Fitar Tsiro Hausa Novel

 FITAR TSIRO

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: FITAR TSIRO


  Rufaida UmarPaid book: 500

Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB


Phone number: 09034973645


Free page 2


Cikin sauri ta shirya cikin kayan makarantarta na sakandire mallakin gwamnati dake a unguwarsu, ta kusan makara wannan dalilin yasa ko tsayawa shan ruwan shayi da ƙosan da Umman ta ajiyemata ba ta yi ba. A gaggauce ta kammala ta fice bayan ta shaidawa Umman ta ɗauki muƙullin gidan don ba za ta bi ta kasuwa ba yau, Umman na kwalamata kira akan ta zo ko a leda ne ta ƙullamata abin karin amma ko waigowa ba ta yi ba face sakin guntun tsaki. Babban burinta ta ganta a ajinsu tare da Hindatu kawai don ta labarta mata yanda suka yi da Mijin Umman. Ba ta ko damu da gwajin ajin  da zasu yi ba a ranar don ko nutsuwar karatu ba ta samu damar yi ba, koda ta isa abin takaicin ba ta ƙaraso ba. Hakanan ta shige ciki ta fiddo ƙaramar dardumarta a jaka ta shimfida ta zauna don kusan rabin ajin a ƙasa suke. Har Malaminsu na koyon turanci ya shigo, babu alamar Hindatu, sai can ta shigo kamar an wurgo ta. Kayan jikinta duk sun yi ƙura saboda aikin shara da aka sanya ta matsayin hukuncin makara. Hasken fatarta kusan ya zarce na Haulatu don ita tana haɗawa da mayuka hakan yasa har wani ja take yi, sai dai daga ta buɗe ƙafafunta za ka fahimci hasken ba na halittar ba ce, ƙafar baƙiƙirin. Ba ta da tsayi kamar yanda ba ta kasance cikin jerin gajeru ba, tana da jiki da girman halittar mama wanda hakan ya ƙara mata girma, ta zama kamar wata uwar mata a cikin abokan karatun nata. Wannan ya sanya ƴan ajin suka fi yi mata laƙabi da BigMama. Ba ta daukar raini, ba ta da munafunci balle gulma, faɗa ko ba da ita ake yi ba, za ta shigarwa mai gaskiya ta buga rashin mutunci son ranta. An sha ba ta hukuncin zaman gida (suspension), hakanan an sha kiran mahaifiyarta. Da yawa na mata kallon ƴar mace don a hannun mahaifiyarta ta rayu ba don wai Babanta ba ya raye ko wani abun ba, ko kusa, ana cewa ma ko Uban bai ji dadin zama da mahaifiyarta ba, dakyar da karfin addu'a ya samu ya fitar da ita daga rayuwarsa. Ko gidan Uban ba ta zuwa balle ta saba da wani a can, ita kuwa Uwa ƴar kasuwa ce, ba ta can ba ta nan, sai ta fice daga garin har ma wasu lokutan ta tsallaka boda zuwa Nijar da zummar kasuwanci ta bar Hindatun a gida daga ita sai sauran masu zaman haya sai abin da ta ga dama take yi da taƙamar gidan mallakin uwarta ce, a haka dai uwar ke samarmusu abin rufawa kai asiri su ci su sha, su sanya sutura mai kyau daidai gwargwado don kuwa suturunta ya take na Haulatu. Burin duniya kuwa ta ɗora akan Hindatu, tana mata kallon wata kadara da nan gaba za ta ci riba a kanta. Ta sanya a ranta da zarar Hindatun ta kammala sakandire za ta yi cuku-cukun kai ta jami'a don ta ƙara wayewa da gogewa. Wannan yasa tarbiyyar Hindatun ya zama sai a hankali, babu wani ko wata da ya isa ya juya tanƙwarata hakan yasa ta ke cin karenta ba babbaka.


"Ke! Tsayuwar me kike?"


Malamin ya yi mata magana a tsawance, ta ɗan bishi da kallo tana ƙunƙuni, a duniya idan da wanda ta tsana cikinsu har da Malam Bukari, yana cikin wadanda ba su fiye ba ta ƙofar kawomusu wargi ba. Ta kauda kai ta yi ciki, sai da ta gama kallon mazauna saman bencinan da ba su fi biyar ba a ajin, ta watsa musu harara kafin ta yi ƙwafa ta zauna gefen Haulatu saman darduma. Malam Bukari na juya baya ciki bada umarnin a yi sauri a bada amsoshin tambayoyin da ya rubuta a allo a ƴar takarda, ta kalli Haulatu cike da ɓacin rai da murya ƙasa-ƙasa ta ce.


"Wai ke meyasa idan kin zo ba kya tashi shegu daga benci ki kama mana wuri? Kinsan dai na tsani zama a ƙasa ko?"


Haulatu ta wurga mata harara. 


"Toh sannu Uwani, tunda kin zo ai sai ki tashe su. Kinsan tun lokacin da nake jiranki ne?"


Hindatu jin haka ta ɗan fiddo idanu kaɗan.


"Haba? Ki ce da labari."


"Akwai labari amma fa ba wani mai dadi ba. Bari dai wannan ya fice naga idanunsa a kan mu."


Wannan bai sa Hindatu damuwa ba, kallonsa ta yi kadan sannan ta ja guntun tsaki bayan ta kauda kai tana mai karɓar takardar da Haulatu ta fillo mata a cikin littafi. 


"Ke dallah rabu da shi, ni faɗamin kawai, duk na matsu na ji me Mijin Umma ya aikata don nasan dai tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi."


Ita dai Haulatu sai ta yi dariya kawai ganin idanun Malamin dai na kansu, a dole Hindatu ta bar zancen sai bayan ya fita ne ta tashi wasu akan tebur suka koma, ganin haka Haulatu ta basu aron dardumarta su zauna a ƙasa. Ba yadda suka iya face su karɓa sanin da suka yi idan ma sun ƙi wannan zaluncin da Hindatun da ta yi musu babu wanda zai iya taka mata burki. Koda kuwa an yi magana, toh fa abin da zai biyo baya bai wuce ta tare su a hanya ta ci zalinsu son rai ba. 


"Ina jinki." Cewar Hindatu. 


Hakan ya ba Haulatu damar fayyace mata batun Ciyaman Nazifi. Wani uban ashariya da Hindatu ta yi murya a ɗage, sai da ƴan ajin duka suka dube su. Ta banka musu harara.


"Uban me ku ke kallo?" Sai kuwa suka kauda kai, wasu kuwa suka ja tsaki. 


"Amma mijin Umman nan ya cika azzalumin ƙarshe, wallahi kar ki sake ya tauyemaki haƙƙinnan. Ke me kike jira da ba za ki bi shawarata ku bar masa gidan ba?"


Cikin rashin kulawa da kiran Baban da azzalumi da aka yi, Haulatu ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki.


"Wannan matar ce za ta yarda mu bar gidan? Ai ko asiri ya yi mata sai haka. Amma wallahi kin ji dai na rantse, ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zan bari ya cimma wannan halakakken burinnasa a kaina ba. Zan nuna masa nima na iya rashin kirkin."


"Ato, idan ba haka ba ko mu zo mu sha biki."


Faɗin Hindatu cike da tsokana tana dariyar shaƙiyanci, duka ta kai mata a baya, aikuwa ta gantsare. Haka suka cinye lokacin babu wani Malamin da ya shigo ajin da har aka fita hutun rabin lokaci. Dama sun saba, malamai ba su wadaci makarantar ba wannan ta sa ɗalibai da yawa suna zuwa ne kawai ba don suna samun wadataccen ilimi ko fahimtar abinda aka koyar ba yanda ya kamata. Zasu iya zuwa su wuni amma bai fi su sami darussa uku kacal ba. Wannan na ɗaya daga cikin illar da dalibai ke fuskanta a ire-iren makarantun na gwamnati. Hakan kan jawo nakasu da koma baya a harkar iliminsu. Sai ka ga ƴar sakandire babu turanci a bakin, hakanan shi kansa rubutun ba kowanne ya iya yanda ya kamata ba. Sassauƙar kalma sai ta gagari ɗalibi rubutawa. 


Haka suka cinye ranar a makaranta da darussan da basu wuce uku ba aka tashe su. A hanya su na tafe su na hira inda Hindatu ke ƙara rura wutar tsanar haɗin auren a zuciyar ƙawarta. Aikuwa haƙanta ya cimma ruwa don Haulatu sai da ta ji ƙarfin gwuiwa fiye da na baya akan shirin yin gudun fanfalaki don tseratar da kai daga wannan mugun nufi na Mijin Umman. 


Har suka zo hanyar da ta raba su hirar da suke yi kenan, ƙarshe dole suka bar sauran da zummar gobe Juma'a zasu hadu a gidan su Hindatun. 


Kai tsaye Haulatu gida ta nufa, tun daga nesa ta hango su zaune saman benci ƙasan bishiyar darbejiya dake ƙofar gidan nasu. Wani guntun tsaki ta ja, majalisarnan ta su Audu Maada ya tsaya mata a ƙahon zuci, babu wani a unguwar da bai san da zamansu ba. Duk wani hira na dabanci da ma bushe-bushen hayaƙi ya tattara ne a wurinsu. Rigima ba irin wacce ba'a yi ba a unguwar akan majalisar nan amma hakan bai sa ta rushe ba sakamakon ɗaurin gindin da suka samu daga shi Uban gayyar, wato Maigidan, inda ya ce ai ƙofar gidansa ce ba ta wani ba kuma babu wanda ya isa ya hana su zama tunda ba shirginsu suke shiga ba. Magana har wurin ƴan sanda sai dai kasancewar shi ɗin mutum ne mai idanu cikin gwamnati yasa babu inda ƙarar ta je aka yi watsi da ita. Wannan ce ta sa kowa ya zuba musu idanu kawai, iyaye na takatsantsan wurin ja wa yaransu kunne akan shiga sabgar su Audu Maada balle kuma su kai ga shiga gidan. 


Ta ƙara jan guntun tsaki gami da ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa. Haka har ta ƙaraso ƙofar gidan, za ta gifta su ta ji sun soma maganar tasu ta rainin wayo inda ta tsinkayi muryar Ɗan Aljan ya yi wani busa da baki sannan ya ce.


"Kai! Kai!! Ni fa wallahi Oga Maada ba don da manya a gabanmu ba, babu abin da zai hana ni farautar wannan babbar tsokar. Billahillazee tana..."


"Kai dallah ware can! Kai daɗina da kai ka cika zalama. Ina kai ina shiga gonar Ciyaman? Ai babu mai ninkaya a wannan kogin idan ba shi ba!"


Suka kwashe da dariyar zancen Duuna, Haulatu ta dube su ta watsamusu harara kamar idanunta za su faɗo sannan ta ƙarasa tura ƙofar bayan ta fidda kwaɗon ta shige, tana jinsu suka ƙara sakin wata dariyar ba ta ko saurare su ba don ya ci ace ta saba da haukansu da ba shi da magani. Maida ƙofar gidan ta yi ta rufe ruf sanin da ta yi ba su da kai, don su ce zasu shigo kai tsaye ba komai ne a wurinsu ba. Wanka ta soma yi ta sanya riga marar nauyi gami da ɗaura zani,  ba ta tare da yunwa saboda Hindatu ta siyamusu wainar fulawa sun ci sun yi nak a makaranta, madadin ta yi sallah kawai sai ta shimfiɗe a tsakar gidan inda iska mai sanyi da daɗi ke bugowa, aikuwa nan da nan bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Ba ita ta motsa na sai da ta ji kamar ana faman dukan ƙyauran gidan, a dole ta tashi tana murza idanu gami da ƙarewa garin kallo, ga dukkan alamu dai yamma ta yi ganin yanda rana ta yi sanyi sosai. 


"Ina zuwa!" Ta furta cikin muryar bacci, tana jin sadda Garba ɗaya daga cikin almajiran Umma masu yi mata dakon kaya na fadin. "Tana ciki, yanzu tayi magana."


Hakan ya fahimtar da ita Umman ce ta dawo. Koda ta buɗe, ta gan su tsaye ga uban manyan kuloli biyu da tarkacen kasko da sauran kayan girki. Ba wannan ba har da su Ɗan Aljan tsaye da yake bin ta da kallo kamar wani tsohon maye. 


Fadi yake "Ai Ranki ya daɗe dama na faɗamaki tana ciki, muna nan ɗazu ta shige. Sai dai ko ta ɗan harba duniyar Mass (Mars)." Ya ƙarashe da dariyar shaƙiyanci, ita kuwa daga yanda Umman ta haɗe rai tana kallonta yasa ta fahimci kuskuren da ta yi na fitowa kai babu ko kallabi sai zanin da ɗaura saman ƴar rigar, duk dai ga ta a birkice alamun mai bacci. 


Bayan ta shige ciki, yaran su uku suka bi bayanta da kayan suka sauke, sai da Umman ta sallame su ta ba su abinci da kudi sannan ta dawo kan Haulatu. Rai a ɓace ta ce "Kin yi sallar Azahar da La'asar?"


Ta turo baki kaɗan. "Yanzu fa na tashi daga bacci, shi zan yi."


Cike da takaici Umma ta girgiza kai. 


"Ki ji tsoron Allah Haulatu, wannan rayuwar da ki ke yi na rashin sauke haƙƙin Allah a lokacin da ya kamata babban kuskure ne. Kina tunanin matsalolinki za su warware alhalin kina yiwa Allah yanda ki ke so? Wato yau ma ba ki yi ko tunanin zuwa Islamiyyar ba ko? Kin kyauta, ki cigaba, nidai Allah na gani ina iyakar bakin ƙoƙar.."


"Kai Umma, nifa ba cewa nayi ba zan yi ba. Haba don Allah, wannan masifar ma da kike ta yi ai sai ya ƙara cinye lokacin."


Umma ta saki baki kawai tana kallonta har ta cika ruwa a buta ta shige banɗaki tana ƙunƙuni, yanke ta idan tana cikin magana wannan ba sabon abu ne a wurinta ba, amma kalmar tana masifa ya yi mata ciwo ƙwarai. Haulatu sau da dama idan ta yi magana kamar an buɗe masai tsabar rashin sanin abin da ya dace ta fadi. Sam, ba ta iya tauna harshe kafin ta furzar ba, komai ya zo mata hakanan ta ke jinsa daidai a wajenta. 


"Allah ya shirya." Abin da ta iya fadi kenan zuciyarta babu dadi sannan ta shiga tattara kayan, tun a kasuwa ta saka yaran sun wanke komai, maida su ta yi kawai kicin ta adana, abincin da ta rage musu da zasu ci, shi ta juye cikin madaidaitan kwanuka sannan ta shige daki don rage kaya ta watsa ruwa. Koda ta fito daga dakin, ta iske ta a tsakar gidan ta tayar da sallah bayan ta zura dogon hijabin Umman dake ajiye saman tabarmar. Ita kuwa bokiti ta ɗauka ta cika ta shige. 


Haka Haulatu ta yi sallolinta kafin ta miƙe ta dauko faranti, kai tsaye ta dibi shinkafa da waken ta sanya kabeji da mai a samansu. Tana cikin ci Umman ta fito, cikin sakin fuska Haulatu ta dube ta. 


"Lah Umma yau dai kin yi sa'ar mai, babu warin nan irin na rannan."


Ganin yanda ko kallonta ba ta yi ba ta shige ɗaki sai ta sha jinin jikinta.


"Ita kuma wannan ita da wa?" Ta yi tambayar a fili babu mai amsa mata, sai kuma ta ja guntun tsaki tunawa da ta yi mai yiwuwa rashin zuwa islamiyyarta ne ya yi wa Umman ciwo. Hakan yasa ta miƙe duk abincin ma ta ji ya fice a ranta don ita fa ba ta kaunar ta ga ko alamar ɓacin rai a fuskar mahaifiyarta. 


"Umma ni ce ko? Ban je makaranta ba, kiyi hakuri na dawo kaina na ciwo. Amma zan je ran Lahadi tunda gobe juma'a." Kasancewar makarantar hutun juma'a da asabar ake yi. 


Umman dai ba ta ce uffan ba ta zura doguwar rigarta ta shan iska, ganin dagaske dai ba za ta kulata ba yasa hankalinta tashi. Nan fa ta shiga ban hakuri har da su hawaye, Umma ta dube ta, dagaske ita laifinta ɗaya ta ke hangowa kanta, wato na ƙin zuwa makaranta, a ganinta shi ne dalilin fushinta. Ta ɗan yi shiru tana nazarin wannan wauta na ɗiyarta. Can kuma ta numfasa gami da soma magana. 


"Shikenan, amma ki sani kalmar da kika yi amfani da ita na ina masifa, ba daidai ba ne yiwa babba ita. Ba ma wannan kaɗai ba Haulatu, ko kaɗan bai kyautu ace babba na magana ka katse shi ba, wannan yana nuni da rashin ladabi gareshi. Sannan ba sau ɗaya ba, na sha nunamaki illar wannan tsakin da kike yawan yi ga babba balle kuma ni da nake mahaifiya gareki ba daidai ba ne, na lura ya riga ya zamar maki jikin da yanzu da kuma nan gaba zai iya haifar maki da tarin matsaloli, koda ace ba a wurina ba, za ki iya samun matsala da gidan da za ki je nan gaba."


Cikin rashin fahimta Haulatu ta ce.


"Gida kuma? Ni zan je? Wayyo Umma kin amince kenan mu bar masa gidansa?"


Ta ƙarashe a ɗokance tana jin nesa ta matso kusa, burinta zai cika sai dai kuma girgiza kan da Umman ta yi ya sanya ta yi kamar ta ja tsaki sai kuma ta tuma ta saita leɓɓan da ta turo gaba da farko. Sosai ta lura da abin da ta yi niyyar yi, ta sani yarinyar sai a sannu za ta gyara. 


"Umma wane gidan zan je na bar ki?"


Ta katse mata tunanin da ta tafi. Ta numfasa.


"Ita mace ai ba ta zama ba ce, dole wataran ki tattara ki je gidan wanda Allah ya ƙaddara shi ne mijinki."


Dariya sosai Haulatu ta sanya. 


"Kai Umma kina magana kamar a irin Indiyarnan mai fassarar Hausa. Aure manya. Ai fa, Iro dai zai ga wacce zai kai gidan wancan tsohon ƙwarton mai sa..."


"Haulatu!" Tsawar Umman ya dakatar da ita. A zafafe ta cigaba da magana.


"Meyasa kika da taurin kai da kunnen ƙashi ne? Mahaifinki kike kira da wannan banzan sunan wai Iro? Na fadamaki duk lalacewarsa shi din Uba yake a wurinki! Kar ki kuskura ki kai ni maƙura! Aure kuma ai dole wataran ki yi shi! Kin fi kaunar ki zauna kina rayuwa cikin waɗancan ƴan daban masu shirin farautarki a kowane lokaci? Idan ke har yanzu ba ki san meke maki ciwo ba, ni na sani!"


Umman na kai wa nan ta fice daga ɗakin. Dagaske sosai Haulatun ta sha jinin jikinta, ko mene ne ta aikata, tana da tabbacin wannan faɗan ba iyaka nan ya tsaya ba, akwai wani abin da ke ran Umman da ta kasa fahimtarsa. Kusan ta mance rabon da ta ga bacin ranta irin wannan. Wannan yasa duk ta rasa sukuni. Daƙyar da suɗin goshi ta shawo kanta har ta sake bayan ta mata nasiha akan gyara kalamanta ko don gaba musamman ma na wannan sunan da ta sanyawa mahaifinta daga Ibrahim zuwa Iro. 


Haulatu dai ta amsa da toh za ta gyara don komai ya wuce amma har a zuciyarta ba ta jin yana da wani sunan bayan Iro, ko a makaranta ma da Muhammad take amfani matsayin sunan Uba. Umma ba ta hana ta ba tunda dai ana jika, ita ta san sunan mahaifin baban Haulatun ne sai kawai ta rabu da ita. 


***

 Ya yi shiru yana juya cokali cikin kofin ruwan shayin dake ajiye saman teburinsa a ofis. Numfashi yake ja gami da furzarwa tamkar wanda ya ci gudu. Can kuma ya cire hannun ya ɗan bugi tebur har ruwan shayin na ɓata wasu takardun dake ajiye gefe. Hakan ya ɗan tsoratar da mutane biyun dake zaune a ofishin tare da shi. Babu wanda ya samu damar cewa uffan a cikinsu har sai da uban gayyar ya soma magana don kansa.


"Kai Ɗan Mutuwa! Ba fa zan yarda da wannan soki burutsun naka ba! Ya kake ƙoƙarin haramtamin abincin da Allah bai yimin iyaka da shi ba?! Ka fito kawai a mutum, kai tsaye ka cemin ba za ka iya auramin ɗiyarka ba kawai!"


Mutumin da aka ambata da Ɗan Mutuwa cikin maƙurar ladabi ya soma magana.


"Haba Yallaɓai, na rantse ka fi ƙarfin dukkan wata alfarma. Ni ko Na'imar ka gani kake so ai zan iya sakarta ka aura ballantana kuma abin da yake ƙarƙashin ikona? Kawai dai akwai babbar matsala ne."


Ya ƙarashe murya a ƙasa da tunanin ƙaryar da zai shirgawa Ciyaman ya samu su rabu lafiya. 


"Wace irin matsala ce kai kuwa Ɗan Mutuwa da har za ka kasa biyawa Yallaɓai buƙatar da ba ta fi ƙarfinka ba?" Cewar wani kakkauran mutumin dake zaune a kujera suna fuskantar juna. Ɗan Mutuwa ya sauke ajiyar zuciya, ya kula gaba ɗaya hankulansu na gareshi wannan ya sanya shi haɗiyar yawu daƙyar.


"Mata maza ce."


Abin da ya tsinci harshensa da furtawa kenan, babban burinsa wannan ta kawo ƙarshen zancen, ya kasa haɗa idanu da su duka. Kirjinsa na bugawa tamkar zai fito. Kalaman Haulatu ɗiyartasa ke amsa kuwwa a dodon kunnuwansa cewar da ta yi za ta fallasa dukkan sirrinsa. Toh kuwa da fashewar ruɓaɓɓen ƙwan nan baragurbi, wanda warinsa zai shafi mutane da dama, ai ya gwammace ya yi wa maganar auren kisan gilla ko ta wace hanya.

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: FITAR TSIRO


  Rufaida Umar


Paid book: 500

Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB


Phone number: 09034973645


Free page 1
Bismillahir Rahmaanir Raheem. 


Ina roƙon Allah yanda muka fara ya bani ikon kammala maku lafiya. Allah ya baku ikon riƙe amanar labarina, ku bar shi a inda ku ka gani ku karanta. Nagode da kauna, Allah ya bar zumunci. Ameen.


***


Ta ɗaga idanunta tarr ta sauke saman mahaifinta wanda ke tsaye riƙe da belt yana huci, zuciyarta ta zo iya wuya ta soma magana a kausashe.


"Wallahi sai dai ka kashe mu, amma har abada ba zan taɓa yarda da auren nan ba. Idan kuwa ka takuramin sai na tona asirin ƙazamin sana'arka wajen hukuma idan ya so ka tsire ni da raina!"


Bai san lokacin da ya saki belt din ba, a razane wannan karon yake dubanta kafin ya maida duba ga Mahaifiyarta wacce ke kuka ga jikinta duk a fashe tsabar dukan da ta ci a hannunsa. Ya ƙara duban ɗiyarsa karo na biyu, babu ko digon tsoro ko fargaba a kwayar idanunta sai ma wani ƙarfin gwuiwa da jarumta. Da rawar murya ya soma magana bayan ya maida duba ga Mahaifiyarta. 


"Na'ima...ni kika tonawa asiri wajen ɗiyarki?"


Yana maganar yana matsowa kusa da ita, ji ta yi numfashinta ya kusan ɗaukewa tsabar tsoro da tashin hankali. Tana kuka tana ja baya tana girgiza kai.


"Wallahi wallahi ban sanar da ita komai ba. Ban san a inda ta ji ba. Haulatu, a ina kika ji?"


Yarinyar da aka kira da Haulatu ta dubi Mahaifiyarta hawaye kace-kace saman fuskarta ga wani malolon abu da ya tokare mata wuya tsabar takaicin irin wannan shakkar da Ummanta ke yiwa Baban, mutumin da bai dauke su a komai ba face wani nauyin wahala da yake buƙatar yakicewa ta kowane hali. Sai ta ji gaba ɗaya ma ta kasa magana, tamkar wacce aka naɗewa harshe. Ta miƙe kawai ta shige ɗaki a fusace. Ta yi zaton zai ƙara kai hannu jikin Ummanta da zummar duka sai kuma ta ji shiru. Karshe ta ji an buga ƙyauren gidan da ƙarfi shaidar ya fice kawai sai ta haɗa kai da gwuiwa ta shiga rusa kuka. A wannan yanayin Umman ta shigo dakin, cike da tashin hankali ta hau jijjigata idanu waje. 


"Haulatu, faɗamin a inda kika san wannan baƙar sana'ar ta mahaifinki? Wa ya fadamaki?"  Ta ɗago tana sheshsheka ta ce.


"Umma don Allah ki rage tsoron wannan mutumin. Ki yarda mu gudu mu bar masa gidansa. Wallahi idan ya dage zai aurar da ni ga Nazifi za ki neme ni ki rasa, ni zan tseratar da rayuwata tunda kin ji kin gani za ki iya rayuwa da shi."


Ta yi shiru kawai tana duban ɗiyarta, ta kasa ce mata komai sai ruwan hawayenta dake fita gami da numfashin da take saukewa lokaci zuwa lokaci ga uban radadi da jikinta ke yi wanda ba domin ba a sabo da wahala ba sai ace ya ci ace ta saba. 


Haulatu ta ƙara duban Umma da rinannun kwayar idanuwanta yayinda take wani ɗan murmushin takaici.


"Na sani, dama wannan shirun da kika saba yi a duk sadda na nemi mu gudu, shi za ki yi. Shikenan, Umma ki cigaba da shirun idan har kina ganin wannan ne mafitar da kika zaɓamana. Kin fi kaunar yanda nake rayuwa a makaranta ana tsangwamata saboda halayyar mahaifina, toh shikenan, zan cigaba da rayuwa da ke a unguwar da ko makwafta ba sa shiga harkar mu su na mana kallon mutunen banza duk adalilin mijinki, babu wanda ke ganinmu da mutunci sai ƴan daba dake dandazo a kowace rana a ƙofar gidan nan suna taya ɓera ɓari, su na ƙara yiwa mijinki kirari da Oga kansa yana fasuwa.  Zan cigaba da zama watarana nima na bi sahunsa na zama mai siye da siyarwar ƙwayo..."


"Yimin shiru Haulatu! Rufemin baki tun ban zubarmaki da haƙora ba!"


Tsawar Umman ta katse zantukan da take yi kusan ba'a hayyacinta ba, sai kuma jikin Umman ya yi sanyi, tana kukan ta rungume Haulatu a jikinta. Ita kaɗai tilo ɗiyar da ta haifa ban da cikin da mijinta ya dinga zubar mata har sau shida, samun Haulatu da ta yi Allah ne ya ƙaddara sai ta fito duniya. 

Itama Haulatun tana kuka ta rungume Umman, a duniya babu wacce ta fi ta a wurinta. Tana mata so da kaunar da har abada ba ta ji za ta iya nunawa ga wanda yake amsa sunan mahaifinta, mutumin da har abada ba ta jin za ta ba shi wannan ragamar. Tana da burin ace watarana ta kwatarwa Umman ƴancinta ta kuma ga ƙarshen wannan zaluncin da ya ke yi musu. Tauye haƙƙoki ba iyaka, sun shallake tunanin dukkan mai tunani, ana zama ne don ba wata inuwar da za'a raɓa a ji sanyi, wannan inuwar ta zama ta dole amma hakikanin gaskiya abin ya soma kai ta maƙura. 


"Umma don Allah kar ki bari ya aurar da ni ga Alhaji Nazifi. Wallahi mutuwa zan yi."


Ta ɗago fuskar ɗiyarta tana share mata hawaye lokaci guda tana mai girgiza kai.


"Ba za ki mutu ki bar ni ba Haulatu, in sha Allahu za ki yi rayuwa mai tsawo, za ki samu farin cikin da nake yawan mafarkinki da shi. Aurennan kuma ba zai yiwu ba, ina ji a jikina daga yau an bar maganarsa. Mahaifinki ba zai ƙara tayarwa ba."


Haulatu ta runtse idanu, zafi take ji na gaske a kirjinta, duk sadda aka alaƙanta sunanta da shi takan ji tamkar ta tsire kanta, ita fa ba ta kaunar a kirashi da mahaifinta. Ta dai ji abin da Umman ta furta amma fa ba don ta gamsu ba sai ma ta shiga al'ajabin ta yanda Umman ta aminta ɗari bisa ɗari cewar an bar zancen gaba ɗaya.

  Kiraye-kirayen sallar la'asar ne ya katse musu shirun, Umma ta miƙe ta fita don ɗora alwala yayinda Haulatu ta ja jiki ta jingina jikin bangon ɗakin.


   Har Umma ta shigo ta shimfida abin sallah a gefenta ba ta sani ba, ta dube ta sosai, jinkirta lokacin sallah ba wani abu ne sabo a rayuwar ɗiyarta ba, wannan yana daga cikin abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya, ta sani kamar yanda kakarta ta wajen uwa ta faɗi mata kafin mutuwa ta raba, sallah babu musibar da ba ta magancewa hakan yasa duk runtsi take matukar kokarin yi akan lokaci ta kuma dage wurin gani Haulatun itama tana yi, sai dai tana mamaki yanda koyaushe sai an sha fama kafin ta miƙe ta yi. Tana tsoron ace ta dauki wannan mummunan ɗabi'ar na mahaifinta wanda sallar ma ba ta dame shi ba. Hakan yana daga cikin dalilin da ta tsaya ka'in da na'in take kokarin ganin Haulatun ba ta yi wasa da zuwa Islamiyya ba. Wasu lokutan ta je, wasu lokutan kuma ta fake da cutar ƙarya ta lafe a gida. 

   

"Haulatu."


Kiran sunanta da ta yi ya sanya ta firgigit ta dube ta. Wani abu ya tsirgawa Umma a zuciya, ta danne ta hanyar haɗiye miyau. Da muryarta mai nuni da rauninta ƙarara ta ce.


"Maza tashi ki ɗauro alwala ki yi sallah, wannan tunanin da koke-koken babu amfanin da zasu yi maki. Kinji ko?"


Ta yamutsa fuska sannan ta miƙe gami da jan ƙaramin tsaki, ba ta ce uffan ba ta fice daga ɗakin. Idan da sabo da wannan halayyar ta komai aka ce ta yi tsaki, Umman ta saba, ita dai tana kokarin ganin yarinyar ba ta sauka a kan turba ba, daidai gwargwado tana yi mata gyara a wasu guraren na kalolin rashin kunya ko ace tarbiyya, amma ta sani ƙarfe ɗaya ba ya amo. Addu'a ita ke maganin komai. 


Da wannan ta share zantukan zucin, ta tayar da sallar. Kafin ta idar itama Haulatun ta iso ta zura hijabinta ta tayar. Umman ta riga ta miƙewa ta fice tsakar gidan don kama aikace-aikace. Ita kuwa Haulatu koda ta fito sai ta nemi wuri ta zauna gami da zubawa uwar idanu yayinda take kiciniyar kaɗa omo don fara wanke-wanke. 

  Doguwar mace mai hasken fata da kyawun dirin halitta don idan suka jera ba za ka ce ita ta haife ta ba sai dai ko a kirata da yayarta ko kuma ƙanwar uwa saboda irin matan nan ne masu baiwar jiki mai kyau. Ta tabbatar da ace su na gudanar da rayuwa ne ta daula ko kuma rufin asiri ko yaya, da Allah ne kadai ya san irin gogewa da tsantsar kyawun halittar da za'a ga mahaifiyarta da shi. Sai ta ji murmushi ya suɓuce mata wanda nan take ya mantar da ita matsalolin da suke ciki, ta tafi hasko kawunansu cikin rayuwar da take da buri da mafarki a koyaushe. Wai ace ga su nan a gida mai kyau da tsari, Ummanta na daga zaune ga ma'aikata sai hidima suke yi. Duk abin da Umman ke buƙata na jin dadin rayuwa babu wanda babu a gidan, ita kuma a lokacin ta zama ƙwararriyar lauya mai kwatarwa jama'a haƙƙoƙinsu, ta hasko kanta a kotu tana mai ba Ummanta kariya akan shari'arta da Mijinta, gashinan har an yanke masa hukunci su kuma sun samu ƴanci. Haka ta dinga saƙe-saƙe a cikin ranta har hankalin Umman ya kai gareta. 


Ganin yanda ta zubamata idanu tana murmushi sosai ya ba ta mamaki, kar fa damuwa ta taɓamata kwakwalwar ƴa.


"Ke, tunanin me kike yi? Kallon na mene ne haka?"


Wannan magana ta Umma ya maido ta cikin hayyacinta. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da ɗan lumshe idanu kadan.


"Ba komai Umma. Ki taya ni addu'a, Allah ya cikamin burina."


Umman ta murmusa. 


"Haulatu kenan, kin fi kowa sanin cewa kina sahun farko a cikin addu'o'ina na kowacce sallah da ma sauran ibadu. Sai kuwa iyayena da mijina."


Ta ƙarashe murya a raunane. Haulat ba ta ce mata uffan ba jin sunan da ta ambata a ƙarshe, ba yau farau ba, ta ce mata itama ta dinga sanya shi a nata addu'o'in, Allah yana karɓar adduar mace ga mijinta kamar yanda yake karɓar na ƴaƴa ga iyayensu, sanadin hakan sai ta ga Ubangiji ya nufe shi da tuba kafin mutuwa. 


"Tashi ki duba ko sauran manjan nan zai ishe mu sai ki siyo mana gawayi a dafa sauran taliyar can a ci ko?"


Haulat ta amsa, ta tuna dazun Baban ya yi tamola da kaskon da manjan ke ciki kafin ya soma sababin wai Alhaji Nazifi ya zo zance amma ta ƙi fita wajensa. Ita ya soma kai wa mari kafin shigowar Umman tsakiya ya sanya ya maida dukan kanta ta hanyar zaro belt ya hau jibgarta, acewarsa ita ta hana ta fitar. 


Allah ya taimaka ta iske akwai saura kadan, idan har za su gauraye taliyar a kaskon tasan zai wadatar tunda dama babu Maigidan a tukunyarsu, koyaushe da ƙulli yake shigowa gidan. Ko na indomie, ko nama da gurasa kodai naman kai, wasu lokutan kuwa kaza. Ya ci iyakar cinsa babu wanda zai yiwa tayi acikinsu. 


Ta ɗan ja tsaki, sannan ta shaida wa Umman akwai.  Naira ɗari ta miƙa mata, Haulat ta ɗora hijabi saman doguwar rigar dake jikinta na wata koɗaɗɗiyar atamfa ta fice daga gidan lokaci guda tana share ƙwallar da ta cicciko mata. Koda ta dawo da kanta ta hura ta ɗora ruwan taliyar, kafin nan tuni Umman ta kammala wanke kwanuka tana hada-hadar share tsakar gidan, ita ta karɓi sharar hakan ya ba Umman damar komawa ɗaki. 


Koda ta kammala sharar madadin ta  bi ta sai kawai ta maida tabarma ta zauna a tsakar gidan don ba ta son takurawa Umman, a wannan lokaci na tsakanin La'asar da Magriba, baiwar Allahn na iyaka kokarin wurin gudanar da ibada a wannan sa'in, azkar da karatun Alkur'ani da salati. Tana son ta dinga koyi da ita wajen ibada amma ita kam ta sani a yanzun son jiki ba zai bar ta ba wanda ta biyewa zuciyarta ta kasa yaƙarsa. A ranar dai har ta yi bacci Baban bai shigo ba, ita kuwa Umma koda ta soma gyangyaɗawa sai ta yi firgigit ta farka cike da fargabar da yadda Mijinnata zai shigo. 


Aikuwa sai gashinan wuraren sha biya da mintoci ana bugun gidan kamar za'a ɓalla. A razane ta miƙe jiki na rawa ta bude ƙofar dakin ta fito tsakar gidan, ƙarasawa ta yi ta buɗe mishi ƙofar ya shigo yana tangaɗi, toshe baki ta yi tana jin wani zafi a kirjinta. Ashariya ya watsamata gami da fadin.


"Don ubanki shi ne ina bugun ƙofar ba za ki buɗe da wuri ba? Ko tare da ubanki Saleh mai kalangu muka haɗa kuɗin muka sayi gidan?"


Ita dai Umma ba ta ce uffan ba bayan kaucewar da ta yi ya faɗa gidan har yana buge kai da bango. Ta ƙarasa da sauri ta rufe ƙofar da sakata. Tana kallo ya shige dakinsa, idanunta ta ɗaga tana duban farin watan Rajab na daren goma sha hudu da ya haske tsakar gidan, lumshe idanu ta yi hawayenta suka zubo tana mai ambaton Allah a ƙasan ranta. 


Daga ɗaki kuwa, Haulatu babu abin da ba ta tsinkaya ba, ta ƙara tura kanta cikin zanin rufarta ba tare da ta iya ko hawaye ba, ya ci ace ta saba da wannan baƙaƙen halayyar na mijin Ummanta kamar yanda take laƙaba masa. Wai ace mahaifin da ya cancanta da ba ka tarbiyya, shima babu tarbiyyar tattare da shi? Aikuwa bai cancanci ta kirashi Uba ba. Wannan abu na mata ciwo, ta tuna da tsiraru daga cikin ƙawayenta na makaranta idan ta je gidajensu, har ba ta kaunar ta fito saboda ganin irin kyakkyawar mu'amalar iyayensu da ma yanda mahaifansu ke takatsantsan da duk abinda zai ruguza tarbiyyarsu. Har sha'awa take yi idan ta ga budurwa na shakkar wai mahaifinta ya ji ta aikata abu marar kyau koda kuwa a misali ne irin na hirar ƴan makaranta, amma ita kuwa, ta sani babu wannan ranar cikin babin rayuwarta. Sanadin nata Uban ta rasa ƙawaye da dama daga kan boko har islamiyya, mafi kuma yawansu iyayensu ke musu iyaka da ita. Abin ya kai itama an soma yi mata ƙazafin tana shaye-shaye. Ga kuma maza yan iska da suke mata kallon kamar itama fanko ce don wasu ma sun sha nemanta da hujjar ai iyayenta bariki suka haɗu kawai itama ta basu hadin kai tarihi ya maimaita kansa. Abin ya kai ko neman taimakon abinda za su sa a baki ita da Ummanta ta je, sai an nemi ta bayar da budurcinta sannan a taimaka musu, wannan dalilin yasa ta gwammace ta yi suyar awara a gefen titi. Nan din ma dai ba ta tsira ba don ƴanniskan samari ke taruwa, idan ta yi magana a yaɓa mata baƙa, hakan yasa ta tattara ta daina. Sana'o'i dai na cikin gida in zasu shekara su na yi babu mai kallonsu, daga an fara siya kamar abin arziki sai a ɗauke ƙafa gaba daya wannan ne dalilin da yasa suka hakura da sana'a a unguwar, Ummanta ke zuwa can kasuwar kantin kwari tana waina da miya da rana, tana da almajirai masu kai mata kaya da kuma taimaka mata da wasu abubuwan a kasuwa, ita kuwa ta fice makaranta sai an tashi ne take zuwa wajen uwar nan ma bisa umarnin Umma sai ta sanya niƙaf ta rufe fuskarta, ba don tana son niƙaf din ba sai don hakan ta sani zai fi mata kwanciyar hankali ita kanta kuma ya zame mata katanga wurin ɓata gari yasa ba musu ta bi umarnin. Itama kuma Umman ba ta bada fuskar da za'a kawo mata zantuka marasa ɗa'a ba wannan dalilin yasa mafi yawa ke girmama ta, tsakaninsu sai gaisuwar mutunci da kuma hira ba na kaucewa hanya ba. Anan za ta taimakawa Umman su wanke abin da ya kamata a wanke, su shirya kayayyakin cikin ɗan sahu su koma gida. Kusan kudin sai tace Baban ake nemowa, don duk sadda aka dawo toh fa sai Umma ta ba shi nasa kason, wataran ma sai ya ce dole ta ba shi duka kudin zai biyata ana binsa bashi. Sun sha yin kwanaki ba su yi sana'a ba saboda Umman ta yarda da romon baka wani sa'in kuma tursasawar Baban ta ba shi kudaden. Haulat kan ji haushi ƙwarai har kuka take yi da daukar alwashin ba za ta ƙara bin Umman kasuwa ba tunda kudaden Baba take damƙawa. A ƙarshe kuma ta huce. Idan zaman babun ya ishe su Baban ya ƙi ba su kudin da zasu ci su sha, takan faki idanun Umma ta shiga dakin Baba wanda koyaushe yake garƙamewa (bai san ta zare mukulli daya cikin muƙullayensa ba) ta lalubo musu kuɗi a ma'ajiyarsa. A ranar ba ta ba Umma ba sai a washegari ta ce ai ta ranto mata ne a hannun Mamar ƙawarta don su koma sana'arsu idan an tara riba za ta mayar mata da kuɗin. Duk ranar da ta yi haka kuwa Baban zai zo ya yi ta ɗura ashariya yana tambayar wa ya taɓa kudadensa sai dai ba ya wani faɗan kirkin a zo a gani yake bari tunda ya sani shi kaɗai keda muƙullin ɗakin babu wanda ke shiga yana dai mamakin lamarin, tun Umma ba ta gane abin da take yi har ta fahimci idan sun rasa jari ga yanda Haulat din ke samo musu. Anan fa za ta dinga fada da nunamata illar sata, Haulat ko a jikinta don kuwa a ganinta raba arne da makami ma ai ibada ne tunda akwai haƙƙoƙinsu da yawa da bai damu da saukewa ba. Ranar da ya gano Haulatu ke ɗaukar masa kudi ta ci duka tamkar zai kashe ta. Daga wannan lokacin ne ya ci alwashin aurar da ita ga wani ubangidansa da yake yiwa bangan siyasa a baya, Ciyaman Nazifi. 


Ta runtse idanu sakamakon sarawar da kanta ya soma, tabbas idan ta ce za ta zurfafa cikin tunane-tunanen abin da ya faru da su a rayuwa sanadin mahaifinta toh lallai za ta kwana cikin azabar ciwon zuciya da na gangar jiki wannan ne dalilin da ya sa ta fidda komai a ranta ta yi addu'ar kwanciya bacci, tana jin Umma ta miƙe ta fita ta dora alwala ta dawo dakin ta rufe, a haka bacci ya dauketa. 


***


 

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: *FITAR TSIRO*


 *©️Rufaida Umar*


Paid book: 500

Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB

Phone number: 09034973645


Free page 3
"Ɗan Mutuwa, ni za ka kawowa wasa?"


Cikin dakiya ya girgiza kai gami da ƙara narkar da fuska kamar muminin da ya tuna kwanciyar kabari.


"Wane ni na zo maka da wasa Yallaɓai? Wa ya ƙi ɗakinsa da ƙwan jimina? Ai bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne. Tunku, ya san jibar da yake yiwa kashi, ba irinku ake zuwa gabanku da ƙaramar magana ba."


Jin haka sai kuwa jikin Ciyaman ya yi sanyi, komawa ya yi ya jingina da kujerar gami da ɗan rufe idanu. Tabbas dole ya yiwa abin tufka kafin wankin hula ya kai shi dare. Bai so ace wai Haulatu, mace ta uku cikin wadanda ya so aure amma ba a dace ba. Ga dai tafarkin da bokansa ya ɗora shi a kai, ruwansa ne ya yi gaggawar aure nan da sati lafin guguwar siyasa ta motsa, ruwansa ne ya yi fatali da zancen ya ci karo da sakamako mafi muni a rayuwa. Sharuɗɗa biyu bokannasa ya ba shi, ɗaya shi ne ya nemi matashin namiji su aikata alfasha, ɗayan kuwa shi ne ya nemi budurwa marar kowace nakasa ta kowane ɓangare ya aura, wato sabuwa dal a leda wacce aka yi mata kyakkyawar shaida ta kamun kai. Muddin ya cika waɗannan sharuɗɗan bayan layu da ya sa aka binne a sabon gawa, to babu abin da zai hana shi cimma nasara da yin tamola da abokan hamayyar kujerar takararsa na ɗan majalisar dokoki na Jaha. Budurwar farko ya samu rahoton tana shaye-shaye, ta biyu kuwa tana biye-biyen maza. Idanunta sun bude da son abin duniya hakan yasa take iya komai don ta samu biyan buƙata. Sai ga Haulatu wacce ya samu shaidu sama da hudu a kanta ta bakin majalisar su Maada cewar ba ta tsayuwa da kowa ba ta kula kowa. Asalima haushin ubanta take ji da munanan ɗabi'unsa, itama ashe ya yi kura ce lulluɓe da fatar akuya duk da dai abin ba daga gareta ba ne.  


"Ayi hakuri ranka ya daɗe."


Faɗin Ɗan Mutuwa karo na biyu, Ciyaman ya sauke ajiyar zuciya bayan ya dawo daga kogin tunanin da ya afka. 


"Shikenan, kar ka damu. Kuturu da kuɗinsa ai alkaki sai na ƙasan kwano, zan samu daidai da zaɓina. Nasan inda zan nufa kuma."


Suka dube shi su biyun duka, shi dai Ɗan Mutuwa bai fahimci abin a zo a gani ba, shi kuwa ɗayan mai suna Mahadi, kasancewarsa na hannun damar Ciyaman ya gane karatun don haka ya dubi Ɗan Mutuwa.


"Kana iya tafiya." 


Ɗan Mutuwa cike da jin haushin irin wannan mulkin mallaka da Mahadi ke nunamasa a gaban Ciyaman ya miƙe yana ɗaure fuska ya kama hanyar fita, Ciyaman ya maido shi baya ta hanyar kiran sunansa hakanan ya dawo kirjinsa na ɗan bugu, duk a zatonsa ƙullinsa ne zai warware. Sai kuma ya ji saɓanin tunaninsa. 


"Ka je gobe war haka ka dawo ka karɓi saƙo hannun Mahadi."


Ya dubi Mahadi karo na barkatai, shima Mahadin fuskarnan babu fara'a, shi fa bi yarda da zancen Ɗan Mutuwa game da ɗiyarsa kawai dai yana ji a jikinsa akwai wata a ƙasa. Dama can ba son tarayyar Maigidannasu da Ɗan Mutuwa yake ba. Babu yanda zai yi ne kawai saboda akwai hannun mutumin dumu-dumu acikin ɓoyayyiyar harƙallar da suke yi. Ga wata baiwa da yake da shi na saurin siyar da dukkan kayan da suka shiga hannunsa ya kuma ninka riba har fiye da yanda aka tsammaci zai kawo. Sai dai har gobe ba ya kaunarsa, kuma yana fatan ranar da zai kawo ƙarshen alaƙarsa da Maigidan duk kuwa da sanin cewa abu ne da sai ya zage damtse. 


Har ƊanMutuwa ya yi godiya ya fice bai bar watsamasa harara ba. 


"Yanzu mene ne abin yi Mahadi? Kai kasan komai dangane da sharudɗan Na Kan Tudu, wa kake ganin ya dace na nemi aurenta wacce aka yarda da salihancinta da kamun kai?"


Ya gyara zama. 


"Toh Ranka ya daɗe nifa na gama dukkan lissafina, tunda dai duk inda aka bi ba ya ɓillewa, me zai hana mu koma can gida Rano mu samo daga cikin dangi."


Ciyaman ya ɗan yi shiru kafin ya amsa. 


"Nayi wannan tunanin, amma kuma ba ka tunanin asirinmu ya tonu sanadin auren ta gidan?"


"Ba zai tonu ba, ai da ace bamu da Boka Na Kan Tudu, shi ne zamu tsaya wala-wala. Ai ba banza ba, mallake yarinya za'a yi ya kasance sai yanda aka yi da ita. Ni dai a nawa ganin can ɗin ya fi rufin asiri kan ko'ina. Aka ƙulle bakin mutum me ya isa ya faɗi?"


Dariya sosai Ciyaman ya yi, sai a lokacin ya samu nutsuwa sosai. Ya kuma ji daɗin samun mutum irin Mahadi, koyaushe idan ya kasa samun mafita na matsala, sai ya zo masa da mai kyau. Har ya soma hango kansa a ɗakin taro na majalisu na Jaha ana damawa da shi. A nan suka yanke ranar da ta dace su kama hanyar garin. 


***

Ɗan Mutuwa ya koma wurin aikinsa na kanikanci inda yake fakewa da guzuma yana harbin karsana. Zuciyarnan fari ƙal saboda ko ba komai ya kashe maganar da ta fi kowacce damunsa a ruhi. Ya iske yaransa na ta faman aiki, tun kan ya ƙarasa wurin ɗaya a cikinsu ya iso inda yake yana yi yana waigen sauran da ke faman harkar gabansu sannan ya juyo da muryar ƙasa -ƙasa ya ce. "Boss, tun ɗazu fa yaron Prince ke jiranka zai karɓi kaya."


Jin haka ai sai wani sabon annashuwa ya ƙara lulluɓe Ɗan Mutuwa. Ba shiri suka ƙarasa, yaransa na gaida shi yana amsawa cike da kulawa, can kuma ya ƙarasa ga wata baƙar mota Honda Accord wacce ta sha baƙaƙen tinted. Ya kalli ɗan tsamurmurin saurayin dake tsaye gefen yaran wurin.


"Afuwan Harɗo, na tsaida ka."


Wanda aka kira Harɗo ya maida waya aljihu yana dan murmushi ganin hankalin kowa a kansu. 


"Ai fa, jira ya zama dole tunda Prince ba ya buƙatar kowa ya taɓa motarsa sai kai. Mu ƙarasa don Allah na soma gajiya dama."


Daga haka suka yi dariya suka yi can gefe inda motar take. Suna isa Ɗan Mutuwa ya shiga mazaunin direba shi kuwa Harɗo ya zagaya ta ɗayan gefen, idan ka hango su daga nesa sai ka rantse babu wani abu da ke wanzuwa face makaniki da ya mayar da hankali ga duba mota da kuma mallakin motar. 


"Na fa jima anan, Prince sai kirana yake gaba ɗaya ya rasa control."


Ɗan Mutuwa bai ko kalle shi ba ya amsa.


"Na je ganin Maigidana ne. Yanzu dai wanne za ka karɓa?"


"Tayoyi za ka ba shi da turaren wuta."


Ya jinjina kai yana wani murmushi.


"Ya ci sa'a kuwa akwai su." Daga nan ya zura hannu cikin takalminsa sawu ciki, ya fiddo wata ƙaramar leda mai ɗauke da Codein (ƙwaya) ya miƙa masa ba tare da hankalin wani ya kai kansu ba. Ya zura hannu cikin rigarsa ta ƙasa inda yake adana tabar wiwi cikin wata ƙaramar jaka da yake ɗaure ta a ƙugu, idan ba jikinsa ka goga ba, ba za ka taɓa sanin da zamanta ba, ya fiddo na adadin da suka nema ya damƙawa saurayin. 


Sosai Harɗo ya ji dadi. Nan take ya fiddo waya ya turamasa damin kuɗaɗe cikin asusunsa na banki da tuni ya jima da adana shi cikin wayarsa.

Sai bayan sun fito daga motar ne, Hardo ya fiddo takardun kuɗi har dubu uku ya ba shi a hannu yanda idanun kowa zai gane mishi. 

Da haka suka yi sallama Ɗan Mutuwa ya koma gurin aikin nasu yana ta washe haƙora don ya sani yau kam akwai shagali.


***

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: *FITAR TSIRO*


 *©️Rufaida Umar*


Paid book: 500

Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB

Phone number: 09034973645


Free page 4


Ta daki ƙyauren gidan sau uku da ƙarfi kafin ta shiga da sallama, mata biyu ne zaune a tsakar gidan jikin ƙofar ɗaki inda ɗaya ke yiwa ɗayar kitso sai kuwa yaro da ke shimfiɗe saman tabarmar, suka amsa mata fuska a sake. 


"Wai ke kam Haulatu nidai ban san dalilinki na son buga gidan nan kafin ki shigo ba." Faɗin matar da ke yin kitson. Tana dariya ta ɗan dubi kewayen su Hindatun ganin a buɗe ya ba ta tabbacin tana nan kafin ta ƙarasa ga matar tana mai ba ta amsa. 


"Ni haka na fi so ai Baraka, da wannan kaɗai ku ke gane ni ce na zo. Nasan dai duk duniya bayan ni babu mai muku wannan sallamar. Amaryar gidan taku har ta soma fita ne?" Ta ƙarashe tana duban ƙofar ɗakin da ke gefen na Baraka. 


"Inye, ka ga masu gida, wato har rabin jikin taki ta labarta maki."


Daidai nan Hindatu ta ɗan leko daga jikin ƙyauren da ya yi musu katanga da sauran mutan gidan daga ita sai ɗaura ƙirji, kallo ɗaya za ka fahimci daga wanka ta fito. Caraf ta karɓe zancen.


"Me za'a fasa to? Mutuwar ko kuwa hisabin? Ai ni kin tunamin ma ban labarta mata cewar tare da ni aka ci kazar Amarcin ba."


Suka yi dariya. Ita dai wacce ake yiwa kitso kallonsu kawai take, tana dai jin labarin Haulatun a bakin su Baraka kasancewarta makwafciyarsu amma ba su taɓa haɗuwa ba sai a yau. Yarinyar da ba ta wuce sa'ar ƙanwarta  ba, kyakkyawa ta bugawa a jarida kuwa sai dai tana tuna ance iyayenta ƴan bariki ne sai ta ji ta ba ta tausayi ta shiga yi mata addu'ar neman tsari daga shiga halaka. 


Har Haulatun suka miƙe da zummar tafiya ɓangaren su Hindatu bayan sun gama caftarsu da Baraka, ba ta iya ta kauda kai daga kallonta ba har sai da ƙilu ta ja bau. Haulatu na ganin yanda ta ƙure ta da idanu ta yi dariyar mamaki ta ce. 


"Ke kam baiwar Allah wannan kallon fa? Ko dai na maki kama da budurwar mijinki ne?"


Ta ƙarashe har lokacin fuskarta ba ta sauya daga yanayin baya ba, itama Hindatu na taya ta darawa ta ce. "Ke dallah, Lubabatu ce fa, na taɓa baki labarinta na ce ta haifi ƴan biyu har ma ɗaya ya koma? Wacce na ce maki ƙaninta ya na sona?" Hindatu ta ƙarasa maganar da murya mai kama da raɗa. 


Baraka ta saba da wannan gwaɓa magana irin ta Haulatu wanda har ka ɗauki zafi ita ko a kwalar rigarta don ba ta gane ta yi kuskure ba, Lubabatu kuwa sosai kalaman sun daki zuciyarta, ranta ya ɓaci. Kafin ta kai ga tankawa sun ɓace daga idanunta sun shige ciki. 


"Haulatu kenan, sarkin iya magana." Cewar Baraka. 


"Wannan yarinyar na yarda ba ta da mafaɗi, wai Baraka ba ki ji dakyau baƙar maganar da ta yaɓamin ba?"


Ɗan murmushi Baraka ta yi tana mai sakar mata gashi ganin ta ƙi ba ta damar yin tufka mai kyau. 


"Kaɗan kenan in dai Haulatu ce, kwanaki can da ta zo daga na ce mata Haulatu wannan kwalliyar fa sai ina? Buɗar bakinta cemin ta yi ai gidanmu za ta je neman sadaka tunda Iro bai ba ta na karin kumallo ba ai gwara ta je wurin Idi. Hum, ke tun daga ranar na ɗauke mata wuta, kuma abin da zai ba ki mamaki fa wallahi wai ita wasa ne ta yimin, har da za ta tafi sai da ta shigo wurina mu yi sallama. Ni dai daga baya ta yi zuwa kusan biyu amma babu alamar ta san ina wani abu wai fushi, sai da ta tambaye ni don kanta ko ta yimin laifi ne, na nunamata kurenta, ke yarinyarnan har da su ƙwalla wai ita wallahi wasa ne ta yimin. Na nunamata iyaye ba abin wasa ba ne ta daina. Ta ce ai wai ganin Idin sunan kakana ne. Nace ko kakan kakana ne kuwa. Toh ban ce ba ta ƙara gwaɓamin ba amma dai na iyayen gaskiya ba ta kuma maimaitamin ba. Shi dai Baban nata Iro da ba ta ganinsa da gashi ko kaɗan kamar yanda na taɓa faɗamaki, shi dai ba ta fasa ba."


Lubabatu ta girgiza kai gami da sakin huci. 


"Amma dai kam ta kiyaye harshenta idan kuwa ba haka ba nan gaba zai haifar mata da tarin nadama nan gaba. Ai tunda ta fito daga irin wancan gidan, fiye da hakan ma za ta iya aikatawa. Kai, Allah dai ya kyauta, ya shirye ta kuma. Ga dai kyau iyakar kyau masha Allah, amma ina gujemata faɗawa halaka nan gaba. Don idan har za ta cigaba da zama da wannan yarinya da uwarta, toh abin fa sai du'ai. Mutanen da idanunsa kw buɗe da son naira."


Baraka cikin raɗa-rada ta ce. "Kinga matar nan ki rufamin asiri, dama ya lafiyar giwa balle an jefe shi da kashi? Allah dai ya mallaka wa mazajenmu gidajen kansu mu yar da ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda kamar ya yiwa su Habiba gyaɗar dogo suka tashi."


Lubabatu ta amsa da amin suka yi dariya. Nan kuma aka dasa gulmar Hindatu da Mahaifiyarta da irin zaman haƙurin da ake yi a gidan dalilinsu. 


***

Hindatu kuwa, su na shiga ɗaki suka kwashe da dariya. 

   "Wallahi ke kam Haulatu ba ki da kirki, ni na tabbata Lubabatu ta ji zafin maganarki. Ke ko kadan ba kya saita bakinki ko?"


"Au, daga wasa sai ta ji haushi? Toh ni kuwa ina nasan ma mijin nata da har abin zai mata ciwo?"


Murmushi kawai Hindatu ta yi bayan ta shiga mulka a jikinta. Haulatu ta fisge robar. 


"Ni dallah ki faɗamin, me na fadi mai zafi da kike tunanin ban kyauta ba? Bari na je na ji daga bakinta."


Da sauri Hindatu ta dakatar da ita ta hanyar riƙo gyalenta.


"Ke wasa nake maki fa, ba komai. Ai ke da zuciya daya kika yi mata wasan. Yau fa baƙo zan yi."


Haulatu ta koma ta zauna. 


"Waye zai zo? Tj ko Nazifi?"


Tana wani murmushi da fari da idanu ta ce. 


"Ba ɗaya, wani sabon kamu na yi.  Sati biyu kenan da Momi ta ba shi lambar wayata sadda ta je siyayya a shagonsa. Shi ne fa zai shigo yau."


Cikin rashin fahimtar zancen ta ce "Ban gane ma Malama, yimin dalla-dalla. Shi ne duk jimawarnan ba ki labartamin ba komai ba?"


Dariya Hindatu ta yi. 


"Toh ai jira nake na kama dahir. Ke Momy ce ta je kasuwar kwari sarin kaya shi ne fa hira ta yi hira har ake maganar mata yanzu ba su iya kula da gidajensu ba. Mutumin ya nuna ra'ayin shi fa yanzu aure ma yake son ƙarawa, aikuwa Momi ta ce masa tana da ɗiya sai dai ita karatu ta ke son na yi, ya nuna shi ba shi da matsala da karatuna, idan har nayi masa zai bar ni naga ko ƙarshen biro da takarda ne. Toh nidai wallahi daga waya naji ya burge ni don ba laifi ya iya tsara kalamai ga lallaɓa mace da tarairaya kamar kwai. Nikam muna zana SSCE zan shiga daga ciki."


Baki galala Haulatu ke kallonta har sai da ta kai aya kafin ta magantu.


"Kina cikin hayyacinki kuwa? Mutumin da ko ganinsa ido da ido ba ki yi ba? Ba ki san halayyarsa ba amma daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi? Wai ke ce dai me ikrarin sai mun shiga jami'a an dama da mu kuma mun ci karenmu ba babbaka?"


Farr da idanu ta ƙara yi tana duban Haulatu sai kuma ta yi dariya. 


"Ke Haulatu, cemin ya yi fa gidana daban, kuma duk abin da nake so zan yi? Ke har mota ya yimin alƙawari. Kuma kike maganar bamu ga juna ba wa ya fadamaki, ya turomin hotunansa ta whatsapp nima kuma Momi ta bani kuɗi na je an min kwalliya na yi hotuna tun wancan satin fa na turamasa. Ba kin ga hotunan da nayi ba kwanaki a wayata har na ce maki biki aka yi a makwaftanmu? Toh ƙarya nake yi, adalilinsa na ɗauka."


Haulatu jikinta ya ɗan yi sanyi, ba ta yi zaton a cikin amintarsu akwai wani abu da suke ɓoyonsa ga juna ba. 


"Yanzu har akwai wani abu daman da za ki iya ɓoyemin? To idan kin faɗamin mene nawa ciki?"


Hindatu ta ɗan yi shiru, Momi ce ta zuga ta akan kul ta sake ta labartawa Haulatun. Tunda dama can ba son amintarsu take yi ba, ganinta Haulatu ta fi ta kyau ta ko'ina, ga fatarta luwai-luwai kamar mai cin kaza. Uwa uba ba ta shafe-shafe farinta daga Allah ne. Momi ta ce tsaf za ta iya yi mata ƙwacen saurayi, uwa uba kuma ta iya barikanci irin na gidan da ta fito. Ta kuma tuna akwai saurayinta da suka taɓa rabuwa akan Haulatun, tun ganin da ya yiwa Haulatun ya sauyamata, a karshe ya fito mata a mutum ya nuna Haulatu yake so. Aikuwa suka hadu su biyun suka ci mutuncinsa da ya jawo sanadiyyar daƙile alaƙar baki ɗaya. Ita ba ta san ma ƙaiƙayin bakin da ya kai ta yin zancen a yanzu ba. 


"Kiyi hakuri tawan, hirar ce ba ta zo kansa ba. Kin san idan mun haɗu zantukan namu ba sa ƙarewa."


Murmushi mai ciwo Haulatun ta yi, tana ji a ranta akwai wani abun bayan wannan. To ko dai itama Hindatun tana mata kallon ƴar barikin ne irin wanda saura sa'anninta na makaranta suke kallonta? An sha kawo mata zancen wai ita ɗin usulin iyayenta bariki, don haka za ta iya ƙwacewa mutum saurayi ko miji wannan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa kowa na unguwar ƙara nisanta kansa da ita. Ba ta mance ba akwai wata Amarya da aka taɓa kawowa unguwarsu, har sun fara sabawa kawai sai gaba daya ta sauyamata, a ƙarshe ma ta fito mata a mutum ta nuna ita fa mijinta ya hana ta sjiga sabgarta. Kafin ta kai ga ficewa a gidan sai ga mijin ya dawo, daga yanda kuma ya tarbe ta cikin sakin fuska ta fahimci ƙarya ne. Sai daga baya ta ke jin wai Amaryar ce aka gargaɗe ta da shiga shirginta. 

  Haulatu na kai wa nan a tunaninta ta ji kwalla sun ciko mata, ta yi gaggawar kauda su. Sai kuma ta miƙe tana gyara zaman mayafi sannan ta ɗauki ƴar jakarta. 


"Wai don Allah mene haka? Kina nufin ki ce ba za ki tsaya ku gaisa ba? Daga zuwanki har za ki tafi? Ke ko dai haushi kika ji?"


Ƴar dariyar da ba ta kai zuci ba ta saki kafin tana mai janye yatsun hannunta cikin na Hindatun da ke ƙoƙarin dakatar da ita. 


"Haushi a na me? Ko ɗaya, kawai dai dama Umma ta ce kar na sake ta riga ni dawowa gida. Kuma kinga yamma ta yi, gwara na lallaɓa."


Sakin ajiyar zuciya Hindatun ta yi, ita kam koda ba haka bane, za ta so tafiyar Haulatun gudun kar Momi ta dawo daga amsomata rubutun da ta tafi su yi kiciɓus, don a yau Momin ba za ta so ganinta ba musamman tunda babban baƙo zasu yi. 


"Shikenan, amma don Allah kiyi hakuri. Kinsan ba ma ɓoyewa juna komai ko? Na rantse to mancewa nayi."


Ƙaramin dariya ta ƙara saki karo na biyu. Ta ya ya mutum zai mance da hirar wanda ya fi so da kauna? Kawai dai ta karɓi zancen yanda ya ta faɗi don a zauna lafiya.


"Dallah can sai ka ce ni na haifeki kina wani faman damun kanki da rantsuwa. Kar fa ki damu na fahimceki. Bari na wuce nidai, sai Monday idan mun haɗu a makaranta. Ki gaida Momi."


"Aa, bari na taka maki." Fadin Hindatun da sauri tana mai janyo hijabinta ta zura. Ita kuwa Haulatu tuni ta fito. 


A tsakar gidan su Baraka kuwa, tuni Lubabatu ta miƙe tsaye tana gyara goyon ɗanta da ta yi, sun kammala kitson. Ta yi musu sallama ba tare da ta biyewa Baraka da ke tambayar ko lafiya daga zuwa sai tafiya ba ta fice, Hindatu na biye da ita. A daidai ƙofar ta jawo mayafinta. Suka dubi juna, Haulatu cikin kokarin danne ɓacin ran ta ɗan harareta. "Wai ke Malama lafiya kike ta ja min gyale? Bana ce maki magana ta wuce ba?"


Cikin karyar da murya Hindatu ta ce "Kin tabbata har a ranki Haulatu? Na fa san ba ki da riƙo."


"To kin san ba ni da riƙon mene ne abin damuwa? Ni don Allah koma ciki ki shirya kar ki je ya yi maki zuwan bazata ya ganki hakanan ba kwalliya sai ɗaura ƙirji da hijabi. Big Mama, inji ƴan aji."


Suka yi dariya.


"Ƴan duniya ba. Shikenan to ki gaida Umman."


Ta amsa da toh sannan ta yi gaba, Hindatu ta ɗan bi ta da kallo. Taɓ, wato da gaskiyar Mominta da ta ce Haulatu tsaf za ta sace zuƙatan maza fa dama, ga ta dai bilhaƙƙi ta ke tafiyarta amma sai mutum ya rantse da biyu take girgiza jikinta. Ta ji wani abu ya tsaya mata a rai mai kama da haushi da burin inama ita ce mai kyawun halittar. Sai kuma ta yi saurin kauda zancen gudun kar shaiɗan ya jefamata wani abun daban mai akma da hassada da kishi. Ta ji gwara ma da Haulatun ta bar gidan da wuri.


***

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: *FITAR TSIRO*


 *©️Rufaida Umar*


Paid book: 500

Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB

Phone number: 09034973645


LAST FREE PAGE. 


Da daddare misalin ƙarfe tara tana kwance saman ƴar katifarta ta yi shiru gami da zubawa rufin kwano idanu. Dagaske Hindatu itama tsoronta take ji? Ashe ita ce kawai ke zaune da ita da zuciya guda? Kodai ta yarda da abin da mutane suke yi mata ƙazafi a kai ne? 


Ta juya tana fuskantar tagar ɗakin, idanunta fes akan  farin watan da ya hasko su. To idan ma hakan ne, ai bai kamata ta ga laifinta ba, komai da ke faruwa a rayuwarta silar tsatson da za ta fito ciki ne. Nan da nan hawaye suka wanke mata fuska. Ba zato ta ji hannun Ummanta a kan ƙafafunta.

  "Haulatu, tashi zaune mu yi magana."


Ta share hawayen gudun kar Umman ta gani sai dai tuni ta makara, zama ta yi jikinta duk a mace ta ƙurawa ledar ɗakin idanu wanda duk ya cinye ana ganin ƙasar dake a ƙasa. 


"Tun da yamma da na shigo gidan nan na fuskanci akwai abin da ke damunki amma ƙoƙarin nunamin kike babu komai. Kina da wacce ta fi ni ne?"


Ta girgiza kai, kukan da ta ke dannewa a ƙirjinta kawai ta saki gami da faɗawa jikin Umma. Ba ta hana ta ba, sai da ta yi mai isarta ta yi shiru kafin Umma ta ɗago kanta. Cikin murya ta rauni irin na Uwa ta ce.


"Faɗamin meke faruwa?"


Ta labarta mata yanda Hindatu ta yi mata ɓoyon sabon saurayinta har tsawon sati biyu, da kuma nunawa Umma abu ne da ba su yiwa juna. Ita komai da ya dangance ta Hindatun ta sani. Ta ƙara da faɗin.


"Umma na soma zargin ko dai itama tana guduna ne saboda ƙazafin da jama'ar unguwa ke yimin wai nima yar bariki ce zan musu ƙwacen miji ko saurayi idan naga fuska. Ko dai shi ne dalilin da Mominta ba ta taɓa nuna tana kaunar alaƙarmu da ita ba? Umma zuciyata na zafi idan na tuna wai iyayena ba ku da asali. Dagaske ne a bariki ku ka haɗu kamar yanda ake faɗa? Don Allah ki taimaka yau ki fidda ni a duhu."


"Haulatu, kenan dama duk zaman da nayi da ke na baki tarihin aurenmu da mahaifinki bai gamsar da ke kin yarda cewa ni ɗin ba ni da wani aibu ba? Ban fadamaki ban san inda mahaifiyata take ba? Duk bayanan da nayi maki bai gamsar da ke ba?" Umman ta yi maganar cikin nuna dakiya a zahiri, amma can ƙasan ranta ita kaɗai ta san baƙin cikin dake dunƙule a ciki. 


Ta ƙara duban mahaifiyarta fuska cike da rauni ta ce. 


"Ai ban ce ƙarya kike yi ba Umma, kawai dai so nake na ƙara sanin wani labarin dangane da rayuwarki. Yanzu ace ko sunan dangin mahaifiyarki, babanki bai taɓa sanar da ke ba? Anya zan yarda da wannan?"


Ran Umma ya ɓaci da irin kalaman Haulatun. Magana idan ta furta shi gareta kai ka ce da ƙawarta Hindatu ta ke yinsa. 


"Kalmar ƙarya da kika ambata a maganata da ke kuskure ne, kar ki sake ki ƙara gangancin furtawa ga wani ma ba ni ba. Ina jiyemaki yanda kike furta kalamai gatsal ga kowa, don Allah ki yi kokarin koyon magana, duk abin da na hane ki na kuma ci gyaranki a kansa, ki dinga matukar kokari wajen kaucewa maimaici a zancenki na gaba. Kin ji ko?"


Ta gyaɗa kai kawai don ita fa ba ta ga abin zafi ko wani abu da ta furta ba daidai ba cikin maganarta. Ta fi tunanin kodai Umma ba ta son zancen ne ta wayance da cin gyaranta. Sai can kuma ta tsinci muryarta cikin sanyi ta soma magana. 


"A rayuwa sai kin kauda kai kin kima koyi toshe kunne. Ba komai ne mutum zai yi ya dameki ba, kar ki sake ki kasance cikin masu zargi, ki kyautatawa ƙawarki zato tunda ba ki taɓa kama ta da laifi makamancin wannan ba. Kuma mene ne ciki idan ta yi maki ɓoyon samarinta? Komai ne ya zama dole ki sani na rayuwarta? Ko kuwa dole ne ta san komai dangane da ke? To me za ki amfana da shi idan kin san labarin saurayinnata? Ki koyi kauda kai a duk abin da ba'a nemi ki sa baki ciki ba."

Umma ta ɗan numfasa sannan ta ɗora zancen ba tare da ta ba Haulatun damar cewa kanzil ba. 


"So kike na yi ta maimaita maki baƙin tarihina? Mene ba ki sani ba a kaina yanzu? Kin san mahaifina Kalangu shi ne sana'arsa, mahaifiyata kuwa an ce tun ina ƙarama ta maido ni hannunsa ba ta ƙara waiwayata ba. Kauna tsantsa, babu irin wacce ban gani a hannunsa ba, ya yi iyaka kokarinsa na ganin ya tsaremin mutuncina bai bar ni na faɗa hannun ƴan barikin da ke farautana ba koyaushe. Haka na taso ya sanya ni makaranta boko da arabi, ban yi nisan kirki ba iyakata sakandire ya cire ni ya aurar da ni ga Mahaifinki. Abu uku na sani game da mahaifiyata, na farko sunanta Asma'u, na biyu kuwa, ya cemin daga babban gida ta fito, alokacin za'a yi mata auren dole. Ya kuma ce ƴar Katsina ce. Bayan wannan abu ukun, babu abin da zan iya faɗi game da ita. Shi kuma mahai..."


"Ni bana son sanin komai a kansa. Iyaka wannan ya wadace ni." Ta katse mahaifiyarta cikin sauri da jin zafi a kirjinta, a duniya anya akwai wanda ta tsana sama da shi? Kai ba za ta ce ga shi ba. 


Umma murmushi ta yi mai ciwo, sai dai ta kasa cewa komai. Ta tabbatar muddin za ta nunawa Haulatun hoton da ta ke ɓoyo shekara da shekaru wanda Babanta Mai Kalangu ya ba ta sadda yake kwance cikin ciwon ajali, to fa a taurin kai irin nata, za ta iya bazama ta ce za ta Katsina nemo mata asalinta idan ya so komai zai faru ya faru. Tun a baya ta yi niyyar ta nunamata hoton wanda a bayansa hatta da cikakken sunan Asma'un akwai da na mahaifinta wanda ba ɓoyayye ba ne har a yanzun ma koda ace ba ya raye, sai dai yanda ta kula da zafin ƙiyayyar yarinyar akan Uban nata sai ta fasa. Ita kuma a ranta ta riga da ta ƙullaci mahaifiyarta Asma'u da har za ta iya yin watsi da lamarinta har haka, ta tafi ta bar ta a bariki saboda kawai son zuciya irin nata. Ba ta taɓa muradin zuwa inda take ba har a yanzu da take jin zai wahala ace tana nan a raye ciki duniyarnan. Wasu lokutan takan fiddo hoton ta zubamata idanu idan Haulatun ba ta gida, ta yi hawayen ta share sannan ta mayar ma'adani, har ma ta tsinci kanta da sanya ta cikin addu'a. Babu yanda ta iya tunda wannan na daga cikin haƙƙin iyaye akan yaransu. Ba ta fasa yi ba. 


Yanda uwar ta zurfafa cikin tunani, hakanan Haulatun ke fidda hawaye tana tunanin baƙaƙen ɗabi'un mutumin da ya kasance uba a gareta. Bugun gidan da ake yi ne kamar za'a ɓalle ƙyauren shi ya fargar da su. Eani guntun tsaki Haulatu ta ja gami da komai katifarta ta runtse idanu tana jin wani raɗaɗi a kirjinta, bugun da yake yiwa gidan ji take inama za ta iya zuwa ta ɗauki mataki a kai, sai dai inaa, ta san hakan ba mai yiwuwa bane. Tana jin fitar Umma daga ɗakin ta ƙara jan zani ta rufe fuskarta. 


***

Ya dube ta sama har ƙasa, ta kauce ya shigo ta rufe gidan. Shigewa ya yi bai ce mata komai ba ɗauke da ƙullin baƙar leda a hannunsa ko sannu da zuwan da ta yi bai amsa ba. Ba wannan ne farau ba. Ita dai duk sadda ya shigo ba a buge ba ta sani akwai dalili babba. Har za ta koma ɗaki ya dakatar da ita.


"Ke, ki zo ina son ganinki."


Umma ta ji zafin kalaman sosai, ta tabbatar ɗiyarta sai ta ji. Juyowa ta yi ta amsa. 


"Ina zuwa."


"Kina zuwa? Har in ce maki ki zo ki cemin kina zuwa Na'ima? To ban baki iznin shiga ɗakin nan ba, ki zo ki shige yanzu." Ya faɗi cike da jin isa. Dama tun can Ibrahim Ɗan Mutuwa bai iya wani abu wai lallaɓa ta ba, ta ga dai yana yiwa ƴan barikinsa hakan don kafin ta haihu har gidan yake kawo su, idan ta yi magana ta sha jibga.


Zuciyarta zafi take yi sosai, wai ace mutum ba ya tashi tunawa da kai sai idan ya ga dama? Ko kuma ya nemi ƴan barikinsa ya rasa? A cikin rayuwar aurensu babu abin da ta fi gujewa kamar haɗa shimfiɗa da shi. Ba za ta iya zama ya goga mata cutar da za ta nakasta mata rayuwa ba. Ta gwammace sai dai su yi wacce za su yi. Har ga Allah ta san babu kyau juyawa miji baya, amma fa ita kam miji irin na...


Tunaninta bai kai aya ba ta ji an haɗe kanta da ƙyauren ɗakin ji ka ke kau! Ta bugu a goshi. Sam ba ta ji tahowarsa ba hakan yasa abin ya zo mata bagatatan.


"Don ubanki mai kalangu ni nake maki magana kina ji kika mai da ni wani banza? Ai ko sadda na ci zamanina Ubanki ma bai isa na yi magana ya ji ya yimin kunnen uwar shegu ba ballantana kuma ke da kanki!"


Idanunta a runtse cikin jin zafi da raɗaɗin maganganunsa. 


"Ka daina zagin ubana, na faɗamaka ba ya min dadi."


Ta furta cikin dakiya, ya kuwa kai mata bugu a baya, hakan bai masa ba sai da ya zaro belt.


"Ni kike gayawa na bar zagin Ubanki? To yau kuwa za ki ci uban naki Na'ima! Kuma ki kwana da shiri don aure zan ƙaro naga uwar uban da zai hana ni! Wato na taimaka Ubanki na rufamasa asiri na karɓi sadakar da ya bani shi ne yau ki ke nunamin ni Ibrahim ban isa na kiraki ɗakina ki zo ba ko?"


Bai jira amsarta ba ya ɗaga belt ya shiga lafta mata, ihun ma ta kasa yi wannan karon yayinda idanun suka bushe ta kasa fidda ruwa hawayen. 


Haulatu dake kwance a ɗaki tana jin komai, zuciyarta na wani irin suya, jikinta ya ɗauki rawa saboda tsananin ɓacin rai. Wani irin kaɗawa idanunta suka yi. Tana ji ana laftawa Mahaifiyarta belt akan abin da ba ta ɗauke shi laifi ba, ba ta san lokacin da ta miƙe daga katifarta ba kamar yanda ba ta san ya aka yi sai tsintar kanta ta yi a waje, Umma har ta kai ƙasa tsabar duka, yana yi yana zubamata ruwan ashariya da gori har da kiranta shegiya marar asali. Caraf ya ji an riƙe belt ɗin, ya juya yana duban ɗiyartasa wacce hasken farin wata ya haske masa fuskarta. Ya rasa dalilin da yasa tun sadda ta yi mishi barazanar tona masa asiri yake ɗan jin shakkar yarinyar. Sai dai ai sunansa Ibrahim Ɗan Mutuwa, ba zai taɓa bari abin da ya haifa ya gagareshi ba a cewarsa don haka ya ƙara tamke fuska yana kallonta. Kafin ya samu abin fadi, Umma tuni ta mike ta riƙo ta. Cikin rawar murya take faɗin. 


"Ke, me ya fito dake? Me ya tashe ki? Sakar masa, na ce ki sakar masa mu je ciki!"


Magana ta ke yi amma ina! Haulatu ko gezau, har lokacin jikinta babu inda baya rawa, hawayen kuwa zubowa suke yi kawai saman fuskarta. Kallon Uban take ido cikin ido, jira take ya ce tak! Ta maida masa mai zafi. 


Umma kuwa hankalinta ya yi masifar tashi, ba za ta so abin da Haulatun ke yawan faɗi ya tabbata ba a yau. Shakka babu za ta yi kaico na gazawa da ba ɗiyarta ingantacciyar tarbiyya, kawai sai ta shiga jerawa Allahu kirari a ƙasan ranta. Ta zuba idanu tana kallonsu duka har lokacin ba ta saki Haulatu ba.***

Nan na kawo ƙarshen na free,  ga duk wacce ta shirya biya na a lahira, ta fitarmin da labarina.

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: "Sakar min." Ɗan mutuwa ya furta bayan ya tattaro jarumtarsa. Sai a sannan ta samu zarafin magana, tana yi tana jijjiga hannunta haɗi da nasa dake riƙe da belt ɗin.


"Idan na ƙi fa? Cigaba da dukan uwata za ka yi a kan idanuna? Daga inda ka tsaya nan za ka ɗora? Kai Iro! Bar ganin wai ina maka shiru ina kyaleka  ka na kai hannu jikin Mahaifiyata ka yi tsammanin ko tsoronka ne ya sa, ka yi kaɗan! Nace ka yi kaɗan na tsorace ka! Waye kai? Me ka taɓa yi mana a rayuwa? Shi babanta da ka raina har ka ke zagarmata shi, ka fi shi ne?! Ai gwara shi na tabbata bai kafa wannan mummunan tarihin da ka ke kafawa a yanzu ba kuma ko ba komai ta hanyar aure ya haifar maka ita. To ina maka rantsuwa! Daga yau, yanzu, duk sadda ka ƙara gigin kai hannu jikin Umma ka rubuta ka ajiye sai na yi shari'a da kai! Sai na fallasa dukkan sirrinka! Kai ni ba ka cika namiji ba idan a wannan daren ba ka tsinke igiyar aurenka da Umma ba! Har ka na mata barazana da za ka yi aure? Aurenka ɗin wofi! Ai ba ka daga cikin salihan mazan da aurensu zai girgiza zuƙatan mata! Da Umma ta cigaba da rayuwa da kai wallahi ni Haulatu na gwammace ta rayu da mahaukaci!"


"Haulatu! Rufemin baki! Mahaifinki kike jifa da waɗannan baƙaƙen kalaman?" 


Ta runtse idanu ta ture hannun Umma daga kafaɗunta bayan ta saki belt ɗin, murya a ɗage yanda maƙwafta na kusa duk za su iya ji ta ce. 


"Ni ki daina kiransa mahaifina! Mai irin halinsa bai haife ni ba! Wallahi gwara na kira mahaukaci Ubana da dai na ba Ɗan Mutuwa wannan matsayin! A kansa kina ji kina gani ana kiranmu ƴan bariki, ana yi min kallon karuwa mai ƙwacen miji! Ana yi maki kallon marar asali mai fakewa da siyar da abinci tana aikata masha'a! A dalilin wannan (ta nuna shi da yatsa), na rasa dukkan wani gata! Ki faɗamin nauyina ɗaya da ya taɓa ɗauka tun faɗowa ta duniya?! Umma ki faɗamin ko Ibrahim ya taɓa taimaka ma ki da kuɗin siyan magani idan cuta ta kwantar da ni? Ba zan taɓa kiran wanda ya yi yunƙurin ya kashe ni tun ina cikin ciki da sunan Uba kuma mahaifina ba! Gwara min kare a..."


Wani wawan mari Umma ta kai mata, maimakon hakan ya kashe bakinta sai ma ta riƙo hannayen Uwar ta ɗora saman wuyanta, da muryarta da ta dusashe tsabar kuka da ɗaga murya ta ce "Ki kashe ni! Don Allah Umma yau ki kashe ni. Na rantse na yafemaki har a gaban Mahaliccinmu. Amma don Allah ki kashe ni, na gaji da rayuwar nan Umma. Na gaji da kallon bariki da ake yimin. Wayyo Allahna!"


Sai kawai ta durƙushe sakamakon wani abu da ta ji kamar ya tokare ƙirjinta, numfashinta na kai kawo, tun tana jin muryar Umma na faman kiran sunanta da ƙarfi har gani da jin nata suka yi ɗif.


Umma ta tarairayo ta zuwa jikinta tana mai jijjiga ta gami da salati. 


Shi kuwa Gogan kamar wanda aka daskarar a wurin, shi dai Ibrahim Ɗan Mutuwa ake zazzagawa rashin mutunci ya kasa kataɓus? Dama akwai wannan ranar a tafe? Babban tashin hankalinsa dare ne, kuma yana da tabbacin makwaftansu sun ji komai. Ai kuwa bai kai ga gama tunaninsa ba ya ji ana bubbuga ƙofar gidan da ƙarfi. Ya san kururuwar da Na'ima ke faman yi na neman agaji ya yi sanadiyyar hakan. Da sauri ya shige ɗakinsa ya rufe, takaici da baƙin ciki suka lulluɓe shi. Wai har akwai ɗiyar da za ta kalli tsabar idanunsa ta zage shi tas ya kasa ɗaukar mataki? Ƴar ma ta cikinsa? Ya furzar da iska ta hanci da baka kafin ya yi kwafa na tunanin matakin da zai ɗauka kan Haulatun.  Ya kasa kunne jin da ya yi Na'ima ta buɗe ƙofar gidan. 


Makwaftansu maza su biyu sai kuwa matasan samari su ma duk ƴan unguwa sai ko mata da ba ta iya tantance ko su waye ba. Wannan ne karon farko a tsawon shekarun da ta yi a unguwar da ta ga fuskar wasu a gidanta masu suffar kamala. 


"Na'ima, lafiya kuwa? Meke faruwa da Haulatun?"


Faɗin wata mata kakkaura tana ɗaga tocilar da ke hannunta da zummar hasko inda Haulatun ke kwance. Umma ta ji kuka ya ƙwace mata, cikin tashin hankali ta mata nuni da ɗiyarta.


"Don Allah da soyayyarku da Ma'aiki (s.a.w) ku taimakamin kada na rasa ƴa ta."


Ganin haka yasa suka danna kai ciki, nan da nan mata aka haɗa ƙarfi aka ɗaga Haulatu, wasu kuwa cikin tawagar da gulma ce ta kawo su, gidan suke haskawa su na ƙaremasa kallo. Hatta da belt ɗin Ɗan Mutuwa dake yashe a ƙas sai da suka gani. Nan da nan aka fice da Haulatu, Umma dakyar ta samu nutsuwar ɗauko hijabin wanda garin sauri ma na Haulatun ne ta zura sai takalmi ƙafa daban-daban ta mara musu baya.


Ƙa'idar lokaci na masu ɗan sahun tuni ya wuce hakan ta sanya cikin gaggawa wani magidanci da gidansa ke kallon na su Haulatun ya fiddo motarsa aka hau. Daga Umman sai mata biyu sai ko mai motar da wani a gefensa.


Nan fa wadanda suka yi saura a wurin suka hau maida zance, wasu na fadin ko dai cikin shege ta yi, wasu kuwa kira suke watakila ma shaye-shayenta ta yi har ta sha ya fi ƙarfin garkuwar jikinta. Maƙwaftan da suka fi kusa da su ne suka hau ba da labarin abubuwan da suka tsinci Haulatun tana faɗi. Wasu da yawa sun ji tausayi ya tsirga musu, hakan har ya zama sanadiyyar wanke Haulatu da Umman a zuƙatansu, yayinda ƙalilan ke ganin ai dama tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka kuma kowa ya siya rariya ya san za ta zubda ruwa, da ace mahaifiyarta ba ta biyewa kwaɗayi da burika ba tun farko har ya kai ta ga auren mutum irin Ibrahim Ɗan Mutuwa ba, da yanzun wani labarin ake ba wannan ba. Haka dai suka yi ta tufka da warwara kafin daga bisani kowa ya watse. 


***

Alhamdulillah, cikin ikon Allah bayan likitoci sun yi iyaka ƙoƙarinsu aka samu Haulatu ta farfaɗo. Bisa shawarar likitan, ya ce a daure a daina bari tana shiga damuwa mai ƙarfi irin wannan da ya janyo ta yi doguwar suma, irin wannan yanayin zai iya jawomata hawan jini da kuma ciwon ƙirji. Ƙarshe ya yi mata allurar samun bacci don ko da ta farka maganar ɗaya ce ta ke maimaita "Wayyo Umma, duniyar ta ishe ni. Ku bar ni na mutu."


A dole don samun nutsuwarta ya yi mata, ya kuma roƙi duk a fita a ƙyale ta da mutum ɗaya mai jinyar. 


Duka aka fito har Umman da ta yo musu rakiya. Tana ta zubamusu godiya ga hawayenta ya ƙi tsayawa, duk su ne suka ɗauki nauyin asibitin, daga mai siyan magani sai mai biyan kuɗin gado.


"Haba kar ki damu, kawai ayi fatan samun sauƙinta. A kuma kiyaye abin da likita ya ce. Allah ya sawaƙe ya ba ta lafiya."


Cewar motar da ake kira Alhaji Shu'aibu Mijinyawa. Ɗayan kuwa Malam Bukar ake kiransa sai mai ɗan jikin Hasiya, ita ce matarsa da kuma bazawarar ƙanwarsa Murjanatu. Haka ta yi ta zuba musu godiya daga ƙarshe suka ce ta koma wurin Haulatu kar a bar ta ita daya. Da wannan ta juya su kuma suka tafi. 


A motar ma sai jimami da tausayi suke yi, nan mazan suka yi ta tattaunawa ta yanda aka yiwa gidan gaba ɗaya mummunan shaida. Sun kuma fahimci sosai Uwa da yarinyar na buƙatar taimako, ga dukkan alamu ba su jin dadin zama da uban. Haka dai har suka isa gida lokacin ma asubahi ta gabato. 


***

Umma har ta yi sallar asuba ba ta iya ta rintsa ba, idanunta a bushe sai ciwon kai, ciwon jiki kuwa dama ta saba da shi. Hannunta duk ya yi ja saboda duka. Ga shatin belt kwance. Yanzu tunaninta bai wuce makomar rayuwar ɗiyarta ba. Shakka babu ta tsorata da Haulatun da ta gani a jiya da daddare, tana kuma da tabbacin tarbiyyar yarinyar na dab da samun matsala muddin za ta cigaba da ganin waɗannan munanan ɗabi'u na mahaifinta. Ta san zai wahala ya fasa dukkan abin da ya yi niyya, wannan na daga dalilin da yasa tun a baya mutane ke kiransa da Ɗan Mutuwa. Shi fa ko za'a mutu baruwansa, inda ya sa gaba sai ya ga ƙarshensu abun kafin ya haƙura. Anya lokaci bai yi ba da za ta fice a rayuwarsa su gina tasu rayuwar a wuri na daban? 


'Ba kya tsoron a cewa ɗiyarki ƴar mace? Kuma ina za ku je?'


Wadannan tambayoyin a koyaushe idan za ta yi tunanin rabuwa da Ibrahim, su na cikin dalilin da dole take haƙura ta fasa. Ta zurfafa cikin tunani a gefe guda kuma bakinta na motsi tana tasbihi sai jin motsin Haulatu ta yi, cikin sauri ta miƙe ta nufi gadon. Haulatun ta dubi ɗakin da ta ke kafin ta maida duba ga Umma wacce ta riƙe mata hannu. Ɗan murmushin da bai kai zuci ba ta sakarmata, itama Umman ta maida mata martani. 


"Alhamdulillah, kin farka? Sannu, bari na kira likita."


Da idanu kawai take bin Umma har ta fice daga ɗakin, can suka dawo tare har da wata Nos. Ya tambaye ta ko akwai inda ke mata ciwo, ta girgiza kai, ya gama gwaje-gwajensa kafin ya kalli Umma.


"Masha Allah, komai na ta lafiya lau yake. Anjima zan sa a sallame ku. Yanzu tana buƙatar ta ɗan ƙara hutawa amma a samu ta sa wani abu a cikinta sai ta sha magani."


Umma ta amsa da toh, ita duk sai yanzu ma ta tuna da wai ana cin abinci, yanzu haka za ta bar ta ita ɗaya ta koma gida ko ya ya?


Cikin taimako na Allah, ba ta kai ga gama tantance abin yi ba, suka ji ana buga ƙofar ɗakin, bayan Likitan ya bada iznin a shigo, sai ga matar Alhaji Shu'aibu, Hajiya Mabruka tare da Mama Hasiya (kamar yanda yan unguwa ke kiranta), sai ko wata budurwa da ba ta fi sa'ar Haulatun ba riƙe da kwandon abinci. A bayansu kuwa wani ɗan matashi ne wanda zai girme wa Haulatun da kaɗan hannunsa riƙe da filas na shayi. 


Suka gaisa da Likita sannan ya fice tare da Nos. Cike da girmamawa Umma ta gaishe su fuskarnan a sake. Zuciyarta kuwa tamkar an mata albishir da gidan aljanna, wai yau ita ce tare da makwaftanta haka a lokacin da ta ke cikin tsananin buƙatar wani a kusa? Nan aka zauna, ita dai Haulatu kallonsu kawai take. Ta kai duba ga budurwar mai suna Bahijja wacce ba baƙuwa ce a wurinta ba don islamiyyarsu guda kuma ajinsu ma haka, sai dai kawai babu mai shiga shirginta, asalima ƴan cikin su Bahijja sun fi kowa tsanarta kai ka ce wata sabuwar tuba ce a cikinsu. A bakinsu ta soma jin ana mata ƙazafin ƙwacen saurayi ko miji. Ta kauda kai daga gareta zuciyarta na zafi, lumshe idanu ta yi yayinda take sauraron Umma na yi musu bayanin da likita ya yi. Babu wanda ta kula cikinsu sai amsa sannun da ake yi mata ta hanyar gyaɗa kai. Mama Hasiya ce ta taimaka mata ta miƙe bayan fitar saurayin siyo brush da toothpaste, ta shiga bandaki ta yi tsarki da alwala. Can ya dawo ya miƙawa Bahijja sannan ya fita, ita kuwa ta kwankwasa ƙofar bandakin, Haulatu ta leƙo ta karɓa fuskarnan babu ɗigon walwala asalima kallon fuskar Bahijjar ba ta ƙaunar yi. Ai har da ita cikin masu yi mata mugun ƙazafi. Bahijja kuwa duk jikinta ya yi sanyi musamman a hanya da Mama Hasiya ta ba su labarin duk abin da ya afku a daren har sadda suka ji kururuwar Umma. Wani irin tausayin Haulatun take ji yana tsirga mata. 


  Sai da ta yi sallah, aka zuba mata ruwan shayi ta soma sha kafin su yi musu sallama su tafi domin duk yanda Mama Hasiya ta so Umma ta koma gida ta kimtsa ta dawo ta nuna ita sam ba za ta iya motsawa ba. Sun sha godiya sosai, Hajiya Mabruka har kudi ta ba su saƙo daga maigidanta. 


Wuraren biyar na yammacin ranar aka ba su sallama, ɗan sahu suka shiga zuwa gida. A hanya Haulatu sai tunani, Umma abin har ya soma ba ta tsoro don tun da ta farfaɗo ta ƙi yin wata maganar arziki ga kowa. Daga um sai um um sai kuwa murmushi mai kama da yaƙe sai gyaɗa kai. 


***

 Ina labarin Ɗan Mutuwa?

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Tun bayan fitarsu ya ke ta muzurai shi ɗaya a ɗaki. Ya san dai ko mutuwa yarinyar tayi, Na'ima ba za ta ɗagamasa ƙafa ba. Koda dai ya kula itama ta samu bakin yi mishi musu yanzu idan ya yi magana. Fitowa ya yi a ɗakin bayan ya kwashi abin da zai buƙata don ya rantse idan ya bar gidan ba zai dawo ba sai bayan kwana biyu. Ƙunshin nama da gurasar ya shigo da shi a daren ko kallonsa bai ba, sai da ya ji unguwar ta yi shiru shaidar kowa ya shige gida ya fito ya miƙi hanya. Bai zarce ko'ina ba sai gida Hajiya Adama Loma.

  

Gida ne da ba ya rabo da mutane safe da dare, babu ma kamar da daddaren. Yana ɗaya daga cikin manyan gidaje a unguwar, babu ruwan wani da wani musamman da ya kasance wurin yawanci baƙi ne, wasu ƴan Lebanon ne, sai ko ƴan China da Hausawanmu waɗanda boko ya ratsa.  Kowa harkar gabansa yake yi babu takura. 

Itama Hajiya Adama ta mallaki gidan ne da maƙudan kuɗaɗen da ta ci gadonsu daga tsohon mijinta da ya kasancewa Balarabe ɗan Libya, bayan rasuwarsa ne ta ci gadon gidan, ta kuma zama Hajiyar kanta don jifa-jifa gidan ba ya rabo da gyare-gyare wadanda yawanci duka manyan Alhazawan da take cuɗanya da su ke yi mata kyautuka na bajinta. Ga uwa uba tana buga kasuwancinta na siyar da duk wani abin ado na jiki da ma na amfani na mata. Katafaren shago ta mallaka a wuraren Unguwar da ta ke wato Nassarawa GRA. Kadarorin da ta tara shi ya zama rufin asiri na asalin sana'ar da ta ke yi a ɓoye. 

  Ibrahim Ɗanmutuwa yana cikin mutanen da ba'a yi musu shamaki da shiga ko'ina a gidan na Hajiyar, sun yiwa junansu farin sani tun ma duniya na kwance. Kusan shekarunsu ɗaya a bariki, asalima shi ya kasance kamar wani abokin shawararta tun a baya. Uwa uba da shawararsa aka kashe mijinta ta sigar da ba kowa zai fahimta ba. Sosai ta ba shi nasa kason a baya sai dai kuma kuɗaɗe a hannun Ɗanmutuwa sam ba su zama. Haka ya dinga kashewa ƙadangarun bariki ba tare da ya amfanawa kansa ko matarsa da komai ba. 

   Haka ya nausa ciki har babban falon Hajiya Adama bayan Maigadi ya buɗe masa ƙofa. Ƴanmata ne da ba su fi shekaru sha biyar zuwa sama ashirin ba, su huɗu kwance ba su san ma inda kansu yake ba, kallon da ya yiwa kwalaben da ke wurin ya fahimci mankas suka yi. Kai tsaye ɗakin da yake yawan sauka idan ya zo nan kawai ya zarce sai dai ya ji a rufe gam! Koda ya ɗan kara kunne ya ji ana jan munshari ya ja guntun tsaki. Dole falon ya koma ya ajiye jakarsa gami da fiddo sigari ya kunna ya soma zuƙa, kansa gaba ɗaya tururi yake, shi fa har a sannan mamakin wannan ɗanyen aikin da ƴar cikinsa ta yi mishi yake. Wato don uwarta don ta samu ya bar ta tana shaƙar iskar duniya bai hallakata ba tun tana jaririya shi ne har ta ke da ƙarfin cin zarafinsa. Ya yi ƙwafa, haka ya tashi da kara uku na sigari kafin ya kora da ruwan codein ya sheme a saman three-seater na gidan babu ko damuwa akan sallah. (Wa'iyazubillah).


***

Tana zaune a bakin ƙofar ɗakinsu ta yi shiru, daga ita sai vest da zani kan babu ko dankwali, gashinta baƙiƙirin marar tsawo sai cika tufke da ribbon, gefe guda ta ƙurawa idanu tana sauraron shirin da ake yi a gidan rediyo dake magana akan tarbiyya. Wanda Malamin ke nuni da muhimmancin tarbiyya da kuma haƙƙin yara akan iyayensu. Shirin ya sa ta shiga fidda ruwan hawaye, ƙarshe kuma ta ɓige da kuka sosai. Cikin wannan yanayin ta ji ana ɗan bugun ƙofar gidan. Ta sani Umma ba ta jima da fita zuwa sana'arta ba hakan ya ɗan ba ta mamaki. Ta kashe rediyon sannan ta goge fuskarta. Miƙewa ta yi har ta kama hanyar ƙofar sai kuma ta dawo da baya ta ja hijabin Umma dake saman igiya ta zura. 


"Ana zuwa." Ta furta cikin shaƙaƙƙiyar murya. Wacce ta gani kwarai ta yi mamaki, Bahijja. Za ta iya cewa tun soma wayonta ita kam ba ta taɓa ganin ƙeyar mutum ɗaya a  ƴan gidansu ya shigo ba. Tare suke da ƙanwarta Nasiba, ta yi fuskokinsu farin sani tunda islamiyya guda suke. 

  "Ko mu juya?" Faɗin Bahijja cikin zolaya tana ɗan murmushi. Itama sai ta tsinci kanta da maida mata martanin murmushin kafin ta shige ciki ta yi mata iznin ta shigo. Bahijja na gaba riƙe da kwando sai Nasiba biye da ita ɗauke da wata baƙar leda mai ɗan girma, tsayawa ta yi tana bin tsakar gidan da kallo. Ba wani babba ba ne, ɗakuna biyu ne sai kuwa wani gefe da ta ke zaton nan ne kicin sai ƙofar banɗaki daga ɗan lungu. Haka ta yi ta nazarinta har Haulatu ta shimfiɗa musu tabarma. 


"Wai dama tabarma ki ka shiga ɗaukowa? Wallahi sauri ma muke zamu je islamiyya ne, dama Mama ce ta aiko mu, tana maki sannu. Ga wannan kuma ta ce a kawo."


"Lallai, wato kin fi ƙarfin ki zauna a tabarmar gidanmu ko? Ai shikenan. Ki ce mata da sauki, an gode."


Riƙe baki Bahijja ta yi.


"Kai Haulatu, ni ba haka nake nufi ba don Allah kar ki fassara ni. Ai ke kin sani na shiga ajin ƴan hadda. Kiyi hakuri, ai yanzu muka soma aminci, na tabbata sai kin gaji da gani na a gidanku."


Haulatu ta ɗan taɓe baki.


"Ni dai mai ƙwacen samari?"


Maganar ba ta yiwa Bahijja dadi ba, cikin sanyi ta amsa.


"Kiyi hakuri, ki yafe min duk abin da na furta mai muni gareki a baya. Rashin sani ne da kuma jita-jitar mutane. Amma ina tabbatar maki yanzu na fahimceki."


Murmushi kawai Haulatun ta yi, ai ita ta sani babu wani mai fahimtar ta bayan uwar da ta haife ta. Kawai dai ta bi ta da to, haka suka rabu ta taka musu har bakin ƙofa tana ƙara jaddada saƙon godiya ga Mamarsu.


Abinci ne lafiyayye, shinkafa dafaduka a wata cooler ɗin kuwa farfesun kaza ne. Sai leda mai ɗauke da sabulai na wanka da kuma wanki sai kuwa omo. Kai har da auduga na mata leda biyar da mayuka har kala biyu na shafawa. Shiru ta yi tana kallon kayan, karon farko da irin wannan abin arziƙin ya haɗa su da makwaftansu. Haka ta mayar da komai cikin ledar, ta ajiye su a gefe. Ba ta tare da yunwa don haka  ko sha'awar abincin ba ta yi ba. Ta gaji da zaman tunani ta ja guntun tsaki ta miƙe, gaba ɗaya zaman gidan ba dadi yake yi mata ba ta ji inama ta bi Umma zuwa kasuwa, ƙarshe kawai sai ta ƙara zura hijabin da ta cire ta fito ƙofar gidan ta ɗan tsaya. Yana ɗaya daga cikin abin da Umman ba ta sonta da shi sai dai tana ji hakan kaɗai ta fi buƙata a yanayin da zuciyarta ke ciki. Hankalinta ya kai ga su Maada waɗanda suka ɗan kalli inda take. Ta kauda kai gami da ƙara tamke fuska. Ta rantse wataran sai ta sa ƴan sanda sun kawomusu cafka muddin ba za su daina zama a ƙofar gidansu ba. Ta tsinkayi muryar wani cikinsu mai suna Kwarkwar ya buga wani ihu na ƙwararrun ƴan daba kafin ya ce.


"Kai! Ni fa barewar can tana kashe ni billahillazi! Oga Maada! Ya kamata idan Ciyaman ba zai iya farautarta ba mu, ya bari mu shiga da ƙwarinmu."


Maada ya ja tsaki yana fesar da hayaƙin sigarin da ya zuƙa.


"Kai don tsohuwarka ina tambayarka inda Ɗan Aljan ya shiga kana yimin maganar banza da wofi. Ai inda amana ruwa ba zai dafa kifi ba, duk runtsi kar wanda ya ƙara kai idanunsa ga irin gidan Boss."


Kwarkwar da sauran mutane ukun da ke zaune tare da shi, suka harɗe hannuwansu suna kirarin kowa ya bi. Can kuma Kwarkwar ya ce.


"Nifa Oga ban dan inda Ɗan Aljan ya yi ba, na fi tunanin ya haɗu da Kashi (ƴan sanda) sun sa mishi lalle (sun kama shi).  Kasan fa shi Boss ya aika gidan Cuna ya kai tayoyi! To ka san halinsa, ya fiye Nakura (tsoro), ƙila ya yi saranda." Ya ƙarashe yana mai ƙamewa kamar wanda ke gaban soja. 


"Aikuwa da matsala. Amma ina zuwa bari na sallami waccan ƙaguwar." Faɗin Maada, Haulatu ta saci kallonsa ta gefen idanu, can kuma ta kai duba ga inda ya nufa, wata budurwa ta gani daga can kan kwana ta rufe fuskarta da niƙab. Waige-waige ya yi kafin ta ga ya sa hannu cikin aljihu ya fiddo wani abu da ba ta iya tantance ko mene ne ba, ita kuwa ta karɓa da sauri ta cusa a jaka ta fiddo kudi ta miƙamasa daga haka ta bar layin da sauri. Shi kuwa ya dawo ya zauna suka bi shi da sowa. Iya Haulatu mamaki ma abin ya ba ta, ba su ko tsoron ta tona asirinsu? 

  

  'Tsoron me za su ji tunda dai halinsu guda da mijin Ummanki?' Wani sashi na zuciyarta ya ba ta amsa. 

  Hirarsu ta ƙara ɗaukar hankalinta, magana suke yi akan budurwar. Maada ke labartamusu cewa ai yau taro ne da su na birthday hakan ya sa zasu gwangwaje. 


Ganin tun tana fahimtar kan hirar har ta bari ga wani jiri da ta ke ji sakamakon jimawar da ta yi a tsaye yasa dole ta juya ta shige gida gami da zura sakata. 


Yinin ranar sam bai yiwa Haulatu dadi ba, har Umma ta dawo ba ta da wani walwala. Sosai Umma ta yaba da karamcin Maman Bahijja. Sai da aka yi Magriba suka ci suka ƙoshi, tana da lura da Haulatun. Anan take sanar da ita kiran da Hindatu ta dinga yi a wayar Umman tana nemanta. Yamutsa fuska kawai Haulatu ta yi, ita fa mamakin Hindatu take har lokacin, ta kuma ci alwashin sai ta nunamata rashin jin dadinta a fili. 


Umma na so ta tambayi ɗiyar ko Mahaifinta ya shigo gidan, sai dai ba ta kaunar ta tayarmata da abin da ya wuce. Yau kwana biyu da faruwar al'amarin kuma tun sannan ba su ƙara ganinsa ba a gidan. Ga diyar, hakan ya fi nono fari har addu'a ta ke yi a ranta akan Allah ya sa mota ce ta kaɗa shi ya mutu. Ga Uwar kuwa, duk ta damu. Zuciyarta na mata ba dadi, ko ba komai uban ƴarta ne. 

  A ranar ma har suka kwanta bacci babu labarinsa, tun Haulatu na jin Umma na juyi da sintirin fita tsakar gida, har dai bacci ya yi awon gaba da ita. 


***

  Hajiya Adama, mace ce mai jiki sosai, tana zaune a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falonta. Ta ci ado har ta gaji kamar koyaushe don tana saka ran tarbar manyan Alhazai da za su zo zaɓar iri daga cikin sabbin ƴanmatan da ta tanada musamman domin su. Daga ita sai Danmutuwa a falon. Shi ne abokin mutuwarta kamar yanda ta ke faɗi "Ɗanmutuwa abokin mutuwata." Haka kirarinsa yake a wurinta. Duk wani sirri nata ya sani kamar yanda ta yi mishi farin sani. Ya labartamata duk abin da ya faru tsakaninsa da Haulatu da Na'ima. 

  Ta yi murmushi yayinda take cigaba da taunar inibin da aka sanyamata cikin wani ɗan bowl na tangaran. Dama ta lura tun zuwansa daga yanda yake ta faman yiwa kansa mankas wata damuwar ce sai dai ba ta ɗauke ta mitsitsiya hakanan ba. 

  

  "Ita Haulatun ba za ka iya kawomin ita mu gaisa ba?"


Shi ne tambayar da ta jefamasa ba tare da nuna wata damuwa akan cin kashin da yarinyar ta masa ba a nasa tunanin. 


Ya yi shiru, sai lokacin ta dube shi dakyau har sannan murmushin bai bar saman fuskarta ba. 

  

  "Ina fatan ka gane inda na dosa?"

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Ɗanmutuwa ya gyara zama bayan kora ruwan lemun da ke ajiye saman tebur a cikinsa. Ya dubi Hajiya Adama.


"Wannan tunanin shi ya yi silar da ki ka ga na zo gareki da zancen. Ai nikam idan har kwalliya ta biya kudin sabulu to ba ni da wata matsala face na cigaba da sheƙa ayata son rai. Sai dai kuma ba nan gizo ke saƙar ba."


"Ban fahimceka ba." 


Ya ɗan dakatar da ita da hannu. 


"Yanzu zan fahimtar da ke. Na'ima mace ce mai haƙuri na sani koda dai haƙurin na dole ne don duk faɗin ƙasarnan ba ta da gatan da ya wuce ni Ɗanmutuwa. Duk ranar da na yi watsi da ita, ina mai tabbatar maki sai kare ya fi ta gata."


Hajiya Adama ta ɗan yamutsa fuska. 


"Ni fa daɗina da kai kenan, inda aka dosa daban, inda ka ke nufa daban. Mene ne haɗin abin da na nema da wannan soki-burutsun?"


Ya yi ɗan murmushi.


"Ai da ba ki katse ni ba, kin fiye ƙawa zuci, dalilin yin maganar Na'ima don na nunamaki ƙarfin ikon da nake da shi a gidana. Duk taurin kai irin na wannan yarinyar ba za ta gagare mu juyawa ba. A shirye nake na kawo maki ita ko ta ƙarfi da yaji ne. Ya rage naki ki san dabarun da za ki yi ta bada kai bori ya hau. Kinga gaba ta kai mu gobarar titi."


Suka yi dariya. 


"Ko kai fa, yanzu ka yi magana mai kyau. Sai dai fanakwai sauran rina a kaba, kana da tabbacin ta cika duk sharuɗɗan da nake nema a wurin ƴan shila kafin ɗora ta kan network?"


Bai ji ko ɗar dangane da tambayar ba sai ma dariya da ya yi karo na biyu.


"Kin manta wace ce uwarta Na'ima ne? Ɗawisu muke kiranta fa. To ai ko ni ba don na ga jiya da yau ba, ba za ki jera ni sahun..."


"To sarkin yabon kai, kar ka sauka daga kan layin da muke kai. Ka kawo min yarinyar kawai."


"An gama Hajjaju."


Da wannan suka ajiye zancen inda suka shiga tattaunawa dangane da abinda ya shafi kasuwancinsu. 


"An sanar da ni an kama yarona ɗaya, Ɗan Aljan, ya kamata a san abin yi kafin lokaci ya ƙure." Faɗin Ɗanmutuwa kenan. Ta duba lokaci a wayarta sannan ta ja guntun tsaki. Sai da ta fara watsi da maganarsa ksfin daga bisani ta dawo kan turba.


"Nifa mutanen nan ba su san bana son saɓa alƙawari ba, mun yi da su ƙarfe uku amma ka ga har huɗu ta gota. Batun Ɗan Aljan ai ba matsala ba ce tunda muna da Kwamishina, ka sani ai dole ya fito. Yanzu fa nima na ƙara samun wata babbar kwastoma ta kaya. Kar ka yi mamaki a cikin garin nan ta ke fa, ita matan aure su ne abokan cinikayyarta. Matar inda ta burgeni duk wata hanya da za ta bi ta shigewa mace ta sani, za ta nunamata wannan hanya ita kaɗai ce ta gusar da damuwa, ya kuma sanya bacci mai dadi da munshari. Nifa Ɗanmutuwa duk inda zan ga masu jarumta da rashin tsoron gudanar da aikin kasuwancinsu burge ni suke yi ba kaɗan ba. Kaga akwai matashiyar da na sanya ta ke kawomin matasa cikin tafiyar, codein sai ya ƙare a ƙasa da minti talatin. A hankali su na sabawa da shi mu kuwa mu dinga ƙara farashi son ranmu."


Ɗanmutuwa ya dara. 


"Ai sosai lamarin na tafiya yadda ake so. Ni fa kinga akwai wani yaro ana ce mishi Prince, ɗa ne ga wani babban Soja, ai idan kina neman hatsabibi ki ka sami ɗan gidan Major Musa Ahmad Gwadabe kin gama. Yana min cinikin sama da dubu dari biyu a wata."


"Amma ba'a gani a jikinka, daɗina da kai ba ka iya tattalin kuɗi ba Ɗanmutuwa. Ka ƙi gina gida balle ka siyawa kanka suturun arziƙi. Ba dole irinsu Mahadi su rainaka ba su na ganinka da Ciyaman? Dubi fa suturar jikinka yadi duk ya koɗe."


Ya yi ƙwafa bayan ya bi jikinnasa da kallo.


"Shege ba, idan akwai wanda na tsana to fa ya biyo bayan mutumin nan. Amma kin yi magana, zan yi ɗinkunan kece raini don kwanan nan ma zan yi aure. Ba zan iya zama da Na'ima kaɗai ba."


Ƴar dariya Hajiya Adama ta yi, kafin ta tanka sai ga sakatariyarta ta gidan ta shigo da sauri. Nan ta ke sanar da ita isowar manyan Alhazawan, hakan yasa suka miƙe.


"A tabbatar yaran can sun kimtsa kinsan ba na kaunar matsala." Ta amsa da toh sannan ta fice. Su kuwa suka nufi waje domin yi musu tarba ta musamman. 


***

Cikin kwanaki uku Haulatu ta wartsake kamar ba ita ba, ta shiga harkokinta na yau da kullum. Ta koma makaranta, koda suka haɗu da Hindatu ko kallonta ba ta yi ba. Maganar duniya Hindatu ta yi amma ta share ta, haka har aka tashi ba ta bada wata fuska ba. Ta kama hanyar tafiya don yau kasuwa za ta leƙa wurin Umma, har ta isa bakin titi tana tsaye ta ji muryar Hindatu a gefenta. 


"Wai Haulatun Umma ni kike yiwa wannan wulaƙancin? Magana ta ƙi ci ta ƙi cinyewa? Matar da har haƙuri na ba ki? Ni wallahi kinsan dai ban iya gaaba ba, don sonki da Allah da Ma'aiki s.a.w ki yi hakuri. Kin ji? Haba Aminiyar kirki."


Sam ba ta ma zaci tana bin ta ba, ba tare da ta kalle ta ba ta amsa.


"Ai komai ya wuce."


"Me kike nufi da ya wuce? Tun a aji kike nanata wannan kalmar, kina nufin kin yanke zumuntarmu ko me?"


Cikin ɗaure fuska Haulatu ta amsa.


"Aa, ai ba duka na yanke ba, da kika shigo ajin ba mun gaisa ba?"


Kai, Hindatu haka ta dinga naci, ƙarshe sai ga ta a cikin ɗan sahu sun kama hanyar kasuwa tare. Haulatu dariya ta taso mata amma ta danne a zuciya, ta fiddo niƙaf ɗinta ta ɗaura gudun kar ta aikata abin da Umma ba ta so. Tun tana share ƙawarta tana mata mitar ba ta sauka ba ta da kudin da za ta biyamata na mota ita kuwa Hindatu na rantsuwa sai ta bi ta sun shirya a gaban Umma har tana fadin.


"Kuma ma ai kasuwar tawa ce tunda ina da miji a cikinsa, kudin mota kema na hutar da ke zan biyamaki."


Duk shariyar da Haulatu ta dinga yi haka ta haƙura ta sauko, kafin su ƙarasa sai hira da dariya kamar ba su ba. Anan Haulatun ke labarta mata ciwon da ta yi ba ta kuma ɓoyemata dalili ba, hatta da ɗasawar da suke yi da Bahijja da ƙawayenta ba ta ɓoyemata ba tunda dama Hindatun ta san da batun Bahijjar. Itama nan ta hau ba ta labarin zuwan Alhajin da kuma yanda ya ruɗe dagaske aurenta zai yi da zarar sun fita daga ajin da suke. A lokacin su na dab da rubuta jarrabawa wanda idan sun ci sun haye gwamnati za ta biyamusu NECO. 

Sosai Haulatu ta taya ta murna, ta kuma bi ta da fatan alheri. Har hotonsa ta nunamata a waya, babba ne ba yaro ba, yana da mata ɗaya da yaransa biyar. A iyaka ra'ayi irin na Haulatu, ko da ace tana da ra'ayin aure ba ta tunanin auren irinsu balle kuma babu auren ma a zuciyarta kwata-kwata. Tsakaninta da samari, sai ɗaure fuska da kallon banza. Duk wanda ya nuna yana sonta to fa taka masa burki take yi. Cikin samarin unguwa dama ba wanda ya taɓa nuna yana sonta a yanda gidansu yake. Sai ko ƴan bana bakwai. 


  Har suka isa kasuwar kwari su na ta hirarrakinsu. Haka suka dinga kutsawa Hindatu na faman mitar ya kamata Umma ta bar zuwa kasuwa tunda tana da suruki ɗan kasuwar yanzu (saurayin Hindatun kenan), ya fi ta dinga sarin kaya itama tana siyarwa yanda Mominta ke yi. Ita dai Haulatu murmushi kawai ta yi. Ba su ƙarasa ga Umman ba sai da Hindatu ta siya facemask ta rufe hanci da bakinta wai kar saurayinta ya hango ta wurin siyar da abinci. 


Umma ta yi mamakin ganin Hindatu.


"Ke kuwa me ya kawoki nan daga makaranta? Kin sanar a gida ne?"


Ƴar dariya ta yi.


"Aa Umma, kar ki damu Momi ba ta gari ta je Katsina kai wasu kaya. Ni kaɗai ce a gidan."


Umma ta jinjina kai ba ta ce komai ba. Abincin ta zubamusu sai da suka ci suka ƙoshi ta ce su tashi su kama hanya har Haulatun ganin wajen ya soma cika da samari. Kuma ga Hindu duk wanda ya tankamusu sai ta ga ta cafe zancen har su na dariya. Ita dai Haulatu ba ta yi wannan karambanin ba don ta sani muddin ta aika to fa za ta ɗanɗana kudarta a wurin Umma, balle ma irin rayuwar ba burge ta take yi ba sam. 


Sun bar wurin Umma sun yi nisa ta dakatar da ita.


"Lafiya?" Faɗin Haulatu. 


"Don Allah muje ki raka ni mu gaisa da Noor. Minti biyar kacal."


Zaro idanu ta yi.


"Lallai ma BigMama, so kike Umma ta yanka ni ashe. Kuma ke yanzu girmanki ne ki bi saurayi har shagonsa? Nikam ba inda zan je. Malama zo mu tafi ko na bar ki anan."


"Kai Haulatu, amma dai kinsan ba ani abin zan yi marar kyau ba ko? Kawai dai mun yi waya da shi ɗazu ai kinga sadda na tashi, ya cemin idan ban shiga mun gaisa ba zamu yi rigima. Taimaka don Allah, ni wallahi ko a bakin shagon ki tsaya muna gaisawa sai mu wuce."


A dole, babu yanda Haulatun ta iya haka suka nufi shagon bayan ta ƙara gyara zaman niƙaf ɗinta. Ta gan shi a zahiri, ita sam ba ta ga abin burgewa a wurin mutumin da Hindatu ta kira da Noor ba, ainahin sunansa Alhaji Badamasi, ta shiga shagon ta zauna suka gaisa. Ta maida hankali ga matan da suka shigo siyayya, tana ji su na hira yana cewa meyasa ƙawarta ta rufe fuskarta, ba ta ce musu uffan ba. Can da ta ga abin ba na ƙare ba ne ta miƙe. Ganin haka tuni Hindatu ta miƙe itama suka yi sallama, ya takomusu har waje ya miƙawa Hindatu kudi har dubu uku su yi kuɗin mota. 


***

Ya shigo gidan yana ɗaure fuska babu ko sallama. Haulatu na zaune tana wanke kayan makarantarta. Umma dake shara ta dube shi, zuciyarta ko ba komai ta yi sanyi. 


"Sannu da zuwa." Ta furta baki na rawa. 


Ita kuwa Haulatu tamke fuska ta yi ba ta ko ƙara kallonsa ba, ɗan waƙen nishadin da ta ke rerawa tuni ta daina. Ƙirjinta zafi ya shiga yi tsabar takaici. Tana kallo ya shige bai ko amsawa Umma ba. Ita kuwa har da sauke ajiyar zuciya fuskarta babu yabo ba fallasa ta cigaba da shara. 


"Ke."


"Na'am." Umma ta amsa da sauri kafin ta shiga ɗakin. Tsabar bakin ciki ya sa Haulatu miƙewa ta bar wankin ta shige ɗaki. 

  

 

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro 

   Page 9

Watanni uku da suka biyo baya, a wajen Haulatu sam ba masu dadi ba ne a rayuwarta cikin gidan, a makaranta kuwa sun zana jarrabawar qualify har kuma cikin ikon Allah tana cikin waɗanda suka yi nasara gwamnati za ta biyamusu kudin NECO. 


Gaba daya rayuwar gidan ba dadi ta ke yi mata ba kuma ba dalilin kowa ba sai mijin Umman da ya zame mata tamkar ƙadangaren bakin tulu. Duk iyakar kokarin da ta ga yana yi a gidan don nuni da lallai ya shiga taitayinsa ya nutsu hakan ba burgeta ya ke ba, tana kuma ƙara ji a jikinta cewar duk wannan abu da yake yi na banza ne kuma akwai lauje cikin naɗi. Sosai take son samarwa Umma hujjar da yasa take kokwanto amma ya toshe dukkan wata ƙofa. Don ta jarraba shi har cewa Umma ta yi, ta nunamasa ba ta son zaman majalisar su Maada a ƙofar gidan. Ta sha mamaki da ya amsa da cewar daga lokacin zamansu ya zo ƙarshe, kuma abin mamaki hakan ce ta tabbata. Har shigowa suka yi gidan suka yi sallama da Umman wani salon bariki da Haulatu ta yiwa abin kallo har da neman gafara. 

    "Madadin ki tsaya ƙoƙarin binciko laifukansa, kamata ya yi ki ƙara godiya ga Allah da ya karɓi addu'armu ya shirya bawansa."


Haka Umman ta taɓa ce mata, a take kuwa ta zabura.


"Wallahi ba dai addu'ata ba. Ni ban taɓa saka mijinki cikin addu'o'ina ba. Toh na tsaya ma na maida hankali ga yiwa kaina addu'ar mana. Hum um!"


Daga haka ta tashi a lokacin don ba ta kaunar a ja magana. Tun sadda kacokam ragamar abincin gidan ya koma hannun Ɗanmutuwa, daga lokacin Haulatu ta bar cin komai da Umman za ta girka. Ta gwammace shiga gidan su Bahijja ta ci ta yi nak, ko kuma ta ci sauran abincin siyarwar Umman. Yanzu sosai suke zumunci da su Bahijja, tare da su take zuwa islamiyya, a dole ma ta ke zuwa don babu yanda za ta yi ta zauna a gidan baƙin cikin mijin Umma ya kashe ta. 


Cikin wannan lokacin ne aka sanya ranar auren Hindatu da ya kama watanni biyar bayan kammala sakandire ɗinsu. Ta shirya daga ita har Umma don zuwa yi musu fatan alheri. Suna tafe su na hira gwanin sha'awa, Umma har ta ɗan murmure kaɗan saboda kwanciyar hankali da nutsuwar da ta samu. Babu abin da ya kai damuwa jefa zuƙata cikin damuwa da takura. Idan ka gan su sai ka rantse Yaya ce da ƙanwarta, sam ba za ka kawo a rai wai Uwa ce da ɗiya ba domin Allah ya halicci Umma da kyawun jiki. Suna tafe su na hira abinsu, Haulatu cikin nishaɗi ta ke jinta da walwala sakamakon albishir da Umma ta yi mata cewa zuwa litinin, tunda yau su na Asabar, za ta ba ta kuɗin WAEC ta je ta biya. Sosai take murna, don dama Hindatu duka biyun za ta zana. Ba ta ci Qualify ba ita, amma Mominta ta biyamata duka jarrabawar guda biyu, daga Waec har Neco din. 


  "Amma dai Umma kin tabbata kuɗin daga hannunki za su fito ko?"


Umman ta ɗan yi shiru sai kuma ta haɗe fuska.


"Kina tunanin zan aikata abin da nasan ba kya muradi? To shikenan, bari a hakura da biyan sai ki zana..."


Da sauri ta katse Umman ta hanyar ruƙunƙumeta tana dariya ita ta mance ma a hanya suke. Har sai da Umman ta tsawatar kafin ta sake ta.


"Na tuba Uwata ƴar aljanna. Kiyi hakuri don Allah."


Umma ta yi murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba. Can ƙasan zuciyarta ta ji wani iri, tabbas kudin daga aljihun Ɗanmutuwa zasu fito, shi da kansa ya cewa Umman zai biyawa Haulatun kuɗin WAEC sadda ya ji tana maganar za ta haɗa ƴan kuɗaɗen ta biyamata, shi ne ya soma kwaɓarta akan kada ta sanar da ita don ya sani ko za'a yi me, kafiyar Haulatu ba zai sa ta amince ba. Ko an biya daga baya ta ji labari, to fa ƙarshenta a yi asarar kuɗi. 


Har suka shiga abin hawa Haulatu hira kawai take jan Umman tana ba ta labarin saurayin Hindatun da irin kudin da yake shirin kashemata a bikin. 


Sun iske mutanen gidan duk suna nan ba su fita ba, Amarya da kuma Baraka. Kamar kullum wannan karon ma buga ƙyauren gidan ta yi da ƙarfi wanda har sai da Umma ta ɗan razana.


  "Ya Salam, kina da hankali kuwa? Dama ashe har yanzu ba ki bar yi musu wannan sakarcin ba?"


"Ina fa za ta bari, ai mun riga mun saba da wannan idan dai Haulatu ce." Faɗin Baraka dake aikin tankaɗe garin tuwo. Ita kuwa Amarya dake zaune ƙofar ɗakinta tana gyaran salad ta yi dariya kawai. Suka gaida Umma, ta amsa fuska a sake. Itama Haulatun sai sannan ta gaida su. 


"Wai ni ya naji shiru ne? Ko waccan yar duniyar ba ta nan? Bayan na fadamata zamu shigo."


"Hindatun ce ƴar duniya?" Fadin Umma. 


"Lah, ai Umma idan dai su biyun nan ne kya ji abin da yafi haka ma."


Umma ta girgiza kai kawai tana murmushi.


"Ba sa nan ne?" Ta tambaya. 


"Suna ciki. Hajiyar ce ba ta jima da shigowa gidan ba, suna ƙule a ɗaki."


Fadin Amarya cikin tsegumi. Haulatu dai dariya ta yi ta yi gaba Umma na biye da ita. Sallamar Haulatu da shigarta ɗakin duka lokaci guda ne, nan da nan ta ga Momin na tura wata leda ƙasan gado, ta kai idanunta ga layar da ta fito a ƙoƙarinta na tura ledar, tana gani ta wayance ta tura shi gami da hawa faɗan borin kunya.


"Ke dai an yi marar hankali. Yanzu ana girma ana cin ƙasa daga sallama kawai kik banko labulen ɗaki, ai sai ki jira a amsa maki ko?"


Ita kuwa Hindatu dake zaune gefe duk ta sha jinin jikinta, ta ɗan washe baki ganin har da Umma. 


"Wa'alaikumussalam, lah Umma sannu da zuwa."


Momi ta ɗan saki fuska suna gaisawa da Umma, ita kuwa Haulatu zama ta yi gwuiwa a sake, wai ita Momi mene matsalarta da ita? 


Nan suka yi musu fatan alheri, har dai aka gama zaman babu alamar za'a nuna musu kayan sanya rana. Haulatu da ba ta shiru tuni ta mance da wancan ɓacin ran ta dubi ƙawarta. 


"Wai ke ba za ki nunamin leshin d kika ce ɗan dubu tamanin ɗin ba?"


Umma ta watsamata harara amma ko a kwalarta, Momi nan da nan ta daure fuska. 


"Kayan ai an kai su ajiya, ba zan bar su anan ba kaya masu tsada a biyo dare a yi mana ɗan hali. Kinsan ban yarda da ɓerayen da muke zaune da su ba a gidannan." 


Ita kuwa Hindatu ta rasa dalilin Momi na ƙin nunamusu kaya, a iyaka zatonta wannan na daga burin Momi, kowa ya zo ya ga kayan bajintar da aka kawowa ɗiyarta. 


"Allah ya kyauta toh." Faɗin Umma sannan ta miƙe.


"Bari mu koma. Allah ya sanya alheri Hindatu. Ya nunamana lokacin."


"Ameen Umma nagode." Umma dai ta ɗan cika da mamaki, toh kenan su ma dai yaran yanzun ba kunya ne da su ba, irin amsawar da yarinyar ke yi ita kunya ma ta ji, tabbas dole ta yi addu'ar Allah ya fitowa da Haulatu miji itama ta yi aure duk da ta san yanda Haulatun ke fatattakar duk wanda ya zo da sunan soyayya wajenta. 


Haulatu dai ta tsaya tana kalle-kalle har idanunta ya kai ga wata babbar akwati sabo fil, kamar ta yi magana sai dai ta fasa ta miƙe. 


"To Amarsu, sai mun haɗu a makaranta. Allah ya sanya alheri Momi."


Momi ta harare ta bayan ta juya baya. A fili kuwa ta amsa cike da gadara.


"Ameen."


Hindatu ta miƙe da zummar yi musu rakiya, ta gefen idanu Umma ta ga sadda Momin ta danne mata hannu wanda dole ta sanya ta komawa ta zauna.  


Sai da suka fice ne Momi ta dube ta tana harara.


"Kina saka ran zan yi sake ne su ga kayan bayan kina sane da cewa duk duniya idan akwai waɗanda na tsani na buɗi idanu na gan ta tare da ke bai wuce wannan shegiyar yarinyar ba mai idanu kamar mujiya? Ke ki sani, muddin kika yi aure toh ƙawancenku ya zo ƙarshe. Ba zai yiwu ina can ina tufka ba kina gefe kina min warwara. Wannan da kike gani baƙar inuwa ce ita, gwamma rana da ita. Amma ya rage naki, idan kin ga dama ki sakarmata fuskar da za ta yi maki illah a rayuwa. Mutum da gishirinsa, in ya ga dama ya dafa ƙaho."


Hindatu shiru kawai ta yi, koyaushe idan Momi tana nusar da ita akan raba hanya da aminiyarta. Ita a iyaka tunaninta ai abokin cin mushe ba a ba a ɓoye masa wuƙa. A yau dai sam ba ta goyon bayan Mominta hakan yasa koda Momin ta fita ta dawo ta jawo ledar rubutuka da layun da ta karɓo wurin bokanta ba ta mayar da hankali wurin sauraronta ba. Ƙarshe ma miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin uwar na kwalamata kira amma ta yi burus. 


***

  A hanya Umma ba ta ce uffan ba sai sauraron Haulatu take wacce ke faman mitar wulakancin da Hindatu ta yi mata ita da Babarta. Ta yi ƙwafa. 


"Wallahi Umma na ga akwatin, kuma na tabbatar shi ne na sanya rana saboda shi Hindatu ta nunamin an haɗa bidiyo da hotonta har da su buhun shinkafa da su tabarma. Amma dai Momi ta rainamana hankali wallahi, toh kenan su Baraka ne ɓarayin ko kuma mu da muka shiga gidan? Kut! Ai..."


"Kin ishe ni haka, za ki kama bakinki kimin shiru ko sai mun raba hanya da ke yanzu? Ban da shashanci muna tafe kina ɗaga murya kina hayagaga kina jazamana kallo?"


Umma ta katse ta a zafafe, sai lokacin ta ɗan waiga ta ga wasu yara gefe suna ta kallonta can gefe kuma wasu samari ne su ma masu zaman majalisa sai ko na tafe da ke waiwaye. Turo baki ta yi ba ta ƙara magana ba. A ranta sai ayyana kalar rashin mutuncin da za ta yiwa Hindatun take yi, ta kuma ci alwashin ba za ta yi ankon bikinta ba. 


Koda suka je gida Umma ba ta ce mata uffan ba. 

 Sai ranar litinin ne ma bayan ta ba ta kudin WAEC da kuma na karamin hoton passport sannan ta gargaɗeta akan nunawa Hindatu wani abu koda kuwa a fuska ne. 


"Muddin kika yi magana za ki tabbatar da zargin Uwar na cewa kina hassada ga ƴarta ne. Ki nuna hakan da aka yi kamar bai dameki ba. Bana son kananan magana, kema dai Allah ya nunamin naki mijin na aurar da ke."


Dariya maganar Umma na ƙarshe ya sanya ta. 


"Umma kenan." Iyaka abin da ta ce kenan kafin ta fice.  


 ***

   Kwanci tashi ba wuya a wurin Allahu, har lokacin jarrabawar su Haulatu ya yi. Hakanan suke zuwa, ba ta ko damu da karatu yanda ya kamata ba tunda a ɓagas ake rubuce musu komai a allo su rubuce. Wannan tsarin na jarrabawar sam bai yiwa Umma ba.


"To Umma ai komai yanzu sai da taimako. Ai iyaka nan ne, gaba ba zamu yi haka ba."


"Um um Haulatu, juma'ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta."


Wannan amsar ta samu daga Umma. Ko a jikinta, ita dai ta san idan an yi abu a aji tana fahinta, matsalar bai wuce rashin Malaman kirki da ba su da shi ba a makaranta don akwai darussa kusan hudu da zasu yi jarrabawa a kansu, ba a taɓa koyamusu ba a makaranta. Sai a wurin Bahijja ne ta ɗan koyi wani abun a ciki. Ita sosai makarantar kudin da yaran gidan su Bahijjar suke zuwa ke burgeta. Sosai Bahijja ta iya turanci, aikuwa tun lokacin Haulatu ta ƙwallafa ran sai ta koyamata. Wannan yana daga abinda ya dauke mata hankali da wuni tare da Umma a gida tana shan takaicin yanda Umman ke rawar jikin yiwa Ɗanmutuwa girki da gyaran ɗaki. 

  

***

  Dariya suka kwashe da shi a lokaci guda. Hajiya Adama ta nuna Ɗanmutuwa ya yatsa.


"Kai, kai, wallahi kai kam ba ƙaramin ɗan bariki ba ne. Kuma gashinan har wani kyallin angonci ka ke yi."


Ya yi dariyar mugunta.


"Ai sai kin ga yanda Na'imatu ke faman rawar ƙafa a kaina. Komai take yi don ta burge ni ne."


"Lallai kam, kai dai shegen kanka ne. Yanzu dai wace mafita ka samo? Lokaci ya ja, ya ci ace yanzu mun san matakin ɗauka. Lokaci ya zo da za ka kawo su gidan nan, na ga Haulatu da idanuna."


Ya jinjina kai gami da sauke ajiyar zuciya. 


"Hakane, kar ki samu damuwa, na gama yanke duk abin da ya kamata nayi ba tare da an zarge ni ba. Za su zo koda sau daya ne, amma ba yana nufin a lokacin ne zan bar maki Haulatu ba tunda dai ciniki bai faɗa ba, har yanzu da saura. Na fi kaunar ya kasance koda za ki ɗauke ta, ya zamana ko daga makaranta ko wani abin na daban. Kinga zai fi toshe dukkan wata kafa da za'a zarge ni. Af, ai na tuna, kwanaki Na'ima na cemin za'a yi bikin wata ƴar makarantarsu. Me zai hana a lokacin bikin ki sa yaranki su ɗauko maki ita?"


Ta yi shiru can ta ce. 


"Idan kuwa hakane, babu amfanin zuwansu gidana, hakan kamar ƙofa ce  wanda zai jawo zargi idan bincike ya tashi."


Ɗanmutuwa ya jinjina kai. Haka suka yi ta ƙulle-ƙullensu, yana ƙara koɗawa Hajiya Adama ɗiyartasa, yana mata rantsuwar sai ta ture fadar dukkan ƴan gaban goshinta saboda za ta kawomata ribar da wasu ba su taɓa kawo mata ba daga wurin Alhazawa. (Wa'iyazubillah).

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 11

"Yanzun nan ta fita, ku fara bin bayanta, duk inda ta sa ƙafa ku sanya. Ku tabbatar kun fesa mata hodar yadda ko kun kai ta ba za ta iya gane hanyar dawowa ba. A kuma faɗawa Hajiya Loma, ina nan tafe anjima."


Jin alamun zai katse wayar, jiki na rawa Umma ta fice zuwa ɗakinta. Jin kamar motsin mutum ya sa Ɗanmutuwa saurin juyowa gami da ɗan zura kansa ta tagar ɗakin, kasancewar tagarsa saitin ta Umma ce, hangota ya yi tana ta kiciniyar shiryawa. Ya yi tunanin ba ta ji komai ba don haka ya yi musu sallama da zummar zai ƙara kira kafin ya shiga ma'ajiyarsa na miyagun ƙwayoyi ya hau lissafa adadin da wasu suka buƙatar ya kai. 


Ɓangaren Umma kuwa, shirin dole ta kama jikinta sai rawa yake. Babban burinta kar ta yi wani motsin da zai ankarar da shi ta ji. Hakan yasa ta shiga jan Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un a zuciyarta, sai da ta kammala saka kaya ta ji ya rufe ƙofar ɗakinsa ya fito. 


"Na'ima." Ji ta yi ya kira sunanta, sai da ƙirjinta ya buga. Tsanarsa take ji sosai ga kuma tsoron abin da ake shirin yiwa ɗiyarta. Sai da ya kira na biyu kafin ta fito tana murmushin dole. 


"Na'am, yi hakuri ina sauri zan shirya ne. Fita za ka yi?"


Ya yi wani murmushin mugunta.


"Eh Ɗawisuna. Ni zan fita. Ba sai an yi girki ba kar na wahalar da ke. "


Ta gyaɗa kai tana ƙara murmusawa a dole.


"Ina godiya. Sai ka dawo."


"Kema sai kin dawo. Ki kularmin da ɗiyarmu."


Daga haka ya fice, ta bishi da banzan kallo wanda take ji kamar ta shaƙo shi. Da sauri Umma ta koma ɗaki, hijabinta kawai ta zura, wayarta ta ciro ta shiga gwada kiran Haulatun sai dai ta ji a kashe. Hankali a tashe ta dannawa Hindatu kira, nan ma yana ta ƙara ba su ɗaga ba. Ƙirjinta ta dafe tana ambaton Allah da nufin ya samar mata mafita. Nan da nan Hajiya Mama ta faɗo ranta, da sauri ta fita ta rufe gidan ta faɗa gidanta. Hajiya Mama na zaune a falo tare da baƙuwa sai ganinta suka yi kamar an jefo ta. Nan da nan suka miƙe, sosai ta tsorata su. 


"Maman Haulatu, lafiya?" Cewar Hajiya Mama. Cikin kuka ta riƙe hannunta jikinta ko'ina na rawa. 


"Haulatu na cikin hatsari Hajiya, don Allah ku taimaka min. Naji Babanta na waya yana bada umarnin a bi ta a kama ta."


"Tana ina yanzu?" Ta tambaya a gaggauce. 


Umma ta ɗan watsa yatsunta. 


"Nima ban san inda ta nufa ba, na san dai wajen da ake yiwa Hindatu kwalliya ta nufa. Ku taimakamin don Allah."


Nan da nan Hajiya Mama ta fiddo waya ta kira mijinta ta sanar da shi, ya ba da umarnin su je gidan iyayen Hindatun a ji inda take. Shi kuma zai sa direbansa da Mujahid (Yayan Bahijja) su je wajen. Ya buƙaci a turo masa lambar Hindatun. Ba musu kuwa suka yi sallama, Hajiya Mama ta karɓi lambar wurin Umma ta aikamata. Haka suka ɗunguma har baƙuwar wacce ƴar uwa ce ga Hajiya Mama. 


 Momi ba ta yi gardamar faɗamusu inda Hindatun ta tafi ba ganin babbar mace kamar Hajiya Mama wacce da gani ka san ba daga rigija-rigijan gida ta fito irin nasu ba. 


***

 Haulatu kuwa tsabar takaicin kiran da Hindatu ke faman jeramata ne yasa ta kashe wayarta baki ɗaya, ko kusa ba ta kula da motar da ke biye da su ba. Mai adaidaitarsu kuwa tun yana ganin kamar ba binsu ake yi ba, har dai ya fahimci duk kwanar da suka yi nan motar da ta sha baƙaƙen gilasai ke yi. Dab da zasu ƙarasa wurin shagon Ayyush inda nan ne dai ake yiwa Hindatun kwalliya ta ji mai Napep din ya yi magana. 


"Anya wannan motar ta baya ba mu take bi ba?"


Haulatu ta ɗan leƙa kanta kafin ta ja tsaki. 


"Kyale ɗan wahala. Wataƙila zancen wofi suke son yi mana. Don Allah ƙara gudu ina sauri ne."


Shi kuwa jin haka ya ƙarawa napep ɗinsa gudu. Faɗi yake yi amma bai taɓa ganin maye irin wannan mai motar dake bin su ba. Da gani masu bin mace su ce su na sonta ne. Amma fa shi abin wai na ba shi mamaki yanda ko akwai sarari ba sa wani kokarin yin overtaking. A bayan dai suke bibiyarsu. Ita dai Haulatu ba ta ko tanka ba sai ma wayarta da ta kunna, daidai lokacin suka isa shagon, ta fito da sauri ta sallame shi. Ko motar ba ta kalla ba. 


Su kuwa su Maada suna tsaye can gefen hanya, Duuna ya dube shi.


"Boss, wai idan ba anan area ba, ina kake tsammanin za mu cafke ta ba tare da an samu matsala ba? Tun ɗazu eh cewa nake ka yi overtaking amma eh ba ka yi ba."

 

Maada bai ko dube shi ba har sai da Mai Napep dinnan ya yi ribas ya wuce su har da leƙensu ya dinga yi amma ya kasa ganin ko inuwa. Haka ya haƙura ya yi gaba. 


***

 Hindatu ta yi kyau sosai kamar ba ita ba, duk wannan kwalliyar bai hana ta hararar Haulatun gami da ɗuramata ashar ba. Itama ta maida martani kafin kuma ta zauna a soma yi mata nata kwalliyar, Hindatu cike da masifa ta ke fadin.


 "Ban taɓa ganin Aminiya irinki ba.  Wa ya taɓa raba hanya da Amininsa ranar bikinsa?"


Ta harzuƙo za ta yi magana mai kwalliyar ta ba ta hakuri da fadin don Allah kar ta motsa ba a yiwa kwalliya haka. Dole ta yi shiru tana huci. Ita ji take kamar ma ta fasa kwalliyar. Wayar Hindatu ta yi ƙara sa'ilin da ake ƙoƙarin yi mata ɗauri. 


"Madam tun fa ɗazu ake ta kiranki ya kamata ki ɗaga wayar nan. Wayasani ko Angon ne." Fadin Ayyush dake zaune can gefe tana cin abinci a robar takeaway ga drinks ajiye gabanta. Masu yin kwalliya a shagon mutum biyu ne ƙwararru. 


Hindatu ta ɗauki wayar tana ɗan murmushi, ganin baƙuwar lamba ya sa ta ɗan yamutsa fuska da tunanin ko masu damunta da neman kwatance ne. Sai kuma kawai ta ɗaga, jin muryar babbar mutum ya sa ta amsa da sallama. Nan ya nemi kwatancen inda suke bayan ya sanar da ita shi din makwafcin su Haulatu ne kuma yanzu haka tana cikin hatsari. Nan da nan cikin Hindatu ya ɗuri ruwa, ta sanar da shi ya kashe wayar bayan ya ce kar ta sake ta sanar da Haulatun. Haka aka cigaba da shirin ita duk jikinta ya yi sanyi, Haulatu kuwa ana cikin yi mata kwalliyar ba'a kai ga kammalawa ba sai kawai suka ji tsayuwar mota. Hindatu ce ta dubi waje don gilashin ana iya ganin na waje amma shi ba zai ganka ba. Ganin wasu maza biyu kuma matasa sai ta yi zaton ko su ne masu neman Haulatun. Suka kwankwasa gilashin wurin. Ayyush ta mike tana mita.


 "Su waye kuma? Maza ba sa shigomin wuri fa." Ta leƙa, ita Haulatu ko a jikinta, Hindatu kuwa ana ɗauri tana gocewa tana kallonsu sai da mai ɗaurin ta yi magana kafin ta nutsu amma kunnuwanta su na waje. 


Ayyush kafin ta kai ga magana sai ga motar ƴan sanda ta faka. 


Daga waje kuwa su Maada su na ganin motar hukuma ba shiri suka yi wani wawan ribas da ya ɗauki hankalin jami'an tsaron suka yi gaba, ganin haka tuni su dinma suka bi bayansu a guje. Ayyush dai ta gama tsorata, kirjinta ya hau bugu da ƙarfi. Mujahid ne ya fara tambayarta inda Haulatu take. 


 Jin an ambaci Haulatu ya sa Hindatu miƙewa har tana sa mai mata ɗauri soke hannunta. Haulatun ma miƙewar ta yi, gaba daya suka nufi ƙofa. Mujahid na ganin Haulatu ya sauke ajiyar zuciya. Ita kuwa ji ta yi gabanta ya fadi. Me zai kawo yayan Bahijja wurinta? Ta ya ya ma yasan cewa tana nan?


"Yaya Mujahid? Lafiya?" 


Ya girgiza kai.


"Lafiya kalau, kar ki damu. Ki.."


Bai kai ga ƙarasawa ba motar su Hajiya Mama ta tsaya, su dinma duk a ruɗe suke. Haulatu ta yi saurin fitowa daga ita sai doguwar rigar ankon bikin na ƴanmata. Ta ƙarasa ga Umma jikinta na rawa, ta samu nutsuwa da ganin Umman don a farko ta yi zaton ko wani mummunan abun ne ya fari da ita. Umma ta rungumeta tana kuka, itama kawai ta ji kwalla sun cicciko mata tun kafin ta san dalilin kukan mahaifiyarta. 


 "Ya isa hakanan don Allah Na'ima tunda ga ta nan kin same ta cikin kwanciyar hankali. Allah ya kiyaye gaba."


Haulatu dai kallonsu take yi. 


"Umma meke faruwa ne?"


Nan Umma ba ta labarin abin da ta ji Ɗanmutuwa na shirin aikatawa gareta. Haulatu ta yi wani dariya lokaci guda mai haɗe da hawaye. 


"Umma kukan me kike? Mamakinsa ki ke yi? Dama ban faɗamaki ba? Ban faɗamaki mugun mutumin nan ba zai taɓa sauya hali ba? Ban ce maki yaudararki ya ke yi ba?  Yau ga shi nan, wataƙila cinikina ya je ya yi ba tare da kin sani ba."


Ta karashe muryarta na dusashewa tsabar wani daci da maƙogwaronta ke yi. Hajiya Mama ce ta dakatar da zancen, ta nemi Hindatu ta shiga a ƙarasa yi mata shiri. Haulatu kuwa komai fita ya yi a ranta amma Hajiya Mama ta dage ta tsaya a yi komai da ita. Mujahid ke sanar da su an cafke mutum biyu cikinsu amma saura sun gudu. Wannan ne ya haifar da nutsuwa a zuciyar Umma sai dai kuma abin da ke binne a zuciyarta da kuma ƙudurin da ta yi na matakin da za ta ɗauka wanda zai fiye musu alheri ita da ɗiyarta. Ta yi alƙawarin tafiya Katsina neman dangin uwarta koda ace ita ba su shirya karɓar ta ba suna mata kallon shegiya, to za ta nemi alfarmar su riƙe mata ɗiyarta ko bayan ranta. 


  Bikin dai na Hindatu bai yiwa Haulatu dadi ba sam duk da irin burin da ta ci wa bikin na za ta yi rawa har sai jikinta ya yi ciwo. Gidan Hajiya Mama suka koma da rayuwa don ƙeyar Ɗanmutuwa ba'a ƙara gani a unguwar ba. Umma ta dauke duk wasu muhimman abubuwanta da ta sani zai sadar da ita ga dangin Mahaifiyarta Salma. 


Bayan komai ya lafa da kwanaki biyar Umma ta soma shiri tun safe, ta kuma tashi Haulatu da ke bacci akan ta yi wanka ta shirya za su yi tafiya. Haulatu ta na mutsika idanu ta dubi Umman, tun faruwar lamarin ko digon fara'a ba ta ƙara gani a fuskarta ba. Ta sha farkawa ta gan ta saman darduma tana kuka cikin sujjada. Itama sai ta ɓoye kanta cikin zanin rufa ta sha nata kukan. 


 "Umma ina zamu je?"


"Katsina." Ta ba ta amsa kai tsaye, Haulatu ta yi shiru tana tunani, Katsina dai? Wa suke da shi a Katsina? Duk kokarinta ba ta iya cankar komai ba. Ganin Umman ta cigaba da aikin shirya jaka yasa dole ta miƙe ta faɗa wanka.

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 10

Tafiya ta yi tafiya, har a yau aka wayi gari su Haulatu suna bikin kammala sakandire. Sabbin uniform din da ta sanya gaba ɗaya an mata kaca-kaca da shi da biro. Duk zare idanu irin nasu ita da Big Mama Hindatu, hakan bai yi tasiri ba a ranar. Su kansu ba su jin manyantan a wannan rana, sauran ɓurɓushi na fushi da Haulatu ta ɗauki lokaci tana yi duk a wannan ranar ta ji ya kau. Suka ɗinke tamkar ba su ba. Haka aka rabu cike da walwala da kuma jin kewa. Wasu har da hawayensu. 


*** 

 Zumuncin da ya ƙullu tsakanin Haulatu da Bahijja shi ne babban abin da ya fi faranta ran Umma. Shigowar Bahijja rayuwar Haulatu ya sanya ta a dole take mayar fa hankali wajen zuwa Islamiyya duk da kasancewar a sannan Bahijja ta yiwa Haulatun zarra a karatu. Ita tana cikin masu hafizan da ake saka ran makarantar za ta yaye, yayinda Haulatu ta koma ajin baya. Zuwa lokacin Malaman ba su yunƙurin dukanta idan ta gwaɓa musu zance sai dai ko hukuncin shara ko wankin banɗakin makaranta. A hankali kuma suka ƙara fahimtar cewa hakanan ta ke sai dai ko yau da gobe idan a na nusar da ita ta hanyar yi mata gyaran kalami zai taimaka ƙwarai wurin shiryuwarta. 

  Albarkacin zuwa makarantar da take ne ya jawo Ɗanmutuwa ke samun arziƙin gaisuwa, hakan ma a daƙile ta ke yi don har wani ɗaci take ji a maƙoshinta. Wannan albarkacin kaɗai ya soma ci a kwanakin, shi ɗin ma darajar Umma ya ci ganin sosai Umman na damuwa da yadda take nuna halin ko'in kula da duk wata kyautatawa da Uban ke yi mata. Har gobe dai ba ta taɓa yarda ta ci abin da ya fito daga hannunsa, wani tsire da kaza da yake kawowa Umma duka ba burge ta suke yi ba. Umma itama tun lokacin da ta gwada sau ɗaya ba ta ƙara ba don a gaban Ɗanmutuwa Haulatun ta rantse ba za ta ci kayan haram ba. Har a lokacin Umma ta so kai mata bugu sai dai Ɗanmutuwa ya tare. Wannan rana kusan kwana Haulatu ta yi tana kuka, wai yau ita Mahaifiyar za ta kai wa duka akan wanda bai taɓa daraja a idanunta ba. Washegari kuwa ta tashi da ciwon kai mai zafi, wannan ya tashi hankalin Umma, tsoronta kada ta jefa ta a ciwo irin na can baya. Ita kanta sai daga baya ta fahimci mugun kuskuren da ta yi na ɗaga hannu da zummar dukan ɗiyarta.


 Tun ana sauran sati uku a fara bikin Hindatu, aka kawo lefe. Wannan karon Haulatu ko leƙe don ta rantse ba za ta ƙara zuwa Momi ta wulaƙanta ta ba. A lokacin Haulatu ta mallaki wayarta ƙarama wacce Umma ta yi mata kyautarta na taya murnar kammala sakandire. Ba ta ji mamakin komai ba kawai ta saka a ranta kuɗaɗen da Umma ke adashi ne ta karɓa. A sannan wani abu wai Chatting bai ko damu Haulatu ba, ba ta taɓa ma kallonsa da sha'awa ba. Iyaka saninta ba ta da wani ko wata da za su yi hira da shi. Ta gwammace duk sadda za ta yi waya da Aminiyarta ko Bahijja idan ba su haɗu ba, ta kira su ta waya, idan kuwa babu kudi ta yi ta dokamusu beep call har sai sun gaji sun kira don ji me ta ke so. 


Ko kusa ba ta yi karambanin cusa kai a sha'anin bikin Hindatu ba gudun jin baƙar magana daga bakin Momi. Hindatu har abin ya ba ta haushi don sai da ta tako har gida ta kawo ƙararta wajen Umma akan ta ƙi yi mata rakiya gurin gyaran jiki da na gashi kafin ta amince su je. 


 Ranar da aka fara gyaran jikin, ta sha mamakin irin haɗuwar wajen, koda dai unguwar ma kanta ta manya ce, can wuraren Lamiɗo Crescent ne. Wurin na wata Basudaniyar mata ce ana ce mata Ayyush.  Haka Haulatu ta yi zaune tana kallon ikon Allah yanda ake ta mulkewa ƙawarta jiki. Zuwansu na farko amma sai ta ga har ta sauya. Matar ta dube ta. 


  "Kema dai ya kamata a yi maki, za ki yi kyau sosai tunda na ganki ba baya ba Masha Allah."


Ɗan murmushi kawai ta yi, ita kuwa wace hidimar ce za ta tasar mata ta yi gyara irin haka? Ita da babu ma aure a ƙoƙon ranta, mene haɗin biri da gada? 


"Ai wannan da kike gani babu ma aure a gabanta yanzu. Sai na kai ta an yi mata ruƙiyya sannan."


Ta harari Hindatun, tana ji matar ta hau yi mata faɗa da ƴar nasiha akan muhimmancin aure da kuma kuskuren cin alwashin ba za ka yi shi ba tunda ba kai ke iko da kanka ba. Sai ta yi dariya. 


"Toh ni ina ruwana? Ku da kuka ga za ku iya ai ga fili ga mai doki."


Tun daga nan fuskar Ayyush ta sauya, Hindatu sam ba ta ji dadin zancen na Haulatu ba. Tun da ta kalli fuskar matar ta tabbatar Haulatu ta musu kwaɓa. Haƙuri ta shiga ba ta kafin cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce 


"Ita fa muddin za'a yi mata zancen aure iskokanta tashi suke yi."


Kasancewar Ayyush da tsoron abin da duk ya shafi aljani, hakan ya sa ba ta ƙara zancen ba. Ta kuma aminta da batun Hindatun wannan dalili ya sa ta ɗan saki fuska gami da yi wa Haulatun uzuri. 


 Haka suka jera sati tana yiwa Hindatu rakiya gurin gyaran jiki, sau biyu suka haɗu da Alhaji Badamasi shima ya zo ɗaukarsu ne ya maida gida, ta dai kula mutum ne mai shegen kallo da sa idanu don tun ganin da ya yi mata na farko ta ji ta tsane shi saboda yawan kallonta. Tana daga kujerar baya amma haka yake saita madubinsa ya na kallonta ta ciki. 

  Sau biyu da aka yi ba ta ƙara yarda Hindatu ta fita da Hindatun ba tare da niƙaf ba. 


  Koda aka soma biki sun fara ne da Bridal Shower kamar yadda zamani ya zo da shi. Wannan rana yana daga cikin ranakun da Hindatu ta jima tana mafarki, babban burinta a gudanar da Bridal Shower. Ta kuwa samu yanda ta ke so, gidan wata ƙawar Mominta ko ace Uwar ɗakin Momin, Hajiya Zulai, nan aka ba su aron babban falonta aka yiwa falon tsari mai kyau na ado. Ƙawaye ma sai da ta zaɓa domin duk ciki ban da Haulatu aminiyarta, mutum biyu kacal ta gayyata a ƴan makaranta sauran wasu ƴan duniyan ƙawaye ne da ta haɗu da su  rayuwar soshal midiya. 


 Haulatu Ta yi ƙunshi ta yi kitso, ba ƙaramin kyau ta yi ba ranar. Shigar fari da ruwan gwal ɗin da suka yi, sosai ya fiddo ta. Duk yanda ta gujewa yin kwalliya haka Hindatu a dole ta matsa sai da aka yi mata. Sun ci sun sha kayan maƙulashe, ga mai hoto na musamman da Alhaji Badamasi ya kawo, haka ya dinga ɗaukar su, sai wuraren takwas na dare suka watse. 


***

 Washegari kamu haɗe da yini wanda za'a yi a wani ɗakin taro na musamman. Marar kati ba zai samu shiga ba. Tare zasu je da Umman amma yanda Hindatu ta dinga jera mata kira tana ɗuramata zagi kan ta taho inda ake mata kwalliya tare za su tafi yasa a dole Umma ta ce ta wuce kawai zuwa yamma ita sai ta tafi tunda akwai waya zasu yi magana kawai. 


  Sadda ta kammala daukar duk abinda take da buƙata a leda, ta fito a gaggauce suka kusan cin karo da Ɗanmutuwa, guntun tsaki ta ja kafin ta yi baya. Ta san da ace Umma ta ji wannan tsakin ranta ne zai ɓaci, shi kuwa shigowa ciki ya yi wannan karon ko arziƙin gaisuwar da ya saba ci bai ci shi ba. 


  Wayarsa ta yi ƙara ganin mai kiran ya sanya shi saurin shigewa ɗakinsa, daidai lokacin ita kuma Umma ta fito daga nata ɗakin, sam bai kula da ita ba, ta ƙarasa, kafin ta kai ga shiga ta yi saurin ja baya tana sauraron abin da yake faɗi. Tashin hankali! Gobarar gemu kenan.

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 12

A ɓangaren Ɗanmutuwa kuwa, tun lokacin da suka yi waya da Maada yake ba shi lamarin ƴan sanda sun tarfa su, ya shiga mugun tashin hankali. A sannan yana kwance tare da abokiyar hutawarsa a ɗaki a gidan Hajiya Adama. A hargitse ya ja kayansa ya mayar ya fito ya nufi wurin Hajiya Adama ya sanar da ita komai. Hannu ta ɗagawa mai yi mata tausar ƙafa gami da ba ta umarnin ta bar falon. Rai a ɓace ta dube shi.


"Garin ya ya ka yi sake har wani ya ji wannan shiri? Ni na tabbata akwai sila, ba hakanan kawai labari zai kai ga ƴan sanda ba. Ko akwai munafuki a cikin yaranmu ne?"


Ɗanmutuwa wanda duk sanyin falon bai hana shi fitar da zufa ba, cikin tsananin ɓacin rai ya amsa.


"Ke ai kin san ni, ba zan yi sakacin da har wani zai ji wani abu ba. Na yi waya a gidana, amma ko alama babu wanda ya ji, asalima sadda na yi daga ni sai Na'ima, ita kuwa tana ɗakinta tana ƙura adakar fita biki. Yaran nan kuwa ƴan a mutu ne ko a yi rai kin san da haka."


Ran Hajiya Adama ya ɓaci.


"Ji fa, ashe ga inda aka haihu a ragaya nan. Kana tunanin za ka yi waya a gida amma Na'ima ta kasa fahimtar komai?"


Ɗanmutuwa ya girgiza kai.


"Ban maki musu ba, amma dai ina tabbatar maki cewa ba ta ji ba. Matsoraciyar mace irin Na'ima ban hangi ta inda za ta shanye tashin hankali irin wannan ba ta yadda ko a fuska ba zan gane ba."


Ɗan murmushin ba ka da wayo Hajiya Adama ta yi mishi. Sai kuma ta yi ƙwafa. 


"Shikenan, muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Ai kare na yawo zabo na yawo wataran za'a haɗu, idan ka ji labari za ka ce na faɗamaka."


Aikuwa yin maganar da kwana ɗaya, labari mai zafi ya zo daga bakin Gwaska cewa ai Umma da Haulatu a yanzun sun tare gidan makwafcinsu Alhaji Mijinyawa. Ya kuma samu labari cewa ana zargin Ɗanmutuwan da yin garkuwa da ɗiyarsa Haulatun. Wannan magana ta jefa Ɗanmutuwa cikin tashin hankali. 


"Ya akai wannan zance ya fito?" 


"Ba ga shi nan ba! Ai na faɗamaka! Yanzu sai dai mu sa manya a gaba a kashe zancen. Raina kama kenan ka ga gayya. Yanzu ga shi nan ta shayar da kai mamaki."


Wannan amsar ya samu daga bakin Hajiya Adama. A ƙarshe suka yi duk wata ƙulla-ƙullarsu aka tura Ɗanmutuwa wai ƙebantaccen gidan gona na wani  babba a ma'aikatar Custom dake harƙallar miyagun ƙwayoyi da su. Kusan su na ji sosai da Hajiya Adama a fagen kasuwancinsu wannan dalili ya sa duk wata alfarma tana samuna wurinsu. Ɗanmutuwa kuwa ya zame musu wannan mutum mai sa'a, duk wani kaya da zasu damƙa a hannunsa to fa nan da nan zasu ƙare. Wannan yana daga dalilan da suka ɗauke shi da muhimmanci a tafiyarsu. 


  Haka Ɗanmutuwa ya koma can Gwarzo inda gidan ginar yake, sai dai zuciyarsa ta kasa sukuni, ba kuma tsoron za'a cafkeshi yake ko wani abun ba, sai don jin bakin ciki da haushin Na'ima wacce ta jawomasa asarar maƙudai. Ya kuma sha alwashin idan komai ya lafa sai ya ɗauki mataki a kanta. 


Wannan kenan.


***

Hajiya Mama da Mijinta zaune a saman kujera a falo, yayinda Umma da Haulatu ke gefe saman kafet. Ganin irin halaccin da suka yi musu ya sa Umma warware musu zare da abawa na asalin dalilin da yasa ta auri Ɗanmutuwa da kuma zamanta a cikin ƴan  bariki wurin mahaifinta. A ƙarshe ta miƙawa Abban su Bahijja hoton mahaifiyarta wanda ke ɗauke da sunan gari da kuma zuri'ar da ta fito. 

Da mamaki tsantsa Abban Bahijja ya dubi sunan, ba don wai ya yi mai sunan keɓantaccen sani ba, a'a, sai don sunan ba ɓoyayye ba ne tun zamanin iyayensu har kuma zuwa yanzu da matasan jikokin gidan suke nasu tashe na kuɗi da ma ilimin boko da arabi. Ya maida duba ga Umma dake sharar hawaye na fargabar abin da za ta je ta tarar a cikin dangin mahaifiyarta. 


"Na'ima, kina son cewa mahaifiyarki ɗiya ce ga Tsohon Attajirin nan Alhaji Bello Shu'aibu Malumfashi?"


Hajiya Mama jin sunan ya sa ta kalli Abban da mamaki kafin ta kai hannu ta karɓi hoton, matar kamar an tsaga kara tsakaninta da Umma sai ko ta juya ta ga rubutun. Asma'u Bello Shu'aibu Malumfashi. Katsina. Har da kwanan wata na sadda aka yi hoton. 


"Ikon Allah." Shi ne abin da Hajiya Mama ta furta. Umma bayan ta amsa da Abban Bahijja da eh, shima jinjina kai ya yi cike da tsantsar mamaki. Ya sani akwai sauran rina a kaba a ɓangare na rayuwar Umma, bai ce ko ba za su karɓe ta ba ko wani abun makamancinsa ba, sai dai babban zuri'a ne da ya tara yara da jikoki. Yana da tabbacin wannan rayuwar da ta shimfiɗa a waje daga baya ta zo musu, za ta fuskanci wasu abubuwan dole kafin ta samu karɓuwa. A hasashen Abban Bahijja kenan. Ita kuwa Haulatu ta ma kasa gane me take ji, ita ba farin ciki ba ita kuma ba akasinsa ba. Ta dai sani Umman ta bata mamaki yanda ta iya ɓoyemata wannan hoto tun tsawon waɗannan shekarun da take nacin sai ta nemo danginsu. 


Haka suka rabu bayan Abban ya sa direba ya miƙa su tasha, ya kuma ba Umma kudi masu ɗan kauri cewa su riƙe. Ba iya nan ya tsaya ba sai da ya bi ta da nasiha akan ta yi hakuri ta jure dukkan wani abu da za ta fuskanta a cikin zuri'ar. Umma ta yi godiya sosai. Haka suka kama hanya bayan sun shiga har gidan makwaciyarsu  Maman Hasiya itama sun mata sallama. Haulatu ko ta kan Hindatu ba ta bi ba don tun abinda ya faru Hindatun ba ta ko neme ta a waya ba bayan biki ta ji ya ake ciki wannan ya sa itama ta watsar da ita. 


   Ƙarfe sha ɗaya daidai motarsu ta ɗaga daga tasha suka kama hanyar Katsina.  Abban Bahijja ya tabbatar musu cikin Katsina iyalan ke da zama kaf dinsu, ba wai a Malumfashin ba. Ita kuwa Hajiya Mama lambar wayar wata yar uwarta ta ba su akan su fara sauka a can su huta, ta kuma kira ta yi mata bayani, babu musu ta ce za ta jira su. 

A hanya haka ta dinga kira ta ji ko sun shigo. Suna isa kuwa, ta ce su nemi adaidaita sahu, su ba shi waya ta yi mishi kwatance. 

  Suka kama hanyar unguwar Dutsin Safe Low cost, ita dai Haulatu tana kallon wurare. Ta sani nesa ba kusa ba za ta haɗa garuruwan biyu ba a fagen abubuwa da dama, sai dai kuma muddin kwanciyar hankalinsu a nan yake, ta shirya shimfiɗa sabuwar rayuwa a Katsina, za ta taya Ummanta zaman haƙurin da ta ji Abban Bahijja na magana akai, akan dai ta ƙara rayuwa da mutum irin Ɗanmutuwa. 

  Ta kalli Umman ya fi a ƙirga, ko kusa babu ɗigon fara'a a fuskarta, ta dai bar zubar hawayen sai ko kumburin da idanunta suka yi da kuma ja da fuskar ta yi. Ta yi ɗan kwafa, a ƙasan ranta ta ce. 

  'Umma kukanki ya zo ƙarshe in sha Allahu koda ba a karɓe ki a dangin Mamarki ba, babu mu babu ƙara komawa Kano.'


Wannan shi ne alwashin  da Haulatu ta ci. Sai a sannan ne ma ta ji ranta ya yi fari ƙal, har wani murmushi ta yi. 


Sun samu tarba mai kyau daga wurin yar ƙanwar babar Hajiya Mama, wacce ake kira Hajiya Rabi'atu. Mace ce babba sai dai ba ta kai Hajiya Mama a shekaru ba, gidanta madaidaici mai kyau da tsari. A falonta akwai tafkeken hotonta ita da miji da yaranta su bakwai har da ƴan biyunta maza masu ƙananan shekaru. Ta ba su lafiyayyen abinci da abin sha suka ci suka ƙoshi sannan suka yi sallar Azahar. Duk yadda Umma ta so ta bar su su ƙarasa gidan da zasu je a ranar ƙi ta yi, ta rantse sai sun kwana. Mace ce mai fara'a da son mutane ga hira. Nan ta dinga ba su labari na irin tarin arziƙin gidan Bello S Malumfashi, fadi take. 


"Ai Maman Haulatu ba komai ba ne daga arziƙinsa idan an haɗa da na matasan jikokinsa. Sai dai fa naji ance akwai rikici iri-iri a wannan gidan da kuma shegen gasa, kowa burinsa ya fi ɗan uwansa. Amma dai kaf cikinsu naji ance akwai ɗaya da ya fi su a komai, ni ko jikan Hajiya Saratu ne ko wa? Na dai manta. Ke na san fa duka wannan labarin a bakin wata ƙawata da Hajiya Iklima, ita ɗiyarta na auren wani ɗan riƙo a gidan ne."


Haka ta dinga zuba hira wanda Umma duk hankalinta ba ya kai, fargabarta na kan abin da zai je ya zo. Yayinda Haulatu ta baza kunnuwa tana sauraro sai faman washe haƙora ta ke, babu ma kamar Hajiya Rabi da ta dage sai ta yi musu rakiya a goben, acewarta za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an karɓi Umman hannu bibbiyu. 


"Uhm." Shi ne kawai abin da ya fito a bakin Umman. 


***

  *LATE ALH BELLO S MALUMFASHI RESIDENCE.*

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 14

"Kina so ki cemin ke ƴar gidan Saleh ce?" Hajiya Babba ta fisgo tambayar daƙyar daga kwakwalwa zuwa harshenta. Murmushi mai ciwo Umma ta yi. 


"Ni ɗiyar Saleh da Asma'u ce. Akwai abin da kike tantama ne? Ko ki na so ki cemin kin manta sadda ki ka yi watsi da ni a bariki ba ki ƙara waiwayata ba?" 


"Bariki?" Faɗin Hajiya Rabi da Baba Saude a lokaci guda cike da wani irin mugun kaɗuwa. Ita Hajiya Rabi ai ba komai Hajiya Mama ta baje mata a faifai ba. Ga Baba Saude kuwa, kallon Hajiya Babba kawai ta ke yi, burinta ta ji gaskiyar zance daga bakinta. 


Gumi kawai Hajiya Babba ke yi, ranta ya ɓaci. Wato Saleh sai da ya karya alƙawarin da ya ɗaukarmata? Sun yi da shi duk runtsi ba zai taɓa barin ɗiyarsu ta san asalinta ba balle ta kawo kanta wataran ko kuma ya kawo ta, sun ƙulla wannan yarjejeniya shekaru masu yawa a baya wanda sanadin hakan ne ta yi mishi kyauta da wasu kuɗaɗe masu yawa da daraja irin na zamaninsu.


"Me kika zo nema a wurina yanzu? Wace buƙatar ce ta kawo ki?"


Haushi da bakin ciki suka mamaye zuciyar Umma, ta ma rasa me za ta ce.  Ita kuwa Haulatu wani irin kallo na mamaki take yiws Hajiya Babba. Ga ta nan dai a kallo ɗaya ta amsa sunanta da dattijuwar mace mai cikar kamala. Kalamanta sun bambanta da suffarta. 


"Granny! Granny!!"


Maganar ta yi daidai da ƙofar da aka buɗe na ɗaya daga cikin kofofi hudu dake a falon. Gaba daya suka dube ta,  yarinya ce da shekarunta za su kai biyar a duniya. Tawul fari ƙal ɗaure a ƙirjinta sai kuwa gashinta mai cika da baƙi wanda ya sha tufka da ribbon. Yanayin yadda ruwa ke zuba daga jikinta za ka fahimci wanka aka yi mata. Tana zuwa ta faɗa jikin Hajiya Babba tana fadin. 


"Granny, ki cewa Mami kar ta shafamin mai. Bana so."


Ya yi daidai da fitowar wacce ta kira da Mamin daga ɗaki hannunta riƙe da  kaya da kuma man shafawa na yara. 


"Ke Baby ki..."


Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon mutanen da ta gani zaune a falon, su dinma kallonta suka yi. Za ta yi shekaru ashirin a duniya, doguwa ce kuma baƙa mai ɗan jiki. Ta gaishe su mamaki dauke saman fuskarta na ganin wata mai ɗiban kama da ƴan gidansu. Wuri ta samu ta zauna kuwa. Hajiya Babba ta ture yarinyar.


"Maimuna, ja hannunta ku wuce ɗaki ina da baƙi."


"Baƙi kika ce fa Hajjaju? Ai ce mata za ki yi ɗiyarki ce da kika bar wa duniya ita ta dawo."


Muryar Haulatu ta zo musu a bazata, zuwa lokacin ta gama kai wa wuya dama, ta kula Hajiyar za ta kawo musu rainin hankali da wayo.  Hajiya Babba duban Haulatu ta yi amma ta kasa magana. Ita kuwa Maimuna sai ta yi turus cike da tsantsar kaɗuwa. 


"Assalamu alaikum." Aka faɗi da murya kakkaura. Hajiya Babba ba ta san sadda ta miƙe tsaye ba. Wannan shi ne abin da take jiyewa tsoro, babban burinta ta san yadda za ta yi da su Umma kafin wani ɗan uwan nata ya shigo. Baba Saude da Maimunatu suka gaishe shi. 


Dattijon mutum. Dogo mai cikar farin ƙasumba. Kallo ɗaya za ka fahimci girman da ya kama shi sosai. Dakta Suleiman B.S Malumfashi kenan. 


Ɗa na huɗu a wurin Marigayi Alhaji Bello. Su biyar ya haifa. Hajiya Asma'u ita ɗaya ce mace a cikinsu. Su uku kawai suka rage a yaransa. Shigowar da ya yi ta musamman ce, magana ya zo su yi da Hajiya Babba akan jikarta Maimuna da ta yo yaji kuma Hajiyar ta ɗauremata gindin zama. 


Umma ta dube shi, shi ma Dakta ita ya zubawa idanu yana amsa gaisuwar su Baba Saude. 


"Yaya, sannu da zuwa." Fadin Hajiya Babba da rawar baki. Idanunta nan da nan suka kawo ruwa tsabar tashin hankali. Yau dai abin da ta binne shekaru masu yawa zai tonu. 


"Yauwa. Asma'u, wace ce wannan din?"


Ya yi tambayar yana ƙara gyara zaman gilashinsa. Tuni Haulatu ta yi caraf ta ce. 


"Ni jikarta ce, wannan kuma (ta dafa kafaɗar Umma) ɗiyarta ce ta cikinta da ta haifa ta bar ta a hannun mahaifinta Saleh Mai Kalangu ba tare da ta ƙara waiwayon rayuwarta ba."


"Saleh Mai Kalangu?" Dakta ya maimaita sunan, shiru ya ɗan yi yana nazarin inda ya  taɓa sanin wannan suna kafin ya yi salati a fili yana duban Hajiya Babba wacce tun shigowarsa ta miƙe tsaye kawai sai ta fashe da kuka. 


"Asma'u, kodai ban ji da kyau ba. Ɗiyarku ke da Saleh Mai Kalangu? Wannan zancen gaske ne ko kuwa dai wasa ne aka zo a ynda hankulanmu?"


Ta kasa magana sai kukan, ranta na suya da zafi tana ji kamar ta kama Haulatu ta jibga tsabar yanda ta yi mata tonon silili a idanun mutumin da take yiwa kallon Uba kuma ɗan uwa mafi kusa da ita. Mutumin da ba ta taɓa ɓoyemasa komai ba kasancewarsu saƙo da saƙo kuma jininsu ya haɗu sosai fiye da sauran yayyunta maza. Yau dai ga babban sirrin da ba ta taɓa gigin sanar da shi ba. Bayan ita da wasu bayin Allah biyu da ta rayu da su a can wani gari, sai ko uban gayyar Saleh Mai Kalangu, babu wanda ya san da batun cikin Na'ima balle a san da wanzuwarta a doron ƙasa a dai nan garinsu Katsina. 


Shiru ma magana ce inji Hausawa, tabbas shirun da Hajiya Babba ya tabbatarwa Dakta zarginsa. 


"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un." Ya maimaita a karo na biyu. Wayarsa ya fiddo ya danna kira, yayansu babba da ya rage ya kira ya ce masa ga su nan zuwa da baƙi, magana ce mai muhimmanci. 


Yana katsewa ya dubi Hajiya Babba, gaba daya idanunsa sun kaɗa. 


"Ku muje can ɓangaren Alhaji a yi magana. Wannan ba ni zan yi hukunci ba."


Ya ƙarashe da jin ɗaci a maƙoshi. Daga haka ya sa kai ya fice daga falon bayan ya ba Maimuna umarnin ta yiwa su Umma jagora sashin Alhaji. 


***

  Babban falo ne mai dauke da ababen mora rayuwa daidai gwargwado. Tsaruwarsa ya shafe na sashin Hajiya Babba. Wani tsoho ne zaune saman dardumarsa ta ibada. A gefensa wasu matasa ne biyu wadanda duka ba su wuce shekara ashirin da takwas ko tara ba. Hira suke yi kafin wayar da Dakta ya yiwa Alhajin ta katse su. Ko bayan kammala wayar shiru suka yi baki daya domin da yawan lokuta Alhajin yana amsa waya ne ta hanyar sanya ta a handsfree. Wannan ya ba samarin damar jin abin da ya ce. Ɗaya a cikinsu wanda ya fi ɗan uwannasa jiki da kuma hasken fata ya miƙe. 


    "Bari na ƙarasa ofis kafin wancan Baturen ya kore ni."


Jin haka ɗayan ya yi dariya gami da faɗin. 


 "Kai Haidar, ka iya bakinka fa, ko ka mance a gaban amininsa ka ke? Wannan ɗan tsohon ko tusa aka yi sai ya fesa mishi."


Alhaji ya kai mishi duka da sandarsa dake ajiye a gefe. Aka yi dariya baki daya. Ya amsa.


"Ja'iri, kun fi kowa sanin ai Sadaukina daidai yake da ku. A hankali zai saita ku kowannenku ya shiga taitayinsa tunda na kula ku kam ba ku da aiki sai kashe-kashen kuɗi. Kai kuma mai kiransa da Bature kamar a kunnensa."


 Wanda aka kira da Haidar ya kama kunne.


"Tuba nake tsoho mai ran ƙarfe, Ango kuma miji gurin Hajja Bilkisu mai gadon zinare. Allah ya ja da ranka, idan ka mutu kuma Allah ya haɗaka da ita a aljanna."


"Amin, amma mutuwa kam ba yau ko gobe ba da yardar Allah. Ɓacemin kafin ka kashemin jiki."


Matasan suka tuntsire da dariya karo na ba adadi. Kafin su kai ga tashi sai ga sallamar Dakta, wannan ya sa duka suka ɗan nutsu. Dakta da Hajiya Babba suna daga cikin kakannin da sam ba su sakin fuska yadda ya dace ga jika. Babu ma kamar Hajiya Babba wacce ake masifar shakka idan ta tubure ta hau faɗa da bala'i akan duk abin da aka yi bai yi daidai da ra'ayinta ba. Ita ce ƙaramarsu amma su na ji da ita sosai don suna yawan cewa ita ɗin amana ce ta iyayensu, kuma sun musu Allah ya isa idan har sanadinsu ta shiga wani yanayin. Wannan ya sa ba a komai suke tsawatar mata ba sai idan sun ga tura ta kai bango. 


 Samarin suka gaida Dakta cike da girmamawa. Kafin su maida duba ga wadanda ke shigowa falon. Duban junansu suka yi da tsantsar mamaki. Bayan sun zauna sai ga Hajiya Babba itama ta shigo. 


Idanun Baba Dakta ya rufe bai ma nemi su Haidar su tashi ba ya korawa Alhaji komai da ya je ya tarar a sashin Hajiya Babba. Ya yi mishi nuni da Umma gami da ba ta umarnin ta tashi ta matso kusa. 


Umma ta miƙe ba musu har jiri take ji tsabar damuwar da ke cinta ga wani zafi da take ji daga ƙirjinta sai kuwa kai dake sara mata lokaci guda. Har Umma ta ƙaraso ta durƙusa gaban Alhaji ta ƙara gaida shi bakinsa bai bar furta sunayen Allah ba. Alhaji ya dubi Dakta kafin ya maida kai ga Hajiya Babba wacce ke faman kuka na takaicin wannan ranar. 


"Ya Allahu, Sule, ai wannan Asma'u ce zaune a gabana."


Dakta ya yi ƴar dariyar baƙin ciki. 


"Ita ce Yaya, ɗiyarta ce ta cikinta. Ta ɓoye mana bamu da labarinta. Haka iyayenmu ba su san da wanzuwarta ba har ƙasa ta rufe idanunsu. Watakila ba don Allah ya yi zamu san gaskiya ba, da har ƙasa ta rufe namu idanun ba mu da masaniya a kanta."


Haidar dai sun yi mugun kaduwa da jin wannan labari, wayarsa da ta yi ƙara ce ta sanya Dakta ankara da su. Nan ya ce maza su fice. Suka miƙe don su dai kam sun gama jin kan labarin. 


Suna fitowa Haidar ya dubi ɗan uwana Jabeer.


"Kai! Don Allah ɗan mintsile ni na ji ko dai mafarki nake?"


Jabeer da shima ya yi mutuwar tsaye don mamaki ya kuwa girgiza kai bakinsa a bude, can kuma ya yi wata ƴar ƙaramar ashariya ya ce.


"Kai! Yau akwai labari a gidan nan. Wai Allah, wa ya kamata na fara kira?"


Haidar ya yi wata dariya. 


"Amma ashe tsohuwarnan ma ta buga duniya har haka take neman shigar mana hanci da ƙudundune?  Kalli fa kamanni kamar ta yi kaki. Ai wallahi wannan ta fi kama da ita akan Anti Maryam. Kai! Akwai fa labari a gidannan! Ai mu shiga group kawai."


Suka yi dariya, dariya irin ta mamaki da kuma ganin bala'i da masifar da abu kaɗan Hajiya Babba ta jefa akan jikokinta da ma wasu a yaran ƴan uwannata, sai ga su nan sun bayyana a tattare da ita. Suna da yaƙinin cewa labarin nan zai girgiza wannan zuri'a ta su. 


***

  Hajiya Babba ta dubi Alhaji bayan ta gyara zama. Alhaji ya jefamata tambaya har sau kusan uku akan dagaske ɗiyarta ce amma ta kasa amsawa, sai a yanzun da ya haɗa da tsawa cikin muryarsa ta tsufa kafin ta yi yunƙuri na ba shi amsa. Haulatu kawai harararta take yi don a farkon ganin tsohuwar ta ji ta burgeta, sai dai a yanzu kam ji take yi babu wacce ta tsana sama da ita tun daga yadda ta nunamusu da farko.


 "Eh, ɗiyata ce da na haifa tare da Saleh."


Ta ba da amsa kai tsaye, Umma ta sunkuyar da kai gami da lumshe idanu, hawaye kawai ke fita daga idanunta. Alhaji ya yi salati.


"Ɗiyarki ce dai kenan Asma'u. Garin ya ya haka ta faru? Kin ce mana guduwa kawai ki ka yi daga gida kuma kika dawo bayan zuciyarki ta yi sanyi. Kin nuna mana ke ba Saleh kika bi ba, Asma'u wannan maganar kuma daga ina ta ɓullo?"


Girgiza kai Hajiya Babba ta yi, wannan masifa da me ta yi kama? Meyasa asirinta bai tashi tonuwa ba sai bayan da tsufa ya zo mata? Kai, ita ta ma yi zaton tunda har labari ya risƙeta na mutuwar Saleh tun a baya, to ɗiyar itama ta mutu. Ashe dai dama  akwai sauran rina a kaba? Ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara duban Umma karo na barkatai sannan ta maida duba ga yayyunta. 


"Ranar wanka haƙiƙa ba a ɓoyon cibi, saboda ita Na'ima, zan ba da labarin komai tun farko har zuwa lokacin da na dawo gida wajenku. Da kuma irin rufi na asiri da marigayi mijina Yusufa ya yimin sadda muka yi aure."


Gaba daya hankali sai ya koma kan Hajiya Babba har Umma. 


***

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 13

*Late Alh Bello S Malumfashi Residence*


Haka aka rubuta a ƙaramin allo wanda ya sha adon baƙi da kuma ruwan zaiba da aka liƙe a daidai tafkeken gate na shiga gidan. Haulatu ta ɗauke kai daga saman allon ta mayar da idanunta kan gidan wanda kusan tun farkon layin har zuwa ƙarshe shi ne ya ci ɓangaren dama. Gida ne mai adon fari da ruwan toka. An ƙawata wajen da shukoki masu kyau inda aka gewaye wurin shukokin da wasu fararen ƙarafina sai kuwa fitilu dake jikin bangon wanda ko ba a faɗi ba idan dare ya yi su na taimakawa wurin daɗa ƙawata su. 


  "Madams, ina zuwa?"


Hankalin Haulatu ya koma ga jibgegen ƙaton dake tsaye jikin ƙofar shiga gidan, idanunsa akan Umma, sosai yake ganin kamanninta da mutan gidan, sai dai shigar da ta yi ko ƴan aiki albarka. Hajiya Rabi cikin sauri ta amsa.


"Mun zo wajen Hajiya Babba ne."


Ya ƙara duban Umma kafin ya dubi Haulatu, kai shi abin mamaki yake ba shi, to ko ƴan uwansu ne daga Malumfashi? Ƙarshe dai ya ce su jira yana zuwa. Cikin ɗakinsa na gadi ya koma ya danna kira ɓangaren Hajiya Babba. Koda aka amsa ya yi bayanin an yi baƙi, babu ɓata lokaci aka ba da umarnin su shigo. Ya sani dama idan har ɓangaren Hajiya Babba ne, ba a fiye disga baƙo ba. Matuƙar aka zo ganinta, to fa koda ace jikin girma ya hana ta fitowa wurinka, ba za ka tafi hakanan ba. 


Dawowa ya yi ya yi musu iznin su shiga. Nan fa suka shigo farfajiyar gidan da ya kusan tafiyar da numfashin Hajiya Rabi da Haulatu. Ita dai Hajiya Rabi tun da take ba ta taɓa shigowa gidan S Malumfashi ba sai dai ta ji ana koɗa shi a wani wurin, ga Haulatu kuwa, ta sha jinin jikinta don ba ta hangi inda za su sami matsagini a gidannan ba ita da mahaifiyarta. Umma kuwa ƙirjinta ke bugu da sauri-sauri, hatta da jikinta rawa yake yi. Ta daure ta shiga ambaton sunan Mahaliccinta. 


"Kun san hanyar kuwa?" Suka ji sautin Maigadin na tambaya. Kamar wasu ƙadangaru haka Hajiya Rabi da Haulatu suka shiga girgiza masa kai. 


"Hey! Siii!" Suka dubi wanda yake kira don su gaba daya yanda suka shagala da kallon gidan bai sa sun kula da wanzuwar wata halittar bayan su huɗun ba. Wani ne sanye da irin uniform din dake jikinsa, ga dukkan alamu shi dinma abokin aikinsa ne sai dai shi saurayi ne bai kai shi shekaru ba.  


"Kai su wajen Hajiya Babba."


Ya dube su, baki ya ɗan buɗe ganin Haulatu, da idanunsa suka sauka kan Umma kuwa, sai da ya ɗan fiddo idanu. 


"Wai ba ka ji ba?" Cewar babban a ɗan fusace hakan ya sa shi soma tafiya su na binsa a baya. 


Haulatu ta ƙirga gidaje masu kala iri guda biyar curr sai kuwa wasu gidajen a gefe guda masu kala daban. Har suka ƙarasa ɓangaren matar da aka ambata da Hajiya Babba ba su ci karo da kowa ba kai ka ce babu kowa sai su ɗin. Saurayin ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar, can babu jimawa aka buɗe. Wata ƴar dattijuwa ce.


"Baba Saude, ga baƙin Hajiya nan. Bismillah ku shiga."


Ya faɗi yana mai ba su wuri, Dattijuwar da aka kira da Baba Saude ta dube su, ta ƙurawa Umma idanu tana mai cika da ɗumbin al'ajabi da mamaki. Hanya ta ba su suka shiga ciki, har sannan kallonta take yi. 


"Wannan fa?" Ba ta san tayi furucin ba sai da ta ji Saurayin nan ya amshe zancen.


"Kema kin ga kamanninta da Hajjaju ko? Ba ƴar uwarku ce ba daga Malumfashi kuwa?"


Ya yi tambayar cike da son jin ƙwaƙwaf, Baba Saude ta harareshi. 


"To shaida, kai dai Bilya ban san sadda za ka shiga taitayinka ba. Wuce ni ka ban wuri."


Daga haka ta rufe ƙofar shi kuwa ya yi dariya ya bar wajen. 


Su Umma kuwa da Hajiya Rabi duka su na tsaye suna sauraronsu, ba su yi karambanin ƙarasawa cikin falon ba. Sai dai su na bin ko'ina da kallo, falon daidai gwargwado ya tsaru, har da wajen dinningtable a gefe, sai kuwa wani tafkeken talabijin a jikin bango dake faman aiki kai ka ce za ka yi magana na cikinsa ya amsa. Falon sai ƙamshin turaren wuta yake ga lafiyayyen kafet dake shimfiɗe. 


"Bismillah ku shigo ku zauna." Ba musu suka ƙarasa suka nemi wuri ƙasan kafet suka zauna. 


Baba Saude ta ƙaraso aka hau gaisuwa ita dai idanunta ya kasa kaucewa akan Umma da Haulatu masu tsantsar kama da Hajiya Babba. 


"Bari na yiwa Hajiyar magana." Daga nan ta miƙe ta nufi wani ɗan tsukakken wuri da aka yi bene. 


"Wai Allah, Allah ka yi mana arziki duniya da lahira. Hajiya Na'ima Allah yasa kun shigo a sa'a. Ni wallahi wannan fargabar da kike yi ne bana so, ki yi ta addu'a in sha Allahu komai zai tafi daidai. Naga gaba daya tun zuwanmu kin rasa sukuni."


Umma dai ɗan murmushi ta yi wanda ya fi kuka ciwo jin maganganun da Hajiya Rabi ke yi, amma dagaske a tsorace ta ke. Ko wace ce Hajiya Babbar nan? Ita ce mahaifiyarta ko kuma mahaifiyarta ma ta jima da rasuwa ne? Waɗannan tunane-tunanen su ne suka yi ta ƙara jefa ta cikin faɗuwar gaba. 


***

Hajiya Babba, tsohuwa mai ran ƙarfe. Yanayi na hutun da take ciki ya taimaka ƙwarai wurin ɓoye tsufanta. Allah ya yiwa zuri'a baiwa ta kyawun jiki. Tana zaune saman darduma hannunta riƙe da carbi bayan ta idar da sallar walha. Sallamar Baba Saude ce ya sa ta dubanta gami da yin gyaran murya na yi mata iznin shigowa. Ta shigo ta nemi gefe ta zauna. Mintuna uku kafin Hajiya Babba ta shafa addu'a ta dube ta. 


"Saude, akwai abin da ake buƙata?"


Cike da girmamawa Baba Saude ta amsa. 


"Ko ɗaya Hajiya, baƙi kika yi."


Hajiya Babba dake kokarin cire gilashin karatun da ta maƙala a fuskarta, ba tare da ta dube ta ba ta janyo gidan gilashin ta ce.


"Su waye haka da safe?"


"To, nima dai ban gane fuskokin ba. Ba zai wuce wasu cikin yan uwanku na Malumfashi ba don na ga kamanni."


Ta ɗan yi jim kafin ta amsa.


"Ikon Allah, ba damuwa, shigo da su nan."


Baba Saude ta mike bayan ta amsa mata da toh. Ita kanta za ta so sanin su waye a cikin dangin nasu don ba ta taɓa ganin fuskar ba sai a yau. Ta ƙarasa sauka gami da yi musu iznin su biyo ta. Suka mike suka soma taka matattakalar, Umma dai ƙirjinta dukan tara-tara yake. Yau ne karo na farko da za ta sadu da wani a cikin zuri'ar mahaifiyarta, ko wani irin tarba za ta samu? Allah masani. 


Sallamar Hajiya Rabi ce ta sa Hajiya Babba kallon hanya.


"Wa'alaikumussal..."


Sauran sallamar ya maƙale a bisa fatar bakinta sadda ta ci karo da photocopy ɗinta sadda take Hajiya Asma'unta. Umma ma kallonta take yi jikinta babu inda ba ya rawa, idan har wannan matar ba ta kasance Uwa a gareta ba, shakka babu jininta ce. 


"Asma'u Bello?" Umma ta samu bakinta da furucin cike da rawar murya. Hajiya Babba ta haɗiyi wani miyau maƙwat ya wuce jin sunanta ɓaro-ɓaro a bakin wannan baiwar Allah. Ga Haulatu kuwa ta dubi Ummanta ta dubi Tsohuwarnan, hakanan Hajiya Rabi da ta yi sandar tana ganin ikon Allah. Bambancin Na'ima da wannan tsohuwa sai fa shekaru. 


Umma kuwa, ambaton sunayen Allah da ta dinga jerawa a zuciyarta shi ya ba ta damar jin ƙarfin gwuiwar soma magana.


"Hajiya Asma'u Bello, wajenta na zo."


Hajiya Babba ta ji kirjinta ya buga, leɓɓanta suka yi nauyi. Kar dai ace allura ce za ta tono garma? Kada dai asirin da ta riga ta binne a bayanta, shi ne bai tashi tonuwa ba sai da shekaru suka miƙa har tafiya ta yi tafiya? Wani gumi ta ji ya tsirfo mata. Kafin ta kai ga ba da amsa ta tsinci muryar Baba Saude na fadin.


"Ai da ita kike magana Baiwar Allah. Wannan ɗin ita ce Hajiya Asma'u ake kiranta da Hajiya Babba. In ce dai lafiya?"


Jin haka yasa Umma ƙara kallon Hajiya Babba da gaba daya ta ruɗe. Ta rasa me za ta yi, murna ko baƙin ciki. Ɓangaren Haulatu kuwa, murmushi kawai take yi mai bayyana haƙora. Ita sosai ta ke jin wani dadi tana ƙara bin gidan da kallo sannan ta maida hankali ga tsohuwar da ta kasance kaka a wajenta. 


 "Wace ce ke? A ina kika san ni?" Tambayar da Hajiya Babba ta watsamata kenan. 


"Ku zauna mana kuna tsaye."

Cewar Baba Saude don ganin abin na yi ne. Bayan sun nemi wuri sun zauna ta baza kunnuwa don jin abin da zai fito daga bakin Umma. Sai dai madadin Umma ta yi magana, kawai sai ta sa hannu ta fiddo hoto ta miƙamata tare da wani abin hannu na azurfa mai kyau da ba ta taɓa karambanin fiddo shi ba ko a baya, ta yi mishi ajiya mai nisan da ko hoton ba ta adana haka ba domin shi din sunan Asma'un ne da Maikalangu a haɗe wuri guda. 


Hajiya Babba hannu na rawa ta karɓi hoton gami da abin hannun. 


"Saude ina gilashina?" Ta furta da rawar baki. 


Baba Saude ta cika da mamaki, da sauri ta dauki gilashin ta miƙamata, Hajiya Babba ta zura ta karanta rubutun dake jikin azurfar kafin ta kai duba ga hoton har da juya bayansa ta ga kwanan wata da kuma na gari da aka rubuta a jiki. Shikenan, ta faru ta ƙare wai an yiwa mai dami ɗaya sata! Yau ranar wanka ce da ba a ɓoyon cibi. 


  'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Hajiya Babba ta furta a zuciyarta. Ta ƙara ɗaga idanu ta dubi Umma wacce ta yi mata ƙuri da idanu ga hawaye kwance saman fuskarta.

Fitar tsiro

 Page 14

"Kina so ki cemin ke ƴar gidan Saleh ce?" Hajiya Babba ta fisgo tambayar daƙyar daga kwakwalwa zuwa harshenta. Murmushi mai ciwo Umma ta yi. 


"Ni ɗiyar Saleh da Asma'u ce. Akwai abin da kike tantama ne? Ko ki na so ki cemin kin manta sadda ki ka yi watsi da ni a bariki ba ki ƙara waiwayata ba?" 


"Bariki?" Faɗin Hajiya Rabi da Baba Saude a lokaci guda cike da wani irin mugun kaɗuwa. Ita Hajiya Rabi ai ba komai Hajiya Mama ta baje mata a faifai ba. Ga Baba Saude kuwa, kallon Hajiya Babba kawai ta ke yi, burinta ta ji gaskiyar zance daga bakinta. 


Gumi kawai Hajiya Babba ke yi, ranta ya ɓaci. Wato Saleh sai da ya karya alƙawarin da ya ɗaukarmata? Sun yi da shi duk runtsi ba zai taɓa barin ɗiyarsu ta san asalinta ba balle ta kawo kanta wataran ko kuma ya kawo ta, sun ƙulla wannan yarjejeniya shekaru masu yawa a baya wanda sanadin hakan ne ta yi mishi kyauta da wasu kuɗaɗe masu yawa da daraja irin na zamaninsu.


"Me kika zo nema a wurina yanzu? Wace buƙatar ce ta kawo ki?"


Haushi da bakin ciki suka mamaye zuciyar Umma, ta ma rasa me za ta ce.  Ita kuwa Haulatu wani irin kallo na mamaki take yiws Hajiya Babba. Ga ta nan dai a kallo ɗaya ta amsa sunanta da dattijuwar mace mai cikar kamala. Kalamanta sun bambanta da suffarta. 


"Granny! Granny!!"


Maganar ta yi daidai da ƙofar da aka buɗe na ɗaya daga cikin kofofi hudu dake a falon. Gaba daya suka dube ta,  yarinya ce da shekarunta za su kai biyar a duniya. Tawul fari ƙal ɗaure a ƙirjinta sai kuwa gashinta mai cika da baƙi wanda ya sha tufka da ribbon. Yanayin yadda ruwa ke zuba daga jikinta za ka fahimci wanka aka yi mata. Tana zuwa ta faɗa jikin Hajiya Babba tana fadin. 


"Granny, ki cewa Mami kar ta shafamin mai. Bana so."


Ya yi daidai da fitowar wacce ta kira da Mamin daga ɗaki hannunta riƙe da  kaya da kuma man shafawa na yara. 


"Ke Baby ki..."


Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon mutanen da ta gani zaune a falon, su dinma kallonta suka yi. Za ta yi shekaru ashirin a duniya, doguwa ce kuma baƙa mai ɗan jiki. Ta gaishe su mamaki dauke saman fuskarta na ganin wata mai ɗiban kama da ƴan gidansu. Wuri ta samu ta zauna kuwa. Hajiya Babba ta ture yarinyar.


"Maimuna, ja hannunta ku wuce ɗaki ina da baƙi."


"Baƙi kika ce fa Hajjaju? Ai ce mata za ki yi ɗiyarki ce da kika bar wa duniya ita ta dawo."


Muryar Haulatu ta zo musu a bazata, zuwa lokacin ta gama kai wa wuya dama, ta kula Hajiyar za ta kawo musu rainin hankali da wayo.  Hajiya Babba duban Haulatu ta yi amma ta kasa magana. Ita kuwa Maimuna sai ta yi turus cike da tsantsar kaɗuwa. 


"Assalamu alaikum." Aka faɗi da murya kakkaura. Hajiya Babba ba ta san sadda ta miƙe tsaye ba. Wannan shi ne abin da take jiyewa tsoro, babban burinta ta san yadda za ta yi da su Umma kafin wani ɗan uwan nata ya shigo. Baba Saude da Maimunatu suka gaishe shi. 


Dattijon mutum. Dogo mai cikar farin ƙasumba. Kallo ɗaya za ka fahimci girman da ya kama shi sosai. Dakta Suleiman B.S Malumfashi kenan. 


Ɗa na huɗu a wurin Marigayi Alhaji Bello. Su biyar ya haifa. Hajiya Asma'u ita ɗaya ce mace a cikinsu. Su uku kawai suka rage a yaransa. Shigowar da ya yi ta musamman ce, magana ya zo su yi da Hajiya Babba akan jikarta Maimuna da ta yo yaji kuma Hajiyar ta ɗauremata gindin zama. 


Umma ta dube shi, shi ma Dakta ita ya zubawa idanu yana amsa gaisuwar su Baba Saude. 


"Yaya, sannu da zuwa." Fadin Hajiya Babba da rawar baki. Idanunta nan da nan suka kawo ruwa tsabar tashin hankali. Yau dai abin da ta binne shekaru masu yawa zai tonu. 


"Yauwa. Asma'u, wace ce wannan din?"


Ya yi tambayar yana ƙara gyara zaman gilashinsa. Tuni Haulatu ta yi caraf ta ce. 


"Ni jikarta ce, wannan kuma (ta dafa kafaɗar Umma) ɗiyarta ce ta cikinta da ta haifa ta bar ta a hannun mahaifinta Saleh Mai Kalangu ba tare da ta ƙara waiwayon rayuwarta ba."


"Saleh Mai Kalangu?" Dakta ya maimaita sunan, shiru ya ɗan yi yana nazarin inda ya  taɓa sanin wannan suna kafin ya yi salati a fili yana duban Hajiya Babba wacce tun shigowarsa ta miƙe tsaye kawai sai ta fashe da kuka. 


"Asma'u, kodai ban ji da kyau ba. Ɗiyarku ke da Saleh Mai Kalangu? Wannan zancen gaske ne ko kuwa dai wasa ne aka zo a ynda hankulanmu?"


Ta kasa magana sai kukan, ranta na suya da zafi tana ji kamar ta kama Haulatu ta jibga tsabar yanda ta yi mata tonon silili a idanun mutumin da take yiwa kallon Uba kuma ɗan uwa mafi kusa da ita. Mutumin da ba ta taɓa ɓoyemasa komai ba kasancewarsu saƙo da saƙo kuma jininsu ya haɗu sosai fiye da sauran yayyunta maza. Yau dai ga babban sirrin da ba ta taɓa gigin sanar da shi ba. Bayan ita da wasu bayin Allah biyu da ta rayu da su a can wani gari, sai ko uban gayyar Saleh Mai Kalangu, babu wanda ya san da batun cikin Na'ima balle a san da wanzuwarta a doron ƙasa a dai nan garinsu Katsina. 


Shiru ma magana ce inji Hausawa, tabbas shirun da Hajiya Babba ya tabbatarwa Dakta zarginsa. 


"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un." Ya maimaita a karo na biyu. Wayarsa ya fiddo ya danna kira, yayansu babba da ya rage ya kira ya ce masa ga su nan zuwa da baƙi, magana ce mai muhimmanci. 


Yana katsewa ya dubi Hajiya Babba, gaba daya idanunsa sun kaɗa. 


"Ku muje can ɓangaren Alhaji a yi magana. Wannan ba ni zan yi hukunci ba."


Ya ƙarashe da jin ɗaci a maƙoshi. Daga haka ya sa kai ya fice daga falon bayan ya ba Maimuna umarnin ta yiwa su Umma jagora sashin Alhaji. 


***

  Babban falo ne mai dauke da ababen mora rayuwa daidai gwargwado. Tsaruwarsa ya shafe na sashin Hajiya Babba. Wani tsoho ne zaune saman dardumarsa ta ibada. A gefensa wasu matasa ne biyu wadanda duka ba su wuce shekara ashirin da takwas ko tara ba. Hira suke yi kafin wayar da Dakta ya yiwa Alhajin ta katse su. Ko bayan kammala wayar shiru suka yi baki daya domin da yawan lokuta Alhajin yana amsa waya ne ta hanyar sanya ta a handsfree. Wannan ya ba samarin damar jin abin da ya ce. Ɗaya a cikinsu wanda ya fi ɗan uwannasa jiki da kuma hasken fata ya miƙe. 


    "Bari na ƙarasa ofis kafin wancan Baturen ya kore ni."


Jin haka ɗayan ya yi dariya gami da faɗin. 


 "Kai Haidar, ka iya bakinka fa, ko ka mance a gaban amininsa ka ke? Wannan ɗan tsohon ko tusa aka yi sai ya fesa mishi."


Alhaji ya kai mishi duka da sandarsa dake ajiye a gefe. Aka yi dariya baki daya. Ya amsa.


"Ja'iri, kun fi kowa sanin ai Sadaukina daidai yake da ku. A hankali zai saita ku kowannenku ya shiga taitayinsa tunda na kula ku kam ba ku da aiki sai kashe-kashen kuɗi. Kai kuma mai kiransa da Bature kamar a kunnensa."


 Wanda aka kira da Haidar ya kama kunne.


"Tuba nake tsoho mai ran ƙarfe, Ango kuma miji gurin Hajja Bilkisu mai gadon zinare. Allah ya ja da ranka, idan ka mutu kuma Allah ya haɗaka da ita a aljanna."


"Amin, amma mutuwa kam ba yau ko gobe ba da yardar Allah. Ɓacemin kafin ka kashemin jiki."


Matasan suka tuntsire da dariya karo na ba adadi. Kafin su kai ga tashi sai ga sallamar Dakta, wannan ya sa duka suka ɗan nutsu. Dakta da Hajiya Babba suna daga cikin kakannin da sam ba su sakin fuska yadda ya dace ga jika. Babu ma kamar Hajiya Babba wacce ake masifar shakka idan ta tubure ta hau faɗa da bala'i akan duk abin da aka yi bai yi daidai da ra'ayinta ba. Ita ce ƙaramarsu amma su na ji da ita sosai don suna yawan cewa ita ɗin amana ce ta iyayensu, kuma sun musu Allah ya isa idan har sanadinsu ta shiga wani yanayin. Wannan ya sa ba a komai suke tsawatar mata ba sai idan sun ga tura ta kai bango. 


 Samarin suka gaida Dakta cike da girmamawa. Kafin su maida duba ga wadanda ke shigowa falon. Duban junansu suka yi da tsantsar mamaki. Bayan sun zauna sai ga Hajiya Babba itama ta shigo. 


Idanun Baba Dakta ya rufe bai ma nemi su Haidar su tashi ba ya korawa Alhaji komai da ya je ya tarar a sashin Hajiya Babba. Ya yi mishi nuni da Umma gami da ba ta umarnin ta tashi ta matso kusa. 


Umma ta miƙe ba musu har jiri take ji tsabar damuwar da ke cinta ga wani zafi da take ji daga ƙirjinta sai kuwa kai dake sara mata lokaci guda. Har Umma ta ƙaraso ta durƙusa gaban Alhaji ta ƙara gaida shi bakinsa bai bar furta sunayen Allah ba. Alhaji ya dubi Dakta kafin ya maida kai ga Hajiya Babba wacce ke faman kuka na takaicin wannan ranar. 


"Ya Allahu, Sule, ai wannan Asma'u ce zaune a gabana."


Dakta ya yi ƴar dariyar baƙin ciki. 


"Ita ce Yaya, ɗiyarta ce ta cikinta. Ta ɓoye mana bamu da labarinta. Haka iyayenmu ba su san da wanzuwarta ba har ƙasa ta rufe idanunsu. Watakila ba don Allah ya yi zamu san gaskiya ba, da har ƙasa ta rufe namu idanun ba mu da masaniya a kanta."


Haidar dai sun yi mugun kaduwa da jin wannan labari, wayarsa da ta yi ƙara ce ta sanya Dakta ankara da su. Nan ya ce maza su fice. Suka miƙe don su dai kam sun gama jin kan labarin. 


Suna fitowa Haidar ya dubi ɗan uwana Jabeer.


"Kai! Don Allah ɗan mintsile ni na ji ko dai mafarki nake?"


Jabeer da shima ya yi mutuwar tsaye don mamaki ya kuwa girgiza kai bakinsa a bude, can kuma ya yi wata ƴar ƙaramar ashariya ya ce.


"Kai! Yau akwai labari a gidan nan. Wai Allah, wa ya kamata na fara kira?"


Haidar ya yi wata dariya. 


"Amma ashe tsohuwarnan ma ta buga duniya har haka take neman shigar mana hanci da ƙudundune?  Kalli fa kamanni kamar ta yi kaki. Ai wallahi wannan ta fi kama da ita akan Anti Maryam. Kai! Akwai fa labari a gidannan! Ai mu shiga group kawai."


Suka yi dariya, dariya irin ta mamaki da kuma ganin bala'i da masifar da abu kaɗan Hajiya Babba ta jefa akan jikokinta da ma wasu a yaran ƴan uwannata, sai ga su nan sun bayyana a tattare da ita. Suna da yaƙinin cewa labarin nan zai girgiza wannan zuri'a ta su. 


***

  Hajiya Babba ta dubi Alhaji bayan ta gyara zama. Alhaji ya jefamata tambaya har sau kusan uku akan dagaske ɗiyarta ce amma ta kasa amsawa, sai a yanzun da ya haɗa da tsawa cikin muryarsa ta tsufa kafin ta yi yunƙuri na ba shi amsa. Haulatu kawai harararta take yi don a farkon ganin tsohuwar ta ji ta burgeta, sai dai a yanzu kam ji take yi babu wacce ta tsana sama da ita tun daga yadda ta nunamusu da farko.


 "Eh, ɗiyata ce da na haifa tare da Saleh."


Ta ba da amsa kai tsaye, Umma ta sunkuyar da kai gami da lumshe idanu, hawaye kawai ke fita daga idanunta. Alhaji ya yi salati.


"Ɗiyarki ce dai kenan Asma'u. Garin ya ya haka ta faru? Kin ce mana guduwa kawai ki ka yi daga gida kuma kika dawo bayan zuciyarki ta yi sanyi. Kin nuna mana ke ba Saleh kika bi ba, Asma'u wannan maganar kuma daga ina ta ɓullo?"


Girgiza kai Hajiya Babba ta yi, wannan masifa da me ta yi kama? Meyasa asirinta bai tashi tonuwa ba sai bayan da tsufa ya zo mata? Kai, ita ta ma yi zaton tunda har labari ya risƙeta na mutuwar Saleh tun a baya, to ɗiyar itama ta mutu. Ashe dai dama  akwai sauran rina a kaba? Ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara duban Umma karo na barkatai sannan ta maida duba ga yayyunta. 


"Ranar wanka haƙiƙa ba a ɓoyon cibi, saboda ita Na'ima, zan ba da labarin komai tun farko har zuwa lokacin da na dawo gida wajenku. Da kuma irin rufi na asiri da marigayi mijina Yusufa ya yimin sadda muka yi aure."


Gaba daya hankali sai ya koma kan Hajiya Babba har Umma. 


***

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 15

"Bayan na kai minzalin da ya dace na shiga makaranta, a lokacin ne na tayar da hankalinsa kan lallai nima ina so na dinga zuwa makaranta tunda ina ji ina gani wani yaro ɗan wata a gidan da ake kira Farida Kulɓa yana zuwa. Yaro ne da ya girme ni da kadan a lokacin, kuma shi ya kasance shege, amma tana ji da shi kamar me. Ganin haka a dole Baba ya sanya ni, tare muke zuwa da yaron nan, Huzaifa. Mu sha zagi kala-kala a wurin ɗalibai har da wasu malaman da ke yawan kiranmu su na bugar cikinmu don jin ko bamu da wasu yan uwa ne muka yarda da zama hannun iyayenmu a gidan ƴan bariki? Wasu lokutan har kuka nake yi, a sannan shi Huzaifa yana firamare aji na hudu. Shi zai yi ta lallaɓa ni yana nunamin nayi hakuri ai tunda dai iyayenmu na son mu shikenan. Hatta makarantar islamiyya ina zuwa. Alokacin ne kuma Baba ya yi aure da wata ƙabila mai suna Iyabo. Ya maida ni hannunta, a gaban idanunsa ta nunamin kauna da so, a bayan idanunsa kuwa babu kalar azabar da ba ta yimin. Har wankin kaya take saka ni, tun ban iyaba saboda ƙarancin shekaru har na koya don dole. Iyabo sai ta hana ni abinci tun safe har sai na galabaita kafin ta ba ni. Ga shi nan idan Baba ba ya gida sai ta yi ta kawo mishi wasu mazan, idan sun tafi ta kama ni ta ja min kunnuwa tare da kashedi akan muddin na sake na faɗamasa sai ta kashe ni. Na kuma amince za ta aikata tunda har cokali ta taɓa sanyawa cikin garwashi ta manna min a cinya kawai don na Baba ya tambaye ni batun karatuna nace masa na fi sati ban je ba. Wasa-wasa Iyabo sai da ta kashemin karatu, tun Baba na maida hankali ga tambaya, na rasa dalili har shima ya yi watsi da maganar. Makarantar islamiyya kam shi ma tana bari naje ne a dole saboda ina yi mata cinikin cincin. A ƙarshe ma ta hana ni zuwa ta koma ɗoramin tallah. Shi Baba idan ya kaɗa harkar barikinsa sai ya kwashe sati biyu ma bamu sanya shi a idanu ba. Haka har na kai shekaru goma sha uku a duniya cikin wahala da ƙuncin rayuwa. Ance ba'a sabo da wahala ba don haka ba sai ince na saba da wahalar Iyabo. Idan zan mutu ina rashin lafiya kallo ban ishe ta ba. Duk tsananin ruwa idan Iyabo ba ta so ba, ban isa na shigar mata ɗaki ba sai dai na kwana a waje. Idan naji ruwan ya yi ƙarfi ne nake komawa zauren gidan kusa da tumakanta na keɓe. Babu zato ba tsammani, watarana da daddare ana muku-mukun sanyi, ina zaure na ƙudundune sakamakon Iyabo ta yi wani baƙon watsewarta suna ɗakin. Ta kuma rantse ko kwakkwarar motsina ta ji sai ta fito ta yankamin wuya. Wannan ta sanya tari kwakkwara ma na kasa yi. Ba zato Baba ya bude gidan da mukullinsa ya shigo. Haske ni ya yi sosai da tocila yana tambayar.


"Wace a nan? Na'imatu! Me kike yi anan cikin wannan uban sanyin? Maza tashi." 


Ya ƙarashe zancen nasa yana mai sa hannu ya kama nawa hannun da sanyi ya kama tamkar an jefa cikin ƙanƙara, haƙorana kuwa kar-kar kawai suke yi suna gugar da juna. Sam Iyabo ba su ji motsi ba, ya ga na tsaya ƙyam na ƙi yarda mu shiga koda falonta ne, kafin ya kai ga yimin magana ya ji muryar wani namijin ba shiri ya saki hannuna ya faɗa ɗakin. Can ba jimawa mutumin ya fito a guje har ya a tunkuɗeni ina zubewa a ƙasa. Ba jimawa kuma na ji ihun kukan Iyabo na tashi, Baba na jibgarta. Haka har ya fito da ita waje, runtse idanuna nayi ganin babu ko kaya a jikinta, a kan kunnuwana ya yi mata saki ya kuma dura mata ashar kala-kala. 

  Da wannan aurensu ya ƙare, zamana ya ƙara komawa gidan ƴan bariki. Rayuwar a sannan ta zama mafi hatsari gareni fiye da baya saboda maza da dama na kawomin hari amma Allah yana tsallakar da ni. Fir na ƙi makaranta saboda habaici da zagi da ɗalibai ke yimin. Wasu na kira na ƴar iska wasu kuwa shegiya kai tsaye. 

  Da na ƙara shekaru na ƙara yin hankali na shiga damuwa sosai, rayuwar gidan ta ficemin a kaina. Kullum cikin takurawa Baba nake yi kan ya kai ni ga Mamana ko yaya take zan zauna da ita. Da dai ya ga abin ya ishe shi ya zaunar da ni ya cemin ai ta tsane ni ba ta sona. Ya kuma ce koda na je wajenta ba za ta taɓa kallona ba. Hakan ya ƙara sanya mini tsanarta cikin raina. Ban ƙara tada maganarsa ba. Ina da shekaru sha shida ne aka soma kawomin hari fiye da baya. Cikinsu har da Ibrahim Ɗanmutuwa, mahaifin Haulatu. Su na cikin samari masu ji da kai da kuma gayu da kudaden da suke burge yanmatansu na bariki. Ba su da aiki sai caca, Babana na daga cikin masu zama a gefe suna waasa su, su kuwa hakan yana ƙara fasamusu kai. A duniyar ƴan caca babu wanda Babana ke so da yawan kurantawa kamar Ɗanmutuwa. Koda dai an masa shaidar cewa babu wata caca da za'a buga tare da shi bai ci ba. A lissafe ma bai fi sau biyu rak! Aka taɓa nasara a kansa ba. 

    Sanadiyyar wani wawan cin ganima da Ɗanmutuwa ya yi a wurin wasan su na caca, shi ya ja Baba yi masa alƙawarin aura masa ni. Wannan magana ta fi komai yiwa Ɗanmutuwa daɗi, a duniyarsa dama ya ɗauke ni kamar wata abar wasansa, abin nufi, tun sadda abokansa suka hau cin alwashin aurena, wasu kuwa na su bai wuce samun galaba a kaina ba, shi ma ya dauki nasa alwashin sai dai wayo da dabara bai sa ya furta musu ba. Lokacin da suke daukar alwashi a kaina, ina daga zaure ina jinsu, ban mance ba ma fita nayi zuwa kanti siyo sukari, a hanyar dawowa suka fara zancena, koda na karasa shigewa gida sai da na dakata na ji inda zancen nasu ya tsaya don ina tsoron su ƙulla wani abun da za su cutar da ni ba tare da na sani ba. 


    Maganar aurena da Ɗanmutuwa ba ƙaramin tayar da hankalina ya yi ba. Duk irin roƙo da koke-koken da na yi bai sauya komai daga ɓangaren Baba ba. Kai kusan ma dai kyauta aka ba shi ni, don duka-duka kudin sadaki kawai ya bayar aka ɗaura aurenmu a wani masallaci. Baba shi ya zama waliyinsa. A cewar Baba, Ɗanmutuwa  asalinsa shima Bakatsine ne, amma iyayensa sun mutu. Danginsa kuwa ba su damu da rayuwarsa ba shi ne dalilin shigowarsa Kano neman kudi. Ni dai ba ni da ta cewa. Babu abin da kuma ya kaɗamin ƴaƴan hanji sai ganin tun ranar farko da aka kai ni, na so na yi gardama ya zanemin jiki tas ya yi kuma abin da ya ga dama da ni. Wannan ya haifarmin da mugun shakkarsa, ga shan kayan maye. Haka na rayu da shi cikin ƙunci da rashin galihu, ciki kuwa da na samu yake ba ni magani ya zube. A cewarsa sam, bai kai shekarun tara iyali ba. Ban mancewa har mata yake kawomin cikin gida, ranar da ya fara na nunamasa fushina ya kama ni ya jibga ya kuma ƙulle a ɗaki tun dare bai buɗe ni ba dai washegari da rana. Alokacin na galabaita babu ci babu sha balle a yi batun sallah. Kai tsaye ruwan wanka ya sanya na ɗora musu, a dole jikina har rawa yake yi na kunna risho na dora, ga jiri da nake sakamakon yunwa.

  Babban takaicina bai wuce yadda Baba bai taɓa takowa don duba lafiyata ba kamar dama shi ɗin ma ya gaji da ni neman hanyar rabuwa kawai yake yi da ɗawainiyata. Sai da na shafe shekara ban sa Baba a idanu ba, ko na tambayi Ɗanmutuwa cemin yake yi yana bariki. Wannan amsar ba ta yimin dadi sam, hakan ya sa na ja bakina na yi shiru ban ƙara maganar ba. 

  Ɗanmutuwa bai fasa zubarmin da ciki ba, sai a kan Haulatu ne Allah ya yi ikonsa domin jan bakina nayi na yi shiru ban faɗi ba. Kuma sai Allah ya taimake ni cikin har ya shiga watanni bakwai hankalinsa bai kai gareni ba, kusan ma ya fi maida hankali da harkokin gabansa. Sadda ya farka da cikin kuwa, ranar na sha baƙar azaba kai ka ce kashe ni zai yi. Cikin wannan halin baƙin cikin na haifi Haulatu, makwafciyata ce ta taimakamin da zuwa asibiti da komai. Wannan taimako da na samu shi ya jawo muka tashi daga unguwar muka koma wata, acewarsa makwaftan sun masa shishshigi kuma har suna ikrarin haɗa shi da hukuma kan ya bar ni a gida ina naƙuda tsawon sati bai ko damu ba. Su ne suka siyamin kayayyakin amfani na jariri da ma nawa. Sosai ya ji haushinsu.

 tafi kafin report din ya fito.


Suna baro office din Sir Ashir Kai tsaye kaantes suka nufa sbd babu Wanda ya zauna ya huta tinda suka dawo suke yawo.


Suna Isa Amnah da gudu tazo ta fada jikin dadynta ya dagata sama Yana sake Jin tsananin so da kaunarta cikin zuciyarsa sbd sai yanzu ne ya tabbatarda yarinyar marainiyace gaba da baya Ashe bayan rashin Uba harda mahaifiyarta ta rasa,Amma ko yayane dai yasan bazata taba maraicin ba bare tasan ma ba sune suka haifetaba.


Gurin Umme suka nufa suka gaisa itama Umme cikeda farin ciki da tsananin son danta ta rungumesa tana hawaye sbd masifun Nan sun fara musu yawa daga anfita wannan Se wannan.


Kofan dakin Bena ya sauke idanuwansa zuciyansa na Wani irin yankawa Dan haka ya miqe yabar sashen ya nufi nasa.


Baiyi mamakin rashin tadda Safnah ba Dan haka Bai Wani damu ba ya wuce bedroom dinsa wanka yafara Yi ya samu Dan qarfin jiki ya fito ya shirya cikin black Balmain Riga da wando yayi sallah 

Yana idarwa Nafisat da Amnah suka kawo masa light abinci da Umme ta dafa masa da kanta.


Bazai iya cin komai ba dan babu Abinda yake masa daidai a jiki da Zuciya harma da bakin.


Amnah a gurinsa ta kwana bayan tayita tambayan Ina mummy dinta shi baisan me zai fada mata ba sbd Shima kaman zaiyi hawayen ne kaman yanda itama takeyi,riqe Kansa kawai yakeyi sbd kada taga hawayensa ta daga hankalinta kokuma tasan Wani Abu ya samu mummy din nata.Har gari ya waye Bai iya rintsawa ba Dan haka zazzabi zazzabi ke Neman shigarsa sbd Bai Saba da qunci da damuwa ba bare wahalan tinani.


Daga shi har Amnah kusan zazzabin suka kwana dashi suka tashi dashi Dan Daman ita matiqar mummy dinta Bata tareda ita kusan kullum zazzabin dare takeyi sbd ta Saba shigewa jikin mummynta tayi bacci cikin tsananin so da kulawan Mummyn.


Hakanan Kansa na ciwo yayi sallar Asuba suna idarwa kusan dukkaninsu a tare suka jima masallacin Saida gari yayi haske kafin suka fito ko ciki Basu qarasa ba Kiran Sir Ashir bello ya shigo wayar dd babban dake hannun Abbakar Kuma shine ya dauka yaji sakon Sir Ashir din Wanda Shima Bai rintsaba ko kadan shi da yaransa kwana sukai Aiki da bincike tareda zuwa gidan DD na highbridge suka duba fingerprints na Safnah dake gidan wanda yazo daidai da Wanda yaje jikin ledan da DD yakai musu hakama same fingerprints ne dake jikin motan da Bena tayi accident da ita kwanakin baya da ake bincike Akai itama a boye da dd babab ya saka.


Shiru Abbakar yayi bayan kashe wayar Sir Ashir bello din Yana Rasa ta yanda zai isar da bayanin da Neman da Sir Ashir din ke musu.


Dukkaninsu musamman DD da idanuwansa sukafi na iyayen nasa kaifin kwarjini suka zuba masa suna jiran Abinda zai fada shikuwa so yeke iya dd babba zai isarwa sakon.


DD da ransa ya Baci ya hade fuska dakyau tareda kallan Abbakar cikin kamewa da Bata Rai yace


"Banajin akwai sauran Abinda ake boyewa Wanda bansaniba,idanma akwai zan sani ayau din,.ka fada me Sir Ashir bello din yace,Ina sauraronka."


Shiru Abbakar yayi kafin ya Kalli dd babba Wanda Shima yanzu sakon kawai yake buqatan sani shikuwa dad kaante kallan mamaki duka yake musu sbd baisan binciken me duk suke jiran sakamakonsa har haka cikin daga hankali ba.


Numfashi Abbakar ya sake Yana San kasa kallan DD yace


"Sir Ashir Yana buqatan ganinka acan sbd kace baka buqatan zuwansa Nan koyaushe kawo report sbd kada a ankarar da yan jarida Amma yace Yana buqatan zuwanka sbd sakamakonsa komai ya fita na qwayoyin da aka shayar da DD da Wanda aka shayar da kakarsu Bena harma da sakamakon binciken accident din Bena.....


Wani irin Kallo DD yayiwa dd babba cikin matsanancin mamaki da zuciyarsa dake daukan Wani nauyi da harbawa ba daidaiba sbd Bai taba sanin accident din Bena bana Allah bane akwai zargin da akeyi akan Hakan shine aka boye masa akwai Wanda ke bibiyab matarsa da Wani sharri,

Meyasa zaa boye masa dan kuwa da tini zai fara Bata kariyar da ko Kansa bai sametaba.


Shi Kansa dad kaante mamakin ya shiga sosai Yafara rarraba idanuwa cikin firgicin meyake faruwa da familyn nasu wai.


Dd babba kuwa Kai tsaye Bai iya cewa kowa komaiba ya wuce gaba Abbakar na bayansa ya je ya dauko key din motarsa da sauri.


Shima DD Kai tsaye Naseer ya kira Wanda Shima ranar a cikin Kaantes ya kwana take ya fito cikin qananun guntayen kaya Shima ya tada motar DD din Suma suka rufawa dd babba baya 

Dad kaante na kasa tsayawa yayi Dan andena barinsa Baya tinda Shima babba ne a familyn ya dauko key da Kansa Bai tsaya Kiran driver dinsa ba yaja ya mara musu baya.


dd babba ne yafara Isa yau Yana fatan komai yazo karshe sbd zarginsa da hankalinsa Daya kasa kwanciya akan matar DD Dan haka baya cewa komai har suka Isa 


Fitar tsiro

 Page 14

"Kina so ki cemin ke ƴar gidan Saleh ce?" Hajiya Babba ta fisgo tambayar daƙyar daga kwakwalwa zuwa harshenta. Murmushi mai ciwo Umma ta yi. 


"Ni ɗiyar Saleh da Asma'u ce. Akwai abin da kike tantama ne? Ko ki na so ki cemin kin manta sadda ki ka yi watsi da ni a bariki ba ki ƙara waiwayata ba?" 


"Bariki?" Faɗin Hajiya Rabi da Baba Saude a lokaci guda cike da wani irin mugun kaɗuwa. Ita Hajiya Rabi ai ba komai Hajiya Mama ta baje mata a faifai ba. Ga Baba Saude kuwa, kallon Hajiya Babba kawai ta ke yi, burinta ta ji gaskiyar zance daga bakinta. 


Gumi kawai Hajiya Babba ke yi, ranta ya ɓaci. Wato Saleh sai da ya karya alƙawarin da ya ɗaukarmata? Sun yi da shi duk runtsi ba zai taɓa barin ɗiyarsu ta san asalinta ba balle ta kawo kanta wataran ko kuma ya kawo ta, sun ƙulla wannan yarjejeniya shekaru masu yawa a baya wanda sanadin hakan ne ta yi mishi kyauta da wasu kuɗaɗe masu yawa da daraja irin na zamaninsu.


"Me kika zo nema a wurina yanzu? Wace buƙatar ce ta kawo ki?"


Haushi da bakin ciki suka mamaye zuciyar Umma, ta ma rasa me za ta ce.  Ita kuwa Haulatu wani irin kallo na mamaki take yiws Hajiya Babba. Ga ta nan dai a kallo ɗaya ta amsa sunanta da dattijuwar mace mai cikar kamala. Kalamanta sun bambanta da suffarta. 


"Granny! Granny!!"


Maganar ta yi daidai da ƙofar da aka buɗe na ɗaya daga cikin kofofi hudu dake a falon. Gaba daya suka dube ta,  yarinya ce da shekarunta za su kai biyar a duniya. Tawul fari ƙal ɗaure a ƙirjinta sai kuwa gashinta mai cika da baƙi wanda ya sha tufka da ribbon. Yanayin yadda ruwa ke zuba daga jikinta za ka fahimci wanka aka yi mata. Tana zuwa ta faɗa jikin Hajiya Babba tana fadin. 


"Granny, ki cewa Mami kar ta shafamin mai. Bana so."


Ya yi daidai da fitowar wacce ta kira da Mamin daga ɗaki hannunta riƙe da  kaya da kuma man shafawa na yara. 


"Ke Baby ki..."


Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon mutanen da ta gani zaune a falon, su dinma kallonta suka yi. Za ta yi shekaru ashirin a duniya, doguwa ce kuma baƙa mai ɗan jiki. Ta gaishe su mamaki dauke saman fuskarta na ganin wata mai ɗiban kama da ƴan gidansu. Wuri ta samu ta zauna kuwa. Hajiya Babba ta ture yarinyar.


"Maimuna, ja hannunta ku wuce ɗaki ina da baƙi."


"Baƙi kika ce fa Hajjaju? Ai ce mata za ki yi ɗiyarki ce da kika bar wa duniya ita ta dawo."


Muryar Haulatu ta zo musu a bazata, zuwa lokacin ta gama kai wa wuya dama, ta kula Hajiyar za ta kawo musu rainin hankali da wayo.  Hajiya Babba duban Haulatu ta yi amma ta kasa magana. Ita kuwa Maimuna sai ta yi turus cike da tsantsar kaɗuwa. 


"Assalamu alaikum." Aka faɗi da murya kakkaura. Hajiya Babba ba ta san sadda ta miƙe tsaye ba. Wannan shi ne abin da take jiyewa tsoro, babban burinta ta san yadda za ta yi da su Umma kafin wani ɗan uwan nata ya shigo. Baba Saude da Maimunatu suka gaishe shi. 


Dattijon mutum. Dogo mai cikar farin ƙasumba. Kallo ɗaya za ka fahimci girman da ya kama shi sosai. Dakta Suleiman B.S Malumfashi kenan. 


Ɗa na huɗu a wurin Marigayi Alhaji Bello. Su biyar ya haifa. Hajiya Asma'u ita ɗaya ce mace a cikinsu. Su uku kawai suka rage a yaransa. Shigowar da ya yi ta musamman ce, magana ya zo su yi da Hajiya Babba akan jikarta Maimuna da ta yo yaji kuma Hajiyar ta ɗauremata gindin zama. 


Umma ta dube shi, shi ma Dakta ita ya zubawa idanu yana amsa gaisuwar su Baba Saude. 


"Yaya, sannu da zuwa." Fadin Hajiya Babba da rawar baki. Idanunta nan da nan suka kawo ruwa tsabar tashin hankali. Yau dai abin da ta binne shekaru masu yawa zai tonu. 


"Yauwa. Asma'u, wace ce wannan din?"


Ya yi tambayar yana ƙara gyara zaman gilashinsa. Tuni Haulatu ta yi caraf ta ce. 


"Ni jikarta ce, wannan kuma (ta dafa kafaɗar Umma) ɗiyarta ce ta cikinta da ta haifa ta bar ta a hannun mahaifinta Saleh Mai Kalangu ba tare da ta ƙara waiwayon rayuwarta ba."


"Saleh Mai Kalangu?" Dakta ya maimaita sunan, shiru ya ɗan yi yana nazarin inda ya  taɓa sanin wannan suna kafin ya yi salati a fili yana duban Hajiya Babba wacce tun shigowarsa ta miƙe tsaye kawai sai ta fashe da kuka. 


"Asma'u, kodai ban ji da kyau ba. Ɗiyarku ke da Saleh Mai Kalangu? Wannan zancen gaske ne ko kuwa dai wasa ne aka zo a ynda hankulanmu?"


Ta kasa magana sai kukan, ranta na suya da zafi tana ji kamar ta kama Haulatu ta jibga tsabar yanda ta yi mata tonon silili a idanun mutumin da take yiwa kallon Uba kuma ɗan uwa mafi kusa da ita. Mutumin da ba ta taɓa ɓoyemasa komai ba kasancewarsu saƙo da saƙo kuma jininsu ya haɗu sosai fiye da sauran yayyunta maza. Yau dai ga babban sirrin da ba ta taɓa gigin sanar da shi ba. Bayan ita da wasu bayin Allah biyu da ta rayu da su a can wani gari, sai ko uban gayyar Saleh Mai Kalangu, babu wanda ya san da batun cikin Na'ima balle a san da wanzuwarta a doron ƙasa a dai nan garinsu Katsina. 


Shiru ma magana ce inji Hausawa, tabbas shirun da Hajiya Babba ya tabbatarwa Dakta zarginsa. 


"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un." Ya maimaita a karo na biyu. Wayarsa ya fiddo ya danna kira, yayansu babba da ya rage ya kira ya ce masa ga su nan zuwa da baƙi, magana ce mai muhimmanci. 


Yana katsewa ya dubi Hajiya Babba, gaba daya idanunsa sun kaɗa. 


"Ku muje can ɓangaren Alhaji a yi magana. Wannan ba ni zan yi hukunci ba."


Ya ƙarashe da jin ɗaci a maƙoshi. Daga haka ya sa kai ya fice daga falon bayan ya ba Maimuna umarnin ta yiwa su Umma jagora sashin Alhaji. 


***

  Babban falo ne mai dauke da ababen mora rayuwa daidai gwargwado. Tsaruwarsa ya shafe na sashin Hajiya Babba. Wani tsoho ne zaune saman dardumarsa ta ibada. A gefensa wasu matasa ne biyu wadanda duka ba su wuce shekara ashirin da takwas ko tara ba. Hira suke yi kafin wayar da Dakta ya yiwa Alhajin ta katse su. Ko bayan kammala wayar shiru suka yi baki daya domin da yawan lokuta Alhajin yana amsa waya ne ta hanyar sanya ta a handsfree. Wannan ya ba samarin damar jin abin da ya ce. Ɗaya a cikinsu wanda ya fi ɗan uwannasa jiki da kuma hasken fata ya miƙe. 


    "Bari na ƙarasa ofis kafin wancan Baturen ya kore ni."


Jin haka ɗayan ya yi dariya gami da faɗin. 


 "Kai Haidar, ka iya bakinka fa, ko ka mance a gaban amininsa ka ke? Wannan ɗan tsohon ko tusa aka yi sai ya fesa mishi."


Alhaji ya kai mishi duka da sandarsa dake ajiye a gefe. Aka yi dariya baki daya. Ya amsa.


"Ja'iri, kun fi kowa sanin ai Sadaukina daidai yake da ku. A hankali zai saita ku kowannenku ya shiga taitayinsa tunda na kula ku kam ba ku da aiki sai kashe-kashen kuɗi. Kai kuma mai kiransa da Bature kamar a kunnensa."


 Wanda aka kira da Haidar ya kama kunne.


"Tuba nake tsoho mai ran ƙarfe, Ango kuma miji gurin Hajja Bilkisu mai gadon zinare. Allah ya ja da ranka, idan ka mutu kuma Allah ya haɗaka da ita a aljanna."


"Amin, amma mutuwa kam ba yau ko gobe ba da yardar Allah. Ɓacemin kafin ka kashemin jiki."


Matasan suka tuntsire da dariya karo na ba adadi. Kafin su kai ga tashi sai ga sallamar Dakta, wannan ya sa duka suka ɗan nutsu. Dakta da Hajiya Babba suna daga cikin kakannin da sam ba su sakin fuska yadda ya dace ga jika. Babu ma kamar Hajiya Babba wacce ake masifar shakka idan ta tubure ta hau faɗa da bala'i akan duk abin da aka yi bai yi daidai da ra'ayinta ba. Ita ce ƙaramarsu amma su na ji da ita sosai don suna yawan cewa ita ɗin amana ce ta iyayensu, kuma sun musu Allah ya isa idan har sanadinsu ta shiga wani yanayin. Wannan ya sa ba a komai suke tsawatar mata ba sai idan sun ga tura ta kai bango. 


 Samarin suka gaida Dakta cike da girmamawa. Kafin su maida duba ga wadanda ke shigowa falon. Duban junansu suka yi da tsantsar mamaki. Bayan sun zauna sai ga Hajiya Babba itama ta shigo. 


Idanun Baba Dakta ya rufe bai ma nemi su Haidar su tashi ba ya korawa Alhaji komai da ya je ya tarar a sashin Hajiya Babba. Ya yi mishi nuni da Umma gami da ba ta umarnin ta tashi ta matso kusa. 


Umma ta miƙe ba musu har jiri take ji tsabar damuwar da ke cinta ga wani zafi da take ji daga ƙirjinta sai kuwa kai dake sara mata lokaci guda. Har Umma ta ƙaraso ta durƙusa gaban Alhaji ta ƙara gaida shi bakinsa bai bar furta sunayen Allah ba. Alhaji ya dubi Dakta kafin ya maida kai ga Hajiya Babba wacce ke faman kuka na takaicin wannan ranar. 


"Ya Allahu, Sule, ai wannan Asma'u ce zaune a gabana."


Dakta ya yi ƴar dariyar baƙin ciki. 


"Ita ce Yaya, ɗiyarta ce ta cikinta. Ta ɓoye mana bamu da labarinta. Haka iyayenmu ba su san da wanzuwarta ba har ƙasa ta rufe idanunsu. Watakila ba don Allah ya yi zamu san gaskiya ba, da har ƙasa ta rufe namu idanun ba mu da masaniya a kanta."


Haidar dai sun yi mugun kaduwa da jin wannan labari, wayarsa da ta yi ƙara ce ta sanya Dakta ankara da su. Nan ya ce maza su fice. Suka miƙe don su dai kam sun gama jin kan labarin. 


Suna fitowa Haidar ya dubi ɗan uwana Jabeer.


"Kai! Don Allah ɗan mintsile ni na ji ko dai mafarki nake?"


Jabeer da shima ya yi mutuwar tsaye don mamaki ya kuwa girgiza kai bakinsa a bude, can kuma ya yi wata ƴar ƙaramar ashariya ya ce.


"Kai! Yau akwai labari a gidan nan. Wai Allah, wa ya kamata na fara kira?"


Haidar ya yi wata dariya. 


"Amma ashe tsohuwarnan ma ta buga duniya har haka take neman shigar mana hanci da ƙudundune?  Kalli fa kamanni kamar ta yi kaki. Ai wallahi wannan ta fi kama da ita akan Anti Maryam. Kai! Akwai fa labari a gidannan! Ai mu shiga group kawai."


Suka yi dariya, dariya irin ta mamaki da kuma ganin bala'i da masifar da abu kaɗan Hajiya Babba ta jefa akan jikokinta da ma wasu a yaran ƴan uwannata, sai ga su nan sun bayyana a tattare da ita. Suna da yaƙinin cewa labarin nan zai girgiza wannan zuri'a ta su. 


***

  Hajiya Babba ta dubi Alhaji bayan ta gyara zama. Alhaji ya jefamata tambaya har sau kusan uku akan dagaske ɗiyarta ce amma ta kasa amsawa, sai a yanzun da ya haɗa da tsawa cikin muryarsa ta tsufa kafin ta yi yunƙuri na ba shi amsa. Haulatu kawai harararta take yi don a farkon ganin tsohuwar ta ji ta burgeta, sai dai a yanzu kam ji take yi babu wacce ta tsana sama da ita tun daga yadda ta nunamusu da farko.


 "Eh, ɗiyata ce da na haifa tare da Saleh."


Ta ba da amsa kai tsaye, Umma ta sunkuyar da kai gami da lumshe idanu, hawaye kawai ke fita daga idanunta. Alhaji ya yi salati.


"Ɗiyarki ce dai kenan Asma'u. Garin ya ya haka ta faru? Kin ce mana guduwa kawai ki ka yi daga gida kuma kika dawo bayan zuciyarki ta yi sanyi. Kin nuna mana ke ba Saleh kika bi ba, Asma'u wannan maganar kuma daga ina ta ɓullo?"


Girgiza kai Hajiya Babba ta yi, wannan masifa da me ta yi kama? Meyasa asirinta bai tashi tonuwa ba sai bayan da tsufa ya zo mata? Kai, ita ta ma yi zaton tunda har labari ya risƙeta na mutuwar Saleh tun a baya, to ɗiyar itama ta mutu. Ashe dai dama  akwai sauran rina a kaba? Ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara duban Umma karo na barkatai sannan ta maida duba ga yayyunta. 


"Ranar wanka haƙiƙa ba a ɓoyon cibi, saboda ita Na'ima, zan ba da labarin komai tun farko har zuwa lokacin da na dawo gida wajenku. Da kuma irin rufi na asiri da marigayi mijina Yusufa ya yimin sadda muka yi aure."


Gaba daya hankali sai ya koma kan Hajiya Babba har Umma. 


***

[04/09, 1:44 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 15

"Bayan na kai minzalin da ya dace na shiga makaranta, a lokacin ne na tayar da hankalinsa kan lallai nima ina so na dinga zuwa makaranta tunda ina ji ina gani wani yaro ɗan wata a gidan da ake kira Farida Kulɓa yana zuwa. Yaro ne da ya girme ni da kadan a lokacin, kuma shi ya kasance shege, amma tana ji da shi kamar me. Ganin haka a dole Baba ya sanya ni, tare muke zuwa da yaron nan, Huzaifa. Mu sha zagi kala-kala a wurin ɗalibai har da wasu malaman da ke yawan kiranmu su na bugar cikinmu don jin ko bamu da wasu yan uwa ne muka yarda da zama hannun iyayenmu a gidan ƴan bariki? Wasu lokutan har kuka nake yi, a sannan shi Huzaifa yana firamare aji na hudu. Shi zai yi ta lallaɓa ni yana nunamin nayi hakuri ai tunda dai iyayenmu na son mu shikenan. Hatta makarantar islamiyya ina zuwa. Alokacin ne kuma Baba ya yi aure da wata ƙabila mai suna Iyabo. Ya maida ni hannunta, a gaban idanunsa ta nunamin kauna da so, a bayan idanunsa kuwa babu kalar azabar da ba ta yimin. Har wankin kaya take saka ni, tun ban iyaba saboda ƙarancin shekaru har na koya don dole. Iyabo sai ta hana ni abinci tun safe har sai na galabaita kafin ta ba ni. Ga shi nan idan Baba ba ya gida sai ta yi ta kawo mishi wasu mazan, idan sun tafi ta kama ni ta ja min kunnuwa tare da kashedi akan muddin na sake na faɗamasa sai ta kashe ni. Na kuma amince za ta aikata tunda har cokali ta taɓa sanyawa cikin garwashi ta manna min a cinya kawai don na Baba ya tambaye ni batun karatuna nace masa na fi sati ban je ba. Wasa-wasa Iyabo sai da ta kashemin karatu, tun Baba na maida hankali ga tambaya, na rasa dalili har shima ya yi watsi da maganar. Makarantar islamiyya kam shi ma tana bari naje ne a dole saboda ina yi mata cinikin cincin. A ƙarshe ma ta hana ni zuwa ta koma ɗoramin tallah. Shi Baba idan ya kaɗa harkar barikinsa sai ya kwashe sati biyu ma bamu sanya shi a idanu ba. Haka har na kai shekaru goma sha uku a duniya cikin wahala da ƙuncin rayuwa. Ance ba'a sabo da wahala ba don haka ba sai ince na saba da wahalar Iyabo. Idan zan mutu ina rashin lafiya kallo ban ishe ta ba. Duk tsananin ruwa idan Iyabo ba ta so ba, ban isa na shigar mata ɗaki ba sai dai na kwana a waje. Idan naji ruwan ya yi ƙarfi ne nake komawa zauren gidan kusa da tumakanta na keɓe. Babu zato ba tsammani, watarana da daddare ana muku-mukun sanyi, ina zaure na ƙudundune sakamakon Iyabo ta yi wani baƙon watsewarta suna ɗakin. Ta kuma rantse ko kwakkwarar motsina ta ji sai ta fito ta yankamin wuya. Wannan ta sanya tari kwakkwara ma na kasa yi. Ba zato Baba ya bude gidan da mukullinsa ya shigo. Haske ni ya yi sosai da tocila yana tambayar.


"Wace a nan? Na'imatu! Me kike yi anan cikin wannan uban sanyin? Maza tashi." 


Ya ƙarashe zancen nasa yana mai sa hannu ya kama nawa hannun da sanyi ya kama tamkar an jefa cikin ƙanƙara, haƙorana kuwa kar-kar kawai suke yi suna gugar da juna. Sam Iyabo ba su ji motsi ba, ya ga na tsaya ƙyam na ƙi yarda mu shiga koda falonta ne, kafin ya kai ga yimin magana ya ji muryar wani namijin ba shiri ya saki hannuna ya faɗa ɗakin. Can ba jimawa mutumin ya fito a guje har ya a tunkuɗeni ina zubewa a ƙasa. Ba jimawa kuma na ji ihun kukan Iyabo na tashi, Baba na jibgarta. Haka har ya fito da ita waje, runtse idanuna nayi ganin babu ko kaya a jikinta, a kan kunnuwana ya yi mata saki ya kuma dura mata ashar kala-kala. 

  Da wannan aurensu ya ƙare, zamana ya ƙara komawa gidan ƴan bariki. Rayuwar a sannan ta zama mafi hatsari gareni fiye da baya saboda maza da dama na kawomin hari amma Allah yana tsallakar da ni. Fir na ƙi makaranta saboda habaici da zagi da ɗalibai ke yimin. Wasu na kira na ƴar iska wasu kuwa shegiya kai tsaye. 

  Da na ƙara shekaru na ƙara yin hankali na shiga damuwa sosai, rayuwar gidan ta ficemin a kaina. Kullum cikin takurawa Baba nake yi kan ya kai ni ga Mamana ko yaya take zan zauna da ita. Da dai ya ga abin ya ishe shi ya zaunar da ni ya cemin ai ta tsane ni ba ta sona. Ya kuma ce koda na je wajenta ba za ta taɓa kallona ba. Hakan ya ƙara sanya mini tsanarta cikin raina. Ban ƙara tada maganarsa ba. Ina da shekaru sha shida ne aka soma kawomin hari fiye da baya. Cikinsu har da Ibrahim Ɗanmutuwa, mahaifin Haulatu. Su na cikin samari masu ji da kai da kuma gayu da kudaden da suke burge yanmatansu na bariki. Ba su da aiki sai caca, Babana na daga cikin masu zama a gefe suna waasa su, su kuwa hakan yana ƙara fasamusu kai. A duniyar ƴan caca babu wanda Babana ke so da yawan kurantawa kamar Ɗanmutuwa. Koda dai an masa shaidar cewa babu wata caca da za'a buga tare da shi bai ci ba. A lissafe ma bai fi sau biyu rak! Aka taɓa nasara a kansa ba. 

    Sanadiyyar wani wawan cin ganima da Ɗanmutuwa ya yi a wurin wasan su na caca, shi ya ja Baba yi masa alƙawarin aura masa ni. Wannan magana ta fi komai yiwa Ɗanmutuwa daɗi, a duniyarsa dama ya ɗauke ni kamar wata abar wasansa, abin nufi, tun sadda abokansa suka hau cin alwashin aurena, wasu kuwa na su bai wuce samun galaba a kaina ba, shi ma ya dauki nasa alwashin sai dai wayo da dabara bai sa ya furta musu ba. Lokacin da suke daukar alwashi a kaina, ina daga zaure ina jinsu, ban mance ba ma fita nayi zuwa kanti siyo sukari, a hanyar dawowa suka fara zancena, koda na karasa shigewa gida sai da na dakata na ji inda zancen nasu ya tsaya don ina tsoron su ƙulla wani abun da za su cutar da ni ba tare da na sani ba. 


    Maganar aurena da Ɗanmutuwa ba ƙaramin tayar da hankalina ya yi ba. Duk irin roƙo da koke-koken da na yi bai sauya komai daga ɓangaren Baba ba. Kai kusan ma dai kyauta aka ba shi ni, don duka-duka kudin sadaki kawai ya bayar aka ɗaura aurenmu a wani masallaci. Baba shi ya zama waliyinsa. A cewar Baba, Ɗanmutuwa  asalinsa shima Bakatsine ne, amma iyayensa sun mutu. Danginsa kuwa ba su damu da rayuwarsa ba shi ne dalilin shigowarsa Kano neman kudi. Ni dai ba ni da ta cewa. Babu abin da kuma ya kaɗamin ƴaƴan hanji sai ganin tun ranar farko da aka kai ni, na so na yi gardama ya zanemin jiki tas ya yi kuma abin da ya ga dama da ni. Wannan ya haifarmin da mugun shakkarsa, ga shan kayan maye. Haka na rayu da shi cikin ƙunci da rashin galihu, ciki kuwa da na samu yake ba ni magani ya zube. A cewarsa sam, bai kai shekarun tara iyali ba. Ban mancewa har mata yake kawomin cikin gida, ranar da ya fara na nunamasa fushina ya kama ni ya jibga ya kuma ƙulle a ɗaki tun dare bai buɗe ni ba dai washegari da rana. Alokacin na galabaita babu ci babu sha balle a yi batun sallah. Kai tsaye ruwan wanka ya sanya na ɗora musu, a dole jikina har rawa yake yi na kunna risho na dora, ga jiri da nake sakamakon yunwa.

  Babban takaicina bai wuce yadda Baba bai taɓa takowa don duba lafiyata ba kamar dama shi ɗin ma ya gaji da ni neman hanyar rabuwa kawai yake yi da ɗawainiyata. Sai da na shafe shekara ban sa Baba a idanu ba, ko na tambayi Ɗanmutuwa cemin yake yi yana bariki. Wannan amsar ba ta yimin dadi sam, hakan ya sa na ja bakina na yi shiru ban ƙara maganar ba. 

  Ɗanmutuwa bai fasa zubarmin da ciki ba, sai a kan Haulatu ne Allah ya yi ikonsa domin jan bakina nayi na yi shiru ban faɗi ba. Kuma sai Allah ya taimake ni cikin har ya shiga watanni bakwai hankalinsa bai kai gareni ba, kusan ma ya fi maida hankali da harkokin gabansa. Sadda ya farka da cikin kuwa, ranar na sha baƙar azaba kai ka ce kashe ni zai yi. Cikin wannan halin baƙin cikin na haifi Haulatu, makwafciyata ce ta taimakamin da zuwa asibiti da komai. Wannan taimako da na samu shi ya jawo muka tashi daga unguwar muka koma wata, acewarsa makwaftan sun masa shishshigi kuma har suna ikrarin haɗa shi da hukuma kan ya bar ni a gida ina naƙuda tsawon sati bai ko damu ba. Su ne suka siyamin kayayyakin amfani na jariri da ma nawa. Sosai ya ji haushinsu.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 16

Haulatu na da wata biyu a duniya, Ɗanmutuwa yace na shirya zamu yi ƴar tafiya. Nidai ban san dalilin da yasa na dinga ji gabana na faɗuwa ba, tasha muka nufa muka shiga motar Kaduna. Wani gida ya kai ni bai ko damu da ya shiga ba sai ma cikin hali na ko'in kula ya sanar da ni wai Baba ne a ciki ba shi da lafiya, na zauna zuwa gobe zai shigo mu tafi gida. Jin haka hankali tashe na faɗa ciki da sallama. Ɗan ƙaramin gida mai ɗakuna falle biyu sai banɗaki. Baba na kwance saman ƴar katifa cikin hali na ciwo, sallamar da na yi ce ta fito da wata mace daga wani ɗaki. Itama dai babu alamar cikakken lafiyar tattare da ita. Tana tambayar ko wace ce ni sai dai na kasa ba ta amsa har na ƙarasa makwancin Baba na tabbatar shi ɗin ne, shima kuma ni ya ƙurawa idanu can cikin rawar murya ya kira sunana. Na ƙarasa na zauna kawai sai na fashe da kuka. Anan yake bani labari ai tun bayan aurena babu jimawa ya auri matar da na gani mai suna Falmata. Sai dai babu jimawa ya kamu da cuta mai wuyar magani amma a sannan ya ma ƙi faɗin sunan cutar. Ya cemin koyaushe ina ransa, ya ba da saƙo sau ba adadi ga Ɗanmutuwa akan ya kai masa ni mu yi magana kada mutuwa ta ɗauke shi, amma firr ya ƙi. Sau biyu Ɗanmutuwa ya zo duba shi, kuma duk zuwan shi ne ke matsawa abokn Ɗanmutuwar kan lallai su ce ya zo yana buƙatar ganinsa. Daƙyar ya samu ya zo. Zuwan ƙarshe ne kuma har kuka ya yi masa kan ya taimaka ya kawo ni, shi ne muka je. Na ce meyasa bai je asibiti ba, ya yi ƴar dariya kawai ya ce min an je asibitin ya fi a ƙirga amma sun ce ba su gane mai ke damunsa ba. Haka na wuni zaune muna hira da Baba wanda ke magana daƙyar, ya ga Haulatu amma koda na miƙa masa ita don ya ɗauka girgiza min kai ya yi ya nuna aa. Ya cemin itama kamannin kakarta ta biyo. Sai da dare ya yi, Falmata tuni ta kwanta, Baba ya ciro wata baƙar leda ya damƙamin, ya ce wannan ko babu shi a raye, zai taimakamin na je ga mahaifiyata ko danginta, kuma yace duk radda na samu zuwa na nemar masa gafararta amma bai faɗamin dalili ba kawai sai na sa a rai watakila dai saboda halin rayuwa yau da gobe akan saɓawa mutum. 

  Allah ya ƙaddara ina garin Mahaifina zai rasu domin ba a wayi gari da shi ba, cikin dare ya rasu babu wanda ya sani daga ni har Falmata sai da gari ya waye. Kukan da na yi a lokacin ba zai misaltu ba, na shiga tashin hankali irin wanda ban taɓa zato ba. Anan ne Ɗanmutuwa ya zo domin mu tafi, jin Baba ya rasu shima na ga jikinsa a ɗan sanyaye. Ko ba komai na san, ya tuna da kaunar da Baba ya nunamasa ko dai wani abin da shi ya bar wa kansa sani. Sai da na ƙara sati guda cif a garin Kaduna kafin mu tattara mu koma Kano. Sai bayan komawarmu ne na bude ledar naga abin hannun azurfa da hoton Mahaifiyata, a bayansa an rubuta adireshi da kuma cikakken sunanta. 


  Shekarar Haulatu biyu a duniya, muka bar unguwar da muke dalilin makwaftan da Ɗanmutuwa ya ce suna shigar masa hanci da ƙudundune, sun saka wa rayuwar gidansa idanu kan kawai watarana yana dukana wani makwafcinmu ya buga masa ƙofa ya ce matuƙar bai bari ba zai haɗa shi da hukuma. Shi ne silar komawarmu inda muke a yanzu. Ya cemin dai kyautar gidan ma aka ba shi. Anan ne komai ya ƙara dagulewa na rayuwar Ɗanmutuwa, ba shi da aiki sai tara majalisar ƴan daba, mun taso a rayuwa da babu makwaftan da ke raɓar mu bisa tunanin mu ɗin tsoffin ƴan bariki ne. An sha Haulatu ta fita waje wasa ta dawomin tana kuka wai yara na ce mata shegiya. Yana daga cikin dalilan da yasa na hana ta fita wasan. Zama a lokacin ya ƙara tsananta, Ɗanmutuwa ya bar ba ni ko sisi, ni kuma duk sana'ar da nayi, daga na fara na soma samun abin rufawa kai asiri, sai daga baya a daina zuwa siya wai ba za su ci bin hannun karuwa ba. 

   A ƙarshe na yanke siye da siyarwar abinci a kasuwa, shi dama Ɗanmutuwa koda na ce masa ga abinda zan yi cemin ya yi shi fa ko wasu mazan ma zan bi ko a kwalar rigarsa. Haka muke rayuwa da Haulatu, tun tana ƙarama take ganin yadda mahaifinta ke dukana, wannan ne silar jefa tsanarsa a zuciyarta. Tun ba ta mallaki hankalin kanta ba take cemin ita dai mu gudu daga gidan nan, ita ta tsani mijina domin tun a bayan ma ba ta kiransa da suna Baba. Kai ko shigowa gidan ya yi suka yi kiciɓus a hanya zai ɓallamata harara ko kuma ya sa ƙafa ya shure ta yace wai ta kafe shi da mayun idanunta. 

  

  ***

Daga haka Umma ta labartamusu duk abin da ya faru dab da za su bar Kano zuwa Katsina. Hajiya Babba ta girgiza da jin kalar rayuwar da ɗiyarta ta yi, koda dai dama a bariki ta bar ta, ta sani komai zai iya faruwa gareta. Jikinta ya yi mugun la'asar, anya kuwa haƙƙin Na'imatu zai bar ta? Lallai da gaskiyar Alhaji da yace ta godewa Allah ma da ya sa tana da rabon ganin Na'imatu har ta nemi gafararta. Umma kuwa kallon su Baba Dakta ta yi karo na barkatai ta ce. 


"Na kawo mata jikarta, koda ace ni ba zan samu karɓuwa a wurinta ba. Ta taimake ni kar rayuwar ɗiyata ta wulaƙanta irin yadda nawa rayuwar ya tafi a wulaƙance. Zan iya sadaukar da komai akan samar da farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwar ɗiyata."


"Um um, bari faɗin haka Na'imatu, ai nan da kike gani, kin zo kenan da yardar Allah. Shi kuma maigidan naki duk inda ya shiga a faɗin garin Kano ko wajenta, in sha Allahu zamu neme shi a raba auren sannan ya fuskanci hukuncin abin da ya shuka maku a rayuwa. Ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne, yau ko Asma'u ba ta raye, mu ba zamu taɓa gudunki ba ballantana kuma ga ta nan a zaune da ranta da lafiya cikin iko na Allah. Abin da dai ya faru ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba. Ki kwantar da hankalinki, ina maki alƙawari kan cewa babu wata matsala da za ki ƙara fuskanta kwatankwacin ta baya."


 Baba Dakta ke wannan kalamin cike da kwantar da murya. A ƙarshe ya ce Baba Saude ta ja su Umma ɓangaren Hajiya Babba su huta su ci abinci. Haulatu ta dube shi.


"Don Allah Baba kar a kai mu ɓangaren matarnan, kai ina ne ɓangarenka? Nan nake so."


Umma ta dubi Haulatu, ita kam a ko'ina sai ta kwaɓa magana. Hajiya Babba kuwa hawaye take yayinda ta kai hannu da zummar riƙo na Haulatun aikuwa ta yi wani irin fisgewa tana huci.


"Wallahi kar ki ƙara gangancin riƙe ni. Yanda kika tsani Ummata, nima na tsaneki kuma har ki mutu ba zan yi fatan Umma ta yafemaki ba."


"Ke Haulatu, yimin shiru." Umma ta furta cike da murya mai nuni da rauni duk a kokarinta na son tanƙwara Haulatun. 


"Rabu da ita Na'imatu, ko mene ne ni na jazawa kaina. Don Allah ki yafemin Na'imatu. Na yi kuskuren da ba zan iya maida hannun agogo baya ba ballantana na gyara shi. Na bar maki tabon da zai yi wuyar goguwa a tarihin rayuwarki, haƙiƙa ban cancanci ki kira ni da sunan uwa kuma mahaifiya gareki ba. Ki yi hakuri ki yafemin kin ji?"


Tun soma maganar Hajiya Babba, Umma ta sunkuyar da kanta ba tare da ta ce uffan ba. Ta fi mintuna biyu ba ta ce komai ba, Haulatu kuwa sai hararar Hajiya Babba take tana ji ba don Umma ta kwaɓe ta ba, to fa babu abin da zai hana ta gasa mata maganganun da za su hana ta bacci. Wani tunani ne ya zo kanta, ai idan ma suka bar sashen Hajiya Babba, babu damar da za ta dinga ƙuntata mata a gidan tunda dai ta lura da tsarin gidajen nasu, za'a iya kwana da wuni ma ba'a sanya juna a ido ba. Wannan dalilin ne yasa Alhaji na ɗan saka baki da zummar tausar Haulatu akan ta zauna sashin kakarta, idan ma ba ta so duka ɓangarorin ta duba wanda ya yi mata, sai su zauna a ciki. Nan take ta ce ta amince da zama ɓangaren Hajiya Babbar. Ita dai Umma ba ta ce komai ba don da alama ta ɗan soma karaya. Wannan raunin nata shi Haulatu ba ta so, sai mutum ya gama cutar da ita a lokaci guda idan ya yi ƴar murya sai zuciyarta ta wanku.  Suka miƙe har Baba Saude suka nufi ɓangaren Hajiya Babba inda suka bar ta tare da yayyunta suna ƙara yi mata faɗa da kuma nasiha. 

  A hanyarsu Haulatu sai cin alwashi take a ranta, ta rantse zaman da za ta yi a gidan nan sai Hajiya Babba ta raina kanta. Sai ta san cewa ita din jikar Saleh Maikalangu ce, ko ba komai ta haɗa iri da barikin tunda dai haka take kallonsu. 

   Baba Saude ta kai su wani ɗaki mai kyau da girma, babban gado ne a cikinsa sai kuwa bandaki. Ga na'urar Ac ga kuma fanka. Ce musu take yi. 


  "Anan Hajiya Nafisa ke sauka idan sun zo daga Malaysia. Ai ita can take aure amma nan kusa za su zo za'a yi bikin jikan Baba Dakta."


"Kenan idan ta zo kina so ki ce zamu bar ɗakin ko?" Fadin Haulatu tana kallonta. Umma ta harare ta, ta yi kamar ba ta gani ba. 


Baba Saude kuwa ta yi ƴar dariya.


"A'a ƴar nan, ai akwai wasu ɗakunan har ma a can ƙasa. Ku huta ku yi sallah, bari a haɗo maku abinci."


Tana kai wa nan ta fita. Hajiya Rabi ta dubi Umma dake zaune gefen gado bayan shigar Haulatu bandaki ta ce. 


 "Kai Na'imatu a gaisheki, gaskiya kin ga rayuwa. Kin yi kokari ba kadan ba. Allah yasa ƙarshen wahalar kenan. Amma fa da alama wannan ɗiyar taki ba ta huce ba."


 Umma ta ɗan yi murmushi ba tare da ta ce uffan ba. Ita kadai ta san me take ji a ƙirjinta, tun tahowarsu har wani jiri ke neman ɗibarta, sam ba ta jin dadi ta sani. Akwai abinda ke mata ciwo a jiki tabbas, ga ciwon kai dake damunta. Wannan ya sa ba ta son magana. Ita zancen ma gaba ɗayansa ya ishe ta. Fitowar Haulatu ya sa Hajiya Rabi ta bar surutan da ko kusa ba shiga jikin Umma suke yi ba, itama ta faɗa banɗakin don kama ruwa da yin alwala don lokacin ɗaya ma ta gota. 


***

  "Which kind of nonsense is this?" 


"Haidar anya ba ka soma abar ba?"


"Please dagaske? Kar fa ku sa a gan ni a Babban gida yanzu?"


Ire-iren waɗannan tambayoyin har m da masu aiko ƴan aljanun sitikoki a cikin whatsapp group ɗin nasu na Zuri'ar Bello S. Malumfashi. Labarin zuwan Umma da Haulatu ne, Jabeer da Haidar suka fesa musu. Nan fa maza da mata aka fito aka yi caa ana tattaunawa. Rantsuwar da suka yi ce ta sanya aka yarda. Nan fa gulma kowa ya ɗauka, abin ma har ya ba wasu haushi musamman jikokin Hajiya Babba, suka fice daga gidan. Ya zame musu tamkar dai fitina. Masu cewa mugun bakin da Hajiya Babba ta yi musu saboda tana ganin suna aikata ba daidai ba a rayuwa shi ne ya koma kanta, manyan ciki kuwa na kokarin su ga an kashe zancen. Akwai wacce ma aka tashi aurenta da wani da uwa ta nuna ba ta so ita a barta da zaɓinta, nan Hajiya Babba wai ba irin zagi da cin mutuncin da ba ta yi gareta ba, har da cewa in sha Allahu sai ta haifi kangararriyar ƴa irinta. Aikuwa jin wannan labarin har da muryarta ta aiko tana guɗa, tana fadin gashinan ta haifi yaranta har biyu salihai, amma Allah ya nuna iko akan Hajiya Babba. Maganar ba ta mutu ba sai da labari ya je kunnen manyan jikokin gidan su hudu wadanda ko group din ba sa ciki. Nan da nan ɗaya a cikinsu ya danna kira ga ɗaya cikin wadanda aka ce su ne admins na gidan ya ci musu mutunci kafin a samu a bar zancen. Aka kuma rufe gidan ta yadda babu wani ko wata da zai iya magana a ciki bayan admins.  


***

 Ƙarfe uku da mintoci, tuni gidan ya soma ɗinkewa da manyan iyaye da ma wasu a jikoki.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 17

Yara biyar na Alhaji Bello S Malumfashi, Allah ya albarkace su sun hayayyafa. Kafin rasuwa Amadu, ɗansa na farko, yana da yaransa bakwai cif waɗanda matan suka rinjayi mazan, maza biyu ne sai mata su biyar. Uku a cikin matan na tare da iyalinsu a nan birnin Katsina yayinda biyu ke aure a Malumfashi. Iyaye mazan kuwa, su biyun duka suna da nasu ɓangaren a Babban gida, Alhaji Ridwan wanda ya bi sahun mahaifinsa ya zama cikakken ɗan kasuwa da har yake fita ƙasashen waje sarin kaya, sai ko ƙaninsa Alhaji Yusuf da suke kira Baban kowa saboda son jama'a irin nasa. Shi kuwa yana harkar chanji na kuɗaɗe ne kafin ya samu karayar arziƙi sai dai hakan bai sa yan uwansa kasa yin tsayin daka wajen ganin sun yi iyakar yin su na kyautatawa iyalinsa ba. Sau wajen uku ana ba shi jarin amma abin ba kamar baya ba, dole ya rungumi ƙaddararsa. 


  Mu'azzam kuwa mai bi ma Amadu, shi Allah bai yi shi mai yawan yara ba a duniya. Yaransa uku. Namiji ɗaya ne, Barista Dawud sai mata biyu. Nuratu (mai sunan mahaifiyarsu ake kiranta Mami) an musu auren zumunci da Alhaji Ridwan, sai ko Aishatu mai auren wani babban Farfesa a garin Kano. 


  Usman wanda shi ne a yanzu suke kira da Alhaji, yana da yara biyar tare da Bilkisu wacce suke kira da Nene.  Biyu sun rasu tun ma kafin su kai ga girma sai uku da suka rage. Hajiya Zaituna, mai auren wani babban soja a garin Kaduna, sai Engr Faisal dake zaune da iyalinsa a can gefe guda cikin Babban gida, sai ko Malama Safiyya. Ita mijinta ya rasu ya bar ta da marayun yaransu huɗu wadanda duk sun zama matasa, tana zaune a unguwar Tudun Matawalle. Sam ta ƙi yarda ta yi aure duk da cewa ba shekaru ne da ita na a zo a gani ba. 


    Suleiman, da suke kira Baba Dakta kuwa. Yaransa biyar a duniya da matarsa Maijidda. Ɗiyarsa ta farko ita ta ci sunan Hajiya Babba, wato Asma'u ake kiranta Husna, yara kuma su ce Umma, tana aure a garin Kaduna itama. Sai mai bi mata Dakta Hashim. Shi kadai ne a mazan da ke cikin garin Katsina, ke rayuwa a muhalli na daban bai yi gini a babban gida ba duk kuwa da cewa gidansa babu tazara sosai da nan din. Zakiyya tana zawarci sanadiyyar rabuwar aurenta da mijinta, yaranta uku duka su na hannunta. Maryam kuwa aure take a Daura. Sai autar Baba Dakta da har a sannan Allah bai kawo miji ba, shekarunta talatin da takwas a duniya, Mabruka suke kiranta da Anti. Ita da Zakiyya duka su na zaune a ɓangaren Baba Dakta sai dai wasu lokutan tamkar su na ganin hanjin juna, sam ba su jituwa duk kuwa da girme matan da Zakiyya ta yi da shekaru kusan uku ma. 


  Asma'u kuwa, wato Hajiya Babba. Idan ka cire Na'imatu, akwai Nafisatu dake ƙasar waje, sai Hadiza mai auren wani tsohon ɗan siyasa a cikin Katsina sannan Bello mai sunan Abba wanda ke aikin Custom, yana zama a Yobe tare da iyalinsa. 

  

  Waɗannan a taƙaice su ne suka haifar da zuri'a mai girma ga Marigayi Alhaji Bello S Malumfashi da  Hajiya Nuratu. 

   Su biyar ɗin, su ma sun gina rayuwar yaransu cike da tsari na ilimin boko da arabi har suka girma suka ƙara bunƙasa zuri'ar ta hanyar haifar musu jikoki masu jini a jika. 

   Daidai gwargwado kowannensu yana taƙama da kuɗi, hakan ya sa idan wannan ya kawo tsarin wani gyara a gidan yau, sai idan an kwana biyu wani a ciki ya kawo nasa shi ma. Ga matasan jikokin kuwa, burin kowannensu su yi abin bajinta da burgewar da zai faranta ran iyayensu. Ga su nan Allah ya halicce su da baiwar kyau na fuska da ma na gangar jiki. 

   Manyan matasan gidan kuma jikoki masu ji da kai ga aji da kuma uwa uba kuɗi. Su huɗu ne cif, kowannensu harkar gabansa kawai yake yi, ba su fiye shiga harkar juna ba. Idan ma wani abin ya faru, aka ce wancan ya tsawatar toh wani a ciki ba zai sanya baki ba. Haɗuwarsu ma kan yi wuya a wuri don ba su da lokacin shiga sabgogin gidan. Idan kuwa iyayen ko kakannin na buƙatar ganinsu, sai ko sun sanar musu a waya kan su shigo don dukkansu suna da gidajensu ba kuma sa sha'awar rayuwa a cikin gidan. Ƙarshen boko dai su ne. Sauran jikokin gidan har sunaye na daban suka sanya musu. Ƴanmatan kuwa da aurensu bai haramta ba, nan duniya kowacce da wanda take hari a ciki duk kuwa da cewa biyu a cikinsu ma suna da aure amma ba su da babban burin da ya wuce su kasance cikin masu sa'ar auren ɗaya a ciki. 

   

   Wannan kenan. 


***

  Duk wanda ya shigo gidan babu inda yake fara zuwa sai ɓangaren Alhaji saboda anan ne Haidar da Jabeer suka ce an haɗa taron. Sai dai duk wanda ya shiga sai ya ga babu kowa face Alhajin, kuma kana shiga zai zaunar da kai. A haka har ya fahimci tabbas labari ya je ga jikokin gidan. Ya kuma yanke dama zuwa bayan Magriba za'a haɗa taro a sanar da kowa halin da ake ciki. Na nesa kuwa, sai a ba su labari. Ya dubi matasan mata da maza dake zaune a falon nasa. 


  "Ku tashi ku je, mun yi waya da iyayenku bayan Magriba kowa ya zo nan akwai muhimmiyar magana da za'a yi."


Wata budurwa baƙa mai kakkauran jiki, tana sanye da riga da wando na Pakistan, ta rufe kanta da hula, ta ɗan taɓe baki.

  

"Atoh, gwara dai a yi ta ta ƙare Kakus, don a bambance tsakanin aya da tsakuwa."


Ta ƙarashe tana ɗan yin dariya ta rainin hankali lokaci guda tana satar kallon gefen wata matashiyar budurwa dake fidda hawaye. Ranƙwashi ta ji a saman kanta, ta juya ta kalli mai wannan aikin. Yayanta ne wanda daga shi sai ita a gidan Engr Faisal. Shekara ɗaya ya ba ta wannan ya sa ta fusata kuwa ta miƙe ta kai masa duka, nan za su fara kokawar da suka saba Alhaji ya yi musu tsawa.


"Bana son shashanci, duk ku tashi ku fice daga ɗakin nan, ba kuma na son na ji koda wasa kun aikata wani abu da zai ja magana. Ku yi hakuri komai za ku ji zuwa bayan Magriba, kai na mayar ma bayan sallar isha'i, hakan zai fi."


"Haba Baba Alhaji, kafin lokacin ai mun suma mun farfaɗo, so muke mu san komai. Dagaske ne waccan matar, oh sorry, Autarku ta taɓa haihuwar shege?"


Daƙuwa Alhaji ya yiwa mai maganar, saurayi ne da bai fi shekaru goma sha takwas ba, sanye da wando 3 quarter da riga marar hannu. Kansa kuwa wani shegen aski ne, kai daga kallo ɗaya ma za ka fahimci akwai fitina tattare da shi. 


"Ko uwarka Zaituna ba ta isa ta yimin wannan zancen banzan ba ballantana uban naka da kake taƙama shi Soja ne. Kar kuma ku ƙara sheganta matar da aka haifa ta hanyar aure. Maza ku tashi ku ba ni guri, na kuma mayar bayan isha'i, ni da iyayenku zan yi ba da ku ba."


Sum sum suka miƙe, ya bi su da kallo kafin ya girgiza kai cike da jin takaici a ransa. Laifin duka na Hajiya Babba ce, da ace ba ta ɓoyemusu ba tun farko, hakan duk ba zai faru ba. 


***

  Haulatu na zaune tana danna ƙaramar wayar Umma, ƙoƙari take ta cika umarnin Umman na kiran su Abban Bahijja ta sanar musu cewa sun isa gidan. A lokacin Hajiya Rabi tuni ta yi musu sallama ta tafi bayan ta ci abinci, yamma ta yi sosai, Umma na kwance dai idanunta rufe, ga dukkan alamu kan ya matsa mata da ciwo. Haulatu ma ta sha mamakin kwanciyarta da la'asar don ba ɗabi'arta ce ba, asalima ita ke hana ta.  Aka turo ƙofar aka shigo babu ko sallama, Haulatu ta ɗaga kai ta kalle su. Su uku ne, ɗaya babbar mace ce, sai wata da za ta girmi Haulatun riƙe da bebi a hannunta cikin shawul sai ko budurwa da ba za ta fi sa'arta ba. Suka ƙarasa shigowa su na musu kallon tara saura, Umma ta ɗan miƙe zaune jiri na kwasarta daga kwancen, Haulatu ta ɗaure fuska ta yi tsai da idanu tana kallonsu, a shirye take da duk wacce suka zo don ba ta ga alamun rahma a saman fuskarsu ba. 

  Budurwar ido waje ta dube su.


"Kai! Unbelievable! Wallahi sun yi mugun kama fa Adda."


Wacce aka kira da Adda mai riƙe da bebi ta yamutsa fuska idanu saman Haulatu wacce ta maida kai ga danna wayar da a wajensu ko ƴan aikinsu sai haka. 


 "Sannunku." Faɗin Umma da raunanniyar murya. 


"Yauwa." Babbar matar ta amsa kafin rai a cunkushe ta juya ta fita. 


"Aikin banza, da alama wahalar rayuwa ce ta koro su wajenmu."


Faɗin wacce aka kira Adda kafin ta ja tsaki. Haulatu ta yi murmushi.


"Kuma dole a karɓe mu ba."


Baki sake Adda ke kallon ikon Allah, ita kuma wannan da ƙarfinta ta shigo gidan?


"Da me kike taƙama?" Faɗin Adda zuciyarta na tafarfasa, dama can ga ƴan adawar ɗakin nasu suna musu dariyar wannan mugun abu da ya faɗo ɗakin nasu. 


Dariyar rainin hankali Haulatu ta yi kafin ta watsamata wani kallo da manyan idanuwanta masha Allah. 


"Da me zan yi taƙama? Ai koyaushe Allah ke bamu ya rufa mana. Kuma gidan nan mun shigo shi kenan, abin kunya dai Asma'u ta riga ta yi. Ta bar muku baya da ƙura tunda ta haifi ɗiyar so Umma Na'imatu babu yanda ku ka iya karɓa dole. Ku godewa Allah ma da ba a gidan rediyo ku ka sha labari ba."


Umma juya kai kawai take idanunta a runtse.


"Haulatu." Shi ne kawai abin da ta iya furtawa bayan haka radadin da kanta ke yi ya hana ta magantu. A harzuƙe budurwar nan ta soma magana.


"Kut! Sunan Hajiya kike kira kamar ki na magana da sa'arki?"


Itama a fusace ta amsa.


"Ke kika san ta a Hajiyar."


Kafin su yi wani yunƙuri na magana ko rashin ta ido, Hajiya Babba ta faɗo ɗakin. Ta dube su a fuska a daure, kasancewar ana shakkarta ya sa duk suka nutsu idan ka cire Haulatu da ta haɗa su tana watsa musu harara. 


"Ku fice min a nan." Ba musu suka fice rai a ɓace. Ta ƙarasa shigowa ba ta ko bi ta kan Haulatu ba ta dubi Umma cike da kulawa, murya na ɗan rawa ta ce.


"Na'imatu meke samunki?" Ta ƙarashe tana kai tafin hannunta saman goshin Umma. Aikuwa ta ji ya ɗauki zafi rau. 


"Innalillahi, ai ba ki da lafiya. Bari na kira Khaleefa."


"Daga baya kenan, sau nawa tana yin cutar a duniya kin taɓa kulawa? Sai yau?"


Faɗin Haulatu tana harararta, nasihar Umman ta ɗazu ce akan abin da ta aikata a falon Alhaji yasa ba ta yi gigin ture hannunta daga jikin uwarta ba. Hajiya Babba ta kalle ta, wai yau ita ce ake faɗawa baƙar magana? Dama akwai ranar da za'a yi jikar da za ta gasamata mai zafi haka? Tana kallo Umma na girgizawa Haulatun kai, ita kuma ta juya a sanyaye ta fice don kiran Khaleefa ya zo dubamata ɗiyarta.


Bayan fitar ta Umma ta dubi Haulatu, kafin ta kai ga magana rai a tunzure Haulatu ta katse ta.


"Don Allah Umma kiyi hakuri, wallahi idan na gan ta raina baƙi yake yi. Kuma na rantse ba zan iya cusa kaunarta cikin zuciyata ba."


Kawai sai ta fashe da kuka ta miƙe ta shige banɗaki. Umma dai ajiyar zuciya kawai ta yi. Ta sani dama ya lafiyar kura ballantana an jefe ta da kashi? Fatanta Allah ya yayyafawa lamarin ruwan sanyi domin ita kam ba ta ma san yanda ta dauki Hajiya Babbar ba a yanzu. Haƙiƙa tana buƙatar ko na lokaci ne kafin ita ko Hajiya Babba wani ya riga kwanciya a dama, su rayu cikin aminci da zumunci. Ko ba komai ta nuna nadamarta a fili.


***

  Fuska a ɗaure ya bi wayar da kallo, sunan Hajja da ya gani ya sa shi fahimtar mai kiran. Ya dubi nurses din dake tsaye kansu na kallon ƙasa sakamakon faɗa da yake kan sakacin da suke yi mishi da marasa lafiya. Da muryarsa tausassa ya nunamusu hanyar waje da yatsa gami da fadin.


"Out."


Suka ƙara furta Sorry Sir, kafin su sa kai sum sum kowannensu ya fice. 


  Khaleefa Dawud S Malumfashi kenan.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 18BAYAN SATI BIYU...


Jikin Umma ya yi sauki ta warware tamkar ba ita ba. Kulawa sosai ta ke samu wurin Hajiya Babba da Haulatu. Zuwa lokacin tsegumi ya lafa, ƴan uwa masu zirga-zirga a gidan don son ganewa idanunsu Umma da Haulatu sun yi safa da marwarsu a gidan sun gaji domin Hajiya Babba ta hana kowa takurawa Umma sadda take fama da jinya. Asalima ba ta bari a shiga wurinsu, shakkarta da ake yi ya sanya kowa ya ja bakinsa. 

  Dr Khaleefa kuwa, bayan zuwansa na farko sai da ya ƙara zuwa har biyu don tabbatar da samun sauƙinta. A duk zuwan da zai yi kallo ɗaya ke hada su da Haulatu take gane mamufarsa a dole ba don ta so ba take ficewa ta bar shi da Umman a dakin tana ƙunƙunin da bai isa ya ce ga abin da take faɗi ba. 

   Gaba daya zama wuri daya ya ishi Haulatun, Umma dama tuni ta ɗan soma fita falon Hajiya Babba ta ɗan zauna, tun kwanciyarta rashin lafiya yanda ta ga Hajiya Babba ta sadaukar da lokacinta duk da jiki na girma da tsufa tana takowa ta zauna tana jinya duk kuwa da irin waƙe-waƙen habaici da kuma gwatsalewar da take sha daga Haulatu hakan bai sa ta fasa ba, dalilin keman da ya sa zuciyar Umma sanyi, ta ji kuma tausayin tsohuwar, ta saka a ranta kawai duk wani abu da ya faru a rayuwarta, nata ƙaddarar kenan. Haka kuma Allah ya tsara mata babu yanda ta iya ta kaucewa hakan. Da wannan ta kwaɓi Haulatu ta kuma bi ta da gargadi sosai akan koda wasa kar ta ƙara faɗawa Hajiya Babba baƙar magana, da ma dukkan wani abu da ta ke yi da zummar ɗaukar fansa ta haƙura ta watsar da makamanta. 


"Ni ta haifa ta watsar, ni ta yiwa ba ke ba. To hatta ni ɗin da ta yiwa, ki sa a ranki na yafemata. Ya wuce a wurina, na kuma fidda shi a zuciyata, yanzu ta lafiyata nake yi, ke a matsayin na mai ƙaunata ai na yi zaton taya ni kula da lafiyata ya fiye maki duk wani rikici da ke ƙasan ranki a kan baiwar Allahn nan."


Wannan magana ta Umma yasa Haulatu ta ɗan yi sanyi amma ko kallon Hajiya Babba ba ta yi ballantana ta ci arziƙin gaisuwa. Hajiya Babbar ce ma ke son ganin Haulatun ta saki jiki ta dinga matsawa da son yi mata magana tana amsa mata daƙyar kamar an mata dole. Har auna su aka zo aka yi za'a yi musu dinkuna, Hajiya Babba har siyayyar mayuka da kayan amfanin ƴanmata masu kyau ta saka aka yiwa Haulatun, ta dai karɓa ganin idanun Umma yasa ta yi godiya. Yar budurwar da aka aika jikar Baba Dakta ce kuma sa'ar Haulatun da ake kiranta Safeena. Sosai take son ƙulla zumunta da Haulatun amma babu fuska, kusan ma ba ta bari ta fito falon. 


Yau ma kamar koyaushe tana kwance a ɗaki tana latse-latse a wayar Umma, yayinda Umman ke falon Hajiya Babba su na hira. Wayar ta yi ƙara, ta duba dakyau, baƙuwar lamba ce, sai da ta ɗan yi tsai cike da tunanin wa zai kira Umma da baƙuwar lamba kafin ta danna ta kara a kunne ba tare da ta ce uffan ba don so take ta ji ko waye. 


"Hello, Umma ina yini."


Jin muryar da ba ta yi zato ba yasa ta miƙewa zaune tana washe haƙora. Jimawar da suka yi ba a gaisa ba ya sa Haulatu ta nemi wancan fushin da take yi da Hindatun ta rasa shi.


"Toh ƴar guguwa, ba Umman ba ce, wai dama kina duniya?"


Daga can Hindatu ta yi wani ihu na farin ciki, suka kara sakin shewa da nanayensu. Rabon da Haulatu ta tsince ta cikin walwala har haka ba za ta iya tunawa ba. 


"Kee shegiya, kina nan don wulakanci shi ne ba kya ko nema na a gaisa ko?"


Sai a sannan ma ta tuna da abinda ta riƙe Hindatun da shi a baya, ta dan taɓe baki.


"Bar maganar Malama. Ya kike to, ya amarcin? Ina Alhajin naki? Ba ku tafi shi honeymoon din da kike ta mafarkin zuwa ba?"


"Uhm, wane honeymoon ina shiga nayi tuntuɓe da ciki. Mts. Wallahi kin ga laulayi nake fama da shi mai ɗan karen wahala, kusan koyaushe muna hanyar asibiti."


"Lallai, ki ce abin nema ya samu, matar ɗan sanda ta haifi ɓarawo. Momi sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha."


Haulatu ta karashe tana wata dariya. 


"Me kike so ki ce? Dama burinmu samun cikin ko me?"


Hindatu ta watsamata tambayar, kawai sai kuma ta waske.


"Aa, ina ruwan biri da gada? Ni wani abu nace? Yo wace uwar ce ba ta so ta ga jikanta na farko a duniya?"


"Uhm, ke kika sani dai. Wai kina ina ne? Kinsan fa rasa lambobi nayi tun sadda na yi Iphone, sai da muka hadu da Momi ne na dauki lambar Umma a wayarta."


"Au dama tana da lambar Umma?" 


"Ji wani zance, to sau nawa nake kiranki a wayar Momin? Ni na yi mata saving. Wai yaushe za ki zo gidana? Kuma yanzu kina ina? An kama wadanda suka so sace ki? Me kika yi musu ma ne?"


Ita Haulatun dariya ma ta yi kafin ta ja guntun tsaki. Abu ne da ta bar shi a ranta da zummar duk wuya duk runtsi sai ta daukarwa mahaifiyarta fansa da ma ita kanta a wajen Ɗanmutuwa. Ba ta son tattauna zancensa da kowa, hakanan ba ta kaunar tattauna abin da ya shafe shi a yanzun. 


  "Ina Katsina fa. Mun zo gidan family din Umma."


"Katsina? Dama kun san su? Amma ba ki taɓa ban labari ba."


"To ai komai yana da sila. Ma yi maganar dai. Zan kira ki."


Ba tare da ta jira amsar Hindatu ba ta katse kiran tana kallon Baba Saude wacce ta shigo dakin da sallama. 


"Ƴar gidan Umma, ki zo tana kiranki."


Ta ɗan yi murmushi da fadin toh. Zuwa lokacin ta saki ranta da duk wanda ya nuna musu ƙauna idan ka cire Hajiya Babba. Ita kadai ta ke jin kamar ba za su yi sabo ba musamman da ta kula kamar ma ana shakkarta ne  a gidan.  Idan ta tsawatar ba musu suke bi, wannan ma na daga cikin dalilin da yasa ba ta zama falon, a ganinta iko da nuna gadarar Hajiyar ma ya yi yawa. 


Sai da Baba Saude ta fita da minti kusan daya kafin ta mike ta fito kanta babu ko kallabi sai gashinta dake a tsefe babu kitso da ta tufke a ƙeya. Tana ɗan buɗe ƙofar ta hango Umma tare da matar da ganinta da ita kusan na uku kenan a gidan, Hajiya Zakiyya kenan wacce ta ji ana kira da Maama. A sashen mahaifinta, Baba Dakta ta ke zaman zawarcinta. Ita ke fuskantar ƙofar dakin hakan yasa dole Haulatu ta tura gaba daya ta fito. Umma ta bi ta da kallo ganin babu ko ɗankwali a kanta, Hajiya Babba na daga gefe ɗaya suna magana da Baba Saude, lokacin ƙarfe uku da mintoci na yamma. 


Ta ƙarasa ba tare da ko ta kalli inda Hajiya Babba take ba, ta gaida Maama. Ta amsa fuska a sake gami da fadin. 


"Zo nan ɗiyata, kya dinga zama ki ƙunshe kanki a ɗaka ke daya? Ai zaman shirun ba shi da dadi."


Haulatu ta ɗan murmusa kawai. 


"Ato, ki yi mata faɗa ko za ta ji." Faɗin Umma kenan.


"Shirya maza ki yimin rakiya unguwa."


Jin haka Haulatu ta saki fuskarta sosai, ta dubi Umma da zummar ta ji amsar da zai fito bakinta, Umma ta gyaɗamata kai. Aikuwa da murnarta ta miƙe ta faɗa dakin. 


"Kai Zakiyya amma kam kin kyauta. Ni na rasa irin wannan yarinya koyaushe tana ɗaki a ƙulle kuma na sani don ni take wannan shaƙiyancin. Toh ai kuwa dolenta ta sake da ni tunda dai na haifar mata uwa."


Aka yi dariyar maganar Hajiya Babba har Umma. 


"Hakane Hajja, ai nima ba nisa zamu yi ba. Matar Khaleefa ce ba ta jin dadi kwana biyun nan shi ne zan leƙa mata. Jibi ne kawo lefen Raudha ko?"


Ta ƙarashe da tambayar Hajiya Babba. 


"In sha Allahu. Ita Batulu sai sati na sama."


"Allah ya sanya alheri, ya sa zamu gani."


Aka amsa addu'ar Maama Zakiyya da amin. 


Anan take ƙara yiwa Umma bayanin, ai Raudha diya ce ga Alhaji Ridwan, ita kuwa Batulu ɗiyar Barista Dawud ce. Gidan iyayensu duka na kusa da su ba tazara sosai. Umma ta dan murmusa. 


"Ai na ga yaran, Hajja ta nunamin su da suka shigo kwanaki. Su ma iyayen mun gaisa. Allah ya nuna mana."


Aka ƙara amsawa da Amin. Daidai nan Haulatu ta fito cikin wata doguwar rigar abaya samfurin dubai. Blue black mai adon farin duwatsu, ta yafa mayafin a kanta, sosai ta yi kyau fatarta ta ƙara murjewa da kuma haske kai ka ce dama can ta saba da rayuwar jin dadin. Maama sai nazartarta take yi, tabbas yarinyar Allah ya mata baiwa na musamman. Nan gaba za ta gwara kan samari idan ta ƙara wayewa. Mutum ɗaya ta yi wa sha'awarta, ta sani kuma zai wahala ma ya kalle ta da sunan so da kauna. Ajiyar zuciya ta yi kafin ta miƙe tsaye. 


"Masha Allah Haulatu kin fito tsaf. Muje kafin yamma ta ƙara yi."


Fadin Maama tana gyara zaman ƙaramin mayafin da ta ɗora saman doguwar riga ta yadi da aka yiwa ɗinkin bubu. Maama doguwa ce kuma kakkaura, ba ta da muni, baƙinta mai kyau ne. Idan ka gan ta ba za ka ce ta haifi yara samari har uku ba, koda alama jikinta bai nuna tsufa ba. A karon kanta ta ƙi bada dama ga maneman aurenta sai dai a ƴan kwanakin nan akwai wanda ya matsa har ya ja su Alhaji na maganar ta ba da dama ya fito ta yi aure. Ita kuwa a nata lissafin, ta rufe babin aure a rayuwarta. 


Haulatu ta yi sallama da Umma, Hajiya Babba na a dawo lafiya, ganin idanun su Umma da Maama yasa ta amsa da Amin. Daga haka suka fice. 


***

  Tafe suke a motar Maama tana tuƙi cike da nutsuwa har suka iso unguwar Modoji inda anan ne gidan Dr Khaleefa ya ke. Wani ƙerarren gida ne a cikin gidajen dake kan layin da suka shiga, nan ta ga Maama ta saka hancin motarta gami da yin hon. Maigadi yana ganin motar ya gane da sauri ya tura ƙaton ƙyauren gidan ta shiga. 

   Flat house ne mai ɗan karen kyau, wurin parking bai fi na motoci hudu ba. Anan Maama ta adana motarta ta fito tana mitar ta san wancan agogo sarkin aikin ba ya gida. Ita dai Haulatu tun a hanya ma da ta gane gidan wanda za su je ta ɗan tsuke fuska. Maama ta rasa inda za ta zaga da ita ganin gari a Katsina sai gidan Dr Khaleefa? 


Haka ta bi bayanta tana tura baki kaɗan, mutumin da kullum cikin harararta yake yi, ya za su ƙare yanzu tunda ta tako ta zo inda ya ke rayuwa? Amma jin Maama ta ce da wuya idan yana gidan, ya sanya ta ɗan ji wasai. Yanzu burinta ma ta ga matarsa ta ga ya take? Ta san dai tana haƙuri da shi don daga ganinsa masifaffe ne kuma zai yi mugunta.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 20

Malama ta karɓe su fuska a sake, Haulatu dai daga gaisuwa ba ta ƙara cewa komai ba sai shiru da ta yi tana ƙarewa falon kallo yayinda suke ta hira da Maama. 


"Kinga fa yarona na zo gani ba ke ba. Ya dage na zo akwai magana."


Malama ta ɗan taɓe baki cike da takaici.


"Au, kenan ke ya kira ki taushe ni ko? Aikuwa dai ina nan akan bakana. Ke kam kina son biyewa shiriritar yaran nan naki."


Maama ta yi turus.


"Toh kinga dai ban san komai ba, amma kin ɗauko hanyar fesamin. Wani abun ne ya faru? Ko kuwa bai kai girman da Zaid ya ɗadɗago ni ba?"


"Aa, ai ba kya ji a bakina ba. Waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ki dai je yana can wajen nasa tunda shi ya nemi ki zo. Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, duk za ku zo ku same ni."


Dariya Maama ta yi tana mai miƙewa.


"Allah ya kyauta toh. Har na matsu ma na je na ji meke faruwa. Haulatu ki jira ni."


Ta amsa da toh kawai, bayan ficewar Maama daga falon Malama ta ɗan girgiza kai tana duban Haulatu ta ce.


"Ke kam kin huta da alama ba ki da surutu ko? Koda dai gidan nawa ne ba  abokan hira da yawa.  Yarana duka ukun maza ne, mace ɗaya ce za ki iya ba ta shekaru biyu zuwa uku, ta jw makaranta amma nan kusa za ta dawo."


Murmushi Haulatu ta yi, wai ita ake cewa ba ta da hira. Lallai, don dai Malamar ba ta dan wace ce ita ba. 


"Kina zuwa makaranta a can inda kike?"


Tambayar da Malama ta kara yi ya fahimtar da Haulatu dagaske hirar ta ke so, kuma ga dukkan alamu matar ba ta da girman kai, tun soma zancen fuskarta ma a sake take. Aikuwa ta gyara zama ta shiga labarta mata yanayin karatunta, hatta da irin hantarar da ake mata idan ta fita ana kiran gidansu gidan karuwai babu irin abin da ba ta  kwashe ta faɗawa Malama ba. Sosai tausayinta kuwa  ya mamaye zuciyar Malama Safiyya. Ta kuma karanci abubuwa da dama a kan Haulatun. Yarinyar tana buƙatar nusarwa akan wasu daga cikin ɗabi'u da ladabin magana. A yanayin da ta ke ba ta labarin tamkar da wata sa'arta, kamar misali takan yi amfani da 'Hum, ke na ga rayuwa fa.' Ko kuma ta ce 'Ke ba za ki fahimta ba.' Da dai sauransu. A shekaru da wayewa irin na Malama Safiyya sam ba ta ga laifinta ba duba da yanayin rayuwar da ta taso a ciki, itama mahaifiyarta ba lallai ta samu wadataccen ilimi ba da kuma wayewar mu'amala da mutane ba. Sai ta ji inama za'a yi mata kyautarta koda na watanni ƙalilan ne, ita kuwa za ta yi iya yinta don ganin ta gyara koda kaso sittin ne cikin ɗari na daga ɗabi'unta. Tun zuwan da suka yi gidan, sam ba ta taka ta je ba saboda ta jima kwance ba lafiya, kwanakin nan ne ta ɗan samu ta warware. Amma ta ji labari daga yan uwanta cewa Haulatun ba ta da kunya, wai kowa ya je tana dubansa ne ta maida mishi magana. 

 

 Haka ta yi ta kula da ɗabi'un Haulatun, ita kuwa ko a kanta, bilhaƙƙi take ba ta labari amma ko kusa ba ta ce ga mummunan sana'ar da Mahaifinta ke yi ba don tuni Umma ta kwaɓe ta da furtawa wani, ba kuma ta sa dalilin rufamasa asirin da Umma ke yi ba. Tana dai kokarin nunawa Malama yanda ta tsani ƊanMutuwa a rayuwarta. 


"Allah ya shirye shi idan mai shiryuwa ne. Sai hakuri, abin da ya faru da ku, kaddara ce. Ki saka a ranki haka ya tsara maku. Kin ji ko?" Faɗin Malama Safiyya kenan a ƙoƙarinta na datse zancen iyaka nan ganin hirar ma babu daɗin ji ga ƙarancin ladabin magana da Haulatun ke da shi. 


Aikuwa jin abin da Malama ta fadi yasa Haulatu yin wata dariyar.


"Aikam mun ga rayuwa. Tab din! Ai wallahi Hajja ta rufawa kanta asiri ma da ta karɓe mu idan ba haka ba wallahi daga nan har gidan rediyo."


Ita dai Malama ta cika da ɗumbin mamaki, shakka babu akwai tarin gyara da yarinyar ke buƙata. Ta yi shiru ba ta ƙara uffan ba, ba kuma za ta ce wai ta ji wani tsana ko haushin Haulatu ba face ma tausayin da ta ba ta. Ta san wahalar tarbiyya, ta yi msta uzurin kalar gidan da ta rayu a cikinsa. Murmushi ta yi kafin ta miƙe.


"Bari dai mu yi haramar sallah, na ga lokacin Magriba ya gabato. Tashi muje na nunamaki ɗakin Auta ki yi alwala."


Ta amsa da to, daidai sadda wata yar yarinya mai shekaru sha uku ta shigo da sallamarta rangaɗaɗau. Suka dube ta, tana sanye da kayan islamiyyarsu. Yarinya ce ƙarama amma fa akwai ƙiba masha Allah. Ba ta da hasken fata, sai karen hanci da hasken idanu. Ta shigo tana nishi gami da wurgi da jakar hannunta.


"Mama yunwa nake ji wallahi." Ta furta kamar ta yi kuka. Sai ma a sannan ta ankara da Haulatu, sai ta washe baki.


"Lah, Anti Mimi, yaushe ku ka zo Katsina?"


"Ba ita ba ce Bebi, wannan sunanta Anti Haulat, maza raka ta ɗakinki ta yi alwala ki zo ki ci abincin. Ki dauke jakarki kuma."


Ta amsa da toh kafin ta dauki jakar tana ƙara satar kallon Haulatu wacce itama ta ke tsaye tana jiranta. 


*** 

  Zaid El-Yakub. Matashin saurayi son kowa ƙin wacce ta rasa. Allah ya mishi baiwa ta iya lafazi da kuma ilimi na boko da arabi don idan Zaid ya juye harshe yana larabci kai kace balaraben ƙasar Saudia ne, kusan kaf a jikokin gidan maza, su biyu kacal Allah ya ba wannan baiwar ta jin harshen larabci sosai, Zaid da Abeed (Sadaukin Alhaji). Uwa uba kuma ga kyawun fuska ga kuma na gidan rana da Allah ya ba shi. Da murmushinsa kawai, sai ya narkar da zuciyar mace. Mutum ne da ya iya tausar mace musamman idan tana cikin yanayi na fushi da zafi. Sai dai duk da wannan nagartar tasa bai taɓa tara shirgin ƴanmata ba. Ba ya kuma ba da fuskar da ma zancen soyayyar za ta haɗa ku, komai alaƙarka da shi muddin ya fahimci daga ƴan uwantaka ka faɗa kogin kaunarsa to fa zai ja baya da kai ya sauyamaka baki daya. Ko Zaituna ƴar malaysia da ta yi mutuwar sonsa, daga sabo na zumunta ne ya juye a wurinta ya koma so ɗin. A duniya kuwa ba abinda ya tsana sama da auren zumunci, sam ba ya burge shi. Wannan na ɗaya cikin dalilan da ya sanya shi kawo maganar abokiyar karatunsa Jalilah, har a yanzu ta kai su ga aure. Sosai ya yaba da nutsuwarta tun ma zamanin da suke tare a makaranta, tana sonsa sai dai koda alama ba ta taɓa furtawa ba. A karan kansa ya gane hakan. Bai kuma ƙara tabbatarwa ba sai da ya fara zuwa gidansu da sunan zance. Ga shi a yanzu ta kasance mata a gareshi.


"Mutanen Abuja."


Ya ɗago kai daga saman laptop din ya dubi ƙofar, lokaci guda ya saki murmushi gami da shafar sumar kansa da ba ta da yawa. 


"Maama, bismillah."


Bayan ta zauna ya gaishe ta cike da girmamawa. Kafin ta tambaye shi Jalilah. Anan yake sanar da ita ta je gidansu. Ba su wani ɓata lokaci ba yake faɗamata ƙudurinsa na tafiya da Bebi can Abuja wanda Malama ta ce sam ba ta amince ba. Harararsa ta yi kafin ta ja guntun tsaki.


"Ga ka nan dai wani lokacin idan ka yi abu kamar kai ne Autan ba Bebi Ayyush ba. Yanzu Zaid akan wannan ka sanya ni zuwa fisabilillahi? Wannan ai magana ce da a karan kanka ka san ba mai yiwuwa ba ne, Malamar ka ke son ta zauna ita ɗaya a gida?"


Ya yamutse fuska.


"Maama ta ina za ta rayu ita daya, ga Jafar, Nabeel duka, itama Juwairiyya gobe za ta dawo daga Malumfashi. Sannan ba fa hakanan zan tafi da Bebi ba, zaman shirun ne babu dadi, Jalilah na damuwa tunda idan na fita tun safe ba na dawowa sai Magrib. Aron Bebi da za ta ba ni na kwanaki kaɗan ne kafin su yi resuming school. Ina ce ma biki za'a yi nan kusa?"


"Hakane, to Islamiyyar fa?"


Ya yi murmushi.


"Zan koyar da ita a gida."


Maama ta girgiza kai.


"Da ace na san wannan dalilin ka sanya ni zuwa Zaid, tun a waya ba zan amsa maka ba. Ni ka ga tafiyata kafin Haulatu ta ƙosa." 


Ya yi saurin riƙe gefen mayafinta yana mai narkar da wuya.


"Please mana Maama. Wace ce kuma haka da ba za ta iya jira ki taya ni wannan yaƙin ba?"


Takaici ya cika Maama.


"Tsakanin Khaleefa, Mu'az da Sadauki na rasa wanda ya fi wani mayar da ni abokiyar wasansa. Ni fa har yanzu ban dauki wannan magana da muhimmancin da za ka kira ni na zo ba. Wato kai mai mata ko?"


Ya ɗan haɗe fuska. Ta kuma san dalilinsa bai wuce na haɗa shi da Sadauki da ta yi ba. A duniya ta rasa dalilin rashin jituwar Khaleefa da Mu'az, haka Sadauki da Zaid. Idan ka ga kowannensu a wuri guda to tabbatar abu ne na dole babu yanda suka iya kowa cikin zuri'ar na wurin. Amma fa idan an hadun za'a gaisa.  Magana mai karfi zai wahala ta shiga tsakaninsu dai. Zaid da Mu'az ke ɗasawa saboda barkwanci irin na Mu'az, Zaid kuwa na son ababen ban dariya. Khaleefa da Sadauki kuwa tasu ta zo ɗaya idan an haɗu za su yi ta tattaunawa akan abin da ya shafi matsalolin rayuwa da gwamnati. Kowa dai da nashi zaɓin.  Alhaji ya yi nasihar da faɗan, amma ina. A cewarsu su fa lafiya suke zaune da juna kawai dai halayyar ce ta bambanta. 

  

   "Shikenan Maama, zan zo gidan gobe mu ƙara magana. Muje na taka maki."


Ya furta yana mai miƙewa gami da gyara zaman armless rigarsa kalar dark blue gami da zura hannu a aljihun dogon wandonsa marar nauyi fari ƙal. Gaba ɗaya damatsan hannunsa a waje, ko'ina na jikinsa gargasa ne mai laushi duk a kwance. 


Maama ta girgiza kai ta yi murmushi, ta sani sarai sunan Sadauki da ta ambata ne ya ɓata hirar baki daya. A ganin Zaid, Sadauki fa mutum ne mai nuna isa da ganin ya fi kowa a zuri'ar kawai don Alhaji na ji da shi. Wannan ma yana daga dalilin da yasa sam ba ya son sabga ta haɗa su. Idan abu ya haɗa kuwa, koda wani ya kawo shawara, Sadauki zai nuna ba ta yi mishi ba. Nan da nan kuwa mutane da dama za su goyi bayansa. Wannan ma yasa shi ƙara nisanta kansa da shirginsa. 


Har ƙofar falon ya takawa Maama hirarsu suke yi amma fa ta abin da ya shafi babban gidan, Maama ke ce masa ai tare ta zo da jikar Hajiya Babba wacce suka bayyana a gidan kwanaki ita da Ummanta. Ya jinjina kai gami da ɗan ɗaga kafaɗa.


"Na samu labari."


Ya furta cikin nuna ko a jikinsa. Hajja ai ta gama sire mishi a rai tun sadda ta tsinemasa albarka don bai auri jikarta  Zaituna ba. Wannan ma daya ne cikin halin Zaid da sam ba ya burge mutane, riƙo. Shi mutum ne mai riƙo. Ko ya shiga babban gida, kallon ɓangaren Hajja ba ya yi ballantana ya taka ya shiga. Malama ta yi fada ta yi nasihar, amma ya gwammace su gaisa da Hajja idan ya haɗu da ita a tsakar gida ko kuwa falon ɗaya cikin kakannin nasu. A barandar suka rabu, ya koma don ɗauro alwala ya tafi masallaci yana magiya akan Maama ta yi jiransa. Ita kuwa ta shige falon.


***

Bayan idar da sallah suka yi shirin tafiya amma ina, Malama ta ce sai fa sun ci abinci a dole suka haƙura. 


"Ai kin ji, nifa so nake na gudu kafin wannan yaron ya dawo ya tasa ni a gaba akan abin da nima ba zan goyi bayansa ba."


Dariya Malama ta yi jin batun da Maama ke yi.


"Ku dai ku ka sani. Dama ni na san ai babu inda maganar za ta je. To wa zai dauki wannan salon da ya zo da shi?"


Murmushi Maama ta yi. Suna cikin cin abincin sai ga shi ya yi sallama ya shigo. Wannan karon doguwar jallabiya ce jikinsa ruwan makuba mai adon zare ruwan madara. Tun shigowarsa Haulatu ta yi ɗif tana kallonsa kamar yau ta soma ganin wata halitta wai ɗa namiji a duniya. 


 "Shi kuma wannan wane ne?" Ta yi furucin ƙasa-ƙasa. Bebi ta dube ta murya a ɗan sama ta ce.


"Lah, Yaya Zaid ne. Ba ki san shi ba?"


Amsar da Bebi ta bayar ya sa Haulatu ɗan kama leɓɓanta, ashe zancen zucin da take yi ya fito? 


'Wai! Hindatu ba don kin yi aure ba ai da nace ki zo ga miji. Wannan ai shi ake kira mijin novel.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa kauda kai ta yi daga kallonsa ganin sun haɗa idanu. Shi kuwa Zaid ƙarasowa ya yi ya zauna gefen Maama, har a sannan idanunsa ba su ɗauke daga kan Haulatu ba. Ya ji wani tun daga tsakiyar kansa har babban yatsar ƙafarsa. 


"No! Innalillahi! Ya Salam!" Ya furta duka a lokaci daya can ƙasan ransa yana mai yin ƙasa da kai. 


"Yauwa, ka shigo ko? To mu yanzu zamu wuce. Haulatu ba ki gaishe shi ba. Ga Haulatun da nake faɗamaka."


Ya ji zancen Maama, kwarai ya shiga kunnensa. Ya kuma kallon Haulatun karo na biyu. Wannan lokacin itama shi ɗin ta ke kallo da nata dara-daran idanunta na gado. Sai ta kasa sukuni da kallon da yake watsa mata, ita ba ta ma taɓa sanin tana da kunya ba sai a wannan rana. Ta gaida shi ya amsa da motsa leɓɓansa. Bai ƙara magana ba sai shiru, abinci kuwa cewa ya yi sai bayan isha'i. Maama har ta mike hakanan Haulatu da ta ke ji Zaid ya takura mata da kallo ta yi saurin mikewa da gyara zaman ɗankwalin abayarta. 


 Yana ji suka yiwa Malama sallama, miƙewa ya yi jikinsa babu kuzari don ya taka musu. 


Ya dafa motar ya leƙo ta gefen Haulatu, ta ji numfashinta na neman ɗaukewa, ita ba ta taɓa jin namiji kusa da ita har haka ba. Kawai sai ta ji wani iri, shi kuwa kallonta ya yi kafin ya maida idanunsa kan Maama.


"Shikenan sai na shigo din?"


Maama na kokarin tayar da mota ba tare da ta dube shi ba ta amsa.


"Eh Zaid, sai ka shigo. Amma fa ba za ta sauya zani ba. Wancan maganar a bar ta."


Ya yi wani murmushi mai ƙara ƙawata fuskarsa ya dubi Haulatu. Ita dai ba ma kallonsa take yi ba don wannan kusancin ya ishe ta, ga ƙamshin turarensa da ya cika ƙofofin hancinta. 


"Yes, an bar ta. Ganinki kawai zan zo."


"Ai shikenan. Allah ya kawo ka lafiya."


Maama ta ba shi amsa daidai sadda ya matsa jikin motar yana sauke numfashi, daga haka ta ja motar bayan Maigadi ya wangale ƙaton ƙyauren gidan ta fice. Ta ji sadda Haulatu ta sauke ajiyar zuciya.  


"Gajiya ko? Sorry yau dai na saka ki nisa da Ummanki. Yanzu za ki gan mu a gida in sha Allah."


"Uhm." Shi ne kawai abin da ta ce. Daga nan ta ja bakinta ta yi shiru. Ita dai wannan Zaid din bai kwanta mata ba sam, haka kawai yana wani bibiyarta da kallo kamar zai hadiyeta. Ta ja guntun tsaki wanda har ya fito fili, Maama kallonta kawai ta ɗan yi ba tare da ta ce komai ba ta cigaba da tuƙi abinta. 


***

  Washegari haka Safina ta shigo har ɗakinsu tana jan ta da hira. A dole Haulatu ta sake don ta sani ba fa za ta iya rayuwa hakanan babu abokan hira ba tunda yanzu Hindatu ta yi mata nisa. Tun ba ta sake sosai ba har sai ga shi nan suna ƙyaƙyata dariya. A ƙarshe Safina ta yi ta roƙonta kan ta fito su zaga gidan, ba musu kuwa ta biyemata. Ɗan fitar da ta yi da Maama ta ji dadinsa sosai, zuwa lokacin manta ji ba ta kaunar rayuwa a dakin don har falon takan fito. Hajja da Umma abin ya musu dadi. Umma dai dama ta san duk daren dadewa dama za'a zo gurin. 

 Koda ta gansu sun sauki ƙasa ita da Safina murmushi ta yi. Ta maida hankali ga taya Baba Saude girki don acewarta zaman shiru babu wani aiki takura ta yake yi. 


"Umma zamu je mu dawo." Fadin Haulatun. Kai kawai ta gyaɗamata kafin su fice tana sanye da riga doguwa ta atamfa ɗaya daga cikin wacce aka karɓo daga wurin tela. Ta yane kanta da mayafi. Kusan hatta tsawonsu ya zo ɗaya da Safina bayan shekarun da dama ɗaya ne. 


Su shiga can, su faɗa nan, kowa ya ga Haulatu mamakin yanda aka yi Safina ta shawo kanta yake har ta yarda ta fito. A ƙarshe suka ƙarasa ɓangaren Alhaji don gaishe shi. Tun daga ƙofar shiga Safina ta yi saurin dakatawa gami da riƙo hannun Haulatu. Ta dube ta cikin rashin sanin dalilinta. A ɗan tsorace ta ce.


"Ke mu wuce kawai, Yaya Sadauki na ciki. Yanzu kya ji ya balbale ni da faɗan rashin zuwa makaranta alhalin ciwon mara ce ta hana ni ɗazu amma yanzu na warke." Yamutsa fuska ta yi.


"Shi kuma waye hakan?"


Zaro idanu Safina ta yi.


"Ba ki san shi ba? Taɓ. Ai wallahi ya gan ni kashina ya bushe."


Haulatu ta ji wani irin haushin Safina yanda duk ta ruɗe akan wani ɗan adam. Ita a duniya ta tsani ta ga mace mai tsoron namiji kamar haka. Babu ma abin da take tunawa a kanta sai mijin Umma da kuma yanayin shakkarsa da Umman ke yi. 


"Wallahi sai na shiga. Ke dallah taho muje. Ai dai ba zai kashe ki ba ko?"


"Yes, ba zai kashe ta ba. Amma kuma zai hukuntaki ke mai maganar."


Suka juya da sauri. Mu'az ne tsaye a bayansu yana ɗan murmushi. Ba yau ta fara ganinsa ba tunda yana leƙawa wajen Ummanta, kusan ma har sun ɗan fara sabo da Umman. Ita ce dai gaisuwa kawai ke haɗa su nan din ma sai sun hadu ba ta ƙule a ɗaki ba. 


"Ina wuni Yaya Mu'az." Faɗin Safina, ita kuwa Haulatu dai huci take jin abinda ya ce, wai wani ƙato zai hukunta ta. Ita akwai ma namijin da ya isa ya yi mata ba ta rama ba? Ba ta tunanin akwai shi. 


Mu'az na hankalce da yanayin yanda take cika da batsewa. Madadin ya amsa gaisuwar Safina sai ya ƙara fadin.


"Ku shiga mana kun tsaya. Ai ba dodonku ba ne Sadaukin."


Safina dai gaba daya jiki ya dauki rawa, ta zame hannunta daga na Haulatu ta ja baya.


"Aa, dama ni wajen Baba Dakta Daddy ya aike ni. Bari na je."


Kafin Haulatu ta dakatar da ita tuni ta fice da gudu-gudu. Ta ciji lebbanta na ƙasa don takaici ta maido kallonta ga Mu'az wanda shi din ma ita yake kallo da murmushi. Ya lura yarinyar dagaske ƴar diramar da ake faɗi ce. Sai ya ji ta burge shi. Shi yana so ya ga mutum mai kasada a rayuwa marar tsoro. Ko don hakan na daga cikin ɗabi'arsa? Bai dai sani ba. Ya rungume hannuwa a ƙirji ya ce.


"Kin san waye Sadauki kuwa?"


Ba ta san sadda ta ɗan harare shi ba, ya yi ƴar guntuwar dariya mai nuni d mamaki. Shi dai ƙanwar ƙanwarsa ke harara yau? 


"Ko waye shi ai ba mala'ikan daukar rai ba ne. Kuma Allah ma bari ka gani sai na shiga."


Juyawar da za ta yi a fusace ta ci karo da mutum har wayar hannunsa na faɗuwa a ƙas. Ta waro idanu tana kallonsa, shi ɗin ma ita yake kallo ransa a tsananin ɓace.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

  Page 19

'Falon ƴan boko.' Faɗin Haulatu a ƙasan ranta bayan ta bi ko'ina da kallo. Babu tarkace sosai amma fa an zuba kaya masu kyau kalar fari da ruwan zaiba. Zama ta yi saman kujera mai fuskantar wani ɗan corridor inda ta fahimci a can ne ɗakunan matar gidan suke don hanyar da ta ga Maama ta nufa kenan. Dama ta ji ance auren gida Khaleefa ya yi da matarsa. Duk da dai ba zuri'arsu ɗaya ba amma ɗiyar abokin mahaifinsa ne, Barr Dawud. Sun zama tamkar yar uwa na jiki a irin zumuntar dake tsakaninsu da zuri'ar ma baki ɗaya.  Taɓe baki ta yi kamar a lokacin ta ji Hajiya Babba na labartawa Umman. Ita a duniyarta ta rasa dalilin mutane masu ƙaƙabawa kansu son auren zumunci ita dai ba ya burgeta kuma ta ƙudurce a ranta koda a duniya za ta yi aure, ba ma za ta yi irinsa ba musamman a irin wannan gidan nasu da ta ga ba ya rabo da ƙananun magana. 

  Maama ce ta dawo ta zauna gefenta. 


 "Wash! Sannu Haulatu na bar ki ke ɗaya. Meyasa ba ki kunna tv ba? Ai da sai ki kunna ya ɗauke maki hankali. Kin ga ashe Hafsat na sauƙi ya samu sai fatan Allah ya raba lafiya."


Ɗan murmushi ta yi, ina ita ina ƙarfin hali a gidan mugun mutum irin Khaleefa? To a zancen Maama hakan na nufin ciki ne da Hafsat din? Kuma ai ta ji ance suna da ɗa guda daya, amma ba ta ga alamun wani a gidan bayan ƴar aiki ba. Ta dubi Maama, Kafin ta ce wani abu sai ga matar gidan ta taho, Haulatu ta kalle ta. Baƙa ce, irin baƙin nan mai sheƙi da kyau. Tana ɗan tsayi sai dai ba ta kai mijinta ba. Siririya ce, ba laifi daidai gwargwado tana da ɗan karan hancinta da ƙaramin baki wanda ya ƙawata fuskarta. Ga dukkan alamu ita din mace ce mai fara'a don har ta ƙaraso ta zauna fuskarta a sake take. Suka haɗa idanu da Haulatu ta sakarmata murmushi, ganin hakan yasa Haulatun ma maida mata martanin murmushin. 


"Ina wuni. Ya jikin?"


 "Lafiya kalau ƙanwarmu. Ya baƙunta? Koda dai yanzu kin zama ƴar gari ko?"


Ta yi dariya kawai ba ta ce uffan ba. Sai take mamaki, a hakan mace mai sakin fuska da komai, amma Maama a mota take cewa matar ba ta da hali, mijin haƙuri yake yi da ita? Nan da nan kawai ta saka a ranta shi ne ma mugun, shi yake zaluntarta. Dama mazan ai su ke cutar da matayensu a zamantakewa. 

  

  "Atine! Atine!!"


Ta shiga ƙwalawa ƴar aikinta kira. Da rawar jiki yarinyar da ba ta wuce shekaru goma sha uku zuwa huɗu ba ta fito daga wani ɗaki dake jikin falon tana mai durƙusawa a gefe.


"Naam Anti, gani."


"Kawo musu ruwa mana, ke komai sai an faɗamaki?"


"Aa ta bar shi ma, sallah kawai zamu yi mu kama hanya. Yamma ta yi ai. Haulatu da alwalarki ne ko za ki ɗauro?"


Haulatu ta gyaɗa kai. Hafsat ta nunamata bandaki da yatsa, ta mike ta shiga. Koda ta fito tuni har Maama ta tayar da sallah. Itama ta gyara zaman mayafin abayarta ta tayar. 


Suna idarwa kuwa suka yiwa Hafsat sallama suka tafi tana ta godiya. 


 A hanya Haulatu ta kasa haƙuri ta dubi Maama.


"Maama, ni na ji kina cewa matar nan ba ta da hali, kuma sai na ga kamar ba haka ba. Dubi yanda ta karɓe mu da fara'arta da komai fa."


Hankalin Maama na kan titi, murmushi ta yi. 


"Haulatu kenan, ki dinga ce mata Momin Annur, haka yan uwanki ke ce mata. Abu na biyu, ki sani, ba a saurin yankewa mutum hukunci a farkon haɗuwa da shi. Ki bari zama ya yi zama, ko kuwa wata mu'amalar ta haɗa ku, anan za ki gane waye ɗan adam. Hafsat tana da fara'a idan ta ga dama, da ace na bar ki a gidan ki kwanar mata biyu za ki gane halinta. Ba ta son kowa ya raɓe su ita da mijinta. Ba kuma ta yin aiki ko na kawar da tsinke a gidan, wannan dai ƴar yarinyar da kike gani Atine, ita ke shan wahalar aiki. Tana da dattijuwa mai zuwa yi musu girki ta tafi. Abin da ke baƙantawa Khaleefa rai kenan, mace a gidan mijinta, amma ba ta iya girki ba sai dai ƴar aiki ta dafa ta ba shi ya ci. Ga fita aiki da take yi tun safe sai yamma, aikin banki, rashin lafiya ce ta sa kika gan ta a gidan. Ba laifi muna shiri da ita tun farko, mai yiwuwa kuma ganin Khaleefa ɗan gidana ne ya sa itama tamu ta zo ɗaya. Duk shawara ta duniya kafin ya nufi mahaifiyarsa da ita, ni ya ke zuwa mu kashe mu binne ba tare da wani ko wata ya ji ba. Shiyasa za ki ji wasu lokutan ana ce masa Ɗan Maama."


Ta jinjina kai, ta kuwa ji sunan a bakin Baba Saude, duk sadda ta shigo da haka take kiransa idan zasu gaisa. Wayar Maama ce ta yi kara, ba tare da ta duba ba ta cewa Haulatu ta ɗaga ta ga waye. Ba musu ta ɗauki wayar daga gefen Maama ta duba sunan. 


  "Zaid."


Ta furta a fili. Da sauri Maama ta karɓi wayar har fara'arta na ninka na farko. 


"Mutanen Abuja, jiyan nan nake samun shigowarku."


Ko me aka ce, ta yi dariya kafin su gaisa take fadin "Ina Amarya?"


Daga nan ko me aka ce. Ta amsa da fadin.


"Yes na fita ne, gidan Khaleefa na shiga duba jikin Hafsat."


Can kuma kamar magiya yake mata akan ta biyo yana son su yi magana mai muhimmanci ita kuwa fadi take ba za ta zo ba, ya tako gida ya same ta. A karshe dai Haulatu ta ji Maama ta amsa da toh ga ta nan zuwa. Daga haka suka yi sallama. 


 Madadin su yi gida Maama sai ta dauki wata hanyar ta daban, ta dubi Haulatu.


"Kifin rijiya, ke fa aka bar ki sai na kai ki na siyar ma ba ki sani ba ko?"


Dariya suka yi a tare, yau dai ita zuciyarta fari ƙal take jin ta, sosai ta ji dadin wannan fitowar da Maama ta saka ta yi. 


"Maama ai gida zamu yi ko?"


Tana murmushi ta amsa. 


"Zamu biya gidan Zaid. Watansa biyar da aure, Abuja yake da zama yana aiki a ma'aikatar CBN. Ɗa ne ga Malama Safiyya, za ki san su duka a hankali. Zaid shi ne babban ɗanta, shi yake riƙe da gidansu tun bayan rasuwar mahaifinsa, ba don ma aiki da ya kai shi Abuja ba, sam ba ya son ya yi nesa da mahaifiyarsa. Shi sam ba auren zumunci ya yi ba don a ra'ayinsa ma sam ba ya kaunar hakan tun sadda a sanadinsa wata fitinanniya a zuri'armu ta gwada shan maganin ɓera Allah ya kiyaye bai sa ta sheƙa lahira ba, shi kuma ya yi rantsuwa babu kaffara kan ba zai aureta ba. Ƙarshe sai haƙura ta yi amma fa har yanzu ma ba ta yi aure ba."


"Wace ce ita Maama?"


Murmushi Maama ta yi. 


"Yar uwarki ce, ɗiyar Hajiya Nafisa ta Malaysia. Farko a hannun Hajja ta ke don a nan ta soma karatu, faruwar lamarin nan iyayen suka dauke ta, ta koma hannunsu. Ai ba za ta fi shekarunki ba, koda za ta girmeki bai fi da shekara ɗaya. Dalilin da yasa Hajja sam ba ta shiri da Zaid, wai ya kusa kashe mata jika kuma ya ƙi aurenta."


"Uhm" Abin da kawai Haulatu ta ce kenan. Ko ma wace ce yarinyar tunda dai jikar Hajiya Babba ce ta aikata abinda ya fi haka, a cewarta. Daga haka ta cigaba da sauraron hirarrakin abin da ke faruwa a zuri'ar daga bakin Maama har suka iso wani gida. Daga ganin gidan ka san ginin ba na  yau bane sai dai tsaf bai nuni da alamun tsufa sosai ba. 


"Nan gidan Malama ne, anan Zaid suka sauka. Shi bai kai ga kammala gininsa ba. Dama ba ki taɓa ganinta ba ko?"


Ta ƙarashe tana kallon Haulatu. Gyaɗamata kai kawai ta yi. To watakila ma ta taɓa ganin nata amma ba ta san wace ce ba.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 20

Malama ta karɓe su fuska a sake, Haulatu dai daga gaisuwa ba ta ƙara cewa komai ba sai shiru da ta yi tana ƙarewa falon kallo yayinda suke ta hira da Maama. 


"Kinga fa yarona na zo gani ba ke ba. Ya dage na zo akwai magana."


Malama ta ɗan taɓe baki cike da takaici.


"Au, kenan ke ya kira ki taushe ni ko? Aikuwa dai ina nan akan bakana. Ke kam kina son biyewa shiriritar yaran nan naki."


Maama ta yi turus.


"Toh kinga dai ban san komai ba, amma kin ɗauko hanyar fesamin. Wani abun ne ya faru? Ko kuwa bai kai girman da Zaid ya ɗadɗago ni ba?"


"Aa, ai ba kya ji a bakina ba. Waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ki dai je yana can wajen nasa tunda shi ya nemi ki zo. Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, duk za ku zo ku same ni."


Dariya Maama ta yi tana mai miƙewa.


"Allah ya kyauta toh. Har na matsu ma na je na ji meke faruwa. Haulatu ki jira ni."


Ta amsa da toh kawai, bayan ficewar Maama daga falon Malama ta ɗan girgiza kai tana duban Haulatu ta ce.


"Ke kam kin huta da alama ba ki da surutu ko? Koda dai gidan nawa ne ba  abokan hira da yawa.  Yarana duka ukun maza ne, mace ɗaya ce za ki iya ba ta shekaru biyu zuwa uku, ta jw makaranta amma nan kusa za ta dawo."


Murmushi Haulatu ta yi, wai ita ake cewa ba ta da hira. Lallai, don dai Malamar ba ta dan wace ce ita ba. 


"Kina zuwa makaranta a can inda kike?"


Tambayar da Malama ta kara yi ya fahimtar da Haulatu dagaske hirar ta ke so, kuma ga dukkan alamu matar ba ta da girman kai, tun soma zancen fuskarta ma a sake take. Aikuwa ta gyara zama ta shiga labarta mata yanayin karatunta, hatta da irin hantarar da ake mata idan ta fita ana kiran gidansu gidan karuwai babu irin abin da ba ta  kwashe ta faɗawa Malama ba. Sosai tausayinta kuwa  ya mamaye zuciyar Malama Safiyya. Ta kuma karanci abubuwa da dama a kan Haulatun. Yarinyar tana buƙatar nusarwa akan wasu daga cikin ɗabi'u da ladabin magana. A yanayin da ta ke ba ta labarin tamkar da wata sa'arta, kamar misali takan yi amfani da 'Hum, ke na ga rayuwa fa.' Ko kuma ta ce 'Ke ba za ki fahimta ba.' Da dai sauransu. A shekaru da wayewa irin na Malama Safiyya sam ba ta ga laifinta ba duba da yanayin rayuwar da ta taso a ciki, itama mahaifiyarta ba lallai ta samu wadataccen ilimi ba da kuma wayewar mu'amala da mutane ba. Sai ta ji inama za'a yi mata kyautarta koda na watanni ƙalilan ne, ita kuwa za ta yi iya yinta don ganin ta gyara koda kaso sittin ne cikin ɗari na daga ɗabi'unta. Tun zuwan da suka yi gidan, sam ba ta taka ta je ba saboda ta jima kwance ba lafiya, kwanakin nan ne ta ɗan samu ta warware. Amma ta ji labari daga yan uwanta cewa Haulatun ba ta da kunya, wai kowa ya je tana dubansa ne ta maida mishi magana. 

 

 Haka ta yi ta kula da ɗabi'un Haulatun, ita kuwa ko a kanta, bilhaƙƙi take ba ta labari amma ko kusa ba ta ce ga mummunan sana'ar da Mahaifinta ke yi ba don tuni Umma ta kwaɓe ta da furtawa wani, ba kuma ta sa dalilin rufamasa asirin da Umma ke yi ba. Tana dai kokarin nunawa Malama yanda ta tsani ƊanMutuwa a rayuwarta. 


"Allah ya shirye shi idan mai shiryuwa ne. Sai hakuri, abin da ya faru da ku, kaddara ce. Ki saka a ranki haka ya tsara maku. Kin ji ko?" Faɗin Malama Safiyya kenan a ƙoƙarinta na datse zancen iyaka nan ganin hirar ma babu daɗin ji ga ƙarancin ladabin magana da Haulatun ke da shi. 


Aikuwa jin abin da Malama ta fadi yasa Haulatu yin wata dariyar.


"Aikam mun ga rayuwa. Tab din! Ai wallahi Hajja ta rufawa kanta asiri ma da ta karɓe mu idan ba haka ba wallahi daga nan har gidan rediyo."


Ita dai Malama ta cika da ɗumbin mamaki, shakka babu akwai tarin gyara da yarinyar ke buƙata. Ta yi shiru ba ta ƙara uffan ba, ba kuma za ta ce wai ta ji wani tsana ko haushin Haulatu ba face ma tausayin da ta ba ta. Ta san wahalar tarbiyya, ta yi msta uzurin kalar gidan da ta rayu a cikinsa. Murmushi ta yi kafin ta miƙe.


"Bari dai mu yi haramar sallah, na ga lokacin Magriba ya gabato. Tashi muje na nunamaki ɗakin Auta ki yi alwala."


Ta amsa da to, daidai sadda wata yar yarinya mai shekaru sha uku ta shigo da sallamarta rangaɗaɗau. Suka dube ta, tana sanye da kayan islamiyyarsu. Yarinya ce ƙarama amma fa akwai ƙiba masha Allah. Ba ta da hasken fata, sai karen hanci da hasken idanu. Ta shigo tana nishi gami da wurgi da jakar hannunta.


"Mama yunwa nake ji wallahi." Ta furta kamar ta yi kuka. Sai ma a sannan ta ankara da Haulatu, sai ta washe baki.


"Lah, Anti Mimi, yaushe ku ka zo Katsina?"


"Ba ita ba ce Bebi, wannan sunanta Anti Haulat, maza raka ta ɗakinki ta yi alwala ki zo ki ci abincin. Ki dauke jakarki kuma."


Ta amsa da toh kafin ta dauki jakar tana ƙara satar kallon Haulatu wacce itama ta ke tsaye tana jiranta. 


*** 

  Zaid El-Yakub. Matashin saurayi son kowa ƙin wacce ta rasa. Allah ya mishi baiwa ta iya lafazi da kuma ilimi na boko da arabi don idan Zaid ya juye harshe yana larabci kai kace balaraben ƙasar Saudia ne, kusan kaf a jikokin gidan maza, su biyu kacal Allah ya ba wannan baiwar ta jin harshen larabci sosai, Zaid da Abeed (Sadaukin Alhaji). Uwa uba kuma ga kyawun fuska ga kuma na gidan rana da Allah ya ba shi. Da murmushinsa kawai, sai ya narkar da zuciyar mace. Mutum ne da ya iya tausar mace musamman idan tana cikin yanayi na fushi da zafi. Sai dai duk da wannan nagartar tasa bai taɓa tara shirgin ƴanmata ba. Ba ya kuma ba da fuskar da ma zancen soyayyar za ta haɗa ku, komai alaƙarka da shi muddin ya fahimci daga ƴan uwantaka ka faɗa kogin kaunarsa to fa zai ja baya da kai ya sauyamaka baki daya. Ko Zaituna ƴar malaysia da ta yi mutuwar sonsa, daga sabo na zumunta ne ya juye a wurinta ya koma so ɗin. A duniya kuwa ba abinda ya tsana sama da auren zumunci, sam ba ya burge shi. Wannan na ɗaya cikin dalilan da ya sanya shi kawo maganar abokiyar karatunsa Jalilah, har a yanzu ta kai su ga aure. Sosai ya yaba da nutsuwarta tun ma zamanin da suke tare a makaranta, tana sonsa sai dai koda alama ba ta taɓa furtawa ba. A karan kansa ya gane hakan. Bai kuma ƙara tabbatarwa ba sai da ya fara zuwa gidansu da sunan zance. Ga shi a yanzu ta kasance mata a gareshi.


"Mutanen Abuja."


Ya ɗago kai daga saman laptop din ya dubi ƙofar, lokaci guda ya saki murmushi gami da shafar sumar kansa da ba ta da yawa. 


"Maama, bismillah."


Bayan ta zauna ya gaishe ta cike da girmamawa. Kafin ta tambaye shi Jalilah. Anan yake sanar da ita ta je gidansu. Ba su wani ɓata lokaci ba yake faɗamata ƙudurinsa na tafiya da Bebi can Abuja wanda Malama ta ce sam ba ta amince ba. Harararsa ta yi kafin ta ja guntun tsaki.


"Ga ka nan dai wani lokacin idan ka yi abu kamar kai ne Autan ba Bebi Ayyush ba. Yanzu Zaid akan wannan ka sanya ni zuwa fisabilillahi? Wannan ai magana ce da a karan kanka ka san ba mai yiwuwa ba ne, Malamar ka ke son ta zauna ita ɗaya a gida?"


Ya yamutse fuska.


"Maama ta ina za ta rayu ita daya, ga Jafar, Nabeel duka, itama Juwairiyya gobe za ta dawo daga Malumfashi. Sannan ba fa hakanan zan tafi da Bebi ba, zaman shirun ne babu dadi, Jalilah na damuwa tunda idan na fita tun safe ba na dawowa sai Magrib. Aron Bebi da za ta ba ni na kwanaki kaɗan ne kafin su yi resuming school. Ina ce ma biki za'a yi nan kusa?"


"Hakane, to Islamiyyar fa?"


Ya yi murmushi.


"Zan koyar da ita a gida."


Maama ta girgiza kai.


"Da ace na san wannan dalilin ka sanya ni zuwa Zaid, tun a waya ba zan amsa maka ba. Ni ka ga tafiyata kafin Haulatu ta ƙosa." 


Ya yi saurin riƙe gefen mayafinta yana mai narkar da wuya.


"Please mana Maama. Wace ce kuma haka da ba za ta iya jira ki taya ni wannan yaƙin ba?"


Takaici ya cika Maama.


"Tsakanin Khaleefa, Mu'az da Sadauki na rasa wanda ya fi wani mayar da ni abokiyar wasansa. Ni fa har yanzu ban dauki wannan magana da muhimmancin da za ka kira ni na zo ba. Wato kai mai mata ko?"


Ya ɗan haɗe fuska. Ta kuma san dalilinsa bai wuce na haɗa shi da Sadauki da ta yi ba. A duniya ta rasa dalilin rashin jituwar Khaleefa da Mu'az, haka Sadauki da Zaid. Idan ka ga kowannensu a wuri guda to tabbatar abu ne na dole babu yanda suka iya kowa cikin zuri'ar na wurin. Amma fa idan an hadun za'a gaisa.  Magana mai karfi zai wahala ta shiga tsakaninsu dai. Zaid da Mu'az ke ɗasawa saboda barkwanci irin na Mu'az, Zaid kuwa na son ababen ban dariya. Khaleefa da Sadauki kuwa tasu ta zo ɗaya idan an haɗu za su yi ta tattaunawa akan abin da ya shafi matsalolin rayuwa da gwamnati. Kowa dai da nashi zaɓin.  Alhaji ya yi nasihar da faɗan, amma ina. A cewarsu su fa lafiya suke zaune da juna kawai dai halayyar ce ta bambanta. 

  

   "Shikenan Maama, zan zo gidan gobe mu ƙara magana. Muje na taka maki."


Ya furta yana mai miƙewa gami da gyara zaman armless rigarsa kalar dark blue gami da zura hannu a aljihun dogon wandonsa marar nauyi fari ƙal. Gaba ɗaya damatsan hannunsa a waje, ko'ina na jikinsa gargasa ne mai laushi duk a kwance. 


Maama ta girgiza kai ta yi murmushi, ta sani sarai sunan Sadauki da ta ambata ne ya ɓata hirar baki daya. A ganin Zaid, Sadauki fa mutum ne mai nuna isa da ganin ya fi kowa a zuri'ar kawai don Alhaji na ji da shi. Wannan ma yana daga dalilin da yasa sam ba ya son sabga ta haɗa su. Idan abu ya haɗa kuwa, koda wani ya kawo shawara, Sadauki zai nuna ba ta yi mishi ba. Nan da nan kuwa mutane da dama za su goyi bayansa. Wannan ma yasa shi ƙara nisanta kansa da shirginsa. 


Har ƙofar falon ya takawa Maama hirarsu suke yi amma fa ta abin da ya shafi babban gidan, Maama ke ce masa ai tare ta zo da jikar Hajiya Babba wacce suka bayyana a gidan kwanaki ita da Ummanta. Ya jinjina kai gami da ɗan ɗaga kafaɗa.


"Na samu labari."


Ya furta cikin nuna ko a jikinsa. Hajja ai ta gama sire mishi a rai tun sadda ta tsinemasa albarka don bai auri jikarta  Zaituna ba. Wannan ma daya ne cikin halin Zaid da sam ba ya burge mutane, riƙo. Shi mutum ne mai riƙo. Ko ya shiga babban gida, kallon ɓangaren Hajja ba ya yi ballantana ya taka ya shiga. Malama ta yi fada ta yi nasihar, amma ya gwammace su gaisa da Hajja idan ya haɗu da ita a tsakar gida ko kuwa falon ɗaya cikin kakannin nasu. A barandar suka rabu, ya koma don ɗauro alwala ya tafi masallaci yana magiya akan Maama ta yi jiransa. Ita kuwa ta shige falon.


***

Bayan idar da sallah suka yi shirin tafiya amma ina, Malama ta ce sai fa sun ci abinci a dole suka haƙura. 


"Ai kin ji, nifa so nake na gudu kafin wannan yaron ya dawo ya tasa ni a gaba akan abin da nima ba zan goyi bayansa ba."


Dariya Malama ta yi jin batun da Maama ke yi.


"Ku dai ku ka sani. Dama ni na san ai babu inda maganar za ta je. To wa zai dauki wannan salon da ya zo da shi?"


Murmushi Maama ta yi. Suna cikin cin abincin sai ga shi ya yi sallama ya shigo. Wannan karon doguwar jallabiya ce jikinsa ruwan makuba mai adon zare ruwan madara. Tun shigowarsa Haulatu ta yi ɗif tana kallonsa kamar yau ta soma ganin wata halitta wai ɗa namiji a duniya. 


 "Shi kuma wannan wane ne?" Ta yi furucin ƙasa-ƙasa. Bebi ta dube ta murya a ɗan sama ta ce.


"Lah, Yaya Zaid ne. Ba ki san shi ba?"


Amsar da Bebi ta bayar ya sa Haulatu ɗan kama leɓɓanta, ashe zancen zucin da take yi ya fito? 


'Wai! Hindatu ba don kin yi aure ba ai da nace ki zo ga miji. Wannan ai shi ake kira mijin novel.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa kauda kai ta yi daga kallonsa ganin sun haɗa idanu. Shi kuwa Zaid ƙarasowa ya yi ya zauna gefen Maama, har a sannan idanunsa ba su ɗauke daga kan Haulatu ba. Ya ji wani tun daga tsakiyar kansa har babban yatsar ƙafarsa. 


"No! Innalillahi! Ya Salam!" Ya furta duka a lokaci daya can ƙasan ransa yana mai yin ƙasa da kai. 


"Yauwa, ka shigo ko? To mu yanzu zamu wuce. Haulatu ba ki gaishe shi ba. Ga Haulatun da nake faɗamaka."


Ya ji zancen Maama, kwarai ya shiga kunnensa. Ya kuma kallon Haulatun karo na biyu. Wannan lokacin itama shi ɗin ta ke kallo da nata dara-daran idanunta na gado. Sai ta kasa sukuni da kallon da yake watsa mata, ita ba ta ma taɓa sanin tana da kunya ba sai a wannan rana. Ta gaida shi ya amsa da motsa leɓɓansa. Bai ƙara magana ba sai shiru, abinci kuwa cewa ya yi sai bayan isha'i. Maama har ta mike hakanan Haulatu da ta ke ji Zaid ya takura mata da kallo ta yi saurin mikewa da gyara zaman ɗankwalin abayarta. 


 Yana ji suka yiwa Malama sallama, miƙewa ya yi jikinsa babu kuzari don ya taka musu. 


Ya dafa motar ya leƙo ta gefen Haulatu, ta ji numfashinta na neman ɗaukewa, ita ba ta taɓa jin namiji kusa da ita har haka ba. Kawai sai ta ji wani iri, shi kuwa kallonta ya yi kafin ya maida idanunsa kan Maama.


"Shikenan sai na shigo din?"


Maama na kokarin tayar da mota ba tare da ta dube shi ba ta amsa.


"Eh Zaid, sai ka shigo. Amma fa ba za ta sauya zani ba. Wancan maganar a bar ta."


Ya yi wani murmushi mai ƙara ƙawata fuskarsa ya dubi Haulatu. Ita dai ba ma kallonsa take yi ba don wannan kusancin ya ishe ta, ga ƙamshin turarensa da ya cika ƙofofin hancinta. 


"Yes, an bar ta. Ganinki kawai zan zo."


"Ai shikenan. Allah ya kawo ka lafiya."


Maama ta ba shi amsa daidai sadda ya matsa jikin motar yana sauke numfashi, daga haka ta ja motar bayan Maigadi ya wangale ƙaton ƙyauren gidan ta fice. Ta ji sadda Haulatu ta sauke ajiyar zuciya.  


"Gajiya ko? Sorry yau dai na saka ki nisa da Ummanki. Yanzu za ki gan mu a gida in sha Allah."


"Uhm." Shi ne kawai abin da ta ce. Daga nan ta ja bakinta ta yi shiru. Ita dai wannan Zaid din bai kwanta mata ba sam, haka kawai yana wani bibiyarta da kallo kamar zai hadiyeta. Ta ja guntun tsaki wanda har ya fito fili, Maama kallonta kawai ta ɗan yi ba tare da ta ce komai ba ta cigaba da tuƙi abinta. 


***

  Washegari haka Safina ta shigo har ɗakinsu tana jan ta da hira. A dole Haulatu ta sake don ta sani ba fa za ta iya rayuwa hakanan babu abokan hira ba tunda yanzu Hindatu ta yi mata nisa. Tun ba ta sake sosai ba har sai ga shi nan suna ƙyaƙyata dariya. A ƙarshe Safina ta yi ta roƙonta kan ta fito su zaga gidan, ba musu kuwa ta biyemata. Ɗan fitar da ta yi da Maama ta ji dadinsa sosai, zuwa lokacin manta ji ba ta kaunar rayuwa a dakin don har falon takan fito. Hajja da Umma abin ya musu dadi. Umma dai dama ta san duk daren dadewa dama za'a zo gurin. 

 Koda ta gansu sun sauki ƙasa ita da Safina murmushi ta yi. Ta maida hankali ga taya Baba Saude girki don acewarta zaman shiru babu wani aiki takura ta yake yi. 


"Umma zamu je mu dawo." Fadin Haulatun. Kai kawai ta gyaɗamata kafin su fice tana sanye da riga doguwa ta atamfa ɗaya daga cikin wacce aka karɓo daga wurin tela. Ta yane kanta da mayafi. Kusan hatta tsawonsu ya zo ɗaya da Safina bayan shekarun da dama ɗaya ne. 


Su shiga can, su faɗa nan, kowa ya ga Haulatu mamakin yanda aka yi Safina ta shawo kanta yake har ta yarda ta fito. A ƙarshe suka ƙarasa ɓangaren Alhaji don gaishe shi. Tun daga ƙofar shiga Safina ta yi saurin dakatawa gami da riƙo hannun Haulatu. Ta dube ta cikin rashin sanin dalilinta. A ɗan tsorace ta ce.


"Ke mu wuce kawai, Yaya Sadauki na ciki. Yanzu kya ji ya balbale ni da faɗan rashin zuwa makaranta alhalin ciwon mara ce ta hana ni ɗazu amma yanzu na warke." Yamutsa fuska ta yi.


"Shi kuma waye hakan?"


Zaro idanu Safina ta yi.


"Ba ki san shi ba? Taɓ. Ai wallahi ya gan ni kashina ya bushe."


Haulatu ta ji wani irin haushin Safina yanda duk ta ruɗe akan wani ɗan adam. Ita a duniya ta tsani ta ga mace mai tsoron namiji kamar haka. Babu ma abin da take tunawa a kanta sai mijin Umma da kuma yanayin shakkarsa da Umman ke yi. 


"Wallahi sai na shiga. Ke dallah taho muje. Ai dai ba zai kashe ki ba ko?"


"Yes, ba zai kashe ta ba. Amma kuma zai hukuntaki ke mai maganar."


Suka juya da sauri. Mu'az ne tsaye a bayansu yana ɗan murmushi. Ba yau ta fara ganinsa ba tunda yana leƙawa wajen Ummanta, kusan ma har sun ɗan fara sabo da Umman. Ita ce dai gaisuwa kawai ke haɗa su nan din ma sai sun hadu ba ta ƙule a ɗaki ba. 


"Ina wuni Yaya Mu'az." Faɗin Safina, ita kuwa Haulatu dai huci take jin abinda ya ce, wai wani ƙato zai hukunta ta. Ita akwai ma namijin da ya isa ya yi mata ba ta rama ba? Ba ta tunanin akwai shi. 


Mu'az na hankalce da yanayin yanda take cika da batsewa. Madadin ya amsa gaisuwar Safina sai ya ƙara fadin.


"Ku shiga mana kun tsaya. Ai ba dodonku ba ne Sadaukin."


Safina dai gaba daya jiki ya dauki rawa, ta zame hannunta daga na Haulatu ta ja baya.


"Aa, dama ni wajen Baba Dakta Daddy ya aike ni. Bari na je."


Kafin Haulatu ta dakatar da ita tuni ta fice da gudu-gudu. Ta ciji lebbanta na ƙasa don takaici ta maido kallonta ga Mu'az wanda shi din ma ita yake kallo da murmushi. Ya lura yarinyar dagaske ƴar diramar da ake faɗi ce. Sai ya ji ta burge shi. Shi yana so ya ga mutum mai kasada a rayuwa marar tsoro. Ko don hakan na daga cikin ɗabi'arsa? Bai dai sani ba. Ya rungume hannuwa a ƙirji ya ce.


"Kin san waye Sadauki kuwa?"


Ba ta san sadda ta ɗan harare shi ba, ya yi ƴar guntuwar dariya mai nuni d mamaki. Shi dai ƙanwar ƙanwarsa ke harara yau? 


"Ko waye shi ai ba mala'ikan daukar rai ba ne. Kuma Allah ma bari ka gani sai na shiga."


Juyawar da za ta yi a fusace ta ci karo da mutum har wayar hannunsa na faɗuwa a ƙas. Ta waro idanu tana kallonsa, shi ɗin ma ita yake kallo ransa a tsananin ɓace.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 21

Ɗan Mutuwa bai yi tsammanin za'a shafe sama da sati ba balle har a tunkari wata ɗaya bai ji labari cewa Umma ta dawo gidansa neman inda yake ba. Kansa ya ƙulle baki ɗaya, ya kuma rasa mene ne abin yi? Shi ba wai neman Umma yake da zummar yana kaunarta ko son cigaba da zama da ita ba a rayuwa, aa, ko kadan, sai dai yana so ne ya koyamata hankali daga ita har Haulatun da bai taɓa jin ƙauna irin na ƴa da uba ba a kanta. Duka wannan kwanakin ya yi su ne a gidan gona a can Gwarzo. Ya kuma gaji da zaman, ya ƙosa komai ya lafa ya san inda dare ya mishi. Ya ji labarin an yankewa su Maada hukuncin zama a gidan yari na wasu shekaru wanda ya sani babu inda zancen zai je za'a sallame su, su fito tunda su ke da manya a sama. 

  Yau ma waya yake yi da Hajiya Adama Loma inda yake mata ƙorafin shi fa ya gaji da zaman marinar nan da yake yi. 


"Toh yanzu kai Ɗan Mutuwa idan ka fito ina ka dosa? Kar fa ka manta har yanzu wutar can ba ta mutu ba. Ana nemanka ruwa a jallo."


Ya ja guntun tsaki ransa a ɓace yake fadin.


"Ana nema na, ai ba Kanon zan koma ba. A san yanda za'a yi dai ko wani garin nesa da Kano ne na koma can na shimfiɗa sabuwar rayuwata. Kuma kina sane da cewa ina da labarin zuwan Oga a satinnan. Ya kamata ki yi duk abin da ya dace nima na samu halattar zuwa taron nan, akwai burin da nake son Oga ya cikamin shi. Ko ba komai, ai na jima ina nawa ƙoƙarin wajen tafiyar da harƙallar mu."


Ta yi ƴar dariya ta cikin wayar. 


"Wannan ne kaɗai damuwarka? Toh ka kwantar da hankalinka, jibi ne dai za'a gudanar da taron, zamu san yanda za'a yi ka halarta. Har yanzu babu labarin matarka ko?"


Ya ƙara jan tsaki karo na biyu, ta sosa mishi inda ke mai ƙaiƙayi.


"Babu, amma ni na sani wancan munafukin makwafcin nawa da sanya hannunsa a kuɓutar su. Kuma ya san inda take, ban kuma san dabarar da zan yi na sani ba."


"Babu wani wuri da kake tunanin za ta je? Ko dangin uba ko na uwa?"


Ya yi wata dariya ta zallar rainin wayo.


"Ke ma dai Adama da mantuwa kike. Na'imatu fa ɗiyar Mai Kalangu, toh har wani dangi gare ta? Haihuwar bariki rainon karuwai? Ko ni nan da nake mata kurin na san asalinta ƙarya ce kawai da kuma barazanar kada ta yi gangancin guduwa ta bar ni. Abu daya da na sani, ubanta da uwarta ƴan Katsina ne. Ke bar wannan batu fa, amma ai har ta mutu ba za ta samu wani a danginsu ba. Na dai fi tunanin duniya ta shiga. Idan kuwa nan ne, samunta ba zai wahala ba. Mu ne barikin."


Suka kwashe da dariya. 


"Shegen sama, wai kura ta hangi biri. Ɗan Mutuwa namu kenan. Wato idan ana neman baƙin mugu aka same ka a shafa fatiha."


"Af, ai kifin ruwa ba ya gasa da na kogi. Na'imatu da ni take zancen, duk inda take dai ai ba za ta sauya daga matata ba ko? Toh kuwa za ta je ta dawo ta same ni tunda ba ta da gatan da ya wuce ni. Kuma a lokacin zan murza kambuna."


"Atoh. Ka san da hakan ma kake tada jijiyar wuya? Kai da ma za ka yi aure kwanan nan?"


Dan Mutuwa ya yi dariyar nishadi tunawa da abar kaunarsa Lantana, 


Daga haka suka tattauna dangane da abin da ya shafi harƙallarsu ta miyagun ƙwayoyi.


  Babban Ogansu ne wanda ya ke na kusa da manya manyan kusoshin gwamnati wadanda matsayin Ɗan Mutuwa da ma na Hajiya Adama ba su kai girman su san su ba, shi ne zai bayyana a babban taron da za su gudanar kan matsalar dake shirin tunkaro su, tun bayan zaɓe da ya gudana a ƙasar baki daya sai ya kasance mutanensu da yawa an sauke su daga muƙamansu. Waɗanda ke kai kuwa masu gyara musu hanyoyin ɓarna  a baya, yanzun duk ba su da wani ƙarfin ikon a zo a gani. Ga wasu manyan shugabanni masu tsoron Allah da suka fara tono asirin wasu a ciki inda suka kama wasu motoci manya har biyu dauke da hodar iblis da ma codein. A yanzu haka ana kan binciken wani tsohon Sanata a garin Gombe wanda suke ji da shi. Abin da ya sa za su yi taron kenan da ma dai duk wani abu da za su ƙara kiyayewa. 


  Wannan kenan.


***

   Ta murtsuke idanunta ganin wani kwali ajiye gefen gado kamar na waya, ta ƙara murtsukawa karo na biyu ai kawai sai ta miƙe zaune babu shiri gami da kai hannu ta ɗauka. Akwai ƙaramar takarda a jikin kwalin an rubuta. 

 "Ƴar ƙauye, nasan mafi yawa kanawa ba sa jin turanci ko? Naki ne, daga ɗan uwanki, MM."


Ƴar Ƙauyen da ta gani ya sa ta gane Mu'az ne. Kafin ta kai ga magana sai ga Umma ta shigo dakin. Lokacin sha biyu na rana ya gota. 


Umma ta shirya tsaf ta yi kyau, idan ka ga yanda fatarta ta goge kai ka ce ba ta taɓa ɗanɗana wata wahala ta rayuwa ba sai dai a can ƙasan ranta akwai damuwar da ta lulluɓe ta musamman ma da Baba Dakta suka tabbatar mata cewa duk iya binciken da aka yi ba a gano inda Ɗan Mutuwa yake ba , so suke a kama shi a hannu kafin a zartar da kowane hukunci. Rabuwa kam dama sun ce dole a raba aurenta da shi. Ita tashin hankalinta, bai wuce kar ya ƙara yunƙurin raba ta da Haulatu ba. Don batun ma za a iya kama Ɗan Mutuwa a wasa ta dauke shi. Ai ba yau aka taɓa kwata kamensa ba akan zargin siye da siyarwar miyagun ƙwayoyi amma  kwanansa biyu kacal aka sake shi. Wannan maganar tsohuwa ce tun ma ba ta san za ta haifi Haulatu ba. 


"Kin tashi? Ga waya Mu'azu ya siyomaki, nima ya sauyamin tawa. Sai ki mishi godiya."


Duk da haushin da yake ba ta sai da ranta ya yi sanyi babu ma kamar na Umma da ta ce ya sauyamata. Aikuwa jiki na rawa ta bude kwalin lokaci guda ta dubi Umma tana dariyar farin ciki.


"Umma, Iphone ce fa? Wai Allahna. Kai! Dama zan riƙe wannan wayar a duniya? Umma ke wace iri ya kawo maki?"


Umma ta ɗan yamutsa fuska.


"Na ji ance samsan ne ko sansam? Ga ta can dai gefen gadon."


Haulatu ta kwashe da dariya.


"Kai Umma, kar ki bari wannan ɗan rainin hankalin Mu'az ya jiki, a takarda rubutu ya yimin da Hausa, wai kanawa ba mu iya turanci ba. Yanzu idan ya ji kin kasa furta sunan wayar ai sai ya samu abin dariya. Samsung ake cewa."


Ta kai karshe tana saukowa daga saman gadon gami da daukar wayar Umma dake ajiye sabuwa fil sai sheƙi take yi. Da murmushi Umma ta girgiza kai gami da fadin.


"Ki dai tashi ki yi wanka, ace daga sallar asuba ki koma bacci kamar mai baccin mutuwa har sha biyun rana? Yau za'a karɓi lefen ƴan uwanki, kinsan gidan dai baƙi za'a yi."


Ranta fari ƙal ba ta ji komai da wani taro da za'a yi ba. Asalima ita murna take yi wai yau ita ke riƙe da babbar waya, babban burinta kawai ta gan ta a whatsapp yanda za ta ba Hindatu mamaki. Dama ta sha mata mitar wai ba ta hawa whatsapp ballantana su yi hira sosai. Har Umma ta fice tana nan tana sarrafa wayar Iphone wacce komai an saita hatta da layi an saka mata Mtn da Airtel. Shigowar Safina ɗakin da sallama ya sa ta miƙewa kamar wacce aka tsikara da murnarta ta ke nunamata wayar da Mu'az ya kawo mata har da ta Umma. Sosai Safina ta taya ta murna. Daga haka ta shige bandaki don yin wanka ita kuwa Safina takardar da ta gani ta jawo ta karanta. Dariya ta kwashe da ita, Yaya Mu'az akwai tsokana. Wannan halin nasa na sakin fuska na burge ta. Ta ƙurawa rubutun idanu tana kallo, ji take yi ina ma kalaman soyayya ne ya rubuto mata? Ta riƙe takardar a wurinta don ita kam tana son kalar rubutunsa. Har Haulatu ta fito tana zaune ta kira lambarta daga wayar Haulatun bayan ta duba ta ga akwai katin dubu daya a kowane layin. Ta adana lambar Haulatun a wayarta sannan ta adana nata lambar a wayar Haulatun, tana wannan aikin suna hira ita kuwa tana shiryawa gami da mitar yunwa take ji. 


  Tare suka fito falon Hajja. Nan suka iske Hajiya Hadiza da budurwa ɗiyarta sai Ihsan da kuma autanta Areef. Sai wata farar mace kamar ka taɓa jini ya fito mai jiki, ta tuna kan su fito ta ji Safina tana fadin Mamarta ta zo. Jikinta ya ba ta ita ce ko ba komai suna kama. 


 Ihsan da ƙanwarta Fahima dake aikin latsa waya, tun shigowar Haulatu falon suke dubanta da mamakin irin sauyawar da ta yi, fatarnan ta ƙara haske ga ɗan cika da ta yi ba kamar a farkon zuwanta ba. Taɓe baki Fahima ta yi ta kauda kai tana huci, ita tun da ta ji Hajja na ba su labarin wai Yaya Mu'az ya siyo musu manyan wayoyi ta ji wani ƙululun baƙin ciki, wato abu ne da bai taɓa haɗa ta da shi ba. Ba ya ma sakarmusu fuska idan ba Safina ba da suke ɗan ɗasawa. Zai yi dai hira da annashuwa idan yana tare da iyayensu amma su kam sai ba da umarni kawai. 


  Mahaifiyarsu Hajiya Hadiza kuwa, kallon Haulatu take da murmushin yaƙe amma can ƙasan ranta zallar takaici da ɓacin rai ne. Ta yi iyaka kokari wajen ganin ta gasawa Umma magana a bayan idanun Hajja ta yanda Umman za ta fice don kanta ta bar gidan amma haƙanta bai cimma ruwa ba domin Umma hakanan ta shanye dukkan zantukanta, kuma ba ta jin Umman akwai mahaluƙin da ta yiwa zancen. Da ace ta furzar, tabbas za ta fuskanci ɓacin rai wajen Hajja. 


 Umma kuwa sam ba ta kallonta da komai, ta bayar a ranta kawai zafi ta ji a sannan sakamakon ba kowace zuciya ce dama za ta kaunaceka ba. Ba kowa ne zai yarda da mutumin da rana tsaka zai shigo rayuwarsu da sunan shi ɗin tsatsonsu ne ba. Ta kuma yi mata wannan uzurin, ba ta sa a rai dole Hadiza da ma sauran kannenta yaran Hajja su ba ta girma ba, ko kusa a'a, balle hakan ya dame ta.


 "Ina wuninku." Haulatu ta gaishe su da ɗan bada girma. Suka amsa fuska a sake. 


"Masha Allah, Na'imatu wannan budurwar ɗiyar taki ai da ina da babban ɗa namiji shi zan aurawa." Fadin Hajiya Fatima kenan mahaifiyar Safina. Umma ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba. Fahima kuwa hankalinta na ga wayar dake riƙe a hannun Haulatun. Ai ba ta san lokacin da ta miƙe zaune sosai ba tana ƙara waro idanunta kan wayar. 


"Kutmar! Iphone 13 pro max nake gani wai a hannunki? Shi ne wayar da Yaya Mu'az ya siyamaki? Lallai ma Yaya Mu'az, matar da ba ta san darajar wayar ba ma balle wani pro.."


Ta haɗiye sauran zancen da ke tafe a bakinta sakamakon ganin wanda ya shigo ya kuma yi tsaye a ƙofa yana kallonta fuskarnan a murtuke. Sadauki ne. Shigowarsa falon dalilin Alhaji ne wanda ya nuna ɓacin rai kan ƙin zuwa da ya yi su gaisa da ɗiyar Hajja. Har ya jawo Alhaji Ridwan dake wurin yi mishi faɗa shi ma sosai gami da nunamasa rashin kyautuwar hakan. Yana sanye cikin wani tsadadden yadinsa ruwan toka an mishi ƙaramin aiki a wuya da h ceannuwan bakin rigar. Ya sanya hular da ake kira da Minista kalar yadin sai dai ya ciza. 

    

  "Fahima, kina cikin hayyacinki kuwa? Toh ko uwarki ba ta isa ta yi wannan rashin mutuncin a gabana ba balle ke haihuwar yau!" Hajja kert ga wannan sababin a lokaci guda tana miƙewa tsaye har zaninta na neman kuncewa tana ɗorawa. Fahima dai tun kallon da ta bi Sadauki da shi ta ji hantar cikinta ya kaɗa. Kafin shi kansa ko wani ma ya ƙara yunƙurin wani abu, Haulatu da ta fusata ta isa dab da Fahima, ji take yi tamkar ta dauke ta da mari sai dai ta kai zuciya nesa ta dunƙule hannunta na dama ta  shiga maida martani ba tare da ta damu ta ƙara kallon Sadauki a karo na biyu ba don a ɗazun katse zancen da Fahima ta yi kowa ya ankara da shi.  


 "Kin ƙara yunƙurin ci mana mutunci karo na biyu, na rantse maki duk radda ki ka ƙara gangancin yin na uku sai na nuna maki ba ki da wayo.  Banza mai warin baki. Ke har kina da bakin kallona ki ce ban kai na riƙe wayar nan ba? Eh ban san darajarta ba kuma na mallaki abin da na tabbata ko ƙamshinsa ba ki taɓa ji ba. Tsabar baƙin ciki da hassada irin naki wato har ki kasa ɓo.."


"Ya isa, Haulatu rufemin baki kan ranki ya ɓa..."


Kafin Umma ta ƙarasa Haulatu ta dube ta ranta na zafi ta katse ta.


"Umma ki yi shiru don Allah, ki bar ni na nunawa wannan.." Ba ta kai aya ba ta ji saukar mari tas! A gigice ta dube shi, duba na tsantsar tsana. Yau ita namiji ya mara? Tabbas ta sani, duka halinsu guda ne. Hajja kira take "A'a A'a Sadauki amma ina! Sai da ya aiwatar da marin. Sam a farko bai yi niyyar hukunta ta ba, ya ji zafi da mamakin maganganun da suka fito a bakin Fahima, sai dai yarinyar ta nunamasa ba ta da kunyar dagaske. Ransa a tsananin ɓace yake dubanta. Murya a kausashe ya ke magana.


"Ƙaryarki, kin ci ƙarya ki zo gaban jama'a kina rashin kunya a zuba idanu a kyale ki. Har ana dakatar da ke kina botsarewa? Wannan koda ba mahaifiya take gunki ba sa'arki ce?"


"Ai bari faɗi ma, mahaifiyarta ce ita ta haife ta." Umma ta sunkuyar da kai jin amsar da Hajiya Hadiza ta bayar. Zuciyarta a cunkushe, wai yaushe Haulatu za ta nutsu ne ta koyi haƙuri a rayuwa. 


"Ɓace ki bani wuri." Ta dube shi tana haɗiyar yawu mai ɗaci kafin ta juya da sauri bayan ta saki wayar a tsakar falon ta fice ɗaki cike da zafin rai. Safina da sauri ta sa hannu za ta dauki wayar ya dakatar da ita, ɗauka ya yi ya jefa a aljihun wandonsa, ganin haka ta juya ta bi bayan Haulatu ɗaki. Fahima kuwa kallo ya watsa mata kafin ya ba ta umarnin fita waje ta yi jiransa. 


Sai kuma ya dawo daidai tamkar ba shi ba. Hajja ta cika ta yi fam tana mitar don me zai mari wacce aka zalunta alhalin ba ita ke da laifi ba taɓo ta aka yi, bai ko biyewa ƙorafin Hajja ba ya maida hankali ga Umma ya gaishe ta a mutunce. Ta amsa tana murmushin da ta saba yi na danne damuwa wanda ya zamo ɗaya cikin ɗabi'unta. Koda ya yi musu sallama ya fita, Hajja miƙewa ta yi ta nufi ɗakin don rarrashin Haulatu


"Allah yasa kar ta ba ki kunya." Cewar Ihsan tana dariya don ranta ya yi haske da marin da aka wanke Haulatu da shi. Umma dai ba ta ce uffan ba. 


 Fahima kuwa wayarta yasa ta koma ta ɗauko ya karɓe kafin ya kuma rantse muddin ya kuskura ya ji labarin ta riƙe waya sai ya yi mugun saɓa mata. Wannan hukuncin ya yiwa Fahima tsauri matuƙa, dama mahaifinta mai shegen tsaurin bala'i da ya ya bata wayar? Sai da ya bi ta da ruwan kashedi iri iri na muddin ya kama ta da wani laifin to fa babu ita ba riƙe waya sai a dakin mijinta. Ballantana kuma ya ji Sadauki ne ya ƙwace, ai kuwa ta shiga uku, zai dau lamarin ba na wasa ba tun da ya yiwa Sadauki farin sani. Haka ta koma falon Hajja tana kuka wiwi, Hajiya Hadiza ranta ya ɓaci da wannan hukunci na Sadauki. Hajiya Fatima ke fadin ai gwara da hakan ta faru tunda ita ba za ta iya saita bakinta ba. Umma dai ba ta tanka ba. 


 A ɓangaren Haulatu kuwa, kuka wiwi haka ta dinga yi, har Safina ta shigo tana aikin rarrashi amma ko kallonta ba ta yi ba. Ita a ganinta ai wannan son kai ne da son zuciya. Ta ya ya ita aka yiwa laifin kuma zai ɗau hanu ya mare ta? Ita tun ganinsa da ta soma yi dama ta fahimci baƙin azzalumi ne da ba ya ƙaunarta. Da ace ya san yadda ta tsani namiji mai bugu da bai yi kuskuren ɗora yatsunsa a sama fuskarta ba. Hajja itama ta shigo ta hau rarrashi da sababin ita Sadauki bai kyauta mata ba. Yanda ta dinga nuna fushinta a kai har tana ikrarin za ta kira shi ta yi mishi tas tunda dai ko ubansa bai isa ya ja da ita ba. Sai abin ya ɗan yiwa Haulatu dadi a rai, ba ta kuma taɓa ji Hajja ta burgeta ba sai yanzun. Kiran da aka shigo yiwa Hajja kan cewa ta yi baƙi yasa ta fice daga dakin, lokacin hayaniya sosai ya kaure a falon ga dukkan alamu an ƙara yawa ne a gidan.


"Ki yi hakuri ki tashi muje ƙasa ki ci abinci."


Jin abin da Safina ta ce yasa Haulatu miƙewa zaune cikinta har yana ƙara amma damuwarta da ɓacin ran sun shafe wancan. 


"Don Allah Safina wai rashin kunya na yiwa Umma?"


Safina ta ɗan yi jim, ita kuwa Haulatu wai wace iri ce ne? Yanzu ba ta ga irin katse zancen Umma da ma ɗaga muryar da ta yi mata ba? Can ta dube ta dakyau cikin sanyin murya ta amsa.


"Gaskiya har ga Allah kin ɗaga wa Umma murya. Ta kuma nuna ƙarfin iko da isa a kanki ta hanyar dakatar da ke daga maganganun da kike yi sai ki ka nuna ba ta isa ba. Ba zan ɓoyemaki ba ni kaina yanayin da kika yiwa Umma magana bai min dadi ba Haulatu. Wannan kuskure ne babba. Ki yi hakuri da marin da Yaya Sa..."


"Ni ba maganarsa nace ki yimin ba. Na yarda na yiwa Umma laifi. Wallahi na ji babu dadi, ta ya ya zan ba ta hakuri? Ni na sani Umma yanzu ranta ya ɓaci da lamarina. Wallahi ni ban san ma sadda na ɗaga muryar ba."


Sai ta fashe da wani sabon kukan mai nuni da tsantsar nadamarta da dana sani. Shigowar Umman ya sa suka dube ta. Fuskarta a sake ta dubi Safina. 


"Safina, maza je ki wajen Baba Saude ki karɓo muku abinci, an kammala."


Ta amsa da toh kafin ta mike ta fita. Umma ta shigo dakin sosai, da sauri Haulatu ta mike tsaye ta ma kasa kallonta, ta rasa me za ta yi? Sai kawai gani ta yi Umman ta riƙo hannunta ta zaunar a gefen gadon. 


"Ba ki kyauta ba ko kadan Haulatu. Me kika son ki nunawa mutanen gidan nan? Ni uwar banza ce?"


Har a sannan murmushi mai ciwo Umma ke yi, Haulatu ta girgiza kai sai ta ƙara karfin kukanta. Fuskarnan ta yi ja, ga kuma shatin hannun Sadauki kwance a gefen kumatunta. 


"Wallahi ban san na yi ba. Ki yafemin don Allah Umma. Ba zan ƙara ba."


"Ya wuce. Amma ki ƙara hankali da rayuwa da kuma zaman duniyarnan Haulatu. Idan ba ki iya zama da mutane ba, za ki wahala a rayuwarki. Yanzu dai kusan a farko ke aka yiwa laifin, amma me? Sai ki ka nuna gajen hakuri har kika dauki matakin da ya haifar maki da dana sani. Da kin yi shiru da bakinki, kina tsammanin Fahima za ta sha ne a hannun mutanen da ke falon koda kuwa ni ban yi magana ba? Don Allah ina roƙonki ki koyi hakuri da kuma danne zuciyarki. Kar ki sake kuma ki ce za ki tsani ɗan uwanki don ya mareki, gyara ya yi maki. So yake ya ga kin fahimci kuskurenki. Kullum ina ƙara fahimtar da ke yanayin rayuwa, idan ba ki koyawa zuciyarki hakuri yanzu ba, sai yaushe? Akwai namijin da zai dauki wannan sakarcin naki?"


Ta turo baki kaɗan jin Umma ta sako batun wani namijin. 


"Ki yi hakuri." Ta ƙara maimaitawa karo na biyu. Sai a sannan Umma ta yi murmushin da ya fito tun daga zuciyarta.


"Ya wuce. Allah ya shiryamin ke, ya yi maki albarka."


Cike da jin dadi ta yi dariya tana mai amsawa da amin gami da rungumar mahaifiyarta. Dawowar Safina dakin dauke da faranti na abinci har da flask na ruwan shayi ya sa Umma mikewa ta bar dakin zuwa falo. Nan suka shantake suka shiga hira ran Haulatu ya yi fari ƙal tamkar babu wani abu da ya faru don a yanda ta zuciya ta rantse ma ko wayar ya maido ba za ta karɓa ba tunda ta ji Safina ta ce wai ya dauke wayar bayan ta bar falon.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 22

Su na kammalawa, Safina ta dube ta.


"Zo mu tafi kiga Anti Raudha, suna can gidan Abba."


Zuwa sannan ta gane waye Abban tunda yana shigowa su gaisa da Hajja, kuma ta gan shi mutum mai sakin fuska, koda ba ta falon to fa sai ya tambaye ta. Alhaji Ridwan kenan mahaifin Sadauki. Wannan ne ba ta sani ba. Ta yamutse fuska.


"Da wannan yatsun da suka kwantamin a fuska na wancan mugun kike tunanin zan fita a samu abin magana?"


Safina ta dubi fuskar sosai.


"Lah, wallahi ko kadan ba a ganewa gaba daya ya goge sai ɗan ja da wurin ya yi kuma shi ma nasan zuwa anjima za'a nema a rasa. Don Allah taho mu je ki gan ta."


Jin haka Haulatun ita ma ta miƙe, sai da ta ƙarasa gaban madubi ta ga dagasken ba lallai a gane ba kafin ta yarda da fitarsu. 


Falon Hajja a cike ba ta ko kalli kowa ba ta fice ta bar Safina na aikin gaishe-gaishe tunda dai ita ba sanin su ta yi ba duka baƙin fuska ne. 


Gidan Alhaji Ridwan a cikin kewayan babban gidan yake, shi ne kalarsa ta bambanta da na su Hajja da Alhaji. Ba ta taɓa shiga ba, ko sadda Hajja ta kai Umma gidajen yaranta da na yan uwanta koda wasa ba ta yi yunƙurin bin su ba don a lokacin sosai take jin haushin Hajjar. 


 Tun daga farfajiyar gidan da suka shiga ƙaton ƙyauren, ta ga ya sha bamban da duk gidajen da ta taɓa sa ƙafarta ciki tun zuwanta Katsina. Baki ta buɗe tana kallon yanda aka ƙawata shi har da wani gefe na ƙaramin garden da aka zagaye da wani gajeran katanga an yi shuka mai kyau da burgewa a cikinsa ga wani kujera mai lilo, a iyakar hangen Haulatu dai ta tabbata wajen akwai abubuwan burgewa a ciki. Idan yamma ta yi zai fi dadin zama. Ba ta ƙara tsinkewa da tsaruwar gidan Alhaji Ridwan ba sai da suka shiga wani babban falo da ya ji kayan ƙawa iri-iri masu tsada koda kuwa ba a fadi, inda anan ne suka ji tashin waƙa da kuma muryoyin yanmata wadanda suka iya waƙar su na bi muryar kowa a sama, ga rawa su na tiƙa abin su. Ga dai Ac ta ko'ina tana aiki amma ina, tsabar rawa da suke tiƙa da kuma yawan da aka yi ya sa falon ke tashin zafi. 

 

   "Ikon Allah, yanzu wannan duk murnar na kawo lefe ne?" Fadin Haulatu a fili, amma kasancewar wurin akwai ƙara da hayaniya bai bari ko Safina dake gefenta ta ji ba. Wuri ta nema ta zauna ta dora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallonsu. Daga yanayin yanda ake yiwa wata ƴar baƙa gajeriya mai ɗan jiki guɗa a kai bayan wata ta shigo ta sanar da batun zuwan masu kawo lefe ya sa Haulatu fahimtar ita ce Amaryar. A lokacin ne kuma suka kashe kiɗan aka hau rububin zuwa ganin lefe jin wata na fadin ai lefen haɗe yake da kyautar wata haɗaɗɗiyar mota. 


   "Wash! Wallahi ni dai na gaji, ku je ku dawo ku bani labari."


Haulatu ta dubi mai maganar, kusa da ita ta zauna gumi duk ya gama jiƙa mata jiki, sai numfashi ta ke saukewa yayinda hannunta ɗaya ta dafe kanta da shi da ya ɗan soma sarawa. Za ta girmi Haulatun da shekara ɗaya ko biyu ma. Siririya ce baƙa. Tana sanye da wata doguwar riga ƴan kanti da ta kama jikinta. 


"Haba ta Yaya Sadauki, don Allah ta so muje."

 

Haulatu ta ɗaga kai ta kalli mai wannan kirarin, ta ji ɗazun an kira ta da suna Jannat. Sai ta ji wasu hudu a gefe sun kwashe da dariya gami da cafkewa.


"Ta Yaya Sadauki manya, aikin ɓurr, da ace ma ya san da zamanta shi ne. Amma babu abin da ya haɗa fura da kashi. Manyanta ma basu ishe shi kallo"


Nan da nan sai ta gefen Haulatun ta zabura ta mike tana mai nuna wacce ta yi zancen da yatsa, cike da jin masifa har idanunta na ƙanƙancewa take fadin


 "Kinsan Allah, ina gargadinki da babbar murya ki fita a harkata Fa'iza, idan ba haka ba zan maki rashin mutunci. Ai gwara ni akan ke da kike son Yaya Khaleefa kuma kina ji kina gani ya yi aurensa da masoyiyarsa ya ƙyale ki kika yi bandaro."


Jin haka sai abin ya kusan zame musu faɗa, Haulatu wani takaicinsu ya kama ta, ta mike ta fice a falon tana jan tsaki. Ta yarda akwai mahaukata a wannan zuri'ar tasu. Ita kaf a matasan gidan nan ba ta ga wani wanda har a rai ta ji ya burge ta da sunan soyayya ba. Daga wancan mugyambon da ya mare ta, sai wancan likitan mai shegen taƙama kamar wani basarake, sai kuwa wancan ɗan Malamar mai shegen kallo kamar idanunsa za su faɗo. Mu'az kuwa ta ɗan ga kirkinsa tunda ya ci darajar ƙawarta kuma ƴar uwa Safina, uwa uba ya nuna damuwarsa a kanta har ya siya musu waya ita da Ummanta. 


  Kai tsaye sashin Hajja ta yi niyyar komawa sai kuma ta tuna Umma ta ce ta dinga zuwa tana gaida su Baba Dakta da Alhaji, hakan yasa ta fara da ɓangaren Baba Alhaji. Da sallama a bakinta ta shiga, babu kowa sai ƴan aiki don su Nene suna can wurin lefe sashen Hajja. Bayan sun gaisa ta tambayi ko Alhaji yana ciki. Dije ta ba ta tabbacin yana can barandarsa. Ganin ba ta fahimci wajen ba ne sai Dije ta taka mata har can cikin falonsa gami da yi mata nuni da wata ƙofa dake a bude ta hango kafafunsa yana daga kishingiɗe ne saman darduma. Da sallamarta ta ƙarasa bayan ya amsa ta shiga. Ganinta ya sanya shi ajiye littafin da yake dubawa, ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa fuska a sake yana dubanta ta cikin gilashin dake idanunsa 


"Kamar ɗiyar Na'imatu?"


"Ni ce." Ta amsa tana murmushi. Shi kuwa ƴar dariya ya yi. 


"Wato ke sai na dinga biya zan dinga ganinki ko? Yaushe rabon ki zo mu gaisa?"


Sai ta ɗan ji kunya ya kama ta. Ai za ta iya cewa rabonta da ɓangarensa tun sadda suka yi dirama da Sadauki, gwara ma Baba Dakta ya gan ta a jiya sadda ta shiga kai wa Maama saƙon dambun da Ummanta ta dafa. 


"A yi hakuri Baba Alhaji."


Ya yi murmushi. 


"Ba kya laifi ai ke Amarya ce."


Ta zaro idanu.


"Eh? Ban fahimta ba, Amaryar wa? Aure za'a yi min?"


Dariya ya ɗan yi. 


"Aa, wa zai maki auren dole? Ai ke ce ta ƙarfen tawa."


Ta sauke ajiyar zuciya na samun sukuni.


"Au, ni fa na yi zaton ko aure ku ka yi shawarar yimin. Hum um, ai wallahi da ba zan zauna ba. Ni na tsani aure."


Alhaji ya kalle ta dakyau. Bai ga alamar wasa koda a fuskarta ba, hakan ya ba shi tabbacin iyakar gaskiyarta ta faɗi. 


"Kul, kar ki ƙara cewa kin tsani aure. Aure ai sunnah ce ta Ma'aikin Allah (s.a.w). Kuskure ne babba ki ƙara furta hakan. Mu a gidannan ba ma yiwa yara auren da ba su so, idan har ya kasance ɗaya ke so, ɗaya ba ya so, akan haƙura da yin sa, domin mun fi kyautata zaton barin shi ya fi alheri. Idan kuwa ɗaya ba ya so, amma ya kwantar da kai da niyyar yin ladabi ga hukuncinmu, mukan girmama ra'ayinsa mu kuma ji dadin ya yi biyayya gare mu. Ƙarshe kuma cikin iko na Allah sai ki ga auren ya yi albarka, an samu ƙauna da fahimtar juna a ciki."


 Ta jinjina kai tana ɗan murmushi.


"Na gane Baba Alhaji. Ni amma ba zan yi auren ba ne a rayuwata. Ba zan jure namiji ya dake ni ba, na rantse ramawa zan yi. Ni ina da zafi ba irin Umma ba ce da ta yi sake mijinta ke tafkarta kamar ya samu jaka ba." 


Alhaji ya ɗan girgiza kai, ya fahimci illar da Ɗan Mutuwa ya haifar a tunani da kallon da ɗiyarsa ke yi wa aure. Yana daga babbar illar dukan uwa gaban yaranta, wataran ma idan hakan ya ci gaba da faruwa, tsaf za su kai hannu su ramawa uwarsu. Kafin Alhaji ya ƙara magana, ta ɗauko masa hirar irin dukan da Ummanta ke ci a wurin Ɗan Mutuwa. Bai katse ta ba, yana sauraro ne da ka lura da yanayin fitar lafuzzanta wadanda ke cike da kura-kurai da ma rashin nuna ladabi ga wanda ke gaba da kai. Ganin muryarta ta raunana za ta fara kuka ya sa shi saurin dakatar da ita.


"Ya isa hakanan, na fahimce ki, na kuma fahimci dalilinki na rashin son aure duk da kin ce Ummanki tana son ki yi shi. Ke yanzu karatun kika fi sha'awa kenan?"


Ta yi saurin jinjina kai tana kauda hawayen da suke yunƙurin zubo mata. 


"Sadauki? Yaushe ka shigo?"


Jin sunan da Alhaji ya ambata ya sanya ta saurin juya kanta, yana tsaye jikin ƙofa, kusan zai ce tun soma hirarsu ya shigo sai dai ganin da ya yi hankalinsu gaba daya ba ya kansa ya sa shi yin shiru har sai yanzun da Alhaji ya ankara da shi. Ita kuwa Haulatu nan da nan ta miƙe. 


"Zan je wurin Baba Dakta." Alhaji kamar zai tsaida ta sai kuma ya fasa gami da fadin.


"Ki je amma gobe ki zo kamar yanzu ina son mu yi magana."


"Gobe Umma ta ce wai  zan soma zuwa makarantar islamiyyar su Safina." Ta fadi tana ɗan yamutsa fuska da hade rai, don ita tun ganin Sadauki a wurin ta ke cike da jin haushinsa. 


"Masha Allahu. To kar ki damu, ki bari har ku taso. Ba ki gaida Yayanki ba."


Ta turo baki ba ta ko kalli Sadauki wanda tuni ya ƙaraso ciki ya zauna yana danna waya ba.


"Ai mun gaisa ɗazu."


Daga haka ta juya ta fice. Sashin Baba Daktan ma ba ta je ba kawai sai ta koma wurin ƴan ganin lefe, duka ana falon ƙasa, Safina ta jawo hannunta ta katse yunkurin hayewa sama da ta yi.


"Ina kika shige ne? Muna can muna raba faɗa na neme ki na rasa. Zo ki sha kallon abin arziki, har da mota fa aka kawo mata. Akwatuna har set biyu."


Yamutse fuska ta yi.


"Ni kaina ke ciwo, zan koma daki."


Daga haka ta fice ta bar Safina da bin ta da kallo kafin ta juya ta koma cikin ƴan uwanta. 


***

 Yana kwance saman kujera ya lumshe idanu, tun dawowarsu garin Abuja gaba daya hankalinsa ya kasa kwanciya. Komai yake yi sai ya dinga ganin fuskarta da kyawun diri da Allah ya yi mata na mishi gizo a idanu. Dagaske, Zaid bai taɓa ganin abin da ya fisgi hankalinsa lokaci guda kamar Haulatu ba. Sanadinta ya tattara ya dawo Abuja bai shirya hakan ba, hatta Jalilah ta yi mamakin dawowarsu da wuri tunda ya ce sati guda zasu yi kafin su juya sai dai lura da cewa kamar akwai abu da ke damunsa ya sa ta ja bakinta ta tsuke. Shi kuwa kafin su taho koda ya shiga Babban gida, sam bai kalli ɓangaren Hajja ba, alhalin yana da tabbacin a can ɗin ne zai gan ta. Abin kunya ne a gan shi ɓangaren Hajja a yanzu, kowa ya shaida cewa ba ya shiga ɓangarenta tun faruwar lamarinsa da Jikarta Zaituna. 


"Honey, wai lafiya kuwa?"


 Ya sauke ajiyar zuciya jin muryar Jalilah a gefensa tana mai shafar gefen fuskarsa. A hankali ya buɗe idanunsa, cike da kasala ya amsa.


"I'm ok. Kaina ke ɗan sarawa kawai."


Ta numfasa fuskarta na nuni da tsantsar kulawa da damuwa.


"Sorry, bari na kawomaka ruwa da magani ka sha. Watakila gajiya ce."


Gyaɗa kai kawai ya yi. Daga haka bai ce uffan ba har ta mike ta nufi ɗaki don ɗauko maganin. Ya maida duba ga ƙaton frame na hotonsu da ke fuskantarsa. Duk wanda zai kallo Jalilah ya kawo wani kushe a halittarta to fa sai dai mahassadi. Ko shi din ma zai jima bai samu abin kushewar ba. Koda dai shi ba don kyau ya aure ta ba face yabawa da kyawawan halayyarta. A sanin da ya yi mata a shekarun da suka kwashe tare a makaranta, ta samu kyakkyawar shaida na kamun kai da kuma kamala. Wannan ne babban dalilinsa na zaɓo ta matsayin mata ba tare da ya san cewa dama can ta jima tana sonsa ba sai dai irin matar nan ce mai miƙa lamura ga Allah da kuma yawan addu'ar neman zaɓin Allah. Sai ga shi tana zaune Allah ya kawo mata shi ya furta yana kaunarta da kuma aure. Ranar kuwa da ya je suka yi zancen har hawaye ta fitar don farin ciki. Tana girmama shi, tana ba wa Mahaifiyarsa girma, zai kuma ci gaba da darajata, zai yi kokarin ɓoye halin da yake ciki ko don ita. Ba ya burin ya ɓata ranta a ƴan watanni da aurensu. Abin da ke zuciyarsa kuwa, ya bar shi matsayin wani abu na daban da zai yi gaggawar yaƙi da shi, sam ba zai bari Hajja ta ci nasara a kansa ba. Da haka ya rufe babin zancen. 


***

Ta kalli kanta a madubi tana murmushi kafin ta maida dubanta ga Umma wacce ita ma ke kallonta tana murmushin.


"Umma, kayan sun min kyau ko?"


"Sun yi, hankalinki ya kwanta? Kafin ki tafi dai ki yi abin da na sanya ki."


Ta ɗan yi shiru tana nazari can ta tuna, ashe fa Umman ta ce ta kira Mu'az a waya ta mishi godiya. 


"Toh, ina wayar taki?" Umma ta miƙa mata sannan ta miƙe daga saman darduma ta naɗe ta fice zuwa falo. Lambar Mu'az ta lalubo, ba ta ci wuyar ganinsa ba don ko da safe sun yi magana da Umma yake tambayarta ko lafiya bai samun wayar Haulatun, Umman ke labarta mishi cewa ai laifi ta yiwa Yayanta Sadauki shi ne ya hukunta ta ta hanyar karɓe wayar. 


Sau uku ya yi ƙara kafin ya ɗaga da sallama, ta yi gyaran murya ta amsa. 


"Ina wuni." Ta furta tana ɗan hararar iska kai ka ce shi ne a gabanta. 


"Oh, ƴar ƙauyen Kano ce? Lafiya lau."


"Eh ita ce ɗan birni. Dama godiya na kira na yi maka. Allah ya saka da alheri. Na ga waya."


Ya yi murmushin da ta ji sautinsa a kunne.


"Kar ki damu, ai yiwa kai ne. Bai ba ki wayar ba?"


 Taɓe baki ta yi.


"Wai wancan? Eh na bar masa ya ƙara da na hannunsa ya riƙe."


Ya yi ƴar dariya.


"Na kula dai dole taku ta ƙi zuwa ɗaya da Bestina, wato ba kya shiru. Ga tsiwa ga rashin kunya. Anyway, kar ki damu, zai ba ki. Ni na san halinsa."


"Uhum. Ni zan tafi islamiyya."


"Ok, bye." Ya ba ta amsa, daga haka ta katse wayar, har ƴar ƙarar da wayar ke yi dadi yake mata a kunne. Kai abu mai tsada kyau gare shi, ta shiga latsawa har sai da Safina ta shigo kiranta kan ta fito zasu yi latti sannan ta mike suka tafi da ƴar jakarta da Maama ta siyamata mai dauke da litattafan karatu. 


 Tun biyu sai karfe shida na yamma suka dawo gidan, ba ta kula kowa cikin yanmatan gidan kamar yanda ba su shiga harkarta ba sai Safina. Kai tsaye sama ta haye bayan sun gaisa da Baba Saude da wata yar budurwar jikarta dake taya ta aiki. Ganin Dr Khaleefah zaune suna magana da Umma ya sa suna hada idanu ta kauda kai tana cin magani. 


'Ɗayan mugun.' Abin da ta furta a ƙasan ranta kenan, ta ƙarasa ta yiwa Umma sannu da zuwa, Hajja ba ta nan. Ta gaida Khaleefa kamar wacce aka yiwa dole, ya yi kamar bai ji ba ya ci gaba da maganarsa da Umma, ta kula wani sabo ke tsakaninsu don hirar wata marar lafiyarsa ta ji kamar yana yi da Umman. Ɗaki ta shige ba ta ƙara fitowa ba sai da ta ji ana kira Magriba, ta tabbata ya tafi. 


 Sai kusan bayan sallar isha'i ta tuna da kiran da Alhaji ke mata aikuwa ta mike.


"Ina za ki je?" 


Ta dubi Umma.


"Na manta wallahi, jiya Baba Alhaji ya ce na je na same shi bayan Magriba. Ga Isha'i har ya yi."


"Sai ki yi sauri to don yana bacci da wuri." Fadin Hajja da ke gefe saman darduma. Haulatu ta dube ta kawai ba tare da ta amsa ba ta juya ta kama hanya. Hajja dai ta kula jikarta ta soma saukowa daga dokin fushin da ta hau da ita. Bayan fitar ta ta dubi Umma fuska a sake ta ce 

  "Kin kula ɗiyarki an fara sauyamin?"


Murmushi Umma ta yi.


"Dama ai sakarci ne irin nata. Allah dai ya shirye ta."


"Aa fa, ba sakara ba ce. Kar ki kuskura ki ƙara jinginata da wannan kalmar."


Umma ba ta ce komai ba, dama ai ta lura Haulatu ba ta laifi wurin Hajja. 


  A can kuwa, Baba Alhaji ta iske shi saman darduma yana jin rediyo, ganin ta ya sanya shi rage sautin rediyon har yana zolayarta akan saɓa lokaci shi zai bar ba da kudin cefane. Suka yi dariya. Nasiha ce sosai ya yi mata dangane da rayuwa da kuma yi mata nuni da girma na iyaye. Ya nuna rashin kyautatawar abin da mahaifinta ya yi a zamantakewarsu sai dai ya ce ko wace irin cutarwa ya yi mata ita ta yi hakuri ta bar munana kalamai a kansa. Wannan karo na farko ne da Haulatu ta ji ba za ta iya ja da abin da babba ya fadi ba. Sai ta ji maganganun Baba Alhaji na tasiri a wajenta. Ya kuma kara da cewa ta dage ta maida hankali ga karatunta na addini, boko kuma ya mata alƙawarin in sha Allahu za ta yi har sai ta ce ya isa tunda shi ne burinta. Bayan ya kammala tana ta jin dadi da murnar, ƙaunar tsohon na ratsa zuciyarta. Tana shirin tafiya ya dakatar da ita ta tsaya. 


"Ga wannan inji ɗan uwanki."


Ta kalla, wayarta ce da Mu'az ya siya mata. Da mamaki ta ce.


"Au, ya aka yi ya bada?" 


Murmushi Alhaji ya yi. 


"Karɓi, nima ban san da batun waya ba. Dazu da ya zo zai tafi ya ce na ajiyemaki idan kin zo a ba ki."


Ta sa hannu ta karɓa ita har a sannan mamakin yanda aka yi ya bayar take, ai ta yi zaton ita da wayar sai a lahira tunda ance tun can baya ma kafin a ba ƴanmatan ƴancin riƙe waya suke riƙewa a ɓoye, muddin ya ji labari to fa kwacewa yake yi, kuma idan ya kwace ba su ko ganin wulkawarsu shikenan. Ballantana kuma ita da ya kama da laifi. Haka ta yiwa Alhaji sallama ta tafi. Koda ta koma ta iske Khaleefa zaune yana cin tuwo da miyar kuɓewa ɗanya a falon. Har da cire hularsa ya ajiye saman kujera. A gefe itama Hajja nata lomar take yi, sai Umma da alama ita kam ta kammala. Ganinta ya sa Khaleefa tamke fuska kai ka ce ba shi ke ƴar raha yanzu da Umma ba. 


'Aikin kenan. Fuska kamar alkubus.' Ta furta a ƙasan rai. A fili kuwa sai ta yi hanyar daki.


"Haule, kin ci abinci kuwa?"


Sunan Haule da Hajja ta fadi ya sa ba shiri Haulatu dubanta kamar ta yi kuka, rai a bace ta ce.


"Ni sunana Haulatu kar ki kara cemin wani Haule."


Dariya Umma ta yi, Khaleefa ko kamar bai san wainar da suke toyawa ba. 


"Oh to, ai ban san ma na fadi haka ba. Wata mai siyar da fura sunan ke tunamin a Malumfashi. Yi hakuri kin ji? Maza taho ki ci abinci."


"Sai anjima zan ci." Ta fadi a fusace sannan ta yi ɗaki da haushin Hajja ta kira ta da Haule gaban Khaleefa. 


Shi kuwa bayan ya kammala ya wanke hannu sannan ya miƙe. 


"Sai tafiya kenan? An dai ji kunya, mace har mace amma ba ta iya tuƙa tuwo ba?" Hajja ta fadi cike da zolaya. Khaleefa ya yamutse fuska.


"Ke Hajja kin fiye tada zaune tsaye, to ni ne ban nemi a tuƙa ba."


"Ba wani nan, kai dai ka je ka ɗauko matar da ba ta ko matsar da tsinke a gidanta. Kwanan nan zan samo maka mata a Malumfashi. Bari dai su zo bikin yaran nan."


Ɗan murmushi.


"Ba ni Khaleefan ba ko?"


"Gidanku, kai dai Khaleefa. Akwai wani Khaleefa da na sani ne bayan ka?"


"Sai da safenku. Umma, mu kwana lafiya."


Ya fadi yana kama hanyar barin falon lokaci guda yana gyara zaman hularsa. Umma ta amsa mishi tana dariyar diramarsu da Hajja. Har bayan ya tafi Hajja ba ta bar mita da jin takaicin yanda matan zamanin nan ba su maida hankali da gyara cikin mazajensu ta hanyar sarrafa girke-girke masu rai da lafiya. Ta dinga zayyanawa Umma matsalar gidan Khaleefan na cin girkin ƴan aiki da ma rashin tsaftar matar gidan. Komai sai dai yan aikin su yi.


"Ina ce dai Haule ta iya girki ko?"


Murmushi Umma ta yi, dom girki kam Haulatu ta iya wanda ta iya. Sai dai na zamanin da ta ga Baba Saude na sarrafawa. Jin ba wani sosai Haulatu ta iya girki ba ya sa Hajja ta ce ya kamata ta sa ta fara shiga kicin don ta koya. Umma ta amsa da toh. Don ta sani idan har Hajjar ce za ta saka, to fa babu abin da Haulatun za ta yi. Ita din ma da ya ya wasu lokutan take tursasa ta abin da ba ta so? 


 ***

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 23

A can Kaduna kuwa, Ɗan Mutuwa ke zaune a falon gidansa da Hajiya Adama ta mallaka masa halak malak dake unguwar Malali. Hatta da kujeru da labulaye babu abin da ba ta saka ba, farko ma da ya bude ya shiga ya ga irin kayan da aka zuba a gidan sai da ya rikice ya fidda waya ya kira ta dom tabbatarwa da kansa ko tana sane da kudaden da kashe na zuba kayan furnitures, a cewarsa idan ma mantuwa ta yi ba ta saka an kwashe ba kafin zuwansa, toh ta aiko a kwashe mata kar ta bi shi bashi. A lokacin dariya ta sakarmasa.


"Kar fa ka damu, wannan gida da duk kayayyakin da ke cikinsa ba komai ba ne a cikin dukiyata. Ko kaɗan bai girgiza ba. Kai dai ka yi nazari sosai ina jiranka, gida irin wanda na mallaka maka, muddin ka bi shawarata na rantse maka sai dai ka zuba haya ko ka bayar sadaka. Amma kai kam sai ka fi ƙarfin shigarsa."


Zaro idanu ya yi a sannan, bai kai ga cewa komai ba ta yanke kiran. 


Tun sadda suka yi waya ya nemi wuri ya sheme saman kujera yana ta saƙe-saƙen zuci. Kai kuɗi sun fa yi a rayuwa.


'Za ka zama abin da ba ka taɓa kawo wa ba. Hatta siyasar da ka jima kana kwaɗayi, koda ba ka shige ta ba, za fa a dama da kai tunda kana da silalla.'


Haka zuciyarsa ta dinga raya masa abubuwa da dama ya ji sosai son lamarin ya shige shi don haka jiki na rawa ya dau waya ya kira Hajiya Adama. Tana ɗagawa tun kafin ya kai ga cewa wani abu ta amshe.


"Ka amince kenan?"


Jinjina kai ya yi kamar tana gabansa.


"Kwarai na amince. Yanzu ya za'a yi?"


Yana jin sadda ta sauke ajiyar zuciya, murya cike da tsantsar farin ciki ta amsa.


"Ka zo Kano jibi, akwai taron da zamu yi, zan gabatar da kai a nan. Nima kuma na san hakan zai sa na ƙara samun matsayi fiye da wanda nake da shi yanzu a ƙungiyar. Ka yi kyan kai da ka zaɓi hanyar jin dadin duniya cikin sauƙi. Ƙwarai na taya ka murna Alhaji Ibrahim Ɗan Mutuwa."


Wannan sunan da ta faɗi a ƙarshe ya ƙara jin zumuɗi da wani ƙarfin gwuiwa kan hukuncin da ya yanke na ba da kai bori ya hau. Dariya suka saki cike da jin dadin nasarar da kowannensu zai yi nan ba da jimawa ba. Har suka yi sallama wannan suna da Hajiya Adama ta yi kiransa da shi ya na ta yawo a kwanyarsa, ya furta a baki ya kuma nanata a zuciya yana mai cike da jin annashuwa. Sai ya ji ma jibi ya yi mishi nisa, ya sani kafin nan da jibin tunani da mafarkan cikar burinsa sun ramar da shi. 


***

 Katsina...


Umma ta dubi Haulatu bayan ta saurari duka labarin hirarta da Hindatu daga bakinta. 


"Kin kyauta da ki ka ɓoyemusu ainahin inda muke."


Ƴar dariya Haulatu ta yi.


"Ai Umma nifa duk hanyar da mijinki zai samu labarinmu ba kaunarsa nake ba. Ballantana kuma Hindatu da Mominta idon cin naira, ni na san muddin Mominta ta zo ta ga gidan nan to fa sai ta ƙulla wani makircin. Sanin hali ai ya fi sanin kama."


Murmushi Umman ta yi ba tare da ta ce komai ba. A ƙasan zuciyarta dai tana ƙara godewa Allah da ya fara shiryamata ɗiyarta, duk wasu shirme da caɓa magana da ta ke yi sun ɗan ragu duk da kuwa wasu lokutan idan ta yi wata kwaɓar sai ka fahimci da sauranta. 


"Umma." Kiran sunanta da Haulatun ta yi ya katse zancen zucin da take yi. 


"Ni kam me zai hana kema ki koma makaranta, zai ɗebe maki kewar zaman nan. Baba Alhaji ya ce ba a girma da neman ilimin addini."


Wannan magana ta Haulatu ya ƙara saka Umma jinjina girman nisan da ta soma yi wurin koyon ɗabi'un rayuwa da ma ilimin addini. Ita kam tana kara jin kaunar Baba Alhaji a ranta, mutum mai hangen nesa da hakuri da halin yara, zai yi wasa da su kuma su yi raha. A yaransa kaf  Baban Kowa  shi ne ya dauki dukkan waɗannan ɗabi'u nasa. Shi ma akwai son jama'a ga ilimin addini daidai gwargwado.


"Umma kin yi shiru." Cewar Haulatu cike da magiya.


"Farin ciki nake ji a zuciyata ganin ɗiyata ta soma hankali. Yau dai ke da kanki da nake shan fama a baya akan ki je makaranta, ke ce ki ke kokarin nusar da ni na je? Allah abin godiya."

 

Murmushi mai bayyana haƙora Haulatun ta yi tana mai ɗora kai a kafaɗar Umma na dama.


"Umma ba burinki kenan ba? Kar ki samu damuwa, zan dinga iyakar kokarina wajen ganin na maida hankali. Baba Alhaji ma ya yi alkawarin muddin jarrabawarmu ta fito zai sa a nema min admission a Al-Qalam na cigaba da karatuna. Ke dai ki taya ni addu'a kin ji?"


Ita ma Umma murmushin ta yi tana mai kauda kwallar da ta cika idanunta ba tare da ta yarda sun zubo ba. Idan wasu lokutan ta dubi wannan sauyi na rayuwar da suka samu, sai ta ƙara fahimtar a rayuwa ba a fidda rai da rahmar Ubangiji. Komai kuma yana da lokaci idan bawa ya yi haƙuri to fa babu wani abu da ba zai zama tarihi ba. Babban burinta na gaba a duniya bai wuce ta ga auren Haulatu ba. 


***

 Shirye-shiryen azumi ya kankama, ana gobe za'a ɗauki azumi, Haulatu na zaune sashin Baba Dakta suna hira da Maama da Safina sai Radiya da wasu yan mata su biyu na gidan wadanda ba wani sabo ta yi da su sosai ba sai dai a wannan ranar sun dan sake koda sun tsoma baki a hira takan amsa idan an sanya ta ciki. Batun ankon ƙanne da yayyu mata suke yi da aka fitar na bikin su Raudha, ɗayar mai suna Saddiƙa ta na aikin kushewa a cewarta sam kalar atamfar bai mata ba. Kowa dai na faɗin ra'ayinsa a haka suka ji sallamar sa ya shigo falon. Gaba daya suka waiga suna masu amsawa. Haulatu suka haɗa idanu ta yi saurin kauda kai. Ita kam ta shiga uku, me kuma ya kawo wannan mai nacin kallon garin a yanzu? Tana ji ya karaso ana gaishe shi amma kallonsa ma ba ta yi ba. Kusan shi ne ya kula da ba ta gaida shi ba don duka baki suka haɗa wurin gaishe shi, a zaton Maama, har da ita. Maama ta kalle shi fuska a sake daidai sadda yan matan ke mikewa su duka a kokarinsu na fita a falon.


"Mutanen Abuja, dama kana tafe ba sanarwa? In ce dai lafiya?"


Zaid ya yi murmushi, ya dakatar da yan matan.


"Kai ina za ku je? Ku yi zamanku."


Suka ɗan dubi juna jin abin wani banbarakwai, sam ba su saba da zama a wuri idan yana nan ba, kusan kamar wasu dodonni haka suke ganinsa shi da Khaleefa da Sadauki, gwara Mu'az yakan sake idan ya ga dama. Idan kuwa sun kula ranar babu walwala tattare da shi, to fa sukan kama kansu su ja baya daga shiga sabgarsa. 


Haulatu kamar ba ta ji ba ta yi gaba yayinda su kuma suka dawo wajen zaman su. 


"Ke, ba ki ji me aka ce ba?"


Ya yi maganar cikin dakiya don ba ya son fallasa abin da ke ransa. 


"Haulatu ina za ki je? Zauna mana ku cigaba da hirar ku." Fadin Maama.


"Maama zan je ne lokacin shan maganin Umma ya kusa, ni ke tunasar da ita." 


"Toh, je ki idan kin ba ta kya dawo."


Daga haka ta juya ba tare da ta ƙara kallon Zaid ba wanda ta ji a jikinta ita ya ke kallo. Gaba daya sai ya ji ransa ya ɓaci, ya bi ta da idanu har ta fice a falon. Shi kam ba abin ya bi bayanta ba saboda Hajja, bai ga me zai sa ya shiga ɓangarenta ba. 


"Are you ok?" Ya ji tambayar Maama a tsakar kai, lumshe idanunsa ya yi kafin ya dube ta yana mai ƙaƙalo murmushin da bai kai zuci ba, tsaf ta karanci akwai wata damuwar binne a zuciyarsa, sai dai kuma me nene? Ba ta da masaniya, har Safina ta kawo ruwa da lemo da kofi a tray ta ajiye a gabansa bai ce uffan ba, ganin haka sai Maama ta dube yaran ta ce su ba su wuri. Dama su hakan ya fi musu dadi don ba wani sabo suka yi da shi ba. Da sauri suka mike suka yi ɗaki.


"Meke faruwa? Ko wani abu ya faru tsakaninka da Jalilah?"


'No Zaid, you have to control your feelings, zai zama abin kunya wani ya ji kana son jikar Hajja.' Wani ɓangare na zuciyarsa ya kwaɓe shi. Nan da nan kuwa ya saita kansa gami da wayancewa da bude gorar ruwa yana murmushi.


"Ko ɗaya Maama, kawai dai na gaji kaina ke ɗan ciwo. Haka yau na tashi da shi."


Maama ta bishi da toh gami da tambayarsa ko ya sha magani don ita kam ba ta wani gamsu da abin da ya ce ba. Ai ba ta jin ko iyayensu sun yi musu karatun da ita ta yi musu. 


"Yau ka shigo garin amma ko? Don jiya da dare ma mun yi waya da Malama ban ji ta ce kana hanya ba."


"Eh yau na shigo, anjima zan bi jirgi na koma, akwai wasu bayin Allah da nakan sallama a wani ƙauye kusa da Malumfashi duk sadda azumi ya kusa, nakan yi musu alheri haka, wannan karon na mance da batunsu shi ne silar zuwa na ba shiri. Amma har na je na dawo."


Ya fadi hakan ne don Maama ta yarda babu wani abu da ya faru wanda ya yi silar zuwansa ba sanarwa, ya kuma ci sa'ar ta yarda da wannan don daga yanayin fuskarta da furucinta na cewar yanzu ta ji batu yasa ya gane. Shi kuwa dai ya sani ƙarya ce kawai don tun a na saura sati guda ma ya yi waya da wani yaronsa dake ƙauyen, ya aikamasa komai ta asusun banki, sun kuma tabbatar masa matashin ya kai musu kayan masarufi na azumi har suka dinga godiya sai da ya katse kiran. Zuwa ya yi musamman don ganin Haulatu kuma ya gan ta din amma ba irin ganin da yake so ba. Ya na so ya faɗi abin da ke ransa sai dai ya gwammace ya yi shiru gudun zubewar girmansa. Ba ya son raini sam. 


Sun ɗan taɓa hira da Maama kaɗan kafin ya yi mata sallama ya tafi don samun zuwa ya yi shirin komawa a nutse. Ya fito ya kai duba ga sashin Hajja, ya ji zuciyarsa na neman raunana, wai wannan wace irin jarrabawa ce haka yake fuskanta? Yarinya kamar wacce ta yi masa wani aikin, daga gani sau ɗaya shikenan ya bi ya susuce? To ko dai ya samu Alhaji faɗamasa komai? 


"No, ba zai yiwu ba." Ya ba kansa amsar a fili. Haka ya bar gidan da saƙe-saƙen zuci. 


***

 Kano...


Ranar da duniya aka wayi gari da azumin Ramadhan, a wannan ranar ce Ɗan Mutuwa ya shiga Kano ba tare da ya ɗau azumin ba kamar yanda Hajiya Adama ta yi masa kashedi. Koda ace ma ba ta yi ba, ta sani bai damu da ibada ba amma gudun ma kar a yi din ya sa ta yi wa abin tufka. Daidai lokacin kuwa da bayin Allah suke haramar zuwa masallaci don yin sallar isha'i bayan an kai azumi na ɗaya, a wannan lokacin suka shiga shirin tafiya can wani ƙebantaccen wuri a dajin Allah don gabatar da uzurorinsu na duniya. Wuri ne mai nisa da zai kwashe su awanni uku zuwa hudu, hakan ce ta sa Ɗan Mutuwa ke tuƙin sai Hajiya Adama a gefensa sai kuwa wata aminiyarta ƴar ƙungiya, Zulaihatu. Suna tafe su na ƙara kwaɗaitawa Ɗan Mutuwa irin alfarmar da zai samu da kwarjinin da zai dinga yi wa mutane nan da wasu lokuta. Shi kuwa ban da washe baki babu abin da yake yi. Hajiya Adama ke ta nuna masa hanya har suka soma keta daji, sai da suka kai ga wani gida tafkeke mai ƙaton ƙyaure sannan tace ya yi hon, motarta da aka gani bai sa an bude ba sai da ta sauke gilashi wani jibgegen ƙatti su biyu masu gadin ƙyauren suka zuro kai, ganin baƙon fuska yasa su dubanta. 


"Kar ku damu, mun samu ƙaruwa ne."


Suka ƙyaƙyace da dariya idan ka cire sannan suka karasa aka wangale  ƙyauren, suna shigewa da motar aka maida aka rufe ta gam har da manyan padlocks. 

 

  "Ka cire takalmanka ka bar su a mota." Faɗin Hajiya Adama cike da nutsuwa, zuwa sannan gaba daya hatta a fuska ta sauya, wani irin ladabi ta soma kamar tana gaban Uban Dodon. Ɗan Mutuwa ya amsa da toh. Har zai fita ta ce.


"Ba a ɗaga murya, ba kuma a shiga da wayoyi, ba ka isa ka ɗaga kai ka kalli sararin samaniya ba. Ladabi, ladabi, ladabi."


Tana kai wa nan ta ajiye mayafinta, dankwali, da jaka da wayoyi, ta cire takalminta ta fito a sannu sannu. Yanda ta yi, haka ƙawarta Haj Zulaihatu ta yi. Ɗan Mutuwa ya cire takalmi shi ma ya fito, ya ga ba ma su kaɗai ne a farfajiyar wurin ba, manyan mutane da jallabiyoyi wasu kuwa da manyan riguna sai masu sanye da coat haka suke tafe suna nufar cikin gidan. Madadin ya ga falo, sai ganin wani babban fili ya yi a tsakar wajen da wani ƙaton wuri zagaye kamar rijiya an jera kyandir masu ci sai fararen ƙyallaye da kuma ja da baƙi an yiwa kyandiran ado. 


 Hajiya Adama suka tsaya can wani ɓangare mai ɗan tudu, zai bi bayansu aka dakatar da shi. Da wata murya marar dadi aka ce.


"Kai! Koma can baya! Ba ka da darajar zuwa wurin can!"


Ba musu ya ja baya ya koma can gefe, sai ga jikinsa yana rawa, bai san yana da tsoro har haka ba a duniya. 


Wani ihu suka fara yi suna kiran sunan Uban Dodo, can hayaƙinya turnuƙe wajen sai kuma a hankali wani bango daga  kusurwa ya soma buɗewa, wani mutum ne ya fito jikinsa duk gashi babu kaya, zirr yake. Sai wasu mata su ma tsirara su na take mishi baya har gaban wannan wuri mai kyandira. Gani ya yi ana zubewa ana kai goshi ƙasa ana kwasar gaisuwa, ba musu ya yi irin yadda suka yi. Sai Ɗan Mutuwa ya ga wasu ƙatti tsirara sun shigo riƙe da wata ƙatuwar ƙwarya sun ajiye gaban Uban Dodo, can kuma wasu yan mata suka soma zuwa su na rarrabawa kowa wani jan ƙyalle ana ɗorawa a saman goshi. Ana zuwa kansa Uban Dodo ya ce a dakata. Da kakkausar murya ya ce.


"Adama! Fito nan da baƙon ki!"


Jiki na rawa ta bi umarni ta fito tana tafiya a saman gwuiwarta har ta iso gabansa kanta a duƙe, shi ma Ɗan Mutuwa sai ya yi irin na ta da ya ga ta yi. 


 Yana zuwa aka ba shi wani abu a ƙwarya aka ce ya sha. Ɗan Mutuwa ya zaro idanu.


"Kai! Jini?!" Ya faɗi a gigice har bai san sadda ya saki ƙwaryar ba amma bai kai ga zuwa ƙasa ba Adama ta riƙe da sauri. 


Tsawa Uban Dodo ya daka masa.


"Kai!! Anan ba a yi mana musu! Buƙatar duniya ce ta kawo ka! Dole ka bi dukkam umarninmu! Idan kuwa ka ƙi! To haka yana nufin ka zaɓi mutuwarka akan rayuwarka!!"


Jin haka Ɗan Mutuwa ya ji hanjin cikinsa ya kaɗa. 


"Ka bi umarninsa kar ka sake ka ƙara musu. Idan ka ƙara yi kashe ka za'a yi. Koda ka fasa tunda ka shigo nan ka sani cewa mutuwa ce za ka yi ta don haka ka yi duk abin da aka sanya ka."


Hannu na rawa haka Ɗan Mutuwa ya kurɓi wannan jan abun, zai yi yunƙurin amai ya ji an watsa masa bulala a gadon baya a dole ya haɗiye abin da ya yi niyyar yi ya fasa. Uban Dodo ya matso ya shafa masa wani jan abu a goshi sannan ya ɗaura masa jan ƙyallen da kansa. A nan wurin aka fiddo wata akuya aka ce Ɗan Mutuwa ya kusance ta. Ji ya yi kamar an ɗaure masa baki, duk abin da aka ce ya yi, shi kawai ya ke aikatawa da rawar jiki. Sai da ya yi ta yi har ya gama kafin kuma Uban Dodo ya ba da umarnin a yanka akuyar. Jinin akuyar aka ba Uban Dodo ya shanye shi tas. Nan fa aka hau yin wani ihu mai nuni da taya Ɗan Mutuwa murnar shigowa ƙungiya. 


"Za ka yi kudi Ibrahim Ɗan Mutuwa! Za ka samu arziki don kana da sa'a a rayuwa! Za ka yi aure! Sai dai ka sani! Abin da ka fara haifa da matarka zai kasance mallakinmu! Ya kasance ƙarƙashin ikon mu!"


Kan Ɗan Mutuwa ya ƙulle, jiki na rawa ya ce.


"Ai ni ba ni da wacce zan aura yanzu."

 

Wani kalar dariya Uban Dodo ya yi kafin ya murtuke fuska. "Kana da mata kana da ɗiya! Abin da yasa bamu ce ka kawo ɗiyarka ba! Saboda namiji muka fi buƙata a farko da zamu salwantar, ko makusanci ko dan uwa ko babban amini! Kai kuwa ba ka mallaki ko daya ba! Mun hango cewa nan gaba kadan za ka yi wani auren! Za ta haifamaka namij! Daga ranar da ya zo duniya za ka dauko mana shi ka kawo ko wanka kar ka kusa ka bari a yi mishi! Wannan shi ne kashedin! Abu na gaba kuma! Ka je ka tono sabon kabari ka ciro mana harshen wannan gawa! Zamu yi maka babban aikin da za ka samu duniya a tafin hannu!"


Ɗan Mutuwa ya yi turus, tabbas sau daya ya taɓa yiwa Adama aikin zuwa saka layu a bakin gawa, amma ciro harshe? To idan kuma haƙansa bai cimma ruwa ba a ka kama shi?! Sai kuma dai ya ji zuciyarsa ta bushe! Ya ji babu abin da za'a ce ya yi ya kasa! Ya shiryawa komai muddin zai yi wannan kuɗin. Nan take ya cire wasi wasi ya amince da buƙatar Uban Dodo. Daga nan aka yi abin da ya tara na jin matsalar kowa tare da ba su mafita, sai ma Dan Mutuwa ya ji na sa ma da sauki don ciki har da wanda aka ce ya kawo kan matarsa. Wata kuwa cewa aka yi sai ta sadu da Surukinta mijin ɗiyarta sannan ta kawo musu maniyyin za ta cimma wani burinta na duniya. 


Haka aka watse daga taro, sai dab da Asubahi suka shigo cikin gari, Hajiya Adama na jinjina yanda aka ƙara mata matsayi ta ƙara zama a sahun mutanen da ake ji da su a wurin saboda ta kawo sabon ɗan bauta. (Wa'iyazubillah).


***

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 24

Kiran sallar magriba ne ya miƙar da Haulatu daga kujera da sauri ta yi saman ƙatuwar dardumar da Umma suka shimfida aka jera kayayyakin shan ruwa a samansa. Kai tsaye ruwa da soma sha duk da dabinon da Umma ke miƙa mata, ita yau kam ƙishin ruwan ta ke ji. Daga haka kuma ta miƙe ta shige bandaki. Alwala ta ɗauro, sai da duka suka idar da sallah kafin Umma ta shiga zubawa Hajja kunu a kofi. Haulatu kuwa filas ɗin wainarta ta ɗauka da haɗaɗɗen yajin da aka daka mata ta yi gefe bayan ta tsiyaya kunu. Ta sani dama can Umma ba ta damu da wainar fulawa ba, Hajja kuwa ko tayi ba'a yi mata ba don haushin Haulen da take kiranta take yi, dama kuma ita ma ba cimarta ba ne. Sosai ta so hayewa sama ta sha ruwanta a tsanake kafin wannan Khaleefan ya shigo sai dai kuma tana son kallon diramar da zasu yi da Mu'az. Ta soma ci kenan sai ga Khaleefa ya yi sallama, can babu jimawa da zamansa shi ma Mu'az ya shigo. Haulatu dai daga kallon da ta yiwa Khaleefa da kuma gaisuwa sai ta kauda kai, Mu'az ya ji gaba daya fara'ar da ya shigo da ita ta ragu. Kamar ya juya sai kuma ya dake ya ƙaraso ciki, madadin ma zama kusa da Khaleefan sai ya koma gefen Hajja inda Haulatu ke zaune daga can gefen kujera. 


"Taso ki zuba musu Haule, kunun za ku sha ko shayi? Ga ƙosai mai zafi, ga farfesun kifi ga kuma dankali da ƙwai." Hajja ke koro wannan bayanin, ta miƙe kasancewar tana cike da farin cikin haɗuwar Khaleefa da Mu'az sai ba ta ko ji zafin Haulen da Hajja ta kira ta ba. Khaleefa ya ce bai son dankalin, ta zuba masa farfesu a ɗan ƙaramin bowl sai kuwa kunu da ƙosai. Sai kayan marmari a ɗan farantin tangaran ƙarami. Koda ta zo kan Mu'az, dubansa ta yi da zummar tambayar me za ta zuba masa, aikuwa ba ta san sadda dariyar da ta ke maƙalewa ba ya fito, ta shiga yi abin ta.


"Ke, mene haka?" Muryar Umma ta katse ta. Shi kuwa Mu'az sanin da ya yi ta san cewa ya sha faɗamata hakanan ba ya son abu ya haɗa shi da Khaleefa saboda girman kai da jin shi ya isa, ya gane sarai dariyar me ta ke yi. Ai kuwa ya shaƙa. 


"Za ki zubamin ko na tashi na bar wurin?"


"Aa, me ya yi zafi? Yi hakuri ɗan birni. Kai na san ba ka shan kunu ko? Bari a zubamaka shayi sai farfesu da dankalin. Ƙosai da kunu ai sai ƙauyawa irin mu."


Khaleefa ya ɗan ɗago kai ya kalle ta, wai dama tana magana har haka? Koda dai ba zai ce magana ba, tunda a ganin farko ma da ya yi mata, tsiwa take yi. Amma yaushe suka yi sabo da Mu'az da har ta ke mishi irin wannan zolayar? Sai kawai ya maida kai ga kallon tashar Saudia da ake hasko ɗakin Allah, a gefe kuma suna ɗan taɓa hira da Umma. Shi sam haɗuwarsa da Mu'az din a wuri bai fiye damunsa ba, kamar yanda bai nuna akwai wani rashin jituwa tsakaninsu sakamakon bambancin halayya. Ya sani dai shi ɗan baruwansa ne, idan aka sanya shi a zance, to fa zai shiga, idan kuwa babu shi ciki, ba ruwansa da mutum. 


Har ya kammala bai bar jin Haulatu na hira da Mu'az ba, shi ma Mu'az din ganinta a wurin ya sanya shi watsar da batun Khaleefa, har ma zamansu wuri guda ya dame shi. Umma dai tana lura da yanda ba su kula juna, ba yau ta soma gani ba, amma a baya ba ta kawo komai ba sai da Haulatu a hira ta taɓa labarta mata dagaske wai jininsu ne bai hadu ba kamar yanda Mu'az din ya fadi mata. Suna yawan samun matsala da juna, yanzu za su hadu, amma kuma rabuwar zai iya zuwa da fushi ko jin zafin maganar ɗayansu. Sam abin bai yiwa Umma dadi ba, ta kuma ci ɗamarar gyara alaƙarsu da taimakon Allah. Wannan ya sa ta duban Mu'az. 


"Nikam Mu'azu ba na ji kana ƙorafin yawan ciwon baya ba kwana biyun nan? Me zai haka ka faɗawa ɗan uwanka yanda ka ke ji ko yana da shawarar da zai ba ka?"


Daidai nan wayar Khaleefa ta yi ƙara, ya ciro ya ɗaga, Mu'az kuwa kallon Umma ya yi kafin ya ɗan dubi Khaleefan wanda ya yi tamkar bai ji mai ake cewa ba, da alama da Sadauki ma yake waya saboda ya ji shi ya ambaci Saraki. Muddin ka ji Khaleefa na waya ya ce Saraki to ba da kowa yake wayarnan ba face Sadauki. 


"Ni fa na warke Umma. Dama ba wani ciwon a zo a gani ba ne."


"Ke ma dai Na'imatu da neman magana kike, ai shi wannan ya gwammace ko zai nakasa ya yi akan dai Dakta ya duba shi. Wannan baƙin ran nasa irin na uwarsa ban san ina zai kai shi ba. Dakta ya ba ka shekara guda amma daga kai har shi babu aikin da ku ka saka a gaba sai sha wa juna ƙamshi, to ku je ku ƙarata."


Khaleefa dai kallonta kawai ya yi bayan ya kammala wayar, idan Hajja ce ba yau ta saba yi musu caa akan rashin jituwarsa da Mu'az ba. A ganinsa yaron ba sa'ansa ba ne sam, to na mene ne zai tsaya yana wani shiga sharo ba shanu? Ai yaron ma sai ya ƙara raina shi fiye da yanda ya yi a yanzun. 


"Please Hajja, ba na son irin haka."


Haulatu ta saci kallon Khaleefa, aka yi rashin sa'a shi ma lokacin ya ɗan dube ta, hararar da ta samu ne ya sa ta kauda kai tana ɗan yamutsa fuska. 


'Mutum kawai ya baro matarsa ya zo kwaɗayi.' Ta furta a ƙasan ranta. 


Mu'az ne ya fara miƙewa ya yi musu sallama da zummar zuwa shirin tafiya masallaci, tsabar Hajja ta gama ɓata ransa har wayarsa ya bari a saman kujera, da sauri Haulatu ta ɗauka ta bi bayansa. Khaleefa ya bi su da kallo kawai, nan ma bai ce komai ba. 


Sai bayan tashin Hajja da hayewarta sama ne Umma ta maida duba ga Khaleefa. 


"Ɗana, meyasa da girmanku ku ke yin abu irin na yara? Shi yanzu Mu'azu idan ma za'a yi mishi uzuri ganin kamar yana abu wasu lokutan irin na ƙuruciya, kai ai mai hankali ne, ka fi shi sanin rayuwa da yanayi na zamantakewa. Don Allah a yi kokarin kai zuciya nesa, idan ku na nuna wa juna irin wannan hali na ko in kula, me na ƙasa da ku za su gani su yi koyi da shi? Babu dadi ma a ji mutane na cewa jininku bai hadu ba, a ina ne jininku bai hadu ba alhalin duka tsatso guda ku ka fito, uwa uba ma musulunci da ya haɗa ku? Ni dai ban jin dadin wannan abu naku. A ƙoƙarta a gyara."


Khaleefa ya jinjina kai yana mai gamsuwa da maganganun Umma, sosai kuma ya ji har ransa matsayinta ya ƙaru. Ko mahaifiyarsa ba ta taɓa nuna wata damuwa akan rashin jituwarsu ba, asalima sai dai ta ce ya cigaba da jan girmansa kar ya kusa ya sakarwa Mu'az ya raina shi. Ya kuma danganta hakan da cewa watakila kawai saboda ba sa ga maciji da Mamin Mu'az ne. Dagaske suke kishin facaloli a tsakaninsu. 


"In sha Allahu zan yi kokarin gyarawa Umma. Sai dai fa ƙarfe ɗaya ba ya amo. Ni a iyakar sani na, babu abin da ya taɓa yi min, kawai ni ban damu da shiga sabgar wasu ba."


Murmushi Umma ta yi. 


"Ɗan uwanka ne shi, gaisuwa ma ta sakin fuska koda ba hira ku ka yi mai tsawo ba yana da dadi. A daure a kai zuciya nesa. Na kuma ji dadi da ka ce babu abin da ya taɓa haɗa ku. Ya wajen ɗiyata? Jikin dai da sauki ko?"


Sai a sannan ya tuno ma dalilin zuwansa nan shan ruwa, ya je ya tarar gidan kaca-kaca, dama kwanakin nan hakuri kawai yake yi don tun goma ga azumi ƴar aikinta ta tafi gida wai za'a yi mata aure bayan sallah shi ne dalilin da yasa ita kuwa ko tsinke sai ya yi mata jan ido ta ke kawar wa. Girki kuwa sai dai ya siyo a waje, abin ya ishe shi ya kai ƙara wurin Mamarsa madadin ta dauki zafi sai ta nuna ai ba komai laulayin ciki ne kuma ma ba ta saba da aikace-aikacen gida ba, da wanna ta tura musu yar aiki ɗaya cikin biyu da take da su. Sai ta zo ba ta iya girki ba, gidan dai ba laifi takan gyara, yau dai aka yi katari hatta da gyaran bai samu ba dalilin wai ta je gidansu an yi rasuwa, to Hafsat kuma kwanciyarta ta yi dama tun kamawar azumi ba ta yi ko guda ba acewarta ita ba za ta iya ba saboda laulayi bayan jikin ta samu sauki sosai. A fusace ya bar gidan ya kira Umma da zummar zai sha ruwa a wajenta. 


"Lafiya dai ko?"


Tambayar Umma ta katse mishi tunani. Ya yi ɗan murmushin yaƙe, bai fiye son yawan ƙorafi ba musamman akan na kusa da shi don ko Maama sai ta ɓaci sosai yake iya furzar mata. 


"Bakomai Umma, lafiyarta kalau. Ai dayake ma ba ta samun yin azumin saboda yanayi na jiki. Amma da sauki Alhamdulillah."


Umma ta jinjina kai, ta ɗan karanci damuwa a fuskarsa amma sai ta bi shi da hakan tunda ya nunamata babu komai. 


***


 Haulatu ta iske Mu'az na tafe kamar zai tashi sama.


"Ah, ɗan birni saurin me kake har ka na mance wayarka?"


Ta ƙarashe tana mai miƙa masa gami da haɗiye dariyarta. Ya ja guntun tsaki, yanayin fuskarsa babu ɗigon fara'a.


"Dama kin san da zuwansa shi ne ko ta waya ba ki sanarmin na fasa shigowa ba?"


Ta taɓe baki gami da ɗan ɗaga kafaɗa.


"Ina ruwana to? Ɗan uwanka ne fa, tare na gan ku. Ƙiyayyar ai ba ta yi zafin da ba za ku zauna inuwa ɗaya ba."


Ya jinjina kai kawai. Bai ce mata komai ba ya juya ya cigaba da tafiya. 


"Allah ya huci zuciyarka. Sai na taɓo ka whatsapp sai mu shirya."


Bai ko juyo ba, ita kuwa dariya har da riƙe ciki sannan ta koma ciki. Ganin magana Umma ke yi da Khalifa yasa kai tsaye ta nufi hanyar sama.


"Ina za ki je? Maza dawo ki kira Bushira ku tattare wajen nan."


Jin haka Khalifa ya miƙe da zummar wucewa. Suka yi sallama da Umman ya fice. "Wai ke ko a gaida gida ba ki iya yiwa mutum ba?" Fadin Umma tana duban Haulatu baki sake don gani ta yi yarinyar kamar ita ma tana son ɗan uwanta Mu'az wurin basar da lamarin Khalifa. 


"Lah, ni fa Umma ko na yi magana bai cika amsawa ba. Ai kin ma gani sau nawa zan gaida shi ya dinga amsamin kamar yana shan kunun tsamiya."


Girgiza kai kawai Umma ta yi ta tattare shirginta ta haye sama ita ma don ɗauro alwala da niyyar zuwa masallaci. Babban masallaci ne kusa da su kaɗan, ɓangaren maza daban da na mata. Nan suka tafiya gaba daya idan ka dauke su Hajja wadanda ke zama su yi na su a gida. 


Haulatu kuwa idanunta na kan ledar nan, sai ta ji tana son ganin me ya kawomata amma lokacin sallah ya taho kuma ta sani nan kusa za ta ga su Safina da Radiya sun biyo mata tafiya sallah. Da sauri su na gama tattarawa ta dauki ledar ta nufi sama. A daki ta zazzage ledar saman gado, Umma lokacin tana saka kaya ta yi wanka yanda za ta ji dadin gudanar da ibada. 


"Wannan duka tsarabar taki ce?" Fadin Umma tana ɗan mamaki, lokaci guda tana mai karasowa ta kalla. Riga doguwa mai laushi na kwalliya ko yawo a tsakar gida sai na bacci mai kauri guda daya, sai turare mai ƙamshi a wani ɗan gida mai kyau. Sai kuwa agogo da wani set na sarƙa da ɗan kunne kalar silver. Sai ko takalmi irin na yawo tsakar gida mai kyau. Sosai tsarabar ta burge su.


"Masha Allahu, lallai Sadauki Allah ya bar zumunci toh. Idan mun dawo daga sallah ko a waya ki kira ki yi misho godiya. Ki hanzarta an soma kiran sallah." Umma ta ƙarashe tana mai nufar sif son fiddo doguwar riga marar nauyi ita kuwa Haulatu har ta tattara kayan ta shiga banɗaki ta yo wankan ita ma ta fito ba ta bar mamakin wannan kaya ba. Ita a farko ma ta yi zaton ko har da na Ummanta a ciki.

 Koda ta fito ma Umma tuni ta fice, tana shirin saka kaya su Safina suka shigo don haka da gaggawa ta shirya suka fice zuwa masallaci. 


A hanya suke tambayarta me da me Yaya Sadauki ya kawomata tsaraba, ta ƙi sanar da su ta ce sai ta ji na su tsarabar tukunna. Nan Safina ta ce duka dogayen riguna ya kawo musu, wasu kuwa takalma ne. Sai ta ɗan yi turus, to meyasa na ta ya fi na su yawa? 


"Ke kuma me ya kawo maki?"


Ta kara saurin tafiya, layin duka fitilu ne masu haske sosai ga kuma mutane masu parking motocinsu har ma da masu tafiya a ƙafa don tuni an tayar da sallar isha'i. Da wannan ta samu damar fadin


 "Sai ku zauna har mu rasa wannan raka'ar ku na tambayar abin duniya."


Ganin haka suka mara mata baya da sauri, da wannan ta samu aka bar tambayar don ko bayan sun dawo gida, wainar fulawa suka yi zaman ci sannan suka kora da lemun zoɓo, tana ba su labarin diramar da aka yi tsakanin Mu'az da Khalifa, ita da Radiya suka dinga dariya yayinda Safina ta dan ji babu dadi wai an ɓata ran masoyinta.


***


Washegari... "Wallahi kurwar ɗana kur! Ni dai ina maki gargadi da babbar murya, daga ke har mayyar ɗiyarki ku fita hanyar ɗana! Idan ba haka ba zan nunamaku daidai nake da ku. Wato tsabar an shanye shi, ya kasa zuwa wurina shan ruwa, amma ya iya ya dinga safa da marwa a hanyar wajenku neman abin da zai ci! Wannan uban nacin da masifa da me ya yi kama? Barikin da ku ka saba yi a inda ku ka fito shi ne yanzu ku ke gwada shi kan ɗana? To na ga Zakiyya (Maama) ma, ita ma ta yi ta gama! Haka nan ta rabu da ni! Ballantana kuma ke da ba a gama sanin asalinki ba!"


Waɗannan zantukan da suke fitowa daga bakin Momin Mu'az, su ne suka farkar da Haulatu daga baccin ranar da ya kwashe ta. Ƙarfe uku da motoci, Hajja ba ta nan, Najeeb ya kai ta asibiti wurin likitan ido. Ta murtsuƙa idanunta, Momi na tsaye ta riƙe ƙugu ko rufin mayafi ba ta yi a saman doguwar rigar atamfar dake jikinta ba, Umma na daga zaune ta yi shiru kawai fuskarta dauke da tsananin damuwa yayinda Baba Saude da Bushira ke a gefe sai ko wata fitsararriya a cikin ƙannen Mu'az, Nusaiba dake tsaye daga ƙofa kamar wacce ke gadi kar wani ya taho. Kan Haulatu ya yi masifar ɗaurewa. 


"Umma, meke faruwa ne?" Ta yi tambayar tana duban mahaifiyarta. A nan ne ta ga hawaye ya zubo daga idanun Umman ta saka gefen hijabinta ta share su, dama tun bayan sallar azhar take zaune saman darduma tana tilawar Alƙur'ani. A haka Momi ta iske ta ta hau bambamin faɗa. 


"Toh, gwanar na iya! Ke ma ina maki gargadi da babbar murya, kar ki ƙara shiga harkar ɗana. Can inda kuka je ku ka yi gadon barikancinku, ya ƙare a kanku amma ba ku isa ku zo ku gurɓata mana zuri'a ba. Ban da karuwanci irin na mace irinki, ke ma har kin san ki naniƙewa namiji ki liƙe masa kuna wasa da dariya irin wanda ko ƙannensa ba ya sakewa ya yi da su? To kuwa barikin ya ƙare a kanku. Amma wallahi na sha tabara na sha yasin, kuma ɗana zan ƙara tashi tsaye  a kansa kafin ku raba ni da shi." 


Haulatu ta mike tsaye saboda tsananin fusata jikinta har wani rawa ya ke yi. Ta ƙarasa har gaban Momi, ta dube ta da idanunta da suka hadu da bacci da ɓacin rai suka yi jazur. Umma ko kusa ba ta kula ma da ita ba saboda tsantsar zafin da kirjinta ke yi sai jin tashin muryarta ta yi cikin maidawa Momin Mu'az martani mai zafi.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro 

 Page 26

Wata mace ta gani mai haske tamkar buzuwa don duk a yaran Hajja, Hajiya Nafisa ta fi su hasken fata balle kuma da ya haɗu da hutu da rayuwa a wuri mai kyakkyawan yanayi. Yaranta uku, babbar budurwar wacce Haulatu jikinta ya ba ta cewa ita ce Zaituna, ta sha doguwar abayarta ruwan madara mai ɗan karen kyau da ɗaukar ido. Sai da ta saki baki wajen kallon baiwar da Allah ya yiwa Zaituna, doguwa mai ɗan jiki kaɗan sai kuwa hanci har baka ga ƙaramin halittar baki. Sai ko idanunta kalar na Haulatun masu ɗan girma. Uwa uba kuma ga dirin jiki don koda abayar da ke jikinta bai ɓoye halitta na cikar ƙirji da mazauna da Allah ya ba ta ba. Sai mai bi mata namiji da ƙaraminsu shi ma namijin. Dama ta ji a bakin Hajja yaran Hajiya Nafisa su uku ne. Babu abin da ya burge Haulatu har ya sanya ta murmusawa face yanda ta ga Hajiya Nafisa ta rungumo Umma a jikinta har tana ɗan hawaye. Ta san sun sha gaisawa da Umman ta waya idan ta kira Hajja, amma sai ba ta yi zaton kaunar da ta ke yi ga Umman ya kai har haka ba. Nan kuma aka zauna tana ji Hajiya Nafisa ta soma tambayar ina yarinyar da aka ce ta zo da ita, sai kuwa Baba Saude ta yi caraf ta amsa.


"Kin gan ta can tana ƴar laɓe. Haulan Hajja ƙaraso ku gaisa mana."


Ta ɗan ji nauyi ganin gaba daya sun kallo inda ta ke, ta soma tafiya ta ji an sanya tattausan hannu cikin nata. Koda ta duba ta ga Zaituna ce take sakar mata murmushin da har gefen kumatunta na lotsawa. 


"Assalamu alaiki."


Ta amsa mata sallama gami da maida mata martanin murmushin. Ita kuwa Hajiya Nafisa rungumeta ta yi bayan ta ƙarasa wajenta kafin ta zaunar da ita a gefenta. 


"Masha Allahu, wannan dai ni za'a bar wa ta yi karatu a wurina ko? Ki samo mana ɗan Malaysia?"


Aka yi dariya har Haulatun. Aka gaggaisa, tana kula da mutanenta su Ihsan yanda suke cika da batsewa, su sam ba su so ganin wannan tarbar ga su Umma ba daga wurin Hajiyar Zaituna. Hajiya Hadiza ita kanta abin ba haka ta so ba, so ta yi su haɗa kai da ƙanwarta su ware Umman. Ita kaɗai ba za ta iya yin yaƙin ba ko don shakkar Hajja, amma fa da ace Haj Nafisa ta biye mata to fa lallai ko ba su yi nasara a wani ɓangaren ba, za su iya yi a wani. Ita har gobe ba ta son Umma, ta kuma tsani Haulatu fiye da zaton mai zato musamman da ta ji labarin ɗinkunan da Hajja ta ce Sadauki ya ɗinka mata na sallah da ma tsaraba na bajinta wanda dole sai da Umma ta fiddo su ta nunamata. Fahima ta ke yiwa kwaɗayin zama matar Sadauki, wannan ne burinta. Maza irin su Sadauki wahala suke yi, ba ma haka ba, samarin yanzu sun zama mayaudara. Fahimta duk wanda zai zo wajenta da zummar yaudara ne. Ta fi kaunar yi mata auren gida na zumunci, irin auren da ka riga ka san girma da halayyar mutum. Sai dai shakka babu ta tsorata da wannan giggiwar da acewarta Sadauki ke yi akan Haulatun, meyasa ko kyautar turare bai taɓa haɗa su da Fahimar ba? Ƙarƙari dai na barka da sallah wanda kowa ma yiwa ya ke. 


"Haj Hadiza  kin yi shiru ana hira." Faɗin Maman Zaituna kenan. Sai ta yi dariyar yaƙe.


"Uhm, kin ga hankalin ne ya tafi a wani tunanin. Ai ya kamata ku ɗan huta sai ku ci abinci ko?"


"Um um, nikam sai Autan Hajja ya iso ma ci tare. Sai dai ko yaran. Haneef?"


Ta kira sunan Autanta tana ɗan rungume shi da yi mishi yaren Malaysia. Ya kuwa taɓe baki ya ba ta amsa da shi tare da ita zai ci. Ta yi dariya sannan ta tambayi ɗan uwansa wanda ta ke kira da Sayyeed. Shi ɗin ma ya ce sai da ita. 


Zaituna dai ɗakin su Haulatu ta nufa sanin da ta yi nan ne masaukinsu duk sadda suka zo, sai Hajja ce ta dakatar da ita gami da nunamata ɗakin dake gefenta. Ba musu ta juya ta nufi ɗakin. 


Ba su yi ko awa ɗaya da zuwa ba sai ga Abba da iyalinsa sun iso. Ya sha coat abinsa, ɗan boko na gaske. Tare da matarsa da ƴan ukun yaransu da matar ta haifa duka maza ƴan kimanin shekaru tara. Matar dai fuskar babu alamun fara'a, Hajja ta fi ba Haulatu mamaki, duk irin yanda surukar ke wani tamke fuska tana shan ƙamshi amma rawar jikin yi mata hidima ta ke. Koda dai ance dama matar ba kirki ta cika ba sai dai kaunar da Hajjar ke nunawa Autanta Abba ya sa har matarsa ya shafa. Ko kaɗan Haseenah ba ta laifi wajen Hajja. 


Kafin dare, sai ga Zaituna da Haulatu na hira tamkar sa'annin juna, za ta girmi Haulatu da shekara, ko kusa Zaituna ba yarinya ce mai ji da kai ba. Ba ta da ɗaukar kai kamar su Ihsan da Fahima. Mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne mutumin ƙasar Misra da aiki ya kawo shi Malaysia. Sun haɗu da Haj Nafisa ne a Umrah. Soyayya ta ƙullu kamar wasa sai ga shi har ya tako Nijeriya karo na farko a rayuwarsa dominta. Bayan binciken asali da komai Allah yasa aka yi auren har suka haifi su Zaituna, Muhd Sayyid da kuma Haneef. 


Haka Haulatu ta yi ta shan hira a wajen Zaituna da hausarta da ba ta yi tarr irin nasu ba. Ta ce tana jin larabci, turanci da kuma yaren Malay. 


"Yanzu wai duka waɗannan yarukan kina ji?"


Zaituna ta yi murmushi tana lumshe idanun da suka zame mata jiki muddin tana magana ta amsa wa Haulatu tambayarta.


"Na'am, ina ji duka."


Jinjina kai Haulatu ta yi, sai ta ji ta ƙara burgeta. Ita tana son ta iya yaruka daban-daban amma kamar ma ba ta da wannan kwakwalwar da za ta ɗauka. 


"Kina zuwa makaranta ne?"


Tambayar Zaituna ya katse tunaninta.


"Eh, yanzu dai results nake jira na exams da muka yi, an ce Waec ya fito ma. Ban duba ba dai."


Ta ɗan girgiza kai kamar mai ɗan tunani kafin ta ɗan ce.


"Oh, Masha Allah. Allah ya taimaka."


"Amin."


Har suka kammala hirar Haulatu ta yi mata sallama ta tafi don kiraye-kirayen sallar Isha'i da aka soma ita dai Haulatu ba ta bar mamaki ba. Shi kuwa Yaya Zaid me ya kai shi ƙin Zaituna? Yariny mai nutsuwa da daɗin hira, ga yawan murmushi. Sai ma ta ji ya ba ta haushi, a duniya duk namijin da zai wulaƙanta mace ba ya burge ta sam. Za ta so ta ji labarin yanda lamura suka faru daga bakin Zaitunan, sai dai ta sani tayar da zancen kamar yi mata fami ne da abin da take da yaƙinin zai wahala idan bai wuce ba a zuciyarta wannan yasa ko kusa ba ta yi karambanin haka ba. 


***

Tun shigowarsa falon ya ji wani irin ƙarni ya buso hancinsa. Ransa ya ɓaci sosai ganin an yi shara da guga amma fa tiles ɗin ƙarni ya ke yi. Ba yau ya saba da haka ba, sai ƴar aikin ta yi gyara amma fa ƙarni ya dinga tashi. Har liquid detergents ya kawo kala kala masu ƙamshi daban daban akan ta dinga amfani da su wajen gugar, amma sai ta ce wai kumfar yawa yake yi ta kasa gogewa yanda ya kamata. Amma a lokacin sai ta ba da haƙuri da cewa za ta gyara. 


"Sannu da zuwa. Lafiya ka tsaya a bakin ƙofa?"


Ya dubi Hafsat wacce shigowarta falon kenan daga ɗaki, ransa ya ƙara yin baƙi ganin ita ta cakare ta ɗau wanka cikin riga da wandon da ba su kama ta sosai ba don ya hana ta saka abu matsastse saboda cikinta, dama a nan yake samun sauƙin kuma nan ɗin ma sai da ya rantse mata muddin ba za ta dinga gyara jikinta ba to fa babu abin da zai hana ya ƙara aure. Wannan jan idon ne ya sa ta saitu, sai ko ƴar aikin da ta ke rufarsa da masifa da rashin mutunci idan ba ta kammala gyara ba kafin dawowar Khaleefa. Tana son mijinta matuƙa amma ta rantse ita ba ƴar wahala ba ce. Ba za ta yi girki ko aikin da zai jigatar da ita ba balle har fatar hannunta ta yi kaushi madadin taushin da yake da shi. 


"Why ki ke min haka? Meyasa ke tunda kin nuna kin fi ƙarfin ki yi, ba za ki saka masu yi makin su yi abin da ya dace ba? Ace kusan koyaushe sai na yi zancen ƙarnin da ke tashi a gidan nan?"


Ta ɗan marairaice fuska.


"Ƙarni kuma Khaleefa? Ni ban ji komai ba. Kodai hancinka ne?"


Takaici ya sa shi zarcewa ɗakin kawai ya bar ta tsaye tana ware hanci, tabbas ta ji amma ita toh ya za ta yi tund mai aikinta ta tafi tun kafin magriba? Kawai sai ta ɗauki room freshner da ke a can lungun kujerunta ta hau fesawa a falon tana mitar tsirfa irin na Khaleefa. 


Shi kuwa hatta banɗakin sai da ya ji yana ƙyanƙyami tunda abu ne a rubuce, mai aikin ce ta wanke, kamar kullum sai da ya zuba hypo lungu da saƙo ya kora ruwa kafin ya zuba dettol a ruwan wankansa. 


Koda ya fito ya zura jallabiya, bai koma falon ba, tuni ya ciko cikinsa a gidansu wajen Umminsa. Ita kuwa Hafsat dake falo tana chatting jin shiru bai fito don ya ci abinci ba dai ga ta kamar an jefo ta ɗakin babu ko sallama. 


"Wai Khaleefa mene ne haka? Kwanaki nawa ka jera ba ka cin abincin gidannan? Haka za mu yi ta rayuwar ka ƙi ci sai dai ka je waje ka cika cikinka? Salon ka cigaba da jawomin zagi wurin yan uwanka a ga kamar kana cefane ba'a girkawar?"


Duk yanda ya kauda kai ya yi banza da ita sai da maganarta na ƙarshe ya sa shi ɗago kai ya dube ta.


"Ina gargadinki, ki kiyayi harshenki da faɗamin duk abin da ya fito daga bakinki. Kaf cikin ƴan uwana babu sa'an yin ki. Stay within your limits."


Yanda ta ga yanayin fuskarsa da kaushin da muryarsa ta yi ya sanya ta turo baki kawai ta fice daga dakin, ta san halinsa, tabbas sau daya ta taɓa kuskuren faɗin wata magana akan Umminsa aikuwa a ranar ba ta kwana gidansa ba don dai Ummin da kanta ta je biko ta nuna lallai ya yi hakuri tunda ita aka yiwa ita ma ta yafe to shi ma ya yafe mata. Shi ne dalilin da yasa take takatsantsan amma abin na mata zafi. Ai koda ba ita ke girkawa ba a ganinta wulakanci ne ya ci abinci a gidansu. Akwai sadda ta ji har wurin Hajja yake tarewa yana cin abinci daga bakin Fahima don ita din ƴar gidanta ce sosai. Fahima ƙawa ce ga ƙanwarta. Wannan ne dalilin sabon su. Takan zo gidan tare da ƙanwar Hafsat din su wuni ana hirarraki.


***

Ɗan Mutuwa cike da walwala ya dubi Hajiya Adama. 


"Sai fa a soma shiri, aurena za'a yi shagalin da ba ku taba haskowa ba."


Ta yi dariya bayan ta miƙa masa wayarsa inda ya buɗo mata hoton Hindatu wanda musamman ta je ta ɗauka kala-kala a gidan hoto ta turamasa. 


"Ba laifi, ta gaban mota ce. Ina fatan ka yi wa komai tufka gudun samun matsala?"


Ɗan Mutuwa ya yi dariya. 


"Kar ki damu Hajjaju, ai nan zuwa anjima zan je ba ga mahaifiyarta. Komai na tafiya daidai. Ganin farko kar ki so ki ga yanda uwar ta ruɗe a kaina. Idanunt fes ya ke."


Suka sa dariya. 


"Ai irin su an fi cin riba a kansu. Kai dai a wannan ganin da za ka yiwa Uwar ka tabbatar ka jiƙa ta yanda ta dace."


"Ba sai kin faɗa ba, gida na siya mata ma, zan kai matar takardun gidan. Daidai da ma'aikata zan zuba mata."


Hajiya Adama ta yi wata shewa. 


"Ɗan Mutuwa shegen kaya. Ko tsinanne haka ya gan ka ya ƙyale."


Suka yi dariya kafin ya ɗan tamke fuska.


"So nake na shigar da batun Na'imatu da wancan shegiyar yarinyar gaban mai alfarma."


Ta jinjina kai 


"Hakan daidai ne. Amma me zai hana ka bari ka gama da babin auren nan da ka cicciɓo. A gani na gwara koda zuwa wajen Na'imatun za ka yi, ta gane cewa ba zaman jiranta ka tsaya ba. Na gaba ya yi gaba. Ai ni zan fi kowa farin cikin maido Na'imatu rayuwarka. Koda kana da kyau ka ƙara da wanka nake gayamaka, ɗiyarnan taka babbar kadararka ce. Ka samu ka aurar da ita ga wani mai faɗa a ji ɗin. Ko nan gaba sai ka ga an ci gaba da damawa da kai fiye da haka. Za kuma ka ƙara shiga cikin manyan mutanen da ba ka taɓa kawowa a kai ba."


Haka ta ci gaba da rura wutar lamarin a wajen Ɗan Mutuwa har sai da ya gamsu ya kuma yi amanna da dukkan huɗubobinta. 


***

A Katsina kuwa, washegarin ranar da su Zaituna suka iso garin. A yammacin suka shirya don zagayawa sakamakon Zaituna da zaman ɗakin ya ishe ta. Tafe suke da Haulatun don zuwa ɓangaren Daddy Ridwan, Zaitunan ce zasu gaisa da iyalansa da kuma na Baban Kowa, iyakacinta dama wurin Baba Dakta da Baba Alhaji sadda suka zo gidan. Safina ba ta nan sun fita kasuwa da Maama ita kuwa Radiya tana ɓangarensu.  Hajja ta dube su tana washe baki.


"Inyee, ke Nafi dube su kamar dama can sun san juna."


Haulatu da Zaituna suka dubi juna gami da yin dariya. 


"To ai Hajja haduwar jinin kenan. Allah ya ƙara haɗa kawunansu."


Faɗin Maman Zaituna, Umma da su Hajja suka amsa da amin. Hajja ta dubi Fahima  wacce ta zo gidan kenan sai bayan biki. 


"Ke ba za ki tashi ku je yawon tare ba? Ke meyasa kike da baƙar zuciya ne irin na ubanki?"


Fahima dake kwance tana danne wayarta wacce Sadauki ya maida mata ita bayan Haj Hadiza ta saka baki, gaba daya sai ranta ya ɓaci da batun Hajja. Dama can ba wani jituwa ta ke yi na sosai da Zaituna ba, don ita Fahima a duniyarta ta tsani koda ƙawance ne da wanda ya fi ta kyau, ta fi kaunar inda ta fi mutum ta yanda za ta wulaƙantaka son rai. Haɗewae kansu da Haulatu tun zuwansu ya tsayamata a maƙoshi sai da ta ji kamar ta arce ta koma gidansu amma Haj Hadiza ta yi mata jan ido. A cewarta ta ina za ta saka idanun ta kula da takun Haulatun da Sadauki idan har ta ƙi zama ta koma? A dole don tasan tana son Sadaukin yasa ta danne ta haƙura. Yanzu kuwa maganar Hajja sai ta ji ranta ya yi zafi har ta kasa ɓoyewa a fuska. 


"Haba Hajja, ƙila dai ba ta son hayaniya ne. A ƙyalemin ɗiyata ta huta."


Faɗin Umma kenan cikin son nuni da goyon bayan Fahimar, ita kuwa Haulatu ta ji inama Umma ba ta saka baki ba a shigarwa wacce ba ta san ƙimarta ba. Aikuwa Fahima ta ƙara jin zafi na don me Umma za ta kira ta da ɗiyarta? Kawai sai ta miƙe tana tura baki ta yi ƙasa, gwara ta fice daga sashin Hajjar ta ba su wuri. 


Zaituna ta yamutse fuska tana mai zaginta cikin yaren Malay ƙasa-ƙasa yanda ta san Mamarta ba za ta ji ba. Haulatu dai ba ta san me ta furta ba, suka kama hanya suka sauka. Zaituna na mata mitar dama sam Fahima ba ta da hali. Tun can wai ba su jituwa. Ita ta rasa ma dalilin da yasa har mamarsu ba su kwanta mata a rai ba. Wai kamar ba jinin ƴan gidan ba. Halayyarsu ta sha bamban. Ita dai Haulatu murmushi kawai take yi tana duban wayarta ganin missedcall din Hindatu. 


Daidai lokacin da suka isa ga ƙofar fita daga falon, a lokacin shi kuma ya sanyo kai da sallama. Gaba ɗaya suka yi turus, Haulatu ta ɗan yi saroro, ta kalli wancan ta maida idanunta ga wannan. A hankali kuma ta ga Zaituna ta sauke kanta ƙasa. Gaida shi ta yi da harshen larabci, shi ɗin ma cike da basarwa ya amsa mata yana tambayar yaushe suka iso. Ta ce jiya. Daga nan ta ja hannun Haulatu wacce ita gaisuwar ma maƙale mata ya yi a fatar baki suka gifta shi suka fice daga falon. A hanya ta kula kamar Zaituna hawaye take fitarwa don haka ta ce su karasa bayan gidan wajen rumfa su zauna. Aikuwa suna isa Zaituna ta ci kukanta, abin ya ɗan daki ran Haulatu, sai kuma ta tsinci kanta da jin tausayi da haushinta lokaci ɗaya. Namijin me? Akan me za ta tsaya tana zubda hawaye kan wanda bai ɗauke ta komai ba? I

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 25

A ɓangaren Ɗan Mutuwa kuwa, dukkan wasu sharuɗɗan da Uban Dodo ya ba shi babu ɗaya da bai cika ba, ƙarshe aka mallaka mishi wani zobe mai sheƙi idan ka zura a yatsanka. Ranar farko da ya saka sai da ya ji shi kamar an yi mishi katanga tsakaninsa da imaninsa don a lokacin ji ya yi ba iyaka satar wani sassa a jikin gawa ba, saduwa idan aka ce ya aikata da gawar zai iya yi a sannan. (Wa'iyazubillah). Sharuɗɗan shi ne duk runtsi koda zai yi sallah to kar ya sake ya yi ta isha'i da Asubahi, kuma kar ma ya kara tunanin daukar azumi a duniya idan har yana son arzikinsa ya dauwama. Idan yana da aure ko kuma zai yi, toh ana so a yi shagali a yi ɓarin kudi na kata'i wanda haka zai sanyaya ran Uban dodo da aljanunsa, ba ma sai bikin aure ba, duk wani abu na sabga idan ya tashi toh fa a yi ɓarin kuɗi, wato dai a dinga almubazzaranci. Wannan zai ƙara haɓɓaka arzikin sosai. Uwa uba kuwa ga wani akwatim tsafi da aka ba shi yake ajiye a ɗakinsa don tuni ya dawo garin Kano da zama, koda sun haɗu da idon sani kawai sai dai su kalle shi amma babu wanda ke iya yi mishi tambaya kan abin da ya faru a baya. Sai ma ya bar wajen su ke tunawa ashe fa laifi ya yi. Sam ba a tsohuwar unguwar da suka rayu ya siya gida ba, sai ya siya can cikin wata ɓoyayyar unguwa wadanda duka sabbin gidaje ne. Wani irin akwati ne wanda duk sadda ya buɗe bayan ya karanta wasu siddabarunsu, toh fa zai gan shi cike maƙil da sabbin kuɗaɗe ƴan dubunnai. 

  Ɗan Mutuwa jin sa yake a sabuwar duniyar da bai taɓa hasko kansa ciki ba. Ashe haka kuɗi su ke da masifar daɗi? Tabbas ya yarda shiyasa Hajiya Adama ke mishi kallon baƙauye tunda bai san ya zai sarrafa aljihunsa ba ya zama abin burgewa a wurin jama'a. Yanzu kam suturu ya siye su kuma ya bada ɗinki, shi kansa ya sani idan sallah ta zo toh fa zai yi bushasha. Ga mota da ya yi odar ta daga Lagos za ta iso kafin sallah. Abu ɗaya zuwa biyu da ya yi mishi saura a yanzu, aure ne na farko. Sai ya zaɓa kuma ya darje. Yana dai sha'aninsa da matan waje. Yanzu kuma tunda akwai kuɗi, buƙatarsa ta biyu kuwa, nemo Na'imatu. Ko ba komai ta ga yanda rayuwa ta sauya mishi. Kuma zai bi duk wata hanya na ganin ya mantar da ita komai da ya faru a baya, su dawo da ɗiyarsa, har yanzu wannan mummunan ƙudurin da ya yi game da Haulatun yana ransa. Idan ma za ta kawo tangarɗa ai ga Uban Dodo nan, sai a tsaface mishi su ta yanda duk abin da ya ce to fa lallai hakan za su bi. Ko kara idan bai ce su tsallaka ba, ba za su tsallake din ba. Wannan ne mafarkinsa. 


***

Katsina...


Malama ta dubi ɗanta a nutse, fuskokin kowa cike da murnar gobe za'a tashi da sallah sakamakon azumi da aka yi guda ashirin da tara cif kuma aka ga watan sallah. Tun safe suka iso Katsina daga Abuja shi da Jalilah don yin sallah a nan, ita kuwa sai bayan biki ma za ta koma. 

 Bayan falon ya rage daga Malama sai ɗan nata ta soma magana.


"Meke damunka ne haka? Gaba ɗaya ka rame sannan kallo ɗaya za'a yi maka a fahimci kana tattare da wata damuwa. Ko an yi wani abu ne?"


Zaid ya ɗan yi murmushin yaƙe. 


"Babu komai Ummi, azumi ne kawai."


Ta ɗan yi shiru kamar ta ƙara magana sai kuma ta share. 


"Ai shikenan."


"Bari na kai ta gida." Yana nufin Jalilah, Malama ta gyaɗa kai.


"Toh, Allah ya tsare. Ga saƙo ma ina ajiye da shi, yaran nan na dinga bi su kai min babban gida amma kowanne sai ya lafke wai azumi. Jikar wajen Hajja na siyawa sarƙar nan, Haulatu. Ka shiga da kanka ku gaisa da Hajja ka ba ta."


Nan da nan yanayin fuskarsa ta sauya. Hajja dai? Wai Allah, matar da ta faɗamasa magana a bainar jama'ar gidan gaban ƙannensa? Wannan shi ne ga samu ga rashi, abin da zuciyarsa ke kauna ta faɗo a muhallin da ya sani har abada ba zai samu ba. Yau kam daga ma yanayin fuskar mahaifiyarsa babu wasa a zancenta. Kafin ya yi magana ta tari numfashinsa. 


"Har sai yaushe? Sai zuwa wane lokaci za ka cire komai a ranka ya zama tamkar ba'a taɓa yi ba? Kar fa ka manta kai ne babba a gidan nan, yau a dalilinka, daidai da Kamalu ba ruwansa da sashin Hajja saboda kai. Wane irin hali na banza na riƙo ku ke da shi? Ina ƙara tunasar da kai, kai din tamkar madubi ka ke a wajen ƙannenka, idan ka ce abu fari ne, toh su ma a wajensu hakan take babu sauyi. Duk kuwa abin da ka baƙanta shi, ka lura da kyau su ma a wajensu baƙi ne. Riƙo ba ya daga cikin halaye masu nagarta a rayuwar duk wani musulmi na ƙwarai. Ballantana wacce ka riƙe a rai, ba sa'ar yin ka ba ce. Uwa ce a wurina ni mahaifiyarku. Sai dai ka sani, gyaruwar mu'amala tsakaninka da Hajja ya zame maka wajibi muddin ina raye kuma na isa da kai koda kuwa ace silar gyaran a ɓangarenta shi ne aura maka Zaituna."


Duk a maganganun Malama babu wanda ya daki zuciyarsa ta kar furucinta na ƙarshe, wato tana nufin koda ace sulhunsa da Hajja shi ne ya auri jikarta Zaituna toh ya zama dole a wajensa? Ga dukkan alamu kuma umarni ne na kai tsaye, sai jikinsa ya yi sanyi. Bai taɓa ganin Malama cikin yanayi na damuwa da ɓacin rai mai yawa kamar na yau ɗin ba, kuma duk a silarsa. Ita kanta ta sani dole a ga kamar tun farko da laifinta, ya nuna ba ta isa da yaranta ba kuma babu mai iya tanƙwara shi tunda har su Baba Dakta sun mishi faɗa da nasiha akan rashin jituwarsa da Hajja sai dai ko gezau. Asalima ita kanta Hajjar fita ta yi sabgarsa don a cewarta tunda bai ji maganar yayyunta ba, to ita din wace ce? Ya kuma sha zagi sosai a wajenta sadda suka taɓa haɗuwa a ɓangaren Baba Alhaji, lokacin Alhajin bai jin dadin jikinsa. Ta ce idan har sai Zaidu ya gaishe ta za ta rayu toh ya riƙe gaisuwar, ta gwammace mutuwarta. 


Runtse idanu ya ɗan yi tunano kalaman Hajja masu zafi. 


"Ki yi haƙuri Umma, zan gyara. Zan je da kaina bisa umarninki."


"Idan ma ka ga dama kar ka je Zaidu, cigaba da nunawa duniya ɗan mace ne kai da ba ta isa ta sanyaka ka yi ba. Ka yi ta nunawa duniya ban yi iyakar yi na wajen ba ku tarbiyya ba. Wato kai ba ka san zuru ba ko? Hum."


Daga haka ta miƙe ta bar shi a falon shi ɗaya. Ya ɗan yi jim kafin ya dannawa Jalilah kira akan ta fito su wuce. Sai da ta shiga ta yiwa Malama sallama, Bebi na makale da hannunta ita wai ba ta son ta tafi, Juwairiyya kuwa da yake ta dawo daga Malumfashi cewa ta yi sai ta bita kawai kwana biyu ma sun huta. Ita dai Jalilah dariya kawai ta ke yi. Har waje suka raka ta inda Zaid tuni ya shiga mota ya kunna. Sai bayan ta shige suka yi sallama. Ta ɗan dubi mijinta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta kauda kai, ta kula kamar ransa a ɓace yake don ko magana bai mata ba ita ma kuma sai ta ja baki ta yi shiru. Koda suka ƙarasa a zatonta zai shiga gidansu amma sai yace mata dai gobe. Sosai ta ji babu dadi, ko wane irin fushi yake ciki ai bai kyautu ya ƙi shiga gaida iyayenta ba tun da iyakarsu gaisawa a waya. Ya kalle ta.


"Akwai matsala?" Ta share ƙwallar da suka cicciko mata kafin ta girgiza kai. 


"Buɗe boot na dauki jakar kayana."


Koda ya bude ta dauka ta soma tafiya sai kawai ya kashe motar ya fito. Ji ya yi bai kyauta ba a karon kansa. Ba ta san ya taho ba sai ji ta yi ya sa hannu ya karɓi jakar. 


"I'm sorry." Ya furta a hankali. Ta dube shi kadan sai ta yi murmushi ranta ya ɗan yi fes, a duniyar mace tana son ta ga an mata laifi kuma an ba ta haƙuri akan wannan laifin, Zaid yana daga cikin masu iya tattali da kuma rarrashi. Shi dai kawai ka kula da harshenka domin ta lura yana da riko. Sai ka dauka ma ya mance abu kawai bayan kwana biyu ya tunasar da kai a matsayin laifi ne ka yi mishi. Ita har mamakin wannan halin ta ke don haka ta ke yawan takatsantsan gudun ɓata masa rai. 


***

 A can babban gida kuwa, an dinke da murnar dawowa Abba Ridwan da ma Baban Kowa. Kowa dai cike yake da murnar ma gobe sallah. Haulatu tare da Umma suka je har ɓangaren Abba Ridwan suka yi masa sannu da zuwa. Dama sam ba su da matsala da Hajiya Nuratu, mace ce mai fara'a da son mutane. Hakanan shi ɗin ma. Toh kusan a yaran nata ma guda goma cif, Sadauki ne Haulatu ke mishi kallon marar kirki sai ko wasu ƙannensa biyu Fu'ad da Zuhra. Amma hatta da Raudha wacce za'a yiwa aure bayan sallarnan ba ta da daukar kai. 


 "Su Haule an zo kunce jaka. Toh ko gumamar Makkah ba samu za ku yi ba."


Ta juya ta kalli Fu'ad, yaron da za su yi sa'anni da juna da shi, ya yi maganar ne ƙasa ƙasa cikin raɗa don gudun kar Maminsa ta ji. Wani dariya na rainin wayo ya yi, sai ba ta ce masa komai ba ta dauke kai ta rantse kuma sai ta rama ko ba yanzun ba. Hira Umma da Mamin ce ya sanya suka ɗan zaunu a ɗakin don har ƙuryar ɗakinta suka shiga, Mamin ke labartawa Umma labarin ƙasa mai tsarki, ita dai Haulatu duk ta ma matsu su tafi tun bayan da Fu'ad ya yi wannan furucin, wato ma sun zo don a basu tsaraba ne? Ai kuwa zai san ya yi da mai yi. 


Sai da suka tashi da zummar tafiya ne suka tsinkayi sallamar Sadauki. Gaba daya suka amsa, Haulatu ta ɗan dube shi. A lokacin sai ta ƙara ganin kamanninsa da Mami Nuratu. Tsawon ne na mahaifinsa. Ƙananun kaya ne ya sanya farare ƙal, rigar ce a ka yiwa adon baƙi daga gaba. Ya russuna yana gaida Umma, ta amsa fuska a sake ita ma. Haulatu ta gaishe shi, ya amsa ba tare da ya maida hankali ga kallonta ba. Ta ɗan bi gefen fuskar da harara. 


'Sarakin ƙarfi da yaji, sai girman kai.' Ta fadi a zuci. Tana kallon su Fu'ad duka suka fice daga ɗakin saboda dodonsu ya shigo. Miƙewa ta yi ita ma ganin Ummanta a tsaye. Suka yi musu sallama daga nan suka nufi ɓangaren Baban Kowa. Nan ma sun samu tarba daga Maman Radiya, dama ita mace ce mai hakuri ga zurfin ciki. Ita sam ba ta da magana ma. Duk irin taimakon da wasu za su yi maka, ko yaya idan kana halin na rashi sai an fahimta, kawai dai ba laifi akwai rufin asirin. Amma ko daga bambancin ɓangaren wasu da na su sai ka fahimta. A hakan ma Haulatu ta ji irin taimako da yan uwan ke yiwa Baban Kowa da iyalinsa daga bakin Safina, ta ce hatta da karatun yaran Alhaji Ridwan ya dauke. Abubuwa dai na alkhairai suna samu sosai. Suturu kuwa nan ma Safina ta ce Sadauki na yi musu sosai. Baban Kowa dai an ce yanzun shi ke riƙe da ƙatuwar gonarsu na gado, acewarsa ya fi zaman haka.


***

 A hanya suna tafe suna hirar abin da ya shafi rayuwa da Umma. Haulatu ke tuna irin kalar rayuwar makarantar da ta gudanar a baya tana firamare wanda wasu lokutan ma hakanan za ta je makarantar babu abin da ta saka a cikinta, wani lokacin ma babu kudin dinka mata sabon kayan makarantar haka za ta dinga yawo da koɗaɗɗun kaya. Ta ƙara duban Umma tana ƙara damke hannunta kamar wasu ya da ƙanwa. 


"Amma yau Umma kalli gidan da Allah ya jefo mu, cikin zuri'ar nagartattun mutane masu halayyar girma."


Murmushi ɗauke saman fuskar Umman ta kalli ɗiyarta da hasken fitilun da ya kewaye gidajen ya haske. Ga wani iska mai dadi da ke gudana a daren. 


"Alhamdulillah, ɗiyata ta fara hankali."


Ta yi murmushin ita ma. Umma kuwa daga nan shiru kawai ta yi, mafarkan da ta ke yi kwanakin nan a kan Mijinnata yana matuƙar tsorata ta. Abubuwan dai na tashin hankali da hana sukuni. Sai dai duk sadda ta yi ba ta komawa bacci take tashi ta yi alwala da nafila, wani lokacin shi ke nan ta farka kenan har asubahi. Haka har aka shiga goma ƙarshe da ta hana kanta baccin dare. Babu wanda ta taɓa furtawa, ta dai dage da addu'o'inta ta kuma bar abun a rai.


  A falon Hajja na ƙasa su na shiga suka ga mutum a tsaye daga gefe a kofa, shi bai ƙarasa shiga ba, kuma bai fita ba. Yana dai tsaye kamar an dasa shi. 


Jin muryarta ya sa shi juyowa gaba daya. Zaid ta gani, shi ma kuma ita ya fara kallo har da sauke wani ajiyar zuciya kafin kuma ya gaida Umma.


Umma ta gane shi, Haulatun ma ba gane shin kaɗai ba, har da tuno labarin dalilinsa na rashin shiga ɓangaren Hajja wanda ta samu daga bakin Safina sai da ta yi, Umma kuwa a ɓangaren Baba Dakta sun haɗu har sau biyu sadda ya je wurin Maama. Ita din ma ta san da tarihin Zaid ba ya shiga wajen Hajja, daga bakin Hajjar. Har sai da ma a lokacin ta ji dama ba ta tambaya ba don Hajja sosai ranta ya yi zafi ta yi ta zagin Zaid har da Mahaifiyarsa don a cewarta har da nata laifin. 


Haulatu dai shigewa ciki ta yi ta bar shi da Umma, kai tsaye sama ta nufa don ta je ta fesawa Hajja baƙonta na ranar. Umma ce ta ja shi zuwa falon suka zauna aka ƙara gaisawa duk sai wani ɗar-ɗari yake. 


***

 Hajja na zaune tare da Baba Saude suna kallon ƙasar Saudia su na hira, sai ganin Haulatu suka yi kamar wacce aka jefo. 


"Ke Haule, lafiya? Wa ya biyo ki?" Faɗin Hajja a ɗan birkice. 


"Uhum, Hajja wai kinsan waye baƙonki yau? Tab! Wallahi Yaya Zaidun gidan Malama ne su na falon ƙasa ma shi da Um.."


Ba ta kai aya ba sai ga sallamar Umma sun shigo Zaid din na bayanta. Hajja ta miƙe tsaye ranta a ɓaci. 


"Zaidu? Idonka kenan a ɗakina? Yau kuma wace gulmar ce ta kawo ka? Ai na ɗauka bakar zuciyarka irin ta arnan farko ne. Na ce maka uban me ka zo yi min? Ko har soyayyar da ta hanaka kallon jikata ya ƙare?" 


Zaid ya ji tsaf zai iya shanyewa, duk domin Haulatun da ya samu damar gani. Zuciyarsa ta yi sanyi. Ya na jin ya shirya durƙusawa gaban Hajja ya ba ta haƙuri. Ɓacin ran Mahaifiyarsa a kansa da ma kuma kaunar Haulatun da yake jin tamkar ba zai iya gudanar da rayuwarsa ba tare da ita ba ya sanya shi ƙarasawa ya ɗan russuna gaban Hajja. 


"Ki yi hakuri. Ki yafe min."


Kalaman da suka fito daga bakinsa kenan, Hajja ta yi shiru sai huci take, ita kuwa Umma ta saka baki wurin ƙara ba Hajjar haƙuri gami da nunamata tunda har ya gane kurensa toh ta haƙura. Maimakon Hajja ta saduda sai ta fusata.


"Zaidu, ka tashi tun kafin raina ya fi haka ɓaci ka fitarmin daga gida tunda ka mance matsayina a wurin Mahaifin Uwarka, gaabar da ka ɗauka da ni, za ka iya yin ta da Kakanka Alhaji. Toh dakyau, ni Asma'u za ka sha mamakina Zaidu. Ka tashi tun kafin na cusa maka ashariya "


Umma ta kula dagasken ran Hajjar a ɓace yake, kusan ma kamar ta fi Haulatu zafin zuciya. Sai ta kama hannun Zaid  ba musu ya miƙe suka sauka yana riƙe da ledar saƙon wurin Malama.  Ita kuwa Haulatu sai ta ji ya ɗan ba ta tausayi duk kuwa da a farko ta ji zafinsa sosai na labarin abin da ya faru da ta ji. Amma yanda Hajjar ta rufe idanu har ya durƙusa ta ki kallonsa sai ta ji babu dadi. 


"Kai Hajja, gaskiya kin dauki zafi da yawa."


"Ni sa'arki ce? Maza wuce ki bani wuri!"


Haulatu ba shiri ta yi dakinsu, ta yarda dagaske ran Hajja ya ɓaci, ba ta taɓa yi mata kallon banza ba tun zuwansu sai a yau da har ta haɗa tsawa. Ta bar Baba Saude da fadin a yi hakuri, ita kuwa Hajja sai bambamin faɗa take yi wai don me Umma za ta bi shi. 


A falon ƙasa kuwa, Umma haƙuri da nasiha mai ratsa jiki ta yi wa Zaid. Ta kara nunamasa muhimmanci zuri'a a duniya, da kuma yanda ta ci wuya a baya a dalilin rasa su da ta yi. Jikinsa dai ya kara sanyi. Ya ce ta taya shi ƙara ba Hajja haƙuri. Daga haka kuma ya miƙa mata ledar da Malama ta aiko shi da ita a ba Haulatu. Ta karba ta yi godiya suka rabu. Ya na ta kallon benen ko za ta sauko amma ko ƙyallinta bai gani ba, haka ya haƙura ya fice. 


***

 Ranar Sallah...

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 27

"Ki yi haƙuri." Kalmar da Haulatu ta iya furta mata kenan, ta ma rasa ta ya za ta rarrashe ta. Zaituna ta jinjina mata kai kafin ta share hawayen fuskarta, abin ka da farar fata tuni fuskarnan ta yi jazur ga idanun ma sun ɗan sauya kala. 


"A duniya idan akwai wanda na so kuma nake so har gobe, bai wuce Zaid ba. Na kaunace shi tun ban san ma me nake yi ba. Kaf a ƴan uwan Mamina babu wanda na shaƙu da shi kamar shi a zamana a hannun Hajja, don a nan na soma karatun secondary. Allah ya yi ni da son zaman Nijeriya, duk ƙin Abeena da haka, saboda son da yake min ya haƙura ya bar ni wajen Hajja. Muna chatting sosai da Zaid koda ba ya kusa, hakanan idan ya zo babban gida muke hira sosai, zai ɗauke ni mu je wurare masu kyau mu sha ice cream da sauransu. Wautar da na yi, ina yiwa hakan kallon so, ashe ƙuruciya da hauka su ke faɗamin ƙarya. Hum, Zaid bai taɓa sona ba, ban fahimci hakan ba sai da na kasa haƙuri na furta masa. Ya fututtuke ya sauyamin jin da ya yi na furta da bakina ina kaunarsa kuma da aure. Ya tabbatarmin shi ba ya kallona da hakan face ƙanwarsa wacce ya ke ji da ita. Ke tun fa daga lokacin ya sauyamin. Ban iya soyayya ba Haulat, haka na yi ta bibiyarsa da kuka da roƙo, na kwanta ciwo. Sanadin wannan ciwon ya sa kowa ya gane halin da nake ciki don har suma na dinga yi. Hajja da kuka wiwi ta ce ita fa kawai a daura auren koda Zaid bai amince ba. Shi kuma a gaban su Baba Alhaji da su Baba Dakta, Zaid ya rantse ba zai aure ni don bai taɓa sona ba kuma shi ba ya kaunar ma auren zumunci sannan har abada ba zai yi shi ba.  Sannan fa ina dab da zana jarrabawar fit daga sakandire amma komai ya ficemin a rai. 

  Anan ne Hajja ta zo wuya, ita ma tace duk wanda ya ƙara roƙon Zaid ya aure ni Allah ya isa ba ta yafe ba. Haka suka yi baram-baram da Zaid da Hajja. Tun daga nan jikina ya yi sanyi, na gane dagaske Zaid ba ya sona kuma kamar yanda ya furta har abada ba zai aure ni ba ya sanya ni haɗiyar maganin ɓera amma Allah ya so ni da rahmarSa ban mutu a wannan yanayin ba. Bayan na farfaɗo   su Baba Alhaji  suka dage akan lallai sai Zaid ya aure ni, anan kuma na nuna musu na fasa aurensa, na roƙe su akan su janye ƙudurinsu na cewar sai sun auramin shi. Na tabbatar musu muddin aka yiwa Zaid dole akan aurena to na rantse zan kashe kaina kowa ya huta. Nace a zuri'ar ba a taɓa yiwa wani auren dole ba, to kar saboda ni a fara, ƙarshe ma na ce musu ni na daina sonsa. Haka na tayar musu da hankali kan cewa ni  Malaysia zan koma. Na kira Mamina na labarta mata komai ina kuka sannan nace kar ta faɗawa Abeena, ita ma ta ce me ya kai ta?  Saninsa da muka yi da zuciya da ɗaukar zafi, zai iya cewa ba zan ƙara zuwa Nijeriya ba. Yana mataƙur son yaransa, ba ya kaunar duk abin da zai taɓa mu, akan mu sun sha samun saɓani da Maninmu. Duk da dai na sha tambaya da tuhuma akan rama ta da kuma dalilin da yasa ban tsaya na rubuta jarrabawa ba. Dakyar aka kashe maganar ya aminta da cewa rashin lafiya ce ta hana ni. Hajja ita ma hankalinta ya fi kwanciya da komawata Malaysia don sosai ta kai wuya da Zaid, ta kuma rantse ta kuma muddin tana numfashi wataran sai ta rama abin da ya yi min kuma ya yi mata. Sannan ni kuma ko zan mutu ba za ta bari ya aure ni ba ko mai runtsi. Hum, Haulat ba zan iya misalta maki halin da na shiga ba sadda na ci karo da IV na bikin Zaid da Jalilah, anan cutar sonsa ya dawomin sabo. Ina ƙaunarsa fiye da tsammanin ni kaina Haulat, da wata ce kallonsa ba za ta ƙara yi ba bayan cin fuskar da ya yi mata da wulaƙanci, amma har gobe yana raina, na kasa fidda shi. Ganin da na yi mishi yanzu ya ƙara tayar da tsumin sonsa. Na kasa bayar da dama ga masu sona su fito neman aurena, asalima na cewa Abee sai na kammala karatu, da wannan na samu ya goyamin baya. Yanzu haka ina aji na biyu a jami'a a can, ina karantar pentadbir perniagaan."


Haulatu ta yamutse fuska har ta sa Zaituna yin dariya. 


"Sorry, ina nufin Business Admin."


Ita ma Haulatu ta murmusa. Zuciyarta cike da tausayin Zaituna da kuma jin babu daɗi game da halayyar maza waɗanda take yiwa mafi yawa kallon masu son kai da zalunci. Domin a baya dukkansu abu ɗaya ta ɗauke su, mugaye. A hankali yanzu da ta fahimci rayuwa ta kuma gane yanayin zamantakewar wasu ma'auratan musamman a babban gida yasa ta ɗan sassauta, uwa uba ilimin addini da ya soma ratsa ta da kuma tarihin zamantakewar Annabawa da Sahabbai da matayensu a yasa ta gane jahilan cikin al'umma ko masu son kansu su ne da hali irin na azzalumai. 


"Don Allah yar uwa ki ƙara watsar da lamarinsa. Kar ki ƙara kuskuren shan guba akan wanda bai san darajarki ba. Ki na da qualities ɗin da kowane ɗa namiji zai kaunace ki dominsa. Ni na tabbata ba ke ce da asara ba, shi ne ya rasa mace. In sha Allahu za ku samu wanda ya fi shi."


Zaituna ta jinjina kai tana murmushinta wanda har gefen kumatunta na lotsawa. Sannan ta miƙe tana amsawa da In sha Allah. Daga haka suka bar wurin. 


A ɓangaren Zaid kuwa, ganin Zaituna ya sa shi fasa shiga ɓangaren Hajja, suna barin wurin ya juya ya shiga motarsa ya bar gidan zuciyarsa a cunkushe. Babu abin da yake ƙara tunanowa sai yanda abubuwa suka kacame a baya, yana da yaƙinin za'a yi masa dariya idan ya furta ga wani a gidan cewa yana kaunar Haulatu jikar Hajja. Zuciyarsa ta raya masa akan kawai ya nemi kaunarta, matuƙar tana sonsa to fa babu abin da zai hana aurensu. Balle ma yana ji babu wata ɗiya macen da za ta kalle shi ta ji ba ta sonsa. Ya san wannan ƙarya ne. Da wannan ya yanke cewa zai soma hira da Haulatun ta chat har ya samu ya shawo kanta ta so shi. Abu ne mai sauƙi a cewarsa.


***

Kano...


Mommy ta ruɗe yayinda hannuwanta suka shiga rawa tana mai zaro idanu lokaci guda ta dubi takardun da Ɗan Mutuwa ya sanya a hannunta sannan ta dube shi. 


"Dagaske kake Alhaji? Gida fa? Gida suntum ka siyamin a gadon ƙaya? Allahu Akbar."


Ya yi ƴar dariya yana ɗan sunna kai kamar surukin gaske. 


"Haba Mommy, ai wannan ba komai ba ne daga abin da na ci burin yi maki a rayuwa ke da Hindatu. Dagaske nake sonta kuma a ƙarshen satin nan zan turo idan kin min izni. Zan rungumi Hindatu da hannu bibbiyu ko don maraicinta."


Washe baki Mommy ta ke yi, sam ta kasa rufe baki, nan ta shiga zuba ruwan addu'a da godiya. A ranta tana ƙara jinjinawa Bokanta, dama ya ce mata babu wani abu da zai hana auren Alhaji Ibrahim da ɗiyarta. Kuma za su samu arziƙi fiye da tsammani. Aikuwa gashinan kafin ma ta kai ga batun turowar shi ya zo da maganar. Ɗan Mutuwa ya yi mata sallama bayan ya dire mata rafar dubu har guda biyu, ai Mommy ji ta yi kamar ta sume a nan don dadi. Ya kuma ce su shirya a gobe direba zai zo ya kai su ganin sabon gidan kafin su yi shirin tarewa. Ya ce ba shi da matsala ko a goben ma suka ga za su tare. Haka ya tafi ya bar Mommy cike da sumbatu. 


Hindatu dake gefe ta kasa furta komai tsabar razana, wannan kyauta anya ba ta yi yawa ba? Sai da Mommy ta kai mata bugu a cinya gami da mata nuni akan ta tashi ta yi mishi rakiya kafin ta iya miƙewa jiki a sanyaye. Har ga Allah yanzu tana jin son Alhaji Ibrahim don ta kula ya iya tattalin mace amma kuma tana tsoron wannan hidimar da yake yi musu. 


A zauren gidan suka haɗu da mijin ɗaya a cikin mata biyu dake haya a gidan, kamar ya yi me tsabar girmama Alhaji Ibrahim yana washe baki, ita dai Hindatu kallonsa take yi, ta san dalilin bai wuce saboda kyautar bajintar da ya yi musu ba kwanaki ƴan gidan ya gwangwaje kowane magidanci a cikinsu da kayan abinci. Alhaji Ibrahim kuwa ya amsa har da yi mishi kyautar dubu goma nan take. Ya karɓa ya na ta bin sa da addu'ar Allah ya ba shi Hajiya Hindatu. Don yanzu kaf ƴan gidan Hajiya suke kiranta. Ita dai jin su take yi. 


Koda suka yi sallama ya tafi, ciki ta koma tana danna wayarta ganin Haulatu ba ta biyo bayan kiran da ta yi mata sai ta yi zaton ko wani abun ne ya hana ta. Mommy sai sumbatu take har da rawa, kasa bacci ma ta yi kwata-kwata a wannan ranar. Daga Hindatu ta fara bacci sai ta ji uwar ta taɓo ta wai ta tashi su soma haɗa tarkacensu wuri guda ita a goben ma zasu iya tarewa a cewar Mommyn. 


***

Katsina...


Ana saura kwana uku bikin Raudha da Batulu ne Haulatu ta ciro sakamakon jarrabawarta na Waec a Cafe. Tun sadda ya shigo hannunta bakin nan ya ƙi rufuwa, babu wanda ba ta nunawa ba a saman Hajja. Ƙarshe kuma da rawar jiki ta wuce ɓangaren Baba Alhaji, duk da Umma ta ce ta bari sai bayan bikin sakamakon cikar da aka yi a gidan, baƙi daga Malumfashi har ma da mutanen Kano da Kaduna da dai sauran ƴan uwa na nesa duka sun zo amma ina, rawar jikin da ta ke yi kawai don ta nunawa Baba Alhaji wanda ya yi nata alƙawarin shiga jami'a muddin ta fito da sakamako mai kyau. Ba ta damu da jama'ar dake falon ba ta dai gaishe su a tsaitsaye sannan ta nufi ɓangaren Baba Alhaji. Da sallama ta shiga, ya amsa mata ba tare da ta kula da wadanda ke zaune a tare da shi ba tsabar murna baki ya ƙi rufuwa ta durƙusa gabansa ta miƙa masa result dinta. 

  

"Baba Alhaji, ga result ɗina ya fito na Waec, kuma na ci Maths da English har da sauran topics na Arts dama ka ce idan na fito da sakamako mai kyau to zan tafi jami'a ko?"


Ya karɓa yana ƴar dariyar farin ciki irin nasu na manya. 


"Masha Allah, Alhamdulillah. Sadauki maza karɓa ka karantomin idanun nawa ba ƙwari sai da gilashi."


Jin sunan da ya ambata ne ya sa ta saurin kallon gefen da yake miƙa takardar. Caraf suka haɗa idanu, yana sanye da riga baƙa da dogon wandon jeans. A gefensa kuwa wata fuska ce da ba ta san ta ba. Amma dai bai kai shekarun Sadaukin ba, kusan ma bai fi sa'an su Najeeb da Haidar ba ƴan ashirin da huɗu zuwa biyar. 


Ta yi gyaran murya ta gaida shi. Ya amsa yana duban takardar. Ita kuwa ta kasa kunne ta ji ko zai yaba da ƙoƙarin da ta yi. 


"Ta yi koƙari, amma a yanzu ba a gane ƙoƙarin mutum sai ya soma zuwa jami'a. Mafi akasari makarantun secondary, ana rubuce musu jarrabawar ne a allo. Hakane?"


Ya ƙarashe da duban Haulatu. Ta ji kunya ta kama ta karon farko, gaskiya ya fadi dama kam rubucewa aka yi ta kwafa duk da ta san da yawa cikin tambayoyin da aka yi musu. Ta ɗan turo baki kaɗan tana kallon Baba Alhaji.


"To ai ina da ƙoƙari kuma na san yawancin abin da aka tambaya."


Ya taɓe baki gami da ɗaga kafaɗa.


"Amma ba ƙarya na faɗi ba ko?"


Baba Alhaji ya yi dariya ganin yanda Haulatu ta yi narai-narai za ta yi kuka. Duk wannan murnar da ta shigo da ita ya gushe.


"Sadauki, ka rabu da Amaryata ka ga ka sanya min ita kuka ko? Yanzu dai tunda abin haka ne ma, na ɗora maka ragamar nema mata admission."


Wani ɗan murmushi Sadauki ya yi kafin ya shafi sumar kai ya dubi Haulatu da ita din ma ta kalle shi don jin me zai ce wannan karon. 


"Ta yi Jamb ɗin ne? Sannan result din ya yi kyau?"


Haulatu ta ji ta tunzura kamar ta kai masa bugu don haushin rainin hankalin da ya ke mata. Ita kuwa ta yi Jamb, ba ta mancewa daƙyar ma Umma ta bari ta yi don a cewarta gwara ta yi aure a lokacin ta fita daga ƙangin rayuwar da suke ciki na gidan.  Daƙyar ta yarda ta biyamata kuma sakamakon ya yi kyau ba laifi ta fito da maki har 177. 


"Ah ta yi mana. Har nan ta zo ta nunamin. Ni nawa ma ki ka samu?" Faɗin Baba Alhaji. 


Ta yi shiru don ta cika ta yi fam. 


"Ba amsa?"


Ta ɗan dube shi, ya ɗan lumshe idanu ya buɗe yana mata murmushin da ya ƙara masa kyau. 


"One sebin sebin."


Ta ba da amsa bayan ta kauda kai, aikuwa sai ga Sadauki na dariyar sebin sebin, wanda ke zaune a gefensa na taya shi. Ran Haulatu ya ɓaci ƙwarai, ta ma ture mamakin ganin Sadaukin na dariya sai na haushin dalilin da yasa suke mata dariyar kawai sai ta miƙe tana hawaye ta fice daga falon. Baba Alhaji na tsaida ta amma ina, tuni ta bar musu wuri.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro

 Page 28

Da sallama ta shiga falon Momi Nuratu, tana jin hayaniyar su Raudha da ƙawayensu a can falon na biyu. Ta iske ta zaune suna hira da Mamin Khaleefa da Amaryar baban Mu'az (kishiyar mommynsa) sai ko wasu daga yan uwa na Malumfashi. Gaishe su ta yi gaba daya suka amsa fuska a sake. Ta ƙarasa ga Momi Nuratu tana tambayar inda Yaya Sadauki yake, ta ƙara da yi mata bayanin results din da  Baba Alhaji ya sa ta kawo mishi. Momi Nuratu ta kira wata yarinya cikin ƴan aikinta ta ce ta kai ta ɓangaren Sadauki. Bayan fitarsu Mamin Khaleefa ta dubi Momi Nuratu. 


"Wannan kamar jikar Hajjar nan ko?" 


Da murmushi ta amsa.


"Haulatu ba, eh ita ce. Ɗiyar Na'imatu."


Da mamaki Mamin Khaleefa ta ce.


"Kai, kinsan Allah da farko ban gane ta ba. Ni rabon da na sanya ta a idanu ai tun kafin azumi. Sai naga ta ƙara girma da gogewa. Eh lallai, wuya kam ba ta daɗi. Ashe yarinya kyakkyawa ce haka masha Allah."


Dariya Momi Nuratu ta yi.


"Ai kam dai."


"Amma shi Sadaukin har sun yi sabo da shi haka? Ko ba shi na ji tana tambaya ba?"


"Kai Mamin Khaleefa, to idan shi ta tambaya ma ina ce ɗan uwanta ne."


Cewar Amarya. Wata kuwa cikin ƴan Malumfashi mai suna Kubra, ta cafe.


"Aa toh, ki ka sani ma ko shaƙuwar ta kai a yi auren gida."


Mamin Khaleefa ta yamutse fuska. Zancen nan sam bai mata daɗi ba, ita da take fatan ɗiyarta Jannat ta samu cikar burinta na auren Sadauki? Yarinya tun tana tatsitsiyarta take fama da son sa? Ai kam dai ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa. Ta dubi fuskar Momi Nuratu, ko alama babu wani sauyi tattare da ita sai ma dariya da ta yi aka shiga wani hirar yayinda aka bae ta da tauna zancen da Kubra ta furzar. 


***

"Ga hi nan. Nan ne ɗakin." Faɗin yarinyar, Haulatu ta amsa da toh sannan ta ƙwankwasa ƙofar gefe guda ƙirjinta na lugude. Ta ji an murɗa ƙofar an buɗe. Ta dube shi, kallonta kawai ya yi ya juya ya shige ciki yana cigaba da amsa wayarsa. Hararar ƙeyarsa ta yi sannan ta bi bayansa tana kallon yanda ƙaramin falon ya tsaru. Babu dai tarkacen a zo a gani kamar ma ba ɗakin namiji ba komai tsaf. Na'urar sanyaya ɗaki nata aikinta, sanyin da tiles ɗin ya ɗauka ya ratsa tafin ƙafarta, gaba ɗaya ma falon ƙamshin turarukan Sadaukin ya ke yi. Za ta zauna a ƙasa ya yi mata nuni da kujera da yatsarsa don har sannan waya yake yana zuba uban turanci. Ta nutsu kuwa tana ji, ta dai tsinci abin da ta tsinta. Ta kuma fahimci da namiji yake wayar kuma yare mai suna Samuel, magana suke yi akan wasu kayayyakinsu da suka yi oda amma ya maƙale a Lagos. Sai bayan ya kammala ne ya yi gyaran murya kaɗan, ta dube shi gami da gaida shi. Ya amsa yana miƙa mata hannu, ba musu ta miƙa masa takardar. Ya karanta ya yi murmushi. 


  "Shi ke nan, kina iya tafiya."


Ta amsa da toh. Har ta kama hanyar fita ta ji ya kira sunanta. 


"Haulat." Sai ta ji kamar ba ta taɓa jin sunanta a bakin wani mahaluƙi ba sai a bakinsa. Ya fita raɗau ga wani daɗi da ya yi a kunnenta, kallonta kawai ya ke, ita ɗin ma sai ta tsinci idanunta cikin nasa ta kasa magana sai kawai ta sunkuyar da kai ta dawo ta ɗan zauna. 


"Gani Yaya." Ta furta kirjinta na bugu ta shiga ambaton sunan Allah, wai ita mene ne haka take ji kwanakin nan? Ta kasa fahimtar komai. 


"Kina da riƙo. Hakane?"


Ta dube shi idanuwa a waje. 


"No ba zaremin idanu na ce ki yi ba. Koda dai, kin riƙe ni saboda na taɓa lafiyar fuskarki. Ina mai ba ki haƙuri akan hakan. Ina haɗawa har na dariyar jamb score ɗinki da na yi. Hope za ki yafemin?"


Ta ji maganar kamar daga sama, wai Yaya Sadauki ne mai neman ta yafe laifukan da ya yi mata? Ba ta san ma ta shagala da kallonsa ba sai da ya ɗan murza yatsunsa biyu na farko da na tsakiya a gefen fuskarta wanda ya yi sanadin lumshewar idanunta. Ta ɗan girgiza kai.


"Ni na mance ma an yi haka. Ya wuce."


Kamar ya ƙara magana sai kuma ya fasa. 


"Kina iya tafiya."


Ai kafin ma ya rufe baki ta miƙe don dama ta gama matsuwa da hakan. Abu ne da ba ta saba ba, kaɗaicewa da namiji ko waye shi. Ballantana kuma Yaya Sadaukin da ba su ko saba wani gaisawa sosai ba. Tana fita ta shaƙi iskar ƴanci, dagaske fa tana ɗan shakkarsa ita ma, kawai dai ta fi su Safina dakiya ne. Tana tafe tana tunano haƙurin da ya ba ta da ma murmushin da ya yi mata, sai ta tsinci kanta da murmusawar ita ma. Wayarta ta yi ƙarar shigowar sako amma ba ta duba ba, sam ba ta bi ta ƙofar falon Momi Nuratu ba sai ta fita ta ƙofar dake a ɓangaren Yaya Sadaukin. 


Ba ta ankara ba ta ji an ɗan jawo gefen hijabinta, ta juya don duk a zatonta ma Radiya ce, ita ke yawan yi mata wannan wasan idan ta gan ta a hanya. 


"Radiya bana.." Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta ganin fuskar Jannat da ta tsaya ta riƙe ƙugunta da bai gama cika ba tana dubanta rai a haɗe. 


"Lafiya?" Ta furta bayan ta gyara tsayuwarta. Wata harara Jannat ta bi ta da shi kafin ta nuna ta da yatsa. 


"Kin yi kaɗan, kin yi tsaroro ke ko a bariki aka haifi uwar babanki, ba ki isa kuma ba ki kai girma da ƙimar da za ki iya raba ni da Yaya Sadauki. Abeed nawa ne, kuma ni Jannat tasa ce. Wallahi ki ka kuskura na ƙara ganinki da shi sai na maki abin da har duniya ta naɗe ba za ki mance da fuskata ba."


Tun a farko kalmarnan ta bariki ta sosa ran Haulatu, ta danne dai kawai ta kuma jure don ta ji inda zancen ya nufa. Koda ta ji ƙarashen ba ta san sadda ta yi dariya ba. 


"A banza, wanda ki ke yi dominsa bai san da zamanki ba. Ina mace take ma a nan da har Yaya Sadauki zai kalla ta burge shi? Ai ba uwar ubana ce bariki ba, ni ma barikin kaina ce,  da ace Yaya Sadauki saurayina ne, na rantse maki ko inuwarki ba ta ishe shi kallo ba don ni da ace ina da ra'ayin wani shirme na soyayya, ai ba ki kai na haɗa saurayi da ke ba. Ina ƙirar take? Abu kamar kyandir."


Daga haka Haulatu ta juya a fusace za ta bar wurin idanunta duk dauriyarta tuni sun soma fitar da hawaye ba don komai ba sai na takaicin kalmar da har yau da ta samu ƴancin kai ba'a bar danganta su da shi ba. Wato Bariki. Sai dai ba ta kai ko ƙofar ƙyauren da za ta yi sallama da gidan Abba Ridwan ba, ta ji Jannat ta yi mata wani wawan fisga gami da kokarin kai mata mari aikuwa a zafafe ta riƙe hannun ta hankaɗa ta baya da ƙarfi ta kuwa zube a ƙasa, daidai nan ƙawayenta suka yo kanta tuni Haulatu ta fice. 


Haka ta faɗa falon da su Umma ke zaune fuskarnan jage-jage da ruwan hawaye, ko sallama ba ta yi musu ba ta nufi hanyar bene. 


"Ke Haule, zo nan." Muryar Hajja ya tsaida ta, duk yanda ta so ta haye amma ta kasa sai ta dawo jikinta har wani rawa ya ke yi don ɓacin rai, ga wani kuka irin na zuci, babu sauti sai sauke numfashi da sauri sai ko ruwan hawaye.


Hajiya Hadiza na gefe tana sallah amma gaba ɗaya idanunta yana kansu, babu ma nutsuwa a sallar. Ita kuwa Umma da ta idar, kallon Haulatun kawai ta yi ta maida kai ga addu'arta. Maman Zaituna wacce ta fito daga banɗaki ta yi alwala ta ƙarasa ga Haulatun ta ɗago ta daga durƙuson da ta yi gaban Hajja tana kuka babu amsa ɗaya da ta iya ba Hajjar dangane da abin da ya faru. 


"Lafiya? Meke faruwa? Yanzun nan fa ta fita da walwalarta."


"Ina na fahimci wannan lamarin ke kam, kuma kin ga ta ƙi cewa komai. Daga ina take ma?"


"Assalamu alaikum warahmatullah...wajen Sadauki ta je, ke me ya faru a can din?"


Wannan magana ta fito daga bakin Haj Hadiza don dama tana ta zuci-zucin ta idar ta amshe. Sai ga Fahima ta shigo falon kamar an wurgo ta. 


"Ke Haulatu, ki zo inji Momi Nuratu."


Fuska ba walwala Maman Zaituna ta ce.


"Fahima meyafaru ne?"


Taɓe baki ta yi.


"Wai fa dukan Anti Jannat ta yi har ta tunkuɗe ta ta faɗi saman dutse ta fasa goshi. Kuma akan duka su biyun suna son Yaya Sadauki."


Baki sake Haulatu ke duban Fahima wacce ta kantaro wannan uban sharrin ta jefe ta da shi. Umma dai kanta na ƙasa tana tasbihi ba ta ko ɗago ba tun bayan kallon da ta bi Haulatun da shi na farko. Ita kuwa Haj Hadiza hararar Fahimar ta yi, a ranta tana kiranta da banza gaɓuwa marar wayo, tana gefe tana mata yaƙi na samun shiga wurin Sadaukin amma ita kuma kamar ma ko a jikinta taya ƴar uwarta kishin Haulatu take yi. 


"Haka aka yi Haulatu?" 


Ba ta kai ga cewa wani abu ba sai ga muryar Momin Khaleefa ta shigo a fusace. 


"Ina take? Ina marar kunyar yarinyarnan ta ke? Wato don ta cika fitsararra ta kama min ɗiya da bugu har ta ji mata ciwo akan ɗa namiji ko? Wannan mugunta har ina? To mu kam kaf zuri'arnan ba mu taɓa ji ko ganin abu makamancin wannan ba."


Magana ta ke yi murya a sama, ga tawagar da suka biyo ta a baya ganin yanda za ta kaya sai ko na falon sama su Anti Ihsan da tsararrakinta na gidan. 


"Haba Hajiya Rahama, me ya kai na waɗannan zantukan marasa tushe? Ina laifin ma ki tsaya ki ji meyafaru. Sannan duk munin abin ai bai kyautu  ki munana kalamai ga Haulatu ba."


Cewar Maman Zaituna cikin ɓacin rai.  


"Bar ta Nafisatu, ƙyaleta ta gama. Rahama ko? Daidai nake da ita, bar ta ta cigaba da fitsarar da ta zo yi don an taɓa ɗiyarta."


Shaf Momin Khaleefa idanunta ma sun rufe ba ta ko kula da Hajja ba sai a yanzun da ta ji muryarta. Kawai sai ta juya ta fice daga falon tana sababi. Hajja kuwa tuni ta fusata ta hau faɗa wai don an taɓa Jannat shi ne ita mai ƴa ta zo. Faɗi ta ke. 


"Toh yau idan soyayya shi Sadaukin ke yi da Haulatun zan ga uban da ya isa ya hana aurensu yiwuwa. Aikin banza kawai. Ni Rahama har ta kai girman da za ta shigomin wuri ta yimin tsaye a ka tana rashe-rashen kunyarta? Da ni take zancen. Idan ita ban isa da ita ba ai shi Daudan (Dawud, mahaifin Khaleefa) daidai nake da shi. Mahaukaciya kawai."


Haka Hajja ta yi ta sababinta ana rarrashinta, ita kuwa Maman Zaituna sai ta ja hannun Haulatu suka nufi sama. Anan ne ta ji duk abin da ya wakana tsakaninsu har irin amsar da ta ba Jannat, ba ta ɓoyemata ko harafi guda ba. Ta ƙara da faɗin. 


"Don me ba za'a bar jingina ni da mahaifiyata ba da kalmar bariki. Mu ne muka yi barikin ko kuwa? A cikinmu babu ɗan bariki, don an ga kana shiru shikenan sai kowa ya kwasa bolarsa ya watsamana?"


Maman Zaituna ta rungume ta tana rarrashi cike da tausayawa kafin ta ɗago ta.


"Ya isa haka my dota, yi shiru abinki. Komai zai wuce. Abu ɗaya nake so na sani, dagaske ku na soyayya da Abeed?"


Girgiza kai Haulatu ta yi tana ɗan lumshe idanu hawayenta na zuba. Babu abin da ke yawo a ƙwayar idanun face kyakkyawar fuskarsa a sadda ya ke mata murmushi da kuma tausassan muryarsa sadda ya furta mata kalmar ban haƙuri. 


"Aa, babu komai tsakanina da shi."


"Kin tabbata?" 


Ta amsa da eh tana gyaɗa kai. Maman Zaituna ta sauke ajiyar zuciya. 


"To Alhamdulillah, na yi murna da jin hakan ƙwarai. Koda ma ace ku na soyayyar ne, Abeed yaron kirki ne ba zan ji rashin daɗi na alaƙarku ba. Kuma na tabbata za ki yi farin ciki da shi daidai gwargwado in sha Allahu. Sai dai ni yanzu na fi ƙaunar ɗiyata ta yi karatu ta san ƴancin kanta. Ba ƴanci na bijirewa fadin Allah da Manzonsa (s.a.w) ba, a'a, a karon kanki ki san da cewa ke ma kina da wani matsayi da martaba a rayuwarki, Allah da kansa ya girmamaki matsayinki na ɗiya mace. Wasu abubuwan da suka faru a rayuwarki duka har da rashin ilimi. Koda ace ba a hannuna za ki yi karatu ba kamar yanda nake kwaɗayi, to ko anan ɗin ma ki maida hankalinki kin ji ko? Nasan ba za ki ba ni kunya ba."


Suka yi wa juna murmushi. Umma ce ta shigo ɗakin don hayaniyar ƙasan ya ishe ta, anan Maman Zaituna ta labarta mata yanda komai ya faru ita dai Umma murmushi kawai ta ɗan yi. Ta ce Allah ya kyauta daga nan ba ta ce uffan ba ta shiga banɗaki, ita kaɗai ta san ciwon da ƙirjinta ke yi ga kuma kanta dake sarawa. Taron sai ya ƙara haifar da gutsuri tsoma akanta da ɗiyarta. 


***

  Sadauki ba shi da labarin komai don bayan fitar Haulatun shi ma ta ƙofar baya ya bi ya fice daga gidan. Masallaci ya nufa koda aka idar da sallah sai bai dawo ciki ba suka zauna a nan ƙofar gidan suna hira da Khaleefa da wani abokin Khaleefan da ya tarar da su a tsaye. Wayarsa kuma tana silent don haka al'adarsa take muddin zai shiga masallaci to fa ba ya barin ko vibration ne ballantana ringing. Wannan ya saka har wayewar gari bai samu labarin abin da ake ciki a gidan ba. Sadda ta koma ɗakinsa ya tarar da missedcalls din Momi Nuratu da ma na Mamin Khaleefa dare ya yi. 


 Washegari da safe kuwa, Momi Nuratu sam ba ta ce masa komai ba don ita haka Allah ya yi zuciyarta, ba ta iya kwana da abu a rai ba. Sai ma da ya ce mata ya ga kiranta kuma dare ya riga ya yi sannan ta tuna dalilin kiran. An tashi da shirye-shiryen kamu yasa kawai ta ce mishi babu komai ya je za'a kawo masa abin kari. 


 Sadauki dai bai ji komai ba sai a bakin Mu'az da suka haɗu a hanyar zuwa ɓangaren Alhaji. Mamaki sosai ya yi.


"Shi wannan hayaniyar duka dai a kaina a ka yi shi?"


Mu'az ya taɓe baki. Babu abin da ya ɗan sosa ransa sai na zargin soyayyar da aka ce Sadaukin na yi da Haulatu. 


"Haka dai abin ya kasance. A iyaka sanina kuma babu komai tsakaninka da ita. Hakane?"


Sadauki bai ba shi amsa ba face cigaba da tafiyarsa da ya yi fuskarsa ba yabo ba fallasa. Nan ma wurin Maama ya ji ƙarin bayani tiryan-tiryan na yanda Jannat ta danganta Haulatu da bariki. Sai ya ji zuciyarsa ta ƙara zafafa. 


"My son, dagaske ne kana sonta?"


Tambayar Maama ya sa shi ɗago idanunsa da suka kaɗa don ɓacin rai ya dube ta.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: Fitar tsiro 

 Page 29

"Ka yi shiru." Maama ta ƙara furtawa tana dubansa a nutse. Ya kauda kai daga duban Maama kafin ya ce.


"Maama karatunta fa?"


Murmushi ta ɗan yi.


"Tambayar da na yi mala, ka na sonta?"


Ya ɗan ciji leɓɓansa na ƙasa kaɗan kafin ya soma magana a tausashe.


"Duk son da zan yi mata, ina kaunar ta nemi ilimi. Wannan ne dalilin da yasa na fi buƙatar na nemi yardarta yanda mu'amalarmu zai zama ba wani ne ya yi mata dole a kaina ba. Ba na mata so irin na ko ta mutu ko ta yi rai lallai sai ta zauna da ni. Na fi muradin ta ƙaunace ni domin kanta ba wani ya tilasta mata ba. A taƙaice dai, ina sonta Maama."


Ya ƙarashe yana mai ɗan sunkuyar da kai. Maama tun da ya fara aman abin da ke binne a zuciyarsa murmushi kawai ta ke yi tana kallonsa. Koda ya kai aya sai ta furta hamdala a fili. Ta ƙara da faɗin. 


 "Na jima ina maka kwaɗayin auren Haulatu. A yanzun da na ji hanzarinka da ya sa ka zaɓi jan bakinka ka yi shiru, sai na ƙara jin kwaɗayin lamarin. To Allah ya shige mana gaba, ya sa rabonka ce ta alheri."


Sadauki ya yi murmushi yana mai motsa leɓɓansa da furucin amin. Daga nan suka yi sallama. Maama ta miƙe ta fito waje zuciyarta cike da walwala, haƙiƙa ta ji daɗi kwarai na amsar Sadauki tana kuma fatan alheri gare su. 


Sadauki kuwa can wajen Baba Alhaji suka haɗu da Mu'az don dama sun rabu ne akan zai je ya yi magana da Maama. 


***

 Gidan gaba ɗaya ana ta shirin fita kamu da yini a babban ɗakin taron biki da aka kama mai suna Paramount Event Centre. Haulatu gaba ɗaya ta sake don Maman Zaituna sam ba ta yarda ta bar ta hakanan ba walwala ba, tun a jiya take nan nan da ita ga ita kanta Zaitunar da kuam su Safina waɗanda ke nunamata ta watsar da lamarin Jannat. 


 Shiri sosai kowa ke yi, ankon sisters daban domin iyaye fasa ankon aka yi kowa ya saka na shi. Hakanan na ƙawayen Amare ya fita daban. Sai dai kowa ya fi ganin kyawun na sisters ɗin, atamfa ce mai adon ja da ruwan madara. 

  Ɗinkin Haulatu da su Safina iri guda ne, riga doguwa mai ado a wuya da hannuwa sai kuwa daga can ƙasa. Ta dubi kanta a madubi, ita kanta ta san ta yi kyau ga makeup da Zaituna ta yi mata a fuska don sosai ta iya kwalliya. Sai dai ba sana'a ta ɗauke shi ba don a yanda ta nunawa Haulatun ma, sanadin Zaid ta koya tun tana Katsina da ta ji ya taɓa cewa shi ire-iren kwalliyar na burge shi. Haulatu ta jinjina abin a rai, zuwa lokacin ta rage mamakin irin son da Zaituna ke yiwa mutumin da a ganinta sam bai cancanta ba. Ita kanta Zaitunar ta yi kyau ainun, riga da siket ta yi na ƙawaye don ta rantse ita cikin ƙawaye take tunda dai Batulu ƙanwar Mu'az ƙawarta ce sosai. Ta su atamfar ruwan madara ce da baƙi. Amma sai kushewa take yi tana cewa ita da ace ma ta san tun farko na Sisters aka siyamata. Ta ci alwashin kafin Allah ya ƙaddara komawarta Malaysia sai ta siya don ta burge ta. 


"TubarakAllah Masha Allah."


Ta faɗi tana ƙara duban Haulatu bayan ta gama yi mata ɗaurin kallabi. Ita kuwa ta hau farr da idanu tana ɗan jujjuyawa suka yi dariya. Mayafin ma kalar ja, a kafaɗa aka ɗan naɗe shi aka ɗora. Ƙaramar purse ɗinta ja hakanan takalmin. Duka iri ɗaya da su Safina, su kuwa Maman Safina ce ta siyamusu. 


Tare suka fito daga ɗakin su Zaitunan. Da Matar Uncle Abba suka soma kiciɓus, ita dama kullum fuskarta a tamke haka yanayinta yake, da kallo kawai ta bi su amma babu ko yabawa. Ita ma ta ci nata gayun cikin leshinta kore.  


"Ita dai wannan matar kamar tana shan yis, kullum fuska a kumbure." Faɗin Haulatu da murya ƙasa-ƙasa, suka yi dariya har ta tsargu ta juyo amma ganin ba kallonta suke ba sai ta yi gaba. Baba Saude kuwa har da su guɗa tana yi musu kirari da manyan mata, jikoki ga Hajja. Farin wata masu haskaka duhu. Su dai murmushi suka yi, su Umma tuni sun tsufa a wurin taro, babu kowa a falon sai sa'annin Hajja, su ma sun cakare daidai nasu suna jiran mota. 


"Haule, Zaitun, ku ne kuwa? Ikon Allah, kamar daga wata duniya ku ka ziyarce mu? Irin wannan kyau haka?"


Aka yi dariya, idan ka ɗauke Haulatun da Zaituna masu ɓata ran sunan da Hajja ta yi kiransu da shi. 


Safina da Radiya ne suka shigo, a kusan tare suka ce Wow! Gami da ƙarasawa su ɗan rungumi ƴar uwarsu."Kai kun yi kyau wallahi, shegiya kin ganki kuwa?" 


"Kul! Ke Radiya ki fita idona, ban hanaku sheganta kanku ba?" Cewar Hajja daga zaune don fes ta ji su. Suka yi waje suna ƙunshe dariya, Radiya na kira Sorry Hajja. Don dai yanzun albarkacin Haulatun ba kunya su ma takan ja su da wasa kai ka ce ba Hajjar da suka sani mai zafi da tsauri ba. 


Suna isa farfajiyar gidan inda da yawa sun wuce wasu kuwa na tsaye ana jiran mota, Zaituna dai ta bar su a nan ta wuce tawagar ƙawayen Amarya su Jannat. Haulatu na tambayar to su yanzu wace motar za su biɗa, tambaya take ko dai ta gwada kira musu Yaya Mu'az ya kai su? Amma kallon da ta ga Safinar da Radiya na bin ta da shi ya sa ta dakata da maganar gami da watsa musu harara. 


  "Ban ciki da iskanci. Wannan kallon fa sai ka ce yau ku ka taɓa gani na?"


"Ai ba su ba, ni ma haskakamin fuskata ki ka yi na bar taron waɗancan manyan na yo wajenki." Ta ɗaga idanu ganin Haidar ta kai masa duka da purse dinta, ya kauce yana dariya. 


"Kai! Ai ni da nasan kin fi Bebina kyau da ke na lallaɓa ma ki yarda ki jira na kammala jami'a mu yi aure. To mene don na ba ki shekaru uku kacal a duniya?"


Suka yi dariya idan ka cire Haulatu da ta ja guntun tsaki.


"Yaya Haidar mu dai don Allah mota muke nema." Faɗin Radiya kenan tana marairaice masa. Ya jinjina kai 


"Hum um, an gaisheku kun ji. Ni kaina neman wanda zai kwashe ni nake, idan ban samu ba sai na lallaɓa na ja Lifan ɗina ya kai ni. Amma yanda na ci wanka ai ba girma na hau Lifan."


Haka ya yi ta zuba musu hira, kowa ya zo wucewa sai ya tanka Haulatu kafin a yi jam'u a haɗa su duka ukun a tanka. A hankali fadi suka masha Allah tubarakAllah.


Ya yi daidai da shigowar motar Yaya Sadauki gidan, a bayansa kuma motar Mu'az. 


"Ke Safina ga mutuminki nan Yaya Mu'az, na tafi, ku roƙe shi ya kai ku. Kun san dai shi Boss ko giyar wake ku ka sha, ba zai ɗauki manyanku su Jannat ba ballantana ku karan kaɗa..."


Bai kai ƙarashe ba sakamakon hon ɗin da suka ji da ya ɗauki hankalin jama'ar dake wajen, ƙirjin Jannat hsr ɗan bugu ya yi da ta waiga ta ga motar Sadaukinta ne ake zuba wannan hon ɗin. Sai kuma can shiru ya biyo baya, kowa dai ya zuba idanu ba kamar Jannat da take jin kamar idanunta za su faɗo ƙasa don kallo, jira take ta ga da ya tsaya a filin farfajiyar gidan bai karasa wurin parking ba, wa ya zo ɗauka, shi kuwa Mu'az tuni ya fito ya nufi inda Mominsa ke tsaye tana jiransa da tawagarta. Farko sam ba ita ya yi niyyar ɗauka ba face Haulatu, so yake a yau kafin Sadauki ya riga shi cewa komai, ya kasance shi ya riga isar da saƙon zuciyarsa wanda bai gama tantance shi ba sai a daren jiya da ya gama sauraron ɗan hatsaniyar da aka yi akan Sadaukin. Ya na tsoron ya tabbata Sadauki na son Haulatu. Idan har ya riga shi furtawa to zai iya ji har a zuciya ya haƙura. Amma muddin ya samu yaƙinin cewa babu komai tsakani daga ita Haulatun, anan ne zai bajakolin soyayyarsa a wurinta, har ransa yana ji haƙansa zai cimma ruwa. 


Wayar Haulatu da ta ɗauki kara ta duba. Sunan Yaya Sadauki ta gani ɓaro-ɓaro. Ƙirjinta ya ɗan buga, ta dubi motar kafin ta ɗaga. Bai ba ta damar magana ba ya tari numfashinta.


   "Da ke da sauran aljanun da ku ke tare, ku zo."


Daga haka ya katse kiran. Ta dube su, dama kunnuwansu na ga wayar da take yi, shi ma Haidar ya saki baki da hanci da kunne yana son jin me za ta ce. Ta kama hannun Radiya dake tsaye daga damanta. 


"Yaya Sadauki na kiranmu."


Jin haka suka ruɗe, Safina kira take yi mun shiga uku. Haidar kuwa cewa ya ke yi, ai fa shikenan, bye bye, ku je zan baku labarin yanda ta kaya a gidan bikin. Babu ku babu cin Meena's Bites."


Ko kallonsa basu yi ba don ba wannan nutsuwar suka ɗunguma ga motar Yaya Sadauki wacce gaba ɗayanta tinted glass ne a jiki sai gaban kawai da babu. Suna isa ya bude gidan gaba, ya dubi Haulatu. 


"Get in."


Ba musu ta shiga, su Safina kuwa ya ba su umarnin shigewa baya. Nan ma duk suka zauna ya rufe ya yi ribas da motar ya fice daga gidan. Fuskarsa babu ɗigon fara'a, ga shi nan dai ya sha gayunsa cikin wani tsadaddan yadi baƙi da ya fiddo da hasken fatarsa muraran. Hularsa na ajiye daga saman wurin sitiyari, tuƙi kawai yake yi da hannu ɗaya. 


Fitarsu ya sa Jannat jin zuciyarta kamar za ta buga, ta yi baya sakamakon jirin da ke ɗibarta Allah ya taimaka Zaituna da wata ƙawar Jannat ɗin dake tsaye a baya suka ɗan tare ta. Nan fa wuri kuma aka hau ƙus-ƙus din Yaya Sadauki, wato dai ya yi abin da ba ya daga halayyarsa, ɗaukar ƴan biki. Shi karƙari iyaye, sam ba ya bari ƴanmatan ƙannensa su hau mishi mota. Kowa faɗi yake anya ba son Haulatu yake ba, tunda dai sun san kafin zuwanta ai bai kalli inda su Safinar suke ba kuma banda haka ma ita ce a gidan gaba. Zaituna kuwa ta ji wani sanyi a ranta, tunawa da abin da ya faru jiyan tsakanin ƙanwarta da Jannat ɗin, ko babu komai duniya sun shaida wanda ake so da wanda ke son. 


Mu'az da ke ƙokarin tayar da motarsa bayan matsowar su Mominsa, sai da ya ji wani abu ya daki ƙirjinsa, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci. Me Sadaukin ke nufi? Dagasken wai yana son Haulatu ko kuwa dai ganin damar ɗaukarsu ya yi? 


Babban burinsa Mominsa da ƙawayenta su hau ya bi bayan Sadaukin amma sai ya ga sun tsaya su na maida maganar ko me Sadaukin ya gani a jikin Haulatun da ya soma bin ta kamar jela? 


***

  Shi kuwa can ya furzar da huci, ita ma Haulatu ta ɗan yi ajiyar zuciya, ta juya da nufin satar kallonsa, aka yi katari a sannan shi ma ya ɗan karya wuya kaɗan ya dube ta. Ta yi saurin kauda kanta. Yamutse fuska ya yi.


"Ku yanzu don rashin ta ido sai ku je gidan biki a haka mayafi kamar abin tatar koko kun saƙale shi a kafaɗa ko? To wa za ku burge? Saurayi za ku je nema?"


Suka yi shiru babu wanda ya ce uffan don tsoron maganar ma suke, ita kuwa Haulatu kirjinta ke bugu da ba ta san dalili ba, duk dai a yanzu sadda za ta haɗu da shi wuri guda sai ta ji wannan bugun. A gefe guda ta tuno Jannat da ta yi ido huɗu da ita sadda take ƙokarin shiga gaban motar Yaya Sadauki kawai ba ta san sadda murmushi mai dan sauri ya suɓuce mata ba. Safina da Radiya suka waro idanu, Safina dake zaune daga bayanta ta ɗan ja rigarta ta gefen ƙofa. Nan da nan ta shiga taitayinta, duk suka dube shi jin bai ce komai ba, sai ma murmushin da suka ga ya ɗan yi. 


Har suka ƙarasa wajen bikin bai ƙara magana ba, koda ya yi parking ya dubi Haulatu. 


"Oya, maza ku gyara zaman mayafan idan kuwa ba haka ba yanzu zan juya na maida ku gida."


Ai kan ma ya ƙarasa suka hau gyara. Haulatu duk ta kusan susucewa don har ta kammala bai kauda kai daga kallonta ba. Ya zura hannu a aljihunsa ya fiddo chanji ƴan hamsin hamsin yana fadin. 


"Na sani, ba ku da ko sisi sai efizzy."


Su dai ba su saba ba don haka suka yi shiru, ya miƙawa Haulatu. 


"Ku riƙe."


"Yaya mun gode." Faɗin su Radiya suna fita daga motar, Haulatu ta ji ta wajenta a rufe don haka ta juyo ta dube shi da idanunta masu ƙara tsuma shi yana ɓoye yanayinsa. 


"Ya ƙi buɗuwa." Ya ɗan matse fatar leɓɓansa wuri guda yana mai jinjina kai. 


"Ok. Please ban da rawa da rawar kai. My eyes on you."


Ba ta da nutsuwar fassara zancen kawai ta bishi da toh. Sadda ya bude ta zura ƙafa guda za ta fita ya ce.


"Kin yi kyau."


Sai da ta juyo ta dube shi don ta tabbatar shi ya fadi, kalmar ta tafi da ita sosai don baki da idanu ta ware. Ba ta san sadda ta bishi da irin murmushin da ta ga ya jefa ta da shi ba. Ajiyar zuciya ta sauke, hakanan ta ji ta kamar a cikin ƙanƙara don sanyin jiki da kuma annashuwa. 


"Nagode."


Daga haka ta fice da sauri ta rufe mishi ƙofar, Safina da Radiya burinsu kawai ta fito su shiga yanda za su samu damar gulmar abinda duk ya faru a hanya da ma yanzun. Shi kuwa gyara parking ya yi yana yiwa kansa faɗa, ya kamata ya koyi haƙuri da danne zuciyarsa. Ya bi komai a hankali din. Can kuma ya ɗan wurga hannu ɗaya. 


 "To me na yi ma?" Ya yiwa kansa tambayar a fili. 


Zaid da ke tsaye a farfajiyar wajen tsaf ya kula da abinda ke faruwa, wani irin huci ya shiga furzarwa. Haulatunsa ce a motar mutumin da ba sa ga maciji? Me wai ma hakan ke nufi? Sadaukin sonta yake ko kuwa soyayya suke yi? Ya ji ransa na tuƙuƙi yana mai cin alwashin ko shi ko shi. Ba zai taɓa haƙura da Haulatu ba, su zuba su gani. 


***

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: *Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*


*****************

Fitar tsiro

 Page 30


Ba ma iyakar rawa ba, motsin arziki Haulatu kasa yi ta yi, su Safina kuwa shiru suka yi don tun shigowarsu suke jifan Haulatu da tambayar ko dagaske Yaya Sadauki na sonta amma kamar kurma. Munira wacce ta riga su zuwa sai tambayarsu meyafaru take yi? Radiya ta labarta mata. Murmushi ta yi.


"Dama ai na faɗamaku zai wahala idan ba sonta yake yi ba. Ita ma ga dukkan alamu tana sonsa."


Sai a nan Haulatu ta dube ta gami ɗan harara. 


"Ni na faɗamaki? Ko shi ne ya sanar da ke?"


Suka yi dariya, a hankali ita kuma ta sauke ajiyar zuciya, kalmar ta yi kyai da ya furta ta tuna bata san sadda ta saki wani lallausan murmushi ba. Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Kasancewar an ɗan kashe sautin kiɗa MC na sanar da isowar Amare wajen. 

  

_"Duk wanda zai maki so ba zai kai wanda nake maki ba._ Na shirya bayyana maki kaina a kowane lokaci daga gobe."_


Ta ja guntun tsaki, mutum ne da ba ta san ko waye ba, koyaushe saƙon safe daban da na dare, idan kuma ta kira layin sai kiran ya ƙi shiga tun sau ɗaya da ta kira aka ɗaga kuma aka yi shiru ba'a ce komai ba. Ta dinga raba idanu ko za ta ga Yaya Sadauki ya shigo amma har aka kammala aka watse babu ƙeyarsa. Koda suka fito ma babu motarsa a wajen, Mu'az ne ya zo inda take a tsaye don a lokacin su Safina na can ana ta hotuna kamar wanda aka yi a ciki bai ishe su ba. Ta waigo ta dube shi kafin ta sauke ajiyar zuciya.


"Au, ashe kai ne."


Ya ɗan ɗagamata gira kaɗan. 


  "Ki na expecting wani ne?"


Ta girgiza kai. Shi kuwa ya jinjina na shi kan.


"Ok. Wai ke kin ma san matsayinki a zuciyata kuwa? Rashin sanin hakan ne yasa ki ke aikata abin da zai ƙonan raina ko?"


Kanta ya ɗan ɗaure, me yake son ya ce toh? 


"Ban fahimci inda ka dosa ba Ɗan birni?" 


Ya girgiza kai. 


"No, ba za ki fahimta ba ai, zan fahimtar da ke sosai. Gobe mu haɗu mu yi maganar. Idan ma bai samu ba sai na kira ki a waya."


Yana kai wa nan ya yi gaba ganin su Safina sun tunkaro inda ta ke. Haulatu kuwa ba abin da ya faɗomata a rai face saƙon da aka turo mata ɗazun. Gobe? Mu'az ya ce za su yi magana gobe? To ko dai shi ne mutumin dake turo mata saƙonnin soyayya a ɓoye? Idan shi ne da wane idanun za ta dubi Safina? Ranta ya ɓaci ainun, ta shiryawa duk abin da zai faru a goben, za ta ba shi mamaki fiye da zatonsa, ita zai yiwa wasa kwakwalwa? A tunaninsa za ta so shi ne? To ai ko babu Safina cikin alaƙarsu ba ta taɓa yi mishi wannan kallon ba. Ta yi ƙwafa da ya sanya Safina dubanta. 


"Lafiya kuwa? Wani abun ya faru? Dama na ga Yaya Mu'az ya bar wajenki yana cin magani. Ko faɗan da ku ka saba yi ce ta motsa?"


Sai ta ɗan ja guntun tsaki gami da wayancewa.


"Rabu da shi, ai shi ba ya son zaman lafiya. Ɗan rikici ne kamar Mominsa."


"Abin har da cin fuska? To ba na son haka." Fadin Safina tana ɗan harararta. Ita kuwa sai ta ɗan yi murmushin yaƙe. 


***

Washegari aka ɗaura auren Raudha da Batulu. Raudha anan garin Katsina za ta zauna ita kuwa Batulu ɗan Kano ta kwaso. Kowa fuskarsa cike da walwala. Abokan angwaye sun shigo an gaisa da iyaye, yayyunsu sun sha shadda kowanne da kalarsa sai dai masu fari sun fi yawa. Haulatu leshi kalar silver, ta sanya suka yi anko da Zaituna, Maman Zaituna ce ta ɗinka musu, ta yi adonta cikin sarƙar da Sadauki ya kawomata tsaraba sadda ya yi tafiya. Sam ranar ta tashi ne babu wani kuzari, da damuwar wai Mu'az ke turomata saƙo a waya ta kwana ta tashi, tun jiya ta ke kwaɓar kanta cewa kar ta sake ta ba shi amsa har sai sun haɗu ido da ido. Shiyasa ana ta hotuna a falon Hajja da Amare amma ita ko shiga ba ta yi ba, tana tsaye kawai daga ƙafar bene ta ɗan riƙe ƙarfen tana kallon jama'a wanda kaf cikinsu babu Sadauki babu Mu'az hakanan ba ta ga Khaleefa da Zaid ba, ba ta sani ba ko don su ne manyan yayyun, girman suke son kamawa. Jifa-jifa kuma tana kallon wayarta jiran shigowar saƙon mutumin da ta ba kanta cewa Mu'az ne. Ai kuwa ko mintuna uku ba ta yi daga ɗauke kanta daga saman wayar ta ji saƙon ya faɗo. 


"Ki same ni a wajen rumfa."


Ta sauke ajiyar zuciya har tana ɗan hura hanci. Ji take yi ta shiryawa komai. Daidai ta ke da Mu'az, ita ba ta son halin yaudara, hatta da saƙonnin da ya dinga aikomata da wata lambar a ɓoye ta saka a rai cewa yaudara ce zallarta. 


Ficewa ta yi ta ƙofar kicin ɗinsu don ta fi saurin zuwa lambun. Babu mutane sai yara dake ɗan tsalle-tsallensu. Tun kan ta ƙarasa ta hango shi ya juyamata baya yana zaune daga saman dakalin da ya zagaye rumfar ta farko, farar shadda ce jikinsa babu babbar riga, sai ko hula da ya ɗora a ka. Sam ba ta gane waye ba, kawai idanunta ya rufe da tunanin Mu'az ne. Yana daga zaune ba don haka ba da ta kula wannan ɗin ya fi shi tsayi da ma. 


Tun sadda ta hango fuskarsa kafin ta kai ga ƙarasa shiga rumfar, sai ta yi saurin ja baya. 


"Yaya Zaid ina wuni." Ta gaishe shi kuma ba ta jira me zai ce ba ta juya da nufin tafiya don ita bilhaƙƙi ba ta kawo shi ba ne amma ta ji ƙirjinta na dukan tara-tara cike da fargabar kar dai ace shi ne mai aikamata saƙonnin ba Mu'az ba? 


Gani ta yi ya sha gabanta. Idanunsa gaba ɗaya ya shigar cikin nata a ƙoƙarinsa na aikata da saƙonnin da suka jima a ƙoƙon ransa. Ya ɗan narkar da murya. 


"Please yau ki ba ni dama mu yi magana ido na ganin ido."


Haulatu ta waiga hagu da damanta, kafin cike da tsantsar mamaki ta ɗago mishi fuskar wayarta duk da babu abin da ta buɗo, baki na rawa ta ce. 


"Kai....kai...ne?"


Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe su a cikin nata. Kamar mai raɗa ya amsa.


"Yes, ni ne. Duk saƙon da kike receiving ni ke turowa. Na fara sonki tun ganin farko da na yi maki a rayuwata. Na rasa ta hanyar da zan bi na ɓullo maki, dalilin kenan da na zaɓi ragewa kaina damuwa ta hanyar turo maki saƙonnin da ke nuni da bayyana zuciyata gareki. Sai dai na ga hakan kamar ba zai haifarmin da ɗa mai idanu ba, wannan dalilin ya sa na yanke shawarar tunkararki kai tsaye na sanar da ke ina sonki, ina kaunarki. Ba na jin rayuwata za ta cika idan babu ke a cikinta."


Ita dai kamar an shuka ta, kallonsa kawai ta ke yi baki sake, bai tsaya iyaka nan ba, Zaid gwani ne na tsara kalamai masu tausasa zuciya amma babu kalmarsa ko guda da ta yi tasiri a kan Haulatu. Ita mamaki ne ma da kallon abin kamar a fim ya sanya ta yin saroro tana duba da sauraron zantukansa tiryan-tiryan har ya rufe zancen da jefa mata tambayar ko ta aminta da shi? 


Jin shiru, ya sanya shi ƙara magana yana girgiza kai duk ya bi ya susuce. 


"Aa don Allah, please Noor kar ki ce min A'a. Komai nawa ya bar tafiya daidai, tun sadda na ɗora idanu a kanki zan iya rantse maki bana cikakken rabin awa ban tunaki ba. Ƙin karɓar soyayyata daidai ya ke da rusamin dukkan akalar rayuwa."


Wata ƴar ƙaramar dariya ce ta ɗan suɓucemata na takaici da ɓacin rai. Zaid dai wanda ƴar uwarta ke mutuwar so da ƙauna, shi dai da ta ke jin ba za ta iya rayuwa ba tare da shi ba, a yau shi ke ɓarin zantuka wai ya na sonta? 


"Abin da ɗaure kai Yaya Zaid, ni dai ka ke so? Ko ka manta alaƙar da ke tsakanina da Anti Zaituna? Ko kuwa ka manta ni ɗin ma jikar Hajja ce? Tsohuwar da kaf gidan nan babu wacce ka raina irin ta?"


Ta ɗan fiddo idanu da ɗaga gira kaɗan. 


"Ohhhh, na fahimci wani abu, a saboda haka ne ka ke ta ƙoƙarin komai ya wuce tsakaninka da Hajja? Ka fara shigowa sashenta? Ka yi kuskure Yaya Zaid, ka yaudari zuciyarka idan har tunaninka ya ba ka cewa ni Haulatu zan taɓa soyayya da kai. Da Haulatu da Zaituna abu guda ne, yanda ka ke ƙin Zaituna, to wataran ma Haulatun za ka farka daga bacci ka gane ba sonta ka ke yi ba.."


"Wallahi sonki nake yi."


Ya tari numfashinta da sauri, ƙirjinta sai bugu ya ke yi sakamakon zafin da kalamanta ke haddasa mishi. Har wani gumi ya ji a saman goshinsa. 


Ta yi murmushin takaici. 


"Uhum, na gode da kaunar, sai dai don Allah tunda ka ji amsa ta kar ka ƙara aikomin da saƙo. Sannan ka yi duk yanda za ka yi ma ka manta da ni da lamarina don abu ne ba mai yiwuwa ba har abada kuwa."


Daga nan ta gifta shi ta fice a gaggauce don yaran dake wurin sun soma maido hankula gare su. Hawaye ne ya zubo mata ta yi saurin gogewa da tafin hannunta. Wannan abu da me ya yi kama? Yaya Zaid ne ke son ta? Wato bai ko ji kunyar furtawa ba? Sai ta fasa komawa ɓangaren Hajja gudun kar wani ya fahimci yanayin damuwar da ta ke ciki kawai sai ta zarce ɓangaren su Radiya, nan ne take da tabbacin ba jama'a sosai. Ba ta kallon kowa ballantana a kula da yanayinta, ta san dai akwai mutane a filin gidan, amma ba ta ko damu da sanin su waye ba. Sai da ta kusa cimma ɓangaren su Radiya ta ji mutum a gefenta ta ɗago kai ba tare da ta fasa tafiyar ba. Shi ma ita ya ke kallo fuska a ɗan haɗe. Mu'az ne cikin shadda ruwan ƙasa har da babbar riga. Ɗan dakatawa ta yi fuskarta babu walwala ta ce. 


"Lafiya?" Ya zaro idanu waje kaɗan. 


"Lallai ma, wato ni ki ke cewa lafiya ko?"


Ta kauda kai ta yi shiru. Ita tsabar ma ranta a ɓace yake ba ta san sadda ta furta hakan ba. 


"Ina ki ka shiga na karaɗe gidan na ban ganki ba? Kin manta nace za mu yi magana?"


Ta gyara tsayuwarta. 


"Da ka kira wayata za ka same ni. Amma yanzu tunda mun haɗu ina sauraronka."


Ya ɗan yi tsai yana kallonta har sai da ta ƙosa. Sai dai kafin ta furta wani abun ya riga ta. 


"Kamar akwai abin da ya ɓata ranki, ko mu bari ma yi zancen daga baya?"


Ta girgiza kai. 


"Aa kar ka damu, babu komai. Ka faɗi kawai."


Ya jinjina kai gami da furzar da ɗan ƙaramin huci. Ya ji a ransa gwara ya furta ɗin kafin abin da yake tsoron faruwarsa ya farun don haka ya nutsu tamkar ba shi ba. 


"Watakila abin da zan furta ya yi maki daɗi, wataƙila kuma akasin hakan ne. Kin san ni, ban iya wani ɓoye ɓoye ba, a baya ma da na yi shiru, ban gama fahimtar alƙiblar da na dosa ba ne. Amma lokaci guda kuma jiya wani abu ya afku da ya farkar da ni daga baccin da nake. In short, ina kaunarki, sonki nake yi da aure."


Ya ƙarashe da jin wani rauni na murya a dalilin kallon da ta watsa mishi. Sai kuma ta kauda kai, lokacin da wasu mata ƴan biki suka nufi ɓangaren Abba Ridwan, hawaye suka gangaro mata a kunci  kafin ta haɗiyi miyau mai ɗaci ta dube shi. 


"Na san da kalar zancen da wancan ya zo min irinsa zan tsinta daga bakinka. Sai dai ku sani, daga kai har shi ba kwa gabana. Kar ka juya akalar zumuntar da ke tsakanina da kai Yaya Mu'az, ina girmamaka ina kuma kallonka tamkar yayana da muka fito ciki..."


"Aa please, kar ki haramtamin abin da Allah ya halastamin mana. Ba mu fito ciki guda ba, mu ɗin ƴan uwa ne masu matukar kaunar junansu. Mene ne laifi don ina son kyautata alaƙar ta hanyar juya ta zuwa mataki wanda zai jagoran ce mu har ƙarshen numfashi? Sannan ni da waye ki ke maganar? Waye wancan ɗin da ki ka ambata?"


Ya na maganar tamkar wanda ya zare don tashin hankalin da kalamanta suka jefa shi ga ɓacin rai da zazzafan kishin Sadauki irin wanda bai taɓa zaton zai ji shi ba. Jikinsa ya ba shi cewa Sadauki take nufi, wato duk saurinsa sai da ya riga shi?


Haulatu kuwa kallonsa take ganin gaba ɗaya ya hargitse, ta share hawayen karo na biyu gami da ƙara tamke fuska, ta koma Haulatunta ta usuli. Wayarta na ta ƙara amma ko kallon fuskar ba ta yi balle ta ɗaga. 


"Ba huruminka ba ne sanin ko waye shi ba. Ni na faɗamaka, har abada babu alaƙa ta soyayya tsakaninmu. Idan kuwa ka dage akan bakanka, ni kuma na yi alƙawarin yanke zumuntar da muke yi a yanzu. Babu aure a gabana yanzun ballantana kuma wai soyayya. Koda zan yi kuma, har abada na haramta yin ta da kai."


Daga haka ta juya ta cigaba da tafiyarta tana hawaye sosai, ga Zaid kuma ga Mu'az? Anya kuwa lafiya? Duk wai ita suke so? Har ta ƙarasa ɓangaren su Radiya ba ta bar hawaye ba, sai da za ta shiga falon ne ta share fuskarta. Maman Radiya ba su nan kamar yanda ta zata, duka ana can wurin Amare da Angwaye, da ƴar dattijuwar da ke zaune tare da su ta haɗu, suka gaisa sannan kai tsaye ɗakin Radiya ta shige nan ɗin ma babu kowa, kwanciya ta yi saman ƙaramin gadonta ta ci kuka son rai, tausayin Zaituna da Safina ke cin ranta fiye da ita kanta. Har gobe Zaituna ba ta fidda Zaid a rai ba, ga kuma Safina da abin nata kullum ke ƙara gaba kan Mu'az wanda bai san da zamanta ba. Sai gaba ɗaya ta ji su biyun duka suna ba ta haushi, a take ta buɗe lock na wayarta, saƙon Zaid ta ci karo da kiran Zaid har sau wajen uku. Nan take ta rufe lambobinsa ta goge, shi ma Mu'az ta goge nasa bayan ta rufe yanda duk su biyun babu mai kiranta da layukan da ta sani sai dai ko ta wani layin daban. 


Sai da kiran Umma ya shigo wayarta ta ɗaga, Umma ta hau tambayar ina take. Ta amsa mata ga ta nan zuwa. A dole ta miƙe jiki duk ba ƙwari, kwalliyarta duk ta goge, gudun kar Umma ta gane wani abu ya sanya ta shiga banɗaki ta wanke fuskar, ta yi amfani da kayan kwalliyar Radiya na saman madubi ta ɗan gyara ta. Nan da nan ta fito fes idan ka cire idanunta da suka sauya launi kaɗan. Sai kuma ta ja wa kanta tsaki, to mene ne ma na kukan? Wato ta ma ɗauki batun nasu da muhimmanci, ita kaɗai dai ta yi kiɗa da rawarta a ƙarshe ta fice ta rufo ɗakin. 


Ba ta yarda sun haɗu da Umma ba sai bayan ta shiga cikin ƴan uwanta annashuwarta ya dawo, hakanan a sannu idanun sun washe sannan ta ƙarasa gareta. Duk da haka Umma sai da ta tambayi ko ba ta jin dadi, ta gan ta wani iri. Ba ta yi mamaki ba don ba yau Umma ta saba ɗago ta ba idan tana cikin wani yanayin. Sai ta wayance da fadin kanta ke ɗan sarawa. 


"Allah ya sauwaƙe, sai ki nemi wuri ki ɗan huta."


Ta amsa da toh. Ranar ko kai Amarya Raudha ba ta je ba, ba ta son ma ta faɗa motar wani a cikin samarin gidan, ita yanzu duk haushinsu take ji don gani take yi kowa da na shi abin. A gefe ana mata kallon budurwar Sadauki, nan kuma ga abin da ya fito daga bakin Zaid da Mu'az, ya zama dole ta yi takatsantsan da kowa tunda ita ba soyayya ce a gabanta ba. Ba ta taɓa sha'awar ta yi ta ba. Abu ɗaya ta sani, koda su Safina ke mata kallon kamar ita ɗin ma tana son Sadauki, ba ta ce musu uffan ba, kuma har a yanzu ba ta da amsar bayarwa a karon kanta ma balle har su ji. 


 Washegari kuwa aka ɗunguma tare da ƴan uwa zuwa Kano don kai Batulu. Koda sha'awa, Haulatu ba ta ji son bin su ba. To kusan ma babu sa'anninta a tafiyar, daga iyaye sai ƙawayen Batulu da kuma su Zaituna su Jannat. Umma ma ba ta je ba. 


***

  BAYAN SATI ƊAYA...


Suna tsaye a farfajiyar gidan an fito yiwa su Haj Nafisa rakiya za su tafi zuwa Kano don jirginsu na dare ne. Hawaye Zaituna da Haulatu ke yi tamkar ba za su ƙara ganin juna ba. Ita na Haulatu ban da na sabo, har da na tausayin Zaituna musamman hirarsu na ƙarshe a jiya inda ta ke hawaye take jaddada mata cewa ganin da ta yiwa Zaid da bikin nan ya ƙara tayar mata da wani miƙi na sonsa, tana kuma jin ba mace ɗaya ba, ko a ta huɗu ta zo idan har a gidan Zaid ne to fa tsaf za ta zauna kuma ta yi mishi biyayya ta nuna masa ƙauna tamkar su kaɗai ne a gidan. A ganin Haulatu sam Zaid bai cancanci wannan sadaukarwar ba tunda bai san halacci ba. Haj Nafisa ta rungumo Haulatu a kafaɗa tana rarrashi. 


"Ki yi hakuri ɗiyata. Na so kwarai na tafi da ke Malaysia, amma har gobe ban fidda rai ba. Ummanki dai ta ce idan don ita ce, ta bar min ke halak malak, Hajjarmu ce ta ƙi goyan baya. Amma ko ba yanzu ba, duk sadda kika ji kina da buƙatar zuwa gurina ki sanar da ni. Kin ji ko?"


Haulatu ba ta san sadda ta ɗaga kai ta dubi Maman Zaituna ba, duban ƙauna da soyayya. Idan ka cire Ummanta, ita ce mace ta biyu da ta kwanta mata a rai wacce ke ƙaunarta tamkar daga cikinta ta fito. Murmushi suka sakarwa juna kafin Maman Zaituna ta sake ta ta shiga mota. Haka Haneef ya zo suka cafke yanda suka saba, ta yi dariya. Bayan duka sun shiga mota, direba ya ja suka tafi ana ɗagawa juna hannu tamkar kada a rabu. Kasancewar ranar babu islamiyya ya sa ta shigewa ɗaki, lokacin uku da mintoci. 


 Bacci ya soma ɗaukarta bayan tunane-tunanen da ta faɗa mai haddasa ciwon kai, ta ji kamar cikin baccin ana tashinta. A hankali ta buɗe idanunta, ashe zazzaɓi ne a jikinta don wani irin rawar sanyi ta ke yi ga kuma azababben ciwon kan da ya ninka na farko. 


"SubhanAllah, Haule ashe ba kya jin dadi, ina ta mamakin wane irin bacci ne har yamma. Maza tashi muje a kai ki asibiti. Ke Na'imatu!"


Umma jin Hajja na kwalamata kira ta shigo dakin da sauri. Ita ma jin da ta yi Haulatun ba lafiya ya sanya ta ɗan taɓa jikinta. Nan ta taimaka mata ta saka abaya saman riga da siket ƴan kanti dake jikinta. Tsabar zafin ciwo ko'ina na jikinta kakkarwa yake yi ga wani uban jiri dake kwasarta. Karshe haka suka fito tana rungume jikin Umma, Hajja kuwa tuni ta kira direbansu a waya, Allah ya taimaka yana kusa. Dakyar Umma ta lallaɓa Hajjar ta zauna da zummar za ta kai ta. Kai tsaye asibitin su Khaleefa suka nufa. 


***

 KANO...


Biki Buduri...
Ina tafe gobe in sha Allahu idan har na samu dama, idan kun ji shiru, a yi min uzuri. 🥰🥰🥰Love you all.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: *Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*

Fitar tsiro 

 Page 31


********


A cikin wannan satin da ake, a garin Kano, an yi biki na gani na faɗi wanda a wannan shekarar a tarihin Kano shi ne bikin da ya mutane suka yiwa kallon wanda ya fi kowane biki ƙayatuwa da kuma kashe kuɗi tun daga kan lefe. Lefe ne aka kawo akwatuna saiti goma ga kyauta ta mota mai tsadar gaske ga Amarya. Tun daga nan Momi ta ƙara susucewa da lamarin surukin nata, ita kuwa Hindatu ta ƙara shiga tsantsar tashin hankali ta kuma gane dagaske dai Alhaji Ibrahim mai kuɗin gaske ne irin kuɗin da ba ta taɓa hasko su ba. Ba ta ƙara tsinkewa ba sai da aka shiga hidimar biki. Daga suturun da ta yi amfani da su wanda Ango da kansa ya haɗa ta da Hajiya Adama aka ɗinko mata su masu bayyana sura da kuma tsada, har wanda Angon shi ma ya yi amfani da su, abin kallo ne. Ranar kamu inda aka yi shi daban, haka yini. Da kansa ya ce a rarraba bai son a haɗe wani kamu da yini, Momi ta ƙara jin kanta ya fasu, ƴan fadarta da ma waɗanda a baya ke ganin sun fi ta kuɗi ita ɗin mai kawo musu kaya gida su siya ce, sai ga su nan kowa na neman shige mata da son cusa kai. Ta zama ita ce Boss ɗin, idan ka gan su daga ita har ɗiyarta ba ka ce su ne asalin Hindatu da Momi na baya ba. Sun sauya kalarsu ma ta goge sakamakon sauyi na rayuwa. Hatta da Momi kafin zuwan biki ta mallaki mota da kuma direban dake kai ta wurare. Har hotunan biki ta tura wa Alhaji Badamasi don ya ji haushi, sai dai ci kanki bai ce mata ba. 


Gidan Hindatu a unguwar Tudun Yola yake, sabon ginin da Alhaji Ibrahim ya siya. Babu abin da bai saka mata ba na more rayuwa, tun kafin zuwan biki ya sa aka yi mata passport na fita ƙasashen waje. Bayan biki ko sati ba su yi ba, suka ɗaga ƙasar Dubai. Gaba daya ba ta samu damar yin waya da Haulatu ba, ta bar shi akan daga baya ta sanar da ita. Zuwa lokacin ta kurɓi zumar soyayya daga wurin Alhaji Ibrahim, sai ta ji nan duniya babu mai raba ta da shi, ba ta san me ya sauya ta ba, amma wani irin ƙaunarsa ta shige ta na bazata. Babban mutum amma fa ya gwanance a iya tafiyar da mace yanda za ta dulmiya kogin soyayyarsa. 


Shi kuwa Ɗan Mutuwa dama tun farko ya kula da yanayinta na tsoro da fargaba akan auren, bai taɓa nunamata ba shi dai ya san ba na wasa bane, a barikin ma ai kowa da matakinsa. Na'imatun koda ba ta bayar da labari ba, su matan barikin dake maitarsa sun shaida. Koda dai dama ba son Na'imatun yake ba, kafin ma ya san da zamanta a shimfiɗa sai gumu ta yi gumu. Haka suka yi rayuwar suka ƙare.


***

KATSINA...


 Suna isa asibitin kai tsaye wuri Haulatu ta samu a waiting room ta zauna cikin ɗaya daga cikin kujerun sakamakon jirin dake kwasarta. Da file na gidan gaba daya aka yi amfani da shi, sai da wasu mutum uku suka fito sannan Umma ta taimakawa Haulatun suka shiga. Yana zaune yana danna tablet ɗinsa, ya sanya farin gilashi, tun da ya ɗaga file ɗin ya gane daga gida ne yake tunanin toh waye ba lafiya a gidan? Sallamar Umman ce ta sa shi saurin ɗago kai. Ya miƙe cike da girmamawa yana fadin. 


"Umma? Dama ke ce?"


Ganin Haulatun ya sa shi gane ita ɗin ce marar lafiyar. Lokacin kuma Umma ke ba shi amsa da cewa Haulatu ta kawo. 


"Oh." Ya furta kafin ya koma mazauninsa, bayan sun zauna ya gaida Umma ta amsa da kulawa. Ita dai tana kaunar Khaleefa tana jinsa tamkar ɗan cikinta. 


"Meke damunta?"


Da bakinta ta amsa. 


"Zazzaɓi ne sai kaina..ciwo."


Ta ƙarashe hawaye na zubomata. Ya ɗan dube ta kaɗan, tabbas tana jin jiki. Karon farko da ya ji tausayinta har ransa. Test ya bayar na jini, sai da ya tabbatar Malaria ce sannan ya rubuta magunguna don a nan ya saka Nos ta shigo aka ɗauki jinin ta fita. Magunguna da allurar jijiya na ranar da washegari, sai drip da za'a sa mata yanzun sakamakon jirin da take kuma Umma tace abincin ma yinin ranar gaba daya ƙin ci ta yi. Nan ma Nos ya ƙara kira a waya ya ba ta umarni. Jin allura ta zaro idanu. 


"Allura kuma?" Ta furta da narkakkiyar murya na wacce ke jin ciwo tana dubansa. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana mai kauda kai daga dubanta don Umma tuni ta amshe zancen.


"To haka za'a bar ki da ciwo a jiki Haulatu? Ai gwara a yi maki ko zazzaɓin ya sauka. Daure ki tashi muje."


Tana turo baki da yamutse fuska haka Umma ta taimaka mata suka fita a ɗakin. Bayan fitarsu ya fidda gilashin gami da jinginar da kai jikin kujera ya ɗan lumshe idanu. Bai kaunar ganinta cikin wannan damuwa da rashin lafiyar.  Yana hankalce da ita tun soma bikin, duk wani taku da ma abin da ya faru na rigimar da ƙanwarsa suka yi da ita duk a kan Sadaukin babu abin da bai ji ba. Idan har kuwa tana son Sadauki, bai ga dalilin takurawa a kan sai ta ƙaunace shi ba, shi mai mata ma kenan. Ba ya tunanin za ta so shi. Wannan dalilin ya sanya shi zaɓar barin komai da manta komai. Ya kuma zaɓi ya kauda kai daga gareta, sai dai ganinta na yau ɗin ya so warware dukkan shawarar da ya yankewa kansa a kwanakin da suka wuce, shawarar na kallonta matsayin ƙanwarsa tamkar sauran ƴan uwannasa. Bai san kuma sadda abin ya ɗarsu a rai ba da har ya yi wannan zurfin ciki ba. Yana ji ba girkin da ya ji Hajja na mata gori ba ta iya ba, ko tsaftar ce ba ta da ita, zai iya haƙurin zama da ita a kowane yanayi, fiye da haƙurin da yake yi a rayuwarsa da Hafsat. 


'Ina za ta so ka? Alhalin tana da Sadauki? Shi ta ke so?'


Wata zuciyar ta yi mishi tuni sai ya ji wani zafi a rai, don haka ya buɗe idanunsa da suka kaɗa. Ya miƙe ya shiga banɗaki ya wanke fuskarsa ya goge da farin tawul kafin ya fito. Hand Sanitizer ya matsa a hannunsa, daga nan ya fita ya rufe ofis din zuwa inda su Umma suke. 


Can ya tarar ana ta fama da Haulatu wajen neman jijiya za'a sanya mata drip amma ta ƙi tsayawa sai kuka take yi tana riƙe Umma. Babu irin tsawar da jan ido wanda Umma ba ta yi mata ba amma abu ya gagara. 


"Lafiya?" Jin muryarsa tuni ta yi ɗif da ihun, ta dubi yanda ya ɗaure fuska, ya maida kallonsa ga ma'aikatan jinyar biyu da ke kokarin ganin ta ba su haɗin kai. 


"Yauwa ai gwara da ka zo da kanka, ɗazun ma ganin idonka ne ya sa ta tsayawa aka ɗibi jinin."


Faɗin Umman kenan. Tana ƙara cewa a baya sam ta san ba ta da wannan iya shegen na tsoron sirinji sai yanzun ta rasa me ya hau kanta. 


Ita dai Haulatu shiru ta yi tana kukan zuci gami da runtse idanu sa'ilin da Khaleefa ya karɓi kayan aikin ya ba su Nos din umarnin fita. Daga shi sai Umman da ita. Wayar Umma ta yi ƙara ta ɗaga ganin Hajja ce, nan ta shaida mata jikin da sauƙi ruwa kawai za'a ƙara su taho gida. Daga nan ta shiga tambayarta ko su Haj Nafisa sun isa. Anan Hajja ke cewa ai sun jima da sauka a Kano. Ajiye wayar Umma ya yi daidai da kammalawarsa. Ya dube ta. 


"Umma ko akwai abin da ku ke buƙata?" 


Ta yi ɗan murmushi.


"Babu komai sai ruwan sha."


Ya maida mata martanin murmushin gami da amsawa da toh ya fice. Ta dubi Haulatun. 


"Sannu." A hankali ta ɗaga kai. Can kuma bacci ya ɗauke ta. 


***

 Abuja...


 "Wai Zaid lafiya? Tun da muka dawo na rasa gane kanka. Ko girkina ka daina ci, don Allah akwai wani abu ne da na aikata gareka ban sani ba?" Faɗin Jalilah kenan hawaye na kwaranyowa a fuskarta. Tun dawowarsu daga Katsina ya sauya mata, hatta a shimfiɗa ba ya nemanta. Wannan shi ne sanadin shigarta damuwa da rashin sukuni. Lokacin an yi sallar isha'i, duk da laulayin da ta ke ɗan fama da shi, bai hana ta cin ado ba kamar yanda ta saba domin tarbarsa. Yau ɗin ma ya shigo babu walwala, koda ya yi wanka ɗaki ya shige don abincin ma ya ce ba zai ci shi ba. A ɗakin ta ƙarasa ta iske shi da tambayoyinta.


  Idanunsa a rufe kamar bai ji ta ba amma a zahiri babu harafi ɗaya nata wanda bai shiga kunnensa ba. To me zai ce mata? Soyayyar Haulatu ce ta yi mishi mummunan kamun da ke neman kassara shi ko kuwa ƙiyayyar da take mishi gami da furucin ba za ta taɓa sonsa ba ne ke ƙona ransa har yake jin komai ba ya burge shi a rayuwar? 


"Babu abin da za ka ce? Ko dai gajiya ka yi da ni ne? Ko girkin nawa ba ya maka dadi?"


Sai a sannan ya buɗe idanunsa ya dube ta, ita ɗin ma shi take duba da nazarin ramar da ya yi a kwanakin nan. Zaid sai ya ji ta ba shi tausayi matuƙa, ta riga da saba da tarairaiyarsa bai kyautu ace sanadin abin da zuciyarsa ta makance a kai ba, ya yi mata irin wannan sakayyar ba. Ya tuna tana da haƙƙoƙi a kansa wanda bai kamata ya tauye mata ba. Zaune ya miƙe ya ja hannunta ita ma ta miƙe daga durƙuson da ta yi ba musu ta koma gefensa. Hawayen ya share mata da tafukan hannayensa. 


"I am so sorry. Akwai wata ƴar damuwar da nake ciki amma in sha Allahu zan yi iyaka kokarin ganin ban ƙara shiga haƙƙinki ba. Kin ji?"


Ta gyaɗa kai tana ɗan tura baki da ɗan shagwaɓa ta ce.


"Toh meke damunka? Na yi zaton mun zama ɗaya, abin da ya shafeka ni ma ya shafe ni."


Ya yi mata murmushinsa mai kara jefa ta kogin so da ƙaunarsa. Lokaci guda ya sumbaci bayan hannunta. 


"Ya shafe ki, amma Allah ya kiyaye abin da zai dame ni kema na jefa maki damuwarsa. Na fi buƙatar na tattara naki damuwar na haɗa da nawa, su dagula lissafina ni kaɗai."


Wani murmushi ta yi tana mai jin daɗi kalamansa, a duniyarta tana son Zaid ya yi magana. Ya ƙware da kalamai masu daɗi masu sanyaya ruhi. 


"Toh abincin fa?"


Ya ɗan yamutsa fuska.


"Ban tare da yunwa."


"Please ko kaɗan ne ka ci."


Ganin kamar za ta yi kuka a dole ya miƙe. 


"Ok, muje na ci."


Wannan yasa ta miƙe zuciyarta fari ƙal suka fita falon.


***

 Katsina...


 Sai wuraren takwas da mintoci na dare Umma suka shigo gidan. Hajja ta tarbe su tana zuba wa Haulatu ruwan sannu. Mu'az dake falon tare da Hajja, bai jima da shigowa ba ya ji Haulatun ba lafiya, yana kokarin bin su zuwa asibitin ne kuma ya ji Hajja ta ƙara kira sun ce suna hanya, wannan yasa shi zaman jira. Shi ɗin ma gaba ɗaya ya ɗan yi rama, bai taɓa zaton maganganun Haulatun zai dame shi har haka ba. Sai dai ya mishi ciwo, madadin ya ji ta fice a ransa sai ma saɓanin hakan. Ya kwana biyu ba ya ko shigowa sashin Hajja sai a ranar, nan ma kasa jurar rashin gani da jin ta ya yi, dolensa ya saɗaɗo ya shigo. 


"Sannu Haule, Allah ya ƙara lafiya kin ji?" 


Ta gyada kai, ta ɗan ji ƙwarin jikinta sanadin ƙarin ruwan, ganin Mu'az a falon yasa ta kama hanyar bene za ta nufi sama. 


"Aa, dawo maza ki sa wani abu a cikinki sai ki sha magani ki yi sallah ko?"


Ta dubi Hajja sannan ta ce. 


"Ni a sama zan ci, bandaƙi zan shiga yanzu."


Daga nan ta wuce, Umma kuwa zama ta yi tana ba Hajja bayanin cewa Malaria ce ba wani abu ba. Dama tuni ta yi sallarta a asibitin. 


"Mu'azu, ina ka shiga kwana biyu. Ciwo ka yi ne? Na ganka wani iri."


Ya shafi ƙeyarsa jin abin da Umman ta ce, yana murmushin yaƙe, ya sani ba don komai ta ƙi zaman falon ba sai dominsa. 


"Au, ke ma kin kula ashe? Ai faɗan da na gama yi mishi kenan. Gaba ɗaya ya fige kamar kazar mayu. Ka tashi maza kai ma ka je ɗan uwanka ya aunaka." Faɗin Hajja. 


Ya ɗan ɓata rai.


"Ni fa zazzaɓin dare ne na ɗan yi amma yanzu na samu lafiya, na sha magunguna." 


"Sannu, Allah ya ƙara lafiya." Umma ta furta, ya amsa da amin. 


Hajja ce ta sanya Baba Saude miƙawa Haulatu abinci. 


Ta iske tana sallah ta ajiye ta fita. Koda ta idar kwanciya ta yi saman gado jikin duka ba dadi, ba jimawa Umma ta shigo, nan ta hau faɗa kan abincin da ba ta sanya a ciki ba balle ta sha magunguna. Daƙyar ta iya loma biyar, ta sha magani ta bi lafiyar gado bayan ta fidda abayar da ke jikinta. 


***

  Washegari kusan sosai ta ji daɗin jikin, tun safe ƙawayenta suka shigo duba ta, suka hau hira don ɗebe mata kewa. Tana daga kwance a saman gado daga ita sai riga iyaka gwuiwa na shan iska, waƙar da Radiya ta kunna a wayarta tana sauraro na Chiza Dani shi ta maida hankali ga ji yayinda Safina hankalinta ke kan Instagram tana ta kallon hotunan wani aure da aka zuzuta shi ne aure mafi kyau da kashe kuɗaɗe da aka yi a garin Kano a shekarar, abin ma mamakin ganin mutumin ya girmi Amaryar nesa ba kusa ba. Sai dai inda Allah ya taimaka sam ba shi da muni. Ita ma Radiya tana ta leƙa wayar Safinan suna kalla yayinda Haulatu a kwancen hankalinta ke kan waƙoƙin, don tuni an kammala an faɗa wani waƙar na Hamisu Breaker. Lumshe idanu ta yi tana tunano dukkan abubuwan da suka faru a kanta lokacin bikin nan. Sauyawar alaƙarta da Sadauki, daga kallon mugu kuma marar tausayi da take yi masa zuwa na mutum mai sanyi da kuma sauƙin kai. Shi dai, da ake mishi caa da tunanin wai soyayya suke yi. Ta ji tausayin kanta ya kama ta da ta tuno Zaid sa Mu'az da suka furta da bakunansu wai suna sonta. Ita ko me ta mallaka har haka da mazan nan ke bibiyarta haka? 


"Ke Haulatu wai ba za ki kalla ba? Don Allah dube su, wallahi ni dai ba zan iya auren babban mutum ba duk kuɗinsa." Faɗin Safina tana miƙawa Haulatu wayar, karɓa ta yi tana ɗan cije leɓɓanta na yanayin rashin lafiya ga damuwar da tunani ta jefa ta ciki. Kallon wayar ta yi sosai, hoton ta tsurawa idanu, ba haske na fata ko kuma ƙiba da ya ɗan yi ba, ko turai ya je aka sanya shi a inji ba ta tunanin fuskarsa za ta ɓace mata. Balle kuma Hindatun da ta gani. Ta yi masa ta karanta caption na hoton, Ibrahim&Hindatu. Shi ta ga an rubuta. Miƙewa zaune ta yi don kaɗuwa da mamaki.


"Lafiya? Kin san su ne?" Cewar Radiya da suke dubanta. Daidai nan Umma ta shigo ɗakin, ta yi saurin fita daga instagram din gami da cilla wayar ga Safina. Suka dube ta da alamar tambaya, ita kuwa kallon Umma ta yi.


"Au, ba ki shirya ba? Maza tashi ki shirya muje lokacin allurarki ya gabato, sha biyu ya ce." 


Ta amsa da toh cike da ƙarfin hali sannan ta mike don kaucewa tambayoyin da take da tabbacin samun su daga garesu. 


***

A hanya ma tunani kawai take yi tana share hawayenta a fakaice, tunaninta kar bayyanar wannan mutumin ya ƙara haifar da damuwa da tsoro a zuciyar Ummanta, sam ba ta kaunar Umma ta ga abin da zai tayar mata da hankali yanzu, sai dai tabbas za ta je ga Baba Alhaji ta yi musu zancen da kuma nuna musu hoton Ɗan Mutuwa ko don a ƙwatar Ummanta ƴanci. Ko kusa ba ta yi mamaki don ya yi ƙazamin kuɗi ba har haka, ta kawo a ranta harkar ƙwayoyin da yake ne ta samar mishi ko wani mugun abin. Damuwar da take ciki na hoton da ta gani yasa sam babu gardama ba komai ta tsaya aka yi mata allura, ba su haɗu da Khaleefa ba saboda ya shiga theatre. 


Daƙyar ta bari aka yi la'asar rana ta yi sanyi, ta gwadawa Umma ai za ta ɗan tattaka ne don ta ji dadin jikinta, Allah ya taimaka su Radiya sun fice islamiyya. A hankali take tafiyar har ta ƙarasa sashin Baba Alhaji, shiga ta yi da sallama. Ranar ta kama Asabar. Ba ta yi tsammanin ganin Sadauki ba duk da weekend ne dama yakan zo su yi hira da Alhajin. Ba ta ji komai a ganinsa ba ta ƙarasa da sallama. Abin da ke tafe da ita ya ninka damuwa ko tsoron Sadauki a zuciyarta. Ta gaida Baba Alhaji, ya amsa yana mata sannu da jiki har yana jan ta da wasa wai ta biyo shi ba ta jira ya je ya kai kayan dubiya ba. Ita da murmushi ta yi mai kama da yaƙe. Ta maida idanunta ga Sadauki wanda ke nazarinta. Ya kula kamar da magana a bakinta. 


"Ina yini Yaya."


"Lafiya, ya jikin?" Ya furta a tausashe. Ta amsa da lafiya Alhamdulillah. Daga nan ta yi shiru kuma ta ƙi tashi. 


"Meke tafe da ke? An yi wani abun?" Sadauki ke tambayar ba Alhaji ba. 


Ta ɗago ta dube shi karo na biyu, take wasu hawaye masu zafi suka zubo mata. Ta haɗiyi miyau tana jin bakin cikin kasancewarta ɗiyar mutum irin Ibrahim Ɗan Mutuwa. 


Wayarta ta buɗe ta shiga instagram, nemo hotunan bikin ba su yi mata wuya ba don su ke tashe, ta miƙawa Sadaukin wayarta, ya kalla cike da rashin fahimta kafin ya miƙawa Baba Alhaji dake tambayar mene ne? Ya maida duba gareta. 


"Mene haɗinki da su? Ko kin san su?" 


"Wannan kuma waye?" 


Sadauki ya fara tambayar kafin Baba Alhaji. 


"Shi ne mijin Ummana da ku ke nema."


Abin da ta iya furtawa kenan.

[08/09, 5:55 pm] Faty Lawal: *Garaɓasa!* 


*Ƴar uwa kina zaune a gida babu sana'a, tunani da damuwar wace sana'a ya kamace ki da za ki juya sisi zuwa kobo ya addabe ki?* *To ki sha kuriminki, ga dama ta samu, ko yaya abin da za ki samu in sha Allahu zai amfanar da ke ya kuma taimaka makinda wasu cikin ƙananan buƙatunki da zai sa ki rage yi wa mijinki bani-bani.* *Esb enterprises, za su yi maku bonanza ranar juma'a akan naira 500 kacal, za ki koyi yanda ake haɗa graphics* 

*Za su koyar da:*

*Flyer.*

*3d logo.*

*Invitation card.*

*Video invitation card.* *da kuma*

*Cartoon advert.*


*Ƴar uwa duka wannan abubuwan da na lissafo kan naira 500 za ki koya* *Bayan wannan ma tana koyar da yanda ake sana'ar siyar da data a kyauta, tana kuma siyarwa ita kanta.* 


*Za ki koyi yanda ake sana'ar data a kyauta, kar ki bari a yi babu ke ƴar uwa.* *Ki tuntuɓe su ta wannan lamba kamar haka:  07045107521*


*******

Fitar tsiro 32


"Kina nufin mahaifinki mijin Na'imatu?"


Cewar Baba Alhaji. 


Ta runtse idanu jin an jinginata da shi wanda ta sani ya zama dole. 


"Eh shi ne, ita kuma wacce ya aura aminiyata ce tare muka yi karatu."


Baba Alhaji ya yi salati kafin ya ce.


"Amma wannan ya cika shaiɗani, wato har ya samu damar fitowa idon duniya ya ci karensa babu babbaka, wane irin lokaci muke ciki haka da har mai laifi zai fito hukuma na kallonsa babu mai cewa don me? Kuma har ya auri aminiyarki? Ja'irin gaske kai."


"Ita aminiyar taki, ta san cewa mahaifinki ne?" Tambayar da Sadauki ya watso mata kenan. 


Ta girgiza kai. 


"A'a, ba su taɓa ko haɗuwa da shi ba, labarin yanayin zamanmu da shi kawai nake ba ta wasu lokutan."


Ta ƙarashe cike da dauriya sakamakon jin kamar zazzaɓinta ya dawo ga kanta da daman bai bar sarawa gaba ɗaya ba sai raguwa da ya yi, yanzun kuwa sai ya daɗu.

Sadauki da ya maida duba ga hoton yana ƙara kalle fuskar Ɗan Mutuwa cike da jin zafinsa, sosai ya shiga ya bincika shafukan a wayar Haulatu har ya ga ainahin sunan Alhaji Ibrahim. Sanadin harkokin kasuwanci ya san manyan mutane da dama a garin Kano. A take ya fiddo wayarsa ya dannawa wani babban ɗan kasuwa waya, mutumin suna harkar takalma da shi, yana sari sosai a kamfaninsu na nan Katsina, bayan sun gaisa da komai yake tambayarsa ko ya san da wani hamshaƙin mai kuɗi Alhaji Ibrahim wanda ya yi aure a satin da ya wuce? Nan take yace masa kwarai ya san shi. Ya nemi jin bayani game da shi. Ya ce ya ba shi nan zuwa dare duk abin da aka bincika masa zai sanar da shi. Daga nan suka yi sallama. Haulatu da tun soma wayar Sadauki take dubansa tana jin sanyi a rai ba don komai ba sai na yanda ya dauki abin da muhimmanci har a take ya nemi jin inda za'a sami Ɗan Mutuwa. Yana ajiye wayar ya dube ta, ba ta san lokacin da ta sakar masa murmushi ba lokaci guda hawaye na zuba a saman fuskarta. Ya ɗan kauda kai, sam ba ya son kukan mace. 


"Goge fuskar taki, ki tashi ki je ki kuma yi ƙokarin ragewa kanki damuwarnan, damuwa ba shi je kawo ƙarshen matsaloli ba sai dai ya sanya maki wani ciwon."


Daga haka ya maida duba ga Baba Alhaji. 


"Na yi magana da Alhaji Tasi'u Maiplaza, in sha Allah zuwa dare zai sanarmin abubuwa dangane da shi da ma inda za'a same shi. Ku kwantar da hankalinku."


"Alhamdulillah, na ji daɗi kwarai. Allah ya yi maka albarka. Ke Haulatu sai ki yi hakuri har mu ga abin da zai faru. Ki yi ta addu'a, kin ji? Komai zai wuce."


Ta amsa maganar Baba Alhaji da toh. Ta dubi Sadauki karo na uku. 


"Na gode Yaya."


Ya yi murmushi kaɗan, wayarta ya miƙa mata ta karɓa, bisa kuskure har tana haɗowa da yatsunsa, da sauri ta kauda nata hannun, shi kuma ya yi saurin dubanta. 


"Jikinki zafi, zazzaɓin ai bai sake ki ba."


Baba Alhaji ya dube ta. 


"Assha, ka gani ko? Kin sha magungunanki?"


Za ta yi magana ma sai wayarta ta yi ƙara, tare da shi suka dubi fuskar wayar, sunan My Mom da ya gani yasa shi miƙamata. 


"Ki ɗaga amma please kar ki yi abin da za ki jefa ta damuwa."


Ta gyada kai ta amsa wayar, Umma ke tambayar inda ta shiga sai fada take wai ba ta da lafiya ko magani ba ta sha ba amma ta fara fita.


Haƙuri ta ba Umman sannan tace ga ta nan zuwa, tana wurin Baba Alhaji. Sai a sannan Umma ta ɗan sauko tace to maza ta dawo ga Hajja ranta ya ɓaci.  


Bayan sun ajiye wayar ta miƙe tsaye kanta ya yi wani mugun sarawa sakamakon jimawar da ta yi zaune kuma ga ciwo da yake dama. Ta riƙe kan ta runtse idanu. 


"Muje na raka ki. Baba ina zuwa."


Baba Alhaji yana murmushi ya gyara zaman gilashinsa yana dubansu. Ya amsa.


"Toh Sadaukina. Maza raka ta. Allah ya sa kaffara kin ji Haulatu."


Ta gyaɗa kai, ya bi su da kallo har suka fice kafin ya girgiza kai da tausayin Haulatu. 


***

A hankali suke tafiyar kanta yana ƙasa, sunan Allah kawai take ambato a zuciya, ita kaɗai ta san me take ji. Ga radadin ciwo ga na zuci, sam ba ta ji zafin Hindatu ba sai ma tausayinta da ya lulluɓe ta, ba ta san waye ainahin Alhaji Ibrahim ba tunda dama ba su taɓa karo da juna ba, asalima ba ta san sunansa da ɗin Ibrahim ko inkiya ba, kullum a hirarsu idan ba Mijin Umma ba, to sai Malam Khalil idan ta na ji da iskancin na sosai. Su yi shaƙiyancin su dara haka suke yi. Kai a tunaninta koda ma ace ta taɓa ganinsa, ya yi sauyawar da sai na jikinsa ne za su gane shi, na jikin ma ba kowa ba. 


"Babu rayuwar da za ta tafi babu jarrabawa, duk wanda ya yi imani sai an jarabce shi, kar ki bari imaninki ya raunana da ganin tamkar ke kaɗai ce cikin mummunan ƙaddara irin wannan. Ki godewa Allah kina da gatan da wasu ke nema ido rufe. Wani a shege aka haife shi, ya kuma yarda ya yi imani da kaddararsa, ya rungumi rayuwarsa a haka. Kowa da yanayin jarrabawarsa, idan muna kallon wadanda muka fi, zamu kasancewa masu yawan godiya ga Allah, idan kuwa hangenmu yana kan waɗanda suka fi mu, to koyaushe muna cike da ƙunci na zuciya da rashin godewa ni'imomin da Allahu ya yi mana, musamman na lafiya da kwanciyar hankali."


Shiru ya biyo bayan maganganun da Sadauki ke yi idanunsa na ga hanya, ita kuwa jifa jifa tana juyowa ta dube shi har ya kai aya, can kuma ya nisa ya ce. 


"Ki ƙara haƙuri, wataran sai labari. Kina da damarmaki da yawa a rayuwa idan Allah ya ƙaddara, kar ki bari sanadin mutum ɗaya da Allahu ya jarabceki da shi, ki rusa rayuwarki da ma burinki. In sha Allahu za ki zame wa zuri'armu abar alfahari wataran. Kin ji?"


Ya karashe da murya ƙasa-ƙasa yana dubanta. Ita ma aka yi sa'a ta juyo ta dube shi, ji ta yi wani abu tun daga yatsar ƙafarta har tsakar kai, nan da nan ta kauda idanunta tana gyada masa kai. Sadauki ya kauda nasa idanun yana sauke ajiyar zuciya. Tsantsar kaunarta na ƙara mamaye gangar jiki da ruhinsa. Ji yake ina ma yana da damar ɗauke mata dukkan waɗannan matsalolin da damuwa, koda ace bai yi nasarar raba ta da duka ba, to ya zame mata tamkar wani majinginar dafawa. Inuwa yayin da ake tsananin rana, hakazalika bargo a yayin tsananin sanyi. 

  

  "Nagode."


Ta furta a hankali. Har suka ƙaraso ɓangaren Hajja babu wanda ya ƙara magana, dab da ƙofar ya ja ya tsaya cikin dubanta. 


"Na so na yi mantuwa, daure ki zo daga nan."


Ya furta cike da kulawa yana nuna mata gefe guda da ƙofar Hajja gudun kar wani ya ji. Ta kuwa daure ta ƙarasa hannunta ɗaya riƙe da kai. Idanunta har sun ƙanƙance take dubansa. 


"Aminiyar taki kuna tare har yanzu?"


"Eh. Amma mun jima bamu yi magana ba."


Ta faɗi tana tuna yanda suka yi ƙarshen wayarta da Hindatu wacce ke tsoron ma kalar mijin da za ta aura, har take tunanin ko ɗan ƙungiyar asiri ne. Zai yi magana ta yi saurin katse shi.


"Na tuna mun yi magana da ita dab da aurensu."


Ta ba shi labarin duk yanda suka yi, ya jinjina kai. 


"Ok, ina so koda ace kun ƙara magana, kar ki gwada mata wani abu. Idan da dama ki binciki inda take da zama da zummar za ki kawo mata ziyara kwanan nan. Na tabbata ba za ta yi zaton wani abu daban ba tunda kin ce ba ta san da alaƙarku da shi ba. Kin fahimta? Sorry."


Ya furta kalmar sorry lura da yanayinta, ta amsa da toh sannan suka ƙarasa. 


Hajja na ganinta ta hau sababin meyasa ta fita alhalin ba ta jin dadi, sai bayan ta gama faɗan, Sadauki ya gaishe ta ta amsa fuska sake. Ya gaida Umma wacce ta fito daga kicin hannunta riƙe da jug na kunun gyaɗa.  Ta zuba wa Hajja shi ma ta sa Baba Saude kawo kofi ta tsiyaya mishi. Wannan ne ya zaunar da shi, sha yake yi amma hankalinsa na ga Haulatu dake kwance, kunun ma ta ce ta ƙoshi da sha.  


Hajja duk ta damu sai lallaɓawa take don ta samu ta sa wani abu a cikinta.


"Ni youghurt nake so."


Ta faɗi a hankali yanda Hajjar ce za ta ji, Hajja ta ce.


"To anya akwai shi a firij? Sai dai fura. Kin ji wai yagwat za ta sha."


Ta ƙarashe da maida zancen ga Umma. Umma ta taɓe baki.


"Tsirfa ne fa irin na Haulatu, ko an kawo ni na san ba lallai ta sha ba."


Jin haka Sadauki ya miƙe. 


"Umma in sha Allahu za ta sha. Bari na je zan aikomata yanzu ba jimawa. Ta sha maganin kafin nan ko kan zai sauka tunda ta ci abinci ɗazu ku ka ce."


"Yauwa Sadaukin Alhaji. Allah ya yi maka albarka."


Tuni ya fice, Umma kuwa ta dubi Haulatu. 


"Sai ki tashi ki sha maganin, Allah yasa kar ki ba shi kunya ya kawo ki ƙi sha."


Ta miƙe zaune jikinta a sanyaye, ledar maganin ta janyo daga saman tebur ta buɗe ta shiga ɓallowa. 


Aikuwa can ba jimawa sai ga saƙo daga Sadauki, Najeeb ya kawo. Leda ne na manyan robobin youghurt sai kuwa wata ledar daban na gashin kifi mai dankali da sauce a gefe. Ita kanta ta yi mamakin yanda ta ci sosai, kusan rabin kifin nan sai da ta cinye shi a cikinta, youghurt din ne ba ta sha ba wai tsoro take ji kada ta kutirce, an ce ba a son haɗa nono da kifi lokaci guda, Hajja dai dariya ta yi. 


Wayarta take kallo tana duban lokaci ko Sadauki zai kira ta da labarin yanda suka yi da Alhaji Tasi'u sai dai shiru, ga Umma ta hana ta fita ko'ina, ita kanta ba ta jin za ta iya fitar duk da cewa kan nata ya bar ciwo hakanan zazzaɓin ya sauka sai rashin ƙwarin jiki. Ƙarfe bakwai da mintoci ta ji wayarta ta ɗau ƙara, da sauri ta zabura ta dauka har Umma dake gefe tana jan casbaha sai da ta dube ta, duban tuhuma. Sai ta ɗan waske ta saita fuskarta. Madadin Yaya Sadauki, ta ga Zaid ne, guntun tsaki ta ja gami da latse kiran. Bai gaji ba ya kuma kira, sai ta katse kiran ƙarshe ma ta saka wayar a airplane mode ganin Umma na ta dubanta. Koda Umma ta idar da laziminta ba ta ce mata uffan a kai ba ta fita zuwa falo, ita ma zaman shirun da tunane-tunane marasa kan gado ya sa dole ta miƙe ta bi bayanta. Nan ta zauna kusa da  Hajja dake kallon tashar Arewa har aka yi kiran sallar isha'i. Kasancewar ba ta da tsarki ya sa ta miƙewa ta shige ɗaki. Daga kwanciya kuma bacci ya yi awon gaba da ita ba ta farka ba sai wuraren sha ɗayan dare, nan ma Umma ta tashe ta akan ba ta sha maganin dare ba. Ta daga wayarta da tunanin ko Yaya Sadauki ya kira tana bacci, abin takaicin ta ga ashe ba ta kunna ba tun ɗazu.  


"Af, yauwa, Sadauki ya kira ni ya ce ya jikin naki, ya ji wayarki a kashe. Khaleefa ma ya kira ya ce a maki sannu. Sai Mu'azu da ya shigo kina bacci."


Umma ta ƙarashe tana tsaida idanunta kan ɗiyar don nazarinta. Sai ta ga kawai ta amsa da toh ta kauda kai, duk ta tsargu da kallon da Umman ke yi mata. Babu saƙon da ta ji ciwo irin na Sadauki, meyasa ta kashe wayarta alhalin dama ta san zai iya kira ya ba ta labarin halin da ake ciki. Miƙewa ta yi ta shige banɗaki don kama ruwa da sauya auduga. 
A ɓangaren Sadauki kuwa, ya samu tabbacin ƊanMutuwa ba ya ƙasar gaba ɗaya ya yi tafiya Dubai. Hatta da adireshin gidansa sai da aka samo mishi. Ya yi wa Alhaji Tasi'u godiya suka yi sallama. Daga nan ne ya kasa sukuni ya kira Haulatu, ba don ba ta labari ba sai domin tuntuɓar lafiyarta sai dai a kashe. Dole ya kira Umma ya ji ya jikin har tana mishi godiyar abin da ya aiko, ta ce Haulatun ta ci sosai. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba. 


***

 Momin Mu'az ce ta shigo falon sai dai har ta tsaya daga bayansa bai sani ba a dalilin ya buɗe hoton Haulatu a wayarsa yana kalla. A gigice ta daka mishi tsawar da sai da ya juyo har wayar na neman suɓucewa daga hannunsa. Ba iya tsawar ce ta firgitashi ba, har da jin magana a sama tunda bai san da shigowarta falon ba. Zuciyarta har wani tafasa ya ke yi ta nuna shi da yatsa. 


"Me kake kallo? Wace ce nake gani kamar waccan ƴar barikin marar cikakken asali?"


Ya sunkuyar da kai yana mai jin zafin kalaman Mominsa a kan Haulatun. ***

Za mu ɗora gobe in sha Allah ko ba yawa.

[08/09, 5:36 pm] Faty Lawal: *Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*


******

Fitar tsiro 33


Madadin ta ji muryar Haulatun sai ta ji ta Umma. Suka gaisa har Umma ta yi mata Allah ya sanya alheri, ta bi ta da ƴan nasiha kafin ta ce mata Haulatun ta shiga wanka ne. Daga nan suka yi sallama da zummar za ta ƙara kiranta. Kai tsaye ta shiga zagaye gidan nata cike da jin wani nishaɗi, ita dai Hindatu ita ce a wannan gida. Sai ta ji ma yunwar dake cin cikinta ya kau, da sauri ta koma ɗakinta don yin wanka ta haɗa bidiyon da za ta ɗora a duniyar Tiktok. Ko babu komai ita ma ta kai yanzu. Dama ta ɗora waɗanda ta yi a Dubai ta samu mabiya da yawa a kwanakin nan, hakanan masu sharhi a kai da nuna yabawa. A farko ta ɗauka mijinta zai yi ƙorafi sai kuma ta ga akasin hakan, bai yi faɗa ba sai ma cewa da ya yi shi dama yana son mace wayayyiya da ta san kanta. 


***

  A Katsina kuwa, da yamma Haulatu shiri take yi don zasu fita da Maama, za su yi mata rakiya gidan bikin ɗiyar ƙawarta. Ita ɗin ma zuciyarta fes sakamakon admission ɗinta da ya fito har an kammala biyamata kudin makaranta za ta karanci Political Science. Safina kuwa Accounting sai ko Radiya da za ta karanci Microbiology. Bayan babbar sallah za su fara karatun, wanda bai fi sati biyu ya yi saura ba a shiga watan sallar. 


Babban albishirin da Sadauki ya yi mata shi ne na lesson da za ta dinga zuwa duk safiyar asabar da lahadi na koyon harshen turanci da ma karatu don kwakwalwarta ta ƙara gogewa. Wannan ya sa ta ji nan duniya ta ƙara ganin girman Yaya Sadauki duk da mahaifinsa ne ya dauki nauyin karatun nasu su duka.  Sun je makarantar sun yi duk abin buƙata a jiya bayan da ya damƙa musu admission letter dinsu. Da wannan farin cikin ta wayi garin yau. 


Ta kammala shiri ta sha kyau cikin atamfarta ruwan ganye da fari, sai ta yafa farin mayafi madaidaici. Hoda da kwalli kawai ta zizara a fuskarta. Ta yi sallama da su Umma da Hajja ta fice wajen Maama. Can ta iske Radiya da Safina zaune a falo, su ma sun yi tsaf Maama suke jira. 


"Inye, ka ga ƴar jami'a." Faɗin Radiya cike da tsokana. Suka yi dariya. 


"Kai, kun ji yanda nake wani farin ciki. Ji nake kamar na jawo lokacin da zamu fara karatu."


"Ban ga laifinki ba, amma ni ba karatun ba sai ka soma ka ji duk ya fice maka a rai. Ba kamar ni mai Microbiology, naji ance da wuya fa ko?" Fadin Radiya. 


Safina ta harare ta. 


"To wane karatun ne ba shi da wahala? Kawai maida hankali za mu ƙara mu zage damtse. Kun dai ji Yaya Sadauki ya ce idan ba mu yi karatu ba toh da kansa zai cire mu kuma aure za'a yi mana."


Dariya suka yi tunano maganar tasa. 


"Tab, toh ina na ga ma lokacin soyayyar da har zan yi wasa da karatu? Sai ka na soyayya ka ke wasarere da karatunka ai. Ku dai zai yiwa kashedi. Ke mai Dr Yunus da kuma ke mai Yaya Mu'az."


Haulatu ta ƙarashe zancen nata da dariya. Shigowar Anti Mabruka falon yasa suka dube ta, kallonsu ta yi ta kauda kai gami da neman kujera ta zauna fuskarta ba walwala kamar koyaushe dai. Haulatu ta gaida ta don sai yanzu ita ta gan ta su kuwa tun ɗazun an gaisa. 


"Lafiya." Ta amsa ba tare da ta kalle ta ba. Can kuma ta ce. 


"Ina za ku je?"


"Maama za mu raka biki." Cewar Safina. Ba ta yi mamaki na yanda suna tare a wuri ɗaya amma ba ta sani ba, sam ba ta jituwa da Maama, yanzu za su yi daɗi, amma nan da lokaci kaɗan su hau sama. 


Taɓe baki ta yi ba tare da ta ƙara tankawa ba. Haulatu ta ɗan harareta kadan, ita sam matar ba ta burgeta, kawai ta ɗorawa ranta tsana da bakin cikin Maama don Allah bai kawo mata mijin aure ba, kuma ikon Allah a haka Maama ta fi ta farin jinin samarin. Ta tabbata da ba ciki guda ta fito da Maama ba, abin da ma za ta yi mata zai fi haka. 


Shigowar Maama falon tasa gaba ɗaya suka dube ta. Ta ci adonta har ta gaji da kyau, gaba daya suka dube ta, leshinta fari da golden wanda ya sha adon stones ya karɓe ta ƙwarai. Ta saka golden mayafi, idan ka kalle ta sai ka rantse ba daga jikinta su Najeeb suka fito ba saboda baiwa na kyan jiki da Allah ya ba ta. Mabruka kallo ɗaya ta yi mata ta kauda kai tsabar wani abu da ta ji ya tokare a maƙoshinta, ta hau waƙe-waƙenta na habaici. 


"Don Allah a dinga tunani in an girma a san an girma."


Daga haka ta tashi ta nufi hanyar hayewa sama. Maama ko kallonta ba ta yi ba sai ƴanmatan yaranta da ta kalla tana murmushi ta ce.


"Oya, mu je ko?"


"Masha Allah, Maama kin yi kyau sosai wallahi. Allah ya kauda idanun maƙiya."

 Fadin Haulatu tana ɗan buɗe murya don so take zancen ya shiga kunnen Anti Mabruka. Aikuwa karaf ya shiga don sai da ta juyo ta dube ta, ko kallon inda take Haulatun ba ta yi ba, sai su Safina da ke kula da irin kallon da Anti Mabruka ta watsamata. Maama kuwa ta girgiza kai kawai tana murmushi.  Sam ba ta kawo ma da wata manufar Haulatun ta faɗi ba. Don haka ta dube su ta ce. 


"Nagode ɗiyata. Ga muƙullin motar ku je ku jira ni. Bari na ga Inna."


Safina ta karɓa suka amsa da toh, Haulatu ta bi Maama ta gaida Innar dake lazimi,  ta gane gaisuwa ce hakan yasa ta ɗan gyaɗa kai tana mata murmushi, daga haka ta fito ta bar Maama can. Mahaifiyar su Maama ce, matar Baba Dakta da suke kira da Inna, tana daga ɗakinta dake ƙasa, sam ba ta da hayaniya ta samu matsalar kunne ga matsalar ciwon ƙafa da take fama saboda shekaru da suka ɗan tura. Wannan yasa zai wahala a gan ta a falon idan an shigo kusan koyaushe tana ɗaki, Baba Dakta nan yake shigowa su sha hirarsu, wani lokacin kuma takan fito. 


Safina tuni ta buɗe motar ta yi zaman dirshan a mazaunin Maama, Radiya a gefenta hakan yasa Haulatu ta shige gidan baya. Safina ta daki sitiyari.


"Kai! Mota fa ta yi a rayuwa, inama karatun nan da zamu fara kowaccenmu tana da motar kanta." "Sai ki bari yayyunmu ma su mallaka tukunna." Faɗin Radiya. 


Haulatu tana jinsu ta yi murmushi kawai. Radiya ta dube ta. 


"Kai Haulatu ɗazu fa saura ƙiris ki jazamana. Ni nasan da biyu ki ka yiwa Maama addu'ar nan."


"Ashe kin kula kema? Kinga kallon da Anti ta watsamata? Ai wallahi ni dai na sani gaba ɗaya ta tsargu. Kuma ita ma dai ta ɓatan rai, ya za'a yi mutum ya girma amma bai san ya girma ba fisabilillahi. Jiya fa a gaban su Yaya Najeeb ta yiwa Maama rashin kunya wai don ta shigo falo ana kallo ta sauya tasha. Maama ta yi magana don me ba za ta yi kallon a falon sama ba ta bari a kalli abin da kowa ke so a ƙasa. Shi ne fa ta yi wurgi da remote din ta ce toh Uwata Maijidda zo ki dake ni. Maama ba ta ce mata komai ba, Yaya Najeeb kamar za su yi magana amma sun san Maama ba za ta so haka ba dole suka shanye. Yanzu fa wannan Justice din mai neman auren Maama, kar ku so ku ga yanda Anti ke kushe shi. Har zuwa ta yi ta samu Baba Dakta ta ce wai neman mata yake yi, ita ma ya taɓa yi mata zantukan banza a baya. Da Baba Dakta ya bincika ashe ƙarya take, ita fa kawai ta kasa sakawa zuciyarta dangana cewa aure lokaci ne kuma idan tana da rabon yi, za ta yi."


"Uhm, Allah dai ya kyauta. Amma ni dai ba zan juri ta yiwa Maama a gabana na ƙyaleta ba." Faɗin Haulatu ranta duk ba daɗi. Ta tsani ta ga ana wulaƙanta babban mutum, ko ya aka ce wane ya girmeka, to ita ta fi son ka ba shi girma musamman ma idan ya riƙe girman nasa. Suka bar zancen ganin Maama ta fito. 


***

  Bayan sallar magriba, Daddy Ridwan yana zaune a falonsa suna hira da Momi Nuratu. Wayarsa ta yi ƙara ya duba sunan mai kiran. Sanata Hashim ne, abokin karatunsa tun a can baya, an jima ba'a tare kafin su dawo su cigaba da zumunta. 


Momi Nuratu ta ɗan dube shi kafin ta ɗauki remote ta rage sautin talabijin. Gaisawa suka yi sannan Sanata Hashim ya nemi jin ko yana da lokaci gobe zai shigo gidan su yi wata ƴar magana. Daddy ya ɗan yi mamaki amma sai bai kawo komai ba face alheri, ya ce masa ba damuwa. Nan suka tsaida lokaci kan zai shigo nan wajensa ƙarfe sha biyun rana. Koda suka yi sallama ya dubi Momi Nuratu. 


"Sanata Hashim ne zai shigo gobe ya cemin. Ya na son mu yi magana ne."


"Toh, Allah ya sa mu ji alheri."


"Amin."


Ta ɗan sauke ajiyar zuciya. 


"Ni ko daman ina ta son yi maka wata magana."


Ya dube ta a nutse. 


"Na'am, ina sauraronki."


"Shi yaron nan, ba za ku yi mishi magana kan ya fiddo matar da zai aura ba?"


Ya yi murmushi, ya sani sarai Sadauki ta ke magana a kai, amma sai ya ce.


"Wane yaron ki ke magana?"


Ta ɗan harareshi da wasa. Ya yi dariya. 


"Oh, wai ɗanki Abeed? Na yi wannan tunanin, abin da ya sa ban ce komai ba har yanzun, na fi so ya kammala ginin gidansa a nutse daga nan ko mene ne sai a yi. Kin ga hakan kamar zai fi. Ko kin masa zaɓi ne?" Ya ƙarashe fuska a sake. 


Ta girgiza kai kawai . Dama ta sani ba zai ɗauki zancen da ƙarfi ba, ita kuwa ta gaji da wannan kiraye-kirayen wayar da iyayen ƴan uwa ke yi mata ana gwada cusa kai a wurinta don yin haɗin gida. Sam ba ta da ra'ayi ko buri akan Abeed da ya wuce ta ga yau ya samu macen kirki da ta san darajar kula da miji da girmama iyayensa. 


Ji ta yi Daddy ya riƙo yatsun hannunta hakan ya maido da hankalinta gareshi. 


"Kar fa ki damu kanki Nuratu, aure shi lokaci ne.  Abeed namiji ne, ki bar shi ya bi komai a sannu. Yaro ne mai hankali ya kuma san me yake yi. Tunda ki ka ga iyayenmu ba su matsa ba, sun yarda akwai dalili ne. Ke dai matsayinki ta Uwa gareshi, kar ji taɓa gajiyawa da yi mishi addu'a. Na san dai kin matsu ne ki ga jikanki, toh in sha Allahu za ki gani."


Ta ƙwace hannunta za ta miƙe don jin nauyin zancensa na ƙarshe, ya kuwa riƙe ta ta dawo jikinsa yana dariya. 

 

***

 Ɗan Mutuwa ya dubi Sanata Hashim bayan ya cire wayar daga kunne suka yi dariya. Sanata ya ce. 


"Shikenan fa, ai dama na ce maka komai ya zo da sauƙi, abokin karatuna ne shi kuma ko ba komai ana haɗuwa a wasu wuraren akan gaisa. Yanzu dai ka ga kenan dole kwanan ya kama ka a garin nan."


 Ɗan Mutuwa ya nan ɗan girgiza ƙafa ya ce. 


"Dole zan kwana kam, kuma daman da niyyar kwanan na taho duk da ba haka na nunawa Amary ba. So nake na kashe wannan wutar na maida Na'imatu ɗakinta, ni ta ɓangarena ba ni da matsalar komai don na tsara duk wani abu da ya dace da zan tunkari ƴan uwan nata da shi."


Sanata ya jinjina kai.


"Hakane, amma ina fatan ka sanar a gida?"


Idan suka ce gida ga junansu, suna nufin can ƙungiya wajen Uban Dodo, sukan yi amfani da kalmar gida a wasu lokutan don yin ɓadda kama da kuma sirrantawa tunda yanzun suna zaune ne a falon saukar baƙi dake gidan Sanata Hashim din.


"Tuni ma na sanar, an dai ce kar na yi da zafi-zafi, idan na yi da zafi to fa kwaɓa za ta yi ruwa. Zamu bi a sannun sai mu ga abin da ya turewa buzu naɗi."


Suka yi dariya. Sai da suka ci abinci, dama ba maganar sallah don sun shafe ta a babin rayuwarsu, daga nan suka yi sallama da juna inda Ɗan Mutuwa zai wuce hotel ya kwana washegari ya zo su je. 


***

 WASHEGARI....

***

KU YI HAKURI IN SHA ALLAHU GOBE ZAN MUKU POSTING...

[08/09, 5:37 pm] Faty Lawal: 35


A hanya shiru babu wanda ya ce uffan sai can ya dube ta. 


"Kina jin yunwa?" 


Ta gyaɗa kai don dagaske yunwar take ji, rabon ta da abinci tun ƙarfe tara na safe. Aikuwa ta ga kai tsaye madadin ya yi gida, ya zarce da ita wani haɗaɗɗen restaurant, kamar ta yi magana sai kuma ta fasa. Sadauki ya yi musu order na abinci, su biyu kawai a teburin. Sai ta ji wani irin nauyi da kunyarsa ya kama ta. Ta ɗaga cokalin za ta kai baki, sai ta ga kawai ita ya zubawa idanu da wani irin kallo ga murmushi saman fuskarsa. A ransa babu abin da yake ayyanawa sai dadi da farin cikin da za ta shiga idan ta ji batun rabuwar Umma da Ɗan Mutuwa. Ya san babu wanda zai kira balle ya neme su a waya tunda ya sanar da Umma da Hajja kar su damu zai je ya ɗauko ta suna tare. 

A hankali ta maida cokalin ta ajiye tana ɗan gyaran murya. Ya sauke ajiyar zuciya. 


"Sorry, na hana ki cin abinci ko?"


Ta girgiza kai. 


"Bismillah, daure ki ci mu tafi."


Daga nan ya yi bismillah ya soma cin nasa. Ganin ya maida hankali sai ta fara ci ita ma sai dai ba ta wani ci sosai ba don duk a takure take ga rashin sabo da hakan tsakaninsu. 


"Kin ƙoshi?" 


Da sauri ta gyaɗa kai. 


"Ba abin da kika ci Haulat."


Ta ɗan yi narai-narai da fuska.


"Allah kuwa na ci Yaya, na ƙoshi kuma."


Ya girgiza kai.


"No, ban yarda ba. Ki ƙara sai mu tafi."


Wayarsa da ta yi ƙara ne ya sanya shi fadin Ina Zuwa sannan ya miƙe. 


Ita kuwa ta ƙara abincin don dama zamansa a wurin ne ya hana ta cin, kafin ya dawo ta ci ya fi loma biyar don ba laifi ya ɗan jima. Shi kuwa a ɓangarensa har ya kammala zai shigo ya ga ta maida hankali tana ci sai ya gane nauyinsa ne ya hana ta ɗazun wannan dalilin yasa shi komawa baya ya ɗan tsaya don ba ta dama. Can da ya ga alamun ta kammala ya ƙaraso bai ko zauna ba ya ce su tafi. Ta dauki robar lemunta ta yi gaba tana jira ya ƙaraso. Can ya fito, ta saci kallonsa, kai Yaya Sadauki ya haɗu ba ƙarya, sam ba ta ga laifin su Jannat masu bori a kansa ba. Tunowa da Jannat din ta ji wani abu mai ɗan ɗaci  a maƙogwaronta sai ta yi tunanin ƙila saboda sun taɓa samun saɓani yasa ta jin haushinta. Amma ba don komai ba. 


'Da ace ki ga Jannat tare da Yaya Sadauki ba za ki ji komai ba?' Wani ɓangare na zuciyarta ta jefamata tambayar daidai sadda ta buɗe gaban motar ta shiga, haɗaɗɗen turarensa ya bugi hancinta, ta saci kallonsa lokacin da ta rufo motar. Hankalinsa na ga ribas ɗin da yake yi da motar yana kallon side-mirrow, ta bi kwantaccen sumar kansa da ido kafin ta kai duba ga cikar halittar da Allah ya ba shi wanda ya amsa sunan namiji kasancewar tshirt ce jikinsa a yanzu kalar ja da wandon jeans blue. Allah ya kyautata halittarsa, hakanan kuma ta soma kula da yana da ɗabi'u masu burgewa. Ganin zai juyo da sauri ta kauda kai ta maida ga kallon gefen windon tana ji kirjinta na dukan tara-tara. Kai! Ai ba su ma dace da Jannat ba, ita ɗin ma ta san ya fi ƙarfinta. Haka tunaninta ya ba ta. Sai kuma ta koma jin haushin kanta, to me ma ya kai ta wannan duka lissafe-lissafen alhalin babu gurbi na soyayya a rayuwarta? 


"Thinking of me?" 


Abin da ya fito daga bakinsa ne ya sanya ta dubansa da sauri, ya kuma yi murmushi ya kanne mata ido guda sannan ya maida kallonsa kan titi. 


"Just joking." 


Ya ƙara furtawa, ta sauke ajiyar zuciya duk sai ta bi ta tsargu don haka ta kama kanta daga barin tunanin da ta ba shi matsayin na wofi marar amfani. Sadauki kuwa tunaninsa na ga maganar da za ta tarar a gidan, ya so ƙwarai ya yi mata batun kafin ma su ƙarasa gudun kar a faɗamata a lokaci guda ta tashi hankalinta, sai kuma ya yi tunani ya ga kamar zai fi kyau ta ji daga Ummanta hankalinta zai fi kwanciya ta kuma fi samun nutsuwa idan tana da tabbacin dagaske babu inda Umman ta tafi ta bar ta. 


Ya ɗan ja ta da hirar yanayin karatun don ya ji ko tana fahimta, ta amsa mishi, sai dai ya kula ta kasa sakin jiki da shi har a sannan wannan ya sa bai takura mata ba ya ƙyale. Har suka isa ba su ƙara wata magana ba sai ma kiransa da aka yi yana ta magana a waya game da harkar kasuwancinsu har suka iso gida ta yi lamo ta ma kasa fiddo wayarta balle ta ji wane ne ke kiranta har sau uku. 


Bayan sun iso za ta fita a motar ta yi mishi godiya har ta zura ƙafa ya kira sunanta da sigar da ya haifar mata da jin wani sanyi da kuma nutsuwa a zuciya da kwakwalwarta. 


"Na'am." Ta amsa tana mai dubansa. 


"Take care please. Babu bawan da Allah ba ya jarabta, babu jarrabawar da addu'a ba ya maganinta. Kin ji ko?"


Ta kasa gane dalilin wannan zance, sai dai kalaman sun shige ta ainun, don haka ta sauke ajiyar zuciya. 


"Toh Yaya, nagode."


Ya girgiza kai. 


"Ba godiya tsakaninmu."


Ta ɗan dube shi, ya yi murmushi sai ta mayar masa da martanin murmushin kafin ta fita ta rufe motar tana jin wani dadi da annashuwa a zuciya, duk da ranar da ake tsulawa a garin da kuma zafin da ya ziyarce ta lokaci guda sakamakon ta fito daga raɓar AC na mota, hakan sam bai katse mata nishaɗin da take ji a rai ba. Daƙyar ta kwaɓi zuciyarta ba ta juya don sake duban Yaya Sadauki ba. 


***

Babu kowa a falon ƙasa, Baba Saude ma tana daga kicin tana aiki don haka kai tsaye ta haye saman fuskarta dauke da wani murmushi da annashuwa na musamman, a falon saman ma ba su nan, ta san watakila saboda lokacin sallah ne, kowannensu ya shige daki ya yi duk da wasu lokutan ma a falon suke yi. Sai dai tana shiga ɗakinsu da sallama ta hango Hajja zaune gefen gado kamar tana yiwa Umma nasiha da tausarta, ita kuwa tana daga gefe zaune fuskarnan ta yi ja. Koda suka haɗa idanu da Umma sai da Haulatu ta ji ƙirjinta ya buga. Da sauri ta ƙarasa har jakarta na zamewa ta faɗi ta dafa hannun Umma. 


"Lafiya Umma? Hajja wani abu ya faru?"


Umma ta girgiza kai tana ɗan murmushin yaƙe. Hajja kuwa tuni ta soma magana. 


"Ba abin da ya faru sai alheri Haule, yau addu'ar da muke ba dare ba rana Allah ya karɓa. Ya kawo karshen auren wancan azzalumin da mahaifiyarki."


Sai ta yi saranda don ita ta mance wane ma azzulumin da kuma wani batun auren Umma sai kuma lokaci guda ta tuna. 


"Wai Mijin Umma? Ya mutu ne?"


"Uhum, ina fa, Ɗan Mutuwa bai mutun ba, kwanan bai ƙare ba. Har nan gidan ya shigo ya furta sakin ƙwarara har uku rak!"


Mamaki sosai wannan karon Haulatu ta ji, kafin ta ƙara wata tambayar Hajja ta shiga warware mata zare da abawa, hawayen farin ciki suka sulmiyo daga idanun Haulatu, ta rungume mahaifiyarta. Baƙin ciki ko damuwar da suke tunanin za ta yi sai suka ga ko alamarsa babu duk da dai ta danne ainahin damuwar a ƙasan ranta. Kowace ɗiya za ta so yau a nuna mata mahaifinta a mutumin kirki, ta yi mishi kyakkyawan zato da tunanin zai shiryu koda ba sa tare, sai dai da ƙaryar da ya zo har ma da kudaden da ya mallaka a yanzu wanda ko shekara ba'a rufa ba ya tabbatar mata nata Uban ba zai fasa halinsa ba duk muninsa kuwa. Murnar rabuwar Umma da mutum irinsa ya shafe wannan damuwar nata. Tana kuma da yaƙinin yanda a baya bai ci galaba a kansu ba, gaba ma babu abin da zai taɓuka. 


  "Umma shi ne ki ka yi kuka har fuskarki ta sauya? Don Allah kar ki ƙara zubarmasa da hawayenki. Kansa ya yiwa ai."


Faɗin Haulatu kafin ta miƙe zuciyarta wasai don ji take kamar an raba ta da wani nannauyan dutse. Hajja ta bi ta da kallo tana fadin "Yauwa ƴar albarka, ke dai ki nusar da mahaifiyarki. Duk ta bi ta saka ranta a damuwa."


Haulatu ta yi murmushi tunano da kalaman da Yaya Sadauki ya yi mata wanda a lokacin ta yi musu kallon marar dalili. 


Umma kallonsu kawai take yi. Ita ta san Hajja ta fahimci damuwarta saboda ga duk mai hankali ya san mutum irin Ɗan Mutuwa ba mugu ne kuma babu tsoron Allahn da zai yi sanadin dakatar da shi ga aikata wani mummunan abin, shi ne babban dalilin Hajja na tausarta da ƙara yi mata nuni da babu abin da zai faru. Tabbas ta sani, yanzun ma addu'a ce ta yi nasara a kansa har ya zo ya yanke igiyar aurenta uku dake kanta, ta kuma sani a gaba ma addu'ar ce za ta yi tasirin da in sha Allahu ba zai cutar da ita da ɗiyarta ba. Damuwarta me zai yi? Wane matakin zai ɗauka? Ta san shi a zaman shekara da shekarun da suka yi da juna, mutum mai kafiya da shegen taurin kai wanda babu gurbi na yafiya a zuciyarsa kwata-kwata. Ai shi ba ma ya yafe laifi sai ya yi ramuwa a kai. Ga kuma mamaki na wannan uban kudin da ya tara da take da tabbacin ba halaliyarsa ba ce, ko ta wace hanya ya bi ya tara? Gefe ɗaya kuma tausayin aminiyar ƴarta ta ji, haƙiƙa ta jefa kanta a hannun baragurbi wanda nan gaba za ta yi dana sani. 


"Ke Na'imatu, ki fita idona na rufe. Wato duk ɓaɓatun da nake yi ashe ya tashi a banza? Ina nunamaki gabas kina tafiya yamma? Tunanin uban me ki ke yi da nake ta magana ki ka yi shiru?" 


Maganar Hajja ta maido Umma duniyar da ta bari na lokaci, Haulatu wacce ta fito daga banɗaki tana gyara zaman hannun rigarta da ta naɗe don yin alwala ta dubi Umma a raunane ta ce. 


"Don Allah Umma ki cire komai a ranki, abin fa mu godewa Allah ne. Hajja kusan kullum ina yawan kama ta cikin dare tana addu'a tana kuka. Ni na san kuma addu'arki ce Allah ya amsa ya kawo mana waraka har gida." 


Daga nan ta saka hijabi ta shimfiɗa darduma ta bar Hajja na ɗorawa daga inda ta tsaya. 


***

 BAYAN KWANA BIYU...


KANO...

 

A yau ce ranar zuwa taronsu na ƙungiya wannan ya sa ya kasa yin wani baccin kirki ba don komai ba sai don ɗoki da ya ke yi da ma ƙaguwa da ya yi ya je su yi magana da Uban Dodo don a san matakin ɗauka game da Na'imatu. Ya rantse ba zai bar rayuwarta ta zauna cikin aminci ba har sai ya salwantar da ita, ya kuma aika mugun abu wanda zai hana ta sakat a duniyar da ta zaɓa madadinsa. Har garin saurin ya fice taro ya mance bai  fesawa Hindatu hodar da ya saba shaƙa mata ba mai sa bacci. Ita kuwa ƙarfe biyu da mintoci na dare ta farka daga bacci don yin fitsari. Ganin ba ya gefenta ta yi tunanin ko banɗaki ya shiga don haka ta ɗan zauna tana aikin murza idanu gami da jiran ya fito ta shiga, gajiya da zaman ya sa ta fice zuwa banɗakin dake falo ta yi ta dawo, har ta kwanta na ta ji alamun fitowa daga banɗaki ba sai hakan ya sauya tunaninta, to ko dai ba ya ciki ba? Ta miƙe da sauri ta hau buga ƙofar, jin shiru ta bude, babu alamun mutum, ta fito ta rufe gami da fita zuwa sashinsa. Nan ma wayam, ga dai kayansa na bacci da ya saka ɗazun ya cire su ya bar su a saman gadon, bandakinsa ma ta leƙa ba ya nan. Kamar mahaukaciya haka ta shiga duba dukkan ɗakunan gidan sai dai ba ta sauka ƙasa ba saboda tsoro. A ƙarshe ta dawo ɗakinta ta fiddo wayarsa ta kira nan ma a kashe. Ta yi saurin buɗe labule ta leƙa farfajiyar gidan, motarsa da ya fita da ita ɗazun, ba ta nan.  


"Na shiga uku." Ita ce kalmar da ya fito daga bakin Hindatu yayinda wani tsoro da firgici suka mamaye zuciyarta lokaci guda. Ina Alhaji Ibrahim ya tafi toh? Ita ce tambayar da ba ta da amsarta.

[08/09, 5:37 pm] Faty Lawal: 34


Cikin dare misalin ƙarfe uku da mintoci, motsin Umma ya farkar da Haulatu daga bacci. Tana zaune saman darduma ta ɗaga hannuwa cikin yanayi na ƙasƙan da kai tana addu'a tana hawaye sosai. Sai ta ji ba dadi, ta ƙara yin lamo cikin lumtsetsiyar katifarsu, haƙiƙa ta san mahaifiyarta akwai abin da ke damunta kwanaki biyun nan, ko hira ake da ita sai ta cilla duniyar tunani har sai an taɓa ta ko an yi mata magana da ƙarfi. Hajja ta yi ta faɗa na don me za ta dinga jefa zuciyarta cikin damuwa, ta maida hankali ga islamiyyar da take zuwa zai fiye mata. 

Ta yi ta juyi kafin ta ji ita ma baccin ya fice mata a rai don haka kawai sai ta tashi ta nufi banɗaki. Jin motsinta yasa Umma saurin ɗauke hawayen fuskarta, ita ma ɗin sai ta kauda kai tamkar ba ta gani ba. Alwalar ta yi ta shimfiɗa darduma ta yi raka'a biyu sannan ta yi addu'a ta shafa. Tana zaune tana salati, babu wanda ya cewa kowa komai a cikinsu, gyangyaɗin da Haulatu ta soma ne ya sa Umma tashinta da ba ta umarnin ta kwanta kafin a kira sallah. Ba musu kusa ta miƙe ta koma makwancinta. 


***

Washegari tun safe ta ke jin jikinta a sanyaye, a ranar za ta soma zuwa lesson amma ji take kamar kada ta tafi. Sai da Umman ta yi ta magana kafin ta iya miƙewa daga inda ta yi karin kumallo ta koma ɗakinsu don kimtsawa tunda ƙarfe goma na safe ne zuwa karfe daya. Duka-duka awa uku ne, bayan ta yi shirinta cikin doguwar riga na yadi mai adon fulawoyi ruwan madara da ja, ta yafa jan mayafi. Ƴar ƙaramar jakarta da ta saka littafi da bironta ciki sai waya ta rataya a kafaɗarta na dama. Koda ta fito Hajja ta dube ta. 


"Yauwa Haule, ko ke fa. Ke ce fa kika karaɗe kunnuwanmu da murnar soma zuwa karatun nan amma ɗan awannin da za ki je ki yi ki goge a turanci ya na neman gagararki? Maza Hauleta ɗiyar albarka jeki, tun ɗazu Gali ya zo, ke kawai yake jira ya kai ki."


Ta ɗan yi murmushi, ta yi sallama da Umma sannan ta nufi ƙasa. Ƙarar wayarta ne ya sa ta ciro ta daga cikin jaka tana amsa addu'ar Allah ya tsare hanya da Baba Saude ke mata. Sunan Yaya Sadauki ne a fuskar wayar. Ta ɗaga da sallama, ya amsa sannan ta gaida shi. 


"Lafiya lau, are you ready?" Ita ce tambayar da ya jefa mata. 


"Yes. Na fito ma yanzu zamu wuce."


"No, ban ganki ba, ki fito, ni zan kai ki. Ina son magana da Malamar ne."


Ta ɗan yi mamaki don shi ne a jiya ya ce Gali ne zai kai ta yasan wajen amma yau kuma ya sauya ra'ayi? 


"Ba ki ji ba?" Ya katse mata tunani. Ta ɗan numfasa. 


"Toh, ga ni nan."


Daga nan ya katse kiran. 


Ya dubi Mu'az dake tsaye a gefensa fuskarnan babu walwala. Duk wata hira da suke yi sai ya fice a ransa. 


"Are you okay?" Ya tambaye shi. Mu'az ya ɗan yi yaƙe. 


"Yes."


Girgiza kai Sadauki ya yi.


"Ban yarda ba, ka faɗamin meke damunka? Kwanakin nan ka chanza gaba ɗaya. Ba wannan zolayar, ba wasa da dariya. Tsaya ma, yaushe ka fara min ɓoye-ɓoye?"


Sadauki ya ƙarashe da mamaki, shi kuwa Mu'az sai ya kauda kai daga Sadaukin ya maida ga Haulatun dake nufo su. Kwalliyarta ta masa kyau a ido, sai kuma tunawa da furutan Mominsa ya sanya shi kauda kai daga dubanta yana jin sabon radadi, to gwara ma ya fidda rai a kanta, ko ba don kalaman Momin ba, ita kanta uwar gayyar ba sonsa take ba, ta kuma furta masa. 


"Wacce ka ke jira ta fito. Bari na je sai kun dawo." 


Bai ko saurari me Sadauki zai ƙara cewa ba ya yi gaba, ya kula da yanda ita ma Haulatun ta haɗe girar sama da na ƙasa ganin Mu'az ɗin. Ta ƙaraso daidai lokacin da shi kuma Mu'az ya fice. 


"Akwai abin da ya haɗaku da ɗan uwanki?"


Tambayar da ya watsomata kenan bayan ya harba motar saman kwalta sun soma tafiya. Ta ɗan dube shi, hankalinsa na ga tuƙi. 


"Wane ɗan uwana?"


"Mu'az."


Ta ɗan maida kai gefe.


"Aa, babu komai."


"Ok." Shi ne abin da ya ce kawai daga haka bai ƙara uffan ba. Can kuma wayarta ta yi ƙara, ta fiddo daga jaka, yana kula da ita sai dai bai iya ganin sunan mai kiran ba, ya ga dai ta katse kiran kuma ta saka a flightmode, ya ɗan waiga ya ga yanayin fuskarta ta ɗan sauya. Sai ya ji ransa ya sosu, kawai sai ya kawo ko ya makara ne wani ya mishi shigar sauri? Watakila ma faɗa ta yi da masoyinta shi ne dalilin ƙin amsa wayar a yanzu. Ba ya son yin katsalandan ga rayuwarta, kar ta ga kamar ya takura mata wannan dalili ne ya sa ya shanye bai nemi jin ba'asi ba. 


 Malamar tana da kirki, ta karɓe su hannu bibbiyu don dama akwai sanayya tsakaninta da  Sadauki, sai da suka ɗan tattauna da shi sannan ya dawo ga Haulatu dake tsaye tana kallon ajin wanda ƴan tsiraru ne a ciki, har da masu aure, sai dai duka mata ne ma, a ido ma ba su fi a ƙirga ba. Ta dube shi, ta kasa jure irin kallon da yake bin ta da shi ta kauda kai. 


"Shikenan, sai an tashi?" 


Ya furta a ƙasa-ƙasa, yana ji kamar zai tafi ya bar zuciyarsa ne. Ita ma sai sallamar ta shige ta, ta ratsa jikinta, ba wani hira suka yi ba ko a tahowar, amma ta ji dadin hakan a ranta, ta gyada kai a hankali tana duban dogayen yatsun ƙafafunsa. 


"Please kalle ni kaɗan mana." 


Da mamakin abin da ya fito daga bakinsa ya sa ba ta ma san ta ɗago ɗin ta kalle shi ba. Wani murmushi ya jefamata sannan ya soma ja baya.


"Thank you. Wish you all the best. Ki kunna wayarki ki saka a vibrate, kar a kira ba ki sani ba." Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bishi da kallo ranta na mata daɗi kafin maganar Malama Ruƙayya ya maido ta cikin nutsuwarta. Da murmushi ta dube ta. 


"Oya, shiga ko?"


Ta fadi tana nuna mata hanyar ajin,  ba musu ta shiga. Sallama ta yiwa abokan karatunta sannan ta ƙarasa can gefe guda bayan wata ta zauna, kai tsaye jakarta ta buɗe ta ciro wayar gami da bin umarninsa wajen kunnata da maida ta vibrate mode. Daga haka ta maida hankali yayinda Malamar ke ba ta umarnin gabatar da kanta. Babu laifi ta miƙe ta yi kokari, inda ta kuskure kuma aka yi mata gyara, abin da ya burgeta, babu wanda ya yi dariya ko nuna wani yanayin na daban wannan ya ƙara ƙarfafa mata gwuiwa. A na darasin idan ta tuna murmushin da Sadauki ya jefe ta da shi, sai ta ji murmushi ya suɓuce mata. 


'Wai meke damuna?' Da kanta ta watsawa kanta tambayar, ba shiri kuma ta ɗan saita fuskarta, ya dace ta bar tunanin Yaya Sadauki hakanan tunda dai ba wani abun ke tsakaninsu ba. Ita ba ta soyayya, kawai ɗabi'unsa, kallonsa da komai yana jefa zuciyarta cikin shauƙi. 


***

 A ɓangaren Sadauki kuwa, haka ya isa gidan yana jin zuciyarta wasai. Da ace kullum zai kasance tare da ita bai kuma san ya zai ji ba. Kai tsaye ɓangarensa ya nufa don tura wasu saƙonnin a email, bai kammala ba sai wuraren sha ɗaya da rabi, ya nufi falon Daddy,  ya tarar da shi zaune ya kammala kari har ya yi wanka ya shirya.  Bayan sun gaisa ya ce.


"Fita za ku yi ne?" 


Daddy ya girgiza kai yana duban lokaci. 


"A'a, baƙi zan yi ne. Sanata Hashim ne zai zo kawomin ziyara."


Abin ya ɗan ɗaurewa Sadauki kai. Sanata Hashim kuma? Ya san dai ba wani kusanci suke da shi da Daddyn ba, toh wani abun ne ya tashi da ya tuna da Daddyn nasu? 


Sallamar Momi Nuratu ce yasa suka dube ta suna amsawa. Sun riga sun hadu da Sadauki tun safe da zai fita kai Haulatu, ta dube shi.


"Aa, har ka dawo kenan? Ƴar makaranta tana can." 


Ya shafi suma yana murmushi kaɗan tuno masa da Sahibarsa da aka yi sai kuma ya basar. 


"Eh."


"Masha Allah. Yallaɓai an kammala haɗa komai, an kai falon."


Ta maida akalar zancen ga Daddy dake lura da ɗansa yana murmushi. Ya dube ta shi ma. 


"Masha Allah, Allah ya yi albarka. Wace ƴar makarantar da kike magana?"


"Oh, Haulatun Hajja ce fa. Lesson ta soma zuwa kafin su fara karatu. Wai saboda harshenta ya goge da turanci da ma wasu darussan."


Daddy ya jinjina kai.


"Hakan dabara ce. Ni na jima ban gan ta ba ma."


Momi Nuratu ta yi ƴar dariya. 


"Ai kam dai nan ɗin ma ba kullum take shigowa ba, shi ne rannan da suka zo karɓar shaidar admission ɗinsu, nake mata tsiya, nace ta mayar da ni tamkar wata surukarta ba uwa ba, ba ta shigowa a gaisa." 


Sadauki ya ɗan dubi Mominsa kafin ya sauke kai don jin wani nauyi. Daddy kuwa ya yi murmushi. 


"To wayasani ko hakan ne? Abeed me ka ce?" 


Ai da sauri ya miƙe. 


"Amm..Daddy bari na je wurin Baba Alhaji, ya kira ni a waya yana nemana."


Momi Nuratu ba ta fahimci zancen ba, ta ga dai ɗan nata ya ji kunya har ya fice da sauri, shi kuwa Daddy ƴar dariya ya yi nasu na manya. Ta dube shi.


"Ban fa gane yaren da ku ke yi da ɗan naka ba."


Shi kuwa waya ya dauka ya yi kiran Sadauki akan kar ya jima ya zo yanzu ya ta ya shi tarbar baƙi sannan ya maida duba ga Momi Nuratu yana mai amsa tambayarta. 


"Ki ka sani ko surukar taki ce?"


Ta ɗan yi jim cikin sanyin jiki amma ba ta ce komai ba. Wayar Daddy ta yi ƙara ya duba, ganin Sanata Hashim babu ɓata lokaci ya ɗaga gami da sanyawa a kunne. Sun gaisa ya sanar da shi ga su sun shigo farfajiya, nan ya ce ga shi nan fitowa. Dama Maigadi ya san da zuwansu daga bakin Daddy wannan dalilin ne ya sa suna zuwa ya buɗe ƙaton ƙyauren dake a can baya ɓangaren Daddy Ridwan ɗin ba na can gidan gaba ɗaya ba. Koda suka fito a mota, Daddy tuni ya fito wajen, su biyu ne. Da Sanata Hashim sai Ɗan Mutuwa da yake baƙon fuska wurin Daddyn. Nan aka yi musabaha fuska a sake sannan ya ba su umarnin shigowa ciki, shi kuwa Ɗan Mutuwa bin sa da kallo ya yi, ko ba a fadi ba akwai kamanni na jini tsakaninsa da Na'imatu. Suna ƙarasawa falon bayan an zauna ne kuma aka ƙara gaisawa da hirar bayan rabuwa. Har suna jajantawa juna rashin da aka yi kwanaki na wata tsohuwar alƙaliya kuma abokiyar karatunsu. Shi dai Ɗan Mutuwa na zaune yana jin su don ya matsu a zo wurin. Sai can aka ɗan yi shiru Daddy cikin baza kunnen sauraron da me Sanata ya zo. Sanata Hashim ya gyara zama ya ce. 


"Amm..Alhaji Ridwan, na san ba ka san ko waye wannan mutumin da muke tare da shi ba ko?"


Daddy ya ƙara duban Ɗan Mutuwa duba na nutsuwa da tattara hankali sannan ya maida ga Sanata yana jinjina kai. 


"Gaskiya ne, yau na fara ganinsa ma ina tunani."


Sanata ya girgiza kansa. 


"Ba tunani ba ne, hakan ne yau ka fara ganinsa. Sunansa Alhaji Ibrahim, mijin ƴar uwarka Na'imatu, mahaifin Haulatu."


Waɗannan zantukan su ne suka yi dirar mikiya a kunnuwan Sadauki wanda ya sanyo ƙafa guda a falon, sallamarsa ta maƙale a fatar baki lokaci guda ya sanyo kai sosai, ya yi daidai da miƙewar Daddy tsaye shi ma ransa a tsananin ɓace. 


"Ashe yana da kunyar da zai zo gabanmu? Cemin za ka yi Ɗan Mutuwa ba Alhaji Ibrahim ba."


Daddy ke zancen ransa na suya, Sanata cikin sauri ya tari numfashinsa. 


"Haba Alhaji Ridwan, abin bai kai zafin haka ba, don Allah ka koma ka zauna ka ji da abin da muka zo. Shakka babu duk wani abu da ku ka ji daga bakin Na'imatu gaskiya ne sai dai akwai rashin fahimta a wasu wuraren. Sai kuma sharrin asiri wanda aka yi domin shiga tsakaninsu da matarsa. Don Allah ka zauna zamu warware muku zare da abawa."


Daddy ya girgiza kai. 


"Aa Sanata, ba ni kadai ya dace na ji da me ya zo ba, ya kamata ƴan uwana da ma iyaye su san da zuwansa da kuma abin da za ku ce."


Daga haka ya dubi Sadauki dake tsaye ya na ƙarewa Sanata da Ɗan Mutuwa kallo, shi mutum ne wanda da kallo kaɗai yakan gane ƙarya ko gaskiyar mutum, jikinsa ya ba shi maƙaryata ne na gaske, babu ɗaya daga kalaman Sanata Hashim da suka yi tasiri a zuciyarsa. 


 Daddy kuwa umarni ya ba su akan su zo su je can wurin Baba Alhaji a tattauna a can, ko ta kan liyafar da aka shirya musu bai ƙara bi ba. Su ɗin ma ba shi ne a gabansu ba face fatan haƙansu ya cimma ruwa. Ɗan Mutuwa na kula da kallon banzan da Sadauki ke watsa mishi don ko arziƙin gaisuwa ba su samu daga gareshi ba tun da ya ji ko waye. Bai yi ƙasa a gwuiwa ba shi ma ya bi bayan su Daddy ɗin. 


Alhaji na zaune a falonsa sai ga Daddy ya shigo, bayan sun ƙara gaisawa karo na biyu ya ce masa tare yake da mijin Na'imatu ɗiyar Hajja. Alhaji kansa ya sha mamakin yanda Ɗan Mutuwa ya iya takowa ya zo wajensu. Nan ya kira Baba Dakta a waya ya shaida masa. Hakanan ita ma Hajja aka ce ta zo tare da Umma sai dai su din ba su san dalilin kiran ba. 


***

 Umma ta dubi Hajja kirjinta na duka. Ba dai mafarkin da ta yi na wai Ɗan Mutuwa ya zo ba ne zai tabbata? 


"Hajja, lafiya wannan kira haka?"


Hajja ta taɓe baki tana gyara zaman gilashinta. 


"Ina fa lafiya, ko wani abun ne ya faru idan mun je ma ganewa idanunmu. Ni kaina na yi mamakin wannan kiran na Yaya Usman. Alheri ne in sha Allahu."


Ta ƙarashe tana sa ƙafa a waje, ita ma Umma ta bi bayanta tana ambaton sunayen Allah a zuci hakan ya haifar mata da nutsuwa. 


 Suna ƙarasawa Hajja na shiga ta bi bayanta da sallama a bakinta ita ma. Ɗago kan da za ta yi, suka yi ido huɗu da Ɗan Mutuwa, kallonsa take ido waje nan da nan bakinta ya ɗauki rawa ta kasa magana balle ta motsa daga inda take tsaye a bakin ƙofa. Shi ma kallonta yake, ta sauya ta yi kyau gaba daya ta zama kalar ƴan gayu.

[08/09, 5:37 pm] Faty Lawal: 36


Wani wawan ƙara Uban Dodo ya saki kafin ya zaro ido ya dakawa Ɗan Mutuwa dake durƙushe a gabansa tsawa mai firgitarwa. 


"Kai! Ai mu ba'a zuwar mana nan da wasa! Me na ce maka? Ban ce ka bi komai a hankali ba?! Ka san irin ranar da Na'imatu za ta yi maka a gaba?! Shi ke nan, yanzu ka sake ta! Har abada kuma ba za ta dawo gidanka ba! Dama na faɗamaka! Idan ba ka bi a sannu ba za ka yi nadama."


Gumi ya tsirfowa Ɗan Mutuwa, ya sani ba nadamar rabuwa da Na'imatun ake nufi ba don yana sonta, sai don wani babban muƙami da girma da Uban Dodo ya hango masa samun shi nan gaba muddin bai rabu da ita ba. Uban Dodon bai sanar da shi wannan labarin ba sai a haɗuwar da suka ƙara yi a wannan daren. 


"Tuba nake Jagorana, a yafemin. A taimake ni a haskamin wata mafitar." 


"Ƙarya kake yi! Ni Uban Dodo ba na magana biyu. Tun da har ka rabu da ita, wannan rabo wuce ka. Abu na gaba, ina maka albishir da cewa matarka na ɗauke da juna biyu, wanda ya kasance mallakinmu ne. Ranar da abin da aka haifa ya fito duniya, ko wanka bamu yarda a yi mishi ba, ka kawo mana shi har mabiyarsa. Wannan alƙawari ne da ya zame maka dole ka cika mana."


Da girmamawa ya amsa da toh ya yi godiya kafin ya bar gaban Uban Dodon wani ya maye gurbinsa da na sa kalar buƙatar. 


Koda suka fito a hanya Ɗan Mutuwa sai huci yake furzarwa na takaici ya ma kasa magana duk da irin ruwan masifar da Hajiya Adama ke surfawa wai meyasa bai ji shawararta ba ya kwantar da kai har ya samu ya ƙara shawo kan Na'imatun? Ta ƙara da faɗin.


"Ni jikina ya ban tunda har ka ji Uban Dodo ya ce ka bi komai a sannu, toh dama akwai abin da ya hango. Yanzu shikenan, watakila ma rashin sa'a da baƙin jini za ka yi kiciɓus da shi a harkokin siyasar da ka ke son tsunduma saboda rashin Na'imatun."


Ran Ɗan Mutuwa ya ƙara ɓaci, ya dube ta a fusace. 


"Au, kin san da hakan shi ne ba ki ankarar da ni ba sai bayan ta faru ta ƙare? Ina zan san cewa wani abin ya hangar min tunda ba saninsa na yi ba sai yanzun?"


Haj Adama ta ja tsaki. 


"Aikin gama ya riga ya gama, yanzu dai ka yi kokarin cika alƙawari da zarar lokacin haihuwar Hindatun ya yi kar ka kusa ka bari kowa ya raɓe ta,  kuma ka zuba idanu a kanta."


Sunan Hindatun da ta ambata ya tunatar da shi bai fesa mata hoda ba. Ya ɗan bugi sitiyari.


"Kash, kin sa na tuna fa. Yau garin sauri na fitowa mu haɗu ban sumar da ita ba. Ina da tabbacin za ta iya farkawa koyaushe cikin daren nan ta bincika ko'ina da zummar nemana."


Ta ƙara jan tsaki karo na biyu. 


"Wannan kuma matsalarka ce. Sai ka san me za ka yi. Tun farko ai sai da na shawarceka da koyamata ɗan korawar nan, da tana yi ko yaya ai da wataƙila yanzun ta kai Habasha."


Ya jinjina kai. 


"Ni ma ina son ta iya harkar nan, sanadinta mu samu customers. Kin ga idan ta koyawa wasu matan musamman wadanda suke cikin damuwa da tabon ɗa namiji, za su dinga sadaukar da kuɗaɗensu wajen siya. Ba ma su kaɗai ba, ina son har matasan ƴan mata su tsunduma wajen siya, yanzu samarin sun fi ba da haɗin kai yanda ya kamata. Waɗannan duk ƙananun matsaloli ne, yanzu babban takaicina shi ne damar da ta suɓucemin sanadin wautana. Amma ba kya tunanin idan na saka wani ya aure ta kuma ya sakarmin ita ni kuma na ka na aure ta, damar ba za ta dawo min ba?"


Haj Adama ta yi dariya sosai kafin ta girgiza kai.


"Ni ban san wace irin kwakwalwa gareka ba wani sa'in, ban da wauta irin taka, waye zai ƙara kallonka a mutum a cikin zuri'ar su Na'imatu har a ƙara yarjemaka da batun aurenku karo na biyu? Kai Ɗan Mutuwa, ba fa a bariki ake wannan soki-burutsun ba."


Ya ji zafin maganganunta sai kawai ya share bai ƙara tayarwa ba, har suka isa gidanta, ita ɗin ma tun a motar ta buɗe kwalaben codein har biyu ta shanye, waɗannan sam ba su yi mata aiki a jiki yanda ya dace yanzu, zai wahala su bugar da ita ba ta dauke su komai ba sai ta haɗa da ƙwaya. Ba su yi wani sallamar arziki da Ɗan Mutuwa ba ta shige, shi kuwa ya damƙawa Maigadinta muƙullin motar sannan ya shige tasa ya fice. 


Hindatu kuwa a ɓangarenta gaba ɗaya hankalinta ya tashi, daƙyar ta jure aka yi sallar Asubahi sannan ta fito wajen masu gadi da tambayar inda mijinta ya je? Nan suka ce ba su da masaniya, haka ta koma ciki duk ta ruɗe sai kuka, ganin abin zai mata yawa ne ta soma kokarin kiran Mominta kenan ta ji ƙarar hon ɗin motarsa. Ai da sauri ta yi wurgi da wayar ta fito a guje, yana shigowa ya wuce ta fuskarnan a murtuke ya nufi ciki. Jikinta a sanyaye ta bi bayansa har ɗakinsa da ya shiga ya hau fidda kaya. 


Ganin babu fuskar yin wata tambayar yasa ta ja jiki ta fice ta koma na ta ɗakin tana hawaye. Koda gari ya yi haske tarr bai fito ba, da ta leƙa ma ta ga ya bararraje yana baccinsa har da munshari don haka ta ja masa ƙofar kawai. 


Sai wuraren ƙarfe huɗu na yamma ya tashi, tana ta son ta tayar da shi domin yin sallar Azahar amma tana shakkar kada ya rufe ta da faɗa.  


Tana zaune bayan ta kammala cin jellof rice din da Bayarabiyar ƴar aikinta mai kula da ɓangaren girki ta yi. Ta hango shi ya sauko daga bene,  ya yi wanka, kai tsaye inda take wajen cin abinci ya ƙarasa, madadin ɗazu da fuskarsa ke a kacame, wannan karon ya saki har da sumbatarta a goshi kafin ya ja kujera ya zauna yana fadin. 


"Madam, sannu."


Ta yi murmushin yaƙe. 


"Yauwa. Fatan ka tashi lafiya?"


Hankalinsa na ga duba wayarsa don ganin waɗanda suka kira shi tun safe, ya amsa mata kafin ta miƙe ta jawo faranti ta shiga zuba masa abinci. 


Sai da ta ga ya maida hankali wajen ci ta ɗan yi gyaran murya ta ce. 


"Jiya na tsorata da ban ganka ba. Na ma yi zaton ko wani mummunan abu ne ya faru."


Ya ɗan taɓe baki yana fadin.


"Uhm uhm, ko kusa. Dama na san za ki damu. Wani cikin abokaina ne ya kira ni a waya ba lafiya gidansa shi ne fa na je. Uwargidansa ce don ya sanar mata batun zai ƙara aure ta nemi kai shi lahira. Toh yanzu dai case din yana hannun jami'an tsaro. Shi kuma mun kai shi asibiti don ta yanke shi a gefen ciki amma an ci sa'a wuƙar ba ta shiga ciki ba. Sam na mance da na kashe wayata, da ɓacin ran wannan jahilcin na wasu matan na dawo gidan ɗazu. Ki yi hakuri na san na tada maki hankali."


Har zuciyarta ta yarda da tatsuniyarsa, sai a lokacin ne kuma ta ji wannan tsoro da fargabar da ta shiga ma tunanin inda ya je ta kau, sosai ta saki ranta har da taya shi jimamin wannan abu. Daga nan dai komai ya wuce kamar bai faru ba. Shi kuwa Ɗan Mutuwa har wani murmushin cin galaba ya yi, abin da ke sosa ransa yanzu bai wuce na fansar da ya ke son dauka a kan Na'imatu da ɗiyarta ba. Nan da nan zancen Sadauki na ƙarshe ya faɗomasa a rai, Hindatu aminiyar Haulatu ce? Ai kuwa nan ne hanya mafi sauƙi ta samun lambobinsu. Don haka ya umarce ta da ɗauko masa robar tsinken fitar da nama ko wani abin a tsakanin haƙora idan ya maƙale (toothpick) a saman teburin tsakiyar falon sama. Ta kuwa miƙe ta bar wayarta wanda tuni ya san mabuɗin tun zamansu a Dubai. Ya shiga laluba sunan Haulatu sai dai bai gani ba, ya koma na Na'imatu nan ma ya rasa, ya kasa gane wane sunan ta saka, ga shi dai ba ƙwarewa a waya sosai ya yi ba. Jin za ta sauko sai ya wayance da buɗe ma'adanar hotuna ya shiga kallo. Koda ta ga wayar a hannunsa sam ba ta ji wani abu, ba ta da abin ɓoyo tunda ya san tana tiktok da su instagram. Bai kuma taɓa hana ta ɗora hotuna da bidiyo ba. Mominta kuwa sun fi yi waya akan magana ta whatsapp. 


Ya miƙa mata wayar yana karɓar robar ya zari tsinke ɗaya ya dube ta.


"Ke km kamar ba ki da ƙawaye ko? Ban taɓa jin wata ta ce za ta zo maki ba sai dai makwafta masu shigowa."


Hindatu ta yi dariya lokacin da take tattara farantan. 


"Ni kuwa ke da ƙawaye, sai dai gaskiya aminiyata ɗaya ce. Haulatu, amma ta bar garin ita da mahaifiyarta da jimawa."


"Meyasa?" Ya ƙara tambayar yana dubanta a tsanake ba tare da ya maida hankali ga wayarsa dake ƙara ba, ƙarshe ma ya katse kiran.


Hindatu sai ta ji ba za ta iya fitowa ta ba shi labarin rayuwar ƙawarta ba, ta zaɓi ta ɓoye aibunsu don haka ta ce.


"Uwar ce suka rabu da baban shi ne ta koma wajen ƴan uwanta."


Ta zaɓi ta yi mishi ƙaryar da ba ta da masaniyar gaskiya ce a yanzun. Shi kuwa ɗan murmushi ya yi, wato yana yiwa Yarinyar kallon sokuwa ashe tana da wayo? Lallai ya yarda ba ta san shi ɗin waye ba. 


"Kuna waya?"


Ta jinjina kai.


"Muna waya har lambar Ummanta gare ni."


Fuska a sake ya ce. 


"Amma kuwa watarana ya kamata ki kai mata ziyara. Ni na san za ki so hakan."


Ai kuwa ta washe haƙora ta dube shi.


"Dagaske?"


Ya jinjina kai yana ƴar dariya. 


"Eh mana. Ai kin ce aminiyarki ce, duk abin da kike so kuma ni ma ina sonsa."


Ta kuwa rungume shi cike da jin dadi, ya yi dariya. Ta sake shi.


"Na kuwa gode sosai, ni na san Umma da Haulatu za su yi murna da gani na."


"Hakane, sai dai ban taɓa ji kun yi waya ba. Faɗamin gaskiya Bebi, ko ba ki da lambobinsu ma."


Ta ɗan turo baki a shagwaɓe ganin yanda ya ƙarashe zance cike da zolaya. 


"Allah dagaske nake fa muna waya da su, kalli fa ko sati bamu yi da magana da Umma ba."


Ta fadi tana bude wayarta gami da lalubo lambar Umma wanda ta yi saving da My 2nd Mom ta nunamasa. Har wata ajiyar zuciya ya sauke na jin dadi, ya mike yana dariya da fadin.


"Yanzu kam na yarda kuna waya. Bebi bari na je na dawo, maza ɗaukomin turare na ƙara fesawa, saman ne bana son komawa." Da murmushi ta amsa da toh sannan ta juya tana wani rangaji ta nufi matattakala. Tana bada baya kuwa ya dauki wayar ya shigar da lambar Na'imatun don yanzun shi ya fi buƙata ba na Haulatu ba. 


***

 Katsina...


Da tsantsar mamaki dauke a fuskar Malama Safiyya take duban ɗan nata dake tsugunne a gabanta yana russunar da kai. 


"Ka ce me? Haulatun Hajja ka ke so? Zaidu ka san me kake faɗa kuwa?"


Zaid ya kasa ɗago kai ya dubi mahaifiyartasa, zuwa lokacin soyayyar Haulatu ta na neman illata shi, sanadin yawan tunani ya soma samun matsala a harkokinsa na aiki da ma zamantakewarsa da matarsa Jalilah. Ya kai munzalin ko a mutu ko a yi rai, komai ta fanjama fanjam, ya ji ya gani zai juri dukkan wani abu da zai biyo baya. Zai shanye zagi da ma maganganun da zasu biyo bayan fitowar zancen nan. Don haka ya zaɓi yin shiru madadin ƙara jaddada abin da ya fadi, hakan zai sa Mahaifiyarsa ta ƙara fahimtar iyakar gaskiyar abin da ya faɗamata, kamar yanda ta saba fahimta a shirunsa. 


"Ba zai yiwu ba, ka gaggauta fidda ta a ranka. Ko daga yanayinka kaɗai, na fahimci irin zurfin da ka yi a kan haka, sai dai ka sani cewa, ni dai Safiyya ba ni da idanun da zan dubi ƴan uwana ko iyayena na isar da saƙon ka garesu. Ai idan da kunya ma, ba ka fara ba Zaidu. Duka ba ma wannan ba, ita yarinyar ta san da wannan zance?"


Zaid wanda kalaman Malama suka jefa shi cikin firgici da tashin hankali wanda nan da nan ya haɗa gumi ya girgiza kai. 


"Ta sani sai dai ba ta ba ni goyon baya ba."


"Ai dama ba za ta bayar ba, ko an fadamaka za ta kasa samun labarin abin da ka shuka a baya? A'a Zaidu, kar ka sake, kar kuma ka fara. Ni dai babu hannuna cikin wannan zancen. Ka rufa ma kanka asiri ka dauke idanunka a kanta. Ka bar gini tun ran zane."


Daga nan ta miƙe fuskarta babu ɗigon fara'a ta tsallake shi ta wuce zuwa ɗakinta. Zaid ya kasa ko motsi, idanunsa suka kaɗa. Dama ya sani, zai fuskanci sama da hakan, kamar kuma yanda ya yi wa kansa alƙawari, zai jure har ya cimma burinsa. Don haka ya miƙe cikin ƙarfin gwuiwa bisa shawarar da ya yanke na yin zancen da Maama. 


***

 A can babban gida kuwa, shirye-shiryen babbar sallah kawai ake yi, Haulatu sosai take farin ciki babu ma kamar idan ta juya ta ga walwala da annashuwar mahaifiyarta ya dawo har ya ninka na baya. Takan yi hamdala a zuciyarta. Zuwa lokacin ta ɗan samu sa'ida daga yawan kiran da Zaid ke yi mata har ma da turo saƙonni sai tunaninta ya ba ta cewa ya gajiya ne. Shi kuwa Mu'az ta kula ma yanzu babu abin da ke haɗa su face gaisuwa. Ba ya ko jan ta da hira kamar koyaushe. Hatta Umma sai da ta tambayi ba'asi, aikuwa ta sanar da ita komai. Umma ba ta ce uffan ba duk da a ƙasan ranta ta ji daɗin rashin ba sa fuskar da Haulatun ta yi, ko ba komai ta fi kaunar su tsira da mutuncinsu. Sam ba ta kaunar abin da zai ƙara haɗa su da Momin Mu'az. 


Ranar Alhamis ana gobe za'a fara azumin goman farko na Zhul-Hajj. Kasancewar babu islamiyya, Radiya da Safina da kuma Haulatu suka shirya don ziyartar Maimuna jikar Hajja ɗiya ga Haj Hadiza don su duba ɗiyarta dake fama da malaria. A hanyar fita daga babban gate zuwa inda Gali Direba ke jiransu a waje suka ga Zaid ya fito a motarsa. Da sauri Haulatu ta kauda kai ta cigaba da tafiya yayinda Safina da Radiya suka gaishe shi ganin ya nufo su. 


"Noor." 


Jin sunan da ya ambaci Haulatu da shi har yake bin ta a baya duk da ta ƙi tsayawa ballantana ta gaida shi ya sa Safina da Radiya kallon juna baki sake kafin su maida kansu. 


Haulatu kuwa ranta ya ɓaci, fuska ɗaure ta dube shi bayan ya shiga gaba ya hana ta nufar gate. 


"Lafiya?" Abin da ta furta kenan. Zaid ya ɗan numfasa, rabon da ya gan ta ba zai ce ba. Ta ƙara kyau da haske. 


"Idan na aikomaki saƙo ba kya reply, kin ji ni shiru, ba ki damu da sanin halin da nake ciki ba. Rashin kaunar ta kai a yanke alaƙa koda ta zumunci ne?"


Ta dube shi a fisge ta kauda kai, ya ɗan rame. 


"Sauri muke yi, Malam Gali yana jiranmu."


Abin da ta furta kenan cikin bagarar da wancan zancen nasa ganin su Safina sun ma fice daga gate din zuwa waje. Duk sai ta ji ta tsargu, wato Yaya Zaid ya shirya yi mata tonon silili, abin da take ɓoyonsa yake son bayyanawa duniya a yanzu. 


"Ba wannan zancen nake son ji ba Noor...""Please suna na Haulatu. Kar ka ƙara kira na da wata Noor."


Ta na kai wa nan ta ƙara yunƙurin tafiya sai dai ya kuma dakatar da ita ta hanyar riƙe gefen mayafinta. Ta fisge mayafinta. 


"Kar ka ƙara taɓa ni Yaya Zaid. Na ce maka ka fita hanyata amma na ka ke yi ka shigemin hanci da ƙudundune. Da alama ka shirya daɓawa kanka wuƙa, shikenan mu zuba, ga fili ga mai doki."


Ta na kai wa nan ta banka masa harara ta fice. Sam ba ta ganinsa da wani girma ko kaɗan a yanzu. Kallon mutum mai mugun son kansa ta ke mishi. A motar duk yanda ta yi zaton jin wani abu daga Safina da Radiya ta ga ba haka ba, sun share batun kamar ba su kula da komai ba, sai ma hirar duniya da suke yi suna kallon tiktok su na gulma. Ganin babu mai yi mata zancen a cikinsu sai ita ma ta saki jiki ta watsar da zummar daga baya za ta fayyace musu komai idan sun dawo. 


Sun samu tarba daga wajen Maimuna, dama ita ba ruwanta kamar ba Haj Hadiza ce ta haife ta ba. Ta bambanta da Ihsan da Fahima. Yarinyarta guda mai sunan Hajja da ake kira Husna. Ita ke fama da ƙyanda. Gidanta tsaf, mijinta ma'aikacin gwamnati ne. Daidai gwargwado asirinsu a rufe, sun sha hira da dariya. Ta yi musu girkinta mai dadi sun ci sun yi nak. Sai bayan la'asar suka yi shirin tafiya, tamkar kada a rabu, har bakin ƙofa ta yi musu rakiya Husna na ta kukan sai ta bi su ta je wurin Hajja. Sai da dabara sannan ta haƙura. 


***

 Zaid kuwa wannan karon ma Hajja ba ta wani sakar masa fuska ba, suna gaisawa ta kunna rediyonta ta na jin shiri. Umma ce dai ta sakar masa sosai amma duk jikinsa a sanyaye ya miƙe ya fita da zummar ƙarasawa ciki. Bayan tafiyarsa Umma ta dubi Hajja. 


 "Hajja don Allah ki yi hakuri haka ki yafewa yaron nan. Ni tausayinsa nake ji. Gaba daya ya kasa samun sukuni, ke kuma duk sadda ya shigo ko ya kira ba kya wani sakar masa. Tun da dai abu ya wuce mai afkuwa ta afku ba shikenan ba? Sannan mutum fa ba ya aurar matar wani."


Hajja da tun soma maganar Umma ta rage sautin rediyon dama hararar Umman take tana jira ta kai aya kafin ta tanka. 


"Na'imatu kenan. Ke dai ki kalli mutum kawai. Amma ni tsakanina da Zaidu, hum. Na dai yi shiru. Wa ya fadamaki ya wuce kuma? Toh idan ba ki sani ba ki buɗe kunne ki ji ni dakyau, har gobe Zaituna tana mutuwar sonsa. Ni na rasa hasken fatar ke kwasarta ko kuwa wannan tsawonnasa marar ƙira kamar mace."Umma dai ta girgiza kai ba tare da ta ce uffan ba amma haƙiƙa ta ji ya soma ba ta tausayi. Fatanta Allah ya daidaita lamura komai ya wuce. 


"Ni gani nake ma wannan sunne kan da ya ke yi da biyayyar nan duk ta dole ce da sa kai, na fi tunanin ba banza ba. Watakila dai an yi dace uwarsa ta ci galaba wajen tanƙwara shi, wataƙila kuma mutuwa ce ta kusanto shiyasa ya gyara hali."


Maganar Hajja ya sa Umma dariya, ba tare da ta ce komai ba. Wayarta dake gefe ta yi ƙarar shigowar saƙo ba ta ko damu da buɗewa ba don ita dai idan har saƙo ya shigo wayarta bai wuce na kamfanin layukan dake kan wayar. 


***

Cike da mugun kaɗuwa Maama ta saki baki tana kallon Zaid. Ta ma kasa fitar da harafi ko guda ɗaya. Daga yanayin duban da ta ke masa sai ya ƙara jin babu dadi. Kada dai a nan ma ba zai samu goyon baya ba. Sallamar Sadauki ce ta sa nan da nan Zaid haɗe girar sama da ta ƙasa, meyasa bai zaɓi lokacin shigowa ba sai da ya riga shi zuwa gidan? Sadauki shi ma ganin wanda ke zaune ya maida murmushin da ya shigo da shi ciki. Hakan kuma bai sa ya haƙura ya fasa sanyo kai falon ba. Maama ta amsa sallamarsa tana duban Zaid sannan ta maida kallonta ga Sadaukin. Sam ba za ta so su ɗora maganar a gabansa ba. Zai fi ta takawa abin burki tun wuri.

[08/09, 5:37 pm] Faty Lawal: Ya ji zuciyarsa ta yi sanyi, fargabar kada ya rasa abar kaunarsa ta kau. Ko babu komai ya samu tabbaci daga harshen da bai taɓa faɗamasa ƙarya ba, wato daga bakin Maama. Ya ji duk abin da ke faruwa, a gefe guda ga zafin Mu'az da Zaid da ya ji. Maama ta miƙa masa ruwan gora mai sanyi tana murmushi. 


"Oya, ga shi nan ka sha ka ƙara samun nutsuwa. In sha Allahu Haulatu rabonka ce ka ji ko? Kai dai ka ƙara miƙawa Allah lamuranka."


Sadauki ya karɓa ya buɗe gami da yin bismillah ya soma sha. Haƙiƙa sai yanzu ya samu nutsuwar. 


Bai wani jima sosai ba ya tashi, ya ƙudirta a ransa yanzu ne zai soma yaƙi akan Haulatu, irin yaƙi na bi a sannu, ba zai yi saurin furta mata kalma ta so ba, amma fa zai yi iya yinsa wajen kyautata mu'amalarsu ta yanda ya ke fatan a hankali ta koyi sonsa. 


Momi Nuratu ta sha mamakin ganin yanayin da ya dawo mata da shi, cikin nutsuwa ta dube shi.


"Ina ka je haka? Daga magana ka sauya ka fice a hargitse yanzu kuma kamar ba kai ba."


"Ba komai Mami." Iyakar abin da ya furta kenan don ya ma rasa amsar bayarwa, shi fa har gobe yanda yake sakin jiki ya yi zantuka da Maama ba ya iya hakan da Momi Nuratu, ita ma ganin ba shi da niyyar ɗorawa daga faɗin haka sai ma murmushi da ya ɗan yi kawai sai ta rabu da shi tana miƙewa. 


"Bari na shiga ciki. An kusa ƙarasa maka, ko can wajen naka Fu'ad zai kai maka?" Ta ɗan dakata tana dubansa ya amsa da eh, daga nan suka yi sallama ganin dare ya yi, dama shi Daddy sun gaisa tuntuni.
Ita kuwa Haulatu koda suka shige ɗaki da Radiya, Radiya ta dube ta. 


"Ke Haulatu, wata magana na ji fa ta a yawo shiyasa ba shiri ki ka gan ni."


Ajiyar zuciya Haulatun ta yi cikin yanayin damuwa. 


"Ko ba ki zo ba dama na yi niyyar ***

 Washegari Umma ba ta hana Haulatu zuwa wajen Safina ba musamman da ta ji komai na irin son sa Safinar ke yiwa Mu'az. Ita ma ba ta son rashin fahimtar juna ya shiga tsakaninsu. Don haka wuraren sha ɗaya na safe duk da hadarin da ya haɗu a garin bai hana Haulatu jan Radiya da ta san gidan su tafi tare ba. Babu direba hakan ya sa madadin su koma su sanar da Hajja kamar yanda ta ce idan Gali ba ya nan su sanar mata sai kawai ta ce su nemi napep. 


Da Yaya suka soma cin karo tana zaune falo tana raba faɗa tsakanin Ahyaan da ɗan uwansa Hayat akan wai shi Ahyaan din ya ga sadda Hayat ke shan ruwa a banɗaki ya karya azumi, shi kuwa Hayat idanun sun yi kwal kwal yana afkin rantsewa Yaya shi bai sha ba. Sallamar su Haulatun ce ta katse hayaniyar, Yaya ta amsa tana dariyar yaran nata. 


"Ah ƴan ukun Maama, hala kun biyo ƴar uwarku ko?"


Suka yi murmushi. Gaishe ta suka yi ta amsa kafin su Ahyaan su gaishe su. Hayat dake kuka Haulatu ta jawo hannunsa. 


"Kai da wa?" Nan Ahyaan ya yi caraf ya hau basu labari wai Hayat ne ya sha ruwa a bandaki ya karya azuminsa. Yaya kuwa girgiza kai take don ita tsokana irin ta Ahyaan ma har mamaki yake ba ta. Koda dai barewa ba za ta yi gudu ɗan ta ya yi rarrafe ba, Dakta Hashim shi ma haka yake da son tsokana. 


  Haulatu ta sharewa Hayat idanu. 


"Yi shiru abinka, ai mantawa ka yi na sani. Kuma idan mutum ya manta ya sha ruwa, babu komai ko?" 


Ya gyaɗa kai, ta murmusa. Radiya ke tambayar Safina, Yaya ta ce.


"Tana ɗaki tun safe da ta fito ta shige wai kanta na ciwo. Na ce ma ta ajiye azumin ganin kamar har da zazzaɓi amma ta ce ita za ta iya kai wa."


Sauke ajiyar zuciya Haulatu ta yi yayinda wani fargaba ya ɗan shige ta, to kodai ta ji zancen ne? 


"Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya, bari mu shiga mu gan ta." Faɗin Radiya kenan. Suka amsa da amin sannan suka fice zuwa dakin. 


Da sallama suka shiga, tana zaune gefen gado, daki ne da ya sha adon komai pink kalar mata. Da ace a gidan take rayuwa, za ta samu kulawa da jin dadi sosai duk da a can ma tana samu fiye ma da haka, amma Dakta yana ji da yaransa, yana kuma kokarin kulawa da sauke nauyinsu dake rataye a wuyansa. A can din ma ba ya fasa yiwa Safina komai. Radiya ce a gaba sai Haulatu biye da ita, ta kurawa Haulatu idanu, tunani take wai ita ce ta yi mata irin wannan rufin? Daga yanayin kallon da Haulatu ta kula Safina na mata yasa ta fahimci komai, tabbas ta samu labari. Radiya ta zauna gefenta ita kuwa Haulatu ta ja kujera dake ajiye a gaban tebur mai fari da pink na karatu  ta zauna tana fuskantar Safina. Hannunta na dama ta kama. 


"Yar uwa, sannu. Yaya ke faɗamana ba kya jin."


Murmushin yaƙe kuma na zallar takaici Safina ta yi tana duban Haulatu da idanunta da suka cicciko da ƙwalla. 


"Da sauƙi."


Radiya ta dubi Haulatu wacce duk ta sha jinin jikinta, sai kuma ta maida duban ta kan Safina ta ce.


"Amma zazzaɓin ya sauka ko? Da kin ajiye azumin nan kin sa wani abu a cikinki ko kyanji ƙarfin jikin tunda kin ga ko azhar ba ta yi ba, kar ki wahala."


Safina ta jinjina kai kawai, lokacin tana kallon yatsun ƙafafunta sai kuma ta dubi Haulatu. 


"Na ji abin alherin da ya same ki, ashe kuma Yaya Mu'az za ki aura. Allah ya tabbatar maku da alheri."


Ɗan dafe kai Haulatu ta yi tana ambaton Allah. Ta kalli Radiya da na ta manyan idanun da su ma suke barazanar zubar da hawaye don tuni sun cicciko. 


"Kin ji wani ya riga mu sanar da ita ko?"


Jin abin da ta ce ne ya sanya Safina yin wata dariya kaɗan ta kalli Haulatu. 


"Ba ki so wani ya faɗamin ba sai dai na ji daga bakinki kenan? Haulatu kenan. Mamakin da ki ka bani bai wuce na wai ashe soyayya kuke yi da Yaya Mu'az ba, ki ka maida ni sakara marar wayo, na zauna na saki baki na yi ta amayar maki da abin da ke raina, ashe wai ke..."


Ta kasa ƙarasawa ta ciji leɓɓanta saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Haulatu wacce ita ma hawayen ta ke fitarwa ta yi saurin tarar numfashinta. 


"Na rantse maki babu komai tsakanina da Yaya Mu'az. Duk abin da ki ke tunani ba haka ba ne, yanzu ma zancen da nake maki, an kashe wannan magana."


Daga haka ta yi shiru saboda kallo na kin rainamin hankalin da Safina ke watsamata ga dukkan alamu kuma ƙin yarda da hakan ne ya jawo. Radiya ce ta karɓe zancen ta warwarewa Safina komai. Safina ta cika da mamaki, tuni dama hawayenta sun tsaya, ta kalli Haulatu.


"Amma meyasa ba ki taɓa ba ni labari ba?"


"Saboda gudun hakan, ba na so na ƙara karya zuciyarki ne. A baya kin rayu da sonsa cike da jin ƙarfin gwuiwa tunda kin shaida babu kowace budurwa a rayuwarsa, idan na fito na ce maki ya furta yana sona, ban san halin da zan jefa zuciyarki ba. Na rantse, ban ɓoyemaku da gangan ko wata manufa ba, ni na fadamaku daga shi har Yaya Zaid din babu wanda nake so. Ni karatu ne a gabana kamar yanda na faɗawa Baba Alhaji kuma ya mara mini baya. Don Allah kar ki bari saboda wannan mu samu saɓanin fahimta, na yi kuskuren rashin sanar da ke a baya, kuma ni ban taɓa son Yaya Mu'az ba, so irin na masoya, ni ina masa kaunar ɗan uwa ina kallonsa kamar Wa namiji a wurina, idan ma ba ki manta ba na taɓa faɗamaki haka Safina."


Safina ta jinjina kai, akwai sadda suke hirar kusancin Haulatun da Mu'az ta ke cewa ita tana  jindadin yanda ya riƙe ta kamar ƙanwarsa Nusaiba, ba kuma ta sani ba ko don ta tashi ba ta da wani ɗan uwa namiji ko mace shiyasa. Sai jikin Safina ya yi sanyi, wato dai Anti Jannat makirci ta so haɗawa a jiyan, so ta yi ta shiga tsakanin kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninta da ƴar uwarta.


"Amma Yaya ta sani kuwa?" Tambayar da Radiya ta watsowa Safinar kenan. Ta girgiza kai. 


"A gidan nan ban ga alamar wani ya sani ba ma, ni ɗin ma Anti Jannat ce ta zo jiya, wajenta nake ji."


Da tsananin mamaki Radiya da Haulatu suka kalli juna. 


"Anti Jannat?"


Safina ta amsa da eh sannan ta labarta musu dukkan abin da ta ce har ma da amsar da ta ba ta. Sai ga su suna dariya baki daya. 


"Kai Safina, ni wallahi kin burgeni. Ai jira nake yi kawai ku sauke zancen na rufu a kanki da faɗan yanda ki ka bamu kunya gabanta, ashe ba haka ba. Sai da na ji ƙarashen zancen na samu nutsuwa." Radiya ke wannan batun, Safina ta harareta tana murmushi.


"Ji, wai ke din da ba ki da wani faɗa har wani abu za ki iya aikatawa? Da sai Haulatu ce ma nasan yanzu zan sha faɗa da zagi."


Suka ƙara darawa. Nan fa sai ga Safina ta wartsake, ta nemi ciwon kai ta rasa, dama tun sadda ta yi bacci ta farka zazzaɓin ya sauka. Yaya koda ta leƙo ta gansu suna hirarsu da dariya, sai ta fice tana murmushi. Dama ta yi tunanin Safinar akwai wata damuwa a ranta, sai a yanzun tunaninta ya bata watakila ƴar matsala suka samu da juna yanzun kuma aka ɗinke. A ranta ta dinga bin su da addu'ar Allah ya dauwamar da zumuntarsu har jikoki, ya fito musu da mazaje nagari.


Haulatu ba su ne suka tashi barin gidan ba sai da suka sha ruwa. Dakta ma a farko cewa ya yi sai sun kwana, sai dai ba yanda ya iya tunda Hajja ta riga ta aiko Gali ya dauke su. Sun sha dai dariya kamar cikinsu zai ciwo, don idan mutum ya na tare da Dakta Hashim to fa ba zai kamu da hawan jini ba, ko ya hau ma zai sauka. 


***

 Bayan kwana biyu...


Malama ranta a ɓace ta ke duban Zaid dake tsugunne gabanta, a dazun ne Baba Alhaji ya kira shi ya ce ya yi hakuri kar ya ƙara tayar da zancen Haulatu tunda yarinyar dai ta nuna ba ta sonsa, kuma karatu za ta yi to kar ya matsa mata. Ita kuwa Malama, Hajja ce ta kira ta ta yi mata tas tace Zaid ya rainata ba shi da kunya har ya iya kallon idanun manya ya ce yana son jininta, to idan har ta isa da ɗanta, ta gaggauta taka mishi burki. Har ta ke ikrarin ba lallai Malamar ta iya hakan ba tunda ba ta tilasta mishi auren Zaituna ba, to wannan ma ba za ta iya ba. Don haka ita tana can tana jiran ranar da Zaidun zai kwaso jiki ya shigo mata gida. Maganganun dai sam ba su yiwa Malama dadi ba, ta yarda Hajja matsayinta na Uwa a gareta komai ma ta iya faɗa, kuma ba laifin kowa ba ne sai Zaid mai masifar kafiya da naci idan ya sa abu a gaba. 


"Me kuma ya kawo ka wurina yanzu?"


Wannan ita ce tambayar da ta watsa masa, dama tana son magana da shi, amma ganin yanda ya kawo kansa har ya durƙushe ta kyautata zaton wani abun zai ce. A iyakar sanin da ta yiwa ɗanta ya kasance mai kafiyar da ba ta jin haƙuri ya zo bayarwa mai nuni da ya bar maganar Haulatun. Aikuwa ya tabbatar mata da tunaninta sadda ya karya bille ya soma magana. 


 "Na yi maki laifi ne, kin ce na haƙura amma na kasa har na fiddo zancen ga Maama, sai dai ba ni na kai maganar ga Baba Alhaji ba. Ki yi hakuri, ina kaunar Haulatu, ki taya ni ba Baba Alhaji da Hajja hakuri, su bar ni na..."


"Zaidu!" 


Yanayin ɗagawar muryar da ma kaushinta ya sanya shi dakatar da zancen gami da amsawa.


"Na'am."


"Idan har ni Safiyya na isa da kai, idan na isa na ba ka umarni kuma ka bi. Koda wasa ka ƙara shiga rayuwar Haulatu sai na saɓa maka. Har zuwa yaushe ne za ka daina jazamin abin magana? An ƙare da wancan yanzu kuma ka ke neman jawo min wani? To ni ban ma amince ka yi babbar sallah a nan ba, ka tattara iyalinka ku koma Abuja."


Tana kaiwa nan ta miƙe ta bar masa falon, shi kuwa ya ji kansa ya wani irin sarawa, dama kwanakin duka ba shi da sukuni. Batun ya bar Haulatu ma bai taso ba, ya san ba zai iya wannan ba zai dai nemi hanyar da zai lallaɓa Mahaifiyarsa da ma Hajja. Haulatu kam zai bi umarnin Malama da Baba Alhaji, ba zai ƙara nemanta a waya ba. Amma haka ba wai yana nufin ya haƙura ba.


'Za ka iya jurewa?' Wani ɓangare na zuciyarsa ya watsamasa tambayar wanda ba shi da amsarta. Haka ya miƙe jiki duk a sanyaye ya bar falon. 


***

 Ana saura kwana hudu babbar sallah, Uncle Abba autan Hajja ya zo da iyalinsa Katsina. Haulatu sam ta tsani matarsa don ba mace ce mai son mutane ba, shi kuwa Uncle Abba ba ruwansa mutum ne mai son jama'a don halinsa ɗaya da Maman Zaituna, Haj Nafisa. Daɗin daɗawa ma sai ga Fahima, wai ita ma a nan za ta yi babbar sallah. Sai gaba daya ma ɓangaren Hajja ya rage yiwa Haulatu dadi, ga shi sun yi hutun islamiyya. Lesson din da take zuwa ma sai bayan sallah za'a cigaba don haka wurin Maama ko Radiya ta ke tafiyarta. Ita ma Fahima ƙafar yawo ba zama take yi ba, sashin su Sadauki take gudu abin ta dab da shan ruwa za ta ci ado ta fice. Abin dai na ba Haulatu mamaki. Ana gobe sallah kuwa, suna zaune bayan kammala shan ruwa, yinin ranar dama kowa ibada ya shiga idan ka cire Fahima mai afkin kallo a waya, matar Uncle Abba, Anti Haseena da ƴan ukun yaranta ba sa nan sun je ziyarar wata yayarta. 


Bayan gama shan ruwa Haulatu na zaune su na hira da Safina ta whatsapp, ita kuwa Fahima na gefe Hajja na jan ta da tambayar yanzu shikenan sai wata shekarar za ta sake jarrabawa amma tana amsa ciki-ciki don gaba daya ba ta so ma Hajja ke zancen nan gaban Haulatu ba, ta kula ma dariya Haulatu ke yi sai ta yi tunanin ai kawai ma da ita take. Wayar Haulatun ce ta yi ƙara, ta dan yi jim ganin sunan me kiran, Yaya Sadauki ne. Ba ya taɓa kira sai idan da kwakkwarar dalili don haka ta amsa gami da sallama, bayan ya amsa mata ta gaishe shi. Jin ta ambaci sunan Yaya Sadauki hankalin Fahima duka ya koma kanta. 


  "Idan bakya wani uzurin, ki fito ina nan parking space, ina son ganinki."


"Toh." Shi ne abin da ta ce kafin su yi sallama. Ta miƙe ta ja hijabinta da ta yi sallar magriba da shi, daga ita sai doguwar riga mai ƙaramin hannu. Ta dubi Hajja don Umma tuni ta haye sama. 


"Hajja, bari na je Yaya Sadauki na kirana."


Ta fadi ba ta ko kalli gefen da Fahimar ta ke ba, Hajja ta amsa da toh sannan ta fice. Hankalin Fahima idan ya yi dubu to ya tashi. Yaya Sadauki har kiran wayar Haulatu yake yi? Abin da tunda take ko bisa kuskure ne bai taɓa kiran wayarta ba? To ai ba ita ba, ko yayyunta ma ba nemansu yake a waya ba, sai wanda ya kira don ya gaida shi, yakan ɗauka amma kuma amsar a ciki-ciki. Ita kuwa dama koda wasa ba ta gigin kiransa, ta sani ba ya son a dinga kiransa babu dalili. 


"Ke ina magana kin lula wata duniyar,  yanzu kenan shi ubannaki aure zai maki ko kuwa haka za ki zauna jiran shekara ta zagayo ki ƙara zana shi jam din."


Fahima ranta a ɓace ta miƙe tana turo baki.


"Ni ma ban sani ba." Daga haka ta fice, bayan Haulatu ta bi jikinta har rawa ya ke, gwara ko mene ne ta gane wa idanunta.

[08/09, 5:37 pm] Faty Lawal: *LITTAFIN FITAR TSIRO NA KUDI NE. DUK WACCE TA FITAR MIN TA KWANA DA SANIN TA DAUKI HAƘƘINA. BIYA KI KARANTA HANKALINKI KWANCE. 9034973645 OPAY. IBRAHIM RUFAIDA UMAR.*

Sassanyar iskar da ke kaɗawa sakamakon wani haɗaɗɗen hadari har yana ƙugi, da ya kewaye sararin samaniya lokaci guda kuma a na zuba walƙiya, alamu ne na kowane lokaci ruwa kan iya sauka idan Allah ya ƙadarta. Hakan bai hana Haulatu takawa ba a sannu ga iskar dake ɗan kaɗawa tana ɗan manne hijabin a jikinta, wasu lokutan kuma ta yi kokarin ɗaga shi sama wannan ya sa ta zaɓi takawa cikin nutsuwa tana kare jikinta gudun kar wani sashin ya bayyana. Tun daga nesa ta hango shi zaune saman motarsa ya tanƙwashe ƙafa guda a gefe kuma wayoyinsa ne a a ajiye yana kurɓar lemun kwali na Chi Exotic a sannu-sannu. Sanye yake da tshirt ruwan ƙasa, ƙirarsa ta ƙarfi ta fito kasancewar ba dogon hannu ba ce, sam bai mishi muni ba sai ko baƙin wandonsa mai jikin cotton. Ƙafafunsa madadin ɗan silifas na zaman gida  sneakers ya sanya, ga dukkan ma alamu shigowarsa gidan kenan don motar ko shigar da ita rumfar adana motoci bai yi ba, dama kuma ya fi adana motarsa can gidansu akan nan ɗin. Tana tafe ta gama ƙare mishi kallo tsaf, shigar sosai ta haskaka shi. Ganin ya maido hankalinsa kanta ya sanya ta sunkuyar da kai, har ta ƙaraso bai iya ɗauke ƙwayoyin idanunsa daga kanta ba. Ta yi mishi sallama, ya amsa. Saukowa ya yi daga saman motar ya kasance suna tsaye da kafafunsu su duka. Cikin yanayin lumshe idanu sakamakon iska da ke kaɗawa tana kwashe-kwashe ta dube shi. 


"Yaya gani."


Ta furta tana ɗan murza idanu, ya kalli yanda hadarin ke haɗuwa, don haka ya kwashi wayoyinsa ya ce ta biyo shi. Ba musu kuwa ta bi bayansa zuwa cikin rumfar adana motoci, a nan sai suka samu sa'ida kadan daga iskar da ke kwaso musu ƙura. 


Duk wannan budurin da suke yi, Fahima na daga can gefe jikin wata ƴar bishiyar dogon yaro tana hangensu, ga dai iska na barazanar raba ta da ɗan yalolon mayafin da ta yafa a kanta. Har wasu hawaye ta ga sun taho mata, babban baƙin cikinta yanda ta ga sun jera kamar wasu masoya sun nufi ƙasan rumfa. Me za su tattauna, me ya faru? Oho, duk babu ɗaya da ta sani. 


Can kuwa Sadauki ya dubi Haulatu cikin nutsuwarsa ya soma magana.


"Hadari zai hana ni yin doguwar hirar da na yi niyyar yi."


Ya ɗan yi shiru ita kuwa Haulatu tunani ta shiga to wace kalar hira ya yi niyya din? Sai ta ƙara tsintar muryarsa. Na ji dukkan abin da ya faru a baya, don na daukesu matsayin past, ba na fatan a gaba na ji makamancinsu. Karatu shi ne babban burinki na yanzu, please ina so ki maida hankali ga abin da ki ke so domin cikar wannan muradin naki. Taya wanda kake so cikar burinsa muddin bai saɓawa shari'a ba, shi ne babban abin da ya fi kyautuwa. Da ace sun taya ki so da kwaɗayin cikar wannan buri naki fiye da son zuƙatansu, hakan zai yi min dadi. Kar ki ba ni kunya, ki nutsar da hankalinki wuri guda kuma kan abu guda. Ni dai na sani zai wahala idan kina soyayya.  Ko kina da wanda ki ke so ne da ya sa ba ki ba waɗancan dama ba?"


Ya watso mata tambayar daga ƙarshe, ita kuwa cikin jin dadin yanda ya ƙarfafa mata gwuiwa da kuma fahimtar lallai su Yaya Mu'az sun fifita lamarinsu a kan nata, ta ɗago idanunta ta kalle shi, shi ma wani irin kallo ya ke mata mai wuyar fassara, a hankali ta sauke idanunta ƙirjinta na bugu da ɗan sauri-sauri. Girgiza kai ta yi.


"A'a."


"Ko wani mai suna Abeed?" 


Ya furta yana miƙa mata lemun robar dake hannunsa, ta sa hannu ta karɓa shi kuwa ya samu damar kalle zanen baƙin lallen dake a hannunta, ga kuma ja da ta yi irin na salatif ɗin nan ya sha kyau. Ita kuwa fuskarsa kawai ta ke duba da tunanin waye Abeed don gaba ɗaya ma lissafinta ya kauce ta manta da waye mai ainahin wannan sunan don haka a raunane da sanyin murya ta amsa. 


"Allah kuwa ni ban ma san waye Abeed din ba. A ina yake?" 


Ya yi murmushi. 


 "Ƙunshin ki ya yimin kyau. Ki dinga yi kin ji?" 


Ta gyaɗa kai tana ɗan maida hannunta cikin hijab. 


"Yaya."


 Ya ji sautin muryar har cikin kwanyarsa da ya haifar masa da wani yanayin da har sai da tsikar jikinsa ta tashi. Kallonta kawai yake yi bayan ya ɗan karya wuya kaɗan, ta kautar da nata idanun. 


"Dama..um..tambaya zan yi. Waye Abeed?"


Murmushin da bai shirya yi ba ya suɓuce masa, ya ɗan shafi gefen wuyansa. Dama ya sani zai wahala idan ma ta fahimci manufarsa don haka ya dan jinjina kai.


"Ba lallai kin san shi ba, amma dai tambaya nake ko da shi ba kwa soyayya?" 


"To ai Yaya ni ban ma san shi ba fa ballantana ma mu yi soyayyar bayan ma ni karatu ne a gabana yanzu." 


Ta ƙarashe tana ɗan tura baki gami da sosa idonta na dama don tun ƙurar da ta shige mata a ɗazun ba ta fice duka ba. Ya ƙara samun damar bin ƙunshinta da kallo yana mai lumshe idanu da ambaton sunan Allah a ƙasan ransa kafin ya amsa mata.


"Na yarda. Please ki ƙara kiyayewa kin ji ko? Za ki samu wanda ya fi Mu'az da Zaid sonki, koda kuwa sunansa Abeed."


Ta gyada kai kawai tana murmushi gami da riƙe lemun gam a hannunta don ita ba ta gane ma manufarsa ba.


"Kin yi kitso?" 


Da mamakin tambayar ta gyada masa kai. Sauke ajiyar zuciya ya yi da muryar da ta bambanta da na baya ya ce.


"Jeki kar ruwa ya taɓa ki na shiga uku wajen Hajja. Sai da safe ko?"


"Toh, Allah ya tashe mu lafiya."


Ya amsa da amin kafin ta soma tafiya tana tauna kalamansa na ƙarshe, kwakwalwarta ta shiga tunanin waye Abeed? A ina ma ta taɓa jin sunan? 


'Kai, ai sunansa ne. Na tuna an ce sunansa na gaskiya Abeed.' Wani ɓangare na zuciyarta ya tunasar da ita.


Da sauri ta juyo ta dube shi, hasken fitilun da ya haska wurin tamkar rana ya haska mata kyakkyawan fuskarsa yana zubamata murmushi gami da kanne ido guda. Ta yi saurin kauda kai ta cigaba da tafiya kirjinta na faman bugu fat-fat. Wai sonta ya ke yi? Ko kuwa ba shi Abeed din ba? Madadin ta ji zafinsa a silar wannan hasashen sai ma ta ji wani irin dadi da sanyi, ta tsinci kanta da fatan inama ya kasance son nata ya ke yi? Tabbas da ta fi kowa sa'a a duniya. 


Fahima dake tsaye tana kallonta sam ita Haulatun ba ta ma kula da ita ba saboda tuni ta fara ɗan gudu-gudu sakamakon ruwan da ya ɗan soma ƙarfi. Wannan saukar ruwan sam bai damu Fahima ba asalima hawaye take fitarwa sosai. Ta tabbata ko Jannat ba ta kai ta son Yaya Sadauki ba, amma ko irin wannan matsayin da Haulatu ta samu a wajensa har yake mata murmushi ita ba ta taɓa samu ba. Tana tsaye ruwa na ƙarfi yana jiƙa mata jiki har ya shige motarsa ya fice. Sai ta bi bayan Haulatu zuwa falon Hajja.


Hajja ko damar tambayar Haulatu kiran me Sadauki ya ke mata ba ta samu damar yi ba don tuni Haulatun ta tsallake su har Umma da ta sauko a falo ta haye sama, Hajja na kiranta tana ba ta uzurin kaya za ta sauya ruwa ya ɗan taɓa ta. Da wannan ta haye ta shige ɗakinsu ta rufe. Hijabin ta soma cirewa bayan ta ajiye robar lemun da ya ba ta, kafin ta dora saman kujera na gaban dress mirrow ta hau kallon kanta a madubi tana wani irin murmushi mai bayyana fararen haƙoranta a waje. 


'Ke banza, idan kuma ba shi Abeed din ba? Ba kya tunanin wani yake nufi daban?'


Cewar wani ɓangare daga zuciyarta, to wai ma ita da ba ta ra'ayin soyayya, ta kasa gane dalilin da yasa sam ba ta jin zafi idan tana misalta Yaya Sadauki matsayin masoyi. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta sauya kayan jikinta kafin ta dauki lemun ta fito zuciyarta wasai. A falon Hajja ta yi kiciɓus da Fahima, ganinta a jiƙe ya ba ta mamaki. To ita kuwa wannan ina ta fita ta je? Wata uwar harara Fahima ta watsa mata kafin ta kauda kai tana jan tsaki ta nufi hanyar ɗakin da ta ke kwana. Taɓe baki Haulatu ta yi cikin nuna halin ko in kula don idan da sabo ta saba da wannan kallon banzan daga Fahima. Kusan ma yanda zuciyarta ta ke cike da annashuwa ba ta tunanin wata ƙaramar alhaki irin Fahima za ta yi nasarar ruguza mata. 


 Hajja da Umma babu wanda ya tambaye ta me suka tattauna da Sadauki, don gaba daya ma an duƙufa da aikace-aikace na tanadin gobe sallah. Umma za ta yi wainar masa da miyar taushe, ga kuma sinasir. Baba Saude har ma da ƙarin wata dattijuwa  suna ta aikace-aikace na shirin suya na gobe sallah. Wannan ya dauke musu hankula, ita ma ta shiga taimaka musu da aikin. Sai dai duk wanda ya kalle ta sai dai ya ga tana faman zuba murmushi, yanda ma ta ke aikin babu nunawa gajiya ko jin bacci ya sanya ɗora mata ayar tambaya sai dai ba ta ce uffan ba. 


***

 Aka wayi gari da bikin babbar sallah, dakyar Haulatu ta tashi da asuba don jiya har kusan karfe ɗaya ba su yi bacci ba. Sai dai tana yin alwala ta ji baccin ya kau, Umma tuni ta sauka ƙasa don fara aiki. Wuraren ƙarfe takwas suka yi shirin zuwa masallaci. Bayan an sauko wannan karon ba a yi wasu hotuna sosai ba adalilin aikin yanka da za'a yi. Ƴan matan ne kawai da samarin gidan sai ko yara da suka zo hutu. Radiya ta dubi Haulatu ganin sai faman ɗaɗɗaga wuya take. 


"Ke, wa kike ta nema ne wai?"


Ta sauke ajiyar zuciya gaminda yarfa hannu. 


"Wa kuwa nake nema? Kawai kewar ƴar uwata nake."


Radiya ta ɗan ja guntun tsaki. 


"Ke nima fa ina kewar Feenah, da yanzu muna nan tare ana kashe kala."


"Uhum." Amsar da ta bayar kenan. Jikinta ya yi sanyi ganin har aka watse ba ta ga ƙeyar Sadauki ba. 


 Ranar dai sun sha aiki ba laifi, don raguna biyu aka yanka a ɓangaren Hajja, ɗaya na Umma ne saƙo daga Daddy Ridwan, ɗayan kuwa na Hajja. Na Uncle Abba matarsa Anti Haseena ta tubure ita a gidan ƴar uwarta za ta yi nata aikin, Hajja sam ba ta ji zafi ba ta ba shi umarnin ya dauka ya kai mata can ɗin. Shi ne ma ransa ya yi babu dadi ga yaran ta kwashe su ta tafi da su can.  


Tun sallar azhar ta kwanta bacci ba ita ta farka ba sai da Umma ta tayar da ita don yin sallar la'asar. Haka ta miƙe tana mutsistsika idanu kafin ta shiga hamma, sai dai nan da nan ta katse hammar dalilin wanda ta gani zaune a falon yana ɗan kallonta. Ai a ruɗe ta shiga neman hularta ta rufe ƙananun kitson da aka yi mata. Tuni dama ta sauya kaya zuwa doguwar riga irin mai zuwa da mayafin nan. Baƙa ce mai taushi da aka yi adonta da golden din zarurruka a wuya zuwa ƙirji da kuma bakin hannu rigar. 


Ya kauda kai ya maida ga danna wayarsa, sai ta ga ashe ma ba shi ɗaya ba ne, ga Uncle Abba zaune suna hira ga Fahima dake gefe ta wani nutsu kamar gaske, sai ko Hajja. An jera faranti  dauke da gashin nama sai ko na masa da miya sai lemuka, ita duk sai ta ji kunya ta gaishe su sannan ta yi sum sum ta fice zuwa sama. A guje ta nufi gaban madubin ɗakin ta na kallon fuskarta, ba ta yi wani muni ba, idanun dai sun kaɗa sun yi ja hakanan sun ƙara fitowa sai ko gefen inda ta jima kwance da ya yi shatin layi layi. Amma sam babu miyan bacci. Ajiyar zuciya ta sauke duk da haka dai ba ta so Yaya Sadauki ya gan ta a haka ba. Bakin ta wanke ta dauro alwala. Koda ta yi sallar ma kasa komawa ƙasan ta yi, duk sai ta ji ta takura ga wayarta na can. Sai wuraren biyar ta iya fitowa, nan ma sai da Umma ta shigo ganinta kwance ta hau faɗan kar ta sake ta yi mata baccin yamma kafin ta iya miƙewa ta sauka. Ta ga babu kowa ma sai Hajja kaɗai da gyangyaɗi ke ɗan kwasarta. 


***

 Washegari ɗaya ga sallah suka shirya fita yawonsu ita da Radiya, Umma har gidan Haj Rabi'atu (ƴar uwar Maman Bahijja ta Kano) ta aike su da ƙullin nama. Kowaccensu ta cakare abin ta, suna tsaye suna sallama da Umma da kuma Hajja dake zaune, sai ganin mutum suka yi ya shigo da sallama. Nan da nan Haulatu ta tamke fuska, shi kuwa Zaid ya ƙaraso ciki, suka gaishe shi suka yi gaba, yana ta bin Haulatu da idanu babu ko kunyar Hajja da Umma. 


Ya gaishe da Umma, ta amsa fuska a sake tana fadin. 


"Ashe ba ka koma Abujar ba?"


Ya ɗan shafe ƙeya da ya tuno daƙyar ya lallaɓa mahaifiyarsa ta haƙura ta yarje masa yin babbar sallah a garin tare da sharaɗin da yake da tabbacin har a rai ba zai iya cikawa ba. Ya gaishe da Hajja dake faman zuba masa ruwan harara tamkar idanunta za su faɗo. Kauda kai ta yi kamar ba ta ji ba. Sai da ya ƙara maimaitawa har Umma ta karya bille ta yi magana. 


"Hajja, yana gaidaki."


"Uhum, naji ina amsawa. Ko ba Zaidu ba ne? Mai ƙyamatar haɗa zuri'a da tsatsona?"


Umma ta sauke numfashi, kai, ita kam Hajja ba ta bari abu ya wuce ta yi ta dawo da shi baya kenan dama ta ce ba su hadu da Zaid ba tun faruwar lamarin, burinta su hadu ta yi mishi tas, a zaton Umma ai shikenan tunda an yiwa lamarin tufka, ashe dai akwia sauran rina a kaba. Shi kuwa Zaid ko a jikinsa sai murmushi da ya ɗan yi. 


"Ki yi hakuri Hajja, ki yafemin bisa wannan furuci. Amma har ga Allah nake kaunar Haulatu. Ki taimaka ki yafemin abin da na yi a baya."


Wani irin guɗa Hajja ta yi kafin ta yi wani shewa da ya yi sanadin fitowar su Baba Saude daga zagayen da suke aiki, su a zatonsu ma ko wani abun ne na alheri ya samu. Ita ma Fahima da gudu har tana tsallake bene bibbiyu ta sauko tana fadin 


"Hajja mene.."


Ba ta ƙarasa ba ganin Zaid a gefe zaune, ta gaishe shi amma ko kallonta bai yi ba. A shirye yake da dukkan wani abu da Hajja za ta yi mishi ko kuma tace muddin dai kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Ai buƙatar ma je hajji sallah. Komai mai sauƙi ne idan haƙansa ya cimma ruwa. Umma dai shiru ta yi tana salati a ƙasan ranta, idan Hajja na wani abun kawai Haulatunta take haskowa a fuskarta, shakka babu a jininsu yake. Rashin barin ta kwana da halin ramuwa. Wasu lokutan tijarar iri guda ce.

[08/09, 5:37 pm] Faty Lawal: Momin Mu'az ce ta soma magana ganin Bokanyar ta zuba musu idanu ta kuma baza kunnuwa don jin me ke tafe da su. 


 "Ɗana wasu matsiyatan Uwa da ɗiya ƙadangarun bariki suka matsawa. Sun mallake shi sun hana shi sakat har yana tsallake maganata akan yarinyar. Taimakonki nake nema  ki raba ta da ɗana."


Bokanya ta yi wata dariya ta bubbuga wata bulala mai gashi irin wanda yarbawa kan riƙe a hannu kafin ta soma wasu siddabarun maganganu ta yi tsit, su dai sun zuba mata idanu kafin can ta soma magana murya a ɗage. 


"Ke Hajiyayye Lubabatu!"


Da mamaki Momin Mu'az ta dubi Mamin Khaleefa don su kam ba su sanar da ita sunayensu ba. Nan suka ƙara jin ƙwarin gwuiwa a kanta. 


"Ki sa ranki a inuwa, zan raba ta da ɗanki rabuwa ta har abada, zai tsane ta, tsana mai tsananin gaske. Amma fa sai kin yi dagaske wajen ba da makaman aiki sosai, idan ko ba haka ba sai sun yi aure sun hayayyafa ma."


A farko albishirinta ya yiwa Momin Mu'az dadi, bayanan ƙarshe kuwa duk sai ta rikice farat ɗaya.  Faɗi take.


"Mene ne makaman aikin? Na rantse maki ko mene ne shi zan aikata matuƙar Haulatu za ta fita hanyar ɗana Mu'az. A shirye nake na aikata komai."


Dariyar dai Bokanya ta ƙara yi. 


"Ke ba ki san mene ne makaman aiki ba? Toh ga su nan."


Ta fiddo wata rafar ƴan goma goma ta ajiye a gabansu, Momin Mu'az ta ƙara duban Mamin Khaleefa karo na biyu suka yi murmushi, har wata ajiyar zuciya ta sauke. 


"Af, wannan ai mai sauƙi ne. Dama ba mu tako mun zo ba sai da muka shirya, har alƙawarin ƙari nayi maki matuƙar hakan ya tabbata."


Daga haka ta buɗe jaka ta fiddo rafar ƴan ɗari biyar ta ajiye mata. Bokanya ta jinjina kai tana kallon rafar da aka ajiye mata tana ɗan washe haƙoranta da suka rine. 


"Ki sa a ranki kamar an yi an gama kenan!"


Nan zuƙatansu suka cike da walwala. Mamin Khaleefa ita ma ta shigar da nata buƙatar akan Sadauki da ta ke son ya auri ɗiyarta Jannat. Bokanya ta gama buge bugenta da kiraye-kirayen wasu irin sunaye kafin ta tamke fuska. 


"Sai kin yi dagaske don yaron ma aljanu ne da shi, zai wahala ya yi aure a duniya. Idan kuwa ma auren zai yi, toh ban hango masa auron kowa ba sai ita ɗiyar taki. Ke ma aikinki babba ne don sai na mishi turen nawa aljanun sun yi yaƙi da nasa. Wani satin sai ki dawo ku karɓi turare da garin magani wanda za ku tabbatar kun sanya masa a abinci ya ci, turaren kuwa ita ƴar taki za ta dinga shafewa a jikinta duk sadda za ta haɗu da shi. Muddin ya shaƙi ƙamshin a kofofin hancinsa ina mai tabbatar maku ya gama yawo!"


Cike da tsantsar farin ciki da jin dadi ita ma Mamin Khaleefa ta ajiye Bokanya kuɗaɗe masu tsoka kafin su tashi su tafi da zummar wani satin su dawo zuƙatansu fari tas. 


 Fitowarsu ne suka yi kiciɓus da Mabruka dake shirin shiga, sai aka tsaya kallon kallo, mamaki da firgici duka dauke a fuskokinsu. 


"Mabruka? Me ya kawo ki nan?" Faɗin Mamin Khaleefa gaba ɗayanta a hargitse. Mabruka sai tambayar ma ta ba ta dariya ta yi murmushi. 


"Hajiyar Khaleefa, ai abin da ya kawo ku shi ya kawo ni. Kya ce me ya kawo ni? Duk wanda ya zo nan ai ya san ba alheri ke tafe da shi ba face buƙatar son rai. Don haka idan ma ku na son kanku da lafiya tun wuri ku ja bakinku ku gimtse a kan ganin da ku ka yi min, idan kunne ya ji..."


Iyakar abin da ta ce kenan har da ɗan riƙe kunnenta alamar kashedi. Wurin malamin da take zuwa sam ba ta yarda da aikinsa na ci ba, dalili kenan da ta zo wurin Bokanyar nan ta hanyar wata ƙawarta. Ta wuce ta bar su da kallon juna. Sai da suka ɗan bar wurin jama'a kafin Momin Mu'az ya tanka. 


"Ke ma dai, Mabruka ina ne ba za ki ganta ba tunda ta rasa miji kuma ga maƙiyiyarta za ta yi aure? Ai sai inda ta shiga ta fita. Tunda dai an riga an gamu, to babu wani abu da zai faru. Sai mu ja bakinmu mu yi shiru."


Mamin Khaleefa ta ɗan riƙe haɓa.


"Ah, dama wa zai ce wani abu? Kare ne ya cije mu?"


Suka yi ƴar dariya.


Ita ma Mabruka, albishir kala-kala ta samu daga wurin Bokanya akan za'a fasa auren da Maama a daura da ita sannan uwa uba ma za ta hana Maama aure gaba daya. Ta ƙara da cewa ai Maama ita ta yi mata asirin da har gobe take zaune a gida ba ta yi aure ba. Wannan abu ya ƙara rura wutar tsanar Maama a zuciyar  Mabruka. Dama ta jima ai tana zargin hakan, kuma an taɓa faɗamata a wurin biye biyen malamanta, yanzun da ta ƙara samun tabbaci daga bakin Bokanya, sai ta ƙara yarda ɗari bisa ɗari hakan ne. Ita ma haka ta yi mata ɓarin kuɗaɗe har ma da alƙawarin ƙara mata fiye da hakan matuƙar auren ya tabbata da ita ba da Maama ba. Daga nan ta tashi ta bar wajen. 


***

  Daji ne ba gida gaba babu a baya, kamar yanda take gudu da iyakar ƙarfinta tana tsallake itatuwa da duwatsu, haka ita ma ƙatuwar baƙar magen ta ke tsalle da gudu don ta cimmata. A ƙarshe ta ji ta kife tana juyawa ta ga magen nan ta yi tsalle ta dira a kanta, ƙoƙarin kai mata cafka a  fuskarta kawai ta ke yi amma iyakar ƙafinta take sanyawa ta na riƙe ta tana karanto addu'o'i. Sai magen ta yi wani ihu ya jiya ta kai mta yakushi a ƙafafunta, ita kuwa ta ƙara buɗa murya ta hau karanto ayatul kursiyyu da ƙarfi kawai ta nemi magen ta rasa. Daidai nan ta farka a gigice tana mai ambaton sunayen Allah, gumi ta ko'ina ya wanke ta. Ta yi zaton abin iyakar mafarkin ne kawai, sai ɗaga ƙafa ta yi ta ga duk karta na faratunan magen nan. Ta waiga ta kalli Haulatu wacce ta yi nisa a bacci ba ta san ma inda kanta yake ba kafin ta miƙe ta faɗa banɗaki. Umma ta jima saman darduma tana addu'o'i sannan ta koma bacci tunda a lokacin ko huɗu ba ta yi ba. Abin da yake wuya ka ga ta yi, wato makara sallar asuba, shi ta yi a yau, sai da Haulatu ta tashe ta kafin ta miƙe ta faɗa banɗaki. 


 Koda wayewar gari babu wanda ta sanar da batun mafarkinta, ta san dai abu ne mai matuƙar ban al'ajabi, amma kuma ba ta ga amfanin furtawar ba balle ta ɗagawa jama'a hankali. 


  Ranar kuma ta kasance Haulatu za su fara zuwa jami'a. Wannan ma na daga cikin manyan dalilan da suka hana ta makara sallar Asubahi, kusan kullum ma Umman ke tashinta. Ta yi wankanta fes an sha hoda da kwalli, doguwar riga mai haɗe da mayafi ta saka sai ko jakarta da ta rataya. Komai sai da ta tabbatar ya yi tsaf kafin ta ɗauki facemask ta zura a gefen aljihun ƙaramar jakarta da zummar sai ta isa za ta saka. Kai tsaye ta sauko falon ƙasa inda su Umma ke karyawa tare da Hajja, Hajjar ce ma ba ta jin dadi za su je asibiti. Bayan an gaisa take ƙara yiwa Hajja sannu da jiki sannan ta yi zaman kari. Baba Saude sai tsokanarta take yi wai duka wannan kwalliyar na zuwa jami'a ne? Ta yi dariya kawai, tana kula da Ummanta sam ba ta da walwala sai murmushin yaƙe, sai da ta kasa haƙuri ta ce.


"Umma, kema ba ki da lafiya ne?"


Umman ta girgiza kai, ba ta kuma ji wani mamakin tambayar da Haulatun ta yi ba, kaf duniya babu mai iya karantarta kamar ita. 


"Lafiyata kalau, maza dai ki yi ki ƙarasa kar ki bari ƴan uwanki su yi ta jira."


Ta amsa da toh ba don ta gamsu ba, a ganinta ai yanzun duk damuwar da mahaifiyarta za ta shiga yanzu mai sauƙi ne tunda dai sun rabu da Ɗan Mutuwa. Miƙewa ta yi ta yi musu sallama gami da kallon Hajja. 


"Toh Hajjaju, sai a dawo cin gumba ko?"


Hajja ta yi mata daƙuwa murya a ƙasa ta amsa. 


"Nan da kike gani sai na kai uwarki kema na kai ki ɗakin miji."


Haulatu ta yamutse fuska.


"Taɓ, ashe kuwa za ki yi mutuwar zaune da jiran tsammani."


Daga haka ta yi gaba ta bar Hajja na mitar za ta dawo ta same ta yayinda Umma ta kalli Hajja kawai ba ta ce komai ba. Ita ina ta ga wani aure yanzu? Ai sam ita tsoron ma ƙara auren ta ke yi, amma ta kula sosai mahaifiyarta ke son nan gaba idan hankalinta ya ƙara nutsuwa ta cika watan da ya yi mata saura na idda toh ta samu miji ta yi aure. 


***

 A ɓangaren Baba Alhaji suka haɗu da Radiya, ita ma Safina ta ke jira ta kammala su taho. Ganin Safina ko kaya ba ta gama sanyawa ba ne ya ɓata ran Haulatu, ta dubi lokaci, ƙarfe tara saura ƴan mintuna. 


"Kai please Feenah, ya ci ace yanzu muna skul fa."


Yanayin murya na yanga da ƙasa ƙasa da ta yi amfani da shi ne ya sanya suka sanya dariya baki daya. 


"Inye, ka jimin yarinya da iyayi. Toh an ƙi a yi saurin, ni ji nake ma kamar na fasa zuwa fa. Duk tsoro nake ji." Cewar Safina. Radiya ta karɓe.


"To yi zamanki, kinga sai mu cewa Baba Alhaji kawai aure kike so." 


Ta kai mata duka da ɗankwalinta, sua yi dariya kafin a gaggauce ta kammala shiri, sun sani lokutan karatunsu sosai zai iya bambanta tunda kowacce da ɓangarenta. Yau ma kamar yanda Najeeb ya faɗamusu, ba lallai ne su samu darasi ko guda ba tunda a cewarsa har lokacin wasu na ta registration. Dayake can yake kuma yana ajin ƙarshe inda yake karantar business admin, lokutan da ba shi da makaranta ne suke zuwa kamfani wurin Yaya Sadauki shi da Haidar. Shi ma Haidar can yake sai dai shi ɓangaren Accounting yake. 


Aikuwa dai koda suka je ɗin, ba wani karatun aka yi ba, amma sun ɗan ƙara wayewa kan abin da kuma sanin makarantar tunda Najeeb ne ya zagaya da su da kuma yi musu bayanan abubuwa da dama gudun kar su sami matsala.


 A hanyarsu ta komawa gida ne wayar Haulatu ta yi ƙarar kira. Ganin Hindatu ya sa ta ɗagawa, suka gaisa, jin muryarta da yanayin damuwa ne ya sanya ta ba ta uzurin tana kan hanyar gida ta bari za su yi magana idan ta nutsu. A dole suka yi sallama ita kuwa Haulatu ta san ai dama Hindatu zai wahala ta rabu da matsala tunda shi ta aura. Zama da irin Ɗan Mutuwa ai sai wacce ta shirya. Ta kan ji baƙin cikin tuna shi ne mahaifinta. Sai dai ta yi imani da ƙaddara komai ma da zai faru mai kyau ne tunda haka Allah ya tsara. 


"Ke Haulatu, nikam dama ina ta so na tambayeki, Anti Zaituna kuwa tana da labarin abin da ke faruwa?"


Maganar Radiya kenan wacce ta katse tunanin Haulatun. Ta yamutse fuska don ba ta ma son a yi mata tunin Yaya Zaid. Tun da ta samu labarin tijarar da ya yi a gaban Hajja ta ji ya ƙara ba ta haushi.  


 "Ta sani mana, toh me ta ce? Kin san ai tana da fahimta, ita koda ta kira ni ta yimin zancen cewa ta yi na dage da addu'a duk abin da yake alheri ne, Allah ya tabbatarmin a rayuwata. Amma bayan haka ba ta ƙara zancen ba."


"Allah Sarki, ai fa kin san Anti Zaituna babu ruwanta. Za'a iya cewa soyayyar Yaya Zaid ma kawai ƙaddararta ce." Faɗin Safina kenan. 


Jinjina kai Haulatu ta yi don ba ta cikin yanayi na son magana. Daga haka har suka isa babu wanda ya ƙara tankawa.  Koda suka dawo gida sai wuraren yamma ta tuna da Hindatu ta kira ta a waya. 


"Kashe zan kiraki kar na ƙarar maki da ɗan katin naki." Cewar Hindatun. Ba musu kuwa ta katse kiran tana murmushi, a ranta tana faɗin Allah Sarki, da ace Hindatu za ta ga yanda take gudanar da rayuwa maikyau a nan da ta sha mamaki. Sai ta ji kamar ba ta kyauta mata ba bisa duhun da ta bar ta a ciki, duk kuwa da yanda suka kai ga aminci. Amma kuma ai ta yi ne saboda tsaro. Ba ta kai ga ƙarasa tunaninta ba, Hindatun ta kira. Suka gaisa nan ta soma magana.


"Haulatu ina fa cikin damuwa babba, na rasa ya zan yi wallahi."


Sai da Haulatu ta ji faɗuwar gaba, ta dai daure ta ce.


"Mene ne ya faru kuma Big Mama?"


"Um, ba za ki gane ba. Don Allah ya za'a yi ka dinga rayuwa da miji wanda ba ya son sallah? Wai fa gaba daya Ibrahim bai damu da ibadarsa ba. Kinga ba ya sallah kwata kwata sannan ko karatun Alkur'ani ya shigo ya tarar na kunna a gidan zai hau ni da faɗa yana nunamin shi gidansa a tsarkake ya ke, ya sanya an zo an yi sauka sama da goma don haka na bar kunnawa idan ma zan ji wai na saka earpiece. Ki ji fa don Allah? Sai abu na biyu, ba shi da wasu shaƙiƙan ƴan uwa a nan kusa, nayi nayi ya kai ni na ga koda wasu a danginsa ne ya nunamin shi da kowa, ga wata Hajiya Adama ya ce nan duniya idan ina neman yar uwarsa ta jini na same ta na gama. Toh ni gaba daya hankalina ya kasa nutsuwa. Kuma kin ga da cikin dare...."


Ƙit, ta ji an katse kiran, gaba ɗaya hankalin Haulatu ya tashi, duk da dai abubuwa ne da ba baƙonta ba ne a rayuwarsu tare da Ɗan Mutuwa, ta sani sarai sai ya ga dama ya ke sallar asubahi, shi ma a cikin gida ba ya taɓa zuwa masallaci, sauran sallolin ko ba za ta yi hukunci ba tunda a waje yake wuninsa. Amma abin ya ba ta tsoro, babu ma kamar Hindatu da tausayinta ya lulluɓe ta. Kamar ta bi bayan kiran sai ta fasa tunda ba ta san dalilin katse kiran da Hindatun ta yi ba. Kar ta haifar mata da matsala. Kwanciyarta ta gyara saman kujerar tana mai zurfafa tunani na wannan irin Uba nata a ƙarshe daƙyar ta watsar. 


***


 Kano...


 Hindatu wacce ta shagala tana waya da Haulatu, sam ba ta ji tsayuwar motar Ɗan Mutuwa ba sai ganinsa ta yi ya shigo falon, babu shiri da sauri ta yanke kiran a matukar tsorace. Idanunsa na kanta fuskar nan a murtuƙe ya ƙaraso ciki sosai. Sai da ya bi wayar da kallo sannan ya maida dubansa gareta. 


"Sannu da zuwa." Ta yi ƙarfin halin furtawa. Ya gyaɗa kai gami da cire babbar rigar dake jikinsa sannan ya nemi wuri ya zauna. 


"Hala da saurayinki kike waya ganina ya sa ki tsorata?"


Yanayin da ya yi maganar cikin nuna halin ko in kula balle kishi sai ya ba ta mamaki musamman ganin ya saki har da murmushi. 


"Saurayi kuma? Ina da aurena? Ka na mijina kana min wannan magana?"


Ya taɓe baki.


"Toh mene ne don kin ajiye mai ɗebemaki kewa idan ba na kusa? Ni sam kar ki damu ba ni da matsala dangane da haka. Rayuwarki ce, kamar yanda nake gudanar da tawa rayuwar ba na son a sanya min idanu, haka ba zan tauyeki ba kema."


Daga haka ya miƙe yana buga uban hamma don dama jiya ba gidan ya kwana ba shigowarsa kenan da yammacin wai yana da baƙi daga ƙasar waje zasu yi meeting a Hotel, kamar dai yanda ya faɗamata. 


Ta kasa magana gaba daya tamkar wacce ta haɗiyi dutse. Ƙirjinta har wani bugu yake da sauri. 


"Oh, ki sa Favour su shirya abincin mutum uku, wasu amintattun yarana na wurin aiki za su kawo min ziyara anjima da ƙarfe takwas. Sannan kar ki sake ki tashe ni a bacci don na sanki."


Daga nan ya wuce ya nufi ɓangaren ɗakinsa. Ita kuwa Hindatu hawaye ta shiga fitarwa cike da al'ajabin wannan irin watsewar. Mijin aurenta ke ba ta lasisin kula wasu samarin a waje da sunan soyayya? Wannan wane irin masifa ce ta aura? Ta yi kuka sosai kafin kuma ta tuna da saƙonsa ta ja waya ta kira Favour. Nan ta sanar da ita saƙon Maigidan kafin ta tattara kuma ta shige ɗakinta don har wani jiri take ji ga mararta da ke faman ɗaurewa ta ƙasa. Dama kwana biyun nan haka yake mata, likita ta ce ta rage sanya damuwa a ranta zuwan ƙarshe da ta yi, amma abubuwan ne sun fara shallake tunaninta. 


***

Katsina...


 Washegari kuwa koda suka je, su duka babu wacce ba ta fara karatu ba, sai dai Radiya ce ma suka yi har darussa biyu. Su kuwa haka suka cinye sauran lokacin ba a ƙara musu komai ba. 


 Ruwa kawai Haulatu ta watsa ta sauya kaya sannan ta fito don cin abinci. Tana ji Hajja da ta ɗan samu ƙarfin jikinta ba kamar jiyan ba tana ba Umma labarin rikicin da Maimuna ke ciki yanzu da mijinta akan dukanta da yake. Faɗi take. 


"Idan na dauki mataki na ce ba za ta koma ɗakinta ba sai cibi ya zama ƙari a wurin su Yaya Dakta, su bi su ce na ɗaurewa yarinya gaba ta ƙi zaman aure alhalin su ba su san irin wahalar da ta ke ci ba. Shi kuma ubanta (Mijin Haj Hadiza) tunda ɗan ƙaninsa ne sai ya rufe idanu ya ci mutuncin ɗiyarsa a kansa, tsabar tsoron uban ma da suke yi ba sa iya buɗe masa cikinsu sosai. Toh wannan karon idan Salahu ya yarda na taka na dauko Maimuna, ta bar auren kenan har abada tun da ba shi da mutunci."


Umma dai haƙuri ta ke ba Hajja tana nunamata ya fi kyau a kira a yi mishi nasiha da kuma gargaɗi akan dukan, tunda dai ai babu mai son mutuwar aure sai dole. Haulatu kuwa dake gefe tana cin abinci tana sauraronsu duk sai ta ji ta tsani mijin Maimunar da aka kira Salahu, a duniyarta duk wani azzalumin miji mai dukan matarsa ba  zai taɓa burgeta ba. Kamar ta tsoma musu baki a hirar sai kuma ta tuna hakan ba daidai ba ne, a baya dai ta sha yi, kuma ta sha ɓatawa Umma rai akan hakan. Yanzu kam ta nutsu ta bari. 


***

 Bayan Kwana biyu... Tana kwance a gado tana duba abin da aka yi musu a aji yau, gaba daya ita ba ta ma fahimci darasin ba balle ta iya aikin da malamar ta ba su, ta yanke tashi zuwa ga Fu'ad ƙanin Sadauki wanda shi ma fannin da yake karanta kenan amma yanzun shi yana aji na biyu, ta san dai za ta sha wulakanci tunda ba shiri suke ba, amma fa a kan karatun nan ta gwammace da dai ace ta ba kanta da ma Yaya Sadauki kunya, gwara ta jure cin kashin Fu'ad din muddin zai koyar da ita. 

 

 Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo ta whatsapp, kamar ta share sai dai hango sunan Sister Zaituna da ta yi ne ya sanya ta buɗe. 


"Yayana ya yi min zancenki, ya ce na yi hakuri na yafe masa laifukan da ya yi min a baya, kuma na taya shi yaƙi don ya same ki tunda wai a yanda yace na san yanda soyayya take."


Wannan saƙon mai ban haushi da mamaki da bayyana rashin tsoron Allah da kunya irin na Yaya Zaid, shi Anti Zaituna ta aikomata. 


"Na fara yarda Yaya Zaid ba shi da hankali wallahi." Ta furta a fili don ta ma kasa amsawa Anti Zaituna don haka kawai ta ja guntun tsaki ta kashe datar ta kwashi kayan karatunta bayan ta zura hijabi ta fito kai tsaye ta nufi ɓangaren su Momi Nuratu bayan  ta nemi iznin Ummanta.

Cike da tunanin rashin kai na Yaya Zaid ta ƙarasa ɓangaren Momi Nuratu. Ta kuwa iske ta a falo cikin kwalliyarta na zuwa turakar miji. Ganin Haulatun sai ta ɗan faɗaɗa fara'arta gami da amsa gaisuwarta. 


"Lafiya lau Haulatun Hajja, ya Umman taki?" 


Tana murmushi ta ba ta amsa da lafiya lau. 


"Wani abu ki ke so ne?" Faɗin Momi Nuratu, sai ta ɗan kalli inda Fu'ad da Zuhra suke kowannensu da waya a hannu amma tambayar Momi Nuratun ce ta sa su duban Haulatun wacce ita din ma aka yi sa'a ta kai duba ga Fu'ad din. 


"Dama wajen Fu'ad na zo ya koyamin wani Assignment da ban gane ba."


Nan da nan ya haɗe rai gami da zaro ido.


"Wa? Wai ni? Tab! Ai kuwa...zan koya maki."


Ya ƙarashe da abin da ba hakan ya yi niyyar faɗi ba dalilin kaifin idanun Yayan nasu Sadauki wanda ya zuba masa su, shigowarsa falon Momi Nuratun kenan daga na Mahaifinsa. Momi Nuratu ta harari Fu'ad.


"Oh, da ya ke ka ga dodon naka ai ka iya lauyance magana. Je ki ya koyamaki Haulatu."


Ta amsa da toh kafin ta juya ta gaida Yaya Sadauki wanda kwana biyu ba su haɗu ba. Koyaushe kamar ana ƙara masa kyau haka ta ke gani. Ya amsa mata sannan ya ƙaraso ga Momi Nuratu ita kuwa Haulatu ta yi wurin Fu'ad da ya ke harararta a faƙaice. Sai ta bi shi da murmushin ta ci galaba. Shi kuwa babban burinsa Yayan nasu ya bar falon ya gwabza mata rashin mutunci amma ina, su na gama magana da Momi Nuratu, ita ta yi falon Daddy shi kuwa ya ƙaraso cikin falon ya zauna. Ba shiri Zuhra mai danna waya ta ajiye ta jawo jakarta na makaranta, dama ita ma Assignment za ta yi ta ɓige da chatting da ƙawayenta, ita a sannan tana SS2. 


Ganin Yaya Sadauki a zaune ya na ta amsa waya yana zuba uban turanci da abokin cinikayyarsa dake a garin Abuja, ya sa Fu'ad a dole soma yi wa Haulatu bayani dalla-dalla, dama Allah ya ba shi baiwa na karatu, duk kuma daƙiƙancinka idan ya iya tafiyar da mai koyo yanda zai fahimta ƙwarai. Sai kuma aka yi sa'a ita ma Haulatun nan da nan ta ke ɗauka musamman idan ta samu mai yi mata filla-filla. Tun tana ɗan ɗari-ɗari saboda Sadauki da ke zaune yana kallonsu jifa-jifa, har ta saki jiki. Sai shi ma Fu'ad ya ji daɗin karatun nasu saboda shi ya na son ya ga yana karantarwa ana masa tambayoyi masu ma'ana, hakan na ƙara sanyawa ya ƙaunaci koyarwar. Ko bayan tashin Sadauki ya fice bai yi mata wata tsiwa ba, sai ga su kamar irin an saba ɗin nan har ya shiga ba ta labarin wani test da aka yi musu a aji sadda ba ma ya jin dadi kuma bai yi karatu ba a ranar amma ya taɓa karantawa ya riƙe. Amma da aka tashi hatta Malamin sai da ya fiddo shi gaban aji har ya bi shi da kyautar dubu ɗaya da ma ƙarin maki saboda jin daɗin bayanin da ya rubuta. Ita kuwa ta yi ta murmushi, Zuhra da ke hararar Fu'ad ganin ya mance ma da wacce ya ke sai ta ja guntun tsaki, Haulatu ta kalle ta kawai kafin ta maida duba ga Fu'ad cike da nishadi ta yi mishi godiya ta tattara kayan karatunta ta yi musu sallama ta fice. Bayan fitarta Zuhra ta kalle shi. 


"Wai dama karatun na tsakani da Allah ka koyamata? Maimakon ka zura ta a kwalba ta je ta kwaso zero?"


Fu'ad ya taɓe baki gami da ɗan ɗaga kafaɗa.


"Ke ni rabu da ni, idan fagen course dina ne mancewa nake yi da wata ƙiyayya. Balle ma ni wannan ba abinda ta yi mana hakanan muka ɗorawa kanmu wahala." Daga haka ya dauki wayarsa ya fice zuwa ɗakinsa dake kusa da na Yayansa Sadauki. 


Zuhra dai ta bi shi da kallon mamaki sannan ta yi ƙwafa ba ta ce uffan ba. 


  A ɓangaren Haulatu tana tafe tana jin wani sanyi a ranta, ta san a hankali waɗanda ke nuna mata tsana za su gaji su bari, ga dai Fu'ad ya watsar da makaman ya sake mata har yana cewa duk abin da ma ba ta gane ba daga yau ta zo, kuma zai kwaso mata tsoffin handouts dinsa ya ba ta. 


"Kun kammala ne?"


Sai da ta ɗan firgita don sam ba ta ji tahowarsa ba face magana a saitin hannun damanta.  Ganin haka ya ɗan ɗaga hannuwa. 


"Afuwan. Na tsorata ki ko?"


Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta gyaɗa kai. 


"Bakomai."


Ta amsa da ɗan murmushi bayan ta ja ta tsaya. Sadauki ya ƙurawa fuskarta idanu yayinda ita kuwa ta ke kallon hanyar fita daga ƙaton gate ɗin gidan, ta kasa kallon inda yake domin tana ji a jikinta ita ya ke duba. Ji ya yi kalmar ina sonki bai wadatar da shi gurin bayyana yanda ya ke jin ƙaunarta a ransa ba. Sai kawai ya sauke ajiyar zuciya ya ƙara magana.


"Mu je na taka maki tunda na kula akwai ki da tsoro."


Ta soma tafiya ita dai ba ta ce masa uffan ba. Yanayin tafiyar tamkar ba su son rabuwar haka ake yin ta. 


"Kin fahimci karatun sosai?"


Ta gyada kai.


"Eh na gane."


"Good. Please ki maida hankali a karatun, ba na so na ji wata aba da ta shafi zancen saurayi ko hira da samari."


Ta ɗan dube shi kamar ta yi kuka shi ma kuwa ya kai dubansa gareta kafin ya kauda kai gami da ɗan taɓe baki da ɗaga kafaɗu.


"Oh, na dameki da batun samari ko? Saboda na damu nima."


Haulatu ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa don haka cikin ƴar rawar muryarta ta amsa.


"Ni fa Allah kuwa Yaya na fadamaka karatu ne gabana. Ba ni da lokacin ma soyayyar balle na saurari wani."


Sadauki ya yi shiru, yana son hakan, amma kuma abin da ke ɗan damunsa da amsar, toh ko shi ba ta sonsa? Kenan babu ma kowa a gabanta har shi ɗin? 


'Kai za ka gina kanka a zuciyarta, kar ka kusa ka bari a yi maka shigar sauri.' Wani ɓangare na zuciyarsa kenan da ya ba sa shawara. 


"Masha Allah, hakan ya yimin daɗi."


Amsar da ya ba ta kenan. 


"Ni me ne ne ma Jamb Score dinki?" 


Ai sai ta hau tura baki da runtse idanu, muryarta cike da ƴar shagwaba ta ce. 


"Yaya please mana."


Ya yi dariya. Daidai sadda bai fi kaɗan su cimma ɓangaren Hajja ba, suka hango Mu'az dake tafe. Sosai Mu'az ya ɗan ji wani iri a ransa, sai dai ya zai yi? Tunda dai Mominsa ta mishi tsakani da Haulatu, uwa uba kuma Baba Alhaji da ya nemi a bar komai har sai yarinyar ta nuna ra'ayin ɗayansu don kanta. Kamar babu wani abu, haka Sadauki ya miƙa masa hannu suka yi musabaha, Haulatu kuwa wacce kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kai, gaida shi ta yi ya amsa. Sadauki ya bi ta da kallo yana murmushi. 


"Shi ke nan, kina iya tafiya. Sai da safe."


Ta amsa da toh, har ta soma tafiya ya dakatar da ita. 


"Haulat." 


Sai da ta ji wani yarr a jikinta, ta juyo ta na mishi wani kasalallen kallo. Shi ma ya ji shi a jikinsa. Cike da jarumtarsa ya ce. 


"Take care."


Murmushi mai tsada ta bi sa da shi tana mai jinjina kai. Daga nan ta juya ta cigaba da tafiyarta zuciyar kamar ta fasa ƙirjinta ta fito don wani irin daɗi da annashuwar da ta ke jin ta ciki. Wai ko dai ta soma son Yaya Sadauki ne? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta. 


'Toh sai me ma idan son nashi nake? Ya fa kai a so shi.' Ta tsinci kanta da bai wa kanta amsa, ta kasa haƙuri sai da ta ɗan waigo ta kalle shi, tuni ya maida hankali ga Mu'az ba ta san me suke faɗi ba. Juyawa ta yi ta cigaba da tafiyarta ranta wasai. Ita ta mance ma akwai wata alaƙa da ta taɓa haɗa su da Mu'az ɗin. 


A ɓangaren Mu'az kuwa, baki kawai ya saki yana kallonsu, ko ba a faɗi ba, ai shi ba makaho ba ne. Idan ma bai gama sanin wace ce Haulatu ba, yana da cikakken sani akan Bestyn nasa. Ya ji wani ɗaci a maƙoshinsa, tabbas ya rasa Haulatu, damar samunta ya kufce masa, Sadauki ya nuna ya fi su wayo kenan? Ta haka yake so ya kafa gwamnatinsa a zuciyarta? To ko ma dai ya kafa ɗin? Haka ya dinga jerawa kansa tambayoyi iri-iri. Sai bayan ta bar wurin ne Sadauki ya dube shi kamar babu abin da ya faru, fuskarnan ɗauke da murmushin da bai gushe ba. 


"Blood ya aka yi?"


Ajiyar zuciya Mu'az ya sauke ganin irin wannan tambaya ta Sadauki mai kama da rainin hankali. Ya kauda kai daga kallonsa saboda ɓacin rai.


"No, ba komai, dama Maama ta kira ni bari na je."


"Ok. Goodnight." Amsar da ya ba shi kenan da haka ya juya ya koma inda ya fito, shi ko Mu'az sai da ya bi shi da kallo sannan ya juya, ba ya jin ma a yanayin da yake ciki zai iya yarda su haɗu da Maama. Zai yi mata waya kawai ya ce ya yi nisa. Duk yanda zuciyarsa ke mishi tuni da Maama ce fa, amma ina, wannan kishi na ganin Sadauki da Haulatun ya mantar da shi komai. Ya ji ya tsani Haulatu tun da har ta watsa mishi ƙasa a ido, ta nunawa duniya ba ta ƙaunarsa. Ba zai kuma ɓata alaƙarsa da ɗan uwansa ba saboda mace. 


***

 Kano...


Hankali a matuƙar tashe Ɗan Mutuwa ya faɗa gidan Haj Adama. Har ƙuryar ɗaki ya iske ta tana tare da wani ɗan matashin saurayi wanda a haife za ta iya haifarsa, daga shi sai gajeran wando da singilet ita kuwa da ɗaura ƙirji. Ba ta yi mamakin ganin Ɗan Mutuwa ya shigo mata a birkice ba. Bai ko bi ta kan matashin ba ya soma yunƙurin magana. 


"Adama ni za ki nunawa bariki?"


Haj Adama tana wani murmushi ta dubi Matashin nan. 


"Shalelena, ɗan ban mintuna kaɗan na sallama wannan."


Ya amsa da ok sannan ya dira daga gadon zuwa ƙasa ya ɗauki kayansa ya na hararar Ɗan Mutuwa da ya ɓata masa sha'ani ya fita. Yana rufo ƙofar Ɗan Mutuwa ya cigaba da ɓaɓatunsa.


"Ni za ki munafunta? Mun yi cinikin kaya kin sa an riƙe nawa ke kuwa kin bi duk hanyar da za ki yi wajen kuɓutar da naki?"


Ta miƙe ta tako tana mai ɗora hannunta a kafaɗarsa ya kuwa saurin kaucewa. 


"Haba Alhaji Ɗan Mutuwa. Ka tsaya ka saurare ni. Ba ka san taƙamaiman maƙudan kudaɗen da na kashe wajen ganin kayanmu duka sun kuɓuta ba. Iliyasu ya ce na bi komai a sannu, yanda ya yi min ƙoƙarin kuɓutar da nawa kayan zai yi hakan a kan naka. Don Allah ka kwantar da hankalinka, duka fa wannan ba abu ne na damuwa ba.."


"Ya za ki ce ba abin damuwa ba ne? Ta ya za ki soma cewa haka alhalin kin sani muddin wancan mugun shi ke mulkar wannan kujera to fa kashinmu zai iya bushewa."


Ta girgiza kai tana murmushi.


"Kamar ba mu ne da ƙasar ba? Akwai Custom ɗin da ya isa ya tsone mana idanu? Kar ma ka ƙara wannan hangen. Kaya za su fito, babu abin da zai faru."


Dan Mutuwa ya bi ta da kallo irin na wacce ta raina masa wayo.


"Ni za ki mayar sakarai? Ko an faɗamaki ban samu labari daga wajen su Duna ba? Ina da labarin komai, kin ce a yi maki duk yanda za'a yi naki a yi clearing, nawa kuwa ko me za su yi toh su yi. Haba Adama, ai ba yau na sanki ba, ke mace ce mai son kanta muguwa baƙar azzaluma. Toh da ni kike zancen."


Ran Haj Adama ya ɓaci har sai da ta nuna shi da yatsa. 


"Ni ka ke kallon tsabar idanuna ka ke zagi? Yau ni ka ke zagi Ɗan Mutuwa? Eh lallai! Mutum mugun icce! Yau ni Adama ka ke ci wa mutunci?! Ba don ni ba ina ka ga ma arziƙin shigo da kaya mai yawa har haka?"


Madadin ya yi ƙasa sai ya ƙara ɗaukar zafi. 


"Dama ai ku mata ba a raba ku da gori! Mu zuba ni da ke, matuƙar kayan nan ba su kuɓuta ba kamar yanda na ki ya kuɓuta, ni na san mummunan matakin da zan ɗauka."


Yana kai wa nan ya sa kai ya fice kamar zai tashi sama. Haj Adama ta bishi da kallo fuskarnan a ɗaure tamau. Ta yi alƙawarin ɗaukar matakin kafin ya kai ga ɗauka doj haka a gaggauce ta shiga maida suturarta, da haka wanda ta kira da Shalele ya shigo. 


"Ah, Sweety ya haka? Wannan wane banzan ne haka da ya ɓata min mood ɗinki?"


Ta numfasa zuciyar na tafarfasa. 


"Bari kawai Shalele, ma yi magana yanzu fita ce ta kama ni."


Daga haka ta juya ta buɗe bedside drawer dinta ta fiddo bandiran kuɗaɗe ƴan dubunnai har uku ta cilla masa ya kuwa cafe abinsa yana wangale haƙora.


"Ga wannan ka sha madara kafin mu ƙara haɗuwa."


"Godiya nake." Ya amsa kai tsaye sannan ya fice bayan ya ɗauki wayarsa da tarkacen da ya shigo da su. 


Ɗan Mutuwa kuwa, direbansa na tuƙi amma ji yake kamar su na tafiyar hawainiya hakan ya sa har wata tsawa yake yi mishi akan ya yi sauri. So ya ke a gobe ya wuce Abuja don ganawa da tsohon Comptroller-General na Customs, Yahuza Hayatu, wanda yake mutuminsu kuma ɗan ƙungiyarsu ta harkokin miyagun ƙwayoyi, yanzu haka bayan sauke shi da aka yi yana rayuwa ne a Abuja. Ya tabbata shi ba zai rasa hanyar da zai yi a saki kayansa ba. Ya so ƙwarai su yi ta a waya amma Sanata Hashim ya ba shi shawarar takawa ya je da kansa. 


Koda ya isa gida ya iske Hindatu zaune tare da Mominta suna hira. Ganinsa ya sa Momi washe haƙora da fadin.


"Ranka ya daɗe sannu da zuwa." Bai ko kalle su ba ya nufi ɗakinsa. Abun ya yiwa Hindatu zafi wanda ya sanya ta miƙewa. Da sauri Momi ta riƙo hannunta. 


"Ke, ina za ki?" 


"Momi rabu da ni, na gaji da wulaƙancin da ya ke yi maki. Ban ga dalilin da mijin da nake aure zai raina uwata ba."


Baki sake Momi ta ce.


"Haba Hindatu, ke yanzu mijinki har yanzu ba ki gama karantarsa ba? Dubi fa yanda ya shigo rai a ɓace amma ki ke son ki je masa da zancenki na shirme? Ina ki ka ga ya wulaƙanta ni idan ba neman magana ba?"


Zuciyar Hindatu babu dadi ta ke kallo da sauraron Momin har ta kai aya a zancenta kafin ta amsa. 


"Yanzu Momi ke kenan koyaushe cikin mara wa Ibrahim baya don kawai yana da kudi ai ba zai zame masa hujjar da zai ci zarafin uwata ba. Ni kam ba zan aminta da wulaƙanci ba." Daga haka ta tafi fuu, Momin na kira har da haɗawa da zagi amma ina tuni Hindatu ta bi hanyar da zai sada ta da ɗakinsa. Tana shiga ta iske yana waya yana zazzaga masifa da ɗura-ɗuran ashariya. Ba yau ta soma jin sa yana zage-zage ba da girmansa, abun ma kamar bai ta'azzara ba sai da ya gayyato mata wasu ƴan iskan ƴan daba gida suke kwana wai su Duna. Bai ko kula da tsayuwarta ba sai da ya ɗan ɗago ya gan ta ya haɗe rai ya katse kiran. 


"Ke ya za ki shigo ki yimin tsaye ina waya?"


Hindatu ta ɗaure fuska. 


"Ai kai zan tambaya, ta ya ya za ka shigo mana falo babu ko sallama kuma wai mahaifiyata na gaisheka tunda kai ba ka gaida ta, shi ne za ka bi mu da kallon banza ka shigo ɗaki?"


Ɗan Mutuwa ya saki baki.


"Ke! Da ni ki ke wannan maganar?"


"An.."


Ai ba ta ƙarasa ba da ya yi wani taku da bai fi uku ba ya cimmata ya hau jigba yana ashariya, dama neman inda zai huce fushinsa yake sai Allah ya yi ta faɗo tarkonsa. 


 Jin ihun Hindatu ya sa Momi ba shiri ta shigo kamar an wurgo ta. Ganin jinim da ke bin ƙafafun ɗiyarta ya sa ta sakin ƙara. 


"Wayyo na shiga uku! Shikenan ka kashe ta! Shikenan ka ɓarar da cikin!"


Tuni Hindatu ta sume, shi kuwa jin batun ɓarar da ciki sai ya tsaya cak! Ya bi ƙafafun Hindatun da kallo, jinin da ya gani ya sanya shi jin wani irin faɗuwar gaba. Kashedin Uban Dodo ne ya shiga amsa kuwwa a kunnuwansa. 


 _"Idan ka bari muka rasa abin da ke cikin matarka lallai ka sani za ka rasa dukiyarka!"_


Ai bai san sadda ya kinkimi Hindatu ba ya yi hanyar waje a guje, Momi ta bi bayansu ita ma babu batun ɗaukar mayafi balle takalmi.


***

 Katsina...

[09/09, 11:02 am] Faty Lawal: Cike da tunanin rashin kai na Yaya Zaid ta ƙarasa ɓangaren Momi Nuratu. Ta kuwa iske ta a falo cikin kwalliyarta na zuwa turakar miji. Ganin Haulatun sai ta ɗan faɗaɗa fara'arta gami da amsa gaisuwarta. 


"Lafiya lau Haulatun Hajja, ya Umman taki?" 


Tana murmushi ta ba ta amsa da lafiya lau. 


"Wani abu ki ke so ne?" Faɗin Momi Nuratu, sai ta ɗan kalli inda Fu'ad da Zuhra suke kowannensu da waya a hannu amma tambayar Momi Nuratun ce ta sa su duban Haulatun wacce ita din ma aka yi sa'a ta kai duba ga Fu'ad din. 


"Dama wajen Fu'ad na zo ya koyamin wani Assignment da ban gane ba."


Nan da nan ya haɗe rai gami da zaro ido.


"Wa? Wai ni? Tab! Ai kuwa...zan koya maki."


Ya ƙarashe da abin da ba hakan ya yi niyyar faɗi ba dalilin kaifin idanun Yayan nasu Sadauki wanda ya zuba masa su, shigowarsa falon Momi Nuratun kenan daga na Mahaifinsa. Momi Nuratu ta harari Fu'ad.


"Oh, da ya ke ka ga dodon naka ai ka iya lauyance magana. Je ki ya koyamaki Haulatu."


Ta amsa da toh kafin ta juya ta gaida Yaya Sadauki wanda kwana biyu ba su haɗu ba. Koyaushe kamar ana ƙara masa kyau haka ta ke gani. Ya amsa mata sannan ya ƙaraso ga Momi Nuratu ita kuwa Haulatu ta yi wurin Fu'ad da ya ke harararta a faƙaice. Sai ta bi shi da murmushin ta ci galaba. Shi kuwa babban burinsa Yayan nasu ya bar falon ya gwabza mata rashin mutunci amma ina, su na gama magana da Momi Nuratu, ita ta yi falon Daddy shi kuwa ya ƙaraso cikin falon ya zauna. Ba shiri Zuhra mai danna waya ta ajiye ta jawo jakarta na makaranta, dama ita ma Assignment za ta yi ta ɓige da chatting da ƙawayenta, ita a sannan tana SS2. 


Ganin Yaya Sadauki a zaune ya na ta amsa waya yana zuba uban turanci da abokin cinikayyarsa dake a garin Abuja, ya sa Fu'ad a dole soma yi wa Haulatu bayani dalla-dalla, dama Allah ya ba shi baiwa na karatu, duk kuma daƙiƙancinka idan ya iya tafiyar da mai koyo yanda zai fahimta ƙwarai. Sai kuma aka yi sa'a ita ma Haulatun nan da nan ta ke ɗauka musamman idan ta samu mai yi mata filla-filla. Tun tana ɗan ɗari-ɗari saboda Sadauki da ke zaune yana kallonsu jifa-jifa, har ta saki jiki. Sai shi ma Fu'ad ya ji daɗin karatun nasu saboda shi ya na son ya ga yana karantarwa ana masa tambayoyi masu ma'ana, hakan na ƙara sanyawa ya ƙaunaci koyarwar. Ko bayan tashin Sadauki ya fice bai yi mata wata tsiwa ba, sai ga su kamar irin an saba ɗin nan har ya shiga ba ta labarin wani test da aka yi musu a aji sadda ba ma ya jin dadi kuma bai yi karatu ba a ranar amma ya taɓa karantawa ya riƙe. Amma da aka tashi hatta Malamin sai da ya fiddo shi gaban aji har ya bi shi da kyautar dubu ɗaya da ma ƙarin maki saboda jin daɗin bayanin da ya rubuta. Ita kuwa ta yi ta murmushi, Zuhra da ke hararar Fu'ad ganin ya mance ma da wacce ya ke sai ta ja guntun tsaki, Haulatu ta kalle ta kawai kafin ta maida duba ga Fu'ad cike da nishadi ta yi mishi godiya ta tattara kayan karatunta ta yi musu sallama ta fice. Bayan fitarta Zuhra ta kalle shi. 


"Wai dama karatun na tsakani da Allah ka koyamata? Maimakon ka zura ta a kwalba ta je ta kwaso zero?"


Fu'ad ya taɓe baki gami da ɗan ɗaga kafaɗa.


"Ke ni rabu da ni, idan fagen course dina ne mancewa nake yi da wata ƙiyayya. Balle ma ni wannan ba abinda ta yi mana hakanan muka ɗorawa kanmu wahala." Daga haka ya dauki wayarsa ya fice zuwa ɗakinsa dake kusa da na Yayansa Sadauki. 


Zuhra dai ta bi shi da kallon mamaki sannan ta yi ƙwafa ba ta ce uffan ba. 


  A ɓangaren Haulatu tana tafe tana jin wani sanyi a ranta, ta san a hankali waɗanda ke nuna mata tsana za su gaji su bari, ga dai Fu'ad ya watsar da makaman ya sake mata har yana cewa duk abin da ma ba ta gane ba daga yau ta zo, kuma zai kwaso mata tsoffin handouts dinsa ya ba ta. 


"Kun kammala ne?"


Sai da ta ɗan firgita don sam ba ta ji tahowarsa ba face magana a saitin hannun damanta.  Ganin haka ya ɗan ɗaga hannuwa. 


"Afuwan. Na tsorata ki ko?"


Sauke ajiyar zuciya ta yi sannan ta gyaɗa kai. 


"Bakomai."


Ta amsa da ɗan murmushi bayan ta ja ta tsaya. Sadauki ya ƙurawa fuskarta idanu yayinda ita kuwa ta ke kallon hanyar fita daga ƙaton gate ɗin gidan, ta kasa kallon inda yake domin tana ji a jikinta ita ya ke duba. Ji ya yi kalmar ina sonki bai wadatar da shi gurin bayyana yanda ya ke jin ƙaunarta a ransa ba. Sai kawai ya sauke ajiyar zuciya ya ƙara magana.


"Mu je na taka maki tunda na kula akwai ki da tsoro."


Ta soma tafiya ita dai ba ta ce masa uffan ba. Yanayin tafiyar tamkar ba su son rabuwar haka ake yin ta. 


"Kin fahimci karatun sosai?"


Ta gyada kai.


"Eh na gane."


"Good. Please ki maida hankali a karatun, ba na so na ji wata aba da ta shafi zancen saurayi ko hira da samari."


Ta ɗan dube shi kamar ta yi kuka shi ma kuwa ya kai dubansa gareta kafin ya kauda kai gami da ɗan taɓe baki da ɗaga kafaɗu.


"Oh, na dameki da batun samari ko? Saboda na damu nima."


Haulatu ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa don haka cikin ƴar rawar muryarta ta amsa.


"Ni fa Allah kuwa Yaya na fadamaka karatu ne gabana. Ba ni da lokacin ma soyayyar balle na saurari wani."


Sadauki ya yi shiru, yana son hakan, amma kuma abin da ke ɗan damunsa da amsar, toh ko shi ba ta sonsa? Kenan babu ma kowa a gabanta har shi ɗin? 


'Kai za ka gina kanka a zuciyarta, kar ka kusa ka bari a yi maka shigar sauri.' Wani ɓangare na zuciyarsa kenan da ya ba sa shawara. 


"Masha Allah, hakan ya yimin daɗi."


Amsar da ya ba ta kenan. 


"Ni me ne ne ma Jamb Score dinki?" 


Ai sai ta hau tura baki da runtse idanu, muryarta cike da ƴar shagwaba ta ce. 


"Yaya please mana."


Ya yi dariya. Daidai sadda bai fi kaɗan su cimma ɓangaren Hajja ba, suka hango Mu'az dake tafe. Sosai Mu'az ya ɗan ji wani iri a ransa, sai dai ya zai yi? Tunda dai Mominsa ta mishi tsakani da Haulatu, uwa uba kuma Baba Alhaji da ya nemi a bar komai har sai yarinyar ta nuna ra'ayin ɗayansu don kanta. Kamar babu wani abu, haka Sadauki ya miƙa masa hannu suka yi musabaha, Haulatu kuwa wacce kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kai, gaida shi ta yi ya amsa. Sadauki ya bi ta da kallo yana murmushi. 


"Shi ke nan, kina iya tafiya. Sai da safe."


Ta amsa da toh, har ta soma tafiya ya dakatar da ita. 


"Haulat." 


Sai da ta ji wani yarr a jikinta, ta juyo ta na mishi wani kasalallen kallo. Shi ma ya ji shi a jikinsa. Cike da jarumtarsa ya ce. 


"Take care."


Murmushi mai tsada ta bi sa da shi tana mai jinjina kai. Daga nan ta juya ta cigaba da tafiyarta zuciyar kamar ta fasa ƙirjinta ta fito don wani irin daɗi da annashuwar da ta ke jin ta ciki. Wai ko dai ta soma son Yaya Sadauki ne? Wannan ita ce tambayar da ta yiwa kanta. 


'Toh sai me ma idan son nashi nake? Ya fa kai a so shi.' Ta tsinci kanta da bai wa kanta amsa, ta kasa haƙuri sai da ta ɗan waigo ta kalle shi, tuni ya maida hankali ga Mu'az ba ta san me suke faɗi ba. Juyawa ta yi ta cigaba da tafiyarta ranta wasai. Ita ta mance ma akwai wata alaƙa da ta taɓa haɗa su da Mu'az ɗin. 


A ɓangaren Mu'az kuwa, baki kawai ya saki yana kallonsu, ko ba a faɗi ba, ai shi ba makaho ba ne. Idan ma bai gama sanin wace ce Haulatu ba, yana da cikakken sani akan Bestyn nasa. Ya ji wani ɗaci a maƙoshinsa, tabbas ya rasa Haulatu, damar samunta ya kufce masa, Sadauki ya nuna ya fi su wayo kenan? Ta haka yake so ya kafa gwamnatinsa a zuciyarta? To ko ma dai ya kafa ɗin? Haka ya dinga jerawa kansa tambayoyi iri-iri. Sai bayan ta bar wurin ne Sadauki ya dube shi kamar babu abin da ya faru, fuskarnan ɗauke da murmushin da bai gushe ba. 


"Blood ya aka yi?"


Ajiyar zuciya Mu'az ya sauke ganin irin wannan tambaya ta Sadauki mai kama da rainin hankali. Ya kauda kai daga kallonsa saboda ɓacin rai.


"No, ba komai, dama Maama ta kira ni bari na je."


"Ok. Goodnight." Amsar da ya ba shi kenan da haka ya juya ya koma inda ya fito, shi ko Mu'az sai da ya bi shi da kallo sannan ya juya, ba ya jin ma a yanayin da yake ciki zai iya yarda su haɗu da Maama. Zai yi mata waya kawai ya ce ya yi nisa. Duk yanda zuciyarsa ke mishi tuni da Maama ce fa, amma ina, wannan kishi na ganin Sadauki da Haulatun ya mantar da shi komai. Ya ji ya tsani Haulatu tun da har ta watsa mishi ƙasa a ido, ta nunawa duniya ba ta ƙaunarsa. Ba zai kuma ɓata alaƙarsa da ɗan uwansa ba saboda mace. 


***

 Kano...


Hankali a matuƙar tashe Ɗan Mutuwa ya faɗa gidan Haj Adama. Har ƙuryar ɗaki ya iske ta tana tare da wani ɗan matashin saurayi wanda a haife za ta iya haifarsa, daga shi sai gajeran wando da singilet ita kuwa da ɗaura ƙirji. Ba ta yi mamakin ganin Ɗan Mutuwa ya shigo mata a birkice ba. Bai ko bi ta kan matashin ba ya soma yunƙurin magana. 


"Adama ni za ki nunawa bariki?"


Haj Adama tana wani murmushi ta dubi Matashin nan. 


"Shalelena, ɗan ban mintuna kaɗan na sallama wannan."


Ya amsa da ok sannan ya dira daga gadon zuwa ƙasa ya ɗauki kayansa ya na hararar Ɗan Mutuwa da ya ɓata masa sha'ani ya fita. Yana rufo ƙofar Ɗan Mutuwa ya cigaba da ɓaɓatunsa.


"Ni za ki munafunta? Mun yi cinikin kaya kin sa an riƙe nawa ke kuwa kin bi duk hanyar da za ki yi wajen kuɓutar da naki?"


Ta miƙe ta tako tana mai ɗora hannunta a kafaɗarsa ya kuwa saurin kaucewa. 


"Haba Alhaji Ɗan Mutuwa. Ka tsaya ka saurare ni. Ba ka san taƙamaiman maƙudan kudaɗen da na kashe wajen ganin kayanmu duka sun kuɓuta ba. Iliyasu ya ce na bi komai a sannu, yanda ya yi min ƙoƙarin kuɓutar da nawa kayan zai yi hakan a kan naka. Don Allah ka kwantar da hankalinka, duka fa wannan ba abu ne na damuwa ba.."


"Ya za ki ce ba abin damuwa ba ne? Ta ya za ki soma cewa haka alhalin kin sani muddin wancan mugun shi ke mulkar wannan kujera to fa kashinmu zai iya bushewa."


Ta girgiza kai tana murmushi.


"Kamar ba mu ne da ƙasar ba? Akwai Custom ɗin da ya isa ya tsone mana idanu? Kar ma ka ƙara wannan hangen. Kaya za su fito, babu abin da zai faru."


Dan Mutuwa ya bi ta da kallo irin na wacce ta raina masa wayo.


"Ni za ki mayar sakarai? Ko an faɗamaki ban samu labari daga wajen su Duna ba? Ina da labarin komai, kin ce a yi maki duk yanda za'a yi naki a yi clearing, nawa kuwa ko me za su yi toh su yi. Haba Adama, ai ba yau na sanki ba, ke mace ce mai son kanta muguwa baƙar azzaluma. Toh da ni kike zancen."


Ran Haj Adama ya ɓaci har sai da ta nuna shi da yatsa. 


"Ni ka ke kallon tsabar idanuna ka ke zagi? Yau ni ka ke zagi Ɗan Mutuwa? Eh lallai! Mutum mugun icce! Yau ni Adama ka ke ci wa mutunci?! Ba don ni ba ina ka ga ma arziƙin shigo da kaya mai yawa har haka?"


Madadin ya yi ƙasa sai ya ƙara ɗaukar zafi. 


"Dama ai ku mata ba a raba ku da gori! Mu zuba ni da ke, matuƙar kayan nan ba su kuɓuta ba kamar yanda na ki ya kuɓuta, ni na san mummunan matakin da zan ɗauka."


Yana kai wa nan ya sa kai ya fice kamar zai tashi sama. Haj Adama ta bishi da kallo fuskarnan a ɗaure tamau. Ta yi alƙawarin ɗaukar matakin kafin ya kai ga ɗauka doj haka a gaggauce ta shiga maida suturarta, da haka wanda ta kira da Shalele ya shigo. 


"Ah, Sweety ya haka? Wannan wane banzan ne haka da ya ɓata min mood ɗinki?"


Ta numfasa zuciyar na tafarfasa. 


"Bari kawai Shalele, ma yi magana yanzu fita ce ta kama ni."


Daga haka ta juya ta buɗe bedside drawer dinta ta fiddo bandiran kuɗaɗe ƴan dubunnai har uku ta cilla masa ya kuwa cafe abinsa yana wangale haƙora.


"Ga wannan ka sha madara kafin mu ƙara haɗuwa."


"Godiya nake." Ya amsa kai tsaye sannan ya fice bayan ya ɗauki wayarsa da tarkacen da ya shigo da su. 


Ɗan Mutuwa kuwa, direbansa na tuƙi amma ji yake kamar su na tafiyar hawainiya hakan ya sa har wata tsawa yake yi mishi akan ya yi sauri. So ya ke a gobe ya wuce Abuja don ganawa da tsohon Comptroller-General na Customs, Yahuza Hayatu, wanda yake mutuminsu kuma ɗan ƙungiyarsu ta harkokin miyagun ƙwayoyi, yanzu haka bayan sauke shi da aka yi yana rayuwa ne a Abuja. Ya tabbata shi ba zai rasa hanyar da zai yi a saki kayansa ba. Ya so ƙwarai su yi ta a waya amma Sanata Hashim ya ba shi shawarar takawa ya je da kansa. 


Koda ya isa gida ya iske Hindatu zaune tare da Mominta suna hira. Ganinsa ya sa Momi washe haƙora da fadin.


"Ranka ya daɗe sannu da zuwa." Bai ko kalle su ba ya nufi ɗakinsa. Abun ya yiwa Hindatu zafi wanda ya sanya ta miƙewa. Da sauri Momi ta riƙo hannunta. 


"Ke, ina za ki?" 


"Momi rabu da ni, na gaji da wulaƙancin da ya ke yi maki. Ban ga dalilin da mijin da nake aure zai raina uwata ba."


Baki sake Momi ta ce.


"Haba Hindatu, ke yanzu mijinki har yanzu ba ki gama karantarsa ba? Dubi fa yanda ya shigo rai a ɓace amma ki ke son ki je masa da zancenki na shirme? Ina ki ka ga ya wulaƙanta ni idan ba neman magana ba?"


Zuciyar Hindatu babu dadi ta ke kallo da sauraron Momin har ta kai aya a zancenta kafin ta amsa. 


"Yanzu Momi ke kenan koyaushe cikin mara wa Ibrahim baya don kawai yana da kudi ai ba zai zame masa hujjar da zai ci zarafin uwata ba. Ni kam ba zan aminta da wulaƙanci ba." Daga haka ta tafi fuu, Momin na kira har da haɗawa da zagi amma ina tuni Hindatu ta bi hanyar da zai sada ta da ɗakinsa. Tana shiga ta iske yana waya yana zazzaga masifa da ɗura-ɗuran ashariya. Ba yau ta soma jin sa yana zage-zage ba da girmansa, abun ma kamar bai ta'azzara ba sai da ya gayyato mata wasu ƴan iskan ƴan daba gida suke kwana wai su Duna. Bai ko kula da tsayuwarta ba sai da ya ɗan ɗago ya gan ta ya haɗe rai ya katse kiran. 


"Ke ya za ki shigo ki yimin tsaye ina waya?"


Hindatu ta ɗaure fuska. 


"Ai kai zan tambaya, ta ya ya za ka shigo mana falo babu ko sallama kuma wai mahaifiyata na gaisheka tunda kai ba ka gaida ta, shi ne za ka bi mu da kallon banza ka shigo ɗaki?"


Ɗan Mutuwa ya saki baki.


"Ke! Da ni ki ke wannan maganar?"


"An.."


Ai ba ta ƙarasa ba da ya yi wani taku da bai fi uku ba ya cimmata ya hau jigba yana ashariya, dama neman inda zai huce fushinsa yake sai Allah ya yi ta faɗo tarkonsa. 


 Jin ihun Hindatu ya sa Momi ba shiri ta shigo kamar an wurgo ta. Ganin jinim da ke bin ƙafafun ɗiyarta ya sa ta sakin ƙara. 


"Wayyo na shiga uku! Shikenan ka kashe ta! Shikenan ka ɓarar da cikin!"


Tuni Hindatu ta sume, shi kuwa jin batun ɓarar da ciki sai ya tsaya cak! Ya bi ƙafafun Hindatun da kallo, jinin da ya gani ya sanya shi jin wani irin faɗuwar gaba. Kashedin Uban Dodo ne ya shiga amsa kuwwa a kunnuwansa. 


 _"Idan ka bari muka rasa abin da ke cikin matarka lallai ka sani za ka rasa dukiyarka!"_


Ai bai san sadda ya kinkimi Hindatu ba ya yi hanyar waje a guje, Momi ta bi bayansu ita ma babu batun ɗaukar mayafi balle takalmi.


***

 Katsina...

[09/09, 11:02 am] Faty Lawal: Bayan Kwanaki Biyar...


Katsina...


Hajja ce ke faman sababi, ta dage kuma akan lallai sai an ba ta waya ta yiwa Malama Safiyya gargaɗi akan Zaid. Hakan ya samo asali ne daga saƙon ban haƙuri da roƙo da ya tura ga Haj Nafisa babu ko kunya wai su ta ya shi neman gafarar Hajjar ta haƙura ta amince ya auri Haulatu. Ba wannan kaɗai ne ya fusata Hajja ba sai da ta ke samun labari daga Hajiya Nafisar cewa ai har Zaitunar ya aika wa saƙo makamancin haka. 


"Don Allah Hajja ki yi haƙuri. Ita Malama ai babu ruwanta a zancen nan. Yaran yanzu ne..."


"Kin ga fa Na'imatu ki ja bakinki ki yi shiru, wannan maganar da nake yi maki akan Safiyya tun kafin ki zo ake fama da shi. Da ace ta isa da ɗan nata ai da wani zancen ake ba wannan ba. Ke Saude muje."


Baba Saude dai ta rasa abin yi, ga Hajja ba wani daɗin jikinta take ji ba amma ta dage a tafi. Haulatu ko tana zaune na ta tanka na don ita din ma abin ya ishe ta, gwara Hajjar ta takawa abin burki. Umma ce dai ta dauki waya ta dannawa Baba Dakta kira, bayan gaisuwa ta sanar masa komai nan da nan ya ce ta haɗa shi da Hajjar a waya, tuni Hajja ta nufi hanyar fita don haka ta da sauri ta bi bayanta ta miƙa mata. Hararar wayar Hajja ta yi.


"Wa ki ka kira min?"


Kafin Umma ta amsa ta karɓi wayar. Shiru ta yi bayan sallama jin Baba Dakta na ta faɗa ya kuma ce ta zauna zai zo ya same ta yanzu. A dole ta amsa da toh don bai ko ba ta damar yi masa wani bayani ba. 


Wayar ta miƙawa Umma ta komai ciki tana sababin faɗa  wai Umma ta hana ta ɗaukar mataki. Koda Baba Dakta ya zo ta kora masa duk halin da ake ciki, shi kansa abin bai masa dadi ba. 


"Ki kwantar da hankali, ni da kaina zan ja wa Zaidu kunne. Ai Safiyya na iyakar ƙokarinta, ɗan yau ne ka haifa ba ka haifi halinsu ba sai dai addu'a al'amarin. In sha Allahu zan yiwa abin tufka."


Hajja ta gamsu da zancen Baba Dakta don haka ta amince ta ba sa damar yin magana. Bayan fitarsa Umma ta dube ta murya a sanyaye ta ce.


"Toh ni Hajja idan abin ya zama haka, ko dai a haƙura a yarda ya fito a..."


"Na'imatu! Rufemin baki tun ban bubbugeki ba! Kin san me ki ke fadi? Wa zai fito ɗin? Toh na rantse ko ba na duniya a ka yarda a ka ba Zaidu jikata ban yafe ba. Ki ji min wani zance? Au, wato ma so ki ke ki sanya ni kaffara? Idan ban haifi Haulatu ba ai na haifi uwarta. Ki na son nuna min yaron nan ya fi ni kenan? Kin san irin tashin hankalin da ya jefa mu akan Zaituna?"


Sai kawai ta fashe da kuka, nan da nan hankalin Umma da Baba Saude ya tashi suka hau ba ta haƙuri, Umma faɗi take ta tuba ba za ta ƙara maimaitawa ba. Haulatu kuwa da ta ji abin da Umman ke ƙoƙarin faɗi har ta soma hawaye, ta ya ya ma za ta yarda ta auri mutumin da ƴar uwarta ke so? Ko ba ma wannan ba, nacin Yaya Zaid a kanta ya ƙara tunzura zuciyarta wajen tsanarsa. Ai kuwa a cewarta sai dai ya gaji ya haƙura, amma ta rantse ba za ta aure shi ba. Ganin ma abin ya rincaɓe Hajja na kuka sai kawai ta miƙe ta zura hijabi ta fice daga gidan zuwa wajen Safina. A lokacin saura kwanaki uku ya rage a ɗaura auren Maama ba amma duk yanayin ba ya yiwa Haulatu daɗi saboda wannan masifar da Yaya Zaid ya kunno. Wato da ya aikawa Anti Zaituna  saƙo akan ta rarraso masa Haulatu hakan bai ishe shi na tunda Anti Zaituna ta nunamata ita komai ya fice a ranta ta yarda ta aminta da shi ta aure shi, ita kuwa ta ce ba ta ra'ayinsa. Hakan bai masa ba sai da ya tunkari Haj Nafisa da zancen. Ita kuwa koda maza sun ƙare a duniya ta yiwa kanta alƙawarin babu ita babu shi. Ta kalli sararin samaniua da hadari ya haɗo kamar ɗazun ba rana aka gama tsalawa ba, kowane lokaci cikin iko na Allah ruwa zai iya sauka. Ana iska mai sanyi haka ta ƙarasa wurin Safina. Ta iske tana banɗaki don haka ta fito suka yi karo da Anti Mabruka da ta fito daga ɗakin Maama. Ganin Haulatu sai da ta ɗan firgita, ita kuwa Haulatu idanu ta zubamata da mamaki, to mene ne ya kai Anti Mabruka ɗakin Maama alhalin ba su taɓa ganin ta shiga ba? Ko Maama na rashin lafiya ba ta taɓa shiga duba jikinta sai idan sun yi karo ko a falo ko waje ta bi ta da sannu. Sai kuma ta ga ta haɗe rai, gaishe ta tayi ta amsa ciki ciki, daga haka Haulatu ta bude kofar dakin Safina ta shiga amma ba ta rufo ba ta a leƙe, sai da ta ga Anti Mabruka ta fice zuwa falo sannan ta fito, ita dai sam hankalinta bai kwanta ba don haka ta yi ƙarfin halin buɗe ɗakin ta shiga, Maama ba ta nan, to me Anti Mabruka ta shiga yi? Ta ga ko'ina tsaf a gyare sai kawai ta juya za ta fita, wani allura da ta ji ya soki ƙafarta daga jikin doormat din dake ƙofar fita ne ya sanya ta sakin ƙara marar sauti sannan ta duba. Ba ta ga komai ba illah adon gashin dake jikin kafet din, ta kasa nutsuwa sai da ta kai hannu ta taɓa, duk da haka allura ta ji, da sauri ta ɗaga ƙasansa. Wata laya ce a naɗe da farin zare sai ko wani irin abu kamar ɗanyen nama a jikinsa da aka sossoka allurai a jiki. Salati ta yi a fili jikinta har rawa ya ke yi, da sauri ta sanya a cikin hijabinta ta fito ta rufe ƙofar. Kai tsaye ɗakin Safina ta shiga. Ta ci sa'a kuwa ta fito, ganinta tana faman rawar ɗari ne ya sanya ta fadin.


"Ke kuma lafiyarki?" Haulatu ta haɗiyi miyau, a sannan har an soma ruwa iskar na feso shi cikin dakin, da sauri Safina ta ƙarasa ta rufe gilashin windon. Bayan ta dawo ne Haulatu ta buɗe hannunta ta nuna mata. Idanu waje Safina ke kalla kafin ta dubi Haulatun. 


"Innalillahi...Haulatu mene ne wannan? A ina ki ka samo?"


"Ni ma ganinsa na yi a ƙofar shiga ɗakin Maama, ban san wa ya ajiye ba. Na rasa ya zan yi. Ina za mu kai shi? Gaba daya na ruɗe wallahi."


Ita kanta Safinar rudewa ta yi, nan da nan abu ya zo mata a rai.


"Kin san me? Ai gobe zamu je islamiyya, ki bari idan mun fita sai mu fidda alluran jiki mu ƙona ta."


Jinjina kai Haulatu ta yi, nan da nan suka ƙulle Safina ta ɓoye a can bayan sif ɗinta. Duk suka shiga jimami, ita Haulatu sam ba ta son ta ce ga wacce ta gani ta fito daga ɗakin, ita kuwa Safina tana ɗauke da labarin abin da ta ga Anti Mabruka na kokarin barbaɗawa jiya a cikin abincin Maama amma kuma tana tsoron fadi wannan ya sa kowa ya bar wa cikinsa. Sai da suka gama jimami da tausayawa Maama gami da yi mata addu'a akan duk mai nufinta da sharri ya ƙare a kansa. Haulatu ta mike da sauri ta ɗauro alwala don ba ta san sharrin abin da ta taɓa ba. Ita ma Safina ba shiri ta dauro. Sai da suka nutsu take ba Safina labarin abin da ya sa ta taho nan. Ita kanta Safina ta girgiza da ji. 


"Kai jama'a, wai Yaya Zaid ƙalau yake kuwa? Wannan abun ni na tabbatar haƙƙin Anti Zaituna ne ke bibiyarsa."


Taɓe baki Haulatu ta yi.


"Ai ko ba ki ce ba, kuma kinsan ko ɗigon tausayinsa ba na ji? Ni wallahi ba don Malama ba, ai da tuni na kira shi a waya na gasa mishi baƙaƙen maganganu, toh ita din babu ruwanta, kuma ma yanda na rufe layukansa a wayata ba na fatan har abada na buɗe."


"Allah ya kyauta dai."


Wayar Haulatu ta yi kara, ganin sunan Umma ya sanya ta ɗagawa. Tambayar inda take ta yi ganin a na ruwa, nan ta ce mata tana gun Safina, jin haka sai Umman ta samu nutsuwa suka yi sallama. 


"Ke, ni fa na yi sabon kamu ma ban faɗamaki ba."


Baki sake Haulatu ta dubi Safina.


"Wasa ki ke ko? Karatun fa? Kar ki cemin a cikin waɗannan yaran da muke gani a makaranta kike son ɗaya?"


Safina ta yi dariya.


"Wa zai kula ƴan makaranta? Ko ɗaya, wannan fa ɗan abokin Abbana ne. Muhsin, ya matsamin, ai idan ban manta ba kamar mun taɓa hirarsa, ya dage shi lallai yana sona duk irin yanda na ke ja baya amma ya ƙi haƙura. Kinsan fa zuciya yau da gobe, tana son mai kyautata mata. Ni ma na ɗan fara sakarmasa."


Da murmushi sosai Haulatu ta ce.


"Kai na maki murna, Allah yasa shikenan ya ture fadar Yaya Mu'az a ranki."


Wani ɗan murmushi Safina ta yi.


"Anya? Yaya Mu'az ai ƙaunarsa nake yi dagaske na san zai wahala koda zan mance shi, na mance shi baki daya. Amma na saka a raina na haƙura da wanda ba ya sona tunda dai ba a dole."


Jinjina kai Haulatu ta yi.


"Gaskiya dai, ni fatana ma Muhsin ya sace duka zuciyar taki. Amma dai ba za ki yarda ya dinga zuwa zance ba ko? Kinsan fa Yaya Sadauki ya mana gargaɗi."


Cike da zolaya ta amsa.


"Ya mana gargaɗi ko ya maki gargaɗi?"


Da rashin fahimta Haulatu ta ce.


"Ban gane ba, ina ce mu duka ya ja wa kunne akan kula samari."


Dariya sosai Safina ta yi.


"Eh hakane, amma mu kam mun san komai. Tuni mun fahimci Yaya Sadauki sonki yake yi."


Turus Haulatu ta yi don sai da gabanta ya fadi. Wani daɗi ya tahomata har yana shirin nunawa a fuskarta amma ta yi saurin dannewa ta hanyar ɗan sauya fuska da nuni da ƙirjinta.


"Ni kuma? Mts, amma ke da waɗanda ku ke wannan tunanin kun..."


"Har da Maama fa." Safina ta katse ta. Sai ta yi tsit, suka kwashe da dariya sannan Haulatu ta ƙarasa da fadin.


"Kun iya tunani zan ce ai."


Suka ƙara darawa. Ta girgiza kai.


"Kawai fa haka ku ke gani, amma ni babu wata soyayyar da ke tsakaninmu. Mutumin da ba ya ko kirana a waya? Hum um, sai mu jima fa ba mu haɗu ba idan dai ba gaisawa ya shiga yi da Hajja da Umma ba."


"Toh ai ba anan take ba, duk wanda ya zauna da ku ko na ɗan mintuna ne sai ya fahimci kamar ku din kuna son juna. Ni fa har da su Yaya Najeeb da Haidar gulmar suke yi."


Ajiyar zuciyar ta sauke, ina ma wannan hangen ya tabbata? Yaya Sadauki ya kaunace ta? Wai! Tabbas da ta ji daɗinta. 


"Kinsan kuwa wata gulma, wai Anti Jannat ta zo gidannan amma ta sauka a wurin Momi Nuratu wannan karon, ba za ta tafi ba sai bayan bikin Maama. Hum, ace mace ba kamun kai, ki yi ta bin namijin da ba kya gabansa? Zubar da mutunci kawai."


Tun da Safina ta ambaci sunan Jannat wani abu ya tokare maƙoshin Haulatu. Har wani ɗaci take ji a ranta, wato ta zo ne don koyaushe ta dinga ganin Yaya Sadauki? Ranta ya yi zafi, Safina ta gane ta sauya don koda suka ɗora hirarsu tana mata batun ɗinkinsu da zasu sanya ranar ɗaurin aure da walima, don bikin na rana ɗaya ne kawai, amma gaba daya Haulatun hirar ba ta gabanta. 


"Wai lafiya? Kodai don na yi batun Anti jannat ne?"


Ta haɗe rai.


"Ni na ce maki? Ina ruwana da ita? Idan ta ga dama ta dawo zama a gidan nasu baki ɗaya me zai dame ni?" 


Safina duk iyakar ƙoƙarinta na ganin ta danne dariyarta ta kasa don haka kawai ta sake ta ta fito. 


"Mene ne?" Cewar Haulatu tana harararta. Sai da ta yi mai isarta kafin ta ce.


"Ƴar air, a ce maki kina sonsa ki karyata. Duk fa na gane kishi ne ke cin zuciyarki don kin ji na mako batun zuwan Anti Jannat. Hum, wai don Allah kina son Yaya Sadauki? Wallahi kun yi bala'in dacewa."


Tambayar da ba za ta taɓa amsa mata ba don haka ta miƙe tana jan guntun tsaki. 


"Oho, mene abin dacewa a ciki? Ni ba ya gabana. Malama tunda ba ki da abin faɗi ban lema na fice kafin ki ɓatan rai."


Nan da nan Safina ta hau ba ta haƙuri da alkawarin an bar zancen, a dole ta koma ta zauna, aikuwa aka juya zuwa hirar makaranta amma fa batun zuwan Jannat na maƙale a ran Haulatu. Koda ruwa ya dauke mikewa ta yi suka yi sallama ta sauko, dama ta riga ta gaida Baba Alhaji da safe don haka kawai ficewa ta yi daga gidan zuwa nasu. A sannan biyar da mintuna na yamma amma duhun garin sai mutum ya ɗauka magriba ta yi. 


Bayan sallar isha'i kuwa ta kasa nutsuwa kawai sai ta kwashi kayan karatunta, hangowa take kamar ga Yaya Sadauki zaune a falon Momi Nuratu tare da Anti Jannat su na hira. Wannan yasa sam karatun ya ki shiga, ƙarshe ta tattara da nufin tafiya can idan ya so Fu'ad ya koyamata. Amma tana zuwa falo Umma ta rusa fitar don cewa ta yi.


"A na wannan yayyafin za ki fita? Ki hakura mana gobe tunda dai asabar ne kya je ya koyamaki."


A dole ranta babu dadi ta juya zuwa ciki, a saman gadon ta zube gami da rufe idanu. Zuwa a lokacin ta yarda tana son Yaya Sadauki, tana kokarin dannewa da ɓoyewa ne gudun abin da zai je ya zo. Ba ta son ta faɗa tarkon namiji har ya samu damar cin zarafinta, ko ba komai ta ga darussa da dama akan ƴan uwanta da ma mahaifiyarta dangane da maza. Ko su Safina ta yiwa kanta alkawarin za ta jure ba za su taɓa sanin sirrin zuciyarta ba. Takan ji haushin kanta, ita da ba ta yarda da soyayya ba, amma son ya yi mata dirar mikiya a zuciya ba tare da ta shirya ba, tabbas ba ta taɓa hasko hakan a cikin ƙaddarorin rayuwarta ba. Wato soyayya da ma tunanin aure. Amma a yanzun ji take idan har da Yaya Sadauki ne, toh auren ma ta shirya. Daƙyar ta wancakalar da tunane-tunanenta ta miƙe ta yi falon don ɗebewa kanta kewa. 


***

 Jannat tana ɗakin da ta sauka a ɓangaren Momi Nuratu, sai safa da marwa take yi, tunaninta ta ya ya za ta samu damar zuba garin maganin nan na wajen Bokanya a abincin Yaya Sadauki. Wannan yana daga babban maƙasudin zuwanta gidan, sai kuma turaren da za ta yi amfani da shi har ya shaƙi ƙamshinsa. Ta jefa ƙullin maganin a cikin rigarta ta fito zuwa falon cike da burin cimma manufa. Kai tsaye kicin ta nufa inda ta ji Momi Nuratu ta bayar da umarnin a yiwa Sadauki farfesun kaza sakamakon murar da yake yi ya kasa cin komai.


Matashiyar ƴar aikin Momi Nuratu mai suna Ummi, ta kammala haɗa komai na farfesun a wuta bayan tafasa kazar, jira ta ke yi kawai ya ƙarasa ta jiye a flask ta ba Fu'ad ya miƙa kamar yanda Momi Nuratu ta umarta. Tana nan tsaye ta kafa waya a kunne tana sauraron labarin wani littafin hausa da aka tura mata audio ɗinsa Jannat ta shigo kicin ɗin. Ita a farko ma ba ta kula da ita ba sai da ta ƙaraso sosai. Cikin sauri Ummi ta kashe sautin gami da fadin.


"Sannu Anti, wani abun ki ke buƙata?"


Jannat ta dube ta, kamar ta watsa mata harara sai ta danne ta jefamata murmushin yaƙe don ita a duniya ba ta taɓa sakarwa ɗan aiki fuska, ba ma iyaka na gidansu ba, ko a nan ƴan aikin na gulmar irin girman kanta da ma yanayin yanda ta ke wulaƙanta su kai ka ce ba mutane ba ne.  


"Yes, am..ku na da quaker oat a store?" 


Ummi ta ɗan gane me take nufi tunda cimar Fu'ad ce, tana yawan dafamasa da safe. Ta gyaɗa kai.


"Eh akwai."


Jannat ta kai duba ga tukunyar farfesun wacce ƙamshinta ya karaɗe kicin din sannan ta dubi Ummi.


"Ok, je ki daukomin bari na taya ki ɗora ruwan."


"Lah, ai akwai ma a kicin ɗinnan, kin gan shi. Ɗazu na damawa Yaya Fu'ad da safe, na mance ban maida ba."


Jannat ta ji kamar ta shaƙo wuyanta. Sai ta basar da cewa ok. Ita dai Ummi mamaki ke ɗawainiya da ita, matar da tun zuwanta sai dai ta yi ta ba ta umarnin aiki kamar ita ta ajiye ta a gidan, amma kuma yau ita ke kokarin yin abu da kanta. Ita dai ta karasa ta duba farfesunta ya yi, hankalin Jannat na kan Ummi dake kwashe farfesun tana zubawa a foodflask. Ta kammala ta ɗora saman tray ta ɗauraye ɗan bowl da serving spoon sai cokali duk ta goge ta ɗora saman tray din. 


"Na waye?" Cewar Jannat.


Ummi da girmamawa ta amsa.


"Na Yaya Sadauki ne."


"Kawo na miƙa masa, dama yau ba mu gaisa ba ashe ba ya jin dadi."


Kamar kar ta bayar tunda ga umarnin da Momin ta yi mata amma kuma ai ba ta isa ta hana Jannat ba. Ba ta shiryawa cin mutuncinta ba don haka ba musu ta miƙa mata. 


"Idan ya tafasa ki haɗamin kafin na dawo."


"Toh." Ummi ta amsa. Bayan fitarta ba jimawa sai ga Fu'ad ya shigo. 


"Ummi, ina saƙon Yaya Sadauki? Ya kira yana faɗa ban kai masa ba."


"Yanzun nan Anti Jannat ta tafi ta kai."


Ya ɗan bugi bakin ƙofar kafin ya fice yana mitar Jannat za ta jazamasa faɗan da ya fi na farko kenan, ai shi Yaya Sadauki muddin ya sanya ka aiki bai ga ka yi ba wani ya yi, to fa kawai ba ya maka uzuri sai dai ya ce dama ba ka yi niyya ba. A ƙarshe kuma ya hukuntaka. Wannan dalilin ya sanya Fu'ad sauri-sauri wajen bin bayan Jannat. Har ya kusan cimma ta, sai ya ga ta dire tray din a hankali tana waige-waige, ganin za ta juyo ya yi saurin laɓewa a jikin ginin da ya raba corridor ɗin da barandar shiga wurin.  Mamaki ne ya cika shi ganin ta buɗe murfin ta kunce wani gari ta barbaɗa da sauri kafin ta ɗan gauraya ta hanyar jujjuya flas din sannan ta maida ta rufe. Garin kuwa ta yi azamar ƙullewa ta jefa a inda ta ciro. Sosai Fu'ad ya razana, tana soma tafiya ya yi saurin ƙarasowa amma ya yi iyakar kokarinsa wajen shanye mamakinsa da firgicin da ta jefa sa ciki. 


"Sis." Kusan a firgicen ita ma ta waigo, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya.


"Kai amma ka tsorata ni. Sam ban ji tahowarka ba."


Ya yi dariyar yaƙe. 


"Oh, ina ta sauri na cimmaki, uhm, don Allah bani na kai, na rantse idan Yaya ya ga ba ni ne na kai ba faɗa zan sha. Yanzu ma haka ba jimawa sai da ya kira ni yana tambayar wai ina saƙonsa da Momi ta ce na kawo? Shi ne na ƙarasa kicin Ummi ke cemin kin karɓa. Taimaka please."


Daga yanayinsa ta gamsu da cewa bai gan ta ba don haka ta ɗan yi murmushi.


"Shikenan, karɓi ka kai. Dama na so mu gaisa ne na ji ba ya jin dadi. Amma idan ya shigo ciki na gaishe shi."


Ya sa hannu ya karɓa yana maida mata martanin murmushin.


"Yauwa godiya nake."


Daga haka ya ƙarasa zuwa ƙofar ɗakin Yayan nasu ya ƙwankwasa kafin murɗa ya shige da sallama. Sai da ta ga ya shige ya rufo ƙofar sannan ta yi wani tsalle har da rawa don jin dadi, da sauri ta fice son ta sanar da Maminta a waya. 


A ɓangaren Fu'ad kuwa, zaune ya iske yayan nasu a falo yana share hanci da tissue, saman hancin nan ya yi ja ga dukkan alamu yana jin jiki don ko a muryarsa za ka fahimci lallai yana fama da mura. Bayan ya ajiye tray din ya tsaya, shi bai zuba ba kuma bai miƙe ba. Har sai da Sadauki ya rage ƙarar tv dake aiki ya dube shi.


"Lafiya?"


Fu'ad bai yi nauyin baki ba ya labarta masa duka abin da ya faru. Sadauki ya yi mamaki shi kansa, ya sani dama bai wani yarda da yarinyar ba har da zamanta a nan, sai dai bai kawo har wuyanta ya yi wannan kaurin ba. Ajiyar zuciya ya yi. 


"Dauka ka je ka ba masu gadi."


A ɗan tsorace Fu'ad yace. 


"Yaya, kar ya cutar da su."


Murmushi Sadauki ya yi. 


"Kar ka damu, ba abin da zai faru. Ai ba su aka yi wa ba. Na kuma sani, ko mene ne ba zai wuce don abu ɗaya ta yi shi ba. Jeka ka kai musu, koda Momi ta tambaya ka ce ka zubamin na sha kawai."


Daga haka ya kwantar da kai, yunwa yake ji ba kuma ya jin ɗanɗanon komai, amma ya gwammace ya haƙura zuwa gobe. 


"Ko a yi maka wani abun?"


Tambayar Fu'ad ta sanya shi ɗago kansa ya kalle shi. 


"No, kar ka damu, i'm ok."


Daga nan Fu'ad ya dauki flask din ya bi ta ƙofar da za ta sada shi da farfajiyar gidan nasu kai tsaye ba ta ɗayan hanyar da ya shigo ba. Ba jimawa ya dawo ya ajiye kwanukan gami da yi wa Sadauki sallama, har zai fita ya ji Sadauki ya dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Dawowa ya yi.


"Na'am." Ya amsa. 


"Bana son kowa ya san zancen nan. Koda Momi."


"Toh Yaya." Ya amsa ba don haka ya so ba domin jikinsa har tsuma ya ke yi don ya je ya sanar da Momin tasu. Amma kuma tunda har Yayan nasu ya taka masa burki ya sani idan ya aikata zai yabawa aya zaƙinta. 


Shi kuwa Sadauki ko bayan fitar Fu'ad lamarin ya yi ta juyawa a kwanyarsa, duka-duka nawa Jannat take da har ace ta san hanyar gidan ƴan tsibbu? Waye ya koyamata? Anya kuwa a gida an sani? 


Haka ya yi ta watsawa kansa tambayoyin da rashin mai amsawa ya sa kawai ya rufe da addu'ar Allah ya shirye ta. 


A ɓangaren Jannat ko, tana can cikin zullumi a falo, Zuhra na mata hira amma ita rabin hankalin ya na ga ƙofa, so take ta ga shigowar Fu'ad, aikuwa yana zuwa ko zama bai yi ba ta ce.


"Ya jikin Yaya Sadaukin? Ya kuwa samu ya sha farfesun?"


Fu'ad ji ya yi kamar ya zage ta, sai kawai ya daure ya ce eh. 


"Kai Yaya Fu'ad, maimakon ma ka tsaya ya kammala ka kwasomana sauran mu sha?" Cewar Zuhra. Harara ya banka mata sannan ya ja guntun tsaki yana mai miƙewa lokaci guda, shi ba ya ko son kallon Jannat din. 


"Au kodai tare ku ka sha ne ma?"


Zuhra da ba ta haƙura ba ta ƙara furtawa. 


"Ki tashi ki je ki tambayi mai shi ba ni za ki tsaya yiwa tambayoyi ba."


Daga haka ya mike ya bar wurin don shi ko kallon Jannat din ma haushi yake ba sa. Jannat dai dadi kamar ta yi me, ta tabbatar burinta ya kusa cika akan Yaya Sadauki. Tabbas idan ta aure shi ta gama morewa. Wadanda za ta yiwa ɗagawa suna da yawa. 


Da wannan ta yiwa Zuhra sallama ta shige daki don ta ce bacci ne a idanunta. Zuhra kuwa ta amsa da toh kawai don hankalinta ma ya koma lan waya. 


***

Kano...


Hindatu zaune ta yi shiru cikin yanayi na tunani, tun faruwar lamarin da ya kusan yin sanadiyyar zubewar cikin jikinta, ta soma ganin kulawa ta musamman fiye da baya a gurin mijinta Ɗan Mutuwa. Ita ba wannan ke damunta ba a yanzu face wayar da ya yi a kan kunnenta sadda tana kwance a gadon asibiti, duk a iya tunaninsa bacci take yi sai dai tun soma wayarsa ta motsa a lokacin amma kuma ta ƙi nuna komai. Da wani Honarabul suke waya inda yake fadin.


"Kai bari Honarabul, farko na kaɗu ai, duk a zatona cikin nan ya fice, da ban san me zan faɗawa Shugaba ba. Ai yanzu dole zan yi takatsantsan har zuwa sadda zan cika umarnin ƙungiya. Batun Na'imatu kuwa na haƙura tunda dai kana gani Shugaba ya tabbatarmin idan na dage akan sai mun ga bayanta, to karfin addu'ar da take yi zai sa komai ya juya kanmu."


A lokacin jin motsin za'a shigo ne ya sa shi gaggawar katse kiran, ita kuwa ta yi kamar tana bacci har sai da Nos ta ɗan taɓa ta za ta yi mata allura sannan ta motsa. Gaba ɗaya ta kaɗu da abin da ta tsinta yana faɗi, ta ma kasa tuna wace ce Na'imatun a kwakwalwarta tsabar ruɗani. Wato dai ya tabbata zargin da take yi wa Alhaji Ibrahim tun farko hakan ne? Ko kuwa ita ce ba ta fahimta ba? Cikin ta shafa wanda ko watanni uku bai cika ba, cikin jikinta yake so? To wane ne shugaban da zai ba? Tun sadda ta ji wannan zantukan ta ke yawan zama cikin tunani da firgici, ta kuma kasa sanar da ko Momi ce don ta sani zai wahala a yanda idanunta suka rufe ta amince. 


"Bebina, tunanin me ki ke yi?" Yadda ta zabura ta rikice ta miƙe sai da shi kansa Ɗan Mutuwa da ya yi furucin ya tsorata.


"Lafiya?" Sai ta yi saurin girgiza kai da sauke ajiyar zuciya. 


"Babu komai, ban san ka shigo ba ne shiyasa."


Ya yi murmushi ya kamo hannunta ya maida ta mazauninta.


"Ni wannan tunane-tunanen naki sam ba na kaunarsu, ko har yanzu ba ki haƙura kin yafemin ba?"


Yaƙe ta dan yi. 


"Komai ya wuce, dagaske nake."


Ya shafi gefen fuskarta.


"To ki kwantar da hankalinki, ina nan ina nema mana visa, zan kai ki Dubai ki ɗan buɗe idanu ki huta abinki."


Ita sam abin bai burge ta ba sai ma sabon tsoro da ta shiga, ta girgiza masa kai.


"Aa, nagode amma ni dai na fi son garin nan. Ba na son zuwa ko'ina."


Ya ɗan haɗe fuska.


"Mene ne haka? Au, watsamin ƙasa a ido za ki yi?"


Hindatu kamar ta yi kuka don ita komai na gidan ma ba iyaka maigidan ba, tsoronsu take ji. Balle kuma abin da zai fito daga hannunsa.


"Allah kuwa dagaske nake, ni bana ra'ayin zuwa ko'ina."


Ya yi dariya gami da ɗan rungumota kaɗan. 


"To mene ne abin tayar da hankali? Shikenan ya isa kar ki yi min kuka."


Tuni ta soma hawaye don ji take kamar ya ɗosana fuskarta a kan wuta. Ba ta so ta dinga gudunsa da yawa ya zargi wani abun don haka ta share fuskarta kafin ta ce.


"Ni dai ka bar ni na je gidan Momi na yi kwanaki." 


Ɗan Mutuwa ya ɗan yi shiru, sai kuma ya tuna zai fi samun damar aiwatar da shirinsa akan Hajiya Adama shi da su Duna a nutse. Ya rantse sai ya dauki fansar kayansa da ta saka aka kama wanda har Abuja ya je amma bai ci nasarar da suka fito ba, sai dai ya samu sunansa bai fito ba kwata kwata don yaron da aka kama da kayan ko za'a mutu ba zai taɓa tona asirinsa ba, yanzu dai sai an kwana biyu zai san yanda zai yi yaron ya kuɓuta a hannun hukuma. Dalilin kenan da ya dauki alƙawarin illata kayayyakin Hajiya Adama koda hakan na nufin ƙone ɓoyayyen store ɗinta da ke can cikin daji inda take ajiyar kayan ne. 


"Shikenan, kar ki damu, ki shirya gobe ki je sai ki kwana biyu. Sati ɗaya ya yi maki?"


Ta girgiza kai bayan ta ɗago daga ƙirjinsa tana dubansa.


"Please na yi sati biyu?"


Ya ɗan yi shiru yana dubanta, ya kula kamar a tsorace ta ke da shi, bai kawo wai ko ta samu wani labari ba ne face ta tsorata da irin dukan da ya yi mata, wannan ya haifarmata da shakkarsa. Don haka ya riƙo hannunta da ya ji har wani rawa suke yi. Ya bi yatsun da kallo kafin ya dube ta. 


"Bebina kamar tsorona ki ke ji? Na fa yi maki rantsuwa akan ba zan ƙara taɓa lafiyarki ba. Ko ba ki yarda ba?"


Yaƙe ta yi.


"Na yarda."


"To nidai ki bar wannan tsoron, kuma batun sati biyu a gidan Momi, na amince. Yi murmushi na gani?"


Ta kuwa saki fuskarta sosai don ta ji dadi. Za ta samu damar yiwa Momi zancensa. Ita ta saka ma a rai idan ta taka ƙafa ta bar gidan har abada ta bar shi kenan. Wannan dalilin ne yasa koda ta tashi shirya kaya, akwati babba ta ɗauka ta haɗa komai da ta san yana da muhimmanci a wajenta ciki har da takardun makarantarta. 


***

 Katsina...


Haulatu da Safina sun yi nasarar ƙona layar da suka tsinta a ɗakin Maama, hankalinsu ya kwanta hakan ya sa koda suka tashi dawowa daga Islamiyya zuƙatansu fes saboda jin dadi. 


"Wai ku shi ne ɗazu ko ku jira ni ku ka yi ficewarku ko?" Faɗin Radiya tana harararsu.


"Kai Radiya, ke da ban sanki da ƙorafi ba? Zama da Haulatu ta sa kin koya kenan."


Haulatu ta kai wa Safina dundu ta kuwa kauce suka yi dariya. 


"Ai shikenan, na yi shiru tunda kun ɗauke shi matsayin ƙorafi. To goben dai zamu ke gidan ƙunshin ko?""Me zai hana? Bikin Maamanmu guda? In sha Allahu. Kinga Safina don Allah ki tashi da wuri ke ce dama mai shegen nawa idan kin so. Sai a shirya a yi ta jiranki. Ni har kitso ma zan yi a gobe in sha Allahu."


"Kawai kin san idan na tuna ranar bikin sai mun shiga makaranta haushi nake ji fa." Faɗin Safina tana yamutse fuska. 


Haulatu ta bi garin da kallo yanda hadari ke faman haduwa kafin ta ce.


"To ai kuwa zuwa kinsan dole ne, akan biki dai nasan ba za'a bari mu yi fashin makaranta ba sai dai ko idan zamu nuna ba mu da lakca ranar."


"Ni kam da sauki, English ne kawai zamu yi kuma da safe ne, daga shi ba ma komai. Malam Bilal ya maida ajinsa ran Friday da safe." Fadin Radiya tana musu dariyar mugunta, suka bi ta da harara kawai. Haka suna tafe suna hirarsu da tsokanar juna har suka karaso gidan. 


"Ke, ga mutuminki can tare da Yaya Khaleefa."


Jin abin da Safina ta ce har tana ɗan zungurinta ya sa Haulatun kallon gaban ƙaton ƙyauren gidan. Suna tsaye a gefe kusa da shukoki, motar Yaya Khaleefa a fake, Yaya Sadauki sanye da jallabiya baƙaƙirin mai adon golden din zare a wuya da bakin hannu. Irin mai mannewa a jiki da ya taimaka wurin fiddo tsarin halittar da Allah ya yi masa na ƙirar namiji. Sam hankalinsu bai je garesu ba, ga dukkan alamu abin da suke ta tattaunawar mai muhimmanci ne. Ta kauda kai daga kallonsa ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. To mene ne na fitowa bakin titi salon ƴan matan makarantarsu su yi ta kallonsa? Sai ta shiga waige, ta ga kuwa wata budurwa dale tafe tare da ƙannenta uku hankalinta na kansu, saboda tsabar kishi da ta ji ya tokare maƙoshinta sai ta ke ganin kamar ma murmushi budurwar ke jefamasa. Shi ta ke kallo, ba shi take kallo ba, ita dai Haulatu kawai tunaninta ya ba ta hakan. Don haka nan da nan ta tamke fuska, wai sai ta ji Yaya Sadaukin ma na ba ta haushi.

Sai da suka kusan isowa dab da su sannan ne idanunsu ya kai garesu. Sadauki na kula da irin yanda mutuniyarsa ke faman cin magani da hura hanci. Khaleefa kuwa kauda kai ya yi don ba ma ya so ya cika kallon Haulatun, ya yi nasarar fara mancewa da ita, dama bai zurfa da yawa ba, ba ya son abin da zai maido mishi hannun agogo baya. 


"Yaya Khaleefa ina yini, Yaya Sadauki ina yini." Haka suka jero gaisuwar kusan duka lokaci guda, su ma suka amsa musu da lafiya lau. Har za su shige Sadauki ya yi magana yana duban Haulatu. 


"Ita kuma wannan wa ya taɓa ta?"


Safina da Radiya har Khaleefa suka dube shi kafin su maida duba ga Haulatu, Khaleefa ya kauda kai yana ɗan murmushi, ya kula dagaske dai Sadauki yake son Haulatu, sam shi bai wani kula da sauyin fuskarta na a zo a gani ba. Haulatu kuwa kallon Sadaukin ta yi sai ta ga kamar ma har wani haske ya ƙara, irin kallon da yake jifanta da shi ya sanya ta kauda kai cike da jin kunya. Ba su amsa ba sai ita ce ta ce.


"Bakomai." 


"Are you sure?" Bai damu da kallon da  Khaleefa ke bibiyarsa da shi ba ya ƙara tambayar, Haulatu ta gyaɗa kai. 


"Ok, ku shiga gida."


Daga haka suka wuce cikin bin umarninsa. Ya maida kai ga Khaleefa wanda ya ƙuramasa idanu yana ɗan murmushi mai ɓoye abin da ke ransa. 


"Me nayi toh?" Fadin Sadaukin shi ma ya na murmushi. 


Ɗan taɓe baki Khaleefa ta yi. 


"No, ka ji na tanka? Kawai sai ka tsargu?" 


Suka yi ƴar dariya. 


"Have you confess?" Cewar Khaleefa. 


Har lokacin bai bar murmushin ba ya ɗan dubi hadarin da ke ƙara haɗuwa ga iska mai daɗi dake kaɗawa ya amsa. 


"Not yet."


"Ka na jiran me toh? For how long za ka tsaya kana fama da abu guda? Ba ka tsoron wani ya yi maka shigar sauri?"


Da mamaki Sadauki ya ce.


"Tun yaushe ka sani?"


Khaleefa ya yi ƴar dariya gami da dukan kafaɗarsa kaɗan. 


"Ka ga bari na tafi kafin ruwa ya tare ni. Sai mun yi wayar ko?"


 

Murmusawa Sadauki ya yi, ya san ko zai ƙara tambayar idan dai Khaleefa ne ba zai samu amsar ba don haka ya bar maganar shi ma. Suka yi sallama shi kuma Sadauki ya koma ciki. 


***

  Washegari kuwa da wuri suka ɗunguma gidan ƙunshi. Sun ci sa'a babu wani layi, don matar ta iya ƙunshi, kusan ko ba lokaci na biki ko sallah ba, gidan Hasiya Mai Ƙunshi  yakan zama da mutane. An yi musu ja mai ɗan karen kyau sai baƙi a iyakar hannu, sai dai sun zaunu don ba su suka bar gidan ba sai da aka idar da sallar isha'i. Ga gajiya ga yunwa, Haulatu kanta har wani sarawa yake yi. Hajja ta kira ya fi a ƙirga tana masifa wai ita wannan wane irin ƙunshi ne haka ace har yanzu ba su dawo gida ba ga hadari ya haɗu a garin. 


Sadda Hajja ke wayar ƙarshe da Haulatun bayan sallar isha'i tana mitar dare ya yi su jira za ta sanya a zo a ɗauko su, Sadauki na nan ya shigo kawo wa Hajja saƙo daga Daddynsa ya tsaya suna ɗan taɓa hira da Umma da kuma Haj Hadiza da ta shigo gidan tun safe anan ta yini an kira mata mai ƙunshi ta yi mata. Hankalinsa na ga Hajja har ta kammala wayar ta ajiye ta cigaba da sababi.


"Saude, maza zo nan, ko kuma ke Na'imatu karɓi ki bincikomin lambar Gali, ya zo ya ɗaukomin yaran nan."


Jin haka Umma ta miƙe ta ƙarasa ga Hajja, shi kuwa Sadauki duban Hajja ya yi.


"No Hajja, bari na ɗauko maki su. Wane unguwa ne?"


"Kai Allah ya yi maka albarka Sadaukin Alhaji, daɗina da kai akwai kirki. Nan unguwar Sabon Gida. Idan ka je kwa yi waya su maka kwatance."


Haj Hadiza ba ta ce musu uffan ba har Sadauki ya miƙe ya musu sallama ya fita Hajja ba ta bar sa mishi albarka ba, ta kalli Umma dake faman murmushi, ta watsamata kallon banza a ranta faɗi take. 


'Makira, kin ƙullo wani surƙullen nasu na bariki dole ki yi murmushi tunda kwalliya ta biya kuɗin sabulu.'


A fili kuwa miƙewa ta yi tana fadin.


"Hajja bari na zo na tafi kafin ruwan nan ya sauka tun da na kammala, sai kuma jibin idan Allah ya kaimu."


Hajja ta amsa. 


"Toh shilenan, ki gaida gida. Jibin dai ki shigo da wuri, kuma a yiwa wancan mai kunnuwan kashedi, muddin ya hana min Maimunatu shigowa sabga da kaina zan kira shi a waya tunda shi dai bai san mutunci ba."


Dariyar da bai kai zuci ba Hadiza ta yi. 


"Ah Hajja ai ke ce daidai da wannan ɗan naki."


Umma kuwa cewa ta yi.


"Hajja kenan, idan har ya hana ai babu yanda za'a yi sai haƙurin tunda dai ya fi mu iko da ita."


Haj Hadiza kamar ta buge Umma haka ta ji, ta san watakila ma Umman a ranta dadi take ji. A kwanan nan har matsala sosai Maimuna ta samu akan ta je bikin dangin Musbahun mijinta ta kai dare shi ne fa ya sanya mata takunkumin fita. Sun yi fada sosai har kokarin dukanta ya yi, magana dai har gaban mahaifinta ƙarshe aka yi sulhu ta koma. Yanzu kuwa ya ce babu inda za ta ƙara fita idan ba larura ba sai ya hora ta. 


"Ni da kaina zan yi kiran Musbahun."


Umma dai kallon Hajja kawai ta yi gami da girgiza kai ba tare da ta ce uffan ba. Hadiza ta harare ta karo na biyu sannan ta shige ɗakin Hajjar ta kimtsa ta fito, sallama ta yi musu ta fice tana ƙara maimaitawa Hajjar batun zuwan Fahima a gobe. 


Bayan fitarta Umma ta Hajja magana sosai kan rashin dacewar yi wa suruki kutse gudun raini, ba girma a ciki. Hajja ta dube ta. 


"Toh kenan kina nufin na zuba ido ya cutar da Maimunatu? Don ya ganta yarinya ba mai son hayaniya ba?"
"A'a, ba nufina kenan ba. Ki bar ni zan yi magana da Maimunatun, in sha Allahu za'a dace, zai bar ta ta fito. Amma abun duka ba na tashin hankali ba."


"Ai shikenan." Ita ce amsar da Hajja ta ba Umma sannan aka bar maganar. 


***

 Haulatu a can kuwa tun da Hajja ta ce mata Sadauki ne zai zo ɗaukar su ta ji wani irin sanyi a zuciyarta, sai ta nemi ciwon kan ma ta rasa. 


"Wai ke murmushin me kike ta yiwa mutane ne? Ke ko jimamin daren da muka yi ba kya yi? Ni dai na san Mama yau zan sha faɗa." Radiy ke maganar duk ta rikice duk kuwa da sun yi waya da Mamar, ta sanar da ita Hajja ta saka a zo ɗaukarsu amma hankalinta bai kwanta ba.


"Rabu da ita Radiya, ni wallahi dama na ce maki son Yaya Sadauki take yi amma ki na ganin kamar wasa ko? Yanzu ke ba ki kula duk cikin murnar zai zo..."


Haulatu ta yi saurin toshe mata baki ganin wasu mata dake cire lalle su na kallonsu. Cikin ɗan raɗa ta ce. 


"Banza, mene haka wai? Ba kya ganin a cikin mutane muke?" 


Dariya Radiy da Safina suka yi duk kuwa da gajiyar da ke tattare da su, don ma Allah ya sa sun sauke nauyin sallolinsu. 


Wayar Haulatun ce ta yi ƙara, ganin sunan Yaya Sadauki saman screen sai ta nutsu gami da ɗagawa da sallama. Ya amsa mata kafin ya ce.


"Ba wa Safina ta kwatanta min inda ku ke."


"Ai zan iya ma Yaya."


"Ko? Toh ina jin ki. Allah yasa kar ki ɓatar da ni."


Ta yi ƴar dariya wanda shi ɗin ma tana jin sautin nasa murmushin. Tiryan-tiryan kuwa ta yi masa kwatance tunda dama gidan bai da wani ɓata kusa yake da transfomer a gefen titi. Ai kuwa ba jimawa da katse wayar sai ga shi ya ƙara kira ya ce su fito. Dama sun kammala komai suka yi sallama da Hasiya mai ƙunshi da matan dake nan suka fito. Motarsa tana daga tsallaken gidan har ya yi U-turn. 


"Kalli mutuniyar sai wani goge maiƙon fuska take da gefen mayafi."


Radiya ke yiwa Safina zancen ƙasa-ƙasa, tana jin su amma ba ta da sukunin ramawa don gani ta ke yi kamar kowane motsi da za su yi idanun Yaya Sadauki yana kansu.  


Duk saurin da Radiya da Safina ke yi don su samu mazauni a gidan baya amma ina, Haulatu ta yi farat ta buɗe ta shige ta saitin bayan Yaya Sadauki. Nan da nan kuma Radiya ta riga Safina shiga ɗaya ɓarin, a dole Safina ta buɗe gidan gaba ta shiga. Sadauki ya kalle ta bai ce komai ba ya na amsa gaisuwarsu. Sai da ya kunna fitila haske ya mamaye motar, sannan ya dube su, Radiya ya iya gani bai samu damar kalle sanyin idaniyarsa ba don ta maƙale sosai a murfin ƙofar. Kamar ya ce wani abu sai kawai ya fasa ya kashe fitilar. Tafiya yake yi kawai sautin kiɗa na tashi kaɗan-kaɗan na muryar breaker cikin waƙarsa na Burina. Shi ɗin idan ya so nishaɗi yakan kunna waƙoƙi, ranar da ustazancin ke kansa kuwa sai dai ka ji tashin ƙira'a ko kuwa yabo. Sai yake jin waƙar Burina ɗin na shigarsa tamkar da shi ake, to ba shi kaɗai ba, ita kanta Haulatun sai ta lumshe idanu ta yi shiru tana shaƙar ƙamshin turarensa, kaunarsa na ƙara ratsa ta. Kafin su kai ga isa gida tuni an fara ruwa kuma waƙa ɗaya suke ta maimaici, daga Burina ya ƙare sai Sadauki ya ƙara ya ƙara maido ta. Sadda suka isa kuwa ruwan ya yi ƙarfi sosai, ya dube su. 


"Ga ruwa kuma, ko na baku lema tunda dare ya yi." 


Suka amsa da toh, ya ba Radiya umarnin saka hannu a baya ta dauko lemar sannan ta bude ƙofa ta fito da yake ita tana ta gefen wajen ƴar rumfar adana motoci sai ruwan bai taɓa ta ba har ta buɗe lemar. Haulatu ma ta fito ta ɓangaren hannun da Radiya ta ke, tuni Safina ita ma ta fice. 


"Ba zan ga lallen ba?" Maganarsa ta ɗan dakatar da Haulatun daga fita, ta juyo suka haɗa idanu, tarr suke ganin juna cikin hasken fitilar motar da ya kunna. Kusan a tare suka numfasa, ji ya yi lamar ya shekara bai gan ta ba. Ita kuwa Haulatu ta kasa ba shi amsa, ta kuma kasa fita. Can kuma a hankali ta haɗe hannuwanta ta yo gaba da su kaɗan yanda zai gani, ji ya yi inama halal ɗinsa ce, da babu abin da zai hana shi sumbatar hannun saboda yanda lallen ya yi mata kyau ainun. 


"Ya yi sosai, ku je kin bar ƴan uwanki cikin ruwa. Ki ajiye waya a kusa, zan kira."Ta ji abin banbarakwai sai ma ta kasa amsawa da sauri ta fita, duk diramar da suke yi, Safina suna kallo don hasken dake cikin motar ya ba su wannan damar ganin abin da ke faruwa a ciki. Suna kama hanya da gudu gudu suna yiwa Haulatu tsiya, ita ta ma yi laƙwas kamar wacce ruwan saman ya doka. Duk yanda Haulatu ta so su yada zango a gidansu kafin ruwa ya tsagaita amma ina, su kansu sun fi so su gan su a nasu ɗakunan musamman Radiya da Mamarta duk ta damu. Suka yi sallama Haulatu ta shige su kuwa suka yi gaba. 


Umma na ganinta ta harare ta.


"Wato ku ba ku san dare ya yi ba ko? Ku je ku zauna haka, idan da layi me ya hana ku haƙura?" 


Haulatu wacce ta zube a kujera cikinta har wani kuka yake yi tsabar yunwa, ita sai sannan mata ji ashe ciwon kan ba wai ya tafi gaba ɗaya ba ne, tsabar ɗoki da kauna ne ya sa ta ji ya lafa a ɗazun, haƙuri kawai ta ba Umma. Hajja kuwa sannu take mata bayan ta sa jikar Baba Saude da ta dawo daga ƙauye ta kawowa Haulatun abinci. Ita kuwa hannu ta mike ta wanko a banɗakin falon, koda aka kawo abincin tana can nunawa Hajja ƙunshi da Umma, sun yaba sosai, ta dauki farantin abincin da wayarta ta nufi sama. Hajja na fadin ta zauna ta ci tukunna amma cewa take yi sai ta yi wanka tukunna. Nan kuwa tunanin kar Yaya Sadauki ya kira ne a gabansu ya hana ta ci.  


*** 

 Safina kuwa tana shiga ɓangaren Baba Alhaji ta iske a na ta hayaniya,  Najeeb da Haidar ake riƙewa su kuwa suna ta botsarewa musamman Haidar akan a bar su su daki Anti Mabruka wai ta zagi Maama a gabansu. Maama na gefe tana hawaye, ƙarshe ta taso ta daka musu tsawa. Duk suka nutsu, Haidar jikinsa har rawa yake yi. Autan Maama, Nazifi ba ya nan, dama shi hannun Haj Fatima dake Kano, koda yana nan shi yana da sanyin zuciya kamar na Maama ba lallai ne ya ce uffan ba.


Jin hayaniyar ta yi yawa ne Baba Alhaji ya fito yana tokare sandarsa, nan ya dubi kowa ya kuma ba Anti Mabruka da Maama umarnin su zo ɓangarensa. Sai a sannan Najeeb da Haidar suka fice zuƙatansu babu dadi. A bakin mai kula da Nene, Yahanasu, Safina ke jin tun farkon abin da ya hada. Wai Anti Mabruka ce ta iske Maama a falon tana zaune da su Najeeb ta hau yi ja mata Allah ya isa tana kuka tana cewa ita ta yi mata asirin da ta rasa mashinshini kuma har ga shi nan babu kunya ba tsoron Allah duk da ta hayayyafa tana da budurwar zuciya. Abin dai babu dadin ji don har da zagi, dalilin fusatar su Najeeb kenan. Su da a baya ba sa goyon bayan auren Maama, sai suka ji wani kwarin gwuiwa kan ta yi auren bisa kalamin Anti Mabruka. 


 Baba Alhaji sosai ya yiwa Anti Mabruka tas, ya kuma rantse muddin ta sake yiwa ƴar uwarta munanan ƙazafi sai dai ta nemi wani uban ba shi ba. Kuka sosai ta saka wai dama can Baba Alhaji ya fi son Maama a kanta. Maama dama da hawayenta ta shigo, sanadiyyar baƙaken kalaman da Anti Mabruka ta shiga jefowa ya sanya Baba Alhaji jin wani jiri na kwasarsa daga zaune, dama ba wani cikakken lafiya ba, kirjinsa ya hau zafi nan da nan ya sume a wajen, a gigice Maama ta yi kansa tana salati, jin ihunta ya sa su Safina shigowa, duk da ruwan da ake bai hana sautin Maama fita ba, ganin har ruwa an yayyafa amma Baba Alhaji ba shi da niyyar farfadowa ya sa Maama karɓar wayar Safina bayan ta fidda nata password, ta kira Alhaji Ridwan. Ita kuwa Safina sheƙawa ta yi a guje kirawo su Najeeb. Su ma a gigice suka shigo falon Baba Alhaji, babu wanda ya bi ta kan Anti Mabruka da ta yi likimo a gefe kamar wacce aka tsoma a randa.  Ba jimawa sai ga Daddy Ridwan tare da Sadauki duka hankulansu a tashe. Ba a sanar da Baba Dakta ba gudun kar a tada hankalinsa don shi ma yana fama da matsalar ciwon sugar sai kawai a wannan ruwan suka yi asibiti da shi. 


Dalilin da ya hana Sadauki kiran Haulatu a daren kenan. Hajja ma ba ta sani ba, Umma ce kawai Maama ta kira ta sanar da ita bayan an jima har ma an shawo kan Baba Alhaji, hankalin Umma ya tashi sai dai bisa umarnin Maama ba ta sanar da Hajja ba ta ce a bari zuwa safiya tunda dare ya yi. Umma dai duka ba ta samu nutsuwa ba duk da an ce ya samu sauki har ya yi bacci ma. Haulatu koda ta ji sai ita ma ta shiga damuwa. 


Washegari kuwa da safe labari ya baza gida Baba Alhaji na asibiti ba lafiya, hankalin yan uwansa, Hajja da Baba Dakta ya tashi. Nan da nan aka ɗunguma zuwa asibitin duk kuwa da Dakta Hashim (mahaifin Safina) ya hana kowa shiga wurinsa don kar a takura masa amma Hajja da Baba Dakta sai da suka shiga suka gan shi hankalinsu ya kwanta. Ba wani abu ba ne ya haifarmasa da tashin hawan jininsa ba face damuwar da ya shiga, shi faɗan da yake yi ma a zo a sallame shi kar a sanya mutane zaryar zuwa dubiya amma Dakta Hashim, ya ce a bar shi ya samu hutu. 


Bayan sun fito ne Baba Dakta ke tambayar Barr Faisal dake gefensa abin da ya faru. Shi da bai da labarin ya yi shiru sai a bakin Sadauki ya ji komai. Maama ta labartamusu a jiya, hakanan ya samu ƙarin bayani daga bakin su Haidar din. Ran Baba Dakta ya ɓaci. 


"Mutuniyar banza, ashe shiyasa ban ga ƙeyarta a asibitin nan ba. Mabruka anya tana son gamawa da duniyarnan lafiya?"


Haka ya yi ta faɗa ita kuwa Hajja na taya shi. Dama Hajja yanlafiyar giwa... Dakyar dai aka taushe su suka haƙura suka bar zancen. 


A yanda Baba Alhaji ya matsa dole aka sallame shi don ya rantse shi fa a kansa ba za'a ɗaga auren Maama ba. Haka aka tattara aka koma gida sai dai a yammacin sai da Baba Dakta ya tara meeting na iyaka yaransu babu jikokin gidan. Ya wanke Mabruka tas a gaban su Maaman da su Daddy Ridwan, ya kuma sassauta a ƙarshe da yi mata nasiha kan imani da ƙaddara da nunamata komai ai yana da lokacinsa. Anti Mabruka dai ba don ta saduda ba sai don tilas, ta nemi gafarar Maama, har a zuciya kuma Maama ta amsa da ta yafemata. Daga nan dai aka rufe zancen da addu'a. Koda aka fito, Mabruka ji ta yi ta ƙara tsanar Maama, abin sam ya ƙi fita a ranta, wato yanzu ba iyakar iyayensu ba, hatta ƴan uwa kowa ya tsane ta sanadin Maama, ta ci alwashin koda Maama ta yi auren nan, babu ita ba kwanciyar hankali har abada. Da wannan ta shige ɗakinta ranta na susa. 


Haulatu dai kitson da ba ta je ba kenan, hakanan ta haƙura saboda wannan tashin hankali. Fahima ta iso a ranar sai ko wasu baƙi daga Malumfashi. Kirki da mutunci irin na Maama yasa gidan ya cika kamar wannan ne aurenta na farko don ita ɗin ta kowa ce sannan abin hannunta sam bai rufemata idanu ba. 


***

 Washegari...


RAYUWA DA GIƁI  16
Batul Mamman 💖

_Ya Rabbi. Ya Zhuljalal wal Ikhram. Allah ƴaƴanmu sun koma makaranta. Ka duba mana su da dukkan abokan mu'amalarsu da sauran ƴaƴan bayinKa. Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri. Ka kare su daga zamewa kowa sharri. Allah Kada a kai ƙararsu, kada su kai ƙarar wani. Ka basu ilimi mai albarka da amfani. Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini. Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da ƙasarmu take ciki. Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali. Ka makantar damu akan haram. Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu roƙi kowa. Ka buɗa mana. Ka albarkaci nema da samun mu. Ya Rabbi Ka kawo mana sauƙi da sassaucin rayuwa. Ka azurtamu daga taskarKa wadda bata da iyaka. Amin_

***


Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ƙauna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya miƙe tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.


"A duniya bayan iyayena da matata da kuma ƴan uwana da ba su guje ni ba da kuma ƙalilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haɗamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata."


Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da ɗanyen aikin da Taj ya ɓallo.


"Abba..."


Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.


"Kada ka damu Kamal. Ba zan taɓa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ƙara nesanta uba da ɗansa ba."


Daga Taj har Kamal ba ƙaramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce,


"Abba, Alhaji ya daɗe da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai ..."


Kamal ya katse shi da hanzari "wallahi zai ƙara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?" Ya mayar da idanunsa ga Abba "ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba."


Abba jinjina zumuncin ƴan uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faɗa musu.


"Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko shaƙiƙan da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba. Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida haƙuri. Na san za ta yi min uzuri."


"Sai dai idan ni ne baka son bawa ƴarka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta."


"Har a yaushe ka santa?" Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko kaɗan.


"Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode" 


Abba zai shige gida Ƴar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.


"Simagade....au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana ƙasa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta ɗorawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka."


"A'a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ƙiyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min."


Ƙofar gidansa ya ƙarasa da sauri don ƙirjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya faɗi a wurin. Ƴar Ficika aka sake samun abin yi. Ya ɗora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa.


"Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya."


"To, to" ya amsa kamar ba ɗan cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruɗewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe.


Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba. Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba zai yi mamaki ba. Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya haɗa da ɗanyen kai kamar wani ɗan ta kife. Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences.


Horn ɗin mota yaji daidai ƙofar gidan. Ya leƙa Taj ya fito a lokacin.


"Mu kai shi asibiti."


"Ai ka bari a faɗawa Yaya ko?"


Bai ma yi wannan tunanin ba. Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gyaɗa kai. Salatin Yaya su ka ji su ka koma cikin soron. 


"Damuwa ce Yaya. Kada ki ɗaga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki. Za mu kai shi asibiti." Ɗaga shi su ka yi Kamal ya ƙarasa dashi motar. Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi.


"Ƴar Ficika kuma ya ce..." 


Taj ya gallawa Ƴar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri.


"Wallahi ban faɗa mata komai ba."


"Me ku ke ɓoye min?" Ta tambaya hankalinta a tashe. Dama bata ga abin da zai ɗaga masa hankali ya faɗi ba. Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu.


Gani su ka zasu ɓata lokaci sai kawai Taj ya ce Ƴar Ficika ya faɗa mata in sun tafi.


"Amma don Allah ki bar maganar a wajenki kafin ya tashi mu san abin yi. Yanzu hankalin mutane ne kawai zai tashi."


"To, nagode. Idan kun je asibiti ka faɗa min. Sai na kira ƙaninsa ya taho."


Kana ganin yadda take magana sai ta baka tausayi. Da gani hankalinta ya kai ƙololuwar tashi. Tana dannewa ne kawai saboda mutanen cikin gidan.


*


Asibitin kuɗi Kamal ya kai su amma ba wanda ƴan gidansu su kw zuwa ba. Ana buƙatar file Taj ya buɗe musu na family. Aka shiga dashi ciki aka duba shi. Jininsa ya hau sosai shi da bashi da bp. Dole aka bashi gado ana jiran jikin ya daidaita. Drip aka saka masa da allurai sannan ya sami bacci.


Zaman jiran Abdulƙadir ƙaninsa Taj da Kamal su ka yi a ɗakin. Kamal ya dube shi a tsanake.


"Yanzu Happy duk abubuwanbda su ka faru da kai a gida ba su isheka ba? Kai da bakinka kake cewa za ka auri Hamdi. Auren ma gobe goben nan. Less than 24hrs. Har kana yiwa Abba ƙaryar sonta kake kawai don kafi kowa iya rigima."


"Allah da gaske nake ina sonta Happiness."


"Kai ɗin? Ya aka yi ban sani ba?" Ya tambaya don bai gaskata shi ba.


Babu wani juya zance ya ce "Saboda nayi tunanin za ka ƙaryata duk wata niyyata ta janyo Abba Happy Taj. Infact bana tunanin da ka sani ko zuwan farko ba za mu yi gidan ba in ka san waye babanta."


"Lallai ka iya ganganci. Banda ɓoye min da kayi da kuma kana can tayi saurayi fa?"


Taj ya yi murmushi "wallahi a next flight za ku ganni."


"Da ni na ce ina sonta fa?" Kamal ya yi tambayar idanunsa cikin na ɗan uwansa.


"In sha Allahu ma Allah ba zai jarabcemu da son abu ɗaya wanda mutum ɗaya ya kamata ya so ba." Ya haɗe kafaɗunsa don tsigar jikinsa tashi tayi.


"Next time kada ka ɓoye min abin da ya kamata na sani."


Gira Taj ya ɗaga yana ƴar dariya ganin Kamal ya ɗauki zafi da gsske.

"Bros, faɗa min gaskiya. Ba ka ciki ko? Kaga matar yara ce irina."


Fuska Kamal ya ɗaure amma da gani ya sauko "Ji min mutumin nan. To meye marabata da kai?"


"Wata biyar mana. Kai fa kana cikin layin tuzurai."


"Baka da mutumci Taj. Ni ne tuzurun? Kai kuma teenager ko?"


Taj ya gyaɗa kai yana dariya.


"Banda ƙuruciya, teenager kamar ka ina zai kai budurwa kamar Hamdiyya?"


"Inda ake kai matan..."


"Ehemm. Ughhh" Abba ya yi gyaran murya da ƙarfi don ya katse hirar tasu haka. Yaga an kusa zuwa wurin da  bai kamata kunnuwan uba su ji ba.


Kan sa su ka yi suna tambayarsa jiki. Da sauƙi kamar yadda idanuwansu su ke iya gani. Ya ƙara yi musu godiya sannan ya roƙesu da su bar maganar auren nan haka. Allah zai bashi yadda zai yi da iyalinsa. 


"Idan Alhaji ya amince za ka yarda a ɗaura goben?" Taj ya tambaye shi kafin su fita. Shi ko a fuska bai nuna damuwa ba da Abba yake ta maganar su daina zancen.


Shi dai Abba ya gama gajiya da zancen. Sannan ya matsu su tafi saboda so yake ya fice ya koma gida su shawarta da Yaya.


"Me zai hana? Waye zai ƙi jinin Yaya Hayatu ko ma in ce zuri'ar Alh. Sule?"


Jin wannan ya kwantarwa Taj hankali. Ya san Alhaji ba shi kaɗai bane shamakinsa. Shi kan shi Abba za a sha fama da shi. 


***


Salati Yaya ta fara yi kafin ta fashe da kuka. Zaune su ke a cikin wani ɗan falo ƙarami na ɗakin Abba. Ita da shi da kuma Baba Maje, Inna Luba mahaifiyarta da kuma ƙaninsa Abdulƙadir.


Faɗan kukan Inna Luba ta fara yi mata kafin ta koma tausarta. 


"Indai ku ka nunawa yarinyar nan cewa kun karaya na tabbata ciwon da za ta ji sai yafi na fasa auren."


"Yaron nan ya cuce mu" cewar Abdulƙadir.


"Na dai cuce mu. Rayuwar da na zaɓa ce ta zo tana bibiyar ƴaƴana" Abba ya faɗi da raunin murya.


"In ka amince kuma kana jin Sajida ba za ta ƙi ba, yanzu zan kira Baballe ya zo gidan nan a rufe magana. Gobe ya auri ƙanwarsa bakin kowa alekum. Ko kuwa?"


Abba ya nuna farincikinsa da godiya.


"Zan so haka. Amma Maje ka tuna lallai akwai haƙƙi tsakaninmu da yaran nan. Aure ba a son yi masa shigar sauri. Yanzun nan sai ya jagwalgwala abin da ake son gyarawa."


Baba Maje ya dage harda cewa "indai ba kuma rowar ƴar za ka yi min ba ka amince kawai. Ba don ni na haife shi ba amma Allah yaro ne mai biyayya. Ina sa rai in Allah Ya so ba zai bamu kunya ba."


Yadda ya matsa ɗinnan sai Inna Luba ta ce a kira yaron. Ba a mayarda hannun kyauta. Kuma Allah kaɗai Ya san dalilin faruwar wannan al'amari.


Cikin farinciki Baba Maje ya kira Baballe a gabansu. Allah Yasa baya nesa sosai ya ce gashi nan zuwa. Ita Iyaa da Siyama suna can wajen biki. Uwar baƙin hali kuma an tafi bikin ƙawa kamar yadda ta shirgawa Iyaa ƙarya.


Kowa ya yi zugum ana jiran isowar Baballe. Baba Maje ya takura masa da waya saboda basa son ƴan biki su fara dawowa. An gargaɗe su lallai kada su wuce takwas a waje har amaryar.


Baballe ya iso hankalinsa duk ya tashi. Irin wannan kira da wayar bai saba dasu daga mahaifinsa ba. Shi yasa ya dinga tunanin ko wani abu ne ya faru. Kafin ya iso sai da ya kira Iyaa yaji lafiyarta da ta Siyama. Ummi kuwa bata ɗauki wayar ba don kada a ce ta dawo gida. Sam ba ya raga mata akan halayen da ta tsiro musu da su a gidan.


Tiryan tiryan haka Baba Maje ya labarta masa halin da ake ciki a gaban kowa. Wanda shi Abba ya so su keɓe. Don idan Baballe zai ƙi,  ba zai ji nauyin idanuwansu ba. 


"Baba don Allah ko za mu koma soro mu yi magana" abin da ya ce kenan da Baban nasa ya matsa masa akan ya bada amsa.


Gabansa sai da ya ɗan faɗi. Yaran yanzu ba a ci musu laya. Ya gama yabonsa shi ne yake son watsa masa ƙasa a ido.


"Nan dukansu amsar da ka bani dole zan dawo musu da ita. Saboda haka gara ma kawai ka faɗa a gabansu."


"Baba don Allah" ya faɗi yana cije leɓensa na ƙasa. Shiru ba zai amfane shi ba a wannan lokacin. Shi yasa yake son faɗa masa dalilin da ya sa ba zai iya auren Sajida ba.


"Ka je ka saurare shi don Allah. Share ire iren waɗannan abubuwan fa don mun isa su ne su ke zama dalilan yaji ko mutuwar aure. Allah Ya kiyaye." Inna Luba ta faɗi tana nuna musu ƙofa.


Ba don ya so ba ya tashi su ka fita. Ransa duk ya ɓaci don Baballe bai saba yi masa haka ba. Yaro ne shiru shiru mai sauƙin kai. Tsayinsu kusan ɗaya don ma shi shekaru sun ɗan durƙusar da shi. Fuskar Iyaa ma'abociyar fara'a ya ɗauko. Ga shi kyakkyawan matashi mai zuciyar nema. Banda aikin da ya samu ƴan watannin baya akwai shi da buga bugar neman halak. Bai san zama ko kaɗan.


"Ina jin ka. Kada ka ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa min ƙasa a ido ba." Baba Maje ya ce a kausashe.


"Ba haka bane Baba" Baballe ya ce a ladabce "ƴar uwarta nake so. Na ɗan jinkirta faɗa mata ne saboda wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ƙanwarta so na aure." Ya ƙarashe kai a ƙasa.


Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ƙofar cikin gidan.

"Danƙari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faɗa mata ba ai ba zan yi wannan karambanin ba."


"Idan zai bani ƙanwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta komai tunda ban shirya ba." Baballe ya furta da hope ɗin baban zai amince.


"Dama ko wace ai zan faɗa musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su ka yi da Ummi a makaranta?"


Da sauri Baballe ya ce "Zeenatu ce ba Hamdi ba."


"Wace Zeenatu kuma?" Baba Maje ya ce don kansa ya ƙulle.


Baballe ya yi murmushi "Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ƙarshen shekara idan ta gama na san lokacin na ɗan yi tari. Sai na gabatar da kaina."


Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce "banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai kaji ana batun an kawo kuɗi."


Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba musu ido. Baba Maje ya ɗan rissina kai na jin kunyarsu ya faɗa musu yadda su ka yi da ɗansa.


"Alhandulillahi ai duk gida ne." Cewar Abdulƙadir. 


"In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a ɗaura nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ƙare karatunta."


"Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faɗa musu."

In ji Inna Luba.


*


Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba ta kira su har Halifa ɗakin Abba ta faɗa musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma ɗakinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana.


"Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta."


"Ita kaɗai?" Ta share nata hawayen.


"Wata damuwar tana buƙatar kaɗaicewa kafin zuciya ta karɓe ta. Idan tana buƙatarmu da kanta za ta neme mu."


Zee ya kalla da ta faɗa kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai.


"Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?"


Inna Luba tana shafa mata baya ta ce "Ja'ira. Ashe kukan ba na ƙin mijin bane. To ai da sauƙi. Yayyenki kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake." 


"Mijin ma bana so Inna." Ta ce tana ƙara sautin kukanta.


"Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi maƙota za ki tara mana ko me?" Yaya ta faɗi cikin fushi.


Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da take yi, bata so a wulaƙanta su.


Hamdi ce ta riƙe Zee su ka koma ɗaki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma'anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai goshinta ƙasa wurin Allah.


Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiɗa abin sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun ɗazu. Don lokacin shaɗaya ma ta kusa. Alƙur'ani kowacce ta ɗauka ta buɗe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha'awa. Yayinda ta ƴan uwan biyu ke nemawa kawunansu zaɓin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu'ar zaɓin alkhairi. Tana fata kowacce ta sami aminci a ƙaddarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka.


Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi alƙawarin sake haɗuwarsu ko jin muryar juna sai in sun haɗu bisa kuskure. Ba za ta ɗauka ba balle ace ta kasa haƙuri da wanda babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban.


***


A ɓangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu'a kawai. Roƙon Kamal ya yi akan ya kai shi gidan Yaya Babba ya ce babu ruwansa. 


"Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi maka bata shige ka ba."


"Don Allah Abba bai baka tausayi ba?"


"Ya bani, amma addua ce kaɗai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka haƙura da auren Hamdi ni kuma nayi maka alƙawarin auren Sajida."


Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na haƙura da ita ba. Wannan tsiwar yake son ƙurewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faɗo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ƙafar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat ɗaya ba.


Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. Taɓo mai adaidaita sahun ya yi.


"Don Allah ka yi haƙuri. Kantin Kwari zani."


"Malam lissafin kuɗinka fa zai canja."


Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.


"Ko akwai ciko?"


Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.


"Yallaɓai sai dai idan kuma sadaka za ka ƙara min akan wannan."


Taj dake neman taimakon Allah sai ya ƙara masa dubu biyu.


"Idan mun je in jira ka ne Yallaɓai?


"Da ka kyauta. Inda ka đauko ni zan koma."


*


Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store ɗinsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ƙwanƙwasawa tare da sallama lokaci guda.


Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance ɗa a wajen wata da su ke ƴan maza zar da ita.


"Kawu dama..."


"Matsa na shiga" Taj ya ce da ɗan saurayin. 


Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi.


"Me ya kawo ka?" Ya ce da kakkausar murya. 


Yaron da ya nuna masa office ɗin don bai taɓa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ƙofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ƙasa.


"Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne." Ya faɗi yana kallon uban.


"Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?"


Zuciyarsa dokawa take da ƙarfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taɓa auren wadda yake so ba.


"Ka fi ƙarfin komai a rayuwata."


"Shi yasa ka zaɓi barina akan ka ajiye burinka?"


Taj ya girgiza kai "baka bani zaɓi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena."


Zuciyarsa hasala tayi. Ɗan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya ɓata masa rai. 


"Rashin kunya ka zo ka yi min?"


"Ban isa ba." Ya ɗaga kai daga durƙuson da ya yi "aure nake so ka yi min gobe don Allah."


"Ka fara shan ƙwaya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?"


"Ƴar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron ɗinki."


Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu daƙiƙu sai ya buɗe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,


"Me ka ke taƙama da shi ne Taj? Kuɗin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?" Ya nuna ƙirjinsa "Ni? Ni za ka cewa kana son auren ɗiyar Habibu?"


"Bana taƙama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faɗawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana roƙa min."


Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ƙarshe ƙarshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo ɗa irinsa. Duk lokacin da yake son taƙwara ɗansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tanƙwara shi. 


"Shi yasa yanzu ma ka shirya saɓa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?" 


"Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saɓawa Allah akan soyayya..."


"Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faɗawa waɗannan maganganun?" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi.


"Ina sonta Alhaji." Ya faɗa kai tsaye abinsa.


"Ita ƴar Habibun?"


"Eh."


"Zo ka zauna"


Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daɗe yana tunani kafin ya ce da Taj,


"Ka tafi gida ka jirani."


"Gidan Yayan za ka zo?" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi.


"Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani."


Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai buƙatarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Haƙuri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuɗi. 


*


Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ƴarsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faɗa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ƙarshe yadda ya fahimta wanda kuma da ƙamshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu baƙinciki Taj yake son yi. 


Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaɓi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.


*


Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa. 


"Wace tsiyar ka ƙulla?"


"Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa."


A harzuƙe Kamal ya ce "ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. Ƙarshenta ma harbeka zai yi."


Taj ya ƙyalƙyale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj ɗin ne matsoraci.


Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.


"Ɗanka ne ya ɗauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana."


Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.


"Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a ɗaura."


Godiya mara adadi Taj ya yi masa. 


"Ba sai ka faɗawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina."


Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko ɗar ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.


***


Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ƴan biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa.


Banda ƴan mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar ɗaurin auren sai ƴan uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haɗuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tuƙosu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan ɗanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba.


Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar ɗaurin aure kamar yadda aka faɗa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya đauki kabbara. 


Abba yana share ƴar ƙwallar farinciki sai yaji an taɓo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba kuwa.


"Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta."


Abba baki ba rawa ya ce "Yaya Hayatu..."


"Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta."


"Hamdiyya."


Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faɗawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An ɗaura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu ɗari biyu.


A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya ɗuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.


"Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka haƙura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai ɗazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan ɗin ya yi min bayani."


Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya ɗaura aure na uku. Safwan Sabi'u Mamman da Sajida Habib Umar.


Allahu Akbar

Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki.

Tun safe Haulatu ta fice makaranta amma hankalinta gaba ɗaya yana ga bikin Maama, babu yanda ta iya don ba ta son ta yi tsallaken rana. Safina ma kanta ta riga ta tafiya don ko sadda ta aiko mata saƙo cewa ta tafi gida, ita sannan ma suna tsaka da ɗaukar lakca. Ba su ne suka fito ba sai wuraren ƙarfe uku da rabi, gaba ɗaya kuma hankalinta ya yi gida. Ko bi ta wayarta dake faman ruri a jaka ba ta yi ba har ta tako zuwa titi. Tsayuwar jiran abin hawan ma aiki ya zame mata. Can sai ga wata jan mota ta taho  har ta gifta ta, ta yo ribas ta tsaya daidai saitinta. Ganin haka Haulatu ta daure fuskarnan tamkar hadarin kaji karshe ma ta taka ta soma tafiya don ta gwammace ta fara rage zango da dai wannan tsayuwar motar da ba ta san ko ta wace ce ba a gabanta tunda ba ka hango na ciki ba, balle yanzu da duniyar ta zama abin tsoro. 


"Assalamu alaikum." Ta ji sallama a gefenta, juyawa ta yi, wani matashin saurayi ne kakkaura, sanye da shadda. Baƙi ne mai ɗan gemu. Ba ta taɓa ganinsa ba sai a ranar, wani murmushi ya ke mata. Ta kauda kai fuska daure ta cigaba da tafiya. 


"Afuwan, na maki sallama ba ki amsa ba. Nasan ba daidai ne na tsaida ki a titi ba. Idan ba damuwa don Allah ki taimake ni da kwatancen gidanku da lambar waya."


Haulatu kamar ta yi me don ta takaici, ita gaba daya ma ya ishe ta. 


"Ni ba ni da waya kuma an sanya min rana don Allah ka bar bibiyata."


Daga haka ta ƙara gaba, Allah ya taimaka bai kuma biyo ta ba, ta samu abin hawa ba ta ma tsaya ciniki ba ta faɗa. Ba tare da sanin cewa mutumin tuni ya koma mota ya bi bayansu ba. Ji ya yi ba zai iya haƙura ba sam. Suna isa ta iske ƙofar gidan nasu da mutane, baƙin Malumfashi ne maza sai ko wasu cikin abokan matasan gidan, sam ita ba ta ma kula da sauran ba don wurin a cike yake, ko ba komai bikin Maama ake yi, mace mai son zumunci kuma ta mutane.  Koda ta sauka ta biya mai napep ba ta jira komai ba ta faɗa gida kanta na ƙasa. Sadauki da ke tsaye gefe tare da wasu abokansa suna ɗan taɓa hira, ya gan ya kuma ya ga wata mota da ke bayansu, har saurayin ya fito daga motar bai dauke idanu a kansa ba. Ganin saurayin na waige-waige ya sanya shi ƙarasawa gare shi bayan ya nemi ƴan mintuna daga waɗanda suke tare. Sallama ya mishi, dama jiran wanda zai yiwa magana ya ke don haka da sauri ya miƙa hannu suka yi musabaha. 


"Ina fatan lafiya?" Cewar Sadauki yana ƙare masa kallo. Murmushi saurayin ya ɗan yi da shafar suma.


"Lafiya lau, suna na Kabeer Maitama dama wannan baiwar Allah na biyo, sai na ga ta shiga nan shi ne..."


"Matar aure ce."


Shi ne abin da Sadauki ya faɗi kai tsaye kuma fuska a haɗe. Kabeer jikinsa ya yi sanyi, wato dagaske take da ta ce an sanya mata rana kenan? Sai ya ba shi hakuri ya shige mota ya bar wajen. Sadauki koda ya koma ga abokansa ma bai samu nutsuwa ba. Wato dai da gaskiyar Khaleefa da yace idan ya yi sake za'a yi mishi shigar sauri. Aikuwa zai yi kokarin kafa gwamnatinsa tun kan hakan ta kasance. 


 A gidan kuwa Haulatu ta iske jama'a sai hada-hada ake yi.  Yara sun cika wuri suna ta wasanni, dama tun jiya ta ji wai a can babban farfajiyar gidan Daddy Ridwan aka shirya walimar tunda yana da girma sosai don ya fi na ɓangaren kowa ma girma. Koda ta shiga sallar la'asar kawai ta gabatar ta ci abinci sannan ta faɗa wanka. Da ta fito ta kira wayar Safina. Tana ɗagawa ta ji ta cikin hayaniya har ba ta jin me take faɗi saboda muryar Ado Gwanja da ta cika kunnuwanta a waƙarsa ta Warr sai kawai ta katse kiran. So take ta ji sun shirya ko kuwa, ba ta so ace ta riga su sanya kayan. Tana nan zaune da ɗaura ƙirji Umma ta shigo, ta sha ado cikin atamfarta mai gold sai sheƙi take, ba za ka taɓa cewa ta jikinta Haulatu ta fito ba, sai dai ka yi tsammanin ƙanwarta ce. Dama sam ba su ga juna ba sai yanzun aikuwa Haulatu ta washe baki.


"Masha Allah, Ummana kin yi kyau sosai kamar wata ƴanm.."


Daƙuwar da hararar da Umman ta yi mata ne ya sa dole ta katse abin da ta yi niyyar fadi tana dariya. 


"Ni sa'arki ce ko Haulatu? Ban hana ki zama da ɗaura ƙirji ba? Ki tashi ki sanya kayanki."


Ta dan turo baki.


"Ni fa Umma ba na so na saka su Safina ba su sanya nasu ba. Ita kuma ina kiranta a waya ba ta ɗaga ba."


Umma ta girgiza kai. 


"Ai shikenan, sai ki yi ta jira kin ji ko?"


Ta yi murmushi ta na duban Umma, ba kwalliya a fuskarta don ko hoda ba ta shafa ba, amma duk da haka kayan sun sa ta fita fes. Ganin Umma ta zauna gefen gado ta ɗan yi shiru ya sa ta fadin.


"Umma lafiya?"


Umma wacce maganar da Haj Hadiza ta gwaɓa mata akan wai kamar tana jira, ace ba ta kai ga kammala idda ba amma ta cancaɗa adon atamfa haka? Har tana cewa Maman Safina dake zaune wai toh su bi a hankali dai, Na'imatu ta kusan fara zawarci. Wannan abu ya yiwa Umma ciwo duk da cewa Maman Safina sam ba ta da daukar magana asalima cewa Haj Hadiza ta yi, ai babu wani abu, idan kishiya irin masu halin Umma ce a kawomata. Ba irin wadanda ba su san mutuncin mutane ba. Amsar ta yiwa Umma dadi kuma tana gani yanda Haj Hadiza ta haɗe rai wai an faɗamata baƙa, silar dawowar Umman ɗaki kenan. 


"Don Allah Umma mene ne ya faru? Na ganki wani iri."


Tambayar Haulatun ya sanya Umman dubanta ta yi murmushi. 


"Babu komai, jiki da jini, kaina ke ɗan ciwo, saka kayan ki ɗaukomin magani na sha."


Jin haka kawai ta mike ta zura hijabi tana fadin.


"Bari na karɓo maki a wajen Hajja." Daga haka ta fita da sauri zuwa dakin Hajja don ta san inda take ajiyar magunguna. Suka yi kiciɓus da Maman Safina, bayan sun gaisa take tambayarta inda Umma take, nan ta nuna mata daki ita kuwa ta wuce. Ba jimawa ta dawo, ta iske Maman Safina na ba Umma haƙuri akan abin da ya faru.


"Kya biyewa Hadiza ki ɓata ranki a banza?  Waye bai dan halinta ba na shegen ɓakar magana da yada habaici? Don Allah ki saki ranki."


"Babu komai ya wuce. Nima kaina ke ɗan ciwo shi ne fa zan sha magani. Haulatu ina yake?"


 Da haka Maman Safina ta ankara da Haulatun sai ta miƙe da kulawa tana mata fatan samun sauƙi, ita kuwa Haulatu da ta tsinci abin da ya faru, ranta ya ɓaci. Dama ta sani ga dukkan alamu wani abin a ka yiwa Umma, ba mace ce mai saurin nuna abu ba, amma idan ya yi mata ciwo da yawa, to fa ba ta iya ɓoyewa sai na kusa da ita ya fahimta. Ba don darajar Hajja ba ai da ta kai ƙara Haj Hadiza wurin Baba Alhaji amma ta sani har Umman ba dadi za ta ji ba.  Tana kallo Umma ta sha maganin sai dai madadin ta kwanta kawai ta fice tana cewa Haulatu ta ƙulle ƙofar shiga saman idan ta kammala tunda babu kowa. Ta amsa da toh.  


 Kwalliya ta yi sosai wanda ya amsa sunan kwalliya sannan ta fiddo ankon da suka yi su uku abinsu babu wanda suka sa a ciki. Tana cikin shiri sai ga Radiya ta faɗo, kusan a tare suka furta 


"Wow! Masha Allah." Kowacce na santin kyan da ƴar uwarta ta yi, ita Haulatu na kwalliya da ma yanda ɗinkin ya fiddo Radiya, ita kuwa na kwalliyar Haulatun da yanda ya karɓi fuskarta kai ka ce makeup artist ce ta rangaɗa mata. 


 "Malama ki sauri ki shirya, ana can ana ta raye-raye. Bikin Maamarmu gida. Kin ga yanda ake bin mu da kallo ni da Safina? Fa'iza da Fahima sai da suka kasa haƙuri suka yi ƙorafin wai meyasa za'a ce babu anko kuma mu yi? Humm, ni nasan dai mun ja magana."


Radiya ke maganar, Haulatu kuwa dariya ta yi lokacin da ta zura riga ta juya baya don Radiya ta taimaka mata da zuge zif ta amsa.


"Ni nasan a rina, ai sai da na ce maku kar mu yi kar ya zama abin magana. Amma Feenah ta dage. Amma ke gwara da aka yi hakan, tunda dai ai kinsan idan mun nuna musu iyayi za su yi su ce bai yi ba."


Haka dai a gaggauce ta yi daurinta mai kyau, ta fesa turare sannan ta dauki mayafinta ƙarami don a farko cewa suka yi ba ma zasu saka mayafi ba tunda cikin gida ne, amma ustaziyarsu Radiya ta ce ita sam a'a. Dole aka nemi mayafin da ya hau da kalar atamfar. Haulatu ta sanya takalminta baƙi mai tudu mai igiyoyi daga sama, duk ta malƙwaye igiyar daga saman ƙafafun, farar fatarnan ta ƙara wa takalmin kyau don ko yaya tsagar ɗinkinta na gefe da gefe ya fito, sai ka hango. Ga lalle an sha. 


A hanya ma suna tafe ba su tsira da kallo ba, ƴanmatan sai habaici da kauda kai. Har suka isa ɓangaren Daddy Ridwan haka ake bin su da kallo, su gaida manyan dake wurin su wuce, kowa na yaba kyan da suka yi ban da waɗanda suka shaƙa. Suna isa wurin kuwa wanda ya ƙawatu, sai ka yi tunanin ma hall ne tsabar haɗuwar da ya yi, su na soma bi ta kan red carpet din da aka shimfiɗe har zuwa inda Maama za ta zauna, MC ta sa aka saki kiɗa na sabuwar waƙar Gwanja mai suna Sauti. Idanu duka a kan su Haulatu, Jannat da tawagarta a gefe har wata ashariya ta yi na tsabar hassada da kishi. Nan da nan idanunta suka kada fadi take. 


"A gidan uban wa aka ce a yi anko? Wato yan iskan yaran nan anko suka yi ba su sanar ba? Shegu, an fadamusu sun fi mu son Maamar ne?" 


Nan dai ta dinga ɓaɓatu wanda rabinsa ma wadanda ta ke yiwa ba ji suke ba saboda ƙarar kiɗa. Safina dake gefe tana ganinsu kuwa ta taso suka haɗe a tsakiya suna rawa, nan fa Mc ta soma koɗa su. Wai ga wasu ƴanmata kamar wasu taurari. Ba su jima ba suka fice, rawa ce ba ta wani murguɗa jiki ba, ta hankali suka yi. Ba jimawa sai ga Maama ta fito bisa rakiyar samarin yaranta huɗu, Khaleefa, Mu'az, Sadauki da Zaid wanda ke faman cin magani, yana daga gefen Khaleefa, shi kuwa Mu'az suna daga dama tare da Sadauki. Abin sai ya burge sosai, Maama ta sha ado har ta gaji da kyau cikin jan leshi, su kuwa sun fito cikin fararen shadda sai dai kowa da kalar tasa, ba anko ba. Nan aka hau sowa da hotuna, Mc na faman roƙon a yi hakuri a zauna amma kamar ba a jin ta. Har Maama ta zauna sannan suka koma mazauninsu, an ci an sha an kuma yi nishaɗantu, kowa a wajen na murna idan ka ɗauke Anti Mabruka dake ƙume a ɗaka ita da ƙawarta. 


 Kamar yanda idanun Sadauki suka kasa ɗaukewa a kan Haulatu duk motsin da za ta yi a wajen, haka Zaid shi ma don ji ya yi kamar babu gurbin haƙuri a zuciyarsa a kanta. Sam ba zai iya ba. Yau zai tunkare ta, ko me su Baba Alhaji zasu ce yana ji sai dai fa su faɗi.


 Haulatu ko hanya ba kama zuwa ɓangaren Hajja don cire takalmin da a sannan tuni ya dame ta. Su ma wurin an tashi domin haramar sallah. Tana isa ɓangaren Hajja saƙo na shigowa wayarta .


 "Mu haɗu a garden ɗin Daddy, after magrib. Abeed."


Yaya Sadauki ne. Sai ta yi wani murmushi duk kuwa da cewa ta ji faɗuwar gaba, fatanta Allah yasa abinda take ji a kansa shi ma ya na ji. A yau  sai ta ji kamar an ƙaramata sonsa. Ta kuma kasa ɗauke idanu a kansa a wurin, sun sha haɗa idanu sai ta yi maza ta ɗauke kai. Ai kuwa da sauri ta faɗa banɗaki ta yi tsarki da alwala ta kuwa goge kwalliyar tas tukunna kafin alwalar sannan ta fito ta yi sallah. 


*** 

Zaid kuwa a ɓangaren Sadauki suka yi alwala, koda suka dawo daga masallaci shigowa gidan ya yi da zummar neman Haulatu ya yin da Sadauki ya nufi garden zaman jiran hasken idaniyarsa. Mutane duk an tafi shirin yi wa Maama rakiya gidanta.


Sadda Haulatu ta shiga garden din gidan Daddy Ridwan, akan idanun Zaid dake biye da ita, sai kawai ya bi sahu. 


***

 Mu hadu gobe idan Allah ya nufa.

Tun kafin ta ƙarasa ciki sosai ta hango shi zaune saman kujera mai lilo ya kwantar da kai yana kallon sararin samananiya. Lokacin ya cire babbar rigar hakanan kansa babu hula. A hankali ta ke takawa har ta ƙarasa inda ya ke, kasancewar ta sauya takalmi zuwa flat, ya sanya bai ji tahowarta ba sai sallamarta da ya cika dodon kunnensa. Ya buɗe idanu ya kalle ta yana mai amsawa da yi mata nuni da gefensa. 


"Bismillah." Ta zauna jikinta a sanyaye, ƙamshin turarensa mai haifar da nutsuwa ya na bugar hancinta. Ya zauna sosai gami da ɗan dafa gefen kujerar yana kallon fuskar da ba ya taɓa gajiyawa da kalla. Ita kuwa dake duban ɗan adon da aka yi a tsakiyar wurin ta sani ita ya ke kallo don haka duk sai ta kasa sukuni kaɗan. So ta ke kawai ta ji meke tafe da shi. 


Zaid wanda ke bin Haulatu a baya, ya yi matuƙar fusata ganinta zaune tare da Sadauki, ya ji kishinta na neman kashe shi da ransa. Kamar ya ƙarasa sai kuma ya juya kawai ransa na suya, ya yi alƙawarin ba zai rasa ta, Sadauki ya samu ba. Wannan ba mai yiwuwa ba ne. 
"Kin yi kyau fiye da kullum." 


Maganar Sadauki ya katse tunani da fargabar da ta tsunduma ciki. Sai ta ma kasa haɗa kalmar godiya ta furta don mamaki, abin ta ji shi banbarakwai, sai da ta ɗan yi gyaran murya kafin ta amsa.


"Nagode."


"Haulat."


Yanayin da ya kira sunan ta ji shi har ranta, ta kalle shi, amma kuma ta kasa jure kallon da ya ke jifanta da shi hakan ya sa ta sauke kai tana wasa da gefen mayafinta. 


"Uhm, ba ki amsa ba?" Ya yi tambayar cikin kwantar da murya. Ta lumshe idanu sannan ta bude. 


"Na'am." 


"Ke ta musamman ce a wurina, kin samu matsayi irin wanda ban taɓa hangowa zan ba kowace ɗiya mace shi ba. Tun ina ganin kaina a cikin madubi, har ta kai idan na kalla sai dai na ga fuskarki tana min gizo. A taƙaice, ki na cikin manyan burikana ma rayuwa a yanzu."


Wai Allah! Haulatu sai ta ji kamar ta nitse a inda ta ke don dadi da kuma kunya. Ta ma nemi fassarar abin da ya ce ta rasa a kwakwalwarta. Ba ta gama farfaɗowa ba ya ƙara jefa zuciyarta a shauƙi da kalamansa. 


"Haulat, na yi iyakar ƙoƙarin na ga na haƙura da komai har zuwa sadda koda ace ba ki kammala karatunki ba, to ya kasance kin cimma tsakiyarsa. Ni mutum ne da ba na son tauye ra'ayin abin sona koda kuwa zan cutu, dalili kenan da na zaɓi ƙarfafa maki gwuiwar cika muradinki. Sai dai nikam na gaza, haƙurin ya kasa tasiri a kan soyayyarki."


Ya ɗan numfasa, shiru ya biyo baya na sakanni, wayarsa na ƙara amma bai ko damu da dubawa ba. Haulatu babu ita sai gangar jikinta, amma ruhi da tunaninta kacokam sun lula wata sabuwar duniya wacce a baya mafarkinta kawai take yi, a yanzu kuwa ga ta nan a zahiri a gabanta, ga Abeed Sadauki da kansa shalelan Baba Alhaji, ya na amayar mata da abin da ya ke ji a kanta. Ta kasa kallonsa duk kuwa da yanda take ji zuciyarta na ingiza ta da son ta kalle shi ɗin don ta ƙara samun tabbaci wai wadannan kalaman daga bakinsa suke fita, sai dai tana jin nauyin su haɗa idanu. 


"Ba zan tauyeki ba, zan ba ki wadataccen lokaci daga nan har zuwa jibi, duk abin da ki ka yanke a kaina, ina roƙon ki kar ki ki nauyina, koda ta saƙon waya ne, ki sanar da ni. Koda ace ni Abeed ba na daga cikin jerin irin mazajen da ki ke fatan ɗayansu ya kasance matsayin miji a gareki. Feel free ki faɗamin. Na maki alƙawarin zan fahimceki daidai gwargwado in sha Allah."


Ya ƙarashe zancen da wani sanyin murya da na jiki, sai a lokacin ya kai hannu ya ɗauki wayarsa, Khaleefa ne, tambayarsa inda ya shiga ya yi don ana ta shirin tafiya kai Maama gidanta, ya amsa da yana tafe. Ita kuwa yana amsa wayar ne ta dube shi, kalamansa sun haifar mata da daɗin ƙauna da kuma wani tausayinsa a rai. Ta ya ya za ta ce ba ta son namiji irin Yaya Sadauki? Ganin ya ajiye wayar ta yi saurin kauda kai. Ya yi murmushi. 


"Oh, kin ga za'a tafi rakiyar Maama a bar mu ko? Tashi mu je."


Kamar jira ta ke kuwa ta miƙe, saurin da ta yi har sai ta ya ɗan kalle ta ya ƙara murmusawa. Suka jera kowa da tunanin da ya ke. A ɓangaren Sadauki, wani ɓangare na zuciyarsa na son tabbatar masa cewa Haulatu fa tana son shi, yayinda gefe guda ke kashe masa wannan ƙarfin gwuiwar cewa ba haka bane, karatu ne a ranta, watakila ma girmansa ya zube a idanunta. Ko kuma tana shawarar kai sunansa gaban Baba Alhaji shi ma. Bai damu da mutanen da ke bin su da kallo tun daga farfajiyar gidan Daddy Ridwan ba har suka fita zuwa can filin parking na babban gidan baki ɗaya inda tuni motocin tafiya sun hallara jama'a na ta shiga. Mamin Khaleefa dake tsaye tana magana da Jannat akan inda ta kai mata ƴar jakarta, ta hango su. Sai da ta ji gabanta ya fadi, Jannat ma idanunta da ya kai kansu sai da ta ji wani jiri na neman kwasarta. Safina da Radiya baki suka saki suna dubansu, wai dama duk wannan uban neman da suke yiwa Haulatun, tana tare da Yaya Sadauki? Ai hatta Momin Mu'az sai da ta ganewa idanunta, balle kuma Zaid wanda ya ji kamar ya ƙarasa ya shaƙe wuyan Sadauki saboda tsananin kishin dake cin zuciyarsa. 


Haulatu ta dubi Sadauki kamar ta yi kuka ta ce.


"Bari na je na dauko wayata."


Murmushi ya yi gami da kashe ta da wani kallo wanda ya sanya ba shiri ta kauda kai ta juya ta nufi ɓangaren Hajja. Aikuwa Safina da Radiya kamar jira suke suka mara mata baya.  Shi kuwa Sadauki kai tsaye ya nufi motar Khaleefa wanda shi ma tun zuwansa idanunsa ke kansu yana murmushi mai ma'ana biyu, a gefe na taya ɗan uwansa murnar samun cikar buri, a wani ɓangare kuwa taya kansa jimamin rasa wata zarah mai haskaka duhun dare. 


"Na shiga uku! Wayyo Allahna! Mami zan mutu." Cewar Jannat tana kokarin kifewa a wurin tsabar baƙin ciki da zafin da ƙirjinta ke yi. 


Mamin Khaleefa da sauri ta tare ta gami da yi mata raɗa a kunne. 


"Ke nutsu don Allah, mene ne haka za ki bar mana abin magana? Ba kya ganin da mutane a wurin?" 


Sai a sannan Jannat da idanunta suka kaɗa ta kalli gefensu, Amarya ce kishiyar Momin Mu'az tsaye a gefe ita da Maman Safina suna taɓa hira. Can gefe ɗaya su Fa'iza ne da su a Nusaiba ƙanwar Mu'az. Dole ta hadiye kuka da tashin hankalinta amma fa jikinta ma rawa yake yi. Sai wanda ya raɓe ta zai fahimci haka. 


Haulatu kuwa koda suka haɗu da Umma ba ta tambaye ta daga inda take ba tunda su Safina sun zo har nan nemanta, sai dai tambayar na ranta, yanzun hayaniyar jama'a da shirin tafiya rakiyar Maama. 


Tana shiga ɗaki ta ji tashin muryoyin Safina da Radiya a bayanta da sauri ta waigo. 


"To Laila ta Majnun!" Cewar Safina. Ita kuwa Radiya kira take. 


"Rabu da ita, wato ta samu Yaya Sadauki ta mance da mu ko hotunan kirki yau ba mu ɗauka ba ko?"


Ajiyar zuciya ta sauke babu wanda ta ba amsa sai ma ta juya da borin kunya tana jan guntun tsaki da bude sif ta ciro wayarta lokaci guda tana ƙoƙarin ɓoye murmushinta. 


"Ni ba zan biyemaku ba. Mu je kar a tafi a bar mu."


Radiya da Safina suka dara gami da cafkewa. 


"Ko an tafi za'a dawo, mu da muke da mota a hannu? Ko ya kika ce ƴar uwa?" Faɗin Safina. Radiya ta amsa da kwarai kuwa tana dariya. 


Ita dai harararsu kawai ta yi sannan ta soma tafiya. 


"Idan kun fito kwa rufe ƙofar ku ba Hajja muƙulli." 


"Aa jira mu." Sai ta tsaya daga falon ta ba su baya tana ta murmusawa, yau jin ta take yi kamar a wata duniyar ta daban. Wai haka soyayyar take da daɗi dama? Tambaya da babu mai ba ta amsa. Har suka rufe suka zo gefenta ba ta sauya daga yanayin murmusin da take ba. Hakan ya sa suka yi murmushin su ma ba su ce mata komai ba, sun san dai za ta ba su labari idan dai Haulatu ce. 


Motar Yaya Sadauki, Maama ce ta shiga, don haka suka shige motar siena ta gidan.  Gidan Maama ya haɗu iyakar haɗuwa, kayayyaki masu tsada da kyau su Khaleefa suka zuba mata. Su hudun musamman ma Khaleefa, Zaid da Sadauki wadanda suka fi Mu'az samu sosai, sun yi iyakar ƙoƙarinsu wajen yi wa Maama kaya na gani na faɗa wanda jama'ar wurin suka ce ko gidan budurwa ƴar gata sai haka. Ba a wani jima ba duka aka watse, Safina an sha kukan rabuwa da Maama, dama ko bayan ɗaura auren ta yi kukanta ta ƙoshi, ita yanzu kam ta san zaman gidan ba dadi zai mata ba tare da Anti Mabruka, zama ne na haƙuri, da kuma ace ta yi wannan zaman ta gwammace ta tattara ta koma gidansu. Dama tuni ta yanke hakan, Mamanta dai ba ta ce mata uffan ba, shi ko Abbanta ya ce babu takura duk yanda ta ke so hakan za'a yi. 


Koda suka dawo kowa ɓangarensu ya yi, Haulatu ta shiga dakinsu ta watsa ruwa ta yi alwala ta sa kayan baccinta, sallar isha'i ta gabatar da nafila kafin ta miƙe ta nufi ƙasa sanye da hijabinta, ita sai a lokacin ma ta tuna da yunwar cikinta. A hanyar sauka ne ta ci karo da Fahima wacce ita ma tuni labarin ganin Sadauki da Haulatu ya je mata, a bakin su Fa'iza. Za ta gifta ta, kusan tana sani ta sanya mata ƙafa aikuwa ta yi wata irin kifawa ta tafi tun daga tsakiyar benen har ƙasa, nan da nan bakinta ya fashe, wayar hannunta kuwa wata irin faduwa ta yi da screen din ya tsage.  Mutanen dake zaune a falon suka yo kanta suna salati, Fahima tuni ta hayewarta sama da gudu-gudu, gudun kada a zarge ta. 


"Sannu, garin yaya haka?" Faɗin wata dattijuwa cikin baƙin Malumfashi. 


Ita kuwa miƙewa ta yi. Hawaye ta soma, ba na komai ba sai na baƙin cikin wannan abu da Fahima ta yi mata, ita ta sani da gayya ne, amma kuma faɗar ba shi da ma'ana tunda ba lallai a wasu su yarda ba musamman mahaifiyar Fahima Haj Hadiza wacce ta dage ai shegen iyayin Haulatun ne ya sa ta fadi, har da cewa wataƙila ma danna waya take yi. Ita dai ba ta ce uffan ba, Umma ma dake zaune ko miƙewa ba ta yi ba ballantana a ce ta yi wani abin. Maimuna wacce ta samu zuwa bikin bisa iznin mijinta, sai sannu take jero mata. Tsabar baƙin ciki tana wanke bakin amma hawayen bai bar zuba ba, daƙyar jinin dake fita a leɓan ya tsaya amma bakin nan ya kumbura. Ranta ta ji yana zafi, ta rantse Fahima sai ta yi kuka fiye da wanda ta sanya ta. 


 Abincin ma fasa shiga ta ɗiba ta yi, Hajja sai sannu ta ke jerowa, har da yiwa Baba Saude faɗa akan ta yi sauri ta kammala gugan, ba ta bi ta kan wayarta ba ta wuce ta koma sama. A falon sama ta iske Fahimar zaune tana danna waya. Suka haɗa idanu Fahima ta ƙyaƙyace da dariya sai ta wayance kamar mai yin voicenote a whatsapp ta ce. 


"Ke, wani abu na gani ya tunamin da Shrek. Hum, ina ganin salo a gidanmu, ai ina faɗamaki Yaya Sadauki dai ya fi ƙarfin mutum, kuma duk yanda aka ƙwallafa rai a kansa ake mishi tallar ciki da waje ba'a ishe shi kallo ba."


Tsaf ta gane inda maganar ta dosa, rufe ƙofar ɗakinsu ta yi bayan ta shiga, tabbas akwai ranar ba ta amsa, akwai babbar ramuwa tana zuwa. Ba kuma a yau ba. 


Ba ta jima ba sai ga Maimuna ta shigo da sallama, ta amsa mata, abinci ne a faranti ta kawo.


"Ga abinci Hajja tace a kawomaki."


Kamar ta ce ta ƙoshi amma sai ta ji ba za ta iya ba don dagaske yunwar dai take ji, godiya ta yi mata. Maimuna ta zauna tana miƙa mata wayarta gami da furta."Wannan ta ci screen."


Ta karɓa ta ga wani far far yake yi, sai kawai ta ajiye a gefe. Duban Maimuna ta yi.


"A nan za ku kwana?" 


"Aa fa, yana hanya ma yanzu zai ƙaraso mu tafi."


Ta jinjina kai, daƙyar ta ke sa abincin a baka da cokali saboda raɗaɗin da leɓan ke mata. 


"Ki yi hakuri, na san Fahima ce da wannan aikin."


Maganar Maimuna ya sa ta dubanta da mamaki. Ta jinjina kai.


"Na gan ta, zan shiga kicin ajiye kofi, na ga sadda ta saka maki ƙafa ta gudu. Don Allah kiyi hakuri."


Ɗan murmushi Haulatu ta yi, kamar ta tambaye ta dalilin da ya hana ta faɗi amma sai ta share. 


"Bakomai, kar ki damu. Kanta ta yiwa."


"Hakane, ban faɗa ba ne saboda ba na so ya jawo abin magana, kin san yadda Hajiyar tawa take."


Wato Haj Hadiza mahaifiyarsu, Haulatu dai ba ta tanka ba ban da wani murmushin. Wayar Maimuna da ya yi ƙara ne ya sanya ta miƙewa. 


"Kin ga har ya zo ma, bari mu wuce sai da safe. Allah ya ƙara sauki."


"Amin, sai da safe nagode."


Ta na ba ta amsa ma kafin ta kai aya ma Maimuna ta wuce, ga dukkan alamu daga yanayinta mugun shakkar mijin nata take yi. Ta maida hankali ta ci abincin ba wani sosai ba, ko wayar ba ta son kallo tsabar baƙin ciki don wani baƙi ta yi daga tsakiya har ba ka iya ganin fuskarta sosai. Fita da abincin ta yi ta maida ƙasa ta rufe a kicin sannan ta dawo ta yi kwanciyarta bayan ta kashe wayar gaba ɗaya ta jefa a dirowar gefen gadon. Nan kuma ta tsunduma tunanin Sadauki, ta manta da dukkan wata damuwa, kalamansa suka shiga dawowa tiryan-tiryan a kwakwalwarta yayinda ƙaunarsa ke ƙaruwa a birnin zuciyarta. Sai ta ji tana kewar muryarsa da ganinsa, kamar ma sam a yau ba su ga juna ba haka ta ke ji don soyayya da shauƙi. Daƙyar ta samu dai ta yi addu'ar kwanciya bacci ta kwanta, kafin Umma ta shigo tuni ta yi nisa a baccinta. 


***

 Kano....

Mummunan labarin da ya risƙi Haj Adama na tashin gobara a makeken store ɗinta dake a keɓantaccen wuri a daji wanda ba kowa ya sani ba, ya jefa ta cikin kaɗuwa da tashin hankali marar iyaka don har suma ta yi saboda tsabar firgici.  Nan da nan ta baza tare da muƙarrabanta don zuwa ganewa idonta. Sai dai babu wani kayanta da ya tsira, wuri ya shafe ya zama toka. Ai sai ga Haj Adama na maganganu kamar zararriya. Fadi take.


"Allah ya tsinewa Ɗan Mutuwa, Allah ya isa! Sai na ga bayansa! Na rantse sai na zama ajalinsa! Da ni Adama ya ke zancen! Ni na san babu wanda zai min wannan aikin sai shi! Dama ya ci alwashin ramuwa! Ashe ta nan ya ɓullo!"


Sai kawai ta shiga kururuwa da ihu ana riƙe ta. Daƙyar ta iya shiga mota tana kuka wiwi da majina suka bar wurin. Babbar asara ce na kayyakin da ba nata ita ɗaya ba. Ta sani idan kowa ya mata uzuri ya ba ta damar haɗa wasu kayayyakin, to fa ban da Major Musbahu, ba shi da mutunci ko kaɗan. Ko yau wuraren hudu na safe sai da ya dokamata kira akan a fito da kayansa a biyo hanyar Lagos, har ta ji haushi ta rufe shi da faɗan na fa tsoronsa take ba, har da cewa ita daga wannan ma ba za ta ƙara haɗa harka da shi ba. Suka yi zage-zage, ya kuma ci alwashin muddin ba ta aikomasa kaya ba zai yi maganinta. Ashe kuwa kayan da ba za su aiku ba kenan. Sai ta ƙara fashewa da wani gunjin kukan. Wayarta dake ruri ta duba, gabanta ya yi mugun faɗuwa ganin sunan Major Musbahu na yawo saman screen. Hannu na rawa ta miƙawa ƴar amanarta Yakura. 


"Kashemin wayar gaba ɗaya."


Abin da ta ce kenan, ba musu Yakura wacce ta sha man bilitin fiskarnan kamar ɗanyen nama ga hudan hanci da bai mata kyau ba, ta cika umarnin Uwar ɗakinta. 


Haka suka koma cikin gari Haj Adama na saƙe-saƙen matakin ɗauka. 


***

 Hindatu ta zubawa Mominta dake rawar jikin haɗa kaya idanu. Ba na komai ba ne sai na tafiyar da Momin za ta yi Dubai a satin don yo mata siyayyar haihuwa wanda Ɗan Mutuwa shi yake shiryamata komai na tafiya. Duka hakan kuma don ya ƙara wanke kansa a wurin Hindatun ne don a tunaninsa rashin ta idon da ya yiwa Mahaifiyarta ne ya sanya ya chanza.


"Momi." Kiran sunanta da Hindatun ta yi ne ya sa ta ɗagowa ta dube ta fuskarnan cike da annashuwa ta amsa.


"Na'am ƴar Mominta. Shalele mai goshin arziƙi, ta Alhaji Ib..."


"Momi don Allah mana, ni bana son duka wadannan abin, ba na son dukiyarsa hatta shi ɗin ma ya ficemin  a rai. Ni ki maida masa komai a raba aurenmu."


Ai ba ta san sadda ta saki ɗan ƙaramin akwatin ɗan kunnen da sarƙa da take ƙoƙarin jefawa a jakar tafiyar da ɗoki ya sanya ya fara shiri tun wuri ba.


"Eh?? Me ki ke cewa? A raba aurenki da Alhaji Ibrahim? A'a ina jin ban fahimci zancen ba. Hindatu, auren nan ki ke fatan a raba?"


Cikin zubar hawaye Hindatu ta gyaɗa kai tana kallonta. 


"Eh Momi, ba na son auren nan."


A harzuƙe Momin ta amsa tana nuna ta da yatsa. 


"Kin yi kaɗan, ke ban ma yarda ke ce ba, na rantse ture aka yi maki. Ni dai na shiga uku na lalace! Yanzu ɗiyartawa ma ta yi aure maƙiya da mahassada shi ne suka sako min ita a gaba? Burinsu a yi ta ƙirga maki aure? To ba zai yiwu ba! Lallai ɗaukar mataki ya zame min dole. Ina na jefa wayata?"


Daga haka ta shiga laluben waya, Hindatu ta yi shiru sai hawayen dake fita, cike da baƙin cikin jin wacce Momin ta kira, wato sabuwar aminiyarta Hajiya Tani, ta sani bai wuce batun zuwa wajen ƴan tsibbu ba don haka ta fice daga ɗakin. A kujerar falo ta zube ta hau kuka sosai, wannan ne karo na farko da ta ji kewar mahaifinta da ƴan uwanta, da ace yau tana hannunsa, tana da tabbacin abubuwa da dama ba za su faru gareta ba. Aurenta tun daga na farko har na biyu babu wanda aka nema a dangin mahaifinta, Mominta ita ta yi kiɗa da rawarta tare da wasu tsirarun ƴan uwanta maza waɗanda suke da hali irin nata na zalama da haɗamar abin duniya, da  babu hakan  a gabansu, ko kallonsu bai kamata su yi ba tunda Momin ba ta nemansu idan ba kasuwar buƙatarta ce ta tashi ba. 


Ganin kukan ba zai mata magani ba sai ta share hawayenta, ba ta da wata aminiya sama da Haulatu, za ta yi shawara da ita don jin abin da za ta ce, sai dai ko giyar wake ta sha, ba za ta iya fitowa ta faɗamata abin da ta ji da kunnuwanta mijinta ke faɗi ba. Wayarta ta jawo ta kira ya fi sau uku sai dai duka amsar guda ce, a kashe. Haka ta gaji ta koma kiran ta Umma, ta ci sa'a kuwa ta shiga. Suka gaisa da Umma cikin mutunta juna, ita dama ta na ganin dattakon Umma, wasu lokutan har ma ta kan ji inama Mominta ke da nutsuwa irin nata, ga iya kalamai.


"Hindatu, hala ƙawarki kike nema? Wayarta ta samu matsala ne. Ba ta nan ma ta je makaranta."


Abin da Umman ta ce kenan. Da ɗan damuwa ga rawar murya ta amsa.


"Toh Umma. Don Allah idan ta zo ta kira ni." 


"In sha Allahu zan faɗamata, amma ina fatan komai lafiya?"


Kafin Hindatu ta amsa ta ji an warce wayar. Da sauri ta duba, Mominta ce. 


"Da uwar wa ki ke waya Hindatu? Da wanda ke zuga ki ko? Hello, waye a kan layi?"


Momi ta ƙarashe da saka wayar a kunne gami da tambaya har wani huci take fitarwa tana yi tana hararar Hindatu wacce gaba daya ta rame a ɗan tsakankanin nan. 


"Hajiya Shatu, ni ce Hajiya Na'imatu. Ya gida?"


Tsaki Momi ta ja.


"Oh, Na'imatu? Sannunki toh. Ni dama na san ba banza ba yarinyarnan ta.."


"Kwace wayar Hindatu ta yi.


"Momi! Mene ne haka kike yi?! Na ce maki wani ne ya zuga ni?! A karon kaina na yanke hukuncin rabuwa da Alhaji Ibrahim don ba zan iya cigaba da zama da ɗan ƙungiyar asiri ba!"


Shaf ta mance ma ba ta katse wayar ba, ta yi wurgi da wayar gefe ta fice ta ƙyale Momin a tsaye baki sakaka. Madadin ta tsinci abin dubawa matsayinta na Uwa a kalaman ɗiyarta, sai ta ƙara shiga tsoro da firgicin wai an shiga tsakanin ƴarta da mijinta. Ta saki huci ta furzar. Ta rantse matuƙar ta ziyarci malaminta aka tabbatar da sa hannun Na'imatu sai ta kassara rayuwarta. Haka ta yi ƙwafa ta shanye ɓacin ranta ta koma ciki don rarrasarta, tunawa da ta yi da Ɗan Mutuwa wanda ya ce kar a sake a yi abinda zai jefa matarsa cikin ƙunci. 


***

  Katsina...


 Umma kuwa turus ta yi da waya a hannunta, a daidai lokacin da muryar Hindatu ya karaɗe kunnuwanta tana tabbatarwa da Momi cewa mijinta Alhaji Ibrahim Ɗan Mutuwa ɗan kungiyar asiri ne, a sannan Umma na zaune ne a falo ita da Baba Saude suna aikin tsinkar zogale na yin dambu. Duka-duka sannan ƙarfe ɗta da mintoci na rana. Wayar ce ta sanya Umma fidda hannunta a tiren ganyen zogalen. Labarin da ta tsinta na tabbatuwar Ɗan Mutuwa ɗan kungiyar asiri daga bakin matarsa ta yanzu Hindatu, sai ya girgiza zuciyarta fiye da kalaman da Momi ta soma a farko. 


"Hajiya lafiya?" Faɗin Baba Saude kenan ganin sauyin yanayi daga Umman. Murmushin yaƙe ta yi. 


"Babu komai. Bari na kama ruwa na dawo."


"Toh, ai wannan ma zai isa, mun tsinke da yawa."


Umma ba ta iya amsawa ba ta haye sama kai tsaye ta shige ɗaki. A gefen gado ta zauna tana ambaton sunayen Allah, ita kuwa ta taɓa cin karo da mutum irin Ɗan Mutuwa a duniyarta? Ace duk inda hanya ta shiriya da alheri suke ba ya nufarsu? Tausayin Haulatu har ma da na Hindatun duka ya kama ta. Ga nan ɗiyarsa jininsa, da ba ta san daɗin Uba mahaifi ba balle kuma tsawatarwarsa akan mai kyau da marar kyau. Hawayen da ba ta san da su ba ta ji ɗuminsu a saman leɓɓanta sai ta share su. Ita kaɗai ta san damuwar da kalaman Hindatun suka jefa ta ciki, sai da ta yi fatan ina ma ace ba su shiga kunnuwanta ba. A ƙarshe ta tattara tunaninsa ta watsar gami da bin sa da addu'ar shiriya da kuma roƙawa Hindatu kuɓuta daga sharrinsa. 


***

 Ta fito tare da Radiya don tafiya gida, Safina ba ta kammala ba sai ta yi lakca na 4-5pm. Facemask ne ya taimaka wajen ɓoyuwar kumburin leɓanta don ba ta yarda ta cire shi ba sai a aji wanda ya zama dole babu yanda ta iya da wani Malami guda mai tsauri ya ce sai ta cire hakanan masu niƙaf. A dole ta cire tana rufe bakin da hannu. Suna cikin napep Radiya ta numfasa ta ce.


"Safina fa ta dage gidansu za ta koma. Har ta kammala haɗa shirginta."


Haulatu wacce ta lula tunanin Yaya Sadauki da kuma damuwar kar rashin jin ta a waya ya sanya shi tunanin ko saboda shi ne ta katse wayar, maganar Radiya ta maido ta hayyacinta. 


"Uhum, rabu da ita, sai ka ce sauran jama'ar gidan ba mutane ba ne. Amma fa idan har a ɓangaren Baba Alhaji ne na yarda da shawararta, don ko ni ba zan iya jurar zama da mutum irin Anti Mabruka ba. Kuma ta ƙi yarda ta dawo wajenmu."


Murmushi Radiya ta yi.


"Ai fa, nima dai zan fi so ta koma gidansu koda ace za ta bar mu da kewa, kinga dai nan gaba kaɗan aure za ta yi, ko yaya ta ɗan ƙara jin ɗumin Mamanta kafin nan."


Jinjina kai ita ma Haulatu ta yi tana murmushin. 


"Akwai abinda nake son faɗamaku yau, amma ina tsoron shaƙiyancinku."


Da zumuɗi Radiya ta kalle ta. 


"Ah haba kin san ai ba komai ne muke zolayar junanmu a kai ba. Don Allah mene ne?"


Dariya Haulatu ta yi. 


"Ba zan fadamaki ke kaɗai ba, duk mai son jin labari ya zo ya same ni da zarar an yi sallar Magriba."


"Ai kuwa za ki gan mu. Fatanmu dai ya kasance alheri."


Ta lumshe idanu ta na murmusawa ta amsa da in sha Allahu. 


***

Sadauki tun daren da ya yi magana da Haulatu ya kasa sukuni, abin da ya ƙara jefa shi cikin damuwa bai wuce wayar da ya kira ya fi a ƙirga amma bai same ta ba. Tunaninsa har ya soma ba shi tsoro, ko don shi ta kashe wayar? Daƙyar ya iya jarumtar zuwa ofis washegari, ko tashi ba'a yi ba, karfe biyar saura ya taho gida. Madadin ya bi ta gate ɗin gidansu, sai ya zagayo ta babban gida, shi dai kawai ya sanya ta a idanuwansa.  


Koda ya yi parking kai tsaye ya fito ya yi ɓangaren Hajja. Su Najeeb da ya yi karo da su suka gaishe shi da girmamawa ya gyaɗa kai yana amsawa ta hanyar motsa leɓɓa. Sam dauriya yake yi wurin ɓoye haƙiƙanin abin da ke ransa, wato damuwa.


Sallamarsa a falon Hajja ya sa Umma dubansa tana amsawa, ita kaɗai ce a falon, Hajja har a sannan ba ta dawo daga ɓangaren Baba Alhaji ba, yau hirarsu suke sha har Baba Dakta ko kuwa ace maganarsu na abinda ya shafe su matsayin ƴan uwan juna. Sallar la'asar ma can ta yi, Haulatu kuwa tun dawowarta da ta haye sama ba ta sauko ba. Da murmushi sosai a fuskar Umma ta tarbe shi.


"Bismillah, shiga ciki mana Abeed." 


Ya shiga ya zauna ba musu, madadin ta je su gaisa sai ta koma ta ɗaukomasa ruwa ta dawo falon, sai da ta zauna ya gaida ta. Ta amsa da yanayin fuskarta na koyaushe, wato murmushi. 


 "Ya wajen su Hajiya? Ya kuma gajiyar biki?"


"Alhamdulillah Umma, su ma duk suna lafiya. Hajja ba ta nan ne? Ban ji ta ba."


"Yau Hajjah an je sada zumunci, tana can sashen Baba Alhaji."


Ya amsa da ok yana mai buɗe ruwan ya sha. Alamun gajiya har ma da yunwa da Umman ta gani tattare da shi ne ya sanya ta miƙewa, dambun da tuni ya sauka saman wuta ta zubo masa ta jera komai saman faranti ta kawo. Shi kuwa hankalinsa ya yi hanyar hawa benen, yana son tambayar Haulatu amma nauyin Umman ya sanya shi kasa yi. Ƙamshin ne ya soma bugar hancinsa, dambu ne da ya ji gyaɗa da mai ga kuma ganye, sai ko sauce ɗin hanta da aka yi aka zuba a gefe. Aikuwa tuni ya yi bismillah ya soma ci. Umma na ɗan taya shi hira nan da nan kuwa ya shiga amsawa, kan kace me ya kusa tashi da filet ɗin dambu. 


 Daidai lokacin Haulatu ta sauko zuwa ƙasa, tun kafin ta kai ga ƙarasawa ta hango shi, shi ɗin ma ya ɗaga cokali zai kai baki ya ganta, har wata ajiyar zuciya ya sauke, Umma ta ɗan waiga don ganin abin da ya ɗauke hankalinsa har haka, ganin ba ta ga kowa ba sai ta juyo. A lokacin ita kuwa Haulatu kunya ya sanya ta yin baya da sauri, a karshe ma duk da yunwar da take ji bai hana ta sulalewa ta koma sama ba. Ba ta kaunar ya gan ta da wannan kumburin bakin da Fahima ta wuce gidansu yau ta bar ta da shi. 


  Shi kuwa sai ya ƙara jin ma wani kuzari na cin abincin. Yana kammalawa ya kora da ruwa. 


"Bari a ƙaro maka."


Faɗin Umma tana ƙoƙarin miƙewa da sauri ya ce.


"Umma a'a, Alhamdulillah na ƙoshi. Nagode."


Ta yi murmushi ta koma ta zauna. 


Baba Saude ce ta fito daga kicin din suka gaisa sannan Umma ke fadin.


"Wai nikam ɗiyartaki ta sauko ta ci abincin? Me ta ke yi haka?"


Baba Saude ta yi dariya.


"Ai yau dai babu wayar latsawa balle in ce shi ya dauke hankalinta, ga dukkan alamu mulkin ne ya motsa. Bari na bi ta da shi." 


"Aa Baba, rabu da ita, don kanta ta sauko ta ɗiba."


Baba Saude tuni ta fice tana fadin ai ba za'a shiga tsakaninta da Haulatu ba. Yanzu za ta kai mata. Umma dai girgiza kai ta yi. Sadauki jin an zo inda yake so ne ya sanya shi yin magana. 


"Wani abu ne ya samu wayar?" 


Ɗan taɓe baki Umma ta yi.


"Uhum, wai fashewa ta yi ta tsage, jiya tsautsayi ta ɗan zameta faɗo daga bene amma ba ta ji ciwo ba, bakin ne kawai ya ɗan kumbura. To shi ne ta kashe wayar wai ba za ta ƙara aiki da ita ba."


Duk sai ya ji babu dadi, ashe baiwar Allah abin da ya faru gareta kenan? 


"Ayya, Allah ya ƙara ya kiyayewa."


Umma ta amsa da amin. Daga nan ya yiwa Umman sallama ta ce ya gaida su Momi Nuratu, ya amsa sannan ya fice.

Wurgi take da duk abin da ta samu a ɗakin nata kamar wata mahaukaciya, yi take tana ihu da kuka, Maminta na aikin rarrashi da nuna mata wannan sam ba zai zame musu mafita ba.

Ganin abin ba na ƙare bane ta riƙe tsintsiyoyin duka hannunta biyu. 


"Kina hauka ne?! Wannan abu da ki ke yi an fadamaki shi zai haifar da ɗa mai ido? A tunaninki zai sa ki samu Sadauki?"


Jannat ta fisge hannuwanta. 


"Ni Mami ki rabu da ni! Wannan banzar Bokanyar ta yaudare mu ta ci amanarmu kawai! Babu wani abu da ya yi tasiri akan Yaya Sadauki, ko kallon salama ban samu daga gareshi ba, bai ɗauke ni a bakin komai ba sai wulaƙantacciyar ƙanwarsa!"


Mamin Khaleefa ranta ya ɓaci. Tun sadda Jannat ta kira Bokanyarsu da banza ta ji kamar ta kifamata mari don ta tabbata aljanun Bokanyar suna ji kamar yanda ta taɓa shaida musu cewa ita ko ba ta wuri aka ambace ta, aljanunta na kwaso mata komai. Daƙyar ta iya danne fushinta ta ce 


"Ya isa haka, kar ki ƙara magana, idan ya san wata bai san wata ba."


Jannat ta juyawa Uwar ƙeya, ta gaji da gafara Sa ba ta ga ƙaho ba. Ta fi yarda da abinda ta yanke a zuciyarta, wato tunkarar Baba Alhaji ta cire kunya ta ce masa tana son Yaya Sadauki. Ta gwammace ta yi haka da dai ace tana kallo ya auri wata ƴar bariki Haulatu ya kyaleta. Mamin har ta gama surutanta a yanda Jannat ta dauka, ba ta ko kalle ta ba har ta gaji ta fice sakamakon wayarta da ya hau ringing kuma sunan Khaleefa ne. Tana ɗauka yake sanar da ita Hafsat matarsa ta haihu suna asibiti an samu ƴa mace. Dama Annur ɗin tun soma laulayinta ya ke nan a gidan Mamin, nan ta shiga faɗa wai don me bai kira ya sanar da wuri ba ya bar ta ita ɗaya a asibiti. Sai da ya sanar da ita ai Hajiyar Hafsat din na nan sannan ta sauko. Ɗakin Jannat ta dawo fuskarta a sake.


"Hafsat ta yi, an samu ɗiya mace. Shirya muje asibi..."


"Ni babu inda zan je." Ta amsa kai tsaye fuskarnan kamar hadarin kaji. Madadin Mamin ta ji zafinta sai kawai ta share da fadin.


"Dama na san yanayin nan da kike ciki ba lallai ki iya zuwa ba. Ki huta idan kina buƙatar wani abun sai ki yiwa Indo magana ta girka maki. Kinsan Hajiya Shukra ba mutunci ne da ita ba, yanzun za ta ce ba a kula da ƴar ta ba, bari na yi sauri na tafi."


Ko ci kanki Jannat ba ta ce ba.


***

Radiya da Safina zaune sun yi wa Haulatu  ƙuri da idanu ita kuwa sai ja musu rai ta ke. Sun fi minti ashirin da zuwa dakin amma daga bari ta yi shirin bacci sai bari ta shafa mai a kanta yana mata ƙaiƙaiyi. Gajiya suka yi Safina ta fisgo hannunta har murfin man gashin na faɗuwa, ta kuwa yi dariya. 


"Don Allah mene ne haka? Ke daɗina da ke idan kin ga ana son jin labari akwai jan rai. Kin ce mana Yaya Sadauki ya maki wasu maganganu da bikin Maama amma kin ɓige da wanka yanzu kuma shafa mai na tsirfa."


Ta ƙara murmusawa. Umma ba sa nan sun tafi asibiti ganin matar Khaleefa da ta haihu don haka su kaɗai ne a saman ke budurinsu. Ganin sun mata ca ya sanya ta saurin zuwa ta zauna tana ɗaga hannuwanta alamun saranda. 


"Na ji kar ku cinye ni ɗanya." Nan ta shiga ba su labarin duka abin da ya faru, tun soma labarin suke washe haƙora har ta kai aya. Ai kamar jira suke yi suka ruƙunƙumeta suna ihu da dariya. Safina ta mike tsaye har da rawa da juyi. 


"Kai kai! Ba zan iya misalta maki farin cikin da nake ciki ba Haulat, ke kuwa don Allah me ya cije ki da har yanzu ki ka kasa sanar da shi kin amince ta waya? Au, mts, ashe ba wayar." Faɗin Radiya kenan, Safina wacce ta dawo ta zauna ta ƙara sakin wata dariya kafin ta ce.


"O'o, kai, Alhamdulillah. Ke har na hango idanun Fahima da Anti Jannat, ai ni nasan babbar magana ce wannan lamarin zai jawo, sai mun toshe kunnuwanmu duk abin da za'a ce a yi ta faɗi, ni nasan dai iyayenmu za su rungumi lamarin nan da hannu bibbiyu."


"Ki na batun su Fahima, ai idanun Yaya Zaid na fi kaunar na gani, hum, ya yiwa kansa." Radiya ta faɗi, nan Safina ta riƙe haɓa.


"Au, to ai na ma manta, ni Yaya Mu'az ma kamar dai shi na kula ko shiga harkarki ba ya yi, ya biyewa Momi ta raba zumuntarku. Tunda dai ai ko babu aure akwai zumuntar."


Haulatu ta taɓe baki. 


"Su suka sani, ni a farko na ji ciwon yanke alaƙar zumuntar amma yanzu ko a jikina tunda dai ai shi yana da hankali kuma ya yi karatu a addinance ya san hukuncin yanke zumunci." 


Nan suka rufe babin nan, suka yi ta zuzuta yanda Haulatu da Sadauki suka dace ita kuwa sai murmushi ta ke bugawa. Su ne har goman dare su na hira don ma sa'ar da suka ci washegari ya kama Asabar babu makaranta, Haulatu ma babu lesson saboda malamar tasu ta yi tafiya. Ga kuma Safina da ke shirin barin gidan a gobe za ta koma hannun iyayenta. Haka suka yi kamar kar a rabu a wannan daren. 


***

Tun wayewar garin Asabar ta ke cike da damuwar rashin waya, ba don komai ba sai a ranar ne za ta ba Yaya Sadauki amsarsa, babu damar ta yi yanda ya buƙata. Wayar Umma kuwa ba ta so ta yi amfani da shi, ita sam ba ta yanke sanar da Umman yanzu ba duk kuwa da irin yanda sam ba ta mata ɓoyon komai nata. Tsoron yadda za ta karɓi zancen ne ya sa ta zaɓi rufemata a yanzu. Koda ta sauko zuwa ƙasan, ta iske suna karyawa, ta ƙara gaida Hajja da Umma karo na biyu bayan wanda ta yi da Asubahi, zamanta ke da wuya ta soma haɗa shayi kawai sai gani ta yi Hajja ta ajiye mata kwalin waya a gabanta. Idanu waje ta dubi wayar kafin ta sa hannu ta ɗauka. Samsung A24 ce. Ta ɗago kai ta dubi Hajja da wani irin wangale baki na jin dadi ta ce. 


"Hajja, waya ki ka siya min?" 


Hajja na dariya ta amsa.


"Ina dai niyya aka riga ni. Yayanki ne ya aiko yau da safe ya ce a baki. An chaja maki ita tun jiya, har layin waya ya saka, kinga sai ki haɗa da tsohon layinki idan kina so."


"Wane Yayan?" Ta tambaya cikin son sani, don ta ƙudurce idan har Yaya Mu'az ne wannan karon ba za ta karɓa ba. 


"Sadaukin Alhaji." Umma ta amsa mata da murmushi a nata fuskar ita ma. Ko kaɗan ba ta kawo komai a rai ba, kawai dai ta kula jininsu ya haɗu. 


Ita ko Haulatu ai tuni ta yi suman zaune don jin wani sanyi da dadi. Kenan da Umma ta ce mishi ba ta da waya tuni ya saka a rai zai siyamata? Ko da dai gani ya kori ji tunda ga ta ga wayar a hannu, ta ciro ta a kwali ta jujjuya, silver colour ce, ta ganta a kunne. 


"Ki ajiye wayar hakanan ki karya mana." Fadin Umma tana kallonta.


Ba shiri ta ajiye kuwa, tana kammalawa kuwa ta tattara gurin ta kai komai kicin sannan ta kwashi jiki za ta koma sama don kiran su Safina a waya ta ƙara jin muryar Umma. 


"Ki dai kira shi ki masa godiya." Hajja kuwa fadi take.


"Ni dama dai wannan son da wancan mara aikin yi ke maki, Sadaukin Alhaji ne ke yi, ai da na ji dadi."


Haulatu dake amsawa Umma da toh, ta dubi Hajja jin abin da ta ce kafin ta ɗan kalli Umma wacce ba ta ce uffan ba sannan ko a yanayin fuskarta ba za ka fahimci komai ba don haka sai ta yi saurin juyawa ta haye abin ta. Hajja kuwa murmushi kawai ta yi ba ta ce uffan ba. 


***

Ya kalli fuskar wayarsa ta fi a ƙirga, ya fito ya yi kewayen, shi ne har ɓangaren Baba Dakta da Baba Alhaji daniyyar gaida su, ya ci karo da Safina wacce za ta wuce da yamma, ya tambayi ƙawarta? Tana danne dariyar ƙin maida amsar da Haulatu ta ce ba za ta yi da wuri ba sai ya ƙosa ta amsa.


"Ba ta shigo ba duka yau." 


Sadauki ya haɗiyi miyau mai ɗaci, ba ya son tunaninsa ya cigaba da ba sa cewa ba ta sonsa ne. Ya yi shiru ya na sauraron Baba Alhaji na yi jan Safina da tsokana wai ta zauna kawai babu inda za ta koma. Ita kuwa tana fadin ya yi hakuri. A karshe ya mata nasiha sannan ya tambayi ƙawayenta? Safina sai da ta ɗan kalli Sadauki da idanunsa ke kan waya amma kuma hankalinsa na ga amsar da za ta bayar sannan ta maida kai ga Baba Alhaji. 


"Tare zamu je da su. Za su yimin rakiya."


Jin haka Sadauki ya ɗago kai amma bai ce uffan ba. 


"Toh shi Gali yana nan?" 


"Eh amma babu mai a motar ya ce." 


Ɗan gyaran murya Sadauki ya yi. 


"Bari na kai su kawai, dama zan je asibiti ganin Baby." 


Yana nufin jaririyar da aka haifawa Khaleefa. Safina ta yi godiya ta miƙe ta fita tana danne dariyarta, ba za ta faɗawa Haulatu wanda zai kai su ba gudun kar ta ce ta fasa ta ce tana jin kunya. Riba dai biyu, za su je su ga baby wacce a hoton waya kawai suka gan ta da aka turo whatsapp group dinsu na zuri'a. 


***

Biyar da mintuna na yamma, Safina ta kammala duka zagayenta na yiwa kowa a gidan sallama, duk inda ta shiga sai ta fito da wata kyautar, hatta Umma sai da ta bata turmin atamfa. Haka ta dinga fitar da hawaye kamar kada ta tafi duk da dai cikin garin katsina ne amma sabo ake wa kuka. 


Haulatu cikin doguwar baƙar abaya mai kwlaliyar duwatsu, leɓɓanta sun sace daga kumburin da suka yi sai dai ɗan taruwar jini kaɗan da ake gani daga ƙasa. Idanunta ya ɗan yi ja saboda kukan kewar Safina da suka yi ita da Radiya. Hajja ta dinga yi musu faɗa don ita ba ta son kuka, fadi take ai ba mutuwa Safinar za ta yi ba, duk sadda aka so haduwa za'a ga junan. 


Koda suka fito su Najeeb dake tahowa daga wurin motar Sadauki inda suka kai kayan Safinar aka sa a boot, suka yi turus suka dube su. 


"To super glue, wai kewar Safinar ce ta saka ku kuka? Hahaha! Taɓ! Ni kuwa na yi me toh? Me dafamin indomie idan na ji yunwar dare za ta tafi?" 


Haidar ya kai masa bugu. 


"Au abin da za ka ce kenan ko? Sorry Feenah, muna kaunarki, ai ba a rabu ba, kina can ma za ki dinga ganinmu. Ba mu gama jin kewar Maama ba ke ma kin tattara za ki gudu ki bar mu ko? Ai shikenan."


Hon ɗin da Sadauki ya yi ne ya sanya su tuna wanda aka bari da jira. 


"Oh, kai ba ruwana sai anjima. Boss ya ƙosa ku tafi. Sai mun yi waya."


Haulatu ta dubi motar Sadauki kafin ta dubi su Najeeb da har sun ɗan soma takawa. 


"A'a, ban gane ba? Ba za ku je ba? Kuma ki ka cemin Gali ne zai kai mu?" Ta ƙarashe tana kallon Safina. 


"Mu je Haulatu, motar ce kawai ta Yaya Sadauki, yana jira ne a kai mu a dawo zai fita."


Kasancewar tuni su Najeeb sun yi gaba sai ta yarda, bayan ta bude gidan gaba ta sanya kai ta juyo tana kokarin rufe murfin da fadin.


"Malam Gali ina..."


Sauran zancen ya maƙale mata a fatar baki ganin wanda ta yi ido huɗu da shi. Sai ta ga kamar ya ƙara haske don fuskarnan ta yi fayau. Nan kuwa damuwa ce don har wata ƴar rama kaɗan ya yi. Sai ta ga ya yi mata kwarjini ta kauda kai ta gaishe shi, ya amsa mata yana sauke ajiyar zuciya. Su Radiya ma gaida shi suka ƙara yi ya amsa, jin duka sun rufe ƙofofin ya sa itama rufe na ɓangarenta amma tsabar sanyin da jikinta ya yi bai ma rufu sosai ba. Madadin ya ce ta ƙara rufewa sai kawai ya cire seatbelt dinsa ya fita a motar duk suka zubamasa idani don a tunaninsu ko mantuwa ce ya yi, Haulatu kuwa kallonsa take ganin ya zagayo ya buɗe murfin motarta sai da gabanta ya fadi don a tunaninta ko laifi ta mishi zai sauke ta a motar, sai ta ga ya ƙara rufewa dakyau sannan ya zagaya, har wani ajiyar zuciya ta saki, su Safina da Radiya ko kallon juna suka yi da murmushi.  


Madadin ya fara kai su gidan Dakta Hashim, sai ya soma yin asibitin. Ita dai Haulatu babu um balle um um, kallon wayar da ya siyomata take yi, ga kunyar ko godiya ba ta masa ba, shi kuwa a hankali yake bin waƙar da ke tashi kaɗan kaɗan na harshen larabci. Yana tsayawa ya dube ta. 


"Ku shigo muje, na san ba ku zo ganin baby ba ko?" 


"Eh Yaya." Safina da Radiya suka amsa, ya bude murfi ya fito su ma duka suka fito ya rufe. Gaba ya yi su na binsa a baya yana waya, lambar ɗakin aka fadamasa ɓangaren VIP ya tafi. Haulatu sai kallon wurin tame, an ƙara gyara a asibitin kamar ba nan ta taɓa zuwa ba. Tun ganin da ta yiwa Nusaiba a tsaye tana amsa waya a ƙofar ɗakin ta gane Momin Mu'az na ciki. Nusaiba da sauri ta cire wayar a kunne ta gaishe da Sadauki ya amsa ba tare da ya kalle ta ba ya juya ga su Haulatu. 


"Ku soma shiga."  


Safina dake a gaba ta murɗa ta shiga da sallama aka amsa, Mamin Khaleefa ce sai Momin Mu'az da wasu yan uwan Hafsat din ciki har da mahaifiyarta Hajiya Shukrah. Ganin Haulatu ya sa sauyi ƙarara ya bayyana a fuskokin Mami da Momin Mu'az. Haulatu dai ta gaishe su yanda ƴan uwanta suka yi, masu amsawa sun amsa idan ka dauke su biyun. Sai a sannan Sadauki ya shiga shi ma. Ganinsu tare ya baƙantawa Mamin Khaleefa, wato can ga ƴarta na sumbatu a kansa, shi kuwa yana nan ya zama direban Haulatu. Sun dai amsa gaisuwarsa da yaƙen dole, Hajiya Shukrah ce ta sakarmasa sosai don mutuminta ne, sadda Khaleefa ke yayin zuwa gidanta tare suke zuwa. Aka miƙo masa jaririyar mai kama da Khaleefa sak, karɓa ya yi ya shiga yi mata addu'a. Haulatu ƙasa-ƙasa take satar kallonsa ganin yadda bebi ya yi kyau a hannunsa, har wani murmushi ta ɗan yi. Ba zato kuma ya ɗago kai suka haɗa idanu, shi ma murmushin ya yi mata sannan ya miƙa mata bebin. Wannan abu duka a kan idanun iyayen nasu biyu dake adawa da su, ransu ya mugun ɓaci amma suka danne. Momin Mu'az ke tambayar Safina dagaske guduwa za ta yi daga babban gida, dariya kawai ta yi. Ba su wani jima ba suka yi musu sallama suka fice. Kasancewar Sadauki ya riga su ficewa ne ya sa Safina fadin.


"Ku, ni kadai na kula da hararar da su Mami ke bugawa Haulatu?" 


"Wallahi ina shirin magana ki ka rigaye ni Feenah. Hum, ai na ga abin mamaki. Can dai ta matse musu, in sha Allahu na gaba dai ya yi gaba." Fadin Radiya. 


"In sha Allahu." Safina ta amsa. Ita ko uwar gayyar ba ta ce uffan ba don dama ai hakan ba baƙonta ne daga wajensu ba. 


A gidan su Safina ma ya bar su bayan ya shiga an gaisa ya ce zai je ya dawo, sai wurin bayan sallar isha'i sannan ya dawo, nan din ma an tafi da kewa amma wannan karon ba su yi kukan ba. Suna isa gida bayan ya yi parking Radiya ta bude ta fita, ba ta ma tsaya jiran  Haulatu ba don ta san maganar tsakaninsu ne. 


Kafin ya ce komai ta riga shi.


"Yaya nagode Allah ya ƙara buɗi. Wayar ta yi kyau sosai."


Abin da ta ce kenan. Ta ji sadda ya sauke ajiyar zuciya. 


"Nevermind, yiwa kai ne. Kin fa son amsar da nake son ji please. Na ce maki duk abin da ki ka yanke zan yi ƙoƙarin mara maki baya a kai koda zan cutu."


Yanayin da ya ƙarasa zancen sai ta ji ya karyarmata da zuciya, ya kuma ba ta tausayi. Ta buɗe motar ta sauke ƙafafunta a waje, tana kallon waje ta ɗan waigo kaɗan idanunsa a kan gefen fuskarta da ya ga alamar murmushi ta ke, ta soma magana.  


"In sha Allahu Yaya ba za ka taɓa cutuwa ba idan daga gare ni ce. Amsarka ita ce eh, na yarda na amince da kai. Ina roƙon Allah ya tabbatarmana da dukkan alheri a tsakaninmu."


Ta na kai wa nan ta fice da sauri ta rufe motar, ba ta ko kalle shi ba ta cigaba da tafiyarta, shi kuwa Sadauki hamdala ya shiga yi na nuna jin dadi da godiya ga Allah da ya amsa roƙonsa. Kalamanta suka cigaba da yawo a kwanyarsa, haka ya yi ribas ya fita zuwa gidansu yana jin wata sabuwar kauna da soyayyarta na ratsa shi. 


***

Tun zuwan Haidar ya sanar da ita kiran Baba Alhaji take cikin faɗuwar gaba. Jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi, ta san dalilin kiran amma kuma ta kasa gane meke zuciyar Ummanta. Ita ba ta ƙara zancen ba kuma ba ta sauya mata a komai ba. Hajja tuni ta samu labari daga Umman, kuma ɗari bisa ɗari ta ji dadi ta goyi bayan al'amarin. Ganin Haulatu ba ta da niyyar tashi ta wuce ne ya sanya Hajja kallonta. 


"Ke Haule, kiran ne ba za ki ba ko me? Ji min ƴa? Za ki tashi ko sai na zo inda ki ke?"


Ta ɗan saci kallon Umma wacce ko kallonta ba ta yi ba tana aikin shafawa Hajja man zafi a kafafu sakamakon kafafunta da ke mata ciwo. Ganin dai Umma ba za ta ce komai ba sai ta miƙe a sanyaye ta yafa gyalen da ta fita da shi makaranta da safe sannan ta fice. Bayan tafiyarta ne Hajja ta dubi Umma dakyau. 


"Wai ni Na'imatu kodai bakya son lamarin Sadaukin Alhaji da Haule?"


Da ɗan mamaki Umma ta ce.


"Hajja me kika gani? To ai ban ce komai ba."


Ɗan murmushi mai hade da dariya Hajja ta yi.


"Na'imatu kenan, ai koda ace ban yi zama dake a farkon rayuwa ba, yanzu tsawon lokacin da muka ɗauka tare ya ci ace na fahimceki. Damuwar dai tun ta farko ce da ki ka yi ƙorafi a kai ba ta sake ki ba."


Umma ta yi shiru tana maida murfin man ta rufe. Sadda ta samu Hajja da batun Haulatu da Sadaukin, ta yi ne don ta nunawa Hajjar abin bai kwanta mata a rai ba gudun abin da zai je ya zo, Hajjar kuma ta fahimce ta sosai amma ta nuna mata hakan duka ba hujja ce mai ƙarfi da zai sa ta dakatar da yaran ga samun farin cikinsu ba. 


"Na'imatu, ki bar wa Allah komai ki taya ƴarki neman zaɓinsa. Sadaukin Alhaji a kaf matasan nan idan ka ɗauke Dakta (Khaleefa) ya fi su nutsuwa da sanin ya kamata. Ban taɓa jin inda aka koka da halayyarsa ba, don haka kar ki yarda ki sanya damuwar komai a ranki. Ballantana ma ina da tabbacin Nuratu da Ridwanun da ki ke tunanin ba za su amince da Haulatu ba, sai sun fi ki murna da wannan haɗin. Ki cire damuwar nan a ranki mu aurar da Haulatu, kema fatan samun miji nake ta maki don in sha Allahu ba zan zuba idanu da ƙuruciyarki ki tsofe a gida ba sai dai kawai idan Allah bai nufeki da auren ba."


Tsam Umma ta tashi, an zo darasin da ba ta so ta ji Hajja ta ɗauko shi, Hajja ta yi dariya tana bin bayanta da kallo.


"Ka ji min wani shirme? Au auren ne ba kya so a tayar da zancensa? Ai shikenan." 


***

Ta yi zaune gaban Baba Alhaji shi kuwa sai da ya ja ta da hirar makaranta kamar koyaushe har ta ɗan saki ranta sannan ya yi gyaran murya. 


"Haulatun Hajja, ɗan uwanki ne ya zo min da wata magana shi ne mai dadi sai dai ban yanke hukunci a kai ba na fi son jin ra'ayinki tukunna."


Ya ɗan yi shiru yana ɗan tari. Dama ita ta san inda zancen ya kwana, ya ɗora maganarsa da jefamata tambaya. 


"Ke kika amince da Sadauki ya fito neman aurenki?"


Kunya ya sanya ta murmushi kawai kanta na ƙasa, ya kula da hakan, a matsayinsa na babba kuma ya fahimci amsarta sai dai zai fi ƙaunar ji daga bakinta ta amsa. Don haka ya ce. 


"Haulen Hajja." Ya furta kamar yanda ya saba idan yana cikin raha. 


"Na'am." Ta amsa. 


"So nake ki ce min eh ko a'a. Ni yau suruki kika maida ni ne?"


Ta girgiza kai tana murmushi. 


"To ki faɗamin, kin amince da Sadaukin Alhaji, kin ba shi damar ya fito neman aurenki ko kuwa shi ma irin wadancan ne na baya ne, ba da yawunki ya zo ba?"


Ta ƙara girgiza kai sannan ta yi magana murya a ƙasa.


"Na amince Baba Alhaji."


Tana faɗin haka ta yi saurin rufe fuska da tafukan hannuwanta. Ya yi dariya.


"Ja'ira, yau ni kike jin kunya kuma? Toh Alhamdulillah. Na ji dadin wannan amsa taki kwarai, dama can na maki sha'awar miji irin Sadaukina, ban bayyana ba ne don kar ya zama na so kaina da yawa, ba na son tursasawa kowa, na fi so ace ban yiwa kowannenku dole ba a jikokina don dukkanku tsatso guda ku ka fito. Allah ya zaɓa abinda ya fi alheri, tashi ki je, zan yi magana da iyayen naku."


Ba musu Haulatu ta miƙe ta fito, sai ta ji gaba daya zuciyarta ta yi wani sanyi, duka wannan fargabar ta kau, ta sani Umma kawai damuwa ce ta sanya a rai amma ba za ta ƙi aurenta da Sadauki ba. Kuma ta tabbata idan da Ummanta ce, nan ba da jimawa ba komai zai wuce a ranta. Kiciɓus suka yi da Anti Mabruka wacce shigowarta gidan kenan, yanzu ba ta zama kusan kullum sai ta fita, yau ɗin ma ta sha kwalliya kamar wacce ta dawo daga yawon gidan biki. Ta gaishe ta, ita kuwa ta bi ta da kallon sama da ƙasa kafin ta ja tsaki ta maida duba ga ƴar dattijuwar dake kuma da mahaifiyarsu. 


"Inna ta yi bacci?" Ta amsa mata da eh , za ta wuce ta dakatar da ita. 


"Baba Alhaji ya ce idan kin dawo yana nemanki."


Jin haka ran Mabruka ya ɓaci, Haulatu dai tuni ta ficewarta don ba ta ga dalilin da zai sa Anti Mabruka ta lalata mata farin cikinta na wannan rana ba. 


Ita kuwa Mabruka tana shiga Baba Alhaji ya rufe ta da faɗa sosai ya kuma rantse muddin ba za ta bar yawace-yawacen gidan ƙawaye da bokaye ba shi zai yi maganinta. Nan da nan ta zaro ido ta dafa kirji.


"Ni? Baba ni ke bin bokaye?" 


Ya kalle ta kawai, Safina ta ba shi labarin abin da ya faru kafin auren Maama, ya yi shiru ne kawai bai ce komai ba tare da addu'ar Allah ya shiryamasa ɗiyar, amma ya kula abin nata nema yake ya fi ƙarfinsa don har sanyawa ya yi ana bibiyarta a ga inda za ta je, a nan ya gano ba ta sauya zani ba, ya so yiwa yayyunta zancen amma ya sani matakin da zasu dauka zai fi na sa tsaru dalilin kenan da ya zaɓi fara gwada nasa ikon tunda dai ba ta fi ƙarfinsa ba. 


"Na san da komai da kike aikatawa Mabruka, kin maida kanki kamar jahilar da babu arabi balle boko. Kon kasa yarda da kaddararki, a hakan ki ke tunanin za ki samu mijin aure? Maza nawa suka fito suna sonki amma tsabar raina arziƙinsu da ki ka yi, ki ka wulaƙanta su? Yanzu kuma madadin ki bar wa Allah komai ko rungumi kaddarar da ya rubuta mako har mijin aurenki ya fito amma kin gwammace ki yi shirka ko? To ba a gidan nan ba, wallahi kin ji na rantse maki muddin ki ka cigaba da bibiyar gidajen bokaye don yiwa ƴar uwarki mugun abu ko kuma don wata buƙata ta kanki, sai na yanke hukuncin da ba ki taɓa zaton zan ba a kanki."


Ita dai Mabruka ji ta yi kamar ta saki fitsari a wando. To waye yake faɗawa Baba Alhajin abin da take shukawa? Kuma tun yaushe ya sani ya yi shiru bai ce komai ba? Nan da nan ta shiga zufa duk kuwa da sanyin Ac da  ya mamaye falon.


"Baba waye ya soma zuwa ya yimin sharri a wajenka? Ni kuwa Mabruka me ya yimin zafi da zan bibiyi boka ak.."


"Ya isa hakanan, tashi ki je, ni dai na gargaɗeki, ki kiyaye don idan babu wannan rayuwar, akwai wata. Idan ba ki koyi aikin da zai nisantaki da wuta ba, hakika za ki faɗa mawuyacin hali a gaba. Komai ki ka yi hakuri kika bar wa Allah idan rabonki ne sai ya taddo ki a inda ki ke."


Nan dai ya yi mata doguwar nasiha mai ratsa zuciyar duk mai imani, amma Mabruka jin sa kawai take, sai ta ga ma kamar ai raina mata hankali aka yi kawai, komai ace ita ke da laifi, an kasa a cikin manyan abokan yayyunta wani ya samar mata mijin aure ya haɗa su, kuma shi kansa Baban ai yana da yaran abokansa da har gobe suke zuwa gaishe shi, manyan mutane amma bai taɓa cewa zai haɗa ta da kowa ba, sai yanzu da aka ga ta tashi tana fafutukar yanda za ta samu miji ake nema a tauye ta. Har ya sallame ta ta miƙe ta fice a dakin ba ta ko ji ɗarr na tsoron lahirar da kwanciyar kabarin da yake ta kirari ba. 


Baba Alhaji ya bi ta da kallo, shi ya haife ta, ya kuma fi kowa sanin wace ce ita, don haka ya girgiza kai zuciyarsa na ɗaci, sam bai ga alamun saduda ba a tattare da ita. Yanzu kuwa ya yanke zai tara yayyunta su taya shi nema mata mijin aure, idan har auren ne a gabanta gwara a yi shi da koma waye muddin ta amince za ta zauna. 


***

Momi Nuratu ta yi shiru bayan gama sauraron bayanan da suka fito daga bakin Mijinta Alhaji Ridwan. 


"Ya na ji kin yi shiru? Ko ba ki yi farin ciki da zaɓinsa ba ne?" Alh Ridwan ya tambaya. 


Ta girgiza kai gami da yin murmushi. 


"Ko kusa, akan me zan ƙi Haulatu? Na ji daɗi kuma ina fatan Allah ya sa su zamewa juna silar dukkanin alkhairai, Allah ya sa albarka a ciki. Sai dai na samu waya daga Hajiya Rahma (Mamin Khaleefa), wai don Allah na roƙi yaronka ya zo su yi hira da Jannat ko Allah zai sa su fahimci junansu. Har take cemin yarinyar ta tada hankalinta akan ita fa lallai shi take so. Toh ni dai nace mata ta yi hakuri dai har sai na mishi magana tunda yaran yanzu ba a gwada yi musu dole abin ba ya dadi. Akan hakan dai har saɓani muka samu don gani ta yi wai na goyi bayan ɗanka."


"Ikon Allah, ita Jannat din ke son Sadaukin Alhaji? Toh zan kira shi ɗin na ji ta bakinsa."


Daga haka ya ce a bar batun, dama Momi ta sani, idan har Sadauki ba ya so ba zai taɓa takura masa ba. Ita ɗin ma hankalinta sam bai kwanta da Jannat ba, ta san wace ce Hajiya Rahma tun ma zamanin ƴan matancinsu, kasancewar sun je makarantar kwana guda, ta san irin azabtarwar da ta yiwa juniors da kuma bin malamanta ita da mahaifiyarta duk a fadi tashin neman mijin aure mai hannu da shuni. Sam ba ta hanyarta ta haɗu da yayanta Barr Dawud ba, can suka hadu a wani biki har Allah ya kaddara aure. Ita dai ba ta ce komai a kanta ba har aka yi auren kuma ta samu karɓuwa a cikin dangi. Ba ta iya ta ɓata mutum ba, amma kuma daɗin daɗawar samun kwanciyar hankalinta, bai wuce cewar Yayan nata mutum mai yawan ibada da kuma kamewa ba. Ta sani har abada da yardar Allah, Mamin Khaleefa ba za ta taɓa nasara a kansa ba kuma hakan ce ta tabbata don har yau ta kasa mallakar shi yanda take so, Barr Dawud ya ƙi tanƙwaruwa. Sai dai kuma wasu lokutan rigimarsu ta fi tasiri ne akan tarbiyyar yaransa da take neman lalatawa, ba ta damu da suturun da zasu sanya su fita ba, ba kuma ta damu da zuwansu islamiyya kan kari ba. Wataran har cewa take yi su yi zamansu a gida kwakwalwarsu ta huta tunda an sha karatun bokon an dawo a gajiye. Duk tana da labarin komai, ita din ita ce babbar aminiya ta shawarar yayanta Barr Dawud, ta sani hakuri kawai yake yi da Mamin Khaleefa sai dai babu yanda ta iya mishi tunda ya ce shi sam babu ra'ayin kara aure a rayuwarsa ballantana kuma rabuwa da uwar yaransa Rahma. 


"Nuratu!" Kiran sunanta da Daddy Ridwan ya yi har sai da ya sa ta ɗan yi firgigit. 


"Na'am? Magana ka ke yi?"


Ya girgiza kai da mamaki ya ce. 


"Tunanin me kike yi haka ne? Zancen da ku ka yi da Rahma ki ka sa a rai har ta kai haka ko ya ya? Ban gane ba."


Ta wayance da ɗaukar gorar ruwa ta hau kokarin buɗewa.


"Babu komai. Kawai dai wani abin ne ya ɗauki hankalina. Allah ya nunamana, ya sanya albarka a aurensu."


Ba don ya gamsu da maganarta ba ya share ya na mai amsa addu'ar da amin. 


***

  Barr Dawud, mutum mai cikar kamala da dattako. A kallo ɗaya tak idan ka gan shi za ka gane shi ya haifi Khaleefa saboda tsabar kamanninsu. Tsawon, farin, har ma da ƙirar jikin babu wanda ba iri ɗaya ba. Idan ka cire shekaru ba su sa bambancin a zo a gani.

  Yana zaune a falonsa yana kallon labarai a tashar NTA. Shigowar Mami kamar wacce aka jefo ya sanya shi dubanta lokaci guda yana ɗaukar remote ya ɗan rage murya. 


"Rahma, lafiya?" 


Ta nemi wuri ta zauna fuskarta a turɓune ta ce.


"Ina fa lafiya Dawud? Yanzu fisabilillahi kana kallon ƴarka a cikin mugun yanayi akan abin da kake da iko da shi za ka iya magance mata amma ka gwammace ka yi shiru ka zuba idanu rayuwarta ta lalace?" 


Kansa ya ɗaure, yau wace kalar rainin wayo Rahma ta zo da shi? 


"Kin san me kike cewa? Ki shigo min falo ba sallama, ki zo ki hau yi min maganganun shirme da shiririta? Me na cewa ita Jannat ɗin? Ban ce ta haƙura ta fawwalawa Allah lamarinta ba? Ita ba ta san tawakkali ba? Yaron nan ba fa sonta yake ba, kuma ke kin fi kowa sanin ba zan kai ɗiyata hannun wanda ba ya kaunarta ba."


"Na ji na ji Dawud, fito kawai ka cemin Ridwan da Nuratu sun fi ƙarfinka. Ba za ka iya nemawa ɗiyarka auren ɗansu ba saboda ɗansu ba ya so. Shikenan, ni da kaina zan je na samu Alhaji Ridwan din na yi mishi batun Jannat ko..."


"Kar ki fara! Kar ki kusa ki fara."


Ta wurga masa wani kallo mai kama da harara sai kuma ta ja tsaki ta fice ta bar shi da jin ciwon wadannan ɗabi'u nata. Wai shi Rahma ta raina har haka, tsaki, harara, baƙar magana da ma nuna bai isa ba babu wanda ba ta gwada mishi. Idan wasu lokutan ya yi nasarar tanƙwara ta, wasu lokutan takan nuna masa fin ƙarfi. Ya sauke ajiyar zuciya gami da girgiza kai. 


"Allah ya ganar da ke." Iyakar furucin da ya yi kenan daga haka ya cigaba da abin da yake. Ya yanke zai ƙara kiran Jannat ya bita da nasiha da kwantar da hankali, gwara ace ta haƙura gudun abin da zai je ya dawo.


***

Washegari kiran Baba Alhaji ya sanya duka yaransa maza suka isa gidan. Barr Dawud sai da ya fara shiga ɓangaren Baba Dakta suka gaisa sannan ya nufi na Hajja. Da sallamarsa ya shiga falon, Hajja na sama a lokacin ba ta kai ga saukowa ba. Haulatu ta fice makaranta, Baba Saude dake kicin ta fito tana amsa sallamar tare da Umma wacce ke tsakar falon, ba ta jima da idar da sallar walha ba hakan yasa ko hijabinta ba ta cire ba, ya ƙaraso ciki suna hada idanu ta sunkuyar da kai fuskarta a sake ta ce.


"Sannu da zuwa Abban Khaleefa."


Ya amsa mata da dan murmushi saman fuskarsa. Bayan ya zauna ta gaishe shi, nan ma bai kasa a gwuiwa ba ya amsa. 


"Ina Hajja da ƴar gidanta?" 


Umma ta murmusa. 


"Haulatu ta wuce makaranta, Hajja ko tana sama, bari a kiramaka ita."


Ya dakatar da ita daga yunƙurin tashin da take. 


"A'a Na'imatu, ki bari kawai zan ƙarasa wajen Baba Alhaji, idan na fito sai na shigo mu gaisa."


Sai a lokacin ta ƙara dubansa, shi ma har a sannan bai ɗauke nasa idanun a kanta ba, wani abu ya ji yana tsirga masa a zuciya, ta kauda kai karo na biyu.


"Toh. Sai ka fito."


Daga haka ya miƙe suka yi sallama, bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya.


***

Kano...


A gigice Ɗan Mutuwa ya zube a gaban Dodo yana kuka da sheshsheƙa ga majina da ta wanke masa hanci. 


"Tuba nake Uban Dodo, kai kada ne mai yimin da ba ni, ka taimake ni da wata damar bayan wannan! Na yi iyakar yi na amma cikin nan sai da ya fice a jikinta."


Tsawa mai firgitarwa ya daka masa. 


"Ƙarya kake yi! Mu ba ma son mayaudari wanda ba ya cika alƙawari! Ka rasa dukkan wata dama ta arziki! Daga yanzu za ka fara ganin masifu da bala'i iri-iri a rayuwarka! Sai ka zama abin tausayi abin kyama!"


Wani irin mikewa tsaye Ɗan Mutuwa ya yi yana nuna inda Uban Dodo yake da yatsa. Murya a ɗage ya ce. 


"Ba ka isa ba wallahi ka yi kadan! Kai waye da za ka cemin zan ga bala'i! Muddin ba ka yimin abin da nake buƙata ba sai na tonamaku asiri kai da dukkan wadanda ke cikin ƙungi..."


Bai kai ga ƙarasawa ba ya ji an ɗaga shi sama cak an narka a ƙasa. Hakan bai hana shi mikewa yana kurarin sai ya ga bayan Uban Dodo ba tunda ya ci mutuncinsa. 


Wata wawuyar dariya Uban Dodo ya saka tare da mabiyansa baki ɗaya. 


"Ka shiryawa masifu da bala'i a rayuwarka Ɗan Mutuwa! Sai na nunamaka ni Uban Dodo ba'a ja in ja da ni! Ku fice min da shi yanzu!"


Ai Uban Dodo bai kai ga rufe baki ba wasu kattai suka cicciɓi Ɗan Mutuwa suka yi waje da shi.


Hajiya Adama ta bi shi da kallo tana jin wani sanyi a zuciya, ba ta kai ga aiwatar da shirinta akansa ba, sai ga shi nan sakayya ta tabbata da gaggawa. Haka aka cigaba da hada-hadar shan jini da cin naman kare zuciyarta wasai. 


A hanya tuƙi yake yi kawai yana ɗura-ɗuran ashariya. Koda ya koma gidansa ma kasa zama ya yi, komai ya samu jifa yake da shi yana zage-zage. Ƙarshe kuma ya ɗauki wayar ya dannawa Hindatu kira, bai ko damu da cewa dare ne ba. Tana ɗagawa ba tare da ya amsa sallama ba ya ce.


"Baƙar azzaluma mai mugun hali! Ni ki ka ci mutunci ki ka zubarmin da ciki! Ki je na sake ki saki uku don uwarki! Kuma ke da uwarki ku shirya kashin kuɗaɗena da ku ka ci!" 


Daga haka kitt ya kashe wayar ya yi wurgi da shi. Ya mike ya shiga banɗaki don kama ruwa kenan ji kake tim! Ya faɗi ya zube a bakin ƙofar kamar matacce. 

  

   AWANNI BIYAR KAFIN NAN....


Misalin ƙarfe takwas na dare, Ɗan Mutuwa na haramar fita tare da Duna, sauri yake yi ya je su yi zama meeting akan kayayyakinsu da suke saka ran a saka nan da kwana uku, wayarsa ta dauki ƙara. Ganin Hindatu ce ya sanya shi ɗagawa da sauri don dama tun ɗazun yake gwada wayarta ba ta shiga. 


"My Dear.."


"Yi hakuri Yallaɓai, ba ita ba ce. Suna na Mansur daga Dr K's Hospital."


Dakyar ya hadiyi miyau mai zafi. Kirjinsa ya hau bugu da ƙarfi. 


"Ina jinka, meke faruwa?" Ya tambaya a can ƙasan makoshi. 


Nan yake shaida masa hatsari ta yi amma jikinta da sauki, yana iya zuwa yanzu. Ai nan da nan hankalinsa ya tashi fadi yake.


"Cikinta fa? Yana nan ko ya fita?"


Sai da Mansur ya ɗan yi shiru, bai wuce don mamakin yanda bai tambayi lafiyar matar ba sai na cikin da take ɗauke da shi. 


"Komai lafiya." 


Wata doguwar ajiyar zuciya Ɗan Mutuwa ya yi yana mai dafe motar jin kamar zai kife. 


"To shikenan, gani nan zuwa yanzu."


Daga haka ya shiga motar ya ba da umarnin su nufi asibitin. Kasancewar asibitin ba ɓoyayyen asibiti ba ne, ya sa bai bace musu ba. 


Mansur wanda shi ya taimaka wurin kawo Hindatu asibiti, ya tarbe su. Bayan sun gaisa ya musu jagora har dakin da take, Duna ya tsaya a kofa tare da shi, Dan Mutuwa kuwa ya shiga  dakin. Jin an taɓa ƙofar ne ya sa likitan dake tsaye yana tambayar Hindatu ko akwai inda ke mata ciwo ya waigo, nos da Hindatu duk suka dubi wanda ya shigo. Hawaye ne ya zubowa Hindatu a fuska, ga farin cikin rabuwa da cikin dake jikinta, ga kuma na takaicin kanta na auren mijin aminiyarta ba tare da ta sani ba. Kuma na rashin dace a samun mijin ƙwarai. Ta sani wannan duka har da laifin Mominta. 


Shi kuwa Ɗan Mutuwa bayan sun yi musabaha da likitan yake sanar da shi mijinta ne. Nan ya buƙaci su je ofishinsa su yi magana. Ɗan Mutuwa ya dubi Hindatu ya dan shafi gefen fuskarta. 


"Sannu kin ji? Allah ya baki lafiya." Ta kauda kai gefe ɗaya zuciyarta na tuƙuki don ji ta yi kamar ya ɗoramata garwashin wuta. 


Daga haka ya juya ya fita.


A ofishin Likitan ne ya ji abin da ya kusan zautar da shi, wato na ɓarin cikin Hindatun. Ya miƙe ya hau faɗan wai makirci ne ya sa likitan zubar da cikin matarsa kuma ya rantse sai ya yi shari'a da shi. A karshe ya fita yana sababi kamar zautacce har da cire hula ya yi wurgi da ita. Ɗakinnda Hindatun take ya koma wannan karon da ƙarfi ya bugi ƙofar ta buɗe. Ya yi tsaye yana huci a kanta, ita kuwa kallonsa kawai take yi, kallo na tsana. 


"Ba ki isa ba Hindatu! Ni za ki kawowa iskanci da rainin wayo? Ni za ki nunawa bariki! Toh ni Ɗan Mutuwa ni ne barikin da kansa! A cikinta aka haife ni! Kin cuce ni kin zubarmin da burina da mafarkina! Allah ya isa tsakanina da ke!"Daga haka ya kada kai a gigice ya fice daga asibitin har da haɗawa da gudu-gudu. Duna ya bi bayansa da sauri shi ma yana mamakin abin da ya hargitsa uban gidan nasa har haka. 


Tun komawarsa gida ya kasa zama balle sukuni, meeting din da bai samu zuwa kenan ba, babban burinsa dare ya ratsa gari ya yi duhu ya samu zuwa ga mai sharemasa kuka, wato Uban Dodo. Shi ya sani ya ɗebo ruwan dafa kansa. Sai ga hawaye suna fita a idanun Ɗan Mutuwa na jin raɗaɗi da takaicin wannan asara da Hindatu ta jawo masa a rayuwa. Dare na kara nisa ya fice zuwa ga Uban Dodo inda suka haɗu baki daya ƴan ƙungiyar saboda taron gaggawa da ya tashi na hukunta Ɗan Mutuwa akan asarar da ya jawo wa ƙungiya na rashin ɗaya daga cikin ƴaƴanta. 


Wannan kenan.


***

Katsina...


Safina da Radiya suka yiwa Haulatu caa a makaranta da tsokana iri-iri wai za ta riga su aure. Ita dai murmushi kawai ta ke yi abin ta, hirarsu mai daɗi na jiya take tunawa ga shi a yau zai fara zuwa hira wajenta. Zancen tuni ya soma bazuwa tunda iyayensu duk sun sani. 


"Malama ana magana kin ma kasa amsawa sai murmushi. Toh ni ma dai iyayen Muhsin za su zo ganin Baba Alhaji."


Faɗin Safina har da yin wani fari da idanu. Suka dube ta.


"Dagaske?" Kusan lokaci guda suka jefamata tambayar. Ta jinjina kai tana dariya.


"Allah kuwa dagaske, dama tun ba yau ba yake son turowa ni ke tsaida shi, so nake yanda muke aminan nan mu yi aurenmu lokaci guda. Ke fa Radiya dama  Kamal ya yi iya yinsa amma kin hana shi magana, mutumin da tun bayan sallah ya so ya turo magabatansa. Don Allah ki ba shi damar zuwa mu yi aurenmu lokaci guda mu ƙara shaƙawa su Anti Jannat da Anti Fa'iza."


Suka yi dariya. Ba su ne suka yi sallama ba sai da lokacin shigar Radiya aji ya yi, su kuwa kasancewar sun kammala ficewa kawai suka yi ita kuwa ta yi aji. A titi suka rabu kowacce ta nemi napep din unguwarsu.


***

Haulatu sai safa da marwa take yi a ɗaki, ta yi adonta cikin riga da siket na atamfa har da su hoda kwalli, turare mai sanyi ta fesa amma ta kasa sauka ƙasan, Hajja ta faɗawa don ta kasa sanar da Ummanta amma kuma fargabar kada ya kasance Hajja ta mance ba ta yiwa Umman maganar soma fita hira wurin Sadaukin ba ya hana ta fitar gudun samun matsala. 


Wayarta ta yi ƙara ganin Sadaukinta ne ya sa ta ɗaga kamar za ta yi kuka. 


"Baby idanuna suna ta jiran su yi tozali da naki. Ni yangar nan ta ishe ni a yi mata kuɗi na siye."


Duk da halin da ta ke ciki sai da ta murmusa, Yaya Sadauki gwani ne a tsara kalaman tausar zuciya. 


"Yi hakuri Sadaukina, ina tafe yanzu da yardar Allah."


"Ok dear."


Daga haka suka yi sallama, shigowar Umma ɗakin ne ya sa ta ɗan diririce alamun rashin gaskiya. 


"Sadaukin bai iso ba ne?"


Tambayar Umma ya sa ta samun tabbacin sun yi maganar da Hajja. A kunya ce ta amsa da "Ya zo."


Murmushi Umma ta yi, wai yau ita Haulatu ke jin nauyi, lallai ana son Sadauki. Ta bi bayanta da kallo sadda ta fice da sauri-sauri a ɗakin. Girgiza kai Umma ta yi kawai gami da addu'ar nemawa ɗiyarta zaɓin Allah. 


A zaune ta iske shi saman kujera a rumfa, hasken fitilu ta ko'ina ya haske wurin tamkar rana. Ya sha yadinsa mai tsada kalar coffee kansa da hula baƙa. Ta ƙaraso da sallama ya yin da ƙamshinsa ya doki hancinta. Shi ma lokaci guda ya shaƙi nata turaren gami da amsa mata sallamar har ta zauna. 


"Kin yi kyau."


Ta ɗan yi murmushinta mai tsada. 


"Nagode."


Ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi. Hannu ya sanya a aljihu ya fiddo wani ɗan ƙaramin gida na zobe ya miƙa mata. 


"Buɗe ki ga ko zai maki?"


Ta dube shi, ya ɗan kashe mata idanu kafin ta kai duba ga ƙaramin red box ɗin dake tafin hannunsa. Ta kai hannu ta ɗauka ta buɗe. Zobe ne kalar silver mai wani ɗan stone a tsakiya. Murmushi ta yi karo na ba adadi shi kuwa Sadauki ya samu abin kallo har da lanƙwasa wuya. Ita kuwa Haulatu zoben ta ciro ta zura a yatsarta, ya bi yatsar da kallo. Kusan lokaci guda suka kalli juna a wannan karon. 


"Madadin zoben ya haska ki, sai na ga ke ki ka ƙara ƙawata shi."


Kauda kai ta yi har da ɗan lumshe idanu. 


"Nagode." Ta ƙara furtawa karo na biyu. 


"Kina da yawan godiya, da haka ki ke ƙara shiga raina. Ba kya raina abin godiya ko kaɗan."


"Toh ai bai dace ka yi min kyauta ni kuma na ja baki na yi shiru ba."


Ya ɗan taɓe baki kaɗan. 


"Wannan har wata kyauta ce? Ni fa yanzu kyautar da za ki yimin bai wuce ki amince a sanya ranar aurenmu ba kawai."


Ta ɗan kalle shi, ya gyaɗa kai gami da ɗan ɗaga gira.


"Yes, aurenmu nake so a yi nan kusa Baby, na kammala ginina, ina da sana'ata a hannu, sa'annina duka suna aure da ƙannena, so ki ke na tsufa nan gaba ki ga saurayi ki ce bakya sona?"


Ta yi narai-narai da idanu tana dubansa. 


"Mene ne haka don Allah? To ai ni ba cewa na yi halittarka nake so ba, ni kai..."


Sai kuma ta ji nauyin ƙarasawa ta sunkuyar da kai tana murza zoben da ya ba ta. Ya ɗan sunkuyo yana leƙen fuskarta ita ko ta ƙi yarda da kalle shi sai murmushi. 


"Say it."


A hankali ta saci kallonsa ta gefen idanu. 


"Ni fa ba wani abu zan ce ba."


Ya koma ya zauna sosai.


"Ok shikenan na ji, amma dai kin goyi bayan sanya ranar?"


"Baba Alhaji cewa ya yi mu fahimci juna tukunna."


Ta faɗi da zummar tsokana amma ko fuskarta ka kalla za ka rantse dagaske take zancen. Ya ɗan haɗe gira kaɗan.


"Baby wace fahimtar juna ya rage mana yanzu? A haka ba fa zamu taɓa fahimtar junan ba idan ba fatiha aka shafa ba."


Ta ɗan harare shi ta kauda kai, ya yi ƴar dariyarsa mai burgewa. Haka suka cigaba da hirarsu cike da nishaɗi suna masu ji tamkar babu waɗanda ya rage a duniyar face su kaɗai. 


 A lokacin da suke tsaka da hirarsu, Zaid ya shigo gidan, a safiyar ranar ya shigo Katsina. Kai tsaye bayan amsa gaisuwar su Fu'ad da su Najeeb da ke hira a farfajiyar babban gida ya nufi sashin Baba Alhaji don soma miƙa ƙoƙon bararsa sannan ya ƙarasa ɓangaren Hajja ya ga Noor ɗin rayuwarsa. 


Ya yi nasarar iske shi yana karatun Alkur'ani mai girma, sai da ya kai aya ya yi addu'a suka shafa a tare sannan Baba Alhaji ya dube shi yana gyara zaman gilashinsa. 


 "Masu gari, yaushe aka shigo ƙauyen namu?" 


Zaid ya na murmushi ya amsa.


"Ɗazu da safe na shigo Baba. Fatan na same ku lafiya?"


Baba Alhaji shi ma fuska a sake ya jinjina kai.


"Sai godiyar Allah. Ya iyalinka? Ya kuma wajen Safiyyar? Koda dai ita mun yi waya da ita ɗazu da rana."


"Eh suna cikin ƙoshin lafiya."


"Masha Allahu." Daga nan ɗan shiru ya biyo baya, Baba Alhaji duk a zatonsa ko ya ji batun auren Sadauki da Haulatu ne tunda ya sanar da Malama Safiyya komai a jiya da ya nemi ta shigo yana son ganinta, sai da ya ƙara yi mata batun aure don a cewarsa lokaci ya yi da ita ma za ta ba masu sonta da aure damar fitowa, daga bisani ya fayyace mata komai. Kasancewarta mace mai ilimi da sanin ya kamata, ko kusa ba ta yiwa abin kallo da wata manufa ko fuska ta daban ba, fatan alheri ta yi kuma ta ce wani dama bai isa ya auri matar wani ba. 


"Baba."


Muryar Zaid ta sanya Baba Alhaji dubansa.


"Na'am Zaidu."


Zaid ya muskuta.


"A yi kin alfarma a ceci rayuwata a aura min Haulatu, nayi alƙawarin ba zan cutar da ita ba. Zan riƙe ta bisa amana, zan kuma yi kokarin adalci tsakaninta da Jalilah."


Ɗan murmushi Baba Alhaji ya yi, tabbas Safiyya ba ta ba ɗan nata labarin komai ba. 


"Ka yi hakuri Zaidu, kai ne za ka fara ba da shaidar ni a zuri'arnan ba na yarda a aurawa kowa abin da ba ya so, saboda ban yarda da cutar da rayuwar kowannenku ba. Sai dai kuma idan Allah ya ƙadartawa ɗayanku hakan, ba ni da ikon hana faruwarsa. Rashin son da ka nunawa waccan yarinyar Zaituna, ya hana na zartar da hukuncin ka aure ta na dole, ka ga kuwa ba zan zamo mai son kai ba idan ban bari a yanzu Haulatu ta zaɓi abokin rayuwarta da kanta ba matuƙar mun bincika mun ga ba shi da makusa. Ka yi hakuri, maganarta yanzu babu, ta amince da ɗan uwanka Sadauki ta yarda ya nemi aurenta."


Kansa ya yi wani irin sarawa, meyasa akan kowa ta rasa na zaɓa sai Sadauki? Ya ji wani gumi na tsirfowa a goshinsa, idanun suka kaɗa tsabar tsananin kishi da ɓacin rai. Sauran nasihar da Baba Alhaji ke bin sa da shi ma ba wani shiga jikinsa ya ke ba. Ƙarshe ma sai ya murza yatsu suka yi ƙara ya yi wata ƴar dariya. 

 

 "Baba Alhaji kenan, ni na sani dama wannan ranar za ta zo, tun muna yara ka ke fifita Abeed a kanmu har ka kira shi da sunan Sadaukinka tsabar kaunar da kake yi mishi. Na jure duka wannan, yanzu kuma akan matar da nake so, ka zaɓi ka aura mata Abeed koda ba ta so, amma ni Zaid a kyale ni saboda ni mace ce ta haife ni a zuri'arku ba ni da wani ƙarfi tunda ba Ubana ne ya haɗa jini da ku..."


"Kai Zaidu!" Gaba ɗaya har Baba Alhaji da ya ji ƙwalla ta cicciko a idanunsa bisa munanan kalaman da jikansa ke jifansa da su sai da ya dubi mai maganar don ba su yi zaton bayan su biyun akwai mutum na uku a ɗakin ba. Ba kowa ba ne face Baba Dakta. Ya ƙaraso ciki hannunsa riƙe da leda mai ɗauke da magungunan Baban, jikinsa har rawa yake yi tsabar ɓacin rai da maganganu Zaid ya haddasa mishi.


"Are you out of your senses? Ko Safiyya ta isa ta dubi Baba ta faɗamasa munanan kalaman nan ballantana kai da ta haifa? Toh na maka rantsuwa koda Sadauki yau ya fasa auren Haulatu, har abada ba za ka same ta ba! Sakarai kawai! Kuma na yanke nan da sati huɗu za'a ɗaura musu aure!"


Baba Alhaji ma ya kasa magana saboda har a sannan razanin da kalaman Zaid suka jefa shi ciki ba su kai ga sakinsa ba. Kenan tun suna yara irin wannan kallon Zaidun ke masa? 


"Ka yi hakuri Baba." Ya tsinci muryar Zaid din na neman gafararsa bisa umarnin Baba Dakta. Wani murmushi da ya fi kuka ciwo sannan ya ce. 


"Kai ne wanda za'a bai wa haƙuri Zaidu, ka gafarce ni ka ji? Ban san haka kake kallona ba tun kana yaro. Amma ka sani, wannan abu da ka yi, ba zai hana Allah yin ikonsa akan kowa ba. Ina mai ba ka shawara, ka daina tsanan ƙiyayya ko soyayya, dukkansu sukan iya sauyawa kuma ka sha mamaki. Ba ni na haɗa auren Abeed da Haulatu ba, su ne suka shirya kansu, kowannensu da kansa ya tabbatarmin yana son ɗan uwansa, ni kuma ka fi kowa sanin ƙa'idata. Ina mai ba ka hakuri ka ji? Safiyya da Ridwanun da ma ita Nuratun duka tsatsona ne, koda ban haifi iyayensu ba. Kar ka kusa ka ƙara yin wannan gurɓataccen tunanin. Mun taso kanmu a haɗe ne, mun kuma yi iyakar kokarin wajen haɗa kan iyayenku. Ka yi kokarin cire komai a ranka gudun.."


Wani tari ne ya sarƙe Baba Alhaji, nan da nan Baba Dakta ya yi kansa, Zaid ya ruɗe ya tsiyayi ruwa a kofi dake gefe a cikin roba ya miƙa masa. Baba Dakta ya karɓe ya na mai ba Zaid umarnin ya fita ya ba su wuri. A dole jikinsa a sanyaye ya miƙe ya fita a ɗakin. Fushi dai babu abin da yake haifarwa sai nadama, ya san da ace ya kai zuciya nesa, ba zai yi munanan kalamai ga babban Uba garesu da  iyayensu ba. 


Daidai sadda ya fito da zummar wucewa inda ya adana motarsa, lokacin Sadauki ya jero tare da Haulatu suna tafe tamkar wasu taurari fuskokinsu a sake suna murmushi mai haɗe da ƴar dariya. Runtse idanu ya yi kafin ya bude su, suka haɗa idanu da Haulatu ya ga ta kawar da kai kamar ba ta gan shi ba. Sadauki shi ma sarai ya gan shi amma kuma ganin bai tanka masa ba ya sanya shi jan girmansa ya maida hankali ga sahibarsa. Zaid da sauri ya kaɗa kai ya fice daga gidan. 


Shi ko Sadauki sai da ya tabbatar ta shige sannan ya juya ya wuce ɓangaren Baba Alhaji don yi mishi sai da safe. Nan ya iske su tare da Baba Dakta su na tattaunawa, ganinsa ya sanya su amsa sallamarsa. Ya karaso aka ƙara gaisawa. Ya ɗan dubi Baba Alhaji.


"Baba lafiya kuwa?" Ya faɗi ne dalilin sanyin da ya ga ya yi.


"Babu komai Sadauki. Idan ka je ka cewa Baban naka ina son ganinsa gobe ya zo ya same ni." Fadin Baba Alhaji kenan, ya amsa da toh sannan ya musu sallama ya fice. ***

Kano...


"A yau rana ta Alhamis ne, sha biyu ga watan Junairu, jami'an tsaro suka cafke wata jamshaƙiyar mace mai suna Hajiya Adama Loma, wacce ta kwashi tsawon shekaru tana harkar safarar yara da miyagun ƙwayoyi, wanda a ƙarshe ƙungiyar nan mai yaƙi da safarar mata da yara wato Naptip ta yi nasarar kuɓutar da ƴanmata masu ƙananun shekaru sha biyar zuwa ashirin da ake ƙoƙarin fitar da su ta ɓarauniyar hanya ta Nijar. Ɗaya daga cikin yaran tana kuka ta shaidawa manema labarai cewa ita ƙanin babanta ne ya kawo ta har gidan Hajiyar inda suka yi cinikinta kamar wata dabba, aka cika masa lalitarsa ya yi gaba ya bar ta. Wata kuwa, cewa ta yi dama da niyyar karuwanci ta fito daga gidansu, a cewarta iyayenta ne suka hana ta saurayin da ta ke so."


Girgiza kai kawai Hindatu ke yi tana salati, tana daga ɗaki amma duk wannan labaran da ake watsawa a rediyon da makwafciyarsu ta kunna babu ɗaya da bai shiga kunnuwanta ba. Tabbas ta san wace ce Hajiya Adama Loma, ta kuma sha ganinta ta hanyar tsohon mijinta Ɗan Mutuwa. Godiya ta ƙara yiwa Allah da ya kuɓutar da ita daga cikinsu ba tare da sun yi nasarar gurɓata rayuwarta ba. Har aka ƙare labaran ba ta ji an sako muryar Hajiya Adama ba don a cewar ɗan jaridar ta ƙi yarda a yi hira da ita. Shigowar makwafciyar tasu ce da zummar yi mata wanka irin na jego ya katse tunaninta. Sunanta Asabe amma mace ce mai kirki kuma ba wata babba ce ba sosai. Tun zuwan Hindatu gidan ita ke ɗawainiyar kula da ita hatta abinci idan ta dafa sai ta zubamata. Momi har lokacin ba su dawo ba, ta kuma ji dukkan abin da ya faru amma sam ta nunawa Hindatun ba ta yarda ba sharri ne ta ke wa Ɗan Mutuwa don kawai tana so ta rabu da shi. Don ɓacin rai ma ba ta ƙara bari sun yi magana ba ko Momin ta mata a whatsapp ba ta amsawa. Babban burinta jikinta ya ƙara kyau ta tafi wajen mahaifinta. 


***

Su uku ke tsaye a falon, Maada, Ɗan Aljan da Duuna, kowannensu na busa karan sigari, Ɗan Mutuwa sun kai shi asibiti sun ajiye, Maada ya yi amfani da akwatin kuɗin da Ɗan Mutuwan ke yawo da shi a mota ya biya kudin gado da na magunguna daga haka suka fito a cewarsu za su je su dawo. 


"Ni fa kawai mu kwashe abin da za mu kwasa mu samfe kawai. Wannan garan ba tashi zai yi ba, idan ma ya tashi ba wani abun arziƙi za mu yaga a jikinsa ba. Ko ya kuka gani?"


Ɗan Aljan ke wannan kalamin yana dubansu. Wata dariya Duuna ya yi.


"Daɗina da kai akwai ja sosai. Kamar ka san tunanin da nake yi kenan. Ya dace mu yiwa kanmu gyaɗar dogo mu kwashi ganima mu yanka gabas."


Maada dake sauraronsu ya yi murmushi. Dama tunaninsa kenan sai aka yi sa'a nasa da abokansa ya zo ɗaya. Nan suka tsaida shawarar farawa da korar ma'aikatan sannan su yiwa gidan kankat a cikin daren nan su fice da komai su siyar. Da wannan kuwa suka yi nasarar sallamar duka ma'aikatan da cewa umarnin Maigidan ne. Su dai babu abin da ya sha musu kai tunda an musu kyakkyawar sallama don sif guda cike yake da kudade a dakin Ɗan Mutuwa.

A wannan daren suka nemo babbar motar da ta yi musu lodin kaya, babu wani abu da suka bari kama daga kayayyakin sanyawa har kayan furnitures da sauran tarkace. Hindatu dama tun sadda za ta bar gidan ta kwashe komai nata mai muhimmanci don ta saka a rai cewa ta gama aure a gidan, lefenta ba ta ɗauki ko tsinke a ciki ba, haka suka kwashe dukkan komai suna jin dadin wannan arziƙi da suka yi a dare guda. Takardun gidan suka nema ba su samu ba, ko kuma ace sun gani amma ba su san shi ne ba, tunda cikinsu kaf babu mai ilimin bokon balle ya karanta, dama-dama ma Ɗan Aljan, shi har sakandire ya fara zuwa kafin shaye-shaye da bin ɓata garin abokai ya lalata masa rayuwa. 


Motar har ta yiwa kayan kaɗan don dma farfajiyar gidan suka shigo da ita, daga nan suka yanke cewa Ɗan Aljan da direban su soma yin gaba su kai ma'adana su ɓoye waɗannan ɗin sannan su dawo a kwashe sauran. Da haka suka fice aka bar Maada da Duuna na zaman jira. Sai dai kuma har asubahi ta kawo kai babu su babu labarinsu. Wayar Ɗan Aljan ma a kashe, hankalinsu ya tashi. Duuna ya ƙunduma ashariya ya bugi katakon kujera.


"Kada dai ace wannan saunan yaudararmu ya yi ya gudu?"


Maada dake aikin cigaba da dannawa Ɗan Aljan ɗin kira ya koma ga direban, amma ina kowannensu wayar a kashe. Nan da nan suka ƙulle ƙaton ƙyauren gidan suka mara musu baya a ɗaya daga cikin motocin Ɗan Mutuwa, dama tuni sun yi cinikin sauran biyar ɗin tun da haske a gari suka fice da su ɗaya bayan ɗaya, kudaden aka zuba a asusun Maada tunda shi ne Ogansu. Ma'ajiyarsu babu Ɗan Aljan ba dalilinsa. Suka koma har inda direban ke parking ɗin ƙurƙurarsa. Nan ma aka ce ai yana asibiti, can aka tsince shi a gefen titi jikinsa duk sara. Suka kuwa iske shi yana kuka yake roƙon su masa aikin gafara Ɗan Aljan ne ya ce ya yi parking daga nan ya nemi ya fita a motar, gardamar da ya yi ce ta sanya ya sassare shi a jiki. Wannan maganar sam ba ta yi musu dadi ba. Haka suka fice kowannensu na cin alwashin irin kisan da zai yiwa Ɗan Aljan tunda har ya ci amanarsu. Nan da nan suka dinga kiran duka abokan dabarsu da suka sani a wuri-wuri kan cewa duk wanda ya ci karo da Ɗan Aljan ya shaida musu. Daga nan suka koma gidan Ɗan Mutuwa don jira dare ya yi su kwashe abin da ya rage. Sai dai a wannan ranar jami'an tsaro na yaƙi da miyagun ƙwayoyi suka mamaye gidan don kama Ɗan Mutuwa wanda Hajiya Adama ta ce bakinsu ɗaya tare suke aikata dukkan munanan ayyuka. Maada da Duuna ba su tsira ba, haka aka kwashe su, babban jami'in cikinsu da wasu yaran suka nufi asibitin da su Maada suka ce Ɗan Mutuwa na can yana jinya.


***

 Katsina...


 A wannan daren dai duk yanda Sadauki ya so ganin Haulatu hakan bai samu ba dalilin neman da Daddy ke masa akan zancen lefe da ma shirin biki wanda daƙyar suka roƙi Baba Dakta ya amince  ya maida nan da wata biyu, sati takwas kenan. Koda ya fito dare ya riga ya yi don haka kawai sai waya suka ɗan yi ba wata doguwa ba suka yi sallama.


A gefen su Hajja kuwa jin biki wata biyu ya sa ta shiga hada-hadar gyara Haulatu hakan ya sanya ta neman layin Maama, bayan sun gaisa ta ke shaida mata batun auren. Maama ta yi dariya. 


"Na ji labarin komai Hajja, ai Alhamdulillah sai fatan kawai Allah ya nunamana."


Hajja ta washe haƙora.


"Amin amin Zakiyya. Sai ki tasarwa shirya ɗiyartaki."


Dariya karo na biyu Maama ta yi.


"Ah wannan kam ai dolena ne. Zan yiwa Ummu Deedat waya, duk radda take da lokaci zan ce ta leƙo gidana, idan mun kammala magana sai na yi magana da Haulatun. Amma fa aronta za ki bani Hajja na ƴan satika."


"Ai ko na wata ne Zakiyya ba ki da matsala idan jikata za ta fito ras da biki."


Suka yi dariya da yiwa juna fatan ganin lokacin sannan suka yi sallama. 


***

 Barr Dawud ne zaune a chamber ɗinsu na lauyoyi, bai jima da fitowa a kotu ba inda ya kare wani maraya da ake zargin shi ya kashe iyayensa ƙarshe gaskiya ta bayyana cewa Yayan mahaifinnasa ne ya kashe shi. Yau aka yanke hukuncin shari'ar aka kama masu laifi. Zuciyarsa cike da farin ciki na wannan nasara amma damuwar da ya shiga a ɓangare guda ya hana shi bayyana wannan murna gaba daya. Ya gama fahimtar kansa a kwanakin nan, shi ba yaro ba balle ace ya kasa gane kauna ce da soyayya ta aure ya ke yiwa Na'imatun Hajja. Kamalarta, haƙurinta kai har ma da kyawun halittar da Allah ya yi mata, su ne suka haifar da wannan son nata da yake ji. Ba ya jin kuma zai yi shiru, zai gwada sa'arsa tunda su ɗin ba yara bane. Zai yi dai ƙoƙari ya danne zuwa sa'in da bikin ɗiyarta zai kammala. A yau dai ba ya jin zai iya komawa gidansa ba tare da ya je ya ga koda fuskarta ba don haka kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya haɗa ƴar jakarsa. Koda ya fito, yaronsa ya zo da sauri ya karɓi jakar zuwa mota. Shi kuwa ya ƙara yin sallama da abokan aikinsa suna ƙara taya shi murnar wannan nasara da ya yi a yau ɗin. 


 A gidan kamar yanda ya tsammata, hakan ce ta faru. Rikici irin na Rahma har bai san yaushe zai ƙare ba. Zaune ya iske ta a falonsa sai cin magani take tana kumburi, bai ce mata uffan ba ganin ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba kai tsaye ya shige ɗakinsa. Sai da ya fara rage kaya ya yi wanka ya fito ya tarar ta shigo tayi zaune bakin gado tana girgiza ƙafafu. Kallo ɗaya ya bi ta da shi ya nufi sif ya fiddo jallabiya. 


"Wai Dawud ba za ka cemin komai ba kake nufi?"


Ransa na ɗaci amma bai yi magana ba, daidai da miskilancin nan, Khaleefa ya ɗauka a wurin Baban. 


"Wallahi Dawud ba na son wulakancin da ka ke yimin, kuma ka bayar da fuska yan uwanka ke neman tozarta ni, suna nema su kashe min yarinya su jefa ni cikin tashin hankali da masifu!"


Sai a sannan ya dube ta.


"Fitarmin a ɗaki Rahma tun ba ki kai ga ɓatan rai ba."


Mamin Khaleefa ta shaƙa iyaka, sai kawai ta shiga kuka. 


"Eh dama haka za ka ce Dawud, wai ni yarinyar nan ba jininka ba ce ne? Kana ji kana gani rayuwarta na nema ta salwanta amma ka zuba ido ba ka ce komai ba? Shi Sadaukin ba mijin mace huɗu ba ne? Don me za ka kasa roƙon alfarma akan ya aure ta su zauna tare da matar so ɗin tasa?"


Duk yanda ya kai da ɓacin ran sai da ya ɗan ji babu dadi, a duniyar idan da abin da ya tsana bai wuce ya ga mace na kuka ba don haka ya kama hannunta suka zauna gefen gado. 


"Share hawayen, ya isa hakanan, nutsu ki saurare ni dakyau."


Ba musu ta bi umarninsa, ita yanzu ai babu abin da ba za ta iya aikatawa ba muddin ɗiyarta za ta samu abin da take so. Akan farin cikin yaranta za ta iya koma mene ne. 


"Rahma, shi auren nan da kike ganinsa, nufin Allah ne. Wannan koke-koke da kwanciya ciwo da Jannat ke yi, ba shi zai sa ta auri Abeed ba. Na kira ta na mata faɗa, kenan duk abin da nace mata ta bayan kunnenta ya bi? Ta sanya ƙafafunta ta shure? Ai babu abin da za ka same shi ta ƙarfi, da ace namiji ne ma ke son, ana iya cewa ƙila a gaba zai iya siye zuciyar matar ta haƙura su rayu tare. Amma fa ni ba zan kai Jannat inda ba'a sonta ba duk da cewa ina yiwa yaron kyakkyawan zato ba zai bari ya cuci ƴarmu ba, sai.."


"Sai me? Me kuma ya yi saura da ba ki faɗi ba Dawud? Fito a mutum kawai ka ce ba za ka iya samarwa ƴarka cikar burinta ba. Shikenan, muje a hakan, ni kuma yanzu na fara faɗi tashi akan yarana!" 


Tana kai wa nan ta fice fuu kamar za ta tashi sama. 


***

 Ta ɗaga hannu ta wanke fuskar ɗan nata da lafiyayyen mari. Fuskarta kaca-kaca da ruwan hawaye ta nuna Zaid da yatsa. 


"Kai ashe marar hankali da tunani ne ban sani ba? Zaidu akan mace za ka dubi tsakar idanun iyayena ka ci musu mutunci?! Da wane idanun zan dubi Baba Alhaji?"


Kawai sai ta saka salati ta koma mazauninta tana fitar da ƙwalla. Zaid wanda ke daga tsaye don shigowarsa ko zama bai yi ba ya yi karo da tsarabar mari daga Malama. Ya durƙusa jikinsa a matuƙar sanyaye ganin irin hawayen da mahaifiyarsa ke fitarwa a kansa, Bebi autarta dake gefe kuka kawai take yi ganin haka Juwairiyya ta ja hannunta zuwa ɗaki. 


"Ki yi haku..."


"Haƙuri na me? Me ka yi min? Rayuwar da ka zaɓarwa kanka kenan akan soyayyar mace, ka yi duk yanda ka so Zaidu. Amma ina maka rantsuwa ko bayan raina ka auri Haulatu ban yafe maka ba! Shashasha marar tawakkali. Iliminka ya tashi a banza kenan! Ai alhaki kwuikwuiyo ne, da ace ba ka da saurin mantuwa, da ka tuna alhakin Zaituna ke cinka a yanzu. Kuma a gobe ka tattara ka koma Abuja. Ban yafe maka ba idan koda wasa ka cutar da Matarka."


Tana kaiwa nan ta miƙe  a fusace da zummar wucewa ɗaki sai dai ba ta ko yi taku biyar ba ta zube a wajen. A gigice ya kira sunanta.


"Umma!" Kafin ya yi wurinta yana salati, hakan ya yi sanadiyyar shigowar samarin ƙannen Zaid din. Nan da nan ya miƙawa mai bi masa muƙulli akan ya kunna mota, shi kuwa ya cicciɓi Malama ganin ya zuba ruwa amma ba ta farfado ba suka fita. Gaba daya suka shiga motar, Juwairiyya da Bebi ya ce su zauna a gida bayan Al'amin dake gefe ya karɓi hijabinta da Juwairiyya ta kawo. 


Kai tsaye asibitin Baba Dakta suka nufa, ba ya nan sai Khaleefa suka iske tare da wata Dr Aisha. Nurses suka karɓi Malama da gaggawa a ka shiga da ita ɗakin duba marar lafiya. An yi sa'a bayan dabaru na likitoci ta farfaɗo daga doguwar suman da ta yi.  A ƙarshe dai bincikensu ya tabbata da jininta ne ya ɗan hau dalilin damuwa da ɓacin ran da ta shiga. Abin sosai ya motsa zuƙatan yaran tunda ba su taɓa sanin mahaifiyartasu da hawan jini ba. Ƙannen suka dinga jin zafin Zaid har suna ɗaure masa fuska don sun sani silarsa ne komai ya faru.  Shi kuwa wata irin nadama sosai ta shige shi, jikinsa ya yi sanyi. Malama kuwa ta dage akan ba za ta kwana asibiti ba dole suka sallame ta bayan ba da shawarwarin a kara kula sosai. Khaleefa har mota ya rako su yana kara yi mata sannu. Sai da suka tafi sannan ya koma bakin aikinsa. 


Daren ranar Zaid bai iya bacci ba, ya dinga nafila da addu'o'i kan Allah ya cire masa wannan soyayyar da ke wahalar da shi da ma makusantansa. Har ya yi sallar asubahi bai runtsa ba, yana idarwa kuma ya haɗa ƙaramar jakarsa ya shiga suka yi sallama da Malama wacce a farko kallonsa ma ba ta yarda ta yi ba. Sai da ya dinga magiya da neman gafara tare da alƙawarin daga ranar yau ba za ta ƙara jin makamancin haka a kansa ba. Ya haƙura da Haulatu, a nan ne ta iya dubansa har ramar da ya yi ta ba ta tausayi. 


"Na yafemaka, Allah ya yi albarka. Ka yi ta addu'a sannan ka ji tsoron Allah gun sauke haƙƙoƙin da ya rataya a wuyanka na matarka. Allah ya tsare ya kai ka lafiya."


Har wata ajiyar zuciya ya saki na samun sa'ida. Ya jinjina kai.


"Ameen Umma, in sha Allahu na maki alƙawarin kiyayewa. Allah ya ƙaramaki lafiya."


Da haka ya miƙe ta bi shi da kallo har sai da kwalla suka cicciko mata. Addu'ar neman sauƙi da rangwame daga Allah ta ɗaga hannu ta shiga yi wa ɗan nata. 


***

Kano...


"A yau rana ta Alhamis ne, sha biyu ga watan Junairu, jami'an tsaro suka cafke wata jamshaƙiyar mace mai suna Hajiya Adama Loma, wacce ta kwashi tsawon shekaru tana harkar safarar yara da miyagun ƙwayoyi, wanda a ƙarshe ƙungiyar nan mai yaƙi da safarar mata da yara wato Naptip ta yi nasarar kuɓutar da ƴanmata masu ƙananun shekaru sha biyar zuwa ashirin da ake ƙoƙarin fitar da su ta ɓarauniyar hanya ta Nijar. Ɗaya daga cikin yaran tana kuka ta shaidawa manema labarai cewa ita ƙanin babanta ne ya kawo ta har gidan Hajiyar inda suka yi cinikinta kamar wata dabba, aka cika masa lalitarsa ya yi gaba ya bar ta. Wata kuwa, cewa ta yi dama da niyyar karuwanci ta fito daga gidansu, a cewarta iyayenta ne suka hana ta saurayin da ta ke so."


Girgiza kai kawai Hindatu ke yi tana salati, tana daga ɗaki amma duk wannan labaran da ake watsawa a rediyon da makwafciyarsu ta kunna babu ɗaya da bai shiga kunnuwanta ba. Tabbas ta san wace ce Hajiya Adama Loma, ta kuma sha ganinta ta hanyar tsohon mijinta Ɗan Mutuwa. Godiya ta ƙara yiwa Allah da ya kuɓutar da ita daga cikinsu ba tare da sun yi nasarar gurɓata rayuwarta ba. Har aka ƙare labaran ba ta ji an sako muryar Hajiya Adama ba don a cewar ɗan jaridar ta ƙi yarda a yi hira da ita. Shigowar makwafciyar tasu ce da zummar yi mata wanka irin na jego ya katse tunaninta. Sunanta Asabe amma mace ce mai kirki kuma ba wata babba ce ba sosai. Tun zuwan Hindatu gidan ita ke ɗawainiyar kula da ita hatta abinci idan ta dafa sai ta zubamata. Momi har lokacin ba su dawo ba, ta kuma ji dukkan abin da ya faru amma sam ta nunawa Hindatun ba ta yarda ba sharri ne ta ke wa Ɗan Mutuwa don kawai tana so ta rabu da shi. Don ɓacin rai ma ba ta ƙara bari sun yi magana ba ko Momin ta mata a whatsapp ba ta amsawa. Babban burinta jikinta ya ƙara kyau ta tafi wajen mahaifinta. 


***

Su uku ke tsaye a falon, Maada, Ɗan Aljan da Duuna, kowannensu na busa karan sigari, Ɗan Mutuwa sun kai shi asibiti sun ajiye, Maada ya yi amfani da akwatin kuɗin da Ɗan Mutuwan ke yawo da shi a mota ya biya kudin gado da na magunguna daga haka suka fito a cewarsu za su je su dawo. 


"Ni fa kawai mu kwashe abin da za mu kwasa mu samfe kawai. Wannan garan ba tashi zai yi ba, idan ma ya tashi ba wani abun arziƙi za mu yaga a jikinsa ba. Ko ya kuka gani?"


Ɗan Aljan ke wannan kalamin yana dubansu. Wata dariya Duuna ya yi.


"Daɗina da kai akwai ja sosai. Kamar ka san tunanin da nake yi kenan. Ya dace mu yiwa kanmu gyaɗar dogo mu kwashi ganima mu yanka gabas."


Maada dake sauraronsu ya yi murmushi. Dama tunaninsa kenan sai aka yi sa'a nasa da abokansa ya zo ɗaya. Nan suka tsaida shawarar farawa da korar ma'aikatan sannan su yiwa gidan kankat a cikin daren nan su fice da komai su siyar. Da wannan kuwa suka yi nasarar sallamar duka ma'aikatan da cewa umarnin Maigidan ne. Su dai babu abin da ya sha musu kai tunda an musu kyakkyawar sallama don sif guda cike yake da kudade a dakin Ɗan Mutuwa.

A wannan daren suka nemo babbar motar da ta yi musu lodin kaya, babu wani abu da suka bari kama daga kayayyakin sanyawa har kayan furnitures da sauran tarkace. Hindatu dama tun sadda za ta bar gidan ta kwashe komai nata mai muhimmanci don ta saka a rai cewa ta gama aure a gidan, lefenta ba ta ɗauki ko tsinke a ciki ba, haka suka kwashe dukkan komai suna jin dadin wannan arziƙi da suka yi a dare guda. Takardun gidan suka nema ba su samu ba, ko kuma ace sun gani amma ba su san shi ne ba, tunda cikinsu kaf babu mai ilimin bokon balle ya karanta, dama-dama ma Ɗan Aljan, shi har sakandire ya fara zuwa kafin shaye-shaye da bin ɓata garin abokai ya lalata masa rayuwa. 


Motar har ta yiwa kayan kaɗan don dma farfajiyar gidan suka shigo da ita, daga nan suka yanke cewa Ɗan Aljan da direban su soma yin gaba su kai ma'adana su ɓoye waɗannan ɗin sannan su dawo a kwashe sauran. Da haka suka fice aka bar Maada da Duuna na zaman jira. Sai dai kuma har asubahi ta kawo kai babu su babu labarinsu. Wayar Ɗan Aljan ma a kashe, hankalinsu ya tashi. Duuna ya ƙunduma ashariya ya bugi katakon kujera.


"Kada dai ace wannan saunan yaudararmu ya yi ya gudu?"


Maada dake aikin cigaba da dannawa Ɗan Aljan ɗin kira ya koma ga direban, amma ina kowannensu wayar a kashe. Nan da nan suka ƙulle ƙaton ƙyauren gidan suka mara musu baya a ɗaya daga cikin motocin Ɗan Mutuwa, dama tuni sun yi cinikin sauran biyar ɗin tun da haske a gari suka fice da su ɗaya bayan ɗaya, kudaden aka zuba a asusun Maada tunda shi ne Ogansu. Ma'ajiyarsu babu Ɗan Aljan ba dalilinsa. Suka koma har inda direban ke parking ɗin ƙurƙurarsa. Nan ma aka ce ai yana asibiti, can aka tsince shi a gefen titi jikinsa duk sara. Suka kuwa iske shi yana kuka yake roƙon su masa aikin gafara Ɗan Aljan ne ya ce ya yi parking daga nan ya nemi ya fita a motar, gardamar da ya yi ce ta sanya ya sassare shi a jiki. Wannan maganar sam ba ta yi musu dadi ba. Haka suka fice kowannensu na cin alwashin irin kisan da zai yiwa Ɗan Aljan tunda har ya ci amanarsu. Nan da nan suka dinga kiran duka abokan dabarsu da suka sani a wuri-wuri kan cewa duk wanda ya ci karo da Ɗan Aljan ya shaida musu. Daga nan suka koma gidan Ɗan Mutuwa don jira dare ya yi su kwashe abin da ya rage. Sai dai a wannan ranar jami'an tsaro na yaƙi da miyagun ƙwayoyi suka mamaye gidan don kama Ɗan Mutuwa wanda Hajiya Adama ta ce bakinsu ɗaya tare suke aikata dukkan munanan ayyuka. Maada da Duuna ba su tsira ba, haka aka kwashe su, babban jami'in cikinsu da wasu yaran suka nufi asibitin da su Maada suka ce Ɗan Mutuwa na can yana jinya.


***

 Katsina...


 A wannan daren dai duk yanda Sadauki ya so ganin Haulatu hakan bai samu ba dalilin neman da Daddy ke masa akan zancen lefe da ma shirin biki wanda daƙyar suka roƙi Baba Dakta ya amince  ya maida nan da wata biyu, sati takwas kenan. Koda ya fito dare ya riga ya yi don haka kawai sai waya suka ɗan yi ba wata doguwa ba suka yi sallama.


A gefen su Hajja kuwa jin biki wata biyu ya sa ta shiga hada-hadar gyara Haulatu hakan ya sanya ta neman layin Maama, bayan sun gaisa ta ke shaida mata batun auren. Maama ta yi dariya. 


"Na ji labarin komai Hajja, ai Alhamdulillah sai fatan kawai Allah ya nunamana."


Hajja ta washe haƙora.


"Amin amin Zakiyya. Sai ki tasarwa shirya ɗiyartaki."


Dariya karo na biyu Maama ta yi.


"Ah wannan kam ai dolena ne. Zan yiwa Ummu Deedat waya, duk radda take da lokaci zan ce ta leƙo gidana, idan mun kammala magana sai na yi magana da Haulatun. Amma fa aronta za ki bani Hajja na ƴan satika."


"Ai ko na wata ne Zakiyya ba ki da matsala idan jikata za ta fito ras da biki."


Suka yi dariya da yiwa juna fatan ganin lokacin sannan suka yi sallama. 


***

 Barr Dawud ne zaune a chamber ɗinsu na lauyoyi, bai jima da fitowa a kotu ba inda ya kare wani maraya da ake zargin shi ya kashe iyayensa ƙarshe gaskiya ta bayyana cewa Yayan mahaifinnasa ne ya kashe shi. Yau aka yanke hukuncin shari'ar aka kama masu laifi. Zuciyarsa cike da farin ciki na wannan nasara amma damuwar da ya shiga a ɓangare guda ya hana shi bayyana wannan murna gaba daya. Ya gama fahimtar kansa a kwanakin nan, shi ba yaro ba balle ace ya kasa gane kauna ce da soyayya ta aure ya ke yiwa Na'imatun Hajja. Kamalarta, haƙurinta kai har ma da kyawun halittar da Allah ya yi mata, su ne suka haifar da wannan son nata da yake ji. Ba ya jin kuma zai yi shiru, zai gwada sa'arsa tunda su ɗin ba yara bane. Zai yi dai ƙoƙari ya danne zuwa sa'in da bikin ɗiyarta zai kammala. A yau dai ba ya jin zai iya komawa gidansa ba tare da ya je ya ga koda fuskarta ba don haka kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya haɗa ƴar jakarsa. Koda ya fito, yaronsa ya zo da sauri ya karɓi jakar zuwa mota. Shi kuwa ya ƙara yin sallama da abokan aikinsa suna ƙara taya shi murnar wannan nasara da ya yi a yau ɗin. 


 A gidan kamar yanda ya tsammata, hakan ce ta faru. Rikici irin na Rahma har bai san yaushe zai ƙare ba. Zaune ya iske ta a falonsa sai cin magani take tana kumburi, bai ce mata uffan ba ganin ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba kai tsaye ya shige ɗakinsa. Sai da ya fara rage kaya ya yi wanka ya fito ya tarar ta shigo tayi zaune bakin gado tana girgiza ƙafafu. Kallo ɗaya ya bi ta da shi ya nufi sif ya fiddo jallabiya. 


"Wai Dawud ba za ka cemin komai ba kake nufi?"


Ransa na ɗaci amma bai yi magana ba, daidai da miskilancin nan, Khaleefa ya ɗauka a wurin Baban. 


"Wallahi Dawud ba na son wulakancin da ka ke yimin, kuma ka bayar da fuska yan uwanka ke neman tozarta ni, suna nema su kashe min yarinya su jefa ni cikin tashin hankali da masifu!"


Sai a sannan ya dube ta.


"Fitarmin a ɗaki Rahma tun ba ki kai ga ɓatan rai ba."


Mamin Khaleefa ta shaƙa iyaka, sai kawai ta shiga kuka. 


"Eh dama haka za ka ce Dawud, wai ni yarinyar nan ba jininka ba ce ne? Kana ji kana gani rayuwarta na nema ta salwanta amma ka zuba ido ba ka ce komai ba? Shi Sadaukin ba mijin mace huɗu ba ne? Don me za ka kasa roƙon alfarma akan ya aure ta su zauna tare da matar so ɗin tasa?"


Duk yanda ya kai da ɓacin ran sai da ya ɗan ji babu dadi, a duniyar idan da abin da ya tsana bai wuce ya ga mace na kuka ba don haka ya kama hannunta suka zauna gefen gado. 


"Share hawayen, ya isa hakanan, nutsu ki saurare ni dakyau."


Ba musu ta bi umarninsa, ita yanzu ai babu abin da ba za ta iya aikatawa ba muddin ɗiyarta za ta samu abin da take so. Akan farin cikin yaranta za ta iya koma mene ne. 


"Rahma, shi auren nan da kike ganinsa, nufin Allah ne. Wannan koke-koke da kwanciya ciwo da Jannat ke yi, ba shi zai sa ta auri Abeed ba. Na kira ta na mata faɗa, kenan duk abin da nace mata ta bayan kunnenta ya bi? Ta sanya ƙafafunta ta shure? Ai babu abin da za ka same shi ta ƙarfi, da ace namiji ne ma ke son, ana iya cewa ƙila a gaba zai iya siye zuciyar matar ta haƙura su rayu tare. Amma fa ni ba zan kai Jannat inda ba'a sonta ba duk da cewa ina yiwa yaron kyakkyawan zato ba zai bari ya cuci ƴarmu ba, sai.."


"Sai me? Me kuma ya yi saura da ba ki faɗi ba Dawud? Fito a mutum kawai ka ce ba za ka iya samarwa ƴarka cikar burinta ba. Shikenan, muje a hakan, ni kuma yanzu na fara faɗi tashi akan yarana!" 


Tana kai wa nan ta fice fuu kamar za ta tashi sama. 


***

 Ta ɗaga hannu ta wanke fuskar ɗan nata da lafiyayyen mari. Fuskarta kaca-kaca da ruwan hawaye ta nuna Zaid da yatsa. 


"Kai ashe marar hankali da tunani ne ban sani ba? Zaidu akan mace za ka dubi tsakar idanun iyayena ka ci musu mutunci?! Da wane idanun zan dubi Baba Alhaji?"


Kawai sai ta saka salati ta koma mazauninta tana fitar da ƙwalla. Zaid wanda ke daga tsaye don shigowarsa ko zama bai yi ba ya yi karo da tsarabar mari daga Malama. Ya durƙusa jikinsa a matuƙar sanyaye ganin irin hawayen da mahaifiyarsa ke fitarwa a kansa, Bebi autarta dake gefe kuka kawai take yi ganin haka Juwairiyya ta ja hannunta zuwa ɗaki. 


"Ki yi haku..."


"Haƙuri na me? Me ka yi min? Rayuwar da ka zaɓarwa kanka kenan akan soyayyar mace, ka yi duk yanda ka so Zaidu. Amma ina maka rantsuwa ko bayan raina ka auri Haulatu ban yafe maka ba! Shashasha marar tawakkali. Iliminka ya tashi a banza kenan! Ai alhaki kwuikwuiyo ne, da ace ba ka da saurin mantuwa, da ka tuna alhakin Zaituna ke cinka a yanzu. Kuma a gobe ka tattara ka koma Abuja. Ban yafe maka ba idan koda wasa ka cutar da Matarka."


Tana kaiwa nan ta miƙe  a fusace da zummar wucewa ɗaki sai dai ba ta ko yi taku biyar ba ta zube a wajen. A gigice ya kira sunanta.


"Umma!" Kafin ya yi wurinta yana salati, hakan ya yi sanadiyyar shigowar samarin ƙannen Zaid din. Nan da nan ya miƙawa mai bi masa muƙulli akan ya kunna mota, shi kuwa ya cicciɓi Malama ganin ya zuba ruwa amma ba ta farfado ba suka fita. Gaba daya suka shiga motar, Juwairiyya da Bebi ya ce su zauna a gida bayan Al'amin dake gefe ya karɓi hijabinta da Juwairiyya ta kawo. 


Kai tsaye asibitin Baba Dakta suka nufa, ba ya nan sai Khaleefa suka iske tare da wata Dr Aisha. Nurses suka karɓi Malama da gaggawa a ka shiga da ita ɗakin duba marar lafiya. An yi sa'a bayan dabaru na likitoci ta farfaɗo daga doguwar suman da ta yi.  A ƙarshe dai bincikensu ya tabbata da jininta ne ya ɗan hau dalilin damuwa da ɓacin ran da ta shiga. Abin sosai ya motsa zuƙatan yaran tunda ba su taɓa sanin mahaifiyartasu da hawan jini ba. Ƙannen suka dinga jin zafin Zaid har suna ɗaure masa fuska don sun sani silarsa ne komai ya faru.  Shi kuwa wata irin nadama sosai ta shige shi, jikinsa ya yi sanyi. Malama kuwa ta dage akan ba za ta kwana asibiti ba dole suka sallame ta bayan ba da shawarwarin a kara kula sosai. Khaleefa har mota ya rako su yana kara yi mata sannu. Sai da suka tafi sannan ya koma bakin aikinsa. 


Daren ranar Zaid bai iya bacci ba, ya dinga nafila da addu'o'i kan Allah ya cire masa wannan soyayyar da ke wahalar da shi da ma makusantansa. Har ya yi sallar asubahi bai runtsa ba, yana idarwa kuma ya haɗa ƙaramar jakarsa ya shiga suka yi sallama da Malama wacce a farko kallonsa ma ba ta yarda ta yi ba. Sai da ya dinga magiya da neman gafara tare da alƙawarin daga ranar yau ba za ta ƙara jin makamancin haka a kansa ba. Ya haƙura da Haulatu, a nan ne ta iya dubansa har ramar da ya yi ta ba ta tausayi. 


"Na yafemaka, Allah ya yi albarka. Ka yi ta addu'a sannan ka ji tsoron Allah gun sauke haƙƙoƙin da ya rataya a wuyanka na matarka. Allah ya tsare ya kai ka lafiya."


Har wata ajiyar zuciya ya saki na samun sa'ida. Ya jinjina kai.


"Ameen Umma, in sha Allahu na maki alƙawarin kiyayewa. Allah ya ƙaramaki lafiya."


Da haka ya miƙe ta bi shi da kallo har sai da kwalla suka cicciko mata. Addu'ar neman sauƙi da rangwame daga Allah ta ɗaga hannu ta shiga yi wa ɗan nata. 


***

Haulatu ta karanta saƙon sau kusan uku tana mamaki wai daga Mu'az ya fito. Fatan alheri ne ya ke mata akan aure sai kuma addu'ar Allah ya sa gidanta. Sai ko gafararta da ya nema bisa abubuwan da ya yi a baya. Kamar ba za ta maida masa amsa ba sai kuma ta daure ta aikamasa da cewa komai ya wuce, shi ma ta bisa da fatan alheri. 


A sadd ta ba shi amsa, tana tsaye a harabar gidan tana jiran Gali da ya zagaya ya zo ya sauke ta a gidan Maama. Ƙaramar jakarta na kaya yana gefenta. Ba ta ji motsin tafiya ba sai dai jin da ta yi an saka hannu a hankali an zare wayar da take sarrafawa. Tuni ta riga da ta aikawa Mu'az saƙo har ta shiga whatsapp duba saƙonnin group dinsu su uku, ita da Radiya da Safina tana ta zuba murmushin tsokanar da suke yi mata. Da sauri ta juya don ta ga waye, suka yi idanu huɗu da Sadauki yana ɗan murmushi. Fatarsa ta yi wani fresh da kyau, sumar kansa ya sha gyara ga dukkan alamu aski ya yi, hakanan gefen fuskarsa zuwa ɗan gemun da ya zagaye bakinsa. Gashinsa baƙi wuluk mai taushi sai ya ƙara fiddo da zallar haibarsa. Yadi ne baƙi a jikinsa wanda aka yi wa ƙaramin aiki a gaba. Ita kanta ba ta san sadda ta zuba masa idanu da murmushin da ya fito tun daga zuciyarta. 


"Ka fa tsorata ni."


Ta furta kamar mai shirin yin kuka. Ya shafi gefen sumarsa gami da kallon sararin samaniya yanda haɗu da hadari kafin ya maido dubansa inda ya fi gareta.


"Na faɗamaki ki adana min wannan shagwaɓar taki, na siye ta zuwa lokacin da zan soma cin moriyarta."


Sai kunya ta kama ta, ba ta manta sadda ta taɓa shagwaɓe murya a waya sai da ya ɗauke wuta na lokacin kafin cikin wani muryar da ba su saba magana ba ya hau roƙonta akan kar ta ƙara, ta bari sai sun yi aure. 


"Muje ni zan kai ki."


Sai a sannan ta ɗan ɗago kai.


"Malam Gali fa aka ce..."


"Na aike shi, daga yanzu ma duk inda za ki je matuƙar ba wani aikin nake ba ki yimin magana, ni da kaina zan zama direbanki."


Ta yi murmushi. Ya sa hannu ya dauki jakar kayanta suna tafe ita kuwa riƙe da ƙaramar jaka, haka suka ƙarasa har waje inda ya bar motarsa, ta shagala kallonsa ganin ya buɗemata gidan gaba da kansa, shiga ta yi sannan ya sanya jakar a kujerar baya ya zagaya ya shiga ya ja su. 


"Wai ma tsaya, wane gyara za'a yi maki a gidan Maama?" 


Ta ji tambayar bagatatan, ɗan turo baki ta yi. 


"Nima ban sani ba."


Shi kuwa ya taɓe baki kafin ya yi wani ƙaramin dariya ciki ciki yana kallon hanya. 


"Baby."


Ta juyo ta dube shi.


"Na'am."


"Allah ya yi maki tarin baiwa ne mai fisgar hankali masha Allah, a haka ma ya na ƙare? Ballantana idan kin ƙara kyawun da ya zarce wannan? Anya ba so ki ke ki kwace wannan gurbin na sauran ukun da zan ƙara a gaba ba?"


Tuni ɗan murmushin da ta soma ya koma ciki. Ta ɗan harare shi, ya san za'a yi haka dalili kenan da ko kallonta bai yi gaba ɗaya ba sai ta gefen ido. 


"Kamar ya za ka ƙara uku? Me ɗin?"


Ya haɗiye dariyar da ke cinsa. Da yatsu ya yi mata nuni da huɗu. 


"Ni fa mijin mata huɗu ne, haka addini ya halasta min idan har zan yi adalci, kin ga kuwa..."


"Yaya Sadauki, tsaya a nan zan sauka. Na fasa zuwa gidan Maaman."


Ya ɗan zaro idanu kadan gami da ɗan kallonta. 


"What? Kin fasa me? A ina? Oh, bakya so a gyaramin ke? Yau kuma sunan da ban so ki ka faɗi?"


Ta harare shi ta kauda kai, sai kumbura fuskar take kana kallonta ka san kishin ya motsa. Har wata ƴar kwalla ce ta cika idanunta. Ba ta ƙara tankawa ba shi ma bai ce mata uffan ba don ya sani tsokanarsa ba za ta ƙare ba, hakanan zai yi ta sanya ta ɓacin rai dalilin shirun kenan kar ya jawo ruwa. Har suka isa gidan Maama babu wanda ya cewa ɗan uwansa kanzil. 


Ba ta ko jira ya daidaita parking ba bayan sun shiga gate, ta buɗe murfin motar ta fice. Sai a sannan ya yi dariyarsa kafin ya fito ya ɗauki jakar kayanta da ta bari ya rufe motar yana amsa gaisuwar ma'aikatan gidan, har wani ya zo da zummar karɓar jakar ya girgiza masa kai. 


"No, bar shi kawai."Haulatu tana shiga da sallamarta, ƴar aikin Maama mai suna Bintalo ta amsa. Ganin Haulatu ta washe haƙora.


 "Lah Anti Haula, sannu da zuwa."


"Yauwa Bintalo, ina Maama?"


Kafin ta amsa sai ga Maama na fitowa daga kicin, sakin fuskarta ta yi ta dube ta.


 "Har kin iso kenan?" 


Ta ƙarasa gami da ɗan rungume Maama tana murmushi.


 "Eh Maama." Maama ta kamo yatsunta tana ƙare mata kallo kafin ta ce.


"Masha Allah, ke kam wannan yanayin na damina ya karɓeki, sai na ga kin ƙara haske abinki." 


Sallamar Sadauki ta sanya Maama sakin baki, duban ƙofar ta yi tana mai amsa sallama.


"Ikon Allah, wai kai ne ka kawo ta? To ƙaraso."


Ita dai Haulatu tun da ta ji muryarsa ta tura baki ta wuce Maama ta shiga cikin falon ta zauna a kujera mai zaman mutum biyu. 


"Maimakom ka yi magana a zo a ɗauki jakar Sadauki?" Faɗin Maama ita ma su na ƙarasowa cikin falon. Gefen Haulatu ya zauna gami da ajiye jakar yana murmushi.


"Maama komai fa take so ina gwada maki ne zan iya yi ga ɗiyarki. Ki taya ni ba ta haƙuri fushi ta ke da ni."


Ita Haulatu duk sai ya sa ta ma jin nauyin Maama, duk sai ta daburce ta fiddo idanu waje. 


"Waye ke fushin? Ni na mance ma da jakar fa shiyasa ban ɗauko ba"


Diramar sai ta ba Maama dariya don haka ta murmusa. 


"Taso ki dawo nan ki zauna, ni na san halin kayana, wataƙila wata tsokanar ya yi maki."


Ba musu kuwa ta miƙe shi kuwa ya danne gefen mayafinta da yatsun hannunsa ai kuwa ta ja da ƙarfi har tana shirin faɗuwa, harararsa ta ƙara yi kafin ta koma kusa da Maama ta bar shi da bin ta da kallo yana murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa. 


Bintalo tuni ta kawo musu ruwa da lemo bisa umarnin Maama. A sannan Maama ke tambayar Haulatun abin da ya haɗo su, ita kuwa ta yi shiru, ganin haka ya cafe zancen. 


"Wai Maama daga fa na ce mata duk gyaran nan nata so take a yi mata gyaran da zan fasa auren mata huɗun da na yi niyya shi..."


Tuni ya katse sakamakon tashin da Haulatu ta yi da gudunta ta yi hanyar ɗaki, Maama kuwa salati ta yi shi ko sumar kansa kawai ya shafa yana murmushi kai a ƙasa bai ce uffan ba. 


"Sadaukin Alhaji? To ba da ni ba, maza maza tashi ka fice ka ba mu wuri. Kuma ka sani babu gurbin kowace mace a gidanka bayan ɗiyarmu, au kishiya tun ba ta shiga ba? To ai kuwa zan zuga ta a fasa."


Ai sai dariyar da yake yi ta dauke, nan ya hau ban haƙuri, Maama ta ce shikenan. Koda ya miƙe ma dakatar da shi ta yi kan ya tsaya ya ci abinci tukunna. Ba musu kuwa ya koma mazauninsa don dama ya sani fushin Maama a kansa ba ya zuwa ko'ina. 


Ita da kanta ta shiga ɗakin ta lallaɓo Haulatu kan ta fito, dolenta ta fito amma ko inda yake ba ta kalla ba sai faman cin magani ta ke. Maama ta yi kicin, za ta mara mata baya ya yi saurin mikewa ya tare hanya. Ta dube shi, sai kuma ta kauda kai ganin yanda duk ya wani marairaice. 


"Baby, duk wannan so ne ko? Yi hakuri, tsokanarki fa nake."


Ta turo baki. 


"Tsokana da zancen kishiyoyi?"

 

Ya murmusa yana ɗan leƙa fuskarta.


"Na tuba. Ba ni da gurbin kowacce mace a zuciyata, ina da kyakkyawan zato a kanki, ba za ki ban wannan damar ba. Kuma in sha Allah ba zai zamo a cikin ƙaddarorina ba."


 Ta yi murmushi tana ɗan matse leɓɓanta gami da kallonsa ita ma. Ido guda ya kashe mata. 


"Ko ke fa."


"Idan kun gama shirin naku, muje ku ci abincin."


Suka juya a tare, Maama ce daga ƙofar kicin hannunta ɗauke da warmer yayinda Bintalo ke daga gefe ita ma tana wangale baki don sun burgeta ita kanta. 


Kunya ta kama Haulatu, shi kuwa waskewa ya yi, ita ko da sauri ta karasa gami da karɓar kayan hannun Maama. 


Ranar dai sai kusan isha ya bar gidan don har sai da mijin Maama ya shigo suka gaisa ya tafi lokacin ma tuni ruwa ya sauka. Haulatu ce ta raka shi har motar da lema ƙatuwa, sai da ya buɗe murfin zai shiga ita kuwa ta ɗan ja baya sakamakon kusancin da suka samu tsakani don a ƙoƙarinta na tare mishi dukan ruwa, ya sani koda ya yi magana ba ji za ta yi ba dalilin ƙarar ruwa don haka kawai ya shige motar ya rufe, ita kuwa ta koma ciki da gudu-gudu. 


***

 Tun da Haulatu ta je gidan Maama take kwasar darussa kala-kala, tun daga kula da miji, da yanda ake murmushi da dariya a gabansa, tarairaiya da kissa da ma girkuna wadanda ta ƙara gogar da ita a fannin. Sai ko magungunan da ta soma ba ta na sanyi sai ko na mata da ta san ba za su takura mata ba. Idan ka ga ta fita waje, to fa makaranta ce kawai za ta je. Nan ma Maama niƙaf ta siyo mata ta dinga sanyawa har da safa. Tsakaninta da su Umma da Hajja sai waya.

  Ta kula har lefe Maama da Amarya (matar baban Mu'az) su ke ta shiryawa, Momi Nuratu ta bar komai a hannunsu, ba ta ga ko kyallin kayan ba, Maama ce dai ta nemi sanin size din undies dinta. Sadauki bai ƙara tako gidan ba bisa umarnin Maama, dole ya haƙura sai dai su yi waya. 


 Ranar da ta cika sati uku da kwana ɗaya a gidan Maama ne, su na zaune su na hira zuciyarta tas don jin dadin zuwan da Anti Zaituna za ta yi a satin, ita kaɗai za ta zo ƴan gidan su sai dab da biki.


 Maama ta yi shiru tana duban Haulatun da hankalinta ke kan waya a sannan, ba ta son ko kusa Haulatun ta yi wa zancen mummunan fahimta. Ta samu labari ne kan cewa  Mamin Jannat ta samu Momi Nuratu akan ya kamata su yi gwajin cutar hiv kafin a kai ga auren don wai ba a da tabbas tunda a bariki suka zauna a Kano. Wannan batu ya ɗaga hankalin Momi Nuratu, ba don ta yarda ba amma sai ta tsorata sam ba ta yi la'akari da cewa komai Mamin Khaleefan za ta iya faɗi a lokacin don a fasa auren ba. Da hankalinta ya ƙi kwanciya ne ya sa dole ta kira wayar Maama ta yi mata bayanin yanda suka yi da Mamin Khaleefa. Ta kuma nuna mata kawai don zuciya ta samu nutsuwa ne. Maama ba ta ji dadin zancen ba sai dai ta ce babu komai za ta kai ta a gwada ta. 


Ajiyar zuciya ta saki ta dubi Haulatu.


"Ni kuwa kun yi gwajin genotype dinku ke de Sadaukin Alhaji?"


Maganar ya sa Haulatu kallon Maama. Girgiza kai ta yi.


"Aa, ba mu yi ba. Ni bai min ma zancen ba."


Ta kuwa samu dabara don haka ta sauke jinjina kai.


"Ai kuwa dai ya dace a yi. Zuwa yamma sai mu je wurin Khaleefa, shi ma Sadaukin zan mishi magana ya je."


Ta amsa da toh amma jikinta ya yi sanyi, idan ya kasance bai zo daidai da yana ake so ba fa? Shi ke nan ba za su auri juna ba? 


Maama na kula da ita ba ta ce mata uffan ba, ta riga ta san Sadauki AA ne, ta fi kaunar dai ya zamana ta aikata abin da zai sanya zuciyar Momi Nuratu nutsuwa. Sai da ta shiga ɗaki ta yi kira Sadaukin ta ba shi labarin komai. Ransa ya ɓaci da wannan abu na Mami sai dai kawai uzuri ɗaya da ya yi mata bai wuce saboda Barr Dawud ba da kuma Khaleefa da suke ganin mutuncin juna. 


"Kar ka damu da komai, ita ma Momin taka ba don ta gasƙata hakan ba ne, sai dai a yanayin da Hajiya Rahma ta yi batun ne ya jefa ta wasi-wasi, ka san ziga na tasiri a zuƙata."


"Shi ke nan Maama, zan zo in sha Allah."


"Yauwa ko kai fa."


*** 

 Cikin iko na Allah sakamako ya fita fes, Haulatu ba ta dauke da kowace irin cuta hakanan genotype dinta ya yi daidai da na Sadaukin wato AA. Ta kasa ɓoye farin cikinta, shi kansa murmushi ya ke dokawa har da yiwa ma'aikacin lab din da ya kawo sakamakon kyautar kuɗi ya bar Khaleefa da Maama da dariya. Sai a sannan ne ma ita Haulatun ta ji kunya ta rufe fuskarta. Maama kuwa duka sakamakon biyu ta karɓa ta damƙawa Sadauki. 


"Riƙe ka ajiye a wurinka, zamu yi waya."


Sai bayan sun rabu ta mishi text akan ya kai wa Momi Nuratu don hankalinta ya kwanta. 


***

  Khaleefa ne zaune ya je gaida Hajja yake sanar da ita batun zuwansa Kano a gobe don halartar ɗaurin auren abokin karatunsa. Ta taya shi murna sannan ta ce.


"Ka ga kuwa abun ya zo a daidai, gobe ne Zaituna za ta iso daga wancan ƙasar ta su ta larabawa, sai ka taho min da ita ba sai an sa Gali wahalar zuwa ba."


Ya ɗan yi jim, yarinyar da ba wani dogon hira ke shiga tsakaninsu ba? Shi kuma za'a tura ɗaukarta? Sai ya ji inama bai sanyo batun zuwansa Kano ba, da dai ya yi mata sallamar kawai ya fice. Umma da ta kula kamar hakan bai kwanta masa ba ta ce. 


"Ke kuwa Hajja, aiki za ki ba shi dai. Ki ka san ko ba shi kaɗai zai yi tafiyar ba?"


Jin haka ya yi saurin magana.


"Aa Umma, ni ɗaya zan je. Ba komai in sha Allahu zan taho da ita, jirgin ƙarfe nawa ne?"


Murmushi Umma ta yi.


"Ƙarfe huɗu na yamma za su sauka ta ce."


Ya jinjina kai.


"Ba damuwa, Allah ya nuna mana."


Hajja ta shiga sanya masa albarka. Da haka suka yi sallama Umma na bada sallahun ya gaida mata yaransa Affan da kuma bebinsu mai sunan Maminsa Rahma suke kiranta Ummi. 


***

 Kano...

Haulatu ta karanta saƙon sau kusan uku tana mamaki wai daga Mu'az ya fito. Fatan alheri ne ya ke mata akan aure sai kuma addu'ar Allah ya sa gidanta. Sai ko gafararta da ya nema bisa abubuwan da ya yi a baya. Kamar ba za ta maida masa amsa ba sai kuma ta daure ta aikamasa da cewa komai ya wuce, shi ma ta bisa da fatan alheri. 


A sadd ta ba shi amsa, tana tsaye a harabar gidan tana jiran Gali da ya zagaya ya zo ya sauke ta a gidan Maama. Ƙaramar jakarta na kaya yana gefenta. Ba ta ji motsin tafiya ba sai dai jin da ta yi an saka hannu a hankali an zare wayar da take sarrafawa. Tuni ta riga da ta aikawa Mu'az saƙo har ta shiga whatsapp duba saƙonnin group dinsu su uku, ita da Radiya da Safina tana ta zuba murmushin tsokanar da suke yi mata. Da sauri ta juya don ta ga waye, suka yi idanu huɗu da Sadauki yana ɗan murmushi. Fatarsa ta yi wani fresh da kyau, sumar kansa ya sha gyara ga dukkan alamu aski ya yi, hakanan gefen fuskarsa zuwa ɗan gemun da ya zagaye bakinsa. Gashinsa baƙi wuluk mai taushi sai ya ƙara fiddo da zallar haibarsa. Yadi ne baƙi a jikinsa wanda aka yi wa ƙaramin aiki a gaba. Ita kanta ba ta san sadda ta zuba masa idanu da murmushin da ya fito tun daga zuciyarta. 


"Ka fa tsorata ni."


Ta furta kamar mai shirin yin kuka. Ya shafi gefen sumarsa gami da kallon sararin samaniya yanda haɗu da hadari kafin ya maido dubansa inda ya fi gareta.


"Na faɗamaki ki adana min wannan shagwaɓar taki, na siye ta zuwa lokacin da zan soma cin moriyarta."


Sai kunya ta kama ta, ba ta manta sadda ta taɓa shagwaɓe murya a waya sai da ya ɗauke wuta na lokacin kafin cikin wani muryar da ba su saba magana ba ya hau roƙonta akan kar ta ƙara, ta bari sai sun yi aure. 


"Muje ni zan kai ki."


Sai a sannan ta ɗan ɗago kai.


"Malam Gali fa aka ce..."


"Na aike shi, daga yanzu ma duk inda za ki je matuƙar ba wani aikin nake ba ki yimin magana, ni da kaina zan zama direbanki."


Ta yi murmushi. Ya sa hannu ya dauki jakar kayanta suna tafe ita kuwa riƙe da ƙaramar jaka, haka suka ƙarasa har waje inda ya bar motarsa, ta shagala kallonsa ganin ya buɗemata gidan gaba da kansa, shiga ta yi sannan ya sanya jakar a kujerar baya ya zagaya ya shiga ya ja su. 


"Wai ma tsaya, wane gyara za'a yi maki a gidan Maama?" 


Ta ji tambayar bagatatan, ɗan turo baki ta yi. 


"Nima ban sani ba."


Shi kuwa ya taɓe baki kafin ya yi wani ƙaramin dariya ciki ciki yana kallon hanya. 


"Baby."


Ta juyo ta dube shi.


"Na'am."


"Allah ya yi maki tarin baiwa ne mai fisgar hankali masha Allah, a haka ma ya na ƙare? Ballantana idan kin ƙara kyawun da ya zarce wannan? Anya ba so ki ke ki kwace wannan gurbin na sauran ukun da zan ƙara a gaba ba?"


Tuni ɗan murmushin da ta soma ya koma ciki. Ta ɗan harare shi, ya san za'a yi haka dalili kenan da ko kallonta bai yi gaba ɗaya ba sai ta gefen ido. 


"Kamar ya za ka ƙara uku? Me ɗin?"


Ya haɗiye dariyar da ke cinsa. Da yatsu ya yi mata nuni da huɗu. 


"Ni fa mijin mata huɗu ne, haka addini ya halasta min idan har zan yi adalci, kin ga kuwa..."


"Yaya Sadauki, tsaya a nan zan sauka. Na fasa zuwa gidan Maaman."


Ya ɗan zaro idanu kadan gami da ɗan kallonta. 


"What? Kin fasa me? A ina? Oh, bakya so a gyaramin ke? Yau kuma sunan da ban so ki ka faɗi?"


Ta harare shi ta kauda kai, sai kumbura fuskar take kana kallonta ka san kishin ya motsa. Har wata ƴar kwalla ce ta cika idanunta. Ba ta ƙara tankawa ba shi ma bai ce mata uffan ba don ya sani tsokanarsa ba za ta ƙare ba, hakanan zai yi ta sanya ta ɓacin rai dalilin shirun kenan kar ya jawo ruwa. Har suka isa gidan Maama babu wanda ya cewa ɗan uwansa kanzil. 


Ba ta ko jira ya daidaita parking ba bayan sun shiga gate, ta buɗe murfin motar ta fice. Sai a sannan ya yi dariyarsa kafin ya fito ya ɗauki jakar kayanta da ta bari ya rufe motar yana amsa gaisuwar ma'aikatan gidan, har wani ya zo da zummar karɓar jakar ya girgiza masa kai. 


"No, bar shi kawai."Haulatu tana shiga da sallamarta, ƴar aikin Maama mai suna Bintalo ta amsa. Ganin Haulatu ta washe haƙora.


 "Lah Anti Haula, sannu da zuwa."


"Yauwa Bintalo, ina Maama?"


Kafin ta amsa sai ga Maama na fitowa daga kicin, sakin fuskarta ta yi ta dube ta.


 "Har kin iso kenan?" 


Ta ƙarasa gami da ɗan rungume Maama tana murmushi.


 "Eh Maama." Maama ta kamo yatsunta tana ƙare mata kallo kafin ta ce.


"Masha Allah, ke kam wannan yanayin na damina ya karɓeki, sai na ga kin ƙara haske abinki." 


Sallamar Sadauki ta sanya Maama sakin baki, duban ƙofar ta yi tana mai amsa sallama.


"Ikon Allah, wai kai ne ka kawo ta? To ƙaraso."


Ita dai Haulatu tun da ta ji muryarsa ta tura baki ta wuce Maama ta shiga cikin falon ta zauna a kujera mai zaman mutum biyu. 


"Maimakom ka yi magana a zo a ɗauki jakar Sadauki?" Faɗin Maama ita ma su na ƙarasowa cikin falon. Gefen Haulatu ya zauna gami da ajiye jakar yana murmushi.


"Maama komai fa take so ina gwada maki ne zan iya yi ga ɗiyarki. Ki taya ni ba ta haƙuri fushi ta ke da ni."


Ita Haulatu duk sai ya sa ta ma jin nauyin Maama, duk sai ta daburce ta fiddo idanu waje. 


"Waye ke fushin? Ni na mance ma da jakar fa shiyasa ban ɗauko ba"


Diramar sai ta ba Maama dariya don haka ta murmusa. 


"Taso ki dawo nan ki zauna, ni na san halin kayana, wataƙila wata tsokanar ya yi maki."


Ba musu kuwa ta miƙe shi kuwa ya danne gefen mayafinta da yatsun hannunsa ai kuwa ta ja da ƙarfi har tana shirin faɗuwa, harararsa ta ƙara yi kafin ta koma kusa da Maama ta bar shi da bin ta da kallo yana murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa. 


Bintalo tuni ta kawo musu ruwa da lemo bisa umarnin Maama. A sannan Maama ke tambayar Haulatun abin da ya haɗo su, ita kuwa ta yi shiru, ganin haka ya cafe zancen. 


"Wai Maama daga fa na ce mata duk gyaran nan nata so take a yi mata gyaran da zan fasa auren mata huɗun da na yi niyya shi..."


Tuni ya katse sakamakon tashin da Haulatu ta yi da gudunta ta yi hanyar ɗaki, Maama kuwa salati ta yi shi ko sumar kansa kawai ya shafa yana murmushi kai a ƙasa bai ce uffan ba. 


"Sadaukin Alhaji? To ba da ni ba, maza maza tashi ka fice ka ba mu wuri. Kuma ka sani babu gurbin kowace mace a gidanka bayan ɗiyarmu, au kishiya tun ba ta shiga ba? To ai kuwa zan zuga ta a fasa."


Ai sai dariyar da yake yi ta dauke, nan ya hau ban haƙuri, Maama ta ce shikenan. Koda ya miƙe ma dakatar da shi ta yi kan ya tsaya ya ci abinci tukunna. Ba musu kuwa ya koma mazauninsa don dama ya sani fushin Maama a kansa ba ya zuwa ko'ina. 


Ita da kanta ta shiga ɗakin ta lallaɓo Haulatu kan ta fito, dolenta ta fito amma ko inda yake ba ta kalla ba sai faman cin magani ta ke. Maama ta yi kicin, za ta mara mata baya ya yi saurin mikewa ya tare hanya. Ta dube shi, sai kuma ta kauda kai ganin yanda duk ya wani marairaice. 


"Baby, duk wannan so ne ko? Yi hakuri, tsokanarki fa nake."


Ta turo baki. 


"Tsokana da zancen kishiyoyi?"

 

Ya murmusa yana ɗan leƙa fuskarta.


"Na tuba. Ba ni da gurbin kowacce mace a zuciyata, ina da kyakkyawan zato a kanki, ba za ki ban wannan damar ba. Kuma in sha Allah ba zai zamo a cikin ƙaddarorina ba."


 Ta yi murmushi tana ɗan matse leɓɓanta gami da kallonsa ita ma. Ido guda ya kashe mata. 


"Ko ke fa."


"Idan kun gama shirin naku, muje ku ci abincin."


Suka juya a tare, Maama ce daga ƙofar kicin hannunta ɗauke da warmer yayinda Bintalo ke daga gefe ita ma tana wangale baki don sun burgeta ita kanta. 


Kunya ta kama Haulatu, shi kuwa waskewa ya yi, ita ko da sauri ta karasa gami da karɓar kayan hannun Maama. 


Ranar dai sai kusan isha ya bar gidan don har sai da mijin Maama ya shigo suka gaisa ya tafi lokacin ma tuni ruwa ya sauka. Haulatu ce ta raka shi har motar da lema ƙatuwa, sai da ya buɗe murfin zai shiga ita kuwa ta ɗan ja baya sakamakon kusancin da suka samu tsakani don a ƙoƙarinta na tare mishi dukan ruwa, ya sani koda ya yi magana ba ji za ta yi ba dalilin ƙarar ruwa don haka kawai ya shige motar ya rufe, ita kuwa ta koma ciki da gudu-gudu. 


***

 Tun da Haulatu ta je gidan Maama take kwasar darussa kala-kala, tun daga kula da miji, da yanda ake murmushi da dariya a gabansa, tarairaiya da kissa da ma girkuna wadanda ta ƙara gogar da ita a fannin. Sai ko magungunan da ta soma ba ta na sanyi sai ko na mata da ta san ba za su takura mata ba. Idan ka ga ta fita waje, to fa makaranta ce kawai za ta je. Nan ma Maama niƙaf ta siyo mata ta dinga sanyawa har da safa. Tsakaninta da su Umma da Hajja sai waya.

  Ta kula har lefe Maama da Amarya (matar baban Mu'az) su ke ta shiryawa, Momi Nuratu ta bar komai a hannunsu, ba ta ga ko kyallin kayan ba, Maama ce dai ta nemi sanin size din undies dinta. Sadauki bai ƙara tako gidan ba bisa umarnin Maama, dole ya haƙura sai dai su yi waya. 


 Ranar da ta cika sati uku da kwana ɗaya a gidan Maama ne, su na zaune su na hira zuciyarta tas don jin dadin zuwan da Anti Zaituna za ta yi a satin, ita kaɗai za ta zo ƴan gidan su sai dab da biki.


 Maama ta yi shiru tana duban Haulatun da hankalinta ke kan waya a sannan, ba ta son ko kusa Haulatun ta yi wa zancen mummunan fahimta. Ta samu labari ne kan cewa  Mamin Jannat ta samu Momi Nuratu akan ya kamata su yi gwajin cutar hiv kafin a kai ga auren don wai ba a da tabbas tunda a bariki suka zauna a Kano. Wannan batu ya ɗaga hankalin Momi Nuratu, ba don ta yarda ba amma sai ta tsorata sam ba ta yi la'akari da cewa komai Mamin Khaleefan za ta iya faɗi a lokacin don a fasa auren ba. Da hankalinta ya ƙi kwanciya ne ya sa dole ta kira wayar Maama ta yi mata bayanin yanda suka yi da Mamin Khaleefa. Ta kuma nuna mata kawai don zuciya ta samu nutsuwa ne. Maama ba ta ji dadin zancen ba sai dai ta ce babu komai za ta kai ta a gwada ta. 


Ajiyar zuciya ta saki ta dubi Haulatu.


"Ni kuwa kun yi gwajin genotype dinku ke de Sadaukin Alhaji?"


Maganar ya sa Haulatu kallon Maama. Girgiza kai ta yi.


"Aa, ba mu yi ba. Ni bai min ma zancen ba."


Ta kuwa samu dabara don haka ta sauke jinjina kai.


"Ai kuwa dai ya dace a yi. Zuwa yamma sai mu je wurin Khaleefa, shi ma Sadaukin zan mishi magana ya je."


Ta amsa da toh amma jikinta ya yi sanyi, idan ya kasance bai zo daidai da yana ake so ba fa? Shi ke nan ba za su auri juna ba? 


Maama na kula da ita ba ta ce mata uffan ba, ta riga ta san Sadauki AA ne, ta fi kaunar dai ya zamana ta aikata abin da zai sanya zuciyar Momi Nuratu nutsuwa. Sai da ta shiga ɗaki ta yi kira Sadaukin ta ba shi labarin komai. Ransa ya ɓaci da wannan abu na Mami sai dai kawai uzuri ɗaya da ya yi mata bai wuce saboda Barr Dawud ba da kuma Khaleefa da suke ganin mutuncin juna. 


"Kar ka damu da komai, ita ma Momin taka ba don ta gasƙata hakan ba ne, sai dai a yanayin da Hajiya Rahma ta yi batun ne ya jefa ta wasi-wasi, ka san ziga na tasiri a zuƙata."


"Shi ke nan Maama, zan zo in sha Allah."


"Yauwa ko kai fa."


*** 

 Cikin iko na Allah sakamako ya fita fes, Haulatu ba ta dauke da kowace irin cuta hakanan genotype dinta ya yi daidai da na Sadaukin wato AA. Ta kasa ɓoye farin cikinta, shi kansa murmushi ya ke dokawa har da yiwa ma'aikacin lab din da ya kawo sakamakon kyautar kuɗi ya bar Khaleefa da Maama da dariya. Sai a sannan ne ma ita Haulatun ta ji kunya ta rufe fuskarta. Maama kuwa duka sakamakon biyu ta karɓa ta damƙawa Sadauki. 


"Riƙe ka ajiye a wurinka, zamu yi waya."


Sai bayan sun rabu ta mishi text akan ya kai wa Momi Nuratu don hankalinta ya kwanta. 


***

  Khaleefa ne zaune ya je gaida Hajja yake sanar da ita batun zuwansa Kano a gobe don halartar ɗaurin auren abokin karatunsa. Ta taya shi murna sannan ta ce.


"Ka ga kuwa abun ya zo a daidai, gobe ne Zaituna za ta iso daga wancan ƙasar ta su ta larabawa, sai ka taho min da ita ba sai an sa Gali wahalar zuwa ba."


Ya ɗan yi jim, yarinyar da ba wani dogon hira ke shiga tsakaninsu ba? Shi kuma za'a tura ɗaukarta? Sai ya ji inama bai sanyo batun zuwansa Kano ba, da dai ya yi mata sallamar kawai ya fice. Umma da ta kula kamar hakan bai kwanta masa ba ta ce. 


"Ke kuwa Hajja, aiki za ki ba shi dai. Ki ka san ko ba shi kaɗai zai yi tafiyar ba?"


Jin haka ya yi saurin magana.


"Aa Umma, ni ɗaya zan je. Ba komai in sha Allahu zan taho da ita, jirgin ƙarfe nawa ne?"


Murmushi Umma ta yi.


"Ƙarfe huɗu na yamma za su sauka ta ce."


Ya jinjina kai.


"Ba damuwa, Allah ya nuna mana."


Hajja ta shiga sanya masa albarka. Da haka suka yi sallama Umma na bada sallahun ya gaida mata yaransa Affan da kuma bebinsu mai sunan Maminsa Rahma suke kiranta Ummi. 


***

 Kano...


Garin Kano an wayi gari da saukar ruwan samu, misalin ƙarfe goma da mintoci Khaleefa ta ƙarasa shiga cikin garin da motarsa Land Cruiser baƙa wuluƙ mai gilasai masu duhu sai sheƙi take yi sakamakon wankin da ta sha, ga kuma ruwa da ya ƙara wanke ta tas. 

Da kansa yake tuƙin, kai tsaye bai zarce ko'ina ba sai Bristol Hotel inda ya yi amfani da google map har ya ƙarasa. Nan Ango El-Mu'az Ƙaraye ya fito tarbarsa shi da wani abokinsa sun sha babbar riga. A lokacin ruwa ya tsaya sai dai har a sannan garin bai washe ba, ga kuma ni'imantaccen sanyi. Ya fito suka yi musabaha da raha da komai, Khaleefa ba ma'abocin yawan magana ba ne da hira, El-Mu'az ya fi shi wannan sakewar, koda kuwa bai yi niyya ba, idan an haɗu sai an sanya shi magana da darawa. Bai wani jima ba suka ɗunguma zuwa masallacin Umar Ibn Khattab inda anan ne za'a ɗaura auren. Koda aka kammala kai tsaye reception aka tafi aka yi ƙaramar liyafa sannan aka wuce gidan Amarya. 


Nan ma hotuna ne aka yi ta ɗauka bayan gaisawa da iyaye.  


Sai da Khaleefa ya huta sosai a masaukin Otal ɗin har ƙarfe huɗu da kusan rabi ya buga, kiran Hajja ne ya fargar da shi tunawa da aikin da aka rataya a wuyansa. 


"Ya Salam." Ya furta gami da juya akalar motar ta koma hanyar da za ta sada shi da filin jirgin na Malam Aminu Kano. 


"Khaleefa, ka ɗauko ƙanwar taka?"


Ya runtse idanu. 


"Afuwan Hajja, saura kaɗan na ƙarasa shiga Airport ɗin. Abu ne ya ɗan riƙe ni."


"To ba damuwa. Na maka uzuri tunda kai ne, da Mu'azu ne cewa zan yi da biyu ya yi."


Murmushi kawai ya yi sannan suka yi sallama. Can kuma ya ji shigowar saƙo, Umma ce ta turo lambar Zaitunar. Kafin ya ajiye ta kira shi. 


"Ɗana, ga lambar ƙanwartaka na nan, da shi ta yi kiranmu yanzu ba jimawa."


Ya amsa da toh gami da godiya suka yi sallama. Bai gwada ko kiranta ba sai da ya ƙarasa ya nemi wuri ya yi parking. Daidai sadda ya rufe motar ne ya ji ta ɗaga wayar da sallama cikin harshenta da ya haɗu da larabci da yaren Malay ga kuma Hausa.  Sai sallamar ta fita daban da irin na cikakken Bahaushe, ta yi dadi. Ya amsa mata. 


"Khaleefa Dawud ke magana, ki fito ina waje."


Ta amsa da toh, ba jimawa ba, yana tsaye yana kallon ƙofar sai ya hango tana fitowa, wani ɗan matashi yana jan trolley ɗinta. 


Khaleefa daga nesa ya ƙare mata kallo tas. Riga ce ta yadin Abaya kalar ruwan ƙasa mai V shape a jikinta, tsawonta har ya zarce gwuiwa sosai, ta ɗan kama ta kaɗan daga ƙirji daga ƙasan kuwa ta buɗe, sai dogon wanda baƙi da ta sanya sai ko high heel baƙi da ke a ƙafarta. Baƙin mayafinta ƙarami sai ta zagaye fuskarta da shi. Sai ko baƙin sunglasses da ta rufe idanunta da shi. Ta sha hoda da jan bakinta da ya fiddo tsantsar kyawunta. Komai na Zaituna cike yake da burgewa ga uwa uba yarinya ce mai aji da iya gayu. Hannunta babu komai sai wayarta da ƙaramar baƙar jaka da ta riƙe. 


Khaleefa ya kauda kai bayan kallon da ya ƙare mata. Ɗan bakinsa ya taɓe. Ba laifi ta iya kwalliya. Sai kuma ta ba shi haushi ganin kamar kowa a wurin kallonta ya ke yi. Har ta ƙaraso bai kalle ta ba, sai ma ya juya ya nufi motarsa ya buɗe boot, matashin ya sanya jakar a ciki bayan ya tambayi Zaituna ko shi ya zo ɗaukarta ta amsa da gyaɗa kai cike da jin babu dadi na yanda ko gaisuwarta Khaleefa bai amsa ba. Shi kuwa sallamar matashin ya yi ya tafi sannan ya buɗe motar ya shiga, da hannu ya buɗe mata gidan gaba ganin ta kai hannu za ta shiga buɗe ƙofar baya ta shiga. Sai da ya ɗauke farar babbar rigarsa da ke jikin kujerar ya maida baya sannan ta shiga ta zauna da bismillah a bakinta ta rufe ta ɗaura seatbelt. Kafin ta ƙara dubansa tana fidda gilashin ta mayar saman goshinta.


"Yaya Khaleefa, barka da yamma."


Kallonta ya yi fuskar ba yabo ba fallasa. 


"Yauwa, daga yau kar ki ƙara kwalliya idan za ki biyo hanya. Babu amfanin kina mace ki yi ta abubuwan da za ki ɗauki hankulan maza." 


Zaituna ranta ya sosu, nan da nan sai ga ƙwalla sun cicciko mata, Khaleefa da tuni ya maida kansa ga tuƙi yana ƙoƙarin yin ribas bai ƙara kallonta ba. 


"Abu Affan, wallahi ban yi kwalliyar da wannan manufar ba. Bari na goge."


Ya nanata sunan da ta ambace sa da shi, ɗan kallonta ya yi ganin ta zuge jaka ta fiddo tissue wanda ke zuwa  a ƴar ƙaramar leda da nufin goge bakin. A sace ya kalli leɓɓan ya kauda kai.


"Ni ban ce ki goge ba. Bar kayanki."


Kallonsa ta yi sai ta sauke ajiyar zuciya ta maida tissuen cikin jaka. Katafaren wurin abinci da kayan maƙulashe na Albaik dake kan titin Kurna ya yi parking ɗin motarsa. Ta dubi gidan abincin, eh tana jin yunwa don ba ta iya cin komai a jirgi amma fa ta fi ɗokin ta gan ta a gida. Ba dai ta ce komai ba, ya ce ta jira shi sannan ya fita. Ta bi bayansa da kallo, dogo cikakken namiji, babu macen da ba za ta yi fatan Khaleefa a matsayin mijinta ba sai dai marar sa'a da rabo. Ita tunda take da shi ma ba ta wani tsayawa ƙare mishi kallo, yau ɗin ma don yana nesa da ita ne kuma babu damar da zai gan ta tunda ta waje duhu ne.


Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ciro wayarta tana dannawa. Murmushi ta yi ganin saƙon murya daga Haulatu ta whatsapp, buɗewa ta yi ta kunna. 


"Ƴar uwata kun taho kuwa? Allah ya kawo min ke lafiya, na matsu ki ƙaraso."


Ta maida mata da saƙon muryar ita ma. 


"Ni kaina haka my sister, amma fa na ji ance ki na gidan Maama ai."


Koda ta amsa ganin bai shiga baki ɗaya ba ne yasa ta fahimci datar a kashe sai kawai ta sauka ita ma. Ta ɗan ci mintuna kusan biyar kafin Khaleefa ya fito hannunsa ɗauke da ledoji. 


Yana shiga ya miƙa mata, karɓa ta yi gami da furta Thank you. Daga haka ya sanya seatbelt ya yi ribas ya hau titi. Ita kuwa gudun kar ya ji babu dadi ya sanya ta buɗe ledar, shinkafa ce da ta ji kayan haɗi sai kaza, ɗayar kuwa lemu ne da ruwa sai youghurt. 


"Abu Affan, ba za ka ci abincin ba kai?"


Yana so ya ce mata ba ya son sunan da ta ke ambatonsa da shi, amma kuma ya kasa, haka kawai tana wani maida shi tsohon ƙarfi da yaji, eh ya haifi Affan, amma meyasa ba za ta kira shi da Yayan ba kamar yadda sauran ƙannen ke faɗi? Bai kalle ta ba a can ƙasa ya amsa.


"Alhamdulillah. Ki ci."


"Toh."


A nutse ta ke cin abincin kamar yanda shi ma ke tuƙin a nutse. Yana yi ne gudun kar ya yi takun da zai sa ta kasa cin abincin. A hankali ya ke satar kallonta, komai cikin nutsuwa ta ke yi. Ta ci sosai sannan ta rufe ta maida leda, ta yi amfani da tissue ta goge hannun wanda garin cin kazar ta ɓata, ta kora ruwa kaɗan saboda ba ta son ta fitsari ya kama ta a tsakar daji. 


Jingina kai ta yi jikin kujerar a hankali kuma tun tana bin hanya da kallo bacci ya sure ta don a kwanakin sam ba ta samu ta runtsa sosai ba tsabar zumuɗi da kuma yawon shiga kasuwa siyayya. 


Khaleefa jin shirun ya yi yawa ne ya sanya shi ɗan waigo kansa. Fuskarta na kallon saitinsa, bacci take yi cikin kwanciyar hankali abinta. Ta cire gilashin ta ɗora bisa cinya, ya maida kai ga kallon titi sannan ya ƙara juyowa ya dube ta. Ya maimaita hakan har bai san adadi ba, shi kansa bai san me ke ɗaukar hankalinsa ga kallon ba, amma kuma duk sadda ya dubi fuskarta yakan ji ba ya kaunar ya daina kallo. Sallar Magriba ce ta sanya shi tsayawa a wani masallacin gefen hanya cikin wani ƙauye. Jin tsayuwar motar ya sanya Zaituna farkawa, dubanta ya yi.


"Ina zuwa, zan yi sallah ne."


Ta gyaɗa kai sannan ya fice. Wurin akwai jama'a sosai, kamar ma kasuwa ce, kowa dai harkokinsa yake. Wayarta ta fiddo a jaka ganin tana ta ringing. Hajja ce. Tambayarta take ko sun ƙaraso, ta ce mata sun dai kusa kawai don ba ta ma san ina ne nan ba. Suka yi sallama bayan ta musu fatan isowa lafiya. Ba ta koma baccin ba har Khaleefa ya dawo. Sai bayan ya cigaba da tuƙin, wani baccin ya ƙara kwashe ta. 


Suna isa cikin garin Katsina, nan ma ba ta farka ba har sai da ya shiga cikin gidan nasu ya tsaida motar, ya kula dagasken gaske bacci ne a kanta. Farfajiyar gidan babu kowa an tafi masallaci gabatar da sallar isha'i. Zaituna kuwa jin kamar a tsaye suke ya sanya ta farkawa bakinta ɗauke da sunan Allah. Idanuwanta cikin na Khaleefa suka faɗa, ta yi saurin miƙewa zaune tana rarraba idanu, ba ta son yin doguwar magana saboda ta san zai wahala bakinta idan ba ya ɗan tashi sakamakon bacci da ta yi don haka ta kauda kai.


"Ashe mun iso? Abu Affan ba ka tashe ni ba."


Madadin ya ba ta amsa sai kawai ya buɗe motar ya fita, ganin haka ita ma ta fito. Shi kuwa akwatin kayanta ya ciro. Har a sannan sallah ake suna ji daga masallaci ba a idar ba, zagayowa ta yi riƙe da ledojin abincin da ya siya mata da zummar karɓar akwatin, don a ganinta ba girmansa ba ne ya riƙe akwatinta. Fuska a ɗaure ya ce.


"Ki je ciki, zan taho da shi."


Ta ɗan kalle shi tana murmushin da har gefen kumatunta na lotsawa, Khaleefa ya sauke ajiyar zuciya. A zuciyarsa ya furta masha Allah. 


"Nagode sosai Abu Affan."


Daga nan ta juya ta yi gaba ta bar shi da bin ta da kallo kafin ya numfasa ya rufe motar shi ma ya shiga ciki. Ya kula ma kamar da gayya take faɗin sunan da bai wani yi mishi armashi ba. 


Umma da Hajja baki ya ƙi rufuwa suka tarbi Zaituna da murnarsu. Khaleefa kuwa ko zama bai yi ba bayan ya kawo akwatin ya yi musu sallama ya wuce. Zaituna sai da ta yi wanka ta sauya audugar mata dake jikinta kafin ta sauko ƙasan tana yin video call da Haulatu inda take yaba kyawun da ta ga ta yi, fadi take. 


"Sis kin sauya baki daya, har wasu kumatu na ga kin yi."


Ɗan farr da idanu Haulatun ta yi mata. 


"Ka ga Mrs Abeed Ridwan Malumfashi."


"Yes, ita ce."


Suka yi dariya, Zaituna cikin sauri ta maida fuskar wayar ga Umma da Hajja da ke zaune, ai tuni Haulatu katse kiran baki ɗaya. Umma murmushi kawai ta yi gami da girgiza kai. Hajja ko cewa take.


"Ja'ira, wato kam Sadaukin Alhaji ya sauya min ita ko?"


Umma ba ta amsa ba sai Zaituna dake kare ƴar uwarta. 


***

Momi Nuratu ta zubawa takardar idanu tana karancewa ganin babu wani abin tashin hankali a saksmakin gwajin ya sanya ta murmushi gami da sauke ajiyar zuciya lokaci guda tana mai godiya ga Allah.


"Alhamdulillah. Na ji daɗin hakan. Ni dama ba ni da kokwanto, sai dai ka sani, tunda har Rahma ta soma haka, gwara a yi abin da zai toshe bakinta da ƙananun magana. Koda dai, nasan ko hakan ma ba a tsira ba."


Sadauki ya yi murmushi yana mai amsawa da hakane.  Ita kuwa Momi Nuratu ta saka a rai duk radda Mamain Khaleefa ta ƙara zuwa da wani batun to fa ba za ta ƙyale ta ba. Tunda ba ta san kara ba.


***

Washegari tun da wuri Zaituna na kammala shiri ta shiga ɓangaren kowa a gidan aka gaisa, kowa ya gan ta dai ya hau murna da washe haƙora. Yarinya ce mai shiga rai tun a baya, ba ta da girman kai ko kaɗan. Sai da ta yi dagaske kafin ta samu kanta a ɓangaren Momi Nuratu don ita ma gwanar son hira ce. Ɓangaren Baban Kowa nan ne ƙarshen inda ta shiga, sun gaisa, Radiya ma ta fito ta hau ihun murnar ganinta suka rungume juna. Ranar ba zata shiga makaranta ba hakan yasa Zaituna roƙon alfarmar ta yi mata rakiya gidan Maama. 


***

Khaleefa ya tamke fuska sosai yana kallon Jannat da ke kwance tana wani nishi kamar mai naƙuda ya yin da Mami ke tsaye a kanta gaba daya ta ruɗe, faɗi take.


"Ka tsaya kallonta kamar ba jininka ba, matsayinka na likita ba za ka yi kokari ka auna ta a san matsalarta ba?"


Bai ko kalli Mamin ba, idanunsa a kan Jannat wacce Nos ke tsaye a kanta tana ɗan tattaɓa hannu da goshinta. 


"Ku je waje Mami, bari na duba ta."


Ba musu Mamin ta fita, Nos ta bi bayanta. 


"Tashi zaune ko na karairayaki." Ya faɗi murya a kausashe. 


Jannat duk da irin ruɗewar da ta yi, sai da ta daure gudun kar a gano ƙarya take yi, ta ƙara wani juyi da riƙe kai.


"Wash!" 


"Za ki tashi ko sai na wanka maki mari?"


Ai bai kai ga ƙarasa zancen ba ta yi zumbur ta miƙe zaune tana ƙunƙuni. 


"Don ba ki da mutunci akan ɗa namiji ki ke tayarwa da tsohuwarmu hankali? Toh na rantse maki matuƙar ba ki bar waɗannan shirme da shiriritar ba sai kin koma gidana da zama na maki hukuncin da ba ki taɓa zato ba. Banza kawai da ba ta san ciwon kanta ba. Ni na sani babu uwar abin da ke damunki, tsabar kin raina mutane ne ki ke wannan ƙananan iskance-iskancen. Daga yau kika ƙara bari na ganki a asibitin nan saboda mutumin da ba ya ta taki sai na maki allurar mutuwa kowa ya huta."


Ai fa nan ta hau rarraba idanu, hawayen suka wanke fuskar. Dagaske yake babu ciwon komai tattare da ita, ta yi ne don Mamin ta gane ba za ta iya rayuwa babu Sadauki ba. Hakanan Abbanta wanda sam ya ƙi goyamata baya.


Ganin hawayen sai kuma ya ɗan ji tausayinta, zama ya yi a gefe ya shiga yi mata nasiha da nuna mata illar auren wanda ba ya sonka. Jikinta ya yi sanyi, har wani ɗaci ɗaci take ji a maƙogwaronta, dagaske dai ta rasa Sadauki? 


"Yaya, Allah ya ban wanda ya fi Yaya Sadauki." Ta na kaiwa nan ta fashe da kuka sosai, ya ɗan rungume kafaɗarta yana rarrashinta. Son maso wani ciwo ne babba, ta kuma ji har a ranta ta haƙura da shi ɗin. Khaleefa ya fi kowa a gidan kusanci da Sadauki, tunda har ya rantse mata akan cewa Sadauki ba zai aure ta ba, ta ji ta yarda kuma za ta haƙura da shi. Amma fa ko bikin ba za ta iya zuwa ba ko don su Fa'iza da za su yi mata dariya. Har abada kuma ba ta ga zumuncin da za ta yi da Haulatu ba, a cewarta. 


Ya dai cewa Mami ciwon kai ne kawai sai damuwa, ya rubuta magunguna suka fito tare tana lallaɓa ɗiyarta har tana mata raɗa a kunne kan cewa kar ta wani damu, ta san idan an yi gwajin nan Momi Nuratu ba za ta amince ɗanta ya auri Haulatu ba don tana ji a jikinta yarinyar na da cutar ƙanjamau. Ita dai Jannat ba ta ce uffan ba, ba za ta ƙara biyewa Mamin ta dinga kwaɗaita mata abin da har abada ya fi ƙarfinta ba don haka ta yi gaba zuwa mota ta bar Mami tare da Khaleefa. 


***

Zaituna sakin baki ta yi bayan sun gama murna da farin cikin ganin juna da Haulatu, ta yi wani kyau, fatar nan sai sheƙi take yi, ga wani ƙamshi dake tashi a jikinta duk inda ta gifta koda kuwa ba ta shafa turare ba. Ko'ina ya ƙara cika dam dam. Duban Maama ta yi murya a shagwaɓe ta ce. 


"Ni ma Maama ke zan sa ki kira a yi min gyaran jiki idan aurena ya zo."


Maama ta yi dariya, idan da sabo ya ci ta saba da rashin ta idon Zaituna, sam ba ta mata kallon uwa sai wata abokiyar kuka da dariya. 


"Magana ta ƙare ƴata, yanda ki ka ce haka za'a yi. Amma har yanzu dai gafara Sa ake, ban ga ƙaho ba."


Murmushi Zaituna ta yi don dagaske yanzu ba wani da take kulawa, Zaid din ma da ƙarfin addu'a ta cire shi a ranta ta haƙura. 


"A taya mu addu'a Maama."


Maama ta jinjina kai.


"Sosai muke yi sai dai mu ƙara. Su ma ƙawayen nata ba don abin ya zo gab da gab ba, ai babu abin da zai sa a ƙi haɗe bukukuwan wuri guda."


Radiya ta sunkuyar da kai tana murmushi, Haulatu ta ɗan bugi kafaɗarta tana mata raɗa, aikuwa ta kai mata duka a kafaɗa suka yi dariya. Zaituna ta harare su.


"Munafukai, ni Maama ai dama an sani an haɗa, na kula son auren suke yi. Safinar ma kusan kullum whatsapp status dinta kalamai da waƙoƙin soyayya ne."


"Laaah." Haulatu da Radiya suka firta a tare suna haɗa idanu da darawa duka lokaci guda. 


Maama ta girgiza kai ita ma tana dariya. 


"To yanzu kan autar tawa za ki dawo?"


"Auta fa kika ce Maama? Ni dai a'a, muna jira ki kawo mana..."


Pillow ta jefa mata ba shiri Zaituna ta yi shiru tana ƙunshe dariyarta. Maama ta miƙe ta na fadin.


"Bari na sa yanzu a maida ki inda kika fito, ba za ki zo ki takura mana ba."


Nan ta bi bayanta tana roƙon ta yi hakuri.  


"Allah Sarki Anti Zaituna, wallahi ina mata sha'awar samun miji mai nagarta da zai riƙe mana ita hannu bibbiyu."


Faɗin Haulatu kenan tana bin bayan Maama da Zaituna da kallo cikin murmushi. Radiya ma ta ce 


"In sha Allahu za ta samu. Ita yanda na kula, ta fi kaunar aure a ƙasarnan, ba ta son ɗan can."


"Mu ɗin ta ke ƙauna, tana son zuri'arta ne ina ga shi ne babban dalilinta." Haulatu ta ba ta amsa. 


***

A kwana a tashi...

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, har aka wayi gari sauran bai fi sati uku a sha bikin Sadauki da Haulatu ba. 

  An fiddo ankon sisters daban da kuma na iyaye. Haulatu ba ta da wasu ƙawaye sai ko wasu abokan karatunta uku da suke mutunci sosai a makaranta, Fauziyya, Rumanatu da Sadiya. Sai ko aminanta kuma ƴan uwa Safina da Radiya, wannan yasa su biyar ɗin suka haɗe kai suka fidda ankonsu daban wanda za su saka ran dinnerparty da Sadauki ya ce zai shirya. Su biyar din kadai suka san da zaman ankon gudun ƙananan magana sai ko Zaituna da Maama wadanda ake yi a gabansu. Don Zaituna ma takanas ta dawo zama wurin Maama saboda ƙanwarta. 


A yau ta kama Alhamis, ranar ce kuma za ta tattara ta koma gida. Maama ta yi mata iyakar yin ta, ta kuma kai ta wajen ƙawarta ƴar Senegal dake aure a Katsina ta mata nata gyaran har na tsawon sati biyu, jikin Haulatu har wani jaja-jaja yake ban da uban ƙamshi da ke tashi a jikinta. Ita kanta kuma daga yanayinta ta fahimci ba ƙaramin sauyi take ji ba, magunguna ne kala-kala an ba ta ta sha. Ta ci na ci ta kuma shanye romo. 


Rabonta da su saka juna a idanunsu da Angon nata an fi sati biyu. Tun yana zuwa Maama na korarsa ta hana su ga juna har ya yi fushi ko ya zo gidan ba ya neman ya ganta. Ƙarshe ma ganin dagaske Maama take sai ya bar zuwa. Takaicinsa bai ƙaru ba sai da ya ga ko videocall ya kira ba ta so sam ba ta ɗagawa. Wannan abu ya sanya shi yin fushin da har ya yi tafiya Dubai bai mata sallama ba. Ita kuwa Haulatu jin da ta yi ya yi tafiya ranta ya yi mugun zafi, toh mene ne laifinta don ta bi huɗubar Maama? Ta dauka duka ana yi ne don ya ƙara musu shaƙuwa da juna. 


Ko a yau da take faman haɗa kayanta na komawa babban gida sam fuskarta babu walwala. Damuwar rashin ji daga Sadaukinta yana cin ranta, gaba daya komai ya fita a kanta. A gaban Maama dakyar ta ke dannewa ta saki jiki a dinga hira. Sadauki bai taɓa nunawa Maama komai ba koda a waya hakan yasa ba ta fahimta ba. Zaituna ce ta shigo dakin tana amsa wayar Mamanta wacce za su taso daga Malaysia a gobe. Har ta kammala wayar Haulatu ba ta dube ta ba tana zaune gefen gadon riƙe da siket da take shirin ninkewa ta lula duniyar tunani. 


Ganin kamar hankalinta ba ya wurin ya sa Zaituna kai hannunta saman nata wanda ya fargar da ita da sauri. Suna haɗa idanu sai ta sauke ajiyar zuciya gami da saurin miƙewa ta cigaba da ninkin kayan.


"Sis, kin bani tsoro fa. Har kin gama kallon?"


Fadin Haulatu ba tare da ta dubi fuskarta ba don ba ta so ta ga hawayen da ke kokarin zubo mata sai dai ina ta makaro, Zaituna ta riƙo hannunta ta zaunar a gefen gadon. Daidai sadda Haulatu ta share hawayen fuskarta. 


"Meke faruwa ne? Har yanzu ba ku shirya ba?" 


Tambayar da Zaitunar ta yi ya sanya ta dube ta da mamaki. Ɗan murmushi ta yi ta jinjina kai.


"Yes, na san ba kwa gaisawa da Yaya Sadauki, na san kun yi faɗa. Maama ta sha tambayata ko ina ganin kuna waya a ɗaki? Nakan amsa mata da eh don kawai na taya ki ɓoyon abin da kike gudun ta sani kar ranta ya ɓaci. Amma ni na sha ganinki kina hawaye da daddare. Me ya yi zafi har haka tsakaninku?"


Sai ta samu damar fayyace damuwarta, nan da nan ta labartawa Zaituna komai. Shiru ta yi tana sauraronta har ta kai aya kafin ta jefa mata tambaya.


"Kuma da ya yi fushin, ke ma sai ki ka bar yi masa magana? Ko kuwa kin kira shi?"


"Idan fa na kira ko ɗagawa ba ya yi tun ma kan ya tafi. Sannan ko text na yi ba ya ban amsa. Shi ne na watsar da shi nima."


Harararta Zaituna ta yi. 


"Kin watsar da shi amma ai ga shi kina cutuwa. Ni dama ina ganin yanda Maama ke hana Yaya Sadauki ganinki na san ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Ni ban ga wani amfaninsa ba."


Sai kawai ta miƙe tana ta faɗin bari ta sanar da Maama, ganin dagaske ta kama hanyar fita daga ɗakin ya sa Haulatu saurin miƙewa ta jawo ta. 


"Aa Sis, don Allah kar mu yi haka. Wannan tsakaninmu ne, komai zai wuce. Kin ji?"


"Haka ki ke so ku ci gaba da zama babu mai kula wani a cikinku? Kinsan irin da matsalar hakan kan haifar?"


Haulatu ta girgiza kai tana dauke ruwan hawayenta.


Maama wacce ke kokarin shigowa ɗakin sai ta fasa ta juya, ta ji komai dake faruwa, dama zuwan da ta yi don ta kawowa Haulatun wata jarka da ta bari a cikin firij na tsumi. Komawa ta yi ta ajiye jarkar saman teburin dake tsakar falon ta zauna. Wato Sadauki abinda ya aikata kenan? To kada dai ace ta yi babban kuskure na hukuncin da ta yanke a kansu? Ita ta yi ne don a gaba ya ƙara jin matsuwa da son ganin matar tasa har ma da sabuwar ƙauna, ba wai don ya nisanta kansa daga gareta ba har haka. Ajiyar zuciya ya saki, gobe ne zai dawo daga Dubai, dama ya je tare da wasu abokan kasuwancinsa ne. Bari za ta yi ya dawo sannan ta yi mishi magana. 


Ba ta kyale Haulatu haka ba sai da ta kira ta tare da Zaituna, rarrashinta ta yi gami da nunamata ainahin manufarta a kai. A karshe ta ce ta kwantar da hankalinta, ta yi hakuri kar ta neme shi tunda ya nuna ba zai saurare ta ba, ta bari har zuwa goben idan ya dawo daga tafiya. Sosai kuma sai ta samu nutsuwa da zantukan Maaman, ita da kanta ta kai su gida. Kowa ya ci karo da Haulatu ya ga yanda ta koma sai ya kama baki ya tanka kyawun da ta yi. Wai kamar ita ce ta yi rayuwar Malaysia din. Ita dai addu'ar kambun baka take yi a zuciya. Hajja ta washe haƙora.


"Dakyau Hauleta, Masha Allahu la kuwwata illah billahi. Ke ki dinga lahaula gudun baki kin ji ko? Kar ki yi wa kowa alkunya duk wanda bai ba ki yiwa kanki."


Mutan dakin suka saka dariya don tunda aka ga motar Maama, mutanen gidan aka yo caa zuwa wajen Hajja ganim fuskar Amarya. Har da masu gulmar son gani wane irin gyara ne Maamar ta ke mata da aka wani dauke ta daga gidan zuwa can. Fahima dake zaune a falon ko ci kanku ba ta ce ba. Sai ma ta miƙe ta yi sama abinta ba tare da kowa ya kula ba. Umma kuwa ba ta ce komai ba ban da murmushi, kwallar da suka cicciko mata a idanu ta share a faƙaice, a ƙasan ranta kuwa hamdala take yi ga Allah da ya sauya musu rayuwa daga wahala zuwa jin dadi. Fatanta a yanzu Allah ya nunamata auren ɗiyarta, ya sa a yi komai lafiya a kammala. Har Haulatu ta zo ta rungume ta ba ta bar kauda kai ba, Hajja na mata faɗa kan ta rage wannan jin nauyin ita ba ta son abu na mutan da. Ita ko Haulatu kai ta dora a cinyar Umman tana fidda hawaye masu zafi karshe ta fashe da kuka sosai, Umma ma ta shiga nata hawayen tana kallon gefe. Kowa da dalilinsa na kukan, ita Haulatu ga murnar wannan rana na tahowa da take tabbacin burin Ummanta ya kusa cika ga kuma na sauyin Sadauki da ke damunta koyaushe, ita kuwa Umma, baya kawai take tunawa tana cigaba da godewa Allah a ƙasan ranta. Nan aka shiga ban baki

Maama na janye Haulatun.


"Haba Na'imatu, ya za ki biyewa wannan a dinga wani koke-koke ana abin farin ciki da murna. To maza maida mayafinki mu koma gidana."


Jin haka ta shiga share fuskarta, baki a kumbure ta ce 


"Na daina Maama." Aka yi dariya. 


Sai da kowa ya watse sannan Radiya da Safina wacce ta zo gidan da zummar sai bayan biki, kuma babu inda ta yada zango sai ɓangaren Hajja, suka haɗu suka ƙulle a ɗaki. Hira suka shiga yi, Safina na labarta musu diramar da aka yi a daren jiya tsakanin Haj Hadiza, Fahima da kuma su Hajja. 


"Wai fa Hajiya kuka sosai ta zo muna zaune ta shiga rerawa Hajja akan don Allah ta yafe mata. Hajja ba ta ko kalle ta ba nake fadamaki, shi ne ta koma ga Umma. Umma ce ta ce mata komai ya wuce. Dakyar dai Hajja ta saurari Hajiya ta ƙare da yi mata nasiha. Fahima ma har da neman gafara bayan Hajiya ta tirsasa ta. Ni dai jikina na bani tuban muzuru Fahima ta yi, amma Hajiyarta dai na ga alamar dagaske take ko ma dai ba duka ta sauya ba, kuka fa sosai har da su majina. Amma kuma ita ma kun san me?"


"Sai kin faɗa." Fadin Radiya da Haulatu har suna haɗa baki. 


"Uhum, babanta ne zai haɗa Fahima aure da ɗan yayansa. A karshe dai Hajiya ke roƙon Hajja akan ta taimaka ta yiwa su Baba Alhaji magana su saka baki kar a yiwa yarinyarta auren dole. Hajja ta dinga yi mata faɗa akan ita babu abin da za ta ce, gwara ma a yi hakan ko Fahima za ta nutsu. A karshe Umma ce ta kashe wutar ta lallaɓa Hajja, dakyar dai ta ce a hakura zuwa bayan bikin Haulatu sai a yi maganar. Hajiya na ta ƙorafin wai yaron na shaye shaye, amma baban ya dage sai an yi, idan ya so tunda ita mace ce za ta iya juya shi ta maido shi hanyar tsira, ku ji fa?"


Girgiza kai Haulatu ta yi cike da takaici. 


"Abin nan yana ci min tuwo a ƙwarya, sai ki ga namiji na tata duniyanci amma a dage mace wai sai ta aure shi a haka, amma da ace ita macen ke yin wadannan miyagun ayyukan da ta zama abar zagi da ƙyamata. Har ga Allah na tausayamata, ina addu'ar kar Allah ya tabbatar da wannan abin."


"Amin Haulatu, ni kaina ta ban tausayi, ba ku ga ma yanda ta dinga kuka ba daga baya, ba ta ji labarin haɗin auren ba sai da Hajiya ke faɗawa su Hajja. Ita dai Hajiya haka ta yiwa su Hajjar sallama ta tafi wai dama ta zo kawo Fahima ne don ba za ta yarda a yi mata aure da mashayi ba."


Murmushin takaici Haulatu ta yi, duniya kenan. Yau kuma Fahima ce ake son aurawa mashayi. Dole Hajiyarta ta fita hayyacinta. 


"Allah ya magance mata." Abin da kawai ta ce kenan suka amsa da amin kafin su shiga hirarrakinsu. Daurewa kawai ta ke yi tana biye musu, ko kusa ba ta ba su labarin rikicin da suke ciki ba, hakanan ta ji tana son ɓoye sirrinta da Yayan nata. Zaituna ma don dai ta riga ta ɗago ta ne amma da ba abin da za ta ce. 


***

Washegari misalin ƙarfe biyu da mintoci na rana, ana zaune ana hira a falon Hajja, Zaituna ta fito ciki shirinta na zuwa gyaran gashi. Don tace kitso take son yi da biki, wanken kan za ta a ranar. Mamanta ba su iso ba sai dare. 


"To ke kadai babu ɗan rakiya?" Faɗin Umma kenan, Haulatu ta yi caraf ta miƙe zaune daga kishingiɗar da ta yi. 


"Umma ko na raka ta?" 


"Ina?" Fadin Hajja da Umma lokaci guda. Jin yadda suka haɗe baki kamar ta faɗi wani abin gudun sai suka ma ba ta dariya, Hajjah ta ce. 


"Kin ga ki yi shiru da bakinki, so ki ke yau Zakiyya ta mana dirar mikiya. Koda dai, Sadaukin Alhaji uban ƴan kishi sai ya wanke ni ba shiri. Babu inda za ki je."


"Toh Hajja ita kaɗai za ta tafi? Ga Safina na makaranta. Sis ki saka baki please." Ta ƙarashe tana narke fuska kamar ta yi kuka. 


Murmushi Zaituna ta yi.


"Aa fa, babu ruwana. Dama ya lafiyar kura? Bari na tafi kawai, zan leƙa can wurin Momi Nuratu sai na ja Zuhra ta min rakiya."


"Shikenan kuwa. Hakan ma ya fi. Sai kun dawo." Hajja ta amsa. Babu wanda ya yi maganar Fahima sakamakon matsalarta da ake kokarin magancewa don Baba Alhaji ya yi waya da mahaifinta ya nemi alfarma akan ya zo yana son ganinsa. 


Ta juya tana ɗagawa Haulatun yatsunta uku tana mata dariyar mugunta. Haulatu ta kauda kai kawai gami da komawa ta kwanta. Ta sani yau Sadaukinta zai dawo, tun safe take baza idanu da kunnuwa ko za ta ji labarin ya shigo Katsina daga Kano amma shiru. Hankalinta gaba daya yana kansa ta kasa sukuni duk kuwa da ba maganar ke haɗa su ba. 


***

Zaituna na fitowa ba ta wani yi nisa ba, tana takunta cike da nutsuwa cikin shigar doguwar rigar abaya maroon da ya karɓi fatarta sosai, ranar a yau ta buɗe ba kaɗan ba, don haka sai ta ke tafiyar a hankali. Ɗagowar da za ta yi ta hangi Khaleefa na takowa ya fito daga ɓangaren Baba Dakta, sanye cikin shadda sky blue sai ko hula a kansa. Ya yi tsaf abinsa cikin shigar juma'a. Bisa al'adarsa duk rana ta juma'a ba ya komawa gida sai ya shigo gaida iyayensa. A hankali ta sauke idanunta daga gareshi ganin bai bar kallonta ba. 


"Barka da juma'a Abu Affan, fatan an yini lafiya?" 


Ya sauke ajiyar zuciya, tun sadda ta zo garin ba su ƙara haɗuwa ba sai yau. Zai iya cewa kwanakin nan tana ransa, ya kuma kasa cire tunaninta a kwakwalwarsa, Hafsat ba ta ko sakaya sunansa, kai tsaye Khaleefa ta ke ce mishi amma ba ta ambaton sunansa na yanka. Sai dai yana son girmamawa, bai dai taɓa hana ta faɗin abin da ta yi niyya ba. 


"Lafiya. Ya su Hajja?"


Da murmushin jin dadin ya amsa mata ta kara kallonsa ta ce. 


"Lafiyarsu kalau."


Ga mamakinta murmushi ya yi mata, baki ta saki tana kallonsa. Za ta iya rantsuwa bai taɓa yi mata murmushi ba sai dai ta hango yana yi ga wasu. 


"Masha Allah. Fita za ki yi?" 


Tambayar ta ƙara lula ta cikin duniyar farin ciki, ita kadai ta san meke cin zuciyarta kwanakin nan sai dai ba ta son maimaita tarihi dalili kenan da yasa ta ke kwaɓar kanta tana kuma ƙaryata kanta da gangan. 


"Eh, zan je saloon. Zuhra zan kira ta yi min rakiya."


Ya soma tafiya yana amsa mata.


"Ok. Allah ya tsare. A dawo lafiya."


Daga haka ya wuce ta zuwa sashen Hajja, ita kuwa ta amsa da amin da godiya tana mai binsa da kallo har ya gifta ta, kowannensu ya shaƙi ƙamshin turaren ɗan uwansa, Zaituna ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan waiga ta dube shi sannan ta juya ta cigaba da tafiya har a lokacin ba ta bar murmusawa ba ga kuma gefe guda da mamaki ya cika ta. Wai Yaya Khaleefa ke mata murmushi? 


***

Misalin ƙarfe bakwai na yammaci, Sadauki ya shigo garin Katsina. Mu'az wanda ya je ɗauko shi, shi ke tuƙi yayinda shi kuma ke bin garin da kallo yana ji a ransa babu abin da ya fi kewa a ciki kamar Haulatu. Ƴan kwanakin da ya yi a ƙasar waje, ya samu ya yi haske sai ɗan rama kaɗan wanda rashin ji da ganin masoyiyar tasa suka haifar. Babu wani abu da ya yi mishi dadi a tafiyar idan ka cire hotunanta da yake kallo ya ke jin ɗan sanyi a ruhinsa. Ya yanke zai je har gidan Maama, idan ta kama zai kai gwuiwoyinsa ƙasa akan kawai ta bar shi ya yi tozali da Haulatu, ta bar shi ya ji koda muryarta ne har ta yi mishi murmushin nan mai wanke zuciyarsa. 


"Gidan Maama za ka kai ni."


Mu'az ya ji maganar kamar daga sama don ya ma fidda ran za su yi wata hira da Sadaukin tunda gaba daya ba su yi wata magana mai tsawo ba, ya kuma kula kamar akwai abin da ke damunsa. Sai dai maganar da ya yi ya ankarar da shi damuwar don haka ya yi murmushi. 


"Idan dai Haulatun Hajja ka ke son gani, tana cikin gida. Ta dawo jiya."


Ya ɗan ji nauyi amma ya basar. 


"Akwai kayan da zan so na kai wa Maama, amma muje kawai zuwa gobe sai na je."


Shi dai Mu'az toh kawai yace yana murmushi, wai shi za'a yiwa wayo kamar wani ƙaramin yaro. 

 

 Madadin su wuce ɓangarensu, sai ya ce ya tsaya a nan parking space na babban gidan. Ya ce Mu'az ya wuce masa da kayan can ɓangarensu shi zai je ga Baba Alhaji. Mu'az nan ma toh ne na shi, ya yi gaba, Sadauki ko kai tsaye ya nufi ɓangaren Hajja, ya sani shi mai laifi ne ya kuma shirya karɓar kowane hukunci daga Bebin tasa. 


***

  Fitowarta kenan daga kicin, sanye da tshirt fara da siket da bai matse ta ba pink. Sai ko ɗan ƙaramin ɗankwali pink da ta rufe gashinta. Ƙafarta sanye da safa, don Maama ta ce duk inda za ta shiga ya kasance da safa a ƙafarta. Kofi ne a hannunta wanda a ta dama quaker oat, ya ji madara har ya yi fari fat. Daidai lokacin ya shigo da sallamarsa. Muryar da har abada ba za ta gushe a kunnuwanta ba, da wani irin sauri ta kalle shi, ya yi kyau cikin farar tshirt da blue jeans. Yanda ta ke kallonsa haka shi ma ya ke ƙara mata kallon daga sama har ƙasa. Jin muryar Hajja na amsa sallamar gami da yi masa lale marhabin ya ankarar da ita, ta tuna ba sa shiri nan da nan ta yi sama da sauri-saurinta ba ta ko tsaya amsa kiran da Hajja ke mata ba. Ajiyar zuciya ya saki ya ƙarasa ciki. Umma da Safina sun je duba Maman Radiya da ba ta jin dadin jikinta. Fahima kuwa tun da yamma ta koma gidansu bayan mahaifinta ya zo Baba Alhaji ya roki alfarmar ya janye batun aure, ya dai amsa da toh amma babu wanda ya san meke ransa. Da kansa kuma ya yi umarnin ta shirya su tafi. 


"Yaya Sadauki sannu da zuwa. Ina yini." Fadin Zaituna da ke zaune a gefe fuskarta a sake. Shima da sakin fuskar ya amsa mata. Yana tambayar ko su Mama sun iso. 


"Sun ce suna dab da shigowa Katsina, nasan nan ba da jimawa ba za su karaso."


Ya jinjina kai. 


"Allah ya kawo su lafiya."


Suka amsa da amin. Zaituna ta kula dai hankalinsa na ga benen da Haulatu ta haye, kafin ta ce wani abu sai ji ta yi Hajja na fadin.


"Ka ji kuma wani tsohon gulma wajen yarinyar can, ta ishi mutane da zancenka amma yanzu ka zo ta wani kama hanya ta gudu. Ke Zaituna maza kira ta su gaisa."


Ta fadi ne don ba ta ga dacewar ya hau ba, ko babu komai a yanda Haulatu ta dauki wannan kyawun da hasken, zai kara zama hatsari a keɓewarsu a rumfa haka. Shi kuwa dama haka yake so, don haka sai ya yi shiru, Zaituna ta miƙe da sauri ta nufi saman. 


A lokacin Haulatu na falo ta yi shiru hankalinta gaba daya yana ƙasa, ta ga ya yi kyau abinsa amma kuma duk ya rame. Ganinsa da ta yi ya ƙara haifar da sabuwar ƙaunarsa a ranta. Koda Zaituna ta zo mata da batun ta je su gaisa, turo baki ta yi ta nuna ita ba ta son ganinsa. Zaituna ta dungure kanta.


"Ji gulma, matar da ke kwana kallon hotonsa. Malama umarnin Hajja ne, ko za ki nunamin ba ta isa da ke ba ne?" 


Idanun Haulatu cike da kwalla ta dube ta.


"Yanzu Sis, apart from duk abinda ya yi min, kina ganin ya dace na manta da komai da wuri har haka?"


Murmushi Zaituna ta yi karo na ba adadi.


"Ki yi hakuri, ya maki laifi. Amma ki duba ki gani, yanda ya ce mana fa, yanzun shigowarsa garin kenan ko ɓangarensu bai ƙarasa ba. Kuma ni na tabbata don ke ya shigo nan ɗin. Shi ma fa an masa laifi, an hana shi ganin abin da zuciyarsa ke so na kwanaki da dama, don Allah ki manta komai ki je. Ni na tabbatar komai zai wuce kin ji ko?" 


Da wadannan tausasan kalaman na Zaituna ta miƙe ta shiga daki, hijabinta mai kyau wanda Zaituna ta kawo mata matsayin tsaraba daga Malaysia, da kadan ya wuce gwuiwarta, hawa biyu ne da shi, dogo da kuma ƙara iyaka kirji. Fari ƙal. Ta fito ta sauka ƙasan. 


Ganin Hajja kadai ya sanya ta ji har ranta ya ɗan yi babu dadi. Kafin ta tambaya ko ya tafi ta ji Hajja na fadin.


"Ki je yace ki same shi inda ku ke hira tunda kin kwace min miji."


Ta yi gaba kawai ta bar Baba Saude wacce ba ta jima da shigowa falon ba da dariya. 


Ta iske shi zaune a rumfa sama kujera a farfajiyar gidan, hasken fitilu suka haska musu fuskokin juna tun ma kafin ta ƙarasa gare shi. A hankali take takawa har ta kai gefensa ta nemi wuri ta zauna. Kallonta kawai yake yi kamar ya samu waya a hannu. Sallamar da ta yi mishi ce ya sanya shi numfasawa sannan ya amsa. Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ce. 


"Kawai ki ce shirin zautar da Abeed Malumfashi ake yi, shi ne dalilin yi min rowarki? Bebi kar ki ɗauki alhakina. Ina sonki ina sonki, idan ya fi haka akwai matsala."


Ɗan runtse idanu ta yi kanta a ƙasa, tunda suke da Sadauki kalmar ina sonki ba dai ya firta ba amma kuma duka kalmominsa masu nuni ne da tsantsar so ɗin da ƙauna. Yau ga dukkan alamu dagaske ya je maƙura. 


"Ki yafemin, ni mai laifi ne. Na ji zafin hana ni ganinki da Maama ke yi, sai aka zo ke ma madadin ki ji tausayina, sai ki ka biye mata. Tunanina ya ba ni ko dai ba ki wani damu da ni ba ne? Sai na ji ke kanki kin ban haushi, na yanke hukuncin mu zauna haka babu wayar ko tuntuɓar juna zuwa lokacin da kaf duniya babu mai cikakken iko a kanki sama da ni. Amma ba zan iya ba. Na kasa, ba zai taɓa yiwuwa ba. Ki yi hakuri kin ji? Ko na durƙusa?"


Ta kalle shi, idanunsa sun kaɗa, muryarsa ta narke gaba ɗaya, ya yi wani irin taushi fiye da baya. Ba ƙarya duk abin da ya ce ta yarda har cikin zuciyarsa hakan ne. Don haka ta girgiza kai.


"Aa my heartbeat, ni ba na buƙatar ka durkusa min. Na yarda da duk abin da ka ce. Na yafe maka na hakura, ni ma ina roƙon hakan daga gareka."


Ya yi murmushi.


"Ba kya laifi. Naki da nawan duka na haɗe su ya zama ni kadai ke da laifin. Bebi kyau kike ko babu kwalliya. Kin sauya, anya ba ki fi ƙarfin Abeed ba?"


Ta harare shi kadan, ya lumshe idanu yana shafar sumar kansa. 


"Ki bari."


"Na bari." Ta amsa tana kauda kai. Sai a lokacin ta gaida shi da tambayar ko ya iso lafiya? Ya amsa mata ba tare da ya iya kauda kai daga dubanta ba. 


Dakyar dai ta lallaɓa suka rabu ya wuce don ya huta, babu sallah a kansa face sallar isha'i da ake kira yanzu. Har sai da ta shiga gida kafin ya juya ya fice shi ma. Babu jimawa da rabuwarsu, su Maman Zaituna suka iso gidan. Murna ya karaɗe a ɓangaren Hajja, Umma ma a sannan sun dawo. 


 Ranar dai kwanan farin ciki Haulatu ta yi ga waya da suka sha da Sadauki kamar za su cinye juna. 


***

 Biki na ta matsowa, ana sauran kwana uku ne baƙi daga Malumfashi suka iso da yawa. Ga mutanen Kaduna da Kano kamar ba lokacin karatu ba don yara ba su yi hutu ba. Amma an taru sosai, masu yaran kanana kuwa sun bari sai juma'a ranar da za'a fara bikin za su iso. Ɗinkunan fitar biki babu ɗaya da ya fita daga hannun Umma, Abba Ridwan ne ya dauki wannan nauyin, shi da Momi Nuratu, sam ba ta yiwa Haulatu kallon suruka sai ƴarta. A sannan tuni an kawo lefe na gani na faɗa, saiti uku da kayayyakin ga kuma na Uwa da aka yi daban. Komai na cikinsa abin burgewa. Sadauki a zuwansa Dubai ya ƙara yo siyayyar abayoyi da sarƙa sai jakunkuna, ya kaiwa Maama bayan Momi Nuratu ta gani ta sa albarka. 


 An yiwa Haulatu komai a fannin jere, babu abin da ba'a zuba ba, nata kawai shiga gidan. Momin Mu'az da Mamin Khaleefa ko Allah ya sanya alheri na lefe ba su shigo sun yi ba. Akan hakan sai da Hajja ta yiwa mazajensu tas kan su ja wa matansu kunne kar su kawo rarrabuwar kai a zuri'a don ko yaransu ma ba su shigo ba idan ka cire mazan da ba su ko damu ba. 


 Aikuwa kowaccensu ta kwashi kashinta a hannu don Baban Mu'az har kusan sakin Momin Mu'az ya yi akan furucin da ta yi mene ne ya yi saura da zai burge ta a bikin ƴar bariki. Wannan ne ya yi sanadin da ya ce ta tafi gida amma bai kai ga sakinta ba. Ita kuwa Mamin Khaleefa da yake ba ta saba ganin ɓacin rai sosai daga Barr Dawud ba, sai ta yi shiru da ta ga ya rufe ta faɗa ganin  kamar tana neman zagin Hajja wai tana haɗa husuma tsakanin mata da miji. Dole ta ja baki ta tsuke tana tunanin ya aka yi har ya iya ɗagamata murya? Kada dai aikin da take a kansa ya bar ci kwata-kwata? 


***

 Biki Buduri....

Ku ƙara hakuri, in sha Allah ko post biyar ba zai kai ba. Labari ya na dab da ƙaraye.

Ranar Alhamis aka sanya Haulatu a lalle. Umma har hawayen farin ciki ta fitar. A nan farfajiyar babban gida aka yi komai da yammaci aka ƙare. Sosai Amaryar ke fama da ciwon kai, kwanakin ba ƙaramar gajiya ta yi ba. Zagayen zuwa ƙunshi da kuma gyaran gashi ga kuma wani gyara na musamman da Maama ta zo takanas aka yi mata wanda dama shi an bar shi ne sai dab da biki. A wannan daren duk yanda Angon ya so su yi magana bai samu ba, bai takura mata ba. 


Da wuri ta shige ɗakin Hajja inda babu mai takura mata ta kwanta bayan ta sha magani, ai kuwa ko mintuna biyar ba ta yi ba ta yi bacci. Ba kuma ita ce ta farka ba sai washegari da Asubahi. Nan ma Hajja ce ta tayar da ita domin yin sallah. Sai a sannan ne ta ji kan nata ya saki, babu wani ciwo. 


Ranar kuwa ɗaurin aure ne da yini. Wannan yasa tana kammala yin kari, aka ce ta faɗa wanka. Kamar ta yi kuka ta dubi Maman Zaituna. 


"Mama ba sai anjima ba?" 


Maman Zaituna ta yi murmushi. 


"Wane anjima kuma Haulatu? Ke da yau za'a shafa fatiha? Aa, je ki maza ki yi wanka ki fito ki yi shiri. Mai maki make-up ta fi awa da zuwa."


"Au, sai ma an lallaɓata za ta yi? Toh kodai a fasa ne a ɗaura da ni?" 


Cewar Hajja dake zaune a falon wanda cike yake da iyaye, sai ko ita Haulatun da Maman Zaituna ta sa a gaba ta yi kari a kusa da ita. Aka yi dariya. Ita kuwa sai ta miƙe don yau babu baki balle ta rama zolayar Hajja. 


Tana shiga ɗakin nan ma ta haɗu zolayar su Safina, wai sai wani murmushi take yi baki yaƙi rufuwa duk murnar ɗaurin aure. Ita dai ba ta ce musu uffan ba ta ɗauki babban tawul ɗin wankanta ta shige banɗaki. 


***

 "Khaleefa, wai lafiyarka ina magana tun ɗazu ka yi min shiru?" Hafsat ta faɗi ranta a ɓace tana daga tsaye riƙe da ƙugu yayinda shi kuwa ya maida hankali ga gyarawa ɗiyarsa kwanciya a cikin net ɗinta. Sai da ya kammala ya miƙe sanye da jallabiyarsa da nufin fita daga ɗakin zuwa nasa don yin wanka. Da sauri ta sha gabansa. Ya dube ta da idanunsa masu tsananin kwarjini da ya sanya ta duban gefe ta soma faɗar abin da ke ranta. 


"Wai mene ne haka ka ke yi min? Gaba ɗaya tun sadda na haihu ka bi ka sauya, matuƙar ba ni na je maka da sunan buƙata ba, ba ka ko damu ka kalli inda nake ba. Na gaji Khaleefa. Ni ma fa mutum ce lafiyayya."


Daga cikin abin da ya tsana a wurin Hafsat, har da sunansa na kai tsaye da ta ke kira, tuni wani suna da ake kiran masoyi da shi ko kuma yi mishi alkunya da sunan ɗansa babu shi a zamantakewarsu. Ga ƙazantar da ta ninka ta baya. Ayyukan da ta jibgawa ƴar yarinyar dake mata aiki sun mata yawan da take kasa yin komai yanda zai fita fes. Tsaftar jikinta da ta ke mayar da hankalin a baya ma sai a hankali, idan ka cire rashin kula da tsaftar sai ko wasu sinadaran da ya ji babu a tattare da ita wadanda suka rage gamsar da shi tun bayan da ta haihu. Sam ba ya cikin yanayin buƙatarta a kwanakin nan, ya gaji da maganar tunda abin ya ƙi ƙarewa. Daga Mamarta har ta sa mahaifiyar babu wanda ke goyamasa baya sai ba da haƙuri da batun nan gaba ƴan aikin za su goge. Babu mai nuna mata kurenta. 

 Don haka sai kawai ya gifta ta zai wuce, ta ƙara riƙo hannunsa, dole ya tsaya gami da juyowa ya dube ta. 


"Kar ki ɓata min rai Hafsat, kin fi kowa sanin ban da lokacin shirmenki yanzu ko?" 


Cike da takaici ta tari numfashinsa. 


"Haƙƙina fa Khaleefa? Wane ɓangare na shari'a ne ya ba ka damar tauye min?"


Ya ɗan runtse idanu. Yana son ce mata ni haƙƙoƙi nawa ki je tauye min? Fitar da ki ke ba da iznina ba, ko kuwa abincin da ba kya taɓa shiga ki girka sai dai wasu su yi? Sai dai ba shi da isasshen lokacin tunasar da ita baƙaken maganganun da take yaɓa masa duk sadda ya buɗe baki da zummar amayar da abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya, don haka ya sauke ajiyar zuciya ya dube ta bayan ya danne ɓacin ransa. 


"Na ji, ko mene ne ki bari idan na je ɗaurin auren ɗan uwana na dawo sai mu yi magana."


Ta tsuke baki. 


"Ok, ni motata ba mai, ina son kuɗi zan zuba." Ta yi tambayar ba don ba ta da shi ba, sai don kawai tada zaune tsaye. 


Ba ya son jan magana don haka kawai ya ce zai ba ta idan ya kammala shiri. Daga nan ya fice zuwa nasa ɗakin yana kara ji a rai babu abin da zai hana ya ƙara aure face wani ikon na Ubangiji. 


Koda ya shirya ya fito falon, bai ko shiga ɗakinta ba sai kudi da ya bar mata a saman dinning ɗinsu, Affan dama yana wajen Mami, tun sadda Hafsat ta haihu ya koma can don ta ce ɗawainiyar yaran zai mata yawa. Abin ya so zame musu rigima dalili kenan da Maminsa ta raba gardamar ta ce ya dawo gidanta, Hafsat ta fi shi gaskiya. 


Ko irin wannan yana baƙantawa Khaleefa rai yanda ba shi da ikon yanke hukunci a gidansa, matuƙar bai zo ɗaya da ra'ayin Hafsat ba to fa zai samu matsala daga Mami, a dole ya ke haƙura. 


***

  Haulatu ta ci ado cikin leshi fari ƙal sai mayafi da ta yafa a kanta. Fuskarnan ta sha kwalliyar hoda da jan baki, kyan da ta yi za'a iya cewa ɓata lokaci ne gurin fayyace shi. A lokacin ƙarfe ɗaya saura, duka maza na gidan da ma waɗanda suka zo daga nesa sun wuce masallaci sallah da kuma ɗaurin aure. Mata kuwa ana ta hidima a gida, wuri ya cika babu matsaka tsinke. Ba ɓangaren Hajja ba, ba kuma can na Baba Alhaji da su Baba Dakta ba. Amarya Haulatu tun da ta ƙume a ɗaki ta yi shiru jikinta kuma ya yi sanyi. Ba don komai ba sai tunawa da irin wannan rana wanda babu wani tsayayye daga dangin mahaifinta. Tabbas za ta iya rayuwarta babu su ɗin, dama kuma babu ɗin, sai dai tana jin zafi ta yadda burin kowace ɗiya ya kasance mahaifinta shi ke ba da aurenta, amma ita na ta mahaifin bai da irin kwalliyar da za ta yi ado da shi har ma ta bugi ƙirji a ko'ina ta ce za'a yaba. Ba ta san hawaye ta ke fitarwa ba sai da ta ji muryar Zaituna a kusa da kunnenta tana rarrashinta. 


"Kar ki ɓata kwalliyarnan please. Mene ne abin kuka a yau da ya kamata ki yi farin ciki? Ki yi hakuri ki bari."


Sai ta ji kamar ta ƙara mata dalilin kukan ai kuwa ta faɗa kafaɗarta ta shiga rera shi. Tun Zaituna da su Radiya na rarrashi, har da suka ga ta ƙi haƙura aka kira Maama. Ita ce ta bada umarnin duk su fice, a sannan ne ta hau ban baki, ƙarshe da dabara ta ji dalilin kukan. Har Maama sai da hawayen ya tahomata ta yi saurin dauke su kada ta gani, ta tabbatar idan ta gane ita ma abin ya sosa ranta, za ta ji har a zuciya cewa ita ɗin fa dagaske abar tausayi ce. 


  "Kar ki yarda wannan tunani ya ɓatamaki murnarki a wannan rana. Kowa fa da kalar ƙaddararsa Haulen Hajja, ke musulma ce da ki ka yi imanin Allah zai jarabce ki, jarrabawar nan kuma komai muninsa za ki karɓa da hannu bibbiyu hakazalika mai kyau. Ya yi maki ni'imomin da bai kyautu ki yi hawaye akan wannan ba, wasu fa su na can, auren ma ba ta hanyarsa aka haife su ba. Wasu kuwa an haife su da auren, amma hakan bai sa rayuwarsu ta gurɓace ba. Ke kuma Allah ya tsarkake ki, kin samu sauyi a rayuwa irin wanda ko a mafarki ba ki taɓa hasasowa ba. Kukan na mene ne toh? Shi ma mahaifin naki ai ba watsar da shi aka yi ba, shi ya sallama ki, ban da haka, mu ba ƙananan mutane ne ba da har za'a tashi auren ƴa a kasa tuntuɓar mahaifinta. Gatan da za ki daure ki yi ga mahaifinki shi ne kar ki taɓa gajiyawa da bin sa da addu'ar neman shiriya, Allah yana sauya baƙi zuwa fari. Duk fa abubuwan nan da Babanki ya ke aikatawa ko kuma ya aikata, Allah ba ruwansa, idan ya yi tuba cikakke, sai ya yafe masa har ma ki ga ya samu fadar da wani da ya yi shekaru cikin ibada bai same ta ba. Domin rahmar ta Allah ce. Kar na ƙara ganin kin tada hankali kan abin da ba ki isa ki sauya shi ba kin ji ko?"


A hankali ta gyaɗa wa Maama kai, zuciyarta har ta yi sanyi ba kamar a farko ba. Bayan ta gama lallaɓata, a karshe dai kwalliyar sai da aka ƙara gyara ta. 


***

 Misalin karfe biyu saura na rana, dubban mutane abokan arziki suka shaida  ɗaurin auren Abeed Ridwan Malumfashi da amaryarsa Haulatu Ibrahim Khalil. Daidai lokacin Haulatu na kan darduma, ta idar da sallar Azahar, guɗa ya karaɗe sashin Hajja, ga kuma su Safina da sauran ƴan matan dake ɗakin ciki har da waɗanda a baya kallo ma ba ta ishe su ba, yanzun kuwa ta samu mutuncin darajar Sadauki. Da yawansu tun ma ba ta san ya gidanta yake ba sai santi suke suna bada labari. Cikin waɗanda ke wurin har da su Zuhra ƙanwar Sadauki, sosai ta shigo ake damawa da ita kamar wasu sa'anninta. Dama can ba ta da wata hujja mai ƙarfi na ƙin Haulatu. 


Mikewa ta yi tsam ta tada kabbara ta kawo nafila raka'a biyu, dole suka rage hayaniyarsu, ta jima cikin sujjada tana addu'o'in nemawa aurensu albarka da roƙarwa mahaifinta gafara da shiriya, har ma da ingantacciyar rayuwa da ma gamawa da duniya lafiya ga Ummanta sannan ta ɗago ta yi sallama. Tana miƙewa tsaye suka shiga guɗa da yin kanta da shewa da zolaya iri-iri. Ita rabonta ma da Angon nata tun safiyar juma'ar da ya kira suka gaisa, ba su ma samu yin wata magana mai tsayi ba suka yi sallama zai je hotel ɗin da suka sauke baƙinsa da suka zo daga Abuja. Wayar kuwa tun a lokacin ma ta kashe ta ba Hajja ajiya. 


 Manyan iyayen ne aka shigo aka ja ta zuwa falon ƙasa, babu hawaye ko ɗigo a fuskarta, sai dai sunne kai da ta ke faman yi. Jikinta duk ya yi sanyi, haka aka shiga hotuna bayan an zaunar da ita an yi guntuwar nasiha da addu'a. Ana cikin hotunan ita Haulatu ma sai neman inda za ta ga Ummanta ta ke yi, sai da ta gaji ta sa Radiya taya ta nema. Lokacin ne shi ma ango da abokansa suka shigo. Tsoffi aka shiga rangaɗa guɗa tun daga waje da kuma kirari. Sai da ta ji ƙirjinta ya buga jin da ta yi ana kira Angon Haulatu. Daidai sadda suka shigo a hankali ta ɗaga kanta ta kalle su. Khaleefa da wani abokin Sadaukin ne a gaba, sai shi da ke a bayansu. Ya shigo fuskarsa sai wani annuri ta ke yi yana zabga murmushinsa mai bayyana fararen haƙoransa a waje, mutumin da takan jima ba ta gan sa da hula a kai ba, yau kam ya sha hularsa Tangaran. Farar shaddarsa sai wani sheƙi ya ke yi. Shi ma idanunsa ya faɗa cikin nata, sai da ya ji tsigar jikinsa na tashi, kusan a tare suka janye ƙwayoyin idanunsu daga na juna. 


"Mrs Abeed, me ku ke ci na baka na zuba? Da kai da kaya duk mallakar wuya ne fa."


Ta tsinci muryar Zaituna na mata raɗa, ai kuwa ta yi saurin sauke kanta tana wasa da zoben da Sadauki ya ba ta murmushi dauke a saman fuskarta. Zaituna ta mike daga kusa da ita ta ja baya tana dariya har tana karo da mutum, da saurinta ta juyo, suka hada idanu ya yi mata murmushi. Sai itama ta maida masa martani.


"Abu Affan, yi haƙuri." 


Har wata ajiyar zuciya ya sauke. 


"Ba komai, please ki dinga rufe jikinki. Na kula ba kya son yafa mayafi." 


Yana faɗin haka ya yi gaba ya bar ta da binsa da kallo baki sake. A hankali ta kuma ɗan bin jikinta da kallo, sai kuma ta ɗan tura baki. Toh wai shi mene ne ma laifin shigarta? Atamfarta chiganvy ta sha aikin stones a ƙirjin, ya fiddo surarta ta kuma yi kyau ga kwalliyar da aka yi mata a fuska, ta ɗan kalli sauran dake wurin babu mai mayafi a ƴanmatan sosai sai ko kalilan a ciki. Toh don me zai matsa mata? 


'Ko kuma kishinki ya ke ne?'


Wata zuciyar ta jefamata tambayar da har sai da ta murmusa kafin ta kuma ƙaryata tunaninta. Toh me Yaya Khaleefa zai yi da ita? Ita ma ai ta bar soyayya, ba ta kuma son ta yi auren zumunci yanzu. 


'Har da Yaya Khaleefa?' Ta ƙara jin tambayar a cikin kwakwalwarta, a sace cikin cunkoson jama'a ta ƙara dubansa, hankalinsa yana can suna gaisawa da Amarya, kishiyar Momin Mu'az. Tabbas Khaleefa ba shi da makusa ko kaɗan. Miji ne da kowace mace za ta yi burin samunsa. Kafin ka ji mai zaginsa guda ɗaya, ka ji masu yabonsa fiye da goma a fannin halayya da ma sanyin hali. Matsalarsa dai bai wuce miskilanci ba wanda a yanayi na surutu irin nata ba ta jin za ta iya sabo da shi. 


Can kuma ta ji haushin kanta da kunya, to mene ne ma abin wadannan tunanikan alhalin ba wani abu ya furta mata ba? A ɓangaren Haulatu wacce kanta ke ƙasa, ba zato ta ji mutum a gefenta saman kujera har cinyoyinsu na gogar juna. 


"Yauwa ko kai fa, bari a yi muku hotunan." Maganar Maama ta ji, ya ba ta tabbacin ita ta jawo shi daga wurin mutanen Malumfashi wadanda gaisuwar ta ƙi ƙarewa. Suka haɗa idanu karo na biyu, sai ta yi saurin kauda kai. Shi ma basarwa ya yi ya maida hankali ga mai hoton na musamman da aka ɗauko a wannan rana. Mu haɗu gobe in sha Allah. Saura post guda.....😂


"Na fa gaji da hotunan nan, a bar ni na ji ɗumin matata." 


A hankali ya yi furucin ba tare da ya ko kalleta ba, ita kaɗai ta iya jin me yace saboda tsabar kusancinsu, ta kuwa ƙara ji kamar ta nutse a wurin. Umma ma ta zo sun yi hotuna, ashe can ta maƙale a gefe tana hira da Maman Radiya. Har aka yi aka gama babu ƙeyar Zaid, an ce dai ya je ɗaurin auren, bayan an kammala ya taya Angon murna ya fice. Nan ma duka an fi zaton umarnin Mahaifiyarsa ne. 


Haulatu na ji su Radiya na gulmar bayan sun koma falon sama, ba ta ce musu uffan ba. Ina ruwanta da wani Zaid a yanzu? Babu kamar ma tunda ta riga ta zama matar Abeed Sadauki. Wani murmushi ta yi da ba ta shirya ba. 


Da misalin karfe biyar, gidan Maama suka wuce don ya fi kusa da ɗakin taron da za'a gudanar da bikin,  ita da su Safina da sauran ƙawayen makarantarsu su uku. Maama ba ta biyo su ba asalima ta yi gaba can wurin taron don kula da tsarin komai. Ta ƙara sabon wanka ta yi alwala, wata sabuwar kwalliya mai make up ta yi mata na tafiya gurin yini wanda za'a yi a eventcentre. Dinnerparty wanda Sadauki ya shirya kuwa sai a washegari za'a yi.

Wannan karon shigar kayan saƙi ta yi ruwan ƙasa. Ta fito tsaf da ita, sosai kwalliyar ta amshe ta. Duka wannan zaɓen na Maama ne. 


"Masha Allah TubarakAllah. Kin yi kyau sosai sosai Mrs Abeed."


Faɗin Safina tana murmushi, ita ma ta sha nata adon cikin nasu kalar ankon na atamfa su ma ruwan ƙasa da surkin baƙi. Sai da suka yi sallar Magriba sannan suka yi haramar tafiya, motoci biyu ne suka zo don tafiya da su. Idan ka ɗauke Siena na gidan Maama wanda zai kwashi ƙawayenta, sai ko motar Sadauki. Yana zaune a kujerar baya, sai ko wani ɗan uwansu daga Malumfashi mai suna Bilal dake jan motar, Safina ta shiga gidan gaba bayan ta gaishe su, sauran kuwa gaba daya suka ɗuru a ɗaya motar. Shaddarsa ruwan ƙasa amma bai ciza kamar na Haulatu ba. Bayan sun soma tafiya ta ɗan dube shi. Dama idanunsa na kanta, murmushi suka sakarwa juna cike da yaba yanda kowannensu ya burge ɗan uwansa. Murya a sanyaye ta gaishe shi ya amsa mata a nutse. Bai yi kowane yunƙuri ba idan ka ɗauke yatsun hannunta na hagu da ya lalubo ya harɗe cikin nasa. Kusan lokaci guda suka sauke numfashi. Ya lumshe idanu yana ɗan matsa tafin hannun nata cikin nasa a hankali kuma yana ɗan saki, sai da ta shiga kokarin zame hannunta kafin ya haƙura ya bari, kansa ya jinginar jikin kujera ya zuba mata narkakkun idanunsa. Sautin waƙar  Salim smart na So kenan shi ne ke tashi a motar. Hankalin Bilal da Safina ma ba ya kansu, ita tana amsa wayar wasu abokan karatunsu masu neman kwatance, shi kuwa Bilal hankalinsa na ga tuƙi. Har suka ƙaraso Bilal ya nemi wuri ya yi parking, suka soma fita sannan Ango da Amaryarsa su ma suka fito abin su tsaf suka jera zuwa ciki. Kiɗa na musamman mai taushi aka sanya, ƙawayen Amarya su biyar, Safina ita ɗaya a gaba tana ɗan rangajinta sai sauran suka jeru bibbiyu. Kowa a gurin daga mai hoto daga zaune saboda an tsara babu shiga ɗaukar hotuna, sai masu murmushi da wangale haƙora tsabar burgesu da suka yi. Momin Mu'az sai wani murmushi take, ko babu komai ta raba ɗanta da mugun iri a cewarta yayinda Mamin Khaleefa ke kula da ita, sai ta tsargu, wato dai Momin Mu'az ba ta taya ta baƙin cikin rashin Sadauki da ƴarta ta yi kenan? Kodai dagasken ne kamar yadda ƴan uwanta ke yawan yi mata hasashen da biyu take zaune da ita? Ranta ya ɓaci amma sai ita ma ta zaɓi nuna wa duniya ba ta baƙin ciki da abin duk da dai can ƙasan ranta har a lokacin haushin Nuratu da Ridwan har ma da ɗan nasu Sadauki na cin zuciyarta. 

  Jannat ko ƙeyarta babu a wurin, Fahima kuwa dalilin rashin ganinta bai wuce takunkumin fitar da Mahaifinta ya saka mata ba, tun sadda suka kai shi gaban Baba Alhaji akan ya yi haƙuri kar ya aura mata mai shaye shaye ya ji zafinsu, a ganinsa mugun raina hankalinsa a ka yi har a tsaya nuna masa iko akan gidansa. Dakyar ita ma Haj Hadiza ya bar ta zuwa bikin don sai da suka yi fada sosai, karshe yace ita dai ta je amma Fahima babu inda za ta taka. Idan kuwa Fahima ta fita to ƙarshen zaman Haj Hadiza a gidan ya zo kenan. Kuma aure dia ɗan ɗan uwansa babu fashi sai an ƙulla shi, idan an ɗaura ta mutu. Da wannan baƙin cikin ta halarci bikin Haulatu, kowa ya gan ta yasan akwai abin da ke damunta. Ita yaƙen ma ta kasa, tana zaune kawai ta zubawa Haulatu da Sadauki idanu tana ji inama Fahimarta ce da wannan matsayin. Ita dai auren ma ba yabo ba fallasa, ba ta san me take ji a kan aurensu ba. Babu ƙin babu kuma son. Anti Mabruka na gefe kujera guda da wasu hamshaƙan ƙawayenta, kallo ɗaya idan ka yi musu za ka fahimci masu gidan rana sun zauna a nan. Sai tau a cingam suke suna kallon kowa ɗaɗɗaya. Zaituna ce tare da Maimuna sai Zuhra  da Fa'iza suka dinga bi tebura suna rabon ƴar jaka mai kyau na souvenir. Ɗauke da notepad mai biro a gefe sai ko madaidaicin mug mai murfi da aka rubuta Best Wishes, Abeed & Haulatu a jiki sai ko kwanan wata. 


Abin ya ba mutane da dama mamaki don ba a san da kayan rabon ba. Ta yi su ne kaya guda, da kudinta da wanda mahaifinta ya turo mata, kusan shi ne dalilin zuwanta da wuri ƙasar. A Abuja ta bayar da aikin komai, sai kuma ana gobe za'a fara bikin saƙon ya iso kaya guda. Kai tsaye gidan Maama ta sa aka kai, Maama ta ji dadi sosai ta kuma yaba da wannan kokarin na Zaituna, sai da suka ware na iyaye da waɗanda suka cancanta kafin su ƙaraso nan. 


Komai ya tafi a tsari na wayayyu kuma ƴan boko. Koda ta ƙarasa ɓangaren inda su Khaleefa ke zaune, haka ta ajiyewa kowannensu a kusa da shi. Yana riƙe da ɗiyarsa Iman wacce a yau kam ƙamshin turare kawai ke tashi a jikin yarinyar, an mata kwalliya an naɗe ta a shawul. Hafsat kuwa na can zaune tare da su Ihsan yayar Fahima da wasu sa'anninsu. Da murmushi ta dube shi bayan ta ajiye kafin ta maida duba kan bebin, shi kuwa hankalinsa na kanta. Ta yi mishi kyau ainun cikin atamfarta ruwan hoda mai haske da kuma duhu wanda aka ƙawata ɗinkin riga da siket ya zauna ɗabas a jikin. Sai ko mayafinta madaidaici na chantily shi ma pink. Hannu ta kai ta ɗan shafi kumatun Iman tana wani murmushi sai kuma ta miƙa hannuwa. 


"Abu Affan, please ba ni ita." Bai ko san sadda ya miƙa mata ba. Ta sumbaci goshin yarinyar har tana ɗan shafa mata jan baki sai ta yi saurin gogemata da yatsa tana ambaton kalmar sorry. Daga nan ta dubi gefenta inda ta hango Zuhra ta taho, umarni ta ba ta akan ta ɗauki sauran kayan rabon da ta bari a kusa da su Yaya Khaleefa su je. Suna tafe tana nuna mata inda za ta kai. Ita kuwa Zuhra na ajiye musu. Khaleefa ya kasa ɗauke idanu a kanta, duk inda ta je ta dawo sai ya bita da kallo yana ji dagaske har zuciyarsa yana ƙaunarta. Ya yi amanna akan abin da yake ji ba na wasa ba ne, ba kuma wai na kwanaki ne ba kawai a bar shi. A'a, yanayi ne na ƙauna da soyayya da kuma fatan ya mallake ta a matsayin matarsa. 


Duka wannan abu dake faruwa a kan idanun Hafsat wacce tun lokacin da Zaituna ta isa ga mijin nata take kula da su, har ma murmushin da Khaleefan ke bugawa yana bin su da kallo sai da ta lura. Har wani jiri ta ji yana kwasarta daga zaune. 


"Ke, je ki ki karɓomin ƴata a hannun waccan uwar ƴan iyayin." 


Ta ba ƙanwarta Fadila umarni, ita ko da ta maida hankali ga cin abinci, sai a lokacin ne ta lura da abin da ke faruwa. Zaituna tuni ta koma mazauninta tana faman rainon Iman tana sauraron MC da ke ba da umarni akan ƙawayen Amarya da abokan Ango su fito fili. 


"Meyasa za'a karɓo ta? Wani abun ya faru ne?" Tambayar da Fadila ta jefa mata kenan. Ita kuwa ta watsa mata harara. 


"Babu ruwanki, kawai ki karɓo min ƴata." 


Taɓe baki ta yi tana turo baki.


"Gaskiya ki bari na kammala cin abinci wallahi. Ni ba zan iya tashi ba."


Aikuwa tashin da ba ta yi ba kenan, Hafsat ta shaƙa iya wuya, ba kunya ko ta mike da kanta ta zagaya har inda Zaituna ke zaune tare da su Fa'iza waɗanda suka suka kammala rabo an nutsu ana kallon diramar da MC ya ce a yi, wato rawa tsakanin ƙawar Amarya da abokin Ango, duk wanda ya ƙi yi kuma zai yi liƙi ga abokin rawarsa. Lokacin riƙon Iman ɗin ya koma ga Fa'iza, ita a sannan ma ta fidda rai ga samun Khaleefa har ta tsaida mijin aure cikin manemanta. Kawai sai ganin Hafsat suka yi a kansu, ta ja ta tsaya tana mai sa hannu ta karɓi Iman ɗin a hannun Fa'iza har tana kokarin fisga da ya yi sanadin yarinyar ta firgita ta canyara kuka.


"Haba Anti Hafsat? Don Allah ki yi mata a hankali." Cewar Zaituna, duk da ba duka abin da ta ce ɗin ya shiga kunnuwan Hafsat ba sakamakon kiɗan da Dj ya saki, amma hakan bai hana Hafsat watsa mata kallon banza da harara ba sannan ta yi gaba. Zaituna da Fa'iza suka dubi juna kawai. Ita Fa'izar ma har da jan tsaki. Koda ta yi wani furucin, Zaituna sam ba ta ji ba don hankalin ya koma kacokam ga sowar da wuri ya ɗauka dalilin karin da wani abokin Sadauki, Jameel ke zubawa Rumanatu da ke rawa shi ko da ganinsa irin miskilan nan ne wadanda rawar bai dame su ba. 


Ɓangaren Amarya da Angonta kuwa, shi gaba ɗaya ma ya gaji da abin. Sai raɗa yake mata akan ya dace a tashi haka. Tana murmushi ta ɗan dube shi. Ita ma cikin ɗan raɗan yanda zai ji ta ce.


"Wannan fa duk mu ake tayawa murnar aure, don Allah ka ƙara haƙuri, ai an kusa tashi."


Ya jingina kansa jikin kujerar a saitin kunnenta ya ce. 


"Haƙuri ki ke ban? Wani abu na ce maki zan yi? Ko wani abun ki ke so?"


Ta kauda kai tana maida duba ga MC wanda ya yi umarni ga Dj ya tsaida kiɗa. 


"Don Allah ka bari mana." Ta furta a hankali kamar mai shirin kuka da narkakkiyar muryar da ya ruɗa kan Sadauki. Daƙyar ya samu ya saita kansa sannan ya ce.


"Na rantse ki ka ƙara min magana da wannan yanayin daga nan babu inda za ki zarce sai gidana. Idan ya so a biyo ki da kayanki."


Maganar MC ce ta katse Haulatu daga cewa komai, umarnin su fito fili yake ba su. Sadauki ya ji kamar ya buge shi. Fadi yake. 


"Shi kuma wannan kamar wani ubanmu sai mulki da mallaka ya ke nuna mana."


Ita dai ba ta tanka ba sai murmushi a ciki-ciki. Ba ta son ta yi abin da zai sa ya yi wani yunƙurin don haka ta ja baki ta tsuke. 


Koda aka tashi kusan su ne ƙarshen tafiya don sai da Sadauki ya yi bankwana da wasu abokansa da suka zo tun daga Lagos, a gobe da Asuba zasu kama hanyar Kano daga can kuma su hau jirgin dare da zai maida su.  Har gyangyaɗi ta fara, ba don ma Safina na motar su na ɗan taɓa hira ba da babu abin da zai hana baccin ya yi awon gaba da ita sosai.  


Koda suka isa shi kansa Angon a gajiye yake amma fa hakan bai hana shi ɓata lokaci da Amaryarsa ba don Safina na ficewa shi ma Bilal ya bar motar ya fita don ba su wuri su yi sallama. Ta kai hannu za ta buɗe murfin ya sa hannunsa ya jawo ta gaba ɗaya ta dawo jikinsa har suna jin hucin fitar numfashin juna, da sauri ta sa tafin hannunta na dama a saman ƙirjinsa, a hankali kuma ta soma kokarin zamewa ya sa hannu ɗaya ya dafe yatsunta. Ta kasa motsi kwakkwara, zuciyarta na umartarta da ta janye daga jikinsa sai dai gangar jikin ta kasa mara mata baya. Ba ta san ya aka yi aka haihu a ragaya ba, sai dai kawai jin da ta yi sun faɗa ruwa tsundum, ganin abin na neman zarce gona da iri ne ya sanya ta saurin janye fuskarta ta kuma ja baya, shi ma babu wani karfi a jikinsa sai ya jinginar da kai yana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Kasa furta sai da safen ta yi don haka a hankali ta sa hannu ta buɗe murfin motar, za ta fita ya ɗan riƙe yatsunta. Murya kamar ba ta Sadaukinta ba ta ji ya ce. 


"Allah ya tashe mu lafiya."


A hankali ta zame yatsunta daga nasa ta amsa da amin, amsawar da babu lallai ya fita yanda ya dace. 


Ba ta bada fuskar a ja ta da ƙananun tsokana ba amma ina, duk da haka ba ta tsira ba wajen su Safina da Radiya. 


Washegari da asubar fari bayan Haulatu ta yi sallah, Umma ta ja ta zuwa ɗakin da babu kowa ciki sai su biyun. Nasiha mai ratsa jiki ta shiga yi mata na ƙara nusar da ita matsayi da girma na miji. Tun Haulatu na dannewa har hawayenta ya shiga fita. Sun jima sosai kafin a ƙarshe Umma ta bi ta da kyawawan addu'o'in shiga gidan aurenta a sa'a ta kuma yi mata nuni da muhimmancin riƙo da sallah, da karatun Alkur'ani mai girma da kuma addu'a. 


A ranar dama lakca ce za'a yi akan aure sai kuma dinnerparty da Ango ya shirya wanda daga can zai wuce da Amaryarsa.

No comments