SAKAYYAH Book 3 PAGE 8

 


                         By

*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 8*


                    NA




*Aysha Aliyu Garkuwa*




*GARKUWAR* taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*


Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. 


Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.


Ga masu bu?ata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 08069423567 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ?anana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya ku?inki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ?ananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ?atamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ?asar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune????sayan na gari meda kudi  gida.



  GARKUWAR MA'AURATA





Tana wani sassayan tari, wanda take ta son danneshi, cikin sauri suka ?ara sa cikin ?akin da sauri Dr Jameel yace.

“Ha'a ya dai?”.

Momy ce ta ?ago kanta tare da cewa.

“Kamar ?waruwa tayi”.

Cikin tsoro gami da damuwa Moddibo ya kalli Dr Jameel kana yace.

“Jifa tari take ba matsala ko?”.

Kai Dr Jameel ya girgiza tare da fa?in.

“A'a ba matsala bari nasa akawo mata wani magani tasha tarin zai bari”.

Ya ?are maganar tare da kiran Line-line dake cikin wayar ya kira Pharmacy ya fa?a musu su kawo maganin jim ka?an Norse ta kawo maganin kar?a yayi ya bata tasha cikin ikon Allah atake tarin ya bari.

Sai alokacin ta samu nutsuwa numfashi ta fesar kana ta maida kallonta kan Abualeey tare da cewa.

“Abu ina yini”.

Cike da kulawa yace.

“Lafiya lau ya jiki?”.

Ahankali tace.

“Da sau?i ”.

Kai ya gya?a tare da fa?in.

“Masha Allah Allah ya raya abinda aka samu”.

Kar?an Jaririn yayi tare dasa mishi albarka kana ya mi?awa Waziri da Galadima dai-dai lokacin kuma kira ya shigo wayar Khausar Momy anutse ta duba ganin sunan Hajja Nana yasa ta ?auka muryanta cike da farin ciki tace.

“Hajja Nana Alhamdulillah anyi Theater ancire ?a namiji”.

Cikin jin da?i da sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace.

“Alhamdulillah amma tana lafiya ko?”.

”Eh lafiya lau gata nan ma”.

Cewar Momy na mi?a wa Khausar wayar kar?a Khausar tayi suka gaisa cike da farin ciki Hajja Nana tace.

“?ar tsele da zaki kasheni azaune”.

Murmushi Khausar tayi cikin rashin jin karfin jikinta tace.

“Yaushe zaki zo?”.

Fuska ?auke da farin ciki Hajja Nana tace.

“Kwanan nan in sha Allah kafin ayi suna”.

Murmushi Khausar tayi tare da maida kallonta kan Moddibo da idanunsa ke kan Jaririn tace.

“Ayiwa Hajja Nana shiri in Sha Allahu tana kan hanya zata zo”.

Kai ya gya?a mata tare da cewa.

“In sha Allahu”.

Akuma dai-dai lokacin Dija da Yah Aliyu suka shigo Murmushi Khausar tayi tare da cewa.

“Dija”.

Cike da farin ciki Dija tace.

“Na'am Khausar ai mu bamu sani ba Khausar baku fa?a mana ba”.

Still da Murmushi afuskarta tace.

“Kiyi ha?uri Dija gaba ?aya abin ne yazo min atsorace”.

Dariya Yah Ali yayi tare da fa?in.

“Raguwa gaba ?aya kin gigice kin gigita bayin Allah”.

Langwa?ar da kai tayi kana tace.

“Hmmm ba dole inji tsoro ba Yah Ali abinda ance wasu da yawa idan an musu kafin afito dasu ta can suke wucewa”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“A'a ke kam in Sha Allahu kina nan sai kin kawo wasu ?annensa goma sha ?aya sun zama Dozen”.

Idanunta ta zaro tare da fa?in.

“Goma sha ?aya”.

Baki ?aya ?akin suka sanya dariya.

Raudat dake zaune gefen Asma'u ta ?yalkyale da dariya kana tace.

“Addah khausy idan kika haifi Dozen sai ki bani biyun saman na ri?a kulawa dasu kar suyi Miki yawa ai Yah Moddibo zaku bani ko?”.

Ta ?are maganar tana kallon Moddibo kai Moddibo ya gya?a yana Murmushi.

A ranan haka suka yini suna kula da ita.


Bayan sunyi kwana uku aka sallame ta suka koma gida.

 Haka Didi da Momy  suka cigaba da kula da ita suna bata kulawa na musamman...

Washe gari da safe Misalin ?arfe 7:30 Asma'u ta zo zaune ta samu Lalla Khadijah, Rahama, na zaune kan lallausan Darduma Yayin da Didi,Momy,Innayi ke zaune gefe ?aya Hajja Nana kuwa na gefen Khausar da Moddibo dake ri?e da Jaririn yana masa addu'a kana su kuma suna hira.

Ahankali Asma'u ta ?ago fuskarta ?auke da Murmushi ta mi?a wa Khausar wayarta tare da cewa.

“Kalli wani special abu dana ajiye Miki wanda nake da ya?inin sai kinyi min kyauta na musamman”.

?an ware idanu Khausar tayi tana kallon Rahama dake cewa.

“Aikuwa dai Addah Asmeey muma dake gefe muna sa ran samun khauta”.

Dariya Khausar ta sanya kana tace.

“Aikam dai zanso gani”.

Ta ?are maganar tana playing video

Da sauri ta zaro Idanunta waje ganinta kwance kan gado tana surutai.

Moddibo kuwa wani Amintaccen Murmushi ya saki ganin yanda ta zaro Idanunta waje sai kuma tayi saurin ?aga kanta cike da kunya jin yanda suka ?yal?yale da dariya cikin tura baki ta kalli Asma'u tare da cewa.

“Asma'u Ni ko?,Aikuwa kin ci bashi sai na rama”.

Ta ?are maganar cike da kunya ganin yanda suke maimaita maganar.

Asma'u kuwa Gwalo Asma'u tayi mata tare da cewa.

“Aikuwa sai dai ki rame yarinya dama can abinda ke Ranki kika fa?a”.

Khausar kuwa juyawa tayi jin Hajja Nana na cewa.

“Yoh ai gaskiya Asma'u ta fa?a ke da wannan mijin naki duk ba kunya ne daku idan ke baki cikin hayyacin ki kika fa?a ai shi yana sane bare ke?in ma kina sane”.

Rau-rau da idanu Khausar tayi ta shiga bubbuga ?afa daga zaune tace.

“Didi kiji fa abinda Hajja Nana ke fa?a wai bani da kunya”.

Murmushi Didi tayi tare da fa?in.

“Rabu da Hajja Nana am Khausar ?ina kina da kunya sosai ai bada sanin ki kikayi ba”.

Momy kam Murmushi kawai takeyi.

Daidai lokacin Jakadiya ta shigo tare da sanarwa Didi tayi ba?i ?an Barka.

Mi?ewa Didi tayi kana tace.

“Toh ganan zuwa”.

Sai kuma ta kalli Momy dake cewa.

“Mu tafi”.

Atare Didi Momy Innayi,Niyna suka fice.

Kallon Rahamah kalla Khadijah tayi kana tace.

“Rahama muje ki tayani ha?a Alawar Madara da gullisuwa tun jiya naso yi kuma ina zirga-zirga”.

Murmushi Rahama tayi tare da mi?ewa Lalla Khadijah kuwa har taje ?ofa ta juya ta kalli kana tace.

“?anwata kema zo muje”.

Kai Asma'u ta gya?a tare da mi?ewa suka fita.

Falon ya rage daga Khausar, Moddibo sai Hajja Nana da itama ta mi?e ta fita falon.

Cikin shagwa?a Khausar ta kalli Moddibo tare da narke fuska kana ta tura baki tace.

“Yah Mu'allim”.

Murmushi yayi kana ya kwantar da jaririn ya janyota jikinsa bakinsa ya kai saitin kunnenta yace 

“Na'am Minha Viddaaaa ya akayi?”.

Ya ?arashe yana jan sunan.

Cike da shagwa?a tace.

“Jifa yanda na saki baki naita fa?an magana gabansu Momy da Didi kuma baka hanani ba”.

Murmushi yayi yana shafa bayanta yace.

“Ya za'a yi in hanaki fallasa min sirrin dake Ranki?,Taya kike tunanin bakina zai iya dakatar da zinaren kalaman da suke fitowa daga bakinki suna ratsa kogon zuciyata?,Kin kuwa san farin ciki da shaukin dana kasance alokacin?”.

Ya fesar da sanyayyan numfashi mai cike da zallan so da shau?i yace.

“A lokacin ji nake tamkar ina yawo a gajimare ji nake tamkar nafi Mazan duniya Sa'a da samun Nagartacciyan mace irin ki kin nuna min so tun baki san menene so ba shin mai zanyi in biyaki”.

Cikin wani irin yanayi na musamman tace.

“Ka ?aunaceni ka kuma soni fiye da yanda nake son kaina kada ka ha?a ni da kowa atare da kai idan kayi min haka kaga yimin komai Yah Mu'allim”.

Ahankali ya ?ago kanta tare da ?aura lips ?in sa asaman nata yashiga kissing ?in ta...


 Alhamdulillah zuwa yanzu jikinta yayi ?wari bazama ace Thearter  aka mata ba kullum Asma'u da Dija anan suke yini ana I gobe suna Dr Zakariyya, Asiya Hajja Nana, Abban Jameel, Lalla Hafsat suka zo.


Hajja Nana da Innayi ce zaune da Khausar a?aki yayin da Innayi ta zuba mata abinci ta bata taci Momy kuma na ri?e da jiriri tayi masa wankan Yamma ta saka shi cikin wasu fararen kayan sanyu masu masifar taushi pink and white collar.

Anutse Moddibo ya shigo ya same su Kai tsaye bakin gadon ya wuce gefenta ya zauna.

Kallonsa hajja Nana tayi tare da cewa.

“Wai kai kam baka jin kunya ne?”.

Juyawa yayi ya kalleta kana yace.

“Kin iso da sa ido ko? Idon ki be iya gani bakinki yayi shiru ko?”.

Hararansa tayi tare da fa?in.

“Ba dole ba idan bani nake taka maka birki ba babu mai taka maka birki”.

Kallonta yayi tare da cewa.

“Toh sai kiyi mugani in birkin zai taku”.

Anutse Khausar ta kallesa kana ta kalli Hajja Nana tace.

“Yah Mu'allim rabu da ita”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Aima na rabu da ita?”.

Khausar kuwa nutsuwarta ta tattara kana tace.

“Yah Mu'allim gashi har gobe suna in Allah ya kaimu”.

Kai ya gya?a kana yace.

“Eh”.

Ahankali ta langwa?ar da kai tare da cewa.

“Kuma banji ka fa?a min sunan yaron ba”.

Murmushi yayi kana yace.

“Kuma tun a asibiti kafin ayi mishi wanka na masa hu?u ba tun kafin ki farfa?o”.

Murmushi tayi kana ahankali tace.

“Kuma Yah Mu'allim baka fa?a min ba".

Juyawa yayi ya kalli Asma'u kana ya kalli Asiya dake cewa.

“Ai dai kam bamu san sunan yaro ba gashi har gobe Suna”.

Didi kam ido ta zuba mishi tana kallonsa Momy kuwa sunkuyar da kanta ?asa tayi tana sawa Jaririn safan hannu tace.

“Toh menene sunan”.

Sunkuyar da kansa ?asa yayi kana ya motsa la??ansa tare da cewa.

“Sunan shi Jameel”.

Cikin tsananin jin da?i Asma'u ta kallesa tare da cewa.

“Allah sarki Yah Moddibo Ubangiji Allah ya saka da Alkhairi Allah yabar zumunci ayyah Yah Jameel ?ina Allah ya raya shi Allah ya mishi Albarka”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Ameen ya Allah Asma'u, Allah yasa ya biyo halin takwaransa”.

Ya ?are maganar yana Murmushi.

Innayi ce ta amshi zancen da cewa.

“Naji Ibraahim kuna na kiranshi da *Keyan*”.

Kai Modibbo ya jinjina tare da cewa.

“Eh la?anin kenan. Amman asalin sunan Jameel, Allah ya raya mana shi yayi nagarta irin ta mai sunanshi”.

Cikin tsananin jin da?i Asma'u tace.

“Ameen ya hayyu ya ?ayyum ”.

Khausar na Murmushi tace.

“Ameen ya Allah yasa ya biyo halin takwaransa Allah yasa yayi Ilimin takwaransa”.

Cikin jin da?i Didi tace.

“Ka kyauta Babana Allah Ubangiji ya raya mana Jameelu”.

“Ameen ya hayyu ya ?ayyum ”.

Cikin tuno da Jameel Hajja Nana tace.

“Ameen ya Allah ai Jameelu mutumin kirki ne”.

Asma'u kuwa cikin sauri ta ?auki waya tare da kiran Ummi Ummi na ?auka tace.

“Ummi albishir”.

Daga ?aya ?angaren Ummu tace.

“Goro”.

Cike da farin ciki Asma'u tace.

“Yah Jameel ya samu takwara”.

Murmushi Ummi tayi tare da fa?in.

“Hmmm Asma'u kenan kece baki sani ba amma ainin tun ranan Aliyu ya fa?a min”

Murmushi Asma'u tayi kana tace.

“Ummi shine baki fa?a min ba ranan muna hira ina cewa Ala'andi wani suna za'a sawa yaron kikayi shiru ashe duk kin sani”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Na sani mana tun ranan ya fa?a min”.

Murmushi Moddibo yayi tare da cewa.

“Ai TOH na rigaki yin albishir ?in”.

Dariya ta sanya tace.

“Wallahi Yah Moddibo Ina sauri in rigaka ashe ka rigani”.

Haka sukayi yinin ranan anata shirye-shiryen suna, nan washe gari suna akayi ra?in suna da hidindimu kamar yanda al'adan masarauta take. 


Bayan sallar la'asar manyan Fada ne a zaune saboda Aranar Abualeey yake son yin Murabus ya barwa Moddibo sarauta.

Bayan an zauna an cika a Fada anyi komai an taru Sarkin Al'adun Fada ne ya juya ya kalli Moddibo dake cikin wani irin shiga na alfarma da kawa da yayi masifar fitar da ainihin kyawunsa da ?warjinsa kana yace.

“Alhamdulillah kamar yanda al'adun Fada take sarki yana da dama da iko da zai yi Murabus tun yana da rayuwarsa ya dan?a Mulki a hannun ?an sa da yake ganin zai iya gadon mulkinsa kana zai iya kula da Masarauta yanda ya kamata dan haka Sarki Youseef Mohammed Aliyu Mouley ma yayi al?awari zai maida Sarauta ahannun ?an sa Aleeyu Youseef Mohammed Aliyu Mouley”.

Cikin jin da?i Manyan cikin Fada da Manyan Masarautu na gefe-gefe wanda baki ?aya sun san da Maganar an samu sa hannunsu  tun watanni hudu da suka wuce kowa cikin jin da?i da farin ciki yake fa?in Alhamdulillah.


Cike da girmamawa Sarkin Fada ya juya ya kalli Moddibo tare da cigaba da cewa.

“Kuma a wannan ranane za'a ?ara wa Sarki Aleeyu Youseef Mohammed Aliyu Mouley mata kamar yanda atsarin Masarauta sarki bai kasancewa da mace ?aya sai an masa biyu aranan da za'a dan?a mulki a hannunsa”.

Cikin sauri Moddibo ya ?aga kansa ya kallesu sai kuma ya saki wani Murmushi dashi ka?ai yasan ma'anar sa juyawa yayi ya kalli Abualeey dake cikin matsanancin farin ciki kana ya kalli Sarkin Fada tare da cewa.

“Ina son magana da mahaifina”.

Kai Sarkin Fada ya gya?a kana yace.

“Toh shikenan ba damuwa”.

Kana suka shiga ?akin Sirri Shida Abualeey, Waziri, Galadima Wambai Garkuwa...


A dai-dai lokacin kuma acikin gida Khausar ce cikin shiga ta alfarma sanye take cikin wani lafiyayyan Abaya Pinch colour mai masifar taushi da santsi da yasha duwatsu kana ta ?aura Alkyabba ta Masarauta fari ?all mai masifar taushi wanda al'ada ce ta Masarauta wanda ranan da za'a na?a mijinka a Masarauta zaka sa.

Shima Jaririn sanye yake cikin shiga na alfarma wasu picnh colour kayane tausasa kana aka daura masa ?aramin Alkyabba fari irin na jarirai.

Sai hotuna suke ta ?auka dasu Lalla, Khadijah Lalla, Hafsat Asiya, Asma'u, Dija, Rahama, Raudat Asma'u kuwa kai tsaye take turawa cikin group ?in su na class mate ?in su da suka gama makaranta.

Nan da nan cikin group ?in ya kace me da surutu kala-kala kowa na tofa albarkacin bakinsa wata ?awarsu wacce lokacin da suke makaranta bencinsu ke kusa da nasu Khausar mai suna Hawwa  Idris ne tace.

“Ikon Allah wai Khausar ce haka?? girma yazo rawan kai ya gudu?”.

Tayi typing da emotion na mamaki dariya Asma'u ta tura mata tare da cewa.

“Gashi kuwa kinga zahiri”

Cikin Mamaki tayi voice dan gani take typing ?in bai mata sauri kana tace.

“Masha Allah shiyasa akace arayuwa kada ka ta?a wulakanta mutum domin baka san baiwar da Allah ya mishi ba wai yau Khausar ce matar Sarkin Morocco kuma Malam Moddibo?”.

Hoton dariya Asma'u ta sake tura musu tare da fa?in.

“Aikam ikon Ubangiji yafi gaban haka?”.

Wata mai suna  Jidda ce tace.

“Aikuwa dai muma Allah yasamu Adamshin ku Asma'u ku kam kunji da?in rayuwarku”.

Murmushin Samira Sani ta turo tare da cewa.

“Uhmmm kuma ku godewa Allah a yadda kuke ?in”.

Da sauri Khadijah Sule tace.

“Sosai ma kam Samira am”.

Amin kuwa cikin sanyi da nadama tace.

“Alhamdulillah ai in Allah ya baka lfy ka gode masa”.

Haka dai suka cigaba da hira acikin group ?in kowa na fa?in albarkacin bakinsa.


_Daga can gefe  kuwa su ne Rafi'a,Tutus kitchen, Mom sayyeed&Noor Tatti Dija chiroma,  ne da suka halarci wajen sunan ne suke ta Video da hotuna suna turawa cikin Group ?in SAKAYYA Team Moddibo da Khausar kam baki ya?i ruhuwa duk farin ciki ya cika su ganin irin gift da Khausar ta bayar akawo musu._


_Daga can gefe kuma ?an karatun bati siddan na Allah ya isa kenan da basu biya ku?i ba suke wi?i-wi?i da ido duk hakki ya hanasu sakewa da samun nitsuwa..._


Asma'u dake cigaba da hotuna da wayar Khausar wayar ya ?auki suwwa ganin sunan Yah Mu'allim na yawo yasa da sauri ta nufi Khausar dake tsakiyar Didi da Momy suna hoto tayi saurin isa gareta kana ta tsugunna zata mi?a mata wayar kasancewar azaune suke haka yasa ta fito a hoton da yayi masifar kyau.

Asma'u kuwa cikin ra?a takai bakinta kunnenta tace.

“Gashi fa Yah Moddibo yana kiran ki”.

“Mu gani”.

Cewar Khausar tana kar?an wayar tare da kaiwa kunnenta tace.

“Assalamu Alaikum Yah Mu'allim”.

Cikin wani irin yanayin na musamman yace.

“Minha kizo ki sameni a?akina”.

Kai ta gya?a tare da cewa.

“Toh”.

Sai kuma ta mi?e tare da rungume jaririn kai tsaye ta nufi sashen bakinta ?auke da sallama ta shiga falon nan ta samu Dr Jameel, Dr Zakariyya, Ibraahim,Yah Ali, da Yah Abba da sauran yan uwansa.

Yah Abba na ganinta yayi Murmushi tare da cewa.

“Mai jego kin sha ?amashi”.

Murmushi tayi kana tace.

“Ai dai kam”.

Kallonta ta mayar kan Ibraahim tare da cewa.

“Ibraahim Yah Mu'allim fa?”.

Da hannu ya nuna mata bedroom ?in kana yace.

“Yana ciki”.

Ahankali ta nufi bedroom ?in kwance ta gansa akan gadon yana ganinta ya saki sanyayyar ajiyar zuciya tare da bu?e mata hannunsa.

Cike da begensa ta zauna kusa dashi mi?ewa yayi ya ha?a ta da jaririn ya rungumesu ahankali ya ri?a kissing ?in goshinta zuwa wuyanta da kuma sassan jikinta baki ta ?an tura tare da cewa.

“Yah Mu'allim ka matsaneni kuma ?anka ya matse min wajen Theater na”.

Cikin sauri ya saketa kana ya kar?esa ya kwantar dashi tare da jawota jikinsa ya rungumeta sai kuma ya saki sanyayyar numfashi kana ya ruggumeta tsam cike da kulawa da kuma ganin yanayinsa ta shafo sajensa tare da cewa.

“Yah Mu'allim lafiya meke faruwa?”.

Kanta ya tallofo kana ya kalleta ido cikin ido da mamaki take kallonsa ganin yanda idanunsa suka ka?a sukayi jawur dasu cike da kulawa tace.

“Yah Mu'allim lafiya?”.

Sunkuyar da kansa ?asa yayi kana ya ?ago ya kalleta tare da cewa.

“Minha na yiwa Abualeey laifi kuma har yayi fushi dani”.

Cikin sauri ta zare idanunta tare da fa?in.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Yah Mu'allim laifin me kayiwa Abualeey?”.

Araunane yace.

“Minha nayi mishi babban laifi na?in bin Umarninsa”.

Cikin tsoro da ka?uwa tace.

“Ya Ilahi Yah Mu'allim akan me baza kabi umarnin Abualeey ba?”.

Langwa?ar da kansa yayi kan wuyansa yace.

“Saboda kece ban bi Umarnin Abualeey ba!”.

Cikin sanyi da rauni tace.

“Ya Ilahi bana son jin wannan maganar sam maganar babu da?in ji Yah Mu'allim Kabi Umarnin mahaifinka shine abinda ya dace kuma shine *SAKAYYAR* da zamuyi masa”.

Cikin rauni da karyewar zuciya yace.

“Bazan iya ba”.

Cike da mamakin shin wani irin abu ne me nauyi da girma agaresa da yasa har ya yiwa mahaifinsa gardama tace.

“Haba Yah Mu'allim ya za'a yi kace baza kayi abinda mahaifinka keso ba shin wani irin abu ne?”.

Cikin sanyi ya kalleta kana ya lumshe Idanunsa tare da cewa.

“Saboda yau yake so a bani mulkin Masarautar Mouley ahannuna”.

Cikin sauri da jin da?i kana da Jimamin yanayin da yake ciki tace.

“Toh mene Yah Mu'allim mulkin ne baka son rikewa ko me meyesa zaka yi mishi gardama?Kuma ai nikam ma ina son mulkin nan meyesa baza ka kar?i Sarautar ba? Kawai ka kar?i mulkin shine abinda ya dace”.

Kai ya jujjuya tare da juya ?wayar idanunsa acikin nata kana ya ri?o hannunta acikin nasa tare da cewa.

“Ba kar?an mulkin bane matsala Minha”.

Cikin rashin fahimtar abinda ke damunsa tace.

“Toh ka kar?i mulkin mana kayi mishi biyayya akai”.

Hannunta ya dam?e kana yace.

“Ki bari kiji ko menene”.

Fuska ta tsuke tare da cewa.

“Nikam babu abinda zanji Yah Mu'allim kawai kayi mishi biyayya akan abinda yake so ka kar?i mulki Allah ya tayaka ri?o ya baka ikon Adalci kai masa biyayya ka samu lada”.

Cikin sanyi da rauni yace.

“Cewa yayi an bani mulki bisa shara?in za'a bani Auren wata mata ya zama ina da mata biyu!”.

Da wani irin sauri ta dafe ?ahon zuciyarta da yayi wani irin harbawa cikin rauni da fusgar magana tace.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.

Atake jikinta ya fara rawa kar-kar-kar tamkar wacce aka watsawa ruwa ?an?ara atsakiyar hunturun sanyi kana idanunta suka ka?a sukayi jawur tamkar garwashin wuta lokaci ?aya taji numfashinta na Up and down alamar yana shirin barin gangar jikinta jawota yayi ya ri?e ta da damuwa atare dashi yace.

“Kee ki tsaya mana ki nutsu me haka!?”.

Gaba ?aya ta rikice numfashinta sai fusga yake alamun tana gab da suma saboda tsabar masifar kishi, cikin fusgar numfashi da ficewar hayyaci ta dafe ?ahon zuciyarta tare da cewa.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Yah Mu'allim Aure kuma?,Wata matar za'a Aura maka?,ita?”.

Sai kuma ta tsaya da Maganar jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta alamar zata iya rasa numfashinta.

Moddibo kuwa cikin matsanancin mamaki tsoro gami da ru?u yake kallonta tabbas yasan tana da kishi amma bai ta?a tunanin kishinta yakai wannan matsayin ba.

Cikin sauri ya rungumeta tare da ri?o hannayenta kana yana jijjiga fuskarta yace.

“Khausar Khausar ki nutsu mana ki bu?e idanun ki dan Allah ki tsaya ki fahimci abinda zan fa?a miki”.

Da ?yar ta iya bu?e idanunta.

Cikin sauri da tsoro ya sake tallafe Fuskarta ganin yanda ta zazzaro idanunta sukayi wani irin ja.

Ahankali ya fara bubbuga kumatunta tare da cewa.

“Dan Allah Minha ki nutsu kiji abinda zan fa?a Miki”.

Cikin rauni murya da bugawar zuciya tace.

“Yah Mu'allim yanzu mata zasu ?ara maka innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.

Sai kuma ta kife kanta akirjinsa ta saki marayan kuka mai masifan cin rai da zafi kukan data sakene ya temaka wajen daidaiton numfashinta ya tsaya.


Ahankali ya tallafota jikinsa yace.

“Minha shine laifin da nace Miki na yiwa Abualeey saboda nace masa, in dai har sai an ?ara min mata za'a bani mulkin, ni na yafe bana bu?atar mulki abawa Ibraahim nayi al?wari zan rayu daga Ni sai ke sai kuma ?an mu da kuma wa'anda zamu haifa nan gaba”.

Khausar kam wani irin kuka mai tsuma zuciya da tsananin kishi take yi.

Moddibo kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya cigaba da cewa.

“in dai akan mulkine zan yi Miki kishiya abawa Ibraahim in yaso a Aura mishi Mata hu?u a rana ?aya, nayi alkawarin bazan yimiki kishiya a kan mulkiba Amman ban miki alkawarin cewa wai bazan Miki kishiyaba dan bansan ne Allah zai tsara a kanmuba a gaba”.

Da sauri ta tashi kana ta bu?e Idanunta cikin rauni da shesh-she?a tace.

“Mata fa kace zasu Aura maka”.

Cikin kwantar mata da hankali yace.

“Ba kiji mai nace Miki bane indai mulki ne na ha?ura dashi a bawa Ibrahim abarni Ni in rayu dake da ?ana da abinda zaki haifa agaba”.

Ahankali ta shiga sakin ajiyar zuciya Moddibo kuwa cike da tarin ?aunarta ya cigaba da fa?in.

“Na tabbar kun isheni farin ciki kun isheni jin da?in rayuwa kun isheni komai batare da mulkin nan ba Ni na yarda zan kasancewa Ibraahim mai bada shawara abawa Ibraahim mulki shine abinda yafi min kwanciyar hankali hakan ya miki kinji da?i akan haka”.

Cikin matsanancin jin da?i da farin ciki tace.

“Na yarda in dai har Abualeey ya yarda Bama son mulkin mun bar musu mun yafe musu mulkinsu Mukam Bama so”.

Akuma dai-dai lokacin Jaririn yasa kuka cikin sauri ta kallesa cikin shesh-she?an kuka tace.

“Abu J ba ka jiba yana kuka shima baya so a yiwa Mimeeinsa kishiya”.

Cikin sauri ya rungumota jikinsa kana ya ha?a da jaririn ya rungumesu tare da cewa.

“Mu bar musu mulkinsu Minha ba ruwanmu suje can su ?arata da mulkinsu, su ri?e abinsu abarmu haka mu cigaba da jin da?i da kwanciyar hankali yafi mana”.

Dai-dai lokacin Ibraahim yayi knowking kana ya sanar masa zuwan Momy da Didi.

Suna shiga Didi ta kallesa Babu walwala atare da ita tace.

“Yanzu Aleeyu ka kyauta kenan ?acin ran da kasa Mahaifinka”.

Cikin sauri ya mike kana ya tsugunna gaban Didi tare da cewa.

“Didi dan Allah kuyi ha?uri”.

Cikin sauri da rashin walwala Didi tace.

“Shi ya gama yanke hukunci amatsayin sa na Mahaifin ka Sarautace an riga da an baka ita sai kayi abinda kaga zaka iya akai”.

Da sauri cikin shesh-she?a Khausar tace.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Didi yanzu kuma harda Mata za'a ?ara mishi?,”.

Cikin tsuke fuska momy ta harareta tare da cewa.

“Dan Allah rufe mana baki, sokuwar banza sokuwar wofi, in ba'a Aure ke aka Auro ki baza ki taya mijinki yanda zai yiwa iyayensa biyayya ba, sai ki tsaya sokonci kina kuka kina cewa an ?ara masa mata matar kashe ki zata yi, ko kuma akan ki zata zauna?”.

Cikin rauni ta fashe da kuka kana ta jingina kanta da bakin gado cikin shesh-she?an tace.

“Momy ba zaki gane bane bazan iya rayuwa da wata mace tare da Yah Mu'allim ba”.

Ahankali Didi ta ?agota kana ta dafa kafa?arta tare da cewa.

“Kiyi ha?uri Sarauta ce an bashi Mata kuma tunda yace baiso da ?aya zai zauna shikenan tun da dama bawai shariya ?ace ta tsara haka, al'adace”.

Ajiyar zuciya mai sanyi ta shiga saki tana jin nutsuwa na diran mata shi dai Moddibo kan sa na ?asa Didi kuwa cikin kwantar mata da hankali ta cigaba da fa?in.

“Allah da kansa ya basu Umarni suyi Hu?u, Uku, Biyu idan kuma ba zasuyi adalci ba suyi ?aya tunda yace ba zai yi adalci ba laifi.

 Mahaifinsa ya yarda an bashi Sarauta batare da an?ara mashi mata ba”.

Cike da matsanancin farin ciki ta mike ta rungume Didi kana tace.

“Nagode Didi Ubangiji Allah ya miki Albarka”.

Cikin sauri ta saki Didi kana ta tsugunna ta fuski Al?ibla tare da yin Sujudur Shukur ta godewa Allah kallonta ta mayar kan Moddibo dake Murmushi ta mi?a masa hannu tare da cewa.

“Yah Mu'allim Alhamdulillah ”.

Martanin Murmushi ya mayar mata yana mai jin wani irin nutsuwa na ratsa sassan jikinsa ganinta cikin farin ciki ahankali yace 

“Alhamdulillah”

Murmushi Didi tayi tare da ri?e hannun momy kana ta kalli Moddibo tace.

“Idan ka gama murnan ka tashi ka tafi Fada ana dam?a maka sarauta”.

Kai ya gya?a tare da cewa.

“Toh”.

Momy kuwa kallon Khausar tayi kana tace.

“Wuce mu tafi ”

Ta ?are maganar suna fita.


Cikin sauri Khausar ta mi?e tare da fa?awa jikin Moddibo tayi masa wani Amintaccen runguma sai kuma ta tallafo kansa ta ha?e bakinsu ta shiga kissing ?in sa ahankali ta zare harshenta cikin nasa tare da ri?e hannunsa Fuskarta ?auke da ma?aukakin farin ciki tace.

“Ina ?aunarka Abu J My life is nothing without you”.

Murmushi yayi kana ya lakace mata hanci tare da cewa.

“Shikenan kuka ya ?are ko?”.

Dariya ta sanya tare da ?aukan Jaririn tabi bayansu Momy da tuni suka fice kana shi kuma ya fita ya samu su Ibraahim suka wuce Fada.


Aranan aka na?a masa Sarautar Mouley kana aka ?aura auren Rahama da saurayinta kana matar da za'a Aura masa aranan aka Aura wa Ibraahim ita Ibraahim kam. baki har kunne cikin jin da?i da farin ciki aka gama Shagali da daddare aka kaiwa Ibraahim matarsa.

Tun aranan Lalla Hafsat da wasu daga cikin ba?i suka tafi da Rahama kasan cewar ?anin mijin Lallai Hafsat ne mijinta yasa aka wuce Mexico da ita ba?in suna kuma duk an watse lfy...


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar na samun kulawa mai kyau.

 ranan da ta cika sati Uku Alhamdulillah Thearter yayi gwa?i sosai suka je asibiti aka sake dubawa a ranan sukaje asibiti Alhamdulillah aka duba akace babu matsala yayi kyau saboda jikinta yana da kyau yaro yayi ku?ul-ku?ul gwanin sha'awa Masha Allah.


A ranan da suka cika wata ?aya da yammaci Khausar bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin wani riga da skirt na less me kyau jikinta sai ?amshi yake ?an ta yayi ku?ul-ku?ul Masha Allah yayi ?ato gwanin ban sha'awa.

Zaune suke Khausar Innayi da Hajja Nana suke a bedroom.

Yayin da Momy da Raudat ke zaune Side ?in Didi tana ta shirye-shiryen tafiya nan da kwana biyar masu zuwa.


Ahankali Moddibo ya shigo bedroom ?in hannunsa ri?e da Jaririn dake tsala kuka kusa da Khausar ya zauna kana ya ?aura mata yaron akan cinyarta kai ya langwa?ar cikin wata amintacciyar murya me cike da kulawa tare da tsantsar soyayya yace..

“Minha yunwa fa yake ji”.

Ashagwa?e ta tura baki kana ta langwa?ar da kai tare da cewa.

“Yah Mu'allim ?azu fa yasha kuma sai yaita tsotseni”.

Akasalance yace.

“Ki ?ara mishi”.

Fuska ta narkar tare da fa?in.

“Toh tunda ya daina kuka a bari sai anjima”.

Ahankali ya girgiza kai kana yace.

“A'a ki bashi yanzu”.

Mi?ewa Innayi tayi tare da cewa.

“Khausar bari inje inyi Miki ?an wake naji kina cewa kina son ?an wanke tunda kika haihu baki ciba”.

Murmushi tayi kana tace.

“Yawwa Innayi na ayi min shi yaji yaji yayi da?i sosai sannan asa min da  ?wai da lemun tsami akai”.

“Toh".

Innayi ta amsa tare da ficewa.

Hajja Nana kuwa ido ta zubawa Moddibo lokacin daya zuge zip ?in rigar Khausar ta baya.

Cikin Mamaki tace.

“Ohhhh ikon Allah”. Ta fa?a asanda taga yayi ?asa da wuyan rigar  Nonon fito, kan yaron ya tallabe ya sawa yaron abakinsa.

Ta cigaba da cewa.

“Gwara ma ni in tattara mu koma in bar muku gidanku.  hankalin mu ya kwanta wai nan kai Sarki ne guda".

Juyawa yayi ya kalleta kana yace.

“Toh ce Miki akayi Sarauta anayinsa atsakanin Iyalai ne?

Ai sarauta iya kacinta Fada”.

Cikin ta?e baki Hajja Nana tace.

“Ohhh Allah ya kawo mu zamani ai kai ko A Fada idan zaka samu za kayi musu ta?ara”

Murmushi yayi yana shafa sajensa yace.

“Toh Matatace fa,Ko ba matata bace?

Sadaki fa na biya”.

Hararansa tayi tare da cewa.

“Ka biya ko aka biya maka?”.

Dariya maganar nata ya bashi amma sai ya murmusa yace.

“Eh koma dai menene Matatace ni wlh kin isheni da gorin biya min sadaki akayi dan haka ni yau zan biya nawa sadakin”.

Ya ?are maganar yana jan wayarshi tare da ?an danne-danne.

Dariya ta sanya tare da cewa.

“Ohhh baki baya mutuwa ai da kai da ita duk bakin ku ?aya ne”.

Khausar Murmushi take musu tana cigaba da bawa yaron Nono.

Sai kuma ta kalli wayarta jin sautin shigowar sa?o.

Hannunta na hagu tasa ta ?auki wayar tare da bu?e sa?on.

Cikin tsananin mamaki ta zaro ido ganin alert ?in 10 million da Modibbo ya tura nata da rubu a jiki.

*Minha ga sadaki na*.

Cikin ka?uwa tace.

“Yah Mu'allim 10 million fa ka turo min me sanyi dasu, million goma”.

Sai kuma ta ?are maganar da kallon Hajja Nana dake cewa.

“Da gaske”. Cikin tsananin jin da?i Khausar tace.

“Wallahi kuwa gasu kin gani”.

Ta ?are maganar tana mi?a mata wayar da kuma yaron sai kuma ta ruggumeshi tana saki kishi sassayan kiss tako ina a jikinsa.

Ganin yadda ta ru?ene yasa Hajja Nana yarda bawai dan ta fahimci rubutun alert ?in ba.

Haka tai ta murna tare da godiya, kukan da Keyan ya sakan ne yasa ta saki uban ta kar?i ?an kana taci gaba da bashi Nono.

Cikin dariya Hajja Nana tace.

“Daga yau ka huta da gori, kuma dole a bani million ?aya a ciki”.

Murmushin yayi tare da cewa.

“Kawo account inki in baki naki sadakin tunda jikarki na gudun kishi sai in ha?ata dake”.

Cikin dariya tace.

“Yoh ina ni ina aure ai na gama aure kam”.

Dariya sukayi baki ?aya.

Bayan ta gama bashi da kansa ya mayar da Nonon kana ta mike tare da fa?in.

“Kizo muje ki gyara min Siff ?ina ya hargitse”.

Kai ta gya?a kana tace.

“Toh”.

Tare da mi?ewa tabi bayansa da kallo Hajja Nana ta bisu sai kuma ta saki Murmushi tare da ?aukan Jaririn tana mishi wasa.

  

     Suna shiga tsakiyar bedroom ya jawota jikinsa ya rungumeta yana sha?an ?amshin Kwalaccan Sirri da Humran _Aunty Aysha Aliyu Garkuwa_ da tayi amfani dashi sosai ?amshinta ke zautar dashi yana masifar son ya ri?a sha?ar ?amshin jinta yana masifar gigita masa tunani cikin wata kasalalliyar murya me cike da shau?i da fitina yace.

“Minha yanzu dan Allah tsawon kwana nawa kika fara Sallah?”.

Cikin lumshe idanu da yanda lallausan tafin hannunsa ke yawo asassan jikinta ta fesar da sanyayyan numfashi tare da cewa.

“Yah Mu'allim nafi sati biyu da fara Sallah ”.

?an ware idanunsa yayi kana muryansa can ?asan ma?oshi yace.

“Kina tsoron kishiya kuma kina tsoron kyautatawa mijinki da ?auke bukatarsa”.

Ashagwa?e ta ?yafta ?wayar Idanunta cikin nasa tace.

“Yah Mu'allim nifaaaa”

Da sauri ya sake ?an?ameta yana sakin ajiyar zuciya yace.

“Minha kin san dai ina da bu?ata bazan  iya jiran abinda Likitocin nan suka fa?a ba”.

Cikin sanyi da ?an tsoro tace.

“Thearter na fa kada ya ?alle”.

Yana yawo da hannunsa a?ugunta yace.

“Bazai ?alle ba”.

Ya ida maganar yana zama bakin gado kana ya zaunar da ita kan cinyarsa tare da zuge zip ?in rigar ta yayi ?asa dashi kana shima ya cire nashi blanket ya jawo ya rufe su tare da ?aura bakinsa akan dogon hancinta yana tsotsa kana ya mayar kunnenta yana hura mata sanyayyar iskan bakinsa.

Sai kuma ya tsaya jin tana cewa.

“Yah Mu'allim ina tsoron Theater nafa”.

Muryansa can ?asan ma?oshi irin na wanda ke cikin tsananin bu?atuwa yace.

“Na sani zan biki ahankali”.

Bai jira jin Abinda zata ceba ya shiga sarrafa ta cike da bege da kuma shau?i yayin da ya shiga Binta hankali cikin shagwa?a da tsoro tace.

“Wayyo Yah Mu'allim wajen Theater na zafi fa ina tsoro kar ka ?alle min ?inki?”.

Cikin ficewar hayyaci yace.

“Minhaaaaa bazan ?alle Miki ba ki nutsu dan Allah”.

Ita kam cigaba da zuba masa shagwa?a da raki tayi tana cigaba dace masa wajen Theater ta sai da ya ?auki kusan awa ?aya akanta kafin ya janye jikinsa daga nata ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sa mata albarka sai kuma yayi Murmushi yace.

“Matsoraciya sai raki ?inki ?inki ?inki sai raki da tsoro".

Cikin sau?e ajiyar zuciya tace.

“Yah Mu'allim Allah tsoro nake ji kar ya ?alle”.

Yana shafa shafeffen cikinta yace.

“Ba abinda zai ?alla shi Minha”.

Mi?ewa sukayi suka shiga toilet sukayi wanka atare bayan sun fito suka fara jiyo muryan Raudat na cewa.

“Assalamu alaikum.

Addah khausy”.

Da sauri Khausar ta ?arasa jan Zip ?in rigar ta ta nufi ?ofa kallonta Moddibo yayi tare da cewa..

“Kamar Raudat ko?”.

Kai ta gyada kana tace.

“Eh Itace kuma kamar Naji kukan Keyan”. atare suka fita yana gyara wuyar rigarsa yayin da take na?e ?asan rigarta.

Suka fita falon idanunsa ya sau?a kan Raudat dake rungume da jaririn.

Ware idanu Moddibo yayi tare da fa?in.

“Ya Salam Aunty Raudhiy yanzu ke aka bawa Yaron nan?”.

Murmushi tayi tare da kallon fuskar Keyan tace.

“Yah Moddibo ai na iya ri?ewa bazan kada shiba”.

Murmushi yayi tare da fa?in.

“Aikam ba zaki kada shiba kawo shi nan”.

Karbansa yayi ya bawa Khausar ta zauna tana bashi Nono suka zauna gefenta suna ta hira...


Bayan kwana biyar Momy suka wuce Saudi ita da Hajjaj Nana dan Modibbo ya biya musu umra, bayan sun gama aikin umrarsu ne suka koma Nigeria bayan komawar su da sati ?aya akayi.

 Auren Amina da Baban Samira Sani cikin ikon Allah mai gadin gidansu Samira yace yana sonta fahimtar yanayin da take ciki kuma zuwa yanzu Alhamdulillah jikinta yayi sauki arana ?aya aka ?aura Auren Babanta ya bashi gida da jari kana ya nemi wani sabon mai gadi. 

Haka suka tare abinsu Samira da maigadinsu.

 ita kuma Amina tana rayuwarta da tsoho.


Hajiya Bunayya da Hajiya Lami kuwa na can Sycatry suna gallar rayuwarsu da girban abinda suka shuka.


Haka dai Rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar kam Alhamdulillah yaronta ya kai wata shida yayi ?ul-?ul dashi yana zama kana yana wangale baki yana dariya sosai.


A wannan lokaci kuma suka tafi aikin hajji, Ita da Modibbo da ?an Jaririnsu da Hadimar dake kula dashi da kuma innayinsu, Asma'u da Dr Jameel, Asiya da Dr Zakariyya, Dija da Yah Ali, Yah Abba da matar daya aura wata biyu ?aya wuce.

Sai Didi da Innayi da Abu Ali, da kuma Ibrahim da matarsa.


Watansu ?aya a can suka dawo, bayan sun dawo da mako biyu suka je Mexico.

Sosai Lalla Hafsat da Rahama sukayi da?in sosai.

Itama kanta Khausar Mexico tayi mata da?i sosai.

Makonsu uku suka dawo.


Taraba. Nigeria Gembilan 

Yau ya kasance labari cikin ?adda kama Uncle Naseer ya shigo cikin garin Gembila da niyyar kwashe Mahaifiyarsa da Mahaifinsa su koma Indi'a da zama.

Cikin dare ya shiga cikin unguwar su da sauri ya bu?e musu mota tare da cewa Mamansa da Babansa.

“Kuyi sauri kushi ga mu tafi”.

Kai Maman ta gya?a kana tace.

“Toh ai gwara ka kwashe mu mu tafi mu huta da jaraba da Sa idon mutanen gari da gulmace-gulmace”.

Ta ?arashe Maganar tana shiga motar.

Shikam Uncle Naseer cikin sauri ya shiga motar yaja su.

Suka fara tafiya suna gab da fita garin Gembilan motarsu tayi tambul ta ri?a juyawa tana bugawa da tsaunukan gefen titi kafin ta kama da wuta sukayi mugun ?onewa  sai ya Fuskarsu ce ta rage kana kuma b....




No comments