gasu can ka ɗauki iya yadda kakeso,idan ma na cikin nan isn't enough for u,Zan ƙara maka ta acct,hope hakan yayi maka"?yayi tambayar yana kallonshi,.
Washe baki junaid ya shiga yi yana cewa"Babban yaya nagode sosai,wlh duk gidan nan kafi kowa sona,har Daddy ma kafi shi sona,"
Harara Sgr ya ɗan jefa mashi kafin yace"Saboda ina baka kuɗi ko"?_
fashewa junaid yayi da dariya,tare da saukowa daga saman gadon ya nufi wurin dressing mirror,
Mayar da idanuwanshi yayi ya lumshe su,shikaɗai yasan irin feelings ɗin da yake ji,kamar yayi hauka,Kuma shi irin mutanan nan ne,waɗanda basa wasa da lafiyar jikinsu,Komai yaji jikinshi na bukata yinshi yake yi don ya samu cikakkiyar lafiya,shiyasa gashi nan ta ko'ina masha Allah,tun daga kan skin ɗinshi zakasan cewa ba ƙaramin gyara take sha ba,haka sumar kanshi,da sauran parts na jikinshi,yanzu kuma ga wani new abu da yake bukata Urgently,
Zuƙunnawa junaid yayi agaban drawer ɗin,ya buɗe middle ɗinta,Dollars ne ya gani a jere,cike fam da ita,har wani ƙyalli kuɗin sukeyi acikin idanunshi,murza hannunshi ya shiga yi,har wani ƙaiƙayi suke yi mashi,Bandir ukku ya ɗauko ya tura su daƙyar cikin aljihun wandonshi,duk da haka basu isheshi ba,sae daya ƙara da naira,A gida na ƙarshe daya buɗe ajikin drawer chest din,kuɗin nigeria ne,Suma ya ɗauki Bandir uku na dubu dubu kusan dubu ɗari uku kenan,Ya turasu cikin ɗayan aljihun daƙyar suka shiga,Bayan ya kammala ya rufe mashi ita,yana ƙoƙarin miƙewa,idonshi ya sauka akan hoton daya faɗo ƙasan tiles,baisan daga ina hoton yake ba,duk a tunanin shi hoton Babban yayansu ne,
Zukunnawa yayi tare da kai hannu ya ɗauki hoton da ya kife,ya juyo dashi yadda zai ganshi da kyau,
Da karfi ya furta"Sehrish!"miƙewa yayi tare da tunkarar wurin gadon hannunshi ruƙe da hoton yaci gaba da cewa"wlh itace," jin sambatun da junaid keyi ne yasa Sgr ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da wurga eye balls ɗinsa wurin junaid dake tunkaroshi
Zama yayi daga gefen gadon fuskar nan tashi awashe cike fal da farin ciki,ya kuma yace"Wlh itace,Yaya rafayet ina ka samu hoton rishi tana ƴar ƙarama,"
"Junaid what are u talking about"?yayi tambayar a yayin da yake ɗan miƙewa zaune,tare da jingina bayanshi akan gadon,
"Sehrish mana!wadda take yi maka aiki,"
Cike da mamaki Sgr yace"Kana nufin itace a pic ɗin"?
Jinjina kai junaid yayi"ƙwarai kuwa itace,"
Cike da mamaki Sgr ya kuma tambayarshi "taya akai ka gane cewa itace?cos i even asked her last time,amma ta sanar dani cewa ba ita bace'
Junaid yace"ae duk cikinsu,babu mai ɗigon tawada asaman wuyanshi sai ita,duk sauran basu dashi asaman neck ɗinsu,Idan ka kalli hoton nan dakyau,zaka ga ɗigon baki asaman wuyanta,'.
"Lemme see"ya buƙaci ganin hoton,da sauri junaid ya mika mashi,hannu yasa ya kar6a,sannan ya ƙura ma hoton ido yana kallonshi,ɗigon tawadar ya gani asaman wuyanta,closing eyes dinsa ya ɗanyi,yana tariyo kallon da yayi ma ƙirjinta adaren jiya,har izuwa saman wuyanta,tabbas yaga black point ɗin nan,amma abun ya daure mashi kai,ta yadda har ita kanta,bata gane cewa ita bace a hoton,
Buɗe idanuwan nashi yayi akan fuskar junaid sannan atsanake yace"Junaid,dama kallonta kakeyi?" cike da tuhuma yayi mashi tambayar,
Sunnar da kai junaid ya ɗan yi yana sosa ƙeyarshi yace"Nifa ba kallonta nake yi ba,tun lokacin baya ne,kafin ta bayyana amatsayin mace,muna da kusanci sosai da ita,shiyasa ma har nayi mata wannan kyakkyawan sanin,"
"Its okey" ya furta hakan,tare da mayar da idanuwanshi kan hoton,Abun ya daure mashi kai,sai lokacin ya shiga tunanin ko meyasa Uncle Abusufyan ya basu hotonsu shi da Omar?
Muryar junaid ce ta katse shi da cewa"Ka taso muje dining muci abinci pls,nasan kana jin yunwa,'
Runƙo hannun Sgr yayi,har sai da ya samu ya sauko daga saman gadon,Sannan suka fito atare,har lokacin hoton na hannunshi,daga bayane ya zura shi cikin aljihun jallabiyarshi
Saukowa downstairs suka yi,tunkafin su ƙarasa dining ɗin,suka hango Uncle Abusufyan tare da Marshal Omar,ga Jahad da Hosana ma,duk suna azaune suna cin breakfast ɗinsu,Azmee ce atsaye take yin serving ɗinsu,
koda suka ƙarasa,da sauri su jahad suka gaisar dashi"babban yaya ina kwana,an tashi lafiya,"?
"Lafiya,sannunku"ya ambaci hakan kafin ya samu wuri ya zauna,junaid ma ya zauna a kusa dashi,
"Big bro,jiya na jira dawowarka gida baka dawo ba,ina fata kana cikin ƙoshin lafiya,"acewar Marshal Omar,
"Am ok,"ya bashi amsa atakaice,dama fushi yake yi dashi saboda yaso su dawo gida atare,Amma Omar yace sai ya ɗan ƙara kwanaki,
Juyawa ya ɗanyi tare da kallon Abusufyan,wanda shima kallon nashi yake yi,jira yake yaga iya gudun ruwan nashi,zai gaisar dashi ne?ko kuwa jira yake yi shi ya gaishe da shi Ne?
a hankali ya furta"Uncle,ya gajiyar tafiya,jiya kun dawo time ɗin bana nan"
Murmushi Abusufyan ya ɗan saki tare da cewa"lafiyalou Alhamdulillah,gajiya tabi jiki,'
Matsawa azmee tayi ta ɗauki plate ta shiga zuba masu abincin da zasu ci,
Hosana tace"Daddy,rishi fa?kada acinye ita bata ci komai ba,"
Jahad tace"bacci takeyi tun ɗazu,kuma har tashinta nayi tazo muci abinci,amma tace mun in ƙyaleta,bata jin daɗin jikinta,'
"Me ya ke damunta ne"?Omar yayi tambayar,
"Nima bansani ba,tunda asuba dai kamar bata da lafiya,duk ta canza mun,har tambayarta nayi meke damunta amma bata sanar dani ba,"
Abusufyan yace"bai kamata a ƙyaleta ba,yakamata ku kirata tazo muji menene matsalarta,"
Jiki na rawa junaid ya miƙe zaije kiranta,karaf idanuwanshi suka sauka kan fuskar Sgr,wani irin kallo ya wurga mashi mai kama da harara,batare da kowa ya lura ba,komawa junaid yayi ya zauna,tare da cewa"Jahad kije ki kirata mana,"_
"Amsa mashi tayi da toh,kafin ta mike cikin sauri ta wuce bedroom ɗinsu,
Cike da zolaya Marshal yace"Wato har ka fara bata Command ko"?_
Kunyace ta rufe junaid,har ya kasa shan Tea ɗin da ya ke sha cikin cup,Satar kallon Abusufyan yayi,Suna haɗa ido nan fa ya ƙara kame kanshi,
Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba,Hosana tace"Ya Omar,wai yaushe ne abun nan?kace idan kuka dawo za'ayi magana nifa na kagara wlh,"
Gabanshi ne ya fadi rass,Hankali aɗan tashe ya ɗago ya kalleta,ko ajikinta sae ma tura pancake takeyi acikin bakinta,wata irin kunyace ta rufe shi,.
Shi kanshi Abusufyan,kunyarce ta rufeshi,sai faman jujjuya fork yake acikin plate,ya kasa cin Abincin,
Sgr kuwa har ɗagowa yayi ya kalli Hosana da tayi maganar,
Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,jurewa kawai takeyi,
Junaid ne yayi ƙokarin dakatar da ita ta hanyar yi mata raɗa acikin kunnanta,
"Hosana waike baki da burki ne?meyasa zakiyi mashi haka,Duk kinsa sunji kunya,daga shi har Daddy ɗin naku,bai kamata kice haka ba,"_
Turo baki ta ɗan yi tare da cewa"zunubi na aikata ne?kawai kawai saboda nace....."bata ƙarasa maganar ba,sakamakon kallon da taga Omar yayi mata,nan take ta shiga taitayinta,
After some minutes,Jahad ta shigo Dining area ɗin,tunkan ta karaso Junaid yace"ina rishi ɗin take ne"ganin ta dawo ita kaɗai batare da Sehrish ba,
"Tana aciki,yanzu zata fito,"ta karasa maganar tare da samun wuri ta zauna,
A hankali ta zuro da kafarta,har yanzu jallabiyar ce ajikinta,ta laga gyale akanta,ƙafarta kuma na sanye da flat shoes,jikinta sae kerma yake yi,saboda zazza6in daya rufar mata,amma bata so kowa ya gane halin da take ciki,hakan yasa tun kafin ta ƙaraso wurinsu,ta daidaita natsuwarta sosai,sannan ta shigo dining area ɗin,takun takalminta ne ya janyo hankalinsu,duk suka juyo suna kallonta,gabanta ne ya faɗi Rasss ganin Sgr zaune,aikuwa a ruɗe ta juya zata koma ciki,.
Abusufyan ya dakatar da ita,ta hanyar ambaton sunanta"Sehrish,"tsayawa tayi cak,batare da ta ƙara ɗaga ƙafarta ba,wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,kafin a hankali ta juyo ta ci gaba da tafiya,hankalinta duk yabi ya tashi kamar taga wani mugun abu,
Wurin Abbansu ta tsaya,tare da gaisar dashi,"daddy ina kwana,".
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"lafiyalou Daughter,meyasa baki fito ba tun ɗazu,"?
"Bana jin daɗin jikina ne,Amma naji sauƙi yanzu"
"Alhamdulillah,samu wuri ki zauna,"cike da kulawa yayi maganar,
Gabanta sai faɗuwa yakeyi,ta rasa ta ina zata zauna,inda bazata fuskance shi ba,balle har su haɗa ido,
Ganin taƙi samun wuri ta zauna sai ƴan dube dube takeyi,Hakan yasa Omar nuna mata gefenshi yace"Zo ki zauna,"hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,saboda yana a left hand ne kuma suna fuskantar su Sgr dake ta dama,kuma kujerar da zata zauna,ita ke fuskantarshi,jiki a mace ta ƙarasa gefen Marshal ta zauna,muryarta na kerma ta gaisar da Marshal"ina kwana yaya Omar,"
Da fara'a a fuskarshi ya amsa mata,"lafiyalou sister,ya jikin naki,"
"Da sauƙi,"ta bashi amsa,
"Allah ya ƙara sauki,"
"Ameen"
"Yaya rafayet,ina kwana,"daƙyar ta iya gaishe shi,sai dai ko kallo bata ishe shi ba,balle har tayi tsammanin zai amsa mata gaisuwarta,lokaci guda ta gane dalilin dayasa yaƙi amsa mata gaisuwar saboda bashi ta fara gaisarwa ba,a matsayinshi na boss ɗinta,wanda ke asama da mahaifinta,
"Bro baka ji ana gaishe dakai bane"?acewar Omar
Batare daya ɗago ya kalleshi ba yace"Naji,"yayi maganar tare da ɗaukar cup na coffee yana sha,
Murmushi marshal yayi,saboda ya gane reason ɗin dayasa yaƙi amsa gaisuwarta,
Zagayowa azmee tayi kusa da ita,ta ɗan duƙa saitin kunnan sehrish tace"Amaryarmu,me kikeso a zuba maki ne?farfesun nama ko Snacks,"?
Murmushi sehrish tayi har dimple ɗinta ya lotsa,sannan tace"Aunty azmee pls kidaina zolayata,yanzu idan yaji fa?ni zaki jamawa,"cikin raɗa tayi maganar don kada suji mai take cewa,
Azmee tace"Shikenan Mrs rafayet,na daina,yanzu dai me kikeso"?
Sehrish tace"farfesun zaki samun,saboda bakina babu daɗi,"
Su6ul da baka azmee tayi wurin cewa"kice mun kusa samun ƙaruwar baby kenan,"karaf maganarta ta sauka akan kunnan Sgr,kuma cikin whispering tayi maganar,amma wani iko na Allah yaji abunda tace,ko kuwa yayi amfani da motsin la66anta ne Oho,
Kamar daga sama taji yace"Keee!"a ɗan firgice azmee ta ɗago,ba ita kaɗai ba hatta su Uncle sai da suka ɗago suna kallonshi,ya haɗe fuskar nan babu annuri acikinta,.
Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da tabar wurin,Jiki asanyaye azmee ta juya da sauri tabar wurin,
Sam sehrish bata ji daɗin hakan ba,duk sai taji babu daɗi,bata so Sgr ya kori Azmee ba,agaban kowa da kowa wannan kamar Cin fuska ne,Su kansu sauran dake zaune a dining ɗin basu ji daɗin hakan ba,shiru kawai su kayi,tunda basu da yadda zasuyi dashi,
Ganin ya sallami Azmee yasa ta shiga ƙoƙarin yin serving ɗin kanta,plate ta ɗauko acikin jerin plates ɗin dake ajiye saman table din,Warmers din tashiga bubbuɗewa harta buɗo wadda ke ɗauke da farfesun naman kaza,serving spoon ta sanya,ta shiga ɗibarta tana zubawa acikin plate din,sai da tacika shi,sannan ta rufe warmer ɗin,
Sosai ta shiga shan farfesun,har wani lasar baki takeyi saboda daɗinshi da takeji,cinyar kaza ta ɗauko tana ƙoƙarin kaiwa bakinta,Sgr ya ɗago da idanuwanshi,karaf suka shiga cikin nata,nan take tasha jinin jikinta,kasa ƙarasa kazar tayi cikin bakinta,cak ta tsaya,tana kallonshi,
Wannan karon kallon da yake yi mata yasha bambam da irin kallon daya saba yi mata a baya,gaba ɗaya sun shagala da kallon junansu,babu wanda ya lura a wurin,tunani tashiga yi komai yasa yake kallonta har haka batare da ya janye idanuwanshi ba?
Shikuwa gogan jira yake ta kawar da idonta daga kallon da takeyi mashi,kada raini ya fara shiga tsakaninsu,saboda abunda ya faru jiya,musamman da ta ganshi tsurararshi babu kaya a jikinshi,
ƴar harara ya watsa mata,tare da janye idanuwanshi daga kanta,kawar da nata idon tayi,mayar da cinyar kazar tayi cikin plate,gaba ɗaya taji komai ya fita ranta,ba don ta ƙoshi ba,ta miƙe zata bar dining ɗin,
"Whe're u going"muryarshi ce ta dakatar da ita,
daƙyar ta iya buɗe baki tace"Na koshi,"
Zuba masu ido Abusufyan yayi yana kallonsu,
"Koma ki zauna,"Yayi maganar yana nuna mata seat ɗinta,Tamkar ta fashe da kuka haka taji,juyawa ta dan yi suka haɗa ido da daddynsu,kafin ta zauna,taci gaba da shan farfesun da ta rage,
Hannu yasa ya yago tissue,yana goge mouth ɗinsa,kafin daga bisani ya miƙe ya wuce part ɗinsa,
Sai da ya bar wurin sannan,ta samu natsuwa,
"Daddy,ya maganar zuwa kano?sehrish ta faɗamun cewa,da zarar kadawo daga damaturu zaku wuce kano,Wurin neman Oumman mu,"jahad ce tayi maganar,
"In sha Allah gobe nake son tafiya,tunda Asuba before ku tashi daga bacci ma"
Yana kai ƙarshen maganarshi,Hosana tayi saurin cewa"daddy,pls dani za'a tafi,wlh inason zuwa kano,"
Harara marshal ya ɗan wurga mata kafin yace"a haka za'a tafi dake?me kika sani?Faɗamun a wata unguwa kuka zauna a kano"
Wurga ido sama tayi tana ƙoƙarin tunano anguwar da suka zauna a kano
Yatsina fuska tayi tare da cewa"Dawanau ko"?
me zasuyi in ba dariya ba,gaba ɗayansu suka fashe da dariya,ɗaure fuskarta tayi,don ita ba ta faɗi don ayi mata dariya ba,bilhaƙƙi da gaske take ita,
Jahad tace"kai hosana dawanau fa kika ce?Anan ne muka zauna?,' murguɗa mata baki tayi batare da ta ƙara cewa komai ba,
"Daddy dan Allah ka tafi dani,nafi kowa son naje,"acewar sehrish,
Mayar da idanuwanshi yayi kanta tare da cewa"Kin tambayeshi ne?ko kin manta yadda muka yi dake,"_
Jin haka yasa ta ɗan ɗaure fuskarta don tasan cewa,daƙyar ne Sgr yabarta ta tafi kano,
"Ki je ki tambayeshi,idan ya barki tun yau ki fara shiri don da asuba zamu tafi,idan kuma ya hana to zan tafi da jahad ne"
Tuni idanuwanta suka ciko tab da kwalla saboda tasa ran zuwa kano,
Mikewa tayi daga saman kujerar tace"shikenan daddy,zan tambayeshi,Allah yasa yabarni,"ta ƙarasa maganar tare da barin wurin da sauri ta wuce ciki,
Bayan sun kammala yin breakfast ɗin,kowa ya kama gabansa,
A 6angarensu Aunty babba,tafiya ta kankama,Domin kuwa tun yau sun kammala shirinsu na tafiya Enugu,sun kimtsa kayansu da zasu tafi dasu,da asussuba zasu bar Abuja,da farko zasu fara sauka a hotel ne,a washe garin ranar zasu wuce,Cikin dajin da Bokan yake,taci alwashin cewa Sai taga bayan Hosana,saboda itace silar tonuwar asirinta,kuma A sanadinta ne tarasa igiyar auranta ɗaya,Bayan haka kuma taci alwashin saita Sanya soyayyar Abra acikin zuciyar Sgr,fiye da yadda ya Ke son iyayenshi,
Tashin hankali!Rayuwar hosana na cikin haɗari,
Shin ina hayaam dake a kwance gadon asibiti cikin mawuyacin hali,har yau ba ta dawo cikin hayyacinta ba,Gashi likitocin sun nemi wani makusancinta sun rasa,babu wani atare da ita,baiwar Allah,bamu son ya zata ƙare ba,
Gab da sallar magrib,Wayarta dake ajiye saman gadonsu ta shiga ringing,a lokacin tana acikin toilet,Jahad ce kawai acikin bedroom ɗin nasu,tayi zaman cin tuwo saman gadon,ta ƙura ido tana kallon k-drama acikin system dinsu,Hannu tasa tare da daukar wayar Sehrish,ta duba mai kiran nata,Sunan Aunty azeema ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,picking tayi tare da manna wayar a kunnanta,
"Assalamu alaikum,mommy azeema"
On the other hand azeema tace"Daughter,kin ga saƙo na"?_
Murmushi jahad tayi kafin tace"Aunty azeema yanzu baki gane muryoyin mu?Jahad fa ce ba rishi ba,"
Hajiya azeema tace"wlh naso in ɗauki muryarki,Ashe second daughter ce,To ya kike"?
"Lafiya lou Alhamdulillah ina lafiya,"
"Madallah,Amaryar junaid,"
Cike da jin kunya jahad tace"Aunty azeema waya faɗi zancen nan,"
Dariya hajiya azeema tayi kafin tace"oh kin manta matsayina a wurin daddynku ne?Ae shi da kanshi ya sanar dani,kuma naji daɗi wlh,Junaid zai samu kamilar mace wadda zata kula da rayuwarshi,"_
kayataccen murmushi jahad ta saki,ba ƙaramin daɗin maganar taji ba,
"Ina fata zaki kula mana da bugun zuciyar mu?
Dariya jahad tayi tana faɗin"in sha Allah,zan kula maku dashi,"
Hajiya azeema tace"Yawwa My daughter,but akwai abunda nakeso na tattauna tare dake game da junaid!amma ki bari zan kira wayarki,ko zuwa anjima ne,"
"To Aunty Allah yakaimu anjiman lafiya,"
"Ameen daughter,ina sehrish ɗin take ne?inaso nayi magana da ita ne,"
Jahad na ƙoƙarin bude baki tayi magana,sai ga sehrish ta fito daga toilet din,jikinta sanye da bathrobe,wankan marece tayi,dama duk in tana period,kusan sau uku take yin wanka,'
Ganin wayarta a hannun jahad yasa ta tunkarota tana tambayarta wanene ya kirata,
Mika mata wayar jahad tayi"kar6i nan,Mommy azeema ce keson magana dake"
Jiki na rawa ta kar6i wayar,da sauri ta koma gaban mirror,ta zauna saman kujerar,sannan tayi mata sallama,
"Daughter,ya ake ciki ne?ina fata kinga saƙona ko"?
..Sehrish tace"nagani,junaid ya kawomin su,nagode sosai,"
"Yawwa,Zaki ga turarurruka aciki,Tun yanzu zaki fara amfani dasu,akwai wasu sirrika atattare dasu,sannan akwai mayuka na gyaran fata,dana gyaran gashi,Original ne,Cikin one week,kina fara amfani dasu zaki ga sauyi a jikinki,Sannan akwai sauran kayan da ba yanzu zakiyi amfani dasu ba,suna da haɗarin gaske,su kansu turarurrukan nan,Shu'umaine na gaske,Fisgar mutun sukeyi kamar magnet,ƙarfi ne dasu,duk in zaki shafasu ki bari sai in zaki part ɗinsa,idan ba haka ba gaskiya za'a iya samun matsala,"
Natsuwa sehrish tayi tana sauraronta,sun jima suna waya kafin daga bisani su kayi sallama,
Kasa yin amfani da turaren tayi,tsoranshi ma take ji,tunda taji ance fisgar mutun yake yi,kada ta jama kanta bala'e tana zaman zamanta lafiya,
bata shafa turaren ba,Amma ta fara amfani da mayukan gyaran jikin,
Shaf shaf ta shirya cikin Doguwar riga ta material black colour,mai zanen manyan flowers a jikinshi launin ash,rigar tabi shape ɗin jikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba gaban mirror ta koma ta zauna,powder ta murza a fuskarta,Sannan ta shafa man baki,la66anta sae salƙi sukeyi,
Bata yafa komai akanta ba,Iya sumar kanta ce data sauko har gadon bayanta,high hills ta zura a ƙafarta,
Kama hanyar fita daga ɗakin tayi da sauri jahad tace"Ina zuwa?
"Zanje part ɗin babban yaya ne,Inaso na gyara mashi ne,"
Murmushi jahad ta saki tare da mayar da idonta kan system ɗin gabanta,
"Kinyi kyau sosai,kada fa ki zautar mana da babban yayanmu a rasa gane kanshi,"
dariya sehrish tayi batare da tace komai ba,ta fuce daga dakin,
Babu kowa a falon,da alama duk sun tafi yin sallar magriba ne,tana cikin tafiya,kwatsam taji an ruƙo sumar kanta ta baya,a firgice ta juya don taga wanene,Gabanta ne ya faɗi rass!ganin Haroon kamar wani maye haka ya kama dogon gashin kanta,yakai shi izuwa saitin hancinsa yana shinshinar ƙamshinshi,
A wani irin tsorace sehrish ta buge hannunshi,sam batasan cewa zata hadu dashi ba,da batayi kuskuren fitowa daga dakinsu ba,batare da ta sanya mayafi ba,
Fuskarta a daure tace"Dan Allah menene haka"?
Shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"Shauƙi,"
Harara ta watsa mashi,aranta tace"Mai hali bai ta6a canzawa dama saida raina ya bani cewa karyane tuban da yace mun yayi,"
Guntun tsoki taja,da hanzari ta juya zata wuce saman stairs din,aikuwa da sauri ya sha gabanta ƙiris ya rage ƙirjinta ya daki nashi,hakan ba ƙaramin daga mata hankali yayi ba,
"Ka bani wuri na wuce,banason wannan rashin wayon naka,Bakasan cewa ni matar aure bace,"
Ta6e bakinshi yayi tare da cewa"And then so what idan ke matar aure ce?Nafa son komai,auren yarjejeniya ne,mutumin nan fa da kika kwallafa rai akanshi ba sonki yake yi ba,Ni ne mosayinki,inason ki sosai,kuma ashirye nake dana aureki da zarar ya sake ki...."
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta,tuni idanuwanta suka cicciko da kwalla,ta tsani taji ance mata haka,
Ranta a matuƙar 6ace tace"Wlh koda ace mazan duniya sun ƙare duka kaf babu su,kai kaɗae ne ka rage sai dabbobi a cikinta,to na ƙwammace in auri Biri da in aure ka,"
Waro ido waje yayi yana kallonta a hasale yace"Ke!ni kike gayawa wannan maganar?baki da hankali ne?ki rasa dawa zaki haɗani sai biri,kina nufin cewa biri yafi ni mahimmanci a wurinki"?
"Ƙwara shi dabbane,kaifa mutunne mai hali irin na dabbo...."_
Bata ƙarasa maganar ba,a fusace haroon ya sanya tafin hannunshi ya ɗauke ta da mari,Sae dai kafin ya janye hannunshi daga saman kuncin ta,yaji shima an dauke shi da wani irin zazzaffan mari,Kuma kafin yayi wani yunƙuri yaji tafukan hannaye again har biyu asaman fuskarshi,Tashin hankalin
Wasu irin baƙaƙen taurari ya gani acikin idanuwanshi,tsabar raɗaɗin da ya ji ne yasa shi sakin ihu,yana tangal tangal zai fadi,gaba daya duk yabi ya susuce,har fitsari sae da ya saki a wondonshi,saboda tsabar raɗaɗin daya ji,
A galabaice yace"Na shiga uku!Meke faruwa dani ne!dan Allah ataimakamin duhu cikin idanuwana,"
Shessheƙar kuka kawai sehrish keyi hannunta dafe da kuncinta,mutum biyu ne suka mari haroon,shigowarsu kenan Suka ganshi ya sharara mata mari,aikuwa da gudu Abusufyan ya ƙaraso ya kwashe shi da mari,Marshal Omar kuwa,Hannu biyu yasa ya ɗauke shi da Mari ta baya,hakan yasa yaji duuuuum acikin kunnanshi,babu wani sauti kwata kwata,kamar ya kurmance,
Ruko hannunta Marshal yayi"kiyi haƙuri kinji,dan Allah ki daina kuka," side hug yayi mata yana dan bubbuga bayanta,Abusufyan kuwa sam ya kasa magana sai faman huci yakeyi,ranshi yayi mugun 6aci,
"Banaso Sgr ya shigo yaji wannan aika aikar da haroon yayi,don wlh sai ya ɗanɗana kuɗarshi,Sehrish ki wuce bedroom ɗinku,ki barni dashi,zaici ubanshi ne,"
.. Cikin shessheƙar kuka tace"Part din babban yaya zanje in gyara mashi"
Tayi maganar tare da wuce wa upstairs da sauri tana ci gaba da yin kukan,
"Uncle,dan Allah ka shiga daga ciki,Ni zanji dashi,"
Jinjina kai kawai Abusufyan yayi tare da juyawa yabar falon,
Kwakkwaran damƙa Marshal yayi ma wuyan rigar haroon dake a zube ƙasa yana birgima,ɗaɗɗago dashi yayi ya jashi,har izuwa ɗakin da suke hukunta mai laifi,lallai haroon ya ta6o ma kanshi,
Lokacin da sehrish ta faɗa cikin palourn shi,Saman sofa ta zauna tana cigaba da yin kukan,taji zafin marin da haroon yayi mata sosai,abun ya tsaya mata aranta,tsanarshi ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarta,ta jima a zaune batare da ta motsa ba,har aka kira sallar isha'e,sae bayan da aka kammala sallar sannan ta miƙe ta wuce cikin bedroom ɗinshi,toilet ta fara shiga ta gyara mashi,kafin ta dawo bedroom ɗin nashi tana gyarawa,har lokacin bata daina yin shessheƙar kukan ba,
Bayan ta kammala gyara mashi part ɗin nasa,kasa tafiya tayi saboda a ƙagare take daya dawo,saboda tayi mashi maganar zuwansu kano,Addu'arta Allah yasa yabarta taje,
Safa da marwa ta shiga yi acikin bedroom ɗin nashi,gajiya tafara yi da yin yawon,wuri ta samu daga gefen gadon ta zauna,gyangyaɗi ta fara yi a ƙarshe bacci ya kwasheta,bata ƙara sanin meke wakana ba,
*SGR*
Around 12 ya dawo cikin gidan,Army trouser ne ajikinshi,sae farar shirt mai dogon hannu,Lokacin daya shiga bedroom ɗinshi bai ankara da ita ba,rage kayan jikinshi yayi kafin ya shiga toilet,bayan ya kammala yin wankan,Ya fito sanye da bathrobe ajikinshi,gaban mirror ya tsaya sai da ya kammala shafe jikinshi da tsadaddun mayukan jikinshi,ya gyara sumar kanshi sosai,kafin ya koma wurin closet ɗinshi,after some minutes ya dawo cikin ɗakin jikinshi sanye da Sleeping dress Red colour,yayi wani fresh dashi,tunanin kiranta yayi a wayarshi don ta kawo mashi dinner ɗinshi before ya kwanta,Yana ƙoƙarin juyawa don yaje ya ɗauki wayarshi daya ajiye saman drawer ɗinshi,wayar ta shiga ruri,da sauri ya ƙarasa tare da ɗaukar wayar,duba screen ɗin wayar yayi sunan*Uncle donald*ne ya bayyana,
Picking call ɗin yayi a natse ya kara wayar a kunnanshi,Cikin harshen Spanish suka soma yin maganar,wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana cigaba yin wayar,fuskarshi asake da alama ba ƙaramin farin ciki yake da kiran ba,
Sun jima suna magana da uncle ɗin nashi,kafin sukayi sallama,mayar da wayar yayi saman side drawer ɗin ya ajiyeta,sauke ajiyar zuciya yayi tare da kwantar da bayanshi asaman laps ɗin sehrish batare da saninshi ba,lumshe idanuwanshi yayi a hankali ya ɗan waresu,ƙoƙarin juyawa yayi karaf eyes ɗinshi suka sauka akan hannunta,Har sai da gabanshi ya ɗan faɗi rass saboda baiyi tsammanin ganin mutum a cikin bedroom ɗinshi ba,kuma farat ɗaya bai gane cewa ita bace,A sukwane ya miƙe zaune yana kallonta,cike da mamaki,Hankalinta kwance sae sharar baccinta takeyi,Abun ya ɗaure mashi kai har saman gadonshi,
Clapping hands ɗinshi yayi,A firgice sehrish ta farka,Sakamakon sautin da taji na tafin da sgr yayi mata,A Ruɗe ta miƙe daga zaune,sumar kanta duk ta yarfo ta saman fuskar ta rufe mata idanuwanta,hakan yasa bata iya tantance wanene ba,Amma ranta na bata cewar mamallakin ɗakinne ya dawo,Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoro ya hana ta janye gashin kanta daya rufe fuskarta don taga wanene,
Shi kuwa boss man ɗin ya zuba ma sarautar Allah ido,ganin ta kaza yin motsi yasa shi yin magana
"Bacci asaman gadona"?wani irin wahallan yawu ta haɗiya,
Muryarta na kerma tace"Am Sorry yaya rafayet,wlh bansan bacci ya ɗauko ni ba,Asaman gadonka,Na tsaya ne saboda inason yin magana dakai,"
Matsawa yayi kusa da ita,ta maƙure ajikin head board ɗin gadon,
A hankali ya sanya hannu tare da ruƙo doguwar sumar kanta,Ya yarfar da ita gefe guda,ta sauka asaman kafaɗarta,runtse idanuwanta tayi da sauri saboda bazata iya jurar kallon cikin nashi idanuwan ba,Ƙwayar idonshi ba ƙaramin rikitar da ita takeyi ba,Hada ƙarin ƙwayar idon yasa take jin tsoranshi,
"Neman me kike yi mun"?yayi tambayar a yayin da yake saukar da idanuwanshi saman lips ɗinta,
"Dama,na tura maka saƙo ta whatsapp ɗinka,bansani ba ko ka gani,"tayi maganar tare da buɗe idanuwanta,suka sauka kan fuskarshi da sauri ta kawar dasu izuwa saman yatsun hannunta data aza asaman laps ɗinta,
"I saw it already,naji complain ɗinki,Bayan wannan tashinki da nake yi in midnight,baya takura maki"?
"A'a,Nima ina samu nayi sallah,"
Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Okey,je ki kawomin dinner ɗina,'
Amsa mashi tayi da toh,kafin ta sauko daga saman gadon,tayi mamakin yadda yake yi mata magana cikin sanyin Murya babu wannan faɗan,tayi tunanin cewa,Zai ɗauke ta da mari ne,amma sai taga akasin hakan,
Har ta kusa fita daga bedroom ɗin nashi ta ɗan dakata da yin tafiyar,ta juya tare da kallonshi a lokacin harya kwanta,
"Yaya rafayet"ta ambaci sunanshi,
Har cikin kunnanshi,tsayar da idanuwanshi yayi akanta,Yana jiran jin me zatace,
"dama gobe daddy zai tafi kano,kuma yana so ya tafi tare dani,"
Shiru ya ɗanyi na wani lokacin kafin yace"dole sai dake za'a je kano ɗin ne? ba wani wanda zai iya replacing ɗinki"?
tunda taji haka,jikinta yayi sanyi,
Muryarta tamkar zata yi kuka tace"Akwai,"
Bai ƙara tanka mata ba,kama hanya tayi ta fuce,sai da ta sauko downstairs sannan ta fashe da wani sabon kukan,Ta kwalfa rai akan son zuwa Kano,
*tawaga biyu zasu yi tafiya gobe in Allah yakai mu,Tawaga ta farko zasu tafi neman wani da suka rasa a rayuwarsu,Tawaga ta biyu kuma zasu tafi wurin boka neman sa'a,*😱😳
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Na biya bashi😏
Masu buƙatar littafin Suyi mun magana direct ta layina amma fa message ta whatsapp kawai,Ko an kira ba'za a samu ba, 08103884440
❤🤍❤
Tun wuraren ƙarfe Goma,Motarsu Abusufyan tayi dirar mikiya acikin jahar Kano,Da kanshi yake yin driving ɗinsu,Jahad na manne a kafaɗarshi tana sharar baccin da bata ƙarasa ba a gida,
Tunda suka shigo cikin garin murmushi ya wanzu akan fuskarshi,Bakomai yake tunawa ba fa ce irin rayuwar da yayi acikin garin tun lokacin ƙuruciyarshi,
"Jahad!ki tashi mun ƙaraso fa,"cike da farin ciki yayi maganar,
Sai da ya ambaci sunanta kusan sau 5 kafin ta amsa mashi,tare da miƙewa daga zaune tana yin hamma,ta cikin face mask ɗin dake a fuskarta,
Buɗe idanuwanta tayi tare da juyawa tana ƙarewa garin kallo ta cikin glass ɗin Motar,hakanan ta dinga jin faɗuwar gaba rass!rasss!lokaci guda kuma tashiga tariyo abunda ya faru acikin rayuwarsu azamansu garin,
NASARAWA G.R.A
Shine Sunan Unguwar da hajiya Ameenatu Wato Gwaggon katsina tayi rayuwa acikinta tare da ahalinta,a hankali motarsu ta shigo cikin unguwar da matsakaicin gudu,A dai dai jerin wasu manyan gidaje na masu hali,Abusufyan ya tsayar da Motar a bakin gate,
"Daddy wannan gidan wanene'?tayi tambayar tana kallon fuskarshi,
murmushi ya ɗan yi tare da cewa"Wannan gidan da kike gani acikinsa nayi rayuwa tare da mahaifiyarku,Kuma anan kakan ku Marigayi baba buzu yayi gadi,Allah ya jiƙanshi da rahama,
Amsa mashi tayi da Ameen,kafin suka fito daga cikin motar,
"Allah sarki,Kullum idan nadawo a wancan lokacin,Baba buzu nake samu zaune saman benci yana dafa ruwan bununsa,da zarar ya hango motata zai fara yi mun kirari,Ya buɗe mun gate don in shiga daga ciki," acewar Abusufyan,
Jefi jefi mutane ke giftawa acikin unguwar,tun bayan da suka bar kano a lokacin baya,Mijin Gwaggon katsina ne ke zama a cikin gida kafin Allah yayi mashi rasuwa,Tun daga lokacin kuma babu wanda ya ƙara zaman gidan,ko Dr harris idan yazo kano ya kwammace ya kama hotel ya zauna acikinsa,
Hannu ya zura acikin aljihunshi ya curo key ɗin gidan,Ya ƙarasa tare da zura key ɗin ajikin ƙopar dake manne da gate ɗin gidan,Wurin har ya fara tsatsa,ya ciccije daƙyar ya samu ya buɗe ƙopar,
Ya ruƙo hannunta suka shiga daga ciki,
Zuba ma gidan ido tayi tana kallonshi,A ranta tana ayyana irin rayuwar da mahaifiyarsu tayi acikin gidan,Ya haɗu duk da ginin Ya tsufa sosai,akwai fili sosai,Ga wurin buga ball nasu Abusufyan,Ga moto park,da sauransu,
Kaitsaye suka nufi Ƙopar da zata sadaka da Babban falon gidan,ita kuwa ta zuba ido tana ƙarewa gidan kallo,Uwar yanace ta ko'ina yayi datti,ga tarin ƙura musamman ajikin glass ɗin windows dana doors,
Buɗe masu ƙopar yayi da key ɗin hannunshi,Yayi gaba tabi bayanshi,Kamar mai jin tsoro haka ta zura ƙafarta ciki,Matsakaicin falo ne,Yadda kasan bola,ledoji,yayi da sauran tarkace a kasanshi,Tiles ɗin kuwa duk yayi dirty kura ta rufe shi,Sofas ɗin dake a ɗakin duk sun gajarce sunyi ƙanƙanta,yadin jikinsu yayi diƙiƙi,
"Daddy,ina ɗakin da Oumman mu tayi rayuwa acikinshi?ka nuna mun inaso naga ɗakin,"
Da yatsan hannunshi ya nuna mata bedroom ɗin da abu tayi rayuwa,da sauri ta nufi ɗakin,shima yabi bayanta,A datse ƙopar ɗakin take amma babu key ajikinta,da ƙarfi yasa hannu ya turata,ji kake ƙiiiiiiii,ta buɗe a slow,
Faɗawa cikin ɗakin tayi tana bin kayan cikinshi da kallo,labulayen duk sunyi ƙura,sun nannaɗe sun cukuikuye,Carpet ɗin bakin kofar ya fita hayyacinshi,Single bed ne acikin ɗakin,sai wardrobe ta bango,itama duk tayi ƙura,book shelve,Da dressing mirror da sauran tarkace,komai yafita hayyacinshi,
Qur'ani ta hango saman bedside drawer ɗin gadon,
Tun kafin tayi magana Abusufyan yace"Wancen qur'anin da kike gani na mahaifiyarku Ne,mace ce mai son addini tana ƙoƙari sosai,bata wasa da ibada,da haka ta sace mun zuciyata,"
Hawaye ne suka soma sintiri akan fuskarta,ƙarasawa tayi gaban drawer ɗin ta sanya hannu tare da shafa al'qur'anin,ta kakka6e ƙurar dake akanshi,ɗago dashi tayi a hankali ta manna mashi kiss,
"Daddy inason qur'anin nan sosai,zamu tafi dashi,"ta ƙarasa maganar tare da buɗe handbag ɗin dake hannunta,ta zura shi ciki,"
School bags ta hango guda biyu,Anyi hanging ɗinsu a saman bango inda aka bubbuga ƙusa,
Da sauri ta ƙarasa tare da kai hannu ta curo jakunkunan,ta sauko dasu ƙasa,ta zuƙunna tare da buɗe jakar,Littattafan addini ne cikinsu,Ahlari ne,Tajweed,Fiqhu,da sauransu,ɗayar jakar kuma da ta buɗe Littattafanta ne na boko da take zuwa school dasu,komai nata mai tsari,
Abusufyan kuwa wurin wardrobe ɗin kayanta ya wuce,buɗewa yayi yana kallon jerin wasu daga cikin kayanta,Uniform ɗin islamiyyarta ya ɗauko,tare da rungumesu a ƙirjinshi,Sae lokacin hawaye suka shiga zarya akan fuskarshi,
Bazai ta6a mantawa ba,da rana ta farko daya fara sanyata acikin idanuwanshi,a lokacin tana kan hanyar dawowarta daga school,
"Jahad,"ya ambaci sunan ta tare da juyawa yana kallonta
"Na'am Abba,tayi maganar tare da miƙewa ta ƙarasa gabanshi,
"Kin ga waɗannan kayan,dasu ne na fara ganin Oummanku,Uniform ɗinta ne na islamiyya,"
Murmushi ta saki tare da sanya hannu ta kar6i kayan,Rungumesu tayi ajikinta,Sae ta dinga jin tamkar Oumman tasu ta rungume,
6ata lokaci sukayi sosai suna bincike acikin ɗakin Zainabu abu,
Daga bisani ne Yunwa ta fara kamasu gashi gidan babu abinci,Yanke shawarar zuwa nemo masu abincin yayi,ya barta acikin gidan,Gyara masu ɗakin oummansu ta shiga yi,Taci baƙar wahala sosai,Bayan ta share ɗakin har wanke shi tayi,A kitchen ta samu bokiti da ledar detergent,ga ruwa available,sosai ta wanke ɗakin sai ga tiles ɗin yayi haske sosai,Cire zanin gadon tayi ta ɗauko wani acikin wadrobe,Ta shimfiɗa masu bayan ta kakka6e gadon,ta goge jikinshi,
Hatta glass door din sai da tabi tayi scrubbing ɗinsu,ta goge yanar ɗakin,lokaci guda kamanin ɗakin suka canza,Komai na son gyara,Toilet ta shiga nan ma tataras dashi duk sai a hankali,sae da ta fara gyarashi fess,Sannan ta samu ta ɗan watso ruwa tare da ɗauro alwala,
Darduma ta dauko cikin wadrobe ta shimfiɗata,ta kabbara sallar azhar,A tsanake tayi sallar tana kammalawa,agalabaice bacci ya ɗauketa saman dardumar,
Wuraren ƙarfe 2:30 Abusufyan ya shigo cikin gidan hannunshi ɗauke da Ledojin da yayi masu take away na restaurant,
Da sallama ya shiga cikin falon,wuce wa bedroom ɗin yayi,ba ƙaramin mamaki yayi ba,ganin yadda Jahad ta gyara ɗakin tsaf,komai yayi fess,kamar lokacin da Zainabun shi na nan,
Murmushi ya saki tare da samun wuri kasa gefenta ya zauna,Ya ajiye ledojin,Hannu yasa abayanta ya ɗan bubbugi kafaɗarta"Jahad!tashi muci abinci,"
Firgita tayi ta farka tana Sambatu"Ya Rafayet,baisan na taho ba...,"
Ƙiris ya rage yaji abunda tace,
Hannu tasa da sauri ta toshe bakinta,tana kallonshi,Shima kallon nata yake yi,
"Me kika ce"?girgiza mashi kai ta shiga yi,tana faɗin"bakomai Daddy,Ashe ka dawo,nagaji ne shi ne na ɗan kwanta don in huta,"
Murmushi yayi tare da cewa"Ae naga aikin da kikayi,kin yi ƙoƙari sosai,"
"Bari na ɗauko mana plate,"ta miƙe tare da nufar hanyar fita daga ɗakin,
Sai da tafito sannan ta dafe saitin zuciyarta tana faman sauke ajiyar zuciya,a ranta tace"Allah yaso daddy baiji abunda nace ba,dashi kenan zai gano ni,"_
Tayi maganar tare da yin saurin wuce wa cikin kitchen ɗin,A cikin kwandon wanke wanke ta samu tray da plates tare da cups,gaban basin taje ta wanke su tass da klin da soso,ta ɗaurayo su,bayan ta kammala wankesu saman tray din ta jera su,Ta ruƙosu a hannunta sannan ta dawo cikin bedroom ɗin,
"Salamu Alaikum"Ta kwaɗa sallama ta shiga ciki,Zuƙunnawa tayi ta ajiye trayn agaban Abusufyan,
Janyo ledar tayi ta buɗe,tare da sanya hannu ta curo fried meat(tsiren nama)ta jera masu shi asaman tray,hannu yasa ya taimaka mata wurin ɗauko sauran kayan,Cool Drinks ne da sauran kayan maƙwalashe,atare suka shiga ci suna fira gwanin ban sha'awa,bayan sun kammala cin abincin,Abusufyan ya tattara kayan abincin da sukayi amfani dashi,Ya wuce dasu kitchen yabarta zaune tana shan lemu,bayan ta shanye,ta sanya robar a dustbin,komawa tayi saman gadon ta kwanta,cikinta yayi haƙe² saboda cin muguntar da ta yi,wani baccin ne ya sake ɗaukarta,
*Boss Bature*
❤🤍❤
Wuraren ƙarfe 3 na rana Sgr ya dawo cikin gidan,Tun bayan da ya fita da safe Ko breakfast bai nema ba,saboda Emergency call ɗin da akayi mashi acan headquater ɗinsu,Jikinshi na sanye da Tank Top,light green,Tare da wandon kaki,Yayin da kunnanshi ke manne da wayarshi,Cikin harshen faransanci yake yin waya,
Da sauri da sauri ya haye upstairs,direct ya wuce part ɗinshi,tunkan ya shiga ciki ya fara jin daddaɗan ƙamshi nakai mashi ziyara acikin hancinshi,gaba daya yayi tsammanin cewa zai same ta ne a part ɗin nashi amma baiga Kowa ba Wayaam,Bedroom ɗinshi ya shiga,Shaf shaf ya rage kayan jikinshi ya faɗa cikin toilet,After some minutes ya fito waist ɗinshi ɗaure da towel,Yana tsaye agaban mirror yaji motsin mutun acikin falonshi,
"Who's there"?yayi tambayar yana jiran amsa,
"Sehrish ce,"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da cewa"Come in,"
Hannunta na ruƙe da tray na Lunch ɗinshi da ta shirya mashi,tana tafiya gabanta na faɗuwa rass rass
Sallama ta fara yi mashi ya amsa,kafin ta sanya ƙafa ta shiga ciki,sum sum ta lalla6a ta ajiye mashi tray asaman table,Jiki na rawa ta juya zata bar ɗakin,
Zuba mata ido yayi ta cikin mirror yana kallonta,tana ƙoƙarin ɗaga ƙafarta tabar ɗakin taji ya Ambaci sunanta kai tsaye"JAHAD"
DARAAAM!!!!!!Taji gabanta ya faɗi,sanƙamewa tayi atsaye,hankalinta a matukar tashe,tuni zufa ta shiga wanke mata fuskarta,Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya abakinta,Abun ya ɗaure mata kai,farat ɗaya Sgr ya gane cewa ba Sehrish bace,Hatta junaid yau bai ganeta ba,kowa ɗaukar sehrish yake yi mata,saboda sunsa ma ransu cewa da jahad aka tafi,Shiyasa basu natsu sun gane cewa itace ba,"
Wata irin zufa ce ta shiga gangarowa asaman fuskarta,ƙiris ya rage ta saki fitsari a wando,
Slowly ya juyo tare da tunkararta,jikinta sae kerma yake yi,hannunta ya ruƙo tare da juyo da ita ta gabanshi ya kasance suna fuskantar juna,wuƙi wuƙi tayi mashi da idanu tana faman mazurai na rashin gaskiya,
Abun ya ɗaure mashi kai,Wai harshi zasuyi wa wayau,kamar wani soko,An gaya masu cewa a banza yakai muƙamin da yake dashi a yanzu,
goya hannayenshi yayi asaman wide chest ɗinshi,Ya zuba mata ido yana kallon Ikon Allah,
Saboda tsabar rashin gaskiya tun kafin ma yayi mata magana,murya na kerma tace"Amm...um..babban..yaya pls dan Allah kayi haƙuri ka yafe mun,Wayyo Allahna na shiga uku,"a ruɗe tayi maganar,tana yarfa hannuwanta,tsoranta kada ya kwashe ta da mari,
Ruke ha6arsa yayi cike da mamaki yake kallonta from head to toe,
Hawaye ne suka soma shararowa akan fuskarta,tun kafin ma taji hukuncin da zai yanke mata,Zuciyarta sae bugawa take yi ba ƙaƙƙautawa,
"Where's she"?fuskarshi a ɗaure yayi tambayar,
Sunnar dakai tayi kamar munafuka,daƙyar ta iya buɗe baki tace"Wlh baban yaya ni bani nace ta tafi ba,yau ne dama da asuba,ta same ni cikin damuwa take tambayata lafiya shi ne na sanar da ita cewa Ni banso nabi Daddy kano,bansan zuwa garin saboda abunda ya faru damu acikinshi...."
Tunkan ta ƙarasa maganar yace"What!tafiya tayi without My Permission,"ranshi a matuƙar 6ace yayi maganar,
"Ya salam"ya furta hakan tare da zura hannunshi cikin sumar kanshi,
Ya runtse idanuwanshi,
"Am sorry,babban yaya bazan ƙara ba,"_
Jinjina kanshi yayi tare da ware idanuwanshi akan fuskarta,yana kallonta duk tabi ta susuce,
"Kin iya frog jump ko"?
Waro ido tayi tana kallonshi,girgiza kai tashiga yi alamar a'a,
...ruko hannunta yayi ya fito da ita cikin falonshi,fuskarshi a daure yace"Oya,start from here,karki kuskura ki tsaya,if not zaki ga abunda zai biyo baya,"
Jahad tamkar zata fashe da kuka,Zuƙunnawa tayi tare da kama kunnanta kamar ɗan kwaɗo haka tafara yin tsallan tana zagaye kujerun,tun a first round jikinta ya fara gaya mata,Komawa yayi cikin bedroom ɗinshi ya ɗauki wayarshi daya bari agaban Mirror,Numbar Uncle Abusufyan ya lalubo,ya danna mashi Call,
A lokacin Abusufyan,Na acikin kitchen ya tu6e rigarshi daga shi sai shorts,ya dage sai aikin goge goge yake yi da ƴan wanke wanke,ya gyara kitchen ɗin tsaf,
Fitowa Sehrish tayi hannunta ruƙe da wayarshi,har tuntu6e take yi wurin yin sauri donta kai mashi wayar,tana baccinta mai daɗi ringing ɗin wayar shi ne ya tashe ta,
"Daddy,ana kira,"ta ƙarasa maganar yayin da take shiga kitchen ɗin,hannu abusufyan yasa ya kar6i wayar,duba screen din wayar ya fara yi,
*My first in-Law* Shi ne sunan daya bayyana akan screen ɗin,Yayi mamakin ganin kiran Sgr,Picking call ɗin yayi ya kara wayar a kunnanshi,
"Assalamu Alaikum"
On the other hand,Sgr ya amsa mashi"Wa'alaikum salaam,Uncle kun isa Lafiya"?
. "lafiya Lou,ae tun ɗazu muka ƙaraso,"
"Okey,inason magana da sehrish ne,tana a kusa"?
Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"Ae bada ita muka zo ba,ko ka manta ne?
"Uncle,Da ita ka tafi bada Jahad ba,yanzu haka jahad tana a part dinta,Sunyi musaya ne,"
Cike da mamaki abusufyan yace"Jahad tana a gida!"
Gaban Sehrish ne ya faɗi rass,wuƙi wuƙi tayi da ido,ɗagowa abusufyan yayi tare da kallonta,Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,sai lokacin ya shaida cewa Sehrish ce,ya ɗauko amatsayin Jahad,Ko ya akai suka shirya Wannan batare da kowa ya ankara ba,
Sunnar dakai ƙasa tayi,ganin irin kallon da daddynsu yake yi mata,
Rai a6ace ya miƙa mata wayar"Kar6i nan,"
Hannunta na kerma ta kar6i wayar,hankalinta a matuƙar tashe,ta sanya wayar a kunnanta,muryarta tamkar zata yi kuka tace"Ya rafayet........"
Tunkan ta ƙarasa maganar ya daka mata tsawa"Shut up!"nan take ta shiga taitayinta,
"da iznin wa kika bar garin nan"?_
Idanuwanta ne suka cicciko da kwalla,Sae faman kallon uncle take yi,sam baiji daɗin abunda sehrish tayi ba,don yasan ƙarshe kanshi abun zai ƙare,
"Am sorry ya rafayet,dan Allah kayi haƙuri,Bazan ƙara ba,"
dogon tsoki yaja,Kafin yace"Come back home,In ba haka ba,Ranki zai 6aci,"yana faɗin hakan yayi rejecting kiran,
Fashewa tayi da matsanancin kuka,
Hannu abusufyan yasa ya kar6e wayar,
"Koma meya laifinki ne!Ashe baki da hankali Sehrishi!Why kike son Jamin ina zaman lafiyana?,Taya zaki kamo hanya batare da iznin Mijinki ba,?"
Cikin shesshekar tace"dan Allah daddy,kayi haƙuri,na kwallafa raina ne akan son zuwa,nasan nayi laifi,Kuma nayi danasanin yin hakan,Amma dan Allah daddy,Ka roƙan mun alfarma a wurinshi,Yabarni in zauna,Saboda yace in koma gida yau ɗin nan,"ta ƙarasa magana tare da sanya hannu tana share hawayenta,
"I can't Call him Sehrish,rafayet bazai saurari kowa ba a halin yanzu,Kawai kije ki shirya kayanki,in kaiki tasha ki hau mota,"
Jin haka yasa ta ƙara fashewa da matsanancin kuka,tana faɗin"dan Allah daddy,kada ka mayar dani,Nashiga ukuna,"
Sosai take kuka,Shi kanshi ya tausaya mata,duk yadda take shakkar Sgr amma ta kama hanya ta baro gidan batare da izninshi ba,tabbas ba ƙaramin son zuwa takeyi ba,
Muryarshi a sanyaye yace"Kiyi hakuri daughter,babu yadda zamuyi dole ki bi umarnin Mijinki,lokaci yana ƙurewa,ki je ki shirya kayanki,mu tafi tasha,"
Juyawa tayi da gudun gaske,Ta koma ɗaki,Saman gadon ta faɗa tare da fashewa da wani sabon kukan,
Jikin abusufyan ba ƙaramin sanyi yayi ba,yaso ace akwai wata hanyar da zai iya taimaka mata,don ta zauna a kanon,Amma ba halin yin hakan,
yana cikin wannan zancen zucin wayar shi ta shiga ruri,da sauri yakai idonshi kan wayar dake hannunshi don yaga mai kiran nashi,Sunan Yaya Hossein ne ya bayyana akan screen din wayar,
Da sauri ya answer kiran ya kara wayar a kunnanshi"Assalamu Alaikum,Yayana na kaina"_
On the other hand,Abba yace"wa'alaikum salam ƙanina na kaina,Ya kake fatan kun isa kanon lafiya,"
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Mun ƙaraso tun wuraren goma,"
Abba yace"Madallah,naji daɗi sosai,kai dawa kuka tafi ne"?
Shiru ya ɗanyi yana tunanin halin da sehrish take ciki,ranshi ne ya bashi cewar Ya sanar ma Yayan nashi,May be ya iya dakatar da Sgr ɗin,
Calmly ya soma magana"Ya hossein,Wlh an samu matsala,Da jahad na shirya tafiya,bansan ya akai ba,su ka yi musaya ita da sehrish,dama ta kwallafa rai akan son zuwa kano,To yanzu haka zancen da nakeyi maka,Muna tare da Sehrish ɗin,Kuma Sgr ya gane cewa da ita muka zo kano,ya bada umarnin ta koma yau yau ɗinnan,baiwar Allah tana cikin damuwa,yanzu haka tana can tana kuka,"yaƙarasa jawabin yana jiran jin amsar da abba zai bashi,
"Kada ka damu,Ka lallasheta ta kwantar da hankalinta,Ni zanyi mashi magana,duk yadda mukayi dashi,in sha Allah i will inform you,"_
Ajiyar zuciya abusufyan ya sauke tare da cewa"Nagode sosai,Yayana nakaina Allah yabar zumunci atsakaninmu,"
"Ameen Ameen,ƙanina,"abba ya amsa mashi before suyi sallama,
Har hankalinshi ya ɗan kwanta duk da yana zullumin amsar da abban zai bashi,don yasan halin Sgr wani lokacin idan ya burkice,mai tankwarashi sae Allah,
A lokacin da kiran abban ya shiga wayarshi,Yana zaune asaman sofa,ya aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,Yana sanye cikin jeans da t~shirt,yayin da jahad ke zukunne agabanshi,Tayi kneel down fuskar nan tayi jaga jaga da ita,tasha kuka har ta gode wa Allah,
Hannu yakai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman front table din gabanshi yayi picking call ɗin,tare da kara wayar a kunnanshi,Ya furta"assalamu alaikum,"
Acan 6angaren abba ya amsa mashi"Wa'alaikum salaam,My son ya kake ya gida,ya kuma aiki"
"Alhamdulliah"
Abba yace"Yawwa,Rafayet dama game da yarainyar nan ne,Sehrish,"tunda yaji ya ambaci sunanta,Ranshi ya bashi cewar sunkai ƙararsa ne,
"Dan Allah rafayet,ka ƙyale yarinyar nan ta zauna,ba jimawa zasuyi acan ba,Yarinyar nan ta kwallafa rai akan son zuwa can shiyasa harta tsallake ta tafi ba tare da saninka ba,Amma kai shaida ne akan yarda takeyi maka biyayya sau da ƙafa,duk wani abu da zai 6ata maka rai,tana ƙoƙari don taga ta faranta maka rai,pls rafayet ta ci albarkacin wannan,"
shiru yayi batare da yace komai ba,
Har sai da abban ya sake cewa"Rafayet naji kayi shiru,"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa"its Okey daddy,na haƙura,"Yanayin yadda yayi maganar,bada son ranshi ba,
Muryar abba ɗauke da farin ciki yace"Ko kaifa,Wlh har naji daɗi acikin raina,Allah yayi maka albarka "
"Ameen"daƙyar ya iya furta hakan,Sallama su kayi ya janye wayar daga kunnanshi,
mayar da idanuwanshi yayi kan jahad yace"U can go"
Miƙewa tayi tana faman ɗangyasa ƙafarta,tabar falon nashi,ba ƙaramin jiki taji ba,Saukowa tayi downstairs tana cigaba da yin shessheƙar kukan,
adai dai lokacin junaid ya faɗo cikin falon,Tsayawa yayi yana kallonta,ƙarasawa yayi da sauri wurinta yana faɗin"rishi lafiya meya faru"?
...ɗagowa tayi da idanuwanta waɗanda sukayi ja saboda kukan da tasha,Waro idonshi ya ɗanyi tare da ambaton sunanta"JAHAD"
Cikin shesshekar kuka ta amsa mashi"Na,am"
Hannu yasa ya tallabo fuskarta,"Dama bada ke aka tafi kano ba"?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,sannan tace
"Tare da sehrish aka tafi,amma dani muka shirya tafiya,Shine mukayi musaya ni da sehrish,yaya rafayet ya gano ni,Shine ya hukunta ni Hada tsallan kwaɗi ya sani,"
Hannuta ya ruko,tare da samun wuri saman sofa suka zauna,
Ranshi aɗan 6ace yace"Allah dana son da haka bazan bari Babban yaya ya sanyaki yin tsallan kwaɗi ba,Meyasa zai sanya juliet ɗita,Aikin wahala,'?
hannu yasa yana share mata hawayen dake sauka akan fuskarta,cikin lallashi yace"stop crying my juliet,Allah in baki daina zubar da hawayenki ba,Nima zan fara kukan,".
Cike da zolaya,ya sanya hannunshi yana murza idanuwanshi,kamar zaiyi kukan,
Da sauri ta ruƙo hannunshi tana faman sauke ajiyar zuciya tace"Nadaina".
murmushi ya saki tare da cewa"Yaushe zamu fita yawo?Da anjima ko gobe"?
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Mu bari sai gobe,Yanzu har la'asar tayi,Nafiso mu fita da wuri,mu zaga garin nan,"
"Yadda kikeso haka za'ayi,"ya karasa maganar,tare da kai la66ansa zai sumbaci gefen fuskarta,Karaf idanuwanshi suka sauka akan na SGR dake ƙoƙarin saukowa downstairs,da sauri ya janye la66ansa,ya shiga ƴan kame kame,
girgiza kai kawai sgr yayi don yaga abunda junaid ɗin ke ƙoƙarin yi,Fita yayi daga cikin falon batare daya tanka masu ba,
*Boss Bature*
*Sehrish*
hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,jin cewa an barta ta zauna a kanon,taji daɗi sosai acikin ranta,duk da tana fargabar hukuncin da Sgr zai yanke mata idon suka koma gida,
Bayan sallar la'asar,Suka shirya tsaf domin zuwa hotoro,Unguwar da sukayi rayuwa a cikinta,Abusufyan ne ke driving ɗinsu,tana zaune a gefenshi tana latse latsen wayarta,Yayin da can ƙasan zuciyarta ke cike fal da fargabar zuwa anguwar,A hankali Motar ta shararowa da matsakaicin gudu,izuwa cikin unguwar bai direta a ko'ina ba sai a ƙofar gidansu,don bai manta da kwatancen gidan ba,duk da yaɗan so ya ruɗe saboda sabbin gine ginen dake a wurin,kasa fitowa sehrish tayi daga cikin motar,Saboda yanayin da tashiga,ta tsani yin toxali da unguwar,Saboda bata son duk wani abu da zai tuna mata rayuwarsu ta baya,
Fitowa abusufyan yayi daga cikin motar ya zagaya,ya bude mata ƙopar,"Daughter,mun ƙaraso fa,"jiki asanyaye ta fito daga cikin motar,yayin da idanuwanta ke cike tab da kwalla,A wani slow ta wurga kwayar idonta akan gidajensu,Ginin ya tsufa sosai,duk fentin ya ƙoƙe,ya gajarce,An garƙame gidan da ƙaton ƙwaɗo,duk yayi tsatsa,da alama anjima ba'ayi amfani da gidan ba,mayar da idanuwanta tayi akan gidansu maman sadeeq,A rufe yake gidan da makulli,Gidan ya tsufa shima Amma bai kai gidansu tsufa ba,saboda an canza mashi fenti,
Hawaye ne suka soma shararowa akan fuskarta,juyawa ta ɗanyi tare da kallon abusufyan dake tsaye,jikinshi duk yayi sanyi,Saboda tunawa da wasu abubuwa da suka faru a rayuwarshi,
Mutanen dake kai komo acikin Layin nasu sai faman leƙensu sukeyi,musamman ƴan yaran anguwar,
"Daddy,Kamar basu nan fa,naga gidan a rufe,"
Uncle yace"Bari na samu yaro na tambayeshi,Muji ko sun tashi ne,"
Yana ƙoƙarin rufe bakinshi,Yaji anyi mashi sallama ta bayanshi,Muryar wani dattijo ne,juyawa yayi tare da kallon mutumin,tsoho ne amma ba irin tukuf ɗinnan ba,jikinshi na sanye da koɗaɗɗen yadi,ƙafafunshi na sanye da wasu siɗaɗdun silifas duk sun fita hayyacinsu,kamar mahaukaci,
Da sauri abusufyan ya miƙa mashi hannu donsu gaisa,
Dattijon ya maƙe hannunshi tare da cewa"Haba Alhajin Allah,baka ga yadda hannuna yake ba duk datti a haka zaka gaisa dani,"
Murmushi abusufyan ya sakar mashi,"dan Allah kada ka hanani gaisawa dakai,"
Mika mashi hannun tsohon yayi suka gaisa,Sannan yace"bawan Allah,ban ta6a ganinka acikin unguwar nan ba,Kuma da alama kamar wani ku ke nema ko"?
abusufyan yace"ƙwarai kuwa,wannan Ƴa tace,Munzo daga abuja ne,Muna neman..umm....."bai ƙarasa maganar ba,saboda ya manta da sunan mutumin,
Sehrish ce ta ƙarasa mashi maganar"Malam nura muke nema,malamin makarantar islamiyya,"
Dattijon yace"Ae nan ne gidan shi,Sae dai kash,Sunyi tafiya zuwa kankia wurin jana'izar Wani kawunshi daya rasu,"
Jin haka yasa yanayin fuskar abusufyan ta ɗan canza,zuwa damuwa,
"Amma,tun yaushe suka tafi"?
Dattijon yace"tun makon daya gabata,Amma jiya munyi waya dashi ya sanar dani cewa Yau ko gobe zasu dawo,"
Ba ƙaramin daɗi suka ji ba,don har sai da abusufyan ya ɗanyi murmushi,
Hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro kuɗi sababbin ƴan dubu dubu kusan dubu goma sha biyar ya miƙa ma dattijon,
Washe baki tsohon yayi tare da sanya hannu biyu ya kar6i kuɗin,tare da cewa"yalla6ai kamar ka sani wlh yau gidana da yunwa muka tashi,yara sai kuka sukeyi,Hakanan na gaji da zama cikin gidan, nace bari na fito na nemi na abinci,Ashe arziƙi ne ke kirana,Allah na gode maka,da ka haɗani da wannan bawan naka,Ya Allah kamar yadda ya farantamun rai,kaima ka faranta mashi nashi,ka biya mashi buƙatunshi na alkhairi,'yana addu'ar hada ƴar kwalla akan fuskarshi,
Atare suka dinga haɗa baki suna Amsa mashi"ameen ameen,
Abusufyan yace"baba taimakon da zakayi mana,idan sun dawo dan Allah ayi gaggawar sanar damu,Bari na baka lambar wayata,
Ya ƙarasa maganar tare da zura hannunshi cikin aljihun wandonshi ya ɗauko wayarshi,
Hannu dattijon yasa,a gaban aljihun rigarshi,Ya curo ƴar ƙaramar wayarshi tecno,taji jiki duk tafita hayyacinta,miƙa ma abusufyan wayar yayi"kar6inan yaro,sanya mun numbarka,kayi mun saving ɗinta da sunan Mai mutunci,Zanfi ganewa,Da zarar sun dawo in sha Allah,bi'iznil lahi,koda ƙarfe ɗayan dare ne zan kira in sanar dakai,"
Murmushi suka saki gaba ɗayansu,kar6ar wayar abusufyan yayi,madannan jikinta duk sun nutse ciki,daƙyar ya samu ya rubuta mashi numbar,yayi mashi saving da Mai mutunci,Sanna ya mayar mashi da wayar"Gashi baba,mun gode sosai,Sai naji ka,Allah yasa adace,"
Tsohon ya amsa mashi da ameen ameen,ae tunda ka farantamun raina,Kaima sai Allah ya faranta maka naka,har addu'a sai nayi maka idan nayi sallah,
"Ina godiya sosai,"ya karasa maganar tare da ruƙo hannun sehrish suka shige cikin mota,key yayi ma motar,a hankali yayi reverse,tare da karya kwana,da gudun gaske ya fuce daga cikin unguwar,
Nasarawa suka koma,a bakin gate din gidan ya sauke sehrish,Saboda zuwa masallaci,An fara kiran magrib,Miƙa mata key ɗin gidan yayi"kar6i nan,ki rufe gidan da kyau,Bazan dawo da wuri ba,Saboda inaso naje nayi mana siyayyar kayan abinci,dana amfani,"_
"Toh daddy adawo lafiya"tasa hannu ta kar6i key din,kafin ta juya ta nufi cikin gidan,tsayawa yayi acikin motar yana kallonta,har saida ta 6ace ma ganinshi,ya tabbatar da ta rufe ƙopar gidan,Sannan ya tashi motar ya fuce,
A 6angarensu Aunty babba kuwa,basu isa Enugu ba sai wuraren ƙarfe sha ɗaya na dare,Sunsha uwar tafiya,ba ƙaramin jiki suka ji ba,Acikin garin suka kama ɗaki a hotel,Tunda suka shiga ɗakin,kowaccensu ta baje saman gadon ɗakin,suka shiga sharar bacci kamar wasu matattu,Ga uwar yunwa na cinsu,sai da sukayi bacci mai isarsu,Kafin suka farka neman abunda zasu sama cikinsu,Oder sukayi aka kawo masu lafiyayyan abinci,kamar wasu kuraye haka suka tasarwa abincin suna Ci,Sai da suka ci suka ƙoshi,tukunna suka koma saman gadon,Suka dasa wani sabon baccin,ba tunanin yin sallah,a ƙagare suke washe gari yayi su wuce cikin dajin,
*Boss Bature*
❤🤍❤
Har Wuraren ƙarfe 12,Abusufyan bai dawo cikin gidan ba,gashi yabarta ita kaɗai,da farko bata damu ba,falo ta dawo ta zauna saman sofa,daya ke akwai nepa,hasken globe ya gauraye ko'ina,hannunta na ɗauke da littafin oummansu tana karantawa,Kalaman soyayya ne acikinshi,a cikin drawer ta samu littafin,Wani page ta buɗo acikin littafin Sunan oummansu ne akai dana Ya sayyadi,Aikuwa rai a6ace ta sanya hannu ta yage takardar tare da yin wurgi da ita,Mayar da hankalinta tayi sosai akan littafin tana karanta love messages ɗin dake aciki,da zarar taga wanda ke ɗauke da sunan ya sayyadi,jikinta har rawa yake yi wurin sanya hannu ta yage shi,
Tana cikin wannan karance karance,kwatsam!Aka ɗauke da wutar nepa,nan take duhu ya gauraye ko'ina,babu haske ko misƙala zarratin,gashi ta baro wayarta saman drawer cikin ɗakin,Sanin kanku ne sehrish muguwar matsoraciya ne,Tuni ido ya raina fata,Hankalinta yayi mugun tashi,jikinta ya shiga yin kerma,kamar gunki haka ta ƙame a zaune ta gaza motsawa,tana cikin wannan yanayin na tashin hankali,Tajiyo takun takalmin mutum,A matukar tsorace ta shiga ambaton sunan Daddynsu da ƙarfi"Daddy!daddy!dan Allah kana ina,nashiga uku,'
Gabanta ne ya fadi lokacin da ta tuna cewa,daddynsu da Motarshi ya fita,da ace shine ya dawo cikin gidan to tabbas zata ji sautin ƙarar shigowar motarshi,
Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,jin motsin mutumin na tunkarota,a razane ta saki littafin dake a hannunta,ta miƙe daga saman sofa ɗin tashiga ja da baya,tana tafiya saɗaf saɗaf,hawaye duk sun wanke mata fuskarta,zuƙunnawa tayi ta soma yin rarrafe a hankali tana ƙoƙarin gano ƙopar ɗakin oummansu,cikin rashin sani takai hannunta saman wani gwangwanin maltina,aikuwa ya bada wani irin sauti rakwakwas,a gigice sehrish ta miƙe,gudu gudu sauri sauri,ita kanta batasan inda zata tunkara ba,Unfortunately tayi tuntu6e da wani abu,gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa,ta saki wata irin razananniyar ƙara,
Sai dai kafin takai ƙasa,Taji an damƙi qugunta,kwakkwaran ruƙo akayi mata,kafin aka janyota da ƙarfi,ta faɗa saman ƙirjin mutumin,koma waye wannan ba ƙaramin mutun bane,ƙarƙarfan gaske,
Tashin hankali domin son sanin wanene wannan mutumin,Mu haɗu gobe inda rai da lafiya,In Allah yasa muna da rabon ganinta kenan
💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐
*_INFECTION BABBAN CIYO NE_*
Ciyon da yake shiga tsakanin ma'aurata ya hana masu zaman lafiya. Da kwanciyar hankali a zamantakewarsu ta aure , ciyo ne da yake kassara martaban mace harma da mazan Kansu , ciyo ne mai hadarin gaske Wanda duk take dashi to ba ita ba jin dadin aure , saboda yana dauke ni'imar mace gaba daya yana hana mace jin sha'awar mijinta yana saka ciyon Mara mai tsanani idan yayi yawa , Wanda zuwa gaba yake hanawa mace daukar ciki. Ko kuma yawan 'barin ciki Sannan duk abunda mace zatayi domin gyaran kanta to bazai mata wani amfani ba saboda wannan ciyon wannan zaisa mace taga tana ta faman shan maganin mata amma baya mata aiki,
*KADAN DAGA ALAMOMINSHI*
Bushewar gaba
K'aikayin gaba
Fitar kuraje agaban mace
Fitar farin ruwa mai kamar madara ko mai kamar majina
Ko fitar ruwa mabanbanta kala
Rashin sha'awa
Rashin jin dadin kwanciyar aure
Yana haifar da budewar gaba,
Ciyon Mara da sauransu ,
wannan yasa mukazo maku da sahihijn
maganin sanyi wato infection yana wanke duk wani dattin Mara yana maganin sanyi sosai tareda saukowa mace niima maganin 3in1 ne na sha da sabulun tsarki da Wanda zaki dafa kina tsarki dashi , akwai kuma maganin sanyi na maza daban Wanda yanada kyau duk wacce ta siyama kanta to ta siyawa mijinta don kar ayi badi babu rai don ko kinji sauki in shi mijin yanada zai iya shafamaki .......*
07069711327 mmn Yusuf mai kayan mata sokoto🥰🥰
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Am really sorry,🙏
Tayi matuƙar tsorata dashi,kasa ɗagowa tayi daga jikinshi,jikinta sae kerma yake yi,lokaci guda daddaɗan ƙamshin turarenshi ya daki hancinta,nan take ta ruɗe tana ƙoƙarin gano a ina tasan ƙamshin nan,duk duniya mutun ɗaya ne ta sani mai irin wannan ƙamshin turaren mai matuƙar ratsa zuciya,Ruɗewa tayi tana so ta canko wanene,kuma tana kokwanton anya hakan zai iya kasancewa gaskiya?zame hannayenta tayi daga saman waist ɗinshi da ta ruƙe,ta matsar dasu har izuwa mid back ɗinshi,Gabanta ne ya faɗi rass jin ta shafo doguwar sumar kanshi,muryarta na kerma ta furta sunanshi"BABBAN YAYA..!"tana ambaton hakan,Wutar ɗakin ta dawo nan take haske ya gauraye ko'ina tamkar da Rana,zuba mashi ido tayi tana kallon kyakkyawar fuskanshi wadda ke sanye cikin face mask black colour,Launin rigar jikinshi ya lumshe idanuwanshi,slowly ya ɗan waresu akan fuskarta,Ae tana ganin blue eyeballs ɗin nan nashi,Ta ƙara tabbatar da hasashenta,abun yayi mugun ɗaure mata kai,kallonta yake yi from head to toe,fuskarta duk tayi zufa saboda tsabar firgicin da ta shiga,ga hawaye jaga jaga a fuskar,duk don saboda an ɗauke da wutar nepa ta ganta acikin duhu,
Sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,hankalinta har ya kwanta da ta tabbatar cewa shine,Tayi tunanin wani mugunne yazo don ya cutar da ita,tayi farin cikin ganinshi sosai kamar tayi ihu,Amma ta wani 6angaren tsoran hukuncin da zai yanke mata take yi,duk a tunaninta yazo ne don ya hukuntata,tunda ya bata Command taƙi bi,
Ganin irin kallon da yake yi mata ne yasa tayi saurin sunnar da kanta ƙasa,tana wasa da yatsun hannunta,
Hanky ya zaro daga cikin trouser pocket ɗinsa,Ya miƙa mata tare da cewa"Take it,"hannu tasa ta kar6a,ta shiga goge fuskarta sosai,
"In kawo maka ruwa kasha"?cikin sanyin murya ta ambaci hakan,
Girgiza mata kai yayi alamar a'a,kafin ya wuce cikin falon,Ya zura hannayenshi biyu acikin aljihun wandonshi,
juyowa tayi tana kallonshi,A dai dai lokacin suka jiyo sallamar Abusufyan"Assalamu Alaikum",
Amsa mashi su kayi da"Wa'alaikum salaam,"
Shigowa cikin falon yayi,hannunshi ruƙe da key ɗin Motarshi,
Koda yayi arba da Sgr,cike da mamaki yace"Rafayet!Ashe dagaske ne,Abban ku ya sanar dani cewa,zai yi wa Omar magana ko shi ko kai wani yabiyo bayanmu don yaso yana nan muzo dashi,Banyi tsammanin cewa kaine zaka zo ba,Yanzu kawai ina karyo kwana da motata naga sojoji zagaye da gidan nayi ta mamaki cikin raina,Gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba," ya karasa maganar a yayin da yake ƙoƙarin rungumarshi,da alama Abusufyan ba ƙaramin daɗi yaji ba,Sai murmushi yake yi,
"Na same ku lafiya,"?
"Lafiya lou Alhmdllh,Naje masallaci ne,na biya naga wani Abokina daga can kuma na wuce wani store zanyi mana siyayyar kayan abinci,Inata fargabar nabar yarinya ita kaɗai acikin gida",
Sgr yace"nayi mamakin ganinta ita kaɗai zaune acikin gidan,time ɗin dana shigo kuma bansan meya faru ba,duhu ko'ina,so sai daga bayane hasken ya dawo,"
Abusufyan yace"Ae ɗaukewa su kayi da wutar ne,yanzu nima ina kan hanyar dawowa naga sun dawo da ita,"
wurga idonshi yayi kan Sehrish dake tsaye hannunta ruƙe da hanky dinsa,ta kammala goge hawayen,
"Daughter,zonan mana,"ya kirata da hannunshi,wurinsu tazo ta tsaya tana facing din Abusufyan,
"Faɗamun meya faru?bayan na tafi"?
murmushi ta ɗan yi,batare da tace komai ba,
Mayar da idanuwanshi yayi kan Sgr yace"Amma dai ba nan zaka kwana ba ko"?
"I will spend the night here,"
Abusufyan yace"ba ka ga yadda gidan yake ba ne?Ni nasan bazaka iya bacci acikinsa ba,Yakamata ka wuce hotel kawai,ina ganin zaifi maka daɗin zama,"
Girgiza mashi kai yayi"No,i wanna stay here," gyaɗa kai abusufyan yayi tare da kallon sehrish yace
"Sehrish ki kaishi bedroom ɗin da kika gyara,ya zauna acan,Amma dai banso ba wlh,Don nasan cewa zaka takura sosai,Ga zafi ga sauro duk da na siyo maganin sauron,Amma bana tunanin zai iya dakatar da saurayen dake acikin gidan nan,"
Amsa mashi tayi da toh,Sannan ta juya tare da kallon Sgr tace"Mu shiga ciki,"
Gaba tayi yabi bayanta,daƙyar yake iya taka kasan palourn,saboda daudar dake a wurin duk da sun gyara shi,
Shiga cikin bedroom ɗin su kayi atare,Wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana ƙarewa ɗakin kallo,
"Kana bukatar wani abu,in kawo maka,"
"No need"ya ambaci hakan a yayin da yake zaro wayarshi daga cikin aljihun wandonshi,
"Sehrish!"Abusufyan ne ya kwala mata kira,da sauri ta juya ta fita daga ɗakin,
Komawa tayi cikin palourn A tsaye ta same shi,Ga kayan da yayi masu siyayya hada gass cylinder saboda yin girki,Sojoji ne suka shigo dasu,A cikin buhu guda biyu,sae cylinder ɗin da suka ajiye nan,
Ƙarasawa tayi wurinshi,"Gani Daddy,"
"Kunyi magana dashi ya fada maki ko yana buƙatar wani abu?"
"a'a bai bukaci komai ba,"
Shiru Abusufyan ya dan yi,ganin damuwa akan fuskarshi yasa tace"Meya faru daddy," hannu yasa ya ɗan shafa sumar kanshi kafin yace"Daughter,bazai iya kwana acikin gidan nan ba,Ni nasan waye rafayet,Wlh nayi mamakin ganinshi banyi tsammanin cewa shi zaizo ba,Kalli fa gidan nan ki gani,babu wani shiri da mukayi,yanzu da zarar an ɗauke da wutar nepa,Shikenan zafi zai rufe mu,kuma ko kaɗan baison zafi,Gashi da ƙyankyami toilet idan bana bedroom ɗinshi ba,baya shiga na kowa,Kuma dole ya buƙaci yin wanka,Ni bansan ya zamu ƙare dashi ba,"
Murmushi Sehrish tayi,ita kanta ta jinjina ma ƙarfin hali irin na Sgr,yadda yake da ƙyanƙyamin nan,Amma a haka yace zai kwana acikin gidan,Koya zasu ƙare,?
"Daddy,kada ka damu,tunda yaji ya gani,zai kwana anan ɗin ka ƙyaleshi kawai,"
Gyaɗa kai Abusufyan yayi tare da cewa"Shikenan kawai,Yanzu dai bari na shiga da kayan abincin nan kitchen,"
Yayi maganar tare da sa hannu ya dauki buhu ɗaya,hannu tasa itama ta kama ɗayan buhun,taja shi izuwa cikin kitchen,bayan sun kammala kwashe kayan sunkai kitchen,
Ta dube shi tare da cewa"Zan iya dafa mana ko taliya ce?
Abusufyan yace"Kina jin yunwa ne"?
"A'a,bana ji,saboda kai dama zan dafa,naga bamu ci Dinner ba,
"Ki barshi kawai,akwai kayan tea dana siyo da bread,idan kina jin yunwa ki haɗa ki sha,Yanzu dae bacci nake ji,"
Yayi maganar yana hamma,
"A ina zamu kwana"tayi tambayar tana kallonshi,
"Ki wuce inda mijinki yake mana,Ni zan kwana a palour ne,Ki dauko mun bargon da zan ɗan shimfiɗa in akwai"
"Toh" ta amsa mashi tare da
Kama hanya ta fuce daga cikin kitchen ɗin,Shima fitowa falon yayi ya tsaya a tsaye yana jiranta,
Lokacin da ta shiga bedroom ɗin,A kwance ta samu Sgr yana bacci ya ƙure fankar ɗakin har ƙarshe,iska ta ko'ina,hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wurin wardrobe ta wuce ta sanya hannu ta buɗeta,daga gida na kasa blanket din suke tare da bedsheet,hada mosquito net,
Bargo ta dauko mashi,Sannan ta koma falon,har lokacin Abusufyan na atsaye,yana jiranta,
Ƙoƙarin shimfiɗa mashi tayi,da sauri yasa hannu ya kar6i bargon tare da cewa"Yawwa My Own Daughter,nagode sosai,"
"Sae Allah yakaimu Daddy,"fuskarta asake tayi maganar,
"Allah ya kaimu lafiya,take care of my son,don't allow even one mosquito to bite his skin,If not ranki zai 6aci,"cike da zolaya yayi maganar,
Fashewa tayi da dariya,tare da juyawa tana faɗin"don't worry daddy,In sha Allah i will look after him,very well,"
Gyara kwanciyarshi yayi saman sofa ɗin,cikin lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dashi,
Komawa cikin bedroom ɗin tayi,bedsheet ta dauko acikin wadrobe ta shimfiɗa a kasa,sannan ta matsa wurin gadon,ta ɗauko pillow guda ɗaya ta ajiye shi saman zanin gadon,
Wurin switch taje,ta kashe light ɗin ɗakin,Nan take duhu ya gauraye ɗakin amma ba sosai ba,akwai hasken ƙwan dake a falo guda daya da aka bari akunne,ya ɗan haska ɗakin nasu,
Moving tayi izuwa wurin gadon inda Sgr ke kwance yana bacci,addu'o'i ta shiga karantowa tana ɗan tattofa mashi,bayan ta kammala ta koma saman shimfiɗar da tayi,ta gyara kwanciyarta,sai da itama ta karanta addu'o'in tabi ta shafe jikinta kafin ta rufe idanuwanta,bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,
Around 1:30 na dare,Ƴan nepa suka yi tsiyar tasu da suka saba,Tashin hankali,Ƴan sakanni da ɗauke wutar fanka ta tsaya cak,Wani irin zafi ya fara ziyarta ɗakin,Sai ga mutanen da gudun gaske sun fara kwararowa cikin ɗakin,Buuuuuuuuuu da wani irin kuka mai sautin gaske,tun yana juyi saman gadon yana kai hannu yana buge sauron dake ƙokarin attacking ɗinshi,har ya fara ƙokarin farkawa,Wata irin zuface ta soma tsastsafo mashi ajikinshi,Sharkaf ya jiƙe,tuni numfashinshi ya soma kokawar fitowa daga hancinshi,kamar an toshe shi,A firgice Sgr ya farka yana faman zazzare blue eyes ɗinshi,Hankalinshi yayi mugun tashi,arayuwarshi ya tsani sauro ko miskala zarratin baisan halittar nan,bai taso a inda ke akwai taba,Amma yasanta sarai a matsayinshi na Dr yasan irin cututtukan da take haifarwa,Gashi ya tsani duk wani abu da zai naƙasa lafiyar jikinshi,tuni jikinshi ya soma kerma,hannu yasa ya ɗebe rigarshi gaba daya,ya shiga kokawar korarsu daga kusa dashi bayan ya kunna fitilar wayarshi dakin yayi haske,ji kake fass fass!kaff kaff!!haka ya dinga bubbugesu,duk yabi ya ruɗe,
Cikin bacci Sehrish ta dinga jin muryarshi yana faɗa da sauraye yana fadin"Don't come close to me!Am gonna shoot you"tashin hankali Sgr fa ya zauce da alama,duk sun rikitashi sun mayar dashi ƙaramin mahaukaci,Idan ya sanya riga bala'e biyu,ga zafi ga sauro,idan ya cire rigar kuma Sauraye zasu sha jini,bai da choice,
A firgice ta farka,hankalinta a matukar tashe ta mike daga kwancen da take saman bedsheet ɗin,Wurin shi ta ƙarasa,yanayin da ta ganshi gaba ɗaya ya rikice ba ƙaramin tausayi ya bata ba,gaba daya yabi ya susuce ya hargitsa sumar kanshi,
"Ya Rafayet,"ta ambaci sunan shi da wata irin kasalalliyar murya ta mai bacci,ƙoƙarin hawa saman gadon tayi don ta taimaka mashi ta kore mashi su,kafin su san abunyi,ae tana hawa saman gadon,ya ƙanƙameta ya rungumeta sosai,A faɗace yake ce mata ta kori saurayen su fita su bar ɗakin,ko ya harbesu da bindiga,tuni taji hawaye sun cicciko mata acikin idanuwanta,tsananin tausayinshi ne ya kamata,dama sai da Uncle yace bazai iya kwana a cikin gidan ba,Amma yace zai iya,wani iko na Allah,babu halittar da Sgr ke jin shakkarta irin sauro,Gashi Yau Allah ya haɗasu,ƙananun ƙwari sun firgita babban kwaro,Shaggu sun ga Farar fata,burinsu kawai su tsotsi jininshi,Dama abu tubarkalla masha Allah,
gaba daya hannayenta na asaman bayanshi,ya cusa kanshi a kirjinta,numfashin shi da wani irin huci yake fita,
Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Ya rafayet,dan Allah ka natsu,zanje wurin daddy na kar6o mana maganin sauron,"tayi maganar tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi,ƙin barinta yayi,yaƙi yarda ta motsa daga jikinshi,gani yake kamar in tabar wurin Saurayen zasu shanye mashi jinin jikinshi ne,
Ganin yaƙi sakinta yasa takai hannu ta ɗauki rigarshi da yayi wurgi da ita gefe saman bedmattress ɗin,Ruƙo rigar tayi a hannunta,ta shiga kore mashi saurayen dake akewaye dasu,
Duk wannan budurin da akeyi,Abusufyan na kwance saman doguwar kujerar,Shi kanshi zafi ya ishe shi ga saurayen a kewaye dashi,Amma hakan baisa ya farka ba,sae faman juyi yake yi,
(Allah sarki,haka talaka ke fama,da zarar an ɗauke da wutar nepa lokacin zafi,Ya rasa inda zaisa kanshi,ga sauro ga zafi,yayin da masu kuɗi ke can suna shan sanyin A.c,a lokacin zafi,idan kuma na sanyi ne su kunna room heater,Talaka kuma Ya hura garwashin wuta😥)
Jikinshi sae kerma yake yi,Duk da ya ɗan ji sauƙin Zafin saboda fiffitar da take yi mashi tana kore mashi saurayen,ko gajiya bata yi baiwar Allah,Haka ta hana idonta bacci,ta zauna tana kula dashi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi,har lokacin yana manne da ita,
A hankali bacci yayi awon gaba dashi,kamar wani jinjiri,gyangyaɗi ta fara yi,tana fiffitar bacci na fisgarta,idanuwan nan sunyi jawur dasu,taƙi bari bacci ya ɗauketa,saboda gudun halin da Sgr zai shiga,idan ta daina yi mashi fifitar,
Tafin hannunta ta sanya asaman fine face dinsa,ta shafa gefen fuskarshi har izuwa saman pink lips ɗinshi,kafin ta mayar da hannun saman dogon wuyanshi,fatar wurin tayi haske sosai mai matukar jan hankali,la66anta takai asaman cheek ɗinsa ta manna mashi kiss,ɗagowa tayi tare da aza tsinin hancinta cikin sumar kanshi,daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga wurin ta dinga shaƙa,tana faman lumshe idanuwanta,da hannu ɗaya take yi mashi fiffitar,
Tana cikin wannan yanayin,ta galabaita sosai saboda baccin da take ji,Ƴan nepa suka dawo da wutar,a hankali fankar ta soma jujjuyawa,nan take iska ta karaɗe ko'ina na bedroom ɗin,wani irin farin ciki ne ya ratsa zuciyarta,
"Allah na gode maka,da suka dawo da wutar nan,nayi farin ciki sosai,"
Lokaci guda Mosquitoes ɗin nan kowa ya kama gabanshi,saboda wutar mai ƙarfi ce,iska duk ta kaɗa shaggun,
A hankali ta lalla6a ta janye Sgr daga jikinta,ya koma saman mattress ɗin,ta dauki wayanshi ta kashe fitilar ta daura ta saman bedside drawer,gefenshi ta kwanta,tare da jan bargo ta lullu6e jikinta,banda nashi saboda ta lura dashi baisan Zafi ko misƙala zarratin,
*Boss Bature*
Wuraren Sallar asuba,Abusufyan ya farka,Saukkowa yayi daga saman Sofa ɗin,yana faman murza wuyanshi,Wurin yayi mashi zafi saboda kujerar tayi mashi karanta,ya takure kansa sosai,Ƙopar ɗakinsu yaje tare da sanya hannu yana ɗan kwankwasa ƙopar,
Sehrish ce ta farka,saukowa tayi daga saman gadon,sai da ta fara kunna hasken ɗakin,sannan taje ta buɗe ɗakin,
"Daddy,"ta ambaci sunanshi,
"Na'am,Daughter,"
"Wlh jiya munji jiki daddy,dama haka Yaya Rafayet ke da jin Zafi? Ga sauraye suka takura masa,jiya daga ni harshi bamu samu isasshen bacci ba,"muryarta tamkar zata yi kuka tayi maganar,
"Ae dama saida nace mashi,Yaje hotel amma yaƙiya,banji daɗi ba gaskiya,duk ban shirya ma zama gidan ba,dana sani tun kafin muzo,nasa an gyara shi,An sanya generator da A.C an kuma yi mashi feshin maganin sauro,Amma ban yi tunanin hakan ba,Wllh koni jiya naji jiki,"
Ya ƙarasa maganar tare da cewa"Yanzu ya yake?Yana lafiya kuwa,"?yayi tambayar yana jiran amsarta,
"Ya samu bacci,da suka dawo da wutar,bansani ba ko yana lafiya ko kuwa,Still dai bacci yake yi bai farka ba,"
Jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"je ki taso munshi,Yazo mu tafi masallaci,Lokacin salla yayi,"
"Toh daddy"tayi maganar tare da juyawa ta shige cikin ɗakin,
Yadda tabarshi haka ta same shi,kwance yana bacci,
Zama tayi daga gefen gadon,sannan ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet"!shiru bai motsa ba,sake kiran nashi tayi"Babban yaya ka tashi,time ɗin sallah yayi,"_
Ganin yaƙi motsawa yasa takai hannunta saman damtsen hannunshi,ta ɗan bubbugashi,dogon numfashi yaja a hankali ya soma ƙoƙarin buɗe idanuwanshi,
Biji biji ya fara ganinta,kafin idanuwan nashi suka washe,
"Ankira sallah,Daddy yana jiranka a palour,"
daƙyar ya iya furta mata Okey,miƙewa yayi daga zaune,yakai hannu ya ɗauki shirt ɗinshi,Ya zurata ajikinshi,Hada ido su kayi da ita,da sauri ta kawar da idonta gefe guda,miƙewa tayi daga tsaye,ta bashi wuri don ya wuce,
Saukowa yayi daga saman gadon,Ya kama hanyar fita daga ɗakin,
"Adawo lafiya,"
"Okey,"yasa kai ya fuce,
Bayan fitarshi,toilet ta shiga,ta ɗauro alwala,bayan ta fito ta ɗauko darduma ta shimfiɗa,a natse ta kabbara Sallah,tana gama yin sallar ta ɗebe hijabin ta ninke dardumar ta turasu cikin wadrobe,
Wani irin bacci take ji acikin idanuwanta,saboda jiya bata samu isasshen bacci ba,Cire doguwar rigar jikinta tayi tare da sagala ta saman Murfin wardrobe ɗin,
Toilet ta wuce,Saboda jikinta duk babu daɗi,After some minutes ta fito jikinta sanye da Brazier,tare da Short,farare,ba ƙaramin kyau su kayi mata ba,dama dasu ta shiga wankan,
Tunda ta fito kuma,baccin ya ya ci gaba da addabarta don ba karamin dadin jikinta taji ba,bata samu ta sanya kaya ajikinta ba,Saman gadon ta haye taja bargo cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita,bata ƙara sanin inda hayyacinta yake ba,
*Marshal Omar*
Yayi nisa a cikin baccin shi,yajiyo muryar Hosana tana raira mashi waƙa,
_Wataran wata rana_
_za'a kaika gidana_
_matsayin mijina_
_kaine madara na_
_na matsu!na matsu na matsu inga wannan rana_
Cike da jan faɗa take yin wakar hada matsawa saitin kunnanshi,Rai a matuƙar 6ace ya farka,tare da wurga mata uwar harara,tana zaune saman gadon tayi zaman cin tuwo,
A faɗace yace"Hosana!bana hanaki shigomin bedroom ɗina ba?Meyasa baki jin maganata ne"
Hura mashi hanci tayi tare da murguɗa baki tace"Haramun ne idan nashigo ɗakin ɗan uwana,?to idan ma haramun ne,Sai ka aure ni kowa ma ya huta,"
Hannu yasa tare da dafe kanshi,yana faɗin"Allahumma ajirni fi masibati,wa'aklif ni khairan minha,"
A ƙule tace"Ya Omar,Ni ce masifar"?
Banza yayi da ita bai tanka mata ba,
Jin yayi shiru yana kallonta,yasa tace"haushina kake ji ko?to ka kashe ni mana kowa ya huta,"
Yunƙurawa yayi tare da miƙewa daga zaune,yace"Meyasa kike mun haka ne?kin takurawa rayuwata Hosana,A haka kikeso na"?
Turo baki tayi tana ɗan satar kallonshi,
"Baki son farin cikina,kullum burinki ki addabi rayuwata kib hanani sakat,Zunubin me na akaita maki ne,"
Ashagwa6e tace"Bakomai,"
"Kinfi so ki ga hawaye na ko,"
Girgiza mashi kai tayi alamar,A'a,
Hannu yasa ya rufe fuskarshi yana raira mata kukan ƙarya,
Nan fa hankalinta ya tashi,tabi ta ruɗe,
"Ya Omar bazan ƙara zuwa ba,dan Allah kadaina kukan,yanzu zan tafi na barka,"jiki na rawa ta sauka daga saman gadon tana ja da baya baya tana faɗin"ka gani ko?tafiya zanyi,bazan ƙara dawowa ba,dan Allah ka daina kukan toh,"
Ƙasa ƙasa ya dinga dariya batare da taji shi ba,har sai da ta fuce daga ɗakin sannan ya zame hannunshi aranshi yace"fitinanna,Allah yasa Daddy ya dawo cikin week ɗinnan zansa a ɗaura mana aure,At first night,zan koya maki hankali,duk wani hauka da kike ji asaman kanki saina sauke maki shi,"
Yana maganar yana dariya,a yayin da yake saukowa daga saman gadon,jallabiya ce ajikinshi,toilet ya wuce,
Wuraren karfe 8,Sehrish ta farka da wata irin matsananciyar Yunwa,a gaggauce ta miƙe,ta ɗauko jallabiya ta zura a jikinta,kitchen ta wuce,batare da 6ata lokaci ba,ta ɗaura girki,bazata iya jure dafa abu mai wuyar dafuwa ba,Shiyasa ta ɗaura Indomie shaf shaf ta kammala dafuwarta,A cikin plate ta kwasota ta fito daga cikin kitchen ɗin,ta zauna a palour tana ci,sai lokacin ta shiga tunanin ko'ina su Uncle suka tafi?daga fita sallar Asuba har yanzu basu dawo gidan ba,yanke shawarar kiransu tayi idan ta kammala cin taliyar,asaman table tabar plate din da sauran taliyar,ta koma kitchen ta haɗo kakkauran Tea wanda yaji madara da bournvita,dawowa tayi falon ta zauna tana kur6arshi a hankali,
Tana cikin shan tea ɗin nan,taji dirar motarsu acikin gidan,Uncle Abusufyan ne ya fara shigowa cikin gidan,Miƙewa tayi da sauri tana fadin"Daddy,sannu da dawowa,"
A gaggauce ya amsa mata"Yawwa Daughter,ɗaukko mayafinki mu tafi,dattijon nan ya kira ni a waya,badajimawa ba,"
Jin haka yasa ta ajiye cup din hannunta asaman table ɗin gabanta,Jiki na rawa ta wuce ɗakin,jimm kaɗan ta dawo sanye da mayafi tayi rolling ɗinshi,hannunta ruƙe da wayarta,
Shigowa cikin palourn tayi batare da 6ata lokaci ba,Abusufyan ya ruƙo hannunta suka fito waje wurin motarshi,Security ta gani suna tsaron gidan,tana ganinsu ta gane cewa mutanen babban yaya ne,
buɗe motar tayi ta shiga,Abusufyan ya shiga ya zauna a mazaunin driver,tashin motar yayi tare da yin reverse ya karya kwana,da gudun gaske ya fuce daga cikin gidan,Kai tsaye suka haura saman titi,hannunshi har kerma yake yi saboda saurin da yake yi,burinshi kawai su ƙarasa cikin unguwar,
"Daddy,ina yaya Rafayet ɗin?naga banganshi ba,"
"Nabarshi a hotel,tun bayan da muka kammala sallar Asuba,Ni kuma na wuce gidan wani Old friend ɗina dake anan,Na jima acan,ina kan hanyar dawowa Dattijon ya kira wayata,Yake sanar dani cewa Malam Nura ya dawo"ya ƙarasa maganar adai dai lokacin da yake ƙoƙarin juya sitiyarin motar,Cikin unguwar suka shiga,a bakin bishiyar bedi yayi parking ɗin Motar cikin layin,tun kafin su fito daga cikin Motar suka hango ƙopar gidan a buɗe,bayan sun fito daga cikin Motar,Abusufyan ya daga hannunshi sama tare da cewa"Ya Allah kasa muji alkhairi!"
Sehrish ta amsa mashi"Ameeen Daddy,"
A ƙopar gidan suka tsaya,Abusufyan ya kwaɗa sallama,cikin sa'a suka ji an amsa masu sallamar tasu,Jimm kaɗan sai ga wani matashin saurayi dogo siriri ya fito daga cikin gidan,jikinshi na sanye da yadi,
Miƙa ma Abusufyan hannu yayi suka gaisa,kafin yace"baƙi mukayi ne,"Abusufyan yace"Eh,baƙine,muna neman Malam nura ne,Allah yasa yana nan,"
Tunda saurayin ya fito idonshi na akan sehrish,kallon sani yake yi ma fuskarta,ita kanta kallon nashi takeyi,kamar taso ta gane shi,da alama tasan shi tun yana da ƙuruciyarshi,Ranta ne ya bata cewar kodai Sadeeq ne ɗansu ya girma haka"!?
"Da ace kun ƙara minti Biyar baku zo ba,da kun rasa shi,don kuwa yanzu yake shirin komawa Islamiyya,"
Wani irin farin cikine ya lullu6e Abusufyan"taimaka kayi mana sallama dashi,".
"Toh,"ya amsa tare da juyawa ya shige cikin gidan,after some minutes ya dawo hannunshi ɗauke da tabarma,A cikin zauren gidan ya shimfiɗa masu ita,
"Ku shigo daga ciki ku zauna,yanzun nan zai fito,"
"Yawwa mun gode ƙwarai,"Abusufyan ne yayi maganar tare da ruƙo hannun Sehrish suka shiga zauren,A saman tabarmar suka zauna,Suna jiran tsammanin ganinshi,
Wayar Abusufyan dake acikin aljihunshi ce ta soma ringing,da sauri ya zaro wayar,yana duba mai kiran nashi Sunan My first in~law ne,Amsa kiran yayi tare da kara wayar a kunanshi,
"Uncle,A ina zan same ku"?Rafayet ne yayi maganar,
Abusufyan yace"muna a hotoro,Amma kaɗan jira kaɗan zan tura maka da address ɗin gidan,Sai kazo,"
Sgr yace"okey,I will be waiting,"
Rejecting call ɗin yayi,yana ƙoƙarin mayar da wayar cikin aljihunshi,Wani babban mutun ya shigo cikin zauren,bakinshi dauke da sallama"Assalamu Alaikum,"atare suka amsa mashi sallamar,yayin da suka bi shi da kallo,
Daga ganin mutumin ya kwana biyu a duniya,ya manyanta sosai ya fara tsufa,Jikinshi na sanye da shiga ta musulunci,ta waɗanda suka amsa sunansu malamai,hannunshi na ruƙe da cazbaha,kanshi kuwa rawanine,A mutuncen shi yazo,
Kamar yadda suke kallonshi shima haka yake kallonsu,yanayin kallon dayake yi masu kamar kallon sani ne,wuri ya samu agefen tabarmar ya zauna suna fuskantar juna,Shi dasu,
Da sauri Abusufyan ya shiga gaisar dashi"ina kwana baba,mun same ku lafiya,"
Fuskarshi asake ya amsashi lafiya lou,Alhamdulillah"
Gaba daya hankalinshi na akan fuskar Sehrish,kallon ƙurulla ya shiga yi mata,nasan gano a ina yasan fuskar yarinyar,Sunnar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta,
ɗauke idanuwanshi yayi daga kan sehrish ya mayar dasu kan Abusufyan yace"Ince dai lafiya ko?naji kunyi shiru baku gabatarmun da kanku ba,Gashi ni bansan ku ba,"
Murmushi Abusufyan ya ɗan yi tare da gyara zamanshi,Atsanake ya soma kora mashi jawabi,
"Ni sunana Abusufyan,Wannan kuma ƴa tace,Sunanta Sehrish,'
Gabanshi ne ya faɗi rass,aɗan tuɗe ya maimaita sunan"Sehrish"kamar irin ya ta6a jin sunan,
Cigaba da magana Abusufyan yayi"nasan baka gane ta ba,saboda sanin da kayi mata tun na ƙuruciya ne,Amma nasan ba zaka iya mantawa ba,Da ZAINABU ABU BUZUWA MATAR MAKWABCINKA YA SAYYADI,"
Saboda tsabar kiɗima Malam Nura ya zabura tare da miƙewa tsaye yana kallonsu hankalinshi aɗan tashe yace"dan Allah kuyi mun bayanin su wanene ku?menene alaƙarku da zainabu abu da kuma sayyadi"?
Miƙewa Abusufyan yayi yana ƙoƙarin kwantar mashi da hankali yace"pls baba,dan Allah ka koma ka zauna muyi magana atsanake,"
Rai a6ace malam Nura yace"Idan maganar wannan fasiƙin mutumince ta kawoku to ku tattara kubarmin gidana!Banason ganinku,banason ganin duk wani abu daya shafe shi,ku fuce kawai tun kafin ranku ya 6aci a wurin nan "yana magana jikinshi na kerma saboda tsabar 6acin rai,
Ganin yana ƙokarin korarsu yasa sehrish miƙewa tsaye cikin sanyin murya tace"Baban sadeeq,Ka manta da ƴan ukun zainabu abu da ta haifa"?
Mayar da hankalinshi yayi sosai akanta yana kallonta,
"Ni ɗaya ce daga cikinsu,nasan baka manta damu ba,Nice Sehrish ƴar uwarsu Jahad da Hosana"
Cike da mamaki Malam nura ke kallonta,hannunshi na kerma ya nunata da ɗan yatsanshi daƙyar ya iya furta cewa"kek..ke..ƴar wurin zainabu abuce?
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,tace"Ni ce SEHRISH Baban sadeeq,su jahad ma suna nan araye,"
Wasu irin zafafan hawaye ne suka soma sauka akan fuskar malam nura,ruƙo hannunta yayi yana kallonta,la66ansa sae kerma sukeyi,yayi matuƙar mamaki ganin yarinyar,bai ta6a tsammanin cewa yaran zasu rayu ba,abun yayi matukar daure mashi kai,
Cikin shessheƙar kuka yace"Allahu akhbar!Wai dagaske ƴa'ƴan abu suna araye a doron duniyar nan?Dagaske ne abunda idona suke gane mun kuma suke jiyomun